Cutarwa Hausa Novel

Cutarwa Part 1

This entry is part 1 of 2 in the series Cutarwa by ayshercool

CUTARWA!

P1

⚠️⚠️
Ƙirƙirarren labari ne, duk abun da aka gani a ciki, yayi kamanceceniya da wani abu, na zahiri ko makamancin haka, arashi ne

*Haƙƙin mallakata ne, ban yarda a juya mini shi ta kowacce irin siga ba, sai da izinina”

Gagarawa Jihar jigawa.

Kasancewar wata ya nausa, domin kuwa watan jumada ula, ya kai kwanaki ashirin da biyar, wanda yake dai-dai da watan Nuwambar shekarar miladiya.

Mislain ƙarfe biyu da rabi, dare ya tsala, duhu ya mamaye ko ina, baka jin sauti ko motsin komai, sai kukan ƙananan ƙwari, da sautin busassun ganyen bishiyu, da iska ke kaɗawa lokaci zuwa lokaci.

A dai-dai wannan lokacin da kusan galibi mutane ke kwasar bacci, ni kuma har a lokacin idon ta tamkar an soya, babu alamar bacci a tare da idanun nata, sakamakon bushewar zuciya da raɗaɗi da take ji.

Sai yau ta tabbatar da  cewa, nutsuwar zuciya, da kwanciyar hankali, da ƙarancin tunani, suke haɗuwa su haifar da daddaɗan bacci, mai cike da annashuwa.

A hankali ta tashi daga kan katifar da take kwance, na nufi tagar ɗakin, ta buɗeta, wani sanyi ya daki fuskarta, ta kalli ƙaton tsakar gidan, da baka iya gane komai a cikin sa, saboda duhu.
Ta ɗaga kanta,  ta kalli taurari, yadda suka yi wa sararin samaniya ado, ƙudura da iko na Ubangiji na riƙe da su a sama.
Tayi ajiyar zuciya, tare da kamanta rayuwarta da wannan baƙin daren, mai cike da duhu, da ban tsoro.

A lokacin da karin maganar bahaushe ya yi amsa amo, a tsakanin ƙabilar ta hausawa, na cewa dauɗar gora ciki ka sha ta, sai dai kash! Zamani ya zo mana da cigaba, ta hanyar nuna mana muhimmancin lafiyarmu.
Duk da cigaban da aka samu, hakan bai hana a tauye ta ba, a shayar da ita dauɗar gorar ta ƙarfin tsiya ba, wanda hakan yake CUTARWA! Domin kuwa ya zame mata tamkar guba, domin ya zama silar sanya mata ciwon da take ta fama da shi, ta rasa maganin sa, wanda tun yana ɓoye, sai da ya fito yayi tsiron da mutane suke yi mata tambari da shi.
Haka zalika, azancin hausawa na ciwon ƴa mace na ƴa mace ne, ya samu gindin zama a da yawa daga bakunan mata, sai dai ita a nata ganin, ciwon ƴa mace, na ta ne ita kaɗai. Wataƙila ko a cikin ta ta rayuwar ne Allah bai sa ta yi katari da waɗanda ciwon ƴa macen yake zama nasu ba.
Duk iya ƙoƙarin da ta yi wurin haɗiye yawun bakinta, ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi, wani irin zafi zuciyarta ke yi mata, wanda ya haddasa numfashina fita cikin huci.

A hankali ta furta “Me ya rage? Tun da duniya cike take da rikici, da tarin ƙalubale, kowa kansa kawai ya sani, kuma kuɗinka shi ne mutuncinka, tabbas! Tura ta kai bango, na ɗaura aniyar fito na fito da duk waɗanda suka cutar da ni. Tun da babu sani babu sabo, dole in fasa ƙwan da warinsa ka iya sanadiyyar tarwatsewar zumunci, idan ya so na gani, ko suma suna iya jure ɗaɗɗake dauɗar gorar a cikin su, kamar yadda suka yi mini, daga nan na ƙara gaba, na basu wuri tare da gwagwarmayar nemawa kaina mafitar rayuwa.


La’asar sakaliya, wata matashiyar mace ce da ba zata gaza shekaru sha takwas a duniya ba, zaune a ƙaton tsakar gida, tana ta ƙoƙarin tsince waken da zata daka, ta zuba a cikin miyar yauƙin da take yi, cinyarta wata yarinya ce ƴar kimanin shekaru uku da rabi a duniya a kwance, ta saka babban ɗan yatsanta a baki ta na sha, hannunta ɗaya kuma tana wasa da cibiyarta.
Idan ka kalli yarinyar sau ɗaya, sai ka sake kallonta, tare da son sanin daga wace ƙabilar wannan yarinyar take?.

Baƙa ce sosai, mai ƙiba, tana da ɗan goshi, sai dai yalwataccen gashin girarta ya rage fitowar goshin nata, tana da manyan idanuwa farare, sai dai ƙwayar idonta brown ce, maimakon baƙa, bakinta ɗan cukul, sai dai laɓɓanta jawur, tamkar an saka mata jambaki. Babban abun da zai baka mamaki, bai wuce yadda take da dogon gashi ba, baƙi wuluk, mai tsayin gaske, ba curkukuɗaɗɗe irin na baƙaƙen fata ba, tamkar gashin larabawa, kalba aka yi mata guda biyu, amma ta saukko har cikinta, hancinta ba shi da wani tsawon kirki, saboda kumatu ya shanye su.

“Wai Mariya ba zaki ajiye wannan gunsumemeiyar yarinyar ki mayar da hankali ki kammala aikin nan ba. Kawai kin ɗauki ƴa kin narka a cinya ƴa ba kaɗan ba ko nauyi ba kya ji? Na ga dai ba nono za ki bata ba”

Mariya a ranta ta ce ‘Ban da abun iya, ta yaya saniya za ta gaza da ƙahonta?’

A zahiri kuwa cewa ta yi “Yanzu zan kammala iya”

“To ki ajiyeta ta shiga cikin yara tayi wasa mana, wannan uwar matan ta zauna a cinya, kema ki haihu ki yi mata ƙani, kin naɗe kin ƙi haihuwa, kiyi ƙoƙari dai ki haifo wani, ko Allah ya sa a samu mai ɗan dama-dama, wannan ƴa muninta yayi yawa, Ko da yake can danginku ta kwaso wannan baƙin da muni, barebari ai haka ku ke baƙi kamar zunubin mutanen farko”

Mariya ta sunkuyar da kai tayi shiru, ta na jin zafin maganganun nan, amma ba yadda ta iya, haka ta ƙaƙalo murmushin dole, ta ce “Hajiya iya kenan, jikar nan taki mamaki zata baki, idan ta tashi kawo miki siriki, mai maiƙo za ta kawo, wanda zai kai ki makka”.

Iya ta furzar da goron bakinta ta ce “Da wannan baƙin da munin? Maza na rububin farar mace, wa zai kwashi kayan muni, ai ko wannan idon nata, ya isa hanata auruwa, ido abun tsoro kamar ragowar maita, sai ido furi-furi kamar bururrun gawayi”

Sake kwanciya yarinyar ta yi a jikin uwarta, tare da kawar da kanta gefe.

Mariya ta shafa kanta ta ce “Ummina, ki tashi in haɗa abinci, kar yayyenki su dawo ban gama girki ba, ki tashi ki je ki yi wasa da su Auwwalu”

Noƙe kafaɗa yarinyar tayi, tana tura ɗan mitsitsin bakinta, ta sake gyara zama ta mayar da hannunta baki.

Sallamar da aka yi ne, ya sanya su haɗa baki wurin amsawa.

Sai dai ba ƙaramar razana ta yi ba, da jin muryar mai sallamar, dan sai da tayi wani zillo ta tashi zaune, wani ɗan matashin saurayi ne, hannunsa riƙe da wata ƴar jaka.

Iya ta ce “Ahh, idris ka dawo?”

“Eh, an gama abinci ne?”

“Ina fa, tana nan tana laƙai-laƙai tana fama da wannan jibgegiyar yarinyar, ita ba nono za ta sha ba, sai iskanci da taɓara dan sangarta”.

Ya kalli yarinyar ya ce “Ummi, zo mu je na sai miki biscuits, ki bari anty ta gama mana girki”

Maƙale hannunta tayi, tana zazzaro ƴan idanunta, da tsoro ya bayyana ƙarara a cikin su.

“Ummina, dan Allah ki bi yaya idris, in kammala aikin nan”

Hawaye ya cika mata ido, tana kwantar da kanta a jikin mahaifiyarta.

Ya miƙa hannu zai ɗauke ta, ta fashe da kuka mai kama da na shagwaɓa, amma a zahiri na tsoro ne.

“Kai dalla ƙyale mata ƴar ta, dan ta samu za a ɗauke ta, ji iskancin da take, ita shagwaɓar ma ba kyau take yi mata ba, aba ba kyan gani kamar turotso”.

Ta ƙarfin tsiya ya saka hannu, ya ɗauketa, tana ta kuka, mariya kuwa cikin kara da kawaici, ta tashi tana cewa “rigimammiya sam ba kya girma”.

Ya fita da ita a kafaɗarsa, bai tsaya a ko ina ba, sai wani sashi na gidan, a ƙofar wani ɗaki da ba kowa a sashin, yanayin wurin zai nuna maka wurin ɗakin ƴan maza ne.

Ya buɗe ɗakin ya shiga da ita, yana zuwa ya dungurar da ita a tsakar ɗakin.

“Rufe mini baki, ko na shaƙe ki, ki mutu” cikin sheshsheƙa take ƙoƙarin danne kukan nata, gaba ɗaya ta burkice cikin matsanancin tashin hankali.

Ya bankaɗa gefen wata katifa, ya ɗaukko almakashi, ya durƙusa a gabanta ya ce “Kin gaya wa mamanki ko?” Ta girgiza masa kai, hawaye na zuba daga idonta, ga ƙoƙarin haɗiye kuka da take yi tamkar zata shiɗe.

“Kin faɗa ko baki faɗa ba?” Ta sake girgiza masa kai cikin razani.

“Duk ranar da ki ka faɗa, sai na gutsutstsura namanki da almakashin nan, na zuba a leda na kaiwa karen namadi, ya cinye ki, kuma sai na saka ki a murhun da babarki take girki, ai kin taɓa ƙonewa kin san zafin wuta”

Ba ta iya cewa komai, sai bin sa da ido, hawaye na zuba daga idonta.

Ya ajiye almakashin, ya janyo ta, ya fara ƙoƙarin cire ƴar doguwar rigar jikinta.

Sake fashewa ta yi da kuka, har da ɗan ƙara sauti, aikuwa ya zare mata ido, ya shaƙeta ya ɗaukko almakashin, ya saita tsinin a maƙoshinta, jikinta na rawa ta yi gum da bakinta.

Kamar yadda ya saba ɗaukkota yayi mata, haka yau ma idris yayi mata, sai da ya gama abun da Allah ya nufe shi da yi, sannan ya ƙyale ta, sai dai bai taɓa gangancin ƙetara ta ba.

Ya cigaba da yi mata kashedi, tare da firgita ta, a kan idan ta faɗa, sai ya sakata a murhu ya babbaketa.

Ya bar ta a nan zaune, ya kintsa, sannan ya zo ya ja hannunta, da ƙarfi sai da ta ji zafi, amma ba damar yin kuka, tana tsoron kar ya babbakata a wuta ko ya yankata da almakshi.

A wulaƙance, ya tafi da ita kanti, ya saya mata biscuit ɗin naira ashirin, da alewar naira biyar, ya sake fizgo hannunta ya nufo gidan da ita, sai tankaɗata yake yi yana masifar tayi sauri.

“Ba zaki yi sauri ba, sai wani jagwab-jagwab ki ke, kamar tsohuwar talo-talo” tafiyar sa da tata ba ɗaya ba, mussman ita da ke da jiki, haka ya ja ta sai daf da zasu shiga gidan, ya sake jaddada mata, kar ta gaya wa kowa abun da yayi mata. Ya saɓata a kafaɗarsa ya shiga da ita gidan.

“Anty mariya, ga rigimammiyar ƴar ki nan, uwar kuka, ta karɓe mini biskit, amma har muka dawo kuka take, saboda shegiyar ƙyuya”.

“Ohh, Ummi Allah ya shirya mini ke, an girma amma ke ba kya girma, kamar ba ƴan mata ba” gaba ɗaya ummi hankalinta baya jikinta, a tsorace take sosai da sosai, sai dai kasancewar ita kan ta mariyar yarinya ce, shekarunta sha takwas, a zaton ta kawai rigima ce, kasancewar ummi, yarinya mai azabar ƙyuya da miskilanci.

A nan tsakar gida ta yasar da biskit ɗin, ta je ta rirriƙe mahaifiyarta, ana daf da sallar magariba, mahaifin ummi ya dawo, ya ɗauke ta yana juyi da ita a tsakar gida, yana faɗin “Ummi, waye ya taɓa ni ƴa ɗaya tilo, na ga kamar kin sha kuka? Ko dai kin daketa ne?” Yayi maganar yana kallon mariya.

“A’a wallahi, ƙyuya ce kawai, ba zata yi wasa a cikin yara ba, ta maƙalƙaleni, dan idris ya ɗauke ta take kuka”.

“Ki daina ƙyuyar nan dan Allah, na zo miki da alewa daga kasuwa, da yalo ai kina ci ko?”.

But iya ta fito daga ɗakin ta, “Balarabe wannan ƴar ka sunkuta ka ke shillawa sama, sai ƙirjinka yayi ciwo tukuna ko?”

Yayi murmushi ya ce “Iya guda nawa ummin take”

“Ajiyeta dan Allah, duk a haka ku ke sangarta ta, tayi ta taɓara tana iskanci, ƴa sai ka ce teba” cikin jin nauyin mahaifiyar sa, ya ajiye ummi, yana murmushin yaƙe.

“Ina alewa da yalon da na ji ka ce ka zo da su? Bani nan a rabawa sauran yaran gidan, ai ba ita kaɗai ce ƴa ba, nan idirs yanzu ya fita da ita ya kaso mata uban kuɗi, amma kai sai ka zo da abu ka hana sauran yaran? Saboda ka haifi gwal?”

“A’a Inna, ina sayo da su suma, gani na yi ita ce ƙarama, kuma yau kasuwar sai godiyar Allah, tun da ba ranar kasuwa ba ce ba, ɗan kaɗan ne na zo da su ba yawa” yayi maganar yana nuna mata ƴar ledar hannunsa.

Ta ƙaraso ta fizge ledar “To tun da ba ciniki, sai ƴar taka ta haƙura, kai dai balarabe kamar a kan ka, aka yi wahayin talauci, kullum kasuwa ba cigaba, kana kallon yadda ƴan uwanka suke ƙoƙari kowa da abun arzikin sa, kai kuwa ba ka ajiye komai ba, sai son mace da wannan mummunar yarinyar, daɗi aure ba zaka zage ka nemi arziki ba” shiru yayi ya sunkuyar da kansa, dan ba shi da abun cewa.
Mariya kuwa ta mayar da hankali wurin kwashe tuwo, roba-roba.

Malam Hashimu dodo, shi ne mijin iya, gidansu babban gida ne, da aka yi ittifaƙin babu gidan da ya kai su yawa.
Da yayi aure ya ja nasa ɓangaren a cikin gidan su. Kasancewar gidan babba ne sosai, dan kusan duk garin babu mai girman gidan.
Kowa ya san su, saboda galibi ƴan gidan manoma ne, sai masu taɓa kasuwanci, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado.
A hankali wasu suka din ga samun rufin asiri, suna watsewa daga gidan, malam hashimu yana sake shigar da wasu sassan nasa sashin.
Daga baya ya auri iya, bayan matarsa ta ladan noma wato salamatu. Malam Hashimu mutum ne mai hidimtawa iyali, a lokacin boko ba ta yawaita ba, sai karatun allo, dan haka da shi da ƴan uwansa suna da ilimin soro.

Bayan wani lokaci, salamtu ta mutu, ta bar yaranta huɗu, biyu mata biyu maza, iya ta cigaba da riƙon su, da nata ƴaƴan.

Sai dai iya macece me shegen son abun duniya, tamkar ta yi ƙwace, ga ta da iya fuska biyu, a waje ta nuna ta Allah ce, amma na cikin gidan, su suka san gashin da suke sha.
Ba ƴaƴan da aka bar mata ba, har facalolinta, da suke cikin gidan iya na azabtar da su, gwargwadon abun hannunka, da abun da ka ke bata, gwargwadon mutuncinka a idonta.

Aka aurar da ƴaƴan salamatu mata, ɗayan kuma Yahaya, ya ce shi karatun boko yake so. Iya tayi ta sukar abun, amma malam Hashimu da suke kira da baba ya bashi goyon ba.

Ƙaninsa kuma Ilyas, yana zaune a nan ƙauye, amma yana taɓa kasuwanci, nan da nan ya fara tara kuɗi, yayi wuf yayi aurensa, shima ya tare a cikin gidan.

Yaran iya su biyar, biyu mata Shafa da zaliha, uku maza, Sagir, Saminu, sai Bashir wato balarabe. Duk wanda yake da kuɗi shi ne nata, hatta a jikokinta bambanci take nunawa muraran, sagir ne babba shine baban Idris da kuma Hashim suna ce masa magaji, saboda sunan malam ne da shi.
Akwai tarin ƴaƴa da jikoki a gidan, bayan rasuwar  iya ita ke tafiyar da gidan, saboda azabar faɗanta da iya masifa, hatta ƴan uwan malam tsoron ta suke ji, abun da ta dama shi ake sha.

Saboda balarabe ba shi da kuɗi, wato baban ummi, duk gidan shi ne samunsa ba mai yawa ba, dan dako yake yi a kasuwa da ƴan buge-buge dan haka samun nasa galibi sai damina idan yayi noma, hakan ya sanya duk wata ɗawainiyar gidan ta wahala, iya ta sa matarsa mariya ce ke yi, wadda asalinta ƴar Maiduguri ce babarbariya ce, sun zo garin biki suka haɗu, har Allah ya sa suka yi aure.

Tun da mariya tayi haihuwa ɗaya ta haifi, yarinyarta aka saka mata sunan mahaifiyarta, wanda yayi dai-dai da sunan uwar gidan malam, wato Salma ba ta sake haihuwa ba, tsawon shekaru uku kenan, iya ta ɗorawa yarinyar nan Ummi ƙahon zuƙa, da ba’a da cin mutunci, wai ta haifi wata halitta daban, da babu irinta a danginsu.

Ba ita ba har yaran gidan, da sauran mutanen gidan, na yawan kushe halittar ummi, tare da tsokanarta, gashi ayi ta tankata, saboda baƙinta, da kuma ƙibar ta, ga kuma kalar idonta, sai dai kuma mutane na mamakin irin gashin kanta, dam idan mariya na gyara mata kai, ruf gashi yake rufe mata fuska, tamkar na larabawa.

Allah ya albarkaci gidan malam Hashimu, da yawan yara maza a jikokinsa da ƴaƴansa, mata sam ba su da yawa, kuma da sun tasa ake aurar da su.

Dan haka kusan ummi, ita kaɗai ce yarinya mace ƙarama a cikinsu, sai dai hakan ya zame mata babbar barazana ga rayuwarta!!!

   CUTARWA!

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P2

Yawan kyara da hantara, haɗi da kushe halittar ummi, ya sanya ta zama yarinya mara karsashi ko a cikin sa’aninta. Dan wasu har iƙrari suke ko mayya ce, saboda launin ƙwayar idonta da ta sha banban da ta sauran mutane.

Wasu lokutan mariya duk sha’anin da za ayi na taron mutane, ta kan iya haƙura da zuwa saboda ummi, ba ta son mutane.

Abubuwan da wasu daga samarin gidan suke yi mata ne, ya sanya ta sake tsorata da lamarin mutane, ta fara ganin tamkar ita ta ta duniyar daban take, dan idris ne kawai yake amfani da ita wurin biyan buƙatar sa ba.
Mariya bata taɓa fuskanta ba, wasu lokutan har tsoron nuna wa ummi kulawa take yi, a gaban iya, saboda yanzu zata hau masifa da faɗa, wai tana nuna wa ƴar fari soyayya saboda ba ta da kunya. Ko yaya ummi ta ɗan sake a cikin yara, sai su fara cin zalinta, ko su din ga jan dogon gashin ta, ko jan kumatunta da suke tamkar doughnut ya ji yeast, ko yi mata dariya da ihun baƙar tukunya mai ƙyalli.

Takurar yara ya takureta a gida, a gidan ma iya sashinsu, shi ma fitowa tsakar gida idan ba tare da mamanta ba, ba ta fitowa saboda hantarar da kyarar da iya take yi mata.

Haka rayuwar gidansu ummi ta cigaba da garawa, iya kullum tana cikin haba-haba da ƴaƴa da jikokinta, masu kawo mata abun duniya.

Yayin da ta tattara cin kashinta, a kan balarabe da iyalin sa, tamkar ba ita ta haife shi ba.

Ummi ta ɗan ƙara tasawa, kusan kullum sai ta tambayi babanta, yaushe za a kaita makaranta.

Ganin ta ɗan tasa, kuma idan tana tare da mahaifinta, ko mahaifiyarta, ta kan yi hira da su. Sai dai da tayi yinƙurin gaya musu, abun da su Idris ke yi mata, sai ta kasa ta tsorata idan ta tuna suna cewa za su yankata.

Babanta yana bata lokacin sa, yayi wasanni da ita, har da ƴar tsere a tsakar gida. Da iya ta ganshi kuwa ranar ya shiga uku, da masifa da gori.

Kasancewar garin sun ɗan samu cigaba da wayewa, yanzu ana yin karatu sosai, akwai makarantu, ya sanya balarabe ya kai Ummi makarantar gwamnati, aka saka ta a ECC.

Ta din ga murna ganin an saka mata sabon uniform, fari da kore, ga jakarta baba na gode, an saya mata sababbin litattafai, sai washe fararen haƙoranta take yi cike da yarinta.

Tun sha ɗaya da rabi, mariya ta cewa iya zata je ɗaukar ummi a makaranta, iya ta ce “Mariya wai meyasa ba ki da ta ido ne? Ni zan ƙarasa girkin kenan, ki bari ta biyo yara, ko idan su Auwwalu sun dawo sa ɗaukkota. Ni kaita makarantar ma, Allah ya sa ba asarar kuɗi ba ne ba, kar aje yadda fuskarta take haka ƙwaƙwalwar take, ayi biyu babu”.

Wani abu mai ɗaci ummi ta haɗiye, ta cigaba da kaiwa tana komowa, ta faki idon iya, ta ɗau mayafi ta fice ɗaukko ummi, duk da babu tazara sosai, amma yarinya ce ƙarama, ba ta san hanya ba.

Sai dai da ta je ɗaukar ta, ba ta ganta tana wannan murnar kamar lokacin da za a kaita makarantar ba.

Tayi zaton kawai ta gaji ne, dan da yawa yara na ɗokin makaranta, sai an kai su kuma, su ga ba abun da suke so ba, su ce ba sa so daga baya.

Mariya tana cire mata uniform ta ce “Mamana, me aka koya miki a makarantar yau?”

Cike da yarinta ta ce “Lemo aka zana mana”

Tayi murmushi ta ce “sai kuma me?”.

“Bana son makaranta, ba zan sake zuwa ba?”

“Subhanallah, ummina meyasa?” Ta yi maganar cikin kulawa.

“Yala cu na ce mini baka” (Yara suna ce mini baƙa)

Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce “Kar ki kula su Yarinyar kirki, ki din ga mayar da hankali a kan abun da malama take koya muku”

“Ni bana son ana cewa baka”

“Za su daina Ummi, yarinta ce take damun su”

Ummi ta ce “To”

Hargowar iya ta jiyo a tsakar gida”Sai ka ce mayya, kamar a duniya babu wanda ya taɓa haihuwa sai ke, ai ba a banza ba wannan kalar idon na ƴar ki, na fara zargin akwai masu lashe-lashe a danginku, dan baƙar masifa, sai da ki ka tafi yawon ɗaukotta, shafaffiya da mai” Mariya ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Sa’adatu matar Sagir, da tayi sallama a sashin ta tarar da iya tana ta zuba tijara, ta ce “Iya ke da wa kuma a tsakar ranar nan?”

“Wacece idan ba mariya ba? Duniya kamar babu wani mai ɗa sai ita, in dai aka wannan mummunar yarinya ce, ba ta ji ba ta gani”.

“Iya kenan, mutum da ɗan sa ai sai Allah, sauran kunu na zo idan akwai in bawa yaro, ya fara yi mini kukan yunwa”

“Shiga ciki ki duba, ni fita zan yi” tayi maganar tana saɓa mayafinta a kafaɗa ta fice.

Sai da iya ta fita, sannan ta lallaɓa, ta fito yi wa ummi wanka.

“Maman ummi, ashe ummi kuma an shiga makaranta”

Mariya ta ce “Wallahi kuwa, ummi an shiga Ecc”

“Masha Allah, Ubangiji Allah ya yi jagora, ya sa an shiga a sa’a”

Mariya ta amsa da “Amin”

Ummi ta ɗan samu sassauci, daga laluben da samarin gidan suke yi mata, saboda shigarta makarantar boko, tun safe sai sha biyu na rana, daga nan kuma ta kwanta tayi ta bacci, wasu lokutan yaran gidan da ƴan sa’anninta, su zo su tafi da ita makarantar allo.
Duk da kuka wasu lokutan kuka take ba ta so, haka mariya ke tursasa mata ta tafi, saboda shi ilimi, dole a tsayawa yaro yayi shi, ko da kuwa ba ya so, mussaman ma na addini.

Duk da a hakan wasu lokutan ba ta tsira ba, ba ya hana azo har sashin su a ɗauke ta, idan mariya zata hana, iya tayi ta masifa.

*
Yau Mariya ta yi yamma wurin girki, tana ta aiki a tsakar gida, iya tana zaune a kan kujera ƴar tsuguno, ta kasa ta tsare, sai waƙe-waƙenta take yi na mutanen da, waƙoƙin daɓe wasu kamar na batsa,wasu kamar habaici.

Wata mata ce tayi sallama, suka amsa baki ɗaya, matar ta gaida iya, Iya ta amsa mata cikin sakin fuska har da yi wa ɗan matar wasa.

Mariya ta ce “Mai koko ke ce da yammacin nan? Bari na baki abun zama”

Mai koko ta ce “Wallahi kuwa, haja na kawo miki”

Mariya ta shimfiɗa mata tabarma ta ce “Haja kuma, to Allah ya sa ba ta fi ƙarfin talaka irin mu ba”.

Mai koko ta kwance kaya, kayan yari da sarƙa ne da mayafai a taƙaice dai kayan koli ne.

Mariya ta yi ta ɗaɗɗagawa, kayan sun yi mata kyau sosai, ta san idan ta ɗauka baban ummi ba zai ce komai ba, amma ba ta son takura shi, dan haka ta ce “Mai koko muna da ɗan kunne, maɗaurin gashi na so saya wa ummi, sai dai wannan sun yi ƙanana ba zai riƙe gashinta ba, sai dai idan muna buƙata zan yi miki magana da yardar Allah”

Ita ta ce “Ke ma dai mai koko, ke da ki ke neman arziki, ina ke ina kawo wa wannan kaya, ba su da komai sai tsiya da babu, ki kai sashin Sagir, ko gidan iliya, wannan ai da kin taɓa su babu”.

“Na ga alama kam, ban taɓa kawo kaya mariya ta saya ba, kullum sai aukin idan tana buƙata ta aiko ta saya”.

“Kema tun da aka yi ɗaya biyu, ai ba kya bari ayi uku ba, da dai hidimar ƴar ta ce, nan tafi kauri, ta kanainaye mini ɗa ta hana shi arziki”

Tuni mariya ta tashi, ta koma kan aikinta.

Mai koko ta ɗaure kayanta ta ce “Aikuwa iya ki dage da nema masa magani, ƴan uwansa duk suna da rufin asiri ban da shi, sa anjima”

“Yawwa ki gaida gida”

Ba ta sake bi ta kansu ba, kamar kullum yau da wuri ummi tayi bacci, bayan mariya ta kammala girki, ta ɗebi gawayi, ta goge wa ummi uniform ɗin ta, ta gama komai, tana jiran dawowar baban ummi.

Kamar mai kiran kurma, Iya ta ƙwala mata kira, ta fito da sauri a ɗan razane ta ce “Iya gani”

“Maza yafo mayafinki, ƴaron wurin iliyasu ne, ƙaramin ya haɗiye ƙaya, ku ɗauki yaron ki raka Sa’adatu ku je gidan sarkin suu, ya bashi magani”

Ɗan jimmm mariya tayi, so take ta huta, tun safe take aiki a gidan kamar jaka, yanzu kuma iya ta tsiro da wani abun.

Ba yadda ta iya, ta ce “To, bari na goya ummi, dan tayi bacci”

“Wai ke wace irin mace ce, har yaron ya mutu baki gama goyon wannan buhun sumuntin yarinyar ba, ban da rashin kara, ai ke yakamata ki goya mata yaron, dan Allah ki hanzarta ku tafi, ina nan me zai samu ummin, hanzarta maza”.

Haka nan mariya ta ji gabanta yana faɗuwa, kamar wani abu zai faru idan ta tafi, ga Iya sai ɗaga mata murya take a kan tayi sauri.

“Iya zan iya goya ummin, sai in ɗauki yaron a hannu”

“Wai mariya meyasa baki da kunya, ina faɗa kina faɗa? Salon ki je ki kayar da yaron, ga wannan uwar ƴar ta ki, kaya guda a haka zaki ɗauki, yaron ba zaki hanzar ta ba, ko dan ba ɗan ki bane ba, ko da yake ina mai ɗa ɗaya ya san ciwon ɗa ma”

Ta ce “To ko in kawo ta ɗakin ki, sai in kwantar da ita, idan na dawo na ɗauke ta?”

“A’a ba zaki kawo mini ita ta yi mini fitsari ba, wannan samgartacciyar yarinyar, ɗuwawunta ba shi da saiti. Uban meye ma zai kamata a ɗakin, ki wuce ku tafi”

Jiki a sanyaye mariya ta shiga ɗaki, ta ɗakko mayafinta, ta na ta kallon ummi, tana fatan Allah ya sa babanta ya shigo da wuri.

Ta fito tsakar gida wasu daga cikin jikokin iya suka shigo, shigowar su bai sanya iya yin shiru ba, ta cigaba da yi wa mariya masifa.

Duk mutanen da ke cikin gidan, iya ta rasa wanda zata saka yayi rakiyar kai yaron sai ita, saboda dai kar ta huta, kuma kar ta zauna lafiya.

Suna tafe a hanya tana goye da yaron, sai kakari yake yi, saboda yadda ƙayar take sukansa. Ga gidan sarkin su da nisa sosai, haka suke tafe da fitila.

Sai dai zuciyarta sai harbawa take yi da sauri, hankalinta yaƙi kwanciya, ji take tamkar ta juya da gudu, ta koma wurin ƴar ta.

Sai wajen tara da rabi suka dawo, gudu-gudu sauri-sauri ta nufi sashin su, ba ta bi ta kan iya ba, ta nufi ɗakinta.

Sai dai ta kai kai zata shiga ɗakin, shi kuma ya fito da sauri, jikinsa yana tsuma.

“Me ka ke yi mini a ɗaki yanzu? Me ka yi?” Shiru yayi yana tsuma tare da kallon ta, ta hasken farin wata.

“Me ka yi mini a ɗaki i yanzu? Me ya kai ka ɗakina?” Tayi maganar cikin ƙaraji.

Iya ta ce “Wai lafiya kuwa? Kun dawo kenan ya jikin yaron?” Hankaɗe shi ta yi daga gabanta, ta shiga ɗakin da sauri, tana kiran sunan “Ummi”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un. Iya! Iya! Zo ki ga? Iya zo da sauri”

Da sauri iya ta taho da gudu tana cewa “Wai meye ne?”

Ta shiga ɗakin, ta tarar da ummi a kwance, tana ta numfarfashi, jikinta sai rawa yake yi, an tura mata hularta a bakinta, ga wandonta a yashe a gefe gabanta duk jini.

Iya ta dafe ƙirji ta ce “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, wace irin masifa ce wannan, me yaron nan ya zama, kar dai ki ce mini yaron nan ne?”

Cikin kuka mariya ta cirewa Ummi abun bakinta ta rungume ta, cikin ɗaga murya ta ce “Haba iya, da idonki fa kin gani, kina gani fa, waye ya fita daga ɗakin nan idan ba shi ba, na shiga uku na lalace an cuce ni, an cuci ƴa ta”

“Dalla ki rufewa mutane baki, idan kuma kururwar zaki cigaba, ki tonawa kanki asiri shikenan, idan ba wata ƙaddara ta Allah ba, waye ma zai aure ta, balle a san me ya faru da ita” sororo mariya ta bi iya da kallo, wanda hakan yayi dai-dai da sallamar baban Ummi.

Iya ce ta iya amsawa, ya shigo ya same su, mariya rungume da ummi tana kuka.

“Maman ummi, Iya meyafaru ne? Ummin ce babu lafiya?”

Mariya ta ɗaga masa ƙafar ummi, tana kuka ta sanar masa da abun da ya faru.

Salati ya saka ya durƙushe a wurin.

Iya ta ce “Da ki ke ɗorarwa ke kin tabattar shi ɗin ne? Sai ki jirani in bincika in tabbatar ai”. Ta tashi ta fita daga ɗakin.

“Mariya, kina me? Garin yaya? Ya aka yi haka ta faru”

Cikin kuka mariya ta ce “Wallahi iya ce baban ummi, iya ce na shiga uku an lalata mini rayuwar ƴa ta, ina zan saka kai na”

Iya ce ta dawo riƙe da hannunsa, zuwa cikin ɗakin ta kalleshi ta ce “Uban wa ye ya yi wannan aikin? Me ka yi mata, ba sallama ka yi mini ka ce zaka tafi shagonku ba?”

Jiki a sanyaye ya ce “Wallahi iya tsautsayi ne”

A fusace balarabe ya tashi ya shaƙe shi, ya ce “Tsautsayin ka kasa sauke shi a ko ina, sai kan ƴa ta”.

“Zaka cika shi ko sai na ɗauke ka da mari? Ba ɗa yake a wurin ka ba kai ma? Idan ɗan ka ne ya aikata hakan, tona masa asiri zaka yi? Ko idan ka tayar da maganar wani abun hakan zai amfanar, aikin gama ya riga gama.
Kuma bari ka ji in gaya maka, wallahi tallahi, muddin ku ka ɗaga maganar nan, wani ya ji ta, bayan mu ɗin nan, Allah ya isa ban yafe ba, kowaye sai na tsine masa. Ita dauɗar gora ai ciki ka sha ta. Idan baku rufa musu asiri ba? Waye zai rufa musu ko salon zumunci ya lalace? Ƙuruciya ce da ƙaddara da bai wuce kan kowa ba”

Da wani irin mugun sauri zuciyar mariya ke yi, ƙuruciya ga yaron da har ya san, ya toshe mata baki da tsumma, ya keta mata haddi, shi ake kira da ƙuruciya.

Jiki a sanyaye balarabe ya ce “Shikenan iya, duk ba za ayi haka ba, in sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba, an bar maganar da yardar Allah”

Ta kalli saurayin yaron ta ce “Kai kuma wuce ka bani wuri, wallahi ka sake aikata makamancin haka, da kaina zan ci ubanka na hukuntaka. Wuce ka bar ɗakin nan”. Ya fice sumi-sumi ya ci bulus.

“Ke kuma ki daina wannan kukan, ki tashi ki dafa ruwa, ki sakata a ciki, kiyi haƙuri, ko ki cigaba da kuka baƙin ciki ya kashe ki” daga haka ta juya ta fice.

Tana fita mariya ta kuma rushewa da kuka ta ce “Yanzu shikenan baban ummi, yaron nan ya ci bulus kenan? An lalata mini rayuwar ƴa, har iya na cewa wai babu lallai wani ya aureta, wane irin abu ne wannan?”

Zuciyar sa fal takaici da ɓacin rai, saboda kar ya sake karya wa mariya gwiwa ya ce “Dan Allah kiyi haƙuri mariya, ki kwantar da hankalinki, kin ga iya uwata ce, ba yadda na iya, dan Allah ki yi haƙuri ki tayani yi mata biyayya, mu ɓoye sirrin nan, ko dan mutuncin ummi, kar abun yayi mata yawa. Dan Allah ki yi haƙuri mariya”

Tashi tayi ta kwantar da ummi, ta fita tsakar gida.

Babanta ya rungume ta, jikinta ya ɗau zafi, tana jin yadda hawayen sa ke ɗiga a hannunta.

“Ummina sannu kin ji? Meye yake miki ciwo?” Tayi shiru ba ta yi magana ba, sai sheshsheƙar kuka.

Mariya ta kawo ruwa a baho, ta fizge ummi daga hannun balarabe, ta saka ta a cikin ruwan ɗumin. Sai a lokacin ummi ta zabura ta fashe da kuka, ta ce “Mama zafi”.

Tana kuka ummi na kuka, ta yi mata wanka, ta saka mata kaya, ta nemi wuri ta kwanta, ta share balarabe.

Kwana suka yi ummi na koke-koke, ko barci ya ɗan ɗauke ta, sai ta zabura tana turza ƙafarta tana ihu.

Haka mariya ta kwana kuka, da balarabe ya kai hannu zai taɓa ummin, sai ta ɗauke ƴar ta, ta juya masa baya.

Wayewar garin Allah, mariya ta saba zuwa ta gaida Iya, amma a ranar taƙi kula kowa, ta ƙi ɗora girkin gidan.

Yara masu tafiya makaranta, duk sashin ta suke zuwa karɓar kunun safe, su sha su tafi makaranta, ranar shiru ba ta ɗora ba, kowa yazo sai ya koma.

Balarabe ya din ga raragefe, ya rasa me zai cewa mariya, ya san ƙarshen cuta an yi mata, ba ma ita kaɗai ba, har da shi, sai dai ba yadda ya iya sawun giwa ya take na raƙumi, iya mahaifiyarsa ce ba yadda ya iya, dole ya bi umarnin ta.

Yayi shirin sa zai fita kasuwa, jiki a sanyaye ya ce “Mariya, ko asibiti zamu kaita, na ga kamar da zazzaɓi ta kwana”.

“Dan Allah ka ƙyale ni da abun da ya dame ni, ka ƙyale ni bashir ka ƙyale mini ƴa ta, duk muninta daga jikina ta fito, ni na damu da ita, tun da a gurin kai da mahaifiyar ka, ba ƴa ba ce. Tun da baban sa yana da kuɗi dole ta ce dauɗar gora ciki ka sha ta, nayi imani da Allah da ɗan ka ne, yayi laifin nan, kowa sai ya ji” tayi maganar cikin matsanancin kuka.

Lallai mariya ta kai ƙarshe a ɗaukar zafi.

“Ki yi haƙuri mariya, ke kin san ina ƙaunar ƴa ta, ba yadda na iya ne, wallahi mariya ba ki fi ni shiga damuwa da tashin hankali ba, ki yi haƙuri dan Allah”

Ba ta kuma kula shi ba, ta cigaba da shafa kan ummi, da ta ɗan samu bacci, tana zubar da hawaye.

Da son ransa ne, ya wuni tare da su, ya cigaba da rarrashin ta, amma ya san idan ya ƙi fita, wani tashin hankalin zasu fuskanta daga Iya.

Gaba ɗaya girkin ma taƙi yi, ummi kawai ta samawa abun da za ta ci, da ta tuna a yadda ta tarar da ummi, sai ta sake fashewa da kuka.

Iya na son yin tijara, amma tana tsoron kar abun da ya faru ya tonu, dan sun haɗu da mariya a tsakar gida,ta hango tsantsar rashin mutunci da tashin hankali a idon mariya, wanda ba ta taɓa gani ba, dan haka ta ƙudurce a kan balarabe za ta juye.

Haka kuwa aka yi, ana idar da sallar magariba, ya dawo, ya je gaishe ta, ta dira masa bala’i, tamkar ba ita ta haife shi ba, tare da jaddada masa muddin ko shi ko matarsa suka bari zancen nan ya fito, sai ta tsine masa kuma babu ita babu shi.

Yayi ta bata haƙuri, sannan ya nufi ɗakin su, ya tarar da mariya tana goye da ummi kamar jaririya, tana jijjigata tayi bacci.

Sallamarsa kawai ta iya amsawa, daga haka ba ta sake kula shi ba.

“Ya jikin ummin?”

“Ba sauƙi” ta faɗa kai tsaye. Ta je ta kwantar da ummi a kan katifarta da ke ƙasa, ta koma falo kan kujerar da ke ɗakin ta zauna. Da yake ɗakin babba ne sosai, suka raba shi biyu da labule ya zama kamar ciki da falo.

“Ba sauƙi fa ki ka ce maman ummi?”

“Ina sauƙin yake bashir? An yi wa ƴa ta rauni na har abada, waye zai auri ummi ya riƙe ta da amana, alhalin an binne gaskiyar abun da ya same ta tun a lokacin da ya faru, ɗan gata ya ci bulus, koda yake dama an ce ba zata auru ba, saboda muninta, da wanne ummi za ta ji? Wallahi ɗaukar ƴa ta zan yi na bar gidan nan, garinmu zan koma, ko kare Allah ya bani ina so, balle ɗan adam” Ta ƙarasa tana sheshsheƙar kuka.

Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, ya riƙe hannunta, idon sa ya tara hawaye ya ce “Haba maman ummi, ya zan yi, iya uwata ce, dole na yi mata biyayya, idan ki ka tafi da ummi ku ka bar ni, in zauna da wa? Ina son ku wallahi dan Allah kar ki yi mini haka, ummi kuma ba abun da zai hanata auruwa in sha Allah, dan Allah kar ki tafi ki bar ni”

Kallonsa ta yi, har cikin zuciyarsa yake maganar, wani irin tausayin sa ya kamata, har ga Allah yana iya ƙoƙarin sa a kan su, mahaifiyar sa ce ta hana su zama cikin kwanciyar hankali.

Ta kwanta a jikinsa tana kuka, rarrashinta ya din ga yi, yana yi mata magiyar, ta taya shi ya yi wa iya biyayya, ya san ba zasu taɓe ba, kuma rayuwar ummi ba zata wulaƙanta ba.

Abun ka da mata da miji, haka ya lallaɓata ta janye batun yin yajin, har ya fara ƙoƙarin shiga wani abun daban.

Iya ce ta faɗo ɗakin tana faɗin “Wai balarabe ba ka ji ana kiran salla bane, ka shige ka ƙule a ɗaka da mace” a razane mariya ta yi gefe, tana kare jikinta.

“Eh iya yanzu zan tafi masallacin ma dama, dam..dama… Yanzu aka kira sallar”

Ayshercool.

CUTARWA!

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

3

Yanayin da suke ciki, bai sanya iya ja da baya ba, mussaman yadda suka rikice tamkar marasa gaskiya.

“Ina jin duk abun da ku ke faɗa ai, idan ta tafi ta barka ka yi yaya, tun da ta fini a wurinka, kar Allah ya sa ta zauna ɗin mana, ta ƙara gaba, wataƙila dama ita ce ƙashin tsiyar da ta tokare maka ƙofofin arziknka, har ni zan gindaya umarni, ka zo kana lallaɓata? Ki tafin mana waye ya riƙe ki? Ke idan ƴar mutunci ce ina uwarsa har sai ya nemi shawarar ki sannan zai bi umarnina?. To ke idan ban isa da ke ba, na isa da ɗa na, dan haka ki san abun da yake yi miki ciwo, idan ƙabilar ku kun saba asiri ku mallake mazaje, to ni na yi wa kaina da ƴaƴana dafa’i, asirinku bai isa ya kama ni ba”

Ba yau iya ta saba yi musu laɓe ba, dan haka yanzun ma mariya ba ta yi mamaki ba, dan idan da sabo ta saba.

Iya ta sake jaddada musu duk wanda ya fasa abun da ta ce a rufe, bata yafe ba.

Baban ummi ne ya yi ta bata haƙuri, mariya kuwa ta haɗe rai, wani abu mai ɗacin gaske na kaiwa da komowa a ƙirjinta, ji take kamar ta tashi ta ɗurawa Iya ashar, wanna ai shi ake kira da ga mari ga tsinka jaka, gaba ɗaya tsohuwar nan ba ta da imani, ba ta da mutunci, abu ɗaya take girmamawa a rayuwarta shi ne kuɗi.

Bayan sun samu ta fita, ya leƙa ya tabbatar ta tafi, sannan ya dawo ya cigaba da rarrashin mariya, ganin ya shiga tsaka mai wuya, ya sanya mariya ce masa “Ka kwantar da hankalinka baban ummi, ba wanda zai ji maganar nan, ina fatan Allah ya yi wa ummi sakayya, ba wanda zan bari ya sani”

Ya ce “Yauwwa, Allah ya yi miki albarka, in sha Allah zan san abun yi, zan yi ƙoƙarin neman fili a garin nan, na gina mana ko ɗaki ɗaya ne da makewayi, mu koma can, ko kema kya samu sassauci.

Kallonsa kawai take yi, cike da tausayawa dan kuwa ta san tun da iya ta gama raina masa wayo ba shi da abun duniya, ba zata taɓa barin sa ya bar gidan ba, ko dan kar ta huta.

A zahiri kuma ta ce “To Allah ya yassare” ya amsa da amin sannan ya tashi ya fita.

*
Jujjuyar lokaci ya sanya abubuwa cigaba da gudana, wasu da daɗi wasu marasa daɗi, sai dai lokaci ya wuce ba tare da ɗaci da raɗaɗin abun da ya faru da ummi ya bar zukatan iyayenta ba.

Kuma babu kunya, wanda yayi laifin ya cigaba da sabgoginsa hankali a kwance.

Mariya ta ƙara tsananta kula da jan ummi a jiki, babanta ya kaita makaranta, ita kuma ta je ta ɗaukkota, ta daina barin kowa ya raɓi ummi.

Mariya na zaune na ƙoƙarin koyawa ummi assignment a tsakar gida, kasancewar tana aji na uku a sakandare aka yi mata aure, ta iya karatu da rubutu. Iya na zaune suna hira da babarsu magaji da idris.

Ummi taƙi mayar da hankali a kan karatun da mariya take koya mata, sai soshe-soshe take yi, tana ɓata fuska.

“Mamana, wai ba zaki mayar da hankali ba, so ki ke anty ta zane ki?”

“Mama ni bana son makarantar” tayi maganar hawaye na taruwa a idonta.

Cikin damuwa haɗi da kulawa ta ce “Saboda me ummina”

Cike da ƙuriciya ummi ta ce “Tsokanata ake yi, mama dan Allah ki mayar da ni fara, kuma ki rage mini ƙibata”

Mariya ta ɗan yi shiru sannan ta ce “Ummina, ke fa kyakywar yarinya ce, ai kin san sahabban manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, da nake yi miki tarihi ko?” Ummi ta jinjina kai ta ce “Eh, Ina son tarihi”

“Yauwwa ummina, mai kiran salla a zamanin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, sayyiduna Bilal radiyallahu an hu, baƙi ne, kuma Annabi bai taɓa ƙyamarsa ba, haka sahabbai ma”

Ummi ta yi shiru ta ce “To mama kin ce in din ga son annabi, to masu tsokanata ba sa son annabi ko?”

Shiru mariya ta yi, tana tunanin wane bayani za ta yi wa ummi, dan duk da rashin sakewarta da mutane, idan tana tare da mamanta, akwai surutu.

Iya ta ce “Kin ga kar ki sakawa yarinya wani tunani daban, ki gaya mata gaskiya kawai, mummuna ce ko ki so ko ki ƙi”

Babar su magaji ta kwashe da dariya ta ce “Iya wannan jika taki, ai tun yanzu yakamata a fara nema mata maganin farin jini, dan za ayi gwagwarmaya kan a samu mai so, dan ina jin Alhassan ranar yana cewa; da zai samu igiya da ya zargawa ummi, ya tafi tashe da ita a matsayin ɗan biri” tayi maganar tana ɓaɓɓaka dariya ita da iya, ba tare da tunanin, ya mariya zata ji a zuciyarta ba ko ita yarinyar, ummi tayi ƙuri tana kallonsu, duk da yarinya ce, ta san cin mutunci.

Mariya ta ce “Biri kuma, ummin za a yi wasan biri da ita, kuma ki ke dariya, shikenan bakomai” tayi maganar cikin ƙunar rai, ta kama hannun ummi suka tafi ɗaki.

“Mama, da gaske ni biri ce? M, for monkey na bayan littafina?”

Mariya ta goge hawaye, ta ce “Ummina ke mutum ce, mai kyau sosai da sosai, kar ki sake haɗa kanki da biri kin ji ko? Kina da kyau sosai, kalli gashinki fa, duk garin nan kin ga mai irin gashinki?”

Ummi ta girgiza kai alamar a’a.

“Yauwwa ummi, idonki ma mai kyau ne, ina son idonki, duk garin nan babu mai irin idonki”.

Ummi ta taɓa idonta ta ce “Sai akuya ko?”

“Akuya kuma?”

“Eh, malamarmu ce ta faɗa, ta ce ni da akuya irin idonmu ɗaya, eyes sunan ido da turanci in ji anty”

Mariya ta yi shiru tana kallon ummi, yarinyar na cikin taskun ƙalubale, daban-daban, har a kai ga malamarta na kamanta ta da akuya.

Iya kuwa ta cigaba da hurawa balarabe wuta, da shi da mariya, cin kashin yau daban na gobe daban, har ƴan uwansa ma, ware shi suke a wasu abubuwan saboda ba shi da kuɗi, haka zalika mariya ta cigaba da yi wa iyalan gidan bauta, idan anjima su yi mata rashin mutunci, ko a ci zarafin ƴar ta a gabanta ba.

Kusan kullum sai ummi ta ce ba ta son makaranta, dan kuwa abun da mariya ta fuskanta, ba iya ɗaliban ne ke tsokanarta ba har da malamansu a ciki.

Dan idan ummi ta zo da aikin gida, tayi a gida, sai ta ce ba zata nuna wa malamarsu ba, idan ta tambayeta dalili sai ta ce “Malamarmu cewa take yi in fito gaban Allo, a tafawa ƴar baƙa saran daddawa, ayi mini dariya, ni kuma in yi ta kuka sosai, bana son ana tsokanata”

Ba ƙaramin ɓaci ran mariya yayi ba, Dan haka da kanta ta je makarantar, ta roƙi headmaster, a kan ya taimaka ya tsawatar a kan abun da ake yi wa yarinyar, kar son karatun ya fita daga kanta gaba ɗaya.

Yayi mata alƙawarin yin hakan, sai dai ba ta canza zani ba.

Ummi na ta kaiwa tana komowa a tsakiyar ɗakinsu da safe, kasancewar yau ba makaranta, sai fama take da uban gashinta, taƙi tsayawa a gyara, mariya sai fama take da ita ta nemi wuri ta zauna.

Ta kalli babanta da yake cin abinci ta ce “Baba kafi mama loma” tayi maganar tana dariya.

“Eh mana, baki ga na fita girma ba?”

Ummi tayi dariya ta ce “To ni kuma gaba ɗaya ƴan gidan nan, na fi su loma”

Mariya ta ce “Ke ɗin, sai ka ce abinci ki ke ci”

“Mama nafi duk ƴan yara girma fa”

Babanta ya ce “Kin fi su lafiya ne, kuma kin fi su kyau shalelena”

Ta kama kumatunta ta ce “Iya ta ce bani da kyau ai”

“A’a ke kyakywa ce sosai” miƙewa ummi ta yi ta fita daga ɗakin, tana leƙa baƙon ɗan magen da yake wasa a tsakar gida.

Mariya ta yi ajiyar zuciya ta ce “Baban ummi, kana ganin ummi zata iya samun miji tayi aure?”

Ya kalle ta ya ce “Meyasa zaki faɗi haka? Kina mahaifiyar ta, kema kin fara biyewa surutun mutane na cewar ƴarmu ba ta da kyau mummuna ce?”

“Ba haka bane ba, abun yana taɓa ni sosai da sosai, har malaman su ummi su da zasu tsawatar wai har da su a cikin tsokanarta, babar su magaji wai har da cewa Alhassan ya na kiran ummi da biri, kuma ta faɗa suna dariya”

Jiki a sanyaye ya ce “Biri kuma? Cin mutuncin ya kai haka? Wallahi mariya ummi ba mummuna ba ce ba, tana dai da duhu ne, kuma ƙwayar idonta ce da ba irin tamu ba, amma ba mummuna ba ce ba”

Mariya ta numfasa ta ce “Ni ba wannan ba, duk wanda ya ci zarafin ummi, na san bani na halicceta ba, amma abun da yake damuna, a zamanin nan yarinya ta kai mutuncinta ɗakin aure, ya ta ƙare ina ga idan ummi ta samu miji, gaya masa zamu yi ga abun da ya same ta? Idan muna gaya masa waye shaida babu tabbacin a lokacin dukkaninmu da muka sani muna raye. Idan kuma muka rufa, zai yi mata kallon mutuniyar banza, ummi ta san abun da ya faru da ita mummunan abu ne.
Ina tausayawa yarinyar nan abubuwan da suka baibaye rayuwarta, ina tausayawa ƙalubalen da zata fuskanta wataƙila bana nan a lokacin balle na tayata kwasar raɗaɗin, amma ina tausayawa ummi, idan ba ta samu miji mai tawakalli ba, za ta fuskanci wulaƙanci, wa zai so mini ummi tsakani da Allah, ya karɓi ƙaddarar da ta same ta? Wallahi baban ummi ba zan yafe wa yaron nan ba, ya cuce ni ya cutar da rayuwar ummi, ko idan ta ƙara girma zata manta oho, haryanzu bata yadda na bar ta a ɗaki ita ɗaya, an cuce ni” tayi maganar kuka mai ƙarfi yana ƙwace mata.

Balarabe yayi ajiyar zuciya, yana jin ɗaci a zuciyarsa ya ce “Wallahi mariya ni kaina abun nan yana ci mini zuciya, ba yadda na iya, mahaifiyata ta riga ta yi mini kandagarki, ƙetare maganar ta na iya shafar mu baki ɗaya, amma in sha Allah, ina sanya ran Allah ba zai wulaƙanta ummi ba, dan Allah kiyi haƙuri mariya, wallahi idan kina kukan nan, sai na ji kamar na bijirewa umarnin iya, na ɗau matakin abun da aka yi wa ummi”.

Ta share hawayen ta, ta ce “Kar ka yi haka, aikin gama ya riga ya gama, ko ka ɗau mataki, wannan wani miki ne a zukatanmu da ba zai taɓa warkewa ba”.

Yayi shiru ya zubawa mariya ido, shi kansa ya san mariya ba ƙaramin haƙuri take yi ba, zama da shi. Tsakaninta da shi babu wata matsala, amma azabar wahalar da take a gidan, duk ta rame ta yi duhu, soyayar kirki ba sa samun sakewa su nunawa juna, saboda azabar iya.

Ihun Ummi suka ji, hakan ya sanya su yin rige-rigen fita tsakar gida da gudu.

Ummi suka tarar da Alhassan ɗan wurin saminu, ya tattara gashin ummi, ya murɗe shi a hannunsa, jijiyoyin kanta sun mimmiƙe, duk ta gigice.

A guje mariya ta ƙarasa, ta hankaɗe shi, ta ƙwace ummi da ke kuka.

“Alhassan me ummi tayi maka ka murɗe mata gashi haka?”

Cikin fitsara yaron ya ce “Ɗan magenmu take mana wasa da shi”

A fusace mariya ta ce “Kuma saboda zalunci ka rasa me zaka yi mata, sai izaya da gashinta?”

“To waye ya ce ta taɓa mana magenmu, ana ta nemansa?”

Cikin zafin rai, mariya ta ɗauke Alhassan da mari.

Sai da balarabe ya waro ido.

“Tura ta fara kaiwa bango, wane irin zalunci ne haka? Ummi fa ƴa ce ba baiwa ba, wallahi duk wanda ya kuma dokar mini ƴa sai na ci ubansa. Dama a ciki nake da kai, na samu labarin kana ce mata matashiyar buranya, uwarka ce mai kama da buranya ba ita ba”

“Wayyo Allahana iya, a taimake ni ta kashe mini ido” Alhassan ya wage baki yana kwarmato”

Bakomai ya hana balarabe taɓuka komai ba, face sanin idan iya ta fito ba ƙaramar tijara zata yi ba, kuma ƙarshe su zata ɗorawa laifin”.

Buje a hannu iya ta fito daga banɗaki tana faɗin “Menene haka? Kashe yaron zaki yi me yayi miki?”

Alhassan ya kwashe ƙarya da gaskiya ya gaya mata.

Ta kuwa hau sababi “Balarabe kana tsaye take neman yin kisan kai, shikenan an taɓa ƴar gwal sai tayi yinƙurin cire masa ido. Duk ɗawainiyar da ubansa yake yi a gidan nan? Wace irin ɗawainiya ce ba yayi da ku, wasu lokutan ba har ciyar da kai yake ba da iyalin naka, da baka ganin kowa da mutunci sai su, saboda zuciyarka ta riga ta mutu, baka da amfani ka kashe zuciyarka ka auri mai ƙashin tsiya, baka da komai sai sokonci da son mace, wadda maganarta ta fi tawa, tun da tana baka abun da bana baka, to kayi ƙoƙari ta kashe masa ɗa, wallahi duk matakin da ya ɗauka a kanku, babu ruwana ko da kuwa wurin hukuma zai kai ku”

Cikin takaici mariya ta ce “Wato iya saboda baban Alhassan yana da kuɗi shi ne ɗa, da idan aka ɗaukar masa mataki ba zaki hana ba, ummi ce da aka ketawa haddi ba ƴa ba? Iya Allah fa” cikin hanzari balarabe ya girgiza mata kai. Cikin ɗacin zuciya ta koma ɗakinta.

“Ai da ka bar ta ta cigaba da gaya mini magana, ta tabbatar mini da bata da tarbiyya, kai ban da ina tsoron Allah da wallahi tuni na saka ka saketa, ko Allah ya sa ƙofar arzkin ka ta buɗe, idan ya so ka auro falla-fallan mata, mu samu ta haifa mana masu kyau, kadara irin arziki”

Bai cewa iya komai ba, ya shiga ɗaki, ya tarar mariya ta rungume ummi, tana aikin kuka. Zai yi magana ta ɗaga masa hannu, ta yi masa alamar ya rabu da ita, haka ya ƙyaleta ya fice.

Har ya tafi kasuwa tunani yake yi? Ko haya zai nema ya tashi ya bar gidan, ya san ba iya ce kaɗai ke da hakki a kan sa ba, iyalansa ma na da hakki a kan sa, kuma suna buƙatar walwala, amma iya ta takura su da yawa, kuma ya san ba zai iya biyan haya ba, kuma duniya zata zage shi, ya kasa zama da matarsa ya fifita iyalansa a kanta, haka yayi ta tunani, ba tare da samun mafita ba.

Mariya ma wuni tayi tunani da zancen zuci, ita kanta ta san bata isa ta tafi gida ba, ta ce tayi yaji saboda takurar uwar miji ba, ba babanta ba yayyenta maza kawai sun ishe ta, babu mai goya mata baya, dan ko hirar take musu, idan ta je ganin gida, sai ace uwa ce a wurinta idan da kara da tarbiyya.
Gidansu irin iyayen nan ne masu kashe ƴaƴansu su raya na wani a gidan aure, saboda dattaku dan gidansu gidan malamai ne.
Kuma ko kusa ba zata iya gaya musu cewar an yi wa ummi fyaɗe ba, saboda ita kanta da take ta hayagagar rashin bi wa ummi hakkinta, tana yi ne saboda abun yana damunta, mussaman nuna wa da ake yi ƴar kamar ba ta da amfani, saboda babanta ba shi da kuɗi.

“In sha Allah ummi sai ahalin nan sun kwanta a kafaɗarki, Allah ya nesanta ki da talauci, ya baki ikon cin jarrabawar nan da ni da ke baki ɗaya. Allah shi ya san dalilin da ya sanya yayi ki a haka, kuma ya jarrabeki Allah ya baki mai kula da ke, ko bana raye” haka ta wuni cikin kuka da damuwa.

*”
Rayuwa ta cigaba da tafiya, umma ta cika shekaru shida a duniya, sai dai bata sauya zani ba, domin kuwa gorin yau daban na gobe daban, haka iya ke yi, a kan cewa balarabe ba ya iya tsinana komai, a gidan komai shi ne koma baya.

Haka zalika balarabe, ya fara tunanin miƙewa ya nemi kuɗi, ko dan samawa iyalin sa farinciki da kwanciyar hankali, mussaman ƴar ƙaramar yarinyar nan, da aka mayar da ita tamkar wata halitta daban.

Yau suna kwance da daddare tare da mariya ya ce “Maman Ummi kin san wani abu?”

Ta ce “A’a”

“Ina ga ƴan kuɗaɗena da nake tarawa, zan je birni in ga abun da zan iya yi, ko Allah ya sa na samo arziki”

Mariya ta kalle shi ta ce “Baban ummi baka yadda da yadda Allah ya ajiye mu ba? Na san babu daɗi abun da iya take yi maka, amma dai ka yi haƙuri da barin garin nan, ka tafi yawon neman kuɗi, raba bawa da arziki sai mutuwa, dan Allah kayi haƙuri”

Ya gyara kwanciyarsa ya ce “Maman ummi, tun da abun nan ya faru da ummi, ji nake tamkar ina kan wuta, gidan galibi duk maza ne tana cikin haɗari, sannan ki duba ki ga yadda ake yi mata a gidan nan, ɗazu fa suna tafe da yarinyar nan da take ɗaukarta ta tafi da ita islamiyya, yara suna tsokanarta baƙar tukunya mai ƙyalli, ba ki ji zuciyata ba, wallahi yanzu haka bani da burin da ya wuce tashi na bar gidan nan.
Da nayi tunanin ko kano zan je wurin yaya hashimu idan da wata hanya da zai ɗora ni a kan kasuwanci, to kuma bana son na je na ɗora masa ɗawainiya, kuma kin ga shi ɗan boko ne, iya ta ce sai na bi su Rabiu kudu neman kuɗi, bana son yin nesa da ku, amma na fuskanci idan na cigaba da zama a haka, wahala zamu cigaba da sha”.

Mariya ta nisa ta ce “To, ni dai dan ta ni, wallahi baban ummi zan cigaba da haƙuri, komai lokaci ne, amma duk abun da ya shafi umarnin iya, babu ruwana a ciki, Allah ya taimaka ya bayar da sa’a, ummi kam za ta yi gwagwarmaya wadda sai dai mu bata gudunmawa ba zamu iya tare mata ba.

“In sha Allah komai zai zo da sauƙi, kuma zai wuce umminmu zata rayu cikin farinciki”

“Allah ya sa”

Ya amsa mata da “Amin”

Abu kamar wasa, Iya ta din ga yi wa balarabe kwarmato, a kan lallai ta yi magana da Rabi’u maƙwabcin su, lallai ya nemo kuɗi, ya bi shi lagos, ya ɗora shi a kan hanyar neman arziki.

Bashir ba shi da kuɗin da aka ce ya tanada, dan kuwa rabi’u cewa yayi ya tanadi dubu ɗari, harkar fawa yake a lagos, ya je ya koya masa.

Ya ce wa iya ba shi da halin kuɗin nan ta ce “Ai dama ba zaka yi su ba, Allazi babu wanda ya karɓo jakadancin talauci zuwa duniya, ka je ka tambayi ilyasu, ko sagir, ga saminu, ko Yahaya, tun da su masu zuciyar nema ne, kuma ba a rasa nono a riga, su baka aro.
Bashir baya son dalilin da zai sanya ya keta billensa ya nemi alfarmar ƴan uwansa, saboda yadda ba sa yi da shi.

Amma bisa ga umarnin iya, ya tambayi sagir aron kuɗi, amma ya kada baki ya ce “In ara maka kuɗi, ka biyani da me? Gaskiya ba zan iya ba, kuɗin nan masu wahalar samuwa, na baka in yi sadakar dole da ba niyya, kayi haƙuri kawai”. Ya ji ciwon abun da yayi masa, amma ya dake ya gayawa maman ummi.

Ita kanta mariya abun yayi mata ciwo, abun da iya take musu ya sanya ta tsane ta, duk da ita ta haifi mijinta, tattara samirun ta, har da zobenta da aka saya mata lokacin aure ta sayar, sai ganinta yayi da kuɗi, dan ita kanta wulaƙancin da ake yi masa yana bata haushi.

Ya din ga yi mata faɗa a kan sayar da kayanta da tayi.

Ta ce “Idan har tafiyarka zai sanya iya farinciki, a daina wulaƙanta mu, ka tafi kawai Allah ya tsare”

Ya riƙe hannunta ya ce “Na gode mariya, Ubangiji Allah ya saka miki da alkahirin sa, ya ƙara miki haƙuri, kada Allah ya sa na ci amanarki, ko a yanzu ko a gaba, Ubangiji Allah ya kula mini da ku” haka ya din ga zuba mata addu’a kamar ta yaye masa gaba ɗaya matsalolin sa.

Saura kwana ɗaya ya tafi, da ya shiga ya fita, sai yayi musu addu’a, ya sanya musu albarka da ita ummi.

Da daddare mariya ta shirya masa kayansa a wata jaka, tana ta yi masa addu’a. Ya zura mata ido yana kallon ta.

“Wai wannan kallon fa?”

“Da za ace in nuna matar aljanna a duniya, zan nuna maman ummi”

Tayi murmushi ta ce “Zaka fara ko?”

“Allah ba wasa nake ba amaryata” ta kwashe da dariya ta ce “Ko ba amarya ba, da wannan ƴar tamu nake amaryar, in zo in fara tara kayan ɗakin auren ummi, wai wa ya ganni maman amarya ranar auren ummi ba zama”.

Yayi dariya ya ce “Kema ɗin yaushe aka yi naki auren ki ke hango auren ummina, in sha Allah sai ta yi karatu mai zurfi, Allah ya sa kan na tafi ɗin nan akwai rabo a cikin nan, ummi ta samu ɗan uwa”

“Amin ya Allah, ni kaina ina son jariri wallahi”

“To Allah ya bamu mai amfani, ya bani kuɗi na halal na wadata ku, mu rayu cikin farinciki”

“Amin, amma yanzun ma Alhamdilillah, ai kuɗi ba su ne farinciki ba” sosai suka din ga hira, tana ce masa ban da kallon matan yarabawa idan ya tafi lagos, ya din ga yi mata dariya.

Har ta yi barci, amma shi ya kasa bacci, ya tashi daga kan gadon, ya koma shimfiɗar ummi, da ta yi nisa a baccinta sosai.

Ya kunna fitila yana kallonta, sam bai ga munin ƴar sa ba da mutane suke faɗa suna zuzutawa.

Ya din ga shafa gashin ummi, yana kallonta.

Mariya ta yi juyi ta hango shi, ta ce “Baban ummi, ko saka maka ita zan yi a jakar ka ku tafi, wannan ƙauna haka?”

Yayi murmushi ya ce “Ko yara nawa zan haifa ummi ta daban ce a zuciyata, ina ƙaunar yarinyar nan”

Mariya ta ce “To kar dai ummi ta mamaye ko ina a zuciyar, a rage mini wuri”

Yayi murmushi yana cigaba da kallonta.

Juyi ummi ta yi taga hasken fitila, ɗan razana ta yi, saboda haryanzu ba ta manta yadda aka yi mata fyaɗe ba, dan daren da aka yi mata fyaɗe ta tuna, da ƙarfe ta ce “Baba”

Ya ce “Na’am ummina”

“Kai ne” tayi maganar tana shafa fuskarsa.

“Eh Ummina”

Ta ce “To” ta cigaba da lumshe ido zata koma bacci.

“Ina ƙaunar ki ummina, Allah ga ƴa ta da mata ta, Allah ka kula mini da su, ƴar kyakywar ɗiya ta” yayi maganar yana jan kumatunta. Ummi ta ɗora hannunta a kan nasa tana murmushi ta cigaba da bacci.

Washegari da zai tafi har soro suka raka shi, ji yake tamkar kar ya tafi, amma yana fatan idan har tafiyar ta sa zata zama silar walwalar iyalin sa gara ya tafi.

Sai da iya ta fara maganganunta na rashin mutunci, a gaban mutane tana neman yi musu tijara, sannan suka rabu ya tafi.

Kwanaki uku da tafiyar baban ummi, kewa duk ta ishi ummi da mariya, sai dai tafiyar ta sa bata sanya sun samu sassaucin jaraba da masifar iya ba da gore-gore, gashi a lokacin waya bata yawaita ba, dan haka ba wanda ya san halin da wani yake ciki.

Bai fi sati biyu ba da tafiyar sa, abun da ya bar musu duk ya ƙare, gashi abu kamar wasa, muraran yara ke cigaba da cin zalin ummi, ga farmaki da Idris yake cigaba da kai mata, loka-lokaci da wasu daga samarin gidan, dan ma yanzu ta yi wayo sosai da sosai, da ta gansu sai gudu.

Cin zali a wurin ƴan samarin yaran nan maza, tamkar sun samu sa’ar su, saboda tana mace, abu kaɗan sai a kai mata duka, ko ayi mata wata izayar ko a gida ko a makaranta, saboda ana ganin ummin tamkar sokuwa, kuma babu mai tare mata, da mariya tayi magana iya tayi kanta da tijara.

Ɗan abun da ya rage a hannunta, ta fara fanken sayarwa, saboda ta samu abun juyawa, amma sai da iya ta cinye jarin da cin bashi, tare da tula mata ayyukan da zasu hanata sana’ar.

Abubuwa fa suka fara yi wa mariya da ummi yawa, duka ko ta ko ina, wani ta iya karewa, wani ta kasa sai dai tayi kuka ta gaya wa Allah.

Tana tsakar gida tana wanke-wanke, ta samu da ƙyar ta jiƙawa ummi garrin kwaki, bayan ta dawo daga makaranta tana sha, ta ji hayaniya ta yi yawa a waje. Bata damu ba ta cigaba da aikinta.

Da gudu Alhassan ya shigo ya ce “Babar ummi Albishirinki?”

Ta kalleshi ta ce “Albishirina kuma? Menene?”

“Wai baban ummi ƴan fashi suka kashe a hanya, zasu taho gida daga ikko!!!”

Ayshercool

       CUTARWA!

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P4

Wani irin jifa mariya tayi da kwanon hannunta, ta miƙe a gigice jikinta na wata irin tsuma, zuciyarta na bugawa da saurin gaske amma ta kasa magana.

Miƙewa ummi ta yi ita ma, tana bin su da kallo.

Iya ta fito a gigice ta ƙundumawa Alhassan ashariya ya ce “Uban wa ye ya gaya maka haka? In ji wani ɗan iskan”.

Ilyas da saminu ne suka shigo, fuskokin su babu walwala.

“Ku gyara wurin da za a shigo da balarabe, Allah ya yi masa rasuwa, tun safe muka tafi ɗaukko gawarsa”

A gigice iya ta ce “Ƙarya ne ban yarda ba, ya za ayi ace ya mutu? Balaraben ne ya rasu? Waye ya kashe shi, ya aka yi aka kashe shi?”

Sagir yayi sallama tare da idris, ya ce “A ina za a kwantar da shi idan an shigo ne? Ana jira fa”

Mariya ji take abun kamar mafarki, addu’a take Ubangiji Allah ya sanya mafarki ne, Allah ya sa ba mijinta ne ya mutu ba, Allah ya sa ba baban umminta ne ya mutu ba”.

Magaji ya shigo da tabarma, ya shimfiɗa, aka yi sallama tare da ƴan sanda, da rabi’u da suka tafi tare, aka shigo da gawar bashir, tana ta ɗigar da jini.

Nan da nan gida ya cika da jama’a, Iya sai ihu take tana kururuwa tana kuka, kai da gani ka san jahilci ya samu gidin zama a wurin iya, saboda yadda take ihun ta shiga uku ta lalace.

Jiki na rawa mariya ta saka hannu ta buɗe mayafin da aka rufe gawar bashir, fuskar nan fayau kamar yana bacci, kamar wanda yayi wanka ya fito haka gawar take, ga ƙirjinsa in da aka harbe shi, jini yana ta zuba.

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un” shi ne abun da mariya ke ta nanatawa, tare da fatan Allah ya saukar mata da nutsuwa da dangana.

Ummi ta shafa fuskar sa tana faɗin “Baba ka tashi, baba ka tashi daga bacci mama tana kuka” cikin haɗe rai sagir ya yi wa ummi tsawa ya ce ta tashi.

Sa’adatu ta ce “Haba baban auwwalu, ka tausaya musu mana”.

Mutane suka cika gidan danƙam, saboda mutane sun san bashir sosai, mutum ne na mutane mai matuƙar haƙuri da girmama mutane.

Sai ajiyar zuciya kawai mariya take yi, tana rungume da ummi, aka shiga da shi ɗakin Iya, aka yi masa sutura, sannan aka ce su je su yi sallama da shi.

Har a lokacin mariya ta gaza zubar da hawaye, sai wata irin ƙuna da zuciyarta ke yi mata, abu kamar wasa bashir shikenan an yi an gama, rayuwar ta ƙare.

Duk da yarinta ta ummi, amma ta san idan an mutu ba a dawowa, tayi kuka idonta duk ya kumbura, ta dinga taɓa shi tana “Baba ka tashi, ka ce zaka sai mini ƴar tsana in yi addu’a ka samu kuɗi, kullum ina yi maka addu’a”

Mariya kam zubawa gawar ido kawai tayi, tana kallon ikon Allah, wai bashir ya mutu.

Sa’adatu ta ce “Mariya ki riƙe yarinyar nan, za a shigo a ɗauki gawar”

Mariya kamar sokuwa, dan kamar ma ba ta iya gane me ake cewa.

Aka zo aka ɗauki gawar bashir, ana ta iface-iface, ummi ta riƙe ƙafar Saminu wan mahaifinta, da suka ɗaga gawar, tana wani irin kuka, amma babu tausayi ko imani, ya angije ta ƙasa suka yi waje.

Allah sarki, ba ta karaya ba ta sake bin su, tana faɗin “Ku dawo da baban, zai tashi fa, bacci yake yi”

Surayya, wadda take ƴar autar su bashir, ta riƙo hannun ummi tana kuka, ta rungume ta, tana ta rarrashinta.

Gida ya cika da jama’a ana gaisuwa, mariya kuwa ta samu gindin bishiyar da ke tsakar gidan ta rakuɓe, tayi shiru ba ta cewa komai, ita kaɗai ta san azabar da zuciyarta take yi mata.

Bata san hawa ba, ba ta san sauka ba, ta ji muryar iya na bala’i a cikin mutane “Dama ya za ayi mutuwar ta dame ta, ai dama ba dan Allah take zaune da shi ba, kalleta a ƙeƙashe ko kuka ba ta yi ba, alhalin ita ta takura lallai ya tafi neman abun duniya, ya zo ya wahalta mata, wallahi ban yafe miki ba”

Daram! Gaban mariya ya faɗi, jin abun da iya ta faɗa na ƙarshe.

Mutane suka shiga salallami, surayya ta ce “Haba iya, haba iya, baki san kukan zuci yafi kowanne ƙuna ba, gara ke kin yi kukan, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta, da can ba ta ce ya tafi neman kuɗi ba, sai yanzu, dama Allah ya yi ajalinsa a can za same shi”.

Ai nan ta mayar da faɗan kan surayya, wanda hakan ya tilasta mata yin shiru, wasu suka goyi bayan iya saboda makira ce, wasu kuma suka goyi bayan mariya, kowa ya san kusan halinta ɗaya da mijinta, ba sawa ba fitarwa, akwai haƙuri da juriya, mussman a zamanta da iya.

Yadda ta ga rana haka taga dare, abu goma da ashirin, ga raɗaɗin mutuwar mijinta, ga sharrin da iya ta ƙulla mata, wai ita ce silar mutuwar sa, ita ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi.

Ta rasa me ta tsarewa iya, take yi mata wannan azababbiyar ƙiyayyar, saboda kawai tana auren ɗan ta, abun da ba haka take yi wa sauran sirikanta ba, kuma dukkansu babu wanda yake yi mata biyayyar da take yi mata, kawai ta camfata cewar ita ce mai farar ƙafar da ta toshe masa hanyar arzikin sa, ya kasa gaba ya kasa baya, gashi ya ɗauki son duniya ya ɗorawa mariya, yana matuƙar son ta da ƙaunarta.

Ko fuskanta Iya tayi sun yi mu’amalar aure, ta ga sun yi wanka, to wunin ranar, haka zata wuni cikin ɓacin rai da tashin hankali, a wurin iya ta din ga ƙirƙirar mata laifi kenan tana ci mata mutunci, ta rasa wannan masifar, ga uwa uba ummi sunan kishiyar ta ne da ita, wanda hakan ya sa ta ƙara tsanar ummi, ga ƴaƴanta sun riƙe ta uwa, abun da ta dama suke sha, amma tana masifar kishi da uwar su.

Washegari da azahar, dangin mariya suka dira a jigawa, suka zo gaisuwa, haka zalika Yahaya, yayan bashir da yake birni, shi ma ya zo ta’aziyya, ya ji mutuwar bashir ba kaɗan ba, abun ya girgiza shi, dan kaf cikin ƴan uwansa, ko wanda suke ciki ɗaya, basa shirin da suke yi da bashir, saboda biyayyar sa, yana matuƙar girmama shi.

Yana son ummi, kasancewar sunan mahaifiyarsu ne shi ma da ita, marigayiyya uwar gidan malam hashimu.

Ya tarar ana ta fama da ummi, ba ta ci abinci ba, sa’adatu da ba wani shiri suke yi da mariya ba, amma mutuwar bashir, da abubuwan da iya ke ta yi, ya sanya wani irin tausayin su ya kamata.

Yahaya ya ga yadda ake fama da ummi, tana kwance a jikin mariya, ba wanda ya iya cin abinci a cikinsu.

Duk da tana tsoron maza sosai da sosai, kuma shi baya yawan zuwa gidan, amma ta gane shi, dan yana kama da babanta sosai, kuma yana bata tsaraba idan ya zo.

Ya ƙarasa ya ɗauketa, ya saka hannunsa a nata, ya ce “Mamana, ki din ga yi wa babanki addu’a, kuma ki din ga cin abinci, kuka ba zai yi magani ba”

“Baba ba zai dawo ba ko, ya mutu wai?” Tayi maganar hawaye na zubo mata, kamar an kunna famfo.

“Ba zai dawo ba ummi, amma zai ji daɗi idan kina yi masa addu’a”

Cikin kuka ta ce “Na fi son ya dawo” ya din ga share mata hawaye, cike da tausayawa.

Sai dai yayi mamakin yadda iya ke ta hantarar mariya, tana cikin alhinin mutuwar mijinta, ga ƴan uwanta a gida, amma iya na ta masifa da nanata ta kashe mata ɗa.

Ya dubi Iya ya ce “Haba iya, haba iya da wanne za ta ji? Ya za ayi ta yi sanadiyyar mutuwar mijinta, mijin da suka yi auren soyayya, shekara bakwai tare, ko sulhu ba a taɓa yi musu ba, ki ce ita ta kashe shi, ga ƴan uwanta a gida ai babu daɗi”

“Yahaya, ni fa nake zaune da yarinyar nan, ni na san abubuwan da take aikatawa, azabar son zuciyarta ya sanya ta hura masa wuta ya tafi neman kuɗi, gashi nan ya mutu a banza, yaron nan haƙurin zama yake yi da ita”

Yahaya ya ce “A’a iya, idan na zo fa muna hira da bashir, a bar kaza cikin gashinta kawai banda tone-tone, amma batun ace mariya ce ta kashe mijinta bai taso ba, dan Allah ki bari ta ji da alhinin da take ciki”

Kasancewar yana da abun duniya, domin kuwa lecturer ne shi a kano, kuma albashinsa da tsoka, dan haka yana yi wa iya sha tara ta arziki, a dole ta ja bakinta ta yi shiru.

Wasa² magana har waje wurin maza, iya ta tubure tana cin mutuncin sirikarta, wai ita ta kashe mata ɗa.

Yayan mariya har cikin gidan ya shiga, ya yi wa mariya wankin babban bargo.
“Irin tarbiyyar da aka baki kenan dama mariya? Irin zaman da ki ka yi da mijinki kenan, ki kasa zama da shi a yadda yake, ki hura masa wuta ya tafi ajali ya riske shi, kuma gashi an ɗora miki, an ce ke ce sila. Mariya kin ɓata wayonki, wannan ba tarbiyyar gidanmu ba ce ba, kuma ahalinsa ba zasu taɓa mantawa da abun da ki ka yi ba”. Kasancewar yana cikin manyan yayyenta, kuma tana bala’in tsoronsa, dan haka ba ta iya kare kanta ba sai kuka, ga shi a gaban mutane ya din ga yi mata faɗa, mariya ta rasa da wanne za ta ji.

Iya kuwa ta samu damar cigaba da ƙullawa mariya sharri a wurin yayanta.

Yahaya ya tsawatar, saboda shi ɗan boko ne, ya ce ba zai yiwu a saka mariya a gaba ace ita take aikata duk wannan laifukan ba. Idan ma haka ne tana matsa masa kan ya rasu yanzu yana ina? Kuma ai mijinta ne, tana da right na ya yi mata abun da take so.

Ɗakinta ta shiga ta zauna, tayi kuka, tayi kuka, har zuciyarta ta fara raya mata ko kashe kanta zata yi ta huta da wannan azabar.

Ummi ta zo tana kuka ita ma, dan tun ana yi mata faɗan nan ummi take tayata kukan, ta din ga share mata hawayen tana cewa “Mama ki yi haƙuri, ki daina kuka” ita kanta yayar mariya, ta san mariya ba za ta aikata haka ba, yadda iya ke yi wa mariya a gaban su, ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba. Sai dai su al’adar gidan su, muddin ak kawo ƙararka daga waje, ba a taɓa goya maka baya, balle kuma a gidan aure, idan miji gutsurar namanki yake yana ci, sai ace ki je ki cigaba da haƙuri, wataran sai labari, kowa haƙuri yake yi.

Maryam ta tambayeta ina samirunya, ta ga duk babu? Mariya taƙi gaya mata, ta shashantar da zancen.

Bayan kwanaki uku da share zaman makoki, ƴan nesa suka watse, sai masu shigowa jefi-jefi gaisuwa, yayar ta ta zauna da ita, ta ɗan din ga ɗebe mata kewa, zuwa kwana arba’in, aga meye abun yi.

Gaba ɗaya mariya ta gama fita daga hayyacinta, kai daka ganta ka san tana cikin alhini, ko abincin kirki ba ta iya ci. Salla kawai take iya yi, wanka kansa sai ta yi da gaske take iya yi.
Daga kwanciya sai kuka, amma hakan bai sanya ta tsira daga tashin hankalin Iya ba, ga kyarar ummi da take yi kamar ba jininta ba, wanda hakan ya fara tunzura yayar mariya maryam.

Kwanan bashir goma sha huɗu da rasuwa, rabi’u ya zo yayi sallama, suka amsa ya sake yi musu gaisuwa.

Ya ce wa iya “Ina mariya, ina son zan yi magana da ku ne”

Iya ta ce “Dole ne sai ta nan? In dai abun da ya shafi ɗa na ne, gaya mini kawai ina jinka”

“Wane irin a gaya miki kawai? Ai tana da hakkin sanin menene ita ma, tun da mijinta ne” yaya maryam tayi maganar a zuciye kamar ta kife iya da mari, saboda a zamanta ɗin nan ta gane lallai mariya tayi zaman haƙuri.

“Rashin kunya zaki yi mini?”

“Ba wani rashin kunya, maganar gaskiya ce ai. Ke mariya fito za ayi magana”

Jiki a sanyaye mariya ta fito cikin hijjabi, ta zo ta samu wuri ta zauna.

Suka sake gaisawa da mariya, yayi mata gaisuwa, Sagir yayi sallama ya shigo suka amsa masa, shima ya samu wuri ya zauna.

Rabi’u ya ce “Yauwwa, dama ni na yi masa magana tun da yana gida na ce masa ya shigo, Iya kamar yadda ki ka roƙi na tafi da bashir lagos, ya nemo arziki, to mun sauka Lagos lafiya”.

Maryam ta ce “Amma ki ka ce mariya ce ta ce lallai sai ya tafi neman kuɗi”

Iya a fusace ta ce “Wai wace irin mara tarbiyya ce, ƙarya nake yi kenan, matsin da take yi masa ya sanya na yi masa magana, ya tafi da shi”

Maryam ta ce “Amma ai ba haka ki faɗa ba, ki ka saka yayanmu ya din ga ci mata mutunci a gaban mutane, wallahi ki ji tsoron Allah”

Rabi’u ya ce “Dan Allah ku yi haƙuri, ku saurare ni ku ji, bayan zuwanmu Lagos, mun fara sana’ar fawa da balarabe, kasancewar ba shi da account, yake tarawa a account ɗina, ya ce mini mariya ta sayar da kayanta, ta bashi kuɗin, amma shi a bashi ya karɓa, zai mayar mata da kuɗinta, dan haka ba laifi ya tara kuɗi, riba kawai kusan dubu sittin, uwar kuɗin sa da ribarsa da komai, kusan dubu ɗari biyu, basussuka da sauran su, duk na biya masa dubu ɗari da arba’in ne suka rage, mun taho gida da niyyar idan mun zo na cire kuɗin na bashi.

A hanya ƴan fashi suka tare mu, suka ƙwace mana kaya, da kayan tsarabar sa, har sun yi gaba ya tashi kan su ƙarasa barin wurin, shi ne suka harbe shi a ƙirjin sa, kan ya rasu ya ce: kar a raba gado, sai an biya mariya kuɗinta na kayanta, da sauran kuɗin da take bin sa” Ya kalli ummi da ke zaune tana bin su da kallo, sannan ya kalli mariya ya ce “Ya ce; ki kula masa da ummi, sannan ki yafe masa” yana faɗar haka mariya ta sanya tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka.

“Ni bai ce maka komai a kai na ba?” Iya tayi maganar tana kallon rabi’u.

“Yana cikin maganar yayi kalmar shahada, ummin dai ya fi nanatawa”

Ta share hawayen da ke shirin zubo mata sannan ta ce “Ba wani zancen tana bin sa kuɗi, ni ban yi wannan maganar da shi ba, dan haka ka je ka ɗebo kuɗi ka kawo mini”

Maryam ta ce “A kawo miki kuɗi kiyi me da su? Ai kuɗi na magada ne, kuma sai mariya ta gama idda za a raba gado, saboda a tabattar da babu ciki”.

“Ba dai ciki ba, shekara nawa rabonta da haihuwa, tun daga wannan mummunar yarinyar fuska kamar turotso, ba ta sake haihuwa ba, ba haihuwa take ba, dan haka ba ta da wani ciki. Wa ya sani ma ko balaraben baya haihuwa”

“To me ki ke nufi, ummin ba ƴar ku ba ce ba? Wai ke matar nan anya musulma ce ke? Kin yi imani da Allah kuwa?”

Sagir ya ce “Ke malama kar ki sake ki zagar mana uwa, na gaya miki” miƙewa maryam ta yi ta ce “Na zageta ɗin, ka yi abun da zaka yi. Azzalumar tsohuwa mara imani da tausayi, ashe ke ki ka ingiza ɗanki ya tafi neman kuɗi, amma kin saka yarinya a gaba, kina ta yi mata sharri, to wallahi dan kanki, ummi kuma idan ba ƴar ku ba ce, sai ki fita neman ubanta” nan da nan hayaniya ta ɓarke.

Mariya ta tashi ta ce “Dan Allah yaya maryam ki yi haƙuri, in dai kuɗi ne, ni babu bashi tsakanina da baban ummi, na rasa mijina balle abun duniya? Tumunin takabar ma na yafe, a bawa ummi hakkinta, in ɗau ƴa ta in koma in da na fito dan Allah” tayi maganar cikin matsanancin kuka, tare da jan hannun ummi ta tafi ɗaki.

Shi kansa rabi’u yayi mamakin rashin arzikin Iya, kawai ta ɗorawa mariya karan tsana.
Ta sake jaddawa rabi’u ya kwaso kuɗi ya kawo mata, me balaraben ya mutu ya bari, da za a tsaya wani rabe-raben gado.

Maryam kuwa da kanta ta tafi tasha, ya bayar da saƙo zuwa gida, a kan lallai a cewa yayansu ya zo, akwai matsala.

Ko abinci ba a basu, maryam ita ta din ga cefane tana ciyar su.

Yayan su mariya ya dira a garin, Iya sai da ta yi mamakin ganinsa, maryam ta ja shi, ta ce masa akwai matsala cigaba da zaman mariya a gidan nan, tana kallon irin zaman da mariya take yi a gidan, nan ta kwashe komai ta gaya masa.
Abun ba ƙaramin ɓata masa rai yayi ba, wani irin tausayin mariya ya kama shi, karon farko da ya ji zai goyi bayan ƙanwarsa, dan haka ya yanke cewa kawai zasu ɗauki mariya da ummi su tafi.

Dan haka ya je ya samu iya ya ce mata, washegari da safe zasu yi sammako su tafi Maiduguri, yaso su zauna su cigaba da gaisuwa, tayi takaba a ɗakin mijinta, amma wasu dalilai ya sanya sun yanke shawarar su tafi da ita gida kawai.

Iya ta ce “Shikenan babu laifi”

Mariya ta wani fannin ta ji daɗi zasu koma gida, wani ɓangaren wata irin kewar ɗakinta da mai ɗakik wato baban ummi, ta sake mamaye mata zuciya, har take jin anya ba za ta ce a bar ta a ɗakin nan ba, za ta cigaba da haƙuri da ita, kawai dan ya din ga gurbin da bashir yake dabdala.

A daren Maryam ta taimaka mata, ta harhaɗa kayanta, abun da zasu buƙata, Maryam ta ce daga baya azo a sayar da sauran kayanta, dan ba zasu iya dakon kaya zuwa Maiduguri ba.

Da sassafe maryam ta yi wa ummi wanka, suka yi wanka suka karya, ummi tana murna zasu tafi su bar gidan nan, tana fatan Allah ya sa idan sun je can babu yara masu tsokanar ta, ko dukanta.

Sun fito maryam na ce mata, ta yi sallama da mutanen gidan, ta nemi afuwarsu, Iya na tsaye tana kallon su.

Iya ya ce “Ummi zo mana mu yi sallama”. Saroro ummi tayi tana kallon iya, ta ɗaga kai ta kalli mariya, mariya ta ce “Je ki Iya na kira”

Ummi ta tafi sannu a hankali, ta ƙarasa gaban iya.

Caraf iya ta sanya hannu ta riƙe hannun ummi, sannan ta kalli mariya ta ce “To, Allah ya raka taki gona, ummi dai ba da ita ki ka zo ba, kin san wannan, dan haka a sauka lafiya”

Mariya tayi turus tana kallon iya, dan ganin abun take kamar almara.

Maryam ta ce “Ban gane ba, yarinyar da ki ka ce ba taku ba ce ba”

“Ɓacin rai ne ya sanya ni faɗar hakan, ba zan bayar da ita aje ayi mata gurguwar tarbiyya ba, ta tashi tana sa’insa da manya ba, dan haka ni zan riƙe ummi, ita kaɗai ya haifa, na rasa ɗa na, ina buƙatar ganin jinin sa a gabana”.

Cikin kuka mariya ta ce “Dan martabar Allah kar ki yi mini haka iya, ba zan iya jure zama babu ummi a kusa da ni ba, idan ma tafiyar ce na fasa, dan Allah ki bani ƴa ta”.

“A a, a kan me zan hana ki tafiya, haifarki na yi, na rasa ɗa na balle wata ke, Allah ya raka taki gona”

Ƙoƙarin ƙwacewa ummi ta fara yi, tana kiran sunan mama.

“Nutsu dan ubanki” Iya tayi mata tsawa.

Yayansu mariya ya shigo, yana cewa su fito kar su yi rana, amma ya tarar da sabuwar dambarwa.

Juyin duniya, Iya ta ce ba zata bayar da ummi ba.

Mariya ta zube a kan gwiwoyinta, tana gursheƙen kuka, a kan iya ta bata ƴar ta, ta din ga cewa mutanen da suka taru, su saka baki iya ta bata ƴar ta, amma matar nan mirsisi taƙi.

Ummi na kuka mariya na kuka, yayan su ya hasala ya kalli mariya ya ce “Ke tashi mu tafi, in dai ƴa ce su cinye, tashi mu tafi”

“Yaya ka taimake ni, ba zan iya rayuwa babu ummi ba, dan Allah kar a rabani da ƴa ta, dan girman Allah ku yi mini rai, da wanne zan ji, na rasa mijina ƴar ma a ƙwace mini? Dan Allah ku bani ummina”

“Sai dai kiyi kukan jini kuwa”

A fusace ya daka wa mariya tsawa, ya ce ta wuce su tafi.

Iya tayi tsaki ta ce “Aikin banza, ban da rashin tarbiyya, wai a kan ƴar fari take wannan abun”

Idris ya shigo, Iya ta ce “Kai kuma mun yi magana ka ɓata mini lokaci, ɗauke ta ka tafi da ita in da na ce maka”

Ya ƙarasa babu walwala, zai danƙi hannun ummi, ummi ya rirriƙe Iya, tana wani irin kuka, dan a rayuwarta, ta tsani ko haɗa hanya su yi da idris, ta ƙarfin tsiya ya danƙi ummi, tana kuka tana kiran mama, mariya ta bi bayansu da gudu tana kiran “Ka zo ka bani ƴa ta, ku bani ƴa ta ba ƙaunar ta ku ke yi ba, ku bani ƴa ta. Yaya maryam ki karɓo mini ƴa ta, ke shaida ce ba son ummi suke yi ba”

Cikin tausaya maryam ta ce “Zaki kashe kanki ne? In dai ummi ce Allah zai kula miki da ita” shiru ta yi tana kallon maryam, ana gobe bashir zai tafi yake cewa Allah ga ƴa ta da mata ta Allah ka kula mini da su.

“Wuce mu tafi, su je su cinye ta, kema kina da masu sonki” auwwalu ne ya bi bayansu da warin takalmin mariya, dan takalmi ɗaya ne a ƙafarta, hawaye ne kawai yake zuba daga idonta, can ƙarshen hanya ta hango ummi tana ɗaga mata hannu tana kiran mama cikin hawaye!

Iya ta ce “Ba dai ke tsagera ba, daga ke har yayar taki dai-dai nake da ku, ummi ce dai tana hannuna, ba wani uban gado da za a raba, a baki ku cinye, gayyar tsiya arna a idi”.

Page ɗin nan sadaukarwa ne, ga duk matar da ta rasa mijinta ko aurenta, kuma aka zo aka rabata da ƴaƴanta, we know is difficult to endure, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri, ku yi haƙuri 🙏 Allah ya shiga lamarinku, ya kula muku da yaranku

Ayshercool

CUTARWA!

BRIGHT PENS
(FREE BATCH)

P5

Har suka je tasha, jan ƙafa kawai mariya take yi, dan bata gane komai, hankalinta yana kan ummi, wace irin rayuwa ummi za ta yi a wannan gidan? Tana nan ma a ya aka cika, balle yanzu da babu idonta, kuma ya zamana ba ayi rabuwar arziki ba.

“Allah ka kula mini da ƴa ta, Allah kar ka sanya ƴa ta ta lalace, Ubangiji Allah ka duba mini ita, ka tsare mini ita, Allah kai ka san dalilin da ya sanya, ka karɓi mahaifinta ka rabani da ita, Allah ka kula mini da ita. Haka ta din ga wannan addu’ar, jin abubuwan take tamkar a cikin nannauyan bacci, da take fatan ta farka.

Har suka shiga mota suka kama hanya, duk wata nasiha da maryam ke yi mata, ba ji take ba, balle ta fahimta.

Mariya ji take tamkar ta sauka daga cikin motar nan, ta koma ta rayu da ummi, ta san ummi wahala kawai za ta sha, dan iya ba ƙaunarta take yi ba.
Tunawa da tayi da cin zarafin da aka yi wa ummi, ya sake karya mata gwiwa, ta sake fashewa da kuka mai sauti.

“Idan ba zaki rufe mana baki ba, a tsaya ki sauka ki koma, ki je duk uban da za su yi miki, su yi miki, sai ka ce a kanki aka fara haihuwa, duk cin zarafin da suka yi miki bai isheki ba, ba dai ƴa ba ce su je su cinye ta, ai ta su ce da ma, dangin uba su ke da ɗa” tun da ya fara yi mata masifar ƴan cikin motar suka yi tsit, sai da ya gama ake bashi haƙuri.

Maryam ta san abun da mariya ke ji, dan haka ta rungume ta tana rarrashinta, haka tana ji tana gani ta bar garin da duka goma da ashirin, ga rashin miji ga rashin ƴa.

Ummi kuwa sai can daf da magariba aka saka yara suka rakata gida, dan can gidan wata ƴar uwarta ta sanya aka kai ta.

Ta ci kuka ta ƙoshi, sai ajiyar zuciya take yi, ana zuwa gidan da sauri ta shiga ta nufi ƙofar ɗakinsu, sai dai ta tarar da shi da ƙaton kwaɗon da su mariya suka rufe ɗakin da shi.

Ta nemi wuri ta zauna a ƙofar ɗakin, ta cigaba da rera kuka.

Babu wanda ya saurareta, balle ya kula da ita ya rarrasheta.

Sa’adatu ce tayi sallama, ta kawo wa iya tuwon dare.

Ta ajiye mata suka taɓa hira, ta tashi fito, tana daf da shiga sashinta, ta ji ana bin ta a baya, ta tsaya ta waiwayo taga ummi.

“Ke, lafiya ki ke bina?”

“Dan Allah ina mama? Haryanzu ba ta dawo ba, ta buɗe mana ɗaki in yi salla, sanyi nake ji”

Sa’adatu ta yi shiru tana kallon ummi, sam ba ta ga dalilin da zai sanya iya raba mariya da ƴar ta ba, ta san iya ba iya riƙe ta zata yi ba, saboda tsabar mugunta da rashin imani.

“Ummi babarki ba zata dawo ba, ki tafi wurin iya ki je ki kwanta, gari da sanyi”

“Ita ma maman ta mutu? Ba zata dawo ba kamar baba?”

“Ba mutuwa tayi ba, nan kusa dai ba zata dawo ba, ki yi addu’a Allah ya sanya ta dawo ta tafi da ke, can in da aka kai ki kin ci abinci?”

Ummi ta girgiza kai ta ce “Mama ta hana ni cin abinci a gidan mutane”

Sa’adatu ta ce “Kenan wuni ki ka yi baki ci abinci ba, tafi na kai wa iya abinci, ki je ta zuba miki” ummi ta ce “To”

Ta juya jikinta a sanyaye, ta koma sashinsu, ta zauna a ƙofar ɗakin su, tana kallon ƙofar ɗakin Iya, kuka take a hankali tana jin kewar mahaifiyarta, da yanzu mama ta yi mata wanka, ta shafa mata mai ta saka mata kayan sanyi.

Tana nan zaune a ƙofar ɗakin, sanyi sai ratsata yake yi, ga ƙanan ƙwari na bin ta.

Gani tayi an hasketa da fitila, ta saurin rintse idanuwanta, saboda hasken fitilar, bai ɗauke fitilar ba, har ya ƙaraso kanta ya tsaya.

“Me ki ke yi a nan?” Jin muryarsa ya sanya ta tashi a razane ta ja da baya jikinta na rawa, dan ita duk wani namiji tsoro yake bata.

“Me ki ke yi a nan?”

“Mama nake jira ta dawo”

“Kuma sai ki zauna a nan ga sanyi, ki tafi ɗakin iya ki jirata mana”

Ta girgiza kai ta ce “Zan zauna a nan”

“Wuce ki tafi dalla!” Yayi maganar cikin tsawa. Da sauri ta nufi ɗakin Iya, ya bi bayanta.

Sai da iya ta ga ummi, sannan ta tuna ta ce da yamma a dawo da ita.

Iya ta ce “Ke daga ina?”

“A ƙofar ɗakinsu na ganta, wai mamanta take jira, a wannan sanyin, maimakon ta shigo nan ta jira ta”.

Iya ta ce “Ka ji munafuka, an tsotso a nono, amma a gaban idonki ai uwar taki ta tafi barki ko?”.

Hashim ya ce “Kamar yaya ina ta tafi?”

Iya ta ce “Mhmm, ai mariya daga ita har ƴan uwanta ba su da mutunci, zuwa suka yi za su tafi da ita, shi ne zasu haɗa da ummi, na ce ba zai yiwu ba, in rasa ɗa na sannan ita ma su tafi da ita ba, na ƙwace ta”

Yayi shiru yana kallon iya ya ce “Amma iya meyasa? Kin san bata shaƙu da kowa ba sai babarta, ga mahaifinta Allah ya karɓe shi”.

“Ba ka san rayuwa ba magajin malam, mariya sam ba ta da tarbiyya, ba zan rasa ɗa na kuma ta tafi da ƴar sa ba, ta koya mata mugun hali. Tashi ki miƙo mini kwanon can, ki zo in zuba miki tuwo”.

Ummi ta kawo kwano, iya ta zuba nata tuwon masara miyar karkashi, sai dai ummi ba ta son miyar karkashi. Ta jagwalgwala tuwon, ta cinye samansa, ta bar guntun cikin tsoro ta ce “Na ƙoshi”.

Iya ta kalleta ta, ta kalli kwanon tuwon ta ce “Ni zan cinye miki sauran da ki ka bari?” Ummi ta girgiza kai.

“To maza cinye shi” duk ƙoƙarin da ummi tayi, ta kasa cin abincin nan.

Iya ta din ga zaginta, ta ce ta rufe ta ajiye, zata yi maganin wannan sangartar da aka yi mata.

Mariya ƴan uwa na ta tausaya mata abun da ya faru, da alhinin rashin mijinta ga muguntar uwar miji, da kuma rabata da ƴar ta.
Dan sai da mahaifinsu ya so yayi faɗa, yayanta yayi masa bayanin abubuwan da suka faru, da ƙyar ya fahimta, duk da haka dan mariya tana cikin yaran da yake matuƙar so ne, tana da matuƙar haƙuri da biyayya.

Ya ce in dai ƴa ce, tun da sun ƙwace ta, su ƙarata suma ba zasu sake bibiyar a basu ba, idan sun ga dama su din ga kawota, idan ba su ga dama ba su je su ƙarata, dan babban abun da ya baƙanta masa rai, bai wuce yadda aka ce Iya tayi iƙirarin mariya ce ta kashe mata ɗa ba, karo na farko a kan mariya, aka goyi bayan mace ko dan ba ƙara ta kawo ba, zahiri suka gani, dan maryam ta labarta musu komai, har da yadda ake muzanta ummi, da cewar da iya tayi, wataƙila ɗan ta ma baya haihuwa, saboda su kaf danginsu babu kalar ƴar, daga baya kuma ta ce ita zata riƙe ta.

“Ai ban san mutanen kawai bane na basu ƴa ta, dattakun yaron da nutsuwarsa ce ta sanya haka, ina da yaƙinin zuriyata babu lalatacce, kar wanda ya kuma bi ta kan yarinyar, ku ƙyale su da ita, ke kuma idan kin gama takaba, Allah ya kawo miki miji nagari”.

A ɓangaren mariya ba ta ji daɗin wannan goyon baya da aka yi mata ba, mussaman yadda ƴan uwa suka goya masa baya, a kan yanke alƙarsu da in da ummi take, ita a ganinta hakan ba masalaha ba ce, ita da ummi meye nasu a ciki.

Babu bakin magana, haka tayi shiru sai bin su da ido, ta ƙare ta shige uwar ɗaka, ta durƙushe a kan gwiwoyinta, ta din ga rusa kuka, ita ma meya rage mata na bashir da za ta kalla ta ji daɗi ban da ummin? Ta din ga kuka, zuciyarta na wani irin zafi, ji take kamar duniya babu wani abu da ya tage mata da zai sanyata farinciki, mahaifiyarsu ta rasu, yayyenta duk sun yi aure, sai ƙananan ƙannenta da matar babansu, dan ma mutuniyar kirki ce.

Washegari da asuba, iya ta idar da sallar asuba, ummi na ƙasa a duƙunƙune a cikin hijjabinta a ƙasa, ko zani ba a shimfiɗa mata ba, ba wanda ya kai ta tayi fitsrai, ta saba sai mariya ta kai ta tayi fitsari, kan ta kwanta, dan haka ta yi wa iya fitsarin kwance.

Kamar zata daki sa’anta, haka iya ta taƙarƙare ta ɗalawa ummi duka, a gigice ta tashi tana sosa wurin, saboda zafi.

“Dan ubanki fitsarin kwance ki ka yi mini saboda sangarta?” Dubawa ummi tayi ta ga fitsarin tayi, ta yi shiru ta kasa magana, sai hawaye.

“Au kuka ma ki ke yi mini, saboda sangarta da iskanci, zan yi maganinki, fita ki ɗebo ruwa a randa ki zo ki zuba”

Da sauran duhun asuba, dan haka ummi tsoro take ji, ta fito waje ta tsaya tana kuka.

“Ba zaki wuce ba, sai na zo” ta jiyo muryar iya. Cikin sauri ta je ta ɗebo ruwa, garin sauri ta koma ɗakin, ta faɗi sassanyar ruwan randar nan ya sheƙe mata a jiki.

A gigice ta yi wata irin ajiyar zuciya, tana kyarma. Ta tashi da guntun ruwan a moɗa, ta shiga ta zuba a wurin, kamar yadda iya tayi mata umarni, ta dawo ɗakin ta tsaya.

Iya ta kalleta ta ce “Munafuka, shi ne ki ka zuba ruwan a jikinki, sai ki cire kayan ki saka wasu, ga tsummokaranki can”.

Cikin rashin wayo, ta kwance kayan, ta saka uniform ɗin ta, dan ta san ranar monday ce, ta tattara kayan fitsarin, ta haɗa su a cikin masu kyan ta ɗaure, dan kuwa mama ta hanata zubar da kaya ko ina.

Ta juya ta kalli gabas tayi salla, ba tare da tayi alwala ba, dan da ruwan ɗumi take alwala da mama tana nan, dan haka ta zata idan ba ruwan ɗumi, ba sai ka yi alwala ba.

Gari yayi haske, ta je gaban murhu, ta saka hannunta ta dangwalo toka, ta cuccuɗa bakinta, ta kuskure ta koma ɗakin iya, tana jiran iya ta bata abinci.

Aka kawo wa Iyan kunu mai zafi, amma ta kalli ummi, ya ce ta ɗauki tuwon jiya ya cinye, dan ba za a zubar ba.

Miyar karkashin ce ba ta so, dan haka ta sake jagwalgwalawa, ta ajiye ta fito tsakar gida, tayi ta kallon ƙofar ɗakin su, ta ƙarasa ƙofar ɗakin tana ƙwanƙwasawa, wai ko mama zata buɗe, sai da ta gaji, kawai ta fita, ta kama hanyar makaranta, lokacin kusan tara da kwata, tana tafe iska na kaɗata, ga azabar sanyi jikinta babu rigar sanyi, sannan babu mai a jikinta, dan haka tayi busu-busu da ita.

“Ke daga ina?” Malamar da take ajin su ta tambaye ta.

“Gida” ta faɗa a taƙaice.

“Yanzu ne lokacin zuwa makaranta?”

Tuni hawaye ya cika wa ummi ido, saboda tana tsoron duka ta ce “Mama ce bata nan, ba ta dawo ba”

“To kuma gidanku babu wanda zai ce ki taho makaranta da wuri? Kalli jikinki fa ko mai baki shafa ba, kamar wadda zata aikatau ba makaranta ba” ƴan ajin suka kwashe da dariya.

“Silent” malamar ta tsawatar tana kallon ƙafar ummi, da kamar an ciro ta daga haƙa rami, ummi kuwa gwanar kuka, ta kama ƙasan farin hijjabinta, tana goge hawaye.

“Wuce ki je ki zauna”

Ta nufi wurin zamanta, can wuri ɗaya, ta cigaba da sheshsheƙar kuka, tana jin muryar wani yaro, cikin murya ƙasa² yana cewa “Baƙar tukunya, yau an shafeta da toka”

Iya sam bata san makaranta ummi ta tafi ba, kawai sai nemanta ta yi ta rasa, hankalinta ya tashi, ta fito tana zagawa tana nemanta.

Ummi kuwa da ƙyar ta koma gida, saboda azabar yunwa, har wani jiri take yi, tana ta Addu’a Allah ya sa tana zuwa ga mama, sai dai kash, tsakar gidan nan fayau, ko shara bai gani ba, ta kalli wurin murhu da maman ke ɗora girki, shi ma babu komai a wurin, ta kalli ƙofar ɗakin su, ɗakin dai a rufe.

Ɗakin iya ta shiga, ta nemi wuri ta kwanta, ta fara kuka tana share hawaye, tana kiran sunan mama da baba.

Bacci ya ɗauke ta, sai dai hayaniyar iya ta tashe ta, “Dan ubanki ina ki ka je, ki ka tayar mini da hankali, nake ta yawon nemanki, lungu-lungu kamar akuya.

“Makaranta na je”

“Uwar makarantar, kin gaya mini zaki je?” Ummi ta girgiza kai.

“Kawai dan ki tayar mini da hankali, to ubanki ma bai ɗaga mini hankali ba, balle ke” ummi dai tayi shiru ba ta ce komai ba.

Iya ta gama zaginta tsaf, sannan ta bata abincin rana, sai dai ba dan zai isheta ba, haka ta ci.

Da yamma yarinyar da take tafiya da ita makarantar allo, na’ima, ta zo tafiya da ita, Naima ƴar ɗakin mariya ce, dan tana son ummi sosai, ita take tafiya da ita makarantar allo, kuma ta ji labarin mariya ta tafi, iya ta ƙwace ummi. Ta tarar da ummi a zaune tayi shiru, idonta duk hawaye.

“Iya na zo tafiya da ummi makaranta”

“Gata nan, sai kun dawo” iya tayi maganar tana nuna ummi a wulaƙance.

Naima ta tambayi iya kayan ummi, ta gaya mata in da suke, ta ga jiƙaƙƙun kaya a ciki.

Ta ce “Ummi, na ji kayan ki a jiƙe?”

“Fitsarin kwance na yi ban sani ba”

“To ki daina haɗa su da kayanki masu kyau, idan mun dawo daga makaranta, zan wanke musu”

Ummi ta saka mata kuka ta ce “Yaushe mama zata dawo?”

“Ki yi haƙuri, nima ban sani ba, amma za ta dawo” ta shirya ummi ta sakata a gaba suka tafi makaranta, tausayin ummi ya kama ta.

Kwana ɗaya kawai, mariya ji take yi tamkar ta taka da ƙafa, ta koma gagarawa, ta ɗaukko ƴar ta, duk sallar da tayi, bata iya addu’ar komai, sai roƙon Allah ya kula mata da ummi, Allah ya dawo mata da umminta.

A kwana a tashi mariya ta gama takaba, sai da tun bai fi watanni biyu da daowarta gida ba, ta fuskanci tana ɗauke da juna biyu, kuma ta ja bakinta ta yi shiru, ta din ga rashin lafiya, ba cin abinci, duk ta rame ta fita daga hayyacinta, maryam ta rakata asibiti, sai a lokacin da likita yake yi mata tambayoyi ta tabbatar musu da tana da ciki.

Da suka koma gida, aka din ga yi mata faɗa, saboda ya zama dole a sanar da dangin su bashir maganar juna biyun nan.

Watanni huɗu da barin ummi a hannun iya, Ummi ta gane shayi ruwa ne, dan duk da ba girma ne da ita ba, amma tafi samun sauƙi da sassauci, a lokacin da mariya tana nan.
Gashi son makaranta ya shiga ranta sosai da sosai, idan ta yi wa iya laifi, sai iya ta hanata abinci, da ƙyar take iya zuwa makaranta, sai dai da ka ganta a cikin uniform ɗin nan, ka san babu kulawa, da babu wanda ya kai ummi tsafta a makarantar, amma wataran idan ka ganta, kamar ta shekara babu wanka, a wannan shekarun, ita take wanka da kanta, idan gari babu sanyi sosai tayi wanka da ruwan buta, idan da sanyi taƙi yi, dan wataran ruwan kawai take zubawa a jikinta.

Man shafawa sai iya ta ga dama zata bata ta shafa, shi ma ba iya shafawar tayi ba, iya ta daina bata, wai tana yi mata ɓarnar mai.

Wanki kuwa, sai idan na’ima za ta yi nata, sannan ya ta haɗa da na ummin, tayi ta goge mata, idan ba haka ba kuwa, sai dai tayi ta yawo cikin dauɗa.

A wata ukun nan, ummi ta koma kamar rainon mahaukaciya, wannan uban gashin babu mai kula mata da shi, ga cin zali da yara suka cigaba da yi mata, tun ummi na saka ran dawowar mama, har ta haƙura.

Saboda sabo, da sassafe idan ta tashi, sai ta ɗauki tsintsiya ta share sashin, ko da kuwa ba zai fita ba, saboda haka mama take yi, ta wanke bakinta da gawayi, ta jiƙa jikinta da ruwa buta ɗaya.

Idan ba makaranta ta tafi ba, mutanen gidan wannan ya ja ya aika, wancan ya ja ya aika, kamar baiwa, masu aiken nata, wani lokacin idan sun yi abinci su bata, domin kuwa bata ƙoshi da wanda iya take bata.

Duk ranar da tayi kuskuren yi wa iya fitsarin kwance kuwa, ko wani laifin, sai ta kira idris, ta bashi bulala, ta tuɓe ummi, ta ce ya zane mata ita.

Ga shi ya cigaba da kawo mata farmaki, gashi ta yi girman da ba zai yiwu ya ɗauke ta ba, sai ya tsiro da salon aike, ya ce idan ta sayo ta kai masa ɗakin su.

Yau idris ya kasa jurewa, ya aiketa sayen omo, ta dawo ta tsaya tana raɓe-raɓe, cikin ikon Allah sai ga naima, suka yi kiciɓis da ummi a soro ta ce “Ummi, tun ɗazu nake jiranki, ina kallon yadda malam babba ya zane ki, saboda makara, amma shi ne baki taho ba”.

“Yaya idris ne ya aike ni sayen omo, ya ce na kai masa ɗakin su”.

“Ɗakin su kuma? Ina laifin ya ce ki kai wa babarsa, kuma ina sauran yaran gidan? To wallahi ko da wasa, kar ki kuskura wani a mazan gidan nan, ya aike ki ya ce ki kai masa ɗakinsa, ko wani wuri da mutane ko da kuwa zasu dake ki” ta waiwaya ta ga awwalu zai shiga sashin mazan ta karɓi omon ta ce “Kai auwwalu, ka kai wa idiris aiken da ya yi wa ummi, wuce muje ke kuma”

Suka tafi makaranta, ta saya wa ummi awara a hanya, da suka je ta zaunar da ita a makaranta ta bata ta ci.

Suna tafe a hanya naima na sake jaddadawa ummi, kar ta kuskura wani ya aiketa, ya ce ta kai masa ɗakinsa a samarin gidan.

Ta raka ummi har cikin gidan, tana shirin tafiya, Idris ya shigo yana yi wa naima bala’i.

“Wacece ke a wurinta, da har zan aiketa ki hana ta kai mini aike?”

Naima ta ce “kamar yaya, makaranta zamu tafi mun makara”

“Dole tare zaku tafi makarantar? Har in aike ta ki hanata kawo mini saƙona?”

“Amma dai da alama baka da gaskiya, ba dai an kai maka aiken ba, ya zaka din ga aiken yarinya ka ce ta kai maka ɗakin ka” nan da nan bala’i ya kaure abunka da gidan gandu, nan da nan aka taru, ya din ga kurarin zai yi mata dukan tsiya.

Iya ta hau naima da masifa, har da cewa kar ta sake shigowa, tun da sharri za ta yi wa idris.

Ita duk wannan abun ba shi ne damuwar ta ba, tausayin ummi take ji, ta kalli yadda ummin ta rakuɓe tana kuka.

Naima ta ce “Ba abun da zai sake shigo da ni in sha Allah, amma dai wallahi idris ka canza hali, mutumin banza kawai” iya ce ta hana shi, da cewa yayi sai ya zane naima.

Iya ta ce kowa ya watse, har ya nufi hanyar fita, ya dawo ya shaƙo ummi tare da luƙa mata wata irin ashar. Ƙara tayi tana kakari.

“Dan ubanki, daga yau idan na sake aikenki, ki ka biya wani wurin, ko kuma na sake ganinki da wannan yarinyar, sai na kashe ki” ya jefar da ita a wurin, ta riƙe wuya tana tari, wani irin yawu mai kauri na wahala, na zubowa daga bakinta, ta cire hijjabin makarantar ta tana gogewa, gashin kanta kuwa, kalba biyu ce tafi wata, ita ma naima ce tayi mata.

Mariya kuwa sallar magariba ake yi, kawai suka ga ta fito daga ɗaki, tana ƙoƙarin fita, mama wadda take matar babansu, ta riƙe ta, ta ce “Mariya lafiya ina zaki?”

“Mama kukan ummi nake ji, kamar tana ƙofar gida fa”

“Mariya ummi na jigawa, kina Maiduguri ta ina ki ka ji kukan nata?”

“Iya wai ba kya ji ne? Ni kukan ummi nake ji”

Mama ta ce “Iya kuma, nice fa mariya”

Mariya ta yi ƙuri da ido, tana kallon mama, sai yanzu ma ta dawo hayyacinta, gaba ɗaya ta kasa gane menene yake faruwa, bacci take ko idonta biyu, ita dai kamar kukan ummi kunnunwata suke jiye mata.

Ayshercool

CUTARWA

         BRIGHT PENS
        (FREE BATCH)

Shiru mariya ta yi, tana bin mama da kallo, jiki a sanyaye ta ce “Ki yi haƙuri, na zata gaske ne, magungunan da na sha ne, bacci ya ɗauke ni na ga ummi”

Mama ta ce “Mariya ki sassauta wa kanki a kan yarinyar nan, kar ki je ki haukace a banza fa”

Mariya ta amsa da “To”

“Ki din ga yi mata addu’a, Allah zai tsare miki ita” gyaɗa mata kai kawai ta yi, ta koma ɗaki.

Ummi kuwa ta ci kuka kamar babu gobe, saboda zafin shaƙar da ta sha.

Iya ta ritsuta a ɗaki tana tambayarta, ko wani abun take gayawa na’ima, ummi cikin kuka ta din ga girgiza mata kai, tana tsoron kar ta dake ta.

Har gari ya waye, tana jin wuyanta babu daɗi, ta yi wanka, ta sanya cukurkuɗaɗɗun uniform ɗin ta, dan ma an yi sa’a a wanke suke, dama na’ima da yamma ta ce zata yi musu guga, aka yi uwar watsi.

Iya bata kulata ba, dan haka ta yi sharar tsakar gida, ta ɗau kofinta, ta je sashin sa’adatu, da niyyar a bata kunu, sai dai ta tarar ta gama rabawa yaranta, suna sha zasu tafi makaranta.

Ta juyo da kofin a hannunta, tayi karo da magaji.

“Baki tafi makarantar ba ne?” Ta jinjina masa kai.

Ya kalli kofin hannunta, babu komai a ciki.

“Kunun ma baki samu ba? Iya bata baki ba?” Ta jinjina masa kai.

Ya karɓi kofin, ya shiga sashin su na maza, ya fito ya miƙa mata kunun cikin kofi.

Har ƙasa ta tsuguna ta karɓa, ta zauna a kan wani kututture, ta kafa kai ta din ga sha, saboda uwar yunwar da take ji.

Ta shanye ya karɓi kofin, ya bata naira ashirin, ta karɓa ta ce “An gode”

“Kiyi sauri ki tafi makaranta, kar su dake ki” ta ce “To”

Ta kamar hanya ta tafi, jin ta a ƙoshe da kunu ya sanya ta tafiya cikin nishaɗi.

Sai dai yau ma ta makara, a bakin gate discipline mistress ta fara zane ta, tare da ci mata mutunci saboda ƙazanta, jikinta bususu fuskarta duk busasshshen koko, ga sauran kwantsa a idonta.

Ta tafi aji tana kuka, saboda zafin bulala.

Ta je ta tarar ana yi musu darasi, ta buɗe jakarta da yanzu a baƙar leda take zuba su, duk sun zama shara da tarkace, fensirinta kuwa dama tsintar sa tayi, ya zama ɗan mitsitsi da ƙyar take iya riƙe shi ta yi rubutu.

Head master ya shigo ajin, duk suka tashi suka gaishe shi, yayi musu umarnin su zauna.

Ya dubi malamarsu ya ce “Malama, yara biyar zaki zaɓo mini masu ƙoƙari, zamu tafi da su gidan talabijin, za ayi wani shiri da su, a haska su”

Malamar ta ce “Ok sir, yanzu kuwa”

Ta tashi ta kira yara uku, ta huɗu ta kira sunan Salma Muhammad Bashir.

Wani irin farinciki ya kama ummi, saboda  malamarsu ta zaɓeta a cikin wanda za a tafi da su gidan talabijin na jigawa, tana ta murna za ta ganta a talabijin, dan duk da rashin kulawar nan, ummi tana da matuƙar ƙoƙari, in dai aka yi darasi a gabanta, to ta ɗauke.

“Ke!ke tsaya” headmaster ya dakatar da ita a tsakiyar aji.

“Wannan kuma ina zata?”

Malama ta ce “Sir, yarinyar na da ƙoƙari fa, ita ce take first position”

“A hakan, wannan yarinyar da ya take karatun,? Ba ita ake kora ba ba ta biyan kuɗin PTA, da yaya take iya karatun”

Ta ce “A haka, ita take ta ɗaya?”

“Kai canza wata dan Allah, haba wannan tayi muni da yawa, wannan ko an saka mata camera ai ba za a ganeta ba, baƙi ƙirin da ita haka, ji uniform ɗin ta fa, tubarkallah ni wannan tayi baƙi samo wata mai ɗan kyan gani, ke koma ki zauna ba za a tafi da ke ba, ji kayan jikinta kamar ƴar ci rani”
Tuntsirewa da dariya da yaran suka yi,hakan ya bawa hawayen idonta ƙwarin gwiwar zubowa, ta tafi lungun aji ta zauna, tana share hawayen.

Tana gani aka zaɓi wata daban, bayan malamar ta fita, suka ɗora da yi mata dariya da tsokanar ta, har da masu ja mata hijjabi, suna ƙazama ba ta wanka ba ta wanki, waƙar da aka saba yi mata a assembly idan an zo duban tsabta, har misali ake yi da ita, na ƙazamai.

Ana tashi ta fita daga aji, ta nufi gida har da gudunta, dan kar ma ƴan ajinsu su taso, su tireta a hanya, ta ƙarasa tana ta numfarfashi.

Sai da ta ɗan huta sannan ta shiga sashin su da sallama, muryar iya ta fara jiyo wa tana hayaniya, da muryar baba saminu, ba ta san dai faɗan me suke yi ba, ta kutsa kai ta shiga.

Wan mahaifiyarta ta gani, a zaune suna ta jayayya da su iya.

Hayaniyar da suke yi, ba ita ce ta dame ta ba, murnar ta Allah ya sa da mama suka dawo.

Bai lura da ummi ba, sai da ta riƙe hannunsa, ya waiwayo ya kalleta ta ce “Ina maman take?” Yayi ƙuri da ido yana kallon ummi, sai ka ce ba ƴar mutane ba.
Yadda mariya ke ƙalƙaleta, take kula da ita, amma ya ganta kamar an janyota daga ramin ƙasa.

Ya ce “Baki gaishe ni ba” ta tsuguna ƙasa ta ce “Ina kwana”

“Lafiya ƙalau, ya makarantar?”

Ta ce “Lafiya lau, to ina maman take?”

“Mama tana lafiya, ta ce; a gaishe ki”

Ummi ta sake kallonsa ta ce “To zaka kai ni wurinta?”

“Ke wuce ki je ki cire uniform, ki yi salla” Iya tayi mata tsawa. Yayi shiru ransa a matuƙar ɓace, bai taɓa tunanin ganin ummi a cikin wannan mummunan yanayin ba.

Ta fito kanta babu ɗan kwali, gashin nan a cukurkuɗe, sai soshe-soshe take yi, saboda yadda ya addaba mata da ƙaiƙayi.

Ya dubi iya ya ce “Shikenan, tun da kun ce cikin ba naku bane ba, baku san da shi ba, ni ba dan wani abun hannunku ya sanya muka zo muka sanar da akwai cikin ba, saboda a cika umarnin Ubangiji, amma tun da abun haka ne, Allah ya kyauta, mu mun ji mun gani, mun karɓa. Amma dan Allah ku bani ƴar ta in kai mata, mariya ta kasa zaune ta kasa tsaye, hankalinta yaƙi kwanciya, ku bata ƴar ta dan Allah”

“Ba rashin ummi ne ya hanata nutsuwa ba, mugun abun ta ne yake koma mata kanta, hakkina da na ɗa na ba zai taɓa barinta ba, ya din ga bibiyar ta kenan”

Ganin idan ya cigaba da zama, wannan jayayyar zata kai su ga maganar banza, ya sanya ya tashi tsam, ya ce “Shikenan babu laifi, Allah ya kyauta”

Jin ya ce zai tafi, ya sanya ummi fitowa da gudu daga ɗaki, ta ce “Ba zaka tafi da ni, ka kai ni wurin maman ba?”

Ya durƙusa ya shafa kanta ya ce “Ki yi haƙuri, in sha Allah nan gaba kaɗan, zaki koma wurin mamanki, Allah ya yi miki albarka” ya ciro kuɗi dubu biyar, ya bawa iya ya ce “Dan Allah a canza mata uniform, a saya mata wasu ƴan kayan buƙata”

Ba kunya iya ta amshe, tana harare-harare.

Ummi ta tsaya tabi bayansa da kallo har ya fice.

Dukan da aka yi mata a kanta ne, ya sanya ta dawowa hayyacinta, ta firgita ta kalli Iya.

“Duk wanda ya sake zuwa gidan nan, ki ka ce ya kai ki wurin uwarki, sai na saka idris ya zane miki jikinki, wato salon ace ba a kula da ke, saboda ƙwarewa a munafunci kin tsotsa a nono ko?” Tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa.

“Munafuka, ga muni ga kinibibi, tashi ki wanke kwanukan nan na safe” sumi-sumi ta nufi wurin tara kwanukan wanke wanke, ta haɗa ta fara wankewa.

*
Bayan sallar magariba, yaya garba ya je ya samu mahaifinsu ya sanar da shi cewa iya ta ce ba su san da ciki ba, dan haka a nemi ubansa.

Malam yayi shiru, lamarin ya girmame shi ya ce “Haka suka ce?”

“Wallahi, matar nan ba ta da mutunci ba ta da imani ko kaɗan, ba ka ga Yarinyar nan a halin da na baro bata ba, kamar ƴar jari bola saboda azabar datti da ƙazanta”

“Ƙyalesu, yarinya kullum muna yi mata addu’a, in sha Allah babu wanda zai sake bi ta kansu, ita kuma Allah ya raba ta da ciki lafiya”

Ya amsa masa da “Amin”

*
Na’ima kuwa ummi na ranta, amma babarta ta ce mata ba ita ba ummi, dan kakarta ba mutunci ne da ita ba, kar ta yi mata wani sharrin.

Sai dai ta kan ƙulle abinci wasu lokutan, ta tafi da shi makaranta ta bawa ummi.

Yanzu babu mai yi wa ummi wanki balle guga, dan haka dauɗa kamar ka kankarota a jikinta.

Ummi na iya ƙoƙarin ta wurin kaucewa haɗuwa da idiris, ga bala’in tsoronsa da take ji, saboda dukan da yake yi mata idan tayi laifi babu tausayi babu imani.

Allah ya taimake ta, wasu lokutan magaji na taka masa burki a kan wasu abubuwan.

Tsabar rashin gyara, ya sanya kwarkwata cika wa ummi gashi, kayan ta duk suka cukurkuɗe suka yi mata kaɗan, tana zaune har sakkowa kwarkwata suke yi daga kanta, suna bin ta, sai dai ta ɓuya tayi ta kashewa, ba ta son a gani.

Ga wasu irin manyan ƙuraje da suka din ga fitowa a cikin gashin kan nata, suna ɗurar ruwa, suka ƙara bawa kwarkwatar nan damar hayayyafa babu ji babu gani.

Banda zarnin fitsari da warin datti, babu abun da take yi, dan kuwa da kanta take yi wa kanta wankin kayanta, wando sai ya fi kwana uku a jikinta, ba ruwan iya balle ta ce cire ki wanke.

Sa’adatu ce babar auwwalu, ta fara lura da wannan ƙurajen na kan ummi, ta kamata ta buɗe kan, ta ga ƙazantar da take cikin gashin.

Ta nuna wa iya, Iya ta yamutse fuska ta ce “Taɓ gaskiya ba zan iya taɓa wannan kan ba, to gashi ne ba kaɗan ba, gaba ɗaya ba irin namu ba, kalar na mutanen ƙetare, shiyasa nake cewa anya ma kuwa tamun ce, duk zuriyar mu, babu irin wannan gashin, yanzu meye abun yi kar kan ya ruɓe ace ni ce ina kallonta, na bari ya ruɓe ji yadda wani mugun ruwa yake tsatstsafowa da ƙwayayen kwarkwata a ciki”.

“Aikuwa sai dai a aske kan nan, dan ban ga yadda za ayi maganin abun nan ba”

Cikin ƙyanƙyami, sa’adatu ta sauke wa ummi gashin nan tsaf, ta koma sai ka ce namiji, ga hudar kunnenta ma, tana ruwa saboda tsufan ɗan kunne a kunnenta, ba a taɓa cirewa ba.

Iya ta saka aka haɗa kanwa da gishiri, da omo aka wanke kan nan, ummi ta din ga wani irin masifaffen kuka, saboda azabar raɗaɗi, da bal’in zafi haka nan da ruwan sanyi aka tuɓe ta, aka wanketa a tsakar gidan, iya har tana cewa wannan baƙar fatar ba da dutsen goge faso za a wanketa ba kuwa?. Wata irin annakiyar dauɗa ta din ga zuba daga jikin yarinyar. Yara suka cika sashin danƙam suna kallon ummi, da tana ta ƙoƙarin rufe jikinta, amma azabar wahala da zafi ya sanya ta manta da tsiraicinta.

Ummi na ji na gani, aka ɗaure gashinta a leda kaya guda da shi aka zubar, iya ta ce a sakawa kan ummi fiya-fiya, idan ba haka ba, sauran ƙwan zai ƙyanƙyashe kansa.

Ba tare da tunanin wane hali zata shiga ba, suka shafe ƙwallon kan da suka saukewa sumarta da fiya-fiya, hakan ya sa ta din ga tari da atishawa, gaba ɗaya kanta ya juye, ta din ga jiri, kan dare zazzaɓi ya rufe ta da ciwon kai.

Ba wanda ya kula ya saya mata magani, haka ta kwana tana rawar sanyi, da ta yinƙura ta tashi, sai ta tafi luuu zata faɗi.

Da safe gwaggo ta bata, koko da ƙosai, sai dai ta kasa ci, ta cigaba da kwanciya tana burgima a ƙasa, kanta yana ciwo, ga tari da take ta faman yi.

Cikin barccin wahala, ummi ta ji wani ƙamshin turare mai daɗi, ta ji magana sama-sama kamar muryar babanta.

Da sauri ta buɗe ido, ta yi ƙuri da ido tana kallonsa, ga iya a gefe suna magana da shi.

Yayi murmushi ya ce “Uwata ta kaina, kin tashi? Ƙaraso mu gaisa” sai yanzu ta lura ba baba bane ba, mutumin nan ne mai kama da shi.

Tasowa ta yi da sauri, sai dai ta faɗi, saboda jirin da take ji.

Da sauri ya tashi, ya ce “Iya ba ta da lafiya ne?” Iya ta taɓe baki, mussaman jin ya kirata da uwassa ta kansa ta ce “Eh zazzaɓi take”.

“Subhanallah, kuma ba a kaita asibiti ba?”

Ya zaunar da ummi, ya sinsuna kanta ya ce “Ya na ji kamar kina warin fiya-fiya? Ya cire hular kanta, sai ga kai sol ba gashi, ga dagwalon gyambo a kan, ciwon duk yayi baƙi saboda fiya-fiya.

A razane ya ce “Meye wannan? Iya meya sameta a kanta?”

“Kwarkwata ce, da wasu ƙuraje, shi ne aka aske kan aka shafa mata fiya-fiya”

“Innalillahi wa Innalillahi raji’un, iya wannan ai ganganci ne, ina laifin a kaita asibiti, wannan ƙaramar yarinyar a saka mata fiya-fiya a ka, ai shi ya sanya mata zazzaɓi”.

“To ban da kai yahaya, ana ta abun da za a ci, waye yake ta wani asibiti, wa zai bayar da kuɗin kai ta wani asibiti?”

Miƙewa yayi ya ce “Wannan abun kunya da yawa yake”

Cak ya saɓa ummi a kafaɗarsa, yayi waje da ita, iya ta biyo shi tana tambayar ina zai kai ta?.

“Asibiti zan kai ta, idan ta mutu ba makawa ku ne ku ka kasheta” yayi waje da ita.

A mota ya kwantar da ita, ya ja suka tafi.

Sosai likitoci suka din ga faɗa, dan ma asibitin kuɗi ne, aka sake wanke kan ummi, da magunguna, aka saka mata ruwa saboda zazzaɓin da ya rufeta, take ta rawar sanyi.

Ya fita ya sayo kayan marmari, da ta farfaɗo zazzaɓin ya sauka, ya din ga bata da kansa.

“Kana kama da baba” ta faɗa a lokacin da zaƙin kankana ya ratsa kwanyarta, wanda rabon da ta sha har ta manta.

Yayi mata murmushi ya ce “Ai nima baba ne”

“Ai an ce baba ba zai dawo ba, ya mutu yana cikin kabari”.

“Haka ne mamana, kina yi masa addu’a ko?” Ta gyaɗa kai alamar eh.

“Yanzu me ki ke son na saya miki?”

“Littafi” ta bashi amsa.

“Littafin makaranta?” Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce “To shikenan, zan sai miki in sayo miki kifi ko nama, wanne zaki ci?”

“Nama” ta faɗa tana murmushi.

Yayi mata murmushi shi ma, ya ce “To bari su sallame mu, sai na saya miki mu tafi gida”

Har ummi ta ɗan murmuro, ya saya mata tsire a hanya, da babbar robar youghurt, ya sai mata litattafai, da sabuwar jakar makaranta. Babban abun da ya burgeta da shi, shi ne yadda take ta ce masa ta gode, a yanayin tattaunawar da yayi da ita, ya san baƙar azaba kawai take sha, bai ga dalilin da ya sanya iya riƙe ummi ba, kuma shi ma idan ya ce zai tafi da ita can gidansa, faɗa za suyi da Fauziyya matarsa, dan ya san ba zata karɓi ummi ba.

Gashi shi bai san a ina mahaifiyarta take a Maiduguri ba, dan lokacin da balarabe yayi aure, yana kudu karatu.

A mota ya sanya ummi ta ci, har ta ƙoshi, wani irin daɗi take ji, yau ta ci kayan daɗi, wataran tana kallo ake kawo wa Iya, bata sammata.

A ƙofar gidan yayi parking, ya buɗewa ummi ta fito, ya riƙo ledar maganinta, ya riƙe hannunta suka shiga cikin gidan.

“Baƙar randa, baƙin zunubi, an dawo jinsinmu na maza” Alhassan ya faɗa yana ƙyaƙyata dariya”.

Yahaya ya tsaya cak, ya kalle shi ya ce “Alhassan, wa ka ke cewa baƙin zunubi? Ummi ba ƙanwarka ba ce ba? Dan me zaku din ga aibata ta?”

Alhassan ya yi shiru ya sunkuyar da kai.

“Kai da ubanka na halitta, da zai halittoka da wannan kunnuwan kan kamar zomo na zikiri, ga ƙaton kai kamar marmara?”

Ya girgiza kai alamar a’a, nan yayi ta yi masa faɗa, ya shiga cikin gida nan ma ya ɗora, tare da yi wa iya ƙorafi a kan lallai ta sanya ido, a daina ci wa ummi zarafi, idan ba haka ba, zata dashi ba ta karsashi a cikin al’umma, saboda gudun kar a aibanta halittarta.

Jin sa kawai Iya take yi, amma ba dan ta ji zata iya hana wani aibata ummi ba, dan ita ma aibata tan take yi.

Yahaya ya kawo kuɗi ja bawa iya nata, kamar yadda ya saba yi mata alkhairi, ya sanya a ka kira masa magaji, ya bashi dubu goma ya ce “Ga dubu goma, dan Allah duk abun da Yarinyar nan take buƙata, ko na rashin lafiya, ko na makaranta ka cira ka saya mata, idan da damuwa zan rubuta lambar wayata, a kira ni a sanar da ni duk abun da take buƙata, zan biya.
Zumunci bai ce haka ba, mahaifinta ya rasu, an rabata da mahaifiyarta, kuma aƙi tsayawa a kula da ita, dan Allah a kula da marainiya”.

Hashim ya ce “Ina sha Allah kawu, za ayi duk abun da ya dace” ya dubi ummi ya ce “Sannu ummi”

Ta ce “Yauwwa”

Yahaya ya miƙe ya ce “To iya, sai wani lokacin kuma, ayi ta haƙuri, Allah ya rufa mana asiri”

Iya ta kwaɓe baki ta amsa da Amin.

Da sauri ummi ta riƙe rigarsa ta ce “Baba yaushe zaka dawo?”

“Da wuri in sha Allah ummi”.

“To ka ce ina gaishe da mama”

Ya kalli iya, iya ta kawar da kanta gefe, ya ce “Iya yakamata a sanya lokaci a kaita ta ga mahaifiyarta, bai kamata idan ma wani abu ne a tsakanin ku da mahaifiyarta ya shafe ta ba”

Iya ba dan ɗan abun duniyar da ya bata ba, da babu abun da zai hana, ta ɗura masa ashar. Sai dai ta yi masa shiru, ya ƙaraci maganarsa ya tafi.

Hashim ya tafi raka shi, suna tafe yana sake jaddada masa, dan Allah a kula da ummi, babu wanda yafi ƙarfin Allah ya jarrabe shi da irin abun da ya jarrabe ta.

Suka ɗan yi hira a kan karatun Hashim, yake gaya masa ai yayi jamb, ya ce duk yadda ake ciki, idan yana buƙatar wani taimako yayi masa magana.

Suka yi sallama ya dawo sashin Iya, sai dai fa iya nata jibgar ummi da kara, Idris na tsaye yana kallonsu.

Da sauri ya ƙarasa ya ƙwace ummi, ya ce “Iya daga asibiti fa aka dawo da yarinyar nan”

“A’a daga mutuware aka dawo da ita, duk yadda nake ƙoƙari a kan yarinyar nan, bata da wani buri da ya wuce ta tozarta ni, ta nunawa duniya azabtar da ita nake yi”

“To yanzu iya me tayi miki?”

“Ban sani ba, tun da makaho ne kai, baka gani, munafukar yarinya, wallahi duk ranar da wani ya kuma zuwa gidan nan, ki ka yi masa zancen uwarki, sai mai shirin tafiya kabari ya fiki kwanciyar hankali, sai na casa ki, shegiya mai idon munafukai”

Ummi ta cukuikuye rigar hashim tana kuka.

Iya ta kalli Hashim ta ce “Kai ma ɗaya munafukin, bani kuɗin da ya baka, ai ba ita kaɗai ce ƴa a gidan ba, kuma idan bayarwar ne, ai ni yakamata ya bawa”

Cikin takaici ya ce “Amma iya…

“Rufe mini baki, ka bani na ce kan na ɓata maka rai” ya ciro kuɗin ya ajiye mata, ya fice.

Ummi da sauri ita ma ta fita, jikinta na ciwo, ga zazzaɓi na sake son rufe ta.

Ta koma ƙofar gida, ta samu in da rana take da saura, ɗumin yana ratsata.

Auwwalu ya taho da tawagar abokansa, har ya wuce ta ya dawo ya ce “Yara baƙar randa ta koma baƙin namiji, aski aka yi mata fa”

Ɗaya daga cikin yaran ya ce “Haba dai”

Ya ce “Bari ku ga” ya tunkari ummi, yana zuwa ya fara ƙoƙarin ja mata hijjabi, ta rirriƙe hijjabin ta fara kuka.

Ƙarasawa yaran suka yi, suka taya shi, kasancewar maza ne, gashi ba ta da ƙwari ga rashin lafiya, suka kayar da ita, suka yage hijjabin.
Ta saka hannu bibbiyu ta rufe kanta, tana kiran mama.

Saboda mugunta irin ta yara, daga haka suka din ga kai mata duka a ka, wai sun ci ladan aski.

Suka tuburbuɗata a cikin ƙasa, duk ta kurje jikinta, kan da aka yi wa dressing, duk suka cika shi da ƙasa.

Mariya daga alhinin mutuwar miji da rabuwa da Ummi, mariya ta zarce da damuwa, ba ta hira ba ta walwala, sai dai kullum cikin wuni a ɗaki, duk lokacin da ta kwanta, ba ta da wani aiki sai mafarkin ummi, da kuma marigayin mijinta.
Asibiti da maryam ke kaita awo, suka ce da zarar ta fara naƙuda, a kai ta asibiti ta haihu a can, saboda hawan da jininta yayi.
Sai dai kusan kwanaki uku kenan, tan jin ciwo, kuma sai ta yi ta mafarkin gata ta haifi ummi tan jaririya, amma tayi shiru da bakinta, taƙi faɗa.

Mama ta shiga ɗakin, da niyyar tashin mariya ta yi salla, ta tarar da ita tana jijjiga, sai datse harshenta take yi, tana mimmiƙewa ga kuma haɗe da jini na fita daga bakinta.

Ayshercool

Series NavigationCutarwa part 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *