Furar Danko Hausa Novels

Furar Danko Chapter 6

This entry is part 6 of 6 in the series Furar Danko

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣

…….Shiru kawai yay yana kallon takarda da key ɗin motar da sakatariyarsa ta kawo masa na tsawon lokaci, kafin ya furzar da huci mai kauri ya tashi zaune sosai da ga kwanciyar da yay a kujerar office ɗin nasa. Wayarsa mai ƙyau da ɗaukar ido ya ɗauka. Har yay dailing number da akai saving da _Yaya Isma’il_ sai kuma ya katse yana ɗan girgiza kansa. Dan ya san halinsa, wani lokacin ba gane abubuwa yake ba birkitaccen mutum ne. Wata number ya sake lalubowa yay dialing, ring biyu aka ɗauka.

        “Uncle You.. Good Afternoon”.

Aka faɗa daga can, muryarsa a sauƙaƙe ya amsa da “Afternoon dear! How are you?”.

    “Am good Uncle”.

“Haka ake so. Lulu ta dawo ne?”.

   “Yes Uncle tun ma ɗazun. Sai dai tanata masifa wai Uncle Smart ya barta a airport. Amma Deen ya ce ta masa ihu ne a gaban mutane kuma bai mata komai ba kadai santa. Yanzu kuma Daddy ya goya da bayanta wai zata walaƙanta shi ta koreshi. Uncle ALLAH ni bana so sumasa haka, shi ɗin mutum ne nutsatstse”.

        Wani ɗan murmushin takaici yayi da gyada kansa kamar yana a gabansa. “Karka damu Son! bazan bari su aikata hakan ba insha ALLAHU. Kuma zai dawo aikinsa”.

    Sosai yaron ya shiga ihun murna daga can. Shi kuma ya katse wayar yana mai jin takaicin hali irin na ɗan uwansa. Yanda yake training rayuwar Mawaddat na ɓata masa rai. A rayuwa ko ɗa namiji ne bazakace komai ya nema sai ya samu ba duk arziƙinka da matsayinka. Balle mace da wataran aure zatayi ta koma ƙarƙashin ikon wani. Wanin da ba lallai shi ya iya ɗaukar waɗan nan ɗabi’un nata marasa ƙyau ba. Da wannan ɓacin ran yabar office ranar. Kai tsaye gidansa ya nufa dake anguwar ta Hotoro GRA shima. Sai dai ba street ɗin su ɗaya da gidan yayan nasa ba. Da gudu ƙyawawan yaransa guda uku masu kama da shi sukazo tarbarsa. Murmushi yayi cike da jin daɗi, gaba ɗaya ya haɗasu ya rungume a jikinsa bayan sun gaidashi. Yana ƙoƙarin miƙewa da ƙaramin Deen da sukaje ɗaukar Lulu airport mai wayon tsiya a hannunsa idonsa ya sauka akan matarsa. Ƙyakykyawar mace ƴar duma-duma. Murmushi ya sakar mata kamar yanda take masa itama, ya miƙa mata hannu alamar tazo itama. A hankali ta ƙaraso ta shige jikinsa, rungumeta yay da sumbatar goshinta kamar yanda ya saba. Ko’a jikin yaran dan sun saba ganin hakan ga iyayensu, basa aikata wani abu dazai lalata musu tarbiyyar yara, amma su tarbi juna yayin da wani yay ɗan nesa da gida kona yini guda ne sun nunama yaransu hakan ba komai bane face ƙauna, kuma ya halatta miji yayma matarsa, idan sunga hakan ko’a wani waje ba haramun bane ba. Shiyyasa suma yaran suke kallon hakan a normal ne.

        Da ƙyar ya samu ya gudarma Deen dake bashi labarin faɗan aunty Lulu a airport. Bayan yay wanka falon ya dawo ya zauna cikinsu yana shan fruit salad. Matarsa Saleeha da kowa ke kira da Aunty a family ɗin ta kallesa cikin damuwa da sauƙaƙa harshe. “Abul Mahsin kamar kana cikin damuwa? Wani abun ya sake faruwa ne a office ɗin?”.

      Ƙaramin tsaki yaja da ɗan girgiza kansa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya numfasa. “Mawaddat! Halin yarinyar nan nacimun rai matuƙa Sweetheart. Kullum maimakon abubuwan su dinga sauƙi tana hankali amma sake jagulewa yake. Abinda yafi ɓatan rai Yaya. Shi sam nunawa yake kamar ma komai yana tafiya daidai ne a rayuwar yarinyar. Safiyya ina tsoron UBANGIJI ya tuhumemu akan amanar da baiwar ALLAHr nan ta tafi tabar mana fa…”

       “Tabbas hakane, to amma ya zakayi tunda Yaya yana sama da kai ne. Ita kuma ɗabi’un sun riga sun shigeta tankwarata abune mafi wahala duk da ma kana iya bakin ƙoƙarinka tun bata kai haka ba. Amma babu abinda ya canja”.

     “A wannan karon ina son ya canja kota ƙarfi Saliha. Dan gaskiya na gaji da gani, bana son yarinyar nan ta kuma fi haka gagara…”

   “Tankwarawar ta ƙarfi kam akwai damuwa, dan shi icce tun yana ɗanye ake tankwarashi. Idan ya bushe akace za’ayi zai iya karyewa. Sai dai ni inada shawara. A yanda Deen ya bani labarin abinda ya faru tsakaninta da drivern nan nasan zasu ce zasu koresa ne, inaga karka bari hakan ta faru, inma da dama ya zama driver nata ita kaɗai, dan shi naga ba mutum ne mai wasa ba, ba kuma zai ɗauki halinta ba”.

        A hankali ya sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya furta, “Nagode miki dan tunaninmu yazo ɗaya. Sai dai magana ta gaskiya bamma san yanda zan tunkari yaron ba. Kedai kin san a yanda na samosa ai, aikin nan kuma yana yinsa ne saboda tsare mutuncinsa bawai irin sauran drivers nada bane da take takawa yanda take so. Sannan Aliyu yanada zuciya fiye da yanda kike tsammani da hasashe bar ganinsa hak shiru-shiru baya son magana”.

     “Duk ɗan halak dole ya kasance mai kishin kansa Abul Mahsin. Sannan wannan itace cikar kamalar duk wani ɗan adam na ƙwarai. Karka ƙasƙantar da kanka ga kowa ga komai saboda talauci, ka kasance mai tsaftatacciyar zuciya a baɗini da zahiri, ka kuma zama jarumi a neman na kanka koda duk jama’a na kallon hakan da faɗuwa. Ni nasan baka kawosa yay wannan aikin da ƙasƙanci ba, sai dan wani dalilinka da kuma kare mutuncinsa daga taɓarɓarewar abubuwan da ba’asan mafari ba a rayuwarsa. Kamar yanda kuka samu mahaifinsa a farko kai da Ahmad yanzu ma ku sake samunsa insha ALLAHU zai dawo ya cigaba har ALLAH shima ya kawo masa iyakar komai na jarabawarsa”.

      “Shike nan in sha ALLAHU zan gwada nagani. Ita kuma zuwa anjima zanje gidan na sameta”.

   “Hakan yayi, amma Please smile”. Ta faɗa tana kwatantawa da hannunta a kan baki. Hararta yay yana sakin murmushin…..

           ∆••••∆ ★ ∆••••∆

   Washe gari ma baiyi yunƙurin zuwa aiki ba, sai ma tunanin neman wata mafitar da ya tashi da shi. Kamar yanda ya saba bayan dawowa sallar asubahi ya shiga sashen mahaifinsu domin gaishesa duk da tare suka fita massalaci suka kuma dawo. Ƙyaƙyƙyawan dattijon mutum mai cike da tarin nutsuwa. Da ga gashin kansa har zuwa na gemu fari ne fat. Duk da tsufansa ya bayyana a kallo guda zaka tabbatar da zamanin ƙuruciya ansha ƙyau. Duk da ya ɗan ɗago ya dubesa a lokacin da yake shigowa bai ajiye littafin dake a hannunsa ba. Sai ma ɗan turɓune fuska da ya sake yi. Tsahon mintuna uku baida alamar kulashi, har sai da wasu samari biyu suka shigo, abin mamaki sai ga murmushi ya mamaye fuskar tashi, ya ajiye littafin cike da kulawa idonsa akan samarin dake gaishesa bayan sun ma Uncle Smart kallo ɗaya a gatsine sun ɗauke kai. Oho baima san sunai ba, dan basu isa masa a ido cikin ido ba.

       “Abba Barka da safiya”.

Suka faɗa kusan a tare. Cike da kulawa yake jinjina musu kansa. Ya amsa da “Har an shirya fita kasuwar? Ƴan albarka”.

     “Eh Abba”.

Suka bashi amsa suna miƙewa. Albarka ya shiga saka musu, suko tunda suka amsa sau ɗaya ma basu sake ba. Har zasu fice ya dakatar da su. Cikin ƴar damuwa yake kallonsu. “Nabeel yau kam da ban takuraku ba da kun bama iyayenku kuɗin cefane. Na tashi banda ko nera a jikina gashi babu hanyar samuwarsu garan a yau”.

      A turɓune wanda aka kira da Nabeel ke dubansa. Bakinsa a sama ya ce, “Abba kafa san abubuwan sai a hankali. Kuɗin cefanen gidan nan inba kaiba kuma wazai iya. Sannan jiya fa sai da kasa na baka dubu biyu”.

     “Nima ai sai da na bashi dubu ɗaya”.

   Ɗayan ya amshe da sauri shima rai ɓace. Ɗan murmushi Abban yayi, yayinda Uncle Smart kejin wani irin raɗaɗin zantukansu ga mahaifinsu akan abinda bai taka kara ya karya ba. Mahaifinsu jarumin ubane da ya tsaya a kansu da ƙare ƙarfinsa wajen gina rayuwarsu. Amma yau sun zama wani abu kowa najin ƙyashin taimaka masa. Ɗari biyar-biyar suka ajiye masa saɓanin abinda ya tambaya suka fice rai ɓace. Gaba ɗaya sai yaji jikinsa ya ƙara sanyi, cikin ƙarfin hali ya fara gaida Abban dake sake ƙoƙarin ɗaukar littafinsa bayan ya kwashe dubu ɗayan da suka ajiye masa. Maimakon amsa masa gaisuwar a zafafe ya ce, “Shima wannan aikin sun korekan?”.

    Kasa amsawa yayi ya ƙara ƙasa da kansa zuciyarsa na ƙuna. Ba’a kan ƙaddararsa ba, ba kuma akan abinda mahaifinsa ke tuhumarsa ba, sai akan damuwa da halin da mahaifin nasu ke ciki….

      “Wai halan bada Ali nake magana ba?!”.

   Ya faɗa cikin fusata. 

“Kayi haƙuri Abba dama….”

“Dama mi? Mi kake son faɗamin? To wlhy bari kaji a wannan karon bazan ɗauka iskancinka ba. Bari ma na faɗa maka gaskiya in har maganar banzarka ce da ka saba to a wannan karon ka shirya barmun gida, dan bazan iya cigaba da wahala da kai ba bayan wadda nayi kana yaro. Na ciyar da kai abinci, na tufatar da kai sutura, na sakaka a makaranta islamiyya data boko har matakin digiri na biyu sannan na cigaba da wahala da kai. Ga kanenka nan na bayan baya sun tsaya da ƙafafunsu harda masu aure amma kai ban daina cidaka abinci ba, wannan wace irin rayuwa ce. To ba asiri ba a wannan karon ko kukar bulukiya aka sauke a kanka bazan ɗauka ba na gaji da shashancin ka, tashi ka ficemin daga nan na baka zuwa dare wlhy ka tsara mai yuwuwa sakarai kawai cima zaune”.

         Idanunsa da suka kaɗa sukai jazur ya ɗago kaɗan ya subesa. “Kayi haƙuri Abba ALLAH ya huci zuciyarka, dan ALLAH ka gafarce ni”.

    Banza ya masa bai sake tankawa ba. Yasan minene shiru a wajen mahaifin nasu. Dan haka ya miƙe ransa a matuƙar ƙuntace ya fice. Har ya nufi hanyar sashensu na samari ya fasa. Ƙirjinsa zafi yake masa. Ji yake kamar ya saki kuka amma bazai iyaba saboda taurin zuciyar tsiyarsa. Sosai mutane ke kai kawo a cikin layin nasu. A halin da yake ciki baya buƙatar yin magana da kowa, dan haka yay ƙoƙarin juyawa zai koma ciki. Daga motar da tun fitowarsa idonsa ya sauka a kanta amma ya kauda kai aka danno masa horn. Ƙin juyawa yay har sai da aka sake na biyu da ambaton sunansa. Cak ya tsaya amma bai juyo ba har Uncle Yousuf da abokinsa Ahmad suka ƙaraso garesa.

       “Kayi haƙuri”.

    Kalmar data tilastashi juyowa da ga bakin Uncle Yousuf……….✍️

_Alhmdullah, mungode da haƙurinku. Bari muga a fara ko kaɗan-kaɗan kafin na murmure. Mungode sosai da addu’oin ku🙏._

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣

………Hannu ya basu batare da ya yarda ya kallesu ba. Uncle Yousuf yay murmushi da amsar hannun sukai musabaha bayan ya gaisa da Ahamd dake ƴar dariya saboda harar da Uncle Smart ɗin ke masa ƙasa-ƙasa.

        “Idan ban takura da yawa ba ina son muyi magana Please Smart Mawashi”.

     Karan farko ya ɗan ɗago idanunsa da har yanzu suke da damuwa ya dubi Uncle Yousuf mai maganar. Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru. Uncle Yousuf ya sake murmusawa da faɗin, “Please”.

        Bashi da yanda ya iya dole ya amince masa, sai dai maimakon cikin motarsa da ya buƙata suje anan cikin soron gidansu suka zauna saman bench. Shiru na wasu mintuna kafin Uncle Yousuf ya nisa. “Jiya na dawo na samu takarda da key ɗin mota a hanun sakatariyata Aliyu, sai dai ban gamsu da bayanin dana gani a rubuce ba shiyyasa nace Ahmad ya rakoni nazo da kaina”. Ya ƙare maganar idonsa a kansa alamar son jin amsa.

       “Na ajiye aikin ne kawai”.

   Ya faɗa cikin dakewarsa.

“Ko miyasa?”.

Ahmad ya tambaya cikin kafesa da idanu.

Kansa ya jinjina yana ɗan furzar da iska, sai kuma ya dubu Uncle Yousuf maimakon Ahmad da yay tambayar. “Saboda bazan iya ba Alhaji. Ni mutum ne da ba komai zuciyata ke iya ɗauka ba duk da na kasance talaka mai nema.”

      “Haka ake so duk mutum na ƙwarai ya kasance Aliyu Hydar. Amma har yanzu baka faɗa mana dalilin ba?”.

    Murmushi ya saki mai ciwo a karo na farko. Ya ɗan dubi Uncle Yousuf ɗin sai kuma ya ɗauke kai. “Miye amfanin maimaita abinda bashi da muhimmanci koya wuce Alhaji. Kawai na ajiye shikenan ya wuce. Nasan insha ALLAHU zaku sami wanda ya fini, ni kuma zan tara gaba maybe abincina ba’a nan yake ba”.

         “Nasan bazaka juraba kamar na baya da suka shuɗe domin Kanada banbanci da su. Sai dai irinka na jima ina fata ni kuma, dan kai kaɗaine zaka iya da ita har ma ka tankwarata. Har yanzu nasan baka san ni wanene ba Aliyu Hydar, sai dai ka sani ban nema kamin wannan aikin ba dan kana buƙatar aikin da kuɗi zai shigo maka. Tun randa na ganka wajen abokina yayan abokinka Ahmad naji a raina ka cancanta zama wani ɓangare da zai jagoranci haska wata fitila ta rayuwarta. Ita ɗin a fanɗare take, tabbas a haka ta tashi shiyyasa tanƙwarata yayma kowa wahala a cikinmu. Ada kallon komai muke a bigire na ƙuruciya da tunanin wata rana zata daina, sai dai ranar har yanzu taƙi tazo, bamu san kuma ranar da zata zo ba, ko kuma tazo ne ta wuce batare da mun farga ba oho?. Nasan kana da ƙanni mata maybe ma harda yayu, kasan irin zafin da nakeji a raina koda a kwatance ka kwatanta da ace sune, miyasa bazaka gane ba ne….?”

      Yanda ya ƙare maganar a raunane cikin sigar tambaya yasa Uncle Smart fesar da iska mai nauyi. A ɗan zafafe batare daya dubesu ba yace, “In dai har ku da kuka haifeta kun gagara tanƙwarata ni kuma taya kuke tunanin iyawa? Mahaifinta fa na raye, hakama mahaifiyarta, sannan gaku ku ƴan uwanta, Alhaji Please kayi haƙuri bazan iya ba fa. Bana son raini, bana iya jurarsa ga kowa. Bana son wulaƙanci ko ƙasƙanci duk da kasancewata talaka mai nema. Ina ganin kimarka dan ALLAH karka bari mu shiga wata hanya daba ita ta dace mukai ba dan alkairi ya haɗamu kuma bazan taɓa na manta da kai ba, dan kamun abinda mutane da yawa basu minba na alkairi ka gaida gida”.

       Yana gama faɗa ya miƙe. Dakatar da shi Ahmad yayi, kamar bazai tsaya ba sai kuma ya dakata tare da juyowa. Miƙewa shima Uncle Yousuf ɗin yayi yana ɗan murmushi. Hannu ya kai ya dafa kafaɗarsa, “Shike nan na fahimceka kuma nagode sosai. Ina son mutum irinka mai tsayawa akan ra’ayinsa da riƙe mutuncinsa. Zan jima inajin raɗaɗin rabuwa da kai Aliyu. Amma dan ALLAH ina roƙon alfarmar kazo office ko zuwa gobe ne domin amsar hakkinka, kuma bana son kace da ni a’a”.

        Baki ya buɗe zai yi magana Ahmad ya dakatar da shi. “Dan ALLAH karkace a’a Smart, ban sanka da musu ba karka fara akan Yaya Yousuf, sannan kayi nazari akan roƙon da yay maka, nasan kanada damar taimakons…..”.

     Hararar da ya ɗan ballama Ahmad ɗin ce ta sashi yin ƙaramar dariya batare da ya ƙarasa ba. Ɗauke idanunsa yay da faɗin, “Shike nan insha ALLAHU idan na samu lokaci zanje, amma kai ma kasan kawai dai dan ta Yaya boss ne wlhy”.

        “Na sani Mawashi. Yaya boss kuma na godiya da wannan karamci”. Bai ce komai ba, sai murmushi da Uncle Yousuf dake saurarensu yayi. Har cikin rai ɗabi’un yaron birgesa sukeyi matuƙa. Yana son ganin mutum mai nutsuwa musamman matashi kamar haka. Ba irin matasan yanzu da shegen rawar kai yayma mafi yawansu katutu ba…

     Har mota ya musu rakiya. Bayan wucewarsu sai yaji ya kasa komawa cikin gidansu dan baisan da wane irin harshe zaima Ammah bayani akan sake rasa wannan aikin ba shima, duk da dai jikinsa yay ɗan sanyi da kalaman Ahmad na ƙarshe, amma dai bai yanke hukunci ba na sake amsar aikin har yanzu. Sai dai in ya tuno bayanin Abba ya kanji faɗuwar gaba. Tabbas yasan wanene Abbansu, sam baya magana biyu. Mutum ne tsayayye da idan yace e to e ɗinne da har ransa. Idan kuma yace a’a to a’a ɗin ce fa. Da ƙafa yabar cikin anguwar tasu, rashin abunyi da sanin ina zai dosa ya sashi miƙewa a titi yay ta tafiyarsa kawai. Yayi tafiya mai nisa da bai san ina yake jefa ƙafa da ɗaukewa ba ya fahimci kamar binsa akeyi a baya. Tsamm yayi na tsarguwa tare da tsayawa, sai dai abin mamaki babu alamar wani tare da shi a ƙafa, wanda ke a kan mashina ma da napep babu alama, hakama na mota. Dakewa yay ya cigaba da tafiyar, still dai ya sake jin tabbas akwai mai binsan. Yanzu kam bai juyo ba sai ya yanke titin ya shiga cikin wani layi, ya ɗan yi nisa da layin sosai ya samu rumfar wasu masu kayan kafinta ya ɗan dakata cikin dabara kamar mai gyara igiyar takalmi. Ta cikin mirror da aka jingine ya hango wasu samari biyu, sai dai suna ɗan waskewa cikin ɓadda kama. Hakan ya ɗan bashi mamaki, dan shi dai a rayuwa duk da yana da tsatstsauran ra’ayi bashi da abokin faɗa. Cigaba yay da tafiyar dan son gane iya gudun ruwansu badan yasan sirrikan layukan inda yake ba. Sai da sukaje ƙarshen layin sosai ya fahimci akwai matsala, ya ɗan ji wani abu a ransa amma sai ya dake, wata hanyar da yake ƙyautata zaton zata ɓillesa da titi ya bi, sai dai yana shan kwanar tsukin wajen suka sami nasarar rufesa ruf ata gaba da bayansa. Ɗaya bayan ɗaya ya bisu da kallo har ya sauke akan napep ɗin da aka faka a gabansa. Cikin dakewa da ambaton sunan ALLAH ya ce, “Ku kuma fa?”.

     “Zaka sani amma ba’a nan ba”.

Ɗaya ya bashi amsa cikin gatse da nuna masa bindiga dake soke a ƙugunsa. Bindiga bata kasance abar wasa ga kowa ba. Duk ƙarfinka da taurin kai a duk inda mai ita ya kasance shike zama a saman ƙarfin ikon ka. Dan haka ya shiga napep ɗin zuciyarsa na saƙa masa abubuwa masu yawa game da mutanen. Biyun da suka dinga binsa ne kawai suka shiga gefe-da-gefensa, mai napep yaja suka fice daga layin, sai da suka fita gaba ɗaya wanda ke gefen haggunsa ya jefa masa wani ƙyalle a fuska, da sauri na kusa da shi ya kama ya ɗaure masa idanu yayinda wanda ya fara jefa ƙyallen ya ɗora masa bindiga a gefen ciki ta yanda bai isa musawa ba. Duk da ya sake firgita haka ya dake a zahirance, a baɗini kuwa yana mai ambaton sunan ALLAH……

    Tofa, su kuma waɗan nan daga ina?. Wayyo Uncle Smart ɗinmu😫😢

          ∆••••∆ ★ ∆••••∆

   Tun daga main falour na gidan kana iya jiyo tashin sautin kiɗan dake fitowa da ga ɗakinta, duk da kiɗane mai taushi na mawaƙiya Shakira yanda ta ƙure voluen yasa ake iya jiyowa. Tun safe babu wanda zai ce ya ganta yau a gidan har zuwa yanzu da agogo ke nuna ƙarfe takwas da wasu mintuna. Mafi yawan yaran rai a ɓace suke fitowa daga ɗakunan su dan sautin kiɗan data saka ya takurasu da hanasu barcin safen. Hatta da ƙananun Suhaib da Imran da fita makaranta kan hakanasu barcin safen ji suke ta takura musu, musamman Imran dake son ƙarasa Assagment ɗinsa amma ya gagara fahimtar komai. Kaf ɗinsu sun gama hallara a dining, sai dai fuskar kowanne a turɓune da takaici. A haka Daddy da Mommy suka fito suka samesu, a kallo ɗaya zaka fahimci itama Momy ranta a ɓace yake, sai dai shi Daddy kam ko’a jikinsa. Yaran ma na gaidashi bai wani saurarensu ba hankalinsa nakan kiran Tabawa mai aiki. Da ɗan gudu-gudu ta fito a kitchen hannunta riƙe da ƙaramin ludayi da alama girki takeyi.

       “Babyna fa?”.

Ya faɗa kai tsaye yana nuna upstairs. Itama upstairs ɗin ta kalla, cikin sake rissinawa tace, “Barci takeyi Alhaji, tace zuwa ƙarfe tara da rabi na tadata”.

     “Shi kuma wancan kiɗan da ga ina?”.

“Itace ta kunna”.

Nunin ta tafi kawai ya mata batare da ya sake cewa komai ba. Mommy da tai kicin-kicin da fuska ya kalla, sai kuma yabi sauran yaran nasa da kallo. Hafiz dake ƙoƙarin kai shayi bakinsa wanda a haihuwa shike bima Lulu ne ya ce, “Humm Daddy yanzu bazakace komai ba kenan?”.

    “Akan me?”.

“Aunty Lu. Ai ko kafiri ba kowa ke iya saka kiɗa ya kwanta da shi ba. Kuma ina da tabbacin ko sallar asuba batayi b…..”

     “Kai ban san shashanci da ƙazafin banza, wai Hafiz ita ɗin sa’arka ce? Kuma kai ubanwa yace maka batai sallar ba”. 

    “Ai ba sai wani ya faɗa masa ba abinda kowa ya sani ne. Ni ban san wane irin makahon so kakema Mawaddat ba a gidan nan, kuma ka sani wannan ba gata bane kashe mata rayuwa kakeyi matsayinta na mace. Da haka kowace yarinya ake rainonta a gidansu da baka gammu haka ka aura ba matsayin iyayensu Alhaji. Dan ALLAH ya kake so nayi da raina akan Mawaddat ne?”.

       Wani banzan kallo ya galla mata ita da yaran baki ɗaya yana cika da batsewa, sanin yanzu zasuyi sama ya sata miƙewa tabar dining area ɗin zuciyarta na ƙuna da raɗaɗi. Ta rasa mike damun mijin nata akan babbar ƴarsu mace, yana nuna mata ƙazamar rayuwa a matsayin soyayya, iya bakin ƙoƙarinta tana yi akan Mawaddat amma abubuwa sake taɓarɓarewa sukeyi. A hankali hawaye masu raɗaɗi suka silalo mata saman kumatu………✍️

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣

……..A can falo kam tashin Mommy dai-dai da shigowar Uncle Yousuf, da murna yaran suka tarbesa. Sai dai ganinsa kamar rai ɓace yasa jikinsu sanyi. Abba da shima idonsa ke kansa ya baro dining ɗin ya nufosa. Kusa da shi ya zauna idanunsa a kansa ɗan uwansa, yana son ɗan ƙanin nasa namiji ɗaya tilo da ya rage masa a duniya.

    “Anya lafiya kake cika kana batsewa haka?”. Ya faɗa cikin kulawa da dafa kafaɗarsa. A hankali yace, “Ba komai. Sai kuma ya kai dubansa ga sashen Lulu. “Wannan kiɗan fa?”. Shima Daddyn kallon saman yayi, sai kuma yay ɗan murmushi da faɗin “Kaima ka sani sai dai ƴar gidanka ai”.

        Komai Uncle Yousuf bai sake cewa ba, sai rumtse idanu da yay cikin takaicin yayan nasa. Kusan mintuna biyu kafin ya buɗe, “Yaya mika yanke akan yaron dana kawo?”.

     Murmushi Daddy yay mai bayyana haƙwara. Ya ɗan bigi kafaɗarsa cikin sigar zolaya ya ce, “C-mon magajin baba saki fuskar mana, ni idan kana wannan cikar sai naga kamar baba ne ya dawo fa”.

        Baki Uncle Yousuf ya tura masa kamar mai shirin yin shagwaɓe fuska. Sai kuma ya kauda kansa saboda murmushin da ke son kufce masa. Sam baya iya dogon fushi da ɗan uwan nasa. Shima Daddyn murmushi ya sake saki da faɗin, “Yauwa ko kai fa. Yanzu kamun bayani yanda zan gane. Wane yaro kake magana a kai?”.

     A taƙaice ya ce, “Driver”.

  “Okay ni babu abinda na yanke. Dan Babyn ka har yanzu tace tana buƙatarsa ai”.

    “Shi kuma baya buƙatarmu dan ya ajiye aiki”.

         “Wannan ra’ayinsa ne ai. Idan itama ta haƙura sai a nema mata wani ba damuwa bane”.

    Wani shegen takaici ne ya sake kume Uncle Yousuf. Shi bai san wane irin mutum bane yayansa. Sam bai damu da damuwar kowa ba sai kansa da su ahalinsa. Kai kawai ya jinjina yana miƙewa. Daddy dake binsa da kallo ya ce, “Badai wucewa ba?”.

    “Yaya to mizan zauna nayi kuma. Ina son dai ka sake tunani a wannan gaɓar. Domin duk a yanda muke kallon rayuwa da ɗaukarta yaya watarana sai ta tsere mana ta ɗakko wasunmu a madadinmu. Zata iya yuwuwa kuma ta ɗakko waɗanda muke kallo ba kowa ba su kasance a saman tamu damar”.

          “Hakane Auta, sai dai ban san dalilin wannan gugar zanar ba”.

    Murmushi Uncle Yousuf yay mai ciwo. “Nasan ka sani Yaya, duk da ni ba gugar zana nake maka ba. Sai dai akan Mawaddat kana rumtse idanunka da kunnuwanka domin ƙin amsar gaskiya”. Daga haka ya nufi part ɗin nata. Yanda yake haɗa ɗan steps ɗin shiga sashen da bibbiyu zai baka tabbacin ransa a ɓace yake. Sai da ya rumtse ido lokacin daya ɗaura hannunsa kan handle ɗin ƙofar ɗakin nata. Batare da ya yarda ya kalla ɓangaren da gadonta yake ba ya nufi kayan kiɗan ya kashe. Kafin cikin daka tsawa ya ambaci sunanta. A firgice ta tashi tana mai yaye ƙaton lallausan bargon data jibgama kanta. Gaba ɗaya gashin kanta madaidaici a tsaho ya wani hargitse, sanye take da wando da riga na pyjamas farare tas masu santsi da ƙyalli. Kasancewar sun mata bujin-bujin yasa basu bayyana mata surar jiki ba. Ya ɗan samu nutsuwar ganinta da kayan mutunci, dan haka ya kalleta cikin ido babu wasa a tattare da shi ya ce, “Kinyi sallah?”.

        Tana son Uncle Yousuf matuƙa dan shima yana sonta da mata gata. Sai dai kuma baya wasa akan tarbiyyarta da gyara lamarinta shiyyasa take tsoronsa idan ya birkice, dan yasha kwasa mata mari mai gigitarwa. Akwai wani lokaci da ƙawaye suka yaudareta suka sakata dawowa gida a wani yanayi da ga club da ya ɗauketa da wani mahaukacin mari sai da ta yini jinta bai dawo ba. Tuni kuma ta watsakke daga makuwar da tayi…..

        “I say kinyi salla?!!”.

     Ya sake maimaitawa a tsawace fiye da farko. Daburcewa tai ta ɗaga masa kai ta kuma girgiza. Sai kuma ta sauka da gudu a gadon kamar wata ƙaramar yarinya ta nufi toilet ɗin ta. A cikin mintunan da basu gaza biyu ba ta fito fuska da ƙafafu jiƙe da ruwa wai tayi alwala. Abin salla da Tabawa ke faman ajiya a ma’ajiyarsa kamar na ado dan ba sallar take ba sai randa taso ta ɗauka ta shimfiɗa. Akan kayan barcin ta zumbula hijjabin da shima dai baida banbanci da kayan decorations na gida gareta. Uncle Yousuf na daga inda yake tsaye har yanzu cikin ƙunar rai. Fara sallar da bata da fasali balle makama da gamata ba’a ƙulla mintuna biyu cikakku ba. Hankalin Uncle Yousuf ya ƙara tashi. Dan yau ne karan farko da ya fahimci Mawaddat bata iya ko salla a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. “Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un” ya shiga maimaitawa jikinsa na tsuma. Baima san sanda ya kai zaune jagwab cikin kujerar kusa da shi ba. Yanzu nan kamar Mawaddat mai shekara ɗai-ɗai har ashirin da huɗu tana cikin ta biyar, mai karatun matsayin cikakkiyar lauya da duk wanda ta tsayama a shari’a zai iya alfahari da itace babu wata ƙyaƙyƙyawar alaƙa tsakaninta da UBANGIJINTA a ɓangaren bauta masa irin haka. Wane irin sakaci sukan sukai da shagala akan al’amarin yarinyar nan har haka?…..

        “Uncle You! please kayi haƙuri kar kai fushi da ni”.

    Kalamanta cikin damuwa suka katse masa tunani. Tuni ta rarrafo gabansa ma hijjab ɗin na harɗeta batare da ya sani ba. Idanu kawai ya zuba mata dan shi kam tausayi ma take bashi wlhy. Shi mutum ne mai zafi amma kuma yana da saurin sauka da kuma sauƙin kai shiyyasa yaran ɗan uwan nasa ke sonsa, dan ya taso ne kamar duk shi ya raine su. A hankali ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. Muryarshi a rissine bakamar ɗazun ba ya ce, “Mawaddatan-wa’rahmah!”.

        A hankali ta ce, “Yes Uncle”.

   “Mi kikayi haka?”.

“Uncle salla mana da kace”.

“Bani nace ba ALLAH ne yace ayi kuma ba haka akeyi ba. Mawaddat wannan ranar ita nake gudun zuwa gareki shiyyasa nake zaneki idan kikaƙi zama Islamiyya a shekarun baya kafin abar ƙasar nan da ke, shiyyasa kuma na dage a nema miki malamin da zai koyar da ke addini bayan Yaya ya maidaki can. Yanzu ace kamarki, ɗiyan musulmi hausawa ƴar ƙasar Nigeria a arewa amma baki iya salla ba? Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un. Mawaddat da duk mi kike yi ke kuwa a duniyar nan haka? Mi kikaima kanki tanadi na tunkarar UBANGIJI da har kikejin ƙwarin gwiwar baje kolinki a duniya da abinda ke cikinta kawai? Anya kin yarda zaki mutu kuwa? Za ki kuma kwanta kabari? Za kuma a tasheki? Za’a kuma miki hisabi sannan ki ƙarɓi sakamakon makomarki?. Makomar da gida biyune kacal dole kuma ka tsinta kanka a ɗaya wuta ko aljanna………”

       “Uncle Please kabar zancen mutuwan nan mana. Badai sallan bane kuma nayi. Kaga inama da zuwa court zuwa ten ga shi har nine na neman wucewa.”

    “Wato shi zancen sallan baida muhimmanci ko?”.

    “Noo Uncle You! Bance ba fa. Kawai dai ni…..”

    Sai kuma tai shiru. Kansa kawai ya girgiza dan y fahimci ba irin wannan zaman na kai tsaye Mawaddat ke buƙata ba. Yana buƙatar yin nazari akan al’amurinta kafin ya nemo mafita mai ɓullewa. Da hannu yay mata nunin ta tashi da faɗin, “Okay jeki shirya”.

     “Yawwa Sweet Papa na!!!”.

Ta faɗa da ihu tana miƙewa. Kansa kawai ya girgiza yana mai karanto mata addu’ar shiriya wajen UBANGIJI kamar yanda ya saba akoda yaushe ya tashi ya fice dan bata damar yin shirin….

         ∆•••∆ ★ ∆•••∆

    Da ƙyar ya iya buɗe idanunsa da sukai masa tsananin nauyi ya fara bin inda yake da kallo. Falo ne babba mai ɗauke da kaya na alfarma. Sai garadan samari guda biyu dake tsaye a kansa da alama sune suka ajiyesa a wajen. Akan mutumin dake zaune cikin kujera mai zaman mutum ɗaya ya tsaida idanun nasa. Shima kallonsa yake yi. Fuska ya ƙara tsukewa tare da kauda kansa, babu alamar tsoro tattare da shi ya ce, “Su waye ku? Mi nakeyi anan?”.

      A karo na farko mutumin yay murmushi har ana iya jin sautinsa. Kansa ya jinjina da faɗin, “Abinda duk aka faɗamin game da kai naga fiye ma da hakan. Sanin ni wanene gareka baida amfani. Abinda ya kawoka nan kuwa shine aiki. Idan kaso zaka iya ɗaukarsa a business ɗin da zaka ƙaru kaima, idan kuma kai tunanin bijirewa ko cigaba da wannan zafin kan naka to komai zai iya faruwa. Sunanka shine *_Aliyu M. Idris Mawashi._* Mata huɗu ne a gidanku ƴaƴa talatin da biyu. Mahaifiyarka itace ta farko a wajen babanka, ku biyar ta haifa ɗaya ya rasu. Kai kaɗaine namiji biyu sunyi aure kanada kanne mata biyu yanzu haka Maryam da Asma’u. Yanzu haka suna a ajin karshe a sakadire, islamiyya suna ajin hadda. Babbar yayarka na auren Alhaji Abubakar Azare itace amaryarsa. Bata sonshi mahaifinku ya haɗasu, yaranta biyu duk maza. Kanwarka dake bimaka tana auren abokinka Sa’id Ibrahim, yarinyarta ɗaya da ciki. Kana cikin matsanancin rayuwa sosai akan al’amuranka daba sai nayi zaman lissafasu ba ka sansu kaima”.

       “Daka sanni har kamar haka, amfanin mi zai maka?”. Uncle Smart ya faɗa cikin zafin rai.

   Ƙaramar dariya mutumin yayi yana wani ɗage kafaɗa. “Amfani masu yawa kuwa, ciki harda abinda zuciyarka bata kawo maka ba. Dan duk wanda na buƙaci alaƙa da shi dole ne ya amince min. Inba haka ba zai fuskanci abinda babu shi a lissafin rayuwarsa. Idan kuma ya amince lafiya zamuyi mu gama cikin mutunta juna na ƙaru ya ƙaru”.

      “Sai kuma gashi ni ba’aimun barazana?”.

    “Ba barazana nake makaba nima. Ina faɗa maka abinda zan iya yine koda a yanzu ne da kake gabana. Aliyu Mawashi! Ko nace Smart Mawashi ni bana faɗar abinda bazan yi ba. Idan na faɗa maka zanyi to na gama shirya yanda zanyi ɗin ne. Ka kwantar da hankalinka aikin da zakamun bamai wahala bane ba, sannan kaima zaka fita a ƙangin damuwar rashin abunyi da kake a ciki, maybe ma ka tsallake ƙasar nan insha ALLAHU a wannan karon ka samu cikar burinka. Mahaifiyarka ta samu kwanciyar hankali da samun salamar hantara daga kishiyoyi da miji, rayuwar ƙannenka ta inganta kamar yanda kake fata. Mahaifinka ya cire zargin da yake maka da fifita ƴan uwanka a samanka duk da bawata tsiya suma suke tsinana masa ba…..”

      “Waye kai?”………✍️

*_Ku ƙara haƙuri dani dan ALLAH. Idan na ɓalle typing har sai kunce ya isa haka in sha ALLAHU🙏😩_*

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 9️⃣

……..Dariya sosai Alhajin ya kwashe da shi. “Karka damu da sanin ni wanene saboda nasan kai waye? Sanin aikin da zakai min kawai ne yafi muhimmanci. Dan na sanka fiye da yanda na faɗa maka a yanzu. Kaɗan na tsinkulo a sanin danai maka kawai. Gidan daka ajiye aiki nake so ka koma ka cigaba da min aiki. Duk wata zan baka albashin naira dubu hamsin bayan albashin da su suke baka dubu ashirin”. Ya ajiye masa wani envelope gabansa da cigaba da faɗin, “Wannan shine kundin ayyukan da zakamin a gidan Alhaji Isma’il Jiƙamshi. Zan iya baka dama ta kwana ɗaya kaje kayi tunani, sai dai ka sani ko’a cikin ɗakinka idanuna a kanka suke, dan haka da zuciyarka kawai nake buƙatar kayi nazari. A duk sanda nake buƙatar magana da kai zan nemeka tanan” ya ajiye masa waya akan envelope ɗin daya ajiye gabansa. “A yanzu bana buƙatar cewarka anan, kaje kayi nazarin na barka lafiya. Ku maidashi”. Ya ƙare maganar da duban yaransa cikin bada umarni

       Da wani irin kallo mai nuna tsananin zafin zuciya Uncle Smart ya bisa. Sai dai da alama ran ƴan maza ya ɓaci dan ya kasa furata komai…..

        Kamar yanda Alhajin ya bada umarni sun maidoshi har kan titin anguwarsu. Kasancewar magrib yayi a gurguje ya ƙarasa gida domin watsama jikinsa da yay nauyi ruwa. Ya samu wasu daga cikin samarin ƙannensa sun dawo gidan. Wanda ya samu a waje suka gaishesa. Da hannu ya amsa musu kawai ya shige ɗakinsa. Shi mutum ne mai tsafta sosai da ƙwanƙonin tsiya, dan haka ganin ɗakin a yanda ya barsa ya sashi jan tsuki yana ɗan dafe kansa dake masa ciwo. Har yanzu abinda suka shaƙa masa bai gama sakin masa jiki ba. A karan farko ya laluba aljihunsa neman wayarsa, cikin sa’a ya jita. Ƙanwarsa Maryam ya kira, suna zaune a falo suna karatun Alkur’ani kiran ya shigo, cike da zumuɗi Asma’u da wayar ke’a gefenta ta ce, “Lah Yaya ne”. Kallonta Ammi da Maryam ɗin duk sukayi, ita kuma ta ɗaga da sallama. A hankali ya amsa mata cikin muryarshin nan a dake da wasu ke fassarawa da girman kai da suke kallonsa da shi saboda shiru-shirunsa, batare daya bata damar cewa wani abu ba ya cigaba da faɗin, “Zan samu ruwan zafi a wajenku?”.

       “Eh Yaya”.

Ta amsa masa cike da girmamawa. Tana ajiye wayar Maryam tace, “Ya dawo ne?”. Kai ta ɗaga mata da faɗin, “Ya dawo, cayay na kai masa ruwan zafi, inaga wanka zaiyi”. A hankali Ammi ta sauke ajiyar zuciya, sai dai batace da su komai ba ta cigaba da laziminta. Tun safe hankalinsu ke’a tashe, dan bai shiga gidan gaishesu ba kamar yanda ya saba. Da farko Ammi tayi zaton koya fita wani uziri ne, sai da ta shiga gaida Abba ya yanka mata baƙar magana son ransa, kamar yanda ta saba yin shiru akan ƴaƴanta idan yana faɗa haka yanzu ma ta haɗiye, sai da ya gama ta bashi haƙuri, sai dai furucinsa akan zai bar masa gida ya matuƙar tayar mata hankali, har ta aika Maryam kira mata shi ko yana ɗaki amma suka samu baya nan ɗakin ma a buɗe, neman number sa ta shiga yi amma sai ba’a ɗaga ba, daga ƙarshe ma ta daina samunsa. Da wannan damuwar ta yini yau ita dasu Asma’un.

        Koda Asma’u takai masa ruwan zafin sai da ta gyaro masa toilet sannan ya shiga, ɗakin ta shiga kimtsa masa shima. Kafin ya fito harta kammala ta fice. Kasancewar anyi sallar magriba yay tashi a ɗaki sannan ya fice massalaci yin isha’i. Bayan an idar gidan ya sake komawa. Abba bai shigoba, dan haka ya wuce cikin gidan. Kamar yanda ya saba sai da yabi duk ɗakunan matan gidan ya gaidasu. Da ɗakin Aunty Amarya ya fara. Mace ce mai yawan fara’a da son mutane, sai dai kuma bata da yawan magana itama. Duk da zai iya sa’anni da ita hakan bai hanashi girmamata saboda yanda take girmama Ammi a gidan itama kamar ba kishiya ba. Ya gaidata cikin mutuntawa, ta amsa masa da kulawa. Yaranta dake sabgogin gabansu a falon tun shigowarsa duk suka nutsu dama. Duk sun gaidashi, yayinda ƙaramar tazo jikinsa tana kawo masa ƙarar ɗan uwanta dake bima babbar ɗakin nasu cewar ya karya mata pencil ɗinta tana homework. Da sauri yaron mai suna Abbas ya ce, “Yayanmu ƙarya take ita ta karya abunta a makaranta suna faɗa da Ameer. Kuka ta saka itama tana faɗin, “Ƙaryane Yaya shine”. Hannu ya ɗaga musu duk sukai shiru. Aunty Amarya tace, “Ai inba ubansu kaci ba Yayansu ba barin kunnen mutane ya huta zasuyi ba. Tun ɗazu suke rikicin nan ni harna gaji ma da magana”.

      Faɗa yama yaran cikin sigar nasiha, yace da safe kafin su wuce makaranta Anisan tazo ɗakinsa ta amshi sabon pencil. Da ga haka ya fito zuwa ɗakin Umma. Itace ta biyu a gidan, amma itace mai manyan ƴaƴa a sakamakon rashin samun haihuwa da Ammah bataiba da wuri, kusan duk sunyi aure kuma. Sai dai tanada sauran ƴammata biyu a yanzu haka da samari biyu da basuyi aure ba. Ta amsa masa a ɗan fisge, bai damuba dan hakan ba sabon abu bane a garesa. Nusaiba autarta dake gefenta zaune tana cin abinci ta gaidashi itama. Amsa mata yayi yana miƙewa. Dakatar da shi Umman tayi da faɗin, “Yau lafiya kuwa bamu ganka da safe ba?”.

    Ɗan murmushin ƙarfin hali yay mata da faɗin. “Ba komai Umma na fitane da safe sosai wani uziri”.

     “Uhhm to yayi”. Ta faɗa a taƙaice.

     Iska ya ɗan furzar da ga bakinsa kawai ya miƙe yana ficewa. Ɗakin Mama ya nufa, mace ta uku a gidan, sai dai ya samu tana sashen Abba dan itace da girki yau. Mansur ƙaninsa ɗanta na huɗu kawai ya samu a falon da yarinyar ƙanwarsu (jikar gidan) tana barci a kujera. Gaishesa Mansur ɗin yayi yana wani nannoƙe kai na rashin kunya, sai dai babu damar yi dan suna tsoronsa a gidan ba kamar sauran yayunsu maza da suke iyama rashin kunya ba. Amsa masa yayi yana kallon askin kansa na rashin tarbiyya.

      “Idan na wayi gari na ganka da wannan askin bisa kai kayi kuka da kanka”. Daga haka ya fice. Baki Mansur ya tura gaba yana ƙunƙuni da yarfa hannuwa. Sai dai babu damar yi da ƙarfi.

      Ammah na zaune su Maryam a gefensa suna cin abinci da kallo film ya shiga da sallama. A tare suka amsa masa da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa yana kaiwa zaune. Ammah ya gaida da bata haƙurin rashin shigowarsa da safe. Dai-dai nan Maryam ta ajiye masa abinci da fure weter. Ɗakinsu suka shige da abincin dan sun san akwai magana a bakin Ammah. Suna shigewa kuwa ta dubesa da ɗauke kai ta ce, “Lafiya ka fita tunda safe?”.

       Samun kansa yay da faɗin, “Lafiya lau Ammah naje wajen aiki ne”.

        A hankali ta sauke numfashi. “Nasan ba son aikin nan kake ba Hydar. Sai dai mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa. Kafi kowa sanin yanda gidan nan ya koma yanzu, miyasa bazaka sakama kanka haƙuri da mutane ba ka karɓi rayuwa a duk yanda tazo maka. Kowane bawa daka gani akwai irin tashi ƙaddarar, amsarta da haƙuri kuma shine mizanin imani. Zuwa yanzu yakamata ace kun bar mahaifinku ya huta dako ciyar da kune, shekarunsa yaja yana buƙatar hutu na rayuwa dana jiki. Yasha matuƙar ɗawainiya da ku tun kuna ƙanana har girmanku, bai tauye kowannenku ga ilimi ba da ci da sha da kula da lafiyarku har girmanku. A yanzu kune ya kamata ace kun rungumesa shima tare da ƙannenku da suka rage a gabanmu, dan wataran kune zaku maye gurbinmu garesu a yayin da ƙasa ta rufe idanunmu”.

        Gaba ɗaya jikinsa ya ƙarayin sanyi da nasihar mahaifiyar tasa. Idanunsa sun kada sunyi ja, cikin gyaɗa kai da tausasa harshe ya ce, “Inasha ALLAHU Ammah zaki sameni fiye da yanda kike buƙata. Kuyita haƙuri damu kuma kuci gaba da mana addu’a”.

    “Addu’a kullum cikin yimuku muke babu fashi”.

    Sun cigaba da hira da mahaifiyarsa da ƙanensa da suka fito ya nuna musu assagment har zuwa ƙarfe tara da kusan rabi sannan ya fito. Ɗakinsa ya koma dan yasan yanzu Abba ya riga ya kwanta. Sai da yay shafa’i da wutiri ya samu kwantawa, abinda ya faru a yinin ya shiga dawo masa dalla-dalla. Envelope ɗin nan ya ɗakko ya fara dubawa. Takarda ce kawai a cikinsa ɗauke da rubutu mai ɗan tsaho, abubuwan da aka rubuta ɗin ya matuƙar bashi mamaki harma ya rasa wane kalar tunani zaiyi a kai. Shi dai har yanzu babu abinda zai iya ƙaraswa akan Jiƙamshi family na ƙwarai ko akasinsa. In ma akwai abinda zai iya faɗa to maybe akan wannan ballagazar yarinyar ne ta jiya, siririn tsaki yaja saboda tunota da yayi. Takardar ya yasar gefe ya kwanta yana mai lumshe idanunsa dake cike da barci……

        Washe gari da abubuwa da yawa ya tashi a cikin rai. Mafi girman jagorantar ƙarfin gwiwar sa nasihar Ammah, sai kuma wani dalili nasa akan mutumin jiya da son sanin manufarsa ta haƙiƙa, dan yasan in ma bai amshi aikin ba zai iya saka wani yay masa, shiko duk da bai gama sanin suwaye Uncle Yousuf ɗin ba sai yaji bazai iya sakacin barin ƙofar da za’a cuta musu ba har sai yasan gaskiya a kansu. ƙarfe bakwai da kwata a gidan Uncle Yousuf ɗin yay masa. Yana zaune a gate wajen maigadinsu suna ƴar hira kasancewar mutumin Dattijo ne nutsatstse mai aikinsu ta kawo breakfast. Cikin girmamawa ta gaidashi shi da maigadin. Hannu kawai ya ɗaga mata ya ɗauke kansa. Harta juya zata koma maigadi ya tsayar da ita da tambayar Alhaji ya fito ne?.

      “A’a nadai ji aunty na batun tadoshi an kirata a waya wannan masifaffiyar aunty Lu suke kiranta ko ta gidan Alhaji Babba bata da lafiy…..”

    Bata gama rufe baki ba sai gashi ya fito kamar a ɗan rikice. Tun daga nesa ya ƙwalama maigadi kiran ya buɗe masa gate. Miƙewa maigadin yay da hanzarinsa, hakan yasa Uncle Smart ɗin shima miƙewar ya nufesa. Ganin yanda ya daburce yama kasa tantance motar da ya ɗakkoma key yay masa sallama. Juyowa yay ya ɗan kallesa, har ya ɗauke kai sai kuma ya sake jiyowa.

      “Alhamdullah” ya faɗa yana miƙo masa key ɗin batare daya tuna cewa yanzu fa ba ƙarƙashin su yake ba. Babu musu ya amsa key ɗin, dannawa yay motar tai ƙara, dan haka ya nufeta. Sai da ya dai-daita ta sannan, yana batun fitowa ya buɗe masa yaga ya buɗe gaban motar ya shiga yana faɗin, “Yi sauri Please da alama abun babbane, dan duk ciwon Mawaddat da zai iya saka Aunty Kareema ruɗewa irin haka ba ƙarami bane ba”.

         Gudu kawai ya ƙara batare da yace komai ba dan ba fahimtar akan wa ake maganar yay ba shi dai. Bawani nisane tsakaninsu ba, dan layinne kawai ba ɗaya ba………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 🔟

……..Ko parking bai gama yi da ƙyau ba Uncle Yousuf ɗin ya fice, ba’a rufe mintuna biyar cikakku ba sai gashi ya fito ɗauke da Lulu yaran gidan biye da shi cikin tashin hankali. Shi ya buɗe masa motar, sai lokacin ma yasan itace. Wani iri yaji a ransa musamman tuna abinda akace game da ita a takardar jiya da Alhajin nan ya bashi. Da wannan tunanin yaja motar suka fice a gidan. Kai tsaye wani babban p-hospital mai suna *_SHIRA’S HOSPITAL_* suka nufa. Yanda aka tarbesu zai tabbatar maka da an san da su. Har yay zamansa a mota sai kuma ya fita yabi bayansu, dai-dai nan suma ƴan gidansu da suka biyo bayan su motarsu ta iso cikin asibitin.

       Duk wani kai kawo da ake a kanta shi dai nashi ido ne. Yayinda acan ƙasan zuciyarsa yaketa tufƙa da warwara akan abubuwa da dama. Musamman akan abinda ya dawo da shi aiki cikin wannan family ɗin a karo na biyu. Tabbas ya amshi aiki, sai dai kuma bada manufar wanda ya bashi aikin ba. Dan ko kaɗan baiji wani kurari daga gargaɗinsa sun tsoratashi ba. Hasalima shi wanda ya bashi aikin da yasan shi ɗin wanene maybe dabai bashi ɗin ba. Amma zaiyi, dan in bai amsa ba zai bama wani da zai iya masa yanda yake so… Ringing ɗin wayarsa ne ya katse masa tunani, ya ciro wayar daga aljihu yana miƙewa ya fito. Sallama yay bayan yakai wayar kunnensa, daga haka bai sake magana ba sai saurare. Bayan ya katse kiran ya cire wayar a kunnensa yana furzar da iska kaɗan. Cike da iya nazari yake bin farfajiyar asibitin da kallo a kaikaice, can idonsa ya sauka akan abinda yake nema. Basarwa yay ya share na wasu mintuna, kafin ya nufi fita gate ɗin a nutse. Dai-dai inda almajirai ke zaman bara ya dakata, naira ɗari biyu dake aljihunsa ya ciro ya saka a kwanon barar wani gurgun almajiri dake kan katako mai tayu, almajirin ya shiga jera masa addu’a. Yana ƙoƙarin juyawa matashin saurayin dake gefensa kaɗan yazo ta gefensa suka bangaji juna, kallon juna sukai kamar cikin jin haushi. Sai dai shi saurayin yay saurin faɗin, “Yi haƙuri abokina ban lura bane ba”. Kai kawai ya kaɗa masa yabar wajen batare daya tanka ba.

      Maimakon komawa cikin asibitin sai ya samu waje a harabar ya zauna abinsa, can kusan mintuna uku yay ƙoƙarin ciro wayarsa a aljihu sai yaji takardar da saurayin nan ya saƙala masa a aljihu sanda sukai karo batare da ya lura ba. Zarota yay ya warware cike da mamaki, sai kuma ya shiga ɗan waige-waige amma babu alamar saurayin ko wani da zai ce hankalinsa a kansa yake.

        _“Ni kamar iska nake, a duk lokacin data kaɗa sai anji sautinta a dukkan ƙofofin gashi na jiki. Idan kuma nai shirin zuwa waje matsayin guguwa tarwatsa komai da kowa na gari nake hatta ruwan kogi baya tsira da ga mamayata. Ka kula, in ba hakaba ni na ƙulleka a cikin ƙullina Aliyu Hydar Mawashi”_.

     Wani irin tashi tsigar jikinsa ta farayi na ɓacin rai. A take zuciyarsa ta fara kaikawo da sauri-sauri cikin ƙirjinsa. Takardar ya ninke ya maida aljihu, yana batun tashi waya ta sake yin ringing a jikinsa. Wayar dai da Alhaji nan ne ya bashi jiya, yana kuma ƙyautata zaton takardar nan ma da ga garesa take duk da ya kirashi ne ɗazun a wayarsa. Shi sam yama manta da wayar. Cirota yayi daga aljihun, kamar bazai ɗaga ba sai kuma miya tuna ya ɗaga tana gab da tsinkewa ya kai kunne. Baiyi magana ba daga can ma akai shiru, ganin ana neman shafe minti guda ya katse shirun da faɗin, “Inada abinyi fa Malam”.

     Ƙaramar dariya akai daga can tare da faɗin, “Wannan girman kan naka da gizago kesani ƙara jin ka dace da buƙatar aikina Smart Mawashi. Mutanena sun sanar min ka koma aiki, weldone daka kasance mai biyayya irin haka da saurin gane abu….”

           “Na koma ne badan kurarinka ko farfagandarka ba! Ko a tunaninka sakawa ana bibiyata da kawomin wasu banzayen saƙwanni a takarda ko kiran wayata zaisa nayi abinda kake so?”.

    Ya faɗa cikin katseshi murya a dake. Dariya akayi da ga can, Alhaji ya ce, “Muɗauka haka ɗinne to. Sai dai ka sani ni samaniya ne mai rufe rufin kowanne gida da daji. Abinda kaga ya faru har ya kawoku asibiti yau ka ɗauka shine signing na contract ɗinmu da kai. Ya rage naka ka fara aiwatar da ayyukanka yanda ya dace ko kai kuskuren nunamin zafin kai na cigaba da nuna maka sauran kalolina. Dan a duk inda Jiƙamshi family suke ni nan da kake ji da gani zagaye nake da su har a cikin ɗakin kwanansu, har ma da kai kanka a yanzu….”

     Baki ya buɗe zai yi magana ƙittt aka yanke wayar, da sauri ya cirota daga kunnensa, ƙoƙarin kiran layin ya shigayi sai dai yaƙi shiga, ya koma wajen massage danya tura sai ya gama babu app na massage a wayar kwata-kwata. Cikin tsarguwa ya ɗan fara dube-dube, sai dai babu alamar wani da hankalinsa ke a kansa a eriya ɗin wajen gaba ɗaya. Wayarsa ya ciro ya kwashe number da zummar yin kira sai dai kuma taƙi shiga, wadda aka kirashi a farko ya gwada kira itama taƙi shiga. Yay ɗan shiru ransa a dagule, tunanin kiran wani abokinsa yay da zummar masa tracing layukan sai kuma ya fasa saboda tuna maganar mutumin. (A duk inda kake idanuna a kanka suke koda a cikin ɗakin barcinka ne). Fasawa yay ya maida wayar aljihu yana jin zuciyarsa ta masa nauyi da tunani kala daban-daban. 

        Gaba ɗaya wannan yinin haka ahalin Jiƙamshi gaba ɗaya suka yisa a asibitin tare da shi. Bai yi yinƙurin komai akan son sanin abinda ke damunta ba. Yana dai biye da motsin kowa har zuwa azhar da Uncle Yousuf ya buƙaci ya kaishi gida zai ɗan watsa ruwa. Sai da suka hau hanya yake tambayarsa ya mai jiki. Cikin damuwa Uncle Yousuf ya ɗan furzar da nannauyar ajiyar zuciya tare da dafe kansa ya ce, “Da sauƙi za’ace, dan tunda muka zo sai yanzu ne aka samu kanta har barci ya ɗauketa. Shiyyasa nake son a yau mubar ƙasar nan dan ban taɓa ganin Muwaddat a cikin halin ciwo mai tsananin irin wannan ba. Ban san mi yarinyar ke son maida kanta ba, ban taɓa tunanin rashin jinta ya kai haka ba sai yau, yanzu doctor ya ɗan fara min bayanin wai shaye-shaye ne ke son jawo mata matsala, ban san wane irin rayuwa yarinyar nan take son kai kantaba kuma. Amma duk laifin Yaya ne da ke nuna mata ƙazamin gatan da shi a gurinshi yake ɗauka so ne…” yaja tsaki mai nuna tsananin ƙunar da zuciyarsa ke masa. Da gani kasan yana jin zafi ne a ransa har yake furta abinda bai kamata ya furta a gaban driver kamarsa ba. Sai dai shi kansa ya matuƙar girgiza dajin kalaman Uncle Yousuf ɗin. A ransa faɗi yake (No wander idanunta sam babu kunya da mutunci a cikinsu ashe ƴar shaye-shaye ce) wani irin tsanarta yaji ta sake ɗarsuwa a ransa, ashe bayan ballagazanci harda shaye-shaye. Da ƙyar ya iya furta ma Uncle Yousuf cewar “ALLAH dai ya bata lafiya Alhaji. Sai dai addu’a, a wannan zamanin yara mata da yawa suna cikin wannan mummunar ɗabi’ar ta shaye-shaye, wasu samari ke ɗorasu wasu ƙawaye, wasu matsin rayuwa maimakon suyi tawakkali da haƙuri su maida al’amarin su ga UBANGIJI sai su zaɓi wannan hanyar mara ɓillewa. Wasu ko tsabar gata ne da jin daɗin duniya ke kwasarsu. Sai dai fatan ALLAH ya shiryesu ya kare wanda kuma basu fara ba dan abin tashin hankalin harda matan aure ma yanzu”.

         Cikin tsananin damuwa Uncle Yousuf yace, “ALLAH ka shiryar mana da su. Kayi mana maganin duk wasu azzalumai dake safarar mugayen abubuwan nan zuwa ƙasashenmu suna ɓata mana yara”.

     “Amin ya rabbi”.

Ya amsa masa dai-dai yana shiga layin gidan Uncle Yousuf ɗin…..

        ★A ranar bai samu damar zaman yin magana da Uncle Yousuf kan batun dawowarsa aiki ba. Dan yana shiga yay wanka sake fitowa yay suka koma asibitin. Zuwa yanzu kam ta samu barci kamar yanda yaji ƴan uwan na faɗama Uncle Yousuf. Sai a lokacin ya samu damar gaisawa da Daddy daya iso yanzu da ga Abuja da Mommy ya jajanta musu. Cikin ƙarfin hali Daddy ya ce, “Kamar yaron nan daka kawo ne kace kuma ya ajiye aiki jiya Yousuf?”.

       Kai tsaye Uncle Yousuf ɗin ya ce, “Shine Yaya. Sai dai banyi magana da shi ba dai bayan wadda nace maka nayi, amma inaga ya dawo aikinsa ne”.

       Daddy ya ɗan ja numfashi da faɗin, “Dama Baby batace bata buƙatarsa ba ai. Amma mu jira har ALLAH ya bata lafiya sai muji ta bakinta dai”.

     “Uhum”

Kawai Uncle Yousuf yace. Mommy ma dai dake jinsu batace komai ba sai ma ɗauke kanta tai gefe dan haushin mijin nata akan ƴarsu da zata iya rantsuwa da ƙazamar soyayyar da yake matane duk ya zama silar komai na halin da take ciki a yanzu. Duk da dai basu ji komai da ga bayanin likita ba amma yanzu zasuje garesa suji ɗin. Su duka ukun suka nufi office ɗin Doctor Khalil Shira………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣1️⃣

……..Nagartaccen likita nutsatstse da ya san makamar aikinsa. Cikin girmamawa ya gaida Mommy da Daddy, Uncle Yousuf kuma ya bashi hannu sukai musabaha dan zasu iya zama sa’anni. Kusan mintuna uku ya nisa yana mai gyara gilashin idanunsa da ɗagowa ya ɗan kallesu. “A ɗazun mun ɗan fara magana da Yousuf wani hanzari ya katseni, shiyyasa na buƙaci ganinku ku duka saboda muhimmancin abinda zan faɗa game da lafiyar Muwaddat”.

        “Doctor ALLAH dai yasa ba wani mummunan ciwo bane, idan kasan akwai matsala dan ALLAH ka barmu mu wuce da ita ƙetare kar sai al’amarin ya ƙwace azo ana wallahi tallahi zuciyarmu bazata iya ɗauka ba”.

          “Ka kwantar da hankalinka Alhaji, bawai matsalar zamanta anan ko fitar da ita zuwa ƙasar waje ne damuwar ba. Sanadin abinda ya haddasa mata ciwon nake son ku sani domin a ɗauki mataki….”

     “Minene likita?”.

  Daddy ya sake faɗa a zabure cikin katse Dr Khalifa Shira.

            “Kwantar da hankalinka Alhaji”. Khalifa ya faɗa yana sake gyara zama. Cigaba yay da faɗin, “Ina son ku fahimci maganata da idon basira duk da ban sani ba ko kun san halin da take ciki kafin yau ɗin. Bincikemu ya nuna mana ba komai ya haddasa mata matsalar da take ciki ba yanzu sai Shaye-shaye..”

      “What?!!”.

Daddy ya faɗa yana miƙewa zumbur. Jikinsa har rawa yake wajen nuna Dr Khalil Shira. “Yarinyar tawa zakaima sharri, miya haɗa wata Muwaddat da shaye-shaye? Yarinyar da bata san komai ba sai karatunta. Amma kai dai wlhy anyi…….”

      “Yaya Please ka bari ya faɗa mana abinda ke faruwa mana. A wannan zamanin har wani gardama ko shaidar yaranmu za’ai akan hakan”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin damuwa da takaicin Daddy. Mommy ma kallonsa take cikin tashin hankali da ɓacin rai, duk da ba itace ta haifi Muwaddat da cikinta ba bazata so ace yarinyar ta lalace kamar haka ba. Tasha wahala a hannun mijinta akan mahaifiyar Muwaddat matuƙa, bayan rasuwarta kuma tabar baya da ƙura dan Daddy wani sabon shafin wulaƙanci ya buɗe akan al’amarin Muwaddat gareta….

      Bayanin da likita ya fara ne ya katse mata tunaninta. Dr Khalifa Shira ya cigaba da faɗin, “Alhaji a wannan zamanin da muke ciki wannan ba abin mamaki bane. Yara mata da yawa sun shiga wannan mummunar aƙidar abin tashin hankali harda matan aure ma. Iya gaskiyata na faɗa muku Muwaddat na shaye-shaye, kuma da alama ta jima a cikin wannan al’amarin dan gashi har ya fara taɓa mata lafiyarta. Idan kuma har bata dainaba komai zai iya faruwa ciki harda rasata. Ya dace kusa ido akanta da duk wani motsinta na rayuwa, idan da dama ma a nisantata da komai cikin hikima, sannan a rabata da duk abokan mu’amalarta akan hakan harma da inda take zuwa ta shawo dan alamu sun nunamin baku san tanayi ba. Iyaye da yawa sunfi maida hankali da damuwa akan kar ƴaƴansu mata su lalace wajen zubar da mutuncinsu akan huɗubar maza (zina), a tunaninsu wannan itace kawai matsalar dake iya tauye mace ko fanɗarar da tarbiyyarta. Shiyyasa sai yaran har suyi nisa a lalacewar da basu jawoma kansu tunaninta ba misali irin wannan ta shaye-shaye daketa ƙara yawaita a cikin al’ummar mu a yau. Hakama mazaje da yawa sakacinsu da son zuciya ya haifarma matansu da yawa shiga irin wannan halin batare da sun fargaba. Yayinda wasu ɓangare na matan kan jefa kansu ne ga ɗabi’ar shaye-shayen saboda son zuciya ko zama da abokai ko ƙawaye ko samari dakan koya musu. Ya kamata ku binciki silar faɗawarta wannan yanayin kuyi kuma gaggawar maganceta duk da abin ya rigada ya mata nisa sosai sai addu’a gaskiya. ALLAH ya bata lafiya ya kuma shiryar damu da zuri’armu baki ɗaya akan tafarki na gaskiya”.

        Uncle Yousuf da Mommy ne suka iya amsawa da Amin. Daddy kam da alama ma hankalinsa sam baya jikinsa. Dr Khalifa Shira ya ɗan ƙara musu da shawarwarin yanda zasu fuskanci rayuwar Muwaddat ɗin. Kafin ya sallamesu. Har lokacin Daddy bai iya sake furta komai ba. Dan da zasu tafi ma sai da Uncle Yousuf ya taɓashi, sai dai yana yunƙurawa zai tashi juwa ta kwasheshi ya tafi zai zube ƙasa sai da suka taro shi. Hankali tashe shima aka bashi gado. Nanfa Jiƙamshi family suka sake shiga maɗaukakin tashin hankali mara misali.

       Haka suka yini ranar zubir a asibitin. Shi kansa bai samu kansa ba sai wajen goma na dare bayan ya maida Aunty Saliha matar Uncle Yousuf gida da yaransa yace ya dawo masa da motar ya wuce kawai shi dole zai kwana anan saboda Daddy shima dole an bashi gado. Dr Khalifa kuma yace bazasu sallamesa ba har sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu da rai. Godiya yay masa da hakan dan harga ALLAH ya matuƙar gajiya dama ga yunwa dake cin hanjinsa kasancewar bai wani samu abincin kirki yaci a yinin ba sai wata ƴar gurasa. Sai dai babu yanda zai yi tunda hanyar neman abincinsa ce. Koda ya shiga gidan bai nema kowa ba ya shige ɗakinsa. Sai da ya kammala komai na al’adar rayuwarsa sannan yay zaman cin indomie ɗin daya saya wajen Haladu mai shayi. Tare da shayinsa daya sabarma kansa sha yaci, dan ya samu an dafa masa sabo a flaks. Yasan aikin ƙannensa ne dan basa gajiya da hidimarsa. Hatta ɗakinsa ƙal yake da gyara, dan ko kayansa ƙananu basa ƙyashin zama su wanke masa fes su goge, manyan kayanne dai irinsu shadda sai dai ya kai wanki. Badan kuma bazasu iyaba yake kaiwar, sai dan rage musu aiki ne. Ya jima baiyi barcin ba yana ƙullawa da kwancewa akan al’amuran rayuwa da suka haye masa badan ya tsara su a cikin rayuwarsa ba. Tun yana yaro a kullum burinsa shine buga ƙwallon ƙafa da yin kasuwanci, sai gashi yau ya tsinta kansa a wani matsayin ɓoyayyen aiki da ya zame masa haye. Dan lamarin wannan ɗan taran da bai san miye manufarsa ba yana sake kutso rayuwarsa cikin rayuwar mutanen da har yanzu ya kasa samun amsa ko dalilin dangantakar da ALLAH ya ƙulla a tsakaninsa da su batare da su sun san ma’anar hakan ba suma na cimasa rai. Su dai kawai kallon driver a ƙarƙashinsu suke masa kamar yanda Uncle Yousuf ɗin ya ɗakkosa tun farko yi. Sai kusan ɗaya da wani abu ya samu barcin ya ɗauke sa mai cike da mafarkai marasa daɗi da suka shafi Jiƙamshi family, kodan ya kwanta da tunanunsu ne a rai oho. Ai ko sai gashi ya kusa makara da asuba. Da ƙyar ya iya tashi yay alwala ya wuce massalaci…

      Sashen Abba ya fara shiga kamar yanda ya saba a kowace safiya duk da sunga juna a massalaci. Gaishesa yayi cikin girmamawa da ƙanƙan da kai tare da masa bayanin komawarsa aiki jiya. Karan farko Abba yay ɗan murmushi irin na manya. Tare da faɗin, “Naji daɗin haka sosai, ina kuma maka addu’ar fatan alkairin ALLAH ya baka ikon jurewa. Aliy ba sonka bane banayi da kaga ina maka faɗa. Zaman nan naka ne bana so a hakan. Kai ba aiki ba, ba aure ba, ba wani sana’a ƙwaƙwƙwara ba. Ka duba ƙannen bayanka kusan huɗu sunyi aure har ma ana batun yima wasu ukun. Ba maganar mata nake ba dan su dama dan hakan ta faru ba komai bane ba ai tunda matane”.

      “Kayi haƙuri Abba in sha ALLAHU zaku cigaba da samuna a yanda kuke fata. Ku gafarceni da duk ɓata muku da nake yi”.

         “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, amma ka dage dai ka nema matar aure zamanka ya isheni haka, kaima ina son ganin jininka kafin ƙasa ta rufe idanuna”.

    Ɗan murmushi kawai yayi kansa a ƙasa. Yau ya ɗan jima a wajen Abban har wasu a cikin ƙanensa suka ɗan shigo gaida Abban. Bayan barinsa nan cikin gida ya shiga. Kowane ɗaki sai da ya leƙa suka gaisa, a ɗakin Ammah ya ɗan sha shayi a tsaitsaye yay mata sallama ya fito ganin yana neman makara. Wanka yayi a gurguje yay shirinsa cikin uniform ɗin aikinsa ya fice a gidan….

      ★ Yau ma dai gidan Uncle Yousuf ya nufa kai tsaye, saɓanin jiya ya sameshi a compound zaune tare da baƙo. Bai zauna wajen maigadi ba ya nufesu. Uncle Yousuf dake dubansa da murmushi ya ce, “Uncle Smart na yara”. Murmushi yayi da ɗan shafa kansa suka gaisa cikin girmamawa. Baƙon nasa ma suka gaisa. Yana ƙoƙarin barin wajen Uncle Yousuf ya tsaida shi tare da nuna masa wajen zama. “Kaga zauna muyi magana shima ɗan gida ne. Dama kuma akan abinda ya shafi aikinka muke maganar. Sunansa Tajuddeen, surukina ne kuma ɗan uwana. Yaso Muwaddat da muka kai asibiti jiya kuma yana akan sonta dan har ranar aure an saka musu shekaru uku da suka gabata, sai dai taƙi yarda ai bikin. Abinda yasa nace maka zaman ya shafeka saboda taimakon da muke son kai mana ne tare da sake roƙonka kan ajiye aiki da kai niyyar yi. Aliyu a haɗuwarku ɗaya da Muwaddat kawai na fahimci zaka iya bamu taimako akanta, dan kafin kai mun saka drivers da yawa tun dawowarta ƙasar nan amma tsoronta sukeji saboda azababbiyar yarinya ce da kake ganinta, gashi bata shakkar kowa. Shiyyasa basa iya yin komai kan al’amarin ta. Akan Muwaddat kam nasan aikine mai wahalar gaske zamu baka amma dan ALLAH ka taimakemu kaine kawai hope ɗinmu a yanzu game da yanayin da take ciki.”

        Ganin yanda yakai ƙarshen maganar kamar a yanayin son jin ta bakinsa ya sashi nisawa. Cikin dakewar nan tasa ya ce, “Alhaji zan iya taimaka muku, sai dai fa akwai matsala dan zamanmu inuwa ɗaya da ita bazai yiyu ba. Kayi hakuri bazan iya ɗaukar ƙasƙanci ba, idan tace zata wulaƙantani bana zaton kallonta matsayin wadda nakema aiki zan ɗauki mataki kanta ako ina ne kuma”.

       “Na baka wannan damar, dan hakan nafi buƙata nima”.

      “Shikenan, wane irin taimako kuke buƙata da ga gareni?”.

     “Sanya mana ido akan al’amuranta, ƙawayenta, abokan mu’amalarta, inda take zuwa bayan wajen aiki. Kai hatta waya da zatayi idan san samune musan dawa take yi. Bayan ka gama sanin waɗan nan sai muje mataki na gaba”.

           “Indai wannan ne babu damuwa in sha ALLAHU”.

     Godiya sukai masa, tare da tabbatar masa zai fara aiki da ita da zarar an sallamota asibiti. Sun kuma ninka masa albashinsa……….✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣2️⃣

……..A ranar dai bai yi aikin komai ba sai zama tare da maigadi suka sha hirarsu, abinci ma daga cikin gidan aka kawo harda nashi. Yaso ƙin ci dan shi irin mutanen nan ne masu tsantsenin tsiya. Abu indai ba nasu ba kona gidansu sukan iya hana kansu koda suna buƙatarsa. A hakan ma kaɗan yaci ya cire hannu. Sai bayan sallar la’asar ya tafi kai Aunty Saliha asibiti tare da su Deen. Kasancewar da kayan abinci ta tafi ya taimaka mata wajen shiga da su ciki. Anan ne ya samu damar ganinta. Kwance take rai-rai a kan gado Mommy na zaune ta jingina da jikinta, a kallo ɗaya zaka tabbatar da taji jiki, dan kwana ɗaya kacal harta faɗa da ƙarayin wani fayau da ita. Bayan ya gaisa da su Mommy ya gaisheta da jiki itama a taƙaice. Kaɗan ta ɗago idanunta dake nuna yanayin halin da take ciki na ciwo ta dubesa. Maimakon amsa masa sai ta watsa masa wani kallon rashin mutunci ta ɗauke kai a yatsine.

       Mommy ce ta dubeta cikin ɗan faɗa-faɗa. Sai dai kafin tai magana Deen ya ce, “Aunty Lu Uncle Smart fa na gaisheki da jiki baki amsa masa ba kuma kina masa harara”. Harara ta zubama yaron, muryarta a ɗashe irin na mai ciwo tace, “To maganatu naƙi na amsa ɗin, an kuma hararesan. Yaro sai sa idon tsiya. Ko dokace kowane trash idan ya gaisheni sai na amsa”. Baki ya tura mata da matsawa jikin uwarsa yana ɗan ƙunƙuni. Zata sake magana Mommy ta tareta. “Wai nikam yaushe ne zakiyi hankali Muwaddat? Yanzu kina a gadon asibitin ma bazaki bar masifa ba. Jiya i yanzu fa kina nan keba matatta ba keba mai rai ba hankalin kowa a tashe. Haba ayi mutum babu haƙuri sam sai baƙin tujaran tsiya kamar mara mafaɗi”.

      Sosai ranta ya sosu ganin yanda Mommy ke mata faɗa a gabansa. Badai ta tanka ba amma tayi alƙawarin koya masa hankali tunda har akai mata haka a kansa. Bata sake magana ba ta gyara kwanciyarta ta juya musu baya, dan koyaya tana shakkar Mommy ɗin kasancewar bata yarda ta bata fuskar rainata ba duk da abinda Daddy kemata akanta tun tana a showal. Shima ficewa yay daga waje abinsa yana sake jinjina halin yarinyar mai ido a tsakar kai…

         *_BAYAN KWANA UKU_*

     Kwanakinta uku a asibitin aka sallamosu, dama shi Daddy tun washe gari aka sallamesa sai dai Dr Khalipa ya bashi shawarar ɗan yin nisa da asibitin har ya samu nutsuwa. Shiyyasa bai sake zuwa ba akan tsayawar Uncle Yousuf amma duk da haka kullum sai yazo da dare ya dubata. Alhmdllh jikin nata da sauƙi sosai. Sai dai har sannan batajin ƙarfinsa. Ga buƙatar kayan shaye-shayenta da take matuƙar yi sai dai babu damar shansu. Shine ya ɗakkota tare da Mommy. Yanda kowa ke tattalinta na bashi mamaki kamar wata ƙaramar yarinya. Musamman ma Daddy dake yi kamar zai maidata cikinsa. Ko yaya ta motsa sai ya tambayi ba’asi. Idan ko tace wash yaringa jera mata sannu kenan kaji har muryarsa na zuga dan damuwa.  Kasancewar sallamar dare akai musu yana ajiyesu ya wuce gida. Da ƙyar ya samu napep saboda yanayin anguwar tasu. Ana sallar isha’i ya shiga gida. Wanka ya farayi sannan ya shiga gaida su Ammah. Yau kam ya samu Umma da Mama na rikici akan yara, duk da abune da bai cika faruwa ba a gidan irin haka kaga suna faɗa a zahiri sai da yaji ransa ya sosu. Aunty Amarya ce tamai bayanin tushen faɗan wai Mubarak ne ya daki Sakina saboda ya aiketa taƙi zuwa har ya jimata ciwo a gefen ido fuskarta ta kumbura. Ita kuma Mama tai magana akan ita bata hanashi dukansu idan sun masa ba dai-dai ba. Amma yasan inda zai daka saboda gudun nakasa mutum. Umma kuma dake kamar a jirace ta amshe faɗan shine fa suka rikice haka. Daga inda yake ya ƙwalama Sakinar kira, fitowa tai da ga ɗakinsu da taimakon Yayarta Khadijah. Hankalinsa ya tashi shima da ganin yanda kusan rabin fuskar yarinyar ya kumbura, gashi ciwon kamar ma akan idon ne ba gefe ba.

      “Kawo mata Hijjab” kawai yace yana kallon Khadijan. Da to ta amsa masa. Su Umma dai nata sa’insar su Ammah na basu haƙuri. Shikam wayarsa ya cigaba da dannawa kamar ma bai san mi ake a gidan ba har Khadijah ta dawo. Mayafi ta kawo mata dan hijjab ɗin zai takura mata, baice komai ba yay gaba Sakina ta bisa a baya. A rukunin ɗakunsu na samari ya tsaya, kira ya dannama Mubarak dake ɗaki zaune shiru alamar akwai damuwar abinda ya aikata tattare da shi shima, dan tunda abin ya faru baya cikin nutsuwarsa yayi dana sani babu adadi, jin hayaniyar su Umma ta sake ɗaga masa hankali shine ya koma ɗaki ya rakuɓe.

      “Fito nan ina son ganin ka”.

Bai gama ajiye wayar ba Mubarak ya fito dan suna shakkarsa sosai a gidan. Gaba yay suka bisa baya su duka biyun, kasancewar akan titi layin gidansu yake a ƙofar gida suka samu napep, shi da Sakina suka shiga baya, Mubarak kuma kusa da driver. Wani babban canix na anguwar tasu dake can ƙasa sukaje, yanda suka tarbesa da alama sun sanshi sosai. Dan babu ɓata lokaci aka hau duba Sakinar. Bayan an rufe ciwon da bandeg mai camix ɗin ya basu shawarar kaita asibiti da safe gudun kar idonta ya taɓu. Godiya ya musu ya biya kuɗin suka fito. Dama Uncle Yousuf ne ya bashi su da safe dubu biyar.

       Sun sami gidan yanzu tsit, dan Umma da Mama na gaban Abba da ya gama musu tijara yace kuma su sameshi. Suna shigowa Sadiq yace suje Abba na kira. Su kaɗai suka shiga shi kuma yay shigewarsa ciki, ya zauna sun fara gaisawa da Amma Sadiq ya shigo shima yace yazo Abba na kiransa. Miƙewa yay yabi bayansa. Ya samu Abban nata zagin Mubarak, shi kuma kansa a ƙasa kamar ma yana kuka. Koda ya zauna yana kallon yanda Umma ke hararsa. Bai damu ba ya fuskanci Abban dake cigaba da zagin Mubarak.

         “Abba ayi haƙuri haka nan, yayi kuskure kuma dama nima zan hukuntashi akan laifinsa duk dai ya amsa laifinsa kuma ya bada haƙuri da yin nadama. Itama kuma tace ta yafe masa, amma duk da haka so nake taji sauƙi sai na zauna da su…”

    “Ikon ALLAH ƙarfin hali, ni kana bani mamaki a gidan nan Hydar. Ka dinga wani ɗaukar gabara kamar kaine ubansu. To ko Salim dake yayanku gaba ɗaya yana wannan aikin ne? Ko sai kai sarkin iya zartar da hukunci…”

        Tsawa Abba ya daka mata har sai da ta zabura. “Ke Usaiba ki kiyayeni a gidan nan. Da kike faɗin kamar ubansu ai uban nasu ne shi tunda babba yake garesu. Shi Salim ɗin dake babba miya amfanama kansa ma balle wani, shiko da kike ganin bai miki dai-dai ɗin ba tsaye yake akan tarbiyyar har ƴaƴanki. Badan Aliyn ba a gidan nan sai ƴaƴan ɗakinki sunfi kowa zamemun fanɗararru saboda banzan halinki nason ƴaƴan tsiya. Wlhy sonai ma ya masa dukan mutuwa shima ya fasa masa ido kamar yanda ya fasa mata…”

      “Saboda ita ƴar sonka ce da uwarsa. To wlhy ya dakesa ai gashi nan yaga in ban rama masa ba. Har yau ne yabo ya tashi a kansa gareka. Da kake kiran Salim mara amfani wlhy sai dai in shine mara amfanin. Dan koba komai yarona nada iyalinsa da gida da motar hawa ga aiki bashi dake yawon gal-gal ba babu makama sai watsewa a gari. Auren ma da zai ajiye iyali ya gagara sai bin ƴaƴan mutane ana lalubewa a sorayen iyayensu, da yake tsoron uwarsa kakeji ka kasa magana…”

        Sosai ya rumtse idanunsa dan jin zafin maganganun Ummar garesa. Cikin dakewar nan tasa da sanyaya harshe ya ce, “Dan ALLAH Abba kuyi haƙuri abar maganar. In dai Mubarak da Sakina ne zan hukuntasu akan laifinsu.”

       Mama da tun ɗazun batace komai bace ta karɓe zancen da faɗin, “ALLAH yay maka albarka ɗan halak, wannan shine girma na gaskiya ga babba Hydar, ba ɗagawa da alfahari akan abinda ALLAH shine mai badawa ba. Koda yake iyakar mutum ma alfaharin kawai tunda bai isa tanƙwara ɗan ya masa yanda yake so ba sai dai yaga yanama iyalansa”.

       A take falon ya nema sake rikicewa tsakanin Umma da Mama ɗan kai tsaye dai akan Salim ɗin da Umman ta gama kurantawa ne Mama ta yaɓa mata magana. Wata gigitacciyar tsawa Abba yay musu data sakasu nutsuwar dole su duka. Dan dama shi kam a yanzu ne kura tai lafiya saboda girman shekaru da yau da kullum. Amma tsayayyen mutum ne a gidansa kusan ma halayensa ne Uncle Smart ɗin ya ɗakko a gidan. Masifa sosai ya musu tare da wankesu tas. Shi dai bai sake magana ba har Abban ya gama ya sallamesu. Koda suka shigo gidan Umma nata cigaba da ƙananun maganarta kamarma zata maida faɗan kan Amma ne. Ammah nunawa ma tai bata san da ita take ba. Duk da ita mutum ce mai zafi da rashin ɗaukar raini, mace ce mai kawaici musamman akan al’amurin yaranta. Dole Ummar dai tagaji tai shiru dan kanta. Koda Uncle Smart kuma ya koma wajenta bai mata maganar abinda ya farun ba, ba kuma ta tambayesa ba, ya ɗan tsakuri abinci ya ƙarama su Asma’u karatun Alkur’ani da suke jiransa.

      Koda ya koma ɗaki ya jima maganganun Umma na masa kai kawo a zuciya da ruhi, yana jin matuƙar ciwo da zafi a duk sanda aka zagesa da ƙaddararsa a gidan musamman akan aiki. Dan shi akan aure bawani yana gabansa bane har yanzu. Zaima iya rantsewa bayan Kubrah ɗiyar ƙanwar Ammah da suka haɗasu daga ƙarshe iyayenta suka wargaza abun wai akan baida aikinyi bai taɓa tsayawa da ƴar wani da sunan soyayya ba. Ko ita ɗin da farko ko kallo bata ishesa ba, sai da Ammah ta zaunar da shi ta masa nasiha kasancewar gwaggon tasu ce ta buƙaci haka da kanta saboda son da yarinyar ke masifar masa. Har ranar aure an saka musu kafin abubuwa su rikice iyayen suga mai kuɗi suka canja shawara. Ko a yanzu haka da yarinyar ke’a gidan aure tana masifar son sa, dan a duk sanda ALLAH zai haɗasu sai tayi kuka dan ma baya nuna ya fahimci mitake ciki ne……..✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣3️⃣

_______________________

……..Washe gari da ranakun da suka biyo baya babu wani ƙwaƙwƙwaran aiki da yayi kasancewar wadda aka ɗaukesa aikin a yanzu da ita bata fita. Sai dai yaje ya zauna wajen masu gadi har lokacin tashi yayi ya koma gida. Ganin hakan yasa yau bai fita da wuri ba yabi su Maryam makaranta kamar yanda yakan yi lakaci zuwa lokaci batare da sun sani ba. Yakan ɗan binciki halin da suke ciki da yanayin karatunsu. Sai goma yabar makarantar. Lokacin da ya iso gidan aikin nasa sha ɗaya saura kaɗan. Tunda ya turo gate ɗin ya shiga akanta ya fara sauke idanunsa. Tsaye take a can jikin wata farar mota da ke ƙaton compound ɗin nasu. Kallo ɗaya da yay mata bai sake marmarin ƙarawa ba saboda shegun kayan da ke jikinta. Skert ne blue da ya kamata ɗam-ɗam ya fidda mata halittar jikinta da ƙyau, sai ƴar riga mai santsi kalar gwaiduwar ƙwai. Babu ko ɗigon kwalliya a fuskarta sai wani ƙaton glasses data toshe idanunta da shi, kanta da hula irin ta zamani da ake yayi. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, sai dai ga ɗabi’a da tarbiyyar ɗiyan musulmi bahaushen arewacin Najeriya babu abinda shigar tata ke nufi ga duk wanda zai kalleta sai ƙarancin tarbiyya da wayewar banza. Ga wayayyu kuma irinta hakan normal ne.

     Tsaki ya ɗan ja a ƙasan maƙoshi yana ƙara tsuke fuska. Su maigadi dake zaune kamar a tsorace duk ya bama hannu suka gaisa. Yanda suke kamar a noƙe ya bashi mamaki. Sai dai yana niyyar kaiwa zaune mai wanki ke faɗin, “Ɗan uwa Hajiya Muwaddat fa kai take jira. Tsaiwar da kaga tayi can tun ɗazun take zuba tijara har mu ma nan sai da muka samu rabonmu na zagi, kasan ita sanda aka raba mutunci tana cikin bargo ƙudindine shiyyasa bata samu ba”.

        Shiru kamar bazai amsa ba. Sai kuma zuwa can a dake ya ce, “Tunda kun maida kanku sakarkaru gareta ba”. Da ga haka yaja bakinsa ya tsuke tare da ciro wayarsa da ga aljihu zai fara sana’ar danne-dannen nasa. Wata irin gigitacciyar tsawa Lulu data gama kaiwa wuya da takaicinsa ta daka masa. Sai dai ko gezau wai an tsikari kakkausa. Cikin takun nan nata na izza da yanga ta ƙaraso gate ɗin. Ashariya ta mulmulo tare da faɗin, “Wai kai ɗan uban wanene? Mi kake taƙama da shi ne, tsabar kai cikakken mara mutunci ne kazo a makare ina tsaye tun 8:30 ina jiranka amma kazo ka zauna anan irin ma kai baka gannin nan ba. Na rasa mi Daddy da Uncle Yousuf suka gani gareka suka takura da sai kai ne zaka zama driver na a gidan nan illiterate irinka..”

      A hankali ya rumtse idanunsa sai kuma ya buɗesu a kanta. Wani irin yankawa zuciyarta ta shigayi da sauri-sauri, dan wani irin kwarjini mai cika idanu yay mata. Amma saboda tsabar ƙarfin halinta da taurin zuciya sai ta cigaba da masifar kamar zata cinyesa ɗanye. Harda cewa sai tayi maganin rawar kansa a gidan. Sosai su maigadi ke’a rikice. Shiko yanda ya dake sai ma ka ɗauka ba dashi takeyi ba. Dan tuni ya maida hankalinsa ga wayarsa…

       “Wai ya akayi ne?”.

   Mommy da hayaniyar Lulu ke zuwa mata cikin kunne sama-sama tun ɗazun ta fito dan ganema idonta ta faɗa tana ƙarasowa. Cikin masifar nan tata ta juya tana faɗama Mommyn abinda yay mata. Dai-dai nan shima Daddy ya fito da alama ma wanka ya fito dan bathrobe ce a jikinsa. Mommy ta juya ga Uncle Smart, sai dai kafin tace masa komai ya shiga gaidasu ita da Daddyn da sai yanzu Mommy da Mawaddat suka lura da shi cike da girmamawa kamar bashine ya watsar da al’amarin Lulu ba tun ɗazun. Cikin kulawa suka amsa masa, Daddy ya dubesa cikin alamar sanyin yanayin daya riskesa a kwanaki biyun nan akan halin da Lulu ke ciki tare da faɗin, “Ya akai ka makara haka Aliyu Hydar?”.

        Bai iya ƙarya ba ko kwana-kwana. Sak yake shi akan komai. Dan haka kai tsaye ya ce, “Alhaji na ɗan biya ta school ɗin ƙannena ne dan sanin halin da suke ciki akan karatunsu tunda naga kwana biyu ba wani waje nake zuwa ba”.

      Lulu zatai magana a hargitse Daddy ya katseta cikin lallashi. “To kiyi haƙuri haka tunda dai kinji uzirinsa ai ko Babyna. Kuje ya kaiki haka nan rana na ƙarayi wannan gyaran jikin naki dake ɗaukar lokaci kamar za’a sauyaki”.

     Takaici kamar ya kashe Mommy da ke kallon mijin nata. Sai dai batace komai ba.

        Lulu dake wani cika da batsewa ta ce, “Amma Daddy kana ganin kofa haƙuri bai bani ba. Tsabar wulaƙanci kallo ma ban ishesa ba balle gaisuwa sai da Mommy ta fito ma ya taso da ga inda yake zaune tsabar shi mashahurin mara mutunci ne”.

      “Oh oh”.

Daddy ya faɗa yana dafe kansa. Sai kuma ya dubesa da faɗin, “Kaga dan ALLAH bata haƙurin nan a rabu lafiya kaji Aliyu”.

     A harzuƙe ta ce, “Bana buƙatar haƙurin nasa Dady, sai da aka roƙa min. Ka barsa zanyi maganinsa tare da sauke masa girman kansa, banza mutum ba kowan kowa ba sai ɗaukar kai wata tsiya kana driver. Shiyyasa na tsani irin jahilan nan da ko primary basu yi ba sai ji da kai motsoww!!”.

         Maganganun ta sun masa zafi, amma sai ya miƙe kodan darajar Daddy da Mommy. Key ɗin jikinsa ya ciro yana nufar motar. Tsawa tai masa tare da wurga masa wani key ɗin. “Ba ita nake so ba stupid Men! illiterate kawai”.

    Key ɗin data jefa masan yabi da kallo na kusan minti ɗaya, kafin ya ɗago ya ɗan kalleta sai kuma ya ɗauke kansa yana mai cije lips ɗin sa ya ɗauka batare da yace komai ba nan ma. Daddy ya ɗan girgiza kansa da faɗin “ALLAH ya shiryeki Muwaddatan-warahamah. Koda ya gyara motar zuwa gabanta ƙin shiga tayi. Daddy da ke tsaye zaman jiran ganin sun fita lafiya yay masa nunin ya fito ya buɗe mata. Bai musa ba ya fito fuskarsa na karayin wani kicin-kicin. Batare daya kalleta ba ya buɗe mata ƙofar. Sai da taja tsaki da faɗin, “Motsoww! baƙauye kawai da ko aikinsa bai sani ba” sannan ta shiga. Maidawa yay ya rufe suka fice a gidan. Karan farko Mommy ta saki murmushi, dan tabbas tasan a wannan haɗin akwai ƙura. Lulu masifa da izza. Aliyu jan girma da rashin ɗaukar raini. Taga dai yanda wasan zai cigaba da kasancewa tsakanin ɓera da mage.

     Karaf murmushin Mommyn a idon Daddy da ya juya zai koma ciki. Ya wani ɗaure fuska da faɗin, “Aniyarki ta biki idan ma wani abu kike ƙullawa akan yarinyata”.

       Sarai Mommy ta jisa amma sai bata tanka ba, dan ta fahimci masifa yake nema da ita akan Muwaddat ɗin tunda suka dawo asibiti. Itako taƙi bashi kowacce irin damar cimata mutunci dan a yanzu kam bazata ɗauki abinda ta ɗauka a baya ba kan Mahaifiyar Muwaddat ɗin da ita kanta yarinyar. Suna shiga ciki tai wucewarta ɗakinta bata bisa ba duk da ƙananun maganar daya cigaba da faɗa masu ƙona zuciya. Har da cewa ƙilama itace taima Muwaddat ɗinsa asiri take shaye-shaye saboda tana baƙin ciki da ita a gidan. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Sai da tai mai isarta ta share hawayenta, dan duk yaran sun wuce makaranta da ga ita sai masu aiki. Duk yanda take jurewa da dakewa akan al’amurin mijin nata game da ƴarsa a yanzu hakan yana neman fin ƙarfinta. Dan al’amarin akwai ciwo sosai matuƙa gaya. Cikin ƙanƙanin lokaci tai ninƙaya a tunanin shekaru ashirin da shida da suka shuɗe kafin yau….

*_SHEKARA ASHIRIN DA SHIDA DA SUKA SHUƊE_*

     Malam Ibrahim Jiƙamshi shine sunan mahaifin su Isma’il (Daddy), yayinda Malam Salisu Ibrahim Jiƙamshi ya kasance ƙaninsa ɗaya tilo da iyayensu suka haifa (Mahaifinta). Sun rasa iyayensu tun suna ƙananun yara, dan haka suka tashi da tsananin ƙaunar juna da shaƙuwa a hannun kakarsu Iyan Jiƙamshi. Iyan Jiƙamshi kakarsu itace har taga aurensu su duka biyun, dan ALLAH yay mata rasuwa ne bayan haihuwar Isma’il da ita Kareema. Duk da bawani wayone da su sanda ta rasu ba bazasu iya manta wasu ƴan abubuwa da suka shafeta ba. Iyan Jiƙamshi ita tabarma Ibrahim da Salisu wasiyyar haɗasu aure idan sun girma, ba komai yasa haka ba sai ganin yanda Isma’il (Daddy) ke yawan kaffa-kaffa da ita tun tana jinjira kasancewar ta ita ɗaya ƙanwarsa da yake gani. Bayan rasuwar Iyan Jiƙamshi da shekara biyu ALLAH yayma mahaifinta Salisu rasuwa shima. Wannan mutuwa ta matuƙar girgiza Ibrahim matuƙa da har takaisa da baro garin Jiƙamshi gaba ɗaya ya dawo cikin Kano tare da ita Kareema daya amshe wajen mahaifiyarta dan bayan ta kammala takaba anta bashi shawaran aurenta ciki harda mahaifiyar su Isma’il (Daddy) amma yace bazai iya ba. Bazai taɓa iya auren matar ƙaninsa Salisu ba. Wannan daliline yasa iyayenta cewa ta bashi ƴarsu tazo gida ta samu miji. Ba rabuwar daɗi akayi ba, dan mahaifiyarta ta tafine ta barta tana kuka mai tsanani, haka ma Ibrahim da matarsa da Isma’il. Riƙonta ya koma hannun iyayen Isma’il (Daddy), inda suke tattalinta da kulawa matuƙa su da ɗan su Isma’il. Dawowarsu Kano da shekaru uku aka haifi Yousuf, inda ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa itama a wajen haihuwarsa. Abubuwa sun sake rikicewa, inda mutuwar ta sake taɓa rayuwar Ibrahim matuƙa har sai da ta zama sanadin kamuwarsa da ciwon ajali shima. Yayi jinya sosai ta kusan shekara takwas, yayinda ita da Isma’il suka raini Yousuf tamkar uwa da uba a garesa……….✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣4️⃣

______________________

……..Wannan haɗin kan nasu da ƙaunar juna ya ɗan dinga ragema Malam Ibrahim raɗaɗin ciwo, dan duk da yana kwance a duk sanda suke tattalin Yousuf a tare kamar wasu mata da miji duk da ƙarancin shekarunsu sai yaji farin ciki har fuskarsa kan nuna hakan. Gashi shima suna kulawa da shi matuƙa sai kace wasu manya. Yana da shekara biyar kwance ya yanke shawarar ɗaura musu aure saboda halin rayuwa, a lokacin shekarar Isma’il goma sha tara a duniya. Itako nada goma sha huɗu. Maƙwafcinsu ne ya jagoranci komai, ranar wata juma’a sun dawo makaranta Isma’il ya gama jarabawar ƙarshe ta kammala sakandire, ita kuma jsce suka iske an ɗaura musu aure. Ita bata wani ɗauki abin da muhimmanci ba, kasancewar da sauran ƙuruciya a tare da ita. Sai ma biyema Yousuf dake da shekara biyar a duniya tai suna murnarsu. Yayinda Isma’il ya shiga yanayin damuwa, dan shi harga ALLAH kallon ƙanwa yake mata uwa ɗaya uba ɗaya bawai matar dazai iya aure ba. Lura da hakan da Malam Ibrahim yayi ne ya sashi zaunar da shi yay masa nasiha mai ratsa jiki data saka jikinsa yin sanyi, tun kuma da ga wannan lokacin ya fara koyama kansa sonta ita Kareema (Mommy) tunda dama akwai ƙauna ta jini da shaƙuwar zaman waje ɗaya a tsakaninmu. Karatu muka cigaba da yi abinmu batare da anyi maganar tarewa ba, haka shima Yousuf an sakashi makaranta, gefe kuma muna cigaba da jiyyar babanmu malam Ibrahim. Isma’il na shekara ta uku a jami’a, ni kuma shekarar ƙarshe a sakandire jikin Baba ya sake rikicewa, ganin haka yasa maƙwafcinmu da muka zama tamkar ƴan uwan jini a yanzu shirya bikinmu ni da Isma’il dan yana fatan gani kafin yabar duniya. Haka ɗin kuwa akayi, aka gyara gidan tare da kawo abubuwan da suka dace da amarya sati ɗaya da kammala jarabawata ta ƙarshe akasha biki. Anan dai gidan muka tare, inda kwanaki goma sha ɗaya da tarewar tamu ALLAH yayma Baba rasuwa shima. Mun shiga ruɗani da tashin hankali matuƙa irin wanda bazai misalu ba. Dan da ƙyar al’amura suka daidaita mana bayan wani lokaci. Mun cigaba da rayuwa cikin shaƙuwa da soyayya mai ban mamaki, ga ɗan ƙaninmu Yousuf da muke tattali matuƙa, inda wanda bai sani ba zai iya ɗaukama ɗan mu ne sai idan ka kalleni ne zaka san ban kai haihuwarsa ba. Alhamdullah Isma’il ya kammala jami’a bayan rasuwar Baba da shekara biyu, ya kuma samu result mai ƙyau. Haka shima Yousuf ya shiga fimare 4. Burina a kullum shine na koma makaranta na cigaba da karatu nima, sai dai Isma’il na lallaɓani akan na bari ya samu aiki abubuwa su sake warware masa. Banyi musu ba nayi haƙurin, cikin ikon ALLAH kuwa sai ga aiki ya samu cikin sauƙi kasancewar a wancan lokacin ma neman masu irin kwalinsa ake ido rufe suna yanga dan aiki saima sun zaɓa. Wannan samuwar aiki shine mafarin komai, dan daga lokacin abubuwa suka fara canja salo a saɓanin yanda nake kallonsu ko na tashi na sansu.

         *_Alhaji Sufi Ado Garko_* shine ya kasance ogan Isma’il a wajen aiki, mutum ne mai tarin dukiya da mutunci. Bashi da mugunta da ƙeta, dan ba aikin gwamnati kawai ya dogara da shi ba ɗan kasuwane babba da akeji da shi sosai a lokacin. Ƙwazo da amanar Isma’il ta fara janyo masa soyayya a wajen Alhaji Sufi ya fara jansa a jikinsa tare da ɗorashi akan wasu harkokinsa na kasuwanci a bayan fagen aikinsu na gwamnati. Alhamdullah wannan al’amari ya fara canja mana rayuwa, dan kuɗi sun fara shigowa Isma’il fiye da farkon samun aikinsa. Inda ya cika alƙawarin maidani makaranta, shima Yousuf ya shiga Sakandire. Shekarata ɗaya da komawa makaranta sai ga ciki. Isma’il da Yousuf da ni ɗin kaina mun shiga matuƙar farin ciki da baida misali. Na haihu lafiya bayan ciki yakai haihuwa, inda ALLAH ya bani ɗa Namiji wanda yaci suna Ibrahim muna kiransa da Abba. Na cigaba da rainon Abba koma nace Yousuf ya cigaba da rainonsa, dan tattalin yaron yake tamkar ƙwai a cokali. Sai dai ALLAH baiyi mai zama bane yanada shekara ɗaya da wata uku ya rasu. Yousuf ya sha kuka sai mune muka koma lallashinsa. Sai dai me ashe a lokacin ma ina maƙale ne da ciki batare da mun sani ba. Sai bayan rasuwar Abba ne ya bayyana. Munyi murnar hakan na cigaba da rainon ciki da karatu, yayinda ALLAH keta ƙara ɗaukaka Isma’il ta silar Alhaji Sufi Garko. Bayan isar cikin jikina haihuwa shima na haifesa, sai dai wannan karon ƴan biyu ne duk maza. Wayyo murna zo kaga farin ciki a wajen Yousuf da Isma’il dama ni kaina. Yara sun sake cin sunan Ibrahim da Salisu iyayenmu. Ana kiransu da Hassan da Hussaini ɗinsu. Bayan haihuwar ƴan biyu da shekara biyu na kammala karatuna, sai dai Isma’il yace bazanyi aiki ba sai da naita roƙonsa ni da Yousuf harda kukanmu sannan ya amince. Shine ya amshi takarduna da kansa domin nemamin aiki kamar yanda ya sanar min mai-gidansa Alhaji Sufi Garko yace ya kawo zai sama min gurbin a kamfaninsa insha ALLAHU. Kasancewar yace ya kai masa takardun gida a cikin weekend ya sakashi shiryawa ranar wata asabar. Wannan shine karo na farko a rayuwarsa da zai je gidan ogan nasa. Tare da Yousuf suka tafi, inda akai musu tarba ta mutuntawa, gidane katafaren gaske da ya basu mamaki, dan a ranar suka sake tabbatar da lallai Alhaji Sufi Garko mai kuɗi ne sosai. Suna zaune a falon Alhaji Sufi da aka saukesu saboda karamci saɓanin falon baƙi ƴarsa ƙyaƙyƙyawar budurwa data dawo daga karatu da ga ƙasar larabawa ta shigo falon amsar saƙo wajen mahaifinta. Tunda ta ɗora ido akan Isma’il ta kasa ɗaukewa, dan Isma’il ƙyaƙyƙyawan mutum ne ɗan gaye sosai, ina faɗa muku zancen gaskiya ne badan yana mijina ba. Ba Isma’il kawai ba hatta Alhaji Sufi ya lura da irin kallon da ƴar tasa kema yaronsa na ƙurilla. Yayinda Yousuf shi kuma abin ya bashi haushi saboda kishina ni ƴar uwarsa. Wasa-wasa Muwaddat ta kasa barin falon tana manne da su har suka bar gidan duk da bayan gaisuwar shi Isma’il bai sake kulata ba ma. Aiki dai an ɗaukeni ta silar Alhaji Sufi, sai dai tunda Yousuf ya bani labarin ƴarsa da abinda ya faru naji komai ya fitamin arai. Ban dai yima Isma’il maganar ba, amma kullum cikin kasa kunne nake naji abinda zai biyo baya. Shiru-shiru banji komai ba har na shiga wata shida da fara aiki ga kuma ciki ya sake samuwa. Abinda ya bani mamaki a wannan karon Isma’il bai wani nuna murnarsa sosai akan cikin ba kamar nasu ƴan biyu da Abba. Sai dai banyi magana ba. Bayan haka al’amuransa da yawa sun ɗan fara canjawa a yanda na sansu. Zai fita aiki da sassafe batare daya karyaba yanzu, bai dawowa kuma sai goma na dare. Wani lokacin ya tsakuri abinci, wataran ma baya ci sai yace min ya ƙoshi a gajiye yake. Tun bana ɗaukar al’amarin wani abu har ya fara damuna naima Yousuf maganar. Shima da yake yaro ne mai hankali da lura ashe ya fahimta yay shirune kawai. Kuɗi na sake shigoma Isma’il abubuwa na ƙara rikicewa a tsakaninmu da ban san kansu ba, dan haka Yousuf dake ƙoƙarin kammala sakandire ya lallasheni akan zai bincika. Yaron nan shine yay ƙoƙarin binciko mana komai, inda ya gano ashe Isma’il soyayya suke da Muwaddat ta bugawa a jarida, saboda shi ma yanzu haka ta koma aiki ma’aikatarsu. Hankalina ya tashi da gani har Yousuf, inda duk yanda naso danne abun a raina na kasa Isma’il na dawowa na taresa da maganar. Da farko naga shock a fuskarsa, amma da yake halin maza sai ya dake ya shiga borin kunya akan wane munafuki ne yay masa sharrin nan. Ƙin faɗa masa nayi, amma duk da haka yace yasan Yousuf ne. A daren ya tado Yousuf da ga ɗakinsa ya zagesa tas. Hakan da yay ya sake ɓata min rai muka kwasa da shi sosai abinda bai taɓa faruwa ba har ya kaisa ga marina, ya kuma tabbatar min nama shirya aure shi da Muwaddat babu fashi sai dai mu mutu ni da Yousuf ɗin. Kamar yanda ya faɗa kuwa ya cika, dan baifi sati biyu dayin rigimar tamu ba aka tsaida bikinsu shi da Muwaddat. Wannan tashin hankalin dana sakama kaina saboda yanda ya sake birkicemana a gidan ni da yaran da Yousuf yasa cikin jikina ya ɓare. Bai nuna ya damu ba ya cigaba da shirye-shirye aurensa. Inda Alhaji Sufi Garko ya ce ƴarsa fa tace bazata zauna a gidan da muke ba. Dan haka ya bashi mukullin ƙaton gida da dalleliyar motar hawa, nima mota da kayan faɗar kishiya kai kace ma nice amaryar kuma wai da ga gidan iyayenta. Shima Yousuf da ƴan biyu da nasu hidimar. Wannan abu ya sake ɗagamun hankali dan a ganina Isma’il dai auren jari ma yake shirin yi. Taruwa mukai muka tada masa hankali ni da Yousuf amma yace ko zamu mutu auren Muwaddat babu fashi wlhy. Hakan kuwa akayi, dan wata ɗaya kacal da komawarmu sabon gidan da ya zama dole garemu akai bikinsa shi da Muwaddat……..✍️

     *_Karku rikice wannan Mawaddat ɗin mahaifiyar Lulu ƙamshi ce ba Lulun muke nufi ba😂_*

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣5️⃣

________________

……..Anyi shagalin biki kam na nunama tsara, dan har a gidan tv na ƙasa da jiha an nuna. Kuɗi sunyi kuka abin sai wanda ya gani. Mudai namu ido ni da Yousuf dan ko shagali ɗaya bamu halarta ba Isma’il ya hanamu wai baƙin ciki muke masa. Amarya ta tare ita da abubuwan ban mamakinta. Dan kuwa dai Mawaddat ta shigo gidan ne a tsaitsaye da tarin gadararta irin na ɗiyan wasu masu arziƙin. Dan sai da takai hatta kwanakin girkina wani lokacin Mawaddat cemin take wai ta saya tazo ta diremin kuɗi a gaban Isma’il baya cewa komai kuma. Akwai lokacin da sai da nai wata guda babu miji, dan kuɗi maƙudai tazo ta diremin wai ta sayi kwanakin girkina na wata ɗaya dan tana buƙatar hutawa da mijinta yanda ya kamata. Nayi kuka nayi kuka har na rasa hawayen zubarwa a wannan lokaci, sai Yousuf ne ke lallashina shima idan ya koma gefe yasha kukansa dan yanzu tsakaninsa da ɗan uwansa da ga faɗa sai ƙyara. Wannan damuwar tasa yana kammala sakandare da Mawaddat tace ta samar masa gurbin karatu a ƙasar ƙetare bai wani ja zancen ba ya amince ya tafi dan gara ya bar musu gidan. Tafiyar Yousuf ta sake sakani a cikin ƙuncin rayuwa dan abubuwa sun sake rikicewa sosai tsakanina da Isma’il. Takai yanzu sai dai su shirya su tafi yawon shakatawarsu ƙasashe daban-daban su huta sannan su dawo. Ɗan fita aikin da nakeyi ne yake ɗan ragemun nauyin zuciya, amma sai rana tsaka Isma’il ya hanani fita aiki wai ya dakatar dani. Ban taɓa shiga damuwa ba irin wannan lokacin, dan takai ko kuka ma na daina iya yi sai na zuci kawai. Dole kuma nabar aikin na cigaba da fuskantar matsalolin gidan masu ƙona zuciya. Ashe wasa farin girki, dan kuwa ba’ai komai ba sai da ciki ya bayyana a jikin Mawaddat, naga abu iri-iri wasu ma bazasu faɗu ba. A haka na cigaba da haƙuri sai dai na rungumi ɗiyana nai kuka na share hawaye har ALLAH ya kai wannan ciki watan haihuwa lafiya suka fara shirin tafiya ƙasar waje wai haihuwa. Sai dai kuma suna nasu ne ALLAH yana nashi, dan suna saura kwana biyu su wuce Mawaddat ta tashi da naƙuda, ga shi lokacin Isma’il ya fita gidan. Naso shareta dan ihun kuka sosai ta dingayi har part ɗina ina jinta, sai dai kuma na kasa saboda hakkin maƙwaftaka da daraja irin ta ɗan adam. Karan farko dana shiga sashenta, haɗuwa kam ya haɗu iya haɗuwa, dan ma ban iya masa kallon tsaf ba saboda halin da take ciki. Ni ɗin dai maƙiyyarta ni na taimaketa, ganin yanda take murƙususun kuka da ihun naƙuda gashi inata kiran Isma’il yaƙi ya ɗagamin ya sani samo ruwa nai mata addu’a a ciki, ina ƙoƙarin bata dai-dai nan ya shigo gidan, da wata irin sassarfa yay kammu, babu wani tunani ko bin ba’asi yasa hannu ya kaɓe ruwan, sai dai harta rigada tasha. Sosai ya balbaleni da masifa yana tabbatar min da duk abinda ya samu matarsa bazai barni ba. Kuka na fashe da shi ina masa bayani amma bai sauraren ba ya ɗauketa sukai asibiti tana kukan faɗin na yafe mata dan ALLAH. Tausayi ta bani, dan haka na bisu har harabar gidan ina faɗin, “Na yafe miki Mawaddat, ALLAH ya saukeki lafiya, nima ki yafemin”. Da ƙyar ta iya furta “baki mun komaiba sai alheri” dai-dai yana sakata a motar. Dazai barni dana bisu, amma rashin ganin fuska da ga garesa ya sani haƙura na bisu da addu’a zuciyata duk babu daɗi, ga jikina yay matuƙar sanyi da ganin yanayin nata.

       Kafin su isa asibiti ta haihu a mota dan haihuwar tarigada tazo, gaba ɗaya ya rikice yama rasa miya kamata yayi, ga holdup da suka samu a hanya da ƙyar suka fita, kafin su isa asibiti Mawaddat ta zubda jini sosai har jikinta ya saki. Ko taɓata likitocin basu kai dayi ba UBANGIJI ya amshi abarsa, sai jaririya da aka samu gyarawa. Bayyana muku irin tashin hankalin da Isma’il ya shiga da wanda na fuskanta a garesa ma ɓata lokaci ne. Dan duk da bayanin da likitoci sukai masa akan dalilin rasa ranta cayay sam bai yardaba nice na kasheta, dan ya samu ina bata abu. Wasa-wasa rigima tai girman da har sai da hukuma suka shiga ciki, ALLAH ya soni mahaifinta mutum ne da yasan abinda ya kamata, shine ya balbale Isma’il ɗin da masifa tare da bani kariya har ALLAH yasa zancen ya mutu. Sai dai fa Isma’il ya koma mana kamar wani zautacce, jaririya kuwa tana manne da shi ya hana kowa ɗaukarta har iyayen Mawaddat. Duk kuma yanda sukai masa kurari da jan ido bai basu ɗin ba dole suka barshi da kayarsa. Randa akai addu’ar bakwai mahaifin Mawaddat Alhaji Sufi Garko ya raɗama yarinya sunan mahaifiyarta Mawaddat. A taƙaice dai Isma’il shine ya koma rainon Mawaddat da hanunsa, yayinda soyayyar mahaifiyarta kacokan ta koma kanta, tare da tausayinta. Komai shine kema yarinyar, a saboda ita ya ajiye aikinsa ya koma rainonta. Ko motsi idan tana barci babu wanda ya isa yayi. Idan kuma akayi kosu ƴan biyu ne ya kamasu yay musu dukan mutuwa. Nasha shan mari a wajensa saboda Mawaddat. A haka yarinyar ta taso a taɓare babu kwaɓa komai sai wanda take so za’ayi. Lokacin data isa shiga makaranta ya sakata a mafi tsada dake cikin garin na Kano, Islamiyya ce dai dole ya barta atasu ƴan biyu saboda tsayawar Yousuf da ya kammala karatunsa ya dawo, sai dai bai yarda ba sai da ya kafama malaman sharaɗi akanta. Sabbin matsaloli sun fara akan zuwan Mawaddat Islamiyya, dan bata karatun sai jibgar ƴaƴan jama’a, idan malami yay mata faɗa koya daketa koda akan karatu ne saita faɗama mahaifinsu, shiko ba kunya zai ɗebo ƴan sanda su kama malamin su rufe, wani lokacin ma har marin malaman yake da kansa. Yousuf ne da ya fahimci al’amarin na neman zama wani abu daban ya fara tsayawa akan tarbiyyar Mawaddat, dan ni ko kallon yarinyar na cikayi yanzu zaice itama ina son kashetane kamar uwarta. Dole duk yanda nake kwaɗayin janta jikina kodan maraicin mahaifiyarta da bata sani ba na haƙura na zuba ido dan a zauna lafiya. Dai-daita rayuwar yarinyar da Yousuf ke son yi ce yasa Isma’il ganin ɗan uwan nasa na takura mata. Dan haka ya tattarata ya ɗauke bayan gama Nursery school ɗinta ya maida ƙasar Garmany da zama. Ya ɗauka mata Nanny acan ƙasar aka sakata makaranta. Shima dai wasu harkokin kasuwanci da mahaifin Mawaddat ya sake ɗirasa akai ne yasa zamansa yafi ƙarfi a Garmany ɗin, ga kuma ƴar sonsa da ya maida can. Tafiyar Mawaddat babu jimawa na sake haihuwar yarona Namiji da yaci sunan Mubeen, bayan shi na sake ƴan biyu duk mata da gabonsu Suhaib sai auta Nazeer. Tunda aka ɗauke Mawaddat daga Nigeria bamu sake ganinta ba sai Yousuf dake zuwa akai-akai ganinta, dan shima Isma’il ya tsindumasa akan harkar kasuwancin kawo motocin da yake kanyi a yanzu, duk da dai kuma yana aikinsa anan ƙasar Nigeria saboda shine hubby nasa. Rayuwa ta shuɗa Isma’il ya sake bunƙasa haka ma Yousuf da yay aurensa, ya auri yarinyar kirki mai tarbiyya da sanin yakamata Saliha ɗiyar maƙwafcin nan namu da ya jagoranci bikina da Isma’il. Dan muna zaune lafiya kuma tana matuƙar girmamani. Mawaddat dai bata dawo ba, ko hutu bata taɓa zuwa ba har sai da ta kammala sakandare ɗinta a can sannan tazo mana. A halayen banzanta babu abinda ya canja sai ma ƙaruwa da yayi, dan yarinyar gaba ɗaya a fanɗare take babu wanda ya isa ya sakata ko ya hanata. Ko kallon banza kamata sai ta maida maka murtani, Yousuf ne kawai ke iya tsawatar mata ta nutsu. Hankalina ya tashi matuƙa, dan koba komai Mawaddat ɗiyar Isma’il ce, ita ɗin jininace ai koba aure tsakanina da shi. Dan haka na duƙufa da addu’a akanta kamar yanda nakema nawa yaran. Tawani ɓangaren kuma ina ɗan janta a jikina cikin hikima sai dai ban bata wata ƙofar da zata kawomin raini ba ko kaɗan. Kusan watanta shidda ta sake barin ƙasar zuwa London karatun ta na University, daga haka bata sake zuwa ba sai da ta kammala ta zama cikakkiyar lawyer. Da ƙyar daya ALLAHU Yousuf ya tilastata dawowa gida Nigeria, amma shi Daddynsu ko’a jikinsa. Dawowar tata kuma baisa abubuwa sun canja a yanda suke ba kanta a can baya tsakanina da Isma’il, dan ƙiri-ƙiri yake nuna bambanci tsakanin yarana da Mawaddat, idan nai magana yace arziƙin uwarta da Kakanta muke ci, dole na tattara na watsar da al’amarinsu, dan dama da ƙyar ya biyama su ƴan biyu kuɗin karatu zuwa Saudiyya, a yanzu haka kuma sun dawo suna aikinsu sai dai ba’a nan cikin Kano ba, shiyyasa sai Lokaci-lokaci suke zuwa mana weekend. Mubeen ne kawai tare damu sai ƴanmatana da da Suhaib da auta…..

      Wannan kenan.

  ∆••••∆ ★∆••••∆

         A ɓangaren su Uncle Smart da Lulu ƙamshi sun bar anguwar gaba ɗaya amma taƙi ta faɗa masa inda suka nufa. Shi kuma ya shareta ya cigaba da tafiyarsa a nutse. Yanda yake juya steering motar a nutse ya sata ɗan tsira masa ido a kaikaice. Sai dai ga duk wanda zai iya kallonta zai ɗauka hankalinta nakan tab ɗinta ne. Kamar wadda ta tuna wani abu kuma sai ta yamutse fuska da jan siririn tsaki ta maida hankalinta ga tab ɗin. Sunyi nisa sosai da anguwar dai-dai wasu gungun masu sai da kayan fruit ta ce, “Malam dakata min”.

      Yanda tai maganar a gadarance ya sashi ɗan cizar lips ɗinsa. Ƙoƙarin wucewa yake ta sake maimaitawa cikin daka tsawa. Ƙin tsayawa yay sai da ya gota sosai ya gangara gefen titin ya kashe motar. Jitai wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ya turniƙe mata zuciya har ta kasa yin magana ma. Sai huci take lips ɗinta na motsi amma ta kasa furta komai. Shiko ko’a kwalar rigarsa wayama ya ɗauka yana dannawa batare da ko kallonta sau ɗaya yayi ba.

       “Amma kai babban illiterate ne!!”.

  Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai. Idan motar ta motsa to shima ya motsa ballema ya nuna mata yasan da shi take. Zata sake magana akai knocking glass ɗin motar, nan ɗin ma bai motsa ba, bai kuma sauke gilashin ba sai itace ta buɗe motar ta fita zuciyarta na mata wani irin tuƙuƙi, ji take bata taɓa tsanar wani mutum a duniya ba kamar wannan guy ɗin, dolene ma ta ɗauki mummunan mataki a kansa ta yanda ko ƙarar takalminta da warwarayen hanunta yaji sai hanjin cikinsa sun kaɗu………✍️

       *_Ina bayanki ta wajenmu, karki bari ya raina ki😏, mutum sai ɗaukar kan tsiya aljihu babu manda🥱 gidan sanyi ma shiru ne. Bari nayi nan dan yau nasan namana ɗanye ga ƴan Smart team🚴😜🤪_*

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣6️⃣

………Wanda yay knocking glass ɗin ya gaisheta cikin girmamawa. Hannu kawai ta ɗaga masa. Bai damuba dan yasan halinta. Cikin yarensu na gayu ya ce, “Mi hajjaju ke buƙata?. Kankana, lemon zaƙi, abarba ko tuffa?”.

     “Wanne gareku a ƙasa”.

   “Duk akwai hajjaju, akwai ma sabon ɗiba daga lambu kuma sabon icce ne nata tsumayenki ko zaki shigo amma shiru”.

         Karan farko hankalinsa ya ɗan fara komawa garesu. Kaɗan ya ƙara sauke gilashin motar yana kallonsu ta mirror. Muska taɗan yamutse da faɗin, “Daga wane garden aka kawoshi?, miye kuma tsaftarsa da ɗanɗanonsa?”.

      “Hajjaju akwai sirri a ɗanɗano kam, gashi ya nuna luguf amma dai zan iya haɗa miki da shi kije kiga samfur”.

     “Okay” kawai ta faɗa da miƙa masa kuɗi masu yawa da zasu iya kai naira dubu hamsin. Da sauri ya juya ita kuma ta buɗe motar ta zauna batare data rufeba ƙafafunta a waje. Shiko Smart cikin hikima ya cigaba da bin saurayin da kallo ta mirror da ya saita har yana iya hango wajen masu fruit ɗin. Yanda saurayin ya ɗanyi diri-diri zuwa ƙasan teburinsa kafin ya ɗago ya fara zuba fruit a ledan hanunsa ya sashi sake maida hankali garesa. Bai wani jimaba ya dawo da leda shaƙe da fruit. Ta ɗayan gefen ya zagaya ya ajiye gefenta, ita kuma ta shiga ta maida motar ta rufe. Ƙin taɗa motar yay har kusan minti ɗaya. Badai tace masa komai ba sai ma ƙoƙarin kai waya take a kunnenta.

        “Kina shago ne?”.

    Yaji ta faɗa batare da tayi sallama ba. Bai kuma san mi’akace mata da ga can ba ta dai katse wayar. Batare data kallesa ba ta faɗa masa inda zasu a taƙaice. Shima komai baice ba ya harba motar saman titi zuciyarsa na faman kai kawo. Lokaci zuwa lokacin yakan kalla ledar fruit ɗin ta cikin mirror. Sun ɗan samu huldup a hanya dan haka suka ɗan ɓata lokaci kafin suzo. Tun daga waje zaka san wajen saloon ɗin babba ne kuma na manyan mata masuji da manda a gidan sanyi. Ƙin fita tai ita a dole sai ya fito ya buɗe mata. Shiko ya shareta kamar bai fahimta ba. Aiki ta cika tai fam, dama ƙulle take da shi ta fara zazzaga masa masifa har mai saloon ɗin data kasance ƙawarta ta iso. Ita ta buɗe mata cike da murna tana faɗin, “Oyoyo my Lulu ƙamshi gawa taƙi rami” tai maganar tana jawo ganunta dole ta fito suka rungume juna. Suna niyyar barin wajen ta balla masa harara da jan tsaki tana faɗin, “Ka kuma jirani harna gama villager kawai Mtsowww”.

       Idanu ƙawar tata ta wani tsira masa dan sai yanzu ta lura da shi. A hankali ta furta “Woow vary handsome fa, my Lulu Ina kika samo sa?”.

      Harara ta balla mata da jan tsaki ta fisgi hanunta suka bar wajen. Itako sai ƙara waigowa take dan ba ƙaramin tafiya da imaninta Uncle Smart ɗin da tun kallo ɗaya da yay mata ta mirror ya ɗauke kai bai sake ba dan itama dai irin Lulu ɗin ce. Sanye take cikin skert da riga na atamfa sun masifar matsata kamar tai nishi su yage. Ga uban attachment kan yasha da zaro-zaro na farce da gashin idanu kamar ɗiyar aljanu. A dire take kuma ƙyaƙyƙyawace amma hakan baisa yaji ta ishesa kallo ba. Yanda take tafiya da waigensa yasa Lulu cikin takaici faɗin, “Wai ke Deeyah wace irin banzar yarinyace ban san kayan zubar da mutunci fa kema kin sani”.

      “Wayyo my Lulu bazaki ganeba wlhy, Guy ɗin nan yay masifa-masifar haɗuwa dan ALLAH ina kika samosa?”.

     “Mtowww! Ban sani ba banza kawai”.

   Ta faɗa dai-dai suna shigewa cikin shagon saloon ɗin. Tuni yaran Nadeeya suka fara zubewa gaisheta dan sun san halin masifarta. Ko kallo basu isheta ba takai zaune a ɗaya daga kujerun saloon ɗin. Babu kowa a wajen sai Nadeeyar dama da yaran, dan duk randa Lulu zatazo gyara dokar da take sakawa kenan kar a amshi kowa bata buƙatar hayaniya da gwamutsen numfashi. Duk da hakan na tauye Nadeeyar haka take haƙuri tabi yanda take so dan a zauna lafiya. Amma kuma tana biyanta kuɗi sosai da yafi na aikin duk da itama Nadeeyar da ga babban gida ta fito, sai dai ko kama ƙafar kuɗin gidan su Lulu basuyi ba, su Lulun ma zasu iya kallonsu a faƙirai.

       Nadeeya fa ta damu da son sanin wanene. Yayinda Lulu ta mata banza. Batai zuciya ba tama cikin yaranta sginal da ido. Fahimtar abinda take nufi da yarinyar tayi ya sata kaɗa mata kai. Cikin fakar idon Lulu ta ɗauka drinks da ruwa ta fita. Har yanzu yana zaune a motar ko buɗewa bai yiba, sai dai ya sauke gilashin tare da kwantar da kujerar yanda zaiji daɗi.

       Ita kanta yarinyar sai da taji wani iri datai tozali da shi. Dan Uncle Smart ƙyaƙyƙyawan mutum ne kuma nutsatstse ɗan gaye ga masifar tsafta, irin mutanen nan ne masu shegen tsaftar shiya da a wajen wasu suke ɗaukar harma tai yawa, duk da baida kuɗi bai kuma tashi cikin dukiya ba ALLAH ya bashi lafiyayyen fata mai ɗaukar idon mai kallonsa ga kamala da cikar haiba. Rashin yawan walwalarsa da shiru-shiru na zame masa adon kwarjini ga duk wanda zai dubesa ko zama da shi. Cikin ɗan daburcewar harshe ta gaishesa. Hannu kawai ya ɗan ɗaga mata dan tunda yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Cikin ɗan in’ina ta ce, “Dama Aunty tace a kawo maka wannan”.

      Kamar zai share sai kuma yay magana cikin deep voice ɗin nan nashi mai rikita marasa jin magana musamman ƙannensa, mai kuma saka ƴammata da yawa mutuwa a kansa, “Waye aunty?”. Cikin motsa lips ɗinsa a hankali.

      (Masha ALLAH kaji wani dakakkiyar murya mai ratsa zuciya) ta faɗa a zuciya. A zahiri kam tai saurin faɗin, “Madam ɗinmu ƙawar aunty Lulu ƙamshi, Aunty Nadiy…..”

      “Ba buƙata”.

Ya katseta cikin ɗauke kansa da lumshe idanu yamayi sama da gilashin gaba ɗaya. Tsaye tai sororo kamar kayan ado, sai kuma tabar wajen jiki a sanyaye. A cikin shago har an fara kwance ma Lulu kalbar kanta da wanke mata ƙafafu, yayinda suke hira da Nadeeya ƙasa-ƙasa. Sai dai hankalin Nadeeyar gaba ɗaya na kan ƙofa ne. Da mamaki tabi yarinyarta data dawo da abinda ta fita a hannu. Sai dai batace komai ba gudun kar Lulu ta ganota. Kusan mintuna biyar da barin yarinyar wajen ya buɗe idanunsa. Haka kawai zuciyarsa ke masa kaikawo akan ledar fruit ɗin nan. Duk da wani gefe na kwaɓarsa ya kasa hana kansa dubawa. Ɗakkota yay, ɗaya bayan ɗaya ya fara fidda fruit ɗin da aka loda a sama. Kamar yanda zuciyarsa ke raya masa acan ƙasa wasu abubuwa ne daban, fiddosu yay baki ɗayansu ya maida fruit ɗin ciki tare da ajiye ledar a inda ya ɗauka. Wani irin dokawa ƙirjinsa keyi da sauri-sauri ganin mugayen ƙwayoyin dake a ƙasan, kasancewar shi ba ma’abocin shaye-shayen bane babu abinda ya fahimta a tare da su, sai dai yasan dole ƙwayoyin zasu zama na shaye-shayen ne. Sake naɗesu yay da ƙyau ya adana acan ƙasa inda ƙafafunsa suke, da ga haka ya sake buɗe motar ya fiddo ƙafafunsa dan yasha iska.

        Awani kusan huɗu Lulu ta kwashe a wajen gyaran jikin nan. Dan sai wajen 3 ta fito. Kallo ɗaya da yay mata sai da gabansa ya faɗi, yay saurin ɗaukewa yana jan siririn tsaki. Oho ita bama ta lura da shi ba. Dan yana da ga can gefe a bench na wani mai sai da ƙwa-ƙwa da aya da dabino dake ɗan jikin symbol ɗin shigowa harabar plaza ɗin. Tana da ga tsaye tana hararar motar da tunanin ko yana ciki amma shiru, a fusace ta fara knocking glass ɗin nan ma babu alamar za’a buɗe.

        Ashar ta mulmulo cikin ƙufula da faɗin, “Mi wannan illiterate ɗin ke nufi da nine wai? Barin wajen yay ko mi?”.

        “Kai haba shi ya fara wannan ganganci kamar bai san wacece Lulu ƙamshi ba ne”. Nadiya ta faɗa cikin ƙara fasa mata kai.

     “Ai da alama har yanzu ban sanar da shi ɗin ba. Guy ɗin nan fa mara mutuncine da kike ganinsa. Na barshi ne ban koreshi ba tun a ranar farko saboda sai na gama wulaƙanta rayuwarsa sannan da nuna masa banbancin da ƙasa da sama ke da shi”.

          Cikin ƴar dariya Nadiya ta sake faɗin, “Ai wannan karon drivern naki ne sam bai kama da driver ba wlhy. Irin wannan haɗuwa haka, da gani kuma akwai girman kai fa, koda yake ya kai yayi ne dan ya haɗu ba kary…..”

      “Mtsowww kema shashasha ta biyu da har kika zauna masa kallo haka. Ina wani abin haɗuwa mutum na warin talauci da jahilci. Ƙaton banzar bana zaton (A) kota kai girman garinsu ya sani”.

     Cikin dariya Nadeeya ta ce, “Kai Lulu harda sherinki, wannan ɗan ƙwalisar ne za’ace bai san miye A ba?. Da gani yayi karatu wlhy danni kamar ma na taɓa sanin fuskarsa a cikin ƴan ƙwallon Kano pillars sai dai nasan da wuya ace wancan ne”.

           Tsaki Lulu ta sake ja cikin gatse ta ce, “Sai dai ƴan ƙwallon kwashe gotta ɗin anguwarsu. Dalla malama ni kin isheni”.

      Nadeeya zata sake magana ya iso wajen, dan duk da ba jin mi suke faɗa yake ba da ga inda yake haka kawai zuciyarsa ke raya masa maganarsa suke, maganar kuma da bazata wuce zagi ya sha ba a wajen ƴar balaja’un tsagerar yarinyar nan. Wani banzan kallo Lulu ta watsa masa. Sai dai batace komai ba. Shima ɗin bai nuna yasan tana yi ba ya buɗe mata motar batare daya jira shigarta ba shi ya shige nasa mazauni………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣7️⃣

……..Sai da ta zagesa ciki-ciki da kalmar illiterate sannan ta shiga motar Nadeeya ta rufe da faɗin, “Sai mun haɗu anjima. Dan yau dole ne a warware gajiya Lulu ƙamshinmu ta samu lafiya. Barama na nemo Ɗan-takife ya haɗa mana kayan aiki yau network na gasken-gaske zamu hau”.

     Yatsu biyu ta ɗaga mata tana murmushi, shi kuma yaja motar batare da bari ta faɗi abinda tai niyyar faɗa ba. Dama tun a kallo ɗaya da yayma Nadeeya ya fahimci itama tana shaye-shayen. Dan ita har jikinta ma ya fara nuna kansa saboda har taba tana sha. Masifar da batai masaba a farko ita ta fara zazzaga masa yanzu akan dan mi yasa zaija mota bata bashi iznini ba. Ko sau ɗaya bai nuna yasan ma tanai ba balle ya tanka. Hakan kuma na ƙara fusatata da cimata rai akan al’amarin sa, dan a duniya ta tsani tayi ma mutum abu ya mata shiru, amma shi kulatama bayayi balle ya bata haƙuri kamar yanda sauran masu aiki ƙarƙashinsu ke mata. Suna isa gida tun bai gama tsayawa ba ta fice a motar, cikin gargaɗi ta ce, “Sai nayi maganin wannan zafin kan naka baƙauye kawai”.

      Da kallo kawai ya ɗan bita, sai kuma ya janye idanunsa yana ambaton auziyya saboda yanda skert ɗin yay mata ɗam illahirin surarta na juya kansu. Bayan ya kashe motar ya ɗan ja kusan mintuna biyu zaune shiru abubuwa da yawa na masa kai kawo, ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana mai cigaba da ambaton ALLAH tare da buɗe idanunsa dake lumshe har kalarsu ta canja. Ledar nan daya cire a fruit ɗinta ya ɗauka ya fito a motar, kai tsaye ya nufi wajen su maigadi. Suna cikin gaisawa Nazeer autan gidan ya fito. Sai da ya gaishesu dan sukam Mommy tsaye take akan tarbiyyarsu, bata yarda sun raina kowane ma’aikaci ba a gidan duk da wani lokacin su Hussaina kan so ɗaukar hallayar Lulu suce zasu taka ma’aikatan a bayan idonta. Duk kuma randa ALLAH yasa kunnenta yaji ko idonta yaji bata musu da wasa, shiyyasa ma suke shakkar aikatawar. Cikin ladabi Suhaib daya maida hankalinsa garesa ya ce, “Uncle Smart Aunty Lu ce tace na ɗauka leda a mota. Ta kuma ce wai karkaje ko ina yau har sai idan itace tace”.

        Karan farko da al’amarinta ya so fara bashi dariya. Amma sai bai nuna ba ko’a fuska. Miƙewa kawai yay yaje ya Bama yaron ledar data aiko a ɗauka. Wadda ganin bai biyota da ita bane yasa ta fara masifa, da farko ma catai Suhaib ɗin ya kira mata shi, Mommy ce ta hana tace ya amso kayan kawai. Duk rashin mutuncinta tana jin shakkar Mommyn, dan haka ta cema Suhaib ɗin to ya faɗa masa yau kar yabar gidan nan sai da izinin ta. Kai kawai Mommy ta girgiza, a zuciyarta tana tausayin hallayar Mawaddat ɗin, dan tsaurin idonta da izza na bata tsoro. Koba komai ɗiya mace take, komai daɗewa ƙarƙashin ikon wani zata koma. Wanin ma da bata san shi kuma tashi kalar tsagerancin ba.

      Koda Suhaib ya kai mata ledar fruit ɗin sama-sama kawai ta cire ta ajiye musu ta shige da sauran ɗakinta. Babu wanda yayi magana sai binta da sukai da kallo kawai. Duk da tana buƙatar wanka hankalinta ba’a can yake ba. Kayan shaye-shayenta kawai take buƙatar ɗan ɗorawa, dan kwana biyun nan da bata sha ba jinta take kamar mara laka a jiki, kuma kamar ana mata susa a brain. Tsaf ta gama zazzage kayan fruit ɗin a ƙasa batare data damu da yanda aka gyara ɗakin ƙal-ƙal ba. Duk da ba wani a cinkushe suke ba haka ta shiga tonawa da mamakin rashin ganin waccan ledar. Da gaske dai babu alamar ledar, dan haka ta miƙe zumbur, bataima kowa magana a falon ba ta fice. Har yanzu yana zaune a wajen su maigadi da sauran masu aikin gidan. Hira suke suna kwasar dariya shiko yana zaune shiru sai waya da yake dannawa, wani lokacin yakan ɗanyi murmushi da hirar tasu musamman idan sun sakosa a ciki. Cikin jan tsaki a zuciyarta ta ce, (Baƙauyen banza sai jin kan tsiya ko ubanwa zaima) dai-dai wajen motar da suka dawo ɗin ta dogare tana faɗin, “Kai!!”. Dukansu juyawa sukai suna kallonta. Shikam ko motsi ma baiyiba balle ya nuna yasan da zuwanta.  

      Baƙin ciki, takaici kamar zasu kashe Lulu. Cikin takaici da izza tace, “Wai kai banzan nan bada kai nake ba”. Yanzun ma shiru bai ɗago ba. Sai dai mai-wanki ya zunguresa da faɗin, “Aliyu da kaifa take inaga”.

          Nan ma shiru yay yaƙi nuna yaji. Dan haka ta nufo wajen a fusace. “Wai kai mika ɗauki kanka? Waye ubanka a ƙasar nan?!!”.

     Idanunsa ya ɗan rufe sai kuma ya buɗesu a hankali. Karan farko ya ɗagosu a buɗe gaba ɗaya ya zuba mata su. Wani irin motsawa zuciyarta tayi, dan wani irin kwarjini da shakkarsa ce ta daki ƙirjinta har zuciyarta na sukur-sukur a cikin jiki. Cikin ƙarfin hali ta watsa masa harara da faɗin, “Dalla malam daina kallona da wannan shegunayen idanun naka uwa na macizai”.

      Bai janye idanun ba, haka kuma bai tanka mata ba dai, sai ma sake tsatstsareta yay da idanun duk da masifar da hakan ke haifar masa shi kansa. Neman daburcewa take, dan tama kasa cigaba da masifar da ke ta mata tuƙuƙi a zuciya. Fahimtar hakan da yay ya sashi motsa laɓɓansa karo na farko da nufin yin magana. Cikin deep voice ɗin nan tasa dake fita da dakewar da nutsuwar fitar da lafazi ya furta, “Duk macen data cika mace mai suturtawace akan kanta koda ga muharramanta ne, hakan kansa ko bata kira daraja gareta ba, darajar kanzo ta risina mata a gaban wanda ya fita ma balle wanda ke a ƙarƙashin ikonta. Wannan gata da musulunci yayma mace har a lafazinta ana so ta zama mai ƙyautatawa akan harshe”. Yana gama faɗa ya miƙe tare da miƙa ma mai-wanki dake kusa da shi key ɗin motar. “Mu kwana lafiya” ya faɗa cikin miƙa masu hannu ɗaya bayan ɗaya sannan ya nufi hanyar gate batare da ya sake ko kallon inda take tsaye ba.

       Babu abinda ta fahimta a kalamansa, sai dai abin mamaki ta kasa koda motsa yatsanta garesa balle maida masa murtani ko yin masifa kamar yanda ta saba har ya fice gidan abin sai kace wani siddabaru.

     “Aunty wani abu za’a ɗakko a motar?”.

    Mai-wanki ya dawo da ita hayyacinta. Kamar wadda aka farkar a barci a zabure ta ce, “Ubanka zaka ɗakko min wawa kawai” ta juya zata bar wajen. Sai kuma ta dawo ta shiga nuna maigadi da yatsa. “Idan har kabar wancan ɗan iskan ya shigo gidannan a gobe a bakin aikinka kaima. Shima kuma ba ƙyalesa nayi ba, sai naga waye ubansa a garin nan, mi kuma yake taƙama da shi? Dan wlhy sai na wulaƙanta rayuwarsa ta yanda ko sunana yaji sai ya saki fitsari a wandonsa”.

      (Ko kuma ke ki saki ba) mai-wanki ya faɗa ƙasa-ƙasa yana danne dariya. A zahiri kam kawunansu a ƙasa babu wanda ya motsa harta isa motar da suka dawo ta buɗe, ko’ina sai da ta leƙa amma babu alamar abinda take nema. Rai ɓace ta nufi komawa dan a zuciyarta ta fara bata *_Ƙwaro_* bai saka mata abubuwan nan bane. Dai-dai tana shigewa motar Uncle Yousuf nayin horn. Da sauri maigadi ya tashi ya buɗe gate ɗin. Fitowar Uncle Yousuf ɗin a motar shi da Smart ya sakasu sakin ajiyar zuciya a tare, a hankali mai-wanki ya saki dariyar da yake ta riƙewa tun ɗazun ganin Uncle Yousuf ya dawo da Uncle Smart ɗin tun ba’aje ko’ina ba. Hakan yasa mai bayin fulawoyi tayasa shima. Sai da sukai mai isarsu sannan mai-wanki ya ce, “Yau fa gamai maganin fitsararriyar nan. Ga kuma Alhaji ƙarami ya dawo da shi tun minti biyar basu cika ba, maga yaya wasan zai kaya. Dan wlhy ya mugun burgeni guy ɗin nan. Ga shi da alama ta tsorata da shi. Ai ban taɓa tunanin anan kusa za’a samu mai maganin masifaffiyar matar nan ba, sai gashi kuwa a cikin waɗanda tafi rainawa da cima zarafi wato mu ma’aikata, dan kawai muna neman guminmu a ƙarƙashin dukiyar gidansu sai take jin mune ƙasar takawarta a duniya”.

        Nisawa maigadi dake kaiwa zaune yayi yana sakin wani ɗan murmushin manya. “Ai ni tun randa yaron nan ya fara zuwa nasan ba kanwar lasa bane ba, dan a cikin idanunsa zaka fahimci shima taƙadarin kansa ne”.

     “Shine dai-dai da ita ai. Wulaƙancin yarinyar nan wanene bamu gani ba. Sau biyu fa tana marina”. Mai-wanki ya faɗa cikin ƙunar rai alamar har yanzu yana jin raɗaɗin marin a zuciyarsa, sai dai babu yanda zai yi…

      Kafaɗarsa mai bayin fulawoyi ya dafa shima cikin ƙunar rai dan ya taɓa shan marin Lulun, “Ai ga mai rama mana nan yazo da ikon ALLAH. Fatanmu dai ALLAH yasa Alhaji Yousuf ya tsaya kan hanata korarsan da tace”.

   “Ai insha ALLAHU bazata taɓa samun wannan damar ba ma. Dan randa ta dawo ashe shi aka aika ɗakkota tai masa halin nata yay tahowarsa ya barta acan, kamar dai yau ɗin nan da ya manna mata hauka, amma Alhaji Yousuf ɗin yaje ya dawo da shi aiki matsayin ma drivern ta, kaga ko da ace dane ai tun ranar zata koresa bayan taci masa zarafi kamar yanda takema na baya ko, kuma ya koru ɗin kenan. Nima a wajen Mubeen naji yana labartama yayansu Husain ta waya jiya”.

        “Ai Alhaji ƙarami yana birgeni wlhy”. Cewar maigadi. Haka suka cigaba da gulmar Lulu da a gabanta to tari basu iyawa bare satar kallonta……….✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣8️⃣

………A ɓangaren Lulu kam sosai ta haukacema ƙwaro ta waya da masifa shiko ya dinga rantsuwar ya saka mata. Har abokinsa da yay komai a gabansa ya bama wayar ya zame masa sheda amma taƙi yarda. Sai ma katse kiran tai da tabbatar masa sai ya san ita ya cuta wlhy… Gado ta faɗa zuciyarta na mata wani irin tafasa, babu abinda ke mata kai kawo a rai irin maganganun drivern ta, haka kawai zuciyarta ke ingizata akan son sanin ma’anarsu. Wayarta data yasar gefe ta jawo. Nadeeya ta kira, ana ɗagawa daga can Nadiya ta fara da faɗin, “Bastie dama fa yanzu zan kiraki, dan gama wayata da Gajere kenan yace za’a samu kaya a wajen ogansa kona mil. ake s…..”

       “Kinga ni ba wannan ba…”

    Ta faɗa cikin katse Nadeeyar.

“Oh to ina saurarenki, na jiki kamarma cikin ɓacin rai, miya faru kuma? Badai driver ɗin ba kuma?”.

      “Komai ma ya faru, har ma abinda banyi zaton faruwarsa ba ya faru. Wani Hausa nake son ki fassara min”.

   “Tofa! Wane Hausa kuma?”.

Batasan ta haddace abinda ya faɗa matan ba sai da ta zayyanosu tsaf a yanda ya faɗesu babu ko gargada. _“Duk macen data cika mace mai suturtawace akan kanta har akan muharramanta, hakan kansa ko bata kira daraja gareta ba, darajar kanzo ta risina mata a gaban wanda ya fita ma balle wanda ke a ƙarƙashin ikonta. Wannan gata da musulunci yayma mace har a lafazinta ana so ta zama mai ƙyautatawa akan harshe”._

     “Woow Madam irin wannan kalamai haka kamar wata mai tsara baitikan waƙe, dan ALLAH waya shiryasu haka….”

    “Mtsoww malam dilla fassararsu nake buƙata nace”.

    “Oh sorry, tab wlhy fa kalaman sunyi tsauri, ni kaina ban san yanda zan fassarasu ki gane ba dan hausan ba gama isata yay ba. Amma ina zuwa bari na tambaya”.

         Tana ƙoƙarin ajiye wayar cikin jan tsaki Suhaib na mata knocking. “Uwar miye?”. Ta faɗa cikin masifa. Cikin tunzura baki Suhaib da ke da ga ƙofa dan bai shiga ba ma ya ce, “Uncle Yousuf ne yazo, ya ce kizo” da ga haka yay wucewarsa.

      Tana son Uncle Yousuf matuƙa, tana kuma girmamashi saboda wasu dalilai nata na kanta. Dan haka tace ma Nadiya tana zuwa ta yanke wayar. Da mamaki mai nuna ɓacin rai take duban Smart da ke zaune a ƙayataccen falon nasu kusa da Uncle Yousuf. “Mi wannan abun yazo yimana nan Uncle You?”. Ta faɗa tana nuna Smart da ke zaune babu alamar ɗari-ɗarin nan irin na ma’aikaci da iyayen gidansa a tare da shi. “Ni na kirawoshi” Uncle Yousuf ya bata amsa cikin ɗaure fuska. “Uncle nifa bana buƙatar sake ganinsa” ta faɗa itama a harzuƙe.

      “Da yay miki mi?”.

   Baki ta tura gaba cikin kumbura fuska ta ce, “Wlhy na tsanesa, har ni wannan mutumin zai zaga. Korar ma da nai masa yanzu ba’ita kenan ba Uncle, ya jira hukuncin da zai biyo bayanta. Har ni zaima banza ina masa magana, sannan ya biyoni da baƙaƙen maganganu a gaban su maigadi, har shi waye? Mi yake jin kansa? Ɗan u……”

     Hannu Uncle Yousuf ya ɗaga mata, “Ya isa haka. Mawaddat wai yaushe zakiyi hankali ne dan ALLAH. Yanzu abinda kike yi ko su Suhaib ƙannenki zasu aikata ne? Ke kullum cikin korar mutane. Yanzu dai ina son ki nutsu ki kwantar min da hankalinki, dan shiyyasa ma na dawo da shi gidan a yanzu dan na haɗu da shi a hanya ne. Ban kawo Aliyu gidan nan dan ki koresa ba, zan ƙara jaddada miki a yanzu shi ɗin zai dinga kaiki duk inda kike so dan saboda ke kaɗai ma na ɗaukesa aiki. Zai zo ƙarfe bakwai da rabi saboda takwas kike fita aiki, zai dawo da ke ƙarfe biyar da rabi kamar yanda kike dawowa shike nan ya tashi sai kuma washe gari period na gama magana.”

       “Amma Uncle….”

Hannu ya ɗaga mata alamar baya buƙatar ta sake cewa komai, rai ɓace tabar wajen kamar zata fashe dan haushi. Da ga haka ya juya ga Smart da ke zaunensa a yanda ta shigo ta samesa batare da yabi takanta ba. “Wannan shine lokacin zuwanka aiki da tashin ka. Amma weekend zaka iya zuwa da ga goma zuwa huɗu sai ka tashi. Zan baka duka tsare-tsaren fitarta a rubuce, sai kuma idan zuwa wani waje ya kamata kasan aikinsu yana sakasu ɗan yinan-yinan koba shiri. Dan ALLAH ka ƙara hakuri, al’amarin Mawaddat sai addu’a, ga yanayin da take ciki na ƙara kangarar da ita. Kai tsakaninku ma akwai cigaba, dan naga alamar tana shakkar ka sosai”.

      Karan farko ya saki ɗan murmushi da shafa kansa. “Alhaji wane tsoro kullum ana zageni da kirana illiterate ko villager. Kawai dai zanyi haƙuri domin mutuncinku da ceto rayuwarta, dan koba komai nima inada ƙanne mata, ina son kuma ALLAH ya karemin su a duk inda suka shiga.”

     “Gaskiya ne wannan Aliyu. Ina godiya matuƙa a gareka da sake baka haƙurin di. Yanda ALLAH ya haɗa wannan zuminci a tsakaninmu ALLAH yasa muci moriyarsa har a gidan aljanna. Amma ina son naji wannan kalamai da aka faɗama yarinyata haka har suka harmutsa min ita, duk da nasan abu kaɗan ma fusata Mawaddat yake”.

    Murmushi Smart ya sake yi a karo na biyu da faɗin, “A Alhaji ai ba’ayi haka ba. Tunda ya wuce a barsa kawai sai na gaba idan ALLAH yasa za’ayi a gabanka, duk da ina tsoron kuma karta kwaɗa min mari dan yau ma dai da ƙyar na sha shiyyasa ma na gudu”.

       Dariya sosai Uncle Yousuf yake kwasa da faɗin, “A lallai ka tsira da ƙyar, dan a ma’aikatan gidan nan ɗai-ɗai ne basu sha marin Lulu ƙamshi ba kam”.

    “To kaji ko Alhaji. Bara nayi nan kafin ta sake fusatowa ma, nasan yanzu bai zama lallai na sha ba”.

Dariya Uncle Yousuf ɗin ya sake kwashewa da shi, shi kuma ya fice yana ɗan murmushinsa mai sanyi, har ga ALLAH yana ganin mutunci da kimar Uncle Yousuf, yaji kuma zai iya haƙuri da yarinyar kodan shi ɗin. Mutum ne da yasan daraja da kimar mutane, duk yanda kake baya wulaƙantaka ko nuna maka ɗagawar shi ɗin wani ne. Ya iske har lokacin su maigadi na gulmar Lulu, ganinsa baisa kuma sun daina ba sai ma kwarzantashi da suka shigayi akan abinda yaymata. Komai baice musu ba sai kansa da ya ɗan girgiza kawai ya ciro wayarsa ya fara sana’ar tasa, ba kuma wani abu yake a ciki ba face game ɗin ball.

       Bayan kamar awa ɗaya Uncle Yousuf ya fito zai wuce gida, Lulu ce tai masa rakkiya har wajen motarsa, aiko ta dinga antayama Smart da bai san tanayi ba harara. Dariya Uncle Yousuf ya dingayi ƙasa-ƙasa, dan sarai ya lura da ita, sai dai baice komai ba yayma su maigadi alheri kamar yanda ya saba. Godiya da addu’a suka shiga kwararo masa. Murmushi ya dinga musu kawai, dan harga ALLAH yana jin matuƙar daɗin addu’oi nan nasu. Duban Lulu da keta faman yamutse fuska yay, cikin tsokana ya ce, “To Daughter kin bani aron drivern naki ko na tafi da shi”.

       Fuska ta sake kwaɓewa da faɗin, ni nama bar maka Uncle You, Dan bana buƙatarsa sai shegen girman kan tsiya”.

     Dariya yayi, yana mai kiran Smart dake zaune kansa ke ƙasa. “Shiga muje” kawai yace masa. Bai musa ba ya raɓa ta gaban Lulu dake faman binsa da kallon banza, ciki-ciki ta furta, “An samu motocin banza sai hawa ake”.

       “Ko ke kika zama mota hawa zanyi”. Ya faɗa shima a ƙasa-ƙasa lokacin da yake shigewa cikin motar.

   “Kai ɗin banza! Shashasha!”

Ta faɗa a zafafe har tana zaburowa. Wani shegen murmushi ya sakar mata a karon farko yana ɗan ƙara gimtse fuskarsa kamar bashi ya furta ba ya shige motar abinsa. Wayyo ba’a taɓa Lulu ba ma ya aka ƙare balle. Dariya sosai Uncle Yousuf yake yi, dan ya fahimci akwai abinda ya faru duk da Smart ɗin ya fuske abinsa kamar bai aikata komai ba. Har yaja motar suka fice bata bar masifar ba.

     “Na kula dai kai kake fara kunna min yarinya ka noƙe”. Uncle Yousuf dake dariyarsa har yanzu ya faɗa dai-dai yana harba motar saman lafiyayyen titin anguwar. Kaɗan Smart ya shafo kansa yana ɗan murmushi batare da yace komai ba. Sai da sukai ɗan nisa ya zaro ledar da ya cire a cikin kayan fruit ɗin Lulu. Buɗeta yay, tarin ƙwayoyi kala-kala suka bayyana. Motar neman ƙwacema Uncle Yousuf ɗin tayi, da sauri ya gangara gefen titi cikin rawar harshe ya furta, “Wannan fa Aliyu?”.

      Cikin damuwa da ɓacin rai shima ya bashi amsa da, “Fitar da mukai ɗazun abinda muka fara tsayawa akai order kenan a wajen wasu masu fruits kafin mu ƙarasa inda tace zataje”.

       Sosai jikin Uncle Yousuf ke rawa, dan har ga ALLAH shikam bawai bai yarda da maganar Doctor Khalifa bane, kawai dai rashin ganin al’amarin a zahirinsa ya sa bai kai masa ƙololuwa a rai ba, shiyyasa ma ya ɗora Smart ɗin dan ya samu tabbaci. Kamar wanda ya shiga ɗimuwa ya sake furta, “Aliyu Hydar! Ka tabbata a jikinta ka samu waɗan nan ƙwayoyin?”.

       Cikin salon dakewar nan tasa da rashin son magana ya ɗan ɗage kafaɗunsa da faɗin, “Yaah! A gabana ma aka saya”.

   “Dolene na saka a kama yaron nan dake sayar mata, bara ma na kira CP….”

Da sauri Smart ya dakatar da shi. “Niko a nawa shawaran Alhaji kamar kama yaron ba shine mafita ba tun a yanzu. Domin inaji a jikina ba dashi kaɗai take huɗɗa ba. Dan ka saka an kamashi kamar ka fargar da itane ta sake sabon salo ita da abokan mu’amalarta. Kaga kenan ba hanyar da zamu rabata da al’amarin muka ɗakko ba kenan, dan yanzu aka fara wasan kamar”.

     Sosai maganarsa ta shigi Uncle Yousuf ɗin, dan haka ya ɗan dakata da ga ƙoƙarin kiran cp da yake shirin farawa, sai dai idanunsa sun kaɗa jazur harda ƴar guntuwar ƙwalla a cikinsu. Shiru babu wanda ya sake magana a motar har kusan mintuna huɗu, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa.. Shine ya kashe shirun nasu da furzar da iska mai zafi. “Alhaji ni zan wuce, dan yamma nayi gashi ina son na isa gida da wuri”.

     Cikin damuwa ya gyaɗa masa kai batare da ya iya furta komai ba har sai da ya fita yana ƙoƙarin rufe ƙofar motar ya kira shi a hankali. Ɗan duƙowa yay yana amsawa, Uncle Yousuf ya miƙa masa kuɗi masu yawa. Kansa ya girgiza da faɗin, “Kayi haƙuri Alhaji, tun farko na faɗa maka kada irin haka ya dinga shiga tsakaninmu. Hakkina kawai nake buƙata a kowane ƙarshen wata kamar yanda mukai alkawari. Na barka lafiya”.

        Ajiyar zuciya mai ƙarfi Uncle Yousuf ya sauke ta re da sakin ɗan murmushi yana mai binsa da kallo. Tabbas a girme yasan zai iya bama Aliyun shekara bakwai. Amma dattako da kamunkan yaron na sakashi jin ya cika masa ido tamkar wani babba garesa. Wata irin kima da kwarjini yake masa a zuciya da cikin udanu. Yana matuƙar son ganin mutumin da yasan ciwon kansa a rayuwa da riƙe mutuncinsa. Ya yarda ya nema halak ɗinsa koda za’a kallesa a mai riƙe da sana’a mai ƙasƙanci, amma bai yarda ya ƙasƙantar da kansa ba wajen a bashi ya amsa balle zuciyarsa ta mutu. Insha ALLAHU zai taimaki rayuwarsa………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenku😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣9️⃣

……..Smart kam tuni ya shanye titin layin zuwa babban titi, da ƙyar ya samu napep. Tafiyar da bata wuce mintuna talatin ba ta kawosa anguwarsu. Kasancewar da sauran hasken gari koda ya shiga sai ya ɗan watsa ruwa tare da zuwa ya gaida Abba da su Ammah, sai dai ya iske Ammah ma ta fita ita da aunty Amarya Barkan ƙanwar Aunty Amaryar da ta haihu a can Gadon ƙaya tun la’asar, sai su Maryam kawai da suka dawo islamiyya. Dan haka bai zauna ba suna gama gaishesa ya fito ya koma ɗakinsa. Ba wasu abokai ne da shi ba shi dama sai Ahmad kuma ba anguwar yake ba. Dan Mutum ne mai ƙarancin kwaramniya. Idan kaga abokinsa da har zasu iya zaman doguwar hira to sai dai abokan karatunsa, amma na cikin anguwa sai gaisuwar mutunci kawai, duk da dai a da anyi abotar yarinta, sai dai kasancewar sa mara sakewa da mutane suke masa kallon mai girman kai duk suka janye jikinsu da shi, shi kuma bai nuna ya damu ba. Abokan karatun kuwa akan jima ma ba’a haɗu ba sai ta waya ko wani taro mai muhimmanci ya haɗa. Shiru ya kwanta kamar mai barci, da gani kasan duniyar tunani ya faɗa, dan babu abinda yake sai furzar da huci akai-akai da ga bakinsa, hakan kamar ɗabi’a ce data zame masa jiki in dai yana cikin damuwa.. Abubuwa ne masu yawa ke ci masa rai, ciki harda batun bauɗaɗɗiyar yarinyar can, shi mutum ne da baya shiga sabgar da ba tashi ba koda kuwa a cikin gidansu ne sai idan yaso, amma sai yake ji zuciyarsa na ingizashi akan taimakon ubangidan nasa da yarinyar, badan komai ba sai dan ƙannensa mata da bazai taɓa fatan su tsinta kansu a irin wannan rayuwar ba. Yasan idan har ya tsamota da ga wannan musifar yayi jihadi, sai dai bai san ta ina zai farama taro wannan al’amari nata ba. Karan farko yaja sirrin tsaki, sai kuma ya tashi zaune yana ɗan furzar da huci tare da kai hannunsa saman goshinsa yana ɗan murzawa. Ganin yaƙi samun nutsuwar hutawar da yake buƙata ya sashi tashi ya fito a ɗakin, nan ƙofar gidansu ya zauna yana ɗan gaisawa da mutane masu wucewa har akai kiran sallar magrib. Bai fito da ga massalacin ba sai da akai isha’i, yana kwaɗayin shiga gidan suyi hira da Ammah dan wannan ɗan lokacin kawai yake da damar haka gareta, amma zuciyarsa nata masa tuni akan Lulu da abinda yaji suna magana ita da ƙawarta zasuyi a daren na yau da sunan wai murnar samun lafiyarta. duk yanda yaso yaƙar zuciyarsa abin ya gagara, saboda yana ji a ransa ba alkairi za’a shuka ba wajen, dan haka ya fito da ga layinsu ya samu Napep zuwa hotoro gra. bai damu da kuɗin da suka tsuga masa ba. Ɗan nesa da gidan ya sauka, amma ya tsayar da mai napep ɗin, ya samu jikin wata bishiyar dabino kusa da katangarsu ya tsaya, ya kai mintuna talatin da wani abu a wajen yaji motsin an buɗe gate ɗin gidan, ido ya zuba na son ganin wanda zai fito. Ilai kuwa Lulu ce, dan a kanta idanunsa suka sauka saboda haske dake tako ina a street ɗin, gashi ta sauke glass ɗin motar sosai har kana iya hango kalar kayan da take sanye da su. Tayi ƙyau matuƙa ga uban ƙamshinta na isowa har inda yake tsaye saboda yanda ta gumbuɗashi kamar ba mace ba. A ɗan kasancewarsu na kwanaki ya fahimci sam bata tausayawa ƙamshi, haka kawai sai yaji tanan ɓangaren ta ɗan samu sassauci a garesa, duk da tana saka nata ƙamshi ne ba bisa ƙa’idar da ya kamata ace mace ta saka ba. Da sauri ya ƙarasa ga mai napep da ke zaman jiransa. “Kabi wannan motar Please, amma karka bari ta fahimci muna biye da ita”. Ya faɗa yana nuna ma mai napep ɗin motar Lulu da ke tafiya a hankali kamar bata son tuƙin yau. Yanda take tafiyar ya bama mai napep ɗin damar binta cikin hikima har zuwa wata sabuwar anguwa, dai-dai wani gida da alamu suka nuna shima ba’a daɗe da kammalashi ba ta tsaya, da ga inda suke yana hangen yanda ta kai waya a kunnenta alamar kira take ko an kirata, tana ajiye wayar ana buɗe gate ɗin gidan. Da sauri ya fita tare da miƙama mai napep kuɗi yana faɗin, “Abokina nagode ko”. Bai jira amsarsa ba ya nufi gidan, kasancewar akwai ƙarancin haske a anguwar dan kamar ma basu da wuta sai ƙarar gen… Ɗin gidan data shiga yake jiyowa ya samu damar bin motar tata ta gefe suka shiga tare batare da mai-gadin ya lura ba. Motoci ne kusan bakwai a gidan duk an parker a babban compound ɗin kamar wasu masu biki, tun kafin ta fito a motar ƙawayen nata suka baibayeta da ihun faɗin, “Sai Lu ɗin mu!!!, sai ƙamshin mu!!!”.

          Fuskarta ƙawace da wani shegen murmushi ta fito. Wani shegen gown ne a jikin nata ta lafe mata kamar babyn roba. Da sauri ya kauda idanunsa yana mai jan sirrin tsaki da taune lips ɗinsa da ƙarfi. Bai sake kallon inda suke ba har suka shige ƙofar da yake ƙyautata zaton ta cikin gidan ce. Huci mai zafin gaske ya furzar tare da gyara tsaiwarsa. A ɓangaren su Lulu kam suna can cikin ƙaton falon gidan da ya sha kayan alatu. Abinda zai baka mamaki bawai iyakar su kaɗai bane ƴammatan ashe, akwai dattijan maza a shekaru bawai a cikar kamala ba har su huɗu, tun shigowar su Lulu kusan su duka suka zubo mata idanu fuska a washe, yayinda ita kuma nata murmushin ya ɗauke ta wani yamutse fuska tana kallon Nadiya, sai kuma ta juya ta fito a fusace. Da sauri Nadiya tabi bayanta tana faɗin, “Please Lu ki saurare ni.”

       “Anƙi a saurareki ɗin, Nadiya kin san dai na tsani irin wannan ko…?”

     “Na sani, amma bamu da wani zaɓi ne wlhy Lu.., dan ALLAH ki fahimce ni, kin san dai bazanyi abinda zai ɓata miki rai da gangan ba….”

    “In ba kinyi da gangan ɗin ba miya kawo waɗan nan tsoffin banzar nan? Ni ban hanaki huɗɗa da su ba, amma ki sani duk randa suka zubar da ke bayan gama lalata miki ƙuruciya kiyi kukanki ke kaɗai kar ki tunkareni. Amma ki daina sakamin su a sabgogin rayuwata”.

        Ɗan murmushi Nadiya tayi cikin rashin ɗaukar zancen na Lulu da muhimmanci ta ce, “Naji, ni dai yanzu kiyi haƙuri mu koma ciki dan ALLAH. Dan wannan fa zaman naki ne, dan ke akayisa, mun riga mun gama tara mutane, su Shony fa tun daga ktn suka taho a yammacin nan domin wannan shagali kawai. Abinda yasa ki ka ga su Alh. Baita anan ma saboda su Shony ne, dan sun riga sun kirasu cewar zasu shigo Kano, amma wlhy badan ke bane ba”.

     A hankali ta furzar da iska, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya. “Shike nan amma ki kiyaye gaba, dan in har kika sake sakamin sabgar waɗan nan mutanen a tawa wlhy sai mun rabu. Suma su Shonyn idan suna buƙatar haɗuwa da su ne suje can su haɗu bai shafeni ba”.

        “Naji na yarda baza’a sake ba. Suma kuma zan musu bayani yanda zasu gane Muje to dan ALLAH suna jiranmu”.

    “Bani details ɗin mai kayan nan na tura masa kuɗinsa karna shiga wata sabgar. Sannan wannan gidan na waye uwar kwashe-kwashe kika kawo mu kuma?”.

       Gidan Nadiya ta kalla tana ƴar dariya tare da faɗin, “Gidan wanda ya sayar mana da kayan ne, wlhy Guy ɗin akwai kirki gashi so handsome kuma, ya bamu shawara ne muzo nan musha shagalinmu dan zaifi mana sirri kasancewar kinga dare ne, ke kuma ba cika son shiga clubs na nan Kano kikai ba kin ce ƴan hayaniya da ƴan iska sun cika yawa”.

          Cikin rashin damuwa ta ɗage kafaɗa kawai, batare da ta sake tofa komai ba ta bar wajen. Binta Nadiya tai suka shige tare…. Gaba ɗaya zuciyar Smart ta sake jagulewa da takaici, dan duk abinda Lulu da Nadiya ke tattaunawa yana jinsu  batare da su sun lura da shi ba. Shigarsu da kusan mintuna uku sautin kiɗa ya fara tashi kaɗan-kaɗan saboda rufe windows da sukai duk dan kar kiɗan ya fita wa mutanen anguwa. Kansa ya ɗan dafe yana mai ambaton sunan ALLAH, gaba ɗaya ma ya rasa miya kamata yayi, duk da yazo nan ɗinne da burin ganin abokan sheɗanar tata da kuma hanata shan komai. To amma ta ina zai fara ma?. Ya kwashe kusan mintuna ashirin yana ƙullawa da kwance ta yanda zai shiga wajen…. Ƙarar hayaniya da ta fara tasowa kaɗan-kaɗan da ga cikin falon ta maidosa da ga dogon tunanin mafita da ya tafi, ajiyar zuciya yaja kamar wanda aka farkar da ga barci tare da tsurawa ƙofar idanu. Wasa-wasa hayaniyar ta daɗa karfi har yana iya shaida muryar Lulu saboda tsayawar ƙarar sautin kiɗan da ke tashi, da alama sun kashe ne ko wata matsala ta faru. Falon ya nufa da sauri batare da tunanin komai ba ko neman izinin ya tura ƙofar ya shige, yanda ya gansu a yamutse ga Lulu na ɗurama wani hamshaƙin Alhaji zagi har tanayi kamar zata tsole masa ido da ɗan yatsa ya sashi yin turus, mamaki ne ko takaici oho baima sani ba, kayan shaye-shayene da na ciye-ciye ko’ina a barbaje, yayinda alhazan nan guda huɗu da ya shaida fuskar biyu a cikinsu kasancewarsu wasu manyan ƙusoshin attajirai kuma ƴan siyasa masu faɗa aji a garin na kano ɗaya ke tsaye cikin fusata kamar zai daki Lulu, sauran ukun na zaune sun zuba mata ido harda wanda take zagin da shi fuskarsa ma ƙawace take da murmushi kamar bashi akema tujarar ba. Kalaman Lulu ne na ƙarshe-ƙarshe da kukan da ta fashe da shi ya dawo da shi hayyacinsa………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣0️⃣

……..Cikin kuka da dafe kanta tana ɗan layi alamar ta fara shiga maye ta ke faɗin, “Wlhy! Idan baka fita sabgata ba sai na keta maka rigar mutuncin tufafi da mutanen gari ke kallonka da shi, dan dama shi kaɗai ya saura gareka. Nace banayi! Banayi wai na minene wannan takura duk inda na saka ƙafa kana biye dani, shine yau harda bani wine saboda kai tsinanne ne, ka taɓa ganin na sha wine ne duk rashin ji na azzalumi!! Shin wai ku kuna ɗaukar duk macen da ke shan wannan abubuwan dan bama kanta farin ciki ita ɗin ƴar iska ce ko me? Manyan banza manyan kawai, ku gama hura hanci ga al’umma ku dawo bayan fage kuna lalata musu tarbiyyar yaransu. Ka sani har gaban abada bazaka taɓa samun wannan jikin ba, bama kai ba duk wani maye sai gani sai hange dan ni ba mazinaciya bace, bar ganin ina wannan rashin jin nasan ciwon kai na wawa kawai da ƙi ƙ…..” ta kasa ƙara sawa saboda shuuu da tai zata faɗi. Da sauri Nadiya ta tarota. Fisge jikinta tai tare da ɗagowa gaba ɗayanta kan ƙafafunta ta ɗauke fuskar Nadiya da mari haggu da dama.. A fusace Alhajin nan da ke tsaye tun ɗazun cikin ɓacin ran zagin da Lulu kema abokin nasa yayo kanta. Hannu ya ɗaga zai kwasheta da mari shima, sai dai cak ya tsaya jin an riƙe masa hannu ta baya. A karo na farko duk wanda ke’a falon ya farga da shi. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Alhajin da ke faman huci. Idanu ya lumshe cikin girgiza kansa da faɗin, “Haba kai kuwa ai babba babba ne, ba’asan namiji kuma da faɗa da mace ba. Bakaga abokinka yanda ya nuna mazantaka ba? Tunda kun gama zubar da kimarku garesu banga abin tada jijiyar wuya ba idan irin haka ta taso a tsakaninku ai……”

      “Kai kuma a matsayinka na ubanwa anan?”.

          Maimakon amsa sai ya ƙara tsaresa da idanunsan nan masu kwarjini da suka gama ƙwarewa a kallo mai girgiza zuciya cikin nuna gargaɗi (Na macizai inji Lulu😂). Sakin hannun Alhajin yayi, kafin cikin yanayin nan nasa a daƙile da kowa ke ɗauka girman kai ya ɗage kafaɗunsa da ɗan taɓe lips ɗinsa. “Sanin ɗan waye ni bazai maka amfani ba, idan dani kake son sani sai na baka amsa da cewar drivern ta ne”.

        “What?! Driver fa?!!. Ubanwa to ya baka damar shigo mana nan har da tsoma baki a cikin abinda bai shafeka ba?”.

     Shi ba mai yawan magana bane, dan haka maimakon amsa masa a yanzun ma sai kawai ya zuba masa ido. Hon. HD Nakowa sai ya sake fusata. Magana zai sakeyi cikin fusata Alhaji Ɗan-kande Baita ya dakatar da shi.

          “Kaga HD please it’s ok mana. Kai ɗan saurayi jeka kawai waje ka jirata nan ba huruminka bane ba”.

      Wani banzan kallo Smart ya watsa musu su dukan, sai dai baice komai ba ya juya ga Lulu da ke zaune a kujera sharɓe tanata surutai da zagi har yanzu. Hanunta kawai ya fisga ta miƙe, batare da wani binta a hankali ba ya jata tana turjewa sukai waje. Da ƙyar ya iya kaita har motarta, dan haka ta maido da zagin da take ma Hon. Babale Misau kansa. Hakan bai damesa ba, sai ma rufeta da yay a motar ya koma falon ɗaukar handbag ɗin ta dan key ɗin motar na ciki….

         “Ban yarda da wannan yaron driver bane ba, dan haka ina son a binciko min ɗan uban wanene shi a faɗin garin nan na kano”. Hon. HD Nakowa ne ke faɗa dai-dai Smart na sake shigowa falon ɗaukar tarkacen Lulu. Nunawa yay kamar baiji mi Hon. Nakowan ya faɗa ba, ya nufi handbag ɗin da ya gani ɗazun a hanunta da takalmanta masu azabar tsini ya kwashe ya sake juyawa ya bar falon ko kallo basu ishesa ba…..

       Gotawarsu kaɗan da gidan wata dalleliyar mota ta iso ƙofar ita kuma. Horn yay aka buɗe masa. Yanda sautin kiɗa ke tashi a cikin motar zai baka tabbacin yana cikin nishaɗi matuƙa. Duk da yasan taro ake a gidan nasa hakan bai hanashi jin mamakin ganin wasu manya-manyan motoci guda uku ba, bawai ƴammatan bazasu iya zuwa da motocin bane, a’a kawai dai yasan sun musu girman da bazai yiwu ace sune suke hawansu ba. Cikin kai-kawo zuciya ya fito yana ƙara ƙarema motocin kallo, cikin ɗan basarwa irin na masu akwai ya ɗage kafaɗu da ɗan taɓe baki yay ciki abinsa ransa fal nishaɗi yau zai haɗu da mafarkinsa. Yayi alƙawarin sai ya ɗanɗani yarinyar nan dan ta tsare masa ko’ina na zuciya tun a randa ya ganta. Da wani irin sauri yaja birki ya tsaya yana ƙarema falon nasa da ya hargitse kallo, bawai na tarkacen da suka zube bane kawai dan yasan wannan ne ya kawosu ai. Iya shegen da ake aikatawa a falon duk da shima yasan yana aikatawa ya sashi zama turus, dan shi dai Nadiya batace masa zasu gayyato namiji ko ɗaya ba. Amma sai ga har mutum huɗu manyan mutane sa’ar Daddynsa, kai abinma tashin hankalin shine harda abokan Daddyn nasa ma da suka sanshi ya sansu. Da baya-baya ya koma ganin hankalinsu su bai kai kansa ba saboda shagala a ɓarnar da suke aikatawa da yaran mutane. Duk cikinsu baiga Lulu ba, gashi kuma an tabbatar masa da tazo wajen awa biyu baya da suka shuɗe. Waya ya ciro yay kiran Nadiya, an jima ba’a ɗauka ba dan har tana batun tsinkewa sannan aka ɗauka. Cikin wata irin murya ta ce, “Ranka ya daɗe barka da dare”. Sai da ya ɗan cije leɓen haushi kafin ya amsa mata da “Ta iso ne?”. Cikin muryar nan na wadda ta gama buguwa da shiga yanayin masha’a ta amsa masa da “Tazo amma shegen driver ɗin nan nata ya kwasheta sun tafi”.

      “What!!” MM Atik Kumo ya faɗa da ƴar tsawa. Bai jira cewar Nadiya ba ya yanke wayar ransa a ɓace. Mota ya shige ya zauna tare da kwantar da kansa kan steering. A karo na biyu ya rasa damarsa akanta, tunda yake wata mace bata taɓa shiga ransa irin haka kamar yanda Lulu ƙamshi ta shiga ba. Da gaske sonta yake, yana kuma tsananin buƙatar mallakarta. Bai damu ace sai da aure ba, dan shi a halin yanzu babu maganar aure  ma a gabansa duk da kullum faɗan momynsa kenan shine yay aure. Sai dai da to kawai yake amsa mata a duk sanda ta titsiyesa. Tun randa suka haɗu da Lulu a airport ya kasa hutawa da tunanin surar yarinyar da tsiwarta, burinsa kawai ya gusar da ƙishinsa gareta dan kowace mace tama daina birgesa a dalilinta yanzu. Sake kaiwa steering duka yay tare da tashi zaune yayma motar key a fusace ya bar gidan……

       ★★

    Driving ɗin yake cikin ɓacin rai da takaici, yayinda ita kuma ta keta faman surutai da zaginsa akan ya maidata sai ta koyama Hon. Babale Misau da Nadiya da suka haɗa baki hankali. Faɗi take ita ba ƴar iska bace, duk wanda yace zai mata iskanci sai ta wulaƙanta shi…..

    Wani irin baƙin ciki ne ya sake turniƙe zuciyar Smart dan surutanta sun ishesa, sake tunzura fushinsa suke zuciyarsa na ƙuna. Wani shegen birki ya taka a harzuƙe har sai da tai gaba ta bugu da kujerar gabanta ta sake buguwa da jikin ƙofa sannan ta koma ta zauna daɓar. Dafe kanta tai dan azaba kamar zata fasa kuka, sai kuma ta harzuƙo cikin fushi da masifa ga rashin kasancewa a hayyaci da ya ƙara hauhawar masifar tata ta ce, “Kai wai miyasa baƙauye ne akoda yaushe? Mugu so kake ka kasheni ka gudu da motan ko? Illiterate kawai, ba abinda ya iya sai shashashanci baƙauye”.

       Idan motar nan ta motsa Smart to shima ya motsa, yakai matuƙar wuya so yake ya mata masifa dan maƙogwaronsa sai kaikawo ya ke a wuya amma yanata ƙoƙarin hana kansa, sai ma wayarsa da ya ɗauka ya fara danne-danne abinsa. Hakan ya sake fusata Lulu, da ma yaya lafiyar kura balle ta tsinke. Tana ƙalau ma yaya aka ƙare da jaraba balle yanzu da ya haɗa da maye. Sosai ta cigaba da zazzaga masa masifa ko haɗiyar yawu ma batayi, ganin badai zai kulata ba ta kama murfin ƙofar zata buɗe ta fita amma sai taji yayi lucking motar. Wayyo azabatun azaba. Yau dai kam yaga masifar ƙare dangi, dan bakinta baiyi shiru ba har sai da barci ya fara rinjayar mata idanu. Da wahala kaga Lulu tasha abu ya sakata barci, shiyyasa ko cikin abokanta ake ji da ita da kwarzanta ƙarfin kanta, amma yau da yake wani mugun haɗine MM Atik yay mata batare da ko Nadiya ta sani ba yasa abinda yafi ƙarfin kanta kala-kala wani ma bata taɓa shansa ba. Tun randa suka haɗu a airport bai huta ba, biye yake da ita yana ninƙaya cikin al’amurranta har sai da ya gama sanin ita ɗin wacece. Dan haka ya jawo Nadiya a jikinsa ya dinga jiƙata da kuɗaɗe harta amince da shi bawai yazo dan ya cutar da aminiyar tata bane son gaskiya yake mata. Ita da shi suka haɗa plan ɗin wannan phaty na samun lafiyarta, ya kuma saya musu duk kayan shaye-shayen tare da basu gidan hutawarsa da ya gama ginawa kwanan nan, shi yayi hakane dan ya rutsa Lulu a can, yayi imanin in har ya sameta sau ɗaya da kanta zata cigaba da nemansa kamar sauran ƴammatansa tana kawo masa kanta. Sai dai kuma kash, bayan ya gama wahalar haɗa dukkan plan ɗinsa wani shegen driver ɗinta ya zo ya rusa masa komai………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣1️⃣

……..Wayar da yake faman daƙila ya ajiye, dan dama yana dannawar ne kawai badan yana fahimtar komai ba da yake yi. Ta cikin mirror yake kallonta, sai kuma kamar wanda aka tsikara ya janye yana jan tsuki. Da sauri ya furzar da iska zuciyarsa tana masa kai-kawon tunanin ina ya dace ya dosa da ita. Gidansu ko gidan Uncle Yousuf?. A gidansu tana da ƙanne, kuma basu san halin da take ciki ba bayan iyayensu, ganinta a haka garesu zai ƙarasa zubar mata da mutunci ne a idonsu har ma da ma’aikatan gidan nasu da take takawa kamar ƙasa a duk sanda taso. Gidan Uncle Yousuf kam yaransa basu da wayo sosai kasancewarsu ƙanana, zai ma iya yiwuwa yanzu sunyi barci, ajiyar zuciya ya ɗan sake ja da kallonta ta mirrorn sai kuma ya janye idanunsa a lokaci ɗaya. Har ya ɗauki waya da nufin kiran Uncle Yousuf ɗin sai ya fasa, key yayma motar kawai ya cigaba da tafiya. Kaɗan-kaɗan sai ya dubeta ta mirror har suka iso gidan. Horn yay maigadi ya buɗe ƙofa ya fito, dan ba’ace masa wani zaizo gidan ba a irin wannan lokacin dan ƙarfe sha ɗaya saura. Ƙarasowa yay jikin motar sosai, Smart dake kallonsa shima yay ɗan murmushi da faɗin “Baba Barka da dare yaya aikin?”.

      Murmushi shima maigadi yayi, dan ya ganesa. Cike da kulawa ya ce, “Mazan fama kaine yanzu da dare haka?”.

     “Eh baba na kawo wannan ne”. Yay maganar yana nuna baya, ɗan leƙawa baba maigadin yayi, ganin Lulu kwance a bayan ya sashi ɗan yin baya yana dafe baki dan shi a zatonsa ko barcin isa ne take yi. Da sauri ya koma ciki ya buɗe gate ɗin. Har gaban ƙofar shiga falon gidan Smart yay parking. Sai da ya kashe motar ya fito sannan ya ɗaga waya ya kira Uncle Yousuf. Ba’a jima ba aka ɗauka. Shi ya fara gaidashi dan a girme dai ya girmesa. Uncle Yousuf ya amsa da ƴar fargaba, sai yay saurin tambayarsa badai wani abu ya sake haɗasa da Mawaddat ba?.

         “A’a Alhaji komai bai faru ba. Itace dai na kawo nan ɗin gamu a ƙofar falo”.

     Da mamaki Uncle Yousuf ya miƙe zumbur, Jallabiyarsa ya ɗauka ya zura dan har sun kwanta ma. Ko amsa tambayar lafiya da Aunty Saliha ke masa baiyi ba ya fice cikin sassarfa yana faɗin, “Ina zuwa”. Shi da kansa ya buɗe motar ya leƙa, ƙirjinsa yay matuƙar bugawa, ɗagowa yay yana kallon Smart kallo na neman ƙarin bayani. Fahimtar hakan shi kuma ya sashi furzar da iska kaɗan. “Bayan tafiyata ta fita, jin hirarsu da ƙawarta a ɗazun ya sani sake dawowa, sai na samu zata fita shine na bita”.

        “Ya Arrahaman harma ta sha kenan?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin matsanancin damuwa.

     Tausayi sosai ya bama Smart, ya ɗan cije lips da faɗin, tana buƙatar saka ido sosai dan koba wannan halayyar bai dace ace mace kamarta tana fitar dare ba haka Alhaji”.

          “Gaskiya ka faɗa Aliyu, na kuma gode sosai da ƙoƙarinka, duk laifin na yaya ne da bazai iya tsawata mata ba a duk sanda yaga zatai fitar, amma inasha ALLAH zan ɗauki mataki ni da kaina. Sai dai abin damuwar nima ɗin wani lokacin bana nan tunda ina tafiye-tafiye, da zaka min alfarmar dawowa kusa da mu da naso haka Aliyu, wlhy na yarda da kai, ina jinka tamkar ɗan uwana na jini, zan iya bar maka amanar Mawaddat batare da jin ko ɗar ba a zuciyata….”

        “Nagode sosai da wannan karamci Alhaji. Sai dai maganar dawowa nan kam abun ne mai wahala gareni, dan Abba ma bazai yarda ba balle kuma Ammah. Sannan nima inada ƙanne, kuma suna buƙatar saka ido duk da dai ba wayona ke tsaremin su ba ko jajircewa. ALLAH ne gafurin rahimun”.

      Duk da Uncle Yousuf ya gamsu da bayanin nasa amma bai so hakan ba. Dan yana matuƙar buƙatarsa tare da su. Yaron nada wata nagarta mai matuƙar ƙayatarwa. Ga nutsuwa da cikar kamala tamkar ba talaka ba. Godiya yay masa tare da fiddo Lulu da ke sharɓan tana ɗan surutanta jefi-jefi a cikin barcin, wanda ba komai bane sai zagin Hon. Baita. Shi dai sallama yay masa zai wuce. Dakatar da shi yay da faɗin, “Kaga dare yayi yanzun. Kaje da motar gida dan abin hawa zai iya maka wahala”.

     Kamar zai ce a’a sai kuma ya tuna maganar Uncle Yousuf ɗin gaskiya ce. Dan haka ya gyaɗa kansa tare da godiya. Saida ya ga ya shige ciki sannan shima ya shiga motar ya tayar ya bar gidan. Mubarak kawai ya samu a waje alamar dai shi ake jira, cikin washe baki Mubarak ɗin ya taso yana masa sannu da zuwa da shafa motar har ya kasheta ya fito yana lucking. “Yaya ka sayi mota ne?”. Mubarak ɗin ya faɗa cikin zumuɗi. Karan farko yayma yaron ɗan murmushi. Cikin deep voice ɗin nan tashi da ta gaurayu da gajiyar son yin barci ya ce, “Daga ganin sarkin fawa sai miya tai zaƙi Mubarak? Ta mutane ce”. Kamar an zarema Mubarak lakar jiki ya ɗan rausayar masa da kai gefe kawai. Daga haka suka shige ciki gidan shiru alamar duk anyi barci, sai wasu a  ƴammatan dake waya da samarinsu, idan ka cire Asma’u da Maryam dako wayar Yayansu yama hanasu riƙewa sai ta Ammah suke ɗan ɗauka. Ɗaki kawai ya shige dan kwanciya yake matuƙar buƙata…….

         ★★★ ∆∆ ★★★

      Da asuba Uncle Yousuf da kansa ya shiga ɗakin aunty Saliha da ya kai Lulu dan ita a ɗakinsa ta kwana ya tadata yin salla. Sam bata da nauyin barci, damma yau akwai na maye tare da ita, da alama kuma ya bugar da ita da yawa, dan ma tana da jini mai ƙarfi, da ace tana da saurin buguwa ma abubuwan da MM Atik Kumo ya harmutsa mata zata iya ƙara shanye yinin yau bata san inda kanta yake ba. Amma sai gashi Alhamdullah ita da sauƙi ya saketa. Zata fara masa gardama ya daka mata tsawa. A firgice ta tashi zaune zumbur jin Muryar Uncle Yousuf tana mazurai. Sosai take zazzaro idanun mamaki, shiko ya watsa mata harara da faɗin, “Karna dawo Massalaci na tadda baki tashi kinyi salla ba, zan matuƙar ɓata miki rai”. Kai kawai ta gyaɗa masa mamaki fal ranta akan ganinta nan ɗin. Sai kuma abinda ya faru a daren jiya ya shiga dawo mata ɗaya bayan ɗaya. Cikin wani irin takaici da jin ƙuna a rai ta dafe kanta tana jan tsaki. A fili ta furta, “Sai nayi maganinka wlhy, illiterate kawai ko wa yace ya kawoni nan? To wai ubanwa ma ya nuna masa can ɗin da har ya bini?” Anya mutumin nan baida iskoki bisa kai ko? To inba mai iskoki ba itako mizata kirashi? A jiya dai tasan ya tashi a aiki ai da wuri ma. Amma kuma sai gashi ta gansa a inda babu wani mahaluki da yasan zataje. Kai wannan lamari da mamaki, dole ne tasan yanda ma akai ya bita can, kuma sai ta koya masa hankali akan shiga abinda bai shafesa ba. Nadiya ma sai ta shuka mata rashin mutuncin da bazata taɓa mantawa da shi ba da ga ita har su Hon. Baita ɗin. Jin ana neman idar da salla ya sata sauka a gadon dan tasan Uncle Yousuf babu wasa ne, ba ruwansa rufe ido zaiyi yaci mata uwa babu ruwansa da shirin da sukeyi. Wanka ta farayi sannan ta ɗauro towel Dan tana so ta sake wattsakewa. Batako zaman jiran tsanewar jikinta ba ta zura abayar Aunty Saliha. Sallar tai babu wani nutsuwar a cikinta, tana zaune a inda ta idar tana kulla mai fishseta Uncle Yousuf ya leƙo, gaidashi tayi, sama-sama ya amsa mata duk da yaga yanda ta koma kalar tausayi. Ba yanzu ya shirya mata magana ba dan haka yay ficewarsa. Ji Lulu tai gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi, sam bata ƙaunar fushin Uncle You a rayuwarta, har gara ma Daddy yay fushi da ita dan shi tasan abu ɗaya zata masa ya rikice ya dawo lallaɓata. Kuka take so tayi, sai dai ita mai juriya ce da shegen taurin kai, ba a komai take iya kuka ba komai ƙololuwar ɓacin rai ko tashin hankali da zata tsinta kanta a ciki. A karan farko taji kunyar haɗuwa da mutanen gidan, tashi tai jikinta duk babu ƙarfi, bata ko nemi jakarta da takalminta ba ta fice cikin sanɗa, taji daɗin rashin samun kowa kuwa, da sauri tabi ta ƙofar kitchen ta baya. Tunda ta fito bayin fulawoyi ke mata kallon mamaki da ga nesa, dan shi dai bai san sanda tazo gidan ba kam, ƴar tsawar da tai masa ta sakashi dawowa a hayyacinsa. “Wawa mi kake kallo ne? Dilla buɗe min ƙofa!!”. Jikinsa har kakkarwa yake duk da kuwa a girme ma zai iya girmarta shima, kuma ba aikinsa bane, ta watsa masa harara lokacin da take ficewa tare da jan tsaki. Yasan laifinsa dan haka ma baiji haushi ba. Mawaddat ta tsani taga ana kallonta, gashi kuma yau shi ta kamasa dumu-dumu. Ya san dai bala’i bai ƙare ba, dan duk randa ta dawo gidan zai sha masifa. Ƙila ma harda zagin ƙare dangi za’a haɗa masa.

        Da ƙafa ta isa gida, kasancewar garin da sauran duhu ga ɗan sanyi-sanyin da aka fara na lokacinsa. Acan ma sai da maigadinsu ya samu rabonsa na zagi. Dan shima dai galala yay yana mata kallon mamaki. Amma tunda ta fara danna masa na maguzawa sai ya nutsu ya koma gaisheta a daburce. Bata amsa ba tai shigewarta tana jan tsaki……….✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣2️⃣

……..Anan kam tasan basa barin ƙofa a buɗe, dan haka ta zagaya ta window ɗin ɗakin Iya Tabawa. Tana kuwa zaune tana addu’oi tun bayan idar da salla. Ba yau Lulu ta fara mata haka ba, shiyyasa koda ta kirata bata firgita ba. Sai ma miƙewa da tai a ɗan ɗarare. A kausashe Lulun ta ce, “Dalla Malama ki buɗen ƙofa kin wani tsaya kallo na”. Haƙuri Iya Tabawa ta bata ranta fal wasi-wasi. Zuciyarta ta fara raya mata ko dai yawon banza Lulu ke fita ne, tunda ba taɓa ganinta cikin maye tai ba. A ƙasar Hausa kam mafi yawan al’umma sukan fassara yawon dare na ɗiya mace da tazubar ne kawai, da wahala hasashensu ya wuce haka har su hango wasu abubuwa masu illa a rayuwar ƴaƴanmu mata bawai zina kawai ba. Sun manta a rashin ji duk abinda namiji yasa kansa iyawa wasu matan kan kwatantashi ba wai sai iskanci kawai ba. (Ya rabbi ka shiryar damu da zuri’armu baki ɗaya).

     Tana shiga ɗakinta a saman katafaren gadonta ta zube tana mai sauke numfashi, lamo tai cikin lallausan bedsheet da duvet ɗin gadon masu ltaushin tsiya da ƙamshi. Tunanin matakin da zata ɗauka akan tsageran driver ɗinta takeyi, da su Hon. Nakowa, sai dai kuma barcin da bai gama fita idonta ba ne yaci ƙarfinta……

       ★Kasancewar alerm data saita ƙarfe takwas ta farka badan barcin ya isheta ba. Sai dan tana da shari’a mai zafi a yau ɗin da zata gudanar wadda a yau ɗin take fatan alƙali ya yanke hukuncinta. Cikin rashin kuzari ta tashi ta faɗa toilet, sai da ta gamsu da gyara jikin nata a fannin wanka sannan ta fito. Shiri tayi tsaf da ita cikin suit na mata kalar baby pink, rigar cikinta fara. Dan ƙyau kam tayi ƙyau, ga shegun takalmanta masu dogayen dudduge ɗin nan da tsabar ƙwarewa a sakasu yasa ko gargada batayi a tafiya da su. Yau dai anyi abun arziƙin saka ƙaramin baby hijab fari da yay mata ƙyau sosai, sai dai iyakarsa kafaɗarta dan ƙaramine. Ƙamshin nata na fitar hankali ta bulbula a jiki har ita da kanta tanajin ƙamshin na hawa mata kai, sai dai haka take buƙatarsa. Cikin takun nan nata na isa da gadara ta fito, illahirin jikin nan na motsa kansa kamar wata tarwaɗa a ruwa. Mubeen kawai da Daddy ta samu a dining suna breakfast, sai Mommy tana tsaye a tsakkiyarsu da alama abincin take haɗa musu.

       “Good morning Daddy & Mommy!”. Ta faɗa kanta tsaye babu wani alamar respect gareta matsayinsu na iyayenta. Musamman ma Daddy dake amsa sunan mahaifi. Kowa dai yasan yanda ƴaƴa ke shakkar iyayensu maza fiye da mata a ƙasar hausa. Mommy dai kallonta kawai tai ta girgiza kanta. Shiko Daddy fuskarsa a washe da murmushi, duk da dai kamar alamunsa na nuna yana cikin damuwa ne yake dannewa.

        “Morning sweet heart. Kin tashi lafiya? Yaya ƙarfin jiki”.

          “Komai normal Daddy”. Ta faɗa tana ɗaukar shayin gabansa da yake sha ta kurɓa da ga tsayen da take. Da kallo ya bita har yanzu da murmushi a fuskarsa. “Babyna zauna mana kisha ba ƙyau shan abu da ga tsaye ai”.

     “No Daddy, hakan ma it’s ok for me. Ina sauri ne 9:30 inada Shari’a”.

   “Allah yay miki albarka, ya kare munke ga duk wani sharrin maƙiya na gida dana waje”.

           “Amin sweet Papa na”.

     Sarai Mommy ta fahimci harda ita a addu’ar tasu. Hakama Mubeen. Dan tuni sun gane abinda mahaifin nasu kema Mommy akan ƴar uwarsu. Sai dai ko sunce zasu ɗauki mataki hanasu yin hakan Mommyn take yi. Babu yanda suka iya dole suke haƙura. Amma badan jajircewarta a kansu ba ba ƙaramar tsanar Lulu sukeji ba a rai. Wani lokacin ma hatta shi Daddy ɗin takaici yake basu  shiyyasa su ƴan biyu sam basu son zaman gidan. Harta ɗan sha shayin na Daddy kusan sau bakwai ta ajiye Mubeen bai mata magana ba itama batai masan ba. Batama nuna tasan da zamansa a wajen ba kamar yanda shima ya nuna. Tana shirin sauka a ɗan steps ɗin hawa dining ɗin Daddy ya dakawa Mubeen ɗin tsawa.

       “Kai dan uwarka ita ɗin sa’arka ce da bazaka gaishe ta ba?!”.

     Kallon Daddy ɗin Mubeen keyi zuciyarsa a bushe, sai kuma yaja numfashi mai nuna zuciyarsa na yunƙurowa, sai dai kallon gargaɗi da Mommy ke masa ya hanashi cewa komai da ga tarin abubuwan faɗar da ke cikin bakinsa game da mahaifin nasu. A hankali ya furta “Daddy kayi haƙuri” kawai yaja bakinsa ya tsuke.

            Tsaki daddy yaja dai-dai Lulu na ficewa a falon gaba ɗaya. Bata jira jin abinda Daddyn ke shirin faɗa ba. Karo na farko a rayuwarta taji kamar babu daɗi akan abinda Daddy ɗin kema ƴan uwanta saboda ita. Har ga ALLAH tana ƙaunar ƴan uwanta, hasalima bata haɗa son su da komai ba. Hatta su Yaya Hassan batajin daɗin rayuwar doya da manjan da ke a tsakaninsu. Dan ko gidan su ƴan biyun sukazo basa kulata bata kulasu, saboda sun riƙe abubuwan da mahaifiyarsu ta fuskanta da ga mahaifinsu dalilin mahaifiyarta da ita kanta. Goshinta da yay mata nauyi saboda abinda ta sha jiya bai gama sakinta da ƙyau ba ta ɗan shafo tana furzar da iska. Ba ƴan uwanta kaɗai ba hatta Mommy tana jin ƙaunarta, dan kallon uwa take mata a zahiri da baɗinin rayuwa. Ta sani duk wanda yasan gidansu ma ya sani Mommy bata taɓa cutar da rayuwarta ba koda da harara, idan dai tayi laifi yanda take ma yaranta faɗa itama haka take mata. Shiyyasa duk rashin mutuncinta har abada bazata taɓa kwatantashi ga Mommy ɗin ba. Musamman ma idan ta tuna nasihar da Kakanta Alh. Sufi Garko kanyi mata a duk sanda taje garesa game da Mommy ɗin da halaccinta ga zamantakewarta da mahaifiyarta. Duk da dai itafa har yanzu bata taba jin labarin ainahin zaman da Mamanta tayi da Mommy ɗin ba…… Gaisuwar da ma’aikatan gidan ke mata ce ta katse mata tunani, batare data kalli ko guda a cikinsu ba take wucewarta kawai da takun nan nata na yauƙi da isa. Tana gab da isa motar da take buƙatar hawa idanunta suka sauka akan Smart da ke zaune wajen maigadi kamar kullum hankalinsa a waya yana buga game ɗin ball da yake matuƙar bege. Sake tamke fuska tai da ɗauke kanta, abinda ya faru jiya ne ya shiga mata kaikawo cikin kai. Sosai taji ɓacin rai ya sake baibayeta da takaicin su Nadiya da suke son jamata rainin nan wajen wannan shashashan, ta jima tana shaye-shaye, amma duk wanda yay mata sani na haƙiƙa bai san wannan halayyar tata ba, a koda yaushe cikin ƙoƙarin binne sirrinta take, amma sai gashi a haɗuwarta da mutumin da tafi tsana fiye da kowa a duniya shi ya ganta a yanayin. Ƙwafa tai da balla masa harara, cikin borin kunya ta cilla masa key da sake jan tsaki. Idanunsa da ke nuna alamun barci bai ishesa ba ya ɗan lumshe ya sake buɗewa, batare da ya kalleta ba ya miƙe zuwa gaban Motar data ɗakkoma key ya buɗe mata bayan, sai da ta shiga ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver, motace mai tsadar gaske da ɗaukar hankali, kasancewarta ƴar gatan gidan hatta Daddy tafi yawan motoci. Dan motarta biyar kuma duk ƙosassu, sai ƙarama ɗaya da sha’awa kawai ya sata matsawa Uncle ɗinta Khamil ɗan uwan mahaifiyarta dake Abuja saya mata ita. Dai-dai suna barin kan titin layin nasu ya miƙa mata handbag ɗinta ta jiya da key ɗin mota, a hankali ta ɗago da ga duba takardun da takeyi ta ɗan sake hararsa sannan ta kalla kayan a yamutse. Murya a dake sai dai acan ƙasan maƙoshi ta furta, “Waya gayyaceka inda nake jiya?”.

        Sarai ya jita, amma sai yay kunnen uwar shegu da ita ya haura kan babban titin bayan motar da ya dakatama ta shige layin da ya fito. “Malam da kai nake yi”. Ta sake faɗa cikin zafin rai da borin kunya. Karan farko ya ɗan ɗago idanu ta cikin mirror ya dubeta. Ido suka haɗa, tai saurin kauda nata zuziyarta na tsirgawa. Itafa komi za’ai ayi amma kar ya kalleta da wannan shegun idanun na macizai (kamar yanda ta raɗa musu😂🥱). Yanda tai ɗin sai ya so bashi dariya, amma sai baiyi ba ya ɗan saki murmushin gefen baki da maida hankalinsa ga titi cikin salon lumshe idanun nasa kamar yasan suke razanata, babu alamar zai bata amsar da take buƙatar son ji. Ba ƙaramin takaicinsa bane ya kume Lulu, ga wayarta ta isheta da ruri. Nadiya ce keta faman kiranta tun ɗazun, sai dai taƙi ɗagawa dan tai alƙawarin sai ta koyama ƙawar tata mafi kusanci hankali. Tsaki taja a karo na babu adadi, ta fisgi wayar da ke kan rigarta ta lauyoyi ta kashe tare da sake cillar da ita kan rigar da ke a gefenta. Haushin Nadiyar dana sharetan da yay ta tattaro gaba ɗaya ta nufesa da shi.

      “Wai kai mika ɗauki kanka ne da har ina maka magana kana wani cika da batsewa?”.

    Yanda tai maganar muryarta har tana zuga kamar wadda kuka ke son yunƙuromawa sai dai ƙarfin halinta na dannesa ya sashi sake dubanta a karo na biyu ta cikin mirrorn. Sake maida kansa yay ga titin sai kuma ya ɗan muskuta zamansa da furzar da iska. Ƙasa-ƙasa na rashin kuzarin da kasala irin na wanda barcin bai ishesa ba cikin deep voice ɗin nan ta shi ya ce, “Mi kike son sani?”.

           Wata irin kasala muryar tasa ta nema saukar mata saboda yanda yay maganar cikin sanyi da tausasa lafazi, sai dai cikin yaƙi da kai da nuna juriya irin ta masifaffun mutane ta watsa masa kallon banza da yin ƙwafa tana maida kanta ga takardun da take dubawar. Kamar bazata ce komai ba sai kuma bayan kusan minti ɗaya ta ce………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣3️⃣

………“Waya aike ka inda ka sameni jiya? Miye ma dalilinka na bina?”.

        Idanu ya lumshe tare da buɗewa a lokaci guda. Kamar yanda yay magana ɗazun a tausashe yanzu ma haka yayi. “Baki so asan kina aikata abinda na gano ɗin ne?”.

     “Kai ɗin banza da zanji ina son ɓoye maka abu. Shiga abinda ban saka ka bane ya sa nake neman ba’asi dan bana son shiga sharo. Idan kuma kace zaka cigaba da shiga min hanci wlhy zan saka ka dana sani kai da duk wanda ma yake maka kallon arziki. Tsabar kai ɗan haɗin masifa ne ka ɗauke ni ka kai gidan Uncle you.., wlhy kasan mima zaka faɗa masa, in ba haka ba sai naje har gidanku kaima na maka ƙullin da har gaban abada baka isa ka kwancesa ba ɗan sa ido kawai. Idan kuma kaji ƙarya mu zuba ni da kai mai shishshigin tsiya, kai a dole sai ka shiga jikin iyayena dan maular tsiya irin ta talaka”.

          (Maula! Talaka!) Zuciyarsa ta maimaita cikin jin ƙunar kalmomin. Kamar zai yi magana sai kuma ya haɗiye abinsa dan ya fahimci al’amarinta na buƙatar sai da uzuri, idan yace zai biye mata sai ma su zama ɗaya. Yanda bata sake magana ba tana ta faman duba takardun nata shima bai sake kallon inda take ba, sai dai ƙamshin turaren data bulbula ya addabesa har yana hawar masa kai kamar yanda itama nashi ke cizon can ƙasan zuciyarta. A cikin tsare-tsaren da Uncle Yousuf ya bashi nata ya sashi sanin inda zasu je a yanzu ɗin, dan haka kai tsaye babbar kotun da muke kira da (kotun ALLAH ya isa) dake a jiha ya nufa. Tamkar ba safiya ba harabar court ɗin cike da mutane, hancin motar na kunna kai cikin gate ɗin wasu gungun ƴan jarida suka yomusu caa, isowar securitys da ke son hana ƴan jaridar isowa garesu ya ɗan maido hankalin mutane kan motar suma. Kafin ya gama kashe motar har an buɗe mata. Fuska a yamutse da ɗan jan tsoki ta kalla harabar court ɗin. Wanda ya buɗe matan ta miƙama tarkacen hanunta tare da rigarsu ta lauyoyi. Ita kuma ta ɗauki handbag ɗinta bayan ta toshe fuska da wani shegen gilashi mai tsananin ƙyau ta haɗa da hular, dai-dai tana ficewa ta balla masa harara da faɗin, “Saura nan ma kace zaka biyoni kaga yanda zan baka mamaki”.

        Da kallo kawai ya bita, sai kuma ya ɗan furzar da iska ransa fal mamakin yanda bata gajiya da masifa. Da ga can ƙasan ransa kuma yanda ake ta bata wani girma da kariya da ga security ɗin da zallon da ƴan jarida ke faman yi na son isowa gareta ya ƙara ɗaure masa kai da jin takaicin da sun san wacece a zahirinta da ko kallon mutuntawa bata cancanta a garesu ba. Bai iya ɗauke idanunsa garesu ba dan takaici har suka shige wata ƙofa ba ainahin ta Court ɗin ba. A take ya ga gurin ya sake ribcaɓewa, mutane sai faman ɗura kai suke cikin court ɗin. Maganar wasu samari da ke wuce motar cikin ƙaucin shiga kotun ta ɗan ja hankalinsa. Na farko mai riƙe da camara ke faɗin, “Yaufa akwai ƙura, dan na tabbatar barrister Mawaddat Jiƙamshi ba ƙaramin sabon shiri tayo ba duba da yanda Barrister Marafa ya nema zubar da ita a wancan zaman. Kasan fa ita bata taɓa bari a kaita ƙasa musamman a kan irin wannan case ɗin na fyaɗe, ga shi tasan aikinta lawyers ƴan uwanta da yawa har tsoron karawa suke da ita, dan ita ko waye ma ubanka akan fyaɗe sai tayi kutu-kutun turaka jail dan haka kullum ita bata kare mai laifi sai wanda aka zalunta musamman ƴan uwanta mat…….”

     Bai ƙarasa jin abinda saurayin ke son faɗa ba dan sun masa nisa. Da farko baiyi niyyar shiga wajen ba, sai dai saboda gargaɗinta ya ƙudiri shigar dan yaga mizata iya masan. Ƙoƙarin fitowa yay a motar kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share sai kuma ya cirota da ga aljihu. Ƙanwarsa ce mai bimasa Hawwah dake auren abokinsa. Ɗagawa yay, sai dai yana kaiwa kunnesa yay saurin janye wayar yana mai lumshe idanunsa. Buɗesu yay a hankali zuciyarsa na wani irin zallo. Cikin motar ya koma tare da sake kiranta. Ringing ɗaya ta ɗauka. Cikin matsanancin kuka ta ke faɗin, “Yaya dan ALLAH ka barni na taho gida. Wlhy na gaji da wannan rayuwar bazan iya ba. Inko ba haka ba wataran sai mahaifiyar Abban Nasreen ta kasheni a gidan nan….”

       Iska ya ɗan furzar mai ɗaci, tare da faɗin, “Miya kuma faruwa?”. Sake fashe masa tai da kuka, da ƙyar ta iya faɗin, “Mai fa da nake suya airish ma Nasreen da zata wuce school ta kusa kwaramin yau a jiki Yaya. Ban san wane irin rashin ƙauna matar nan take min ba. Wlhy bazata taɓa canja halinta ba nima na gaji da haƙuri da ita.”

         “Shi ina Sa’id ɗin yake?”.

     “Yaya yana fa a gidan, gashi can ya jata wai yana bata haƙuri saboda ni ba’a san ciwona ba. Yanzu Yaya data sameni da man nan haka zai tsallakeni ya bita ke nan….”

    “Kinga ya isa. Ki jirani gani nan zuwa gidan yanzu”. Da ga haka ya yanke wayar batare da ya jira abinda zata ce ba. Fitowa yay a motar ya kulle. Da ƙafa ya fita a habar court ɗin da ta yi tsittt alamar an fara shari’ar ko za’a fara. Yana fitowa a gate ɗin ya samu napep zuwa Daurawa anguwar da gidan ƙanwar tasa take. Kasancewar safiya ce basu wani samu matsala ba, dan haka suka iso da wuri. Bayan ya biya mai napep ɗin maimakon shiga gidan kai tsaye ko yin knocking sai ya ɗaga waya yay kiran abokin nasa Sa’id Ibrahim da sukai karatu a jami’a tare. Yanda Sa’id ɗin ya ɗaga wayar ta isa tabbatar da a rikice yake. Dan duk ya daburce sallamar ma da in ina yayi ta. Sai kuma ya shiga kame-kamen gaisuwa. Katsesa Smart ɗin yay da faɗin, “Gani a ƙofar gidanka ka turo min Hawwah zamu wuce gida”.

        “G…g…gida kuma Mawashi? Miya faru ka…k…kake wannan maganar haka? Ko itace ta kira ka ta faɗ……”

     “Sa’id!!”.

Ya dakatar da shi a harzuƙe. Sake tsurewa Sa’id ɗin yayi dan yasan halin abokin nasa sarai. Bai da yawan magana ko hayaniya, dan bai taɓa ji ko ganin abokin faɗan Smart Mawashi ba a rayuwa. Amma shi kaifi ɗaya ne akan komai da kowa. Duk yanda yake da kai bai yarda ka latsashi ba ko gasu abokai. Yanda ya rikice ɗin sai ya harzuƙa ran mahaifiyarsa da ta hanashi fita duba matarsa. Dan ta rantse ko bakin ƙofa yaje domin Hawwah ɗin sai ta tsine masa. Cikin masifa ta wafce wayar, kunnenta ta kai da faɗin, “To ɗan mulkin mallaka wai shin nikam ko kai ne ka haifa min Sa’id ne ban sani ba? To bazai zo ɗin ba, nace bazai zo ba idan ka isa kai duk abinda kake jin zaka iyayi, ko ita ƙanwar taka autar mata ce da in ya rabu da ita zai kasa cigaba da rayuwa har ya auro wasu huɗun. Aikin wofi kawai anga kuɗi an nanema yaro na”.

     Har tayi ta gama bai ce uffan ba, sai da yaji tayi shiru ya yanke kiran. Yanda yake huci zai baka tabbacin sanin ran ƴan maza ya kai ƙololuwar ɓaci. Number Hawwah yay kira, bugu ɗaya ta ɗaga. Kafin tace komai ya ce, “Ɗakko mayafinki ki sameni waje”. Ya yanke kiran. Minti shida kuwa bata gama cika ba sai ga Hawwah da ƙaton akwati da Nasreen ƴar shekara huɗu biye da ita. Tana ganinsa ta cilla da gudu garesa tana faɗin, “Oyoyo Uncle”. Kaɗan ya saki murmushi, tare da duƙawa ya ɗauketa ita da school bag ɗin da ke goye a bayanta alamar an gama mata shirin makaranta ne. Sau ɗaya ya kalla ƙanwar tasa ya kauda kansa. Batare da yace komai ba ya amshi akwatin hanunta yay gaba tabi bayansa. Napep ya tare musu suka shiga, Nasreen nata zuba masa surutu dan yarinyar ko akku haka ta ganta ta bari kamar ƴar ƙwa-ƙwa akwai wayon jaraba. Dan bakinta ya girmi shekarunta. Sai da ya kaisu har gida sai dai bai shiga ba yace taje ta jirasa zai je ya dawo. Bata musa ba ta fita, shi kuma yace ma mai napep ya juya da shi babban kotun dake jaha. Ya samu har an fito da ga shari’ar, yanda harabar kotun ke’a harmutse da ƙayataccen murmushin da ya hango a fuskar Lulu ya sashi tsira mata idanunsa. Tsaye take a tsakkiyar lauyoyi ƴan uwanta wanda da alama duk ƴan ɓangare ɗaya ne a shari’ar, dan yanda fuskokinsu ke a washe kamar ita saɓanin waɗanda ke gefensu kaɗan zai baka tabbacin hakan. Ƴan jaridar da suka zagayesu ya sashi daina iya hangota, ɗauke kansa yay tare da buɗe motar ya shiga, a kallo ɗaya zaka fahimci damuwar dake zagaye da fuskarsa, dan babu abinda ke faman masa kai kawo sai batun ƙanwarsa Hawwah, shi shaida ne Sa’id na matuƙar son Hawwah, sai dai matsalar mahaifiyarsa da tun farko ta nuna bata son auren saboda ƴar ƙanwarta da taso ya aura shi kuma yaƙi tsayawar mahaifinsa ta sa ta janye ta amince ya auri Hawwah, sai dai tunda take gidan mahaifiyar tasa ke nuna mata hantara da ƙyara musamman idan Alh. Ibrahim mahaifin Sa’id ɗin baya gari. Tasha marin Hawwah ɗin dayi mata abubuwa masu cin zuciya shi yana zuwa ya sasanta bada sanin iyayensu ba. Sai dai a wannan karon ya fahimci dole ne fa a tauna tsakkuwa dan aya taji tsoro. Dan tsohuwar na buƙatar sanin Hawwah nada gatan iyaye da dangi itama, sannan dukiya ba itace rayuwa ba kawai akwai muhimman abubuwa da suka fita a zamantakewar rayuwa. Kai dai kai fatan kawai ALLAH ya rufa maka asiri kafi ƙarfin yau da gobenka. Idan kuma ya azurtaka da dukiyar ka bida ita ta hanyar da kai a karan kanka zakai alfahari da kanka watarana da zaka amsa tambaya akan dukiyar kwabo bayan kwabo……..✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣4️⃣

………Gigitaccen knocking ɗin da akai ma glass ɗin motar ne ya sashi dawowa hayyacinsa. A hankali ya buɗe idanunsa da sukai mugun kaɗawar ɓacin rai ya sauke a kanta. Harara ta balla masa da juyayyun idanun nan nata da shaye-shaye ya gama canjawa yanayin kallo.

         “Kai anya kuwa ka taɓa shiga ajin makaranta? Dan na fahimci baka san aikin ka ba, malalacin banza kawai ka zauna kanama mutane tunanin iska a mota, ko an gaya maka a banza ake mallakar irin motar har ai zaman tunani a cikinta Mtsowww!! Baƙauye”. Ta buɗe motar a fusace ta shige tare da rufe murfin da ƙarfi. Fitowar da yay niyyar yi buɗe mata ya fasa, batare da ya tanka mata ba kamar yanda ya saba yayma motar key. Bata sake bi takansa ba ta maida hankalinta a lap-top itama, yayinda shi kuma yake tafiya a nutsensa. Sunyi nisa sosai batare da ko sau ɗaya ta ɗago taga ina suke nufa ba, dan ita duk zatonta hanyar office ɗinta ya nufa da ita tunda Uncle Yousuf yace mata ya bashi komai nata a rubuce. Jinfa tafiya na neman ƙin ƙarewa ya sata ɗagowa. Da sauri ta ƙara ware Lulu ayes ɗinta tana kallon inda zata iya rantsewa bata taɓa sani ba ma, dan ita dai kusan yawonta wajen Kano a jirgi ne. Gabanta ne ya faɗi, zuciyarta ta shiga mata kai-kawon ko yayi kidnapping ɗinta ne? Amma sai ta dake a masife ta ce, “Kai malam mi kake ƙullawa ne? ina ne kake shirin kaini nan?”.

      Shiru kamar bazai tanka mata ba, dan har ya kunnata ta ƙara ƙarfin hucinta. Sai kuma cike da rainin wayo ya bata amsa cikin halin ko’in kula da cewa “Asibiti ganin likitan ƙwaƙwalwa”. dai-dai yana ƙoƙarin shiga ƙaton gate ɗin asibitin na dawanau.

         “What?! Wai nice ka kawo duba masu taɓin ƙwaƙwalwa kake nufi ko mi?”. Tana sake ware idanunta kan rubutun saman ƙaton ginin inda yay parking. Bai tanka mata ba har sai da ya kammala dai-daita motar a gaban wajen. Kasheta yay gaba ɗaya tare da kai idanunsa kanta ta cikin mirror. Kallon nasa kuwa take itama dan tsabar takaici ya hanata iya sake cemasa komai amsar dalilin zuwansu kawai take buƙata da ga garesa.

       “Kinada kati anan ne ko yau za’a fara yankar miki? Dan naga kamar ƙwayar da kika sha jiyan bata kammala sakinki ba”. Ya faɗa a dakensa.

     “Kai! Wai dama ni kake nufin inada taɓin ƙwaƙwalwar ma kenan?”.

    Idanunsa da take kira na macizai ya wara mata cike da salon sake tura mata takaici. Sai kawai taji ƙwalla na neman cika mata idanu. Tunda take a duniya bata ko tuna an taɓa wulaƙantata makamancin yau ba, ba zuciyarta ba hatta numfashinta fita yake da sassarfa. Wai ita wannan ya kawo asibiti, asibitin ma na masu taɓin hankali. Babu abinda take ji a ranta kamar ta haɗama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa jini da majina da maruka fiye da yanda ya yagata, ta dunƙule hannunta amma hannun ya gagara ɗaguwar aikatawa. Maimakon ma hakan kanta kawai ta dafe dan jin zuciyarta na barazanar tsagewa biyu. Batajin idan ta sake kai mintina sama da uku a motar nan bata shaƙe mutumin nan ya bar duniya ba. A wani irin harzuƙe ta bankaɗe murfin motar ta fita, inda yake zaune mazaunin driver ta buɗe. Shi kansa bai taɓa ganin ɓacin rai tattare da ita irin yau ba, dan tsabar masifa fuskarta har jaja takeyi….

       “Fitar min a mota!!”.

    Ta faɗa da ƙyar muryarta har rawa takeyi. Cikin deep voice ɗin nan tasa da sake dakewa ya ce, “Maizasa na fita bayan akan aikina nak…..”

     “Wlhy zan kashe fuskarka da mari idan baka fitar min a mota ba tunda ban haɗa kuɗi da kai na saya ba!!”. Ta sake faɗa a wani yanayin da muryarta ke fita da cracking. Ya gama sanin ta kai ƙololuwar fusatar da yake buƙata, dan haka cikin taɓe baki ya fice yana wani murmushin da ke sake tafasa mata ruhinta shiko yana sake ƙayatar da kwarjininsa.

       “Ka rubuta ka ajiye sai na wulaƙanta rayuwarka a mizanin mafi munin wulaƙanci”. Ta faɗa dai-dai tana fisgar murfin motar bammm! Ta rufe. Kamar yanda ta saba a guje ta fice a asibitin, dan Lulu akwai iya tuƙin ganganci da wauta balle yau da ya zama an kunnata ne, shiyyasa Daddy yafi son driver ya jata a mota. Da gaske tuƙi take irin na wauta da isa, har takai wasu drivers ɗin na zaginta idan tai wani abun cike da gadara. Tana kan round about ɗin da zata ɗauki titin office ɗinsu ta kusa haɗa accident sakamakon neman shallakewar ƙin tsayama traffic light data nema yi. A fusace drivern data dakarma mota ya fito, itako babu alamar ko ɗar a tare da ita ta ƙara sautin kiɗan wakar Shakira da ke tashi a motar, dan tana matuƙar son waƙoƙin mawakiyar, shiyyasa bata da wakar data bama amanna kamar waƙoƙinta musamman idan tana cikin ɓacin rai irin haka.

         “Ke ƴar uban wacece da zaki da kar min mota ki cigaba da zama a ciki kamar bakiyi ko mai b……..” ya gagara ƙarasawa saboda tozali da abinda baiyi zato ko tsammanin gani ba. “Ni ƴar gidan ubanka ce!!”. Lulu da dama take a harzuƙe jira take a taɓata ta fashe ta bashi amsa a fusace itama. Kansa ya ɗan dafe da wani irin salo yana juya jikinsa kaɗan, sai kuma ya sake jiyowa gareta da ɗan kuzari ya ranƙwafo a motar. “Oh Baby dama ke ce? Please am so sorry”.

     Harara ta balla masa tare da jan sirrin tsaki ta ɗauke kanta. Zai sake magana ta ɗaga masa hannu, tare da ɗakko bandir na sabbin dubu ta jefa  masa a harzuƙe. “Ko basu kake buƙata ba dama?”. Siririyar dariya ya saki mai ƙayatarwa. “Mai sunan gwaggo kenan, ni bance ina buƙata ba, sai dai idan kin bani ƙyauta ne zanso haka. Koba komai ƙyauta da ga masoyiya zuwa masoyi ai abin alfahari ne ko”.

         “Tajuddeen bani hanya na wuce kafin kaja na sauke maka abinda ke kaina wlhy!! Dan inada abunyi”.

       “Zan iya ɗaukar ko miye da ga kanki ko mi nauyinsa, sannan nima inada abunyi dan haka ma kika ganni da farar safiyar nan akan titi, duk da dai naci ribar fitar kodan ganinki da nayi”.

       Maimakon amsa masa sai taja tsaki, tare da yin sama da glass ɗin motar. Da sauri yaja da baya dan neman takashi take yi. Cikin murmushi da cizar lips ya duƙa ya ɗauki kuɗin nan data jefesa da su a ƙasa yana kaisu hancinsa dan tuni ƙamshin turarenta mai ƙarfi ya mamaye su. Duk abinda ke faruwa akan idanun Smart ne da ke cikin napep kamar sauran mutane, dan tana baro asibitin yay murmushi, sai dai da sauri shima ya fito saboda ganin yanda ta fisgi motar cike da ganganci ya kuma san bata san hanya ba sosai, baya fata wani abu ya sameta a dalilinsa, cikin sa’a ya samu napep, dan haka yace masa su bita, sai dai tuni ta musu fintinkau saboda gudun da take zubawa dan har ta ɓace musu, sai gashi kuma sun haɗu a traffic light ɗin. Ƴar hayaniyace ta fara tashi, wasu na zagin Lulu wasu najin haushin Tajuddeen da ya taso gigigi ya kuma koma yay sakwat, daka gansa dai shima kasan akwai nerar balle ace saboda kuɗin data watso masa ne. Sai dai wasu sun fahimci ma dai kamar sun san juna ne shiyyasa, amma hakan bai hana ƙananun maganganun ba dai. Sirrin tsakin da bai shirya bane ya fita a bakinsa a karo na farko. Yana ƙoƙarin ɗauke kansa da yima mai napep maganar su juya titin anguwarsu dan ya fasa bin bayanta da yay niyya idon Tajuddeen ya sauka a kansa. Murmushi ya sakar masa da ɗaga masa hannu, hakan yasa shi dole fitowa fuskarsa a ɗan sake shima ya miƙa masa hannu suka gaisa. “Ya naga yau tafiyar taku daban-daban? Koda yake da alama yau ogar taka fitina take ji”. Tajuddeen ya faɗa da alamar ƴar damuwa, dan harga ALLAH yana matuƙar son Lulu. A karo na farko Smart ya ɗan saki murmushi mai sanyi. Cikin nutsuwar nan tasa, sai dai a can ƙasan maƙoshi ya furta “Ita dama kullum a cikin rigimar take ai. Tunda ta tsere mana ma zan juya gida ne kawai”.

      “A’a ba’ayi haka ba. Bari mu ƙarasa dan office ɗin nasu kusa yake damu”. Badan Smart yaso ba Tajuddeen ya biya mai napep da ya ɗakkosa, shi kuma suka shiga motarsa a tare. Tunda suka bar wajen Tajuddeen ɗin ke jansa da hira. Shi dai nashi murmushi ne kawai bai iya cewa komai. Tajuddeen ya fahimci Smart bamai yawan magana bane, sai dai sam baza’a taɓa kiransa miskili ba. Kawai dai shiru-shiru ne shi bai cika hayaniya bane. Tafiya kaɗan ta kawosu, guri ne mai ƙyawun gaske da ɗan girma dan gaskiya ya tsaru. Tajuddeen yaso su shiga tare da Smart amma yaƙi ya ce ya barsa anan wajen, badan yaso hakan ba ya barsa nan jikin motar shi kuma ya shige. Ya ɗan gaisa da tsirarun ma’aikatan da suke kai kawo saboda sun sanshi dan lokaci zuwa lokaci yakan ɗan zo wajen Lulun, da ga haka ya nufi lifter zuwa 3floor. Offices ne kusan goma a wajen, a office na kusan bakwai, a hankali idanusa suka sauka kan rubutun saman da aka rubuta. *_Barrister Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi_*.

      Kai tsaye Tajuddeen ya shige babu wani neman excuse, ƙaramin falo ne dan table ɗin sakatariyarta ne kawai sai kujeru uku 3sitter da 1sitters guda biyu da table a tsakkiyarsu. Da ga ɗan gefe kaɗan water dispenser ce mai ƙyau sai tv da ke maƙale acan sama. Glass ne ya raba wajen da office ɗin ta, dan haka ya iya hango yanda take ma wata dake tsaye gaban table ɗin ta masifa, duk da bajin mi take faɗa yake ba yanayin yanda take karkaɗa hannu ya bashi tabbacin hakan. Da sauri Tajuddeen ya tura ƙofar ya shiga, a tare Lulu da sakatariyarta da ke shan masifa dan a kanta ta hau juye takaicin Smart suka juyo……..✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣5️⃣

……..Fuska Lulun ta sake tsukewa, yayinda sakatariyar ta risina tana gaishesa dan tasan ko wanene tunda ba yau ya fara zuwa ba.

      “Jeki abunki”.

Ya cema sakatiyar yana kaiwa zaune. Sakatariyar ta ɗan kalli Lulu a tsorace, sai kuma ta dubesa cikin girgiza kai kamar zatai kuka. Shima Lulun da ke faman haɗa takardun gabanta ya kalla, sai kuma yay ɗan murmushi. “Madam please taje?”. Harara ta ɗago ta balla masa, ta sake maida kanta ga abinda take yi. Ƴar ƙaramar dariya ya ƙarayi mai fidda haƙora, tare da yima sakatariyar nuni da hannu alamar taje. Da sauri ta fice har tana neman cin tuntuɓe. Idanunsa da ke ma sakatariyar kallon ƙasa-ƙasa ya janye ya maida ga Lulu… “Miyasa ka biyoni?”. Ta katse maganar da yay yinƙurin mata. “Idan masoyi ya biyo masoyiyarsa laifi ne Mawaddat. Please ki daina wahal damu haka mana, ko so kike sai na kai ƙasa ne?”.

       “Bani da matsala da kaiwarka ƙasa Tajuddeen, matsalata ɗaya shigarmin rayuwa da kake yi. Ka bar wahal da kanka dan bazaka taɓa samuna ba. Ko’a baya na amince ma batun su Daddy ne saboda Grandpa kaima ka sani. Amma ban taɓa jin sonka ba, kai bama kai ba, duk wani namiji ban taɓa jin sonshi da sunan soyayya ba a rayuwata. Idan ka cire Daddy na, Grandpa, da Uncle you. Ina baka shawarar ka daina bibiyata dan ina ɗaga maka ƙafa ne saboda zumincin da ke tsakaninmu, idan kuma ka cigaba zan iya fyatoka ta duk inda yay mun bawai hancina kawai ba”. Daga haka ta miƙe hannunta ɗauke da takardun data tattara. Cikin takun nan nata na yauƙi. Tamkar wanda ta danne bakinsa da dannau ya kasa iya furta komai sai binta da kallo da yay cikin tashin hankalin kalamanta. Ya jima da fahimtar bata ra’ayinsa a yanzu, amma bai taɓa tunanin tun farko ma bata taɓa sonshi ba alfarmar Grandpa ɗin su yaci ba. Hannunsa ya kai saman goshinsa ya shiga murzawa, dai-dai nan sakatariyar Lulu ta shigo. Ɗagowa yay yana kallonta, ta ɗan rissina da girmamawa ta ce, “Sorry sir ta ce na rufe mata office ɗin”.

     Idanu ya ɗan lumshe ya sake buɗewa akan matashiyar yarinyar mai tarin nutsuwa. Sai kuma ya saki murmushi da jinjina mata kansa ya miƙe kawai. “Sorry sir” ta sake faɗa dai-dai yana fita. Hannu kawai ya ɗaga mata batare da ya juyo ba ya fice abinsa zuciyarsa fal damuwa. Koda ya fito ƙurar motarta kawai ya samu alamar ta fice. Ya kalla Smart da ke jigine jikin motarsa da waya a kunne alamar magana yake. Tsaiwar jiransa yay har ya kammala. Bayan ya kammala wayar ya juyo idonsa akan Tajuddeen da fuskarsa ta nuna alamun ɓacin rai da damuwa, kai tsaye ya furta, “Inaga zan wuce gida dan wani uziri ya taso min”. Cikin damuwar dake shimfiɗe a fuskarsa ya gyaɗa masa kai da ɗan ɗage kafaɗa. “Ba damuwa ai itama ta sake tafiyarta”. Sam shi Smart bai ga fitar Lulu ba, dan haka ya kallesa cikin son ƙarin bayani. “Ina magana ne akan ogarka bakaga fitar ta ba?”. Smart ya kai dubansa ga inda ya ga motarta tun shigowarsu, wayam babu ita. Sai kawai ya dawo da dubansa akan Tajuddeen ɗin yana mai girgiza kansa da ɗan furzar ya huci. A taƙaice ya ce, “Bara na wuce”. Ba yanda Tajuddeen ɗin baiyi ba akan ya bari ya kaisa amma yaƙi. Dole sukai sallama ya fito domin samun napep…..

         ★★★

      Sosai ran Tajuddeen yake a dagule, dan haka maimakon office da yay niyyar zuwa sai ya nufi companyn mahaifinsa da yake da tabbacin yana can. Koda ya isa gaisuwar ma’aikatan wajen ma bai iya amsawa da ƙyau, hannu kawai yake iya ɗaga musu. Sun sha mamaki dan sun san shi mutum ne mai saukin kai sosai ga fara’a. Sam baida wulaƙanci, wani lokacin ma idan yana jin barkwancinsa ya shigo Companyn bazaka taɓa cewa ɗan oga bane ba. Kai tsaye office ɗin mahaifin nasa ya nufa batare da jiran sakataransa yay masa iso ba. Alhaji Sulaiman Sufi Garko da ke tsaka da tattaunawa da babban yaronsa da ba’a jin sirrinsu a tare suka zuba ma Tajuddeen ɗin ido har ya ƙaraso inda suke. Hannu ya Bama yaron mahaifin nasa mai suna Isyaku, sai dai ana kiransa da Malami. Malami ya gaida Tajuddeen ɗin da girmamawa duk da kuwa zasu iya sa’anni, to amma ai baba ma da babansa. Alhaji Sulaiman dai kallon ɗan nasa yake kawai bai dai tanka ba, sai wani inkiya da yayma Malami da ido. Kai ya gyaɗa masa dan babu wani yaren jiki na Alhaji da bai haddace ba. Ko tari yayi yasan mi yake nufi. Fita yay ya bama ɗa da mahaifin waje…

         “Auta wani abu ya faru ne na ganka a haka?”.

    Alhaji Sulaiman ya faɗa cike da kulawa ga tilon ɗan nasa namiji kuma auta a cikin ƴaƴansa. Cike da damuwa Tajuddeen ya sake tsuke fuska, sai kuma ya kalla mahaifin na sa da idanunsa da suka kaɗa sosai. “Abba Please ina son zancen aure na da Mawaddat ya motsa mana. Wlhy bazan iya daina sonta ba, dan na gwada hakan amma na kasa”.

             Murmushin manya Alhaji Sulaiman yayi tare da ajiye pen ɗin hannunsa idonsa ƙyar akan Tajuddeen kamar yana son tabbatar da gaskiyar furucinsa…

    “Abba Please say something mana”. Tajuddeen ya faɗa kamar zai saki kuka.

          Alhaji Sulaiman ya furzar da huci yana mai haɗiye sauran murmushin fuskar tasa da ya rage. “Tajjudeen in ce maganar nan ta wuce ai ko?”.

      “Abba bata wuce ba wlhy, dan nikam ina sonta kuma zan zauna da ita a duk yanda take. Dan ALLAH kayi haƙuri ku sasanta da Uncle Isma’il ni dai a auramin ita. Kaga zuwa jibi Grandpa zai dawo da ga Umra ɗinsa, ni dai zan samesa da zancen a karo na biyu tunda har yanzu bawai ta tsaida wani mijin bane. Nima kuma na kasa kallon kowacce mace da sunan soyayya dan ita kaɗai nake so tun ina yarona”.

      “Humm Tajuddeen sasantawa tsakanina da Isma’il abune mai matuƙar wahala. Kuma nasan zai iya wulaƙantani fiye da da saboda ƴarsa. Amma zan iya komai a kanka kamar yanda shima yake jin zai iya komai akan tasa ƴar. kuma kafin ma Baba ya dawo jibin yau zan fara masa zancen a waya”.

     Sosai farin ciki ya baibaye zuciyar Tajuddeen. Miƙewa yay yaje ya rungume mahaifin nasa. Shima fuskarsa da murmushi ya amshesa hannu biyu. Kusan mintuna biyu Tajuddeen ya ɗago. Cikin komawa serious ya ce, “Abba wai dan ALLAH miye ya haɗaku kai da Uncle Isma’il? Nasan dai sanda ina yaro ba haka kuke ba. Kuna ƙaunar juna kamar ƴan uwa na jini, kuna mutunta juna matsayin surukai. Amma abin mamaki sai ga mijin ƙanwarka uwa ɗaya uba ɗaya ya juye ya zama maƙiyika! Abba Please ka sanar min miya haɗaku ko zan iya wani abu mana”.

              “Tajuddeen wannan ba huruminka bane, kai dai ba kana son auren Mawaddat bane? To ka saka a ranka kamar ka samu dan koba komai ita ɗin ɗiyar ƙanwata ce Isma’il bai isa canja wannan tarihin ba. Dan haka jeka ka cigaba da harkokinka Mawaddat ta zama matarka nan da sati biyu kacal”.

       Sosai maganar farko ta tsaya masa a rai, sai dai ta ƙarshe ta masa matuƙar daɗi da sakashi a farin ciki dan haka bai musa ba yay masa sallama ya fita cike da ƙwarin gwiwar ya kusa mallakar Mawaddat.

Ni dai nace hummmm😵‍💫. Kufa masu karatu ya kuka gani🤷?.

       ★★★….★★★

   Kallon mamaki yake ma matar tasa akan furucinta. Fahimtar hakan ya saka Aunty Saliha sake faɗin, “Wlhy da gaske nake Sweetheart bata nan fa. Alamu ma ya nuna ta jima da barin gidan nan kamar”. Sosai ran Uncle Yousuf ya sake dugunzuma. Dan haka ya cije lips ɗinsa da ƙarfi batare da yace komai ba. Ture shayin gabansa yay tare da miƙewa ya fice a falon. Cike da tausayin mijin nata ta bisa da kallo. Baba maigadi ya gaishesa da girmamawa duk da ganin yau fuskar ubangidan nasa babu walwala. Hannu kawai ya iya ɗaga masa. Sai kuma ya furta “Baba ko akwai wanda ya fita a gidan nan ne bayan yara da suka wuce school?”.

      Baba maigadi da ya ɗan daburce ya shiga in-ina da inda-inda. “Baba tambayarkafa nake? Bana son kwane-kwane ka faɗa min”. Uncle Yousuf ya faɗa da ɗan jin haushi a muryarsa. “Kayi haƙuri Alhaji, abunne dai kamar da ruɗewar kai. Hajiya Muwaddat dai ta fita kam tunda duku-duku kafimma yara su wuce, sai dai abinda ya ɗauremun kai da hargitsani ni banga shigowarta bane shiyyasa na fara tunanin ko junnu ne ke son buɗe min idanu n….”

      Takaici ya saka Uncle Yousuf yin gaba batare da tsayawa jin ƙarashen labarin da yayma kallon na soki burutsu ba. Sai dai harga ALLAH shi baba maigadi iya gaskiyarsa da yake faɗa. Sosai hankalin Uncle Yousuf ɗin ke’a tashe, dan zuciyarsa ta fara masa wasi-wasin karfa taƙi zuwa gida. Yana shiga key ɗin motarsa da ke a dining kawai ya bama aunty Saliha umarnin bashi, bai ma ko saurareta akan magiyar yazo ya ƙarasa break fast ɗinsa baiyi ba ya sake ficewa abinsa. Sai ƙarar buɗe gate da fitar motarsa kawai tajiyo. Addu’ar isa lafiya kawai tai masa dan bata da yanda ta iya tunda tasan ƙaunar da yakema ahalinsa dabance a rayuwa. Bai haɗa son su da komai ba. Ita hakan bai taɓa zame mata matsala ba dan itama suna nuna mata ƙauna a cikinsu. Basu taɓa wareta ba ko nuna mata bambancin kasancewarta bare garesu. Hasalima suna ɗaukar mahaifinta matsayin uba garesu a yanzu fiye da kowa har danginsu na Jiƙamshi. Dan haka bazataima ALLAH butulci ba sai dai ma ta tayashi son danginsa itama tare da musu fatan alkairi musamman akan Mawaddat data zame musu tamkar zakka………✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣6️⃣

……..Cikin ƙanƙanin lokaci Uncle Yousuf ya isa gidan ɗan uwan nasa. Anan ma sama-sama ya gaisa da su maigadi. Su ya farama tambayar Lulu tazo gida. Sun bashi amsar da ta sakashi sakin ajiyar zuciya mai kauri. Sai kuma ya samu ƙwarin gwiwar ƙarasawa ciki duk da sun tabbatar masa ta fita aiki tunma ɗazu tare da drivern ta. Kusan karo suka ci da Daddy dake ƙoƙarin fitowa har lokacin yana ƙananun magana wa Mommy akan Mubeen bai gaida Lulu ba. Sai dai duk wanda ya sanshi yaga yanda yake faɗan yasan yana yinsa ne kawai amma akwai abinda ke damunsa mai raɗadi ba abinda Mubeen ɗin yayi bane, shi kamar ya taka sahun ɓarawo ne. Ita dai Mommy bata tanka ba sai ma maida hankalinta tai akan cin abincinta da shi Daddy ɗin ya fasa ci saboda Lulu bataci ba. Mubeen ma na zaune cikin ɓacin ran yanda faɗansa ya koma kan Mommy kamar dai dama Daddyn nasu dama da biyu ya ƙirƙiri faɗan dan ya maidasa kanta ne. Gaishesa Uncle Yousuf ɗin yayi, sai kuma ya leƙa ya gaida Mommy da ga inda yake tsaye, acewarsa yana sauri ne dama ya biyo ne yaga Yaya. Mommy tai ɗan murmushi da masa addu’a. Tare suka fito da Daddyn da ya bar faɗan tun ganin Uncle Yousuf, dan yasan yana ji zai fara kare Mommy koma shi ya maida faɗan a kansa.

       “Yaya magana ce da ni mai muhimmanci”. Ya faɗa cikin rashin walwala. Tsai daddy yay yana kallonsa. Sai kuma ya kamo hanunsa da faɗin, “To muje office ɗina ko naka sai muyi a can ko auta”.

    “A’a Yaya, anan gida ya cancanta muyita dan zatafi dacewa”.

   Komai Daddy bai sake cewa ba sai hannun ƙanin nasa da ya sake ja suka nufi falon baƙi da ke can ta wajen garden. Tsaf falon yake dan kullum sai an gyarashi da saka masa turaren wuta. Bayan sun zauna cikin kulawa da san danne damuwa Daddy ya ce, “Ina jinka mike faruwa Auta? Danni duk ka ɗaga min hankali da wannan yanayin naka wlhy.”

          Numfashi mai ɗaci Uncle Yousuf yaja da gyara zamansa. Kai tsaye ya ce, “Akan Mawaddat ne.”

      “Kuma dai Yousuf? To mi ta sake yi?”. Da ga jin a yanda Daddy yay tambayar kasan ransa a jagule yake. Amma sai Uncle Yousuf ɗin yay biris ya cigaba da faɗin, “Gaskiyar da muke buƙatar gani da ido ce na gani jiya a zahirance. Dan an maido min Mawaddat gida a buge tana warin kayan maye kamar ma harda giya”.

        Tsurru Daddy yay yana kallon Uncle Yousuf, sai kuma cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka ya ce, “Yousuf dan ALLAH ka gayamin gaskiya, dan in har wani yazo ya faɗa maka nasan za’a iyama Mawaddat sharri kasanta da magauta. Na rasa mi yarinyar nan ta tsarema wani a rayuwa. Gashi ita bata damu da kowa ba amma ita an dam……..”

      Dakatar da shi Uncle Yousuf yay da faɗin, “Yaya! Kasan dai bazan ma Mawaddat ƙarya ba dan naci riba ko? Kuma ni babu wanda yazo ya faɗa min ni na gani da idanuna. Kuma gashi misawarka tasa na fahimci kai kanka baka san Mawaddat bata kwana gida ba ma. Hakan na nufin dama ba yau ta fara fitar dare ba batare da ka sani ba kuma baka taɓa maida hankali ko damuwa ba akan tabbatar da kowa na gida kafin ka kwanta. Yaya bansan yashe ka koma haka ba, shin dan ALLAH miya canjaka? Anya kuwa son Mawaddat kakeyi da gaske har cikin ranka? Wace irin bahaguwar rayuwace wannan mara fasali. Iyayenmu sun baku tarbiyya gwargwadon iyawarsu kai da Aunty Kareema. Sannan kuma kun bani dan gashi a yanzu ina cin ribarta matsayin nagartaccen mutum da ke banbance fari da baƙi koda a cikin rufewar idanu ne. Sannan sauran yaran ma suna samun irin tarbiyyar dana samu da ga gareku. Shin miyasa komai ya canja akan Mawaddat ne? Miyasa makahon so ya lulluɓe zuciyarka kake ɗorata akan abinda zata iya kaico da kai wataran da tunanin soyayya ce. Ban ce karka sota ba, amma ka dinga dubayya mana. Shin dole ne sai ka nuna mata ƙazamar soyayya zamu san kaso mahaifiyarta kamar haka itama? Ko sai ka mata makahon so zai sanarma duniya ita ɗin ƴar sonka ce da ta fito da ga jikin matar son ka?. Anya yaya ba alhakin Aunty Kareema bane kuwa ke bibiyarku akan Mawaddat kai da mahaifiyarta? Anya ba farkawa ya kamata kayi da ga nannauyan barcinka ba a wannan gaɓar kafin komai ya ƙarasa taɓarɓarewa mu rasa Mawaddat gaba ɗayanta”.

      Sosai jikin Daddy ya ƙara yin sanyi, dan dama harga ALLAH ƙarfin hali kawai yake na son musawa uncle Yousuf ɗin tunda shima ya ga shigowarta gidan a ɗazun da safen batare da ita ko wani ya sani ba. Wannan damuwar ce ya tashi da ita, sai dai ya rasa ta yanda zai tunkari Mawaddat ɗin shine ya huce haushin akan Mubeen da Mommy. A hankali ya damƙo hanun Uncle Yousuf cikin nasa ya ƙanƙame da ƙarfi, so yake ko sau ɗaya yayi kuka akan wannan damuwar ta halin rayuwar da Mawaddat ta jefa kanta a ciki amma ya kasa. Sai dai idanunsa sunyi wani masifar kaɗawa da ja. Cikin rawar murya ya ce, “Nagode ɗan uwana. Nagode da ka kasance mai faɗa min gaskiya komai ɗacinta. Wlhy auta al’amarin Mawaddat shine mafi zama ƙololiwar damuwata a yanzu fiye da komai, dan hanani barci yake yi. Zan faɗa maka gaskiya ko jiya nasan fitar ta a gidan nan, kuma nabi bayanta, sai kuma na samu yaron nan driver da ka kawo shima ɗin yabi bayanta. Dan haka na laɓe a kangwon kusa da gidan data shiga a wajen har kunama ta harbeni jiyan. Ban damu da azabar kunamarba, ni dai burina yaron nan ya fito da ita a gidan lafiya. Cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ya fito da ita a mota, na fito zan sake biyosu duk da azabar harbin kunamar da nake ciki idona ya ganemin ɗan gidan tsohon gwamna M Atik Kumo zai shiga gidan shima. Na shiga tashin hankali matuƙa, sai dai ban tsayaba na biyo motar tata dan naga ina yaron nan zai kawota sai naga gidanka ya nufa da ita. Nutsuwar hakan dana samu ce ta sani komawa da baya can gidan ɗin dai na sake tsayawa a mota, abinda ya sake tadamin hankali Yousuf su Alhaji Baita na gani sun fito a gidan nan dai da Mawaddat ta shiga kusan ƙarfe ukun dare. Wlhy tsabar ruɗani bamma san kunamata ta sauka ba. Da ƙyar na iya sake maido kaina gida shine fa ko rintsawa banyi ba har akai sallar asuba, bayan na dawo massalaci naga shigowarta gidan nan”. Ya ƙare maganar hawayen da yaketa son su zubo na sauka a yanzu masu zafi. Sosai shima Uncle Yousuf ya shiga ruɗani da tashin hankali. Dan jin sunayen manyan mutane da duk wanda ka tambaya zai tabbatar maka ɗunbin ganin mutuncinsu da yake a cikin wannan labari na yayansa……

       Daddy ne ya katsesa da faɗin, “Yousuf kaina ya kulle gaba ɗaya akan al’amurin nan, ka kawo mafita inba hakaba ina gab da kaiwa ƙasa akan lamarin Mawaddat”.

          “Yaya mafita ɗaya muke da ita shine yi mata aure….”

       “Aure Yousuf? To da wa? Kasan dai Mawaddat bata kula kowa. Kana dai ganin duk kurari da jan idon Baba (Alhaji Sufi Garko) yayi ya barta akan sanya ranarta da yaron Sulaiman data bijirewa. Har gargaɗin duk randa wani ya sake zuwa garesa domin santa zai aura masa ita koba amincewar ta da mu kammu yay mata amma bata ɗauki hakan da muhimmanci ba saboda bushewar zuciya. Yousuf na rasa da ga ina na kuskure akan Mawaddat. Shin nuna mata soyayya na nufin ba dai-dai ba kenan?”.

     “Humm Yaya wannan harda laifinka kaima ka sani, ba’a hana iyaye su nunama ƴaƴansu soyayya ba, sai dai ba ƙazamar soyayya irin wadda kaima Mawaddat ba da har tazama jagoran hanata fahimtar minene addininta. Yaya kofa salla nagartacciya Mawaddat bata iya ba a wannan shekarun nata balle azo ga sauran al’amuran addini, hakan kuma duk kuskurenka ne da kasa barinta ta samu tarbiyya irinta uwa a wajen Aunty Kareema saboda son zuciyarka….. Amma dai mu ajiye abinda ya wuce mu kalla na yanzu. Yanzu dai bayan tabbatar da aure ne mafitarmu akan lamarin Mawaddat bani da wani idea kuma. Amma dai ka bani lokaci nayi nazari tukunna. Sannan dan ALLAH ka kwantar da hankalinka. Dan lamarin Mawaddat an baro shiri ne tun rani. Amma insha ALLAHU tsayayyen miji a gareta zai jagoranceta da sabuwar tarbiyyarsa irin wadda tun farko ya kamata ace ta samu da ga garemu. Addu’a ya kamata mu duƙufa mata musamman ma kai ɗin nan. Sannan mu dage da sadaka ALLAH ya shiryar mana da ita, ya kuma kawo mana mafita cikin sauƙi. Sannan ka ajiye batun su Alh. Baita ni da kaina zanyi bincike a kansu insha ALLAHU zan gano alaƙarta da su”.

         “Shike nan Yousuf ALLAH yay maka albarka.”

    “Amin yaya”.

   Daddy ya sake nisawa a hankali da faɗin, “Sai dai kabi a hankali a duk wani bincikenka dan a wannan gaɓar da gaske inajin ƙanina, tsoro na gaske nakeji wlhy a wannan gaɓar. Miya kawo su Alh. Baita cikin rayuwar Mawaddat?”.

         “Bana tunanin wani abu saɓanin wanda zuciyata ke kallo yaya. Kasan dai da yawan wasu manyan ƙasar nan sunata taka wata rawa cikin rayuwar lalacewar yaranmu batare da mun farga ba”.

     “Nafika sanin hakan Yousuf. Sai dai al’amarin ya wuce a yanda kai kake kallonsa da hasashensa. Kai dai kamar yanda na faɗa maka inajin tsoro da gaske a yanzu tsoro nake ji irin wanda a baya babu shi a zuciyata…..”

       “Yaya na kasa fahimtar mi kake nufi ka ruɗar dani fa, Miye ke baka tsiro ne wai?”.

   Murmushi Daddy yayi mai nuna tsantsar damuwa a bayyane. Maimakon amsa sai ya dafa kafaɗar Uncle Yousuf tare da ɗan bubbugawa ya miƙe. “Tashi kaje office auta karka makara”.

       Kallo Uncle Yousuf ya bisa da shi mai tsayawa a rai, sai zuciyarsa ke wani irin rawa dan shi kaɗai yasan mi yake iya hangowa game da ɗan uwan nasa, sai kawai shima yaji kamar ya fara jin tsoron. Tabbas akwai ɓoyayyen al’amari wanda ya kamata ace ya sani amma ta yaya? (Bincike akan alaƙar Mawaddat da su Hon. Babale Nakowa) kansa ya jinjina cikin gamsuwa da shawarar zuciyarsa. Dan haka shima ya miƙa ya fice. Da kallo yabi motar Yayansa dake ƙoƙarin ficewa a gidan. Numfashi ya sauke da ƙyar tare da nufar tashi motar shima.

★★★ ∆ ★★★

   Smart kam tattara al’amarin Lulu yay ya wancalakar gefe domin fuskantar tasa mai muhimmanci. Gida ya nufa kai tsaye saboda kiran da Abba yay masa. Ya samu gidan da ƴar hayaniyar kasancewar zuwan Sa’id da wasu kawunansa uku. Cikin girmamawa ya gaishesu batare da ya kalla inda Sa’id ya ke gurfane ba kamar mai kuka. Ya maida hankalinsa ga Abba da Hawwah ke a kusa da ƙafafunsa kamar tana kuka itama.

      “Abba gani”.

Ya faɗa cikin dakewarsa. Nisawa Abba yay da nuna Hawwah ya ce, “Kaine ka ɗakko Hauwa’u a gidanta?”.

          “Eh tabbas nine Abba”.

      “Me yasa?”.

  Shiru ya ɗan yi kafin ya nisa. “Abba saboda ta kirani akan ga mahaifiyar mijinta na neman ƙonata da mangyaɗa. Banje gidan da nufin ɗakkota ba sai jin ba’asi na kuma sasanta kamar na baya da akai batare da kun sani ba. Sai dai na samu abin ya wuce yanda nake zatonsa shiyyasa na ɗakkota kafin a cutar da ita tunda mu bawai mun daina sonta bane ba. Ba kuma mun bashi bane dan mun gaji da ita a gidan nan kota gundiremu. Abba abubuwa da yawa sun faru akan auren Hawwah amma ina sasantawa a iya can batare da kai ko Ammah kun taɓa sani ba. Bama ku ba hatta da Aunty Bilkisu ban taɓa sanarmawa ba, kuma na gargaɗi Hawwah sanar ma kowa. Shiyyasa wannan karon na ɗakkota kuma bazata sake koma musu gida ba. Yaje ya auri wadda mahaifiyarsa ke son zama da ita haka nan dan ALLAH kowa ya huta.”……..✍️

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*THANKS FOR CHOOSING US*🥰

Zafafa🫶🔥

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣7️⃣

……..Cikin ɓacin rai ƙanin mahaifin Sa’id ya ce, “Ai ba ita kaɗai ce keda iko da shi ba. Sannan kuma ni banga laifinka anan ba yaro. Hasalima abinda kai sai ka birgeni dan kayi abinda ya kamata ace ƴan uwa na ƙwarai suyi akan ƙannensu. Wannan shine girman kuma shine darajtawar.”

      “Tabbas abinda yay yayi dai-dai. Kuma tunda hakane muma kan zamu fidda kammu a wannan zancen ku ɗauki duk matakin da kuke gani shine dai-dai dan halin Rafi’a sam bashi da burgewa. Narasa mitake son maida kanta a rayuwa ita ba ƙaramar yarinya ba amma kullum aita abu guda kamar cin ƙwan makauniya, yanzu da tsautsayi yasa ta samu yarinyar nan da mangyaɗan yaya kenan? Wace amsa take da shi na kare kanta. Dama tausayin yaron nan ya samu tasowa mu biyosa da wuri kafin abin yay zurfi. Amma tunda hakane zamuje muma har sai kun yanke hukunci kafin sannan shima Yaya Ibrahim ɗin ya dawo da ga tafiyar da yayi”.

       Kuka mai tsuma rai Sa’id ya saki, dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar matarsa Hauwa’u da ƴar ɗiyarsu Nasreen da taci sunan mahaifiyar tasa. Amma hukuncin da iyayen nasa suka yanke yasa bazai iya jayayya da su ba. Babu yanda zai yi ya bisu yana kallon Hawwah da kanta ke ƙasa tun shigiwarta batako kalla sashen da yake ba ma……

      Ajiyar zuciya Abba ya saki a hankali, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. A taƙaice ya ce, “Kuje ciki zamuyi maganar a nutse”. Daga Hawwah har Smart miƙewa sukai suka fice. Babu kowa a tsakar gidan sai Umma da ke kai kawon girkin rana. Yanda bata tanka musu ba suma basu tanka mata ba. Sai dai murmushin data saki akan idon Smart. Shi ba ma’abocin maida hankali bane akan irin waɗan nan abubuwan dan haka yay shigewarsa, sai dai murmushin ya sosa masa zuciya da tsaya masa a rai. Ammah dake zaune a falo Nasreen a cinyarta tana shan kunu kallo ɗaya tai musu ta maida hankalinta ga Nasreen ɗin. Zama yay kamar yanda Hawwah da ke sharar hawaye itama ta zauna. Idanu ya ɗan zuba mata tare da furzar da huci kaɗan. “Shi wannan kukan babu amfanin da zai miki, bakuma zai gyara abinda yake faruwar ba. Kisama ranki haƙuri da nutsuwa, dan bazaki koma wannan gidan ba har sai tasan darajarki. Idan kuma kina ganin ba’ai miki gata ba a hakan dan naga k da mijin naki duk shashashu ne ga hanya nan zaki iya binsu” Daga haka ya miƙe.

           “Kayi haƙuri Yaya ni banga laifinka ba, kuma nagode da ƙoƙarinka a kaina”.

     Komai baice mata ba, sai duban Ammah da tai kamar bata ɗakin da yay. “Ammah ni zan koma”.

        “ALLAH ya tsare ya bada sa’a”. Tace masa batare data ɗago ba. Da Amin ya amsa yana ɗan lakatar kumatun Nasreen da itama tai masa a dawo lafiyar. Da ga haka ya fice abinsa badan yasan ina ya kamata ya dosa ba tunda boss ɗin tasa ta korosa yau.

       Sai da ya fito gaba ɗaya da ga layin nasu zuciyarsa ta kwaɗaita masa zuwa ma ya duba trainers ɗinsu. Dan kwana biyu basuga juna ba. Waya ya ciro tare da ɗan ƙura mata ido kamar mai tunani, sai kuma ya ɗan ɗage kafaɗa tare da kai wayar kunnensa bayan yay dailing number daya lalubo. Bugu uku aka ɗaga, yay ƙaramin murmushi da faɗin, “Barka da hantsi sir”. Amsar da aka bashi da ga can ta sakashi sakin murmushi. Sai kuma ya ɗan shafo kansa alamar jin kunya tamkar yana gabansa. “Am sorry Sir na ɗauka laifina. Yanzu ma ina son zuwa gaishekanne shiyyasa nace bara naji inda kake”. Ya ɗan yi shiru alamar saurare. Sai kuma ya amsa da “Okay gani nan zuwa in sha ALLAHU”.

         Tafiyar mintuna ƙalilan da bai wuce ashirin ba ta kaisa babban stadium ɗin da coach ɗin nasa yace masa yana acan. Wajen ya ƙayatu matuƙa. Babu yawan hayaniyar mutane sai isu-isu ƴan wasa da ke ta tsalle-tsalle alamar training sukeyi saboda wasan sada zumunci da suke shirin zuwa kudancin ƙasar. Tunda ya shigo wajen ɗaya da ga cikinsu da ya fara ganinsa ya saki wani irin fito daya jawo hankalin sauran suma. *_“Capten!! Carpten!!”_* suka shiga faɗa cikin ihun da ke nuna tsantsar farin cikin ganinsa. Murmushin Smart ne ya sake faɗaɗa, shima ya shiga ɗaga musu hannayensa duka biyu har ya ƙarasa gaban Trainers ɗin nasu da ke kallonsa shima da murmushi. Har cikin rai yana matuƙar son yaron, ya kuma ci buri a kansa dan Smart ya iya gara ƙwallo mai suna ƙwallo ta gaske, dan ma mun kasance a ƙasa irin ta Nigeria da mai alfarma yafi ma’iyi da tuni wani labarin ake akansa ba wannan ba. Amma duk da haka shima ya damu wasu dama na barin ƙasar ƙaddara ta toshe su. Sai dai ALLAH mai hikima duk da tarin damammakin da yaron ya samu tun yana da shekara goma sha takwas komai yaƙi motsa kansa a inda yake. Hannunsa ya kamo da ga hanashi risininawar da yay niyyar yi, “Yarona irin wannan ƙiba haka anya kuwa kana motsa jiki?”.

       A yanda coach ɗin yay maganar ya saka Smart yin ƙaramar dariya da shafa kai yana ɗan dudduƙar da kansa da faɗin. “Sir ina nan a yanda ka sanni girman rigane kawai”.

    “Bari nace to. Amma badan na yarda ba. Ykk to ya kwana biyu? Tunda ka samu aikin nan ka ɓuya gaba ɗaya ko?”. Ya ƙare maganar yana jan hanunsa suka ƙarasa kan wasu kujeru da ke gefe kaɗan. Smart da har yanzu bai bar murmushi ba ya ce, “Sir aikinne bai barin motsin kirki. Amma kuna raina sosai”.

            “To Alhamdullah babu dai wata matsala kuma ko?”.

      “Da sauƙi dai Sir”.

   “A cigaba da haƙuri, komai yay farko zaiyi ƙarshe. Fatanmu dai ALLAH ya warware mana abinda bamu da ilimin sani akansa”.

       “Amin Sir”. Ya faɗa cikin damuwa idanunsa akan teammate ɗinsa da ke ta tsalle-tsalle su har yanzu. Hira suka cigaba da yi da oga wani kaso na hankalinsa na ga teammate ɗin nasa dai. Kiran wayar coach da akai ta sakashi miƙewa ya ɗan matsa a wajen. Dai-dai nan ɗaya daga cikin ball ɗin da suke training ɗin da ita ta gangaro wajen filin har inda Smart ke zaune. Kamar wanda aka tsikara ya miƙe da alamar tsumin ya motsa. Cikin wani irin salo da iya ƙwarewa a harkar ya buga ball ɗin tamkar abin almara bata sauka ko ina ba sai cikin raga. A take wajen ya ruɗe da ihunsa, kamar waɗanda ake juyawa da remote suka raba kansu yanda ƴan ƙwallo kanyi a cikin fili yayin wasa. Ƙarasa shigewa cikin filin yay shima cikin zafin nama da jin shauƙi a ransa, dan da gaske ball itace hubby na Smart. Tana sakashi karsashi da nishaɗi maƙurar ƙurewa.

        Juyowar coach da ya kammala waya ya sashi waro idanunsa waje sosai na ganin abinda ke faruwa. Sosai ya rikice dan yasan da wahala a wanye lafiya… Ilai kuwa kafin ya kai ƙarshen tunaninsa da yay dai-dai da sake saka ƙwallo ta biyu a raga da Smart yayi ya wani ƙwalla ƙara hannayensa duka biyu dafe da kansa. Kafin su isa kansa ya zube ƙasa a sassanƙame. Hankalin coach idan yay dubu ya tashi, haka ma sauran teammate ɗin nasa duk sun rikice. Babu ɓata lokaci suka fiddashi a filin coach na musu faɗan miyasa suka barshi ya shiga tunda sun san matsalarsa. Su dai basu da tacewa dan mai afkuwa ta riga da ta afku kuma. Sai fatan a kiyaye na gaba dai.

          Duk wani kalan taimakon da sukan masa idan matsalar ta samesa ita Hameed yay masa, sai dai kamar yanda aka saba babu alamar za’a samu kansa a yau ɗin. Sosai ya sake shiga damuwa, ina daɗi da ga zuwansa gaishesa a rarraɓesa a kaima iyayensa shi a haka. Dole yay kiran ƙaninsa Ahmad aboki ga Smart ɗin kenan akan yazo suje gidan su Smart ɗin. Da mamaki Ahmad ke tambayar yayan nasa ko wani abu ne ya faru? Bai wani tsaya kwana-kwana ba ta sanar masa. Hankalin Ahmad ya tashi, babu shiri ya baro office ya nufo stadium ɗin.

      Yana ajiye wayar kiran babban amininsa Yousuf Ibrahim Jiƙamshi na shigo masa a waya (Uncle Yousuf) kamar bazai ɗaga ba sai kuma ya ɗaga ɗin dan sunyi da shi zasu haɗu shi shaf ma ya manta sai da yaga kiran. Furucin Uncle Yousuf da ke faɗin, “To baban ƴan tamaula ALLAH yasa dai ka gama da yaran naka dan bana son zuwa nai zaman jiranka zan koma office saboda baƙi da nake tsumaye bayan azhar”.

        Cikin damuwa coach ya ce, “Wlhy ni nama manta da da batun zuwan naka ina nan a rikice”.

    “A rikice kuma a kan mi?” Uncle Yousuf ta faɗa cikin mamakin aminin nasa.

         Shima amsa ya bashi da faɗin, “Wlhy Aliyu ne yazo mu gaisa fa na ɗan tashi amsa waya ban san yaya akai ba ya shiga cikin fili ka gansa nan sharɓan babu alamar rai tare da shi”.

        “Ya Arrahaman! Aliyu dai Aliyu nawa Smart Mawashi?”.

      Sai yanzu ma shi coach ya tuna ashe Aliyu a ƙarƙashin abokin nasa yake a yanzu. Dan haka ya bashi amsa da cewar, “Yess! Yes! Shifa wlhy”.

        “Ya Salam gani nan a hanya”.

   Kusan a tare Uncle Yousuf da Ahmad suka iso wajen. Kowanne ya fito a motarsa da sassarfa zuwa inda suke zagaye da Smart da ke kwance a ƙasa kansa bisa jikin coach da ke faman shafa masa ruwa yana fatan ya farfaɗo, dan bai son su kai shi gida a wannan yanayin musamman daya tuno irin tashin hankalin da Ammah ta shiga last da abin ya faru da shi. Har rige-rige ake tsakanin Uncle Yousuf da Ahmad, sai dai kowanne ya samu nasarar kai hannunsa jikinsa. Ganin yanda aketa faman saka masa ruwa babu alamar zai farfaɗo Uncle Yousuf ya cema coach “Hameed muje asibiti kawai dan banga alamar zai farfaɗo ba a hakan nan”.

       Cikin damuwa coach ya dubesa shima da bashi amsa da “Yousuf zuwa asibitin nan babu abinda zai canja. Dan mun gwada yin hakan a baya sai dai mu gama zaman banza dan su amsa ɗaya ma suke bamu zuciyarsa ta tsaya da aiki. Al’amarin nasa ne fa kamar abin sihiri gashi nan dai. Gida kawai ya kamata mu kaisa duk da gaskiya hakan na sakani fargaba dan tayarwa iyayensa hankali kawai zamuyi”.

        “Gaskiya kar a kaishi can Brother” Ahmad ya faɗa cikin damuwa. Bai jira cewar kowa ba ya cigaba da faɗin, “Mizai hana muje wajen mutumin nan da ya taɓa bashi magani sanda abun ya takura masa”.

     “Shawara mai ƙyau Ahmad, da ni duk nama rikice wlhy hakan bai zo min a rai ba. Kunga ku kamashi kusa a mota”.

    A bayan motar Uncle Yousuf aka saka shi kamar yanda ya buƙata, shi da coach suka shiga gaba Ahmad a baya ya riƙe Smart. Kai tsaye ƙofar ruwa suka nufa, gudun da coach keyi ya sakasu isa cikin ƙanƙanin lokaci. Gidane irin na talaka mai ƙaramin ƙarfi, sai dai da ga waje shafe yake da siminti tsaf da shi da milk ɗin fenti. Da ga gaban gidan kaɗan islamiyya ce ta ƙanan yara da keta karatu kasancewar akwai ta safe zuwa ƙarfe ɗaya. Tsaiwar motar ta saka wani saurayi da ke tsaye da ga jikin barandar Islamiyyar matsowa garesu yana musu sannu. Basu wani tsaya jan maganar ba suka buƙaci ganin Malam. Kafin ya basu amsa sai ga malam ɗin ya fito da ga gida……….✍️

_Yau dai Smart ɗin ku ya ɗan bani tausayi🥲_

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣8️⃣

_Ya rabbi ka gafartama *Sheikh Abubakar Giro Arugungun*. Ka yafe masa kurakuransa, alkairan da ya isar garemu na wa’azantarwa da koyarwa kasa ya amfanar da mu duniya da lahira. ALLAH ya albarkaci zuri’arsa. Suma iyayenmu ALLAH ka gafarta musu, damu baki ɗaya 😭✍️_.

……..Wata nannauyar ajiyar zuciya Smart ya saki mai ƙarfin gaske lokacin da malam ya shafa masa ruwan addu’oi da yayi tofi a ciki, sautin karatun suratul Naazi’aat da ɗaliban malam ce ta fara shiga cikin kunnensa da wani irin ƙarfi tamkar a iya cikin kunnen nasa akeyi. Ya sake sakin ajiyar zuciya sai kuma ya kai hannunsa ya dafe goshinsa dan kansa wani irin ciwo yake kamar zai tarwatse. Uncle Yousuf ne ya fara ambatar sunansa, dan haka ya sake yunƙurin buɗe idonsa a karo na biyu sai dai ya kasa. A rikice duk suka dubi malam. Ya karkaɗa musu kansa da faɗin, “Kamar yanda na faɗa muku tun wancan karon ku sake jajircewa wajen addu’a da sadaka akansa, dan al’amarin nasa akwai ruɗani kamar na sihiri mai ƙarfi. Sai dai ban tabbatar ba dan UBANGIJI shine kawai masanin gaibu. Amma gaskiya al’amarin nasa yana nuna kamar bugewar junnu ne. Na fara baku ruwan addu’oi a wancan karon amma sai aka daina zuwa a karɓa kwata-kwata, dama ba komai bane face addu’oin karya sihiri wanda ya kamata ma ace duk musulmi kan dingayi a gidansa domin shi da iyalinsa koda lafiya lau ake dan rayuwa kake baka san mike biye da al’amarin ka ba. Koba sirihi akwai baki (kambun baka) da yafi sihiri kaifi a wasu lokutan. Koda ma bazaku juri zuwa nan ɗin a karɓa ba to ku dage da yi masa a gida dan ALLAH”.

      A tare suka amsa da “In sha ALLAH malam” sai kuma suka ɗora da godiya. Ganin yanda Smart keta faman jujjuya kansa malam ya ƙara masa addu’a tare da basu umarnin kaisa asibiti mafi kusa. Godiya sukai masa dan a wancan karon ma haka yay musu. Suka ajiye masa sadaka shi kuma ya basu ganyen magarya da ayoyin da zasu karanta da ga cikin Alkur’ani mai girma. Kai tsaye asibitin suka nufa kuwa, inda aka bashi gado dan a kallo ɗaya idan kai masa dole ne ya baka tausayi, kai kace ba a yanzu kaɗai ya kasance a kwance ba yanda yay sharɓan. Sun bashi taimakon gaggawa har sai da ya samu barci suka ɗan samu nutsuwa. Sun yanke shawarar sanar da gidansu amma sai coach ya ce adai ɗan dakata idan basu sallamesa zuwa yamma bane sai a sanar musun. Hakan ya musu, dan haka sukai yunƙurin fitowa aka barsa da Ahmad ya zauna da shi kafin suje su dawo…..

          ★★★★★

   Duk yanda taso cigaba da gudanar da al’amuran gabanta na wannan yinin hakan sai ya nema gagararta. Ba ƙaramin tsaya mata a rai abinda drivern nata yay mata yayi ba. Dole ta hakura da tattara bayanan case ɗin da zata fara tunkara a safiyar litinin kan dukiyar wasu marayu da wan mahaifiyarsu ke ƙoƙarin handamewa dan zuciyarta a cinkushe take matuƙa. Steering da take murzawa ta kaima duka a karo na babu adadi. Ta cije lips da masifar ƙarfi da faɗin, “Sai na koya maka hankali!”. Kalmace data ambatata yafi sau shurin masaƙi. Ga takaicin daren jiya da ma na cigaba da ci mata rai dan a duniya tai masifar tsanar wani namiji ya raɓeta da sunan taɓata ko soyayya. Shiyyasa shima Tajuddeen lissafinsa ya shiga cikin jerin lissafin abubuwa masu ƙuna da ajiyewa a kudin tarihinta na wannan yinin da take ganin yazo mata a birkice. Office ta koma, inda ta tarar da baƙi kashi-kashi na jiranta. Tabbas batajin magana, sai dai a ɓangaren aikinta ita ɗin jajirtacciya ce, dan ma ɗabi’arta ta shaye-shaye na matuƙar maidata baya a lokuta da dama, dan badan wata hikima ta UBANGIJI ba da Lulu ta jima da daina zuwa wajen aikin ma gaba ɗaya ne. Mummunar hallayya mafi muni tattare da Mawaddat shine sakaci da addini, sam babu abinda ta sani akan addininta sai abinda ba’a rasa ba sakamakon karatun ta na lawyer. Bata san a kira salla ta tashi tayita akan lokacinta ba, to idan ma tayin babu maganar yinta a yanda MANZON ALLAH ya koyar damu. (Kuyi haƙuri ba Lulu kaɗaice a wannan matsalar ba. Wlhy da yawan mutane sunayin salla ne ba’a yanda MANZON ALLAH ya koyar ba. Dan bawai fa muna nufin Lulu bata san salla ba, a’a itama ta tashi ne a yanayin yanda akeyi kawai nakeyi batare da samun ilimin yinta ba kamar yanda da yawa mutane suka kasance. Mafi yawanmu idan da zaman tsayawa akan ibadarmu ta salla za’ai tun daga tsaiwarta ma zamu fara samun gyara.  Please Dan ALLAH a wannan gaɓar kowanmu ya nutsu ya kalla sallarsa da kuma bincike akan yaya ake salla kamar yanda MANZON ALLAH S.A.W ya koyar mu gani ko zamu ribantu da gyarawa). Sanda ta gadama take salla, tana kuma yin tane a yanda kawai taga anayi kasancewar karatun addinin ma gatan mahaifinta ya zame mata cutarwar da bata samesa ba. Masifarta kam wannan halitta ce, wani mai haƙuri wani saɓani haka. Sai ɗabi’ar shaye-shayen data jima tana binnewa wanda har yanzu bamu san tushen farawarta ba ko dalilinsa. Wulaƙanta mutane da takasu a duk yanda taso kuskuren mahaifinta ne da ya ɗorata a turbar komai take so zata samu. A duk sanda ka nunama yaro komai yake so zai samu tofa kansa zai ƙara girmane da tunanin yafi kowa daraja da power a rayuwa, sannan akan komai shine sama da kowa. (Iyaye sai mu kula hakan ba soyayya bace)….

       Yanda ta zube wayoyinta da zama jagwab cikin lallausar kujerar office ɗin nata ya sake bayyanar da ɓacin ranta akan fuska. Hand bag dinta ta jawo tare da fiddo key ɗin drower ɗin jikin decks ɗinta da bata yarda kowa ya taɓa saboda abinda take ajiyewa a ciki ta lalubo. Tana ƙoƙarin buɗe drower ɗin sakatariyarta ya shigo office ɗin da sallama. Wani takaici ya sata ɗago idanunta da suka kaɗe da gajiya. Sai dai gaba ɗaya tama kasa mata masifar da ta saba yi mata a duk sanda tai mata kuskure. Da sauri sakatariyar ta ce, “Please am sorry maa. Wlhy abinda matar can tazo da shi ne yay matuƙar tayarmin da hankali. Jiya ma tazo nace mata ta dawo yau dan kina up 2days sai yau ne zakiyi res…..”

       Hannu Lulu ta ɗaga mata alamar gajiya da saurarenta. Murya a shaƙe ta ce, “Zainab ba wanda zan iya saurare a yau koma minene akazo da shi. Ki sake bama duk wanda ya dace sabon appointment banda yau da gobe. Duk case ɗin da kuma kika sani bani da buƙatarsa a teburina karma mai shi ya shigomin office ok”.

             Zainab da damuwa ta bayyana ma a fuska ƙarara ta gyaɗa kanta da ke ƙasa. Sai kuma cikin rawar murya dan har ta fara hawaye ta furta, “Aunty matar can fa mijinta ne yayma yarinyarta da taje agolanci da ita gidansa fyaɗe. Kuma yarinyar shekararta tara kwata-kwata. Sunje asibiti da yarinyar amma anƙi karɓarsu tun jiyan wai sai da ƴan sanda. Taje police station ɗin kuma ƴan sandan nata mata yawo da hankali. Wlhy bakiga a yanda sukazo da yarinyar ba a jiya da yamma abin babu ƙyan gani….”

      Wani irin matse idanu da damƙe kujera Lulu da jikinta ya fara tsumar mazari tayi. (Mawaddat calm down. Mawaddat calm down. Mawaddat calm down). Wani sashe na zuciyarta ke ta ambata mata. Sannu-sannu ta fara sassauta damƙe kujerar da rumtse idanun nata da tai, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya sunyi jajur matuƙa kamar wadda tasha wani abu a lokacin.

       “Shigomin da ita”.

    Ta faɗa ƙirjinta na ƙara ƙarfin sukar da yake mata. Ga jikinta bai daina tsumar da yake ba. Da ace tanada ilimin addini da addu’a tafi cancanta da harshenta a irin yanayin. Amma sai aka samu akasin hakan a gareta. Da sauri sakatariyar ta ta fice cikin matuƙar sassarfa. Minti biyu basu rufaba sai gasu sun shigo. Matar dai da ka ganta kaga wadda ke’a cikin mawuyacin hali, sai dai da zata samu kulawa ƙyaƙyawar mace ce dirarriya. A lamarin Lulu da talaka a teburin aikinta kawai suke iya shan inuwa ɗaya, shima akan abinda ya shafi aikintane kawai babu ruwanta da rayuwarka. Har ƙasa matar ta kai ga alamun ciki da ya turo a jikinta zata gaida Lulu. Bata hanata durƙusawar ba amma dukkan hankalinta na gareta, sai kuma katseta da ga gaisuwar data fara da tai…

        “Kinga wannan gaisuwar baida amfani faɗamin ina yarinyar take?”.

    Cikin gyaɗa kai da share hawaye matar ta ce, “Tana gidan ƴar uwata da ta rakoni nan jiya, saboda yanda jikin nata yake ne ƴar uwar tawa tace na dawo yau ita ta kula min da ita”.

            “Wane police station kukaje domin kai ƙarar?”.

       “Na nan unguwarmu ne sai kuma da mukazo nan wajen ƴar uwar tawa itama ta kaimu na nan ɗin. Sai dai shima basu ɗauki abin da muhimmanci ba shiyyasa ta ce zata rakoni nan inda take da tabbacin za’a share mana hawaye. Hajiya dan ALLAH ki taimakeni kamar yanda ALLAH ya taimakeki. Yarinyar nan marainiya ce mutuwar mahaifinta ta sani auren wannan tsinannen da tunda na aure shi ban sake farin ciki a rayuwata ba……”

     Cikin jan tsaki da takaici Lulu ta katseta da faɗin, “Kika zauna da shi kuma har ya miki ciki. Malama ni ba rayuwar aurenki nake buƙatar ji ba. Ki tashi kuje zan haɗaki yanzu da wanda zaku sameni a asibiti”. Ta ƙare maganar tana miƙewa cikin matsanancin ɓacin rai. Waya takai kunnenta, da ga can aka ɗaga. Kirari aka fara mata ta katse da faɗin, “Musa ka sameni a office yanzu kai da Shu’aibu Please inada emergency case.”

          “An gama ranki ya daɗe”.

Musa ya faɗa ransa fes dan yasan yau aljihunsu zai kasance a cike. Dan aiki da Lulu yafi masa zaman cikin station aita kayan hamma balle tsaiwar kan titi amsar na goro. Ɗan rubutu tai a takardar data yago ta miƙama sakatariyar ta dake tsaye har yanzu. “Idan sun zo ki basu wannan, suje da ita sai su sameni a wannan asibitin dana rubuta. Kibasu 5k da zasu saka mai a mota”. Daga haka ta fisgi hand bag dinta da ɗayar wayarta da key tai waje…

       Batako kalli sauran mutanen da ke zaune a inda table ɗin sakatariyarta ya ke ba ta fice. Taja ƙaramin tsaki lokacin da take dana unlock ɗin motar tunkan ta ƙarasa gareta. Bazata iya jure wannan zirga-zirgar tuƙin ba fa gaskiya. Dan tun farko ita dama ba gwanar sonyi driving bace. Cikin ƙara jan tsaki lokacin da take ficewa a gate ɗin ta dannama Uncle Yousuf kira. Sai da ta shiga ta tuna abinda ya faru jiya da wasan ɓuyan data ƙudiri aniyar farayi da shi. Da sauri ta rarumi wayar zata katse sai dai harya ɗaga. Babu alamar wasa a muryarsa ya ce, “Lafiya?”.

      Kamar ta fasa ihu haka taji, amma sai ta dake cikin pretending da ƴar shagwaɓa ta ce, “Uncle Barka da safiya. Dama no ɗin mutumin nan zaka turamin koka kiramin shi Please ya sameni a Shira’s hospital”.

       Ɗan jimmm yay kamar bazai amsa mata ba sai kuma cikin dakewar da takan bata tsoro a Duk sanda yayita ya ce, “Wane mutumin?”.

           Yanzu kam sai da taji bugawar zuciya. Da ɗan rawar harshe ta ce, “Driver fa my papa”.

    Har zaiyi yi mata tambayar yaya akai bashi ya kaita office ba sai kuma ya fasa saboda tare ya ke da abokinsa Hameed. “K kina ina yanzu?”. Ya faɗa cikin goce tunaninsa.

       “Ina hanyar Shira’s hospital ɗinne ”.

     “Sai kin ƙaraso”.

Ya faɗa kawai yana yanke kiran…….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣9️⃣

……..Kaɗan ya rage ta bugama motar gabanta. Tai saurin take birkin da ƙarfi. Ganin yanda mai motar ya dakata shima da alama fitowa zaiyi ya sata sake mata key tabar wajen da saurin dan ba wannan ne a gabanta ba yanzu. Tana hango zagin da mai motar ke mata cikin daƙuwa da wanda wasu ke mata na gefen titi. Oho basu bane a gabanta. Furucin Uncle Yousuf ne ke mata kai da kawo. Ji take kamar ta koma su canja asibiti sai dai ta riga kuma tace su Sha’aibu su sameta a can. Sannan yanda uwar ke nuna yarinyar na cikin mawuyacin hali maganar sakaci daga gare ta ma bata taso ba, dan a yanzu al’amarin su drivern ta ya shafe a zuciyarta yanda zata yaga rayuwar mijin matar nan kawai take ƙullawa. A wannan fanin ba’a gayyacesu ba ma taka rawa suke balle sune da bikin. Ai rawa sai kalar wadda sukaso takawa wlhy…..

         “Da gaske dai Uncle You na asibitin nan? To mi ha kawoshi?”. Ta faɗa a fili tana parking idanota akan motar Uncle Yousuf dan babu ta yanda za’ai motocin gidansu su ɓace mata. Cikin rashin sanin abinda take buƙatar sani ta fito a motar. Sai da ta leƙa motar Uncle Yousuf ta tabbatar babu kowa a ciki sannan ta bar wajen zuwa cikin asibitin. A reseption kuwa suka haɗu da Uncle Yousuf ɗin. Karan farko a rayuwa taji bazata iya haɗa ido da shi ba, tsoron ma haɗuwar tasu take yi. Musamman kuma yanda ya zuba mata idanun nasa duk sai ta nema daburcewa. Shi ya fara ɗauke idanunsa da ga kanta yana kai wayarsa da aka kira kan kunne. Hakan ya bata damar nufar inda ake yankar kati, sai dai kuma fa ko sunan yarinyar bata sani ba ma fa ashe. Cikin ɗan yarfar da hannu da juyawa gaba ɗayanta tai facing ƙofa ta ke faɗin “Ouhhh! Saurin banza ma ashe nake”. Dai-dai nan motar ƴan sanda mai ɗauke da matar nan da yayarta da yarinyar suka iso. Shigowar Musa ya sata sauke ajiyar zuciya, shi ya sanar da nurses cewar akwai mara lafiya a waje kafin ya ƙaraso gareta. Kallo ɗaya da Lulu taima yarinyar ya sata rumtse idanunta takalminta har yana gullewa sai da ta dafe kantar reseption ɗin…….

         “★“★ ∆ ★”★”

       “Ranka ya daɗe yaron nan fa daka tada hankalinka kansa ba wani ɗan kowa bane face wani mutum da ake kira Malam Mika’il Idris Mawashi a anguwar fagge. Shi kansa mahaifin nasa a iya layin nasu kawai aka sanshi balle shi. Kuma da gaske drivern yarinyar ne kwata-kwata bai ƙulla sati huɗu da fara aiki gidan Alhaji Isma’il Jiƙamshi b…..”

      “Kace Alhaji wa?!!”.

   Alh. Baita yay saurin tarar numfashin yaronsa da suke kira Goga a kamar razane da jin sunan Alhaji Isma’il Jiƙamshin. Bashi kawai ba hatta Hon. Nakowa da ke tare da shi dan tunda suka baro gidan MM Atik Kumo da ya basu aro anan gidan hutawar Alh. Baitan suka ƙarasa kwanan nasu. Shine tun da farar safiya kuma suka nemi babban yaronsu na bangar siyasa Goga suka sakashi binciko wanene Smart ta hanyar ɗan bayanai da suka samu ga Nadiya wadda itama ta samune ga Lulu randa taje saloon shagonta….

        “Alhaji Isma’il Jiƙamshi nace ƙwarai da gaske oga. Dan shine mahaifin ita yarinyar ma ai.”

      “Babbar magana ƴarsa ta cikinsa?”. Hon. Nakowa ya faɗa wani irin abu mai ma’anoni da yawa na tsirga masa tun daga saman kai har tsakkiyar ƙafafunsa. Cikin tabbatarwa Goga ya gyaɗa masa kai. Tare da masa ƙarin bayanin da zai gaskata hakan duk da shi bai san dalilinsu na jinjina sunan ba tunda shi dai a ɗazun yaga hankalinsu akan yaron yake ba ita yarinyar ba.

      “Kaga jeka”.

Honorable Babale ya faɗa cikin katse masa tunani. Dai-dai Goga na miƙewa ya sake faɗin ka jiramu a waje nan zamu nemeka.” shi dai da to ya amsa musu ya fice kamar yanda suka buƙata. Yana kuwa fita Hon. Nakowa ya firta, “Tabɗi jan inji mata. Dama ƴar iskar yarinyar nan ɗiyar Isma’il Jiƙamshi ce? Haba shiyyasa bata zubar a banza ba.” sai kuma ya wani ƙyalkyale da dariya alamar hakan ya masa daɗi ƙwarai da gaske. Shima Alh. Baita dariyar ya fara. Sai kuma ya buga ƙafa da faɗin, “In kere na yawo zabo na yawo tabbas faɗar masu iya magana watarana za’a gamu. Honorable Please kira mana Hon. Misau mana. Dolene ai wannan shagalin da shi”.

      “Ƙwarai ma kuwa”. Cewar Hon. Nakowa yana wani bula-bula da babbar riga wajen laluben wayarsa. Cirota yay tare da yin danne-danne ya kai kunnensa……

      Tofa masu karatu wata sabuwa kenan. Mi’a haɗin Daddy kuma da su Honorables?🤔.

          ∆★∆★∆★∆

    Tun bayan wucewar ɗan nasa yake ta faman kai kawo a lafiyayyen office ɗin nasa. Abubuwa da yawa ne ke masa sukur-sukur a brain game da buƙatar autan nasa a karo na biyu. Tabbas zai fi kowa farin ciki da ƙulluwar wannan auren dan koba komai dai Mawaddat ɗiyar ƴar uwarsa ce Mawaddat. Ƙanwarsa mafi soyuwa garesa a duk cikin ƙannensa. Wadda yasha bama sirrin al’amuransa batare da tunani ko jin ɗar ba har ALLAH ya ɗauki ranta. Zai kasance mai yin farin cikin ganin jininsa da nata sun zama abu ɗaya. Sai dai kuma matsalar itace Isma’il. Isma’il shine babban bakangizo mai razani da ya gitta a tsakkiyar wannan ƙaunar zumunta mai cike da ababen burgewa ga duk wanda zai iya jin asalinta da wanzuwar ta. Dan tarihin ratsawar Isma’il a cikin labarinsa dana ƴar uwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ya juya akalar waccan ƙayataccen labarin zuwa ɗimautacce mara armashi a yanzu. Ata wani fanin kuma kamar zai zo da sabon armashin kansa da kansa dan labarin zai canja ne da ga na shi da ƴar uwarsa zuwa na shi da Isma’il Ibrahim Jiƙamshi mijin ƴar uwarsa da ƴarsa. Ƴarsa da yasan yana matuƙar ƙauna fiye da komai a rayuwa. Kafin yau da faruwar matsalar farko na tusguɗewar aure tsakanin Mawaddat da Tajuddeen labarin ba a haka ya tsarashi ba, sai dai yana ganin wata dama ce da zai masa editing dan ya zauna dai-dai da zamanin nan na 2023 a ajiye wancan ƙarnin dan ya koma tsohon yayi. Ya wani lumshe idanu da dunƙule hannunsa ya ce, “Yess!! Sulaiman Sufi Ado Garko kai mai nasara ne akoda yaushe. Isma’il Jiƙamshi sabon game, sabbin players and sabon stadium ka zama cikin shiri”.

       Wata sabuwar kuma dai🤔.

★★★★★

         Duk da a yanda take jin matuƙar gajiya bata huta ba har sai da doctors suka rufu akan yarinyar nan da lamarinta ya taɓa duk wanda ya ganta a cikin asibitin. Dan hatta Uncle Yousuf tuni ya ajiye batun takaicin Lulu gefe da shi akai komai na ganin likitoci sun tsaya a kanta. Abin tausayi ita uwar ma zuciyar ta bushe ko kukan zahiri ta kasa sai na zuci. Ganin komai ya natsa dan ana neman  uku na rana ma Uncle Yousuf ya kai dubansa ga Lulu da alamunta suka nuna gajiyarta matuƙa. Dan sai faman yamutse fuska take. Tausayi ta bashi, dan haka ya cigaba da kallonta a kaikaice cikin tausasawa da mata addu’ar shiriya akan halayenta marasa ƙyau. Isowar Ahmad wajen ta sakashi maida hankali garesa. Fuskarsa da murmushi yay ma Lulu magana, amma sai ta amsa masa a ɗan ɗage. Bai damu ba dan ya santa ya san halinta. Hasalima ya taɓa nuna sonta amma ta taka masa burki lokacin tana farkon dawowarta da ga Uk. Uncle Yousuf da yanda tai masa ɗin ya bashi takaici ya harareta, sai kuma ya maida hankalinsa ga Ahmad ɗin da ke faɗin, “Yaya ya farka, doctor ɗin ma ya sallamemu dan ya matsa zaije gida. Kasan Mawashi fa sam bai son asibiti.”

       Murmushin Uncle Yousuf yay, cikin yanayin tsokana ya ce, “Kai haba kamar wani yaro ko mace”.

          Dariya Ahmad yayi, dai-dai nan Smart ya fito a wani ɗaki da ke kusa da inda suke. Coach riƙe da hanunsa kamar wani ƙaramin yaro sai ɓata fuska yake. Dan da gasken fa bai son asibiti shi sam a rayuwarsa. Kuma bai san allura. Yanzu ma ba ƙaramar badaƙala akasha ba kafin ai masa shine ma Ahmad yay fushi ya fito. Ilai kuwa hararar Ahmad ɗin yayi tare da ɗauke kansa duk a lokaci guda, cikin rashin sa’a ya saukesu akan Lulu da tai kicin-kicin da fuska saboda kasancewar Ahamd a wajen, ita ala dole kar a kawo mata raini, dan duk wanda ya taɓa furta cewa yana sonta ko ya nuna basa ƙara shan inuwa ɗaya kuma. Ƙoƙarin janyewa yake sai kuma yay dai-dai da ɗagowarta cikin shirin miƙewa tabar wajen. Ta wani yamutse fuska fiye da yanda take sai kace wadda taga kashi. Shima ƙara tsuke tashi fuskar ya ɗanyi tare da ɗauke kansa gaba ɗaya irin bai ganta ɗin nan ba ma….

         “Ga Aliyu nan babu lafiya sai ki masa sannu. Dama ina son ki gama da wannan kai kawon ne muje ki dubashi ashe ma zasu sallamesa yanzu”. Uncle Yousuf ne yay maganar cikin katse hanzarin Lulu dake niyyar barin wajen abubuwa masu yawa na mata kai da kawo musamman ganin drivern nata a nan. Dakatawar tai, sai dai ta kasa cewa komai sai ɗan hararsa da take ƙasa-ƙasa.

     “Wai nikam bada Mawaddat nake ba?!”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin ɗan kaushin murya dan ya san taurin kanta na tsiya da gadara. Sosai taji haushin hakan, amma babu yanda zatai dan Uncle Yousuf ne. Ta ɗan sake ɗagowa ta kallesa, a taƙaice ta furta, “ALLAH ya bada lafiya”.

        Coach ne ya amsa da “Amin”. Cikin murmushi. Shi kam a zuciya ya amsa mata. A zahiri kam ya ɗauke kansa gefe kamar bai san da shi take ba. Sosai ta sake tunzura da salon rainin nasa. Tana mai tabbatar ma kanta a zuciya sai ta koya masa hankali da sauke masa wannan girman kan nasa. Batare da ta sake kallon kowa ba ta ce, “Uncle You ni na koma Office. Uncle Hameed ka gaidamin Aunty Rukayya sai nazo gaisheta”.

        Coach yay ɗan murmushi da faɗin, “Zan sanar mata idan da gaske kike Daughter. Dan na sanki ke da sabgoginki marasa ƙarewa.” karan farko da ta saki sassanyan murmushinta da kan ƙawata ƙyawun fuskarta, sai dai batayinsa sai ta gadama. Kai Ahmad da zuciyarsa tai wani irin tsargawa ya ɗauke gefe. Dan Lulu cikakkiyar mace ce da kan iya jan hankalin mafi yawan maza musamman irin matasanmu na yanzu masu fifita ƙyale-ƙyale ga mace fiye da nagarta. Sai kuma ka kwasa ka kai gida ka samu fanko ce ko addininta bata sani ba sai duniyar kawai aka saka a gaba da son birge al’ummar cikinta….

       Suma a tare suka fito su huɗun, Coach da Ahmad da Smart suka shiga motar Ahmad da ya koma ya ɗakko. Uncle Yousuf kuma ya shiga tasa motar dan Lulu kafin su fito ma har ta bar asibitin. Babu wanda ya sake bi takanta. Godiya Smart yay ma Uncle Yousuf sosai tare da su coach ɗin ma gaba ɗaya. Da ga haka kowa yaja motarsa. Har gida suka kaisa. Ahmad yay masa rakkiya har cikin ɗakunan kasancewar ba baƙonsa bane ɗakin dama. Bai wani zauna ba saboda Yayansa dake jiransa a mota. Yay masa ALLAH ya ƙara lafiya ya tafi…….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣0️⃣

…….Bayan yay sallar la’asar barci ya sake sha har kusa da magrib batare da kowa yasan yana a gidan ba. Dan sanda su Ahmad suka maidosa basu ga kowa a ƙofar gida ba. Wanka yay da alwalar magrib ya fito. Yanayin yanda yake jin jikinsa babu ƙarfi ya sashi yin sallarsa a ɗaki. Bayan ya idar ya fita zuwa cikin gidan. A kallo ɗaya zaka iya fahimtar baida lafiya ƙarfin hali ne kawai. Sai dai hakan bai hanashi leƙa duk ɗakunan gidan ya gaida su Mama ba. A ɗakin Umma ya samu babban yayansu Salim yazo gidan shima. Sama-sama suka gaisa Salim ɗin na wani cika da batsewa shi adole mai naira a gida. Ko’a jikin Smart dan shi ba wannan shirmen ne a gabansa ba. Yana juya baya zai fita Salim ɗin da Umma suka raka bayansa da harara. Oho baima san sunai ba shi dai.

        A falo ya samu ƙannen nasa duka. Sai Nasreen dake ta faman tsalle-tsalle ita da autar Aunty Amarya. Gaisheshi suka shigayi, ya amsa yana zama tare da ɗan dafe kansa da har yanzu bai gama saki ba. Ammah da tun shigowarsa take kallonsa ta ajiye littafin addu’oin da ke a hanunta da faɗin, “Baka da lafiya ne Hydar?”. Hannun ya janye da ga goshinsa ya ɗan furzar da iska. “Kaina ne ke ɗan ciwo kaɗan kawai Ammah, na kuma sha magani ma. Ina yini”. Maimakon amsawa sai ta cigaba da kallonsa cike da nazari. Ganin yanda ta kafesa da ido ya sashi duban Hawwah cikin son kauda hankalin Ammah ɗin ya ce, “K babu wata damuwa dai ko?”.

         Kanta ta jinjina masa itama da ɗan damuwar ganin yanayin nasa. “Ba komai Yaya Hydar. Sai dai kamar ba ciwon kan bane kawai ke damunka. Ka wani zabge a lokaci ɗaya kamar wanda ya kwanta ciwo.”

   Baiyi mamakin jin furuci nata ba. Dan a duk lokacin da ciwon ya bugesa ba ƙaramar fyaɗa yake masa ba. Ya ɗan sake furzar da iska yana tashi zaune da ƙyau da kamo hannayen su Nasreen. “Ciwon kai ne kawai kin san bai min da wasa”. Badan sun gamsu ba dai suka yarda da hakan. Maryam ce ta kawo masa abinci da faɗin, “Ko sai kayi sallar isha’i”.

        Nan ma iskar ya ɗan furzar da duban kular abincin. Yasan dai shinkafa ce dan ya ga Salim na ci a wajen Umma. Shi kuma sam shinkafa bata da farin jini a wajensa sai dai kawai ya cita dan yunwa. “Ai banama jin zanci abincin nan ɗauke kawai. Ko kuna da ƙullin kamu ki ɗan dama min kaɗan”.

     “Eh akwai. Dama na kunun gyaɗa da Ammah tasa aka markaɗo ɗazun ko shi za’a dama makan”.

     “Yauwa dama min shi ɗin kawai bara naje massalaci na dawo”…

        Ana idar da sallar isha’i ya sake dawowa. Anan yasha kunun gyaɗar da Maryam ɗin ta dama masa Ammah harda badawa a sayo masa ɗanyar awara dan tasan yana so sosai, kasancewar bata da yawa duk kafin ya dawo har an soya. Kusan ma tare suka cinye awarar da Nasreen da ke ta faman zuba masa surutu. Murmushi kawai yake mata cikin ƙarfin hali. Ammah dai da ke ɗan kallon tv duk tana lure da shi. Cikar agogo ƙarfe tara yasa Amma maida channel zuwa NTA, su Maryam ba wani son kallon labaran suke ba sai dai dole. Musamman ma Asma’u. Tashi yay ƙoƙarin yi shima sai dai kanun labaran suka ja hankalinsa. Inda rahoton farko ya kasance akan yanda shari’ar matashin nan Emanuel da aka kama a anguwar Yakasai akan lalata yara ƙanana maza da ya ɗauki tsawon shekaru uku yanayi. Kusan wata huɗu kenan ana tafka shari’ar sai a yau ne aka yanke masa hukuncin bisa jajircewar lawyer ɗin da ke tsaye akan bibiyar hakkin yaran da al’amarin ya shafa. Har tsakkiyar kansa yaji saukar muryarta tamkar a gabansa take kamar ko yaushe. Yanda take magana cikin nuna takaici da kuma jin daɗin samun nasara a shari’ar ya sashi kasa ɗauke idonsa ga tvn. Tambayar da ɗan jaridar yay mata akan miyasa a duk irin waɗan nan cases ɗin in dai tana a cikinsa da wahala bata samu nasara ba, anya ba tana saye bakin alƙalan bane ba ta bayan fage.

       Ƙaramin murmushi da ke sake fidda loɓawar kumatunta duka biyu ta saki tare da yamutse fuska kamar yanda ya santa musamman idan tanajin masifa. Cikin izzar nan tata ta bama ɗan jaridar amsa da faɗin, “Mi zaisa sai na sayi alƙali akan abinda yake gaskiya. Ashe ma karatun da nai akan harkar shari’a da wahalhaluna sun zama a banza kenan in har sai na sayi alƙali akan gaskiya ta. Nasarata itace gaskiyata. Dan bana tsayawa mutum sai na tabbatar da gaskiyarsa. Na kumayi alkawarin cigaba da yaga mutunci da rayuwar duk wanda ya kasance bunsuru mai halayen dabbobi akan mutuncin yaran mutane. Dan ni duk wanda zai iya ƙwatar mutuncin yarinya ta ƙarfi ballema wadda take ƙanƙanuwa bashi da wani suna a gareni face Dabba alade. Yanzu shi wannan da na kai ƙasa ma ai yafi matsayin alade a gareni bamma san mizan kirashi ba. Shege ya baro yankinsa yazo yana ɓarna a namu yankin saboda suna ganin muna haihuwar yara mu saki a titi kamar bamu san ciwonsu ba. Indai akan harkar fyaɗe ne nai alƙawarin ni Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi sai na hana waɗannan aladun shan ruwa da numfashi cikin salama. Dan nan gaba kaɗan abinda suke lalata yaron mutanen da shi zan koma datsewa da almakashi ƴan ƙaniya. Idan aure kuke so uwarmi kuke jira da bazakuje kuyi ba ko ku tafi gidajen karuwai Mtsowww!!”.

      Ɗan jaridar ya ce, “Turƙashi. Da alama dai Barrister Mawaddat Jiƙamshi ta fusata a wannan karon, masu halin binsiraye sai ku kama kawunanku, inba haka ba za’a sake maimaita gilli da girma bayan wanda akasha da ƙanƙanta. Sai dai a yayin da wannan zantuka na Barrister wasu ke nuna goyon bayanta wasu ƙalubalantarta suke musamman akan zance gilli da zata fara da kanta. Dan haka a yinin yau zantukan barrister suka ɗauki ɗumi da zagaye kafafen yaɗa labarai harma dana yanar gizo aketa tafka mahawara. Ballema da wasu ƙungiyoyin mata masu yaƙi da wannan ɗabi’a ta fyaɗe suka fito muraran da cewar sumafa suna bayanta. Dan zasu sayi nasu almakasan su fara sakawa a jakuna dumin tayata aikin gillin. To ALLAH dai ya ƙyauta, kowa rai yayma daɗi ai baran mai shi ne. Shi dai wannan gashi zai ƙare shekaru talatin cif a gidan kaso bisa tasa mummunar aƙidar mai muni, tare da biyan maƙudan kuɗin da za’a fuskanci lafiyar yaran da ya ɓatama rayuwa”.

        “ALLAH yay ma wannan yarinya albarka da iyayen ma da suka kawo ta duniya”.

    Furucin Ammah a bazata ya maidosa hankalinsa. A tare Hawwah da su Asma’u suka amsa da amin. Har Asma’u na faɗin, “Ammah nima in sha ALLAHU lauya zan zama. Wlhy tun randa na fara ganin matar nan kan case ɗin nan nake jin ƙaunarta da sha’awar nima na zama kamarta…..”

        (Ba Amin ba a ɓoyayyar halayyarta) ya faɗa a zuciyarsa yana miƙewa batare da ya ƙarasa jin zancen Asma’un ba. Sallama yay musu ya fito acewarsa zai sha maganin ciwon kai ne ya kwanta. Sun masa addu’ar samun lafiya, yayinda Ammah ta dakatar da shi da faɗin yazo ta kama masa kan. Gabanta ya dawo ya zauna. Ta kai hannun nata saman goshinsa da ke da ɗumi har yanzu. A hankali ya sauke ajiyar zuciya da har ta iya jiyosa, sai dai batace komai ba dan tun ɗazun zuciyarta ke bata kodai lamarin nasa ne ya motsa bai son faɗa, ko kuma yana son ya motsa ɗin. Sosai tai masa addu’a yanata faman sauke ajiyar zuciya kafin ya miƙe yana jin wata nutsuwa ta musamman na ratsa masa jini da ɓargo. Koda ya koma ɗakin ma magungunan da malam ya bashi ya shashsha sannan ya kwanta. Maimakon barcin sai abinda ya gani a tv ya shiga dawo masa tiryan-tiryan. Shi yama rasa a mizai fassara wannan yarinya. Ita dai gata nan rabi mutum rabi muna mutum. Sai dai kalaman nata na yau sun matuƙar tasiri garesa har yana haɗasu da na jiya data dinga faɗa cikin shirmen buguwar ita ba ƴar iska bace. Bawai ya gamsu da hakan bane. Dan babu ta yanda za’ai irinta mai ƙwalewa da kayen maye ta iya furta ita ƙillatacciya ce ya yarda. A yanzu hakan ma wani sashe na zuciyarsa na kallon kalamanta na ɗazunne kawai a gurbin fuska biyu irin na halayyar ɗan adam na yanzu. Ya ɓoye zahirinsa na mutumin banza, ya shiga gaba-gaba wajen bayyanama duniya shi na kirki ne na ALLAH. Guntun tsoki yaja da lumshe idanunsa yana fatan barci ya ɗauke sa…..

     ★★★

★.★.★★

   Tabbas a daren jiya yanda yaga rana haka yaga dare dan ko sau ɗaya bai rintsa ba. Sai faman bulbulama cikinsa hayaƙin cigarette da yay tayi dana shisha. Baya taɓa neman abu ya rasashi, haka ma bai taɓa harar mace sau biyu ba ta zille masa sai a kanta. Duk da ɓacin ran da ya tsinta kansa dalilin rasata a jiya bai ji ko ɗigon sha’awarta ya ragu masa a rai ba. Sai ma ƙaruwa yay yana sake azalzakarsa da sake tunzura buƙatarsa. Neman hanya ta uku ya tsunduma a tunani, sai dai zuciyarsa ta rabu gida biyu. Ɗaya na tabbatar masa ya nema aurenta kawai itace hanya mafi sauƙi. Ɗaya na tabbatar masa bazata amince ba, dan haka kota halin ƙaƙa kawai ya kore ƙishirwarsa, kai koda sakawa a sace masa itane. Ganin ya rasa makamar riƙewa sai kawai ya yanke shawarar neman shawarar abokinsa. Gabanin asuba yay kiransa, bugu biyu kuwa aka ɗaya dan shima a lokacin yana cikin club ne a Abuja……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣1️⃣

………“Mtsoww! Kaifa baka da aiki sai gantali, a ina kuma kake haka irin wannan lokacin?”.

        “Kai mai maganar a ina kake? Kujimin sa ido. Kodan kaje Kano kai ka koma ɗan gargajiya”.

   Ƙaramin tsaki Mm atik yay da faɗin, “Ɗan iska banda time ɗinka. Nifa magana mai muhimmanci na kira muyi, ka ɗan fita gefe Please nasan kana nan nane da cingam gal ɗin nan taka”.

        “Naji, na matsa ɗan shiga sharo, ina saurarenka”.

    Ɗan tsaki MM Atik yayi, dan harga ALLAH ya tsani budurwar abokin nasa da tabi ta kanainayesa ta hanashi rawar gaban hantsi. Cikin ture batunta ya ce, “Akan yarinyar nan ce dana faɗa maka. Plan ɗin mu na jiya fa ya rushe bata shiga tarkon ba”.

      “Whart! Wai kana nufin ka aiwatar?”.

   “Eh mana yau ɗin nan ma, amma sai…..” ya zayyane masa komai da ya faru. Da ga can Arman yay ƴar dariya da faɗin, “Wai driver? To ko dai shima yana hutawar ne?”.

          “Mtoww bana jin hakan gaskiya. Dan randa na fara haɗuwa da ita na gansa. Yanda ta yarfashi ma sai ya baka tausayi. Kawai dai irin mutanen nan ne masu shegen shishshigin tsiya. Nidai yanzu manta bani mafita”.

     “Ni dai mafita ɗaya na hango maka nasan kai kuma baka buƙatarta”.

   “Waccece? Please tell me!”.

“Aure!”.

“Mtsoww auren ƙaniya. Nima ina tunanin haka, sai dai banda shiri gaskiya na zama da mace yanzu, ban san takura kai ma ka sani….”

       “Ka tsaya nakai ƙarshe mana”.

   “Oh sorry ina jinka”.

“Abinda nake nufi bawai auren nata zakai ba. Tunda ka riga ka ƙwallafa ranka ka zama cingam boy kuma ita bazata samu ta sauƙi ba kawai kasa su Dad gaba aje maka neman aurenta…..”

       “Baka da hankali! Dad fa? Kasan waye Dad kuwa?!”.

     “Calm dawn mana my man. Lamarin fa duk lissafine. Yanda Dad keda alfarma na tabbatar sun san juna da babanta tunda kace itama ƴar manya ce. So da zarar magana ta shiga kai kuma sai kaita jan ra’ayinta harka samu cikar burinka. Daga haka mu ƙirƙirar mata laifin da shi Dad ɗin da kansa zai ce bazaka aurenta ba”.

     “Woow! Woow woow my dear wannan salon yayi kuma zai ƙayatar. Sannan ita kanta zan firgita lissafinta tasan ba irinmu ake ja a ƙasa ba. A safiyar yau ɗin nan zan zauna da Dad, nasan zai matuƙar ɗaukar abin da muhimmanci tunda dama burinsa kenan shi da Mom. Kai dai ALLAH ya barka da cingom gal taita ƙarar maka da ruwan kai bye”. Ya yanke wayar yana wani jin matuƙar farin ciki tamkar ya samu Lulu ƙamshi ɗin ya gama ne.

      Ni ko na ce, “Hummm!”

      ★★★

      Kamar yanda Alh. Baita da Hon. Nakowa suka girgiza da jin Mawaddat ɗiya ce ga Alhaji Isma’il Jiƙamshi haka shima Hon. Misau yay matuƙar girgiza da batun. Dan abune da ko’a lissafin hasashe basu taɓa kawowa ransu ba. A take suka zauna teburin shawara. Dan kuwa tabbas wata dama ce a yanzu tazo hannunsu akan Alhaji Isma’il Jiƙamshin. Kuma lokaci ne na ɗaukar fansa da zai goge tarihin baya labarin yazo da salon alƙalamin da sune zasu zama masu rubuta shi.

     Tsaf suka kammala tsara komai a yanda suke buƙata. Fatansu kawai nasara da kuma sake sabon bincike dan ƙara riƙe hujjoji masu ƙarfi musamman akan Alhaji Sufi Garko da suka yanke shawarar tunkara a farko. Dan tabbas babban ɗaurin huhun goro suka shirya yima uban da ƴar gaba ɗaya dan su kasance gaba ɗaya a tafin hannunsu. Basu sa wasa ba tun a ranar suka nema appointment ɗin ganawa da babban ɗan kasuwar, kuma ƙusa a ɓangaren siyasar arewacin kasar musamman ma Kanon ta dabo Alhaji Sufi Ado Garko. Tsoho da kuɗi kenan abokin tafiyar yara, manyan kuwa baba suke kiransa dan ya kere ya kuma zarce koda a tsaransa. An tabbatar musu yaje Umrah sai dai nan da kwanaki biyu idan ya dawo washe gari su shigo. Sun samu wannan damar ne dalilin shaƙama babban yaronsa kuɗaɗe masu kauri, sai kuma mulki da Hon. Nakowa da Hon. Misau ke riƙe da shi wannan ma babban makami ne…..

     ★★★….

      Ga Alhaji Sulaiman Sufi Garko ma ya gama shiryawa tsaf domin tunkarar mahaifin nasa game da auren Tajuddeen da Mawaddat. Dan a wannan karon ya ɗau aniyar koda yardarta, ko babu sai wanan auren ya ƙullun. Dan ya gama tanadar kalaman da zai tsara mahaifin nasa da su tsaf komai ya tafi dai-dai. Tajuddeen ya samu cikar burin shima ya samu nashi…..

      ★★★….

      A ɓangaren Lulu ƙamshi da bata san mi suke ba gaba ɗaya hankalinta na kan case ɗin yarinya da akaima fyaɗe ne. Dan anata neman mijin matar amma an rasashi wai ya gudu yabar gari tun a randa yay abun. Wannan takaicin ne ya taru yay mata yawa ta tada hankalin su Sha’aibu ɗan sanda dama na duk wanda ke mata aiki idan irin wannan case ɗin ya taso. Hatta Daddy bata barsa ya huta ba. Ga takaicin Smart yaƙi dawowa aiki itako ta gaji da tuƙi dan sunata zirga-zirga. Shiko Uncle Yousuf ne yace ya zauna gida ya huta har sai jikinsa yay masa ƙarfi. A washe garin kwana na biyu da take saka ran dawowar Grandpa ɗinta da ga umra duk da tarin ayyukanta haka tai wancakali da su ta shiga tawagar ƴan tarbarsa a airport dan ya kwana biyu baya Nigeria, saboda daga uk ganin doctor ɗinsa ya wuce Saudiya Umrah. Tana kewarsa dan tana matuƙar so da ƙaunar kakan nata daya haifi mahaifiyarta da bata sani ba sai a hoto. Shi takema kallon uwa ga shi kuma shine kaɗai ya rage mata a kakanninta dama. Shima kuma a karan kansa yana nuna mata tsagwaron soyayya kasancewar ta ɗiya ga Mawaddat dinsa da ya rasa dan ita kaɗai ya taɓa rasawa a cikin ƴaƴansa shiyyasa yake matuƙar tausayin Lulu.

          Ƙarfe kusan sha biyu jirginsu ya sauka. Duk da hango ƴan uwanta jikokin Alh. Sufi Garko da tai su Tajuddeen da sukazo tarbarsa suma ƙin fitowa tai tana daga motar har sai da taji ance jirgin da ya taso da ga Saudiyan ya sauka sannan ta fita. Sanye take cikin gawn ta material mai taushi da santsi da sukai matuƙar mata ƙyau da fidda mata ƙyaƙyƙyawar surarta kamar wata ƴar tsanar roba. Ɗaurin kanta da Amrah (Hussaina) tai mata yayi ƙyau ya kuma rufe mata gashi, sai ta gaba kaɗan da aka zamashi ake iya ganinsa baƙi siɗik a kwance, Kasancewar a ɗaure yake da ribbon sai yay tilluwa a cikin ɗankwalin da aka rufesa da shi ruf. Siririn mayafi kalar material ɗin ta ɗora a kafaɗa babu zancen yafawa. Sai dogon takalmi kamar koyaushe duk da kuwa ita ɗin doguwa ce amma bacan ba tsaka tsaki. Ƙaramar handbag ɗin hanunta ta sake gyarawa da gilashin idonta da ya sake ƙawata kwalliyar tata duk da kuwa a fuskarta babu ko ɗigon kwalliya bayan hoda dan itafa bata kwalliya, sai lips glose data saka a lips ɗinta kaɗan. Yanda take taku kamar wata tarwaɗa da sautin da takalmanta ke badawa ga ƙamshin turarenta data bulbula ya sata janyo hankulan mutane gareta musamman na kusa da ita. Sosai numfashin Tajuddeen ya dinga kaikawo a ƙirji har ta ƙaraso garesu. Ya haɗiye busashen yawun da ya kasa wuce masa a maƙoshi yana ɗan sakin murmushi. Ɗauke kanta tai kamar bata gansa ba, sai ma yatsu biyu data ɗaga musu a taƙaice tare da faɗin, “Hy girls and boys”. Duk wanda yasan Lulu a family ɗin yasan ba kanwar lasa bace, ba kuma wani take ragawa ba. Duk da mafi yawansu sunada labarin tushen asalin arzikin mahaifin nata da ga kakansune wani bai isa furtawa ba tai masa wankin babban bargo ita babu ruwanta. Yanda tai musu gaisuwar cike da raini ya zafi wasu musamman ma matan amma babu wanda ya nuna, to ita bama ta tsaya sauraren amsawar tasu ba tuni tai gaba, dan a dai-dai nan Alhaji Sufi Garko ke fitowa da ga jirgi gefensa p.a ɗinsa ne da shima zai iya kai sa’annin su Daddy. Lallai ya tsufa kam, damma harka irin ta masu hannu da shuni mai wahalar sha’ani. Amma irin wannan tsoho ai kamata yay ace yana zaune gida jikoki zagaye da shi yana hutawa kawai. Cike da ɗoki da farin cikin murmushi mai bayyana haƙora da ke da tsada a fuskar Lulu dan kafin ka gansa ka yara ta nufi kakan nata ta rungume. Shima tashi fuskar ƙawace da murmushin ya tarbi abarsa yana mai farin ciki da jin kewarta har cikin ransa. Sai da ta gama nata farin cikin sannan sauran yaran suma suka matso garesa su Tajuddeen. Suma ya nuna jin daɗin ganinsu dan yana son ƴan jikokin nasa da a yanzu duk suka zama manya samari da ƴammata har ma da masu aure, dan su Lulu kusan sune ƙanana ma duk da dai suma akwai waɗanda suka girma. Da ga haka aka ɗunguma zuwa gida, inda Lulu ta tubure motarta zai shiga dole kuma akai hakan dan kowa yasan rigimarta original ce. Yanzu kam a hankali take tuƙin dan Alhaji Sufi yayi gargaɗi. Daga shi sai ita ne a motar, dan haka taketa masa hira shiko yan biye mata. Tausayinta yake ji fiye da kowa a cikin zuri’arsa saboda maraicinta, ga kuma ƙaunar da yakema mahaifiyarta itama ya shafeta. A gidan ma koda suka iso sai suka samu ƴaƴansa maza da mata da ke cike da gidan duk dai akan dawowar tasa. A duk sanda akai irin wannan taron da wahala kaga Lulu batai kuka ba koda a ɓoye ne saboda jin buƙatar mahaifiyarta itama. Yanzu ɗin ma da ƙyar take iya danne hawayenta, tama ƙi shiga gidan, tana ganin ƴaƴansa sun janyesa ta zame jikinta ta gudu. Tuƙi take tana hawaye da jin kewa mai tsanani, tasan Mommy uwa ce a gareta, amma da gaske tana buƙatar ɗumin mahaifiyarta koda sau ɗaya ne inda ace hakan zai yuwu, sai dai tasan har gaban abada bazai yiwun ba kuma. Gefen titi ta gangara a hankali ta kashe motar ma baki ɗaya ta lafe cikin kujerar idanunta lumshe tai shiru, so take tai kuka amma tana ƙoƙarin hana kanta hakan. Bata cika son shan komai da rana ba musamman a lokacin aiki, sai dai a yanzu babu abinda tafi buƙata kamar tasha ɗin. Duk yanda taso hana kanta taji shan kawai take buƙata. Cikin rawar jiki ta jawo handbag ɗinta, faudanta ta zaro tare da buɗeta acan ƙasa ta ciro wata takarda da’aka naɗa kamar ƙullin magani. Tana warwareta sai ga ƙwayoyi a ciki. Gaba ɗaya kusan fin biyar duk da ƙananu ne sosai ta afa batare da neman ruwa ba ta haɗe abinta tana wani sauke ajiyar zuciya. (Kamar wadda ta haɗu da uwar tata da take nema😔🤦. Ya rabbi ka shiryemu ka shirya mana zuri’a ka rabamu da mummunar ƙaddara😭🙏)………..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣2️⃣

……..Motar taima key ta cigaba da tafiya duk da ta fara jin kanta ya ɗauka. Da ƙyar ta iya kai kanta office saboda abinda tasha ɗin ya fara aikinsa. A yanda ta shiga duk da bawai tana layi bane yasa mutane da yawa ɗan binta da kallo. Office kawai ta faɗa tare da maidashi ta rufe harda saka key. Tai jifa da handbag ɗinta da key da takalma har ma da mayafi da ɗan kwali. Zama tai jikin kujera ta dunƙule jikinta waje guda tana mai tura kanta data dafe da duka hannu biyu tsakanin ƙafafunta. Surutai takeyi ƙasa-ƙasa irin wanda idan ba kusa da ita kake sosai ba bazaka taɓa iya fahimta ba…

       _(Kai jama’a shaye-shaye baiyi ba. Shaye-shaye kan zubar da mutuncinka kowane matsayi ka taka. Yana maidaka baya komai ƙarfin ikon ka. Yana ƙasƙantar da kai komai darajarka. Ga lafiyarka kaima da ɓarnar kuɗi. Miyasa ƴan uwa? Mike birgemu? Mike ruɗarmu?. Kuɗi? Ƙawaye? Abokai? Samari? Gata? Kokuwa son zuciya?. Idan duk sune mu tabbata masu ƙarewa ne kamar ba’ai ba. Masu zama labarine kamar basu zo ba. Shaye-shaye wafce mana dukkan muhimman damammaki yake na cigaban rayuwarmu ta duniya da lahira. Kuduba ku gani, duk shekaru irin na Mawaddat bama tasan minene addininta ba, duk da tarin damammakin rayuwa da ALLAH ya bata wannan illar ɗaya take ta shaye-shaye da ke tare da rayuwarta na ƙoƙarin maidata baya. Tun tana ganin tana kiyayewa akan aikinta gashi ta fara kuma a cikin lokacin aikin, mi kuke tunani? Wataran aikin ma sai ta gagara yinsa gaba ɗaya. Da ga sanda ta rasa wannan damar kuma shike nan ta ƙarasa rushewar baki ɗaya sai jiran ta fara bin bola kuma duk da gatan ta😭. ALLAH ka shiryemu ka shiryar mana da zuri’armu da duk masu wannan mummunar ɗabia)._

      ★★…..

       Bayan sallar la’asar Daddy da Uncle Yousuf suma suka shiga jerin ƴan sannu da zuwa ga Alhaji Sufi Garko. Ya nuna farin cikin ganinsu. Dan mutum ne da ya san mutuntawa. Kallo yake musu suma irin na ƴaƴa tun kan aurattayya ta shiga tsakanin ɗiyarsa da Daddy balle yanzu ga Mawaddat ta ratsa duk da babu ɗiyar tasa data zama sanadi a duniya. A hirarsu ne ma suke jin cewar Mawaddat ce ta ɗakkosa da ga airport, yana ƙyautata zaton ma har yanzu tana a gidan tare da ƴan uwanta. Daddy yaji daɗin hakan har Uncle Yousuf ma kansa. Basu nemeta bata suka cigaba da hirarsu hankali kwance. Shigowar Alhaji Sulaiman (mahaifin Tajuddeen) ce ta saka Daddy yin shiru, sai kuma ya dubi Alh. Sufi Garko da suke kira da Baba cikin girmamawa ya ce, “Baba inaga bara mu wuce ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne”.

       Alh. Sufi ya tsatstsare Daddy da idanu batare da ya amsa ba, sai kuma ya maida dubansa ga ɗansa Alh. Sulaiman da ya koma can gefe zai zauna. Cikin bada umarni ya ce, “Isma’il koma ka zauna”. Babu musu Daddy ya koma ya zauna ɗin. Ya maida dubansa ga Alh. Sulaiman da faɗin, “Kaima zonan”. Gaba ɗayansu a gabansa sukaje suka zauna kowa na hararar ɗan uwansa kamar wasu ƙananan yara.

      “Ku yanzu kuna ganin wannan rayuwar bazaku ajiyeta ba. Ko a tinaninku har yanzu ku yarane? Ku duba gashin kawunanku furfura duk ta gitta a ciki. Tunda kun gagara faɗamin matsalarku a tsahon shekarun nan ni bazan cigaba da damuwa da sai na sani ba. Sai dai ku sani idan har abinda ya shafeku kuka bari ya shafi zuri’arku bazan yafe ba. Ku shaida hakan ko bayan ƙasa ta rufe idanuna ne”.

    (Anzo wajen) cewar Alh. Sulaiman a zuciya. Dan haka ya gyara zama cike da makirci ya sake raunana muryarsa. “Baba ni ba laifina bane, tunda kowa shaidane na biyo hanyar da zamu sasanta da shi a shekarun baya amma ya koma bayan fage ya zuge yarinya komai ya sake rushewa. Shine ya sakama ransa ni maƙiyinsa ne kawai. Shiyyasa naso haɗin auren Tajuddeen da Mawaddat dan ya tabbatar ba hakan bane ba. Kuma ko a yanzu in har zai amince ya cire komai a ransa ni a shirye nake komai ya zama labari. Mu kuma dunƙule ƴaƴanmu waje guda matsayin ma’aurata dan ƙara danƙon zumincinmu”.

        Wani irin kallon ɓacin rai Daddy ke masa. Sai dai baice komai ba. Alh. Sulaiman da ke masa kallon ƙasa-ƙasa ya saki wani irin makirin murmushi da kashe masa ido ɗaya. Ƙara tunzura zuciyar Daddy tai amma sai ya danne dan jin Baba ya fara faɗin, “Ni kaina zanso wannan haɗin zumincin, zan kuma so ya zama sanadin canja wannan gabar taku. Sai dai kuma bazan so ya rikiɗe daga manufarmu ya koma abinda bashi muke fata ba zumincin ya taɓarɓare ma fiye da yanzu….”

       “Amma Baba ai yaran suna matuƙar son junansu. Dama tun farko matsalarmu ce ta tilastasu haƙura a wancan karon ma”. Alh. Sulaiman ya faɗa yana sake sakin makirin murmushi. Baba da ba ganin abinda ke faruwa yake ba ya kai dubansa ga Daddy da baice komai ba. “Isma’il bakace komai ba. Abinda ɗan uwanka ke faɗa gaskiya ne?”.

          Murmushin mugunta Daddy dake ƙulla murtanin da zai maida ga Alh. Sulaiman ya saki. Cike da sake girmamawa ga surukin nasa kuma ogansa ya jinjina kansa. “Baba duk ina saurarensa. Sai dai na tafi wani tunani ne, kenan Mawaddat ƙarya tamun ko kuwa rashin jin nata ne ya sata kawo min wani a matsayin miji alhalin suna tare da Tajuddeen har yanzu…”

        “Miji?”.

    Alh. Sulaiman ya faɗa kamar a ɗan razane. Shiko Baba murmushi yayi da faɗin “Miji Mawaddat ɗin ta fitar?”.

   “Eh Baba. Dan dama dawowarka muke zaman jira muzo maka da batun. Saboda yanata ma damuwar turo magabatansa amma ina dakatarwa da cewar har sai ka dawo tukunna”.

        “Wlhy ƙarya kake Isma’il! Wannan makirci ne ka ƙulla dan kar Mawaddat ta auri Tajuddeen, an gaya maka tsoronka nakeji wai ne da na gagara ɗaukar mataki a kanka tun a baya”. Alh. Sulaiman ya faɗa yana miƙewa zumbur. Gaba ɗaya falon suka zuba masa ido. Sai kuma duk ya daburce dan fahimtar yana neman yin ɓaran ɓarama fa.

   “Ka ɗauki mataki a kansa! A wane dalili Sulaiman?”. Baba ya katse shirun. Kame-kame Alh. Sulaiman ya fara, hakan ya bama Daddy damar sakin murmushin mugunta. Sai kuma ya dubi Baba. “Baba ƙyalesa kawai shirmensa ne. Kasan shi Sulaiman idan ya fusata akan abu baida fahimta. Sannan ya iya sakin duk maganar da tazo masa a baki koda ba hakan bane a ransa. Ni dai ba ƙin haɗin auren Mawaddat da Tajuddeen nake ba. Kawai shashancin da tayi ne na kawo min wani matsayin miji da har na sanar da nawa dangin dama jiranka kawai muke ka dawo a tsaida biki alhalin tana tare da Tajuddeen kuma ne yasa ma harna faɗa. Amma ayi haƙuri ni zanje ga babanta Yousuf mu sameta a nutse na mata tambayoyi dan nasan halinta bajin magana take ba. Kaga idan Tajuddeen take so ni bazan hana ba, sai nasan dabarar yi wancan ya janye a rabu lafiya mutuncin kowa bai zube ba….”

       “Mizai hana w kirata yanzu ayita ta ƙare”.

   Cewar Alh. Sulaiman. Shiru kamar Baba bazaice komai ba. Sai kuma ya nisa a hankali da faɗin, “Ku dukanku kunzo da shawara mai ƙyau kuma duk na gamsu da maganarku. Sai dai muyi haƙurin goben sai a zauna a nutse kan maganar. Amma yanzu ina son a kiramin Mawaddat da Tajuddeen”.

      Sosai hankalin Daddy ya tashi, amma ya danne a ransa yana mai addu’ar ALLAH yasa kada Mawaddat ta watsa masa ƙasa a ido. Dan shifa bazai taɓa yarda ya haɗa zuri’a da Sulaiman ba. Shi kansa Uncle Yousuf zancen Yayan nasa ya sakashi a ruɗani. Duk da yasan akwai ƴar tsamar da har yanzu bai san tushen ta ba tsakanin ɗan uwan nasa da Alh. Sulaiman bai san dalilinsa na ambaton wani ba matsayin Mawaddat ta kawo bayan yasan ba hakan bane ba. Kusan a tare suka saki ajiyar zuciya shi da Daddy lokacin da ɗan aiken ya dawo ya tabbatar musu ai Mawaddat ance ta tafi tunma ɗazun. Alh. Sulaiman kuwa bai so haka ba. Amma baice komai ba, sai dai a ransa yana ƙudurta duk Daddy yayi ya gama a wannan karon sai Mawaddat ta zama matar Tajuddeen…..

        😂Anayi muna cin tuwon masara miyar kuka🤪.

              ★★..★★

     Yau gaba ɗaya a gida ya yini saboda tun daren jiya Uncle Yousuf ya ce masa karfa ya fito aiki yau ɗin ya bari har sai yaji ƙarfin jikinsa. Hakan ya saka shi yin zamansa tunda dama sunyi faɗa da ogar tasa. Ɓoye kansa yay a ɗaki ya sha barci, hakan yasa babu wanda yasan yana gidan ballema ya tuhumesa tunda bai sanar musu abinda ya samesa ba. Bayan sallar la’asar gaba ɗaya kuma sai zaman gidan ya gunduresa. Hakan ya sashi miƙewa ya kimtsa. Yayi ƙyau cikin ƙanan kayan duk da shi bawai ya saka don kwalliya bane ba. Ƙamshin turarensa yake mai sanyi da sakama zuciya nutsuwa. Sai da ya fito ya fara tunanin inama ya dace ya nufa? Duk da har yanzu yana jin jikinsa babu kuzari sosai. Rashin mafitar ina ya kamata ya nufa ya sashi kallon agogo, yasan yanzu bata tashi aiki ba, bara ya gwada zuwa idan ta huce sai ya maidata gida kawai, yafi ya tafi yawo mara dalili. Napep ya tare ya shiga.

        Zuwa yanzu gaba ɗaya yanayinta ya sake birkucewa, ta zame ribbon ɗin data ɗaure dogon gashinta da ya sauka har kafaɗarta. Sosai idanunta sunyi jazur haɗe da kumburowa. Surutai take ita kaɗai da gaba ɗayansu na bege ne ga mahaifiyarta. Sai kuma zagin mijin matar nan da yay fyaɗe tare da ɗaukawa kanta alƙawarin koya masa hankali da duk ire-irensa. Hawaye take da murmushi a lokaci ɗaya, yayinda ta ƙurama hoton mahaifiyarta da ta ɗakko saman decks ɗinta dake a cikin wani ɗan ƙyaƙyƙyawan fram ita da Daddynta, hoton anyisa ne bayan aurensu a ƙasar Mexico lokacin sunje honeymoon. Su dukansu suna sanye ne a cikin ƙanan kaya suna kallon juna da murmushi mai nuna tsantsar soyayya da sukema juna. Hannunta ta kai ta shafa fuskokinsu, sai kuma ta rungume hoton tana mai komawa kwance rigingine ta ƙurama p.o.p ɗin office ɗin ido. Ƙwayar tata ce ta fara gaya mata shirme ga mahaifiyarta a wajen cikin farin tufafi tana mata kallo mai kama da tausayi………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣3️⃣

…….Bai san ainahin Office ɗin nata ba, sai dai ganin motarta a harabar wajen ya sake tabbatar masa da tananan bata wuce ba. Tunanin zaman jiran fitowarta yayi, hakan ya sashi samun wajen zama a gurin securitys. Bayan gaisuwa a tsakaninsu bai sake kula kowa ba ya shiga sana’ar tasa ta game ɗin ball a waya. Biyar dai-dai babu alamar zata fito, tun yana ɗan ɗagowa ko zai hangota har ya fara sarewa ganin biyar da rabi har ta gota ma. Ga mafi yawan ma’aikata sun wuce dan motarta da wasu biyu ne kawai suka rage a harabar wajen. Ɗaya da ga cikin security ɗin ne ya dubesa tare da faɗin, “Abokina wanda kake jira har yanzu bai ƙaraso bane? Dan shida dai-dai ake rufe wajen nan fa”.

      Wayar ya ajiye tare da ɗagowa ya dubi security ɗin fuskarsa a ɗan sake, sai dai ba murmushi yake ba. “Wadda nake jira tana ciki dan ga motarta nan, nima ina tunanin ko lafiya har iyanzu bata fito ba”.

          “Kana nufin Madam Mawaddat Jiƙamshi?”.

     Kai ya jinjina masa alamar ita. Shima security ɗin cikin nuna jimami ya ce, “Inaga dai yau aiki ne yay mata yawa gaskiya, dan a kullum zakaga idan bata zama ta farkon tashi ba to zata zama ta biyu. Nima kaina nayi mamakin rashin fitowar tata yau duk da dai naga wani aiki tasa a gaba kwana biyun nan mai muhimmanci. Amma bari na duba maka maybe bata san kana zaman jiranta bane”.

      Kafin Smart ya samu damar cewa wani abu security ɗin yay gaba. Minti kusan uku sai gashi ya dawo. “Abokina inagafa kamar akwai matsala”.

            “Matsala kuma? Tami fa?”. Smart ya faɗa ƙirjinsa na bugawa da sauri-sauri. Amma sai ya dake abinsa kamar babu komai. Security ɗin ya cigaba da faɗin, “Bawai matsalar bace a zahirance, na samu sakatariyarta ce kawai zaune cikin damuwar wai tun ɗazun data fita ta dawo ta shige office ta rufe kanta har yanzu bata fito ba. Ta mata knocking kuma yafi sau ashirin batako ji motsinta ba sai yanzu babu jimawa taji maganarta kamar cikin surutai”.

     Ƙirjinsa ne yaji ya ƙara bugawa, ya kai yatsunsa biyu saman goshi ya ɗan murza. Basai ya nema ƙarin bayani ba yasan wani abu tasha. Sai dai bai taɓa tunanin har a wajen aikinta ma tana shan abubuwan nan ba. Ɗagowa yay idanunsa har sun kaɗa da ɓacin rai. “Kozan iya shiga office ɗin nata?”. Ya tambayi security ɗin.

           “Ah eh mana mizai hana. Ai gara a je a duba mike faruwa ko?”.

    Miƙewa kawai yay, security ɗin yay masa jagora har office ɗin. Sun samu sakatariyarta tsaye jikin ƙofar tana knocking da faman kiran “Aunty! Aunty Please ki buɗe ko kiyi magana dan ALLAH.”

        “Kinga ƙyaleta idan da key bani”. Ya faɗa cikin dakewa. Cikar kamala da kwarjininsa yasa Zainab jin bazata iya musa masa ba. Duk da kuwa yau ne karo na farko data taɓa ganinsa anan ɗin. Sai kuma ganin harda security ya ƙara mata ƙarfin gwiwa. Muryarta a sanyaye ta ce, “Sai dai na duba ko zanga extra keys dan ta shiga da key ɗin ciki”. Kansa kawai ya jinjina mata, ta koma wajen table ɗinta domin bincikawa. Shi kuma ya jingina da bango tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya lumshe idanunsa. Kusan mintina huɗu tana ta binci-bincike har dai ta samo keys ɗin da ƙyar. Gabansa tazo ta miƙa masa cikin girmamawa.

     “Thanks” yace a hankali yana amsa. Koda ya buɗe ƙofar bai yarda ita da security ɗin sun biyosa ba sai da ya leƙa. Saurin rumtse idanunsa yay tare da yo baya, cikin ɗan furzar da huci ya gyara yanayin fuskarsa yanda zasu fahimcesa. “Inaga bata da lafiya ne, kun san halin ogar taku kuma maybe bata buƙatar kowa ya sani shiyyasa taya rufe kanta a ciki, ku barni da ita kar ku samu rabon faɗa kuma”. A yanda yay maganar dole ne ka gamsu, dan haka security ɗin yay murmushi dan kuwa masifar Mawaddat kowa ya santa, idan sukai sanya wajen buɗe mata gate kota saka wani aikin kai mata wasa sai ta tsefeka tas. Balle ma Zainab da tafi kowa sanin wacece uwargijiyar tata. Sallama security yay ya fita, Zainab kuma ta koma mazauninta ta zauna duk da ya kamata ace ta tashi, amma dai tafi yarda taga sai Mawaddat ta fito lafiya sannan. Ƙofar ya sake turawa ya shiga ya maida ya rufe tare da jingina jikinta kansa a ƙasa bai yarda ya sake kalloba. Kamata yay ya kira Zainab, sai dai baya son ta ganta a yanayin. Har yanzu tana kwance a tsakkiyar sofas ɗin da aka shirya dan zama bayan ta zamanta da wanda ke a gaban table ɗin nata. Ta ture Centre table ɗin tsakkiyar kujerun tana kan carpet ɗin gashinta yaɗan barbaje. Har yanzu idanunta na kallon p.o.p ɗin office ɗin, hira take da mamanta da idanunta ke gani ko nace ƙwaya take siffanta mata. Hawaye share-share a fuskarta ga murmushi. Tsaiwarsa gurin shiru na wasu sakanni ya sashi ɗan jin soki burutsunta. A karo na farko ya ɗaga kansa ya dubi p.o.p ɗin shima jin tana faɗin, “Mammah karki sake tafiya ki barni kinji. Kiyi zamanki muyi hirarmu, inma bazaki min magana ba ni zan na miki murmushinki ya wadatar dani. Kar kiyi kuka a kaina bana son ganin hawayenki ki bari Please ki bari…” ta faɗa cikin wani irin sanyin murya sai kuma ta fashe da kuka. Da farko bai ɗauki surutun nata komai ba sai shirme irin na masu shaye-shaye, sai dai Mammah da take ambata ya tsaya masa a zuciya. Ganin yana ɓata lokaci ya sashi furzar da ƙaramin iska tare da cigaba da takawa cikin office ɗin, ƴan dube-dube yake yi duk da baiyi tsammanin zai iya dacewa da abinda yake neman ba. Dama baiyi tsammanin ganin ba ai. Fita yay inda sakatariyarta ta take, tana zaune dai har yanzu sai dai yanzu da waya a hannunta, dan tunda ta turama Uncle Yousuf text take tsammanin shigowar kiransa amma shiru kake ji.

     “Ko zamu samu Hijjab?”.

   Firgigit ta dawo a hayyacinta dan jin saukar deep voice ɗin sa a bazata cikin kunnen ta. Sake maimaita mata yay ganin kamar bata jisa ba. Kanta ta gyaɗa masa da sauri tana nufar inda ta jiye hijjab ɗin sallarta ta ɗakko masa. Amsa yay kawai ya koma ciki. Yana ɗan sauke ajiyar zuciya, yanzun ma bai yarda ya kalletan ba ya warware hijjab ɗin tare da kaiwa duƙe gabanta. Karan farko na rayuwarsa ya ambaci “Mawaddat!” cikin ɗacin murya da tausasawa, sai dai acan ƙasan makoshinsa zaka iya fahimtar jin zafinta. Ƙarfin muryarsa da yanda yay kiran nata ya saka shigar sautin cikin kunnenta a bazata. Kamar wadda aka farkar a cikin barci ta juyo idanunta da suka sake girma da ɗan juyewa kansa. “What!” ta faɗa a zabure tana tashi zaune sosai. Sai kuma ta kalla sama da ɗaga hanunta. “Mammah ki jirani dan ALLAH”.

       Kallonta yay jin abinda ta sake faɗa, hakan sai yay dai-dai da yanda ta zuba masa juyayyun idanunta fuska a yatsine tana wani ƙwaɓeta ta ce, “Who are you? Miya kawo ka nan?”.

      Tsaki ya saki tare da ɗauke idanunsa ya yafa mata hijjab ɗin a jiki. Hannun da takai cikin yar kokawar ture hijjab ɗin ya buge. Da sauri ta janye tare da faɗin “ouch!” saboda zafin da taji. Baibi takanta ba ya ƙarasa saka mata hijjab ɗin batare da ya yarda ya taɓa mata jiki ba. Wata muguwar harara ta watsa masa ta ƙara kai hannu zata cire hijjab ɗin ya daka mata tsawa.

     “Idan kika cireshi na rantse sai na canja ma fuskarki kammani da mari!!”

    Sosai tsawar tasa ta ratsata. Gaba ɗaya sai ya sake juye mata a cikin idanu kamar wani bahagon zaki. Kuka ta saki da duban p.o.p ɗin ta ce, “Mammah kinga yana min ihu ko. Bana son shi yanada girman kai”.

         Bakinsa kawai ya taɓe da cigaba da tattare kayayyakinta data barbaza a office ɗin waje guda, a zuciyarsa yana faɗin (aike naki kan ƙarami ne). A dai-dai nan aka turo ƙofar aka shigo. Juyowa yay da ɗan sauri dan a tunaninsa sakatariyarta ce, amma sai ya ga Uncle Yousuf ne. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan gaskiya yaji daɗin zuwan nasa. Dama sai faman ƙullawa da kwancewar ta yanda zai fita da ita a office ɗin yake. “Barka da yamma Alhaji”.

      Murmushin ƙarfin hali Uncle Yousuf ya saki yana jinjina kasa, sai kuma ya maida dubansa ga Lulu da har yanzu ke sambatunta irin na rashin kasancewa a hayyaci. Idanu ya ƙura mata da kamar wanda ya zurfafa kansa a tunani, maganar Smart ta sakashi yin firgigit. Cikin ƙoƙarin shanye abu mai ƙona zuciya ya sake dubansa da murmushi. “Aliyu ya jikin naka? Kai da nace yau karkazo aiki shine kuma ka fito?”.

        “Naji sauƙi ai Alhaji. Kasan zaman gidan isar mutum yake yi shiyyasa na fito. Nafito ɗin kuma na rasa ina zan nufa shine kawai nace Bara na duba ko bata tashi aiki ba sai na maidata..”

       Uncle Yousuf da ke jin zuciyarsa babu daɗi ya kai zaune yana mai tallafo haɓarsa. Kusa da shi ya nunama Smart da ke kallonsa. Babu musu ya zauna sai dai a kujerar gefensa. Ya fahimci irin damuwar da Uncle Yousuf ɗin ya shiga, dan haka sai shi ya ɗan sassauta tasa cikin furzar da ƙaramin huci. “Alhaji damuwa bata zama maganin matsala ba, sai dai ta zama sanadin ƙirƙirar sabuwar matsala wa rayuwa…..”

        “Hakane Aliyu. Amma ka duba fa kenan har a wajen aikinta ma tana sha? Hakan kuma na nufin duniya ta jima da sanin halin da Mawaddat ke a ciki amma mu bamu sani ba”.

     “Banajin hakan gaskiya Alhaji”.

  Idanu kawai Uncle Yousuf ya tsira masa, dan haka office ɗin yay shiru sai surutan Lulu kawai ke tashi cikin sambatun maye. Kiran da ya shigo a wayar Uncle Yousuf ɗin ce ta katse shirun nasu. Kamar zai share sai kuma dai ya cirota a aljihu. Daddy ne, yasan jiransa ya keyi dan sun zauna zasuyi magana ne Zainab ta tura masa saƙo shine ya taho hankali tashe. Wayar ya ɗaga tare da kaiwa kunnensa. Muryarsa a sanyaye ya ce, “Yaya!”.

         Daddy da tun fitowar ƙanin nasa ya kasa zaune ya kasa tsaye ya ce, “Yousef miya faru da ita?”.

     “Babu komai yaya ka kwantar da hankalinka dan ALLAH. Dan nama tadda Aliyu har yazo ma shi….”

   “Waye Aliyu? Ko drivern ta?”.

“Eh yaya.”

“Ka faɗa min gaskiya Yousuf abubuwan tasha ko?”.

        “Yaya dan ALLAH k…”

    “Yousef please”.

Daddy ya faɗa cikin tare numfashin Uncle Yousuf ɗin. Cikin sakin ajiyar zuciya ya ce, “Hakane. Amma dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, gamu nan tahowa gidan ma”. Daga haka ya yanke wayar. Shi ya ɗauki Lulu kamar ranar, Smart kuma ya fita da kayayyakinta a hannu. Zainab da gaba ɗaya hankalinta ya tashi da ganin yanda aka fiddo auntyn tata ya kalla. “Ki rufe office ɗin ki sameni waje a maidaki gida”. Daga haka yay ficewarsa.

       Kamar yanda ya bata umarni hakan tayi, lokacin data fito har Uncle Yousuf da ya saka Mawaddat a motarsa yana ƙoƙarin ficewa a gidan. Yayinda smart ke tsaye yana jiranta. Batare da yi mata magana ba ya shiga motar, itama sai ta buɗe ta shiga kusa da shi. Har gida ya kaita abisa kwatancen da tai masa, godiya taita masa cikin girmamawa, karan farko yay mata guntun murmushi cikin jinjina kai ya ja motar ya wuce……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣4️⃣

…….Idanu kawai Daddy ya zubama Mawaddat hawaye na kwaranya saman dattijuwar fuskarsa. Itako sai surutai take musu. Sai ta kalla Daddy tayi ta kalla Uncle Yousuf shima tayi. “Yaya kukan nan fa bashi da wata ma’ana, addu’a itace kawai. Sannan bazan gaji da faɗa makaba ka bada kaso mafi yawa akan shiga wannan yanayin nata. Sai dai kawai muyi ƙoƙarin gyara kuskuren a yanzu. Ga kuma wannan matsalar data kutso kai, duk da dai ni da za’a bi ta tawa da kawai a aura ma Tajuddeen ɗin tunda mun san dai yaron nan bashi da wani aibu a rayuwarsa…..”

        “Yousuf matsalar ba daga Tajuddeen take ba da ga mahaifinsa ne. Nasan abinda baka sani ba akan sulaiman sani na haƙiƙa. Kamar yanda na faɗa maka tun a wancan karon Tajuddeen an kwaɗaita masa son Mawaddat ne kawai da manufa, sai dai shi yaron ya afka batare da sanin manufar mahaifin nasa ba, ko kuma dama yana son nata shiyyasa Sulaiman yay amfani da wannan damar wajen sake jan zuciyarsa da tunanin hakan zai bashi nasara akaina.”

      “To amma yaya ai shine zai zauna da ita ba Mahaifinsa ba. Indai har mun tabbatar da yana son nata kamar haka banga aibun aura masa ita ba. Na sani ka sani Mawaddat bata kula kowa, ta ina shi mijin daka ambata gaban Baba zamu samar da shi? Dan kasan dai in har babu wannan mijin to dolene Mawaddat ta auri Tajuddeen tunda baba da dangin mahaifiyarta duka sun ɗauki abin da muhimmanci bakuma zasu taɓa bijirema umarnin mahaifinsu ba kamar yanda suka saba”.

            “Duk nasan da wannan Yousuf. Kuma nima damuwata a yanzu shine ta yanda zamu samar da mijin koda ace na wucin gadi ne kafin ƙura ta lafa.”

    “Wucin gadi kuma?”.

“Yes wucin gadi, dan ba zan taɓa yima yaranmu ko ɗaya auren dole ba. Auren ma da jini irin na Sulaiman mai shirye da manufofi masu yawa da sai anyi auren ne sun fara bayyana zaka fara dana sani kai kanka”.

          Shiru kawai Uncle Yousuf yay yana kallonsa, shi kam gaba ɗaya ma a wannan gaɓar ya shiga ruɗani zai ce. Ya kasa fahimtar ainahin abinda ke tsakanin yayan nasa da yayan matarsa da a shekarun baya suka kasance shaƙiƙan abokai da ko ƙuda baya iya jin sirrinsu. Anya kuwa yayansa baya ɓoye masa wani babban al’amari da ya kamata ace ya sani…..

     “Assalamu alaikum”. Sallamar Smart a ƙofar falon ta katse tunaninsa. Daddy ne ya amsa tare da bada izinin shigowa dan ya shaida muryar yaron. Akan Lulu da ke kwance a ƙasa barci na neman rinjayar idanunta tana kokawar hanashi ya fara sauke idanunsa. Kaudasu yay duk da sanye take da hijjab ɗin da ya saka mata har yanzun. A nutsensa ya gaishe da Daddy, tare da ajiye key ɗin motar hannunsa. “Sannu da ƙoƙari fa, ALLAH ya saka maka da alkairi kaji”. Daddy ya faɗa a karo na farko. Ɗan murmushi Smart yay cikin jinjina kai. “Babu damuwa ai Alhaji. Nima na gode. Bara na wuce gida”.

         Godiya Daddyn ya sake masa, tare da zaro kuɗaɗe masu yawa da ga aljihunsa ya miƙa masa. Kallon kuɗin Smart yay da sake sakin murmushi mai ma’anoni da yawa sai kuma ya girgiza kansa. “A’a Alhaji nagode sosai. Amma bazan amsa ba, albashin da ake biyana ya wadatar dani ALLAH ya ƙara buɗi”. Mamaki matuƙa Daddy ya shiga, dan haka ya kalla Uncle Yousuf da tun shigowar Smart ɗin baice komai ba. Kafaɗa ya ɗage masa alamar haka yake. Ai Daddy kasa ƙara cewa komai ma yayi har Smart ya sake musu sallama ya fice abinsa…..

        ★★ *_8:25pm_* ★★

     Ƙarfe takwas da kusan rabi na dare tawagar Hon. Babale Nakowa da su Alhaji Baita suka isa gidan Alhaji Sufi Ado Garko kamar yanda suka tsara. Ziyara ce ta bazata, dan haka Alh. Sufi yay mamakin zuwan nasu duk da kuwa su dukansu sun kasance yaransa ne ta fannoni daban-daban kafin yau. Sai dai duk da kasancewar wannan zuwa nasu ya kasance na bazatan hakan bai hana su sami tarba ta mutuntawa ba. Bayan sun gaisa da Alh. Sufi cikin girmamawa a matsayinsa na _God Father_ nasu sai kuma hira ta ɓalle mafi ƙarfi akan kasuwanci da siyasa. Sun ɗan taɓa hira kafin Hon. Misau ya fara bayani akan abinda ya kawosu.

       “Ranka ya daɗe mufa zuwan nan namu kamar gaisuwa ce da roƙon iri. Munzo mu maka Barka da dawowa da kuma yaya jiki sai kuma babbar magana mai alaƙa da son ƙulla sabon zumincin da muka san kaima zakayi farin ciki da shi”.

    Cikin mamaki da dattijantaka Baba yay murmushinsu na manya idonsa akan Alhaji Misau. “Jeka maganarka kai tsaye Ɗan kande! kasan ni a koda yaushe nafi buƙatar abu abuɗe fiye da rufa-rufa”.

        “Hakane Baba”.

    Cewar Hon.. Misau cikin murmushi da sake gyara zama. Sai da ya ƙara juya zancen a ransa ta yanda zai fito da armashi sannan ya cigaba da faɗin, “Akwai wata yarinya a cikin zuri’arka da Alhaji Haruna ya gani ya kuma ji ta kwanta masa matuƙa a rai saboda nutsuwarta da hankalinta. Da farko mun shirya tunkarar mahaifinta sai kuma mukai tunanin ai baba ma da babansa. Shiyyasa muka dakata har sai yau daka dawo mukazo da ɗumi-ɗumi dan a tabbatar bada wasa muke ba”.

        Murmushin mai cike da jin daɗi Alhaji Sufi Garko ya saki tare da faɗin, “Kai kai Masha ALLAH. Masha ALLAH, naji daɗin hakan kuma zanayi matuƙar farin ciki saboda sani da naima Haruna a rayuwa da nagartarsa. Amma wace yarinya ce wanna haka?”.

     Yanzu kama Hon. Baita ne ya nisa shima da murmushin shinshino nasara akan fuskarsa ya ce, “Baba sunanta Mawaddat. Ƴar wajen Alhaji Isma’il Jiƙamshi. Kaga a gareku ku jikace.”

      “To to! Ko kaine dama yake faɗa mijin data fidda ɗin? Dan ɗazun dama muke magana akan ɗan wajen Sulaiman da aka taɓa son haɗa su sai abin bai yiwu ba da yake a lokacin ba matarsa bace.”

     Kallon juna sukai kowanne zuciyarsa kamar zata ɓallo ƙirji ta fito, sai kuma suka haɗa baki wajen faɗin, “Aiko bazai wuce hakan ba kam”.

      Duk da maganar ta ɗan yima Alhaji Sufi Garko gingirin a zuciya sai kuma hakan bai hanashi jin daɗi ba da nuna farin cikin sa. Dan haka babu wani kwalo-kwalo ko jan magana ya tabbatar musu suje gida insha ALLAHU zuwa gobe su dawo garesa da shirinsu bayan sallar azhar zasu samu amsa mai gamsarwa. Dan ya tabbatar musu duk da shi kaka ne ta ɓangaren mahaifiya yana da nasa ƙarfin ta wani fanin ma ubane shi ga mahaifin nata shima ai. Farin ciki iya farin ciki sun shiga, dan haka suka tafi da ƙwarin gwiwar samun nasara batare da sun sha wata wahala ba. Gefe ɗaya kuma suna dariyar muguntar kama Daddy a tafin hannunsa ta inda bai zato ba ko tsammani. Ko a mota hirar da suka dinga yi kenan cike da jin alfahari…..

       ★★ ……

      Tun bayan wucewar Uncle Yousuf da ya maida Mawaddat ɗakinta batare da ko ɗaya a cikin ƙannenta ya ganta ba shima ya shige nasa ɗakin ya kulle kansa dan samun damar yin isasshen tunani. Ƙarar wayarsa ce ta katse masa dogon lissafin da zuciyarsa tai nisa a yi. Jawota yay cikin jan ƙaramin tsaki zai kashe yaci karo da sunan _Baba garko._ Tashi yay zaune sosai, sai dai bai ɗaga ba har sai da ta yanke shi yay kiransa. Dan haka dama yake masa. Cikin girmamawa ya gaida ogan nasa kuma surukinsa. Da kulawa Baba ya amsa. Ta re da faɗin, “Isma’il ko ka fara barci ne na tasheka amin afuwa. Na kasa haɗiye abin farin cikin nan ne shiyyasa na nemeka yanzu ɗin. Ashe baƙon da kake maganar ɗazun na gida ne…..”

       “Baba baƙo kuma?”.

    “Eh baƙo mana Isma’il. Mai auren Mawaddat mana. Dan yanzu nan suka wuce su sarakan zumuɗin ma sun kasa haƙuri har sun kawo kansu. Ko kuma ja’irar ƴar taka ce ta turosu ma dan kasanta da gaggawa”.

    Sosai ƙirjin Daddy ke lugude. Duk da shi sam yama kasa fahimtar Baba ɗin yanda ya kamata. Kasa jurewa yay dai yace, “Baba kai min afuwa. Wlhy ban gane akan wa kake magana ba. Dan inada tabbacin Mawaddat bata turo kowa ba kasancewar ma ni bamu zauna magana ba dan na sameta kwance a gida ma kanta na ciwo tun bayan ɗakkoka airport”.

          “Tofa wata sabuwa kenan? Su Alhaji Baita ne fa suka sameni a daren nan kan wai Hon. Haruna Dauda Nakowa na son Mawaddat har ma sun dai-daita kansu kaima kuma kasan maganar ma. A yanzu haka ma na basu damar dawowa a gobe idan ALLAH ya kaimu da shirins…..”

     Cikin suɓutar baki Daddy ya furta, “What! Su Alh. Ɗan-kande Baita fa kace baba?”.

        “Eh ƙwarai su ɗin fa na faɗa Isma’il. Shin akwai matsala ne?”.

    Yawune ya nema sarƙe Daddy, da ƙyar ya iya figo glass cup ɗin ruwa dake a bed side drawer ya kwankwaɗa. “Baba ni wlhy bamma san akwai wata alaƙa tsakanin Mawaddat da su Alhaji Baita ba sam. Sannan kuma bana jin ita ɗince ma ta turosu. Dan yaron da take so ɗin wanine daban”.

         “Ikon ALLAH to mi hakan ke nufi?”. Cewar baba. Daddy da takaici da damuwa suka lulluɓe a lokaci guda ya ce, “Baba wlhy ban san manufa ko dalilinsu nayin duk hakan ba. Danni nasan Mawaddat bata da wani alaƙa da su”.

     “Uhhmm to kaga ina ganin mu ajiye maganar nan to. Amma ka tabbatar gobe idan ALLAH ya kaimu a  wajen taruwar meeting ɗin nan kazo min da Mawaddat, idan ma zai yiwu harda shi wanda take so ɗin”.

      Godiya Daddy yay masa. Yayinda tuni yay jagaf da zufa. Kamar wanda ya fito a wanka. Gaba ɗaya lissafinsa ya rushe shi yanzu ma baya gane komai ma. Wayar ya ɗauka yay kiran Uncle Yousuf. Ba’a ɗaga ba sai da tai gab da tsinkewa. Ko sauraren tambayar da Uncle Yousuf ɗin ke masa bai yiba. Sai ma katsesa yay da faɗin, “Yousef akwai matsala. Tabbas akwai matsala. Amma ka jirani ina zuwa gidanka ɗin yanzu”.

    “Haba-haba yaya da kanka. Inaga ka jirani kawai gani nan zuwa”.

    “Karka damu Yousuf kai dai ka jirani kawai. Nan ɗin zaifi sirri ”.

   Babu yanda Uncle Yousuf ya iya dole yabi umarnin nashi yay zaman jiransa. Mintinan da basu wace goma sha ba sai ga Daddy ya iso……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣5️⃣

…….A harabar gidan ya sami Uncle Yousuf ɗin tsaye da alama shi yake jira shima. Ciki suka shiga har falonsa. Tsaf daddy ya kwashe ya sanar masa da duk abinda surukinsa kuma ogansa ya kira shi yanzu nan. Karan farko shima Uncle Yousuf ya girgiza. Duk da sam bai gane ainahin manufar shiga Daddy a ruɗani ba. Kwantar masa da hankali Uncle Yousuf ya shiga ƙoƙarin yi, amma sai Daddy ya dakatar da faɗin, “Yousuf bamu da wani lokaci isashe. Minene mafita. Dan wlhy wlhy kaji na rantse maka. Suma da wata manufa sukaje ga baba, kuma lallai dole akwai wata a ƙasa …”

      “A ƙasa kamar ya?. Nifa yaya ƙara dilmiyar dani kake wlhy akan al’amarin nan, sannan ka fara bani tsoro. Dan ALLAH ka bani abuɗe mana ko zanfi sanin makamar riƙewa ta ƙwarai”.

         “Zan baka amma ba yanzu ba Yousuf. Yanzu hanyar kuɓutar da Mawaddat da mu kammu gaba ɗaya kawai ya kamata mu nema dan ALLAH. Idan ba haka ba komai zai canja da ga yanda muka sanshi zuwa a yanda bamuyi zato ko tsammaninsa ba. Miye mafita? Wa zamu kai matsayin miji ga Mawaddat? Dan fa dole ne mu samar da wannan mijin saboda Baba baya magana biyu. Sannan duk waɗan nan mutanen suna da tasirin da zai iya zartar da hukuncin basu Mawaddat ko ina so ko bana so musamman akan abinda ya faru a baya da kuma gargaɗi da sharaɗin daya shimfiɗa mata kan duk wanda yazo neman aurenta zai bashi kota yarda ko bata yarda ba”.

      “Hakane yaya, sai dai yanzu mu a ina zamu iya samo miji? Sai nake ga ya kamata itama Mawaddat ɗin mu tuntuɓeta ko?”.

         “Tuntuɓar tata yana da amfani, sai dai kuma zuciyata na raya min wani abu. Mizai hana mu jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya ne”.

    “Okay yaya kamar ya kenan?”.

“Yauwa abinda nake nufi anan itama mu barta a rufen kawai mu samar da mijin amma na bogi dan fatana kawai mu nunasa ga Baba dan abar zancen, ita kuma mu nuna mata hukuncinta kenan akan wannan halayyar tata, sai ta gama wajiguwa matuƙa sannan mu faɗa mata gaskiya mu kuma bata damar fidda mijin da take so. Amma yaya ka gani kai?”.

          Uncle Yousuf da shima ya gama tsara nasa tunanin tun fara maganar yayan nasa yay wani shegen murmushi da faɗin, “Tabbas hakan yayi, kuma ina ganin mutum ɗaya ne zai iya mana wannan aikin, sai dai maganar riƙe hakan matsayin hukunci gareta ko barazana bazai taɓa canja abinda muke fatan canjuwarsa ba da ga gareta. A halin da Mawaddat ke ciki canjata na nufin bin wasu matakai daki-daki dan tayi nisan da ƙyamatar ta ko mata hargagi bazai kasance hanyar gyarata ba”.

    “Na yarda da kai auta, shiyyasa akoda yaushe nake kasancewa a farin ciki da ƙwarin gwiwa idan kana a kusa da ni. Amma wanene shi ɗin?”.

       “Aliyu drivern ta Yaya”.

     Da sauri Daddy ya ce, “Haba Yousuf driver fa? Ina mudai samar da wani mai darajar da tafi tashi ko cikin yaran abokaina haka ko a cikin ma abokanka”.

          “Yaya kenan, amma karka manta fa cewa dai ba auren za’ai ba. Zamu samar da mijin ne kawai dan ai mata kurari sannan mu toshe waccan damuwar da aka kasa a teburin Baba. To indai hakane ai kuwa shi wannan da kake ganin bai kai ba ne dai-dai da wannan shirin namu. Amma waɗan can zasu iya zamar mana ƙarfen ƙafa, shi kaɗai ne makamin da zamu riƙe, inada yaƙinin zai taimake mu wajen yakin nan har muci nasara”.

       “Eh kuma fa haka ne gaskiya Yousuf na fahimceka kuma. Yanzu minene mafita?”.

        “Karka damu bar komai a hannuna. Kai dai ka zama cikin shiri kawai itama Mawaddat ɗin ka barni da ita, ka koma kawai gefe ka zama ɗan kallo”.

     Sosai daddy yaji nutsuwa da kwanciyar hankali. Yanata jerama ɗan ƙanin nasa addu’a da fatan gamawa lafiya kafin su ɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama ya tafi. Uncle Yousuf ɗin ne dai yay masa rakkiya kusan har gida. Dan sai da ya ga shigarsa sannan ya juya ya koma yanata sakin murmushinsa da shi jaɗai ya san dalilin kayansa sai kuma UBANGIJI da ke kallon dukkanin motsin zuciyarsa. Koda ya koma gidan maimakon kwanciya sai yay alwala ya nutsu wajen miƙa kukansa da buƙatar neman zaɓin alkairi ga abinda yake ƙudirtawar duk da ba yau ne dama ya fara irin wannan addu’a ɗin ba……

     Tofa Uncle You mi kake ƙullawa haka kaima😂🥱?.

        ★….★

    A washe gari data kasance safiyar alhamis a duka ɓangarorin huɗu kowa ya tashi da shirinsa game da abinda ya kwana da shi a rai. Ɓangaren su Hon. HD. Nakowa sun shirya tsaf da shirin zuwa neman auren Mawaddat a wajen Alhaji Sufi Ado Garko kamar yanda ya basu dama. Haka ma a ɓangaren Alh. Sulaiman da ɗansa sun gama tsara komai a daren jiya domin cikar burinsa da kuma burin ɗansa Tajuddeen da ke ƙaunar Mawaddat har cikin zuciyarsa. Ɓangare na uku shine MM Atik Kumo da shima ya tunkari iyayensa da maganar samo mata da yay, sai dai ya gagara tunkararta yana son iyayen nasa su fara zuwa masa neman izinin nemanta ga nata iyayen. Sosai mahaifinsa da Mom ɗinsa suka shiga matuƙar farin ciki, dan babban burinsu dai a rayuwa shine suga auren ɗan nasu daman. Sun samu wannan damar kam bazasuyi sakaci da itaba, musamman ma da sukaji yarinyar ta fito ne da ga zuri’ar Alhaji Sufi Ado Garko da duk wani ɗan siyasa a jihar Kano ke masa kallon uba. Hakama ƴan kasuwa domin a duk ɓangarorin biyu yana taka rawar gani da tarihi bazai iya mantawa da shi ba ko bayan ransa. Rukuni na gaba sune gidan allurar da kowa ke iyo cikin ƙaton kogin domin nema, wato _Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi_.

       Mawaddat da tun a daren jiya ta dawo cikin hayyacinta sam bata san duk wannan babban yaƙin basasa da ake shiri a ɓangarori uku domin ita kaɗai ba. Hasalima ita ta wayi gari ne da babban shiri akan mijin matar nan da yay ma yarinya fyaɗe. Har yanzu yarinyar na asibiti cikin mawuyacin hali. Da farko ta hana ƴan jarida yayata zancen har sai ta kama shegen, sai dai a yau wani tunani datai yasa zata bama ƴan jarida damar fitar da komai, tana ganin hakan zai taimaka musu wajen kamashin. Yau da wuri ta kammala shirinta cikin wandon jeans dark blue da milk color ɗin riga. Rigar nada ɗan tsaho musamman ta baya. Ƙaramin veil ta naɗa a kanta tare da bulbula ƙamshin nan nata. Cikin takunta na yanga da izza ta fito, babu alamar jama’ar gidan wani ya tashi, sai su Iya Tabawa dake ta aikin gyaran gidan. Gaisheta suka shigayi cikin girmamawa. Hannu ta ɗaga musu sau ɗaya tai ficewarta dan bata cikin mood ɗin yin magana yau. Karo suka kusan ci da Uncle Yousuf da ke ƙoƙarin shigowa a main falour. Tai saurin komawa baya da faɗin “Sorry Papa ban san ka taho ba”.

       “Ina zaki haka?”.

   Ya faɗa a dake maimakon amsa maganarta ta farko. Ɗan kallonsa tai da mamaki, sai dai ganin yanda shima ke kallonta babu alamar wasa a tattare da shi ya sata maida kanta ƙasa cikin tsarguwa, dan dama dauriya take kawai, amma tun a daren jiya take ƙullawa da kwancewar ta yanda zata iya haɗa ido da shi, da kuma yanda zata shukama drivern ta rashin mutunci a wannan karon tunda har ya sake bari Uncle Yousuf ɗin ya ganta a cikin wannan yanayin…..

      “Baki ji bane? Ina zaki je?”.

  Ya sake faɗa cikin katse mata tunani. Firgigit ta dawo hankalinta. Cikin in ina ta ce, “Uncle You office, amma zan fara zuwa nai magana da ƴan jarida akan case ɗin yarinyar nan shiyyasa zan fita da wuri”.

     “Shi kuma naki case ɗin kiyi yaya da shi?”.

    Da sauri ta ɗago ta dubesa. “Uncle case ɗina kuma? Ni ai babu abinda ya faru da ni”.

           “Zai farun ne ai. Biyoni”.

       Kamar wadda aka bugama guduma a kai haka Lulu ta tsinta kanta a wannan lokacin. Sai dai bata da zaɓin da ya wuce bin bayan nasa kamar yanda ya bata umarni. Duk abinda ke faruwa Daddy na kallonsu da jinsu. Ya haɗiye hawayen da ke neman zubo masa. A daren jiya ko sau ɗaya baiyi barci ba, sosai jininsa ya hau har bugun zuciyarsa ya fara canjawa. Sai da Mommy ta bashi shawarar yin karatun Alkur’ani sannan ya samu ƴar nutsuwar ganin wayewar gari lafiya. Mommy dai bata san ainahin mike faruwa ba. Amma zuciyarta na bata akan Mawaddat ne, dan a yanzu babu wata damuwa da ke neman kai mijin nata ƙasa sama da al’amarin yarinyar, bayan kuma tun farko shine yay shukar datai tsirran da ya samar da ita a haka.

       A falon baƙi da ke a garden kam babu abinda zuciyar Lulu keyi sai bugawa da sauri-sauri. Ga Uncle Yousuf yay matuƙar ɗaure fuska ta yanda bata taɓa gani da ga garesa ba. Zama tai jiki babu ƙari da faɗin, “Uncle gani”.

        “Na ganki ai”.

      Ya bata amsa shima kai tsaye yana gyara zama. Tambayar da tai matuƙar girgiza mata zuciya ya jefa mata. Babu shiri ta ɗago a firgice ta dubesa. Sake maimaitawa yay babu alamar wasa a tare da shi. “Nace wanene Hon. Haruna Dauda Nakowa a gareki? Miye alaƙarku?”.

    “B…b…bamu da wata alaƙa wlhy Uncle”. Ta faɗa cikin in ina da firgici.

         “Amma yaje neman aurenki ga Baba a daren jiya”.

    “What!! Uncle You aure fa? Ni kuma Mawaddat?!”.

           Cikin sigar harara Uncle Yousuf ya bata amsa da “K ɗin fa, bayan shi kuma Tajuddeen ma ya dawo. Dan a jiya mahaifinsa a gabanmu ya sake gabatar da zancen ku ga Baba. Nasan kuma baki manta da alwashi  Baba ba na cewar duk wanda yazo neman aurenki ko da amincewarki ko babu ko da tamu ko babu zai aura masa ke. Kinga hakan na nufin a cikin biyun nan dole ne ki zaɓi ɗaya”.

        “Wlhy Uncle You bana son kowa a cikinsu. Kuma shi tsinanne Haruna ɗin nan ni ban taɓa magana da shi ba ma balle maganar aure na rantse maka Uncle”.

     “Ni wannan ba matsalata bace Mawaddat. Dan a yanzu haka ma Baba nacan na zaman jiranmu ni da ke da Yaya akan wannan maganar dan haka ma na dakatar da ke daga fita. Idan kuma kina da wanda kike so sai ki faɗa mana yanzu mu nemosa aje da shi gaban Baba ki kuɓutar da kanki, dan hakanne kawai zai hana Baba bama ɗaya da ga cikin waɗan can ɗin aurenki kamar yanda kika san shi baya magana biyu”………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣6️⃣

……..“Na shiga uku Uncle, ni ban shirya yin aure ba wlhy. Dan ALLAH ka faɗa mini ya zanyi?”.

    “To ni Mawaddat taya zan san ya zakiyi. Yanzun ma na faɗa miki ne dan bana son a miki abinda nasan baki so. Dan Baba bazai taɓa canja ra’ayinsa ba a wannan karon kin sani na sani. Ga kuma Yaya wajen ƙoƙarin ganin ya kare ki sai ya sake wata ɓaranɓaramar wai kina da wanda kike so”.

        Fuska ta kuma kwaɓewa idanunta na cika da ƙwalla. “Uncle You wlhy guduwa zanyi”.

    “Guduwa kuma? A ganinki itace mafita Mawaddat?. To ai ina ganin dan kin gudu kinyi a banza, dan in dai Baba ne zai aurar da ke ɗin babu fashi ya kuma saka mijin taddaki har inda kika je ɗin ko shi yaje da kansa ya dawo da ke ya danƙama mijin. Kinga anyi ba’aiba kenan ko. Ni dai ina ganin kawai mu ɗauki kariyar da Yaya ya baki muyi amfani da ita dan ki kuɓuta gaba ɗaya”.

          “Uncle wacce kenan?”.

    “Samo wani matsayin wanda kike so kuma zaki aura. Sai dai ni da ke ne kawai muka san ba haka bane, bayan ƙura ta lafa shike nan sai ki cigaba da sabgarki, idan Baba yayi magana muce iyayen yaron muke jira dan sunce a ɗan jinkirta musu zai ƙarasa gininsa ko dai mu samo wani abu  da zai ɗauke hankalin Baba da ga kanki gaba ɗaya”

      “Hakan yayi, to amma Uncle kasan fa baba da shegen bin ƙwaƙwƙwafin abu idan kuma ya gano fa?. Sannan ma wa zamu iya samu ya mana wannan aikin batare da an samu wata matsala ba?”.

            “Eh kuma fa kema kinzo da maganar dubawa gaskiya. Dan Baba kam zai ma iya sawa ai masa bincike. To amma ina ganin mizai hana shi wanda zamu samar ɗin kawai ki yarda kuyi auren contract da shi, komai mune zamu tsara masa ayi auren amma bayan wata ɗaya ya rabu da ke, sai dai da sharaɗin kada kowa ma yasan ya sake ki har sai bayan wasu shekaru.”

      Shiru Lulu tai tana auna zancen Uncle ɗin nata. Sai dai da ace tana da ilimin addini da ya kamata tai hasashen yin hakan fa zai iya zama kamar ta zurma kanta ne. Amma a maimakon hakan ita wani tunani take da ban, dan tana ƙiyasta faruwar al’amarin ne cikin sauƙi kasancewar a inda ta girma cikin turawa wannan ba komai bane yin auren yarjejeniya.. ganin yanda tai nisa Uncle Yousuf ya katseta da faɗin, “Mawaddat bamu da wani isashen lokacin dogon tunani a yanzun fa”. Firgigit ta dawo hankalinta, sai kuma ta langaɓe kai cikin shagwaɓa. “Uncle You ni gaba ɗaya ma kaina ya kulle ne, dan ban san inda zan samo wanda zamuyi hakan ba”.

         “To mizai hana ki yarda da batun Tajuddeen kawai, yaron nan yanada hankali da nutsuwa ga ilimi. Yana aikinsa sannan yana matuƙar sonki”.

    “Uncle wlhy ni bana son sa, na tabbatar kuma bazan taɓa son shi ba. ALLAH idan aka matsamin kan na auresa zan iya halakash….”

        “No! no! Kar na sake jin haka. Tunda har baki sonshi shike nan kawai abar maganarsa. Mu koma kan maganar mu kawai ta nemo wanda zai zame mana makamin kuɓuta da ga Baba.”

     “Uncle bazan ɓoye maka ba wlhy na tsani duk wani abinda zai haɗa mu’mulata da wani namiji bayan ku, balle ma ace mu kasance wai ma’aurata. Impossible hakan ya kasance dan bazan taɓa aure ba.”

        Har cikin rai kalmar (Bazan taɓa aure ba) ta daki Uncle Yousuf, dan a karo na farko zuciyarsa ta fara hasaso masa wani al’amari mai girma dangane da Mawaddat ɗin. Dolene akwai abinda ya kamata su sani da ke ɓoye a ƙasan zuciyarta, sanin kuma na nufin haƙurin bin matakan daya dace. Wannan tunanin ya sashi cigaba da faɗin, “Mizai hana muyi amfani da Aliyu, dan yaron nada nutsuwar da bazai taɓa iya bamu ciwon kai ba koda anan gaba”.

       “Aliyu kuma? Waye shi?”.

     *_“DRIVERN KI”_*

  Fitar kalmar da ga bakinsa da zaburowar zuciyarta tamkar ragabzane a tsakanin jirgi da jirgi a sararin samaniya. Badan Uncle You bane, da bayan zaburar da tai abinda zai biyo baya shine lailayo masa zagi mai kawuna bakwai ta dire masa shi a tsaye sannan ta tisa da wanke fuskarsa da marin da sai ya hango yanda yaƙin duniya na uku zai kasance tun kafin lokacin faruwarsa. Sai dai kash furucin ya fito da ga bakin da ko harara bazata iya binsa da ita ba balle ɗaukar mataki. Uncle Yousuf da ya zuba mata idanu, sai dai a ƙasan ransa dariya ce ke cinsa yana dannewa da ƙyar yay mata nuni da kujera, tare da faɗin, “Sit mana kika wani zabura kamar wadda na faɗama mummunar magana. Nifa ba nace dole bane, shawarace kawai dan neman mafita. Amma idan batai miki ba muje kawai dan lokaci ma ya cika gashi ana jirana a office. Kije ki zama cikin shiri da yin sabon tunani akan wani tunda naga baki aminta da zancen shi Aliyu ba”.

       Bakin data tura gaba ta buɗe zatai magana sallamar Daddy ta dakatar da ita. Alamar zip Uncle Yousuf yay mata wai kar Daddy yaji. Daddy da gaba ɗaya ya gama jin tattaunawar tasu dan tun ɗazun a laɓe yake dama sai ya sake fuskewa cikin pretending ya ce, “Wai mi ake tattaunawa ne kuka shige haka shiru?”.

        Cikin ɗan ɗage kafaɗa Uncle Yousuf ya bashi amsa da “Sirri ne tsakanin baba da ƴarsa yaya”.

     Dariya Daddy yayi, sai kuma ya juya hanyar fita yana faɗin, “Oh to bari nayi nan tunda ba’a buƙatar naji”.

      A karan farko Lulu tai dariya tana mai kamo hannun Daddyn nata cike da shagwaɓa. A haka suka fito suna ƴar dariya…..

      Fitowarsu tayi dai-dai da shigowarsa gidan. Kamar ko yaushe sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsar jikinsa. Ƴar ramar da yay ta ciwo ta sashi zama wani fayau da shi a idon mai kallo. Cikin girmama juna ya gaisa da su baba maigadi sannan ya ƙaraso inda suke tsaye. Anan ɗin ma da girmamawa ya gaisa da Daddy da Uncle Yousuf. Lulu da ke gefensu tana danna waya tai jiran jin ya gaisheta amma sai taji shiru. Karo na farko ta ɗago idanunta ta kallesa tana mai sake tsuke fuska. Ƙoƙarin barin ma wajen yake alamar ita bazai gaisheta ba kenan. Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki ne da takaici ya shaƙure mata wuya har taji tama kasa yin magana, sai dai yanda take binsa da wani mugun kallo ya sa Daddy farga da ita. Ya kuma fahimci miya fusatata ɗin.

      “Aliyu!”.

  Yay kiran sunan Smart da ke ƙoƙarin komawa inda su baba maigadi suke. Cikin girmamawa ya amsa yana mai juyowa garesu. Uncle Yousuf da ya sha jinjin jikinsa da tunanin ɓaranɓaramar da Yayan nasa ke shirin yine yay saurin faɗin “Am yaya inaga muje na ajiyekan tunda malam Zaidun bai dawo ba, in yaso daga can sai ya sameka Office ɗin. Aliyu zuwa 1:30 ku samemu a Nasarawa G.R.A please karku makara”.

        “In sha ALLAH Alhaji”.

     Smart ya faɗa cikin gyaɗa kai abubuwa da yawa na masa kai kawo a rai musamman da Uncle Yousuf ɗin ya ambaci Nasarawa G.R.A. Huci ya ɗan furzar kaɗan, a yanzun ma dai bai kalla inda taken ba ya nufi motar da mai wanki keta faman gogewa alamar ita zasu shiga. Baya ya buɗe mata, batare da ya jira tazo ta shiga ba ya koma mazaunin driver ya shiga yana karanto addu’ar shiga abin hawa. Harta ƙudiri aniyar ƙin shiga, sai kuma mita tuna oho mata ta tako cike da yauƙin nan nata da yanga ta shiga. Mai wanki ya maida motar ya rufe yana jera mata addu’ar dawowa lafiya. Motar yaja suka fice, zuciyarsa cike taf da abubuwan da suka faru jiya a waya tsakaninsa da Uncle Yousuf….

       A daren jiya bayan ajiye motar Mawaddat da ya kai sakatariyarta Zainab gida shima gida ya koma abinsa. Kai tsaye wajen Abba ya nufa suka gaisa, sun ɗan taɓa hira da Abban sai dai hirar batai masa daɗi ba sosai kasancewar da ga maganar Hawwah ta juye maganar aurensa. Sosai Abba ya dinga zuba masa faɗa akan infa har bai nemo matar aure ba a cikin watannan tofa shi zai nemo masa da kansa duk da ba aƙidarsa bace yima ƴaƴansa auren dole. Haƙuri shi dai yayta bashi da tabbatar masa cewa in sha ALLAHU zai kawo matar auren nan kusa. Kamar Abba ya gamsu da hakan sai kuma shigowar Umma ta sake saka Abban hayewa sama. Dan kamar wadda dama take a laɓe tana saurarensu tana shigowa sai kawai ta shiga assasa wutar kan cewar shi dai baiyi niyyar yin auren bane kawai. Inba haka ba baga yarinyar maƙwaftansu ba nan Nazifa yarinyar na matuƙar sonshi amma yaƙi saurarenta. Kallonta yay da mamaki, dan kowa dai yasan wacece Nazifa a anguwar. Yarinya ce mara jin magana dan tsabar bleaching fuskarta har yellow takeyi. Tabbas Nazifa ta jima tana nuna masa soyayya, sai dai shi bai taɓa nuna yasan mi takeyi ba. Kai shi ko magana tai masa ma da ga gaisuwa bai sake kulata. Wannan halin watsar da ita ɗin da yake yi yasa tun tana juriyar bibiyarsa har tai fushi ta daina kulashi. Amma da har abubuwa take saye ta aikoma Ammah ko ta bama su Asma’u. Nan ɗin ma dai bata samu nasarar ba dan Ammah tace ita babu ruwanta, idan yaga zai aureta bazata hana ba, za kuma ta bisu da addu’a dan koba komai yayi jihadin raba Nazifa da rayuwar banza da kowa ya shaida tanayi. Yanajin Ammah ta bada goyon baya ya samu Nazifa yay mata gargaɗi na ƙarshen ƙarni ya kuma yima Yayanta magana akan ta fita sabgarsa, shi kuma Yayan yaji haushi ya gaggaya masa magana  bai kulashi ba shi dai dan ya yanke magana. Da ga ranar bai san miya faru ba bai sake ganin Nazifa ba. Amma shine dan tsabar sharri Umma ke tisa zancen a yanzu bayan shekara kusan uku kenan da ajiyesa gefe. Tuni Abba ya ƙara tujaresa da faɗa amma baice komai ba akan Nazifa, hasalima ya fahimci kamar faɗan nasa na son zama zargi ne ko minene bai dai fahimta ba. Jiki a sanyaye ya baro wajen Abba, ɗakinsa ya nufa dan bai buƙatar zuwama Amma a wannan yanayin. Ya gama cire kayansa kenan zai shiga wanka kira ya shigo masa. Yayi mamakin ganin Uncle Yousuf, sai da ya kalli agogo ƙarfe kusan sha ɗaya da rabi fa. Haka dai ya daure ya ɗaga cikin taraddadi………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣7️⃣

……..“Alhaji badai wata matsala bace ba ko?”. Ya faɗa maimakon sallama da Uncle Yousuf ɗin yay masa. Murmushi da ga can Uncle Yousuf ya saki tare da gyara zamansa a kujerar falon da ya fito. “Babu komai sai alkairi Aliyu. Wata magana ce mai muhimmanci tasa na kiraka. Ina dai fatan baka kwanta ba na tasheka ko?”.

      “Ina dai shirin kwanciyar ne Alhaji. Amma dai lafiya?”.

    “Eh lafiya kamar yanda na sanar makan”.

    “To Alhamdullahi Alhaji, ina saurarenka”.

   Ɗan jimmm Uncle Yousuf yay kafin ya furzar da huci kaɗan. “Aliyu shawara nake nema a wajen ka”. Cike da mamaki ya amsa da, “Alhaji shawara? Sannan kuma ma a wajena?”.

          “Eh Aliyu. Kuma ina fatan zaka bani wadda zata fiddani da ga ruɗanin da nake ciki” bai jira cewarsaba ba ya cigaba da faɗin. “Kasan na faɗa maka an taɓa sakama Mawaddat rana da Tajuddeen ai. Amma ALLAH baiyi auren nasu ba wasu matsaloli suka gitta, mafi yawansu da ga Mawaddat ne sai dai kuma akwai ɓoyayyen sirrin saɓani a tsakanin Yaya da mahaifin Tajuddeen da shima ya taka rawar gani. So an share maganar aure kowa ya haƙura, sai dai kakanta na ɓangaren mahaifiyarta Alhaji Sufi Ado Garko ya ɗauki alwashin duk randa wani yazo domin neman aurenta koda yardarta ko babu zai amince masa ya aurar da ita. Wauta ya sata amincewa. Bayan nan magana bata ƙara tashi ba sai a yau ɗin nan a gaban Alhaji Sufi ɗin, shi Alhaji Sulaiman ya sake kawo maganar, amma Yaya yayi saurin cewar ai Mawaddat nada wanda take so………” Tsaf ya kwashe komai ya sanar masa har zancen su Hon. HD Nakowa da Daddy ya sanar masa suma sunje bayan barowarsu. Hakan ya matuƙar bashi mamaki dan tuna abinda ya faru a tsakanin Mawaddat ɗin da su Hon. HD Nakowa. Cikin kasa daure abinda ke bakinsa ya ce, “To amma Alhaji naga kamar ita da shi Honorable ɗin sam basa shan inuwa ɗaya. Taya zaije yace yana sonta da aure?”.

       “Muma shine abinda ya ɗaure mana kai Aliyu. Shiyyasa muka kasa zaune muka kasa tsaye akan al’amurin, dan Hon. Nakowa nada ƙarfi sosai a wajen Baba, saboda yaronsa ne, hasalima shine ya zame masa kamar wani ƙashin baya a harkar siyasa.”

     “To amma Alhaji mizai hana ku sasanta shi Alhaji Babba da mahaifin shi Tajuddeen ku aura musu juna kawai a wuce wajen”.

          “Hakan bazai yiwuba Aliyu. Dan ita Mawaddat sam bata son Tajuddeen, ta tabbatar min idan aka aura mata shi komai zai iya faruwa. Sannan abinda ke tsakanin yaya da mahaifin Tajuddeen abune babba bawai yanda kake zaton zai sasantu cikin sauƙi bane. Kaga ko maganin ayi zumunci ya wargatse ai Gara kar a fara ko”.

      “Hakane kuma Alhaji”.

   “To Miye mafita Aliyu? Dan Baba fa sam baya magana biyu. In har gobe idan ALLAH ya kaimu Mawaddat bataje da wanda take son aura ba babu fashi cikin biyu dole ayi ɗaya. Shiyyasa ma na kiraka domin neman taimako. Ina son idan ban shiga huruminka ba dan ALLAH Mawaddat ta nunaka a matsayin kai ne zaɓinta, da zaran Baba ya yarda a wajen shikenan. Ni kuma zanyi ƙoƙarin ganin ta fidda miji kafin Baba ya sake magana”.

         “Ni kuma Alhaji?!!”.

      “Eh dan ALLAH Aliyu ka taimakemu. A yanda rayuwar Mawaddat take yanzu muna buƙatar nutsuwa kafin sama mata mijin da zai saita mata rayuwa. Ni kaina bazan so ta auri Tajuddeen ba duk da nasan mutumin kirki ne amma bazai iya control ɗin ta yanda yake so ko ya kamata ba. Sannan Hon. HD Nakowa, kai ne shedar a inda ka gansu tare, maimakon gyaruwar Mawaddat aurenta da shi sai dai ya ƙarasa lalata ta kawai, shi kuma Baba duk bai san waɗan nan halayyar ba. Amma kaga idan muka kuɓutar da ita a wannan gaɓar sannu a hankali sai irin mijin da muke fata ya samu, kai kawai ta nunakan a gobe shine kawai dan Baba ya aminta ya bar waɗan can ɗin. Amma na baka damar kayi tunani, sai dai bamu da isashen lokaci daren yau ne kawai……

         “Wai kai malam ba magana nake da kai ba! Tsabar baka san muhimmancin rayuwa ba kana driving kana ma mutane tunaninka na iska!!”.

    Firgigit ya dawo hayyacinsa tamkar wanda aka tada a barci. Sam bai san tunanin nasa har yayi zurfi irin haka ba. Gefen titi ya gangara a hankali tare da kai hannunsa saman goshi ya dafe yana mai furzar da iska. Gaba ɗaya ma ba hanyar da ya kamata yabi da su yabi ɗin ba tsabar hankalinsa bama a tuƙin yake ba gaba ɗaya. Karan farko a rayuwarsa da tunda ya fara aiki matsayin driver ɗinta ya furta mata “Am sorry”. Cikin tausasa harshe kuma. Cak numfashin Lulu ya nema tsayawa a ƙirjinta. Haka ma maganar bakinta kasa ƙarasa fita tai tsabar kalmar ban haƙurin tazo mata a matuƙar bazatar da bata taɓa tunanin hakan da ga bakinsa ba kasancewar kallon da take masa mai shegen girman kai. Har ya sake tada motar da juyawa bata iya sake yin ko tari ba kamar wadda aka ɗinke ma lips. A nashi ɓangaren bai kawo komai game da shirun nata ba, a tunaninsa maganar Uncle Yousuf ce ta jiya ke damunta kamar yanda shima da ya kasance ɗan karoro kawai a ciki take neman jefa shi a ɗimuwa. Har suka isa office babu wanda ya sake magana. Kafin kuma ya fita ya buɗe mata har ta buɗe ta fice. Kallo ya ɗan bita da shi, dan duk da yau ma dai irin kayan daya tsani gani a jikin mace tana yawo kan titi ne a jikinta ɗan zoɓawar rigar da ga baya ya taimaka wajen suturta wani ɓangare na jikin nata. Janyewa yay tare da furzar da huci. Dai-dai nan Zainab ta fito ɗaukar mata kaya dan babu abinda ta ɗauka tai shigewarta. Ganinsa ya saka Zainab yin murmushi, ta risina cikin girmamawa ta ce, “Yaya ina kwana”. Kalmar yaya da ta kirashi da shi ce ta sakashi maida mata da murtanin murmushin nata itama. Cike da kulawa ya amsa mata kuma. Handbag ɗin Lulu da laptop da riga ta ɗauka sai wasu tarkacen takardu, shi kuma ya fito a motar tare da kulleta ya nufi security ɗin nan na jiya dan su gaisa…..

        Duk yanda Lulu ta so fuskantar aikin gabanta hakan ya gagara. Abubuwa ne da yawa ke cizon zuciyarta musamman shawarar Uncle You da yace ta nuna drivern ta matsayin wanda take so a gaban Grandpa ɗinta. Kai ina a gareta wannan ai ƙasƙanci ne ma, kenan ma ya samu hanyar cigaba da kawo mata raini fiye da wanda yake son gwada mata a yanzu, dan ma dai ita tsayayya ce yana shakkarta. Kai maganar gaskiya shawaran nan na Uncle You baiyi ba sam. To amma a yanda guri ya ƙure ɗin nan idan ba shi ba wa zasu samo yay musu aikin batare da an samu matsala ba?. Wannan tambayar ita ta shiga cizon zuciyarta tama kasa iya aiwatar da komai na gabanta. Tana buƙatar shawara, gashi ƙawarta kuma Nadiya ce kawai da har take iya faɗama damuwarta. Kai ina bazata kira Nadiya ba, dan sai ta koya mata hankali. Kai anya ma bada saninta wannan tsohon kwandon Hon. Nakowa yazo neman aurenta ba? Lallai akwai lauje cikin naɗi, dan zuwa yanzu ta fara shakkar al’amarin Nadiya, ita shiyyasa fa bata ƙawa musamman da ya zam ƙawaye sun taka rawar gani suma wajen bar mata wani tabo a zuciya da har yanzu gyambonsa ke kan yin ruwa da mata ciwo. Kodai Uncle Yousuf zata kira ne tace ta fasa a nema wani? Aminta da wannan shawarar ya sata kiransa.

        “Lafiya dai ko Daughter!”.

    “Uncle you ba lafiya ba, shawaran nan ne yaƙi zama a zuciyata. Kodai mu nema wani can daban yay mana aikin nan, kasan fa bana son raini”. Murmushi yay da ga can har tana iya jiyo sautinsa. “Mawaddatan’warahma!”. A hankali ta amsa da “Da yes papa”. Dan tana matuƙar son ya kirata hakan.

       “Ki kwantar da hankalinki Please, sannan ku tuna bamu da wani isashen lokaci, a yanzu haka fa awowi kaɗanne suka rage mana dan za’ai amfani da ɗan break na lokacin sallah ne wajen zaman meeting ɗin kafin kowa ya koma office. A tunaninki a irin wannan tsukun lokacin wa zamu samu mai amana da hankali kamar Aliyu da zai mana aikin nan batare da wata matsala ba? Ko kina son mu ɗakko wanda zai mana baragada har Baba ya gane ya zartar miki da hukuncin auren ɗaya da ga cikin waɗan da baƙya son?”.

        “A’a Uncle You… ALLAH idan yace sai na auri wani a cikinsu zaku iya rasani dan na tsane su”.

      “To mafita ɗaya ce ta kufce musu shine bin abinda muka tsara. Shin kin san da yaya ma shi Aliyun ya amince zai mana aikin? Da ƙyar fa na iya shawo kansa wlhy”.

          A zuciyarta ta ce (kuji ɗan iya, dama ya samu aka sakashi zai wani kawowa mutane iyayi. Mtsowww banda ma dai wannan Grandpa ɗin da matsalarsa shi ko’a mafarki ya isa ma na kallesa balle wani kalman so can na wofi. Bari ana gama zaman nan korarsa zanyi dan karma ya ɗauka ya samu wata damar kawo min raini…..)

       “Hello Mawaddat! Kina jina kuwa?”.

   Ajiyar zuciyar dawowar hayyaci ta saki, cikin shagwaɓa ta ce, “Shike nan Uncle sai mun haɗu”.

       Dariya yay sosai daga can bayan ya katse kiran. Dan harga ALLAH dariya suke bashi. Dama yanzu ya gama waya da Smart ɗin shima. Haka kawai sun sakashi komawa lauyan dole. Ya tsara wannan ya tsara wannan. ALLAH dai ya bashi nasara burinsa ya cika akan abinda ke ransa game da su su duka biyun……..✍️

     🥱Ba abun faɗa.

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣8️⃣

…….Ƙarfe ɗaya da minti biyar ta fito da ga office saboda kiran da Uncle Yousuf yay mata da gargaɗin karfa su makara. Kamar ko yaushe babu kwalliya a fuskar tata, sai dai an toshe idanu da glass. Tabbas glasses na mata matuƙar ƙyau shiyyasa da wahala ka ganta babu shi, gashi bata saka ƙarami sai in zatayi aiki. Duk irin manyan nan ne na manyan mata masu ji da gayu. Shima ɗin dai kiran Uncle Yousuf ɗin ne ya sashi dawowa, dan tun kusan sha biyu ya wuce gida. Yanzu kam ya canja kayansa zuwa shadda ash color da tai masa matuƙar ƙyawun da har ita sai da ta saci kallonsa irin wanda bata taɓa yi ba. Dan tunda ya fara tuƙata bata taɓa ganinsa da manyan kaya ba sai yau har da su hula. Gaba ɗaya sai ya sake mata wani kwarjini da cika waje, dan haka ta sake jan girma tai tamau da fuska tare da ɗauke kai sama kamar bata gansa ba. Ita a dole kar waccan maganar tasa ya kawo mata wargi tunda Uncle Yousuf ya tabbatar mata ya sanar masa. Shima ɗin dai tasa fuskar a ɗauren take, dan baya son ta taresa da wata maganar banza, ta wani ɓangaren kuma ransa ne a ɓace, dan zuwa gidan nan da yay ya samu Umma na tujara harda yima Ammah gori akan ƙaddararsa wai a bincike wannan ƙin auren nasa sai dai idan yana samun abinda auren ne kawai zai iya bashi a bayan fage. Kenan tana nufin shi ɗin mazinaci ne. Bai san miya kawo rikicin ba, bai kuma shiga gidan ba yaji ba’asi tunda muryar Umman kawai yake ji, dama kuma yasan Ammah bazata tanka mata ba. Ganin Lulu ta dogare tana wani huhhura hanci irin na ubangida da yaronsa ne sashi jan ƙaramin tsaki ciki-ciki, batare da yace komai ba ya buɗe mata ƙofar, shiga tai fuska a yamutse, shi dai baibi takanta ba ya maida ya rufe sannan ya koma mazaunin driver.

       A hankali yake murza steering Lokaci-lokaci yana ɗan furzar da iskar takaicin kalaman Umma da sukai masa kane-kane a zuciya. Yayi nadamar zuwa gidan nan ma….

     Kusan lokaci guda suka iso da su Daddy, dan haka Uncle Yousuf ya dakatar da shi a gate, fita yay a tasu motar yazo inda suke. Lulu da keta ɓata fuskar shagwaɓa ya kalla. “Mawaddat ya haka kuma? Maza koma gaba karma wani ya ganki”. Zatai magana yay mata nunin tai shiru kawai ta koma. Fitowa tai baki a sama ta koma gaban, kusan a tare ƙamshin turaren junansu ya daki hancinansu duk da dama tun ɗazun suke shaƙar. Shi dai baice komai ba, hakama Uncle Yousuf ya koma tasu motar shima, sun samu ƙaton compound ɗin gidan cike da motoci, ya dai samu gefe yay parking. Hango Uncle ɗinta Khamil na Abuja ya sata sakin murmushi, cike da zumuɗi ta buɗe motar ta fita…. Baki ya taɓe tare da ɗauke kansa. Sai ma ya lumshe idanunsa kamar mai shirin barci tare da kwantar da bayansa a jikin kujerar yay luf…

      Suna shiga aka fara taron dan kamar sune dama na ƙarshen zuwa. Ana tsaka da tattauna batun Tajuddeen ɗin da Lulu da aka kira amma ta botse musu akan ita fa bata son Tajuddeen, shi ko ya marairaice fuska kamar zai fashe da kuka yanata faman mata alamar roƙo amma tai kamar bata gansa ba. Takaici ya saka Alh. Sulaiman fara zagin Mawaddat ɗin, ana hakan saƙon isowar su Hon. Nakowa ya iso falon. Damar shigowa Baba ya basu. Su ukune kamar dai jiya. Shi mai gayya mai aikin Hon. HD Nakowa da aminansa Hon. Misau da Alh. Baita. Bayan anyi gaisuwar mutunci tsakaninsu da su duk da Alh. Sulaiman yayi mamakin ganinsu a gidan nasu Baba ya gabatar da su da dalilin zuwansu cikin meeting ɗin tare da buƙatarsu. Shiru falon yay kamar waɗanda ruwa ya cinye. Sai Lulu ce ke antayama Hon. Nakowa harara tamkar idanunta zasu zubo ƙasa. Cikin katseta Baba ya kirayi sunanta. Amsawa tai tana ƙoƙarin danne fushinta. Baba da ya gama lura da duk hararar da take antayama Hon. Nakowan ya cigaba da faɗin, “Bayan maganar Tajuddeen ga Hon. Haruna. Nasan shima dai kin sanshi tunda yace kece kika turosa wajenmu kamar yanda Mahaifinki ya tabbatar mana dama akwai wanda kike so”.

        Da sauri Lulu ta kalla Hon. Nakowan, cikin fushin da ya fara fallasa kansa a maƙoshinta ta ce, “Baba ni bamma san wannan mutumin ba face a poster. Magana kuma bata taɓa haɗani da shi ba kota gaisuwa balle zancen soyayya. Ni bashi bane wanda nake so kuma shi yana a waje”. Maganar ƙarshen ta fito a bakinta cikin suɓucewar harshe da ita kanta sai da ta gama faɗa ta tsinta kanta cikin matuƙar takaicin kan nata. Dan haka ta wani yatsine fuska, a zuciyarta tana faɗin (ALLAH ya kiyaye naso driver na can dai)…

         “Waye shi? Miye sunansa? Ɗan wanene kuma?”.

    Jerarrun tambayoyi da ga bakin Alh. Sulaiman cikin makirci da shirin da ya kammala tsarawa tsaf tun a daren jiya, dan ya ɗauki alwashin ƙararma da Daddy man kai tsaf kasancewar yana ji a ransa shirine kawai, dan a bibiyar da yake ma Mawaddat ya tabbatar bata da wani saurayi, duk wanda ma ya raɓeta da batun soyayya yagashi takeyi. Uncle ɗin nata ta kalla a ɗan daburce, sai dai kafin tace wani abu Baba da hankalinsa ba’a kanta yake ba balle ya fahimci halin da take ciki ya furta “Jeki shigo da shi”. Kamar wadda dama take jiran umarnin, zumbur kuwa ta miƙe ta fice. Har yanzu yana kwance a motar, sai dai saɓanin ɗazun yamzu karatun Alkur’ani yake saurare a wayarsa. Darajar waɗan da ke ɗan kai kawo da gudun kar wani ya ganta ya sata masa knocking a hankali. Tun fitowarta ya riga ya ganta, tsaiwarta a wajen da hararar data dallarama motar wadda yasan tasace kuma duk a kan idonsa ne. Amma sai yay buris har sai da ta ƙara na biyu cikin ɗan fara tunzura. Gilashi ya sauke ƙasa a hankali, babu zato idanunsu suka shige cikin na juna. Kusan a tare suka janye da sauri, ita tana jan tsaki da ƙarewa da kwafa.

        “Sai ka fito malam. Saura kuma idan ka shiga kaima mutane ƙauyancin da ka saba. ALLAH sai na koya maka hankali”.

      (idan baki koyamin ba ni zan koya miki) ya faɗa a zuciya, a zahiri kam kansa ya gyaɗa mata kamar wani salihin gaske (😔🥱) itako sai taji kan nata ya ƙara girma. Matsa masa tai ya fito tana watsa masa hararar ƙasan ido. Shi dariya ma ta bashi, amma sai ya kanne, a ransa kam ya riga ya gama tsara haukan da zai manna mata a ciki, dan ya gama shirya kwance mata zani a kasuwa, ya san dai Uncle Yousuf zaiji ba daɗi, zai bashi haƙuri kawai a wuce wajen dan gaskiya shikam ba za’ai wannan aikin rashin gaskiyar da shi ba. Dan garama ya zame kan nasa kakan nata yay mata auren dolen da shi yafi dacewa da ita ma kodan tarbiyyarta da ke ƙara neman taɓarɓarewa. A jere suka tafi tana wani ɗan murmushin da iyakarsa lips. Shima kuma yana murmushin muguntar da ya gama shirya mata. A nutsensa yay sallama. Duk da yawan mutanen da ke a farlon baiji ko ɗar ba a ransa, sai ma gaishesu da yay a jimlace cikin cikar kamala. Da yawa ya burgesu, sun kumaji a aransu lallai Mawaddat ta iya zaɓe, ashe girman kan nata da izza bazai ƙare a banza ba irin wannan hot guy haka. Tajuddeen kam sumar zaune yay kansa a juye, haka suma su Hon. Nakowa idanu kawai suka zuba masa cike da ɗimuwar rashin makamar yin tunani. Baba ne yay murmushi bayan ya gama ƙarema masa kallo da ga sama har ƙasa cikin ƴan sakkani. Cike da dattakonsa ya nunama Smart gefensa da faɗin, “Ƙaraso nan ka zauna kaji my Grandson”.

       Baiyi musu ba ya ƙarasa garesa, sai dai maimakon inda ya nuna masa sai ya zauna a ƙasa gaf da ƙafafunsa dan haka kawai tsohon yay masa wani irin masifaffen kwarjini. Murmushi mai ma’anoni da dama Baba ya sake saki, haka ma Uncle Yousuf. Cikin tsantseni da noƙewa ya sake gaishe da Baba da ya miƙo masa hannu alamar su sake gaisawa. Nan ma murmushin Baba ya sake yi da faɗin, “Shike nan tunda baka so mu samu ladan juna. Minene sunanka yaro na?”.

        “Aliyu Hydar M. Idris Mawashi”.

   Ya bama Baba amsa cikin girmamawa. Kai baba ya jinjina da faɗin, “Masha ALLAH suna mai daraja. ALLAH yasa kayi koyin ainahin mai sunan. Ali mazan fama, Ali gadanga ƙusar yaƙi. Ali zaki, Ali sadauki.”

      Kirarin da Baban yay masa ya saka wasu da yawa sakin murmushi a afalon ciki harda shi kansa Smart ɗin. Baba ya cigaba da maganarsa kai tsaye. “Sadauki minene alaƙarka da jikata Mawaddat?!”.

     Wani irin bugun ƙirjinsa tambayar tayi har acan ƙasan rai, amma sai ya dake cike da bama kai ƙwarin gwiwa ya ɗago kaɗan da nufin kallon Lulu cikin ido ya bama Baba amsa da (babu komai) amma aka samu akasi a bazata idanunsa suka sauka akan mutumin daya saka aka satoshi, ya kuma damƙa masa aiki akan Jiƙamshi family. Cikin ido suka kalla juna shi da Alhaji Sulaiman Sufi Ado Garko da shima ya kafeshi da idanu cikin wani irin yanayi mai wahalar fassara. Matuƙar girgiza Smart ya shiga, sannan mamaki ya nema halaka shi, (wanene shi anan ɗin?) Zuciyarsa ta ayyana masa bayan ya janye idanunsa. Bashi da mai bashi amsa, sai dai yana da damar neman amsar ta dalilin amsar da zai bama Baba a yanzu. Dan haka kai tsaye ya furta, “Ranka ya daɗe alaƙar soyayya da muke fatan ta kaimu ga aure. Kuma harta yarjemin turo magabatana duk da kasancewar baka nan ya kawo tsaikon hakan”..  

         “Masha ALLAH Alhamdullah, ai yanzu gani na dawo. Mawaddat! Ga Tajuddeen, ga Haruna, ga kuma Aliyu Hydar, wanene zaɓinki? Ina son ki faɗa ko nace ki sake faɗa a gaban kowa domin samun daidaito da rufe wannan babin mu fuskanci na gaba”.

     Da ƙyar Lulu ta haɗiye yawun takaicin Smart da ya maƙure mata maƙoshi da cimata zuciya. Ta ɗan dubi inda Uncle Yousuf yake, cikin sa’a ta samu ita yake kallo sai ya gyaɗa mata kai a yanayin bata ƙwarin gwiwa. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye, tare da danne zafin da takeji da ƙyar ta gyaɗa kanta da faɗin, “Grandpa ni shi nake so”.

          “Wa ɗin?”

      Sai da ta rumtse idanunta sannan ta furta “Hydar” a hankali kamar mai raɗa………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓  3️⃣9️⃣

……..“Ƙarya kike yi munafukan yarinya”. Alh. Sulaiman ya faɗa cikin suɓucewar baki. Yayinda Daddy da Uncle Yousuf suka saki wata irin ajiyar zuciya a ɓoye. Shiko Smart ƙirjinsa ne yay wata irin yankawa har sai da ya lumshe idanunsa yana mai ambaton sunan ALLAH. Furucin Alh. Sulaiman dana Tajuddeen da shima a zabure ya furta, “What! Drivern naki? Kai ina wlhy ƙarya kike Mawaddat akwai wani shiri a wannan zancen naki”.

      Falon ne ya nema ruɗewa kowa na ƙoƙarin faɗin albarkacin bakinsa. Yayinda Smart ya dilmiya cikin kogin ninƙayar nazari. Dan abinda Alh. Sulaiman ɗin yayi ya sake zaburar da shi ne har wasu abubuwa masu girma da ya gama tsara gujemawa suka fara bijiro masa. Tsawatarwar Baba ta saka falon yin shiru. Hakan ya sake bama Smart da Alh. Sulaiman damar yin kallon kallo, kai tsaye Smart yake nazartar gargaɗi mai firgitarwa da ga idanunsa, dan haka ya sakar masa wani shegen murmushi da masa alamar 1-0 ya kashe ido ɗaya. Rawa jikin Alh. Sulaiman ya fara, sai dai ƙoƙarin ganin ya nutsar da kansa yake. Ganin fa hakan bazai faruba ya sashi miƙewa a zabure ya kama hannun Tajuddeen suka fice. Babu wanda ya hanasu. Ganin haka ma sai suma su Hon. Baita suka ce zasu wuce. Godiya Baba yay musu da basu haƙuri yana mai sake tabbatar musu bazai ma Mawaddat auren dole ba. Amma yana mai basu haƙuri tare da dama idan har akwai wata da Hon. Nakowa zai iya so a cikin zuri’arsa bayan Mawaddat ya bashi dama yazo ya sake gwada sa’arsa su dai-daita”.

     Godiya sukai masa da tabbatar masa yin nazari akan maganar tasa, suka kuma yi fatan alkairi ga Mawaddat ɗin duk da dai ta ciki fa na ciki. Bayan wucewarsu Baba ma addu’a ya saka ayi ya sallami kowa, sai dai banda Daddy da Uncle Yousuf da Smart. Amma har Lulu yace taje. Koma ba’ace taje ɗin ba batai niyyar zama ba, dan in har ta cigaba da zama a falon zata iya aikata ɓaranɓaramar da komai zai tashi a wajen….

         Tambayoyi na mutuntawa Alhaji Sufi Ado Garko ya sake yina Smart, shiko ya amsa masa cikin nutsuwa kuma kansa tsaye. Hakan ya saka Uncle Yousuf jin farin ciki, sai dai umarnin Baba na ƙarshe akan Smart na cewar ya je ya sanar ma iyayensa suzo a cikin satin nan ya girgiza Daddy matuƙa har ya ɗan waro ido sai da Uncle Yousuf ya zunguresa. Shi kansa Smart maganar ta girgiza shi, dan da ƙyar ya iya haɗiye yawu ya gyaɗa masa kai…..

       🤣Wayaga cakwakiya mai taurari. Kai Smart ka ɗauka abin wasa ne kenan, ai gashi nan Baba yay maka ɗaurin huhun goro 🤪🚴.

           ★★★…..

   “Kai Yousuf bazai yiwu ba. Ina bazan taɓa yarda Mawaddat ta auri yaron nan ba gaskiya. Da ace nasan wannan shawarar ka yanke dana kwaɓeka tun farko. To gashi nan DAGA WASA KARAMAR MAGANA  NA NEMAN ZAMA BABBA. Dama kai kana tunanin yin wasa da hankalin Baba ne?”.

          Daddy ne mai wannan magana cikin tashin hankali da damuwa wa Uncle Yousuf da ke driving. Cikin dakewa da nuna alhini kamar gaske shima Uncle Yousuf ɗin ya ce, “Yaya sam ba haka nai tunanin kasancewar al’amarin ba fa. Banyi zaton zaice Aliyu ya turo magabanasa da wuri kamar haka ba. Shima fa yaron da ƙyar na shawo kansa ya yarda zai mana aikin. Ni yanzu ma gaba ɗaya kaina ya kulle na rasa mima ya kamata nayi”.

     “Faɗama Baba gaskiya mana. Dan nasan Mawaddat bazata taɓa yarda ta auri drivern ta ba. Kai koni ma hakan bai min ba Yousuf. Ina impossible kamar yarinyata mai daraja irin Mawaddat ta ƙare da auren drivern ta, sai kace wani almara ma”.

         Ɓacin raine sosai ya dunƙule zuciyar Uncle Yousuf, cikin matsanancin takaici yake duban Yayan nasa, sai dai baiyi magana ba ya sake maida kansa ga titi har suka isa gida. Shima Daddyn ya fahimci ran ƙanin nasa ne ya ɓaci, amma bai fahimci ainahin miya ɓata masa ran ba. Suna isa gida Uncle Yousuf baiko fita a motar ba yay shirin juyawa. Da mamaki Daddy da ke kallonsa ya furta, “Ya zaka koma kuma bamu gama magana ba Yousuf”.

     Idanu Uncle Yousuf ɗin ya rumtse sai kuma ya buɗesu akan Daddy. “Yaya to wace magana kuma ta rage? Kace bazata auri driver ba, shike nan magana ta ƙare ai, dan ni kam iya abinda zanyi nayi k….”

        “Kaga sakko muje ciki wannan ba maganar mota bace.” kamar zai ce a’a sai kuma dai yabi umarninsa ya fito. Falon baƙi suka nufa, dan in har zasu maganarsu ta sirri sunfi buƙatar zuwa can kasancewar babu wanda zai iya jinsu. Suna shiga Daddy ya ce, “Yousuf ka fahimceni mana. Ni fa ba ina nufin bakai ƙoƙarinka bane ba. Amma Please ka duba mana. Yaron nan fa driver ɗinta ne….”

      “Shi driver ba mutum bane? Ko kuwa shi dama mai arziƙi ALLAH ya tabbatar masa shine mafifici ga kowa a duniya da da lahira?. Gaskiya yaya ka fara bani tsoro, matuƙar tsoro ma kuwa. Wai kai kuwa wani irin so mara fasali kake ma Mawaddat? Ko kai ne zaka aure ta….”

    “You’r vary stupid Yousuf! Wane irin banzan magana ne wannan?”.

   “Dolene na faɗi hakan ai Yaya. Dan al’amarin naka ya fara wuce makaɗi da rawa kuma. Idan ka manta shekarun Mawaddat ashirin da huɗu har da watanni balle kace bata isa aure ba. Tun tana shekara ashirin aka saka mata ranar aure ka goya da bayanta al’amarin ya wargatse. Idan kace wancan yana da wani aibu shi wannan minene aibunsa? Dan kawai ya kasance driver mai neman halaliyarsa? To wlhy bakai ya kamata kace Mawaddat tafi ƙarfin Aliyu ba. Aliyu ne ya kamata yace yafi ƙarfin Mawaddat kodan halin da take a ciki wanda kai ne gaba-gaba wajen zama silarsa. Kai ne ya cancanta kai ƙoƙarin ganin ka gyara ko neman hanyar da zata gyaru ta zama cikakkiyar mutum kafin kowa amma baka ƙoƙarin yin hakan sai sake bata damar ma da zatafi yanzu lalacewa kake yi. Ina ji maka tsoron ranar da Baba zai fahimci halin da Mawaddat take a ciki, in dai maganar Aliyu ce kuma na bari…..”

      Da sauri Daddy da jikinsa yay sanyi ya riƙoshi. “Kaga kayi haƙuri auta.”

          Batare da Uncle Yousuf ya yarda ya juyo ba ya ce, “Kai zan bama haƙuri ai Yaya. Dan na shiga hurumin daba nawa ba. Na manta Mawaddat ƴarka ce kai ɗay….”

     “Shiiii! Ni ba haka nake nufi ba auta. Amma tunda zuciyarka ta kaika ga hakan amin afuwa. Ni kaina wani lokacin yanda nake ɗaukar al’amarin Mawaddat na bani tsoro. Amma dan ALLAH ka tayani da addu’a. Sannan kayi haƙuri ka cigaba da duk yanda kake ganin shine dai-dai. Ba Mawaddat ba ko ni ka isa dani ai ko. Wlhy a duk sanda kake faɗamin gaskiya akan lamarin Mawaddat fuskar Mahaifinmu nake gani akan fuskarka, yayinda muryarka kan juye min tamkar ta mahaifiyarmu. ALLAH yay maka albarka auta. Ina alfahari da kai a matsayin ɗan uwana da ga kai har Kareema. Wlhy itama fahimtata ne kawai batayi tun farko, amma tana da wata daraja da kima mai girma a gareni”.

      Tsira masa idanu kawai Uncle Yousuf yay kalaman nasa na bashi mamaki da al’ajabi. Anya kuwa Yayan nasa bashi da Alhaju? Dole ne yace haka, dan yau wai bakin Yayansa ne ke yabon Aunty Kareema. Kai anya kuwa dai…..

         Kamar Daddy ya fahimci abinda ke a ran ɗan uwan nasa ya saki murmushi mai ciwo. “Mamaki kake ko auta? Kana mamakin yabon Kareema a baki na. Humm bazaku gane bane, dan tun farko bakubi hanyar da zaku gane ɗin bane shiyyasa kuke min kallo irin wanda bashi ya kamata kumin ba. Kaje kawai abinka. Na kuma maka alƙawarin bazan sake saka baki ba akan al’amurin auren Mawaddat dan kai ne ubansu dama ni ɗan kallo ne. Sai dai a wannan gaɓar ina tunatar da kai suma su ƴan biyu ya kamata ka sakasu suyi aure fa. Kaje ALLAH ya huta gajiya”. Da ga haka Daddyn ya fice idanunsa taf da ƙwalla. Da kallo kawai Uncle Yousuf ya bisa zuciyarsa na kaikawo a ƙirji. Dan ba ƙaramin ratsa masa zuciya kalaman ɗan uwan nasa sukai ba yau……

       ★★….

     A ɓangaren Lulu da bata san hukuncin da Baba ya yanke ba suna fitowa a street ɗin gidan Baba a gadarance ta cema Smart “Malam tsaya da motar nan”. Kamar zai shareta sai kuma ya gangara dan yanzu ba shirmenta bane a gabansa. Abubuwa ne masu yawa ke masa kaikawo a zuciya. Fita tai ta koma baya, bai ce komai ba ya sake tada motar suka cigaba da tafiya. Sun ɗan ƙara nisa motar shiru babu mai magana, shi hankalinsa ya rabu biyu, wani a tuƙi wani a tunanin al’amarin da ya faru yanzun nan. Ita kuma hankalinta nakan tab… Ɗinta ne tana aiki har suka iso. Ita ta buɗe da kanta dan hankalinta nakan abinda takeyi, sai da ta zura ƙafarta ɗaya waje zata fita sannan tai magana batare data kallesa ba. “Malam ina fatan baka ɗauki abinda ya faru a gidan Grandpa wani abu ba. Idan kuma ma ka ɗauka ɗin to ka ajiyeshi a motar nan karma ka koma gidanku da shi dan zai zame maka dakon wahala ne, dan ba Mawaddat ba ko mai aikin gidanmu tafi ƙarfin nunaka matsayin abin sonta balle ni, ka cigaba da zama matayinka na yarona kana amsar albashinka hankali kwance a samu na koko da ƙosai”. Ta ƙare maganar da balla masa uwar harara da jan tsakin tabbatar da gargaɗinta ganin yanda ya wani tsareta da idanu ta cikin mirror. Kansa ya ɗan girgiza bayan ficewar tata, sai kuma ya saki wani shegen murmushi da cije lips ɗinsa yana mai kai hannu ya shafa tattausar sumar ƙasumbarsa. A hankali ya furta, “Kema lokaci yayi da zaki fara cin koko da ƙosan ai ƴar gidan madara”. Ya ƙara cije lips ɗinsa da kashe ido ɗaya….

      (Makiri Smart. Mi kake shirya mana ne🥱😨).

______________________

        “Dad! Wlhy wannan abun ƙarya ne shiri ne kawai. Amma babu wata soyayya a tsakanin Mawaddat da shi. Drivern ta ne fa, hasalima Alhaji Yousuf dani muka zauna muka roƙesa  akan ya tuƙata saboda muna son ya bibiyar mana al’amarinta akan s…..”

     Sai kuma yay shiru tuna ɓaranɓaramar da yake neman yi ga kallon da mahaifin nasa ya kafesa da shi. “Ya ka dakata? Ƙarasa mana akan mi?”.

          “No Dad share. Wannan bashi bane mai muhimmanci, musan gaskiyar zancen da tabbatar ma Grandpa shine nafi buƙata a yanzu. Idan ba hakaba wlhy sai na tada hankalin kowa a family ɗin nan dan Mawaddat kaɗai nake so, da ita kawai nake buƙatar zaman aure”.

      “Tajudden ka kwantar da hankalinka, in dai Mawaddat ce babu fashi kai ne mijinta. Yaron nan kuma nima na tabbatar sakashi akai ko kuma shine ya sa kansa. Amma barni da shi, zan tabbatar masa wanene ni dan naga yana son yin wasa da wuta ne a tafin hannunsa batare da ya sani ba. Kaje ka cigaba da shirye-shiryen aurenka nan da kwanaki takwas”.

          “Amma miyasa ba gobe ba Dad? Ni gobe nake so Friday a ɗaura. Next Friday ai shagalin biki na nunawa Sa’a ta tare a gidana.”

      “Ka ɗauka yanda ka tsara labarin, haka za’a bugashi a jaridu da mujallu a yammacin gobe cewa Tajuddeen Sulaiman Sufi Garko ya zama angon Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi”.

    “Thanks You Dad”.

Tajuddeen ya faɗa cike da zumuɗi yana mai rungume mahaifin nasa, dan yasan baya magana bai tabbatar da ita ba……

       Gaba ɗaya tattaunawar ɗa da mahaifin acikin kunnenta ne, dan tun farawarsu ta iso ƙofar falon bisa umarnin auntynta da ta aikota. Da sauri ta tallafe tray ɗin dake hanunta mai ɗauke da kayan motsa baki jin zai suɓuce mata. Juyawa tai da sauri zuwa apartment ɗin yayarta cikin sassarfa kamar zata faɗi ga idanunta na kwarar da hawaye masu zafin gaske……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣0️⃣

…….“K! K! Lafiya kuwa naga kin dawo min da shi haka kamar ma wadda take a firgice?”.

     Ƙasa ta dangwarar da tray ɗin tare da faɗawa jikinta ta sake fashewa da kuka. “Aunty Abasiyya wannan karon ma zan rasashi. Dama ashe abinda ake ƙullawa a gidan nan kenan amma baki faɗamin ba kika barni inata shirme na?” ta ƙara fashewa da kuka. “Mtsoww! Wai nikam Ramlah yaushe ne zaki hankali? Kimin bayani danni ba fahimtarki nake ba. Kinga tashi zaune”. Babu musu Ramlah ta tashi, ƙyaƙyƙyawar yarinya kuma ƴar gaye. Bata damu da share hawayen da suka gagara tsaya mata ba, ta ce, “Aunty Abasiyya zaki cemin baki san shirye-shiryen auren Tajuddeen ake ba a gidan nan kuma da mayyar yarinyar can dai”.

       “What! Auren Tajuddeen fa? A gidan nan kuma ban sani ba? Lallai Alhaji ya sake zama abinda ya zama. Wlhy Ramlah sam ban san da zancen ba, sai dai tabbas naga anata wani ƙus-ƙus tsakaninsa da matarsa na munafunci tun jiya, yau kuma ya ɗauketa suka fita sai dai ban san ina sukaje ba”.

     “To Aunty babban gida sukaje, dan inaga Baba ya dawo…..”

   Ta kwashe kaf abinda taji Tajuddeen da babansa na tattaunawa ta sanar mata. Tare da faɗin, “Aunty dan ALLAH ki taimake ni, wlhy idan na ƙara rasa Tajuddeen a wannan karon zan iya rasa rayuwataa gaba ɗaya ina sonsa matuƙa fiye da yanda nake son kaina”.

             “Hummm Ramlah kenan, badan nasan minene zafin soyayya ba da nace baƙya kishina. Ina matsayin yayarki uwa ɗaya uba ɗaya amma kina son ɗan kishiyata da bata taɓa ƙaunata ba a gidan nan, da ace ma tanada dama da tuni ta kawar dani a duniya. Gaskiya wannan soyayyar taki bataimin adalci ba. Sai dai bazanƙi taimakonki ba, dan nima hakan zai taimakeni wajen ƙuntata rayuwar Hajiya Turai. Dan haka ki kwantar da hankalinki, yanzun nan zan warware musu ƙullin nasu ta inda basu taɓa zato ko tsammani ba.”

     Cike da ɗoki Ramlah ta ce, “Aunty mi zakiyi?”.

    “Jira ki gani”.

Ta faɗa tana janyo wayarta. Daddanawa tai takai kunne tare da miƙewa ta shige ciki tana faɗin, “Baba barka da rana…….” iya abinda Ramlah taji kenan…..

        ★ Alhaji Sulaiman kam da basu san Ramlah ƙanwar amaryarsa da take riƙo taji tattaunawar tasu ba tuni Tajuddeen ya fice da waya a kunne yana waya da telansa kan ya jirashi a shago yanzu zai zo da ɗinkin ujila… Da kallo Alh. Sulaiman ya bisa yana wani murmushin mugunta. Shima ya kai wayarsa kunne. Bugu ɗaya Malami ya amsa da ga can. Batare da ya amsa gaisuwar Malamin ba cikin bada umarni ya furta, “Yaron dake mana aiki a gidan Isma’il Jiƙamshi ina buƙatarsa”.

      “Angama ranka ya daɗe”.

   Malami ya faɗa cikin tsantsar girmamawa tamkar yana a gaban ubangidan nashi ne…..

      ★★……

   Alhaji Sufi Ado Garko da ke zaune a falonsa na baƙi har yanzun, dan bayan fitowa sallar la’asar ya sake wasu baƙin da suka sake rikita masa lissafi. Ba kowa bane face tsohon gwamna sannan babban ɗan kasuwa M Atik Kumo mahaifin MM Atik Kumo da tawagar abokansa uku neman izini wa ɗan nasa fara neman soyayyar Mawaddat. Sun gama masa bayanin kenan ya tabbatar musu da abinda ya faru game da kawo wanda Mawaddat ke so a yau har ma sun basa damar turo magabatansa suka masa godiya da bada haƙuri dan mahaifin MM Atik mutumin kirki ne. Ya fahimci bayanin Baba ya kuma gamsu suka rabu cikin girmama juna dan Baba ya kasance tamkar uba ga duk wani ɗan siyasa to. Bayan fitarsu ne yana ƙoƙarin tashi ya shiga ciki dan ya huta da hayaniyar da ya sha kiran matar ɗansa Alh. Sulaiman ya shigo masa. Bai kawo komai a ransa ba dan shi surukansa tamkar ƴaƴa suke garesa. Bayan sun gaisa tai masa barka da sauka da yaya jiki tare da bada haƙurin rashin zuwa tarbarsa saboda batajin daɗi ne. Ya gamsu da abinda ta faɗa tunda tabbas bai ganta ba a cikin gidan dan haka ya saka mata albarka. Ɗan jimm da tai ya sakashi fahimtar akwai wani abu, dan haka ya tambayeta. Sai da ta sake kwantar da murya cike da kissa ta zayyano masa dukkan abinda ƙanwarta ta tabbatar tajiyo, sai dai tace itace taji ba ƙanwar tata ba. Ta kuma kira ta faɗa ne dan kar abinda zasuyi ɗin ya taɓa kimar Baba da Family ɗin. Amma dan ALLAH bata son kowa yasan ita ta faɗa gudun abinda zaije ya dawo. Murmushi Baba ya saki irin na manya. Ya sake saka mata albarka sannan sukai sallama. Yasan Sulaiman zai aikata abinda ma yafi hakan, kuma shima yayi tunanin wani abun zai iya ɓullowa game da hukuncin nasa. Sai dai abinda ya bashi mamaki mi yake faruwane haka maneman Mawaddat ɗin keta karakaina a wannan gaɓar? Ko dai rawar data taka ne game da shari’ar mutumin nan ta kwanan nan data ɗauki hankalin mutane da yawa ce? Dan duk da baya ƙasar kunnensa da idanunsa na a Nigeria ɗin. Yafi zaton hakan shiyyasa bai ɓata lokaci wajen zurfafa tunani ba. Sai ma ya dannama Uncle Yousuf kira dan ya gama tsara kafin Sulaiman ya ƙulla abinda yake tsarawa shi zai tabbatar masa wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi……

          ★★…..

       Sosai mamaki ya dabaibaye Uncle Yousuf da ke sauraren Baba. Dan ya masa bayani ne akan zuwan su M Atik Kumo kafin hukuncin da ya yanke a yanzu-yanzu saboda labarin da ya samu na shirin ɗansa da jikansa. Cikin girmamawa da godiya Uncle Yousuf ya tabbatar masa yanzu nan zai tura a isar da saƙon in sha ALLAHU. Suna yanke wayar kuwa yay kiran abokinsa Coach ɗin su Smart Abdull-Hameed, wanda ta sanadinsa ya fara sanin Smart ɗin dama. Tun yana waya da Hameed ɗin kiran Yayansa (Daddy) ke shigowa, bai ɗaga ba har sai da ya kammala da Hameed ɗin. Wani kiran ne ya sake shigo masa, ya ɗaga yana kaiwa kunne da faɗin, “Yaya irin wannan kira lafiya dai ko?”.

       “Inafa lafiya Yousuf! Wai kaji suma su M Atik Kumo sunzo nemawa ɗansu izinin neman Mawaddat. Anya abunnan na lafiya ne? Ni bama wannan ya damen ba, dan M Atik mutumin kirki ne, ɗan nasa ne kawai sai a hankali, dan wlhy da ace ya kasance mutumin kirki kamar mahaifinsa da hankalina zaifi kwanciya da aura masa Mawaddat fiye da yaron nan daka kawo….”

       Cikin gatse Uncle Yousuf ya ce, “To kodai a bama ɗan M Atik ɗin dama kawai, tunda shi dai ai ba wani abu ya taɓa aikata mana ba. Sannan a a bayyane ban taɓa jin ance ga aibun yaron ba…”

     “No no no Yousuf bar wannan maganar kai dai. Dan wlhy ina gama waya da Baba yanzu na ɗan fara bincike kan yaron wajen wani aminina al’amarin babu daɗin ji, dan akuyace lulluɓe da fatar kura bai gado uban nasa ba. Kayi haƙuri bakwai kushe yaron nan Aliyu nake ba. A’a kawai ina tunanin taya zai iya riƙemun yarinya bashi da aikin yi, danni ban ɗauki direbanci wani abunyi ba face hanyar maƙalewa domin rage matsaloli…”

           “Humm Yaya kenan. Nifa ban tsawwala ba, idan akwai wani da kake ganin hankalinka ya kwanta da shi game da Mawaddat ƙofa a buɗe take ka kawosa mu canjashi da Aliyu dan shi dama bawai ya ɗauki abun da girma bane tunda auren wata ɗaya kacal ne zai saketa, ni kuma na gaji da maimaita magana ɗaya”.

       “Ina ai zancen wani ma bai taso ba auta. Yanzu fa Baba ke sanar min kuma munafukin can abinda yake ƙullawa akan ɗansa. Kaga ko ai bamu da wani isashen lokaci. Mu ƙarasa da Aliyun kawai sai dai zamuyi komai a rubuce da ƙa’idoji dan karma da ga baya wani abu saɓanin wanda akai a rubuce ya biyo baya tunda mun samu Mawaddat ɗin ta amince babu rigima. Sannan zan basu gidan da zasu zauna a kuma canja masa aiki”.

       Sosai takaici yake neman shaƙure wuyan Uncle Yousuf. Amma sai ya danne ya ce, “Nima munyi waya da baban yanzu. Yanda kuma kake so haka za’ayi. Zan cema Aliyun ya tsaya idan ya kawota sai muyi maganar, idan kuma zamu bari ne sai zuwa weekend zaifi a nutse”.

     “Eh weekend ɗin yayi kawai ALLAH ya kaimu”.

    Sallama Uncle Yousuf yay masa tare da kashe wayar gaba ɗaya ma. Takaici yakeji na ɗan uwan nasa da halayyar da yake nunawa akan al’amurin Mawaddat mara fasali. Ya rasa wane irin soyayya yakemata irin haka. Ya kamata ace yayi nadama da neman hanyar gyara. Sai dai kash, nadamar tasa alokacin da ya ganta cikin wani hali ne kawai yake yinta…..

          ★★…..★

    Duk wannan cakwakiya da ƙura da take cigaba da tashi a wannan yini da ga mai gayya da aiki kam normal ne. Dan tuni ta tattara komai ta watsar ta tattara hankalinta akan case ɗin yarinyar nan da akaima fyaɗe dake neman caza mata kai. Tun bayan isarsu office bata wani zauna ba ta fito suka sake fita. Kasancewar hankalinta ga a inda yake ya sa yau tsakaninta da drivern nata babu masifa. Sun ɗanyi yawace-yawace har kusan bayan sallar la’asar sannan suka koma office. A hanyar komawar ne ya fahimci ana binsu a baya. Da farko bai kawo komai a ransa ba sai da ya ga bayan ta shiga office tai zaman kusan mintina talatin ta fito zai maidata gida a hanya ya sake ganin motar ɗazun ɗin nan dai da napep a biye da su. Yaji a ransa cikin biyu dole ai ɗaya. Kodai su Honorables, ko kuma Alhajin nan da ya sa aka sace shi wancan karan a yau kuma ya ganshi a gidan Baba. Yafi buƙatar ya kaita gida lafiya daga nan koma mizai farun ya faru, dan haka ya take motar ya tsere musu cikin salon canja titi gaba ɗaya……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣1️⃣

…….Mawaddat da ke da burin amsar saƙo ta kallesa fuska babu wasa. “Malam miye na canja hanyar? Dalla ka koma tacan ina buƙatar amsar saƙo”.

      Shiru kamar bazai tanka mata ba sai kuma ya bata amsa a taƙaice. “Akwai holdup ta canne, ga shi lokacin sallah ya kusa bana buƙatar rasa jam’i”.

          “To ɗan iya wannan kuma matsalarka ce. Bai kuma damen ba. Ka koma ta inda nace bana buƙatar sharhi”.

      Hanyar ya canja batare da ya sake cemata komai ba, amma kuma ba wadda dai take son abi ɗin ba dai ce. Dan zuciyarsa ta bashi kayan shaye-shayen nata ne zata amsa. Takaici ya turniƙe Lulu. Dama ga gajiya na nuƙurkusarta, ai tuni ta balbale sa da masifa amma yay biris da ita kamar yanda ya saba, bai ƙara tari ba har suka iso gida. Buɗe motar tai a fusace ta fito, dai-dai da shima yana fitowar da nufin buɗe matan. Ta zabga masa uwar harara da wani banzan kallo. Nunashi tai da ɗan yatsa tare da tattaro dukan ƙarfinta na zazzage masa abinda ke a ranta amma ko kalma guda ta gagara fita mata a harshe saboda yanda ya wani tsareta da idanunsa data raɗama suna irin na macizai. Sai lips ɗin ta ne kawai ke rawa kamar wanda ya ɗaureta da idanun nasa. “Kaje na koreka, da ga yau bana buƙatar sake ganin wannan shashashar fuskar taka illiterate velleger…!”

        A hankali ya lumshe idanun nasa sai kuma ya sakar mata wani shegen murmushi da ya kusa fisge mata numfashi gaba ɗaya. Jitai kamar zata zube a wajan tsabar wani ƙudu dun takaici da murmushin sa ya haifar mata. Dan bata fassarashi a komai ba face na rainin wayo. Fahimtar ya samu nasarar ƙular da itan da yake buƙata ya sashi matsota a hankali, cikin ƙasa da murya da wani maidata can ƙasan maƙoshi ya furta, “Oh! Kin fison sake ganin angon naki kawai a ɗakin barcinmu ke nan AMARYA, ba damuwa a bani albashina dan da shi zan biya sadaki”.

         “What!!!” ta faɗa da ƙarfi tare da kai ma fuskarsa mari da gaba ɗaya ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata a jiki. Baya yay cikin wani salon da ta samu iska shuuu, ya ɗago yana murmushi tare da kashe mata ido ɗaya, sai kuma ya nuna fuskar tasa da yatsa yana ɗan sake matsota harda ranƙwafowa kaɗan. “Duk randa wannan hannun ya sauka kan wannan fuskar da sunan mari to kisa a ranki MAZA sun faɗi, faɗuwa irin ta MUTUWA. dan itace kawai damar da ƘYANWA zata iya samun yin birgima a gaban ZAKI yanda take so”. Ya ƙara kashe mata ido ɗaya yana ɗaga mata yatsu biyu da faɗin, “Bye *MATAR ILLITERATE*”. Yay gaba abinsa.

       Yuuuuu!! Lulu ta dinga jin hajijiya na neman kwasarta, wato itace ma ƙyanwar yake nufi. Dariya sosai Uncle Yousuf da ke cikin motar dake a kusa da su batare da sun san akwai mutum a ciki ba ke tuntsurawa harda ƙwalla. Ashe zaton da yakema yaron nan ya wuce nan. Kai jama’a har ya fara tausayin ƴar tasa gaskiya. Dan tabbas akwai babban wasa a wannan tafiya yanzu ne kuma za’a fara. Ganin yanda ta wuce tana haɗa hanya ga hawaye sun wanke mata fuska ya sashi daina dariyar ya buɗe motar ya fito, sai dai duk yanda yake son binta ya haƙura dan lokacin sallah yayi. Ya kai dubansa ga su Smart da ke alwala sai kawai ya nufesu yana gyara yanayinsa kamar bashi ya gama kwasar dariya ba a mota…

         Bayan an idar da salla kusan a tare suka fito. Uncle Yousuf ya dakatar da Smart da ke sallama da su maigadi akan ya jira su wuce tare. Kamar zai ce a’a sai kuma dai yay shiru dan kiran da Abba yay masa suna ƙoƙarin shiga massalaci akan idan ya dawo gida ya sameshi falonsa yanzun nan. Yasan maganace da Abban, shi kuma da yayi niyyar bama masu bin san nan a baya dama dan ya tabbatar ba haƙura sukai ba su kamashi dan yana son yin magana da koma waye ya turosun. Babu yanda ya iya dole yabi Uncle Yousuf ɗin, shiko ya ƙaunaci ALLAH ya kaisa har gida yau. Tunda suka fito kuma yaga motar nan sai dai ba napep ɗin yanzu, motar dai ce ke cigaba da binsu yanzu ma. Suna isowa titin anguwarsu yaga sun dakata cikin takaici direban motar na kaina sitiyari duka alamar ba haka sukaso ba. Sai dai kuma abinda bai sani ba shima Uncle Yousuf ya san da su shiyyasa ma ya ɗakkosa ya kawo har gidan.

       “Alhaji yau na saka ka aiki, Nagode sosai”.

    Murmushi Uncle Yousuf da idonsa ke kan mirror yana kallon mutanen nan ya saki, tare da faɗin, “Har yanzu dai ina a Alhaji na? A tunani na na zama Uncle yanzu tunda ƴa zan bayar duk da auren wucin gadi ne”. Yanda Uncle Yousuf ɗin ya ƙare maganar ne ya saka Smart kallonsa, sai kuma ya ɗauke kansa yana sakin murmushi ya ce, “To ayi haƙuri Uncle”.

       “Shike nan na haƙura, dan dama ba’a san iyaye da fushi da ƴaƴansu ba.  Ina fatan zaka samu Abba da maganar yau ko?”.

     “Da wuri haka?”.

Smart ya faɗa da mamaki yana kallon Uncle Yousuf ɗin.

              “Dole ne muyi da wurin, dan ɗazun Baba ya sake kirana akan zuwan M Atik Kumo shima yana nemawa ɗansa aurenta, sannan Alhaji Sulaiman da ɗansa sun gama ƙulla matakin da zasu ɗauka a gobe idan ALLAH ya kaimu…..” tsaf ya zayyane masa komai shima. Mamaki ne ya sake lulluɓe Smart, yayinda a ƙasan zuciyarsa yake ta lissafi akan yanda zai canja salon wasan a yanzu tsakaninsa da Alh. Sulaiman. Kafin yanzu shi bai wani ɗauki zancen da muhimmanci ba, dan har ya gama ƙulla yanda zai kuɓuce wa al’amarin, sai dai a yanzun nan ya canja sabuwar shawara. Duk da bai san minene dalilin Alh. Sulaiman ɗin ba ya kamata ace ya nuna masa shima tsageran kansa ne a wannan gaɓar. Bai damu da zancen MM Atik Kumo ba…..

       “Aliyu kayi shiru!”

   Uncle Yousuf ya katse masa tunani. Iska ya ɗan furzar kaɗan sai kuma ya fuskanci Uncle Yousuf ɗin. Cikin sake furzar da wata iskar ya ce, “ Please Uncle kozan iya sanin yaya kuke da shi Alh. Sulaiman ɗin?”.

    “Yerh babu damuwa Aliyu. Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko ɗane ga Alhaji Sufi Ado Garko. Sannan Yaya ga mahaifiyar Mawaddat uwa ɗaya uba ɗaya. A shekarun baya ɗan uwana mahaifin Mawaddat abokai ne da Alh. Sulaiman na ƙut-da-ƙut, dan sun haɗu ne tunkan ya auri mahaifiyar Mawaddat ɗin adalilin shi Baba da ya ja Yayana jikinsa. Sai dai a yanzu ba haka bane, dan bamu san minene ya shiga tsakanin wannan amintaka ba abokan biyu suka zama maƙiyan juna ta yanda ko inuwa ɗaya basa sha. Iya tambaya na yima Yaya amma yaƙi faɗa min komai. Shi iyakarsa fita harkar Sulaiman, amma shi Sulaiman a bayyane yake nuna tsanarsa garesa da mu ma ahalinsa gaba ɗaya shiyyasa Yayana yay ruwa yay tsaki wajen hana aure tsakanin Tajuddeen da Mawaddat dan yace akwai manufa. Wannan shine iya abinda na sani gaskiya”.

       Kai Smart yake jinjina wa cike da gamsuwa. Sai da Uncle Yousuf yay shiru sannan shima ya bashi labarin kamasan da Alh. Sulaiman ɗin yayi a randa yazo shi da Ahmad suka roƙesa ya koma aiki, ya kuma sanar masa aikin da yace ya koma yay masa tare da nuna masa motar yaran Alh. Sulaiman da ke tsaye a bakin layinsu kasancewar suna iya hango su da ga nan ƙofar gidan su Smart ɗin da ke a bakin titin.”

      Sosai al’amarin ya girgiza Uncle Yousuf ɗin, ya kuma tabbatar masa da shima dalilinsa na kawoshi gida yanzun. Dan tunda suka kammala waya da Baba yaji a ranasa Alh. Sulaiman zai iya ɗaukar mataki kowane iri ne akan Smart shine ya saka wani ɗan sanda zuwa office ɗin Lulu ya saka masa ido, ɗan sandan ne ma a Napep ashe, sai ko gashi bayan tahowarsu gida ɗan sandan ya tabbatar masa ana binsu… “Wato Aliyu idan na fahimta tun fara aikinka da mu Alh. Sulaiman na biye da lamarinka kenan? Kuma bana raba ɗayan biyu a wajen Tajuddeen ya sani. Lallai ya kamata musan dalilinsa danni zuwa yanzu har Tajuddeen ɗin ma na saka masa alamar tambaya”.

      “Sanin dalilinsa abunne mai sauƙi Alhaji, yanzu dai barshi na fara masa duka a ciki, bayan cikin ya ƙulle zai amayar da duk abinda ke a ransa da kansa. Sannan Tajuddeen bai zama lallai yasan komai ba, zata iya yiwuwa amfani uban keyi da shi batare da shi ma ya sani ba”.

    Murmushi Uncle Yousuf yayi tare da bubbuga kafaɗar Smart, dan tsaf ya fahimci inda zaurancen nasa ya nufa game da duka a ciki. Murmushi shima Uncle Smart ɗin yayi tare da buɗe motar yay masa godiya ya shige gida, shi kuma yaja motar yana ƙara jin ƙaunar yaron har tsakkiyar ransa. A rayuwa yana matuƙar ƙauna da son jarumin mutum. Musamman ma matashi irin Smart mai tsayyar zuciya. Wannan nagartar tasa ya fara hanga a filin ƙwallo ya shige masa zuciya, faruwar ƙaddarar data nema dakushesa da ga cikar burinsa ta fara sakashi jin tausayinsa da laluben hanyar da zai iya taimaka masa. Bayan yin dogon nazari ya yanke shawarar kusantosa gefensa domin ƙara tabbatar da halayensa kafin ya ja hannunsa hanyar da ya gama shiryawa domin kaisa ga cikar burin nasa. Sai kuma ga al’amarin ƴar ɗan uwansa ya gitta a cikin labarin tamkar bakangizo a tsakiyyar gagarumin hadarin da ke gab da zubda ruwa. Fatansa kawai ta kasance bakangizo mai amayar da ruwan da ta shanye bamai haɗiyewa ba har abada………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣2️⃣

…….Bai samu ganawa da Abba ba sai bayan sallar isha’i ya samesa a falonsa. Bayan sun gaisa cikin dakewa Abban ya ce, “Aliy!”.

    Ya amsa da “Na’am Abba”.

  “Aliy!”

Ya sake ambata. Shima sake amsa masan yayi kamar farko. Malam Mika’il bai gajiya ba ya sake kiransa a karo na uku shi kuma ya amsa masan dai kamar yanda yay na farko da na biyu.

         “Na kiraka sau uku ko?”.

    Kai ya gyaɗa masa alamar eh.

“Na kiraka badan tisa maka sunan da ni na saka maka ba ne, na kiraka ne domin a yau zan tabbatar maka da magana ta ƙarshe ne akan aurenka. Dan duk maganganun da Yahanasu ta faɗa ɗazun akanka sun sosama mahaifiyar ka da nima kaina zuciya. Kuma mun ɗauki alƙawarin bazaka sake rufa wata anan gidan babu matar aure ba. Dan haka a yanzu ina son jin ta bakinka, idan kana da wadda kake so sai ka faɗeta, idan kuma babu mahaifiyarka ta maka mata, nima kuma na maka sai ka zaɓi guda a ciki.”

       Sai da ya ɗan rumtse idanunsa da jan numfashi, sannan ya ɗago a hankali ya kalli mahaifin nasa. Sai kuma ya sake maida kansa ya duƙar. “Kuyi haƙuri Abba duk ni ne na ja muku, amma insha ALLAH komai yazo ƙarshe, ba sai kun nemomin mata ba ni da kaina ma na samota”.

     Wata irin ajiyar zuciya Abba ya sauke a hankali, sai dai cikin dakewar san nan ya ce, “Wacece? Ƴar wanene? A ina kuma ta ke?”.

           Duk da yawan tambayoyin bai gazaba wajen amsasu ga mahaifin nasa. Ya ce, “Yarinyar da nake aiki gidansu. Ɗiya ga Alhaji Isma’il Jiƙamshi. A yau suma kuma suka buƙaci na turo iyayena dama in har na shirya”.

      “Alhamdullahi. Aliyu Hydar ka daɗe baka faranta min rai irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Ya yaye maka dukkan damuwarka. Ya ɗauraka akan maƙiyanka. Ya kawo maka mafita ga al’amuranka. Na amshi zaɓinka badan ta kasance ɗiyar Alhaji Isma’il Jiƙamshi ba, ko dan yana da kuɗi, sai dai dan nasan kai nagartaccen mutum ne da bazai taba yin zaɓen tumun dare ba.”

     (Abba ka gafarceni wannan dai kam zaɓen tumun asubace ma ƙarewar dare) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam murmushi kawai yayi da faɗin, “Nagode Abba. ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani. Ku gafarceni akan dukkan abinda nai muku ba dai-dai ba kuma insha ALLAHU zan cigaba da zama a fiye da yanda kuke buƙata”.

     Sosai Abba yay murmushin jin daɗi, Aliyu na cikin ƴaƴan da yafi ƙauna a cikin ƴaƴansa, sai dai shi kansa a wasu lokutan bai san mike danne soyayyar ba yayta kyararsa da hantararsa a dalilin ƙaddarar da wani bai isa ya canjata ba. Albarka sosai ya saka masa sannan ya sallamesa. Koda yabar wajen Abba cikin gida ya shiga, sai dai kai tsaye ɗakin Ammah ya shige yau bai gaida kowa ba a matan gidan. Ya samu tana shirin fitowa kaima Abba abinci dan yau itace da shi. Ya fahimci tana cikin damuwar da ya san babu makawa akan abinda ya faru ɗazune tsakaninta da Umma. Ƙannensa kansu yau basa cikin walwala. Suna gama gaisawa Ammah ta fice, annan ne Hawwah ke bashi labarin faɗan da akai sosai ne ai yau ɗin kuma duk a sanadinta ne. Da ga ƙarshe aka ƙare da musu goron halin da yake a ciki. Sosai ya ƙara jin zuciyarsa ta Zafafa. Sai dai komai bai ce ba yay musu sallama ya tafi makwancinsa……

          *_WASHE GARI_*

     Washe gari batare da sanin kowa ba Abba da tawagarsa suka nufi gidan Alhaji Isma’il Jiƙamshi nemawa Aliyu Hydar auren Mawaddat Isma’il Jiƙamshi. Sun sami tarba ta mutunci dan har Baba ma yazo gidan shima. Abinda zai birgeka babu ƙyama ko hantara irin ta mai kuɗi ga talakawansa. Abin farin ciki da mamaki ashema Alh. Sufi Ado Garko school mate ɗin Abba ne ma a secondary school. A take hira ta kaure a tsakaninsu har zuwa kan abinda ya tarasu. Sai dai kuma bayanin da shi Baba yazo da shi ya girgiza su a wajen. Dan a ganinsu babu wani shiri ai tare da su game da haka. Baba ya kwantar musu da hankali tare da tabbatar musu da dalilansa masu ƙwarin gaske ta yanda su duka suka gamsu da hakan. Sun ɗan ƙara tattaunawa sannan sukai musu sallama cike da jin daɗin karramawar da suka samu suka suka taho akan sai anjima idan sun haɗu ɗin….

        ★★……

      Sam Smart bai san mima ake ciki ba. Dan hatta zuwan nasu Abba bai san da shi ba saboda yau bai ma fita aiki ba. Tunda ita tace ta koresa da kanta a ganinsa babu amfanin ya koma su sake raba hali. Dan haka ya zaɓi yin kwanciyarsa a ɗaki yayta buga game ɗinsa hankali kwance har lokacin sallar juma’a ya gabato. Yana shirin shiga wanka Ahmad yazo gidan. Zuwan Ahmad gidan ba sabon abu bane garesa dan haka bai damu ba. Haka koda ya bashi shadda sabuwa fil yace ita zai saka bai kawo komai a ransa ba dan Ahmad ɗin ya sha musu ɗinki irin hakan, haka shima kansa yasha yi musu ɗinki a taren.

     Bai wani ɓata lokaci ba ya fito a wankan, Ahmad na zaune har ya kammala shirinsa. Yayi ƙyau matuƙa kamar ka sacesa ka gudu. Ahmad ya wani shiga masa ruwan turare. Warce turaren Smart yay yana hararsa da faɗin, “Kaifa a duniya kamar baka san wahalar kayan duniyar nan ba. Anata wannan yanayin zaka ƙaramin turare haka dan neman hanyar talautani”.

           Dariya kawai Ahmad yay masa da kashe ido ɗaya ya furta “Am sorry Zakin zaki”.

     Shima dariyar yay a karo na farko. Dan duk sanda ya kira shi da Zakin zaki yana nufin shi ɗin na Coach Hameed kenan yayansa. Cikin nishaɗi da farin cikin tsokanar juna da suke na kiran tuzurai suka fita. Jan Ahmad yay suka shiga ciki gaida Ammah. Ta saka masu albarka tare da addu’a data so tsayama Smart a rai. Amma sai ya danne ta a ƙasan rai da tunanin Ammah tayi addu’ar ne kawai domin gabansa. Daga haka suka taso suka fita acewarsu zasuje sallar juma’a su dawo nan suci biranuskon da Amma keyi matsayin abincin rana…

        “Wai wane massalaci zaka akaimu haka ne?”.

    Cewar Smart yana kallon Ahmad dake drivering a nutse. Murmushi Ahmad yay masa idonsa a titi ya bashi amsa da “Mi kakeci na baka na zuba? Zaka gani ai”. Baki Smart ya ɗan taɓe da cigaba da game ɗinsa a waya. A haka suka cigaba da ƴar hirarsu har suka iso massalacin juma’ar. Zamansu babu jimawa aka fara khuɗuba, dan haka suka nutsu wajen saurare har aka kammala. Ana ƙoƙarin tada salla ya hango Uncle Yousuf da Coach da ke isowa yanzu, da alama sun makara ne. Baice komai ba ya gyara tsaiwarsa aka tada salla. Kasancewar bayan idar da sallar juma’a yin ɗaure-ɗauren aure a massalacin normal ne yasa bai kawo komai a ransa ba. Sai dai haka kawai yake jin sa wani iri yau kamar wani abu na shirin faruwa da shi. Ga kansa da ke ciwo ƙasa-ƙasa amma dai sai ya daure tunda bawai ya matsa masa da yawa bane. Wani irin harbawa da dokawar ƙirji ce ta samesa a lokaci guda a dalilin jin sunansa matsayin angon da aka ɗaurama aure da amarya mai suna Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi. Shi al’ajabi ne ma ko ruɗani yama rasa ganewa. Ya dubi Ahmad da ke kallonsa yana dariya, “Kai nifa ban ganeba wlhy, wai waye haka mai irin sunana komai da komai fa”.

       Sake tuntsirewa da dariya Ahmad yayi har da riƙe ciki. Sai da yaga Smart ya turɓune fuska har yana harararsa sannan ya ɗan sassauta. Sai dai maimakon amsa masa sai ya miƙe dan yau dama ɗaurin auren biyu ne kawai ma, bayan an ɗaura na farko da ya kasance Smart da Lulu na biyun kuma aka fahimci shima dai da amaryar farko ne da wani angon, dan kuwa dai Alh. Sulaiman ne ya ƙulla, abin mamaki kuma babu shi a massalacin sai Tajuddeen kawai da gayyar abokansa. Yana jin kuma an ɗaura auren Lulu da Smart ya yanke jiki a wajen ya faɗi. Su dai mutane basu fahimci minene matsalar ba, haka ma su Abba magabatan Smart dan sai da aka tashi idonsa ya gane masa mahaifin nasa da tawagar dattijan anguwarsu. Sagade kawai yay yana kallonsu kamar television. Abba da ke kallonsa da murmushi ya ce, “Ɗan nema daina kallona ni, ko duk murnar ce ta saka sumar tsaye”.

       Dariya dattijan suka sanya har da Baba. Uncle Yousuf da ke jin ALLAH ya gama masa komai a yau ya matso ya kama hannun Smart cikin nasa ya jasa ya rungume. “FATAN ALKAIRI SURUKINA”. ya faɗa cikin kunnensa. Kamar wanda aka farkar a barci Smart ya ja nannauyar ajiyar zuciya. Cikin marairaice fuska alamar yaya haka.. yake kallon Uncle Yousuf. Shiko ya sake faɗaɗa dariyarsa da ɗan ɗage kafaɗa alamar nima ban sani ba. Coach ma rungumesa yayi yana mai jera masa addu’oi. Shi gaba ɗaya ma ya kasa iya furta komai. Sai da Ahmad yaja hannunsa gaban su Baba sannan ya motsa gaɓɓansa da ƙyar. Rissinawa sukai suka gaida Baba da ke zagaye da manyan mutane ciki harda gwamna. Abin zai baka mamakin yanda har aka iya haɗa mutanen bayan auren babu wani shiri a cikinsa. Koda yake ba abin mamaki bane idan akai dubi da girman Alh. Sufi Garko ɗin da ƙarfin ikon da yake da shi wajen manyan jihar. Sosai manyan mutanen nan suka dinga saka masa albarka kowa na jansa jiki ganin yanda Baba ya damƙe hannunsa cikin nashi shima. Daddy ma sun gaisa yana ƴar fara’arsa dai. Daga haka suka ringuɗa zuwa government house. Dan sakamako gwamna ne ya bada auren Mawaddat matsayin waliyyi yasa shi shirya liyafar cin abinci bayan ɗaurin auren. Smart dai ya zama kamar wani butun butumi. Komai ɗaukarsa yake kamar a mafarki. Ga kansa dake ƙara nauyi matuƙa har idanunsa na ɗan rinjayar ganinsa. Amma dai yanata dakewa kodan fidda mahaifinsa kunya. Dan duk da Malam Mika’il Idris Mawashi ba mai tarin dukiya bane. Dattijo ne nagartacce mai cikar kamalar da masu kuɗun dole suga girmansa da jin shakkar kawo masa raini. Shi da kansa ya biyama ɗansa sadaki naira dubu ɗari biyu. Sai dai Baba ya ce ɗari kawai zasu amsa ALLAH ya sanya albarka. Hakan ya ƙara sakama Abba jin kimar mutanen. Dan shi mutum ne mai girmama mutumtaka fiye da dukiya. A Government house mutanen da suka taru har sunfi na massalacin yawa saboda wasu sun iso a makare sai dai walimar zasu samu kasancewar sakon gayyatar ɗaurin auren yazo musu a ƙurarren lokaci dan a jiya jiyan nan da dare duk Baba yasa aka watsa shi a waya ta hanyar contacts ɗinsa dana Uncle Yousuf da na Daddy. Amma da ace shirine na musamman ai sai ma an rasa masaka tsinke. Sai dai hakan ma Alhamdullah, dan basuyi zaton taruwar mutanen kamar hakan ba amma sai gashi kamar wasa a kaso uku da suka gayyata kaso kusan biyu sun halarta bayan wanda sukaje massalacin salla kawai. Anci ansha anyi asuwaki da kaji yanda ya kamata, sai dai ango ya gagara cin komai. Ga abokansa ko nace teammate ɗinsa na ball zagaye da shi sunata masa shaƙiyanci da masa ciwon bakin jin auren a ƙurarren lokaci da sukai. Haka dai yayta daurewa har aka kammala cin abinci aka shiga hotuna. Nanma dauriyar yay tayi kasancewar duk wanda zai ɗauki hoto sai an jajubosa musamman ma manyan mutanen nan da ke nanuƙe da Alh. Sufi Garko. Shigowar lokacin sallar la’asar ne yay belinsa. Da ga salla kuma kowa zai kama gabansa……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣3️⃣

……Sam Lulu bata san wace waina ake toyawa ba. Dan yau ma dai tashi tai da ciwon kai har da zazzaɓi sakamakon mura da ta mata ɗaurin kazar kuku. Da ƙyar ta iya tashi kusan 12 da Mommy ta tasheta akan tai wanka. A sannan ne ma suka san bata da lafiyar. Bayan ta ɗan samu tai wankan ne ta sha tea da Mommy ta haɗa mata da kanta mai kayan ƙamshi sosai. Wani irin faɗuwar gaba takeji ga rashin lafiyar da ta kadata. Da ƙyar ta samu ta ɗanyi waya da Zainab dan jin yaya ake ciki a office, sai kuma Sha’aibu ɗan sanda da yay kiranta yay mata albishir ɗin cafke mijin matar nan da suka sami nasarar yi. Hakan ya ɗan faranta mata rai da jin zazzaɓin nata ma ya sauka har ta fito falo. Anan taci karo da yayunsu su Twins sun zo. Sama-sama sukai gaisuwa ita da su dan sam babu jituwa tsakaninsu. Fasa zaman falon tai ta juya ta koma ciki ranta na ƙara dagulewa. Ta rasa mitai ma ƴan uwan nata suke jin zafinta irin haka. Hira da ta samu sunayi da sauran ƙannensu har da dariya, amma ita tana fita duk suka gimtse fuska sai Suhaib da Nazeer ne suka gaisheta, sai kuma Amrah da tai mata yaya jiki. Wannan abun ya jima yana damunta, sai dai rashin riƙe abu a rai kansa ta watsar ta cigaba da al’amarin ta musamman idan tasha wani abu haka. Gadonta ta koma ta kwanta dan da jikinta yay mugun zafin zazzaɓi, barci ne mai nauyi ya ɗauketa batare data shirya hakan ba. Hakan yasa har su Abba suka fita massalaci tare da yayunta da Mubeen da su Suhaib bata sani ba. Ba kuma ta farka ba har bayan la’asar da ƴar hayaniyar da gidan ya ɗauka ya farkar da ita da ga barcin da take mai cike da mafarkin mahaifiyarta da take matuƙar bege, sai drivern ta da bata san daga ina kuma mafarkin nata ya yayo mata shi ba dan ita dai bata kwanta da tunanin ko mai kama da shi ba balle ace. A hankali ta ɗan ja tsaki da murza goshinta da yay mata nauyi. Zazzaɓin nata ya sauka, sai dai nauyin da kan nata yay mata da rashin jin ƙwarin jiki. Landline phone da ke saman bed side drawer ɗinta ta ɗauka tai kiran sashen masu aikin gidan. Batare da jiran jin waye ya ɗauka ba balle amsa sallamarsa tai umarnin ganin Iya Tabawa ta yanke wayar ta ajiye. Cikin mintuna kaɗan kuwa sai ga iya Tabawa na faman washare baki. Kallo ɗaya tai mata ta ɗauke kanta cikin bada umarni kamar yanda ta saba ta ce ta haɗa mata ruwan wanka.

         “An gama ranki ya daɗe”. Iya Tabawa ta faɗa tana nufar bathroom cike da farin cikin abinda su Daddy suka shigo da shi gidan cewar an ɗaurama Lulu aure. Harga ALLAH da gasken gaske son yarinyar take da ƙaunarta. Duk halayyar Lulu a gidan ta taka ma’aikata baisa taji ƙinta ba. Dan duk wulaƙancin da take musu hakan bai hanata ƙyautata musu randa ta so ba kuma musamman ma ita. Ba kuma komai ya ƙara girmama farin cikin ta ba sai jin wanda Lulun ta aura, dan ita sam bataga hakan komai ba duk da sauran ma’aikatan gidan na can na dariya da gulmar wai alhakinsu ne ya kamata ta ƙare da auren drivern ta. Dan su sosai abin yay musu suga da kallon cewar Lulu tayi faɗuwar baƙar tasa. Tana ƙoƙarin shiga wankan ta bama Iya Tabawan umarnin haɗa mata farfesun kifi mai yaji sosai dan Lulu na matuƙar son kifi a rayuwarta. Harta nufi ƙofar fita Lulun ta dakatar da ita.

      “Wai lafiya ne a gidan aka ishi mutane da hayaniya? Kema naga sai wani washare baki kike”.

     Iya Tabawa da murmushi ya kasa barin fuskar tata ta ce, “Muma dai bamu san mike faruwa ba Aunty, munga dai su Alhaji ƙarami (Uncle Yousuf) nata farin ciki inagama aure dai ya ƙara”.

              “What?! Uncle You ɗin ne ya ƙara aure ki kike nufi?”.

        “Bani da tabbacin hakan Aunty, hasashen dai kawai nake”.

     Tsaki Lulu taja cikin taɓe baki ta nufi bathroom ɗin cikin ƙunƙuni take faɗin, “Kai wannan tsohuwa da neman masifa kike. Haka kawai da ranar nan tsaka ace amma Aunty Saliha kishiya ai akwai ƙura. Dan koni nan na korar mata shegiya”. Daga haka ta shige.

      Ta fito a wankan tana cikin shiryawa da kaya marasa nauyi na wando da riga akai mata knocking ƙofa. “Waye?” ta faɗa tana fesa turarrukanta. Uncle Yousuf ya amsa mata da cewar shine. Ƙofar ta nufa da sauri tana faɗin, “Uncle You!”.  Amsa mata yay yana turo ƙofar ya shigo, dan haka suka kusa cin karo. Baya taja da sauri tana mai zuba masa ido. Cikin kasa danne abinda ke bakinta ta ɗan waro manyan idanunta ta da faɗin, “Oh god wai da gaske ne kenan?”.

       “Da gaske mi?”.

   Ya faɗa idonsa a kanta. Fuska ta ƙwaɓe da wani yamutseta. “Kishiyar kaima aunty Salihar mu Uncle?”. Yanda tai tambayar da wani tsuke masa fuska taso bashi dariya. Amma sai ya dake ya ce, “Eh haramunne?”.

      “Kutt! Wai da gaske ne ma?”.

   Kasa jurewa yay yanzu kam sai da ya dara. Dan a masifaffiyarta ta sake tambayar. Ya ce, “Kinga maida wuƙar Daughter ba haka bane. Ai auntynku ita da kishiya sai a aljanna”.

       “Oh har na samu relief”.

   Ƴar dariya yayi yana kaiwa zaune a kan sofa. Ya nuna mata wajen zama itama. “Kinga zauna bani da lokaci magana nazo muyi.”. ganin yanda yaci serious ya sata kaiwa zaunen cikin bashi dukkan attention nata. Shima sake gyara yanayinsa yay da nutsuwarsa ya ce, “Mawaddat!”.

     “Yes Papa”.

  Ta amsa cikin sake nutsuwa. Cigaba yay da faɗin, “Kin san daga ina muke?”.

      “Massallaci”.

  Murmushi yayi da jin jina mata kai. “Yes daga massalaci muke, sai dai bayan yin sallar juma’a an ɗaura aure. Auren kuma bana kowa bane sai naki”.

       Wani shegen dariya ta saki a lalace. Tace, “Uncle You ALLAH ka iya tsokana, sai kace wata babyn roba ”.

    Murmushinsa ya sake faɗaɗawa da gyara zamansa. “Mawaddat ba wasa nake ba. Kema kuma kin san bana miki kalar wannan wasar ai”.

      A take fara”ar fuskarta ta ɓace ɓat gaba ɗaya. Ta tsirama Uncle Yousuf ɗin ido kamar wadda tai suman wucin gadi. Fahimtar yanayin data shigan ne ya sakasa riƙo hanunta a cikin nashi yana girgiza mata kansa. “Kinga calm down sweet heart. Wannan aure ya tafi ne kamar yanda muka tsara da ke. Abinda yasa kuma akayisa yanzu ba tare da saninki ba kema shine a jiya da yamma……” ya kwashe komai game da ƙudirin su Tajuddeen da mahaifinsa ya sanar mata. Ya ɗora da hukunci baba dama abinda ya faru yau a massalaci yanzu haka ma Tajuddeen na asibiti an kwasheshi.”

        A hankali ta lumshe idanunta. Sai kuma ta koma jikin kujera ta lafe  dan ƙirjinta wani irin bugawa yake da sauri-sauri. Da’ace ta iya addu’a ita ya kamata ace ta karanto a wannan halin, sai dai kash hakan bai samu ba. Taja wasu mintuna a haka kafin Uncle Yousuf ya dawo da ita a hankalinta.

    “Mawaddat Please relax. A yanzu haka fa tare muke da Baba a gidan nan. Kuma son ganinki sukeyi. Ina so. Ki nutsu kisa hankalinki waje ɗaya dan kar kije ki canja abinda muka tsara kuma ta ƙwaɓe, dan idan Baba ya fahimci shirinmu bake ba hatta ni da Yaya da bai san komai ba sai ranmu ya ɓaci. Ki dake zuciyarki ki nuna jin daɗinki ga hukuncinsa ta haka ne kawai zai kauda kai akan ki mu samu cikar burinmu dan zuwa dare zan nemo Aliyu yazo ayi komai a rubuce ma”.

          “Uncle karfa ya bamu matsala. Wlhy guy ɗin nan yanada taurin kan masifa fiye da yanda kake tsammaninsa”.

       “Karki damu insha ALLAHU babu abinda zai faru. Komai bazai canja ba da ga yanda muka tsara in har kin yi abinda ya dace yanzu a gaban Baba ta yanda bazai fahimci komai ba”.

    Kanta ta jinjina masa muryarta a shaƙe ta ce, “Shikenan zanyi yanda kace. Amma Please bana son ganinsa yau sam”.

       Murmushi Uncle Yousuf yayi yana miƙewa. “Baki da matsala da hakan tashi kisa mayafi muje. Koma dai ki canja kayan nan zuwa atamfa haka ki lass ok”.

     Badan taso hakan ba ta gyaɗa masa kai kawai. Ya fita yana sake jadadda mata ta kiyaye dai ta kuma kula kar wanda ya fahimci halin da suke a ciki……

        ★…..

  A ɓangaren Smart kam tunda suka bar government house hannunsa riƙe yake da kansa. Tun su Ahmad na masa shaƙiyanci da wasu a cikin teammate ɗinsa da suka biyosu a motar Ahmad ɗin har suka fahimci shirun nashi bana lafiya bane. Dan duk da dama shi bamai yawan magana bane koyaya ne zai musu murmushi ko yace wani abu koda sau ɗaya ne, balle wannan ranar a gareshi ta musamman ce, tunda su dai basu san komai game da auren ba.

        “Mawashi lafiya dai?”.

   Cewar Ahmad yana gangarawa layin anguwar su Smart ɗin. Kansa ya nuna masa da hannu kawai. “Subahanallahi ciwo yake maka kan?”. Kan ya sake gyaɗa masa. Shiru motar tai na ɗan lokaci duk suna kallonsa, sai kuma suka shiga jera masa. Kusan tare motar tasu ta tsaya da ta su Abba suma. Dan haka suka firfito a tare, dole ya sake daurewa dan a cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar gidan shima ya fara tara mutane ƴan taya murna, dan al’amarin kamar busa usur zancen auren ya dinga shiga kunnuwan mutane, dama gashi juma’a ce yawancin mutane duk sun dawo gida……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣4️⃣

……..Gayyar yayunsa da ƙanne su Salim da sai da sukaje wajen ɗaurin aure suka san dawa aka ɗaura kusan ransu duk a ɓace yake, dan gani suke kamar Abban ya rufe zancen ne dan yafi son Hydar ɗin a gidan kamar yanda iyayensu kan faɗa. Komai ya sake tsaya musu a rai jin ƴar wanda ya aura da kuma Gwamna da yay waliccin auren. Zuwa walimar cin abincin ma a gidan gwamnati sai da Abba ya nuna ma wasun su ɓacin rai sukaje. Su dai su Mubarak ƙanana ko’a jikinsu, sai ma farin ciki suke ballema yau gasu a cikin government house. Sune suka fara isa gida da labarin wannan aure na bazata, dan sun riga su Abban tahowa, sune kuma suka baza batun auren a anguwar.. Smart yayi dauriyar tsayawa amsa gaisuwar mutane da taya murna kafin su shiga ciki. Sun tadda gidan a ɗan harmutse, dan kamar kowa jiran shigowar Abba yake. Shiko Abba da yasan da hakan a tsumensa ya shigo, dan haka dole kowa ta kama kanta sai dai ƴar ƙus-ƙus a ɗaki tare da yaransu dan har na ma’auri matan yau suna gida kasancewar hakan kamar ɗabi’ar yaran gidan ce duk juma’ar ƙarshen wata anan suke yini su da gayyar ƴaƴansu..

      Umarni Abba ya bama Smart ya biyoshi falonsa. Ya kuma aika Musaddiq tattaro sauran jama’ar gidan suma. Cikin ƙanƙanin lokaci kowa ya hallara har falon na neman musu kaɗan. Dan kuwa dai ALLAH ya azurta malam Mika’il Idris Mawashi da baiwar ƴaƴa. Matan ne suka shiga gaisheshi da sannu da dawowa dan sanda wasunsu suka iso shi ya fita. Ya amsa musu da tambayarsu mazajensu dama yaran duk da yasan sukam duk suna tare da su anan. Zakuma su zo gaisheshi. Duk da ran wasun su a dagule yake haka suka dinga amsawa mahaifin nasu kamar yanda suka saba. Shima ya lura da yanayin wasun su ɗin, amma sai bai damuba dan yasan iyayensu mata ne suka gama kunnosu, ya kuma san bai wuce akan wannan aure na Hydar da ya sirrinta ba. Yayi gyaran murya da sake tsare gida yana maida kallonsa ga matan nashi duka huɗu.

       “Zan fara da ku matsayinku na iyaye. Alhamdullah da farko zan fara da sanar muku yau dai ALLAH yayi an ɗaurama Aliy aure. Nasan abin zai iya zama abin mamaki a gareku har ma da ka-ce-na-ce. To bazan hana hakan ba, sai dai zan fahimtar da ku muma a haka al’amarin yazo mana. Ga mahaifiyar sa nan ita kanta sai a safiyar yau na sanar mata cewar zamu kai kuɗin auren Aliy domin iyayen yarinyar da yake so ɗin sun buƙaci haka sakamakon ɗan rikici da abokan neman auren nasa suke son kawo wa a ciki. Ni kaina kuma a yau ɗin munje ne da batun kai kuɗin aure  sai suka buƙaci kawai a ɗaura domin hakan ya zama masalaha ya kuma bama kowa kwanciyar hankali. Sosai hakan yamun daɗi, dan ganin auren Aliy a yanzu yana ɗaya da ga cikin abinda ke damuna, bayan mun dawo naso zaunar da ku na muku bayanin halin da ake ciki sai ya zam guri ya ƙure, dan haka nace bari mu bari har sai mun dawo. To Alhamdullah yanzu dai ta ƙare, shima Aliy ya shiga sahun ƴan uwansa, sai muyi masa fatan alkairi da zaman lafiya da zuri’a mai albarka kamar saura, an ɗaura aure ne kawai sai zuwa wani satin insha ALLAHU za’ai biki duk da mu hakan dai yazo mana a ƙure amma ALLAH muka riƙe mun san kuma bazai bamu kunya ba….”

         “Tofa bazawara ce kenan?”.

    Cewar Umma a gatsine. Murmushi Abba yay da kafeta da idanu, sai kuma ya janye yana jinjina kansa. “Yarinya ce budurwa ba bazawara ba, ɗiya ce ga Alhaji Isma’il Ibrahim Jiƙamshi, sannan jika ga Alhaji Sufi Ado Garko”.

      Kusan duk falon musamman matan babu wanda bai zabura da jin sunayen guda biyu ba. Dan daga Alhaji Isma’il Jiƙamshi har Alhaji Sufi Garko babu sunan da bai zama mai shura ba a cikin Kano da wajenta musamman ma shi Alhaji Sufi Garko ɗin. Ƙwarai da gaske sun girgiza har mazan a yanzu dan suma dai basu san kuma amaryar tanada alaƙa da Alhaji Sufi Garko ɗin ba sai yanzu. No wander dole gwamna yay walicci kam ashe. Ƙus-ƙus ɗin da falon ya ɗauka ne ya saka Abba yin gyaran murya, a take duk sukai tsit. Abba ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda na faɗa muku sati mai zuwa za’ai biki amarya ta tare, sai kowa yaje kamar yanda tsarin wannan gida yeke kowa ya kawo gudunmawarsa, a kuma kasance cikin shirin biki.”

         “To amma yanzu Abbansu a sati guda ɗin nan har wane shiri za’ayi? Bayan kowa yasan Hydar bai ajeba bai ba ma wani ajiya ba. Gashi ya kinkimo ƴar babban gida da su komai sunfi buƙatar ganin dozin”. Mama ce da wannan magana itama dai da alama ranta a jagule yake, dan fa jin Smart ya samo ƴar babban gida ransu fal kishi da hassadar ba ƴaƴansu bane.

        Caraf Umma ta amshe da faɗin, “Kema kike ta wannan ai ga zancen gudunmawa da yaywa yaran nan. Maganar gaskiya ba’ace gudunmawa ba kuma a irin wannan ƙurarren lokacin Abban su. Yanda abubuwa sukaima mutane yawa kowa na fama da kansa da iyalinsa, shi Hydar ɗin yasan bai shirya ma auren ba ya kinkimo ƴar masu hannu da shuni shi ba sana’a ba ba komai ba. inba dai sune zasu masa komai ba dan da’alama ma sadakin sune suka biya masa ko?”.

         Kallonsu kawai Abba yake yi, su kansu kuma a cikin yaran duk sai sukaji kunyar abinda iyayen nasu keyi kamar wasu ƙananun yara sun kasa ɓoye baƙin cikinsu. Abba ya maida kallonsa ga Ammah da tunda ta shigo kanta a ƙasa yake baiwar ALLAH. Ajiyar zuciya ya sauke da sake maida idonsa kansu Mama ɗin. “Yalwati da Yahanasu nasan dai kun san da Aliy da yaran nan duk nawa ne ko? Kuma ni ne na bada umarnin haɗo gudunmawa kamar yanda nake basu akan kowacce hidima anan gidan tunda ba yau na fara ba. A kaf ɗinsu kuma ba gori ba babu wanda Aliy bai taka rawar gani a hidimar aurensa ba a bashi da aikin yin dai. Maganar kuma sati guda yay kaɗan ba’a shirya ba wannan komai na ALLAH ne babu ruwanku. Sannan sadaki ga ƴaƴanku nan ku tambayesu a duka aurensu ni ne na biya musu sadaki, ko akan Aliy ne zan canja abinda nake tun farko?. Ƴar babban gida kuma data tsole muku ido ALLAH ne ya bashi kasancewarsa mai ƙyaƙyƙyawar zuciya da nagarta, fatanmu ALLAH ya taya shi riƙo dan shi bai auri ƴarsu dan kuɗinsu ko sunansu ba”.

        Sosai murtanin Abban ya hana kowa sake yin motsin kirki. Sai ma a cikin yaran ne maza jikin wasu yay sanyi suka shiga bama Abban haƙuri, tare da masa alƙawarin yin zaman meeting na musamman akan bikin. Albarka ya saka musu tare da sallamar kowa. Smart ne kusan ƙarshen fita, dan haka Abba yace masa bayan sallar isha’i ya samesa. Kai kawai ya jinjina masa ya ƙarasa ficewa cikin dauriya.. Fitowar tasa ta bama wasu da ga cikin ƴan uwan nasa damar tayashi murnar da suka gagara yi a ɗazun. Murmushin kawai yake musu da amsawa cikin dauriya, da ga haka ya wuce ɗakin Ammah. Ya samu Aunty Bilkisu da ƙanwar Ammah da tazo gidan babu jimawa suna tattauna abinda su Ummar sukai yanzu a gaban Abba. Yayinda su Asma’u ke ta faman murnarsu sukam finally Yayansu yayi aure shima gorin Umma ya ƙare. Gaban Ammah yaje ya zauna, yayinda Gwaggo Sa’adah ƙamwar Ammahn ta muƙe tana masa ghuɗa da kirari kasancewar sunan mahaifinsu ne ya ci, dan duk ƴan gidan su Ammah Babangida suke kiranshi ko suce Hydar, shiyyasa ma ko’anan gidan nasu Hydar ɗin ta bisa, Abba ne kan kirashi da Aliy shima wani lokacin yakance masa Baba. Idanunsa ya rumtse da sauri dan har cikin tsakkiyar ƙwalwar kansa ghuɗar nan ke ratsashi. A take kansa ya fara juyawa ya ringa ganin kamar ɗakin na juya masa shima. Ɗayan hannunsa ya kai ya ƙara dafe kan da hannu biyu. Hawwah ce ta lura da hakan, da sauri ta ce, “Yaya Hydar lafiya kuwa?”. Yanda tai maganar cikin zaburowa ya sa Gwaggo Sa’adah dakatawa, Ammah ma ta haɗiye murmushin fuskarta ta maida dubanta garesa. Aunty Bilkisu ma da ke ta faman turama dangi saƙo ta wayar Ammah ta miƙe zumbur. Ammah da ke kusa da shi ce ta samu nasarar taroshi jikinta, dan gaba ɗayansa ya tafi zai zube damma a zaune yake……

       ________________★

    Ƙololuwar ɓacin rai Alh. Sulaiman ya shiga sakamakon kiransa da akai masa cewar ga Tajuddeen a asibiti sakamako auren Lulu da mahaifinsa ya ɗaura yau da shegen tsageran yaron nan da yakema kallon abin alhaki. Abu mafi ɗaure masa kai shine ta yaya Baban yasan da shirinsa har yaje ya ɓata masa shiri haka? Ya san dai da ga shi sai Tajuddeen suka ƙulla hakan. Dan ko mahaifiyar Tajuddeen ɗin bata san komai ba akai. To kodai cikin waɗanda ya aika sumasa waliccin auren ne? Kai bayajin hakan zata kasance ai. Dan Kawu Laminu mutum ne makwaɗaici yasan kuɗin da ya shaƙa masa bazai barsa buɗe baki ya faɗama wani ba. To ko Tajuddeen ɗinne yay ɓaranɓarama a gaban wani? Shima dai hakan bai kama hankali ba gaskiya dan yasan yanda Tajuddeen ke son auren nan bazai taɓa bari wani ya samu ƙofar rusa masa shi ba. Tattare komai yay ya ajiye gefe yabar maɓoyar tasa zuwa asibiti. Dan yazo nan ɗin ne ya ɓoye saboda Baba har sai ƙura ta lafa zuwa gobe kamar yanda ya tsara idan an ɗaura aure da Tajuddeen. Lokacin da ya isa ya samu Tajuddeen ko farfaɗowa baiyi ba ma. Ga shi labari yazo masa su baba na government house ana liyafar cin abinci bayan a gabansu Jikansa ya faɗi amma ya shure saboda bai ƙaunarsa shi da ɗansa. Sosai zuciyarsa ke ƙara tafasa, yayinda yake saƙa abubuwan alkaba’i da zai rusa rayuwar Smart da duk wanda ke tare da shi. Dan a ganinsa duk shine ya ruguza masa shirinsa, sai yanzu ma yake nadamar bayyana masa fuskarsa a waccan ranar… Farfaɗowar Tajuddeen babu jimawa mahaifiyarsa ta iso, sai dai daga zuri’arsu kaf babu wanda ya leƙo asibitin dan Baba ya hana. Ya kuma tabbatar musu duk wanda yaje sai ya ɓata masa rai fiye da yanda yake zato ko tsammani……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣5️⃣

…….Shigowar Abba da Asma’u ta fita ta kira da sauran ƴan uwansa maza da basu kai ga fitaba yasa matan darewa. Tallafosa Abba yay da ga jikin Ammah da ke tofa masa addu’a a nutsenta, duk da a rikice take amma a zahirinta babu alamar ruɗewa dan mace ce kamila mai tarin nutsuwa akan komai. Faisal ne yay hikimar matso da fanka kusa da su yana faɗin, “Ku ɗan matsa a kansa yasha iska mugani”. Fita duk matan sukai a ɗakin, sai Ammah da su Umma da suka shigo. Aunty Amarya ta ce, “Ko dai a masa hayaƙin maganin nan dan yanayin nasa kamar na matsalar can ne da ke bugunsa”. Cikin gamsuwa Gwaggo Sa’adah ta ce, “A kawo ɗin sai a gwada a gani. Rushin wuta Hawwah ta ɗibo, Maryam ta ɗakko maganin a ɗakin Ammah aka saka masa, yayinda Ammah da Abba ke cigaba da tofa masa addu’a su da sauran ƴan mazan gidan. Kusan minti talatin ana abu ɗaya kafin ya fara motsawa. Sai kuma ya fara wata irin atishawa mai ƙarfin gaske. Yayi tafi sau bakwai sai kuma ya dafe kansa yana mai ambaton sunan ALLAH da faɗin, “Ammah kimin addu’a kaina kamar zai fashe. Wayyo Ammah kaina kimin addu’a”.

      Da ƙyar Ammah ta danne hawayen da suka cika mata idanu, ta kamo hanunsa cikin hannunta ɗayan kuma ta ɗaura a saman goshinsa da faɗin, “Kayi haƙuri Hydar gani nan kusa da kai ina maka addu’an in sha ALLAHU zai bari, kai dai cigaba da ambaton ALLAH”. Addu’a ya cigaba da yi a ransa, tare da sake kai hannunsa saman goshinsa ya ɗaura kan na Ammah data dafe masa… Cikin amincin ALLAH a haka aka samu barci mai nauyi ya ɗaukesa kusan gab da magrib. Abba ne ya saka ƴan mazan ɗaukarsa aka maida ɗakinsa dan zai fi samun ƙarancin hayaniya a can ɗin kasancewar nan akwai yara (jikokin gidan). Aunty Bilkisu da Hawwah ne sukaje can suka zauna da shi. Itama Ammah bayan ta idar da salla sai ta nufi ɗakin nasa da ruwan addu’oi da tayi a kofi ita da Gwaggo Sa’adah dan su Aunty balikin su samu suzo suyi salla suma……

         ★………..

    A gaban su Baba Mawaddat (Lulu) zaune bayan ta gaishe da Baba da tunda ta shigo yake Binta da kallo fuskarsa ƙawace da murmushi. Kusa da shi da ya nuna mata ta zauna takai zaune gab da ƙafafunsa. Kanta ya dafa yana mai saka mata albarka da addu’oin zaman lafiya da mijinta da zuri’a masu albarka. Saurarensa kawai take amma ba komai take fahimta ba a halin yanzu. Sai da Baba ya gama Addu’oinsa su Uncle Yousuf na amsawa da Amin sannan ya kirayi sunanta cike da kulawa. Amsa masa tai batare data ɗago ba. Bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Mawaddat ƴar Mawaddat yau kema kin zama babba mai kima da darajar da aure kawai ke Bama kowacce ɗiya mace a duniya. Dan daga yau zuwa ko yaushe kema za’a iya kiranki da suna UWA. Alhamdullah kin kawo mana mijin aure a jiya kuma a jiyan babu sanya muka saka akai mana bincike a kansa muka kuma ɗaura muku aure a yau kasancewar rayuwarsa cike take da abubuwan birgewa daban sha’awa irin wanda duk wasu Iyaye na gari zasuji alfaharin kasancewarsa ɗan su ko suriki. Na tayaki murna matuƙa da mu kammu ma ahalinki. Ina fatan zaki zama mace tagari da shima tashi zuri’ar zatai alfahari da ke da tarbiyyar da muka baki. Ina sake tayaki murna da tsintar dami a kala. Dan irin waɗan nan nagartattun yaran kamar Aliyu tamkar tsintar dami ne a kalla musamman idan mukai la’akari da lalacewar zamanin yanzu da matasanmu suka saka baɗala ta shaye-shaye da neman mata a gaba fiye da cigaban rayuwarsu. Fatanmu ki kasance mai biyya da haƙuri, Mun kuma ɗaura aurenki ne a wannan gaɓar babu shiri sakamakon son kwantar da ƙurar da ke son tashi, fatanmu bazakiga laifinmu ba. Sannan munyi alƙawarin shirya miki biki kamar na sauran ƴan baya da akayi hakama iyayenki gasu nan a shirye suke da shirya biki domin farin cikinki next week a kaiki ɗakin mijinki kamar kowace ƴar gatan dangi. ALLAH yay muku albarka ya jiƙan mahaifiyarki da namu iyayen muma baki ɗaya”.

       Uncle Yousuf ne ya amsa da Amin shi da Uncle Khamil da Uncle Amin da suka rako Baba, sai Daddy da shima yake a falon. Uncle Khamil da Uncle Amin ma sun mata tasu nasihar. Ita dai batace komai ba saurarensu kawai take. Sai dai a ƙasan zuciyarta ayyanawa ta ke, (Grandpa kenan, kuma bar wahal da kanku ko ɓarnata kuɗinku auren wata ɗaya ne kacal. Biki kuma ko kiɗan ƙwarya babu mai mana a gidan nan). Babu wanda ya lura da halin da take ciki sai Uncle Yousuf da ke hankalce da yanda take ta faman taɓe baki duk da kanta a ƙasa yake. Dariya da tausayi ta bashi, amma sai ya kanne bai nuna ko ɗaya ba a ciki har akai zaman mata nasihar da ya san ba wai shigarta take ba suka miƙe. Rakkiya tama Baba har mota, hakan ya sake bashi tabbacin lallai tana matuƙar son wannan yaro. Sai hakan ya ƙara masa kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya dan abinda yafi fata kenan. Shi babu ruwansa da wai ɗansa ko jika sai sunyi auren ƙwarya tabi ƙwarya ɗin nan. Duk wanda kika kawo ko ka kawo iyakarsa dai yasa ai bincike. Inhar yaro ko yarinya sun fito da ga gidan tarbiyya kuma suma masu itane babu abinda ya shallesa zai bada goyon baya ya kuma sanya albarka a ciki. Hakan kuma na sake ɗaga darajarsa da kimarsa ga al’ummarsa.

       Bayan wucewarsu Lulu tai komawarta ciki babu alamun wata damuwar auren tattare da ita. Daddy dai mamakin hakan yake, yayinda shi Uncle Yousuf ya san bata ɗauki abin da muhimmanci bane saboda yace mata auren contract ne. Sannan fa dama Lulu a wasu lokutan shahararriyar ƴar I don’t care ce ta bugawa a jarida duk da masifar nan tata…….

      “Ita ko damuwa ma batai ba”.

  Cewar Daddy cikin nuna mamaki yana kallon Uncle Yousuf. Ƙaramar dariya Uncle Yousuf ɗin yay da ɗage kafaɗu duka. Yace, “Nima abinda keban mamaki kenan”.

           “Amma auta baka tsoron ko wani abu take ƙullawa. Kasan fa wacece Mawaddat akan rashin ji”.

     Dariya Uncle Yousuf yayi da faɗin, “Kwantar da hankalinka babu abinda take shiryawa face sanin cewar auren na wucin gadi ne”.

         “Da wannan kuma”.

    Cewar Daddy cikin samun ƴar nutsuwa. Daga haka suka shige ciki dan ganawa da Mommy da yaran gidan suma duk da sudai duk sun san mike faruwa dan tun a jiya da dare Daddyn ya sanarma Mommy, Uncle Yousuf kuma ya sanarma ƴan biyu shiyyasa tunda safe suka iso Kano. Haka ma su Mubeen duk Mommy ta sanar musu a yau da safe. Sun sha matuƙar mamaki yanda auren yazo damma dai basu san dawa za’a ɗaura ɗin ba har ita Mommy ɗin sai da sukaje wajen ɗaurin auren ne suka sani, bayan sun dawo ɗinne sukai zaman jinjina al’amarin.

       Kallan kallo aka shigayi tsakanin Mommy da ƙannen Lulu jin wai da Smart drivern ta akai ɗaura mata aure yau. Karan farko Hussain yay murmushi har haƙoransa na bayyana bayan Mubeen ya gama basu labarin yanda take yaga Smart ɗin. Duk da ganin harar da Daddy ke masa bai iya haɗiye abinda ke bakinsa ba sai da yace, “Uncle You kuma itace tace tana son sa da kanta?”.

             Murmushi Uncle Yousuf ɗin yayi shima da faɗin, “Hussain ai matar mutum kabarinsa inji hausawa. Fatan alheri yanzu suke buƙata garemu baki ɗaya. Sannan kuma sai kuyi himmar naku auren dan zamanku haka ya ishemu. Dan haka na baku da ga nan zuwa ƙarshen shekara inba haka ba kuma mu koma Jiƙamshi a duba a cikin dangi ni babu ruwana”.

       Dariya Mubeen ya shiga tuntsurawa, su Amrah na tayashi ƙasa-ƙasa dan suna tsoron ta fita aci ƙaniyarsu. Da ga haka kuma aka cigaba da hira, ganin hirar na daɗi babu Lulu kuma Uncle Smart ya aika Suhaib yay kiranta. Koda ta fito taga har da su twins sai tai kamar zata koma. Sai dai kiran da Uncle Yousuf yay mata ya sata dole ƙarasawa. Kamo hanunta Mommy tai ta zaunar a kusa da ita tana murmushi. Ta ce, “Haba yarinyata miyasa zaki koma kuma?”.

        Kasancewarta ba mutum mai ɓoye-ɓoye ba ta ce, “Mommy to bakowan kesan ganina anan ɗin ba. Kinga babu amfanin na zauna ko”.

    Karan farko Mommy taji wani iri a ranta, dan yanda Lulu tai maganar cikin rashin sakewa zai tabbatar maka halin ko’in kula da ƴan uwan nata ke nuna mata yana cimata rai matuƙa musamman su manyan. Shi kansa Uncle Yousuf wani tunani ne ya fara zo masa a rai akan furucin nata. Daddy kuwa tuni fuskarsa ta nuna ɓacin rai, ya bi su Hassan ɗin da wani irin mugun kallo. Sai kuma ya miƙe tare da zuwa har gaban Mommy ya kama Hannun Lulu ga miƙar. “Tunda basu son ganinki sai suzo su kasheki ai Mawaddat, sannan su haɗa da ni nima” ya jata suka fice a falon. Babu wanda ya iya cewa komai sai Uncle Yousuf ne da ya kafe su Twins ɗin da kallo ya furzar da iska. “You see wannan shine abinda nake ta so ku fahimta tun ba yanzu ba. Amma sai kuka kasa fahimtar tawa saboda idonku ya rufe da cewar Yaya baya son ku sai Mawaddat. Anji shi kan kuskure yake, amma koyaya dai mahaifi sunansa. Amma ita minene laifinta tunda ba itace tace yay mata hakan ba tun bata san kanta ba. Sannan har yanzu Mawaddat bata san minene ya faru kafin haihuwarta ba, ta yaya zaku dinga hukuntata da laifin daba ita tayi ba. Duk da rashin jinta da ake gani a ranta tana matuƙar son kusanci da ku, sai dai rashin damar da kuke bata yasa ta zaɓi kaɗaice kanta bata da wani amini sai Yaya a gidan nan”.

        “Amma Uncle ai Mommy ta jata a jiki Daddy yay katanga ma hakan saboda yana ganin zata cutar masa da ƴar gwal”.  Hassan ya faɗa cikin ɓacin rai dan yanada zafi. Murmushi mai ciwo Uncle Yousuf yayi, “Yes Aunty Khareema ta jata Yaya yay ƙoƙarin hana hakan, amma ai ba Mawaddat bace ta ƙi aunty Khareema ko. Ku zauna kuyi nazari akan wannan matsalar kuma Kanada taku gudunmawar a ciki, sannan a yanzu na ƙara fahimtar a fanɗarewar Mawaddat harda dalilin ɗaukar kanta ware da kuke nuna mata. Ku manyanta ne, kun fita hankali da sanin ya kamata, ku kuma ajiye halin Yaya gefe ku zauna kuyi nazari akan duk abinda ke faruwa a tsakaninku da ita kuyi alƙalanci tun kafin kuzo kuyi nadama da ga baya”.  Da ga haka ya miƙe batare da jiran cewar kowa ba yay ficewarsa. Shiru falon kowa ya kasa cewa komai, dan hatta Mommy kalaman Uncle Yousuf ɗin sun shigeta. Sai take gani kamar itama tana da nata kamshon mai girma da bata taɓa zama wajen matsa musu canja abinda suke kallo ba yanda yake faruwa ba tunda Mawaddat dai ba ita yace Daddy yay mata irin wannan rikon ba, sannan yarinyar bata taɓa ƙin ƴan uwan nata ba, barta dai da tsiwarta sai kuma gatan da Daddyn ke nuna mata na fitar hankali sama da sauran yaran a komai na rayuwa………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣6️⃣

…….Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, duk yanda take ta son dannewa hakan na neman gagara. Ga shi Kasancewar ƴaƴanta na nan ta rasa ta yanda zatai kiran aminiyar ta su tattauna wannan ruɗani da ke neman kaita ƙasa a yinin yau. Ganin hankalin duk jama’ar gidan ya koma kan halin da Smart ke a ciki ya sata sirarewa ta koma ɗaki. Can ƙuryar ɗakinta ta shige ta rufo. Takaicin yanda wayar keta ringing anƙi a ɗauka ya sata jin kamar ta kaima bango naushi. Sake kira na biyu tai bayan katsewar na farkon. Yanzu ma har ta fidda rai da za’a ɗaga ɗin, amma jin an ɗauka ya sata sakin wata wawuyar ajiyar zuciya. Cikin haushi da ƙosawa ta ce, “Haba Hajiya Naqiba ina kika shigane ke kuwa inata kiran waya..”

       “Yi haƙuri ina falo ne da mutuniyarki, wai munafukan tazo tana faɗa min tsolon ƴar nan tata ragowar ciwo ta samu miji amma Alhaji ya ƙi saurarenta, acewarsa sai ta gama makaranta fa maganarsa ba canji”.

      “Mtsoww aikin banza. Banda haukarta ma wannan sikila ɗin ko auren tai dawo mata zatai”.

    “Hhhhh ashe kin gane Aminiya. Shiyyasa mafa ni yarinyar sam bata cikin lissafina wlhy……..”

           “Aminiya ina cikin tashin hankali wlhy yau ɗin nan, tun ɗazun na rasa taya zan kiraki ɗaki cike da Ƴaƴa kin san yau juma’ar ƙarshen wata”. Umma ta katse ƙawar tata Hajiya Naqiba.

     “Tofa mike faruwa kuma Aminiya. Ke da kin gama kame gida tsaf baki da wata matsala a yanzu, banda ma waccan shegiyar sirikar taki matar Salim na neman buɗe mana aiki itama….”

          “Aminiya masu son buɗe mana aikin ai sun ƙaru. Kin san shegen yaron da muka cimmawa da ƙyar yau Alhaji ya ɗaura masa aure……”

      “Aure kuma? Wai kina nufin ɗan wajen Hafsatu”.

    “Aminiya inba shi ba wane shegen tantirin yaro ne ke bani wahala a gidan nan. Kedai shaidace akan kuɗin dana dinga kashewa ga al’amarinsa sai da ƙyar muka samu malamin nan na zuru yay mana aikin da ya ci. Yau kuma wai sai ga Alhaji da wannan mummunar labari, abu mafi ƙona rai ka ƴar masu garin Kanon fa……” ta kwashe komai ta sanar mata har halin da Smart yake a ciki yanzu.

          Sosai Hajiya Naqiba ta jinjina al’amarin. Dan tasan aikin Malam na-zuru kam garanti ne. Cikin jimami da taya ƙawar tata takaici ta ce, “A lallai dole ki shiga ruɗani Hajiya Yahanasu. Kuma bamuga ta zama ba dole mu shiga Zuru a gobe. Ƴar gidan Alhaji Isma’il Jiƙamshi fa? Kin san kuwa wanene wannan mutum? Shahararren mai arziƙi ne wlhy balle kuma wai jikan Alhaji Sufi Garko masu juya ƙasar nan a yanda suke so. To banda masifa ma irin ta wannan hatsabibin yaron ina ma suka haɗu? Ai in har kuka bari wannan yarinyar ta tare to kun gama kaɗewa, dan Hafsatu ta gama yi muku fintinkau. Shi ko kinga ai batun wani ƙwallo ya ajiye kuma ga komai a gashe sai dai ci. Ai ko ƙasar nan bana zaton zai cigaba da zama kuma….”

          “Aminiya kina ƙara rikitani wlhy. Bakiji yanda kaina ya ƙara ɗaukar zafi ba. Yanda na tsani mutuwata haka na tsani yaron nan a gidan nan dan na jima da fahimtar son da Alhaji ke masa. Ga abinda malamin can ya faɗamin a kansa tun yana ɗan ƙaraminsa…….”

      “Kinga ki kwantar da hankalinki, kawai dai duk ma yanda za’ai kiyi gobe ki fito muje mu wajen Malam Na-zurun”.

     “To shike nan. Bari naje kar a juya ba’a ganni ba kuma a zargi wani abun kin san dai munafukan matan gidan nan musamman ma shegiyar Fatin can (aunty amarya) da take abu kamar Hafsatun ce ta haifeta, na rasa mitai mata masheranciyar take mata irin wannan biyayyar itama shegiyar ta biyu”.

             “Duk zamuyi maganinsu. Itama sai a kaita ai gobe a sabunta mana aiki a kanta kawai.”

   Sosai Umma taji daɗin wannan shawaran. Dan haka ta ƙara jerama aminiyar tata godiya sannan sukai sallama jin Hannatu ƴarta na ƙwala mata kira da ga falo…..

      (Ke kuma Umma haka kike ashe. ALLAH ya rabamu da ɓatan basirar zamowa mushrikai akan kishi da abin duniya🤦, duk abinda ka gani rubutacce ne da ga ƙaddarar mutum. Kai baka isa canjashi ko sakawa ba. Dan mi zakaita wahal da kanka da ɗorama kai zunubi ga asarar kuɗi. ALLAH ka shiryar damu dai🙏).

____________________

       A falon Daddy Uncle Yousuf ya samu Mawaddat kwance, yanda tai lamo sai ya fahimci kamar kuka ma tayi. Tausayi ta bashi, dan zuwa yanzu ya ƙara fahimtar akwai wani tabo a zuciyarta da take ɓoyewa kuma ya kamata ace sun sani. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da aro murmushi ya azama fuskarsa yana kaiwa zaune da kiran sunanta. Idanunta da ke a lumshe ta buɗe tana kallonsa. Sai kuma ta tashi zaune fuskarta har yanzu da alamar damuwa ta ce, “Uncle You sai yaushe ƴan uwana zasu daina jin tsananta ne?. Na rasa mina musu da girma haka. Na rayu ba’a cikinsu ba, kullum cikin begen son ganinsu neke a zuciyata duk da basu taɓa zuwa inda nake ba sai a hoto idan ka nuna min su. Amma sanda na iso da zumuɗin ganinsu fuskar da suka fara tarbata da shi shine na tsana. Har yanzu kuma irin wannan tsanar nake gani a cikin idanunsu bata taɓa sauyawa ba. Su Amrah ne kawai ke sakewa da ni, suma a wasu lokutan nasha samunsu suna zagina sai dai ban taɓa nuna musu na sani ba. Kodai dan ba Mommy ta haifeni ba kamar su shiyyasa basa sona….”

       Kai Uncle Yousuf ya dafe, sai kuma ya ɗago duk a lokaci guda yana girgiza mata kansa. “No Mawaddat ba haka bane ba. Amma ina so ki kwantar da hankalinki zamuyi magana a nutse. Ni yau ɗin ma naga duk kin zama kamar wata raguwa kamar bake ba. Bakin duk ya mutu kar fa Aliyu yay miki dariya idan ya ganki haka yay zaton kin karaya ne”.

     Baki ta tura gaba tana yamutse fuska. “ALLAH ya kiyaye Uncle You. Ni kawai yau bana jin daɗin raina ne. Ni bari ma na shiryo na bika wajen Aunty Saliha nai weekend a can kawai”. Kafin yace wani abu harta fice a falon. Ya buɗe baki zai kirata Daddy da ke fitowa a ɗaki yace, “Yousuf barta kuje can ɗin kawai.”

            “Yaya yanzu fa tana da aure. Kasan ko bai dace ba. Amma ina zuwa ”. Yay maganar yana zaro wayarsa. Idanu Daddy ya tsira masa cike da zargi, sai dai bai ce komai ba. Tsaf Uncle Yousuf ya lura da shi, amma yay biris ya cigaba da kiran no ɗin Smart. Sai dai har ta yanke ba’a ɗaya ba. bai gajiya ba ya sake kira. Maryam ce ta ɗaga, cikin nutsuwarta tai sallama tare da gaishesa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Yayan baida lafiya ne”.

      Cike da mamaki Uncle Yousuf yace, “Baida lafiya kuma? Aliyu fa nake nema”.

     “Eh shi ɗin”. Ta sake faɗa da ladabi. A rikice Uncle Yousuf ya ce, “Ya salam miya samesa? Yanzu fa babu jimawa muka rabu da shi. Kinga ina zuwa”. Ya faɗa yana yanke wayar. Number Abba yay kira, bugu biyu kuwa ya ɗaga suka gaisa da sakema juna bangajiya. Sannan Uncle Yousuf ya ɗaura da tambayar abinda ke bakinsa. A nutse Abba yay masa bayanin komai, tare da ɗorawa da faɗin, “Al’amarin Aliy ya fara bani tsoro a wannan gaɓar, dan in har ba shafar junnu ba to lallai dole akwai sihiri mai ƙarfi jikin yaron nan. Dan sai a yau na sake fahimtar wani abu. Halan ma auren da muketa matsa masa yayi amma yaƙi duk akwai dalili, sai yau da ALLAH ya kawo iyaka akayin kuma yazo cikin bazata shine hakan ta kasance?”.

        Numfashi Uncle Yousuf yaja mai ƙarfi. “Tun lokacin da Hameed ya bani labarinsa na fahimci makamancin hakan gaskiya. Kuma malamin nan dama ya faɗa cewar sihirine mai ƙarfi tattare da shi wanda aka ƙulle duk al’amarin rayuwarsa masu girma. Sai dai kuma addu’a tafi ƙarfin komai da kowa, wata rana duk ƙarfinsa zai zama ya warware in har aka cigaba da gayama ALLAH shi maji roƙon bayinsa ne. Kuma insha ALLAHU muna fatan warwarewar lamuranne suka fara zuwa”.

       “To ALLAH ya tabbatar da hakan Yusufa”.

     “Amin ya rabbi malam. In sha ALLAHU yanzu zan zo gidan tare da malam ɗin ku kwantar da hankalinku”.

     Bayan Uncle Yousuf ya ajiye wayar yayma Daddy bayani. Shima ya nuna alhini da jin tausayin Aliyun. Sai kuma ya ɗora da faɗin, “Maganganinka sun sani a ruɗani fa akan yaron. Har kayi masa sani irin haka dama Yousufa?”.

           “Yaya na san fiye ma da haka akan Aliyu. Sai dai yanzu bamu da lokaci, amma ka bini bashi wataran zan maka bayani insha ALLAHU”.

   Daddy bai ja zancen ba kawai ya gyaɗa masa kai da ƙara yima Smart addu’ar samun lafiya. A haka Mawaddat ta dawo ta samesu. Bai mace mata komai ba sukai ma Daddyn sallama suka wuce. Ko a hanya bai sanar mata halin da Smart ɗin ke ciki ba ya kaita gida ya ajiye. Sai dai bai shiga ba ya koma shi ita kuma ta shige cikin cike da zumuɗin son ganin Deen ɗin ta. Dan tana matuƙar ƙaunar yaron ita dai…

     Bayan sallar magrib kaɗan Uncle Yousuf da Hameed (Coach) suka iso gidan tare da Malam da sukaje har gida suka ɗakko. Har ɗakin Smart ɗin suka shiga bayan su Gwaggo Sa’adah sun fito. Malam ya ƙara masa addu’a sosai tare da kwantar musu da hankalin in sha ALLAHU komai zai dai-daita. Yau ɗin ma dai ruwan addu’oin nan ya sake basu da sake jaddada musu dage masa da addu’a shi kuma ya ƙara dagewa da yin azkar da sadaka. Har suka bar gidan Smart bai farka ba yanata barci, sai kusan ɗaya ya farka da azababben ciwon kan da dole sai da aka nemo wani ma’aikacin asibiti a anguwar saboda yanda yake ta complain kansa kansa kamar zai fashe. Dubasa yay da yi masa allura ya kuma saka masa ƙarin ruwa sannan aka samu wani barcin mai nauyi ya sake yin gaba da shi………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣7️⃣

…….*_WASHE GARI_* da asuba da ƙyar Lulu ta iya tashi sallar da Uncle Yousuf ya sa aunty Saliha ta tadata yi. Dan kuwa dai daren jiya suna gama hira da Aunty Saliha ta shige ɗaki sakamakon dawowar Uncle Yousuf gidan a gajiye ta samu sirof ɗin ta da wani ya kawo mata a gidan bayan sallar isha’i ta fita a sulale ta amso bada sanin aunty Saliha ba har kwalba uku tasha. Dan yanda kanta yau ya ɗauki zafin nan ta tabbatar sai tazo kwanciya komai zaita dawo mata a rai ta kwana cikin damuwa. Sam bata buƙatar hakan kuma. Ga shi dama abin yazo mata a dai-dai wato weekend. Dan dama fa duk weekend kusan sune ranakun da tafi ƙwalewa son ranta ta sha barcinta. Kafin a gane tana shaye-shaye sai aita ɗauka gajiyar aiki ce ke sata mahaukacin barcin da take sha. Balle ma Daddy kan hana a tadota  a cewarsa a barta ta huta. Hakan na bata dama ƙwarai da gaske ita kuma ta sha abinda take son batare da sun gane komai ba.

       Sabon barci ta sake dasawa har kusan sha ɗaya sai da Uncle Yousuf nan ma yasa Aunty Saliha tadata. Tun a yanda ta fito ya fahimci wani abu ta sha a jiyan, bai ce komai ba kan haka duk da zuciyarsa tayi babu daɗi sai cemata da yay ta koma ta shirya yana jiranta zata rakashi wani waje. Kai kawai ta gyaɗa masa da komawa ɗakinta dan tana da ɗaki dama a gidan. Ta jima a toilet ɗin kafin ta fito tanata ƙamshin shower gal mai ƙamshin tsiya, dan anan bata da turarrukan wanka duk ta ƙarar da su ta kuma manta ta kawo ta ajiye dan bata iya cikakken sati biyu batazo nan ta kwana ba ko yin weekend. Tana tsaka da shiryawa Deen ya shigo. “Akku mai bakin magana kenan”. Ta faɗa tana kallonsa. Ai ko yay zaman dirshan ya fara tsiyaya mata surutu itako tana biye masa dan kaf ƙannen nata tafi ƙaunar yaron fiye da kowa. Shima kuma yana son aunty Lu ɗinsa. Sai da ta gama shirinta tsaf cikin doguwar riga ta atamfa da tai masifar lafe mata a jiki kamar wadda akaima fenti. Dan Lulu koda ta saka kayan hausawa irinsu lass atamfa material zaka samesu dai babu wani ɗinkin mutunci a tare da su. Shiyyasa ma kayan basa wuce fitet gwan ne. Dan ko skert da riga ba sosai ta cika yi ba, inma tayin zaka samu suma dai sai sun mata ɗamm kamar zatai nishi su yage. Kasancewar kuma tana da ƙyaƙykyawar sura sai sukan mata ƙyau kamar an haliccesu a jikin nata ne. Dan telan nata kam ƙwarone wajen iya ɗinkin shegantaka. Ba kuma kowa ya haɗata da shi ba sai Nadiya. Yau ma ko takan ɗan kwali ba’abi ba dan dama Amrah ce a mafi yawan lokaci kan mata ɗauri idan tai irin wannan dress ɗin. Sirrin mayafi milk color da ya shiga da zanen atamfar ta yana kawai bisa kai aka ɗora ƙaton google tare da dogayen takalmanta. Dan ƙyau kam tayi ƙyau ga wani mahaukacin ƙamshi mai ɗaukar hankali na tashi. Uncle Yousuf bai fito ba harta kammala breakfast da ba wani na kirki taci ba. Dan shaye-shaye ya gama cinye Lulu ko abincin kirki bata iya ci a rayuwarta. Barta da son cin chocolate kamar shazumamu, dan ko a handbags nata baka rabata da su bayan ƙwayoyinta na shaye-shaye. A tare aunty Saliha da Uncle Yousuf suka sakko da ga sama. Dan haka su duka suka zuba mata ido. Aunty Saliha ce ta fara faɗin, “Babyn Uncle badai da kayan nan zaki fita ba musamman ma ɗan mayafin nan?”.

        Sosai mamakin furucin aunty Saliha ya sata waro idanunta manya da suka juye. Sai kuma ta kalla kanta. Dan tasan dai ba yau ta saba fita a kahaba ai. “Mamy miye laifin kayan nan kuma?”. Ta faɗa fuska a turɓune. Murmushin aunty Saliha tayi da faɗin, “Haba dai Mawaddat ai yau ba jiya bace. Ko kin manta yanzu ke matar aure ce”.

       Wani mugun yamutse fuska tayi dan ita tama manta da wani batun auren. Musamman da ya kasance abinda tasha a daren jiyan ya mantar da ita duk wata damuwarta. Kamar Zatai magana sai kuma tai shiru jin Uncle Yousuf yay gyaran murya da faɗin, “Kinga barta kawai muje ai a mota ne, kuma babu inda zata fita sai a can”.

     Sosai aunty Saliha ta zubama mijin nata ido da mamakin abinda ya faɗa. Dan abu ne da batai zaton ji daga garesan ba sam. Kasa sake magana tai har suka fice Lulu na mata bye ita da Deen da ya maƙale zai bita. Ta ja ajiyar zuciya da faɗin, “Ai masa sannu sai kun dawo”. Da kai kawai Uncle Yousuf ya amsa mata yana ficewa. Yasan abinda yay ɗinne ya ɗaure kanta. Sai dai shima yanada hikimarsa tayin hakan bawai bai san abinda yake yi bane.

        A motar tuƙinsa yake tayi, yayinda ita da Deen suketa surutunsu da dariya. Dan indai Lulu da Deen ne kam babu mai shiga tsakani. Sai ya ƙulleta da haushi ta mammakesa da kiransa mai shegen surutu kamar akku. Sun tsaya a wani ƙaramin super market Uncle Yousuf ɗin ya fita shi ɗaya. Bai jima ba ya dawo, sai kuma a wajen masu fruits, nan kam da ga motar ma yay bayanin abinda yake so aka kawo masa ya bada kuɗin suka cigaba da tafiya. Lulu dai bata tambayi ina zasuje ba. Hasalima hankalinta gaba ɗaya naga Deen ne. Sai da motar ta tsaya ne sannan hankalinta ya dawo ga inda suken. Kallon anguwar take a ɗan yamutse, duk da ba wani datti bane ko makamancin hakan, hasalima titi ne shimfiɗe da ya miƙe samɓal kasancewar gidan su Smart na a farkon shiga layinne. Sai dai yanayin gine-ginen da kai kawon mutane dana ababen hawa riiiii yasa zaka tabbatar dai irin tamu ce dangin malam Shehu….

       “Papa nan fa?”

   Cewar Lulu a gatsine.

Maimakon bata amsa wayar da yake dannawa ya kai kan kunne. Ta daiji yana amsa gaisuwa, sai dai bata fahimci mi ake cewa da ga can ba. Sai kuma taji Uncle Yousuf ɗin na cewa, “Kai dai kaɗai ne a ɗakin ko? Okay gani nan shigowa”. Daga haka ya yanke wayar tare da buɗe murfin yace, “Oya ku muje”.

        “Uncle…..”

    “Shiiiii…” yay saurin katseta tare da mata alamar zip a baki. Dole ta haɗiye abinda take son fadar dan babu alamar wasa akan fuskarsa. Shi da kansa ya kwashi ledojin, ita kuma ta fito riƙe da hannun Deen tana ta faman yamutse fuska. Sauƙin ma babu kowa a ƙofar gidan. Wanda ke iya hango su kuma ba sosai suke iya ganinsu ba duk da harda masu leƙe saboda son gulma irin ta mutane. Soron ta dinga bi da kallo duk da shima dai fes yake gashi kuma lailaye da sumintinsa. Hakama koda suka shigo gidan ko’ina fes babu wani datti, ga gidan shiru babu yawan hayaniya sosai dan yaran sun wuce ismaliyya, sai ma matan anguwa da wasu a dangi dake ta faman shigowa yin ALLAH ya sanya alkairi da auren Smart ɗin da ba’a san da shi ba. Sai kuma wanda suka san baida lafiya na ɗorawa da jajanta yaya jiki musamman maƙwafta. Anan dai ta inda suke basu haɗu da kowa ba har suka shige sashen ɗakunan samarin gidan da ke a farkon shiga. Anan sun ɗan haɗu da wasu. Bakowa bane kuma sai Mubarak da kema Smart wankin kayansa na ciki, sai Abdull a gefensa yana kallon film a waya da eirpiese a kunnensa. Mubarak ya shiga musu sannu da zuwa cikin girmamawa dan ya gane Uncle Yousuf, itako Lulu dama kallo guda tai musu ta ɗauke kai gefe a ranta tana ƙunƙunin ina ne nan Uncle You ya kawosu. Duk da dai gidan babu wani makusa tare da shi a ɓangaren tsafta a ginensa dai na masu ƙaramin ƙarfi ne. Ita ba hakanne ya dameta ba, kawai bata cika son zuwa irin wajejen nan bane, shiyyasa ko aikinta ya ratsa da hakan zaka ganta cikin rashin sakewa da son a gaggauta abar wajen. Abdull da Mubarak ya zungura shima ya shiga gaishesun. Duka dai Uncle Yousuf ne ya amsa da tambayarsu ko Aliyu na nan? Duk da yasan yana nan tunda dai yayi waya da shi. Sun amsa masa da girmamawa Abdull ya tashi yay musu iso.

        Tunda Uncle Yousuf ya ambaci Aliyu ta kafesa da idanun son jin ƙarin bayani, sai dai bai kulata ba yay gaba dole suka bisa a baya. Yana zaune a saman katifarsa da ƙarin ruwan da doctor ya ƙara saka masa babu jimawa saboda rashin ƙarfin jiki da ya tashi da shi. Wando ne 3 quarter a jikinsa da ƙaramar t-shirt data kama masa jiki sosai. Ainahinsa na tsayayyen mutum ya fito sosai. Fes ɗakin yake ga ƙamshin turaren wuta mai daɗi da Maryam ta saka masa bayan ta share. Gefensa kaɗan flaks ɗin shayinsa ne da cup da ya sha sai kayan tea a wani basket mai ƙyau harda bread alamar dai nan ɗin ne wajen ajiyarsu. Sai kuloli biyu da jug mai riƙe zafi da aka dama masa kunun gyaɗa. Sallamar Abdull da ta Uncle Yousuf ta sashi ɗago idanunsa da ke kallon tv ya zubama ƙofar tare da amsawa. Abdull ya fara shigowa da faɗin, “Yaya Smart baƙi ne”. Kalmar baƙin ta bashi ɗan mamaki, dan shi a tunaninsa Uncle Yousuf ɗin ne kaɗai kasancewar su Daddy basu jima da tafiya ba su. Kafin ya kai ƙarshen tunaninsa Abdull ya gama ajiye ledojin da ya amsa a hannun Uncle Yousuf Deen ya shigo, Uncle Yousuf biye da bayansa Lulu a ƙarshe. Harga ALLAH sai da gabansa ya faɗi, bawai na tsoro ko makamancin hakan ba, shi dai kawai ya samu kansa da jin bugawar ƙirji. Sai dai kuma abinda bai sani ba bashi kaɗai ba. Ita kanta Lulun sai da nata ƙirjin ya harba. Hannu ya miƙama Deen yana faɗin, “Welcome my little handsome”. Cike da farin ciki Deen ya nufesa shima yana murnar ganinsa. Zama Uncle Yousuf yay a sofa ɗin ɗakin ƙwara ɗaya yana murmushi, yayinda Lulu ta wani cakuɗe fuska da yamutse ta duk da taji shock ɗin ganin inda Uncle You ɗin ya kawo ta ta danne, dan tunda tai masa kallo ɗaya a yayin shigowarsu bata sake ba.

          Smart da ke sauraren surutun Deen da ya karaɗe ɗakin ya dubi Uncle Yousuf cike da girmamawa ya ce, “Uncle Barka da safiya”.

      Shima cike da kulawa yake kallonsa da tausayawa. Amsawa yay da “Barka dai Aliyu yaya jikin naka?”.

       “Alhmdullah ai na miƙe”.

   “Kana dai dauriya Aliyu ga shi harda su ƙarin ruwa. ALLAH ya baka lafiya yasa kaffara ne”.

    “Amin ngd”.

Ya faɗa can ƙasan maƙoshi yana bin Lulu da ta dogare tsaye da kallo ƙasa-ƙasa. A take wani abu ya tokare masa maƙoshi akan shigar jikinta. Lallai yasan akwai babban yaƙi a tsakaninsu. Dan shifa bazai yarda da wannan shigar shegantarkar ba gaskiya. Uncle Yousuf da shima ya juya yana kallon Lulun ya nuna mata gefen katifar yana faɗin, “Zauna mana kikai mana tsaye a kai Mawaddat. Ba kuma kiga Aliyu babu lafiya ba?”.

       Kamar zata fasa ihu taji, ta sake yamutse fuska da ɗaureta a taƙaice ta ce, “Uncle nan ma it’s ok”. Sai kuma ta dubi Smart fisha cike da gatsali ta ce, “Sannu fa”…….✍️

        *_Kuma sannu fa🙋 dangin Smart 😂🤣🤩. Dangin mu Lulu’s team Barka da rana😚😘😉._*

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣8️⃣

……..Bai nuna ma ya jita ba balle ta samu amsa. Sai ma sake tattara hankalinsa da yay ga Deen. Uncle Yousuf ne yay mata nunin ta zauna cikin harara. Zaunen ta kai a ɗofane gefen katifar kaɗan badan taso ba. Bayanin da Smart ke masa na cewar su Daddy sunzo da twins da Mubeen har da su Suhaib sun dubashi babu ma jimawa suka wuce ya sashi maida hankalinsa garesa.. har cikin rai yaji daɗin hakan, dan baiyi zaton Yayan nashi zai yi wannan abin kirkin ba. Da ga haka suka cigaba da ƴar hira jefi-jefi. Kusan mintuna goma Lulu dai na zaune tana bin ɗakin da kallo ƙasa-ƙasa, sai dai duk ta matsu su wuce amma taga Uncle Yousuf baida niyyar ma hakan. Dan hankali kwance suke hirarsu kamar ma sun manta da ita a ɗakin. Deen kuwa yay matashin kai da ƙafarsa yana buga game ɗin ball da yace ya kunna masa dama shine tushen amintakarsa da yaron tun farkon fara aikinsa. Kiran wayar Uncle Yousuf da akai ta katse musu hiran, tashi yay ya fita a ɗakin domin amsawa.

      Shiru ɗakin ya ɗauka baka jin komai sai hayaniyar game ɗin da Deen ke bugawa. Dan tvn ma da ke aiki dama ƙasa-ƙasa ƙararta take. Sosai yanzun kam ya zuba mata ido duk da iya bayanta da ɗan gefen jikinta zuwa fuska kawai yake iya gani, ƙasa-ƙasa yay ƙwafa da ɗaukar ƙaramar wayarsa da ke gefe yay ɗan danne-danne ya kai kunne. Ana ɗagawa da ga can a cinkunshe ya ce, “Bama Nasreen ta kawo min hijjab”.

        Da mamaki Maryam ta ce, “Yaya Hydaar hijjab kuma?”. Ƙitt ya yanke kiran batare da ya amsa mata ba. Kafin ya ajiye wayar kira ya shigo, Uncle Yousuf ne dan haka ya ɗaga. Kafin ma yace komai da ga can Uncle Yousuf ɗin ya ce, “Aliyu am sorry ina ɗan zuwa bazan jima ba uzirin gaggawa ne”.

      “To Uncle ALLAH ya tsare sai ka dawo”. Da ga haka ya ajiye wayar. Dai-dai nan Nasreen tai sallama. Duk da ƙarancin shekarunta bata shigo ba sai da tace, “Uncle in shigo?”.

     “Eh Angel”.

Ya bata amsa idonsa a kan ƙofar. Lulu da muryar yarinyar ta ɗauki hankalinta itama ta zubawa ƙofar ido. Sai ko gata ta shigo hanunta ɗauke da gogaggen hijjab fari da keta tashin ƙamshi. Ɗan tsayawa tai tana ma Lulu da ta zuba mata ido kallon rashin sani. Sai kuma ta ce, “Aunty ina kwana”. Batare data jira amsawarta ba ta nufi Smart, sai dai tana tafiyar tana ɗan waigowa ta kalli Lulun, dan ita dai ƙaton gilashin data toshe fuska ne mafi ɗaukar hankalinta. Karan farko Lulu ta saki murmushi tun shigiwarta ɗakin, sai kuma ta sa hannu ta cire gilashin dan sosai ƴar yarinyar ta tafi da hankalinta. Kodan basu da baby girl kamarta a gidansu ne oho. Sanda su Afrah suke kamarta kuma bata Nigeria. Zamanta ta gyara ta yanda zata fuskanci Nasreen da ƙyau, hakan kuma sai ya bata damar fuskantar Smart, dan ta fuskanci katifar ne kai tsaye shi kuma yana a gicciye ne.

       “Baby Girl how are you!”.

   Ta faɗa tana kai hannu ta kamo na Nasreen da ta gama miƙama Smart hijjab ɗin da ta kawo. Yarinyar sai da ta kalli Smart fuska a ɗan ƙwaɓe, ya ɗaga mata kai ciki lumshe idanu alamar taje sannan ta dawo da kallonta ga Lulu a hankali ta ce, “I am fine”.

   A zuciya Lulu tace (tofa ashe tana jin turanci) a zahiri kam sai ta matso ta jikinta. Ga dai yarinya fess kuma ƙyaƙyƙyawa, amma batai zaton samunta wai tana jin yaren turanci ba. da turancin ta sake tambayarta sunanta. Nan ma ta amsa mata tsaf, ta tambayeta shekararta nawa, ajinta nawa kuma a makaranta. Nan ma ta bata amsa dai da turancin. (Ikon ALLAH) ta sake faɗa a zuciya. A karan farko kuma ta dubi Smart da ya zuba musu idanu. Da farko dai magana tai niyyar yi, sai kuma tuna dawa take a ɗakin ta fasa dan yanda ya zuba musu ido ga kayan jikinsa da haka kawai suka sakata jin wani iri, ɗauke idanunta tai da ɗaukar Nasreen cak ta maida saman cinyarta ta zaunar. Nasreen ta kallesa a ɗarare ta ce, “Uncle wacece ita auntyn nan ban santa ba?”.

      “Kema wacece ai bamu sanki ba?”. 

   Cewar Deen cikin tare numfashin Nasreen cike da haushin hawa masa cinyar Aunty Lu da tayi. Aiko Nasreen ta balla masa harara shima ya rama yana kaina ƙafarta tsunguli. Doke masa hannu Lulu tai da faɗin, “karka taɓa min Baby”. Baya yaja yana tura baki. Smart ya riƙosa yana murmushi. “Kaga ƙyalesu kaima ba gaka da ni ba”. Dariya yaron yay da faɗin, “Yes Uncle” sai kuma yayma Nasreen gwalo. Itama ramawa tai da faɗin, “Ai dai Uncle ɗina ne, kuma yafi so na”.

     “Mai ƙarya yafi sona. Ko Uncle Smart?”.

Deen ya faɗa kamar zai yi kuka. Murmushi Smart yay masa da gyaɗa kai. Cikin raɗa ya ce, “Ai namiji na namiji ne, mace kuma ta mace. Itama ga aunty ta samu. Kaga 1-1 kenan. Dan haka kuyi gaisuwa banda faɗa”. Dariyar jin daɗi Deen yayi, tare da miƙama Nasreen hannu. Sai yarinyar ta maƙe kafaɗa da faɗin, “Halamun ne gaisawa da maza, a islamiyya an faɗa mana duk mai gaisawa da maza za’a sashi wuta. Ka gaisheni dai a haka. Ko aunty?”.

       Matuƙa gaya Nasreen ta burge Lulu, fuskarta da murmushi mai ƙayatarwa ta gyaɗa mata kai. “Hakane sweet heart”. Cikin jin daɗi Nasreen tace, “Kaji ko”.

    “Ai nima an faɗa mana a Islamiyyar mu”. Cewar Deen shima. “Lah da gaske? Zo muje to kaga littafaina”. Nasreen ta faɗa itama. Babu musu Deen ya miƙe yana ajiyema Smart wayarsa akan jiki. Itama sai ta tashi suka fice a tare.

            A hankali Lulu da ke binsu da kallo cike da sha’awa ta wani lumshe ido fuskarta da murmushi har sannan. Idanunsa masu kaifi ya zuba mata, sai kuma a hankali ya motsa lips ɗinsa wajen faɗin, “Kin fara tunanin kema nan da 5years kina da kamarsu ne?”.

     Idanun ta buɗe da sauri a kansa tana haɗiye murmushin fuskarta. Sai kuma ta balla masa harara tare da ƙoƙarin miƙewa. Sai dai yanda rigar tai mata masifar ɗam-ɗam a jikin yasa sai da tai ƙoƙarin dafa kujera. Fuska ya sake tamkewa da miƙo mata hijjabin. Batare da ya bata damar cewa wani abu ba duk da ya fahimci akwai abin faɗar a bakinta ya tareta da faɗin, “Haramunne matar aure ta fito a shiga mai bayyana ainahinta ga wasu, kai koda ma mara auren ce. Dan haka ki kiyaye inada kishi mai zafi. Wannan kuma ya zama first and last dan ban shirya rabarma kowanne sankaran ido ba, duk abinda akace nawa ne to nawa ɗinne ni kaɗai koda bana ra’ayinsa”.

        Tuni wani irin tuƙuƙin takaici ya maƙure maƙoshin Lulu. Cikin kaushin murya da jifansa da wani malalacin kallon sama da ƙasa ta ce, “Kai a matsayin wa? Da ka isa hanani yin abinda yake ra’ayina!”.

           “Ni a mijinki da ya biya sadakinsa”. Ya bata amsa cike da gadara da kaushi ga idanunsa da ya wani tsatstsareta da su kamar zai cinyeta.

    Rasa abin faɗa dan takaicin da ya ƙulleta ya sata faɗin, “Mtsoww! To baka isa ba. Kayi tsararo Shash…..”

      Bata kai ƙarshe ba ya tareta da faɗin, “To ke da kike jin kin isa ki sake sakawar ki fito ɗin zan tabbatar miki isar tawa kuwa.” ya ƙare magana yana jefa mata hijjab ɗin a saman cinya ya maida hankalinsa ga cire ruwan da ake ƙara masa dan ya ƙare. Mamaki ne, ko takaici, ko tsoro ne ya saka Lulu yin sagade tana kallonsa oho itama bata gama tantancewa ba. Idanunta sunyi masifar kaɗawa ga tarin masifar da take tattarowa na mata kai kawo a ƙirji. Ƙarasa miƙewa tai tana hucin bala’i, hakan yasa hijjabin ya faɗi ƙasa. Shima miƙewar yay duk da baya jin ƙarfin jikinsa, sai kawai ganinsa tai a jikin ƙofa yana saka mata key”.

      “Kai wai mika ɗauki kanka ne?”.

   “Duk yanda zuciyarki ta baki”.

“Mtsoww banda lokacin ka ban hanya na wuce”

       “Idan kinbi abinda nace kenan. Saɓanin hakan na nufin cigaba da zama a ɗakin nan matsayin kinzo ke nan”.

       “Mtsoww kana buƙatar ganin likita. Wlhy kaban hanya kona illataka”.

     “Muyima juna illa dai. Dan wlhy idan kinga kin bar ɗakin nan to kin saka hijjab kuwa. In ko ba haka ba kimayi kiran waya gida tun yanzu a fara tattara miki kayanki a aiko miki”. Ya na gama faɗa ya bar wajen ƙofar yana zira keys ɗin cikin aljihun 3 quarter ɗinsa, sai ma ya shige toilet abinsa. Karo na biyu kenan da take jin an mata wulaƙanci mafi muni, randa ya kaita dawanau da kuma yau. Wai ita illiterate drivern nan nata zai ce ma sai ta saka hijjab sannan ta fita a ɗakinsa. Uncle You duk ya ja mata wannan rainin da tozarcin. In ba haka na velleger ɗin nan ko’a hanya yama isheta kallo ne bare har ya kalla cikin idonta wai ya bata umarni. Lallai dole ne ma wannan drama ɗin ya tsaya a haka. Dan bazata iya wannan auren contract ɗin ba kuwa…..

        Motsin fitowarsa ya katse mata tunani. Ta buɗe idanunta da suka gama kaɗewa da ɓacin rai ta ɗan bisa da kallo. (Ƙaton banza) ta faɗa a zuciyarta tana mai kauda idanun nata da ga kansa. Saman katifarsa ya koma ya zauna, jug ɗin kununsa ya buɗe ya zuba a cup, sai kuma yasa sugar kaɗan da madara ya juya. Jan jikinsa yay baya ya zauna da ƙyau ya fara shan abunsa hankali kwance tare da ɗaukar wayar tasa ya fara sana’ar buga game ɗin ball tamkar ma ya manta da ita ne a ɗakin.

    Fiitt yaji an warce wayar. Sai ya ɗago a ɗan zabure ya kalleta yana wani ɗan buɗe baki. Harara ta watsa masa kai kace Luulu eyes ɗin nata zasu zubo ƙasa ne. Kansa ya shafa yana wani ƙasa-ƙasa da nasa idanun. “Madam ni fa hararar nan tana sani tunanin kamar nayi wani abu, gaskiya in dai ana son a rabu lafiya to a daina, kin san abinka da ba sabin ba tuzuru da mata”. Ya ɗan sake ɗago ido ya kalletan sai kuma ya maidasu ƙasa kamar mai jin kunya.

       Iya matuƙar kunnuwa kam Lulu ta kai maƙurar kunnuwa. (Mi wannan abin yake nufi?) Ta ayyana a zuciyarta, tsaf kuwa ta fahimtar da ita inda ya dosa. Wani irin waro idanu tai da faɗin, “What! Wait! Wait! Wai mi ma kake nufi?!”. Tsabar yanda take jin masifa da ɓacin rai takaicinsa jikinta har wani tsuma yake yi. Ya samu yanda yake so, dan kuwa ta kunnun fiye ma da yanda yake buƙatar. Idanun ya sake ɗagowa ya kalleta cikin son sake kaita maƙura ya ce, “Ni fa Madam ina jin kunya ne, amma idan kince na nuna miki a aikace sai na rufe ido, kema Please ba sai kin kalle ni ba sai ma mu kashe fitil……”

      Wani irin mugun wawura ta kaima filos ɗin saman sofar ɗakin ta shiga jefa masa su ɗaya bayan ɗaya. Hannu ya sa ya dinga kare kansa. Ta ce, “Kai har ka isa ma yin wannan tunanin a kai na, har abada kai gaban abada ma ƙazamin yatsar hanunka ma bai isa zuwa ko kan veil ɗina ba ma illiterate velleger!”.     

      Dariyar da ke neman kufce masa ya keta faman dannewa. Dan muryarta har rawa ya ke na matsanancin takaicinsa, filos ɗin da ta gama loda masa a jiki da jifa ya shiga janyewa yana faɗin, “Ba sai kin ƙirƙiri hanyar maidani asibiti ba. Ni dai ina tsoratar miki ganin aikin jahilin baƙauyen nan a aikace. Dan kin san mu idan muka ɓalle ba’a iya taro mu saboda ƙazamin hannun nan da wahala idan zaiji bari fa. Sannan ki bar fassarani in da banje ba karki lalatama Ammah yaro tun ban tafasa ba ki ƙona ni Aliyu ba inda kike nufin na nufa ba”……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣9️⃣

__________________

___________________

…….Banza ta masa yanzun kam, dan ta tabbata ta cigaba da kulashi ƙarshenta fasa masa kai zatai kawai ya baje a ƙasa ko zata samu sassaucin tuƙuƙin da zuciyarta ke mata. Ta fara takaicin daɗewar Uncle Yousuf. Wayarta ta ɗauka tai kiransa, bugu biyu kuwa ya ɗaga. Muryarta na nuna alamar ɓacin ran da take ciki ta ce, “Papa wai kana ina?”. Ya fahimci ranta a ɓace ya ke, dan haka ya bata amsa da “Gani nan a hanya”.

     “Papa bama ka nan?” ta faɗa a shagwaɓe, batare data jira cewarsa ba ta cigaba da faɗin, “ALLAH idan bakai sauri kazo ba zanma mutumin nan duk abinda zuciyata ke ayyana min na tsanesa”. Ƙitt ta yanke kiran kafin ma Uncle Yousuf ɗin ya samu damar cewa wani abu. Smart dariyarsa ya ke kwasa a zuciya, a zahiri kam ya fuske yana shan kununsa idonsa a tv. Ring ɗin wayarsa ya sashi kallar wayar dan tana a wajenta har yanzun. Itama wayar take kallo a yamutse cikin kuma harara. Sai dai bata da alamar bashi….

      “Ni dai ki daina hararar min waya karta fashe ba kuma kuɗin sayen watace da ni ba gaskiya” yay maganar yana miƙo hannu ya ɗauka. Hararar da take ma wayar ta maida a kansa. Sai kuma tai ƙwafa dan tayi alƙawarin bazata sake tanka masa ba. Amma zai gane kurensa dan sai ta koya masa hankali. Kiran Uncle Yousuf ɗin yay back dan har wayar ta riga ta katse. Yana ɗagawa da ga can ya ce, “Aliyu su sameni waje ba sai na shigo ba anjima zan dawo in sha ALLAH”.

     Cikin girmamawa ya amsa masa da to. Yana ajiye wayar ya dubi hijjab ɗin da ta jafar saman katifar sannan ya kalleta cikin komawa serious. “Kin shirya tafiyar ne ko nace masa ya je kawai ke kin tare?”.

         “ALLAH ya isa tsakani na da kai”. Ta faɗa cikin tare masa numfashi. (Sai dai fa ALLAH ya isar) shima ya faɗa a zuciya. A zahiri kam sai ya ƙara ɗaukar hijjab ɗin ya miƙa mata baice komai ba. Sai da taja kusan minti ɗaya tana zabga masa muguwar harara sannan ta warce hijjab ɗin da ga hannunsa. Dan zuciyarta ta gama bata shawarar kawai ta saka ɗin ta bar ɗakin maganinsa kuma tayi da ga baya. Sannan ko mi Uncle Yousuf zai mata sai dai yayi yau ɗin nan sai an warware wannan auren dan taga raini ya ke son haddasa wa tsakanin ta da drivern ta. Baba kuwa zata fito ta faɗa masa gaskiya idan ta tubure dai ai dole ya barta. Karan farko a rayuwarta da ta saka hijjab bayan sakawar yin salla. Amma da sunan fita waje wai ta suturta jiki abune da bai taɓa faruwa ba koda da ga ɗakin barcinta ne zuwa falo kuwa. Yako mata matuƙar ƙyau duk da iyakarsa gwiwa, ga shi kuma mai hannu. Ƙamshin da yake na turaren wuta da aka turara masa yay matuƙar saka mata nutsuwa. Shima a hankali ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya acan ƙasan maƙoshi yana kallonta ƙasa-ƙasa. Sai dai yayi kamar ba kallon nata yake ba har sai da ta balla masa harara da faɗin, “Malam sai ka buɗe ai ko” cikin jan tsaki ta ƙare maganar.

       Ɗagowa yay da ƙyau ya dubeta. Da ace zata yarda hoto zai mata, amma yasan son yin hakan wani sabon yaƙi ne kuma. Dan haka ya shanye maitarsa ta son yin hoton ya miƙe batare da yace komai ba ya nufi ƙofar. Koda ya buɗe ya bata hanya sai da ta zuba masa hararar nan dai da jan tsaki a kausashe ta ce, “Sai na koya maka hankali wlhy” sannan ta fice. Wani shegen murmushi ya saki da kai hannu ya shafo kansa yana binta da kallo. Sai da ya ga ta ɓacema ganinsa yay ƙaramar dariya da faɗin, “Mu koya ma juna dai ƴar madara” ya ƙarasa fitowa ya bita duk da baya jin ƙarfin jikinsa.

      Tunda ta fito Uncle Yousuf yay wani sagade yana kallonta kamar wata sabuwar halitta. Aiko ta ƙara ƙullewa da haushi. Fuuu ta wuce ta buɗe motar ta shiga batare data tanka masa ba. Hannu ya kai ya tare bakinsa dan dariya ke neman kufce masa. Dai-dai nan Smart ya fito. Jin jina👍 yay masa da hannu yana wani kashe ido ɗaya. Smart yay murmushi kawai da ɗan shafa kai, cikin basarwa ya ce, “Uncle sannu da dawowa”.

         Ƙasa-ƙasa Uncle Yousuf ya ce, “Ya akai ta saka hijjab?”.

      Yanzu kam ƙaramar dariya Smart yayi, sai dai kafin yace wani abu ta katsesu da faɗin, “Papaaa!”. Yanda taja sunan kamar zatayi kuka ya sashi faɗin, “Sorry Baby gani nan zuwa”. Shi dai Smart dariya suke bashi ma. Buɗema Uncle Yousuf ɗin yay yana faɗin, “Deen ya samu Nasreen sai dai anjima na kawoshi ayi haƙuri”.

           Cikin rashin damuwa Uncle Yousuf ya ce, “Oh to bara mu kama hanya. ALLAH ya ƙara lafiya you are the best Son”.

      Murmushi Smart ya sake yi yana ɗan kai dubansa ga Lulu. Ta ɗauke kanta gefe irin ma bata buƙatar kallonsu ɗin nan. Godiya ya ƙarama Uncle Yousuf ya rufe motar yana matsawa gefe har sai da ya ga wucewarsu sannan ya koma cikin gidan yana dariyar ƴar balaja’un tasu. Dan ba yace tasa ba tunda ance masa anma fasa auren.. yana shiga ɗakin da gyalenta ya fara cin karo, da alama zamewa yay ya faɗi sanda take saka hijjab ɗin batare data sani ba itama. Hannu yasa ya ɗauka ya ɗan jujjuyashi, ƙamshi yake na fitar hankali dan Lulu bata san sassautama turare ba, gashi kuma da kusan kala bakwai take amfani. Iska ya ɗan furzar da buɗe drawer ɗinsa ya jefa gyalen sannan ya zo ya kwashe filos ɗin da ya sha jifa ya maida saman kujerar ya koma kan katifar ya kwanta shiru kamar mai barci…….

     ____________★

       “Dama sai da na faɗa muku wannan yaron sam baiyi kama da driver ba amma kuka ƙi yarda. Yanzun ai kun yarda ko?”.

    “Baita relax bafa munƙi yarda bane ba. Kawai dai a munce da kai akwai dai wani a ƙasa nunasa da sukai matsayin wanda zata aura. Kaima fa kasan shekara kusan uku kenan ina bibiyar rayuwar yarinyar nan, na sani ka sani bata tare da kowane namiji. Kuma yaron nan binciken mu ya nuna mana kwata-kwata bai wuce wata ɗaya ma da fara aiki tare da su ba. Kuma ƙaninsa ne ya kawosa ma matsayin driver gidan”.

         “Humm Honorable karka yaudari kanka mana. Ka zauna kayi tunani da hankalinka dan ALLAH. Wata ɗaya da kaisa gidan matsayin driver, amma an ɗauki ƴa an bashi a jiya matsayin mata! Bafa babyn roba bace. Anya bai kamata ka tabbatar da akwai wata a ƙasa ba. Ni da kai duk mun san wanene Jiƙamshi ai bama buƙatar ƙarin bayani”.

      Ido suka zuba masa su duka biyun. Maganganusa na musu kaikawo a zukata da tasiri ɗaya bayan ɗaya. Kamar an tsikari Hon. Misau ya zaburo yana karkaɗa hannu. “Gaskiya fa maganarka abar a duba ce Baita. Ko kun lura ma tsakanin Alh. Sulaiman da yaron akwai magana. Kun dai san waye Sulaiman Garko baya raina abokin gaba. Sannan a labarin da nake samu yanzun nan shima ɗan Sulaiman ma yaje massalacin cikin shirin auren yarinyar amma ya yanke jiki ya faɗin jin an ɗaura da wannan ɗin, shi kuma Sulaiman ɗin baije massalacin ba”.

          “Eh to lallai akwai ƙullaliya a ƙasa”. Cewar Hon. Nakowa. Alh. Baita ne ya bashi amsa da “Babba ma kuwa. Dan tabbas Alh. Sulaiman nada tasa manufar na son yaronsa ya auri yarinyar duk da kuwa ɗiyar ƙanwarsa ce. Kuma shine sanadin auren uwar yarinyar da Isma’il ɗin”.

     “Yess wannan gaskiya ne. Dan sai yanzu kuka dawo da ni cikin hankali na. Wai ya akai ma mu tun kafin yau muka kasa gane yarinyar nan ɗiyar Isma’il Jiƙamshi ce”.

          “Lokaci ne bai yiba kawai sai yanzu”.

    “Amma lokacin nan kam bai mana adalci ba. Sai dai inaga ya kamata muma muyi amfani da wanda ke kaɗawa a yanzun”.

         “Kamar ya?”.

     “Muna buƙatar zuwa duba ɗan Sulaiman asibiti, mu gyara abinda muka ɓata a baya sannan mu sabunta abota”.

     Gaba ɗayansu kai suka shiga kaɗawa da gamsuwar abinda Hon. Nakowan ya faɗa. Dan haka suka miƙe a tare Alh. Baita na faɗin, “Da zafi-zafi akan bugi ƙarfe..”

       ★★……

    Sai a safiyar yau aka samu dai-daituwar Tajuddeen yanda ya kamata. Faruwar hakan ta kawoma Alh. Sulaiman ƴar nutsuwar dawowar hankali cikin jikinsa. Yana matuƙar so da ƙaunar Tajuddeen. Dan shi kaɗai ne ɗansa tilo namiji. Sauran huɗun duk mata ne. Amaryarsa kuwa Abasiyya bata taɓa haihuwa ba har yanzu shekararsu kusan goma kenan kuma da aure. Dan haka ya ɗauki son duniya ya ɗorama Tajuddeen fiye da kowa a gidan. Gata yake masa na bala’i sai dai kasancewar mahaifiyarsa Hajiya Turai tsaye take kan tarbiyyar ƴaƴanta Tajuddeen ɗin bai lalace ba. A asibitin ya kwana, sai yanzu da Hajiya Turai ta zo dan ita gida ta koma ta kwana. Da ƙyar ta samu ya tafi gida dan yin wanka. Koda yaje gidan wayar da yake amfani da ita a kiran Smart ya lalubo. Yana ƙoƙarin kunnata amaryarsa ta shigo, ƙaramin tsaki yaja yanda bazataji ba yana ajiye wayar. Sannu da zuwa tai masa da tambayar mai jiki. Amsa mata yay a taƙaice da bata umarnin haɗa masa ruwan wanka. Duk yanda yake son kiran shegen yaron nan a ransa dole ya cije har sai da yay wankan ya tsakuri abincin da ta ajiye masa. Yana kammalawa ya ce ta kwashe ta bashi waje yana buƙatar hutawa. Baki ta taɓe da tattare kayan ta wuce, a ranta tana ƙun ƙunin takaicinsa da ga shi har matar tasa. Sai dai kuma ranta fes jin auren da suka so ƙullawa bai ƙullin ba, ta kumayi alƙawarin yin amfani da wannan damar ƙanwarta ta samu cikar burinta ita ma, amma dai zata basu lokaci har Tajuddeen ɗin ya samu lafiya…

         Tana fita ya sakama ƙofar key, bedroom ɗinsa ya shige nan ma ya saka key sannan yay zaman ƙasaita cikin sofar ɗakin da waya a hannu…….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣0️⃣

……..Idanunsa da ke lumshe ya buɗe a hankali ya saukesu akan wayarsa da ke ruri. Har wayar ta kusa tsinkewa yana kallon number da ake kiran nasa da ita, sai kuma yay murmushi yana mai cije gefen lip ɗinsa da ɗaukar wayar ya sa a hansfree tare da maida idanunsa ya lumshe, cikin nutsuwarsa da deep voice ɗin nan ya ce, “Assalamu alaikum. Ina magana da waye?”.

       Alh. Sulaiman da ke huci da ga can ya ji wani irin takaici ya sake maƙure masa maƙoshi. A kausashe ya ce, “Da ubanka ne. Kai har kai ne zan kira ka ce min da waye?”.

           Murmushi Smart ya saki mai bayyana sautin da har ya shiga cikin kunnen Alh. Sulaiman. Babu alamar ɗar a tare da shi ya ce, “Yes kaima uba ne kam. Dan koba komai na auri ɗiyar Sister ɗin ka. Uncle ina yini. Nafa gode da ƙyauta ALLAH ya saka da alkairinsa, insha ALLAH nan da wata tara zakuga tukuycin jika maybe ma sunanka zai ci. Sai dai bazanyi fatan ya gadoka ba, mai asalin sunan nake son ya gada da ƙyawawan halayensa nagartattu….”

       “Yaro baka san wuta ba sai ka taka. Kana tunanin kai har karanka ya kai tsaiko kenan? Da har zan baka aiki ka koma gefe da tunanin cin dunduniyata! Wlhy ba kai ba hatta ahalinka sai sunyi nadamar kasancewarka a cikinsu. Ni Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko sai na maida rayuwarka abar kwatancen da ko faɗar sunanka akai sai an tofar da yawu….”

        Wata shashashar dariyar rainin wayo Smart ya saki cikin katsesa ya ce, “Da ace alƙalamin ƙaddarata a hannunka ya ke da tun kafin yau na kasance a ƙarƙashin inuwar tsoron cika bakinka. Sai dai kash kai baka isa ko dakatar da kaɗawar daƙiƙa ba na cikin ƙaddarata. Aliyu M. Idris Mawashi UBANGIJINSA kaɗai yake tsoro ba ɗan adam irinsa mai kashi da barci ba. Amma zan baka shawara idan ka shirya ka koma ka canja shiri, idan kuma baka fara ba ka ƙaro matakan shirin naka dan da kura kawai ake wasa a cikin kasuwa ZAKI sai kallo da ga nesa dan ko shafar jikinsa sai da dabara. Kamar yanda na faɗa maka nafi ƙarfinka kuma ni ba’amun barazana. Dan haka shawara ɗaya da zan baka ka goge tarihin alaƙar data taɓa alaƙantani da kai a baya, ka ɗauki sabuwar alaƙar zamantowarka suruki na sai mu amfana da tagomashi mutunta juna. Idan kuma ka ce a’a lallai zan cigaba da gara rayuwarka a tsakkiyar harabar gidan Alhaji Sufi Ado Garko fiye da yanda yara ke gara katantawar wasa a saman suminti. A yanzu bana buƙatar cewarka anan kaje kayi nazari. Na Barka lafiya sai nazo gasheka tare da AMARYAR ƘAMSHI bye Kawu”. Ya yanke wayar ƙittt. Kansa ya dafe yana wani irin furzar da huci a jajjere na ɓacin rai. Hannunsa ya kai saman goshinsa yana murzawa. Shi kam wace irin masifa ce wannan kuma ya shiga. Da ga wannan sai wancan. Sake furzar da iskar yay saboda abinda zuciyarsa ta ayyana masa cewar (Jarabawa ce).

       Haukacewa Alhaji Sulaiman ya nema yi jin Smart ya yanke masa waya bayan ya gama yaɓa masa maganganu masu zafi. Cikin wani irin bahagon ɓacin rai ya shiga ƙoƙarin sake kiransa amma ana nuna masa busy alamar yayi blocking ɗinsa ma kenan. Dai-dai nan kiran Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen ya shigo masa a ɗayar waya. Ɗagawa yay da sauri yana mai kaiwa kunnensa. Sai dai jin kukan data fashe da shi ya sashi zabura har da bugewa “Ke lafiya kuwa zaki ɗagamin hankali haka da kuka?”.

      Cikin kuka ta ce Alhaji babu lafiya. Tajuddeen ya farka gashi nan yana aman jini, shike nan zamu rasas……” ai kusan da gudu ma ya fito da ga sashen nasa har yana neman faɗuwa. Ba ƙaramar tsorata maigadi yayi ba. Hakama drivern sa da yaronsa Malami. Da ƙyar ya iya sanar musu “Muje asibiti” ya buɗe gaban motar ta shiga batare da ya jira an buɗe masa ba. Dole suma suka shiga da hanzarinsu….

      Tofa Tajuddeen yaya dai? Karfa ciwon son Lulun mu ya kasheka😔🚶.

        ___________________★★

   A ɓangaren su Umma da aminiyarta masu tafiya garin Zuru da ƙyar ta samu Abba ya barta bayan ta lafta masa ƙaryar zuwa garin su duba Innarta, acewarta ƙanwarta tai kiranta da dare ta sanar mata jikin Innarsu ya motsa. Bai kawo komai a ransa ba tunda yasan Innar tasu dama jiyya take kusan shekara huɗu kenan. Ya jajanta mata da bata izninin tafiya dan haka ana sallame sallar asuba taima ƴan gidan sallama ta wuce. Duk da asubancin tafiyar da sukai basu iso garin Zuru ba sai bayan sallar azhar. Burinsu su kammala komai su koma garinsu Umma ɗin a yau su kwana. Sun koyi sa’ar samun Malam Na-zuru a gidan kamar ma su yay zaman jira kasancewar tun kan su taso sunyi kiransa sun sanar masa. Bayan gaisuwa da tambayar juna bayan rabuwa ya dubi Hajiya Naqiba dan ita kam bata rabo da zuwa inda yake har ma ta saba dan ta riga ta gama kama mijinta a hannu a sake take kamar akuyar fulani. Umma kam Abba bai kasance a ƙarƙashin ikon nata ba ɗari bisa ɗari shiyyasa zuwan ke mata wahala kai tsaye sai idan gagarumin abu ne ya faru.

      “Hajjaju yau Aminiyar ki ta tuna damu kenan ko? Idan ban manta ba rabonta da nan kusan shekara uku kenan fa”. Cikin ƴar dariya Hajiya Naqiba ta ce, “Gaskiya za’ayi kam malam. Kasan ita akuyar ɗaure ce ganinta sai anyi sake ko tsautsayi ya gifta ta kufce”. Ta ƙare maganar tana kallon Umma. Dariya sukayi gaba ɗaya. Kafin Malam Na-zuru ya tsagaita da maida hankalinsa ga Umma yace, “Hajiya Yaha mike tafe da ke?”.

       “Abubuwane da yawa kashi-kashi malam. Sai dai mafi girma a cikinsu aikin yaron nan ne mai shegen taurin kai ya ke neman buɗe min wlhy….”

     “Tofa badai yaro mai tamaula ba ko?”.

    “Wlhy shi kuwa malam. Dan jiya-jiya aka ɗaura masa aure da ƴar wani hamshaƙin attajiri”.

          “Aure kuma? Ya akai haka ta faru Hajiya? Kina ina akai wannan babbar ta’asa bayan kin san da ƙyar muka samu yaron nan ya shiga hannun mu? Wannan kuma yana a cikin babban abinda muka ƙullesa da shi fa”.

      “Wlhy malam nima ban san yaya akai hakan ta faru ba. Sai dai na lura tsabar munafunci ne na ubansu ya sa aka rufe mana komai sai ɗaurin aure kawai mukaji bayan an riga an ɗauro. Malam ka taimakeni dan ALLAH. Kai kanka ka sanar min yaron nan yanada taurari masu ƙarfin gaske da zasu iya disashe kaf ƴaƴan gidan nan ya zam babu hasken wanda ake gani sai shi, bayan kai malamai kusan huɗu sun sanar min hakan wasu ma sun kasa aiki a kansa sai kai ne da kayi akaci nasara. Gashi kuwa na fara gani dan aure fa akai masa, kuma da ƴar Alhaji Isma’il Jiƙamshi, wannan abu ya hanani samun barci sam a daren jiya”.

          “Tirƙashi! Dolene ki kasa barci. Dan aurensa na ɗaya da ga cikin abinda muka ƙulle masa har sai ya tsufa a haka ta yanda babu mai ɗaukar ƴa ya bashi. Ba ƙaramin duka a ciki mijin nan yay mana ba gaskiya. Dan yaron nan yanada ƙarfin nacin ibada shiyyasa muka jima muna aiki yana tafiya a iska, na ƙarshen nan ma da ƙyar kina gani muka samu ya haushi da taimakon anfani da gashin mahaifansa da nashi…..”

      “Na sani Malam, dan ALLAH ka taimakeni wannan aure ya watse kafin ma cikar sati ɗaya na tarewar wannan yarinya. Sannan a matse minsu waje guda su rasa gabas su rasa yamma akan wajen da zai zauna da abinda zasuyi hidimar biki. A sakama duk danginta tsanarsa a zuciya hatta da jaririn yaro. A birkitamin lissafin yarinyar ta ce bata son sa”.

      “Aikin nan yana da wahala Yahanasu. Amma dai zaɓi ɗaya anan mu gwada mu gani”. Ya ƙare maganar da ajiye mata tazbaharsa gabanta. Da ƙyar ta iya tsaida nutsuwarta wajen ɗaukar ɗiyan tazbahar ɗaya ta miƙa masa. Amsa yay ya duba ya sake ajiye mata yace ta ɗauka. Sai da sukai haka sau uku sannan ya kalleta cikin jinjina kansa. “Gaskiya akwai babban aiki a gareki. Dan gaba ɗaya fa an riga an lalata aikin sai kaɗan ne bai bar jikinsa ba. Wanda kuma ya ƙulla wannan auren mutum ne mai nasibi matuƙa shima, dan komai yayisa ne da hikima kasancewar ya fahimci akwai ɓoyayyen al’amari akan rayuwar yaron……”

      “Kenan babu yanda za’ai malam? Sannan waye shi wannan matsiyacin da ke tare da shi haka ba sani ba tun da wuri?”. Umma ta faɗa kamar zatayi kuka. Malam Na-zuru yay gyaran murya yana gyara zama. “Baza’a rasa yanda za’aiba kam. Sai dai dole za’a canja taku kuma. Shi wannan mutumin da kike tambaya yanada alaƙa da yarinyar matuƙa, sannan yana ƙaunar yaron da zuciya ɗaya, mutum ne kuma mai wayo da hikima gaskiya. Samun nasara a kansa kuma shima sai munyi yaƙi na gaske. Amma ita matar da aka ɗaura masa auren da ita mu maida akalar aikin namu ta hanyarta kawai inaga hakan zai taimaka mana”.

     “To amma malam matar da ba’a bukatar ma ta tare miye amfanin kafa harsashin aiki kanta?”. Hajiya Naqiba ce yanzu tai masa tambayar dan Umma dai damuwar jin labarin waye Uncle Yousuf ya hanata magana ma. Amsa ya bata da faɗin, “Gaskiya in har kuna son cimma burinku akan yaron nan dole sai anbi ta hanyar ita wannan yarinya. Hakan na nufin kuma dole sai ta tare da shi sannan komai mu bisa a sannu…..”

          Da sauri Umma ta ce, “Malam kana nufin ma har sai ya kusanceta a shimfiɗa kenan?”.

       “A’a ba wannan nake nufi ba. Ko tarewa a gidansa tai matsayin mata to ya wadatar damu. Dan muna buƙatar kayan da aka kawota gidansa da shi a ranar, da wanda shi kuma zai shiga gareta da su. Sauran aikin ya rage namu mukuma”.

       Jimmm Umma tai alamar tunani kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da faɗin, “Shike nan malam zanyi wannan ƙoƙarin. Sai kuma akan kishiyoyin nawa ina son a sabunta min aiki musamman uwar yaron nan. Dan na tsaneta fiye da kowa a gidan nan. Bana son koda ganinta matsiyaciyar. Yanda ta saka katanga tsakanina da masoyina har sai da ta fara zama matsayin matarsa na tsawon shekaru kafin ya kalleni bisa tirsasawar iyaye, wlhy itama sai na gunzuga mata baƙin cikin da har ta mutu bazata fita a cikinsa ba.”

         “Burinki zai cika kuwa. Mudai je zuwa mataki-mataki zaki sha mamaki”.

    Sosai farin ciki ya mamaye Umma, ta cigaba da zayyano ma Malam Na-zuru duk yanda take buƙata akan Ammah da zuri’arta. Suma sauran matan kowacce da kalar nata shirin da take so ai mata. Sai matar ɗanta Salim da itama ke neman zame mata ƙarfen ƙafa akan janye mata ra’ayin Salim ɗin. Basu dai baro garin Zuru ba sai bayan la’asar, a hakan ma ɗan basu tsaya yin koma ba. Sun jigatu kam gwargwadon iko sai kusan goma sha ɗaya na dare suka iso garin su Umma da nufin duba mahaifiyar Tata su kwana…….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣1️⃣

………Tunda suka baro gidan babu abinda Lulu keyi sai haɗiyar zuciya. Ko sau ɗaya bata tankama hirar da Uncle Yousuf ke mata ba, hijjab nema da ya tambayeta ina ta samo cikin takaicin da har yanzu yaƙi sakar mata maƙoshi ta amsa masa da, “Uncle You mutumin nan fa ni bazan tare ba na fasa ko zaman wata ɗayan. Shiko dai yanata danne dariyarsa har suka iso gida. Sai da yay parking ya dubeta cikin nutsuwa ya ce, “Saboda mi basai kin tare ba?”.

         “Ni dai kawai nama fasa. Dama na gaya maka mutumin nan baida mutunci, to kaga tun kafin ma na fara shuka masa nawa kalar rashin mutuncin kawai mu tsaya iya hakan”.

      “To banƙi ta taki ba, amma yaya kike tunanin duniya da Baba zasu kalla al’amarin? Dan Baba fa zai iya ɗaukar zafin da bamu taɓa zato ko tsammani ba. Ni dai da zakiji shawarata anan ki cigaba da kwantar da hankalinki ayi komai a yanda aka tsarashi. Shima kuma mu bisa a sannu a rabu lafiya batare da kowa yaji ko ya gani ba. Dama jira nake ya sake samun lafiya yazo muyi magana ma ta fahimta ok”.

     Sosai yanda Uncle ɗin nata ke mata magana cikin kulawa da sanyi ya sata jin bazata iya bijire masa ba. Dan haka ta jinjina kanta tana sauke tagwayen ajiyar zuciya ta ce, “Shike nan Papa. Amma dan ALLAH ka masa magana ya kama kansa”.

          “Zan masa kar ki damu”.

    Ya bata amsa cike da kulawa. Wata ajiyar zuciyar ta sake saki sannan suka fita. Da ƙyar Uncle Yousuf ya iya danne dariyarsa shi dai yana binta da kallo, tausayi take bashi, ba kuma ya ganin kowa da laifi sama da Daddy, ya raunana rayuwar yarinyar matuƙa da sunan soyayya, ya kasa fahimtar tarbiyyar uwa ga ƴaƴa daban take da komai a wannan rayuwar musamman ma ɗiya mace, amma sam Mawaddat bata samu ba, shiyyasa abubuwa masu muhimmanci ma duk bata sani ba kuma bata ganesu da yaren fahimta…..

        Koda ta shiga gidan ma aunty Saliha dake yanke ma Ra’is farce a falo sakin baki tai kawai tana kallonta. Ai ko sai ta sake tunzura fuuu aka shige ɗaki. Dai-dai nan Uncle Yousuf ya shigo shima. Da hannu ta nuna masa bayan Lulu. “Miya kunna ƴar taka? Ga shi naga an dawo da hijjab?”.

       Ƙaramar dariya ya saki yana kaiwa zaune. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Aikin surukinki ne”.

    “Woow dan ALLAH fa?”.

“Sosai”.

Ya faɗa cikin gyaɗa kai da lumshe ido abin dariya. Sai kuma ya nuna mata Ra’is da ido. Murmushinta ne ya ƙara faɗaɗa. Sai dai bata sake cewa komai ba….

       ★★……

   A matuƙar tashin hankali Alh. Sulaiman ya isa asibiti. Sai yay dai-dai da isar su Hon. Nakowa da sukaje duba Tajuddeen. Shi baima lura da su ba. Sai dai ganin yanda ya fita a mota a rikice yay cikin asibitin ya sa su tambayar drivern sa ba’asi. Shima ba sani yay ba. Sai dai ya tabbatar musu maybe jikin Tajuddeen ɗin ne. Jin haka suma sukai cikin asibin dan dama tafiyar sun yita a sirrance ne shiyyasa babu wani tare da su sai su ukun. Sun iske kam abubuwa sun ƙwaɓe matuƙa, Hajiya Turai da Alh. Sulaiman rungume da Tajuddeen suna kuka. Sam sunma ƙi bari likitocin suyi aikinsu. Hakan ya bama su Alh. Baita yin ruwa da tsaki akan komai. Dan take anan suka shiga ciku-cikun ganin amma fita da Tajuddeen a ƙasar ta wayoyi duk da sun san shima Alh. Sulaiman ɗin duk yana da wannan alfarmar. To da ace lafiya lafiya ne ko jirgi sukutum mahaifinsa yay niyyar nema dan akai Tajuddeen wata ƙasa neman lafiya hakan ba komai bane. Dan da gasken gaske Alhji Sufi Ado Garko ya tara dukiya irin wadda shi kansa bai san adadinta ba. Alhmdllh burinsu kam ya cika, dan zuwa yamma an kammala komai na fita da Tajuddeen, haka uwar da uban suka wuce batare da sun nema kowa a family ɗin ba. Ita kanta amaryarsa Hajiya Abasiyya sama-sama ya mata bayani lokacin da suka koma gida domin shiryawa……

       ★★★……

   Duk wani abinda ke faruwa har barinsu ƙasar Alhaji Sufi Garko ya sani sarai. Sai dai yaƙi yin ko tari akan hakan dan ransa a ɓace yake matuƙa da ɗan nasa. Babu irin haƙurin da matarsa bata bashi ba amma bai saurareta ba. Sai ma gargaɗin karta sake masa maganar Sulaiman a gidan yay mata. Tare da balbale ta da masifar cewar duk wata fitina da ke a tsakanin ƴaƴansa ai itace tushenta. Dan sakacinta ne saboda kasancewarta mace mai masifar son ƴaƴa. Badan shi tsayayyen mutum bane da kaf ƴaƴansa zasu tashi ne a lalace cikin fanɗararriyar tarbiya. Dan tabbas Hajiya Attine bata tsawatarwa yaranta tun ma da ƙuruciya. Komai yaro ke so shi yake yi, ba’a isa kuma ace yay ba daidai ba sai ta kareshi. Yanzu haka akan auren nan na Mawaddat sai da ta haura sama sosai da mijin nata. A cewarta ai itama tanada hakki akan Mawaddat tunda itace ta haifi uwarta. Ita bata yarda Lulu ta auri talaka ba kamar yanda uwarta ta auri ubanta da ga ƙarshe suka kashe mata yarinya dan suci dukiya. Shiko kasancewarsa jarumi mai tsayawa a gidansa ya ce idan ta isa taje ta warware auren mana. Sun haura sama ƙololuwa koma ace har yanzun a saman suke, dan taso fita duba Tajuddeen nan ma yace idan ta fita a bakin aurenta. Wannan kalma ta matukar girgiza mata zuciya dan bata taɓa tunanin fita da ga bakin mijin nata da suka ɗauki tsahon shekaru kusan saba’in tare ba. Ta san kuma zai aikata dan shi baya magana biyu. Dole dai ta haƙura da fitar tunda suma yaran har ma da jikoki ya tabbatarma duk wanda yaje asibiti duba Tajuddeen sai ya koya masa darasin rayuwa…..

        _______________★

  A cikin gida koda Nasreen taje da Deen a wajen Mubarak suke jin baƙin da sukazo duba Smart ne sukazo da shi. Babu wanda ya damu da sanin da ga ina, duk da dai zuciya na raya musu ko dangin matar tasa ne. Dan yaron dai da ganinsa kasan ɗan gidan madara ne. Kuɓul-ƙubul da shi. Sai dai abinda ya birgesu da yaron yanda duk da ƙanƙantar shekarunsa sai da ya gaidasu. Fuskar Ammah da murmushi ta ɗaukesa ta ɗaura saman cinya tana tambayarsa sunansa. Yako bata amsa da cewar Deen shalelen aunty Luu.. shalelen aunty Luu da ga faɗa ya sakasu darawa, abinka kuma da yaro shi ko’a jikinsa, sai ma janye ra’ayinsa da Nasreen tayi suka kama wasansu batare da ya sake tunawa su Aunty Lu zasu iya tafiya su barsa anan ba. Bayan sallar azhar Smart ya shiga cikin gidan. Sunta jera masa sannu da yaya jiki? Dan sun barsa ne dama saboda maza da keta faman shigowa ƴan nan cikin anguwa dubashi tun safe. Zaune ya kai yana amsa musu da Alhmdllh. Yaji daɗin ganin Deen nata wasanshi, sannan koda aka zuba musu abinci shi da Nasreen babu wani janjeni yaron ya zauna sukaci. Shine ya sake musu bayanin daga inda yaron ya fito, sai dai ba gaya musu harda amaryarsa akazo ba. Anan ya ɗan sake shan kunun gyaɗa kaɗan ya kwanta a doguwar kujerar Ammah yana sauraren tsare-tsaren biki da suke tayi, dan shi sai yanzu ma yake jin wai aunty Bilkisu da Hawwah ashe sun tara masa uban kaya na lefe da suketa saye a hankali da shirin dama duk randa ya tashi aure sai dai a ƙarasa abinda ba’a rasa ba. Idanu kawai ya tsirama ƴan uwan nasa yana jin matuƙar ƙaunarsu a cikin ransa. Suko sunata dariya da tsokanarsa. Shima dole yay murmushi yana haɗiye abubuwa masu dama da ke a ransa. Anan ne Ammah ke masa bayanin shawarar da ta yanke akan inda zasu zauna. Sun gama shawara da ƙanwarta Sa’adah zasuyi magana da Abba a gyara masa gidan da suka gada kasancewar su biyu ne dama ke da shi ta ɓangarensu dan suma sunada ƴan uba. Sai yay zamansa, za’a tashi ƴan hayar gidan.

       “A’a Ammah kar ayi haka. In dama ace babu kowa a gidan ne, amma bazan so saboda ni a tashi mutanen da ke a gida tsahon shekaru ba kuma a ƙurarren lokaci irin wannan. Kudai bani lokaci ina kan nazari in sha ALLAHU za’a sami mafita. Dan dama zance kodai a musu magana su kai tarewan zuwa sati biyu haka ko wata ɗaya”.

      Ammah ce ta katsesa da faɗin, “A’a Hydar kar ai haka. Tunda mutanen nan sukace sati ɗayan kawai mu amsa ayi a wuce wajen. ALLAH shine zai rufama kowa asiri. Dan kaga dai a ɓangaren lefe Alhmdllh matsalarsa kamar ta ƙare zance. Ga dai Hawwah nan da Bilkisu zasu shiga kasuwa da kuɗin da ke hannunsu tun da sunyi alƙawarin dai sune zasu haɗa lefen nan. Ko a yanzu ma suturar da suka tara ɗin fa tafi arba’in tunda kowa na saye ta ɓangarensa. Gashi Alhamdullah duk manya ne kamar sun san inda auren naka zai faɗa dama. Kaga yanzu kam kokawarmu ai ta wajen da za’a zauna ne kawai sai kuma kai ɗan ɗinkunan da zakai amfani da shi na angwanci”.

        “Kai Ammah ni sai nayi wani sabon ɗinki?”.

    Hararar sa ta ɗan yi da faɗin, “Oh da haka kake son shiga angwancin. Haba Babangida, ai lokacin abu ayisa kaji. Kasan kuwa a irin farin cikin da nake ciki tsakanin jiya da yau. Ko auren su Maryam bai damuna kamar yanda zamanka babu mace ke cimun rai. Na gaji da jin gori da habaici akan zaman nan naka babu mace har ma da sheri. Amma Alhamdullah ga iyaka ALLAH ya kawo a gaɓar da bamuyi zato ba sai kuma muƙi nuna godiyarmu garesa.”

         “Hakane Ammah. Amma ai inata sakaku wahala. Sam ba haka naso al’amarin nan yazo ba. Ban so ɗaura nauyin aurena a kanku ba, domin nine ya kamata nai muku hidima bawai ku kucigaba da min ba bayan tun ina ciki kuke min har zuwa yau ɗin nan”. Yanda yake maganar cikin damuwa ya sa Ammah sakin murmushi da miƙewa tana faɗin, “Shi komai lokaci ne da shi. Haƙuri akan jarabawa kuma cikar kamala da imanin ɗan Adam ne. Idan aka cigaba da jurewa duk komai zai cigaba da zama labari tamkar bai faru ba, ko a yanda auren nan ma yazo ai babbar aya ce. Fatana ni dai ka kasance da iyalinka fiye da yanda nake zatonka da tsammani. Ka kuma riƙe mutuncinka dan kar zuciyarka ta ɗora maka cewar dan su masu shi ne shikenan zaka zauna su zame maka rijiyar tatsar abin duniya. Babu ruwanka da dukiyarsu ka tashi ka nema na kanka ka ciyar da ƴarsu ka tufatar da ita da kare mata dukkan wani hakkinta da ke a kanka. Kar ka yarda ka bada wata ƙofa ta amsa da ga garesu da sunan wai kana auren ƴarsu. Duk da dai bana kokwanto a kanka Aliyu. Ina dai sake tunatar da kai ne dan dukiya shu’umar abuce mai shiga rai da jinin ɗan adam harma da ɓargo.”

     Sosai nasihar mahaifiyar tasa ke ratsashi matuƙa. Tana ƙara masa ƙwarin gwiwa akan nasa ra’ayin kuma da ƙyakykyawar manufa………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣2️⃣

……Shirye-shiryen biki kam ya kankama ta kowanne ɓangare. Yayinda shima Abba ya goce batun tada mutane da ga gidan su Ammah a gyarama Smart. Yana ganin hakan zai zama su kuma an cuta musu. Gara dai kawai a kama masa haya na shekara biyu idan zai samu kafin aga abinda ALLAH zaiyi kuma. Ana cikin wannan lissafi sai ga Coach ɗin su Abdull-Hameed yazo da batun Smart ya amsa gidansa da ke anguwar sharaɗa ya zauna har sanda ALLAH zai hore masa nasa. A cewarsa wannan itace tasa gudummawar. Da farko dai Smart ƙin yarda yay, sai dai ya kafe akan zai biya kuɗin hayar gidan, sai da Coach ya nuna masa ɓacin ransa akai sosai harda faɗin ashe shine keta haukansa Smart ɗin bai ɗaukesa matsayin Yaya kamar yanda shi yake masa kallon ƙaninsa Ahmad ba, yay fushi zai tafiyarsa sai da ƙyar Smart ya bashi haƙuri ya tsaya suka tattauna. Da ga ƙarshe dai Abba ya ce an amshi gidan sukai godiya da sanyama Coach ɗin albarka dan ya jima yana ɗawainiya da Smart. Duk wani matakin nasara akan ball shine riƙe da hannun Smart ɗin. Dan tunda ya ga iya ƙwallo na Smart a wani wasan sada zumunta na makaranta da sukai sannan Smart na ss1 ya jashi jikinsa, tun ma suna ɗar-ɗar har suka saki jiki da juna ganin kowanne nada zuciya mai ƙyau. Kusan family ɗin su Ahmad sun san Smart sosai, haka suma family ɗin Smart sun san waye Ahmad da Abdull-Hameed a rayuwar Smart. Babu hanyar da Umma batabi na son ganin ta rabasu ba amma hakan ya gagareta shiyyasa ta tsani Coach matuƙa. Akwai lokacin da har sharri tai masu wai Coach kodai yana ɗabi’ar banza da Smart ne. Sai da Abba ya nuna mata asalin haukarsa a lokacin dan har saki ɗaya yay mata sannan ta dawo hankalinta tana bada haƙuri, da ga nan bata sake maimaitawa ba kuwa.

      Smart yaje ya ga gida tare da Ahmad. Gidane madaidaici zaman mace ɗaya flat. Bedrooms uku biyu manya ɗaya ƙarami kowanne da toilet sai falo babba tare da dining, sai kitchen da store. Harabar gidan zai iya cin mota biyu zuwa uku. Ga flowers an zagaye ko’ina da suka ƙara ƙawatashi. Sabon fenti da gyare-gyare duk an masa, dan ana dawowa da ga ɗaurin auren Smart Coach ɗin ya nema masu aikin gidan aka fara. Dama ƴan hayane suka fita kusan watanni huɗu kenan kasancewar ALLAH ya hore musu suma sun gina nasu, shi kuma sai bai sake saka kowa ba a ciki ya ɗan fara masa gyara sai kuma ya watsar ya rufesa kawai. Sai da idanun Smart ya ciko da ƙwalla, dan a rayuwa yakan rasa mizai ma Coach ya iya kwatanta alkairan da yay masa ne koma yake a kan masa, ya jima yana ɗawainiya da shi kashi-kashi da shi kansa bai san adadi ba.

       Bayan sun dawo suma su Aunty Bilkisu sukaje suka gano, Abba kuma da Ammah sai washe gari ya kaisu suma. Su Umma dai basu san hidimar da ake ba, summa koma gefe sun zuba ido suga wai yaya wasan zai ƙare ne. Dan ta aiwatar da ƴan abubuwan da malam Na-zuru ya bata yanzu jiran ranar tarewar amarya kawai take ta samu kayan da aka kawota da su da wanda Smart zai saka shima. Alhmdllh lefe ma ya haɗu tsaf, dan bayan ƙoƙarin su Hawwah suma dangin Ammah sun taka rawar gani, dama su mutanene masu haɗin kai matuƙa. Gashi kuma yanzu ne Ammah zata aurar da ɗa namiji kuma shi kaɗai tilo gareta. Hankalin su Umma da ya ɗan fara tashi ganin gudunmawar da keta shigowa mai jijjiga zukata da ga ƴan uwa da abokan arziƙi, dan ko kuɗi Smart ya samesu ba laifi. Ana saura kwanaki uku ya amsa kiran su Uncle Yousuf, dan rabonsa da gidan fa tun kafin a ɗaura aurensa da gimbiya. Aiki bai sake zuwa ba, dan itama dai Lulun Uncle Yousuf ya dakatar da ita fitar bisa wayon Aunty Saliha da ta ɗakko mai mata gyara tun daga Sudan da Marocco. Da farko tayi butsutsun nata na bata so Uncle Yousuf ya zauna ya tsarata tsaf a kwali dole tabi. Suma dai shirye-shirye suke na bikin ƴar gata, musamman ma Uncle Yousuf da Baba da Mommy da Aunty Saliha. Ya samu tarba ta muntunawa ga Mommy matsayin suriki garesu a yanzu. Duk da dama dai ita kam bata taɓa wulaƙantashi ba. Shima ya gaishesu cikin mutuntawa da girmamawa kamar yanda ya saba. Da ga haka suka fara tattauna abinda ya tarasu. Shiru yay yana sauraren Daddy da ke masa bayani akan takardun hannunsa. Ɗaya na gida da ya bashi halak malam ƙaton gaske anan cikin anguwar hotoro G.R.A ɗin upstairs ma, sai key na mota da takardunta itama sabuwa fil a ledarta, da zunzurutun kuɗi har naira miliyan ashirin, ya kuma zaɓi duk aikin da yake so ya nema masa. Tunda Daddy ya fara murmushi kawai Smart yake yi amma baice komai ba. Shima dai Uncle Yousuf da Mommy basu ce komai ba dama.

       A hankali Smart ya girgiza ma Daddy da ke miƙo masa takardun da key ɗin motar kai. Cikin tausasa harshe da girmamawa ya ce, “Daddy kayi haƙuri bazan amsa komai da ga gareku ba ni. Na auri Mawaddat ne domin ALLAH da bautarsa. Na kuma muku alƙawarin riƙeta in sha ALLAHU da abinda ALLAH ya azurtani da shi, bazaku taɓa dana sani da ni ba. A yanzu haka inada inda zan ajiyeta, batun neman aiki kuma insha ALLAH shima zan nema abinyi da kaina, hakan zai fi ƙaramin himma da sanin muhimmancin abinda na samu ɗin. Idan nayi ba dai-dai ba a gafarceni dan ALLAH”.

       Tsittt falon yay tamkar ruwa ya cinye kowa. Bakaji komai sai sautin ƙarar ac da ke aiki. Murmushi sosai Mommy da Uncle Yousuf keyi ƙasa-ƙasa. Yayinda Daddy yay wani sansarakwai da shi yana kallon Smart cike da mamaki da al’ajab. Kaba mutum irin wannan dukiyar amma ya nuna maka bai buƙata, matashin saurayi kuma da ayanzu yake fafutukar gina rayuwarsa. Da ƙyar ya iya jan numfashi har sannan idanun nasa dai akan Smart. Ya ce, “Aliyu ban baka wannan abubuwan ba dan wataran ka maido min da madadinsu. Na baka ne saboda kaima yanzu matsayin ɗa kake amsawa a garemu, fatanmu kawai ka riƙe mana Mawaddat cikin aminci da amana”.

       “In sha ALLAHU Daddy zan cika alkawarin riƙeta, koba komai nima inada ƴan uwa mata, bazan so na tsinci rayuwarsu cikin aƙubar zaman aure ba. Zanyi iya ƙoƙarina kamar yanda MANZON ALLAH (S. A.W) ya koyar da mu murayu a gidajen auren mu”.

         Magana Daddy ya ƙara yunƙurowa zai yi cikin ɗan jin haushi-haushi, amma sai Uncle Yousuf yay saurin taresa yana girgiza masa kai da faɗin, “Shike nan Aliyu mun gode da wannan karamcin naka. Dama mu ai hakan muke son ji da ga gareka. Zamu cigaba da muku fatan alkairi dana zama lafiya. ALLAH ya baku ikon sauke hakkin juna. Ga waɗan nan katunan Baba ya ce a baka. Sai dai yace a faɗa maka kayi haƙuri baiyi shawara da kai ba wajen haɗa wannan dinner, yaso yin hakan sai uziri mai girma ya taso masa dan yanzu haka ma yana Abuja. Muma a madadinsa muna sake neman afuwarka da roƙon kayi haƙuri ya haɗa dinner ɗin ne sakamakon yanda ɗaurin auren ya kasance ga kuma mutane da yawa ya cancanci suzo”.

        Ɗan murmushi kawai Smart yayi, duk da harga ALLAH shi a tsarinsa babu batun waɗan nan bidi’oin, amma yana jin nauyin Baba da Uncle Yousuf ɗin. Dan haka ya amsa katunan yace ba komai abin ƴan awoyine ai. Da ga haka yay musu sallama ya wuce da sanar musu baƙi na zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Daddy dai bai tanka ba, hasalima ransa a ɓace yake. Taya zai haifi yarinya, ya raineta tsawon shekara ashirin da huɗu. Rana ɗaya tak wani ya nuna masa iko akan al’amuranta. Idan bai amshi waɗan nan abubuwan daya bashi ba taya zai riƙe masa yarinya da daraja kamarr yanda ya raini abarsa. Sosai Mommy ta fahimci yanda Daddy ke cika da batsewa, dan haka ta miƙe tana cema Uncle Yousuf bari taje tai waya da su Hajiya Aysha da su Aunty Saliha suzo a tsara abinda za’a tarbi baƙin da Smart ɗin ya ce zasu zo gobe. Cikin murmushi da barkwanci Uncle Yousuf ya ce, “Umm bafa sabun ba zamu aurar da ƴar farko a gida”. Dariya ta fita tanayi. Shima yana tasa. Tana gama ficewa Daddy ya miƙe a zafafe.

         “Kai Yousuf bazai yiwu ba. Shiyyasa tun farko nace maka yaron nan zai iya bamu matsala dan na fahimci gadararre ne shi mai girman kai. Taya zan bashi abinda zai inganta rayuwarsa da ma ta duk zuri’arsa darajar ƴata zata shiga cikinsu amma ya nunamin shi yafi ƙarfin hakan bayan baida komai. To gaskiya ayi komai a rubuce wata ɗayan daka ambata ya sakamin yarinya ta kawai……” Haka ya cigaba da zazzaga masifa ko haɗiyar yawu bayayi. Shi dai Uncle Yousuf na zaune kawai yana kallonsa har yayi ya gama. Baice komai ba, sai ma ya tashi tsam ya fice a falon yay tafiyarsa ya bar Daddy da sakin baki yana kallonsa………✍️

       (Uncle You kaima fa ɗan manni ne wlhy🤣).

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣3️⃣

…….A ɓangaren Smart sosai abinda ya farun ya dinga cimasa rai. Amma haka ya danne bai sanarma kowa ba yama kashe wayarsa dan kar wani tsakanin su Daddy yace zai sake kiransa akan batun. Bayan ya koma gida ya shiga ciki gaida Ammah su Hawwah suka buɗe masa lefe ya gani. Set guda na akwati mai biyar, sai ƙwara biyu daban da Abba ya saya da kaya a ciki suma matsayin kayan sa rana. Kaya kam sunyi sai dai maƙiyi, ga shi kuma duk manyan atamfofi da lasses hakama shaddoji da dogayen riguna dai-dai ƙarfin mai rufin asiri dai. Sosai Aunty Bilkisu da Hawwah suka taka rawar gani, dama sunyi alƙawarin duk randa ɗan uwan nasu tilo ɗaya ya tashi yin aure sai sun nuna bajintar da zata girgiza jama’ar gidan nasu kowa ya tabbatar da shi ɗan gata ne. Aiko sun girgiza ɗin, dan ko gidan su ya girgiza matuƙa da ganin wannan lefe da ba’a taɓa tunanin gani ba, sai su Umma suka shiga yada habaicin wai sai dai in iyayen yarinyar ne suka haɗa lefen, da ga Ammah har ƴaƴanta babu wanda yay ko tari har sukaci suka tsire. Gyalillan ciki kaf ya kwashe yabar guda uku, da mamaki su Aunty Bilkisu ke kallonsa, duk da ya lura da hakan baice komai ba ya dubi Maryam ya ce, “Bani saƙon dana baki ajiya”. Tashi tai tana murmushi ta shiga bedroom ɗinsu. Babu jimawa ta dawo da leda babba ta miƙa masa. Amsa yay ya miƙama aunty Bilkisu da faɗin, “Ku saka waɗan nan a kayan, wannan kubarta har sai tazo na bata da kaina. Aunty Bilkisu zatayi magana Ammah ta katseta da faɗin, “Kumasa yanda yake so ɗin kawai tunda baku san dalilinsa ba”. Su masu biyayyane ga umarnin mahaifiyarsu, dan haka babu wanda ya sake magana aka loda hijjabai da suka sha guga har guda goma ciff cikin akwati….

        Washe gari alhamis aka kai lefe, ba wani gayya akai ba. Umma ne da Aunty Amarya, sai Aunty Bilkisu da Inna Mariya. Da wata gwaggon su mai suna Jamila. Sai matan maƙwaftansu su biyu. Ahmad ne ya kaisu da motarsa, sunko samu tarba irin wadda basuyi zato ba. Dan su Mommy da su Aunty Saliha sun nuna karamci mai ban mamaki. Ga gida cike masha ALLAH iyalan gidan Baba suma sun zazzo. Sosai suma kansu su Mommyn sukasha mamakin wannan lefe, dan gaskiya basuyi zato ko tsammani ba. Abu a cikin kwana shida haka. Kai da mamaki. Ga kaya babu na kushewa sai san barka. Harda kuɗin ɗinki, sai dai basu amshi kuɗin ɗinkin ba dai. Su Umma fa sun girgiza matuƙa, dan ganin gidan su Lulun ya ƙara tayar musu da hankali da sake tabbatarwa eh lallai Smart ya shiga inda akafi ƙarfinsa, dan yanda mutanen keda wannan irin dukiya sai dai idan asiri ne yay tasiri, yo inba asiri ba ƴar data tashi a wannan gidan ce zata auri ɗan talakawa kamar Smart. Ammah dai tasan tsiyar data yi ɗan nata ya auri yarinyar nan. Duk wannan abu dake faruwa amarya bata sani ba, tana gidan Aunty Saliha data turketa ana mata gyaran jiki na fitar hankali. Dan ta ƙara wani irin fresh da ita, damuwarta ɗaya kayan shaye-shayen ta da bata samu. Dan a jiya har kuka tayi ita kaɗai a bayi saboda buƙatar son sha da takeyi amma babu dama. Tsoffin nan da aka kawo mata sunbi sun tare ko’ina basa barinta ko motsin kirki. Gasu da ihu da tace zata musu gardama suke rufeta da kwakwazo dole take zama suyi yanda suke so da ita. Sai dai ita kanta tasan ta canja. Dan fatan ta ko daga nesa ka hangota kasan ta ƙara karɓar sunnonin gyara. Ga wani almurin ƙamshi mai ratsa zuciyar mai shaƙa. Ita kanta ƙamshin ne ma ke tafiya da imanin ta shiyyasa wani lokacin take ragama tsoffin ta haƙura su zauna.

      Bayan wucewar ƴan kawo lefe da aka cika da sha tara ta arziƙi suma su Aunty Saliha suka nufi gidan da za’a kai Mawaddat ɗin domin raka Company da Uncle Yousuf ya bama kwangilar shirya mata kaya. Su kansu gidan ya birgesu yanda yake cif-cif abinsa. Duk da nasu ya ninka shi sau biyar girma da ƙyau, shima wannan ɗin nada nashi kalar sirrin ƙyau ɗin da yanayin shiga rai. Bayan Company sun kammala aune-aunensu su Aunty Saliha suka dawo gida suka barsu suyi aikinsu. Dan gidajen biyu sun fara cika da ƴan uwa na jiƙamshi da abokan arziki musamman na tsohuwan anguwar da su ka rayu tun suna ƙanana kasancewar mutanen da da zuminci ga shi kuma Aunty Saliha ma ƴar canne. Anan gidan su Smart ma dai an dawo da labari mai daɗi na tarbar da suka samu da karramawa. Yayinda Umma keta faman haɗiyar zuciya, data samu abokin gulma kuwa tace “Anya yarin nan ba asiri yay ma mutanen ba kuwa? To wannan haba rawa har ina. Ga mutane a jiƙe cikin kogin dukiya amma sunama waɗan nan ɗan abinda muka kai haba rawa haka”. Wasu idan tace musu hakan sukan kulata, wasu ko su gwaleta. Wannan kai lefe ya sake yayata sanin ƴar wa Smart ya aura a anguwar, dan dannan fa masu hassada da masu taya murna aka kafa teburan kace nace kowa na faɗar albarkacin bakinsa. Oho shi baima san sunai ba. Yana can yana nashi ƙoƙarin na ganin walimar da suma suka shirya anan gidan a gobe idan ALLAH ya kai mu juma’a ta tafi dai-dai. Ga kuma can gidan da Company ke saka kaya dole suka raba hankalinsu biyu shi da Ahmad da wasu tsirarun abokansa da basa fushi da shi duk yanda yake sharesu a baya. Harda Sa’ad mijin Hawwah.

       Zuwa washe gari suma fa nan gidan ya cika da dangi, musamman ma dangin Ammah kai harma dana Abban da kuma nasu aunty Amarya, ga ƴaƴan gidan duka dai duk sun hallara ƙwai da kwarkwata. Duk da wasunsu aikinsu tsogumi ne da kushe kamar yanda iyayensu keyi. Bayan an sakko massalacin juma’a aka fara walima da aka gayyato manyan malamai da zasu kwarara wa’azi. Abin mamaki sai ga gayyara Alhaji Sufi Ado Garko a wajen da na Uncle Yousuf da wasu a cikin mata ƴan biki. daddy dai baizo ba, Mommy ma saboda baƙi doke ta haƙura, sai Aunty Saliha ce ta jagoranci matan da akazo da su sai yazam kamar an raba Mommy nacan ita tana nan. Sosai suma gidan su Smart ɗin suka maida alkairi da alkairi, dan sun musu tarba ta mutuntawa duk da ba’asan da zuwansu ba. Amarya dai banda ita, tana can ana mata ƙunshi bayan Uncle Yousuf ya mata filla-filla da masifa yau dan da taƙi yarda ayi, tun yana lallashinta yaga taƙi saurarensa sai ma sake tuburewa take akan itafa babu inda zataje ya sashi yau buɗe mata wuta irin wanda bata taɓa gani daga garesa ba, dan har rantsuwar marinta yay idan bata shiga hankalinta ba. Ga wayoyinta dama ya ƙwace kusan kwana uku kenan. Dole dai ta haƙura ana can ana yarara mata wani lalle na nunama sa’a da tsara. Sosai walima tai matuƙar ƙayatarwa. Ango yasha ƙyau cikin dakakkiyar shadda sai kaiƙo take. Tana ɗaya daga cikin ɗinkunan da Abba yay masa har kala biyar domin fitar biki, sai kuma ga Ahmad da nasa kayan mamakin a safiyar yau da ƙaton akwati guda da ɗinkakkun kaya masu ƙyau har kala ashirin shima matsayin tasa gudummawar. Har ƙwalla Smart yayi a ɓoye na godiya ga UBANGIJI da ya rufa asirinsa. Dan baiyi zato ko tsammanin haka ba shikam. Walima ta matuƙar ƙayatarwa ga armashi data ƙara dalilin zuwan dattijon ƙwarai Alhaji Sufi Ado Garko da tawagarsa ta ƴan siyasa har da gwamna da yazo daga baya shi. Aifa sai gashi ƴan jarida sunyi caa anata ɗaukar rahotanni, labaran daran juma’ar nan sai gashi ya zo harda wannan taron walima darajar zuwan su Gwamna wajen. Ranar fa anguwar fagge kamar zata fashe (Kar wani ɗan fagge naji yayi magana😏🥱😂). Duk da babu inda abincin da aka tanada yajema mutane kasancewar abin ya zarce yanda aka tsarashi mutane basu damu ba. Ko’a tv kaga kanka ai ka more🤣 (Su Smart an auri ƴar gidan madara an samu promotion 😜). Tarofa yayi taro fiye da zato, dan da ƙyar aka tashi bayan sallar magrib. Dauriya kawai ango yake da ambaton addu’oi a cikin ransa dan gabansa haka kawai yake ta faɗuwa. Ga ciwon kai ƙasa-ƙasa dake nuƙurƙusarsa. Haka dai yayta dauriya bawan ALLAH dan manyan mutanen nan sai da Uncle Ameen ya kama hannunsa ya kaisa gaban kowanne suka gaisa. Da yawansu sun yaba da nutsuwar yaron, har wasun su najin sha’awar yin koyi da wannan al’amarin aure da a yanzu al’ummar mu suka daina. Da wahala kaga ɗan masu kuɗi ma ya aure mace ƴar talaka balle wannan ace namiji ne ɗan talaka ya auri ƴar masu kuɗi, kuɗin ma irin na gidan Alhaji Sufi Ado Garko da Alhaji Isma’il Ibrahim Jiƙamshi. Lallai wannan abun ayi koyine gaskiya dan sun kafa tarihi matuƙa. Washe gari asabar biki ya koma gidan su Amarya Mawaddatan’warahmah Isma’il Ibrahim Jiƙamshi. ALLAH sarki Uncle Yousuf, yau dai kam duk sai jikinsa kuma yay sanyi, dan haka tun da safe yasa aka kira masa Mawaddat ya lallasheta sosai da mata nasihar ta nutsu dan ALLAH ayi komai yanda wani bazai fahimci akwai wata a ƙasa ba. Ayi a gama cikin farin ciki. Yanda taga yanata lallaɓata da nuna damuwarsa sosai, ga dangin mahaifiyarta tako ina kowa na tattalinta da janta a jiki musamman auntyn ta matar Uncle Khamil Aunty Naja’atu ta Abuja da tasu tazo ɗaya daman. Ga ƴan uwanta su Amrah nane da ita, su twins kansu yau har murmushi sukai mata da tsokanarta da amarya suna faɗa mata har sun fara kewarta duk sai ta karaya harda kukanta. Gefe kuma rashin samun kayan shaye-shayen ta na samunta, ya kumayi matuƙar tasirin sake sanyaya mata yanayi yau ba masifa ba ko maganar kirki ma bata iyayi. Ga mafarkin mamarta da tayi a daren jiya shima ya tsaya mata a rai. Duk sai komai ya haɗu ya tankwarata a yanda su Uncle Yousuf basuyi zato ba. Mai kwalliya ta musamman aunty Naja’atu tazo mata tun daga Abuja, kuma daga Lagos ma aka ɗakkota. Ga Mommy ta mata akwati guda na kayan fitar biki masu tsadar gaske. Dai-dai da gold Mawaddat an saya mata na nunama tsara ne, karku manta itace za’a fara aurarwa a jiƙamshi family bayan auren Daddy da na Uncle Yousuf…….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣4️⃣

…….Itace ɗiya ta farko da zasu aurar. Dan haka kowa burinsa nuna mata ita ɗin cikakkiyar ƴar gata ce. Hatta Hassan da Hussaini ba’a barsu a baya ba wajen nuna tasu bajintar ta saya mata ƙyauta ta musamman. Ƙyau iya ƙyau Lulu ƙamshi tayisa. Dan a yau ta fito a ƙamshinta babu ƙarya. Da safe sunyi kamu anan cikin gidan Uncle Yousuf kamar yanda ƴammatan family ɗin Garko suka shirya, kamu ne da sisters event a tare, abin ya ƙayatar sosai. Yayinda Lulu ta zama ƴar kallo kawai tana mamakin kanta matuƙa wai a matsayin matar Aliyu driver ɗinta fa, wannan illiterate ɗin nan velleger da take faɗi kullum. (Ki kwantar da hankalinki auren wata ɗaya ne fa kacal, yanzu ma anci sati ɗaya a ciki, duk wannan taron da kike gani nuna komai ba komai ba ayishi shine mafitar da wani bazai zargi komai ba balle Baba ya ce zai aura miki ɗaya da ga cikin su Hon. Haruna) waɗan nan kalaman na Uncle Yousuf ne ke ƙara mata ƙwarin gwiwa da nutsuwar shanye komai ta na bin kowa da ɗan murmushin yaƙe. Sai yanda ƴan uwanta keta haba-haba da ita musamman yayunta maza biyu da sai zuwa suke ɗaukar hoto da ita na ƙara sakata jin daɗi. Mubeen da su Afrah kam ai sune ma kamar ƙawayen nata. Ko’ina suna nane da ita, duk sherin da akema Mubeen na kasancewarsa namiji bai bar wajen ba. (Wannan duk yana cikin shirin Uncle Yousuf daya tattarasu bayan ya tsigesu da masifa ya koma lallashi da nasiha tare da tsara musu yanda zasu kasance da ita a wajen taron bikin dan su taimakawa nutsuwarta komai ya tafi dai-dai. Sun kuma yi ɗin suma har a cikin ransu suna jin daɗin hakan kuma). Bayan tashi da ga kamu & sisters event aka ɗunguma da amarya zuwa gidan Daddy inda Mommy da Aunty Saliha zasuyi yinin biki. Gida ya cika tanƙam d jama’a, kowa burinsa yaga amarya data sake shiga ta musamman acikin wani ubansun shadda da taci aiki mai ƙayatarwa. A take ƴan uwa da abokan arziƙi suka zagayeta ana kwarara mata addu’a, sai ga Lulu da hawaye dan gaba ɗaya jitai komai ya sake kwance mata. Balle ma da Daddy ya rungumeta shima yana hawayen. Hotuna dai an shasu kala da iri har babu adadi. A sannan ne kuma tawagar dangin ango su Aunty Bilkisu da basu sami zuwa Kamu & sisters event ba suka isa gidan. Karan farko da sukaga amaryarsu, itama ta gansu. Duk da ba ƴan ɗakinsu kawai bane a kallo ɗaya Lulu ta gano tsananin kammanin Smart a fuskar Hawwah da Aunty Bilkisu. Yanda kuma suka nuna kulawarsu gareta da yanda Hawwah keta faman kiranta da auntynsu duk da tasan ta girme mata ya sata jin wani irin kimarsu da kwarjini. Suko sun ruɗe matuƙa dajin daɗin ganin yanda Yayan nasu ya samo tsuƙeƙiyar mata ƴar gata kuma ƴar ƙwalisa. Da zasu wuce tasa su Amrah ƙara musu gift da aka raba duk da an basu. Hakan da tayi sai ya ƙara mata kima a idon su Aunty Bilkisu suka tafi suna mai yaba mata da murnar kasancewar ta tasu. Duk da ma kwalliyar fuskarta yasa basu gano cewar itace lawyer ɗin nan dake matuƙar burge Ammah ɗinsu ba. Koda suka isa gida camma dai yau cike yake, dan ma sai gobe in ALLAH ya kaimu Ammah ke yinin bikinta, amma hakan bai hanasu kutsawa su kai mata abinda aka basu a gidan su Lulu ba da yabama tarbar da akai musu da karramawar da amaryar ta sake musu. Hakan bai ishi Hawwah ba sai da ta kira Smart da ke tare da su Ahmad acan stadium ana shirin buga gagarumin ƙwallon da coach ya shirya ta kwankwasa masa labari. Ta kumace ya buɗe data ta tura masa hotunan amaryarsa. Shi da farko baima yarda wai Lulun ce tai musu abinda ta faɗa ɗin ba, dan shi dai yasan wacece ya aura basai an bashi labari ba. Dan haka koda ya yanke kiran ma bai buɗe data ɗin ba ya cigaba da harkokin gabansa. Shi dai Coach ya hanashi shiga wasan, dan haka yana cikin ƴan kallo kawai. Stadium ɗin tayi matuƙar cika maiban mamaki, can dai kamar wanda aka tsikara ya ciro wayarsa da ga aljihu ya buɗe data bayan ya shiga WhatsApp nashi. Akan idonsa hotunan suka buɗe zuciyarsa sai motsi take a ƙirjinsa, sai yayi kamar zai fasa sai kuma dai ya daure har suka kammala buɗewar dan sunada yawa. Hoton farko dai babu ita a ciki, na biyu ma haka. Na uku ita kaɗaice zaune ta kare fuskarta da waya alamar bata son hoton, yawu ya haɗiye a hankali dan duk da fuskarta bai fito ba tayi ƙyau. Ƙara matsawa yay na gaba ananne da sai da tsigar jikin yan maza ta tashi, ya ɗan lumshe idanu ya sake buɗewa yana mai furzar da huci kaɗan. Anan kam raɗam ta fito daga sama har ƙasa aka ɗauketa kuma, ta ɗan juya Luluu eyes ɗinta gefe kaɗan tana kallon gefenta. Ɗan bakin masifar nan da yaci lipstick pitch da maroon kaɗan yay wani irin masifar fidda shape ɗin sa. Haka ma zagayayyar fuskarta mai ɗauke da hanci da yay dai-dai da ita ga manyan idanu masha ALLAH. Yau ne karo na farko da ya ga kwalliya a fuskarta. Sake furzar da iska yay kaɗan gaba ɗaya ma ya rasa yazai fassara yanayin da ya shiga. Sai kawai ya zaɓi kife wayar ya ajiye yana mai harɗe hannayensa a ƙirji ya kwantar da bayansa zuwa kansa luf a kujerar da yake zaune ya ɗan lumshe idanunsa sai dai bai rufesu duka ba yana kallon tarin abokan kwallonsa da sukazo da ga gari-gari domin tayashi murnar aure ƙasa-ƙasa.

      Suma wasan nasu yayi ƙyau, sai da akai kiran magrib suka tashi sai kuma an haɗu a wajen dinner, dan Coach shi yay ƙoƙarin bama baƙinsu masauki duk da wasu ma sai yau suka iso dai shine kuma mai gayyatar da Ahmad. “Wai ya naga duk jikinka yay wani laƙwasa ne? Ko ciwon kanne bai saukaba still?”.

    Cewar Ahmad cikin damuwa. A hankali ya ɗan furzar da iska tare da shafo goshin nasa ya ce, “Ai ciwon kan nan inaga kozai barni sai an gama hayaniyar nan. Harma na saba da shi a kwana biyun nan”.

     Sannu Ahmad ɗin yay masa cikin damuwa. A haka suka ƙarasa gidansu Ahmad ɗin dan acan zasu yi shirin tafiya dinner ɗin, kafin su wuce su ɗauki amarya a gidansu…..

         *_DINNER HALL_*

   Ƙaton waje ne na gaske Alhaji Sufi Ado Garko ya kama domin ya gayyaci manyan abokan kasuwancin sa dana siyasa a ciki da bai ɗin Nigeria. Gashi kuma mafi yawansu sun san Daddy shima tun da babban yaronsa ne na amana da duk wanda yasan Alhaji Sufi Ado Garko to yasan wanene Alhaji Isma’il Ibrahim Jiƙamshi a wajensa. Iya tsaruwa wajefa ya tsaru, ga abinci iri-iri an tanada. Haka ma manyan mawaƙa na Hausa dana turanci duk sun hallaro. MC kansa mashahuri aka ɗakko domin gabatar da komai. Ta gefe ɗaya ƴammata da samarin Garko family da suka haɗe da jiƙamshi family sun haɗa babban show mai ƙayatarwa domin nishaɗantar da jama’a. Duk da girman wajen da alamu ya nuna zai ɗauki mutane masu yawa duk wanda zai shiga sai da i.v ɗin sa ne zai zama masa gate pass. Dan haka su kansu su Smart da ahalinsa suka shirya komai a tsari domin mutunta kansu a wajen. Duk da dai Alhmdllh ALLAH ya riga ya mutuntasu, tunda da har zuwa yanzu babu wata ɓaraka data shiga na raina juna a tsakani, ko Umma daketa neman hanyar baƙanta Smart wajen wani a cikin dangin matar tasa har yanzu ALLAH bai bata damar ba. Kafin takwas waje da ya cika yay hani’an da manyan mutane ƴan siyasa da ƴan kasuwa har ma da ƴan bokon da iyalansu. Kowa ka gani shar da shi, dan duk da ba’ai anko da zai zama komai da komai iri ɗaya ba sun rubuta kalar kayan da ake buƙatar ƴammata da samari duk su saka. Koma wani iri ne ka saka kala kawai ake buƙatar tazo ɗaya. Manya ne dai kowai yay yanda yake so….

           Masha ALLAH na faɗa a lokacin da idanuna suka sauka akan ANGON ƙamshi Aliyu Hydar Smart mai masoya da yawa cikin wata dakakkiyar shadda mai tsananin ƙyau da maiƙo taji aiki na musamman. Itace kawai abinda ya yarda ya amsa da ga dangin amaryar tasa dan Baba ya aiko masa da ita matsayin wadda zai saka a yau ɗin, kamar yanda itama amarya ganin nata kawai tayi. Farar shadda ce da akaima wani shegen ƙawataccen aiki da kalar golden mai ɗaukar ido. Takalmar ƙafarsa haif cover suma golden da ratsin fari, haka ma hularsa golden da ratsin fari kaɗan. Sai agogonsa golden shima. Ga gyaran fuska da ya ƙara masa kwarjini da cikar kamala an masa. Sam wannan Smart ɗin ya banbanta da wancan Smart dirver da kuka sani. Ƙamshi har ba’a magana. Tun a gida Ahmad ke jera mar hotuna dan yakai a ɗaukesan. Ya kuma tubure bazai tafi ba sai yaje Ammah da Abba sun gansa. Dole sai da su Ahmad suka kaisa gidan kuwa Ammah da Abban suka gansa da tsaffin da bazasuje dinner ɗin ba. An masa hoto da iyayensa Abba ya rungumesa. Duk kauce-kaucen Ammah sanda za ɗauke su hoto itama sai ya kwanta da kansa a kafaɗarta, hakan yasa ta juyo kamar zata hararesa shi kuma yay murmushi cikin salon shagwaɓe fuska, ga Abba ya kallesu shima yana murmushi. Hoton sai ya zama na musamman……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣5️⃣

……Daga nan gidan Daddy suka ɗunguma ɗaukar amaryar ƙamshi. Lulu lu’u-lu’un Jiƙamshi family, tauraruwa abar buƙatar son ganin kowa.

       “Ya arrahaman!” Ango Smart ya ambata a hankali lokacin da Hussaini ke fitowa da ga gidan riƙe da hannun Lulu. Ni kaina masu karatu sai da alƙalamina yay adungure ƙasa da ƙyar na kamosa na cigaba da muku burutun. Amarya da tayi jiƙaƙƙen ƙyau, idan nace muku ƙyau ina nufin ƙyau maƙurar ƙurewa a cikin ƙarshen ƙure. Wani irin shegen material ne golden color da aka ƙawata da adon fararen stones masu walwali da ɗaukar idanu. An masa ɗinkin gown data kama mata jiki, sai aka ɗaura wani ƙawataccen alƙyabba fara da adon golden kuma a sama, ta rufe jikinta gaba ɗaya tana ɗan jan ƙasa kaɗan. Ɗauri iya ɗauri, ga shi kwalliyar da akai mata ƴar dai-dai misali da bata ɓatar da ainahinta ba a yanzu. Kayan yari komai yaji, ƙamshi kam ba’a magana wayyoni ALLAH kai jama’a. Yaufa Lulu ƙamshi a ƙamshin take ɗan gaske. Takalman ƙafarta su kansu abin kallo ne, suma farare ne da kwalliyar golden sai pos ɗin ta itama farace da kwalliyar golden stones. Kamar shock ne ya jasu a lokacin da Hussain ya kamo hannun Smart ya saka masa na Lulu. A tare suka zabura zasu janye amma tsabar muguntar Hussain ya sake riƙewa gam ya hana hakan. Duk sai sukai diri-diri da idanu (kamar an kama suruki a ɗakin ƙawar kakar matarsa😂😜) cikin wani irin malalacin yanayi ta sakar ma Smart kasalalliyar Harara. Sai kawai ya samu kansa da ramawa shima. Shi Hussain ma sai abin ya bashi dariya. Amma sai ya danne daƙyar baiyi ba ya sake matse hannayensu cikin na juna da faɗin, “Yayana Aliyu Hydar Zakin zaki ga amanar ƙanwata na baka, har abada bana son ka saki wannan hannun ya kasance cikin laluben naka dan ALLAH”.

         Smart da Adams apple ɗinsa keta kaikawo a maƙoshi ya saki murmushi mai sanyi da faɗin, “In sha ALLAHU Yaya Hussain. Na kuma gode”. Murmushin jin daɗi Hussain ya saki jin Smart ya kirashi da Yaya, duk da kuwa yasan Smart ɗin zai iya girmarsa da kusan shekaru biyar ma. Hannayen nasu ya saki yana kallon fuskar Lulu da tai wani irin yin takwaf-takwaf tana neman zame hanunta dake cikin na Smart shi kuma ya hana faruwar hakan ta hanyar damƙesa da kyau, kansa ya girgiza mata da ɗan lumshe idanu alamar lallashi irin na yaya da ƙanwa. Dole ta haɗiye abubuwan da ke mata kaikawo a zuciya da maƙoshi a tare, Hussain ya buɗe musu motar da Ahmad ke ciki yana jiransu a mazaunin driver. Ita ta fara shiga, sannan shima Smart ɗin ya shiga, sai kawai Hussain ya shiga gaba dan Uncle Yousuf ne duk ya tsara musu hakan saboda dai kar mutuniyar ta bada ƙafa🤣 dan tabbas zata iya maida hall ɗin kudanci da ga gabashin da yake a gine😂. Ganin Hussain ɗin kam ya sake saka mata nutsuwa da ƙwarin gwiwa harda sauke ajiyar zuciya kamar Smart ɗin yazo ɗauketa kenan😂. Bata ƙara yarda ta kallesa ba duk da harga ALLAH ya matuƙar canja mata tamkar bashi ba. Ta kuma saka pos ɗin ta a tsakkiyarsu alamar karma yace zai raɓeta. Shima dai dama baiyi niyyar hakan ba, shiyyasa yay zamansa sosai jikin ƙofa suka bada gaf sosai a tsakkiyar. Da ga Ahmad har Hussain sai da suka ji dariya a zukatansu saboda yanayin zaman amarya da angon. Ga shi kowa ya juya kai ya kalli waje tsabar babu ruwan wani da wani ma kenan. Sai da suka fara tafiya Hussain da Ahmad suka gaisa. Da ga haka sukacigaba da ƴar hirarsu a hankali su biyu har suka iso. Wajen fita ne fa dole dai Lulu ta haƙura Smart ya fara fita, dan shine ya buɗe mata da kansa ya kuma miƙa mata hannunsa alamar ta ɗora nata. Ƙaramar Harara tai masa tana ɗauke kanta, sai kawai ya cije lips ɗinsa tare da ranƙwafowa gaba ɗayansa yana tattare hannun rigarsa bayan ya cire link ɗin, miƙa hannun yay alamar zai ɗauketa. Da wani irin bala’in sauri ta waro duka manyan idanunta waje da faɗin, “Kuttt! Mi zakayi?!”.

        “Ɗaukarki mana. Ba haka kike buƙata ba Madam”. Ya faɗa cikin salon ɗage gira ɗaya da kashe ɗayan idon. Tsabar abinda ya tokare maƙoshin Lulu sai taji kamar ta buɗe dukan muryarta ta ƙwala ihun da kowa da ke hall ɗin sai ya fito ma. Ta tsani wannan Madam ɗin da yake kiranta da shi tun daga randa sukaje duba shi. Ganin yanda ta fara cika ya sashi ɗage duka hannayensa (alamar wanda yay surrender) da gyara ranƙwafar da yay yana dungure kansa da faɗin, “Kai Aliyun nan ka nutsu a gaban Madam kake”. Sai kawai ta ƙara watso masa harara da tura baki gaba. Da sauri ya ɗauke idanunsa dan harga ALLAH sai da ƙassan jikinsa suka amsa akan tura bakin nan. Hussain dake dariyar drama ɗin tasu ne ya katsesu da faɗin, “Sorry kinjin Sister bashi hannun kinga su Baba duk suna ciki shigowarku ake jira kawai a fara abinda ya tara mutane”. A hankali ta ɗago yatsunta uku batare data kallesa ba. Shima sai ya saka nasa ukun tsakkiya kamar yanda tayin yana ɗan taɓe baki kamar yanda tayi, sai da ya riƙo hanun nata baki ɗaya sannan ya rumtse cikin nashi. Koda ta fito bai yarda sun bar jikin motar ba sai da yasa ɗayan hannunsa da kansa ya gyagygyara mata rigar alƙyabbar da ƙyau yanda ta sake suturta kuma hakan bai hana fitar ƙyaun da tai ɗin ba. Da ga haka suka ƙarasa inda abokan ango dana amarya ke jira suka tafi a nutse kamar yanda ake raka amarya da ango ƴan gata zuwa ga hi table. Matuƙar birgewa sun burge mutane da yawa, yaro da babba ƴammata da samari. Taro ne da ya haɗa harda manyan mutane da iyaye da kakanni shiyyasa babu wata shiririta ko baɗala a cikinsa. Amarya da ango ma tunda aka kaisu mazauninsu hatta cake a zaunen suka yanka shi. Koda ta ɗibo danta bashi maimakon yin hakan saita lakata masa a hanci. Abin ya burge mutane da basu dariya, dan yanda tayi ɗin sai ka ɗauka duk cikin soyayya ne, itako tayi hakanne danta bashi haushi.

        Shima daya ɗibo ya kai mata baki, buɗewa tai tana shiryama ranta muguntar gallara masa cizo a yatsun dake riƙe da cake ɗin, amma sai da yaje gab da bakin nata sai ya juya hannun ya lunƙuma a nashi bakin yana mata gwalo. Ai hall ɗin kamar zai fashe dan dariya saboda yanda ta sakankance zatayi mugunta amma aka rusa mata plan. Pos ɗin hannunta ta ɗan buga masa a damtsen hannu tana hararasa kamar zatayi kuka dan haushi.

       “Aliyu abin tausayi wannan harara dai ka banu da ita kai kam. Anya an taɓa angon da yasha harara a ranar aurensa sama da ni?” ya faɗa yana mangare kansa da kansa. Karan farko ya bata dariya amma sai ta gimtse, tama ɗauke kanta gefe tana ɗan taɓe baki, dan yau sam bata da ƙarfin yin masifa kuma. Da ƙyar aka samu hall ɗin ya lafa da dariyar batun cake aka cigaba da abinda ya tara mutane. Ko sau ɗaya Smart bai yarda ya tashi ba hakama Lulu bai bari ta tashi ba. Da an buƙaci ganinta a wajen fili zai riƙe mata hannu ya girgiza kansa, itama ɗin dama bata da sha’awar tashin, saita fisge hanunta tana harararsa dan yau ita kaɗai aketa faman antaya masa buhu-buhu. Har fa dai MC ya fahimci ango bai san amaryarsa ta tashi kamar yanda shima bai tashi ba. Masu musu liƙi ma dai sai dai su samesu anan. Alhamdullah duk wanda ya shigo wajen nan zai tabbatar maka yaci ya ƙoshi har ma da ƙullar takeaway,  Smart ya gaisa da mutanen da bai taɓa tunanin ganinsu koda a zahirin rayuwa ba, dan ƴan siyasa sun halarci taron nan matuƙa da manyan ƴan kasuwa. Har akai aka tashi bayan cake ɗin nan da ruwa baici komai ba a wajen, hakama Lulu ita daman cikin nata ya riga ya naɗe abincin ba damunta yay sosai ba. Ganin dare yayi dan sha biyu ta gota sanda aka tashi Uncle Yousuf yace su Smart ɗin suje gida abinsu zai koma da Lulu gida, dan tun a hall ɗin ya ga Smart nata faman dafe kai alamar bayajin daɗi dauriya kawai yake yi. Yako ji daɗin hakan da Uncle Yousuf ɗin yay musu, itama kuma mai gayya mai aikin taji daɗin hakan, dan ko sallama bata tsaya sunyi ba tai gaba tai shigewarta mota tana zare alƙyabba ɗin tata datai mugun damunta ita da ɗaurin ɗan kwalin….

*_WASHE GARI_*

   Washe gari safiyar Lahadi aka tashi da shirin kai amarya Lulu. Dan haka da safe Uncle Yousuf ya ɗauketa da kansa ya kaita gidan Baba. Inda yayye da ƙannen mahaifiyarta suka taru domin mata nasiha. Alh. Sulaiman ne kawai babu, sosai zuciyar Lulu tai matuƙar rauni, dan mahaifiyarta ce kawai babu a wajen bayan mahaifin Tajuddeen. Ita kaɗai suka taɓa rasawa a cikinsu……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣6️⃣

……..Kuka ne sosai ya kufce mata, dan matuƙa tana so da begen mahaifiyarta. (Dan Lulu ta kasance irin yaran nan ne masu ƙulafucin uwa, sai kuma gashi ALLAH bai ƙaddara zata rayu da ita ba) kukan nata ya sake karya zuciyar iyayen nata, haka ma Baba duk da dauriyarsa sai da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Hannunta ya kama ya zaunar a kusa da shi tare da ɗora kanta a kafaɗarsa ta dama yana ɗan bubbuga bayanta alamar lallashi. Sai da suka samu taɗan tsagaita kukan sai ajiyar zuciya da take faman saki sannan baba ya fara mata nasiha. Bayan ya gama kowa a falon yay tasa. Kakarta da suke kira Dada ma dai ta danne abinda ke ƙasan ranta na ƙiyayyar auren tai mata nasiha sama-sama, dan ta ɗauki alwashin sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen raba wannan auren ƙaddarar. Komai da suke faɗa yana shiga kunnen Lulu, sai dai zuciyarta na fassara komai da gargajiyanci da kuma tsauri da yawa saboda ita tunaninta daban da nasu kasancewar babu ilimin addini a tare da ita. Kuka ma da sukaga tanayi na tuna mahaifiyarta ne kawai babu na aure dan a wawtarta auren nan dai na wata ɗaya ne kacal. Duk wata ƙyauta da iyayen nata suka shirya bata anan wajen suka bata ita kamar yanda tsarin family ɗin yake. Bayan an gama Uncle Khamil da Uncle Shu’aib suka ɗauke ta suka maida gidan Daddy dan Uncle Yousuf yana ajiyeta ya juya. Acan ɗin ma dai bayan sallar azhar Daddy da Uncle Yousuf, Mommy aunty Saliha da gayyar iyaye ƴan jiƙamshi suka zagayeta da tasu nasihar, duk da dai Daddy baice komai ba, sakamakon gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, jikinsa duk a sanyaye yake alamar damuwar rabuwa da ƴar tashi. Sai dai yana ƙoƙarin dannewa amma hakan ya gagara. Bayan tashi da ga wannan zaman aka cigaba da kimtse-kimtsen tafiya da amarya, yayinda Aunty Saliha ta sake ɗaukar Lulu ta kaima matan nan masu gyarata suka sake murjeta tas da kayan gyaransu na musamman da tarin ƙamshi kala-kala. Ba kuma a maidata gidan Daddy ba sai huɗu na yamma cikin shirin miƙata gidan iyayen mijinta. Tayi ƙyau matuƙa cikin atamfar da Aunty Saliha ta bata ta saka. Aka kuma ɗora mata alƙyabba ƴar ubansu baƙa mai kwalliyar golden da fari kaɗan, sai stones da suka sake ƙawatata. Shara-shara alƙyabbar take. Takalmanta yau ma flat ne baƙaƙe. Babu kwalliya ko ɗis a fuskarta dan tace bata so. Sai dai hakan bai hanata zama mai cika ido da kwarjini irin na amare ba, ga gyara tasha na fitar hankali dama fatar nan ta sake wani irin ƙyau kamar madara a sabuwar ƙwarya (Dangin Smart ban son jealous 🥱😉) Hankalin Lulu bai tashi ba sai da taga Daddy na hawaye sanda aka fito da ita yana riƙe da hannunta zai sakata a motar da Hassan zai ja, dan sune zasu mata rakkiya shi da Hussain da Mubeen. Sai motar ƴan rakkiyar amaryar su biyosu a baya. Duk da abokan ango sunzo kasancewar amaryar ƴar dangi ce akwai zugar motoci da ga family ɗin biyu na Jiƙamshi da Garko da zasu bisu da nasu motocin. Ba Daddy kawai ba Uncle Yousuf kansa yana can falon Daddyn yana sharce hawaye yamaƙi fitowa shi. Lulu da duk taji karaya tamkar ba ita ɗin nan ba ta rungume Daddy ta saki kuka mai ban tausayi. Itafa auren nan baisa taji komai, amma wasu abubuwa da ga zuri’ar tata kansa zuciyarta ta motsu. Da ƙyar Uncle Khamil ya janye Lulu a jikin Daddy aka sanyata a mota, Hussain da Mubeen suka sata a tsakkiya, gaba kuma Amrah da Afrah ne sai Hassan da zaija motar.

      Masha ALLAH motocin rakkiyar Lulu sun ratsa kwaryar Kano ne tamkar wata gwamna zata gitta dan gatan da zuri’arta suka nuna mata. Duk inda suka ratsa sai anso jin wanene haka? Koda babu mai bada amsa. A haka suka iso anguwar fagge layin su Smart. Yanda aka jera motocin tun daga ƙofar gidansu har kusan ƙarshen titin ya sake ɗaukar hankali matuƙa, hatta mata dake cikin gidaje fitowa suke leƙen wannan sabon lamari, lallai an sake shaida Smart kam dai ya ɗakko ƴar gidan madara.

      Smart da ƴan uwansa mazan gidansu suna falon Abba daya tarasu su duka amaryar ta iso. Daga ɗakin suna iya jin surutai da gidan ya ɗauka da kambama yawan motocin da suka rako amarya. Balle ma motar da aka kawota ciki ta musamman ce da Daddy ya saya mata matsayin gift na aure. Tasha adon ribbon kuwa da balun masha ALLAH. A hankali Smart da ke kusa da Rufa’i mai bi masa babban ɗan Mama ya lumshe idanunsa yana jin wani irin yanayi mai wahalar fassara na saukar masa. Addu’a ya shiga karantowa game da wannan aure nasa mai cike da rikici takowane ɓangare. Ita kanta amaryar da nata.. Addu’ar Smart kamar an saita dai-dai da fitowar Lulu amaryar ƙamshi da ga mota Mubeen riƙe da hannunta. Fuskarta rufe take ruff da hular alƙyabbar dan haka ba’a iya ganinta tako ina sai hannunta mai ƙawace da adon zanen lalle ja da baƙi. Da wani sirrintaccen ƙamshi na musamman mai ratsa ɓargo da jijiya. Har cikin gida Hassan da Hussain da Mubeen da su Afrah sukai mata rakkiya, hakan ya matuƙar sake burge mutane da kallon al’amarin matsayin shaƙuwa ce ta kawo hakan tsakaninsu. Sun kaita har ƙofar falon Ammah da ke cike da ƴan uwanta itama, da ga nan Aunty Saliha da Aunty Naja’atu suka kama hannunta suka ƙarasa da ita cikin falon Ammah. Da ga haka su Hussain suka juya cikin sanyin jiki da basu taɓa tunanin zasu iya ji akan Mawaddat da sukai ƙololuwar tsana a cikinsu ba dalilin fifitata da mahaifinsu yay sama da su da mahaifiyarsu. Mubeen ma sai kawai ya kama hawaye….

     Sauran ƴan rakkiyar amarya sun ɗura ciki suma. Wasu farin ciki ya kawosu wasu ko gulma da jinjina inda ALLAH ya kawo Lulun. Duk irin yanga da jin kai da izza irin tata ta ƙare da aure a getto eria irin haka? Kai lallai da mamaki koda yake tarihine ya maimaita kansa tunda haka itama mahaifiyarta tayi, sai dai akwai banbanci sosai a yanayin tsarin auren. Wasu ma harda dariyar mugunta wasu ko tausayinta suke ji a nasu ganin taci baya gaskiya. Wasu ko tayata farin ciki suke ALLAH ya kawota matakin da ko wacce ɗiya mace ke jin alfahari da ɗaukaka. Abu mafi ɗaukar hankali tarbar mutuntawa da suka samu daga ahalin ango duk da yawansu. Ammah kam da ga ciki su Aunty Nasara na shiga da Lulu ta taso ta rungumeta a jikinta. Haka ma ƴan uwanta sai faman musu lale marhabun akeyi. Ajiyar zuciya Lulu ta dinga saki da sake lafewa aikin Ammah, dan wata irin nutsuwa taji tana ratsa mata sassan jiki da ɓargo batare data san dalili ba. Duk da bata san wacece ita ba, ba kuma ta gani fuskarta abinda matar tai mata ya sata jin ƙaunarta. Bayan kakarta Dada Ammah ce mace ta biyu datai mata runguma irin ta mahaifiya, a hankali hawaye suka shiga ziraro mata daga cikin hular alƙyabbar tsigar jikinta na wani irin tashi. Adda Fati babbar yayar su Ammah da suke uba ɗaya ce tazo ta kama hannun Lulu aka shiga da ita ƙuryar ɗakin Ammah da aka gyara dama dan tarbar amaryar, shiyyasa kowa ya fito aka dawo falo da ɗayan ɗakin dan kowance a gidan dama ɗakuna uku ne a falonta.

        Gida ya sake amsar harami tako ina, dan ƴan kawo Lulu basu wuce ba sai kusan biyar da rabi na yamma. Lulu na can ƙuryar ɗakin Ammah tare da su Amrah dan ita dai fa babu ƙawa, dama da lafiya-lafiya ne da Nadiya ce zata kasance da ita. Sai dai ta riga ta jingine tarayyarsu a matsayin tarihi ita kuma idan ta ɗana tarkon tafiya bata waiwaye. An tara musu abinci da abin sha kala-kala har da su fura mai ƙyau da tsafta. Aiki su Amrah suka shiga cin nama da furar nan dan sun musu da ɗi. Da farko dai Afrah zata fara wani iyayi Amrah tai mata gargaɗi da tuna mata kashedin da Mommy tai musu. Hakan yasa ta dawo hankalinta, sai da suka buɗe abincin kuma taji ɗanɗano sai ta ware ta hau ci. Duk abinda suke Lulu na kwance lamo a gadon Ammah tana kallonsu kawai. Kanta ke mata wani irin masifar ciwo, dan tana cikin matsanancin buƙatar kayan shaye-shayen ta matuƙa. Kwana bakwai fa kenan bata sha komai ba, kai ai tayi ƙoƙari matuƙa. Har ji take ana mata mutsu-mutsu a brain, ga hayaniyar bikin nan na matuƙar caja mata kai itama. Dan ma nan ɗin da aka kawosu su kaɗai ya mata daɗi, duk da sunajin hayaniyar amma da sauƙi ba kamar suna a wajen ba. Su Aunty Saliha basu wuce ba sai bayan magriba su, ƙin shigowa sukai mata sallama dan karsu takalo ta, bayan wucewarsu ma cikin gidan ta fara lafawa da mutane, dan dj da su Mubarak suka sa ya kwashi mata duk anyi waje. Tuni su Amrah ma da ke jiyo sautin kiɗa suka gudu suka barta ita kaɗai a ɗakin. Batace musu komai ba sai lumshe idanunta da tai barci ya kwasheta, cikin mintina ƙalilan zazzaɓi mai zafi ya rufeta ruf ta hau rawar sanyi, ga fanka na juyawa a ɗakin ta kasa tashi ta kashe ta. Barcin take a wahale ga mafarkin mahaifiyarta……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣7️⃣

……..Wajen ƙarfe tara ALLAH ya kawo aunty Bilkisu ɗakin zata ɗauki kayan biki data ɓoye dan bama facalolinta da zasu wuce. Da sauri ta ƙarasa gaban gadon tana ambaton sunan ALLAH. Ta kai hannunta a goshin Lulu dake barci. Zafi zau har tana jin harbawar jijiyoyin kan nata. Bargo taja ta lulluɓa mata, sannan ta kwashi abinda tazo ɗaukar ta fice. Bata san yin kwakwazo hankalin mutane ya dawo nan, dan haka ta sallami facalolin nata sannan ta koma cikin raɗa ta sanarma Ammah da ke a cikin danginta da zasu kwana. Hankalin Ammah ma ya tashi, ta miƙe cikin hikima ta shiga bedroom ɗin, itama dai tattaɓa goshin nata tai, sai kuma ta juyo tana kallon Aunty Bilkisu.

      “Yanzu ya za’ayi kenan? Dan nima bana son kowa ya fahimta baki baka san yanda na wani yake ba”.

     “Hakane Ammah, to kodai a kira Hydar, sai ya samo mata magani”.

    Ɗan jimm Ammah tai na tunani, sai kuma ta ɗan sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Kirashi ɗin to. Ki kuma turomin Auntynku”.

          Da to Aunty Bilkisu ta Amsa tana fita, sai da ta fara zuwa tai kiran aunty Amarya da Ammah tace kafin ta wuce sashen samarin gidan. Duk suna waje wajen dj balle ga ƴammata dama cike da gida, dan kusan duk ɗakunan ma a kulle suke, sai ɗakin Smart ne da ya nuna haske ke tabbatar da mutum a ciki. Sallama tayi aka amsa mata sannan ta shiga. Shi da Ahmad ne kawai a ɗakin, dan abokansu su kam yau duk kowa ya kama gabansa tunma da safe kasancewar gobe idan ALLAH ya kaimu Monday kowa zai koma kan aikinsa. Ahmad da ke zaune yana shan fura ya dubi aunty Bilkisu da murmushi yana faɗin, “Aunty Babba ke da kanki”. Murmushin ta mayar masa da faɗin, “To ya na iya Ahmad, amaryarku ce babu lafiya”.

      “Ya Salam! Miya faru?”.

  Ya faɗa da sauri. Dai-dai nan Smart ya fito da ga toilet da alama wanka yayi, sai dai sanye yake da jallabiya sai ƙaramin towel yana goge sumar kansa. Su biyun duka ya kalla saboda jin abinda Ahmad ya faɗa, da son jin amsar da Aunty Bilkisu zata bada. Cikin damuwa ta ce, “Zazzaɓi ne da ciwon kai mai zafi. Gata can cikin bargo tanata rawar sanyi ma”.

       Smart ya ɗan lumshe ido ya buɗe, sai kuma ya ɗauki turare ya ɗan fesa da faɗin, “Inaga hayaniyar nan ce….”

    “Hakama Ammah tace, shiyyasa ma tace a kiraka”. Aunty Bilkisu ta katsesa da sauri. Ɗan Basket ɗin da yake ajiye magunguna ya ɗauka, sai kuma ya dubi Ahmad da faɗin, “Ina zuwa”. Kai ya jinjina masa da mata addu’ar samun lafiya. Su kuma suka fice. Cikin gidan da sauƙin mutane dan duk ana waje wajen dj, sai ƴan tsofaffin ne da suka gaji sukai zamansu. Aunty Amarya ce ta taresu tun a farkon shigowa tace su biyota. Binta sukai sashenta, falon babu kowa sai yara da aka kwantar, kuma duk yaranta ne, dan ita danginta ma duk sun wace sai ƙanwarta budurwa da zata kwana tana kuma tare da su Maryam. Kai tsaye bedroom ɗin ta suka shiga, Lulu da aka maido nan tana kwance a gado cikin bargon da Aunty Amarya ta lulluɓa mata. Aunty Bilkisu tace “Yauwa nan aka maidota ashe?”. Amsa Aunty Amarya ta bata da “Eh nan ɗin yafi ƙarancin hayaniyane”. Sai kuma ta kalli Smart da ya zubama gadon idanu kawai batare daya ƙarasa ba. Katseshi tai da faɗin, “Hydar ƙaraso, Bara a samo ruwa tasha magani, sai dai banajin ma tunda aka kawota gidan nan taci wani abu. Ko a ɗan samo mata abinci? Ko tea haka ko”.

      A hankali ya ce, “Ko tea ɗin dai zaifi”.

     Babu jimawa Aunty Amarya ta dawo da tea da ruwa. Tana ajiyewa suka fice ita da aunty Bilkisu, sai lokacin ya ƙarasa gaban gadon. Da ga tsaye ya kai hannu kan bargon ya ɗan yaye kaɗan idanunsa suka sauka akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Kamar ko yaushe yau ma babu kwalliya, sai wani irin sirrintaccen ƙyawu data ƙara fiye da yanda ya santa. A karo na biyu bayan ranar dinner daya riƙe mata hannu ya taɓa jikinta yanzu ma. Saukar hannunsa mai sanyin danshin ruwan wankan daya fito ya sata buɗe idanu kamar a ɗan zabure. Cikin sa’a kuwa suka faɗa cikin nasa saboda shima kallonta yake. Sake waro idanun tai da ƙyau, sai kuma ta kai hannu ta buge masa nasa hannun da har yanzu ke akan goshin nata tana hararar sa. Cikin ƙarfin hali ta ce, “Kai kuma waya gayyatoka nan?”. Yanda tai maganar da son yin masifa sai dai babu ƙarfi yaso bashi dariya, amma sai ya danne abarsa baiyi ba, sai ma kaiwa zaune da yay a bakin gadon har jikinsu na gogar juna sai dai ita a bargo take, kanta ya ɗan kifo yana raba hannayensa gefe-da-gefenta ta kasance a tsakkiya. Idanunta data sake rufewa ta buɗe da sauri jin saukar numfashinsa saman fuskarta duk da akwai ƴar tazara a tsakaninsu, ta sake watsa masa harara ta ce, “Kai kuma wai miye haka? Kake yi”.

       Karan farko cikin ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci guda ya motsa lips ɗinsa dan shima dai ciwon kansan nan na tare da shi a yau ma yini guda. Dan ma yanata addu’a da shan addu’oi wajen Malam sannan Abba yay masa kamu ɗazun da magrib shine ma ya ɗan samu barci sai yanzu ya tashi yay ɗan wanka zaiyi sallar isha’i da shafa’i da wutri aunty Bilkisu taje. “Zan dai yi Madam. Amma first ina son sanin mike damunki?”. Yay maganar cikin tausasa harshe sosai.

      “Meya ruwanka malam nifa bana son shishshigi ka sani”. Itama ta faɗa cikin tsiwa da takurar yanayin kusancin nasu.

    “Inafa na sani, sai dai yanzu da kika faɗa zan kiyaye. Amma yanzu dai ni ba faɗa nazo muyi ba, tashi kici abinci kisha magani”.

    “Nace maka ina buƙata ne?”.

  “Basai kina buƙata ba ai”. Ya bata amsa yana ɗaura hannunsa saman bargon zai yaye. Tattaro bargon tai ta da sauri ta tattaro cikin hannunta zata fisge daga nashi. Hakan yasa ya ja shima, itama ta ja, ya ƙara ja, itama ta fisga cikin sake fusata duk da bata da wani ƙarfin kirki a jikinta. Ga bakin masifar sai motsi yake alamar magana take son yi amma bata fita. Da ɗan ƙarfi yaja kasancewar ƙyaleta kawai yake dama, aiko ya ɗage bargon. Gaba ɗaya ta tattaro da hannunsa da bargon ta fisgo cikin takaici sai kawai ya biyo su shima ya faɗa mata a jiki fuskokinsu kan na juna kowa na shaƙar numfashin ɗan uwansa, lips ɗinsa a kan nata. Sosai zukatansu suka hau dokawa da sauri-sauri a tare, sai dai kowanne da dalilinsa. Lulu da wani shuɗaɗɗen al’amari mai matuƙar zafafa zuciya da ƙonata ya fara son hasko mata a memory tasa dukan sauran ƙarfinta ta turesa jikinta na rawa. Hakan bai sakashi yin ko gezau ba, sai dai shima ya matsar da fuskarsa da ga kan nata, sai kuma ya ɗagata jininsa na wani yamutsawa. Zaune ta tashi tana ƙoƙarin sauka a gadon kamar wadda ke neman rasa nutsuwarta dan jikinta rawa yake, yay saurin dakatar da ita cikin sassarfar harshe shima. “Ina kuma zaki je?”. Ganin tana cigaba da janye bargon zata saukan ya riƙota da sauri. Harara ta watsa masa da idanunta da suka kaɗa sosai. Ga jikin nata rawa yake da gasken fa. Magana take son yi amma ta kasa, sai idanunta dake cikowa da ƙwalla. Mamaki sosai hakan ya bashi, amma sai ya sake yinƙurin riƙota.

           Hannunta ta fisge, sai kuma ta dafe kanta wasu hawaye masu zafi na sake wanke mata fuska. Idanu ya zuba mata ganin yanda jikinta ke ƙara ƙarfin rawa, hakan ya matuƙar sake ɗaure masa kai da zuciya, dan yanayine bawai mai nuna ƙin da take masa ba matsayin wanda bata so ko tafi ƙarfin aurensa, ba kuma kuya bace. Al’amarin nata kamar dai like wadda ta tuna wani mummunan al’amari mai firgitarwa da ciwo a zuciyarta da yay kamanceceniya da yanayin da suke ciki. Kanta ta sake girgizawa da sake yinƙurawa zata ƙarasa sauka ya miƙe da sauri ya zagaya gabanta. Cikin nuna kulawa da son maidota a nutsuwarta ya ce, “Kinga Please relax, ko mima zuciyarki ke son ayyana miki ba haka bane ba, koma ki kwanta kinga baki da lafiya”.

        “Idanunta da sukai masifar kaɗawa da ja ta ɗago ta zuba masa. Sai kuma taja da baya da ga kusa da shi har yanzu dai da alamar bata samu nutsuwar da yake buƙatar ba. Shima sai ya matsa ɗin da kallon ƙofa ya kuma sake maido idanunsa kanta. “Kin gane bana son wani ya fahimci akwai wani abu a tsakaninmu saɓanin abinda suke kallo a bayyane. Ki daure zuciyarki na roƙeki koma mi kike tunani ki ajiyeshi gefe”.

        Yaraf ta koma saman gadon ta zauna, hannunta dafe da kanta muryarta na fita da rawa da ɗan kaushi ta ce, “Ka kira min wata a cikinsu bazan iya zama da ga ni sai kai a ɗakin nan ba in har dole sai jikinka ya taɓa nawa”.

      “Wancan ma mistake ne, bakuma za’a sake ba, Kinga ga tea kisha sai kisha maganin ki kwanta”.

      Tabbas yanda yake mata magana a nutse ya taimaka ma ƙwaƙwalwarta wajen dawo da ita hayyacinta kan cewar bafa abinda ke mata kai-kawon bane ba. Sannan kuma tunda take da shi bai taɓa aikata mata makamancin hakan ba, lallai ta yarda mistake ɗinne kamar yanda ya faɗa. Hakane, ƙwarai hakanne mistake ne. Zuciyata ta shiga sake tabbatar mata. Sai ta fara sauke numfashi a hankali a hankali jikinta na ƙara samun ƴar nutsuwa. Gadon ta koma ta zauna ta jingina da fuskar gadon bayan taja bargon ta rufa, sai ya koma shima ya zauna a baki-baki da ƴar tazara a tsakaninsu yana sauke ƙaramar ajiyar zuciya ya miƙa mata kofin shayin da har ya ɗan fara hucewa……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣8️⃣

……..Kai ta girgiza masa alamar bazata sha ba. Sai ya ce mata “Please ko kaɗanne! Kinga magani zaki sha”.

     Yanda yay maganar da ɗan dafe kansa shima ya sata amsa dan har yanzu dai tafi buƙatar ya fitan ko zata fi samun daidaito yanda ya kamata. Kwankwaɗar shayin tai kamar ruwa kawai duk da akwai ɗan sauran zafin. Tasha kusan rabi ta miƙa masa kofin, amsa yay baice mata komai ba ganin ta ɗan sha. Ba tsoron magani take ba, dan haka ta amsa tasha shima salin alin, sai kuma ta zame ta kwanta tare da lulluɓe duk jikinta har kanta ta juya masa baya. Idanu kawai ya zubama bargon da take ciki, har yama rasa mizai hasaso game da abinda ya farun yanzu. Rashin makama ya sashi miƙewa da Basket ɗin magungunan, ya ɗan tsaya a kanta yay addu’ar da ake son yima mara lafiya da kuma ta barci ya tofa mata dan yasan idan yace zai tofa mata a hannu ta shafa bazasu wanye lafiya ba. Dan haka yay yanda zata fisheshi sannan ya fice.

      Su Aunty Bilkisu na falon zaune da alama dakon fitowarsa suke, bai zauna ba ya ce, “Tasha maganin ta kwanta nima zanje na kwanta sai da safe”.

     “ALLAH ya tashe mu lafiya”.

Suka faɗa a tare, yana ida ficewa yake amsawa da Amin. Koda ya koma ɗakin nasa ya samu Ahmad na wanka, dan haka ya zauna jiransa sai da ya fito ya shiga ya sake alwala ya fito. Sallar isha’i ya rama da yin shafa’i da wutri yay karatun Alkur’ani kaɗan dan wancan kiɗan na waje damunsa yake yi. Bai dai ce komai ba yay kwanciyarsa bayan sun ɗanyi magana da Ahmad dake tambayarsa yaya jikin Lulun. Ya amsa masa da cewar da sauƙi zazzaɓi ne. Daga haka ɗakin yay shiru, Ahmad na kallo a MBC Action shi ko yay luf tamkar mai barci, sai dai idanunsa biyu abinda Lulun taine ɗazun ke masa kaikawo a rai. Tabbas akwai abinda ya firgitata a dalilin abinda ya faru a tsakaninsu. Yana kuma tunanin kamar hakan ya tuna mata da wani abu ne da ya shuɗe a rayuwarta ko kuma…. Sai kuma ya ɗan furzar da iska kaɗan, hakanne yasa Ahmad jiyowa ya kallesa.

        “Kai wai dama ba barci kake ba?”

     Idanunsa ya ɗan buɗe ya kalla Ahmad ɗin. Shi kuma sai ya saki ƴar dariya da faɗin, “Oh dama likimo kayi, to kodai mun tauyeka ne da rashin baka amaryarka? Ai bata ɓaci ba yanzu ma sai a kawo maka ita nan ko kuma ku tashi ku wuce karma ku mana abin kunya an…..”

    Bumm!! Yaji saukar filo akan bakinsa. Filon Ahmad ya riƙe yana murza bakin, sai kuma ya kalla Smart dake harararsa ya bushe da dariya. “Kufa dama masu shiru-shirun nan wlhy abin tsoro ne wajen ƙulafucin mace. To maida wuƙar yau ne kawai gobe i war haka kuna can manne…..”

     Sake jawo wani filon Smart yay zai jefa masa yay saurin ɗaga hannu sama alamar surrender yana faɗin, “Yi haƙuri nayi shiru Zakin zaki. Haka kawai kamun dogon baki na kasa samun mai aurena nima”.

     Ƙwafa Smart yayi ya ajiye filon, sai kawai yaja bargo ya lulluɓa yana juya masa baya ma. Dariya Ahmad ɗin ya cigaba da yi masa ta shaƙiyancin a kaikaice. Shi dai bai sake kulashi ba dan sosai abinda Lulu tai yanzu yay masa tsaye a rai yaƙi wucewa…..

          *_WASHE GARI_*     

    Washe gari safiyar litinin kusan kowa ya tashi da ƙyar musamman ma ƴammatan nan da sukasha rawa da su Abdull da suma suka cashe kam basu tashi ba sai wajen sha ɗaya da ƙyar. Baƙi fa nata haramar tafiya musamman ma na nesa dangin Abba. Dan haka buɗar kai ma da wuri za’ayi. Alhmdllh amarya Lulu ma ta tashi garas babu zazzaɓin, sai dai damuwar son shan kayayyakinta da ke ƙara tsikararta. Tare suka kwana da su Amrah a ɗakin aunty Amarya. Koda aka kammala haɗa break fast Asma’u ce takai musu. Yanda ta gaishe da Lulu cike da girmamawa da kiranta aunty yay matuƙar mata tasiri a zuciya, sai taji ƙaunar Asma’un ya shigeta, gata ƙyaƙyƙyawa, kamanninta kuma sosai a bayyane suke da Smart. Tun jiya sun jone da su Afrah dan zasu iya zama sa’anni, sai dai Asma’u ta fisu nutsuwa a bayyane, su kuma sun fita wayewa. Dan haka ta basu hannu suka gaisa kowanne nama ɗan uwansa murmushi, a take kuma hira ta ɓalle a tsakaninsu sai Lulu ta zama ƴar kallo. Asma’u na tare da su har sai da Amal tazo tai kiranta sannan tai musu sallama da cewar zata dawo idan tayi sallar walha.

     “Wannan kuma ina kuka samota?”

Cewar Lulu bayan fitar Asma’u. Kai tsaye Amrah ta bata amsa da “Aunty Lu ƙanwar Uncle Smart ce fa, tace mana itace auta a ɗakinsu. ALLAH yarinyar tana da daɗin zama bakiga yanda suka dinga karramamu jiya ba, mutanen gidan nan nada kirki”.

         Shiru kawai Lulu tai tana kallon Amrah ɗin har na wasu sakkani, sai kuma ta ɗauke idanun nata sakamakon kiran wayar Afrah da akayi. Mommy ce, tana ɗagawa tace a Bama Lulu. Amsa tai cike da ɗokin jin Mommy, ta gaisheta da faɗin, “Good morning Mommy”.

     Daga can Mommy ta amsa mata da kulawa da kuma tambayarta yanda suka kwana a baƙon guri da bin ba’asin babu dai wata matsala ko?. Samun kanta tai da amsawa Mommy ɗin da “Eh babu wata damuwa Mommy.”

        “To Alhmdllh haka akeso. Sai ku zama cikin shiri gasu Auntynku nan tahowa buɗar kai, zasu kuma maidaki gidanki In sha ALLAH”.

    Duk da bawani ta damu da zuwa can ɗin ba ko ɗaukar hakan da muhimmanci ta amsawa da Mommy ɗin da to. Da ga haka ta miƙawa su Amrah wayar ta ƙarasa shirinta dan tayi wanka harma ta saka kaya…..

      Ƙarfe kusan sha biyu dangin Lulu suka iso gidan su Smart da shatara ta arziƙi na kayan gara dana rabo. Acewarsu waɗan nan iya na nan gidan su Smart ɗin ne nashi kayan garar ankai can gidansu. Koda Abba da aka kira yazo kai tsaye yace musu baza’a amsa ba kayan sunyi yawa. Haƙuri su Aunty Saliha sukaita bashi amma fir yaƙi, ya daice an amshi kayan rabo suyi kamar yanda al’ada ta tanadar amma kayan abinci kam a’a sunyi yawa. Wanda aka kaima Smart ɗin sun wadatar. Dole aka haƙura da sauke kayan daga motar da aka ciko da su sai iya na rabon kawai. Duk abinda ake Lulu taji, hakan kuma ya matuƙar bata mamaki, sai dai batace komai ba. Anyi rabo na bajinta daya tsayama su Umma arai, dan a kaf aurarrakin ƴaƴansu maza ko rabin hakan ba’ayi ba, hatta ƙannen Smart da ke ɗakunansu har ƴaƴan Aunty Amarya sai da aka basu abu, daga haka akai ɗan abinda al’ada ta tanadar ciki harda kai Lulu gaban surukinta Abba da tsirarun ƴan uwansa datai ƙyau cikin lass pitch color da yay matuƙar mata ƙyau skert da riga da mayafinsa, ga kayan sarƙa ta ɗora sai ɗaukar ido take duk da kwalliyar kaɗan ta yarda su Amrah sukai mata. Fuskarta a lulluɓe take, ta gaishesu kamar yanda aunty Saliha ta sanar mata tayi tunkan su fito daga ɗakin aunty Amarya. Abba yay mata tarba irin ta uba da ƴa, ya saka mata albarka sosai da yimata nasiha tare da addu’a, hakama ƴan uwansa. Daga nan ɗakin Ammah aka kaita. Itama dai kamar Abban ne, ta mata nasiha da sanya albarka a wannan aure tare da fatan alkairi. Hakama ƴan uwanta. Sai ɗakin Umma da taso yin abin kunya sai da ƴarta ta kwaɓeta, a hakan ma dai sama-sama tace ALLAH ya sanya alkairi. Hakan bai damu su Aunty Naja’atu ba, dan sun fahimci Umma sai a hankali, mace ce da bata iya ɓoye hassadarta. Sai wajen Mama. Ita dai ta matuƙar dannewa dan ƴaƴanta ita na ƙoƙarin ƙwaɓarta idan sukaga zatayi wata ƙwaɓar, ta tarbesu da yima amarya nasiha a taƙaice itama tai addu’a kuma. Sun koma ɗakin aunty Amarya itama tai fatan alƙawari sosai da addu’a. Sannan aka sake maidata ɗakin Ammah, da ga canne aka ƙarasa abinda ya rage na yima juna godiya da fatan alkairi sannan suka ɗauki Mawaddat domin maidata can gidan da zasu zauna. Baƙi na nan kuma suka ƙarasa shirinsu na tafiya dan jiya duk an kaisu sunga gidan amarya bisa tsarin Abba dan yau kar ta zama sun takura musu.

       Sun iso gidan amarya lafiya, Lulu ta buɗe idanu da ƙyau tana kallon ko’ina tunda dai daga ita sai ƴan uwanta. Komai batace ba akan gidan da tsarinsa, ita babbar damuwarta a yanzu kawai ta samu kayan shaye-shayen ta ne, dan shine ya haifar mata da zama shiru-shiru da rashin ƙarfin jiki. Sarai aunty Saliha ta fahimci damuwarta, sai kuma yanzu ta sake gane hikimar Uncle Yousuf da duk ya tsara hanyar toshe mata inda zata iya samun komai da zata sha, dan a dalilin hakan gashi nan sun samu tayi laushin da kowa ke iya controlling ɗinta batare da an samu ko ƙaramar matsala ba. Suna shiga takai kwance a falo ta dunƙule jikinta waje guda ta rufe idanu. Suko suka shiga ɗan gyara abinda zasu gyara su Amrah nata santin yanda gidan ya tsaru duk da bai kasance katafare ba. Sai da suka daidaita komai yanda ya kamata, Aunty Naja’atu ta sakata yin sabon wanka wajen ƙarfe shida na yamma, kafin ta fito sauran mutanen dake gidan duk suka wuce, aka bar su Aunty Saliha kawai sai su Amrah dake ta ƙara goge inda aka ɓata da sassaka turaren wuta. Tsaye sukayi a kanta ta shirya cikin wasu ubansun yadi mai taushi da ɗaukar ido, sai yi take kamar zatayi kuka amma suna lallashinta dan sun fahimci matsalarta, sai dai kowa da yanda ya fahimta ɗin kasancewar aunty Naja’atu bata san Lulu na shaye-shaye ba, dan duk da tamafi samun damar yi idan taje wajensu a Abuja amma iya takunta yasa basu taɓa gane komai ba da ga ita har Uncle Khamil. Sai da suka tabbatar komai ya dai-daita a yanda suke buƙata sannan suka zare jikinsu suka fito a ɗakin, ita dai tana kwance a tunaninta zasuje falo ne, koda taji gidan yayi tsitt barcin dake rinjayar idanunta yasa bata kawo komai a ranta ba ta cigaba da saƙa ta yanda zata samu abinda take muradi……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣9️⃣

……Smart zaune gaban su Abba da Ammah suna masa nasiha. Yayi matuƙar ƙyau cikin yadi mai taushi grey color, ga ƙamshi mai daɗi da saka nutsuwa yana yi. Nasiha mai ratsa jiki Ammah da Abba sukai masa sannan suka rufe da addu’oin samun zaman lafiya da nasarar rayuwa. Tare da tuna masa muhimmancin cigaba da tsayawa akan gaskiya da addu’a da ibada. Kar yaga ya koma bayan idanunsu ya aro halin da basu sanshi da shi ba. Ya ji tsoron ALLAH ya riƙe matarsa da zuciya ɗaya bisa koyarwar MANZON ALLAH (S.A.W) karya barta tai kuka akan abinda yanada ikon share mata hawaye. Abba ya miƙa masa wata leda mai ɗauke da magungunan musulunci yana faɗin, “Ga wannan ɗazun naje na amso maka shi, dan yawan ciwon kan nan naka yana damuna. Ka kula dan ALLAH dayin yanda duk suka rubuta a kuma cigaba da addu’a dan itace gaba da komai muma muna muku ALLAH ya kawo iyaka”.

      Ya amsa da Amin tare da masu godiya zuciyarsa a raunane. Ashe haka akeji idan za’a bar gida. Ashe ba mata ne kawai ke shiga cikin yanayin damuwa ba yayinda za’a kaisu gidan aure. Ji yake kamar ya saki kuka kawai ya huta. Amma dai ya daure ya cije da ƙyar yay musu sallama ya fita inda Ahmad ke jiransa. Sai da ya koma cikin gidan yay sallama da su Umma da dama abinda take jira kenan, cikin dabara tai masa hoto batare daya sani ba, dama sanda aka kawo Lulu haka tayi. Koda ya fito inda Ahmad yake sai da suka tsaya akai sallar magrib a masallacin anguwar sannan suka wuce. Basu ƙarasa sharaɗa ba sai da Ahmad ya tsaya yay saye-saye irin na rakkiyar ango, shi dai Smart baice komai ba, hakan yasa Ahmad komawa tsokanarsa wai kodai a samo masa mayafi ya lulluɓa kamar yanda amare keyi idan za’a kaisu. Dan ya lura shima ɗin fa kukan kawai ya rage yayi. Kunnen Ahmad ya kama ya murɗa da faɗin, “Kai wai bazaka daina sa ido ba ko”.

       Hannun Ahmad ya buge masa. “Mugu ciremin kunne zakai dan kai ka samu ka tsallake.” murmushi kawai Smart yay baice komai ba. Koda suka iso sai da ya fita ya buɗe gate ɗin sannan Ahmad ya shiga, shi kuma ya rufe sannan ya samesa dai-dai yana fiddo ledojin sayayyar da yayi. “Mawashi ya kamata fa gidan nan a nema maigadi gaskiya”.

     Cikin taɓe baki da ƴar harara Smart ya ce, “Yayi me idan an nemosa?”.

      “A’a gadi mana, kana ganin ya dace ace kaine zaka dinga buɗe gate da rufewa idan kun shigo ko Madam ɗin. Sannan shi amfanin mutum a gida ko tafiya kukayi baku da ɗar akan barin gidan babu kowa.”

   Duk da ya gamsu da maganarsa ta ƙarshe sai cewa yay “Kai share wannan batun muje kazo kayi ka wuce dare nayi”.

            “A’a nazo dai nayi na wuce na baka fili kawai zakace malam. Kai jama’a wai kowa da yayi aure sai idonsa ya buɗe, bara dai nazo nai mai yiwuwa, in sha ALLAHU nima bazan ƙetare shekarar nan ba”.

       “Da yafi maka”.

   Cewar Smart yana murmushi. Daga haka suka ƙarasa cikin gidan. Wani irin ƙamshi mai ratsa zuciya ne ya tarbesu, falo kam ya tsaru iyakar tsaruwa dan Uncle Yousuf da gaske ya zuba dukiya a gidan nan ƴar gaske. Zaune Ahmad ya kai, shima Smart sai ya zauna ɗin yana furzar da iska. Ko yaya zata kaya musu a wannan gida cikin wannan rikitaccen aure mai cike da cakwakiya da ƙalubale oho. Yau dai ga shi da ga shi sai Lulu ƙamshi ƴar balaja’un ogar nan tasa da bata raina abin masifa matsayin ma’aurata. Shi yasan akwai babbar ƙura, idan yace ƙura yana nufin ƙura irinta turniƙewar yaƙi da ko tafin hanunka ganinsa bazai yiwu maka ba…”

      “Oh oh tunanin mi kuma ka tafi?”. Ahmad ya katsesa. Iska ya ɗan furzar da sakin ajiyar zuciya. Ahmad yay dariyar shaƙiyanci yana miƙewa. “Ƙalau kake kuwa?” cewar Smart da ke kallonsa. Ahmad ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Kafin kowa sanin ƙalau nake tunda gashi na rakoka wajen amaryarka. Ni kaga nayi nan asha angwanci lafiya kar dai a karya gado da safe a kiramu neman kafinta”.

     “ALLAH ya shiryeka mara mutunci”. Cewar Smart yana miƙewa shima. Yanzun ma shi ya buɗe masa gate ɗin yana faman jera masa godiya. Dan Ahmad yayi matuƙar ƙoƙari a bikin nan. Ko shine angon sai haka. Sai da ya rufe ko’ina sannan ya sauke ajiyar zuciya da bin ƙofofin ɗakin uku da kallo. Duk da biyu a cikin corridor suke ƙaramin ɗakinne a ware shi kaɗai ɗan nesa da su ma. Zuciyarsa tafi kaisa a corridor ɗin dan haka ya nufi can kai tsaye, tafiya yake tamkar wanda ke jin kasala ko gandar takun nasa, hakan yay matuƙar jagorantar steps ɗin nasa wajen kasancewa a tsare, hannunsa ya kai saman handle ɗin ƙofar, sai ya samu kansa da ambaton sunan ALLAH kafin ya murɗa ya shiga da sallama can ƙasan maƙoshi. Hasken ɗakin ya bashi damar hangota naɗe a tsakkiyar gadon, ya ɗan zuba mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙarasa cikin ɗakin da shima keta tashi ƙamshi, yana da ga tsayen ya kira sunanta a hankali, idanun ta buɗe da ƙyar dan bata da nauyin barci, ko abu tasha ta kwanta da wuya kaga barcinta yay nauyin da za’ai abu a kusa da ita bata farka ba. Maidasu tai ta rufe tana wani ɓata rai. Duk da yanda tai ɗin sai bai damu ba ya kai zaune a bakin gadon sai dai nesa da ita kaɗan, koba komai yau ai ita baƙuwarsa ce, ada bai kulata ba ma balle yanzun. Hannunsa ya kai saman goshinta, da zafi sosai alamar zazzaɓi yau ma.

      “Yau ma zazzaɓin ne?”.

   Kamar bazata kulashi ba sai kuma ta ɗaga masa kai kawai. Iska ya ɗan furzar a hankali. Sai kuma ya ce, “Tashi to kici wani abu sai kisha magani”.

      Kalamar magani da ya ambata yasa kanta kawo wuta, cikin gamsuwa da dabarar data zo mata ta tashi zaune da ƙyar tana ƙara cin serious, sai da ta zauna sosai bayanta jingine da gadon sannan ta ɗan kallesa ta kauda idonta, ganin hankalinsa nakan wayarsa yasa taji ƴar nutsuwa dan bata ƙaunar kallo. Cikin ƙara dai-daita plan ɗinta murya a karye ta ce, “Nifa paracitemol bayamin maganin zazzaɓi”.

       Ɗan ɗagowa yay ya kalleta, sai kuma ya sake maida idon nasa kan wayar yana faɗin, “Sai wanne?”. Handbag ɗinta da ke bedside drawer ta ɗauka ta zaro wata takarda a bayan zip ɗin ta miƙa masa. “Wannan shi nake sha in dai ina irin wannan zazzaɓin, in ba haka ba bana warkewa da wuri”. Harga ALLAH bai kawo komai a ransa ba tunda shi ba likita bane, dan haka ya amsa takardar, ganin rubutun Doctor ya sashi sake yarda. Sai kuma ya ɗan kalli agogo, takwas da kusan rabi dare baiyi ba. Idanunsa ya maida kanta, ta janye nata da ke kallonsa a sace cike da basarwa. “Ya kamata kici wani abu to kafin na dawo ko?”. A ɗan yatsine ta ce, “Karka damu har ka dawo.”

        “Okay”.

   Ya amsa mata yana miƙewa. Wani irin daɗine ya ratsa Lulu kamar ta fasa ihu dan farin ciki. Wai yayama akai wannan dabarar baizo mata ba tuni take a wannan bala’in. Zamewa tai ta kwanta tana murmushin da kakan daɗe baka gani ba akan fuskarta dan sai ta gadama take yi.

        Napep ya samu ta kaisa har ƙofar pharmacy ɗin data kwatanta masa ana iya samun maganin, koda ya basu takardar yaron saida ya kallesa, amma sai baice komai ba ya dai wuce wajen ɗakko masa maganin. Koda ya dawo da maganin ya faɗa masa kuɗin ya cire daga aljihu ya bashi. Napep ya sake samu ta maidashi gida. Yanzu kam sai da ya rufe ko’ina da ɗaukar abubuwan da Ahmad ya siya musu sannan ya nufi ɗakin. Inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ta koma ta kwanta. Duk da taji sallamarsa bata motsa ba har sai da ya kai hannu ya yaye bargon data rufa har kanta. Jikinta har tsuma yake lokacin da ya fiddo maganin da ga leda mai tambarin pharmacy ɗin, amma sai tai ƙoƙarin kannewa.

       “Yanzu mi zaki ci?”.

    Ya faɗa yana ɗagowa ya kalleta. “Ni bana jin yunwa, naci abu tare da Mamy”. Ta bashi amsa idonta akan ledar nan dai. Bai san wa take cema Mamy ɗin ba, sai dai yanda tai maganar cikin serious ya sashi gamsuwa, sai kawai ya cire maganin biyu ya miƙa mata tare da goran ruwa. Bata musa ba ta amsa tasha. Sannu ya sake mata da tattare sauran maganin ya ajiye a bedside drawer da ruwan. Zamewa tai ta sake kwanciya da faɗin, “Sai da safe”.

      Murmushi ya ɗan saki ƙasa-ƙasa. Dan ya fahimci korarsa akeyi. Baice mata komai ba ya tattare sauran ledojin ya fice yana rage mata hasken ɗakin. Ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi, sai kuma ta miƙe zumbur da raka bayansa da harara ta dannama ƙofar key sannan ta dawo. Cikin rawar jiki ta fisgi ledar nan ta zazzage kusan ƙwayoyin maganin biyar a tafin hanunta ta afa a baki batare da ruwa ba. Sai da ta haɗiye sannan ta ɗauka ruwan ta kora kaɗan. Wani irin farin ciki take ji na samun kayan nan cikin sauƙi, sai kawai ta faɗa saman gadon cike da jishaɗi tai juyi ta sake juyawa……..✍️

       _(ALLAH ka rabamu da mummunar ƙaddara. Wlhy irin masu ɗabi’ar nan tausayi suke ban. Dan rayuwar kawai suke batare da sun san ina ta dosa ba, idan sukai nisa sai an dage kafin su bari, ku ga dai, kwana biyu batasha ba amma ta koma kamar mara lafiya. Iyaye dan ALLAH mu ƙara dagewa wa ƴaƴanmu, mu bar aibata ƴaƴan wasu idan muka gamsu a irin wannan halin. ALLAH ka shiryar damu😭🙏)._

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣0️⃣

……..Koda Smart ya kai kayan nan kitchen ya adana wanda zai iya lalacewa a fridge sai ya nufi ɗayan ɗakin kasancewar duk yasan sirrikansu, hasalima key ɗin ɗakin na hannunsa dan a rufe yake tun da aka gama shirya masa kaya aunty Saliha ta damƙa masa ko ƴan ganin gidan amarya babu wanda ya leƙa cikinsa. Shima nan ɗin kayane lafiyayyu aka shirya, dan shine ma matsayin master bedroom. Ɗakin yayi ƙyau sosai, komai ya zauna a inda ya dace. Duk da gajiyar da yake ji bai kwanta ba sai ya zare rigarsa da ga shi sai dogon wandon da singlet ya nufi bathroom. Bai jima ba ya fito da alamar alwala yayi, lafiyayyen carpet ɗin gaban gadon ɗakin ya hau dan yin salla. Sallar isha’i yay da shafa’i da wutri. Bayan ya idar yay zaman yin addu’a mai tsayi kafin ya miƙe. Har ya zauna a bakin gadon sai kuma ya miƙe, zuciyarsa ke ayyana masa ya kamata ya binciketa ko tayi sallar isha’i, ya kuma duba ko zazzaɓin ya sauka. Sai dai me, yana taɓa ƙofar ya jita a kulle. Shiru yay yana kallon hannunsa da ke saman handle ɗin, sai kuma ya ɗage kafaɗunsa alamar ko oho ya juya ɗakin da ya fito yay kwanciyarsa dan barci yake ji matuƙa. Dan shi a tunaninsa ko Lulun tayi hakanne dan kar ya nema wani abu a gareta…..

       _WASHE GARI_ koda ya tashi sallar asuba sai da ya ƙwanƙwasa mata ƙofa, ganin zai makara saboda ya tashi shima a ƙurarren lokaci ya sashi ƙyaleta ya wuce. Ana idar da sallar ya dawo gidan, ɗakin nata dai ya sake nufa ya ƙara knocking. Lulu da ke kwance a ƙasa ta buɗe idanunta da sukai matuƙar nauyi da ƙyar ta iya miƙewa cikin takaicin damunta da ake tun ɗazun ta nufi ƙofar ta buɗe, dan ta manta ma a ina take, dai da ta ɗan jingina da ƙofar na wani ƴan sakanni sannan ta murɗa key ɗin ta buɗe kaɗan. Da farko bai niyyar shigowa ba, dan haka yace da ita, “Kin tashi kinyi salla ne?”.

          “Zanyi”.

      Ta amsa masa cikin yanayin muryar maye da tura ƙofar zata rufe dan abun bai gama sakinta ba. Da sauri ya riƙe ƙofar gabansa na faɗuwa, bata da wani isashen ƙarfin dan haka ya samu nasarar shigowa. Yanda ya kafeta da idanunsa da suka kaɗa sukai ja a ƙanƙanin lokaci ya sata zabga masa harara itama da nata dake a juye ta bar masa wajen cikin ɗan tangaɗi na rashin ƙarfi ta je ta faɗa saman gadon a rufda ciki gashinta dake a hargitse ya lulluɓe fuskar tata gaba ɗaya. (Ina ta samu abinda tasha?) Zuciyar sa keta kaikawo wajen son hasasowa amma iya hasashen ya auna a ɗan tsukun lokacin baro gidansu zuwa nan hakan bamai yiwuwa bane, sai dai idan dama tana tare da abunta. Inda take ya ƙarasa ya ɗauki handbag ɗin ta gaba ɗayanta ya zazzage a saman gadon. Babu komai a ciki daya danganci ƙwaya, jakkar ya ajiye cikin furzar da iska sai idanunsa suka sauka kan ledar maganin jiya daya sayo mata, jawo ledar yay ya fiddo maganin, an ƙara ɗiba kusan shida a ciki, ya tsirama maganin ido kallon da yaron pharmacy ɗin ya dinga masa lokacin da ya bashi takardar na dawo masa a rai da zuciya. Tabbas wannan maganin tasha. Kallonsa ya maida gareta ya zuba mata idanu kawai maƙogwaronsa na kai kawo a cikin wuyarsa da ɗan sauri-sauri. Da ga ƙarshe ma sai ya tashi ya fice da ga ɗakin kawai…..

     ____________________★

           Cikin ɓacin rai yake dubansa ganin yanda yake neman haukata kansa. Gaba ɗaya kwanakin nan baida wani aiki sai shaye-shaye tunda ya baro Kano. Ƴar ƙaramar robar giya da ke a hannunsa ya fisge cikin masifa. “Wai mi kake son maida kanka ne kai kuwa MM? Akan mace! Ka zauna ka susuta rayuwarka. Tunda ka dawo da ga kano an kasa gane kanka, ka bar zuwa aiki ka barma fita a gidan nan gaba ɗaya sai shaye-shaye, kana ganin hakan da kake shine zai baka damar samunta? Yarinya sai kace wata autar mata ko hurul-ayni Mtsowww!!!”.

        Murmushin takaici MM Atik ya saki sai kuma ga hawaye sharrrr. Ya miƙa hannu zai amshi ƴar robar giyarsa da abokin nasa ya karɓe amma sai ya hanashi. Lips ɗin sa ya ciza da ƙarfi da faɗin, “Bazaka gane ba Asim, duk yanda zan faɗa maka bazaka gane ba. Aure fa sukai mata, aure da wani bani ba. Idan ban mallaketa ba zan iya rasa raina, ina matuƙar sonta da buƙatarta Asim, wlhy da gaske nake ina sonta da gaba ɗaya zuciyata..”

        “A haba gyara dai zancenka my man, kana dai sha’awarta. Kai har kasan wata soyayya ne. Ni yanzu Indai dan batun yarinyar nan ne ka nutsu dan ALLAH ka dawo hayyacinka. Ba igiyar aure ba ko ɗaurin kabari sukai mata namaka alƙawarin sai ta dawo taka…”

   Wani irin zuba masa ido MM Atik yayi, sai kuma yay murmushi da lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci guda, “Asim karka yaudari kanka nima ka yaudarani. Kasan minene aure a ƙasar hausa kuwa?….”

       “Mtsoww kafin wannan zamanin yake wani abu a ƙasar hausar, amma a yanzu bana jin wasu matan na tuna matsayin auren, dan ajiyesa suke su shigo barikin ko ƴammatan basu kaisu iskanci ba. Balle ma ita munada hanyoyi kala-kala na kamata a tafin hannunmu. Ko an faɗa maka wani son auren take, to nayi bincike mai zurfi na gane komai har ma yanda aka ƙulla auran. Kai dai kawai ka dawo a hayyacinka kasha labari”. Ya ƙare maganar yana tattare sauran kwalaben giya da su cigarette da shisha da MM Atik ɗin ya baza, sannan ya zo ya kamashi ya kai toilet yasa a ƙarƙashin shower ya sakar masa ruwa. “Malam yi wanka ka cire wannan dattin sai warin hayaƙi kakeyi”. Daga haka ya fice ya barsa.

         _____________★

     Da mamaki Ammah ke kallon Umma da ke faman murmushi riƙe da basket irin na saƙar kaba ɗin nan mai ƙyau shaƙe da kulolin kayan abinci wai karin kumallo ta shirya za’a kai gidan Smart. Umma data fahimci Ammah zata iya bata matsalafa sai ta sake faɗaɗa fara’arta da katse mata tunani da faɗin, “To kodai banyi dai-dai bane Hafsatu? Dama dai ganin haka akeyi a gidan washe garin da yaro ya tare da matarsa shiyyasa, kuma kinga dai ai ba’a barki da haɗa  abinci ba duk gamu cike da gida ko, sai dai kuma naga kamar hakan bai miki ba”.

      Murmushi Ammah tayi da ɗan girgiza kanta. Cikin nutsuwar nan tata ta ce, “Ko ɗaya ba haka bane Umman Nasiba, naga kawai an sakaki aiki ne tunda safen nan….”

    Caraf Umma ta amshe da faɗin, “Yo minene ALLAH na tuba. Ai an riga an zama ɗaya. Hydar a gidan nan kuma ai ya cancanci fiye da haka. Shi kaɗaine yaron da bai gajiyawa wajen binka har cikin ɗaki ya gaisheka kullum kuma cikin girmamawa da mutuntawa. Bari kiga Huwaila ta miƙa musu tunda tace zata gane gidan lokaci na ƙara ja”.

          Murmushin ƙarfin hali kawai Ammah ta saki da faɗin, “To ALLAH ya saka da alkairi”.

    Umma ta amsa da “Amin”. tana ficewa

       “Anya wannan al’amarin Hafsatu ba akwai wata a ƙasa ba. Matar da tunda aka fara bikin nan ta kasa ɓoye hassadarta ce zata girka abinci akaima Babangida kuma a barta?”. Addah Rukayya ce mai maganar cikin jimantawa. Kafin Ammah tace wani abu Gwaggo Sa’adah ta fito a ɗaki ita da Addah Suwaiba. Har rige-rigen faɗin, “Wannan yaudara ce akwai wata a ƙasa” suke su biyun. Adda Suwaiba ta cigaba da faɗin, “Babu ma wani batun ai mata kawaici magana ta gaskiya fa, kawai a dakatar da su ba ga Hawwah can na musu girkin ba shi kuma ai yaya da shi?. Matar da bata taɓa ƙaunarki ba tun da jajayen sawu sai yanzu ne zata ƙaunaceki Hafsatu, ai daga ji ma kasan akwai ƙulunboton data shiryama abincin. Ita idan yaran nata sunyi auren barinku take ku girka abinci ku aika musu ko sai ke, naga Yalwati ma ta aurar da yara maza har uku a gidan nan ai batai mata hakan ba dan tasan bama yarda zatai ba sai ke sarkin kawaici”.

         “Addah ni a ganina ku barta, idan ma wani sharrin take nufi ai ALLAH bazai bata nasara ba. Ballema ni sai nakega kawai dai tayi hakane saboda tujarar da malam yay mata jiya da dare”.

     Gwaggo Sa’adah ta ce, “Humm Addah kenan. Yau ya fara mata tujara ne da har hakan zai sakata saduda. ALLAH ki yarda ke dai akwai wani abu a ƙasan kawai. Bakuma zamu gane hakan ba sai anje ankai musu abincin sun cutu mudawo muna dana sani”.

        Duk da zuciyar Ammah ta sake raunana sai bata iya sake cewa komai ba, sai ƴan uwan natane ke cigaba da tattaunawa dan na cikin ɗaki ma duk sun fito. Gwaggo Sa’adah ce ta nufi kitchen inda Hawwah ke girka karin kumalon da za’a kai gidan Smart. Cikin sa’a ta iske ta kammala tana kan zubawa ne. “Yauwa kin haɗa ne Hauwa’u?”.       “Eh Gwaggo” cewar Hawwah. Gwaggo Sa’adah ta ce, “Yauwa to sannu, bara na turo su Asma’un suyi su tafi rana nayi”. Da ga haka ta juya ta koma. Ƙwafa Umma dake leƙarsu ta window tayi, jitake kamar ta fito ta shaƙe wuyar Gwaggo Sa’adah. Oho dai tata ƴar aiken ai harta wuce. Kafin kuma su isa ta tabbatar Hydar da matarsa sunci nata abincin. Tai wata ƴar dariyar gatsa-tsa tana barin window ɗin har ɗiyarta Ismaha na kallonta. Amma sai ta basar dan tasan wacece Ismaha da ɗan banzan jan wa’azin tsiya………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣1️⃣

……..Ƙarfe kusan tara Lulu ta tashi da ƙyar a dalilin kaɗawar alerm ɗin ƙaramin agogon da ke a side drawer ɗinta da ya gallabeta tun takwas. Amma nauyin da jikinta yay mata yasata kasa kasheshi ko ta tashi har zuwa yanzu da ya sake buga taran. Ƙaramin tsaki taja da ɗan kai hannu tana lalube, sai dai sam babu ma alamarsa kusa da itan. Tamkar wadda aka ƙwalama kira sai kuma ta miƙe zumbur, yau fa ya kamata ta shigar da case ɗin mijin matar can court, dama tai alƙawarin sai ya kwana bakwai a police station su Shu’aibu sunci mata ubansa gwargwadon iko sannan, yau kuma kwana bakwan cif. Wayoyinta ta shiga nema, sai kuma ta tuna sunafa hannun Uncle You nan kuma gidan da aka kawota jiya ne. Ƙaramin tsoki taja da dafe kanta da yay mata matuƙar nauyi, dole ta sakko a gadon cikin ɗan tangaɗi kaɗan sai dai bana mayen bane na nauyin jikine dan abinda tasha ɗin sun saketa sai abinda ba’a rasa ba. Bayi ta shiga ta tsaya ƙarƙashin shower batare data cire komai ba daga jikinta ruwa ya fara sauka mata a haka. Ajiyar zuciya ta dinga saki a jajjere, sai da ruwan yay mata sharkaf ta gamsu ta ƙara komawa garau da take buƙata sannan ta fara zame kayan jikin nata ta fara wanka. Tana kammalawa ta jefa kayan a injin wanki dan komai na ƴar gata an ajiye mata shi, sai da ta gamsu sun wankun sannan ta ciresu ta maida indai zai busar. Sai ga kaya ras ta fitar sannan ta fito. Tana buƙatar waya domin kiran Zainab sakatariyarta da kuma su Shu’aibu ɗan sanda, dan haka ta fito da ga bedroom ɗin nata daga ita sai rigar wanka da towel ɗin data naɗe gashinta da take son ruwan data jiƙashi da shi ya naɗe. Sautin muryarsa yana raira karatun Alkur’ani cikin suratul An’aam daya karaɗe corridor ɗin ya sata gane yana a ɗakin dake kusa da wanda take. Sai da ta sake gyara yanayinta dan karma ya kawo mata wani raini sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga kanta tsaye ba batun neman izini, sallama ma sai da ta gama shiga tayita ciki-ciki. Ƙamshin shower gal dana haɗin turarrukan wankan da masu gyara mata jiki suka shirya mata na musamman ne ya fargar da shi shigowar ta, dan cikin abinda baifi sakans ba ɗakin ya gauraye da masifaffen ƙamshinta. Kasancewar yazo inda ya kamata ya tsaya ya sashi rufe Alkur’ani ya ɗago ya kalleta. Kanta ta ɗauke daga kallon da take masa, shima sai ya janye nasa idanun yana ajiye Alkur’anin. Cikin izzar nan tata da gadara ta ce, “Ɗan bani aron phone ɗinka na kira Uncle You ya bada nawa a kawo min”.

       “Kinyi salla?”.

    Ya faɗa maimakon amsa mata abinda tazo nema. A yamutse tana balla masa harara ta ce, “Ina ruwanka. Ka bani aron waya idan zaka bani”.

      “Idan kina buƙatar waya kije kiyi salla. Shin ke bakiji kunya ba a wannan shekarun naki ace sai an tuna miki abinda zai kusantaki da UBANGIJINKI, banbanci kafiri da musulmi shine sallah, duk wanda yabar salla baida maraba da kafiri, sannan duk wanda yabar salla zai iya aikata kowanne irin mummunan aiki, salla itace abinda za’a fara bincika mana a cikin ayyukanmu ranar sakamako, yin salla akan lokaci na ma masifu katanga da samunmu. Salla na ƙaramana kwarjini a idon al’umma da cikar kamala. Taya mai barinta zai samu waɗan can tagomashin dana lissafa wanda kaɗanne da ga cikin nasarorin da mai salla ke samu. Yinta zai baki damar yima mahaifiyarki addu’a da nemar mata rahamar UBANGIJI, sai ruhinta ya kasance cikin sallama tai alfahari da haihuwarki da jin bata bar bayan a banza ba. Mawaddat babu ruwan mutuwa da yanzu kika fara rayuwa, tana ɗaukar ɗan cikin ciki ma tabar uwa, alokacin da kike jin ke kin fara rayuwa wani ma a ranar aka samar da cikinsa. Ki dawo cikin hankalinki ki koyi darasi a duniya ba sai duniya ta shirya koya miki ba. Dan ita ɗayan biyu ce. Ko ka koya a yayin da take koyar da waninka, kota koyar da kai a lokacin da guri ya ƙure maka. Zaɓi ya rage naki”.

     Da ga haka ya tura mata wayar ya miƙe yay wucewarsa toilet. Harara kawai ta bisa da shi ƙasa-ƙasa. Dan gaba ɗaya jitai kamar an danne mata baki a sanda yake maganar. Bakin ta taɓe da matsawa ta ɗauka wayar tasa ta fice abinta. Sai dai tana komawa ɗakin nata ta zauna a bakin gado da nufin kiran Uncle Yousuf hakan ya gagara. Maganganunsa ne suka shiga dawo mata, musamman akan yima mahaifiyarta addu’a kuma zatai farin ciki da ita daya faɗa, samun kanta tai da kiƙewa zumbur ta nufi toilet, babu jimawa sai gata ta fito da alamar alwalar tayi. Wardrobe ta buɗe ta ciro abaya ta saka tare da naɗa gyalenta a kanta ta kabbara sallar.. dai dai nan ya shigo ɗakin shima, dan haka kawai zuciyarsa ta kasa nutsuwa harya fara cire kaya zai yi wanka ya fasa ya biyota dan yaga zatayi sallar. Karo na farko zuciyarsa ta tsarga ganin yanda take salla babu wani bin ƙa’idojinta yanda ya kamata. (Tofa wata sabuwa) ya ayyana a zuciyarsa da ɗunbin takaici. Ashe dole abubuwa suke rikicema yarinyar nan dan babu nutsuwa ko nagarta a cikin al’amarin ibadarta. Tabbas rashin tsaida ibada tamkar wani dafin allura ce a jikin ɗan adam mai karya masa garkuwar nagarta da ɗaurasa akan laifuka. Ashe al’amarin nata ya gawurta da yawa har haka. Zafin rai da takaicin iyayenta ya sake mamaye masa zuciya, domin fa in har ɓera da sata to a bincika itama daddawa nada wari. Shin mi mahaifinta da matar babanta dama Uncle Yousuf keyi haka har balagaggiyar yarinya mai shekaru da yake da tabbacin sun haura ashiri amma bata iya salla ba? Amma a ilimin boko da anyi magana zata iya bugar ƙirji ta kira kanta mai ilimi. Oh ALLAH a wane irin zamani muka tsinta kammu da tarbiyya ke neman kufcewa iyaye saboda soyayyar ƴaƴansu?. Wannan al’amari ya tayar masa da hankali matuƙa, ya tuna lokacin suna yara, idan lokacin salla yay sukaƙi barin wasa suje suyi sai dai kaji saukar tazbahar Ammah a jikinka kawai. Idan ko bakayi ba ranar ko kulaka batayi sai tace ita bazatai magana da wanda yafi son shiga wuta ba. Amma yau sai ga shi wadda ke amsa sunan matarsa bata iya salla ba. A hankali ya jingina da ƙofar yana mai harɗe hannayensa a ƙirji da lumshe idanunsa abubuwa masu yawa na masa kaikawo a zuciya, lallai akwai aiki, dan yaƙine babba garesa akan yarinyar nan, shi duk ma sai yaji tausayinta ya ƙara kamashi..

       A ɓangaren Lulu tunda ta idar idanunta ya sauka akan Smart kamar wani mayan ƙarfe. Sai da taji gabanta ya faɗi musamman da abinda ya faru jiya ya shiga dawo mata a rai, amma sai ta basar tama miƙe tana naɗe abin sallar. Sam Smart shi bai san da ta idar ba. Dan idanunsa a lumshe suke ya afka duniyar tunani. Samun kanta tai da tsura masa idanu, yayinda kalaman Nadiya na waccan ranar na dawo mata a zuciya. Kamar wadda aka tsawatarwa sai kuma ta ɗauke idanunta cikin yamutsa fuska tana jan tsaki. Duk da bai san mi take jama tsakin ba saukarsa a tsakkiyar kansa ya sashi ɗagowa cikin nutsuwar nan tasa ya buɗe idanunsa a kanta.

     “Gadin na miye?”.

  Ta faɗa cikin ƙarfin hali dan ba ƙaramin tasiri idanunsa keyi a duk sassan jikinta ba. Maimakon bata amsa ɗauke kansa yay, hakan kuma sai ya tunzura mata zuciya. Ta buɗe baki zata fara masifar tata yay gyaran murya kaɗan, kamar zata share sai kuma dai ta jiyo ta ɗan kallesa cikin harara tana ƙoƙarin warware gashinta. Ido suka haɗa ta mirrorn ta balla masa harara ta ɗauke nata. Shima ɗauke nasan yay ya maida kan gashinta mai tsaho da alamun samun gyara ya sashi yin wani ƙyau na musamman da sheƙi duk da a jiƙe yake a yanzu. Knocking gate da ake da ɗan ƙarfi ya sashi haɗiye maganar da yay yinƙurin yi. Agogon dake a ɗakin ya kalla sai kuma ya buɗe ƙofar ya fita. Ƙaramin tsaki yaja lokacin da ya fito harabar gidan sosai yaji bugun ƙofar babu ƙaƙƙautawa, sai da yasa key ya buɗe sannan ya zare sakatan. Da sauri Huwaila taja baya tana sissine kanta. Sai da ya gama kallonta ita da kwandon hannunta sannan ya matsa mata fuskarsa na ƙara tsukewa, dai-dai nan napep ta tsaya a ƙofar gate ɗin, dakatawa yay da ga yunƙurin rufewar da yake saboda hango Asma’u na fitowa a Napep ɗin. Fuskarta da murmushi ta ƙaraso garesa tana faɗin, “Yaya ina kwana”.

        “Lafiya Lau” ya amsa mata idonsa akan kayan hannunta, itama kallon hannun tayi har sannan fuskarta da murmushi ta ce, “Yaya abincinku n…..” sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda hango Huwaila da tai a ƙofar shiga falon ɗauke da kayan abinci itama, da sauri ta kalli Yayan nata kamar zatai magana dan ita bata san da zuwan Huwaila ba. Ganin yay gaba abinsa ya sata bin bayansa batare data faɗi abinda ke bakin nata ba. Kallon juna sukai ita da Huwaila da ke hararta ta ƙasan ido, Asma’u ta ɗan girgiza kanta cikin basarwa ta ce, “Adda ai ban san nan zakizo ba da mun taho tare”.

       “Zaku shigo ne ko zaku tsaya surutu”. Smart dake kaiwa zaune cikin kujera ya faɗa. Shiga sukai da sauri, kowa ya ajiye kayan hannunsa suka gaishesa. Amsa musu yay da kulawa, sai kuma Asma’u cikin zumuɗi ta ɗora da faɗin, “Yaya ina auntyn?”. Ɗan jimm yay sai kuma ya nuna mata hanyar bedroom ɗin da Lulu ke ciki.

      “Yaya dan ALLAH barci takeyi?”.

Kansa ya sake girgiza mata nan ma. Miƙewa tai, kafin ma yace wani abu harta kusa zuwa ɗakin, ƙoƙarin dakatar da ita yay dan shi dai yasan wacece matar tasa, kuma baya buƙatar ƴan uwansa su fara sanin wacece itan su tun a yanzun, sallamar da Asma’u tai da ɗan knocking ƙofar ya katse masa tunani.

       “Asma’u!”.

   Ya kira sunanta kamar a kasalance, amsawa tai da “Na’am Yaya”. Tana jiyowa………✍️

     (😂Lulu karki bamu kunya dan ALLAH)

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣2️⃣

…….Dai-dai nan Lulu ta buɗe ƙofar ita kuma waya a kunne ta tana magana da Uncle Yousuf cikin shagwaɓa akan a aiko mata da wayoyinta. Miƙewa Smart yay ya nufosu, sai dai yana isowa Lulu da batama lura da shi ba ta riƙo hannun Asma’u suka shige ciki tana mata murmushi. Turus ya ɗan tsaya yana bin ƙofar da kallo, sai ma ya rasa wane irin tunani zai yi. Sai kawai ya ɗan furzar da isa ya nufi ɗakin daya kwana al’amarinta na ƙara ɗaure masa kai, ya fahimci gane ainahin yarinyar nan sai an shirya.

       Huwaila da ke kallon komai ta cika tai fam, dan ita babu abinda zuciyarta ya bata sai wulaƙantata da nuna mata wariya. Wayarta ta ɗauka tai kiran Umma, bugu ɗaya kuwa ta amsa, daga can cike da zumuɗi Umma ta ce, “Ya ya kin ɗebo ko?”. Sosai Huwaila ta tunzura baki gaba, idanunta akan hanyar corridor ɗin nasu kamar zata saki kuka ta ce, “Umma bayan munafukar yarinyar nan itama tazo, gashi can ya jata sun shige ɗaki wajen matar tasa sun barni ni kaɗai a falo, dama tunda ya buɗen ƙofar yake min kallon banza kin san shi dai da baƙin halin tsiya, balle yanzu yana ganin ya auri ƴar masu kuɗi kamar yafi kowa a gidanmu.”

         Ƙwafa Umma tai da ƙarfi zuciyarta na sake ƙuntata, cikin fusata da jin haushin lusarancin Huwailar ta ce, “To ke bazaki tashi ki bisu ba. Kije duk ma uwar da akeyi a ɗakin ayi da ke. Ki kuma tabbatar kin kwaso min abinda na sakaki”. Ƙitt ta yanke kiran batare da Huwaila ta sake samun damar cewa wani abu ba. Tasan hanlin Ummar su sarai akan jarabar tsiya, dan haka ta miƙe ta nufi inda taga Asma’u ta shiga. Ba knocking ba komai balle aje batun sallama ta afka musu. Asma’u da ke gyaran gado tai saurin jiyowa, hakama Lulu da ke waya da Sakatariyarta Zainab yanzu idanu ta zubama Huwailar.

       “Kai Adda Huwaila ALLAH har kin ban tsoro shigowa haka ba sallama”. Asma’u ta faɗa cikin jin takaici sai dai ta tausasa harshenta. Harara Huwailar ta zuba mata da taɓe baki ta nufi sofa ɗin bedroom ɗin mai azabar ƙyau da ɗaukar ido ta zauna, itama sai Asma’un ta watsar da ita ta cigaba da gyara gadon cikin takaici. Harta kammala ta shiga toilet shima dan ta gyara Huwaila na cigaba da harare-harare, sai dai fa ɗakin ya mata masifar ƙyau, ji take inama a cikin ƴan ɗakinsu ne suka samu wannan duniyar haka.

     Lulu kam tun kallo ɗayan datai mata bata sake ba tana cigaba da wayarta da Zainab da kuma gyara gashinta data kammala busarwa, so take sai ta kammala taji wace ita da kuma dalilin shogo mata ɗaki haka ba knocking. Asma’u data fito daga Bathroom alamar ta kammala ta yafito da hannu, koda ta iso batare da tayi magana ba ta miƙa mata ribbons da yimata nuni da gashinta alamar ta ɗaure mata. Amsa Asma’u tai da murmushi akan fuskarta, ta shaƙi fitinannen ƙamshin da gashin keyi ta lumshe idanu tana tattarosa cikin hanunta. Dai-dai nan Smart ya shigo ɗakin da sallama. Yayi masifar ƙyau cikin wani kwantaccen yadi da ya sake fiddo nagartarsa ta cikakken bahaushen arewacin Nigeria nutsatstse, daga ita har Asma’un ya zubama ido, sai kuma ya ɗan kalla Huwaila da ke gefe ta baje cikin couch tana ta wani faman hura hanci, sai dai shigowarsa ta sata ɗan nutsuwa dan tasan halinsa sarai.

      “Ku tashi mu wuce ku kuma ko?”.

 Ya faɗa babu alamar wasa tattare da shi. Asma’u ta ce, “To Yaya can gidan zaka kaima”. Kansa ya ɗaga mata kawai batare da yace komai ba, amma sai Lulu da ke ɗan kwallonsa ta cikin mirror ta juya kujerar tana dubansa da ƙyau tare da janye wayar kunnenta alamar ta kammala. Kallon ido sukaima juna, kowanne ya janye nashi cike da basarwa. Ƙasa-ƙasa ta ce, “Please ka barmin Auta anan dan su Afrah ma na zuwa kawo min phones ɗina”.   

         Zuba mata idanu yay sosai da alamar mamakinta, dan shi dai bai san yaushe ta fara son mutane haka ba da har ma tasan ana kiran Asma’u da Auta. Maimakon bata amsa sai ya dubi Huwaila da Asma’u. Da sauri suka fice dan dama Asma’u ita tayi niyyar yin hakan, Huwaila ce dai dake kallonsu ta ƙasan ido bata da wannan niyyar. Lulu da ke kallon yanda yaran ke rige-rigen ficewa ta wani taɓe baki, “Kai kowa ma sai ka nuna masa halinka ne, jibi yanda yara ke fita kamar zasu ci da ka”.

      “Oh ni har wani hali ne da ni kuma wanda ban sanshi ba?”. Ya faɗa cikin ɗan ɗage gira ɗaya da ƙanƙance idanunsa. Nata tai saurin ɗaukewa da ƙara taɓe bakin ta koma ta juya ga mirror ɗin batare data bashi amsa ba. Ƙarasa takowa yay jikin mirror ɗin shima ya ɗan jingina tare da ɗaukar wayarsa ya duba dawa-dawa tai kira. Ganin number Uncle Yousuf da dama yana da ita, data Zainab da itama dai yana da itan dan tun randa ya kaita gida ya amsa saboda wataran. Ya ɗan ji nutsuwa dan shikam yanzu ya fahimci sai yayi takan tsantsan, tunda har jiya tai amfani da shi wajen sayo mata ƙwaya batare da ya fahimci komai ba dole ne ya nutsu ya fahimci duk wani dabarun su. Iska ya ɗan furzar kaɗan da gyara tsaiwarsa da ƙyau sai kuma ya fara magana a hankali tare da maida hankalinsa sosai ga kallon yanda take tufke jelar gashin bayan ta sharceta da comb. Yana matuƙar son gashi a jikin mace, dan haka natan ke matuƙar ɗaukar masa hankali.

       “Zanje na gaida su Ammah na dawo bazan jimaba, sai dai ki sani kar fita ta ta baki damar aikata wani abu daban, dan shaye-shaye babbar hanyace ta maida ɗan Adam baya akan dukkanin nasarorinsa da kima da mutuncinsa. A duk inda mai wannan ɗabi’ar yake zakaga baida farin jinin al’umma, kowa bai san raɓarsa balle huɗɗa da shi da ga sanda aka fahimci yanayi. Shi a karan kansa kuma yakan rasa damammaki da yawa na cikin burinkansa ko nasararsa ta duniya da lahira. Misali ga barin salla, da wahala a samu mai wannan ɗabi’ar da tsaida salla akan lokacinta, hakan kuma babban naƙasu ne ga rayuwa. Karatun Alkur’ani, ambaton ALLAH da sanin mi rayuwa take ciki kota dosa duk dama ce dake kufcewa a hannunsa. Ga ɗiya mace in har tana wannan ɗabi’ar hanya mai sauƙi ce a samu damar keta mata mutuncinta. Shin mi kika rasa a rayuwa na ni’imomin ALLAH da bai miki ba, miyasa ki ka zaɓi gode masa ta wannan hanyar? Miyasa kika zaɓi sakama iyayenki da wannan tukuycin da duk iyayen da suka fuskanci yaransu nayi basu da sauran nitsuwar zuciya, ki tuna kema uwa ce wataran. Bazance miki ki kiyaye ba, dan ban isa hanaki ba, sai dai ki sani wannan itace ɗabi’a ta biyu da bazan ɗauka ba bayan barin salla. Ki zauna kiyi nazari. Ga break fast can su Asma’u sunzo da shi. Nima yanzu zan dawo sai na karya a nan ɗin, ina son yin abu mai muhimmanci ne acan”. Da ga haka ya nufi hanyar fita abinsa batare da ya ko waiwayo ba balle yaga halin da tasirin da maganganunsa sukayi gareta. Lulu da tun fara maganarsa abu ya tokare mata maƙoshi ta raka bayansa da kallo wani shegen takaicinsa da mamakin gadarar nan tasa da yake son fara bayyana mata a fili. Wai mi wannan mutumin ke nufi da ita ne? To duk abinda ya shirya ita a shirye take da mafiyinsa su zuba ita da shi a gidan nan ɗan halak ka fasa, ina ruwansa da rayuwarta….

     Dawowar Asma’u da kayan shara ɗakin ya maidota hayyacinta. Ta kalleta tana ɗan waro idanu waje. “Ya barki ne?”. Cikin zumuɗi Asma’u ta bata amsa da “Eh, amma yace yana dawowa zan wuce. Shiyyasa zanyi sauri na shashshare miki aunty dan shifa Yaya baya magana biyu”. Yanda ta ƙare maganar da ƴar shagwaɓa ya sanya Lulu sakin murmushi. “Uhhm kudai autocin nan ko’a ina sai kun nuna hali. Kinga bar batun sharar nan karki wahal da kanki nace su Amrah su taho da Iya tabawa zatazo duk ta gyara ko’ina”.

       “A’a aunty ki kirasu ma kice su barta basai sunzo da ita ba. Zan gyara yanzun nan dan nan ma sharane kawai da gogewa ya rage. Nifa kin san ina son aikin gida sosai, shiyyasa su Aunty Bilkisu idan suna jin lalacinsu har zuwa suke su ɗaukan na musu hutu koda Ammah zataita ƙorafi ne sunta lallaɓata kenan”.

      “Uhhmm sannu busy body ke baƙya gajiya ma kenan. To nidai bazakimin aiki ba, amma zanso Ammah ta bari ki dawo mana nan kinga na samu abokiyar hira ko.”

          “Tab aunty Ammah bazata bari ba, ba irin nacin da mijin Aunty Bilkisu baiyi ba kan a basu ni amma taƙi ita da Abbah. Amma ke ƙila taji kunyarki ta yarda ko weekend nake zuwa dan tasan dai halin Yaya bai son yin magana sai yaso, kina buƙatar abokiyar hira”.

      “Zan gwada na gani to, ALLAH yasa su bani, bari na shirya naci abinci ina ɗan jin yunwa kaɗan-kaɗan, kema ajiye kayan sharar nan Please”.

     Magiya Asma’u tai taima Lulu har sai da ta barta tai aikin nan, dan danan kuwa ta tsaftace ko’ina ta baza kayan ƙamshi. Itako tana zaune a falo tana tsakurar abincin da su Asma’u suka kawo, sai dai tana buɗe wanda Huwaila ta kawo ta maida da sauri ta rufe saboda jin ƙamshin korin da aka zambaɗa a miyar fankason ta dakar mata hanci, sam ita bata ƙaunar kori a abinci shiyyasa ma idan har an saka batacin sa komai son da take masa. Sai kuma ma akai rashin sa’a fankasu ba abincinta bane shima, duk randa ma Iya Tabawa tayisa a gidan to ita sai dai ai mata wani abun, hakama idan taje gidan Uncle Yousuf ko gidan Grandpa ta tarar anyi bataci, bata son su shi da tuwo sam musamman miyan yauƙi ko wani taga yanaci sai zuciyarta ya hau tashi. Wanda Asma’u ta kawo ta buɗa, a hankali ta saki ajiyar zuciya ganin lafiyayyen yam balls ne a kular farko, ta biyu farfesun naman kaza ne yanata tashin ƙamshin attaruhu da albasa. Sai jug irin mai riƙe zafi ɗin nan ɗauke da kunun gyaɗa da yay ƙyau yanata ƙamshi har da su ƙwa-ƙwa a cikinsa. Sai shayi a flaks da yaji kayan ƙamshi shima, anan kam ajiyar zuciya ta sauke harda sakin guntun murmushi ta zuba kunun gyaɗar da farfesu kaɗan ta fara tsakura tana bin Asma’u da keta aikinta a nutse da kallo da sauraren labarin da take bata akan yanda suke matuƙar jin daɗin abinda take yi game da case ɗin fyaɗe. Haka kawai jin ƙaunar yarinyar take a ranta, balle jin abinda take faɗa na yanayin da suke shiga na jin daɗi har itama tana burin zama lawyer kamarta……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣3️⃣

…….A ɓangaren Smart kam suna isa gidan sashen Abba ya nufa domin gaidasa, yayinda Huwaila ta shige ciki fuuu tana ƙunƙuni. A falo ta iske Umma zaune suna karin kumallo da sauran ƴan uwanta da ƴaƴansu da duk ke shirin wucewa gida a yau tunda biki dai ya tashi. Umma ta bita da kallo kamar a firgice, sai dai kasancewar bata son tace wani abu a gaban sauran yaran ya sata ƙyafta mata ido ta cigaba da cin abincinta. Amma Huwaila sai ta dinga ƙunƙuni, da ga ƙarshe dai ta fara bama ƴan uwanta labarin ƙarya da gaskiya akan wai an mata wulaƙanci a gidan Smart, sun shige ɗaki sun barta, yanzu kuma yace Asma’u ta zauna can ita kuma ya taso ƙeyarta sun dawo. Da yawansu sun hau sun zauna. Sai Ismaha ce dai ta ce, “Humm Huwaila gaskiya ban yarda ba. Koda ace hakan da kika faɗa ma ta faru sai dai idan yanada manufarsa, kowa dai yasan Yaya Hydar a gidan nan kan rashin nuna bambanci a tsakaninmu da ƴan ɗakinsu. Da dai Yaya Salim kikace yayi hakan ko musa miki bazanyi ba…” tana gama faɗa ta tashi tai ficewarta. Cikin ƙanƙanin lokaci falon ya kaure da ka-ce-na-ce, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Da wannan damar Umma da hankalinta sam ba’a jikinta yake ba ta miƙe tana kama hannun Huwaila suka shige uwar ɗaka.

        “K lafiya? Ina abinda na aikeki yi na ganki hannu rabbana”.

    “To Umma ya kike so ki ganni, a gabanki fa na faɗi irin wulaƙanci da akai min a gidan can”.

    “Ke tafi can wawuyar banza da wofi, kin ko san muhimmancin abinda na turaki yi da zaki dawo min da wani shirmenki na banza. Wai ke ko Huwaila yaushe ne zakiyi hankali a rayuwarki. Ƙanwar-ƙanwarki Asma’u har ta fiki wayo amma ke gallaƙeƙiyar budurwa da ake shirinma aure baki son ciwon uwarki ba….”

           “To wai ni Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Ni Wlhy ko ƙyallin wani kayan da suka saka jiya suka cire ban wani gani ba a gidan. Tunda kina ganin banyi miki ƙoƙari ba sai kije da kanki ai”. Tana gama faɗa tai waje abinta. Duk irin kiran da Umman ke ƙwala mata ko waiwayenta batai ba. Sai ma jiyo muryar Smart da tai alamar ya shigo gaishe ta. Sai dai yanda taji ƴaƴan nata na gaishesa a gatsine ya sata fita wuff dan taga suna neman ɓata mata shiri, saboda Malam Na-zuru ya jaddada mata a waya ɗazun da safe sai fa ta rage nuna abinda ke ranta a garesu, musamman ma matar tasa tai duk yanda zatayi ta shiga jikin yarinyar hakanne zai sakasu cin nasara cikin sauƙi. Cike da fara’a ta amsa gaisuwar da Smart ke mata tana tambayar ya baƙuntar sabon waje da amarya. Kansa a ƙasa cikin jin nauyi da girmamawa ya ce “Lafiya Lau tana gaishe ku”.

      “To madalla ALLAH yay muku albarka. Kamayi ƙoƙari ai da ka fito tunda safe haka banyi zaton yau zamuga idonka ba a gidan nan kwata-kwata.”

     Shi dai murmushi kawai yay yana miƙewa batare da ya bata amsa ba ya fice abinsa. Sashen Ammah ya shiga dan ya gaisa da mama da Aunty Amarya. Nan ma dai zama yay suna gaisawa da dangin mahaifiyarsa da ke ta jansa da kiransa babansu babansu. Daga haka suka sake ɗora masa da nasiha mai ratsa jiki tare da addu’oin zaman lafiya mai ɗorawa da zuri’a mai albarka. Bai jima ba sosai Adda Suwaiba tace ya tashi yaje yabar matarsa dan ma Asma’u nacan. Daga haka yay musu sallama ya fito bayan sun ɗanyi magana da Ammah a gefe ya kawo kuɗin jikinsa na gudunmawa da ya ɗan sassamu ya bata akan ta basu suyi kuɗin mota. Daga haka ya juya ya tafi akan zuwa anjima zai dawo kafin su tafi gidan su Lulu godiya ta al’ada da ango kanje da abokansa gidan dangin amarya washe garin tashin biki…..

      Har lokacin da ya shigo gidan Lulu na zaune tana tsakurar abincin nan, yayinda Asma’u ke ƙarasa saka turaren ruwa a carpet ɗin falon da labuloli. Ɗaga kai kawai tai ta kallesa ta maida kan abincinta batare data amsa masa sallamar ba. Sai Asma’u ce ta amsa tana masa sannu da zuwa cikin girmamawa. Amsa mata yay da kansa kawai. Da yake hankalinta ba’a kansu yake ba ita bama ta lura Lulu bata amsa masa sallama ba. Ta kammala ta maida turaren a inda ta ɗauka Lulun na mata sannu cikin murmushi. Ta gefen ido yake kallonta da mamakin yanda take sakema Asma’un. Baki ya ɗan taɓe batare da ya kalla Asma’un ba ya ce, “K zoki bani abincin nan na karya”. Amsa masa tai da to Yaya, sannan ta nufi kitchen ɗin ɗakko masa plate kamar yanda ta ɗakkoma Lulu ɗazun. Sai lokacin ya dubi Lulun a kaikaice, cikin deep voice ɗin nan tashi a dakensa ya ce, “Ke baki iya amsa sallama ba balle sannu da zuwa ko, amma kin iya tasa abinci kina ci”.

       “Sauƙin ma bakai ka bani ba balle kamun gori shishshigi master”. Ta faɗa tana balla masa harara. Lips ɗin ta dake motsawa a hankali yabi da kallo, sai kuma ya ɗan cije nasa da ɗauke kansa yana jin wata irin kasala na sake saukar masa fiye data barcin da yake ji. Bai sake magana ba saboda fitowar Asma’u, ta jawo basket ɗin gabansa tana buɗe kulolin da faɗin, “Yaya mizan zuba maka bayan kunu dan nasan dai shikam ba canji”. Ƙaramar hararar data sata saki siririyar dariya ya sakamar mata, sai kuma ya nuna mata yam balls ɗin da faɗin, “Karki sakama kunun komai”. Da to ta amsa masa, sannan ta zuba komai yanda ya kamata kuma dai-dai adadin da tasan zai cinye dan shima yam balls ɗin ma masoyinsa ne. Lulu da ke satar kallon abincin ta gefen ido ta ce, “Hu’umm kuma duk cinyesa zakayi?”. Yanda tai maganar da ɗan waro Luluu eyes ɗinta waje tana riƙe haɓa ya bama Asma’u dariya, sai dai ta danneta da ƙyar ta tashi ta fice da ga falon gaba ɗaya taje waje tai abarta son rai. 

       Smart ya ɗan laɓe baki batare da ya kalleta ba ya fara cin abincinsa da faɗin, “Mi kike tsoro ne a cikin cin abincin nawa? Kina gudun kar ki gagara ɗaukata ne?” ya ƙare maganar da ɗago idanunsa da take kira na macizai ya zuba mata su. Baki ta taɓe cikin masa kallo mai kama da harara ta ce, “Kamar ya? Miya shafen da nauyinka?”.

      A karan farko ya saki wani makirin murmushin da aduk sanda yayisa yake tunzurata dan tafi kwallonsa a murmushin rainin hankali ya cigaba da cin abincinsa. Siririn tsaki taja da ɗauke kanta itama ta cigaba da shan romon farfesun da yaci ace tama manta ta gama ci. Amma ina gayu da yanayinta yasa anata tsakurarsa, ga shi yamata daɗi matuƙa ta yanda ta gagara ajiyesa. Duk da yaji tsakin nata bai sake yin magana ba ya maida hankalinsa ga cin abincin harya kammala zai tashi, sai lokacinne itama take kammalawar. Asma’u ya ƙwalama kira, ta amsa da ga waje dan ta gama zagaye gidan ne tana jin daɗin kallon flowers ɗin da aka ƙawatashi da su. “Zoki wuce gida” ya faɗa yana miƙa mata ɗari biyu. Lulu Asma’u ta kalla cikin shagwaɓe fuska, itama Lulun shi take kallo, ta ce, “Kamarya tazo ta tafi? Nan fa zata kwana”. Yanda take maganar itama kamar a shagwaɓa-shagwaɓa ya sashi kallonta. Sai kuma ya ce, “A ina ɗin zata kwana? No karma ku fara abinda bazaku iya ƙara sawa ba, common Malama ɗakko hijjab ɗinki ki wuce gida, wannan abincin ki tafi da shi a bama wani dan nan dai bacinsa za’ai ba”. Da ga haka yay wucewarsa hanyar bedroom. Sum-sum Asma’u ta nufi kwanikan da suka kammala cin abincin ta tattara zata kai kitchen sannan tazo ta wuce dan tasan shifa baya magana sau biyu. Takaicin wannan nuna isar tasa ya saka Lulu miƙewa a fusace tabi bayansa. Burumm ta shigo ɗakin dai-dai ya zare rigarsa zai cire wandon, amma sai ya dakata ya tsaya kallonta.

      “Malam wai kai miyasa kake son dinga juya mutanene kamar wasu ƴaƴanka?”.

      Kallonta kawai yake yi batare da yace komai ba. Aiko sai ta sake fusata da takaicinsa ta ce, “To babu inda zataje”.

         “Idan kece sama da ni kenan”.

      Ya faɗa yana ƙara tsatstsareta da idanu. Itama a tsiwace ta ce, “Oh da mika ɗauki kanka?”. Karo na biyu ya saki murmushi, dan shi kam ƙarfin halinta tunba yanzu ba dariya ma yake bashi. A hankali ya tako zuwa gabanta daf, ta wani yamutsa fuska tare da matsawa baya tana hararsa, sake matsawa yay shima ta matsa itama, shima ya bitan dai, a masife ta ce, “Miye haka wai?”.

      “Ina son nuna miki abinda na ɗauki kaina ɗin ne Madam” yay maganar dai-dai suna danganewa da bango idanunsa cikin nata. Yanda suke daf-daf ga hannunsa da ya tokare a bangon ya bashi damar dabaibaye ta da ƙyau har tanajin numfashi na neman mata wahalar shaƙa dan in ma ta shaƙa ɗin ƙamshinsa ne iskar da kawai take iya zuƙowa ya sata faɗin, “Aliyu bana son iskanci da raini fa. Dalla matsa min”..

            “Haba Madam! K bakiji kunyar faɗar sunan ba haka gatsal sunan mijinki ne fa”. Yay maganar da sake ranƙwafowa yay mata rumfa ta yanda jikinta ke neman fara rawa. Amma sai ta dake dan bata yarda itafa yaga gazawarta ba. Hannu tasa ta turashi amma ko gezau, sai ma wani lumshe idanun da yay ya sauke akan hannayen nata da ke a saman jikinsa. Da sauri ta janye tana jan tsaki da faɗin, “In ma abinda banzan zuciyarka ke faɗa maka kenan to ka goge, dan tamkar kana mafarki ne a gaɓar da ake gab da tashinka da ruwan sanyi, wannan auren baida maraba da wasan drama ɗan son banza phone store”.

      Idanunsa ya lumshe da buɗewa a lokaci guda yana cafko hanunta dan shirin duƙewa take tabar wajen. “Haba Madam ya kuma zaki wuce ban nuna miki abinda na ɗauki kan nawa ba?”.

          “Aliyu!!”.

     Ta sake faɗa da ƴar tsawar takaicin kiranta Madam da yake yi dana goga jikinsa a nata.

       “Uhmm Madam”.

   Ya amsa mata da wata irin kasalalliyar muryar son sake ƙular da ita yana sake kusanta fuskarsa gab-gab………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣4️⃣

……..Ƙarshen kuma firgita Lulu ta gama kaiwa, sai dai kafin tai wani yunƙuri a matuƙar bazata taji saukar lips ɗinsa masu sanyi akan tausasan nata masu sheƙi da ƙamshin lipgloss ɗin data ɗan saka, cin abinci ma yasa duk ta shanye rabi. Iyakar rikicewa da firgici Lulu ta shiga, gashi ya mata ritsawar da ko iya motsa kanta ta gagara yi balle tace zata iya ƙwacewa. Shi kansa da yayi ne domin kawai tabbatar mata ba drama ɗin data ambata ɗin bane jiyay gaba ɗaya jininsa na yamutsawa, dan karo na farko kenan a rayuwarsa da haka ta faru tsakaninsa da mace. Da ƙyar ya iya juriyar shafe minti guda sannan ya sake mata lips amma bai matsa da ga jikin nata ba, sai ma magana da ya fara cikin kunnenta muryarsa a wani irin sarƙe duk da jarumtar son hana hakan bayyana da yake nunawa. “Waya gaya miki baƙo na kwana gidan sabbin aure ne? Ai sai ya jiyoma kansa abinda zai hanashi barci, bar yarinyar mutane ta tafi gidansu girmanta bai kai ba. Sannan ki rage ɗaukar kanki sama can ƙololuwa, dan a wannan fadar Aliyu Hydar shine ZAKIN KI. Fassara SARKIN KI Mawaddatan’warahmah Isma’il Ibrahim Jiƙamshi”. Ya ƙare maganar da ɗanja baya yana wani kashe mata ido ɗaya ya bar wajen gaba ɗaya.. Suɓul numfashin Lulu ya nema barin jikinta. Takaici ne, baƙin ciki ne. Mamaki ne bata sani ba. Abinda kawai ta sani wannan itace rana mafi abin takaici da koma baya da tazo mata a tarihinta. Bakin illiterate driver ɗinta ne cikin nata, ya zuba mata yawunsa ta sha fa a cikin cikinta. Wayyo ALLAH shike nan tata ta gama ƙarewa….

       Kamar Smart ya san mi take tunani, dai-dai yana hawa gadon ya wani lashi lips ɗinsa da faɗin, “1-0 kenan, amma fa yawunki akwai daɗi Madam. Ina fatan nawa ma akwai ɗanɗano na musamman irin wanda iyali zasu so. Dama na faɗa miki jahilin baƙauyen nan fa ɗan takife ne, ki guji masa gatsali dan bajin magana yake ba. kije ki sallami yarinyar mutane inba haka ba na tashi na ganta a gidan nan ita ranta zai ɓaci, ke kuma zakisha yawun baƙauyenki”.

       Harara ta watso masa da faɗin, “Shash….” bata ƙarasa ba ya yunƙura zai tashi. Da gudu ta fice kuwa tana nunashi da yatsa da faɗin, “Wlhy sai na koya maka hankali. Maye!”.

            Komawa yay ya kwanta yana mai lumshe idanunsa da sakin ƙaramar dariya. A hankali ya furta, “Na samu promotion da ga illiterate velleger zuwa MAYE kenan”. Sai kuma ya kai hannunsa saman lips ɗin nasa ya shafa yana jin wani abu na masa yawo a cikin jini har yanzu. “Ko mima ya kai ni, ni Aliyu Madam ce fa”. Ya sake faɗa yana wani ɓata fuska kamar gaske, sai kuma yaja filo ya ɗaura a saman face ɗin sa da sake faɗin, “ALLAH ya shiryeka Aliyu wannan abun kunyar da ka tafka fa wa ogarka”.

         (😂😂Ɗan manni, amma ka kwana da sanin idan muka tashi ramawa sai ka raina kan ka malam🥱 Tom😏🚴).

       _________★

      A hankali Mommy ta jinjina kanta tare da sakin ajiyar zuciya na ɗunbin mamakin Daddy a karo na babu adadi. Kallonta ta sake maida wa garesa har yanzu yana a yanda yake zaune da tagumi hannu bibbiyu. Abincin data ajiye masa kusan tsawon awa guda har ya ƙandare shayin ko ya koma kamar ruwan sanyi. A tsakanin shekaranjiya zuwa yinin jiya yanayinsa na nuna kewar barin Lulu gidan ne kamar yanda suma duk sunji hakan a ransu, amma da ga daren jiya zuwa safiyar yau yanayin nasa sai ya ninka ko barcin kirki bata tunanin yayi, da farko tayi tunanin ko baya jin daɗin jikinsa ne. Amma koda ta tambayesa amsar da ya bata sai taji ta girmi kunnenta. Tun cikin daren take tunanin anya kuwa mijin nata kuma ɗan uwanta lafiya lau yake? Dan al’amarin nasa kuma ya fara wuce makaɗi da rawa. Ita bama ta fatan ko Yousuf yaji wannan taɓargazar tasa a wannan gaɓar dan abin kunya ne na gaske. Ajiyar zuciyar ta sake saukewa, sai kuma ta miƙe a nutsenta ta koma gefensa ta zauna. Karo na farko akan al’amurin Lulu ta fuskancesa da son tausasawa da nuna masa goyon baya ɗari bisa ɗari. Hannunsa ta kamo cikin nata tana ɗan murmushi da faɗin, “Yaya kayi haƙuri kaci abincin, ka kuma kwantar da hankalinka bari na shirya sai naje gidan na duba mana Mawaddat ɗin, duk da dai inaji a jikina yaron nan bazaiyi abinda zamuce ALLAH wadarai ba. Amma nima zuwa yanzu zuciyata tafi gamsuwa da naje na dubatan tunda babu waya a hannunta balle mu kira, tura yara kuma bazai bamu abinda muke so ba.”

       A karo na farko shima Daddy ya dubi Mommy ɗin da tausasawa a akan lamarin Lulun. Murya a sanyaye ya ce, “Kina ganin baza’ace munyi ba daidai ba Kareema, kin san fa masifar Yousuf akan yaron nan daban ce, na rasa wane irin so yake masa da bai son ace yayi ba dai-dai ba. Ni kuma wlhy ina tsoron ya illatamin yarinya a banza tunda dai ba taɓa auren nan yay ba balle muce zai kamanta dattako”.

        Shike maganar amma Mommy ita kejin kunyar, amma sai ta danne ta biye masa cikin sake kwantar da murya. “Na fahimceka Yaya, dan samarin nan na yanzu kam rawar kai ya musu yawa, duk da shi dai a fuska kamar nutsatstse amma ba’a yabon ɗan kuturu. Yanzu dai kaci abincin bara na canjo maka sai naje na gano ɗin ko yaya kace?”.

     “Shike nan, in dai kina ganin babu matsalar kije ɗin, dan nima dai hakan zai fi sama min kwanciyar hankali. Sannan dan ALLAH ki lallaɓa Yousuf ya bata wayoyinta dan mu dinga jinta akai-akai”.

          “Karka damu idan yazo anjima zan masa magana. Bari na kawo maka abincin kaci namaje na dawo da wuri kafin yazo gidan”.

    Kai ya gyaɗa mata, ita kuma ta tashi ta fice idanunta na cika da ƙwallar tausayinsa. Yayinda zuciyarta ke faman kai kawon anya kuwa mijin nata yana lafiya? Dan ita dai gaskiya a wannan gaɓar ta fara jin al’amarin nasa da girma, wanan wace irin makauniyar soyayya ce? Haka fa idonsa yay masifar rufewa akan mahaifiyar yarinyar nan a lokacin tamkar wanda baya a hayyacinsa. Anya kuwa basuyi kuskuren nutsuwar fahimtar al’amarin nan ba a bai-bai tun a shekarun baya? Kuɗi kam na iya canja mutum fiye da abinda Daddy yayi a kan Mawaddat, sai dai akan ƴarsa Mawaddat kuma fa? Idan ance soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta gaba ɗaya ai abin nasa na neman wuce makaɗi da rawa kuma, sannan ko sanda ya auri Mawaddat yanada abin hannunsa, bayan auren nata ne dai ya sake bunƙasa za’ace, gaskiya tana buƙatar yin dogon nazari a wannan karon fiye da wanda sukeyi a baya game da shi. Koda ta kawo masa abincin ma lallaɓashi tai tayi sai gashi yaci, ta sake lallaɓashi yay wanka ya kwanta dan yau kam babu alamar zaije office ma. Ita kuma ta shirya ta fice a gidan kamar gaske gidan Lulun zataje. Yo ita zata biye masa ne su zama ɗaya miya ja mata wannan abin kunyar. Gidan Uncle Yousuf tai tafiyarta, tai sa’ar samun shima yau ɗin bai fita office ba wai zai ɗan huta a gida…….

      ____________★

           Duk yanda Lulu taso lallaɓa Asma’u ta zauna hakan bai yiwu ba, dan ita dai Asma’u tasan wanene yayan nasu. Haƙuri tai ta bama Lulu akan ai zataje ta dawo kawo musu abincin rana. Amma yanzu idan bataji maganarsa ta tafi ba ya fito zai iya zane ta. Mamakin Lulu sai ya sake ninkuwa, irin wannan tsoronsa da suke ai abin yayi yawa. Amma idan yasan wata ai bai san wata ba. Sai tayi duk yanda zatai Asma’u ta dawo gidan nan da zama kafin cikar sati ukun da zatatai a cikinsa kodan ta tabbatar masa itama ɗin ba kanwar lasa bace. Da ga haka tabarta ta wuce. Kasancewar gidan shiru ita kuma bata son kaɗaici yana tayar mata da hankali ya sata miƙewa ta ɗan zazzagaya, duk da kasancewar gidan ƙarami sosai, dan ko sashen masu aikinsu ya fisa girma bai hana gidan birgeta ba. Balle ma an sake ƙawatashi da kayan da aka zuba mata, wanda har mamakin sakasu tayi ita da zatai zaman sati uku. Sai dai batace komai ba akan hakan. Ta ɗan jima a waje tana shan iska sai kuma ta koma ciki, bedroom ɗin ta, a ranta tana raya gara ta ɗan sha abubuwanta ta kwanta itama tai barci, sai dai me koda ta duba babu ledar maganin ma gaba ɗaya. Shiru tai alamar tunanin ko ta ajiyesu a wani waje ne, kai ina a bedside drawer ta barsu. Da sauri ta buɗe drawer ɗinsa amma babu alamar su, maganganunsa na ɗazun bayan zuwan su Asma’u ne suka shiga dawo mata, to ko ya fahimci abinda tai jiyan. “Wayyo ni” ta faɗa tana dafe kanta. Dama fa tayi matuƙar mamakin jin ya ɗakko topic ɗin nan, sai dai kafin tai masa tambayar da tai niyya ya fita ya barta. “Mutum nan maye ne, ya akai yay saurin ganoni” ta sake faɗa tana faɗawa saman gadon da jan tsaki. Bataso haka ba gaskiya, dan tana ganin ta samu hanya mai sauƙi da zata dinga samun abinda take so cikin sauƙi tana wasa da hankalinsa. “Mugun kai fal gadara da ƙauyanci sai shegen wayo kamar ɗan dila” ta sake faɗa cikin nuna takaici. Da ga haka tai shiru lamo abinda ya farun yanzu babu jimawa a tsakaninsu na sake dawo mata. Tsaki taja mai ƙarfin masifa ta sake juya kwanciyarta dan sam bata son tunawa, dan duk ƙaƙarin aman data dinga yi bayan barowarta ɗakin nasa batai ba, sai ɓigewa tai da yin brush kusan sau huɗu amma hakan bai hanata cigaba da jin saukar lips ɗin nasa a nata ba har yanzu. Tsaki taja tana tunzura bakin gaba. Da ga haka ALLAH ya taimakata barci ya kwasheta mai ƙarfi. Dan koba komai akwai gajiya da ƙarancin barcin na kwana biyu a tattare da ita………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣5️⃣

……..Cike da matuƙar ɗoki Asma’u ta isa gida, kusa da Ammah ta zauna da ke kallonta ganin yanda take ta faman washe haƙora. “Auta lafiya kuwa irin wannan washe baki haka ko suruki na samu?”. Adda Sa’adah ta faɗa cike da zolaya. Su Adda Suwaiba da ke ta shirin wucewa gidajensu suma dai duk idanu suka zubawa Asma’un. Dariyar ta sake faɗaɗawa tana ɓoye fuskarta a jikin Ammah da faɗin, “Kai Gwaggo nifa ba haka bane, zan faɗama Ammah albishir ne”.

      “A to muma sai a faɗa duk muji ai”. Cewar Gwaggo Sa’adah. Asma’u dai na dariyarta ta ce, “Gwaggo dama fa zan sanarma Ammah ne matar Yaya itace lawyer ɗin da take so ɗin nan mai taimakon mutane musamman akan harkar fyaɗe”.

       Kallonta Ammah tai da sauri, dan haka cike da zumuɗi Asma’u ta sake faɗin, “Wlhy Ammah da gaske nakeyi. Barrister Mawaddat Jiƙamshi ce matar Yaya, dama tun shekaran jiya nake ta mamaki dana ga kamanninsu yayi yawa duk da ban taɓa ganin waccan a zahiri ba sai a tv, sai banyi magana ba sai yau dana tabbatar”.

     Wani irin abu ne mai sanyi ya shiga ratsa zuciyar Ammah ta shiga sake tsarkake sunan ALLAH maji roƙon bayinsa. Tun a randa ta fara ganin yarinyar nan ana hira da ita a gidan tv akan wani case data cimmawa na fyaɗe har yarinyar ta kamu da cuta mai karwa garkuwar jiki da wanda yay mata fyaɗen ya goga mata a ranta taji inama ace ɗiyarta ce ita, ko kuma Aliyu ya sameta a matsayin mata. A ranar tai addu’a da fatan idan hakan zai iya kasancewa kuma ya zama alkairi ALLAH ya tabbatar, idan kuma har matarsa ce. Amma da ga baya sai ta cire hakan a ranta sakamakon jin yarinyar ɗiyace ga babban hamshaƙin mai arziƙi nan Alhaji Isma’il Ibrahim Jiƙamshi. Ta cigaba da ƙaunarta kawai a ranta da mata fatan alkairi a rayuwa. Tuna wannan al’amari ya sakata jin ratsawar wannan al’amari mai sanyi har zuciyarta na harbawa da sauri-sauri, tabbas wannan shine ɗaya da ga cikin alkairan son mutum domin ALLAH, dan ita kam taso yarinyar nan domin ALLAH ne……

★★….

      Tunda Mommy ta fara magana Uncle Yousuf ya zuba mata idanu kawai yana kallonta har sai da takai aya. Ta ƙare da faɗin, “Gaskiya Yousuf zuciyata ta fara raya min wani al’amari mai girma. Anya kuwa babu lauje cikin naɗi a wannan al’amarin. Kasan mu mata munada wani hali na rufewar ido a duk sanda muke son ganin buƙatarmu ta biya akan abinda muke so. Ka tuna randa marigayiya ta fara ganin Yaya kuna tare, kuma kaine da kanka ka sanar min tunda yay mata kallo ɗaya ya watsar da lamarinta har kuka baro gidan a wancan lokacin bai sake kulata ba”.

       “Tabbas anyi haka aunty Kareema, amma miya alaƙanta wannan abin kunyar da yake yi yanzu da wancan?”.

     “Ba zamuce sunada alaƙa ba, ba kuma zamuce basu da shi ba. Amma inaji a jikina wannan soyayyar mai zafi da yakema Mawaddat bata lafiya bace.”

          Murmushi Uncle Yousuf yay da gyara zamansa. Ya ce, “Aunty Kareema ban katseki ba ko ƙin fahimtarki anan, amma ina roƙonki karki sakama zuciyarki komai game da abinda Yaya keyi da tunanin wani. Lafiyarsa lau ya kuma san mi yake yi sarai. Akwai dai abinda yake ɓoyewa shiyyasa yake kaffa-kaffa da Mawaddat, dan ba wai tsantsar soyayyar bace ba kawai. Abu na biyu tausayin rasa mahaifiyarta tana laɓuɓuwa ma ya taka rawar gani a kansa. Kin san mu maza munada wani abu akan ƴaƴan mu musamman idan ya kasance mahaifiyar yaro bama tare da su, sai mu dinga jin wadda ke riƙe da su zata cuta musu ne kawai. Shiyyasa zakiga maza da yawa suna samun saɓani da matansu akan ƴaƴan da uwarsu ta fita a gida, kota rasu ta bari.”

        “To haka ɗinne kuma. Amma inaga ya kamata ace munsan abinda yake ɓoye manan ko hakan zaisa mu fahimcesa”.

     “Karki damu zamu sani, lokacin mu sani ɗinne dama baiyi ba, ina kan bincike yanzu haka ma”.

     “To Alhamdullah ALLAH yasa muji alkairi.”

      Da Amin ya amsa mata, da ga haka suka cigaba da tattauna al’amarin Daddy ɗin har zuwa wani lokaci kafin tai musu sallama ta koma gida. Ta samu Daddy na ramuwar barci da ya gagara yi daren jiya, bata tashesa ba har sai da ya tashi da kansa sannan ta labarta masa abinda ya sakasa nutsuwa kamar yanda suka tsara da Uncle Yousuf. Murmushi yay da faɗin, “Ashe yaron nan nada hankali har haka”.

      Dariya Mommy tayi kawai batace komai ba. Shima sai bai sake bi takanta ba ya tashi ya shige bayi fuskarsa ƙawace da murmushi…

     __________★

        Gab da Azhar Smart ya tashi a barcin da yay, yaji daɗin yin barcin kuwa sosai, dan haka ya watsa ruwa da ɗaura alwala yasa jallabiya ya fice massalaci batare daya nema Lulu ba. Sai da aka idar da salla ya dawo gidan sannan ya nufi ɗakinta. Baccinta take hankali kwance, beauty face ɗinta ta sake yin wani fayau kasancewar babu ɗigon kwalliya, hatta lips ɗin ma yanzu babu ko lipgloss ɗin a jikinsa. Samun kasan yay da tsira mata idanun nasa na tsawon mintuna, tabbas ita ɗin ƙyaƙyƙyawace, sannan tana cikin jerin mata masu tsananin kula da jikinsu ta hanyar gyarashi kwaf-kwaf a kowane motsi. Ga izza da gayu da duk wani cikakken namiji bai isa mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa ba, “Sai dai akwai kauɗi da masifa kuma ba” ya faɗa a fili yana ɗan taɓe baki da ƙarasawa gaban gadon ya tadata. Idanunta ta buɗe a hankali ta saukesu kansa. Yanda ya ɗan ranƙwafo kanta ya sata zabura, dan yanayin ya mata kamar wani abu da ya shuɗe a baya. Tashi yay shima tsaye da kyau yana girgiza kansa. Fuska ba wasa ya ce, “Tashi kiyi sallah”.

      Harararsa tai kamar zatai magana sai kuma ta fasa saboda yanda yay masifar kafeta da idanunsan nan da bata ƙaunar ya zuba mata su, dan duk wani ƙarfin gwiwar ta sai ya sare taji komai ya kufce mata. Dama fitsari take ji dan haka ta sauka a gadon tana wani yamutse fuska ta nufi bathroom ɗin. Sai da ya bata ɗan lokaci sannan yabi bayanta, anyi sa’a kuwa zata fara alwala.

        “To alwalan ma a gabanka zanyi?”.

     “Haka ya kamata, ya kuma dace, dan hakki ne a kaina sanin ibadarki da komai naki a yanzun”.

             “Kai a wa?”.

        “Mijinki”.

     “Kana son shigarmin rayuwa da yawa”.

“A ciki nake tsunduma ma ai”

   “Mafarki kenan”.

“Ni da ke duk a ciki muke, mai rabo a cikinmu sai ya fara farkawa ya fuskanci reality. Yi alwala lokaci na tafiya”.

        “Al….”

    Sai kuma ta kasa ƙarasawa saboda tuno abinda ya faru ɗazu a ɗakinsa saboda faɗar sunan nasa. Sai kawai ta ɓige da maka masa harara cikin ƙunƙuni ta furta “Zan koya maka hankali sannu-sannu”.

       Duk da yaji bai tanka ba, dan ya gaji da magana haka nan. Itama sai tai ƙwafa ta juya ta fara alwala. Shi dai yana kallonta harta kammala zata miƙe ya ce, “Dakata. Mawaddat ba haka ake alwala ba sam. Akwai kura-kurai matuƙa a cikin wadda kikayi. Dan haka ina son ki bani hankalinki nan duk abinda nayi kiyi, yanda ake alwala shine. Da farko yin niyya a zuci sannan ki ce Bismillahi, sannan ki wanke tafukanki na dama da na hagu kowanne sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki kurkure bakinki ki zubar da ruwan sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki shaka a hanci ki fatar shi ma sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki wanke fuskarka gaba ɗayanta sau uku, ki lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon goshinki har izuwa karkashin haɓarki, wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a faɗi kuma tun daga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu. Sannan ki wanke hannu tun daga tafuka har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima sau uku. Sannan ki ɗebo ruwa ki yi shafar kai wato a tafin hannu ki shafo tun daga farkon goshi har ki kai ƙeya sannan ki sake dawowa farkon goshi. Sannan shafar fatar kunnuwa na dama da na hagu. Sannan ki wanke ƙafafu na dama da na hagu tun daga tafin ƙafa har izuwa gwiwar ƙafa. Ina fatan kin fahimta, amma zan fara sai kiyi duk yanda zanyi”.

         Batace komai ba, sannan bata nuna zata ƙiyi ba. Dan ita dai tun maganarsa ta ɗazun akan mahaifiyar ta ya matuƙar sanyaya mata jiki, tsaf ta dingayin yanda yake yi har suka kammala, har cikin ransa yaji daɗin rashin gardamarta a wannan gaɓar. Dan haka ya ɗora da faɗin, “Akwai addu’a bayan kammala al’wala. Zan koya miki ita bata da wahala bata kuma da tsaho, sai dai ba yanzu ba sai na kammala shirina akan hakan. Muje kiyi sallarki”.

        Komai batace masa ba yanzu ma tai wucewarta ta fita shi kuma yabi bayanta yana jin wani kaso na takaicin abinda ya faru daren jiya akan sayen magani na raguwar masa a zuciya. “Yanzu bamu da isashen lokacin da zan miki filla-filla akan yanda ake salla, amma zan nuna miki kaɗan a ciki kafin mu fara karatu na musamman akanta.” bai damu data amsa ba ya shiga nuna mata da faɗa mata abinda zata iya fahimtarsa a yanzun, nan ma dai batace komai ɗin ba har ya kammala ya bata izinin kabbara sallarta. Da ga haka ya samu waje ya zauna yana kallonta har ta idar. Ya dubeta zaiyi magana game da addu’a ganin har ta miƙe da ga sallamewa kira ya shigo wayarsa. Ahmad ne, dan haka ya ɗaga yana kaiwa kunne. Shaƙiyanci sosai Ahmad ke masa da ga can, har sai da ya sashi furta, “Ɗan sa ido ina ruwanka to. Kai ni karma kazo min gida ka tsaya nan nazo na sameka mu tafi”. Ƙaramar dariyar da ta saka Lulu kallonsa yayi kaɗan saboda jin abinda Ahmad ya faɗa da ga can. Sai kuma shima Smart ɗin da ya miƙe zai fice taji yana furta, “Irinku ne masu takurama sabbin aure da zarya har sai an cinye kayan gara da k….” daga haka ya fice bata ƙarasa ji ba. Baki ta taɓe kaɗan da ajiye sallayar tana sauke ajiyar zuciya da bata san dalili ba, da ga haka ta ajiye batunsa tai zaman dirshen a kan gado ranta fal tunanin cases ɗin dake gabanta. Dole ne ma gobe idan ALLAH ya kaimu ta fita office, kwana kusan tara yau fashin yayi yawa ai haba. Bata sake jin motsin Smart ba har sai da Mubarak ya kawo abincin rana. Lokacinne ya shigo ɗakin cikin shirinsa da alama fita zaiyi dan yaci wani faran shadda ƙal harda hula baƙa, ƙamshi yake mai sanyi ya fito a angonsa dai kai tsaye. Da ga bakin ƙofa ya dakata yana faɗin, “Ga lunch can an kawo ni zan fita su Ahmad na jirana”.

         Baki ta taɓe kawai batare da tace komai ba. Shima sai bai sake cewa koman ba ya juya yay ficewarsa dan ya fahimci ƴan izza da masifar ne yanzu a kanta. Shi kuma bashi da wani isashen lokacin biye mata a yanzun……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣6️⃣

……..Ya samu su Ahmad na jiransa a ƙofar gida shi da wani cousin brother ɗinsa babban fan ɗin Smart akan ball, da yake kusan sa’ansu ne shima sai suke zumunci sosai duk da shi Smart ɗin yana jajja baya kamar yanda halayyarsa take na rashin sakewa da mutane. Ko Faisal yayi fushi sai kuma ya dawo dan matuƙa Smart ke burgesa a filin ƙwallo, damma ƙaddara ta hana komai gudu ai da yasan yanzu Smart na cikin manyan ƴan ƙwallo da Nigeria ke alfahari da su. Sun gaisa tare da zolayarsa irin na abokai musamman ma Ahmad da ya tasashi gaba sosai kafin su wuce Smart na roƙama Ahmad shiriya. Gidan Daddy suka fara zuwa. Inda suka sami tarba ta musamman da ga Mommy da su twins da basu koma ba. Bayan sun gaisa da Mommy sukai godiya tai musu iso falon Daddy da ya riga yasan da zuwansu. Ya ɗan sake musu fuska harda jansu da hira duk da sunata faman sinne kai musamman ma Smart. Dan koda aka kawo musu abin sha da ruwa da kayan motsa baki Faisal da Ahmad ne kawai suka sha ruwa. Shiko babu abinda ya taɓa. Wasa-wasa sun share kusan awa ɗaya da rabi kafin su baro gidan da wasu kayayyakin Lulu da Mommy ta saka Mubeen kai musu akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kimu za’a kai mata sauran kayan. Da ga nan gidan Uncle Yousuf suka nufa. Anan ɗin ma dai tarba suka samu ta girmamawa ga Aunty Saliha. Uncle Yousuf kuwa babu ruwansa zama yay cikinsu tamkar aboki tunda su duka ukun babu baƙonsa, gara garama Smart ɗin, amma su Ahmad ai tun suna dajinen majina ya sansu. Anan ma sun jima dan har sai da aka kira sallar la’asar sannan suka fito tare da Uncle Yousuf ɗin zuwa massalaci. Bayan sun dawo basu shiga ciki ba sai mota tunda dama sunyi sallama da Aunty Saliha. Anan ma dai an bada wasu kayan Lulu da wayoyinta da laptop da Uncle Yousuf ya amshe. Bayan sun baro nan Smart yace ma Ahmad yana son zaije yaga Malam tunda zuwa gidan Baba da sukai niyya ya rushe sakamakon sanar dasu Baba yayi tafiya Legos da Uncle Yousuf yayi. Ahmad yace babu damuwa. Sun nufi Yakasai wajen Malam Nasirudden. Sunyi sa’ar samunsa kuwa a gida bai fita ba. Bayan sun gaisa Ahmad ya janyo Faisal cikin dabara suka fito suka bar Smart tare da malam ɗin.

          Malam Nasirudden da ya fahimci akwai magana ya dubi Smart cikin murmushi da kulawa ya ce, “Idon Aliyu ango ne haka a waje, kai da ya kamata ace kana can gida sai bayan wata ɗaya ka fito”.

       Murmushi mai bayyana hakwara Smart ya saki a karo na farko, cikin sinne kai ya ce, “ALLAH ya gafarta malam idan hakan ta kasance ai kwa zaneni matsayinku na iyaye”. Dariya shima malam yayi da faɗin, “Ina ai idan hakan ta faru mun san lafiya ce ta ɓoye ka ai Malam Aliyu. Ya amarya da gajiyar biki?”.

            “Alhamdullah Malam”.

       “To Masha ALLAH, ince dai ba jikin bane ba ko?”.

“A’a malam jiki kam Alhmdllh, dan duk yau banji ciwon kan nan ba. Wani abu ne mai muhimmanci ya kawo ni dan ina buƙatar ƙarin haske da shawara”.

     “To Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya mai albarka. Ina saurarenka mike tafe da kai?”.

    Zama Smart ya gyara yana sauke ajiyar zuciya da furzar da iskar bakinsa. “Malam akan ita matar tawa ne nake neman shawara. Kasan yanda al’amuran rayuwar nan suke tafiya a wannan lokaci musamman tarbiyya da ke neman zama wani babban ginshiƙi mai wahalar aiwatarwa ga iyaye ko riƙewa ga mu ƴaƴan, wasu zakaga iyayen nata iya bakin ƙoƙarinsu amma sai su fuskanci jarabawa a cikin ƴaƴan wasu su fanɗare, ko kaga tun fil’azal iyayen ne ma basu bi hanyoyin isar da tarbiyyar yanda ya kamata ba saboda soyayyar yaran. Wannan matsalar tana matuƙar tasiri akan addini da wasu ɗabi’un da takai a yanzu hatta ɗiyanmu mata na shaye-shayen abubuwan mayen nan a cikin gidajen iyayensu ko a gidan aure. Wasu sanadin abokai, wasu samari, wasu kuwa wani daliline kan jasu zuwa hakan. Karna jaka da nisa, ita matar tawa ta tsinta kanta a irin wannan halinne, sannan ba shaye-shaye ne kawai matsalar ba, hatta a ɓangaren ibada tana da matuƙar raunin da zan iya cemaka komai ma bata sani ba, saboda koda tasan wani to babban dalilai ya shafesu da ɓoye abinda ta sani ɗin. Kaina gaba ɗaya a cikinkushe yake yinin yau ka bani shawara dan ALLAH, dan ko mahaifana bana son su fuskanci wannan matsalar game da ita balle sauran ahalina saboda bana son mutuncinta ya samu rauni ko yaya a zukatansu”.

        Numfashi mai nauyi Malam ya sauke yana mai jinjina kansa. “Tabbas kai ɗan halak ne Aliyu, sannan ka matuƙar birgeni na kuma sake ganin kimarka a cikin idanuna. Domin ba kowa ALLAH ke azurtawa da irin zuciyarka ba a wannan ƙarnin. A koda yaushe, a ko wane irin kuskure mutanenmu sukan dubi mai wannan akin abin ƙyama, abin hantara, abin gudu, abin zinɗe, abin shune, a tunaninsu suma wayonsu ne ya hanesu da aikatawar ko ya hani nasu zuri’ar. Muna mantawa itafa rayuwar tamu gaba ɗayanta ma jarabawace, ba kuma lallai ne abinda ya kasance jarabawar waninka kai ya kasance taka ba. A duk sanda kaga gazawa ga wanin ka ba dandalin gulmarsa ya dace ka buɗe ba, da zunɗensa ko shunensa ya dace kayi ba idan zai gifta, ba ƙyamatarsa ya dace kayi ba ko hantara. Nema masa shiriyar UBANGIJI ya cancanta da tausasa masa a duk lokacin da rayuwarsa ta raɓi taka ko wani dalili. Wlhy Aliyu mutane da yawa sukan kasa gane cewar bakunansu ko ayyukansu ke jefa musu ƴaƴa cikin wata musifar. Zakaga kana iya bakin ƙoƙarin ka akan tarbiyyar yaranka, ALLAH kuma ya baka su nutsatstsu da ilimi yanda ya kamata, amma dare ɗaya yaro ya canja alƙiblarsa ka rasa daga ina matsalar take. Matsalar tana a tare da kai, bakinka shine matsalarka, ayyukanka sune matsalarka. Ɗan wancan dake famɗare ya gitta ka zunɗeshi da bama abokan zamanka labarin ai wancan yaron da kuke gani gagararrene, watsatstsene fanɗararre, baida aiki sai shaye-shaye, baida aiki sai bin ɗiyan mutane, baida aiki sai ɗauke-ɗauke. Ciki ta zubar babu adadi bar ganinta a cikin hijjab ɗin can karuwar gida ce, jibi yarinyar can babu abinda ta iya sai shigar banza, ta kwaile fata da bilicin ƴar isaka tafi ƙarfin iyayenta. Laifin uwarne ko ubanne basu bashi ko bata tarbiyya ba….. Waya gaya maka tsaiwarka akan tarbiyyar yaro ce kawai ke tsare maka shi ɗan uwana ko ƴar uwata? Muna mantawa akwai jarabawa, muna mantawa akwai ƙaddara, muna mantawa ƙyaƙyƙyawan furucinmu ga ɗiyan wasu kanyi tasiri ga namu ɗiyan, mummuna kanyi tasiri ga namu ɗiyan suma. A duk fa lokacin da ka ambaci ALLAH yayima wane albarka, ya shiryar da shi, sai kaima mala’iku suce Amin tare da kai da zuri’arka baki ɗaya. Idan kace ALLAH ya wadaran wane fanɗararre taƙadari ɗan iska, sai mala’iku su amsa da Amin tare da kai da zuri’arka baki ɗaya. To ashema yima wani ƙyaƙyƙyawar addu’a ko furuci tamkar kanka kayimawa kenan ko, shiyyasa nace maka harsunanmu sune manyan linzaman da suka zame mana masifu a wannan zamanin bakwai tarbiyyar bace kawai ta suɓuce mana. Da an taɓamu muce zamani, babu babban zamani sama da harsunanmu. Iyayenmu na baya da wahala kaga majalisar aibanta ɗiyan mutane, da wahala kaga wani ya zauna zinɗen yara marasa ji, idan yaga yaro yayi ba daidaiba zai hukuntashi batare da sanin iyayensa ba koya tsawatar masa ko ya masa nasiha. Amma a wannan ƙarnin sai dai mu koma gefe muna dariya ko yin ALLAH wadarai akan abinda munada damar gyarawa ko ambaton shiriyar ALLAH wa wannan yaron kuma tai tasiri garesa. Wani kuma zakaga a gefe sana’arsa itace saida kayan laifi ko wani mummunan abu dake ɓata tarbiyyar yara, shiyyasa sai UBANGIJI ya dawo da mummunan aikinsa wa zuri’ar tasa danta zame masa izina idan zai gane. Abinda kayi na yarda da auren yarinyar nan da ƙudurta gyara mata rayuwa batare da ƙyamata ba da ace haka muka dageyi a cikin al’ummar mu da an samu sauƙin yawaitar lalacewar yaranmu matuƙa. Domin duk wanda ya taimaki wani domin tsamosa daga wata halakar rayuwar duniya data lahira, shima UBANGIJI zai tsamesa da ga wasu masifu ya kuma tsame zuri’arsa ta inda bai zato ko tsammani ba. ALLAH yay maka albarka, ya ƙara mana yawaitar irinku acikin al’ummar mu. Dan irin waɗan nan yaran jawosu a jiki da haƙuri da yanayinsu ya dace muyi mu kuma maida hankali wajen fuskantar minene matsalolinsu. Kaifa abinda kake kallo ba dalili ba, wani a wajensa gagarumin dalilaine da zai iya tarwatsa masa rayuwa. In sha ALLAHU zakai nasara, wataran ba al’umma ba kai kanka sai kayi alfahari da jihadin da kayi da kuma kasancewarta iyalinka. Abu na farko da zakayi shine janta a jiki, karka ƙyamaci halin da take ciki, ka fuskanceta da ƙyau wajen gano minene ainahin abinda ya jefa rayuwarta a wannan yanayin dan na tabbata tanada ƙyawawan halaye itama da fuskantar ta ne zai bayyanar da su, sannan ka dage da addu’a, yin sadaka da ƙyautata mata, ka fuskanci abinda tafi so ka dinga jan ra’ayinta ga shi. Sai kuma ka ɗan dinga yin zafi kaɗan a wasu al’amuran dan irinsu zaka samesu da taurin zuciya da ƙin gane al’amura da wuri, dole idan ka hura wataran sai ka tauna, dan sai ka ɗauki matsayin miji ne wataran, wataran uba, wataran yaya, wataran abokin, wataran ƙani, wataran ma ɗa, haka zaka dinga canja mata kamar hawainiya dan yanda mata kance maza kamar yarane yanda ka renesu haka suke kasancewa, itama mace kamar gold ce, idan ka iya zama da ita ta yanda kaso kake sarrafata da adon da kake buƙata a idon duk wanda zai kalleta. Na ƙarshe shine haƙuri, dole sai kayi matuƙar haƙuri da zama mai juriya, dan wani lokacin zakaga kana tufkane kamar tana warwarewa, kada ka damu sai a hankali ɗabi’ar zata barta dan ta riga ta shigeta sosai ta yanda wannan abunne kawai ke sakata farin ciki da ƙarfafa ta saboda shi take kallo a matsayin dai-dai tunda a haka ta tashi taga kanta. Dolene kasa ido sosai a dukkan motsinta, ma’ana ka zama mai ankarewa akan ƙawayenta da abokan huɗɗarta danka janyeta daga irinta a cikinsu. Sannan fa saika shirya kawo mata wani abu mai ƙyau da idan kana yaƙin rabata da wancan ya zam kana cusa mata wannan, kasan kuskuren da mutanenmu keyi shine, kaita yaƙin cirema mutum halayen gurɓatattu amma baka bashi madadin abinda zai maye gurbinsa da shi ba, tayaya kake tunanin bazai koma ruwa ba. Sai kuma fahimtar da ita addininta, shine babban abinda zai iya tankwara maka ita cikin sauƙi ma fiye da komai. ALLAH yay riƙo da hannayenka kai da ire-iren ka game da irin wannan sadaukarwar. ALLAH ya sakakanka muku da sakamakon alkairi ku da zuri’arku a duniya da lahira da duk ma wanda zai iya koda tausasa harshene akan kuskuren wani.”

        “Amin malam nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara tsahon rai mai albarka. In sha ALLAH zanyi aiki da shawarar ka dan naji daɗinsu na kuma sake samun hasken da nake buƙata.”

       Murmushi malam ya sake yi yana tattaro littatafai daga cikin tarin wanda ke a ɗakin nasa. Sai da ya kammala ya juyi ga Smart. “Ga waɗan nan kaje da su ka fara koyar da ita, ina dai fatan kanada karatu mai zurfi game da addininka?”.

           “Alhmdllh akwai gwargwadon iko, a yanzu haka ma kuma ban daina nan ilimi ba ina zuwa islamiyya Sheikh Aliyu Abdur-ra’uff Maina (MUTUM DA DUNIYARSA) kafin abubuwa su taɓarɓare ne na dakata gaskiya, amma in sha ALLAH ina kan shirye-shiryen komawa na cigaba”.

      “Masha ALLAH kayi ƙyan kai kuwa, Ai Sheikh Aliyu Maina mutumin kirki kuma aminina ne sosai, kaga idan kunyi nisa ka fahimci ta fara tankwaruwa zaka iya sakata Islamiyyar da matansa ke jagoranta suma Malam Jiddah da Malam Maimunatu”.

          “In sha ALLAHU zanyi hakan malam”.

     Sun ɗan ƙara tattaunawa sannan Smart yay masa sallama ya fito saboda su Ahmad dake jiransa. Ya samu sunata hirarsu da ɗaliban malam, amma duk da haka saida ya basu haƙuri sannan suka wuce yana jin zuciyarsa sakayau ba kamar daren jiya zuwa safiyar yau da yake cikin damuwa ba akan lamarin Lulu. Sai kusan shida suka iso Sharaɗa, Smart ya fita ya buɗe musu gate suka shiga har ciki. Suna sauke kayanta da suka taho da shi ya zare jikinsa ya shiga ciki dan fara duba yanayin shigarta kafin su Ahmad ɗin su shiga……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣7️⃣

…….Da sallama ya shiga falon, tana kwance a 3sitter idanunta a lumshe tamkar mai barci, sanye take da doguwar riga mara nauyi milk color data bi jikinta ta fidda ainahin surarta, sai dai bawai ta matseta bane ba, kanta babu ɗan kwali sai gashin data ɗaure a tsakkiya. Buɗe ƙofar da jin shiru kuma ya sata jiyowa tana buɗe luluu idanunta a kansa. Numfashi ya sauke a hankali da ɗan janye idanunsa batare da yace mata komai ba ya wuce ta, itama baki ta taɓe tare da maida idanunta ta lumshe. Minti kamar biyu sai gashi ya dawo riƙe da Hijjab a hannu, cikin motsa lips ɗinsa kaɗan kamar bayaso ya furta, “Ina tare da su Ahmad tashi kisa hijjab”.

        Idanunta ta buɗe fuskarta a tsuke matuƙa da damuwar kaɗaicin da take ciki ita kaɗai a gida ba waya ba wani abin ɗebe kewa dan ba’a haɗa musu ba, kamar zata ɗauke kai sai kuma ta sake yamutse fuska cikin izzar nan tata ta furta, “Dan kawai kana tare da wasu sai na kama saka hijjab. Wai mi kake nufi da ni ne? Ko dan kaga na saka a waccan ranar kake tunanin cigaba da jin kanka sama can”.

         “Mawaddat Umarni ne tashi ki saka hijjab ko nayi abinda bazai mana daɗi ba mu duka”. Ya faɗa shima cikin deep voice ɗinsa da dakewa yana tsatstsareta da idanun da take kira na macizai babu alamar wasa tattare da shi. Kanta ta ɗauke gefe a gatsine ta ce, “To yi ɗin mana”.

  “Okay haka kikafi buƙata?”. Ya faɗa shima a dakensa yana ƙoƙarin kai hannu kanta. Tashi tai zaune tana watsa masa harara, dan babu abinda yazo a zuciyarta sai abinda ya faru tsakaninsu ɗazun, ita kuma abinda bazata iya ɗaukaba kenan taɓa mata jiki balle har yay tunanin sake maimaita abinda yay matan.

        “Au ashe tsiwar taki iya baki ne? Da ki ƙi tashi ɗin mana kiga yanda zan tabbatar miki kan nawa a saman yake.” ya ƙarasa maganar yana jefa mata hijjab ɗin a jikinta ya juya ya fice. Wani irin kallon takaici ya riƙe maka maƙoshin nan ta bisa da shi, a zuciyarta tana ayyana (Mi wannan mutumin ke nufi da ni ne wai shin? Ƙoƙarin takani ko mi? Yimin gadara da nuna zafin kai ko mi? Humm aiko gidan ya tarar in dai nice, zan bashi mamaki a gidan nan mu zuba) ta yunƙura da nufin barin falon batare da saka hijjab ɗin ba. Sai dai tana miƙewar su Ahmad nayin sallama, ƙofar ta zubama ido kawai tama rasa miya kamata tayi har Smart ya shigo a farko, ja yay ya tsaya murmushin fuskarsa na ɓacewa ɓat, sai kuma ya rumtse ido da masifar ƙarfi zuciyarsa na dokawa da sauri-sauri, dan da gaske fa yanada kishi mai zafi, bai fahimci hakan ba kuwa sai a yanzu ɗin nan dan idanunsa har ji yake suna masa wani yaji-yaji. Koda ya buɗesu a kanta ita kanta sai da taji razani ya shigeta, dan cikin ƙanƙanin lokaci sun yi wani irin kaɗawa da canja launi, baice komai ba ya tako inda taken tsaye ya duƙa ya ɗauka hijjab ɗin ya warware ya saka mata. Su dai su Ahmad da sun riga da sun shigo basarwa sukayi, sai kuma ita Lulu a wautarta ganin ran Smart ya ɓaci sai tai niyyar sake ƙular da shi. Sai da ta saci kallonsa ta gefen ido sannan ta juya gasu Ahmad tana sakin wani sassanyan murmushi da faɗin, “Sannunku da zuwa, ni ai da har zan fara fushi”. Ahmad bai kawo komai a ransa ba tunda dama sun san juna da jimawa sai dai bawani mu’amala ke tsakaninsu ba mai ƙarfi dan Lulu fa ita da maza zira’i maitan ne. Shima murmushi yayi yana kaiwa zaune da faɗin, “Yauwa amarya. Ya kuke ya gajiyar biki? Duk da dai naga angon naki shi tun ɗazun”. Sai da ta sake satar kallon Smart ta ga yanda yay kicin-kicin da fuska ya kuma ƙi zama sai ta sake sakin murmushin da bama Ahmad amsa da “Gajiya kam tabi jiki, kuma ya taku gajiyar? Ya su Uncle Hameed”.

        “Alhmdllh, Yaya kuma shima lafiya ƙalau yake”.

      Kanta kawai ta jinjina, ta juya ga Faisal shima ta gaishesa sannan ta nufi kitchen tana dariya a ƙasan ranta. Ruwa da lemo ta ɗibo da kayan cin-cin, babu jimawa sai gata ta dawo ta ajiye gabansu. Yanzu kam Smart ya zauna, sai dai kansa a duƙe yana latsa waya. Komawa tai ta zauna itama tana ɗan murmushin santin da su Ahmad keyi na dubulan. Shi dai gogan kamar ruwa ya cinyesa a falon. Sai da ƙyar yay controlling kansa kodan Faisal dan ta Ahmad mai sauƙi ne zai iya fahimtarsa. Sai dai murmushin Lulu sukar masa zuciya yake kishi na sake riƙe masa maƙoshi.  Haka dai ya danne har suka miƙe, kayayyakinta suka shigo mata da su sannan sukai mata sallama ita kuma ta basu kayan garar data juye musu a leda kowa da nasa ta ƙaro ma sannan ta zuba wanda za’a kaima Aunty Khadijah matar Abdull-Hameed (Coach) dan suna ɗasawa sosai itama kasancewar akwai ƙawance mai ƙarfi tsakaninta da Aunty Saliha. Suna fita ta koma ta zauna tana dariyar jin daɗin ƙular da Smart da tayi. Jinta take rai fess ita kam. A haka ya dawo ya sameta. Zama kawai yay baice mata komai ba dan a yanzu idan har yay magana ɓacin ransa ne zai bayyana a fili, dan haka yafi zaɓar zama shiru har zuciyarsa ta ɗan sassauta masa sannan ya tura mata ledar da wayoyinta ke ciki ya miƙe yabar wajen. Nanma da kallo ta bisa cikin taɓe baki kafin taja ledar ta buɗe. Sosai taji farin cikin ganin wayoyinta da laptop, cike da jin daɗi ta ɗauka tai bedroom domin saka caji dan duk sun mutu ba caji. Ga cajojin duk suna hanunta…..

       Kiran sallar magrib ya fiddosa a ɗakinsa, ya ɗan zubama kayan da su Ahmad suka shigo da shi ido dan suna nan a inda suka ajiye, iska ya furzar batare da yace komai ba ya kwashe su ya fara shiga da su bedroom ɗin nata. Zaune take da laptop data jona a caji gabanta, tun ɗagowar farko da tai suka haɗa ido ta maida bata sake ɗagowa ba har ya kammala shigowa da kayan. Babu alamar wasa tattare da shi ya ce, “Bakiji an kira salla bane?”.

       Tsayawa tai da ga danna laptop ɗin sai dai bata ɗago ta kallesa ba. Amma ta tsuke fuska alamar jira take yace kule tace cass. Takowa yay gabanta a hankali ya rufe laptop ɗin ya tura gefe. Dole ta ɗago yanzun kam ta dubesa da iyakar duk wani ƙarfi dan nuna masa yana shiga mata hanci fa. Kallon tsakkiyar ido sukema juna kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, dan ta gagara faɗar abinda tai niyyar da farko. Ita ta fara janyewa cikin taɓe baki. Sai kuma ta miƙe batare data tanka masa ba ta nufi toilet. Bayanta yabi dan yanzun ma yana son tai al’ala a gabansa kamar ɗazun, kasancewar shi yana da ita sai ya tsaya yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ganin tayi kamar yanda ya nuna matan ɗazun, sai yaji kuma nauyin da zuciyarsa yayi ya ragu, dan har cikin ransa yaji ta burgesa, in dai har haka take da saurin fahimta da ɗaukar abu komai zai zo da sauƙi kenan, kafin dai tayin ne yake ganin zasu dinga kai ruwa rana.

       A karan farko ya ja musu jam’i yau, abi mafi sakata sake nutsuwa a wannan jam’i yanda Smart ke raira karatun Alkur’ani a nutse da fitar sauti nagartacce. Bayan sun idar cikin fuskewa tai yunƙurin miƙewa domin bar masa wajen amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo mata hannu. Hannun ta kalla sannan ta ɗago fararen idanunta ta zuba masa. Shima ɗin dai ita yake kallo dan haka suka zubama juna ido kowanne najin idon ɗan uwansa na ratsashi har tsakkiyar ruhinsa. Da ƙyar Smart ya iya aro jarumta da ga cikin ɗunbin ƙwarin gwiwar sa cikin fitar sauti ƙasa-ƙasa ya furta, “Inada kishi! Inada kishi mai zafi! Inada kishi mai tsanani Mawaddat. Wannan gaskiya ce da nake gaya miki ita danki haddace a cikin muhimman abubuwanki ki kuma kiyaye saboda gudun randa zaki iya tabbatar da ainahina akan wannan kalmar. Komai zan iya ɗauka, idan nace komai ina nufin komai amma banda kasa riƙe kanki ko killace kanki ga wanina koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya suka haifemu da shi. Ki cigaba da sanin *_SMART_* kawai, idan kika ce *_ALIYU HYDAR_* ki ke son gani a zahirance, to fa tabbas wasan zai iya canjawa da ga duk yanda kike iya tunanin ko kwallonsa a tsarin zuciyarki. Duk abinda kikaji nace bana so to da gaske bana sonsa, idan kuma bana son abu bana iya dogon kawaici a kansa game da ɗaukar hukunci mai tsauri. Idan har kina son cigaba da gudanar da duk abinda kika fara da ga gidanku cikin salama to ki kiyaye….”

        Rikitaccen abinda ta hango a tsakkiyar idanunsa mai kama da guguwar hayaƙin turnuƙun yaƙi ya sata kasa iya maida murtani. Ba wai ta fahimci ainahin curarrun kalamansa bane ba a yanda shi yake son ta fahimta ɗin, a salon da yay maganar ne kawai ke son tilasta fassara mata su. Ba’a komai take garaje ba musamman maida murtani, dan haka ta shanye kamar komai bai mata zafi ba dan tana buƙatar fashin baƙi kafin ta maida raddi, dan haka kanta tsaye batare data janye idanunta da ga cikin nasa ba duk da hakan na cutar da ita ta ce, “Ka gama?”…….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣8️⃣

……Ba ita kaɗai ba, hatta shi ma kallon da sukema junan na ƙarshen ƙwal uwar daka na matuƙar zafafa masa garkuwar jiki, amma ya zaɓi nuna jarumtar nan da duk aka san Aliyu Zakin fama da ita ta taurin zuciya da tsaurin shanyewa ya ƙi janyewa. “Gamawata na nufin karɓar umarni na, saɓanin hakan kuma.. hummmm!” yaƙi ƙarasawa sai danne lips ɗinsa da yay da haƙori cikin tabbatar da gargaɗi. Itama saita danne natan da salon muzuba mu gani tana mai ɗaura ɗayan hanunta saman nasa da ke akan natan ta turesa masa. Komai baice mata ba, sai lumshe idanun nasa yay kawai. Saman gadon ta koma ta zauna tare da ɗaukar laptop ɗinta ta cigaba da abinda take yi batare data sake ko satar kallon inda yake ba. Sai dai zuciyarta taƙi samun nutsuwa dan kalamansa ne ke faman mata kai da kawo. Ba wannan ne karo na farko daya mata irin waɗan nan kalaman a cirkuɗe ba, na baya ma kuma sun cimata rai da zafafa ta harta ƙagautu da son jin fasararsu, amma na yau sai batajin suna mata raɗaɗi ƙagautuwar ce kawai ke zaburar da zuciyarta akan hasashen mai iya fassara mata su. Karan farko da taji tana ɗan kewar Nadiya, amma kuma hakan bazai sa tai kiranta ba. Duk da kuwa ta turo mata tarin sakwanni na ban haƙuri amma tai biris, hatta taron bikin nan Nadiya tata roƙon son zuwa, anan ne ta mata reply da cewar (ba’a buƙatar ki) da ga haka kuma bata sake bi takanta ba. Su Afrah kam bata ganin sunada hankalin da zata iya sakasu a sabgarta. (Mubeen ko su Hussain) zuciyarta ta ayyana mata. Mubeen ai ƙaninta ne, ita kuma bata son raini gara ma su twins ɗin, gamsuwa da hakan ya sata ɗaukar wayarta ta shiga WhatsApp, abinda bai dameta ba sai abu mai muhimmanci ya taso mata. Dubawa tai dan ganin wanene online, sai taci sa’ar ganin Hassan dan haka tai masa sallama sannan ta rubuta masa kalaman da Smart ya faɗa mata, (dan Lulu fa irin mutanen nan ne masu ƙwanya matuƙa, tanada saurin ɗaukar abu da haddacesa, ko’a makaranta ƙuruwace ta gaske da kaifin brain yasa zama popular ga malamai da ɗalibai, dan ma abubuwa da yawa sun faru da suka so taɓa mata karatun musamman ma harkar shaye-shaye ALLAH dai ne ya ƙaddara da rabon zata haye da amsa suna lawyer a yanzun). Sai dai anyi rashin sa’a tana turawa Hassan na komawa upline, sai kawai ta ajiye wayar da tunanin bari ta bashi mintuna tasan zai dawo, idan ma bai dawo ba zatai kiransa. Ta cigaba da aikinta sama-sama har akai kiran isha’i, har lokacin kuma Smart na’a ɗakin yana karatu ne shiyyasa shima hankalinsa ba’a kanta yake ba har sai da akai kiran sallar sannan. Yanzu ma koda yace tazo suyi jam’i bata musa masa ba, bayan sun idar ne ya dakatar da ita daga yunƙurin tashi ta hanyar tura mata littatafan da malam Nasirudden ya bashi. Littatafan ta zubama idanu, kafin ta ɗago ta kallesa fuska a tsuke.

       Kafin ma tace komai ya bata amsa da “Naki ne, zamu fara karatu sai ki shirya. Dan ya kamata kisan addininki. Hakan ne zai sake tabbatar miki da ke wacece, ki kuma san yanda zaki bautaba UBANGIJI, ki yima mahaifiyarki da ƙasa ta rufema idanu addu’a, ta haka ne kawai zatai alfahari da ke dajin farin cikin barin baya da tayi, zaki san yanda zaki roƙa UBANGIJI da miƙa masa kukanki akan bukatunki ya amsa miki”.

      Yana gama faɗa ya miƙe batare da jiran cewarta ba. Tayi niyyar maida raddi akan maganar farko, sai dai ta ƙarshe tai mata takunkumi da hakan, tana son mahaifiyarta matuƙa, tana tsananin begenta kuma. Duk abinda zaka jingina mata da ita yana saurin sanyayata koda batai niyya ba tayi, balle ma ita in dai akan neman abinda duk za’ace ilimi ne da zai amfaneta bataga dalilin dazai hanata amsa ba, a ganinta hakan ribarta ce, ta ƙara koyon abinda bata sani ba….

       *_WASHE GARI_* kamar jiya kowa a ɗakinsa ya kwana, garama shi yaɗan leƙata kusan ƙarfe uku na dare daya idar da sallar daya tashi yayi. Samun ɗakin a buɗe ya bashi damar shiga, sai ya sameta tana barcinta a cikin lallausan duvet ɗin gadon, ta rage hasken tabar mai pink. Wayoyinta ya ɗiba duka biyu ya fita da su, kusan akansu ya ƙarasa daren sai gabannin asuba ya kwanta, ana kiran salla kuma ya tashi. Yau ma ya tadata yin sallar, sai dai yana fita ta koma tai kwanciyarta har sai da ya dawo yay mata jan ido sannan ta tashi. A lokacinne ya ajiye mata wayoyinta ya koma can ɗakin ya kwanta sai barci…..

         Kusan takwas da wasu mintuna ta kammala shirinta tsaf, tayi matuƙar ƙyau cikin skert da riga na atamfa da suka fiddata tsaf, kamar kullum babu kwalliya, ɗan kwali ma bata ɗaura ba dan bata iya zaman wahalar ɗaure-ɗauren nan dama a gida Afrah ke mata. Sosai ta baza ƙamshi aka toshe ido da glass bayan ta yana ƙaramin veil a kanta ta naɗesa a kafaɗunta. Dan ƙyau kam tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. Cikin takun nan nata na yanga da gayu ta fito ɗauke da tarkacenta, sai key ɗin motarta da aka kawota da ita kaɗaice a nan ɗin sauran ba’a kawo mata ba. Kanta tsaye ta doshi hanyar fita, sai dai me tana taɓa ƙofar ta jita a rufe. Ƙaramin tsaki taja da duban agogon dake a tsintsiyar hanunta. Sam bata son makara, dan haka ta nufi kitchen da nufi fita ta ƙofar baya, sai dai nan ɗin ma ɓam. Cikin ɗan jin takaici ta rumtse idonta da komawa falon, kayan hanunta ta zube a saman kujera ta nufi ɗakin Smart. Yana tsaka da barcinsa ya ji ana bubbuga masa gefen filon daya tada kai, da ƙyar ya buɗe idanunsa da ke jingim da nauyin barci ya sauke a kanta. Kauda natan tayi da ga kansa a gadarance ta ce, “Malam bani key zan wuce. Ka wani bi ka rurrufe ƙofofi kamar a prison”.

         Kallonta yake shi dai da ga sama har ƙasa har takai ƙarshen maganarta. Ƙoƙarin tashi yay zaune ya jingina da gadon ya harɗe hannayensa a ƙirji rabin ƙafafunsa zuwa ƙugu lulluɓe cikin bargo.”

       “Malam ka tsaya kana kallona kamar wata hoto, bayan kuma kaji na faɗa maka bana son na makara ko? Inada important abubuwa a office”.

       Wani ɗan jan idanunsa yay kamar zai lumshe sai dai kafin ya rufe ɗin ya sake buɗesu a kanta. Cikin yanayin muryar wanda barci bai isa ba da ɗan taɓe fuska ya ce, “Ban fahimceki ba, sake maimaitawa”.

     Kallon takaici ta watsa masa. Dan ta fara hasala. Amma sai ta danne da ƙyar a ɗan zafafen dai ta ce, “Wai kai miyasa komai a wajenka abin wasa ne. Kasan ko mi kake yi? Ka bani key ni ba neman jidali nake ba”.

           “Humm ke idan ance miki ki fita a yau a kuma haka yanda kiken nan sai ki fitan?”.

       Harara ta watsa masa cikin gatsali da faɗin, “Sai ka hanani fitar idan na tashi”.

      “Okay haka kika ce? To ko zan tabbatar miki ko ƙofar gate bazaki fita ba, idan kema kin shiga duniyar mafarkinne sai ki farka, dan idan har kinga kin fita a gidan nan da sunan aiki sai next week ma. Sannan bada wannan shigar ba idan har kina son aikin naki kenan. Dan bazan hanaki yi ba saboda wasu dalilai na, amma ba’a yanda ranki ya raya miki ba. Yanzu a ƙarƙashin ikon Aliyu Mika’il Idris Mawashi kike ba su Daddy ba. Abinda ya tsara a gidansa dole shi za’ayi ko ana so ko ba’a so. Garama ki nufi kitchen haɗa mana break fast”. Da ga haka ya juya yay kwanciyarsa. Wani irin ƙarajin kiran sunansa ta ƙwala a matuƙar zafafe. Sai kawai yaja filo ya ɗaurama kansa ya toshe kunnuwansa ma ya maida idanunsa ya lumshe. Masifa ta fara zazzaga masa zuciyarta na raɗaɗi kamar zata fito ta baki, amma bawan ALLAHn nan yay biris da ita, da ya ga ma filon bazai masa ba sai ya ɗauki bluetooth ɗin sa da ke a bed side drawer ya manna a kunne ya saka ƙira’a abinsa. Fita tayi a ɗakin dan ta fahimci sai ta haɗashi da Daddy. Wayarta ta cira a handbag ta shiga dannama Daddy kira. Bugu biyu kuwa ya ɗaga dan fitowarsa a wanka kenan shima zai yi shirin office. Kafin ma yace wani abu ta sakar masa kuka da faɗin, “Daddy kaga mutumin nan ko? ALLAH ina raga masa ne saboda abinda Baba da Uncle You suka cemin, amma idan ya ce muyi ta inda ya ɓullo zan hargitsa masa rayuwa, nifa babu lallai babu dole zan dawo gida Daddy, garama komi Baban zaiyi yayi….”

       Duk da abinda Daddy keji na yunƙuro masa shima sai ya danne da ƙyar, cikin tausasa harshe ya ce, “Baby kinga relax mi yake faruwa? Mi yay miki?”.

      “Daddy Office fa zanje yabi ya kulle ƙofofin, naje ya bani key amma yay min banza yama saka bluetooth a kunne wai babu inda zanje sai next week, irin like kamar wata baiwarsa da ya saya a kasuwar bayi”.

    Ƙololuwar ɓaci ran Daddy ya kai, a taƙaice ya ce “Ina zuwa”. Ya yanke kiran, number Smart ya lalubo a karo na farko ya danna masa kira. Kasancewar bluetooth a kunnensa ya sashi jin shigowar kiran a bazata, hannu ya kai ya zare guda ɗaya yana kai hannu kan wayar tasa ya ɗauka dan ganin wanene mai kiransa haka. Bai san number ɗin ba, dan baida Number Daddy, kamar zai share sai kuma dai ya ɗaga gudun kar yay mistake.

       “To sannu isashshe”.

Kalmar data fara dukan kunnensa kenan a maimakon sallama………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣9️⃣

……..Cikin sa’a kuma ya gane muryar Daddy. Amma sai ya danne bai nuna ba, cikin dai nutsuwarsa ya ce, “Assalamu alaikum”.

    “Da sallamar nake da buƙata da ita zan maka ai. Miye dalilinka na hana Mawaddat fita office ka kuma kulleta?”.

          Shiru Smart yayi kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya furzar da numfashi kaɗan yana gyara kwanciyarsa. Sake tausasa muryarsa yay fiye da ɗazun ya ce, “Kayi haƙuri Daddy sallama wajibi ne ga musulmi, haka ma amsata ga wanda akaimawa. Kai ya kamata ka tunatar da ni hakan a matsayinka na mahaifi. Dan haka kayi haƙuri ka amsa min sallamata kafin muyi maganar da kake son. Assalamu’alaikum!”.

       A cinkushe Daddyn ya amsa masa, Smart ya ɗan girgiza kansa sannan ya tashi zaune sosai. Cikin sake tsantsan da kai na girmamawa ya ce, “Daddy ina kwana”. Bai amsa masa ba nan kam. Shima sai bai damuba ya ɗora da faɗin, “Zan sake baka haƙuri a karo na biyu Daddy, dan ALLAH karka saka baki a wannan zancen dan a yanzu Mawaddat tana ƙarƙashin na ne. Inada damar zartar mata da hukunci akan abinda ya dace da kuma banbance mata wanda bai dace ba. Kai mana fatan alkairi kawai shi mukafi buƙata da sanya albarkar ku, na riga na gama yanke hukunci akan hakan babu kuma tunanin canjawa a tattare dani amin afuwa. Na Barka lafiya”. Daga haka ya yanke wayar tare da kasheta gaba ɗaya ya koma yay kwanciyarsa ransa fal mamakin halin surukin nasa.

     Ƙaramin hauka ne ya kusan samun Daddy da ga can jin Smart ya yanke wayar bayan ya gama datsa masa zafafan magana kamar yanda zuciyarsa ta fassara masa. Ƙoƙarin sake kira yayi amma sai wayar switch up. Kaɗan ya rage ya maka wayar da ƙasa. Amma sai ya fasa ya maida akalar kiran kan Uncle Yousuf. Suna zaune shi da yara da akaima shirin makaranta suna breakfast kiran Daddyn ya samesa. Bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga, sai dai kiran sunansa da Daddy yay a tsawace ya sashi rumtse idonsa. Sai kuma ya miƙe yabar daining ɗin ya nufi bedroom ɗinsa. Cikin tausasawa ya ce, “Yaya lafiya dai kuwa?”.

       “Yousuf yanzun nan ka kira ɗan iskan yaron can ka faɗa masa ya sakar min yarinya tunda ba ubansa ya haifa min ita ba, har ni yake da bakin gayama Mawaddat ta koma ƙarƙashin ikonsa ya kuma yanke hukunci a kanta bazai canja ba kamar shine ya haifa min ita.”

      “Ya Salam. Yaya Please calm down dan ALLAH muyi magana mana. Wlhy sam ban fahimci mi kake son faɗa min ba. Mi Aliyun yay maka ne?”.

       “Miye ma bai mun ba, babu abinda ya manta na rashin kunya bai faɗa min ba. Shiyyasa tun farko na faɗa maka yaron nan ɗan zafin kai ne zai iya bamu matsa ta duk inda bamuyi zato ba. To gashi ya fara, ya kulle gida ya hanata fita aiki, ta masa magana ya ce sai next week babu inda zataje, ta kirani nai kiransa nai masa magana amma ya daddatsamin magana son ransa tsabar shi ya cika cikakken ɗan iska.”

         Girgiza kai Uncle Yousuf yayi, kafin ya ce, “Dan ALLAH kayi haƙuri ka kwantar da hankalinka, ka dai san mi ɓacin rai ke haifar maka a yanzu. Zan kira shi na masa magana sai naji dalilinsa. Sai dai ma yaya banda abunka ai bai kamata ka biye mata kai kiransa ba, karfa ka manta yau kwana biyu kawai da tarewarsu, ai bai dace ba ta fita aiki sai mutane suyi magana kadai san yanda al’amarin yake yanzu mutane sun bar damuwa da al’amarin su sun koma hango na wasu”.

          “Yousuf bana buƙatar jin komai, sannan ni babu ruwana da wasu mutane ko abinda zasu faɗa, farin cikin yarinyata kawai na sani. Shi wanene da zai tauyeta bayan da aikinta ya ganta, sannan waya faɗa masa shi ɗin har ma yanada wani ƙarfin iko a hannunsa a kanta da zaima mutane wani gadara koda ace auren nasu mai muhimmanci ne. Wannan shine na guda tun farko amma ka kasa fahimtata, shiyyasa kuma nace ayi komai a rubuce amma nan ma ka wani kakkaresa gashi nan tun kan aje ko ina ya fara nuna halinsa, a haka kwanakin da kace ɗin zai cika yay abinda ake so? an faɗa masa akan ƴata zai nuna gargajiyancinsa ne”.

       “Naji duk na ɗauka kayi haƙuri zanyi magana da shi yanzun.” daga haka Uncle Yousuf ya yanke wayar batare da ya jira cewar Daddy ɗin ba. Hannunsa ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya girgiza a hankali ya ɗago yana murmushi mai sanyi. A fili ya furta, “Yaya yaya kenan, kai da gaske jiran cikar lokacin kake kenan? Humm aiki ya sameka. Aliyun dama shine ai dai-dai da kai game da lamarin Mawaddat duka kai da itan. Ashe babu daɗi lokacin da ka dakatar da Aunty Kareema fita aiki a dalilin Marigayiya, duk da hakan ya mata ciwo kuma ta haƙura iyakarta kuka ta share hawayenta, ashe ita daga sama ta faɗo? Kai gashi hana fitar kwanaki kawai da akai ma taka ɗiyar ya zafafaka har haka. ALLAH na gode maka da ka kaini da rai da lafiyar ganin irin wannan ranar, shiyyasa akace yanzu ma tun a duniya ake fara hisabi basai an mutu ba. Muje zuwa yanzu aka fara wasan ai. Mai ƙarfi sai yaci kofin”. Ya ƙara sakin murmushi. Ƙoƙarin kiran Smart yayi sai ya samu wayar switch up. Ya sake sakin murmushi da faɗin, “Kaga mazan ƙwarai”. Da ga haka ya miƙe ya fito abinsa. Ya samu yara har sun wuce, sai Aunty Saliha da ke zaune tana tsumayen fitowarsa dan ya sakata a ruɗani.

        “Abban Ra’is lafiya dai ko?”.

    Ajiyar zuciya ya saki yana kaiwa zaune, ta turo masa kunun data sake zuba masa dan wanda ya bari ya huce. Sai da yasha kusan sau uku sannan ya dubeta. “Yaushe zakuje gidan Mawaddat ɗinne?”.

       “Sai zuwa anjima kaɗan dan muje mu dawo da wuri ko”.

     “Inaga ku kuyi zamanku, su Hussain suje sukai mata, motocin ta kuma a barsu ba yanzu ba.”

          “Amma wani abu ya faru ne?”.

      “Zai dai faru Saliha…….” nan ya zayyane mata komai daya faru. Cikin damuwa ta ce, “Amma Yaya da bai kirashi ba ai. Dan Aliyun ya fishi gaskiya, yaza’ai amaryar da aka kai gidan miji shekaran jiya kuma a ganta a office yau dole zai iya zama abin magana. Inda waɗan nan ƙananun matsalolin zai dinga sawa iyaye na neman sakin ƴaƴansu ai da kowama ya zama babu aure kenan. Ni sai nake ganin kamar maganar Aunty Kareema zata iya zama gaskiya….”

        “Hummm ku mata kullum tunaninku iri ɗaya ne, miyasa komai a rayuwa idan yazo mana a yanayin da ba haka muke tunanin ganinsa ba sai mu dinga ɗaukarsa asiri. Nasan asiri yana ɗaya daga cikin abinda al’ummar mu suke kallon babbar mafita ga al’amuransu a halin yanzu, sai dai bai kamata muna tsuke dukkanin zukatanmu waje guda ba akan kowanne bigire muyi masa kallon asirin. Amma dai bari nai miki wata tambaya, shin ku minene dalilinku na kallon al’amarin Yaya matsayin asiri?”.

        Duk da maganganunsa na farko sun shigeta sai bata gaza wajen faɗa masa hujjojin da suke kallonba su. Ta ce, “Na yarda da zancenka nima, sai dai ka kalla wani abu Abban Ra’is. Kafin auren marigayiya kai da kanka ka bani labarin ba haka Yaya yake ba sam, sannan Yaya nada ilimin addini mai zurfi da yasan minene aure da ƙaddara. Amma kaga yanda idanunsa suke rufewa ta yanda idan wani aka faɗamawa da bai gani ba zai iya ma ƙaryatawa. Dolene muyi tunanin akwai sammu tattare da shi”.

          Murmushi yay da cewa “Hummm! Saliha kenan. Duk ilimin mutum bakwa tunanin son zuciya zai iya sakashi ajiye ilimin gefe ya aikata abinda baida alaƙa dana masu ilimin. A al’amarin Yaya babu wani asiri, akwai ɓoyayyen al’amarin da yake ɓoyewa dai tun kafin auren Mawaddat ɗin, sai da ya auretanne ya fara fitowa, wanda tamkar ALLAH ya jarabcesa da sanya masa tsoron faruwar irinsa akan Mawaddat ne, ba komai ya kawo hakan ba kuma sai dan itace mafi soyuwa a ransa ko kuma ana masa barazana da ita, shiyyasa ma tun farko ya gagara yarda da kowa game da kula da al’amarin ta, a tunaninsa shi zai iya kareta akan komai, sai kuma akai rashin sa’a ƙaddarorinta ba’a fatar jiki suke ba ko mahallin zamanta balle yay tunanin kuɓutar da ita a yanda yaso da kuma ƙarfinsa da wayonsa. Dan haka kuma bar damuwa da al’amarin sa ana gab da zuwa gaɓar da zai fallasa kansa da kansa batare da ya sani ba. Yanzu Mawaddat itace mafi ƙololuwar abar tausayi, dan ina matuƙar jin tausayin rayuwar yarinyar a dalilin halin data tsinta kanta a ciki.”

      Yanda ya ƙare maganar cikin matuƙar damuwa da ɓacin rai yasa Aunty Saliha tasowa ta dawo kusa da shi tare da dafa kafaɗarsa. “Kayi haƙuri Abban Ra’is, tabbas tausayin Mawaddat dolene ga duk wanda ya fahimci muhimmancin rayuwa. Sai dai namu addu’a ce a yanzu tsakaninmu da ita, mu kuma cigaba da bama Aliyu goyon baya akan abinda ya fara, dan a yau na sake gamsuwa da fahimtar hikimarka ta haɗa wannan auren. Inaga kuma lokaci yayi da shima zaka fara aiwatar da shirinka na taimakonsa da tun farko shine dalilin jawosa jikinka da kayi, dan namiji bazai yiwu ya rayu babu abinyi ba yakan ja masa ƙasƙanci tsakaninsa da mace, musamman irin Mawaddat da tunda ta tashi bata san minene babu ba”.

          “Hakane kam, insha ALLAHU kuma a yanzu haka ina kan shirye-shirye ni da Hameed, dan kin san al’amarin nasa sai anbi ta bayan fage yazo a bazata tamkar yanda maganar auren nan tazo a bazata. Dan bayyanawa na nuna zaburar da mai ƙullin ne”.

      “Tabbas hakane, ALLAH ya bada nasara yasa shima iyakar wahalar tasa ce tazo. Ku kuma da kuke ƙoƙarin ALLAH ya saka muku da alkairi ya hana bayanku kuka”.

     “Amin ya rabbi. Bara na kirata idan naga da yiwuwar kuje ɗin to”.

    “To ba damuwa”………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣0️⃣

…….Zaune take a falo dafe da kanta dake matuƙar sara mata saboda ɓacin rai, a yanda take jinta zata iya aikata komai akan mutumin nan, amma ta zauna tsumayen kiran Daddy ne da yace ta dakacesa, sai dai an shafe kusan mintuna ashirin kenan shiru, hannunta ta janye tare da kallon wayarta da idanunta da sukai wani irin jazur. Wayar ta ɗauke da tunanin sake kiran Daddy ɗin kiran Uncle Yousuf ya shigo mata. Wayar ta tsaya tana kallo kawai, sai da ta kusa tsinkewa ta iya ɗagawa ta kai kunne, sai dai tayi shiru dan in har tai magana kuka ma zai iya ƙwace mata. Ƙaramin murmushi Uncle Yousuf yay da ga can da bazata iya jiyo sautinsa ba, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “My Daughter yau babu gaisuwa ne?”.

        Nan ma shiru ta kasa magana. Tofa yasan an kai ƙololuwar ɓacin rai kenan, dan haka ya sake tausasa harshe cikin komawa serious ya ce, “Mawaddat miya faru? Ko baki da lafiya ne?”.

             Hawayen da take riƙewa ne tun ɗazun suka kufce mata, da rawar murya irin ta mai kuka ta ce, “Papa bazan iya ba, bana son damuwa gida zan dawo. Wannan ba rayuwan da zan iya yi bane…”

     “Kwantar da hankalinki sanarmin mike faruwa?” ya faɗa like bai san komai akai ba. Da ƙyar ta iya masa bayanin abinda ya farun kamar yanda Daddy ya sanar masa. Anan ɗin ma murmushi ya sake yi ɓoyayye. Kafin ya ce, “Mawaddat rayuwar aure haka take, a komai ita mace ƙarƙashin ikon mijinta ta ke, wajib ne kuma yimasa biyayya in har shima bai keta dokar UBANGIJI ba ko jagorantar ta saɓa masa. Anan kam ba’a yarda ta masa biyayya ba sam, dan ba’ama wani biyayya ko tarayya wajen saɓama ALLAH……”

         “Bazai yiwu ba Uncle You, domin ni da kai da shi duk mun san matsayin wannan zaman ba sunansa aure ba, Please Uncle kace masa ya sakeni idan ma bazai yi haka a yau ba zan dawo gida idan kwanakin da akai yarjejeniyar sun cika ya sakenin, zan iya ɗaukar komai amma banda kan aiki na, domin shine rayuwata, shine farin ciki na, shine mafarkina, shine babban burina tun kafin nasan kaina, shi waye da rana tsaka zai datse hakan da tunanin nuna gadara ko ƙarfin ikon abinda bashi da ikon!”.

       “Mawaddat aure kona kwana ɗaya ne sunansa aure, da auren nan baida kimar da za’a kirasa ko kwallonsa da wannan martabar da muhimman mutane basu taru cikin shigar kamala domin ɗaurashi ba. Da wasu mutane basu ajiye muhimman ayyukansu ba domin halartarsa. Ki kwantar da hankalinki komai ya tafi cikin tsarin da muke fatansa, Aliyu kuma zanyi magana da shi duk da nasan shima ba son hanaki aikinki yake gaba ɗaya ba tunda ya sanar miki next week zakiyu resuming be a good girl mana sweetheart, maybe ma yana tsokanarki ne dan yaga yaya zakiyi. Dan haka ina son ki zama jaruma mana kamar yanda ya sanki…..”

        “Amma Uncle fitan yanada muhimmanci fa yau. Kasan inada case ɗin yarinya da ke aibiti, tun juya kuma ya kamata naje na shigar da case ɗin court”.

      “Kar ki damu indai wannan ne yanzu zan fita ni zanje da maman yarinyar mu shigar da ƙaran, ke kuma sai ki cigaba da shirinki matsayinki na lawyer ɗin nata hakan yay miki ko?”.

            A hankali ta ce, “Eh”.

       “Yauwa ɗiyar albarka na. Ki daure kinji, kar Aliyu ya samu na tsokanarki, bamma so ki bari yaga hawayen nan, maza ki sharesu ki zauna kurum kamar ba’ai komai ba Kinga kinyi winning”. 

    Ta gamsu da zancen nasa ɗari bisa ɗari, dan dolene itama ta mannama velleger ɗin can haukan da sai ya gagara barci a yau. Da ga haka ta miƙe bayan sunyi sallama da Uncle Yousuf da ke dariya daga can ta nufi bedroom. Fuskarta taje ta wanko da canja kayanta zuwa wando da riga marasa nauyi na zaman gida, ta sake dawowa falon ɗauke da laptop ɗinta. Dai-dai nan ya fito shima, alamunsa sun nuna yay wanka dan sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai matuƙar amsarsa sai ƙamshinsa mai sanyi da ke tashi. Zaune ya kai idonsa a kanta sai dai fuskarsa babu walwala, duk da taji motsin nasa ko sau ɗaya bata nuna alamar hakan ba balle ta ɗago, lap-top ɗinta kawai take ƙoƙarin kunnawa. Shi kuma sai ya tsira mata idanun nan nasa na macizai da take kira, ƙin ɗagowar tata bai hanata jin kaifin idanun nasa a kanta ba, amma ta dake ta cigaba da abinda take yi. 

        “Break fast fa?”.

     Ya faɗa a dake still dai idanun nasa a kanta. idan kujerar da ya ke zaune ta motsa to itama ta motsa. Cije lips ɗinsa yay yana wani sake ƙanƙance idanunsa a kanta. Kusan minti ɗaya yana kallon nata kafin ya miƙe tsam zuwa inda ta ke, lap-top ɗin ya ɗauke da ga jikinta ya ajiye gefe, karon farko ta ɗago ta kallesa da idanunta da suka kaɗa saboda kukan da tayi, fuskarta na nuna matuƙa ranta a ɓace. Nunawa yay kamar baiga kallon da take masan ba, kafin ta furta abinda ke bakin nata ya kwasheta gaba ɗayanta a cikin hannunsa yayi sama da ita kamar wata ƴar baby, (🤣dama abu ba abu ba sai masifa).

         “Bana son wulaƙanci malam miye haka? Dalla sauke ni”. Ta faɗa cikin matsanancin ɓacin rai tana kai masa ƙananun duka a ƙirji, amma ko gezau kansa tsaye ya nufi hanyar kitchen da ita, saman cabinet ya direta, ya juya ya sakama ƙofar key. Dai-dai ita kuma tana dirowa da ga inda ya ɗauratan ta iso ga ƙofar. Wani shegen kallo ta watsa masa da faɗin, “Matsa min”.

    “Idan kinyi abinda nace kenan”.

Ya faɗa cikin halin ko’in kula yana saka key ɗin cikin aljihun wandonsa da jingina da ƙofar yana mai harɗe ƙafafunsa waje guda. Ƙarshen ɓacin rai Lulu ta gama kaiwa, dan haka cikin kaushin murya ta ce, “Kasan na iya fiye da abinda kake tunanin ka’iya na rashin mutunci ko. Aliyu! Ka buɗe ƙofar nan ka bani hanya na wuce kafin na saka dana sanin sani na”.

          Jikin ƙofar ya bari da ɗan taɓe baki batare da yace komai ba ya nufi frizzier ɗin da ke kitchen ɗin ya buɗe, sai da ya ƙarema kayan ciki kallo sannan ya rufe ya nufi store. Daga sama har ƙasa yake bin store ɗin da aka tsatstsage da kayan abinci kala da iri da kallo shima, har da su doya da airish da ruwa da kayan miya da akaima ajiya irin wadda bazasuyi saurin lalacewa ba. Shi sai abin ma ya so bashi mamaki da dariya, to su da suka jibge waɗan nan kayan matar gidan ta iya abinci ne?….

      Shigowar Lulu a fusace ya saka tunaninsa yankewa, ya juyo gaba ɗayansa yana dubanta, huci take sosai idanunta sun juye gaba ɗaya har wani tara ƙwallan masifa sukeyi. Gashi yanda yaga sun ɗan kumburo tun ɗazun ya fahimci kuka tayi, yaji ba daɗi a ransa, dan sam baya son ganin wani ya shiga damuwa a dalilinsa, sai dai dolene yay abinda yayin dan ya fahimtar da ita da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu komai sai da izini… Da sauri ya dubeta jin tana ƙoƙarin saka hannu a aljihunsa alamar son zaro key. Hannun nata ya riƙe yana ɗan waro idanu waje, duk yanda taso fisgewa bai sakar mata ba sai da ya zare key ɗin da ga aljihun nasa, sai kawai ya maƙalashi jikin belt ɗinsa ta inda yasan bazata ce zata ɗauka ɗin ba yana sakin wani shegen murmushin mugunta. Da sauri ta ɗauke kanta da ga dubansa gaba ɗaya tana jin kamar ta fasa ihu, a zuciyarta kuwa tace (ɗan iska).

        “Yanzu mi zaki dafa mana? Dan yunwa nake ji nikam ga shi nace su Ammah kar su ƙara aiko abinci injiki.”

     Harara ta watsa masa cikin gatsali ta ce,  “Ashe zaka mutu da yunwa kuwa a gidan nan”.

             “Zadai mu mutu, dan kema dai duk tsiya dole ki nema ai. A yanzu ma haka idan kina son fita da ga kitchen ɗin nan ki nema mana abinci, inba hakaba ALLAH anan zamu yini”. Ya ƙare maganar yana fitowa da ga store ɗin. Ɗaya da ga cikin kujeru huɗun da aka sakama table a tsakkiya yaja ya zauna. Hankalinsa kwance ya jawo wayar ya fara buga game ɗin ball, ya kuma ƙure ƙarar yanda ta cika kitchen ɗin da hayaniya. Lulu data gagara fitowa a store kanta ta dafe, sai faman haɗiyar rai take zuciyarta na ƙuna. Ta rasa yaushe ne guy ɗin nan yay mata irin wannan rainin har haka, bata taɓa haɗuwa da mutumin da ke latsata a yanda yake so da gadararsa irinsa ba, ya bala’i bala’in shigar mata hanci da yawa. Gadararsa da son nuna shi ɗin wani ne da iya taurin kai na cimata zuciya. Fitowa tai a bisa shawarar da zuciyarta ta bata, ta cije lips ɗinta tana jin kamar idan ta ƙarasa garesa ta shaƙesa kawai, amma sai ta ture tunanin gefe. Kujerar dake kallon wadda yake zaune ta dafa cikin ɗan sassauta zafinta dan ta fahimci ihun da take masan kamar tunzurashi yake da jin daɗin latsata. “Aliyu kafa san aiki nakeyi ka ɗakkoni ka kawo nan, kai miyasa baka bambance lokacin shiririta dana serious?”.

        Batare da ya ɗago ya kalleta ba hankalinsa ma akan game ɗin sa ya ce, “Yima mijinki girki ne ba serious ba?”.

     “Kai kasan mijin ma, Ka bani key na wuce, idan abincin kake so ai kasan gidan abinci, dan in har abinda zan girka zakaci ka siyama kanka wahala dan ban iya ba ma sai kabi wani sarkin”.

       “Hummm ashe kuwa in dai ba zakiyi abinda nake so ba kuma ya dace ga matar aure to aikin ma zai gagareki yi ne, duk da a farko banda wannan niyyar. Dan haka kina da zaɓi kenan, yin yanda nake so kuma na tsara a gidana, ki samu yanda kike so kema. Ko ƙin yi, kema ki ƙi samu. Abinci kuma duk yanda kika iya kiyi zanci a hakan ko baiyi ba”.

            Luuuu tai da idanunta kamar zata lumshe su sai kuma ta buɗe, komai ma ya gundireta, tama rasa yaya zatai da mutumin nan mai shegen taurin kai da gadara. Wai miyasa ma ta amince ne da wannan tsarin da shi? Miyasa bata bada damar a nema wani ba?. Tsaki taja mai ƙarfi da kai hannu ta dafe kanta, sai kuma ta janye tana mai watsa masa hararar zaka banbance tsakanin aya da tsakkuwa ta bar wajen. Da kallo ya ɗan bita ganin ta nufi hanyar store, tana shiga yay mata gwalo da sakin murmushi nan nasa da take kira na mugunta yana kashe ido ɗaya a hankali ya ce, “2-0 Madam”……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣1️⃣

……..Tana fitowa ɗauke da dankali ya fuske kamar bashi ba ya cigaba da game ɗin yana satar kallonta ta gefen ido. Ganin ta fara firar dankalin ya sashi ajiye wayar tasa a table ɗin ya miƙe, gefenta ya tsaya kaɗan, ya ɗauka wuƙar data ajiye saman chopped board ya fara yanka wanda ta fere, bata kulashi ba, ba kuma tayi magana ba ta cigaba da ferewa tana ajiye masa. Shima sai baiyi magana ba ya cigaba da yankawa, idan ya ɗan tara sai ya zuba a cikin ruwan data ajiye a bowl. A haka har suka kammala, kasancewar ta rigashi gamawa ita ta fara barin wajen ta ɗakko preyn fan ta dawo inda yaken ta zuba ruwan sabulu kaɗan ta wankesa da soso ta ɗaureye duk yana satar kallonta. Komawa tai gaban gas ta kunna ta ɗora sannan ta zuba man data ɗakko. Dai-dai nan ya kammala, sai ya wanke mata dankalin ya sake masa ruwa ya tace sannan ya juyo yana miƙa mata robar. Sai da ta hararesa ta amsa, shi dai ya gimtse dariyarsa da ƙyar ya juya yana ɗauraye wuƙa da sauran abinda sukai amfanin. Lulu kam koda albasanta ya soyu ta zuba dankalin sai ta nufi frizzier, kifi tai ƙoƙarin cira sai dai sanyin da ya ratsa mata hannu ya sata faɗin, “Ouchh!!”. Juyawa yay yana kallonta, ganin yanda take yarfe hannun ya sashi nufarta, hannun ya riƙo ya saka cikin nashi ya rumtse ɗumin nasan ya ratsata, sai kuma ya jawota gaban fanfo ya kunna ruwa ya ɗauraye mata hannun, sannan ya jawo ƙaramin towel ya saka mata hannun ciki. Komawa yay ya ciro kifin har biyu masu ɗan girma ya dawo ya wanke su sannan ya dubeta, ɗauke kanta tai da ga kallon gefen ido da take masa. Shiko da ba lura yay ba ya ce mata “Yankawa zakiyi?”.

      Ƙaramar harara ta sakar masa da tura baki gaba sannan tace e.

   “Kai dai Aliyu kana shan harara wlhy abin tausayi”. Ya faɗa yana yanka kifin. Hararar tasa ta sake yi da matsawa gaban dankalinta ta da ke cikin mai……

       Kusan a tare sukai aikin, sai dai itace ke girkin shi kuma yana taimaka mata da yanka miƙo, duk da dai ba itace ke cewa yayi ɗin ba. Ya shiga matuƙar mamakin ganin yanda take girkin dama yanda tayisan, dan harga ALLAH bai kawo ta iya abinci ba. (Sai dai abinda Smart bai sani ba girki yana cikin hubby ɗin Lulu, tana son girki kuma ta iya kalolin girki na zamani sai dai fa sai ta gadamar yi take yin, tamafi sakin jiki tayi idan taje gidan Dada (kakarta matar Alhaji Garko) amma idan kaga tai girki a gidansu ko gidan Uncle Yousuf lallai ƴan arziƙinne a kanta ko taso yima Daddy wani bazata ko Uncle Yousuf ɗin). Abinda tai ɗin ya sashi jin daɗi bai ji ƙyashin tayata suka gyara kitchen ɗin ba duk da ma ba wani ya ɓaci bane dan Lulu akwai iya ƙwaf-ƙwaf ɗin aiki komai aka taɓa ana wankesa ne da zarar an gama da shi, inda ko ruwa ya taɓa za’a goge, tana hakanne kuma saboda yanayin tsaftarta, hakan kuma sai ya sake bama Smart nutsuwa kasancewarsa mutum mai shegen tsantseni da tsantsami. Dining takai komai ta ajiye tai wucewarta bedroom batare da ajiye plate ko kofin da za’ayi amfani ba. Baiyi magana ba saboda kiran Uncle Yousuf da ke shigo masa. Kiran ya amsa ya koma falo ya zauna. Har ya kammala wayar bata fito ba, dan haka ya miƙe yabi bayanta. Samunta yay kwance a kan gado rufda ciki sai dai ta canja kayan jikinta zuwa wasu, a hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da yin gyaran murya. Kamar bazata kulashi ba sai kuma ta buɗe idanun kaɗan a kansa. Cikin ido suka kalla juna, ta janye nata da wani yin gaba da lips kamar mai son yin zinɗe, ta ce, “Wlhy in ma da wani abun kazo bazanyi ba na gaji”.

      Dariya taso bashi dan yanda tai maganar da iyakar gaskiyarta, amma sai ya dake da ƙyar ya ce, “Ni na isa na sake saka Madam aiki ai tsaurin idon nawa ma sai yayi yawa. Sannu nazo yi miki, da kuma ban haƙiri da bikon kizo kici abinci. Har dama tausa idan kina so ƙyauya”.

          Cikin taɓe baki da harararsa akan zancensa na ƙarshe ta ce, “Kai ne handin burum kaje kaita ci”.

      “To Aliyu Hydar ka ƙara samun cigaba kenan, da ga illiterate velleger ka koma Maye, yau kuma handin burum, ɗan Ammah baban Ammah mijin Mawadda….”

     Filon da take kwance ta fisga kafin ma ya kai ƙarshen sunanta da taji ya kamo ta wulla masa. Da sauri ya cafe yana zaro idanu, ya ce, “Madam ina rabaki da halin jifar nan kar wataran ki ɓazge min hanci kamar yanda Iffah tai ma Uwa fa tom”.

     Wasu ta sake fisga tana tashi zaune ta cigaba da jefa masa su, tun yana karewa har ya fita yana dariya dan ya kula dai fushin ake saukewa a haka. Ƙwafa tayi itama da ballama ƙofar harara kamar itace tai mata laifin…..

       Shi da kansa ya ɗebo plates ɗin da spoons bayan ya wanke su, ya zauna a ransa yana faɗin (Bari muci girkin ƴar madara muji). Da tea ya fara, lokacin da ya kai dankali da source ɗin ƙwai bakinsa sai da ya lumshe idanunsa. Wannan fa shi ake kira kama da wane bata wane, UBANGIJI mai rahama. UBANGIJI mai jin ƙai da baya haɗama bawa zafi biyu, idan ya jarabceka ta nan sai ya sauƙaƙa maka ta can dan kaji sanyi. A duk inda kaga mutum da halayya mara ƙyau kar ka yanke masa hukunci da ɗari bisa ɗari ɗin munanan ayyukansa, UBANGIJI shine kaɗai yasan abinda ke cikin zuciya da sirrikan ɓoye ga bayinsa. Ita dai a zahirinta duk wanda ya ganta suna ɗaya zai bata, amma a baɗininta sai UBANGIJIN da ya halicceta ya san kayarsa, sai ko wanda ya ƙaddara ya santan kamar dai shi mijinta a yanzun…

      Yana gab da kammalawa ta fito, sai dai yitai kamar bata gansa ba ta zauna a falo ta ɗauka laptop ɗin ta ta cigaba da aikinta na ɗazun batare da kallon ko inda yake ba ko sau ɗaya. Shi ko dai sai satar kallonta yake time to time. Koda ya kammala sai ya ɗibo farfesun kifin cikin dauriya dan baya son kifi shi sam da tea ya nufota, ƙaramin coffee table ya jawo gabanta ya ajiye, ƙamshin kifin ne daya dakar mata hanci ya sata ɗagowa, harararsa tai ƙoƙarin yi yay saurin faɗin, “Ni dai tausaya min da hararar nan gidan ma zan bar miki karki lashe ni Ammah ko yaye ni batai ba”.

     Hararar tasa dai tai ta ɗauke kai, sai kuma ta sake ɗagowa ta dubesa, karan farko ta saki murmushin da ke bayyana beauty point ɗinta da farare haƙoranta, ga wanda ya santa a kallo ɗaya zai fahimci na mugunta ne, saboda bata murmushi sai ta so, wanda kuma bai santa ba zai ɗauka yinsa matsayin birkita kwanyar duk wanda ya kalletan ne. Girarta a sama ta ce, “Waye zai fitan? Ka manta yau a gidan nan babu shiga babu fita? Ai duk yanda ka dama haka kowa zai sha wlhy. Ta miƙe ta nufi hanyar bedrooms. Da kallo kawai ya bita na mamakinta ne ko na son ƙarin bayani akan maganar tata ne oho masa. Yana a wajen harta da dawo da keys a hannu, a kallo ɗaya ya gane na ƙofar falon ne da ƙofar kitchen ta baya. Sai da takai zaune sannan ta tura su cikin rigarta a gaban idonsa ta gyara tana ɗaukar tea ɗin da ya ajiye mata ta kai baki.

           “Idan ma wasa kike ki daina. Uncle Yousuf fa ke jirana tare da Yaya Abdull-Hameed”.

       “Oh really?”.

     Ta faɗa cike da rainin wayo. Hannu ya kai ya dafe kansa, sai kuma ya kai zaune a kusa da ita cikin lallashi ya ce. “Mawaddat Please seriously wlhy jirana akeyi, babu jimawar nan yay kirana kuma important ne zuwa 12”.

        Batama ko kallesa ba balle ta tanka masa, sai ma kifinta data fara ci a hankali tana wani lumshe idanu taba banza ajiyarsa. Rasama mi zaiyi yay, cikin son ta fahimta yay ƙoƙarin kamo hanunta ta balla masa harara. “Karka kuskura hannunka ya kai jikina. Ka kuma kiyayi yin hakan inba haka ba kasha mamakin sanin ainahin Mawaddat Isma’il Ibrahim Jiƙamshi. Kasan bazaka iya ƙarasa wasan ba miyasa ka fara? Common ƙyaleni bana buƙatar hayaniya, ba kace da ni zaka buga game ba? Muje zuwa”.

       (Tana mun magana kamar wata lady boss) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam kansa kawai ya dafe. Abu tamkar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa har 12 tayi Lulu bata da niyyar bama Smart key ɗin nan, zuciyarsa na raya masa ya turmuzeta ya amsa amma yana gargaɗin kansa karta tada masa aljanu, dan yasan mata da iya aljanu. Sha biyu da kusan kwata kiran Uncle Yousuf ya shigo masa. Ya ɗaga ya gaida shi da mutuntawa kamar yanda ya saba. Da ga can Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu yaya dai? Kai muke jira na ga har 12:15?”.

      Ɗan kallon Lulu da ke ta aikinta a laptop tana zuba murmushin mugunta yayi, a can ƙasan maƙoshi ya ce, “Uncle ta kwashe keys ɗin ne fa, wai tunda na hanata fita nima babu inda zanje”.

           “What! Mawaddat ɗin? Kaga bata wayar Please bana son shiririta”

Maimakon bata sai ya saka a hansfree yanda zataji, kiran sunanta da Uncle Yousuf ɗin yay ya sata ɗagowa ta kalla wayar, sai kuma ta amsa da “Yes Papa good afternoon”.

       “Afternoon Dear. Miya faru kika hana Aliyu fitowa ga shi munata jiransa?”. Murmushin muguntar da take ta faman yi tun ɗazun alamar duniya ta mata daɗi ta sake saki da faɗin, “Uncle You shi ya zaɓi hakan ai, dan haka ka manta da shi kawai, dan yanda ya hanani fita sai dai mu yini tare a gidan.”

     “Mawaddat Please!!”

“Uncle please”.

         Ta faɗa itama kamar yanda yayin tana tura baki. Kai kawai Uncle Yousuf ya dafe da ga can, yayinda Coach ke kwasar dariya dan Smart ɗin kawai ya ke hangowa, kai mace daban ce, yo inba mace daban take ba Smart ɗinsa ne da ya sani mai tsaurin nan da rashin son magana za’a kullema ƙofa a hanashi fita. Aure aunre yayi. A ɓangaren Uncle Yousuf kam iyakar lallaɓa yay ma Lulu tafa ce ba gudu babu ja da baya, har ya koma faɗa amma tai biris, ba komai ke tunzurata ba kuma sai ganin yanda fuskar Smart ta fara canjawa da dauriyar da yake zuwa ɓacin rai. “Uncle bye”. Ta ce cikin siririyar dariya tana miƙewa tare da laptop ɗinta da wayoyinta tabar falon ma tana ɗagawa Smart yatsu biyu na ƙularwa ta ce, “2-1 ka shirya yin game over gaba kaɗan”.

      Wani irin bahagon iska ya furzar da ga bakinsa yana mai dafe kansa. Da ga can cikin tunzura shima Uncle Yousuf ya ce, “Aliyu wai yarinyar nan tafi ƙarfinka ne da karɓar key a wajenta ya gagareka. Be a man mana Son”.

         “Uncle bazaka gane bane wlhy, yarinyar nan azababbiya ce, tafa saka key ɗinne…..”

    Sai kuma yay shiru fahimtar ɓaranɓaramar da yake neman yi. Uncle Yousuf zai sake magana coach ya katsesa da faɗin, “Kaga ƙyaleta muje mu samesa a can kawai nikam, dan amarya dai bata laifi koda ta kashe ɗan masu gida. Zakina jiramu karka damu”.

     Kafin Smart ya ce wani abu an yanke wayar, sai kawai ya girgiza kai. Wannan ma sauƙin kan na Coach ya sa yake sake jin ƙaunarsa a ransa. Mutumin nan shi na musamman ne a garesa, dan ya taka rawa kala-kala a cikin rayuwarsa da har abada bazai manta ba……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣2️⃣

………Cikin mintuna da basu wuce ashirin ba sai gasu sun iso, jin horn ɗin su da kiran da Coach yay masa ya ce gasu sun iso ya saka shi miƙewa ya nufi bedroom da ta shige. Fuskarsa babu walwala da ga bakin ƙofar ya tsaya yana kallonta da faɗin, “Sun iso Please ki kawo naje na buɗe musu”.

      Ɗagowa tai ta ɗan hararesa da maida kanta tana taɓe baki, “Oh wai har yanzu kana tunanin amsa cikin sauƙi ko min wayo? To anƙi a bada ɗin na ƙarfi ne”.

          Kaɗan ya cije lips ɗinsa da jin jina kai yana wani ɗan murmushi, dan ya fahimci sai yayi abinda tun ɗazun yake hana kansa yi sannan. Takowa yay zuwa gaban gadon tare da kaiwa zaune cikin lallashi ya ce, “Mawaddat su Uncle Yousuf ne fa, kuma na faɗa miki magana mai muhimmanci zamuyi….”

      “Nima ai aiki da zan fita yi mai muhimmanci ne ka sani. Gara ma ka bar wani sauke murya ba badawa zanyi ba ehe”. Ta juya ta cigaba da aikinta.

       Lips ɗinsa ya sake cijewa da faɗin, “Amma kin san zan iya amsar key ɗin a duk ta yanda naso ko?”.

         A gatsine ta ce, “To ƙarɓi ɗin mana”.

    “Haka kika ce?”.

         Shiru ta masa kamar bata ji ba, sai ma faman murmushin ta take tana sarrafa system ɗin gabanta cike da ƙwarewa dan charting take yi da wata friend ɗinta ƴar ƙasar Hong kong da sukayi karatu a America tare. Laptop ɗin gaban nata ya janye gefe tare da birkitota, zabura tayi dan batai zaton zai yi yunƙurin amsar ba, sai dai kafin tayi wani yunƙuri ya danneta da rabin jikinsa ya riƙe hannayenta duk biyu a cikin nasa. Rawa jikin nata ya fara yi saboda yanayin na neman maimaita kansa ne da abinda ya shuɗe, amma cikin ƙoƙarin dakewa ta ballara masa harara. duk da shima ya fahimci hakan bai bi takanta ba sai ma baki da ya taɓe da sakin murmushin nan nasa data raɗa ma suna na rainin hankali cikin kashe ido ɗaya ya ce, “Zaki bayar da arziƙi kona ɗauka?”.

        Sosai ta waro idamunta da suka cika da ɓacin rai ta ce, “Saboda kai ɗan is…..”

     Baki ya taɓe da faɗin, “Oh ɗan iska ko?” sai ya ƙara ƙasa da murya yana kai bakinsa jikin kunnenta ya raɗa mata, “Dole ne ma nayi iskancin nan dan banzan amsa sunan nan a banza ba”.

        “Aliyu!!”

    Ta faɗa tana zaburowa gaba ɗayanta sai dai har ya riga ya tura hannunsa a rigarta ya ciro key ɗin. “3-1 Madam” ya faɗa yana sakin mata hannu da ɗagata murmushin mugunta fal fuskarsa ya nufi ƙofa ya fice harda mata gwalo.. Rumtse idanunta kawai tai da masifar ƙarfi tana ƙoƙarin dai-daita numfashinta dake rawa a maƙoshi……

       Koda ya fito cikin girmamawa ya tarbi su Uncle Yousuf ɗin, basu shiga ciki ba kamar yanda ya buƙata, sai suka zauna a ƙarƙashin rumfar bunu da ke a harabar gidan domin hutawa. Ya gaishesu cikin mutuntawa, yayin da Coach ya tasashi a gaba da tsokana, murmushi kawai yake yi amma ya kasa cewa komai. Uncle Yousuf ya harari Coach da faɗin, “ALLAH kai dai anyi Yayan kwabo, ka ƙyale min yaro ya huta”.

      Cikin dariya Coach ya ce, “Oh ashe fa kai yanzu ka tashi da ga Yaya ka koma suruki. No wander bakin Zaki na ya sake zama rumus yau. Bara to na tausaya masa sai ka matsa na ɗora da ga inda na tsaya dan ba barinsa zanyi ba fa”. Murmushi kawai Smart ke yi dan in dai Coach ne ya riga ya saba da wannan barkwancin nasa. Dama kuma can bai iya maidawa balle yanzu da yake ganin Uncle Yousuf da ya ƙara girma a idonsa na wajen. Sake gaisawa sukayi kafin su fara tattauna abinda ya tarasun. “Aliyu nasan ka ɗokantu da son jin dalilin wannan zama namu, kamar yanda muma muke a ɗokancen”.

       “Haka ne Sir, dan da har na fara tunanin ko nayi wani laifi ne ma”.

    Murmushi Uncle Yousuf da Coach sukayi a tare, kafin Coach ya cigaba da faɗin, “Aliyu kai na daban ne ai, duk da dai ɗan adam tara yake bai cika goma ba. Bakai laifin komai ba abinda muketa fatane da buri ya kasance. Yousuf abokina ne koma nace maka ɗan uwana dan ina jinsa tamkar matsayin twins brother, kamar yanda ka sani ya sanni da kai tun kana ƙaraminka, sannan masoyine naka dan yana ɗaya daga cikin wanda suka dinga goyon bayanka matuƙa, sannan ya taka rawar gani matuƙa a baya na son ganin ka ƙetare ƙasar nan amma ƙaddara ta hana hakan. Bai haƙura ba ya cigaba da shigi da fici na ganin abubuwa sun dai-dai har kawo yanzun nan bai huta ba. A yanzu dai a matakin ƙwallo shekarunka sunja Aliyu, sai dai Alhmdllh yanayin jikinka da kula da motsashi yasa kai tsaye baza’a iya cewa ka kai shekarun da kake ɗin ba a yanzu. Dan haka mataki na farko shine mun zabge maka shekaru a rubuce, mataki na biyu yanzu zaka daidaita cin abubuwan da duk suke saka jiki nauyi domin samun daidaito, sannan zaka sake jajircewa da training. Inata kai ka ban faɗa maka dalilin zancen ba. A karo na babu adadi Yousuf ya sake maidaka duniyar ƙwallon ƙafa a yanzu, a kuma matsayin manager ɗin ka. Duk wani abu da zamu iya kallo a matsala yayi iya bakin ƙoƙarin sa na shiga da fita wajen gyarashi da alkintashi cikin nasara kasancewar sa mutum mai kutsa-kutsa da huɗɗa da mutane a ƙasashen ƙetare. A yanzu haka ka samu team a ƙasar London in sha ALLAH signing da abinda baza’a rasa a kawai ya rage”.

      Shiru kawai Smart yay yana saurarensu, har sai da Coach ya kai ayar bayaninsa sannan ya dubesa ya dubi Uncle Yousuf ɗin ƙwalla na cika masa ido. Kai Uncle Yousuf ya girgiza masa da masa alamar zip a baki baya son yace komai kenan. Wani irin al’amari mai girma Smart ya haɗiye tare da duƙar da kansa yay shiru ba tsawon mintina. Ba komai yake ba face kwararoma waɗan nan mutane biyu addu’oi kala da iri, sai da ya kammala sannan ya ɗago cikin ƴar damuwa. “Kun hana nace komai duk da inada abubuwan faɗa masu yawa. Ku na dabanne a garen….”

      “Shiiii!!” Uncle Yousuf ya faɗa cikin dakatar da shi. Dole ya haɗiye tarin yabo da godiyar dake gumtse a zuciyarsa zuwa baki, ya tsira musu idanu kawai, sai kuma ya nisa a hankali “Amma Sir bakwa gudun a sake samun makamanciyar irin waccan matsalar?, bana son ku sake shiga matsala a dalilina”.

        “In sha ALLAHU bama fatan hakan Aliyu. Kuma ai mu fatanmu wannan dabarar ta zama mafita. Ball hubby na ka ne, na sanka komai akace kayi ba ita ba zaka iya yin amma badan hakan na maka daɗi a rai ba. To a rayuwa duk abinda bawa zaiyi badan yana son abin nan ba zakaga yana tafiya ne babu wani armashi. A wannan karon bawai kai tsaye muke son ayi hakan ba, sai da muka duƙufa addu’a mu da su Ammah gaba ɗaya kafin ma duk wannan kai kawon na Yousuf, dan na tabbatar addu’oi nasu ne suka shiga kan gaban komai ya tafi mana yanda mukai fata ƴan matsalolin da suka faffaru ba wasu masu yawa bane gaskiya”.

       “Su Ammah?!…”

   Smart ya faɗa da ɗan mamaki, kai Coach ya gyaɗa masa da faɗin, “Yes da ga ita har Abba sun san komai akan wannan, kuma Alhmdllh bamu sha wahala wajen amincewar tasu ba kamar farkon magana da su akan barinka fara ƙwallo”.

       A hankali ya ɗan furzar da iska yana jin jina kai shima, sai dai a ƙasan ransa yana jin wata nutsuwa mai tarin yawa, dan da gaske ƙwallo abar sonsa ce, burinsa ce tun yana ƙanƙaninsa fiye da kowanne abu da zai iya yi ciki harda zaman office. Takardun da Coach ya fara bashi a farko ya buɗe, ɗan duddubawa yay sai kuma ya ɗago yana kallon Coach ɗin, “Ammah Sir taya kuka samu irin wannan damar haka cikin sauƙi, bayan nasan mutanen kudancin nan namu da iya babbake komai sai su. Su kuma turawan nan da tsantsani akan komai?”.

        “Addu’a ne kawai Aliyu, sannan bawai da sauƙin aka samuba ma, an jima ana yaƙin, amma mutuminka dai ne wannan karon ma ya sake shiga ya fita da tsayawar ALLAH data Yousuf muka samu sunan naka ya zama gaba-gaba. Sai su kuma wasanninka da suka ɗan gaggani na baya ya sake ɗaukar hankalinsu matuƙa. Kaga kenan Addu’ar su Ammah tafi gaban komai”.

      “Hakane Sir” ya faɗa cikin rauni, sai kuma yay murmushi da kallon Uncle Yousuf da shima ke kallonsa da murmushin. “Uncle kayi haƙuri ka barni na faɗa, wlhy ku na dabbanne a gareni a cikin daban. Har abada harshena bazai gushe wajen muku addu’a ba ku da zuri’arku. Uncle……”

          “No no no Aliyu it’s ok! Ya Isa haka ba sai ka cigaba da cewa komai ba, addu’ar nan daka ambata a garemu ita kaɗai ta wadatar, muma bayin kammu bane, ALLAH kaɗai yasan alkairin da ke cikin al’amarin shiyyasa nasarori da yawa suka samu cikin sauƙi. Abinda kawai na sani shine Aliyu kai yaron kirki ne nagartacce da bai kamata ai sakacin da samuwar wata dama irin haka gareku ba, dan arewacin Nigeria na matuƙar buƙatar irinku koma nace Nigeria ko African gaba ɗaya, in sha ALLAHU nan da lokaci ƙalilan sunan Smart Mawashi da ya fara bayyana ƙaddara ta binne sa zai yi zaburar da zata girgiza duniyar ƙwallon ƙafa. Wannan basirar taka bazata wuce a banza ba kamar yanda muke sakaci da ire-iren ku ta hanyar dakushesu a dalilin rashin kulawarmu. Wannan plan ne na shekara kusan biyu da rabi, koda wasa bana son ka kallesa a matsayin dan kana auren ɗiyata ne”.

      Murmushi mai faɗi Smart yayi har wasu ƴan ƙwalla na sake tarar masa a ido kaɗan, sai yaji yama kasa cewa komai kawai. Dai-dai nan Lulu ta iso wajen, maganar Uncle Yousuf ta fargar da shi hakan………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣3️⃣

…….Juyawa yay ya kalleta, sai akai sa’a itama ta kallesan suka haɗa ido. Harararsa tai ta ɗauke kanta. Shima sai ya maida nasa gefe kaɗan yana ɗan murmushi. Bata saka hijjab ba amma ta ɗaura Abaya a saman kayan jikinta tare da yane kanta da ɗankwalinta. Tray ɗin hannunta ta ajiye musu fuskarta da murmushi da shagwaɓa bayan ta gaida su ta dubi Uncle Yousuf da faɗin, “Papa i miss you ALLAH”. Dariya Uncle Yousuf yayi da jin daɗin ganinta yanda yake fata tunkan aje ko’ina. Sai da ya karɓi kofin ruwa data zuba masa sannan ya furta, “Mu kewarki ma bamu san yanda zamu misalta ta ba ai Mawaddatan’warahmah. Na gaban goshinki na can yau da ƙyar ya yarda zaije makaranta”.

     Murmushi tayi da faɗin “Uncle Please a kawo min shi to mana”.

          Shima sai yay ɗan murmushin da faɗin, “Tom ki ƙara hutawa, in dai waɗan nan ne sai kin gaji da su a gidan nan. Dan yanzu haka ma su Auntynki na zuwa”.

       Sosai taji farin cikin hakan, duk sai zumuɗi ma ya hanata zama ta juya ciki wai bari yaje ta shirya kafin su iso. Shi da Uncle Yousuf da kallo duk suka bita, yayinda Coach hankalinsa ke kan takardun nan. “Ina fata dai babu wata damuwa ko?”. Uncle Yousuf ya faɗa cikin katse tunanin Smart. Kansa ya jinjina masa cikin sauke numfashi ya ce, “Da sauƙi dai kam. Dan na fahimci wani lokacin tana da sauƙin kai musamman akan lagon mahaifiyarta da ka bani, dan in har zan jingina mata sunanta akan abu zatayi sa babu musu”.

       “To Alhamdullah, naji daɗi sosai dan hakan ma ci gaba ne. Ka ƙara haƙuri na haɗaka da aiki, amma nasan nan gaba kaɗan zaka gode min kaima. Dan Mawaddat nada wasu ɓoyayyun al’amura musamman halayen masu ƙyau, a yanda ta tashi taga kanta ne kawai babbar matsalar, sai dai duk da haka tsiwa da jin kanta sama sosai a jininta yake, dan mahaifiyarta tamkar tayi kaki ne ta ajiye, itama haka take kamar wata jinin sarauta wajen izza. Bambanci su kawai ita ta samu tarbiyya fiye data Lulu ne, da kuma kasancewar ita da girmanta ta haura wata ƙasa karatu ba kamar Mawaddat ba. Sai dai fa Aliyu yanzu yaƙin bana Mawaddat bane kawai, sannan ba ita kaɗai bace a filin dagar. Na farko sai munyi haƙuri da Yaya, na biyu Alhaji Sulaiman da ɗansa, dan nasan duk da baya ƙasar nan hankalinsa na nan, kuma gab yake da dawowa tunda jikin Tajuddeen ɗin da sauƙi.”

          “Karka damu Uncle Yousuf ku dai ku cigaba da mana addu’a. Daddy kuma insha ALLAH babu komai a tsakanina da shi sai girmamawa, na kuma fahimci son da yake mata ne mai tsanani da tausayinta ke rinjayarsa”.

      “To Alhamdullah nagode daka fahimci haka. Yanzu sai ka fara shirin nan da kwanaki zakaje Legos ɗin kamar yanda suka buƙata”.

               “ALLAH ya kaimu”.

       Da Amin suka amsa su biyun. Da ga haka suka ɗan sake tattaunawa shi da Coach akan abinda ya shafesu na harkar ball ɗin dan yanzu kam zai koma filin daga saboda training, sunja lokaci sosai dan har aka kira sallar azhar kafin su bar gidan su uku suna tsokanarsa da dariya wai yanzu ya koma ɗan 23years. Uncle Yousuf harda faɗin yanzu Lulu ma ta girmesa tunda gashi ma harya fara tsoronta dan yanzu ma dai sai da aka taɓa drama. Dariya yayta yi shi dai abinsa, dan koda ya koma ciki domin kiran Lulun suyi sallama da su Uncle Yousuf a ƙofa ya tsaya saboda gudun karta sake rutsashi. Dan ya manta bai zare key ɗin ba. Kamar kuwa ya sani tayi target ɗinsa akan hakan ALLAH dai ya taimake sa, amma duk da haka sai da tace bafa zai fita ba, sai da Coach ya bata haƙuri akan su Aunty Saliha na zuwa shiyyasa zai fita dan bai kamata su samesa a gidan ba haka akeyi sannan ta haƙura ta barsu, amma yasha harara kamar idanunta zasu faɗo….

    Suna barin gidan su Aunty Saliha na isowa, hakan yay matuƙar ɗauke kewar Lulu da sanyata a farin ciki. Sai a yau taga lefenta na wajen Smart. Tayi mamakin ganin kayan da aka kai ɗin da shan jinin jikinta akan anya kuwa babu wani abu a ƙasa da su Uncle Yousuf ɗin ke shirya mata, wai tayaya aure wata ɗaya duk akaima wannan irin kisan kuɗin. Dauriyar dannewa tai dai batace komai ba har suka kammala abinda zasuyi bayan la’asar suka wuce. Suna wucewa kamar wani shiri sai ga Nadiya da wasu ƙawayensu da sukan haɗu a wajen shaye-shayen su, sai dai ita Lulu bawani tana kulasu bane sosai dan itafa dama can ba ma’abociyar shiga sabgar tarkace bace kasancewar ta wayayyar yarinya, ga kuma ƙawaye da ta daɗe da ajiye babinsu a rayuwarta. Ƙoƙarin rufe ƙofar tai tamkar ma bata gansu ba amma Nadiya ta iso da sassarfa ta riƙe cikin roƙo da magiya. Lulu da gaba ɗaya ganin Nadiyar ya sakata jin fusata ta ɗaga hannu ta ɗauketa da mari haggu da dama, sannan ta nunata. “Wannan shine hukuncin da fuskarki zata cigaba da fuskanta a duk lokacin da kikai yunƙurin nuna min ita, Nadiya duk abinda na ajiye tofa idan baki sani ba da ga yau ki sani na ajiyesa ne har abada dan bana jeka ka dawo, FURAR DANƘO NA KE A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. duk ramin da maciji ya sareni sau ɗaya bana ɗaura ƙafata a wajen karo na biyu. Ni nan da kike gani na fiki fiye da abinda kike tunanin kin iya, bana cin amana ba kuma na zama da maci amana, ki fita a rayuwata, dama ke kika sakko kanki cikinta ban ganyyaceki ba”. Da ga haka ta maida ƙofar ta rufe da ƙarfi har sai da duk suka zabura.

        “He he he babbar bala’i mai citta da kayan sanyi, wai dama haka yarinyar nan take bata da mutunci? Akan kawai saurayi ya bita inda bata gayyacesa ba take wannan tada jijiyar wuyan, ƴar iska bayan ance mana rainon turai ce wane kalar iskanci ne basayi a can amma zatazo nan tana nuna mana ita wata kamila ce. To wlhy zamu bata mamaki, dan wannan marin da tai miki sai ta fansheshi da abinda har abada kuka bazai bar kwaranya a idanunta ba, zata san ta haɗu da ƴan tasha na asali, dan ƙarshen iskanci a Nigeria aka haifesa da yanke masa cibi aka kuma rainesa a ciki yay girma yay furfura, idan ma ya mutu anan za’a biznesa sai ranar bayyanar judal su tashi tare su haɗa ayari”.

        Murmushi takaici Nadiya tai da janye hanunta da har yanzu ke a kan kuncinta tana maida ƙwallar data cika mata ido. Ta ce, “Shuwa Lulu ta wuce duk yanda kike tunaninta, ki kuma iya bakin ki dan ta fiki in dai jidali ne. Lolipop ma tayi bataci riba ba. Ni nai mata laifi dan tun farko ta gargaɗeni akansa amma banji ba, nai mata ma farko tace karna sake na biyu amma na sake kuma, na san nice da laifi dan Lulu ta ƙyautata min a rayuwa, na kuma san bata ƙaunar huɗɗa da maza amma na sake maimaitawa. Shiyyasa nace muku bazan zo ba sai nan gaba ta sake hucewa amma kuka matsa, ga shi abinda sakamakon hakan ya bada kun jamin tozarci…” kafin wani cikinsu ya ce wani abu ta nufi motarta da sukazo ciki ta shiga, bin bayanta sukai da sauri suma duk suka shiga. A guje tabar anguwar damma ba yawan hayaniyar mutane a aria ɗin kasancewar sa babbar anguwa……

          __________★

    Bayan magrib Smart ya koma gida, ya iske Lulu cike fam da taicin su Nadiya har lokacin. Kasancewar bai san abinda ya faru ba sai ya ɗauka fushi take na daɗewarsa. Dan haka yayta satar kallonta da ga inda yake tsaye dan tunda ya shigo batako ɗaga kai ta kallesa ba balle ya samu sannu da zuwa. Aikinta take tayi a laptop da shan chocolate da su Hussain suka kawo mata lokaci-lokaci. Ice-cream ɗin da ya sayo mata da shawarma ya ajiye gabanta, batare da yayi magana ba shima ya wuce bedroom. Wanka yay har zai kabbara salla sai kuma ta faɗo masa a rai, amma sai ya ture zancenta gefe ya kabbarra sallarsa, sai da ya idar sannan ya miƙe, fitowa yay inda ya sake samunta har yanzu ido a laptop babu alamar ma ko kallon kayan da ya kawo matan tayi. Babu alamar wasa a harshemsa ya ce, “Kinyi sallar magrib da isha’i?”.

     Shiru babu alamar zata tanka masa, ya ɗan rumtse idanunsa da sake buɗewa cikin sake kausasa harshe da buɗe deep voice nashi fiye da farko ya sake maimita mata. Yanzu kam dole ta ɗago ta ɗan kallesa, cikin harara ta ce, “Miye naka a ciki idan nayi ko banyi ba? Wai nikam dan ALLAH miyasa kake son shiga min rayuwa da yawa ne haka? Ko gadin rayuwata aka baka ne bani da labari. Bana son damuwa kabar ganin ina ɗaga maka ƙafa ka dinga ganin zaka cigaba da latsani a duk sanda kake so fa, dole ne duk abinda nayi ko baka nan sai na faɗa maka”.

        Idanunsa kawai ya zuba mata, sai dai baiyi magana ba sai hannunsa kawai da ya rumtse waje guda alamar ɓacin rai matuƙa tattare da shi amma yana controlling temper ɗinsa. Dan baya son ko sau ɗaya ya ƙwace wajen bayyana mata ɗayan side ɗinsa a yanzu. Tsaye kawai ta gansa a gabanta, batare da yay magana ba ya ɗauke lap-top ɗin gefe gaba ɗayamta ya ɗauka kamar ɗazun. Yanzu kam ba duka ba har da su cizo takai masa amma ko gezau, bai direta ko ina ba sai bathroom ɗin ɗakinsa, dama a farce take, sai hakan ya ƙara tunzurata, sai dai kafin furucin bakinta ya ida fita ya taka mata birki da faɗin, “Shiiiiii!! Idan ki ka sake cewa tak wlhy sai kin sha mamaki yau.” da ga haka ya juya yay ficewarsa ya barta a toilet ɗin. Tsabar rasa abinyi sai kawai ta saki kuka, hawaye sosai tayi kafin tayi alwalar, koda ta fito batako kalla inda yake ba tai ficewarta, shima sai bai ce da ita komai ba dan ya riga ya kai waya ɗakin nata ya ajiye ta yanda in ma batai ba zai gani. Sai dai kuma Alhamdullah, koda ta shiga can ɗin sallar tayi dan da gaske dama batayi magrib ɗin ba, Azhar da la’asar dai da yake aunty Saliha na gidan tare ma sukayi. Bayan ta idar ta jima zaune a wajen tana tunani akan nasihar da Aunty Saliha ta sake mata musamman akan ibada. Da ga baya ta sake fitowa falon, anan ta sameshi kwance. Inda lap-top ɗinta ta ke ta koma ta zauna ta cigaba da harkar gabanta batare data kulashi ba, shima kuma baice mata komai ba yay shiru ne ma a kwancen kamar mai barci yana tunanin abinda ya faru a yinin yau ɗin gaba ɗaya. Sai da ta shagala a abinda take yi yaje ya ɗakko wayarsa, koda ya duba ya ga tayi sallar sai ya sake samun nutsuwa……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣4️⃣

………Haka abubuwa suka cigaba da tafiya a gidan Smart da ɓangaren kwallonsa. Dan matuƙa ya dage da training da kuma kiyaye cin abubuwa tare da miƙama UBANGIJI al’amuransa, harda azumin kwana uku yayi da sadaka. Maganar shaƙuwa ko hirar arziƙi kam tsakaninsa da Lulu babu. Babu mai shiga sabgar wani ta ɓangaren lalama, garama shi wani lokacin yakan ɗan tsokaleta ita kuma tai masifa. Idan lokacin salla yayi kuma ko baya gidan zai tura mata text message akan tayi dan ALLAH, tai ma mahaifiyarta kuma addu’a. Sosai yake karya lagonta da hakan shiyyasa a yanzu kam Alhamdullah da wahala kaga lokacin sallar ma ya shige bata tashi tayi ba, daya turo saƙon ko batai niyya ba zata tashi taje tayi. Idan kuma yana gidan zai mata magana nan ma tayi. Girki ma dai kullum da rigima ake yinsa na safe dana rana idan har yana gidan, idan kuma ya fita na safen kawai akeyi ita dama ba damuwa tai da abincin ba, da dare kuma shi dama ba damuwa yay da cin abinci ba balle yanzu da yake sake ƙoƙarin daidaita jikinsa. Kayan shaye-shaye dai duk da ya toshe ko’ina da samunsu hakan baisa zuciyarsa ta samu nutsuwa ba, a duk motsinta kaffa-kaffa yake yi, ita kuma duk da ta daure kwana biyu a cikar kwana na biyar sai da yanayinta ya canja saboda matuƙa take buƙatar su, ta rage kulashi suyi faɗa, ta zama shiru-shiru, wani lokacin ma yakan shigo gidan ko ɗakinta ya ganta zaune a lungu ta takure kanta cikin damuwa koma tana kuka, sosai take bashi tausayi, dan haka a duk sanda ya ganta a yanayin sai ya zauna yayta mata nasiha ne cikin tausasawa, yana kuma ƙoƙarin bata ruwan addu’oin da malam ya basa a ɓoye batare da ta sani ba, magani ma na nan zuwa da malam ɗin yace zai haɗa mata inasha ALLAH akan shaye-shayen dai. A ɓangaren karatu da suka fara duk da dai suna ɗan kai ruwa rana wasu lokutan kafin ayi, Alhamdullah ya fahimci tana ganewa, dan a ɗan tsukun kwanakin a ɓangaren salla abubuwa da yawa Lulu ta gyara, tana kuma ƙoƙarin riƙe addu’oi. Nacin fita aiki kuma bata daina ba, shi kuma bai kulata ba. Washe garin da suka cika kwana biyar ranar asabar Aunty Bilkisu da Hawwah da Maryam da Asma’u sukazo gidan, ranar yana gida bai fita ba, dan dama fitar tasa dai ba ko yaushe bace ba, ba kuma ta wuce zuwa gidansu, stadium training, sai ɗan kaikawo akan case ɗintan nan na yarinyar nan da yake mata bincike tunda su Uncle Yousuf sun shigar da ƙara court da mahaifiyar yarinyar da kuma taimakon ƴan sanda. Duk sanda ya fita kuma baya yarda ya daɗe idan yayi tunanin ya barta ita kaɗai dan a ɗan zaman sun nan ya fahimci bata son kaɗaici, sai kuma sauran kai kawon da suke da su Coach akan batunsa na abubuwan da suka saura dole da kansa zaiyi. Tarba suka samu ta muntunawa ga Lulu irin wadda su kansu basuyi zato ba, sai suka ji ƙaunar matar ɗan uwan nasu ta ƙara mamayesu. Fargabar da suke ta wataran zai iya aure matarsa ta rabasu da shi ta fita fit a zuciyarsu. Yana ɗaki yana barci hayaniyarsu ta tada shi, bai san kosu waye ba dan haka ya tashi badan barcin ya ishesa ba ya fito, turus yay yana kallonsu, sai bin Lulu daketa faman murmushin yake da kallo, a zuciyarsa kuma yana wani tunani, musamman akan maganar malam da yace tana da ɓoyayyun halaye masu ƙyau, to amma miyasa masu aikin gidansu su take musu duk yanda taso? Kodan su suna a ƙarƙashin ta ne take gani, na biyu ya fahimci bata son kaɗaici sam, dan koshi idan zai fita gidan sai ya ga yanayinta ya canja zuwa damuwa koda bazatace komai ba. Maryam ce ta fara hangosa, cike da jin daɗi ta ce, “Yaya Hydar sannu da fitowa”. Da kai ya amsa mata, yayinda sauran ma duk suka juyo harda Lulu, sai dai kallo ɗaya ta masa ita ta ɗauke nata idon. Falon ya ƙaraso ya zauna, cikin girmamawa ya gaida Aunty Bilkisu, su Hawwah ma suka gaida shi. Daga haka aka ɗan cigaba da hira sai dai basu yarda sunyi wani abinda Lulu zataji a ranta kamar ita barece a cikinsu ba. Wannan abu yayi matuƙar tasiri a zuciyarta, sannan yanda suke girmama juna da shaƙuwarsu da soyayya mai ƙarfi ya matuƙar sata jin kewa da jin inama itama haka take da nata ƴan uwan. Ta kasance cikin farin ciki a wannan yinin, dan ko abinci Maryam da Hawwah ne sukayi basu barta tai komai ba sai Asma’u data gyara gidan, dan wannan shine kema Lulu wahala kuma duk da bata ƙaunar ƙazanta. Ta masa maganar mai aiki yaƙi ce mata komai, shi kuma ba mai aikin ce baiso ba duk da yasan kuɗin biyanta ma a garesa wani abu ne daban, tsoron kar mai aikin ta zame mata ƴar aikar sayo ƙwaya yake shiyyasa yay mata shiru. A lokacin da su Hawwah ke kitchen suna girki Aunty Bilkisu kece masa. “Hydar baka ganin ya kamata kayi haƙuri Hawwah ta koma ɗakinta, mijinta na sonta sannan yana ƙoƙarin sa a kanta, mahaifiyarsa kuma shima tafi ƙarfinsa ne. Tunda su Abba sun bar komai a hannunka ya kamata ayi haƙuri ta koma haka nan ai anja masa kunne, ALLAH tausayi yake ban kullum yana cikin zaryar zuwa gidan nan, ga Nasreen dake damunta kullum ita Abbanta Abbanta, ita kanta Hawwah dauriya kawai takeyi da kuma bazata iya ƙetare maganarka ba, kayi haƙuri ka duba ta koma gidan mijinta kodan halin Umma da bata gajiya da abin faɗa kullum ta ALLAH a gidan nan kan Hawwah, haƙurin shi yafi komai ko ya kikace Mawaddat?”. Ta ƙare maganar tana duban Lulu da ke saurarensu. Jin jina kai Lulu tai da faɗin, “Hakane Aunty, to amma miya kawo matsalar har haka? Sa’id ɗin bashine na gani a wajen bikin nan ba anata kai da kawo da shi?”.

      “Shine fa…..” nan ta kwashe komai ta sanarma mata. Sosai Lulu tai mamaki, sai dai kuma hakan baizo mata baƙoba dan sun sha cin karo da irin waɗan nan case ɗin wasu ma sai iyayen mijin sun illata yaran saboda ƙiyayya, wasu ko yaranne fitsararru, sannan kakarsu Dada ita kanta fitinanniyar mace ce da tasan tana ƙuntatama matan kawun nanta matuƙa. Duban Smart tai da faɗin, “To amma shi miyasa bazai zauna yay magana ta fahimta da mahaifiyarsa ba, ko kuma yabar gidan nake ganin hakan zai basu masalaha idan basa ganin juna ai Aunty, ko za’a dinga samun matsalolin ba kamar suna zaune waje ɗaya ba”.

       “Kowama haka yake faɗa Mawaddat, to amma maman ce taƙi yarda wai zasu barta a kaɗaici. Shi dai mijinki shi ya kamata yay haƙuri a duba kodan Sa’id ɗin” ta ƙare maganar da kallon Smart.

         Shiru kamar bazaice komai ba sai kuma ya ɗan nisa. Cikin ɗage kafaɗa ya ce, “Aunty Bilkisu bawai zaman nata nima namin daɗi bane, sai dai kuma bazan barta ta koma ba haka salin alin, inada shiri nima dan dolene sai mahaifiyar Sa’id ta fahimci kuskurenta ko kuma ya raba musu gidan, inada hikimata na tsaiwa akan hakan dan har mahaifinsa ya dawo sannan”.

      Cikin gamsuwa Lulu ta ce, “Hakan da yayi ɗin shine dai-dai, inba hakaba komawar tata haka nan babu wani mataki zai cigaba da bada damar faruwar fiye da haka a tsakaninsu……”

      Haka suka cigaba da tattaunawa har su Hawwah suka kammala girki. Wani abu daya saka Lulu farin ciki lokacin da su Aunty Bilkisu sukai zaman cin abincin da suka zuba a tray ɗaya sai ta tsaya kallonsu musamman da Smart ya ɗakko nasa spoon yazo tsakkiyarsu ya zauna yana faɗin “Ni sai a ware ni”. Abune da bata taɓa gani a gidansu ba, itama saita tura baki gaba tace, “Ni baku so naci da ku saboda ba Ammah ta haifoni ba”.

      Da sauri aunty Bilkisu ta kamo hanunta ta zaunar kusa da ita kusa da Smart kuma ɗan shine a gefenta, har suna haɗa baki ita da su Hawwah wajen faɗin, “Karkisa Ammah ta dafamu a tukunyarta da jin wannan kalamai”. Murmushi tayi kamar yanda shima Smart ke kallonta ta ƙasan ido yana yi, sai tana mai jinta kamar sabuwar halitta a yau. Lulu da bata damu da abinci ba yau kam saita saki jiki ta ɗan ci. Da son neman magana Smart ya ɗauki naman gabanta, hararsa tayi da tura baki itama ta ɗauki na gabansa batare da tace komai ba, kallonta yay yana ɗan zaro ido ya ce, “Miye kuma na ɗauka min nama Madam?”.

        “Nawa daka fara ɗauka naka ne”.

    Itama ta faɗa cikin ɗam murguɗa baki kaɗan. Kai kawai ya jinjina alamar zan rama, su dai su Hawwah sai gimtse dariya suke. Can Lulu ta sake ɗaukar naman gaban nasa ta rufe da abinci, sarai ya ganta sai baiyi magana ba sai da ya shammaceta ta ɗakko zata kai baki caraf ya ɗauke sa daga spoon ɗin nata ya lunƙuma baki.  “What!” ta faɗa tana kallonsa, miƙewa yay da mata gwalo yabar wajen dan ya ƙoshi daman. Da gudu su Maryam suka tashi suna dariya. Lulu ta dubi Aunty Bilkisu kamar zatayi kuka ta ce, “Aunty kin ganshi ko? Shi baiso a zauna lafiya kullum sai anyi faɗa yake jin daɗi”.

      Aunty Bilkisu dake danne dariya da ƙyar ta harari Smart da dafa Lulu da itama ke hararsa ta ce, “Kinga ƙanwata barsa zamu rama. Tsarabar dana kawo takine ke kaɗai nama fasa bashi”. Murmushi tai da sake hararar Smart itama ta masa gwalo da faɗin, “7-6”. Ƙwaɓe fuska ya ɗan yi shima da yin ƙwafa ya ce, “Ki jira game over. Aunty kuma gaskiya ba haka akeyi ba”.

     “To ni haka zanyi”. Cewar Aunty Bilkisu tana hararsa. Sai kuma ta kalla Lulu, “Kin san wani abu shi fa dama Hydar akwai zura tun yana yaro, idan aka zuba abinci aka bashi sai yace shi bashi yake so ba na Ammah yake so, idan aka bashi sai kuma yace (Ni wannan ina co) ya sake nuna namu, nan ma a bashi sai ya sake nuna wani nanma yace shi wannan yana co, hankalinsa bazai sake kwanciya ba sai yaga kaf abincin an tara masa gabansa zai bar kunnen kowa ya huta kuma fa ba ci zaiba.

       “Kai aunty miye na faɗa mata kuma” Smart ya faɗa cikin shagwaɓa. Aiko mi Lulu zatai inba dariya ba. Sai ta kallesa tace “Ni wannan ina co” ta ƙyalƙyale da dariya. Sai da takai ya kwashi filos ya fara jefa mata ta tashi da gudu tana cigaba da faɗa. Dole aunty Bilkisu ta dara itama tana sake jin ƙaunar Lulun a ranta. Waɗan nan abubuwan sun matuƙar ɗauke ma Lulu kewa da sakata a farin ciki a wannan yinin, yayinda gefe ɗaya ta takurama Smart da faɗin ‘Ni wannan ina co’ har bayan tafiyarsu. Shima sai abun ya koma bashi dariya dan ya fahimci ta samu abin yi………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣5️⃣

……..Washe gari bayan ya dawo motsa jikin safe da yake fita yace ta shirya zasu fita, da mamaki ta dubi agogo da faɗin, “Da sassafen nan? Ko 8 fa batai ba”.

        Shima agogon ya kalla sai kuma ya dubeta. “Ina ganin kafin mu kammala shiryawan tara ma zata iyayi, dan inada abune mai muhimmanci shiyyasa nake son mu fita da wuri”.

      “Wai ina to zamuje?”.

   “Idan mun fita ai zaki gani, ke dai ki shirya”. Ya faɗa yana ficewa, kitchen ya nufa ya sake ɗaukar ruwa ya sha sannan ya nufi bedroom ɗinsa ya cire kayan motsa jikin dake jikinsa ya faɗa wanka. Itama a ɓangaren Lulun wankan ta tashi ta shiga, dan dama dai tana duba karatun da ya ƙara mata ne kafin fitarsa training. Harga ALLAH tana jin daɗi da farin cikin karatun da sukeyi na addini, abinda kuma ke sake zaburar da ita akan hakan watarana akan wani case an gayyaceta hira a gidan wani tv tare da wani lawyer da basa shiri sam saboda duk karon da tai da shi a shari’a sai ta kaisa ƙasa. A cikin hirar kawai ɗan jaridar sai ya sakko wata magana data shafi addini, amma sai ta kasa amsa masa dan bata sani ba, sai shi lawyer ɗin ya amsa da karsashi da son nuna isa har yana mata shaguɓe akan bata da ilimin addini. Abin ya mata ciwo, tun a lokacin kuma tayi ƙudirin fara neman ilimin sai dai bata san tayaya zatai hakan ba, sannan bata da shaƙuwa da wani a ƴan uwanta da zata iya kawo zancen ta yanda za’a fahimceta, na biyu rashin barin abu a rai da take da shi ya sata tattara abin ta ajiye gefe ta cigaba da sabgoginta. To bayan fara karatun nan da Smart ke koya matan sai ta fara fahimtar abubuwa da dama, sannan tana jin wani nutsuwa da jinta daban da dacan duk da bawani nisa sukai ba can sosai, dan ma dai ƙwaƙwalwarta mai saurin ɗaukar abu ta taimaka mata matuƙa. Kamar yanda ya faɗa sun kai kusan ƙarfe taran, dan sanda ya fito bayan ya shirya koda yaga kayan data saka kai tsaye yace mata ta sakesu. Taso masa gardama amma sai yace tayi haƙuri gidansu fa zai kaita ta gaida su Ammah kuma can zata yini sai dare. A take yaga farin cikinta ya bayyana, dan ita dai tunda Asma’u suka bata labarin yanda Ammah ke sonta da bibiyar abinda take yi sai take jin ɗokantuwa da sake ganin Ammah ɗin duk da a waccan zaman na kwana ɗaya da aka kaita gidansu bazata ƙarar da fuskar kowa ba. Kanta tsaye ta ce, “To dan ALLAH zoka tayani zaɓen wanda zasuyi”.

       Idanu kawai ya zuba mata sai kuma ya saki murmushi zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama. Baiyi zaton zata nuna ɗokin sake zuwa gidansu ba tunda ta kwana a ciki taga yanda yake. Ya fahimci gane wacece ita kai tsaye abunne mai wahalar gaske, dan idan ya gama haddace nan ya buɗe mata sabon shafi sai yaga nan ɗin ma dai akwai abubuwan ban mamaki a cikinsa fiye dana baya daya baro.

          Da kansa ya zaɓa mata kayan kamar yanda ta buƙata. Atamfa mai ƙyau da akaima ɗinkin zani da riga, sai hijjab. Anan ne ta ɓata fuska da ɗauke hijjab ɗin gefe ta ajiye ta ɗauka gyale. Zaiyi magana ta marairaice fuska. Shiru yay baice mata komai ba ganin gyalen nada girma. Sai kuma wajen ɗaura zani ma wata sabuwa. Dan Lulu bata iya ba, da tayi-tayi taga ta kasa saita shiga ƙwala masa kira dan sanda zata saka kayan catai sai dai ya fita, shi kuma baiyi musu ba ya fita ya tsaya a ƙofa. Kiran nasa da tai ya sakashi dawowa. Cikin ɓata fuska ta ce, “A canja wasu gaskiya”.

        “Saboda mi”.

     “Toni na iya ɗaura zani ne”.

  Dariya taso ƙwace masa amma ya danne. Ya ƙarasa shigowa ciki yana faɗin, “Kin yarda na ɗaura miki?”.

    Shiru tai kamar mai tunani, sai kuma ta ɗan hararesa da faɗin, “To wlhy ka rufe idonka, dan inka kallan ban yafe ba”.

          “Oh hakama zaki ce daga taimako?”.

      Baki taɗan murguɗa batace komai ba. Shi kuma sai yay murmushi kawai da ƙarasowa inda taken dan bai son ya biye mata Coach nacan na jiransa. Da taimakonsa ta ɗaura zanin duk da anata masa masifar ya rufe ido kuma karya taɓa mata jiki, duk da yana da abubuwan faɗa baice komai ba shi dai. Ɗaurin ɗan kwali ma bata iya ba. Cikin dafe kai ya ce, “Naga takaina, na auri bahaushiya a zahiri amma bata da banbanci da turawa ni Aliyun Ammah”.

    Harara ta zuba masa ta figi handbag ɗin ta da mayafi ta fice. Sai wata leda da bai san ko minene a ciki ba hartayi gaba ta dawo ta ɗauki kayarta. Bayanta yabi yana dariya da faɗin, “8-6 kenan”.

        Sai da ta hararesa ta ce, “Kama isa. Wlhy 7-6 na sani”.

    “K matsalata da ke rinto, garama ki yarda kinyi game over”.

   “Never give up wlhy, mai sama da hundred ne yay wining”.

  Ta amsa masa nan ma tana hararsa. Ita ta fara fita, shi kuma ya kashe kayan wutar dan an haɗa musu tv yanzu ya kullo ƙofar ya fito. A jikin motarta ya ganta tsaye, sai ya ɗauke kansa ya nufi gate. “Ina kuma zaka je?”. Ta faɗa tana kafesa da idanun ta. Kansa tsaye ya bata amsa batare da ya juyo ba. “Zan sama mana Napep mana”.

     Da mamaki ta ce, “Napep kuma? Ita kuma wannan motar fa? Ni malam bana son ƙauyanci kazo mu wuce danni kam bana hawa Napep. Bamma taɓaba”.

      “Sai ki fara da ga yau”.

   Ya amsa mata yana yin gaba. Tana nan tsaye mamaki da jinjina girman kansa na cimata zuciya, dan ita abinda ta fassara kawai kenan a al’amarin nasa sai gashi ya dawo, baice da ita komai ba ya ɗauka handbag ɗinta da ledar nan ya dubeta da faɗin, “Muje”.

    “Aliyu!”.

  Ta faɗa cikin kaiwa ƙarshen mamakinsa. Amma sai ya ɗaga mata hannu da nuna ƙofa alamar suje. “Sai dai ka tafi kai ɗaya dan gaskiya bazan shiga Napep ba, kaje zan sameka acan”.

        Wani ɗan lumshe idanunsa yay na gundura da maganar a taƙaice ya ce, “Zan ɗauke ki har ƙofar gidan ba ruwana. Dan na faɗa miki ana jirana ko”.

         Yanda yay magana a dake babu alamar wasa ya sake sata tsira masa ido. Sai kuma shawarar da zuciyarta ta bata na ta bishin koba komai yau ta ɗan fita tasha iska ya sata ture komai gefe tai gaba yabi bayanta yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya. Lulu naji na gani a karo na farko na tarihin rayuwarta ta shiga Napep. Sai kuma taji hakan ya sakata a farin ciki batare da tayi zato ba, ga wata iska mai daɗi na rsatsaka tako ina. Sannan kai-kawon mutane da yanda kowa ke sha’aninsa musamman masu tallar abubuwa akan titi yay matuƙar ɗaukar hankalinta da sakata jin tausayinsu. A karon farko zuciyarta ta bata talaka na wahala akan taro da kwabo a ƙasar nan. Wani ɗan yaro da ke tallar papcorn ta yafito da hannu sanda suke tsayawa cikin wani gajeren holdup. Bazai wuce shekara goma sha huɗu ba.

     “Hajiya guggurun na nawa kike so?”.

   Yaron ya faɗa yana ƙoƙarin yago ledan guggurun a jikin ƴan uwansa. Dakatar da shi tai da faɗin, “No ba shi nake so ba. Miya hanaka zuwa makaranta kake nan kan titi?”.

      Ɗan jim yaron yay kamar bazaiyi magana ba, sai kuma ya kalleta ya sake kallon Smart da ke kallonsu kawai batare da ya tanka ba. Muryarsa da alamar damuwa ya ce, “An koroni ne dan Abbana bai biya ba tunda na gama aji uku wai baida kuɗi.”

      Idanu ta zaro na mamaki. Sai kuma ta ce, “Kaga yanzu a titi muke ina ne gidanku?”.

          “A kwana uku muke”.

      Handbag ɗinta ta ɗauka ta ciro jota da pen ta miƙa masa. “Kaga samun Number wayan mamanka anan idan ka sani”.

         “Sai dai na yayata, Umman mu wayanta ya faɗa ruwa”.

       “Idan ba damuwa sakamun ta yayar taka”. Da murna sauri-sauri yaron ya saka dan an sakesu. Ya miƙa mata. Amsa tai da miƙa masa 2k tana murmushi. Da ga haka suka wuce. Mai Napep da ke kallon komai yay ƴar dariya da faɗin, “Hajjaju idan irin waɗan nan yaran kikace zakiyita amsar lambarsu dan basuje makaranta ba aiko zaki amshi sama da miliyan goma a garin nan. Bayan ƴan gari akwai ƴan cirani kamarsa-kamarsa ba adadi. Su dama sauƙi tunda suna neman na kansu ai, wasu kamarsun rashin karatun kesa abokan banza jan ra’ayinsu su faɗa ƙwacen waya da tare yaran da aka aika a lungu su amshe kuɗin. Ko kiga sun faɗa harkar shaye-shaye yara ƙanana kaga yaro na zuƙar maka tabar wiwi ƴan iskan banza iyayensu sun haifa mana bala’i”.

     Wani irin harbawa zuciyar Lulu tai akan zancensa na ƙarshe. Sai taji bakinta yayi nauyi tama gagara cewa komai, sai ɗagowa da tai ta ɗan dubi Smart da yay kicin-kicin da fuska yanzu kam yana ma mai napep ɗin wani shegen kallo. Aiko sai taji mai Napep yay tsitt yana ɗan satar kallon Smart ɗin ta mirror. Har suka iso fagge zantukan na mata juya-juya a zuciya da kartar mata rai. Ba komai ya kawo hakan ba gareta sai tuna itama fa ta fara shaye-shaye ne tana da shekara goma sha uku a duniya. Har ƙofar gida aka kaisu, anguwar da mutane sosai kasancewar Lahadi ne wasu basa fita, ganin yanda akai musu caa da idanu yana biyan mai Napep ɗin yaja hanunta suka shige ciki. Sun samu yaran duk suna nan, basu kai ga wucewa islamiyya ba gidan caka-kai caka-kai. Sai shigowarsa ta sa mafi yawan yaran yin shiru, masu aiki suka maida hankalinsu ga aikin da sukeyi. Asma’u ce dake shanyar kayan Ammah da suke wankewa ita da Maryam ta taho da gudu tana faɗin, “Aunty Oyoyo Oyoyo. Sassanyan murmushi Lulu ta saki ta riƙo hannun Asma’u da ta noƙe gab da zata iso saboda hararar da Smart yay mata ta fasa rungume Lulu da tai niyya, hararsa tai da jawo Asma’un jikjnta dan sarai taga hararar da yayma yarinyar. Maryam ma tasowa tai da fara’arta tana musu sannu da zuwa tare da amsar kayan hanun Yayan nata. Sai suma sauran yaran dake a tsakar gidan duk suka shima musu sannu da zuwa da gaishesu. Suna ganin sun shige falon Ammah kowa ya nufi kaima uwarsa rahoto dan duk suna cikin ɗakunansu aunty Amarya ce kawai a wajen Abba dan yau itace da shi. Sun sami Ammah na sallar walha, sai Nasreen da ke kuka mamanta ta daketa, yayinda ita kuma Hawwahn ke ƙoƙarin saka turaren wuta a rushin da ta ɗibo………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣6️⃣

……..Itama cikin farin ciki take musu sannu da zuwa, yayinda Lulu ke amsawa tana nufar Nasreen. “Oh oh mi akaima wannan princess ɗin ne haka take ɓarnar hawayenta masu tsada?”. Ta faɗa tana ɗaga Nasreen, zama tai ta ɗaurata saman cinyarta. Itako ta lafe cike da shagwaɓa da kuka ta ce, “Ba Mommy bace ta daken dan na kira Abbana a wayanta”.

    “Ayya Mommy ita bata san mun ɗan ara bane muji muryan Abba. Barta daina kukan bazamu bata chocolate ɗinmu ba”. Tai maganar da share hawayen Nasreen ta ɗauka handbag ɗinta ta ciro chocolate biyu masu daɗi da tsada ta baima Nasreen. Tuni ta fashe da murnar dariya ta kaima kuncinta sumbata cike da farin ciki, sai kuma ta ɗaga musu chocolate ɗin tanai musu gwalo. Hakan ya bama Lulu dariya ta saki murmushi, suma duk sai suka fashe da dariya ƙasa-ƙasa. Dai-dai nan Ammah ta idar da sallanta, batai doguwar Addu’a ba ta juyo fuskarta da murmushi mai ƙyatarwa. Akan Smart da ke zaune kujerar kusa da inda take sallan ta sauke, sai kuma ta maida ga Lulu. Kafin tace wani abu ya saukko a kujerar ya zauna kusa da ita yana gaisheta, ganin haka yasa itama Lulu sakkowa da ga kujerar ta zauna ƙasan carpet ɗin da ke a share tas ga ƙamshi mai daɗi na tashi a falon ta ce, “Ammah ina kwana”. Da sauri Ammah ta girgiza mata kai da miƙa mata hannu murmushin ɗunbin farin cikinta na sake bayyana ta ce, “A’a zonan ɗiyata kinji, taso maza taso gareni”.

    Abin mamaki sai Lulu ta samu kanta dajin kunyar Ammah. Da ƙyar ta iya miƙewa ta nufo inda take, zata zauna ɗan nesa kaɗan nan ma Ammah ta riƙo mata hannu ta zaunar da ita jikinta sosai. Ajiyar zuciya Lulu ta saki hawaye na ciko mata ido, amma sai ta daure kanta a ƙasa ta sake gaida Ammah a karo na biyu. Shi Smart ma da abin ya girmesa kasare kawai yay yana kallonsu. Ammah ta riƙo hanunta cikin nata tana amsawa da kulawa.tare da ɗorawa da faɗin, “Ki saki jikinki ɗiyar albarka nan gidanku ne, ni ɗin ban son ki ɗaukeni mamar mijinki mamaki ce dan yanzu kinfi Hydar matsayi a wajena….”

    Cikin waro idanu da ƴar shagwaɓa ya ce, “Ammah! Hakama zaki ce ina babanki ɗin?”.

   “Kai tafi can ai photo copy ne ba original ba wake ta taka. Anata sabon ɗa waketa tsohon ɗa”.

     Dariya su Hawwah suka saka, Lulu ta ɗago ta masa gwalo da nuna masa 8-6 da hannu. Lips ɗinsa ya cije da ƙaramar harara. A dai-dai nan Mama ta shigo tanama baƙuwa lale marhabun. Itama sai Lulu ta gaidata da girmamawa, Mama ta amsa da fara’a tana sanya mata albarka, dan ita dai barta da rashin mutuncinta idan ya motsa ko Umma ta tunzurata. Amma tanada kirki a lokuta da dama, sannan bata saka ƴaƴa a kishinsu inba taƙure ba.

    Yaranne suka shiga shigowa ɗaya bayan ɗaya suna gaidata kamar yanda Mama ta basu umarni, sai dai a ƴaƴan Umma Mubarak ne kawai ya shigo cike da zumuɗi, dan yaso zuwa gaida amaryar yayan tasu Umma ta taka musu birki akan duk wanda yaje koda a bayan idonta saita tsine masa. Wannan girmamawa da Lulu taga an mata ya matuƙar birgeta, (tana son a girmamata a nuna mata ita mutumce mai daraja) koda Umma ta leƙo itama a gatsine wai tana mata sannu da zuwa da ɗan habaicin basu fara shiga ɗakunan su ba Lulu ba fahimtar komai tayi ba. Hasalima kallo ɗaya taima Umman ta duƙar da kanta dan haka kawai take jin Ammah ta mamaye mata ko’ina. Bata taba jin nauyin mutum da kwarjini kamar yanda takeji akan Ammah ba. Ga tsantsar soyayyar ta data hanga a cikin idanun dattijuwar yasata jin wani irin ƙaunarta ta musamman. Smart da shima yake matuƙar jin farin cikin nutsuwar da yaga Lulu tayi a gaban Ammah ya ce, “Da nasan haka za’amun a gidan nan daban zo ba. Amma ba koma a bani shayi nasha nai gaba. Zaku nemeni ne”.

     “Wake buƙatarka balle ya nemeka anan”. Cewar Ammah da murmushi. Fuska ya shagwaɓe da faɗin, “Ammah! Ammah gara dai ki tarairayeni dan da tsohuwar zuma ake magani”.

   “Ga wanda bai sani ba ba”.

  Ammah ta bashi amsa.

“Shike nan na daina magana. Hawwah bani shayi na ƙara gaba, itama fa ku nema mata abinci bamu karyaba muka fito dan zumuɗinta”.

     Ammah ta ce, “Kai Hydar dan ganganci. Shine kuma maimakon ka kira waya tunkan ku taho a ɗaura muku”.

   “Haba Ammah sai kace wasu baƙi”.

“Baƙine mana. Tunda wannan ne karo na farko data fara marabtarmu dan wancan ba’a sakashi a lissafi. Ɗiyata mi kike son ci”.

     Ƙasa Lulu ta ƙara yi da kanta tana girgizawa da faɗin, “Ammah bana jin yunwa ma, abarshi har sai anjima”.

   “A’a bazai yiwu ba Mawaddatan’warahmah. Ƙarfe goma harta gota ace sai kuma anjima”.

   “Ammah bason cin abinci take ba shiyyasa. Idan kika biye nata ma daga nan har dare zata iya kaiwa”. Smart dake ƙoƙarin kai shayin da Hawwah ta kawo masa bakinsa ya faɗa. Ɗan harararsa Lulu tai ƙasa-ƙasa bata dai ce komai ba. Shi kuma yay mata murmushin da take kira na mugunta.

   Yana kammalawa ya miƙe da faɗin shi zaije ya gaida Abba ya wuce, sai anjima zai dawo. Addu’a Ammah tai masa da ta ratsa zuciyar Lulu matuƙa harta tsira musu ido. Karo na biyu yaji wani abu ya tsikarar mata zuciya game da ilimin addini, sai kewar mahaifiya data ratsata, itama fa da Mah-mahn ta nada rai da haka zata dinga mata ko? Sai hawaye suka cika mata idanu. Su Ammah daba lura sukai ba Smart ta ɗan dubeta cikin jin nauyin Ammah ya ce, “Madam na barku lafiya, duk abinda kike buƙata karkiyi fillanci Ammah taki ce.”

    Kanta ta jin jina masa tana ƙoƙarin maida hawayenta. Da ga haka ya fice ya barsu….

   Cikin ƙanƙanin lokaci aka shiryama Lulu breakfast, yayinda gidan ya ɗauki shiru su Asma’u ma sun wuce makaranta. Ammah nata janta da taɗi itako tana bata amsa cike da kunya har Hawwah ta kammala tazo ta zauna. Sai Ammah tace suje ɗaki ko zata fi sakewa ta karya kafin suje ta gaida Abba da matan gidan dan yau dai ba fita zaiyi ba. Jin haka yasa Lulu cewa bari taje ta gaida Abban dan bata jin yunwa. Hakan yasa Ammah jin daɗi, dan haka ta miƙe da kanta domin rakata wajen Abban. Hawwah kuma ta shiga tattare kayan tana maidawa ɗakinsu…

    Sosai Abbah yayma sabuwar surukar tasa tarbar mutuntawa kamar yanda yake ma sauran. Yayinda Lulu shima ta kasa ko kallonsa dan tsohon ya mata kwarjini sosai. Shima ta gaidashi da girmamawa ya amsa mata da kulawa da sanya albarka. Sannan ya ɗora da addu’a zama lafiya a gare su Ammah na amsawa da Amin cikin murmushi. Basu jima sosai ba dan sunga Lulun dai kunyarsu ta sata kamar takura suka fito bayan ta ajiye masa leda madaidaiciya mai ɗauke da turarruka masu tsada da ƙamshi, sai agogo. Da sauri Abbah yace, “A’a ɗiyata maza zoki ɗauka. Gaidamun ma da kuka zo kawai ya wadatar mun kumayi farin ciki”. Marairaice fuska Lulu da kanta ke a ƙasa tai da faɗin, “Abbah dan ALLAH karkace haka. Mu albarkanku muke nema, indai bazan sayama Daddy abu dan neman albarka ya dawo min da shi ba kaima haka nake fata daga gareka”. Abba dake murmushi sai ya jinjina kansa da nisawa. Ya ce, “ALLAH yay miki albarka. ALLAH ya tsare gabanki da bayanki….” ya dinga jera mata addu’oi masu ratsa zuciya Ammah na tayashi kafin suka fito.

    Anan kam saita kira Hawwah akan tazo ta raka Lulu kowane ɗaki. Hawwah ce tai mata rakkiya, inda suka iske Umma cike fam, amma saboda shawarar da Hajiya Naqiba data kira ta labartama mata zuwan su Lulun yasata dannewa ta tarbeta da fara’ar yaƙe, ita kuma Lulun sai ta kasa sakin jiki da ita dan ita kam dai haka kawai taji Ummah batai mata ba, basu wani jimaba Lulu ta ajiye mata ƙaramar leda ta miƙe, sai hakan kuma ya sake zafar Umma. Ɗakin Mama ma an mata tarba ta mutuntawa, nan ma sai sukafi ɗakin Umma daɗewa, dan duk da Mama taji hassadar kasancewar wannan zukeƙiyar yarinya ƴar masu kuɗi ba wani acikin ƴaƴanta ya samu ba ta danne a ranta ko a fuska bata nuna ba, sai godiyar ledar da Lulun ta ajiye mata ya shiga jerawa. Ɗakin aunty amarya kam tarba suka samu kamar wata ƙawa. Dan tsokanarta ma taitayi suna dariya. Sunfi jimawa anan fiye da ko’ina kafin su koma ɗakin Ammah bayan itama ta ajiye mata ledar, bakuma komai bane aciki sai kayan turaren wuta data ɗiba musu da su cin-cin. Itama Ammah ta kawo mata harda turmin zani biyu su Asma’u kuwa kayan kwalliya ta basu jiya da sukaje. Basu zauna a falo ba suka nufi bedroom ɗin su Hawwah ɗin inda ta maida break fast. Duk da Hawwah zata iya ɗan girmar Lulu da ko shekara biyu ne jikinta ta saki da matar yayan nasu, hakan sai ya saka Lulu sakewa abunta dan wayayyace dama kai babu duhu. Duk da ba son cin abincin take ba sai gashi ta saki jiki sunci tare da Hawwah suna hira cikin mutuntawa, anan ne ma Lulu ta samu damar sake jin matsalar Hawwah ɗin sosai, a ranta kuma ta ɗauki ƙudirin taimaka mata, dan haka ta amshi address ɗin gidan nata a cikin hikima batare da Hawwahn ta fahimta ba. Bayan sunyi sallar azhar falo suka dawo wajen Ammah, cikin hikima taita jan Lulu a jiki ganin bata sakewa idan suna tare, da yake abune daga cikin abinda take ƙishirwar samu sai gashi ta saki jikin nata fiye da yanda sukai zato, dan hirar tasu ne ta karkata akan yanda matsalolin fyaɗe ke ƙara yawaita da yanda wasu ma yaran kan rasa ransu a take ko a cutar da su ta hanyar saka musu cuta, da yanda wasu iyayen kan rasa ransu adalilin hakan kosan ɓoyewa saboda kar duniya taji ƴaƴan su tozarta da su kansu. Lulu ta ce, “Wlhy Ammah nakanji kamar na dinga kashe irin waɗan nan aladun da hannuna, akwai case ɗin wata yarinya da har yanzu yake cimun rai duk da shegen na prison kusan shekara uku kenan, danni duk wanda nasan na samu nasarar alƙali ya turashi prison akan wannan laifin cigaba nake da bibiyasu a prison ɗin dan karma ayi amfani da wata dama a sakesu ina nan baki buɗe. Yarinyar tana nan ta zama mahaukaciya kamar yanda Nanny ɗina ta kasance kafin mutuwarta….”

    Wasu irin hawaye suka zubo mata masu azabar zafi saboda tuna mata da abinda ya shuɗe kuma yake sosa mata zuciya da zama sanadin komai da ake kallon zagaye da rayuwarta a yanzu………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

   𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣7️⃣

……..Yanda take kuma ya tadama Ammah hankali matuƙa, ta dawo kusa da ita da jawota jikinta ta rungume tana jin itama hawayen na cika mata idanu. Yanda Lulu ke kukan nan zai tabbatar maka al’amarin na matuƙar taɓa mata zuciya, dan har Hawwah sai da tai hawaye. Sosai Ammah taji ƙarin ƙaunar Lulu a zuciyarta. Sai da tai shiru sannan ta fara mata nasiha da bata addu’oi akan ta dage ta dingayi da yawaita karatun Alkur’ani hakan zai dinga rage mata nauyin zuciya, dan masu irin ayyukansu saboda yanda suke tara abubuwan ɓacin rai da damuwar al’umma daga ƙarshe sai kiga sun kamu da hawan jini dana ciwon zuciya. Sosai yanda Ammah ke jero addu’oi a bakinta taji ta sake birgeta da kwaɗayin akan samun ilimin addini. A haka su Asma’u suka shigo ƙarfe biyu. Da mamaki Ammah ke dubansu dan tasan dai sai biyar suke dawowa daga islamiyya duk ranar weekend. Hawwah ta ce, “Kukuma fa naga kun dawo?”. Kallon juna sukayi kafin Maryam tace, “Adda haddace bamu iya ba shine muka gudo, kin san dai malam Jabeer ba sauƙi wlhy”.

   Ammah data tsira musu ido tace, “Duk karatun da kukai ɗazun da asuba. Kudai faɗi wani ba wannan ɗin ba. Wai Maryam yaushe ma kika fara ƙarya?”.

   Ƙasa Maryam tai da kanta tana shafa ƙeya, Asma’u dake ƙara rakuɓewa jikin kujera ta ce, “Ammah gaskiya da gaskiya dai saboda Aunty muka gudo, kinga fa yini zatayi amma mu banda mu. ALLAH muna son muma mu yini tare da ita shine mukai shiri tare da Adda Maryam idan akai salla muyima Malam Jabeer ƙaryar zamu rakaki asibiti”.

     Hawwah dake dariya tace, “ALLAH ya shiryeku Ammahn kukai ma sharrin ciwo kenan?”.

   “A’a wlhy mu bamuce kowa ba, kawai dai munce zamu rakata asibiti”.

      “Kuma ya yarda? Bayan nasan Malam Jabeer da shegen bin ƙwanƙwanto”.

   Dariya Asma’u tai tana kallon Maryam, ita kuma ta harareta alamar dai akwai wata a ƙasa. “Munafukai mi kuke ɓoyewa?”. Cewar Hawwah tana kallonsu cikin waro ido. Alamar zip Asma’u taima bakinta da faɗin “Ba ruwana ba’a bakina ba”. Lulu da ke murmushi ta ce, “Haba Auta bamu musha mana”.

     “Aunty ba faɗar bane matsalar, sai kun gudu gidajenku ta jibgan a ɗaki ko Ammah bazata bari ta sani ba”. Ranƙwashi kuwa Maryam takai mata. Da gudu tabar wajen tana dariya. “Sonta yake ya kasa gaya mata, gashi kuma ya tsaya kallon ruwa kwaɗo yay masa ƙafa. Dan ga wani tauraro mai babban haske ya faso kai da ƙarfinsa”. Binta Maryan tayi suka shige ɗaki da gudu. Kai kawai Ammah ta girgiza da faɗin, “ALLAH ya shiryeku”. Yayinda Hawwah da ke dariya ta ce, “A gama ɓoye-ɓoyen intai wari maji ai”. Lulu dai murmushi takeyi dan komansu burgeta yake yi. Bakomai ya jawo hakan ba kuwa sai yanayin rayuwar data tashi a ciki ita da nata ƴan uwan. Bayan su Maryam sun cire Uniform suma falon suka dawo aka ɗora hira, anan sukaci abincin da aunty Amarya ta gama, bayan sallar la’asar Maryam tai zaman yima Lulu kitso. Dan nakan Hawwah ta gani ya burgeta ta tambaya duk da ba son kitso take ba. Jin Maryam ce tayi sai tace itama aimata ko kaɗan. Shine sukai zamanyi suna cigaba da hira harda Ammah. Nasreen da suka dawo daga makaranta tana zaune a cinyar Lulu suna shan chocolate dan itama shazumamun ce kamar Lulun. Sallamar Smart ta sakasu tsagaita dariyar da sukeyi dan Asma’u ce ke kwaikwayon Muryar malaminsu Jabeer dake son Maryam wai idan ya ganta har ƙara maƙewa yake yi. Akan Lulu ya fara sauke idanunsa kafin yabi sauran da kallo, ya ƙarasa takowa cikin falon yana kaiwa zaune da faɗin, “Miyay muku daɗi haka kuke kwasar dariya har tsakar gida kun cikama mutane kunne? Ammah duk sun zagayeki sun dameki”.

    Cikin murmushi ta ce, “A’a basu damen ba Hydar, ai ko kurama da ƴaƴanta take wasa a jeji. Sai yanzu muke ganin ka”.

  “Wllhy ki bari dai Ammah. Da ga wani waje mai nisa muke fa, kin san Ahmad da shegen kutse-kutse can wani ƙauye ya samo gona zai gyara yay gidan gona a wajen shine fa mukaje dubawa”.

      “Kai masha ALLAH, ai haka mukeso mu kuyita shiga irin hakan dan nan gaba kaɗan kune manyan goben.”

   Murmushi yay cikin jinjina kansa. Kafin ya maida hankali ga ƙannensa da ke gaishesa. Idon Ammah ya sa Lulu faɗin, “Sannu da dawowa”. Sai da ya maimaita kalmomin guda uku a zuciyarsa yana mai ɗan kafeta da kallo, sai kuma ya janye shima cikin basarwa ya ce, “Yauwa ya gidan”.

    Abinci Asma’u taje ta kawo masa, sai cewa yay ta maida baya jin yunwa, garama in sunada fura dan yasan dai Ammah bata rabo da ita. Asma’u tace masa akwai, taje ta ɗibo masa a fridge ta kawo masa. Daga haka suka cigaba da hirarsu Lokaci-lokaci yana satar kallon Lulu da akema kitso masu ƙyau. Wajen shida ya kalla agogo da faɗin, “Ku wannan kitson yaushe zaku gama shi har mu wuce? Gashi ina son mu biya ta wani wajen”.

    “Ina? Ai ni nan zan kwana yi tafiyarka”. Cewar Lulu da iya gaskiyarta. Murmushi Ammah tayi, yayinda Smart dake mata kallon mamaki ya ce, “Kwana fa? Kin manta gobe Monday zakiyi resuming office?”.

   “Ba damuwa jibi naje”.

  Murna su Asma’u suka fara yi zata kwana. Ya hararesu duk sai suka nutsu. Ammah dai bata ce komai ba har sai bayan sallar magrib da ya shigo ya sameta a ɗaki, lokacin su suna can ɗakin suna tasu sallar. Zama yay kusa da Ammah, hakan yasata yin addu’a ta rufe Alkur’anin. “Ba dai tafiyarba ko?”.

    “Da haka nake so dai ta shirya, da anyi isha’i sai mu wuce dan ina son mu biya ta gaida Kakanta ɗazun Uncle Yousuf ke faɗamin baya jin daɗi ya dawo daga Legos ɗazun, gashi kuma tana batun kwana anan”.

   “Karka damu zan mata magana. Amma Aliyu sai nake ganin akwai wani ɓoyayyen al’amari a rayuwar yarinyar nan dake damunta, na fahimci hakanne a ɗan firarmu da ita ta ɗazun. Sannan bata son kaɗaici, dan ta roƙeni na baku Asma’u ta koma can da zama. Danace mata Abbanku bazai yarda ba ina kula da ita sai da idonta ya cika da hawaye. Mizai hana a ɗan samo mata ko tsohuwa haka da zasu zauna tare, sannan kai kuma ka ƙara ƙaimi wajen janta a jiki dan ka fahimci minene damuwarta. Ko yaya ta sanar maka itama zataji nauyin ya ragu mata a zuciya. Ashe mahaifiyarta bata raye kuma?”.

    “Ta rasu, tana haihuwarta. Inasha ALLAH zan yi iya ƙoƙarina”.

  “ALLAHU akbar. ALLAH ya gafarta mata. Wlhy duk sai yarinyar ta sake bani tausayi. Gata da sauƙin kai da sanin darajar mutane. Sai kuma yanda na fahimta akan aikin nan nata kamar zafinta akan al’amarin fyaɗe nada alaƙa da wani abu daya sosa ranta gaskiya. Ya kamata dai ka zama mai haƙuri da dinga ƙarfafata”.

    “Insha ALLAHU Ammah zan yi iya ƙoƙarina. Batun Asma’u kuma haƙuri zakuyi ta koma can ɗin tunda tana son hakan. Kodan ma tafiyar nan dake tunkarowa.”

  “To bazance A’a ba, amma ka samu Abbanku da maganar kadai sanshi. In akan tafiyane kuwa bazai yiwu dama a barta ita ɗaya ba. Ko ita da Asma’u kawai dole cikin samarin nan wani ya koma can ya dinga kwana da su”.

     “Hakan ma yayi Ammah. Duk yanda kikace haka za’yin”.

  Sun ɗan ƙara tattaunawa akan abinda ya shafesu musamman akan Hawwah, kiran sallar isha’i ya sashi tashi ya fita. Bayan ya dawo sai da Ammah ta lallaɓa Lulu da wayo sannan ta yarda su tafi. Yanda take zubama Ammah ɗin shagwaɓa sai Smart ya zama ɗan kallo. Dan mamakin yanda tai bala’in sakin jiki da Ammahn yake yi har irin haka a ƙanƙanin lokaci. Koda tajema su Umma sallama har yanzu akwai alamar takaicin ƙyautukan data raba musu ɗazun a tattare da ita. Dan kusan ma a tashin hankali ta yini, ga surukar jiya-jiya a gida daga zuwa tana neman fara haskawa, yarinya da baƙin wayo. Ai zama bai ganta ba, dan kuwa kamar ta kashe maciji ne bata dare kansa ba kasancewar Lulu matsayin surukar gidan nan na nufin disashe tauraron ƴaƴanta da ake gani sama dana kowa. Oho Lulu ba damuwa da sabgar da ba’a sakata ba gareta, dan haka ita bata wani fahimci mi Umman ke ciki ba, dan ko kallon su Huwaila dake falon batai ba. Haka kawai jininta dana Umma baizo ɗaya ba, da ƙyar ma ta yarda ta biyo Smart ɗin suka shigo da tace yaje ita zata je ɗakin Aunty Amarya ya sameta ya nuna mata dole ta shiga ko’ina suyi musu sallama. Ganin babu wasa a tattare da shi yasata bin nasa badan taso ba. Daga wajen Umma sai ɗakin Mama. Nan ma basu jimaba suka fito, nan ko Mama ta bata alawar madara da Hannatu keyi ta saidawa. Hakama aunty amarya ta bata farar data soya mata da rana har kwano biyu. Aiko taji daɗi tanata godiya. Abba ma sunyo masa sallama ya haɗa Lulu da tsarabar zuma da mazarƙwaila kasancewar sa masoyinsu yana ajiyewa. Sai da zasu shiga napep Maryam ta ajiye mata ledar tsarabar Ammah. Duk sai Lulu taji ƙaunar bayin ALLAHN nan na sake ratsata. Shi kansa Smart yaji daɗin wannan karamci da sukai mata. Kasancewar mai Napep ɗin ɗan anguwarsu ne zai kaisu har gida da inda ma zasuje kai tsaye ya nufi Nasarawa G.R.A dan Smart ya riga ya sanar masa tun kan Lulu ta fito. Ganin inda suka nufo ya sata jin farin ciki, a Napep ɗin suka bar kayan suka shiga cikin gidan na Alhaji Sufi Ado Garko. Sun sami yaran gidan da jikoki da yawa, inda kowa yay musu ca aga yaya Lulun ta koma. Sai kuma suka ganta fes har wani ƴar ƙiba kamar ta ƙara musu ma su a ido. Alhaji Garko dake kallonsu da murmushi ya nunama Aliyu kusa da shi. Maimakon hakan sai ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafunsa ya gaidashi cikin girmamawa da tambayar yaya jiki. Da kulawa ya amsa masa da sanya albarka. Dada kam sama-sama ta amsa masa tana masa hararar ƙasan ido Lulu na jikinta lafe. Ya gaisa da sauran wanda suke ɗakin suma, daga haka yaja bakinsa yay shiru sai Baba ya takalesa da magana ko tsokana ne yake ɗan murmushi koya bada amsa a taƙaice. Kusan awansu biyu sukai shirin wucewa, anan ne Dada ke cema Lulun “Ku bari sai anjima mana tunda dai mota ce kuma daga nan guda kukai”. Batare da Lulu ta kawo komai a ranta ba ta ce, “Dada a Napep muke fa, babu daɗi mun barsa a waje kusan awa biyu. Kuyi haƙuri zan dawo gobe in sha ALLAHU”.

    A zafafe Dada ta ce, “Napep kuma? To ina motocin naki? Kodan shi baida motar hawan dan bakin ciki irin na talaka kema bazaki hau ba? Kamarki jikar Garko family a garin nan da hawa Napep…”

   Yanda Dadan ke maganar a zafafe da ɗaga murya kowa naji ya saka Lulu duban inda Smart yake, sai kuma ta dubi Dada zatayi magana cikin ɓata fuska amma ta dakatar da ita……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣8️⃣

…….Itama dakatar da itan abinda tai niyyar sake faɗan da tai tana duban Smart da yay kamar baima san akansa ake maganar ba Baba yayi rai ɓace. “Wai miye haka kuma ban son ƙaranta fa. Ke Mawaddat tashi ku wuce gida.”

  Miƙewa Lulu tayi kamar yanda Smart ya miƙe babu alamar komai da zaka iya fahimta a fuskarsa. Sai ma kallon Baban yay cikin girmamawa yay masa sallama tare da sauran jama’ar ɗakin. Wasu sun amsa masa wasu ko nata faman taɓe baki ƙasa-ƙasa yanda Baba bazai gani ba. Koda yayma Dada sallama bata kulashi ba, shima kuma bai nuna ya damu ba yay ficewarsa. Suna fita cikin ƙarfin halin rashin jin daɗin jiki Baba ya balbale Dada da faɗa, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har sai da ta koma bashi hakuri duk da dai fa ta ciki na ciki…..

    Lulu tata satar kallon Smart da tunanin zaice wani abu akan abinda Dadar ta masa amma har sukazo gida baida alamar cewa komai. Bayan ya sallami mai napep ya buɗe musu suka shiga, gaba ɗaya kayan na’a hannunsa har handbag ɗinta ma. Har ɗaki yakai mata kayan sannan ya fita zuwa nashi ya barta da binsa da kallo. Harga ALLAH bataji daɗin abinda Dada tai masa ba. Dan koba komai ita ai daga gidansu take. An kuma girmamata an mutuntata kamar a goyata. Kuma fa duk ta bama Dadan labari a taƙaice amma ta aikata masa hakan. ALLAH ya kaimu gobe zataje sai tai mata magana dan bata son haka. Duk da bata son shi bata kuma tunanin zama da shi bayan na wata ɗayan nan bazata so a wulaƙantashi ba dan itama dai da taje gidansu ba’a wulaƙantatan ba ai. Da wannan tunanin ta shiga wanka.

   Shima a can wankan ya shiga, sai dai duk da ya danne abinda Dadan ta masa yay masa ciwo sosai. Sai dai ya zaɓi shanyewa dan koba komai taci darajar Baba. Sannan bazai taɓa wulaƙantata ba kasancewarta kaka ga Lulu. Bayan yay wankan ya fito shafa’i da wutri yayi sannan ya fito. Shayi ya haɗa a kofi biyu ya nufi ɗakin Lulu da su. Kwance ya sameta rigingine ta ƙurama fanka ido da alamun damuwa tattare da ita. Dan ko sallamar sa bataji ba sam. Zama yay a bakin gadon da yin gyaran murya sannan ta dawo firgigit, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya da tashi zaune. Idanunsa ya janye daga kallon ta yana haɗiyar busashen yawun daya tokare maƙoshinsa dan shi yasan abinda idonsa ya gani kasancewar rigar jikinta ta barci ce mai santsi. Itama sai ta jawo ƴar saman rigar data ajiye gefe ta ɗora akan wadda ke jikinta dan ƙarama ce ma da kaɗan ta wuce mata cinya. Taji kunyar ganin nata a hakan amma dai ta basar. Shayin ya miƙa mata shima cikin basarwar, amsa tai idanunta a kansa, ganin babu dai damuwar da take tunanin gani ya sata jan ajiyar zuciya da faɗin, “Thanks.” kansa kawai ya ɗan jinjina mata. Numfashi ta sauke a hankali sai kuma ta sake dubansa da faɗin, “Kayi haƙuri da abinda Dada tayi, ni ban faɗa mata da wani manufa ba. Ita haka take tana da faɗa ne sosai”.

   Murmushi yay a karo na farko, sai kuma ya ɗan kafeta da idanunsa da suka canja launi kaɗan. cikin tsokana ya ce, “Wajenta kika koyi faɗa kenan?“. Hararsa tayi da ɗan murguɗa baki. Ya sake sakin murmushi da kai shayinsa baki. “Karki damu ai nima kakatace. Ni ban ɗauki abinda tai ɗin komai ba. Yanzu ma magana nazo muyi”. Bai bata damar sake cewa komai ba akan Dadan ya shiga bata bayanan daya ɗan tattara mata game da case ɗin yarinyar can dake a asibiti, sai kawai ji yay ta rungumesa a bazata. Wani irin mahaukacin bugawa zuciyar Smart tayi, jinin jikinsa ya shiga yamutsawa tsigar jikinsa duk ta mimmiƙe. Lulu da bata kawo komai da wata manufa ba game da abinda tai ɗin ba ta ɗago tare da lakace masa hanci tana kallonsa da murmushi ta kashe masa ido ɗaya. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana mai lumshe idanunsa.

   Komawa tai ta zauna da faɗin, “Ashe kana da kirki wani lokacin”. Shi dariya ma ta bashi, sai dai baice komai ba kan hakan ya sake yin murmushi kawai da ɗakko maganar fitarta aiki gobe idan ALLAH ya kaimu ko zai samu daidaiton abinda ke tsikarinsa. Nasiha ya fara mata cikin kwantar da kai da muryarsa data koma ƙasan maƙoshi, tare da faɗa mata dokokinsa akan yanda yake buƙatar ta dinga fita”. Da farko taso daurewa, sai dai jin dokar fita da hijjab har ƙasa ya sata dubansa cikin tura baki ta ce.

     “Hijjab har ƙasa? Ni ce zan saka hijjab har ƙasa, impossible hakan ta kasance, idan mafarki kake ka farka. Wai miyasa kai baka so a zauna lafiya ga son nuna ma mutane gadara akan rayuwarsu? Ka mance wannan auren ba aure bane balle ka dinga tursasani yin abubuwan nan. To ni ko auren gaskiya ace nakeyi bazan zama a ƙarƙashin takalmin namiji ya takani ba, idan zamuyi rayuwa cikin kowa yanada freedom fine, balle wannan auren. Please ka bari kwanakin nan su cika muna masu mutunta juna. Ni harka ma ɓatamin rai na”.

    Kallonta kawai yake yi batare daya fahimci mima take nufi ba, sai dai baice komai ba harta gama. (karku manta Smart bai san da tsarin auren yarjejeniya ba, Uncle Yousuf Daddy da Lulu kawai ya shuka a haka). Tashi tai ta bar masa wajen ta shige toilet dan bata buƙatar abinda zai ɓata mata farin cikin data samu yau a wajen ƴan uwansa, shima sai ya mike ya fita a ransa yana faɗin (akwai ƙura kenan kuwa gobe. Dan shikam wannan tsarinsa ne, ko yau ma ya barta ta fitane da gyalen dan kawai tare zasu fitan, ya kuma san daga gida sai gida kawai….

    WASHE GARI ta tashi da ɗokin fita aikinta, musamman zancen shiga kotu da zasu fara yau akan case ɗin nan. Tsaf ta gama shirinta, sai uban ƙamshi take zubawa dan ta baza turaren nata. Tana ƙoƙarin ɗaura igiyar takalmanta ya shigo ɗakin. Sanye yake da jallabiya ash da bata kai masa har ƙasa ba sosai, sannan gajeren hannu ne da ita. A jikin ƙofar ya jingina tare da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu kawai. Ƙin ɗagowa tai duk da taji shigowar tasa har sai da ta kammala. Koda ta ɗago ɗin ma kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tana miƙewa. Da ga sama har ƙasa ya sake ƙare mata kallo. Yayinda ita kuma ta ƙarasa tattare kayanta ta nufo ƙofar kanta tsaye. Kallonsa tai kamar yanda shima yake kallon nata, a dake ta ce, “Ina kwana bani hanya”.

    Maimakon amsa mata sai ya ɗan kauda idanun nasa a kanta ka ɗan batare da ya motsa ba ko ya tanka. Ta fahimci so yake su maimaita na waccan ranar, ita kuma ba haka take buƙata ba. Dan haka ta danne abinda ke taso mata da ɗan kwantar da murya ta ce, “Please Hydar 9:30 ne shiga court fa, kuma ka sani”.

    Cikin husky voice ya ce, “Idan baƙyason rasa shari’ar ko makarar go and change your dresses. Na faɗa miki duk abinda bakina ya furta shine nake buƙata kuma bana canjawa da ga ra’ayina akan duk abinda na riga na tsara.”

      Cikin ɓacin ran da ya fara yunƙuro mata ta ce, “Aliyu!!…”

  Hannu ya ɗaga mata babu alamar wasa a tattare da shi. Muryarsa vary deep and vary clear ya ce, “Na yanke kuma na zartar, bi kawai shine masalaha Mawaddat. Ke matata ce, nace bana buƙata to bana buƙatar. Kiyi kawai kodan kuma ki sami yanda kike so mu kuma zauna lafiya”.

   Jitai jiri ma na neman kamar ɗibarta. Amma sai batace komai ba tai masa wani irin kallo mai ƙunshe da abubuwa masu yawa ta juya kawai ta ajiye kayan hannunta a saman gadon. Komawa tai wadrobe ta ɗakko hijjab zata saka kawai, amma sai ta tsinkayi muryarsa yana faɗin, “Kayan duk zaki canja zuwa wasu, bana son wannan turaren kuma idan zaki fita, idan zaki saka a gida fine ko zakiyi wanka da shine ba babu damuwa a gareni. Sakawa a fita ne dai bana so dan haramunne ma a gareki ba faɗa ta bace.” bata tanka masa ba, sai kayan data ɗauka ta nufi toilet dan taga baida alamar fita, ita kuma taci alwashin bazata kulashi ba a yanzu saboda abinda ke a gabanta. Tsaf ta sake shiryawa cikin wasu kayan ta saka hijjab ɗin ta fito, sai ya samu kansa da kafeta da ido. Dan tayi ƙyau matuƙa a cikin hijjab ɗin fiye da waccan ranar. Shi da kansa ya ɗibar mata kayan yay gaba tabisa a baya tana taunar lips na danne masifar dake cimata zuciya. Baya ya ajiye mata kayan tare da miƙa mata hannu alamar ta bashi key ɗin motar dake hanunta.

   Rai a ɓace ta ce, “Bana buƙata”.

“Kema kin san aikina ne ai hakan”. Ya faɗa babu wasa shima a tattare da shi. “Aina faɗa maka na kore ka”.

   “Ban koru ba, dan bake kika ɗauke ni aiki ba ai ko”. Ya sake bata amsa a dake yana zare key ɗin tare da jan hanunta ya tura ta kujerar kusa da driver ya maida ya rufe. Zagayawa yay shima mazaunin drivern. Koda yaje gaban gate sai da ya fita ya buɗe sannan ya zo ya fita da motar ya sake komawa ya rufe gidan sannan. Tunda suka ɗauki hanya babu wanda ya tankama wani, gara shi ma ya miƙa mata ƙaramin flaks da ya haɗa mata tea a ciki. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa tana harararsa. Murmushi kawai yay batare da yace komai ba ya maida hankalinsa ga tuƙinsa. Kai tsaye office ya kaita, inda suka samu abokan aikinta suna tsaiwar jiranta duk da safiya ce sosai. Motar na shigowa suka shiga mata marhabun su Zainab na mata spry da ƙyalkyali mai ƙamshi da ga shi har ita. A take aka shiga musu murnar auren. Kamar yanda ya dake yana amsawa itama sai ta dake tana amsawa. Sunci kusan mintina goma a wajen kafin Zainab ta kwashi kayanta suka wuce office, shi kuma sai ya fito bayan sun ɗan yi magana da security ɗin nan da a yanzu suka saba sosai ya samu napep ya shiga ya koma gida………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣9️⃣

…….Alhamdullah yau Lulu zata ce kasancewar abubuwa sun tafi mata yanda take so. Dan duk da zaman shari’ar yau aka fara Alhmdllh tana hango nasara a cikinta. Bayan barin kotu da Hassan yazo ya kaita da kansa office ya sake maidata, ta ɗan taɓa aiki bayan sallar azhar ta fito. Tana jan mota ta fita Security ɗin nan ya dannama Smart waya ya sanar masa. Godiya yay masa sannan shima yay kiran wanda ya saka ya dinga bibiyar masa ita akan yabi bayanta da napep ɗin. Kai tsaye anguwar da mijin Hawwah yake ta nufa, da tambaya ta isa gidansu Sa’id. Mai Napep da ke binta ya kirasa ya sanar masa. Sosai Smart yay mamakin abinda ya kaita, har ya dinga jin son yazo amma dai ya dake da ƙyar dan son ganin iya gudun ruwanta. Sama-sama ta gaishe da maigadin tare da tambayarsa ko hajiyar gidan na nan? Amsa mata yay da eh cikin washe haƙora. Fuska ta yamutse cike da izzarta ta ce, “Sanar mata tana da baƙuwa”. Babu musu ya amsa mata da to yana nufar cikin gidan. Mintinan baifi uku ba sai gashi ya dawo ya ce ance ta shiga.

     Kallon gidan ta dingayi side by side tana taɓe baki, a irin dukiya ta gidansu gidan su Sa’id ɗin ba komai bane ba, sai dai ba laifi suma dai da gani akwai kuɗin sai dai ko kama ƙafarsu basu isa yi ba. Ƙofar da take ƙyautata zaton falon gidan kenan ta nufa, cikin sa’a ma sai ta hango wata yarinya tsaye kamar tana kuka da alama mai aiki ce, isowarta kusa da ita ya sata daina kukan ta risina ta gaisheta. Sau ɗaya ta amsa mata ta ɗauke kanta. Yarinyar ce ta mata iso cikin falon, babbane sosai ya kumaji ɗirka-ɗirkan kujeru kamar bana dattijuwa ba. Kallo ɗaya taima matar dake zaune a falon ta fahimci itace mamar mijin Hawwah ɗin, dan ko’a ido ka kalleta kasan za’a zuba da ita kam. Zama tai kanta tsaye tun kan ma ace ta zauna, maman Sa’id dai kallonta take alamar rashin sani, duk da Lulu ta fahimci hakan sai ta basar, cikin ɗaukar kan nan nata na isa da ƙasaita ta ce, “Hajiya barka da rana. Sunana Barrister Mawaddat Isma’il Jiƙamshi.”

   Sai da zuciyar maman Sa’id ta motsa jin ƴar waye, sannan sunan kansa na Mawaddat ɗin duk mai bibiyar harkokin mata a fanin fyaɗe dole zai santa, ita kanta dama tunanin ina tasan wannan fuskar takeyi. Lulu data lura da hakan ta cigaba da faɗin, “A yanzu haka matar Aliyu M. Idris Mawashi yayan matar ɗanki dan bana tunanin kin halarci bikin sati ɗaya daya shige”.

   Gaba ɗaya Mama duk sai ma taji ta daburce, dan tabbas Sa’id yata roƙarta zuwa bikin amma tace bazataje ba dan ba’a gayyaceta ba, koma an gayyacetan bazataje bikin matsiyata ba dan tasan dai bai wuce tuwo da waina da zoɓo ba. Harga ALLAH bata san ɗiyar wa Aliyun ya aura ba. Da ɗan jimami ta ce, “Da gaske kece matar Aliyun?”.

      Lulu dake mata wani kallo a yamutse ta amsa da, “Oh baki yarda bane? Zaki iya tambayar ɗanki ni yanzu ba wannan ne ya kawoni ba. Nazo nan ne game da case ɗinki da Hawwah, kinyi ƙoƙarin zuba mata mai dake saman wuta da nufin ƙonata, ba kuma wannan ne karo na farko ba da hakan ta faru. Kinci arziƙin ɗanki shiyyasa banzo da police ba a yanzu haka domin kamaki. Amma nazo da kalaman gargaɗi a gareki a karo na farko. Su iyayenta sun barki saboda jin nauyin karamcin ɗanki. To ni kuma a matsayina na mai kare hakkin mata kuma matar Yayanta bazan iya barinki ba. Kin haifi Sa’id ba kin haliccesa bane, yana kuma da damar yin aure tunda bake zaki auresa bane, matsayinki daban matsayin uwa matsayin matarsa daban matsayin mata. Nan gidan aurenki ne, shi kuma nan gidan da aka haifesa ne, kina zaune da mijinki lafiya dan haka itama ki barta ta zauna da nata mijin lafiya. Wannan takardar da kike gani na tattara dukan abubuwan da kikai mata ne, tare da bincike mai yawa akanki a wajen ƴan anguwa da ƴan uwanki dana mijinki, kuma sun bani duk wani information a kanki har ma wanda bakiyi zato ba. Haka ma mijinki nayi waya da shi yanzu haka, dan haka kina da zaɓi biyu zaki saka hannu zan saka hannu Sa’id zai saka hannu hakama Hawwah da sharaɗin zaki fita rayuwar aurensu ki zauna a matsayinki na mahaifiyarsa, zakuma subar wannan gidan su koma nasu, sannan kije da kanki gidansu ki bata haƙuri ki bama iyayenta haƙuri. Zaɓi na biyu ƙin amincewa da shawarar farko na shigar da wannan case ɗin kotu mu zuba shari’a wlhy har sai na kaiki jail dan har video ke gareni na randa kika kusa kasheta a dalilin hankaɗota daga saman upstairs gashi”. Ta ɗaga mata wayar tana mai playing video ɗin, jikin maman Sa’id ya fara rawa, Lulu ta sake shiga wani ta ce, “Ga kuma na randa kika watsa mata ruwan shayi harta ƙone a wuya shima”. Sosai Lulu taga ruɗewa a idanun Mama. Tai murmushi da kaɗa kanta cike da isa. “Ba waɗannan kawai ne ba, akwai wasu tari-tari kuma duk Hawwahn ke ajiyesu, bata nuna bane saboda mutuncin ɗanki. Amma ni yanzu na shirya fiddosu a gaban alƙali. Kin san dai mijinki siyasa yake yi har yana shirin fitowa takara a shekara mai zuwa ko, sannan yayanki a yanzu haka ɗan majalissa ne, to a dalilinki duk zan iya tarwatsa wannan damammakin, dan bayan kasancewa jinin Jiƙamshi jinin Alhaji Sufi Ado Garko nake kuma. Sai ki zaɓa na baki nan da kwanaki uku kacal. Na barki lafiya”. Ta faɗa tana miƙewa murmushi ɗauke da fuskarta ta ɗaga mata yatsu biyu tai ficewarta. Sosai jikin maman Sa’id ke rawa da kakkarwa. Dan kuwa Lulu ta daketa ne a inda taji zafi sosai. Videos ɗin nan sun matuƙar tayar mata da hankali, har tana mamakin yaushe Hawwah duk ta ɗaukesu batare da ita ta sani ba. Na biyu matsayin Lulu da hatsabibancinta akan shari’ar duk da ta saka a gaba. Na uku zancen siyasar mijinta da tai matuƙar ƙwallafama rai da buri a yanzu tare da matsayin ɗan uwanta da shima take taƙama da tinƙaho da shi a duk inda ta shiga. Idan wannan damar duk ta kufce musu ai ta shiga uku wlhy, dan za’a mata dariya matuƙa. Itafa dama kishiyar uwar yarinyar nan ce ke sake tunzurata akan tsanarta (Umma), duk da dai dama bata sonta kasancewarta ƴar talakawa, dan taso ace Sa’id yay auren kece raini ne na ƙwarya tabi ƙwarya. Amma ya ƙare da auren ƴar malam shehu……

    Lulu data fita da ƙayataccen murmushi a fuska ta shige motar tare da yin reverse tabar angur da gudu dan ita kam akwai wauta da mota. Mai Napep ɗin nan dai na biye da ita. Ganin sun ɗauki hanyar Nasara G.R.A yasa shi kiran Smart ya sanar masa. Koda suka iso gidan na Garko daka ɗan nesa ya tsaya, yayinda ita aka buɗe mata gate ta shige ciki. Yau ma da mutane a gidan, sai dai kusan duk matan kawunan ta ne, suma ɗin dai wanda basa fita aiki ne. Ta samu Baba na barci saboda allura da akai masa, hakan ya bama Dada dake cika na batsewa wa matan ƴaƴan nata jan Lulu suka shige ƙuryar ɗaki. Dan fa ita tun jiya ranta a ɓace yake da batun zuwansu a napep. Balbale lulun tai da masifa, ita kuma ta tsaya tana kallonta da mamaki, sai da takai inda take so har tai shiru sannan Lulu ta taɓe baki. “To wai ni kuwa Dada dan ALLAH miye na damuwa anan, shiga napep ɗin shi minene a cikinsa. Kinbi kin saka ma kanki damuwa”.

   “Ya bazan sakama kaina damuwa ba Mawaddat. Kamarki ace kina hawa Napep. To ai ko uwarki datai irin wannan ƙaddararren auren naki bai kai naki watsewa da lalacewa ba. Shi wai cikakken ɗan iska ma, an bashi abinda zai riƙeki har yace baya buƙata. Ke anya kuwa yaron nan ba asiri yay miki ba kuwa?”.

      Dariya Lulu ta kwashe da shi a karo na farko, ta ce, “Ho Dada tamu, Aliyun ne zai min asiri. To wlhy bara na faɗa miki ma shi ustazu ne. Dama cakikai girman kai ya hanashi amsa sai na yarda. Amma ba asiri ba. Yo ni koma asirin ne ina ruwana ma, iyakaci lokaci na cika zan ƙara gaba babu abinda asirinsa zaimun ballema ni nasan ba asirin bane. Kuma nidai ki daina zagar min miji dan nima ƴan uwansa basu zagan ba sai ma girmamani da mutuntani da nuna min soyayya sukeyi”.

    Dada data saki baki tana kallonta ta ce, “Iyyeee a lallai Mawaddat kinyi baki, harni kike gayama wannan zantukan. To inba asiri ba ubanmi zai kaiki auren yaron dake matsayin driver ɗinki. Ko ƙyan nasa ne ya ruɗeki da waɗan nan shegun idanun nasa kamar na ƴan maye. Dubeki fa wai kece da saka hijjabi yau kamar wata tsohuwa. Yo koni dana haifi uwarki na ninkaki shekaru bazan saka wannan abun har ƙasa na fita ba”.

     Baki Lulu ta taɓe tana miƙawa, “Dada bazaki gane ba ke dai. Ya kike so nayi? ya rantse in ban saka ba bazan fito ba gashi inada shari’a mai muhimmanci. Wlhy taurin kan Aliyun nan ya wuce duk yanda kike tsammani. Bar ganinsa yana wani sissine kan nan shegen kansa ne.”

    “A to lallai na sake yarda yaron nan asiri yay miki wlhy, ke yanzu duk yanda na sankin nan da rashin ɗaukar raini har kece taurin kan wani ɗa namiji zai girgiza ki ko ya baki tsoro da saki laushi haka a cikin sati ɗaya kacal. Dolene na miƙe tsaye dan wlhy koma miza’ai sai na rabaki da shegen yaron nan dan baza’a sake maimaita abinda ya faru akan uwarki ba. ALLAH dai yasa baki miƙa masa kanki ba ya lalube shegen”.

   Dariya Lulu tai harda kwanciya, sai kuma ta ɗago cikin dariyar dai ta ce, “Ke kam Dada inda ace a zamanin baya kikazo irinku ne bakwa musulinta da wuri ga riƙe gaba har ƙarshen numfashi. Indai aurena ne ki kwantar da hankalinki bamai daɗewa bane, sati biyu ya rage ana uku na koma free. Sannan kina damuna da habaici akan Daddy na da Mamana, idan na tambayeki kuma kiƙi faɗa min, kin kuma hana kowa gayamin. Mi Daddyna yay miki ne kike jin haushinsa haka, idan dan yaƙi baki riƙona ne ba gashi yanzu na dawo kina ganina ba”.

     “Ke ni ƙyaleni shashasha ba ganewa zakiyi ba. Ni ina tambayarki wani abu ya shiga tsakaninku ne? Sannan kince nanda sati biyu, kin fa sani a duhu”………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣0️⃣

……..Shiru kamar Lulu bazatace komai ba, sai kuma taɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa. Cikin rashin damuwa da kallon abinda zatayi ɗin a wani abu ta kwashe komai dangane da auren contract da Uncle Yousuf ya sanar mata saboda kar Baba yay mata auren dole ta sanarma Dada. Ta kuma faɗa mata ita babu abinda Aliyu yama taɓa nuna yana so a gareta, shiyyasa ma take ɗan ganin girmansa”.

  Salati Dada keyi a zuciya tana tsinema Uncle Yousuf, wato sunyi hakanne dan kar Lulu ta auri jikanta dake gadon asibiti. To lallai idan sun san wata ai basu san wataba kuwa. A zahiri kam bata nunama Lulu komai ba, tunda dama dai bugar cikinta take. Abinka da tsohuwar mace gashi taji abinda batai zato ba, Lulu kuwa har yanzu yarinya ce fa, dan ma ALLAH ya bata ilimi da kaifin basira, sannan ga yanayin rainon data tashi irin waɗan nan makirce-makircen na tsoffin matan ƙasar hausa ba gane kansu take ba. Sun cigaba da hira da Dada data ajiye maganar Smart har sai da Baba ya farka suka fito, Lulu taje ta dubashi. Ta jima a wajensa kafin ta tafi dan tana son komawa office. Mai Napep ɗin nan da yay zaman jiranta dan Uncle Yousuf ya bashi napep ɗin ne domin kawai bibiyar Lulun. Smart ya kirashi har sau biyu amma yana sanar masa tana a ciki bata fito ba. Da ta fito kuma yay kiransa ya gaya masa. Hakama da suka koma office. Ta sake zaman kusan awa biyu a office kafin ta fito Zainab biye da ita d kayayyakinta. Bayan ta saka mata ta sanar da ita gobe ta fito da wuri dan akwai wasu baƙin da take saran zasu zo nemanta. Da girmamawa Zainab ɗin ta amsa mata, ita kuma ta shiga mota sai gida. Sai dai ta tsaya wajen wani mai bread ta saya. Koda mai napep ya sanarma Smart bai kawo komai a ransa ba game da sayen bread.

  (Ni dai nace Humm lulun mu fa ta wuce da saninka Smarty 😂😜).

      ★★★……

  Tun shigowarsu cikin Saloon ɗin nata tai kamar wadda ta suma. Ba ita kaɗai ba hatta matan dake wajen ana musu ayyuka mabanbanta kallon mamaki suke musu dan kowa dai yasan anan mata kawai akema aiki banda maza. MM Atik Kumo ya katsema Nadiya tunani da faɗin, “Hello girl”.

   Nannauyan nufashi ta kawo da dubansa, cikin ƙarfin hali da in ina ta ce, “Ranka ya daɗe lafiya dai?”.

     “Ita ta kawomu. Ko zamu iya ganinki a waje?”. Asim ya bata amsa kai tsaye. Ƴan shagon ta duba, ganin duk sun zuba musu idanu yasata cewa, “Okay muje”. Su suka fara fita sannan tabi bayansu tana jan ƙaramin tsaki da gargaɗar yaranta su cigaba da ayyukan gabansu. A cikin motar su ta samesu, MM Atik dake zaune mazaunin driver yay mata nuni da ta shiga ciki itama. Batai musu ba ya buɗe ta shiga, bayan ta rufe ta gaishesu. Asim ne kawai ya amsa mata MM Atik kam tambaya ya jeho mata na cewar “Yaya ƙawarki?”

    Numfashi ta ɗan furzar da gimtse fuska, a taƙaice ta ce, “Ban san yaya take ba dan bama tare yanzu. Tun a waccan ranar bamu sake kasancewa tare ba”.

   “Saboda mi?”.

 Cewar MM Atik ɗin yana jiyowa gaba ɗayansa gareta. “Hummm saboda naje da su Alhaji Baita wannan get together ɗin fa. Kasan na faɗa maka Lulu ta tsani maza, shiyyasa nake kallon kamar aljani ya aureta ne shiyyasa. Yanzu haka ma zancen bikinta sai gani nai an ɗaura mata aure wai da driver ɗin nan nata a tv, hakama dinner ɗin ta gani kawai nayi ana nunawa duk da kuwa na bata haƙuri ta waya da duk hanyar data dace amma taƙi saurarena”.

    Murmushi MM Atik yayi damin hango irin ruwan bala’in datai masa a randa ya fara ganinta. Nadiyar ya kalla da faɗin, “Ai masifa bata mata wahala. Bar batun auren driver dan kuwa muna ganin da manufa tayisa, sakamakon son gujema auren Hon. Nakowa da wannan ɗan uwan nata Tajuddeen Sulaiman Garko. Ba ita kawai ba nima naji haushin ganinku da tsoffin nan a wancan ranar, kawai dai na miki shiru ne”. Shiru Nadiya batace komai ba akan hakan, shima sai ya cigaba da faɗin, “Manta abinda ya faru ya faru ya wuce, yanzu sabon dil nake son mu ƙulla”.

    “Nami kuma kenan?”.

  “Akan ƙawar taki dai, dan bazan iya haƙura ba.”

“Abu mai wahala kenan, dan ta yanke alaƙarmu, tare da gargaɗin nisantar ta. Nasan halinta kuma sarai idan ta faɗi abu har cikin ranta ne. Abu ne mai matuƙar wahala Lulu ta sake kallona balle har na shiga jikinta”.

      “Zamu iya amfani da wata ai, amma ya zama ke zakina controlling nata”. Cewar Asim.

   Kai Nadiya ta jinjina da faɗin, “Wai babbar magana. Na fahimci bakusan wacece Lulu ba. Kubar ganinta haka batajin magana tasan mitakeyi. Sannan koni kaina nasha wahala kafin mu fara abota gaskiya, dan bata da saurin sakewa da mutane, sannan ba kowa ke iya haƙuri da halin Lulu ba”.

     “Karki damu inhar aka jajirce wannan ba komai bane ba. Sannan kema fa akan aikin nan zakija manda. Dan a yanzu haka zamu sauke miki miliyan ɗaya kafin ma aikin ya fara”.

  Sosai Nadiya ta zaro ido waje, ranta fal farin ciki ta ce, “Yanzu yaya kuke so ayi?”.

  Kallon juna sukai da murmushi, kafin Asim ya miƙa mata card da faɗin, “Ki samemu a wannan address ɗin zuwa anjima”.

     “Wannan yafi komai sauƙi”.

Ta faɗa tana amsar card ɗin……..

      _______________★

  Kwanaki uku kenan da fara fitar Lulu aiki, kullum kuma Smart ke kaita office da safe sannan shima ya koma gidan yay shirin tashi fitar a Napep. Idan ko fita ta kamata a yinin mai Napep ɗin nan da bata san da shi ba na biye da ita. Duk kuma inda ta saka ƙafa ana sanar masa. A lissafinsa dai babu wani abu dake faruwa, dan ranar farko ta sayi bread wanda bai san a tsakkiyarsa aka saka mata kayan shaye-shayen ta ba, kamar yanda takeyi sai zata kwanta tasha hakan tayi, shiyyasa bai gane komai ba sai ya ɗauka kawai gajiyar aikin data koma ce tunda tayi ƴar zirga-zirga. Washe gari dai yaga ta tashi a tsayenta bakamar kwana biyu datai wani sukuku ba. Rana ta biyu ma sai da tai amfani da dabarun nasu ta amsa, hakama jiya. Yau cikon kwana na uku yaso ya ɗan fara tsarguwa, amma dai baice komai ba. Yana son mata tambaya akan zuwa gidan su Sa’id sai kuma dai yay shiru. Sai kuma gashi a yau yana tare da Coach kira ya sameshi da ga Ammah wai yazo da sauri idan yana kusa. Ya Isa gidan da tunani kala-kala sai ya ɓige da samun mahaifiyar Sa’id da wasu ƴan uwanta maza uku dan dangin mahaifinsa sun rantse bazasu zo ba, ita data ɓata taje ta gyara sun dai zo na farko. Ba Smart kaɗai ba kowa ma na gidan nan yau mamakin jin maman Sa’id wai sunzo bada haƙuri ne da neman afuwar Hawwah dan ALLAH tai haƙuri ta koma yake. Smart yace shifa ƴar uwarsa bazata koma wannan gida ba, anyi kenan takardar saki kawai yake buƙata Sa’id ya kawo, dan suna sonta baza’a kashe musu yarinya ba. Sosai Maman Sa’id ke faman magiya akan wancan ma daya faru tsautsayi ne da munafuncin munafukai, amma yanzu ta gane gaskiya. Ankai ruwa rana matuƙa kafin Smart ya haƙura zata koman amma ba wannan gidan ba. Da sauri Mama tace ta yarda, Hawwah ta zaɓi duk inda take so a gidajensu a gyara mata. Wannan abu yaba kowa mamaki, Umma na son magana tana tsoron ta tanka Maman Sa’id tai mata bankaɗa tunda taji tana shaguɓe akan munafukai, ba kowa kuma ne mai zuwa ɓata Ammah da Hawwah a wajenta ba sai ita dama. Bayan wucewarsu kowa ya shiga mamaki, Abba ya tsare Smart akan miya ma maman Sa’id ɗin har tai irin wannan sakkowar lokaci ɗaya. Ya tabbatar musu bashi bane, dan shi target ɗinsa akan jiran dawowar mahaifin Sa’id ne ai. Yana son kawo Lulu a ransa wani gefe na zuciyarsa na musa masa. Amma dai duk da haka bayan ya koma gida da daddare sai da ya kasa haƙuri yay mata tambaya. Dariya kawai tayi taƙi faɗa masa komai, hakan ya tabbatar masa itace kenan tayi koma miye. Sai kawai ya zuba mata ido yana jin wani abu mai girma na ƙara ratsashi a kanta. Jin kaifin idanunsa a kanta ya sata dakatawa da ga abinda take a system ta ɗago, harararsa tai da faɗin, “Malam wannan kallon fa? Ni fa bana son kallo”. Ta ƙare maganar da murguɗa baki. Murmushi ya saki mai sanyi batare da ya janye idanun ba, sai ya samu kansa da furta, “Kullum sake mamaye komai da komai kike yi”. Bata fahimci ina ya dosa ba, sai dai yanda yay maganar a ƙasan maƙoshi da tausasa fitar sautin matuƙa ya sata tsayawa kallonsa, “Lafiya kake kuwa? Kodai kaima ka fara ban sani ba?”.

     “Na fara mi?”.

  “A hawa network mana”.

Ƙaramar dariya yay yana girgiza kansa. “Tom maybe na fara amma nawa ba irin naki bane gaskiya. Kema fata nake ki daina wannan ai ki dawo wannan irin nawan”.

    Nan ɗin ma dai ba fahimtar tai ba, dan haka ma ta taɓe baki da miƙewa tana faɗin, “Ai kai kam wani lokacin kamar mai aljanu. Dolene na sanarma Ammah ta fara maka addu’ar su ko ka kwaso a drivern cin ba’a sani ba”. Daga haka ta wuce bedroom ta barshi yana murmushi………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣1️⃣

………Washe gari gidansu ya wuce bayan ya sauketa, anan ne yake samun Abba da Ammah da batun shifa yana zargin Mawaddat ce tayi koma miye. Dan an sanar masa taje gidan a ranar monday. Mamaki sukaitayi suma da tunanin to mita faɗa ma maman Sa’id da har ta risina haka da sauri. A gefe kuma ƙaunar yarinyar na sake shigar musu zukata. Kamar yanda akace sati ɗaya cikin satin Hawwah ta fara shirin komawa sabon gidanta danƙarere. Hankalin Umma ya sake tashi, da bin ƙwanƙwanto ta gano Lulu ce tamayi koma miye har komai ya dai-daita. Hankali a tashe ta nufi gidan Hajiya Naqiba ƙawarta. Acan suka baje faifain zagin Ammah da bata san sunayi ba da Ƴaƴanta suna neman mafita dan abubuwa fa nata faman kufce musu a hannu, sai dai gaba ɗaya hankalinsu da mugayen ƙudirinsu sun tattara ne ga Lulu yanzu. Dan sun fahimci shigowarta gidan abubuwa da yawa ke neman taɓarɓarewa. Duk da su basu fahimci cewar asirin jikin Smart ma ya gama warwarewa gaba ɗaya ba. Ga aikin Malam na-zuru yaƙi yiwuwa, dan kayan Lulu da Smart dai sun gagara ɗakkuwa. Hajiya Naqiba ce cikin dogon tunani ta ce, “Aminiya anya bazamu canja taku ba?”.

    “Kamarya? Fito kimun dalla-dalla, kin san bana son kwana-kwana fa”.

   “Ina nufin ba asiri bane kaɗai yanzu ya kamata musa gaba dole mu haɗa da makirci da kissa. Kamar dai yanda nai akan shegun yaran can na baƙar dagar tawa.”

  “In dai wannan ne ai mun jima munayi Aminiya, yanzu ko ita akan wannan shegiyar da zata koma Hawwah ai kinga sai da muka haɗa da makirci waccan shegiyar da bamu san mitaje tayi ba ta ɓata mana komai.”

     “Kwantar da hankalinki karki damu, murnarsu zata koma ciki ne. Yanzu mu fara kai wannan baƙuwar hauren ƙasa tukunna dai. Dan wannan ƴar iskar amaryar da aka jajubo muku na fahimci da ƙarfinta tazo, gashi yarinyar nada ilimi fiye da tunaninki kuma goyon turai, ga kuɗi a gida, kuɗi a mota, kuɗi a Office, kuɗi a banki. Idan mukai sake fa komai zai koma wanwarne, ni ko da kishiya da yaƴanta su ji daɗin duniya ko komawa sama dani gara ace kowa ya mutu a ƙasar, ke ama busa ƙaho”.

    Dariya Umma tayi da faɗin, “Hajjaju ke bala’i ce ai, shiyyasa nake sake tausayin Matar gidan nan naki. Yanzu ke miye shawararki?”.

       “Dole ne muyi bincike akan yarinyar mu samo wanda zamu shiga jikinsa nata mu mata rugu-rugu”.

    “Tab babbar magana ta yaya kenan? Bayan kin san daga wane gida ta fito, gate ɗin gidan su ma taɓa shi ba masifa bane balle shiga gidan”.

  “Kwantar min da hankalinki. Akwai matar nan mai min ƙunshi ranar ana labarin dukiyar da aka zubar a auren ita yarinyar da aka kai gidanku take cewa ai ita taga zahiri dan itace kema matar Alhaji Garko ƙunshi shekaru kusan shidda kenan, shiyyasa tasan abubuwa da yawa a gidan nan ko shagalin bikin nan duk akan idonsu akai komai. Ita kanta taci rabonta dan tayi ƙunshi sosai a gidan, sai dai ta fahimci kamar matar Alhaji Garko bata son auren fin ƙarfinta akayi, yarinyar da ɗan uwanta aka saka mata biki lokaci guda ta birkice wai sai yaron gidanku”.

   “Kai haba da gaske wai? Anya ba asiri suka mata ba ma kuwa”.

  “Wlhy haka tace, babu abinda Hafsatu bazata iyaba wlhy, wama ya sani. Shiyyasa nake ganin ya kamata muje gidan Alhaji Garko mu kunnowa Hafsatu wutar da zata ƙoneta ƙurmus har ƴaƴan nata a wannan karon. Ba suna murna sun samu ɗiyar biloniya ba. Zasuci ubansu ne”.

   Dariya suka kwashe da ita suna tafawa……

   _____________★★

     Kwanaki sun ƙara shiɗawa, dan a lissafin Lulu dai next week ne rabuwarsu da Smart. A week ɗin daya wuce ya kaita gidansu da gidan Uncle Yousuf, daga nan ta samu ƙafar zuwa duk bayan kwana biyu haka idan ta fita aiki takan leƙasu duk da dai daga Daddy har Uncle Yousuf ɗin ma dai sunyi tafiya basa ƙasar ma. A ranta a duk sanda ta ƙiyasta tana jin farin cikin komawarta free dan ta fara jin ƙosawa da tsakurarsa musamman ta saka hijjabi da tafi cimata zuciya da rai fiye da komai. Sai dai wani sashe na zuciyar tata na mata kamar babu daɗi musamman idan ta tuna Ammah da ƴan uwansa. Takan faɗa dogon nazari akan hakan, amma idan taje duba jikin kakanta Alhaji Garko da har yanzu dai babu lafiya suna ma shirin fita da shi ƙasar ne duk da yana turjewa sai da Dada taita mata fanfo da zugeta. Wani lokacin Lulun kan nutsu ta saurareta, wani lokacin kuma tace “Kai Dada dan ALLAH wai miye matsalarki da Aliyu ne? Miyay miki?”. Dadan kan zazzageta wani lokacin ko balbaleta da faɗa dan masifaffiyar mata ce. Wannan faɗan da take takura mata da shi yasa kwana biyu Lulu bataje gidan ba, sai dai tai kira a waya taji yaya jikinsa. Hakan sai ya fara damun Dada, dan a ganinta wani asirin Smart ya sake tafkawa Lulu…

    A ranar Juma’a da Lulu ke cika kwanaki uku rabonta da zuwa gidan Smart ya wuce Legos, Maryam da Asma’u aka kawo mata su tayata kwana, sai Mubarak da zaizo da dare, sai su Afrah suma da taje da kanta ta ɗebo. Nan fa shafta ta buɗe. Wucewar su Maryam ya ƙara zafar Umma, tai shiri ta nufi gidan aminiyarta Hajiya Naqiba rai ɓace. Bayan ta gama labarta mata Hajiya Naqiba tace tashi muje yau ayita ta ƙare. Sun je gidan mai ƙunshi da tace zatai musu rakkiya. Daga can suka tafi gidan Alhaji Garko. Sosai Umma ta sake girgiza da dukiyar waɗan nan mutane, nan fa zuciyarta ta ƙara ƙaimi wajen ƙulle-ƙulle na ganin auren Smart da Lulu ya gundile. Sunyi zama fin na awa ɗaya kafin hamshaƙiyar tsohuwa mai ji da kuɗi da hutu ta fito cikin isa da izzarta. Ai sai su Umma sukai saƙale suna kallon ikon ALLAH, dan Dada ta tsufa sosai kawai dai abinka da jin daɗi ne. Cikin girmamawa suka gaisheta tana amsa musu da ƙyar a yamutse. Mai ƙunshi ta mata bayani duk da dama ta fara sanar matan. Amma tsohuwar nan saita dubi su Umma a watse cike da isa ta ce, “Ku tabbatar duk abinda zai fito bakinki bazai zama wuƙar yankaku ba, dan bana son munafunci ni da kuke gani na anan”.

   Muryar Umma na rawa ta ce, “Wlhy Hajiya a duk abinda mukazo miki da shi nan babu munafunci. Yaron nan asiri yayma ƴarku. Idan kuma baki yarda ba kisa malamai su bincika muku zaki fahimci gaskiyarmu. Amma kuyi da sauri dan yanzu haka yayi tafiya wai Niger da abokinsa kin san kuma yanda suka iya asiri bana raba ɗayan biyu wani bala’in zai sake haɗo muku (😂 Niger akacema su Umma Smart ya tafi raka Ahmad sayen shanu).

      Mai ƙunshi da yake itama makirar mace ce tana kuma son sake samun fada a wajen Hajiya Dada sai ta sake taƙarƙarewa tana taya su Umma. Harda cewa zata raka Dada wajen wani malami a duba musu ɗan uwanta ne a Zuru yake. Amma batai maganar hakan ba sai da su Umma suka fito bayan an sallamesu. Hankalin Dada ya tashi, dan haka ta sallami su Umma tace mai ƙunshi tazo ta sameta gobe idan ALLAH ya kaimu bayan an wuce da Alhaji Garko dan zasuyi gaba ƙasar London ita sai nan da sati ɗaya zatabi bayansu. Cike da farin ciki su Umma suka fito da ƙyautar naira dubu ɗari kowa hansin-hansin. Mai ƙunshi kuwa ma basu san mi aka bata ba. Ta kumace dole su cire mata kasonta a ciki dan bazata rakosu a banza ba. Da ƙyar suka bata goma-goma suna ƙunƙuni. Tace oho dai shegu ai ni kunzo min da hanyar samun kuɗi, naci a wajenku, naci a wajenta, naci a wajen malamin da kukace aje.

   Washe garin asabar aka wuce da Alhaji Sufi Garko ƙasar London dan likitoci anan gida Nigeria sun tabbatar poising ɗinsa akayi. Ba’a fahimci hakan ba kuma sai a tsakanin kwana biyun nan da gubar ta bayyana kanta, dan sun bashi wadda bata bayyana kanta da wuri har sai tayima jiki illa ne. Duk da wannan tashin hankalin da ake ciki hankalin Dada nakan Lulu da itama dai yau tazo gidan har da su Asma’u da su Afrah. Sai dai taƙi yarda ko sau ɗaya su zauna da Dada har sanda ambulance ta ɗauki Baba itama sai taja ƴan rakkiyarta suka bisu har airport. Basu baro ba sai da jirgin da za’a ɗauke sa a ciki shi kaɗai sai yaransa maza biyu ƙannen Alh Sulaiman da zasuyi gaba ya tashi. Kowa ya bisu da addu’a kafin yaje. Suna baro airport ɗin jirgin da ya ɗakko Tajuddeen da Alhaji Sulaiman (Tsule🤣) ya sauka shi kuma. Ya samu sauƙi sosai koma muce a zahiri ya warke, sai dai a zuciya kam babu abinda ya ragu na soyayyar da yakema Lulu. Ya samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciyane kawai bisa alƙawarin da mahaifinsa yay masa na sai ya mallaka masa Mawaddat ya kwantar da hankalinsa. Wannan dalili ne ya sashi jin ƙwarin gwiwar biyosa suka dawo. Manyan aminansa na yanzu duk da dama can aminan nasa ne matsaloli suka rabasu Alhaji Baita, Hon. Nakowa. Da Hon. Misau ne sukaje tarbarsu. Dan kaf Family na Garko babu wanda yasan da dawowar tasu a yau…….✍️

    (🤔Tofa! Alhaji Sufi Garko ya tafi jiyya a dalilin poising nashi da akace anyi. Alhaji Sulaiman Sufi Garko ya dawo tare da ɗansa Tajuddeen Sulaiman Sufi Garko daya tashi a jiyyar soyayya babu wani damuwa tattare da al’amarin su. Anya kuwa babu wani abu a ƙasa? Humm kumu dai je zuwa to🚴).

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣2️⃣

…….Dada tayi tunanin Lulu zata sake dawowa gidan, amma bayan duk ƴan rakkiyar Baba sun dawo sai gashi babu ita, sai ma sanar mata da akai ta wuce gidan ta. Hakan ya sake girgiza Dada ta kuma tabbatar da eh lallai da alamar ƙamshin gaskiya a zancen mutanen nan asiri yaron nan yay ma jikarta. A take ta dannama Fulera mai ƙunshi kira, batare dako amsa gaisuwar ta ba tace ta sameta yanzun. Fulera ido a kuɗi tuni tai tsalle tayo waje da ga gidan su, dan dama dai zawarci take kusan shekara tara kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gata a Garko house. Ta sami Hajiya Dada tare da mai aikinta dake mata irin waɗan nan ayyukan na sirri, dan Dada tunda jajayen sawu ƴan hannun bin malamai ne kam. Cikin gurfana Fulera ta miƙa gaisuwa, Dada ta amsa cike da isa. Babu wani jan lokaci ta sanar musu abinda take son a mata. Zasuje wajen mutumin da tace mata a Zuru ita da mai aikinta. Ba haka Fulera taso ba, amma dai babu damar musu dan haka ta amsa da to. Mota Dada ta bada akaisu tare da kuɗin amma sai ta damƙawa mai aikin nata. Nan ma Fulera taji zafi, ta dai danne, damar fara fita data samu kafin mai aikin Dada ta kimtso ta samu ta dannama Hajiya Naqiba kira ta sanar mata komai. Dariya Hajiya Naqiba tai da faɗin, “Kai tsohuwar nan mayyace akwai shegen wayo. Barta ai inta san wata bata san wata ba. Kwantar da hankalinki bari na kirashi kafin ku isa.”

   Haka kuwa akai hajiya Naqiba tai kiran malam na-zuru, duk yanda suke so haka ta tsara masa, shima da yake shegen kansa ne yace karta damu. Abinka da lafiyayyar mota basu sha wahala ba, dan bayan azhar kaɗan suka isa zuru saboda gudu na masifa da drivern yayi. Malam na-zuru da yake yasan da zuwansu kafin ma su faɗi abinda ya kawosu ya shiga zayyane musu wai ai ya gani ne a cikin aikinsa. Tuni mai aikin Dada ta ruɗe ta danna mata kira, nan ma fa sukai magana da malam Na-zuru ya sake fanfa Dada da kalolin sharri wa Smart dangane da auren Lulu, harda cewa ai asiri Smart ɗin yay musu dan yaga kuɗi. A yanzu haka ma yana Niger yaje anyo masa wani babban ƙulli, zaita kwantar musu da kai ya nuna shi na ALLAH ne sai anan gaba kaɗan zai bayyana halayyarsa da mugun nufinsa. Tsaf Dada tahau ta zauna saboda tayi imani da malaman tsubbu matuƙa gaya. Malam na-zuru ya haɗa musu kayayyaki suka sake ɗakko hanya….

   WASHE GARIN Lahadi Lulu da ƴan kwananta ta zubasu a mota ta kaisu sabon Saloon da ta fara zuwa yanzu ana mata gyaran jiki. Tsaf aka gyara ƴammatan nan suka fito tas da su kamar basu ba. Daga Saloon sun shiga wani joint suka ɗan sha ice-cream da abinda baza’a rasa ba. Daga nan suka koma gida. Kasancewar duk sun gaji kuma basa tare da yunwa suka shige ɗakin dake matsayin masaukinsu masu kwanciya nayi masu fira nayi. Itama anan falo ta ɗan kwanta dan ta haɗiyi kayan nata duk da kaɗan take sha dan kar yaran su fahimta. Wayarta ce ta shiga ruri, takai hannu ta ɗauka tana jan ƙaramin tsaki. Ganin Dada ya sata waro idanu waje, sai kuma ta ɗaga da sauri. Kafin tace komai Dada ta ce, “Ina mai gadin naku anata horn kamar ya mutu”. Da mamaki Lulu tace, “Mai gadi kuma Dada? A ina wai?”.

    “Gidan da aka kawoki mai kama da bukkar fulani”.

  Dariya Lulu tai tana miƙewa. Ta ce, “Uhm Dada baƙya gajiya dama mutane sharri idan baki son su. Wannan gidan ko makaho ya shafa ai yasan badaga nan ba. Ina zuwa”. Ta yanke wayar tare da zura slippers ta fita. Da kanta ta buɗe musu gate ɗin. Dada na hakimce a bayan danƙarereiyar motar da sukazo baƙa wulik, sai drivern ta. Koda ya samu waje yay parking sai da ya buɗe mata ta fito tana wani yamutse fuskartar ta tsufa da bin gidan da kallon banza. Yi Lulu tai kamar bata fahimceta ba ta rungumeta tana murnar ganinta. Dada ta tureta da faɗin, “Ni karki kadani fitinanniya”.

   “Ni na isa kadaki Hajiyar Baba Garko. Yanzu yana asibiti yana fama da kansa ke kina nan kina yawo”.

   “Oh kijimin yarinya da ƙulli, yanzu zuwa na dubakin kuma bammayi miki gwaninta ba kenan”.

      “A’a kimun yi haƙuri muje ciki”.

   A falon ma dai Dada sai yamutse-yamutse take duk da ya mata ƙyau matuƙa. Nan ma Lulu tai kamar bata lura ba taje ta kawo mata ruwa da lemo. Tana zama ta jeho mata tambayar “Ina yaran dana ganki da su ɗazun?”. Cikin rashin damuwa Lulu ta nuna ɗakin da su Maryam suke. Ɗan jimm Dadan tai sai kuma ta miƙe, “Kinga muje ɗakin ki magana nazo muyi”. Babu musu Lulu ta miƙe suka nufi bedroom ɗinta da Asma’u ta gyara ƙal sai tashin uban ƙamshi yake yi. Nan ma dai sai da Dada ta gama ƙare masa kallo sannan ta ja numfashi. “Kaya har kaya anzo an zubesu a wannan takurarren gidan.” ƙin cewa komai Lulu tayi, dan haka Dadan ta cigaba da faɗin, “Game da zuwa duba Alhaji ne. Shin zakije ne?”. Ɗan jimm Lulu tayi, sai kuma ta nisa da faɗin, “Ina son naje kam Dada, sai dai yanzu Aliyu yayi tafiya maybe ya dawo gobe. Idan ya dawo mukai magana sai kiji”. Sosai zantukan lulun ke sukar Dada da sake gaskata fa amma jikarta asiri, yo Mawaddat ɗin ta data sani mai zafin nan da ƙyamar abu ga murɗaɗɗen hali wai namiji ke juyawa haka. Namijin ma talaka ɗan talakawa fitik mai amsa sunan drivern ta. Kai wannan al’amari akwai ayar tambaya. A zahiri kam murmushi tai da cewa, “To ba laifi hakan ma yayi. Af kinga zan manta ga wannan kisha maganin ciwon maran nan ne dake damunki dama nace zan amso miki, inata shiririta sai kwanaki aka amso kinata zuwa gidan kuma ina mantawa. Shiru Lulu tayi tana kallon goran ruwan kamar tace a’a sai kuma dai ta amsa, dan ranta bazai taɓa bata Dada acikin jerin wanda zasu iya mata wani abu daban ba, sannan tana saran ganin period ɗinta nan da kwana uku, tasan kuma azabar da take sha na ciwon maran. Amsa tai ta ajiye gefe, amma sai Dadan tace tasha mana. Ai ba’a wasa da magani. Badan Lulu taso ba ta buɗe tasha kusan rabi ta ajiye. Daga haka suka cigaba da hirarsu da Dada wadda duk bugun cikine akan auren nan da son sanin wanene Smart. Ita dai Lulu tana bata amsar abinda ta sani ne kawai, har cikin ranta kuma bata kawo komai ba. Sai da Dada take cemata tafa kula, karta yarda yaron nan ya mata wayo ya kwanta da ita, dan yanda kwanakin nan suka kusa cika zai iya shirya mata muguntar maza. Lulu tai murmushi da faɗin, “Dada kenan nace miki ki kwantar da hankalinki, Shifa Aliyu ba irin waɗan nan da kike tunani bane. Na tabbata tunda har ya amince da auren nan na wata ɗaya ne kuma zai sake ni bazai taɓa saɓawa ba zai sake nin, yanzu haka ma jiran dawowarsa nake mu fara maganar dan shiyyasa nace ki dakata da batun tafiyar nan, cases ɗin dake gabana zanyi ƙoƙarin kammalasu na ɗan ɗauki hutu daga duba Grandpa zan ɗan huta kafin na dawo Nigeria gaskiya”.

   Sosai Dada taji daɗi dan haka ta shiga sanya mata albarka. Daga haka ma sai ta miƙe tana faɗin, “To bara na wuce tunda na kammala abinda ya kawo ni. Sai na jiki ɗin”.

   Da sauri yabar jikin ƙofar ya shige bedroom ɗinsa. Wani irin harbawa zuciyarsa keyi da sauri-sauri. Dan shigarsu ɗakin babu jimawa ya shigo gidan. Duk da yay mamakin ganin mota baƙuwa a waje yay zaton kota Lulu ce aka kawo saboda bai ga driver ba, ashe ya ɗan fita miƙe ƙafa. Ya shigo gidan yaji shiru, ya wuce ɗakinsa kai tsaye ya ajiye kayan hannunsa shine ya nufo ɗakin Lulu da tunanin ko barci take. Kawai yaji Dada na magana a hanakali cikin salon makirci na tsoffin mata tana bugar cikin Lulu, shine fa ya nutsu. Jin komai ya sake tada masa da hankali, dan yanzu ne ya fahimci ainahin abinda take nufi da wata ɗaya wata ɗaya da take ta ambata masa zata koma free. Zuciyarsa ta sosu da tunanin shima Uncle Yousuf yaudararsa yake kenan? Sai kuma wata ke kwaɓarsa akan kada yay zargi cikin fushi, ya bincika dai sannan. Sunayen ALLAH ya shiga ambata har ya samu nutsuwar ajiye tunanin a ransa gefe, sai kawai ya faɗa wanka. Lokacin da yake fitowa yaji fitar motar data kawo Dada, sai kawai ya ƙarasa kimtsawa da yin shirin fita sallar magrib ya fito.

     Lulu da ke kwance a falo ta wani ɗan zabura alamar tsorata da ganinsa. Murmushi ya sakar mata da lumshe idanu yana kaiwa zaune kusa da ƙafafunta. “Matsoraciya relax ba aljani bane ni ne?”.

   “Taya zan yarda da haka bayan kace sai gobe ne zaka dawo, kuma ina wajen banga sanda ka shigo ba”.

  Murmushin ya sake sakar mata, a nutsensa da deep voice ɗin nan tasa dake fita da sanyin damuwar abinda yaji na tattaunawar ta da Dada duk da yana ƙoƙarin dannewa ya ce, “Mun gama abinda ya kaimu ne shine kawai muka yanke dawowa gida. Sanda na shigo kuma kina ɗaki ne da baƙuwa. Namayi zaton har zan kammala wanka nazo mu gaisa duk da bansan wacece ba”.

     Kaɗan ta sauke numfashi da ɗage kafaɗunta. “Dada ce kuma ta wuce. Tazo ne akan maganar zuwa duba Grandpa da aka wuce da shi London jiya”.

   “Ya salam jikin nasa ne dai?”.

  “Wlhy kuwa, fiye ma da yanda ake tsammani, dan a shekaran jiya doctors suka gano wai anyi poising ɗinsa ne da gubar da bata baiyana kanta sai tai kwanaki a jikin mutum”.

        “What! Sai kace wani a film?”.

    Lulu ta ce, “Hummm a tunaninka a Film kawai ake waɗan nan abubuwan? To a Nigeria ma a zahiri anayin fiye da haka. Kasan Grandpa ya Bama siyasar nan amanna matuƙa, shiyyasa muke tunanin ko’a cikinsu ne musamman daya kasance a hasashenmu a zuwa Legos ɗin nan da yay abun ya faru. Yanzu dai haka jami’an tsaro sun duƙufa bincike kan al’amarin ma”.

   Matuƙa Smart ya girgiza. Dan baiyi zato ko tsammanin wai da gaske irin wannan abubuwan da ake gani a Film na faruwa a zahirin rayuwar mutanen ƙasarsa ba. Kiran salla ta sashi miƙewa yana faɗin, “Ina ƴan hutun naki? Naji gidan shiru”. Bedroom ɗin da suke ta nuna masa. “Suna ciki fa, tunda muka dawo saloon suka kwanta wai sun gaji”. Kallonta ya tsayayi kamar zai yi magana sai kuma yay shiru dan shi dai bai san da wani fitarsu saloon ba. Zuciyarsa ta lallashesa akan a tari gaba. Yanzu zantukan ta da Dada ya kamata ya maidama hankali. Kafaɗa ya ɗan ɗage hannayensa duka a aljihu, ya ce, “Okay bari naje salla na dawo. A ɗan samamin wani abu mai ruwa-ruwa haka yunwa nake ji”.

   Harararsa tai da faɗin, “Kafa dawo zaka fara takurama mutane da mulkinka ko”.

   “Ni na isa. Karki damu cikin su Maryam wani yayi ki huta abinki. Ki dai tashi kiyi salla. Bara naje sai na dawo”. Daga haka ya fice kafin ma tace wani abu……….✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣3️⃣

……..Bayan an idar da salla har ya nufo hanyar gidan sai kuma ya dakata. Napep ya tare ya shiga tare da gaya masa inda zai kaisa. Cikin ka ƙanƙanin lokaci suka iso. Ya biya sa kudinsa sannan ya shiga gidan bayan sun gaisa da maigadi. Ahmad na zaune a falonsa ya barbaza takardu ga laptop a gabansa Smart ya shigo. Ɗagowa yay yana kallonsa cikin nuna mamaki. Smart ya watsa masa harara da faɗin, “Lafiya kake kallona?”.

   “Inafa lafiya, kai da nake tunanin kana can kana aikin ALLAH yanzu kodan kewar juna da akai amma sai na ganka anan”.

      Ƙaramin tsaki Smart yay yana kaiwa zaune da faɗin, “Banza ɗan iska kaifa baka tauna magana kafin ta fito maka a baki”.

   Dariya Ahmad yayi da cewa, “Gara na dinga muku ɓaro-ɓaro kuyi ku aurar dani kuma ku huta. Amma fa sai naga kamar kana cikin damuwa. ALLAH dai yasa ba wani abu ka tarar a gidan ba?”.

     Smart baida yawan magana. Sannan akwai zurfin ciki. Duk abinda kaga ya bayyana shi ga waninsa to lallai ya matuƙar girgiza shi ne. Sosai ya nisa da furzar da iska mai zafi. “Ahmad akwai matsala ne”.

    “Ya salam matsala kuma Mawashin. To tami? Akan kuma mi?”.

  Shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya ɗago yana kallon Ahamd ɗin da shima ya zuba masa idanu. “Badan ina son fara tona sirrin gidana bane, al’amarin ya girgiza nine ina buƙatar shawara dan kar na aikata abinda ba haka yake ba. Bayan kun saukeni na shiga gida sai na samu…….”

   Tsaf ya zayyane masa abinda yaji tsakanin Lulu da Dada na tattaunawa. Shima kansa Ahmad yasha mamaki. Amma sai ya dafa Smart yana jinjina kansa. “Niko kaga ko bana jin shi Yaya Yousuf da wata manufa yay hakan. Domin idan ka auna zancen tsohuwar zaginsa take akai-kaice shima. Sai naga yayine domin ma Mawaddat wayo kawai”.

      “To miye na wayon anan Ahmad, aure ne fa kuma ta isa aure tunda ba gunkinta zasuyi su kafe a gidan ba. Kawai dai akwai abinda suke shiryawa a kaina na yaudara”.

   “No no relax kar kabari ka yarda da hakan. Sam sam bazaiyi hakan ba. Amma ina zuwa dai”. Waya Ahmad ya ɗakko yay kiran Uncle Yousuf. Da ƙyar ya samu ya shiga kasancewar har yanzu bai dawo ƙasar ba. Sun gaisa cikin mutunta juna batare daya nuna yana tare da Smart ba. Uncle Yousuf daga can cikin tsokana yace, “Yaya dai Auta ko batun auren ne ya tashi akeso na fara haɗo lefe?”.

       Dariya Ahmad yayi da faɗin, “Kai haba Yaya a’a. Wannan ai sai kun yarda da zaɓina sannan zamuje wannan matakin. Duk da nasan ma kunaji da gudu zaku amince. Wani abu ne fa da na jiyo ya girgizani. Sai nace bari dai na kiraka ko kasan da zancen”.

    “Oh to Masha ALLAH, ALLAH ya tabbatar da khairan sa. Minene kake son ji haka?”.

   “Uhm wlhy Yaya nafaje gidan Smart ne ɗazun sai na samu Mawaddat na waya cewar ai ta kusa komawa free nan da 4days aurenta zai ƙare da Aliyu. Abin ya girgizani matuƙa”.

     “Ya Arrahaman”. Uncle Yousuf ya faɗa daga can cikin dafe kai. “Yaya kama sani kenan?”. Numfashi Uncle Yousuf yaja da saukewa. Sannan cikin nutsuwa ya sanarma Ahmad yanda akai zancen ya fito, ya ɗora da faɗin, “Ni ko ma Aliyun bamma maganar ba dan ba haka bane a raina. Wannan auren ina fatan sai mutuwa ce zata rabashi. Na saki jiki ne da tunanin tana zuwa gidansa zaibi duk hanyar daya dace wajen mantar da ita wannan shirmen. To ashe wata sabuwa ita hakan na ranta. Dole ne na kira Aliyu na sanar masa komai sannan kuma ya ɗauki duk ma matakin daya dace akan hakan. Amma zanyi ƙoƙarin dawowa nima duk da ban gama abinda nake ba. Dan ALLAH kaima ina son ka zaunar da Aliyu ka nuna masa abinda ya dace akan wannan batun. Idan ma yana ma Mawaddat saku-saku ne ya ajiye gefe ya koma wuta-wuta tasan shi bamu bane ba. Idan komai ya daidaita ya mata sauƙin”.

   “Shike nan Yaya insha ALLAHU yanda mukai da shi zakaji”. Daga haka ya yanke kiran. Smart yaji komai dan a hansfree yasa baya buƙatar ƙarin bayani, sai ma ajiyar zuciya da ya sauke dan ya fahimci Uncle Yousuf ɗin da manufarsa akan hakan. Ya kuma daina ganin laifinsa dan ko shine abinda zai yi kenan domin toshe kowace matsala da zata iya ta taso a lokacin…. Ahmad ne ya katse masa tunani da faɗin, “Mawashi a yanzu fa wannan yaƙin naka ne bana wani ba. Kai ya kamata ka nuna mazantaka komai ma za’ayi ayi karka biye mata. Sannan na fahimci kamar ido ka kawo ka zubamata shiyyasa ma take ganin komai normal ne. Dole fa kai ƙoƙarin dashen shukarka dan hana kowace irin barazana tasiri. Dan hatta da ita kanta hakan da zakai zai karya lagonta dan bazata taɓa yarda a tunɓuke wannan shukarba”.

   Tsaf Smart ya fahimcesa dan haka yay ɗan gajeren murmushi yana girgiza kai. “Ahmad bazaka fahimta ba. Mawaddat fa ta wuce duk yanda kake tunani. Sannan ni harga ALLAH bana son zuwa gareta batare da amincewarta ba. Shiyyasa na sake mata tare da nuna mata har yanzun a ƙasan nata nake dan hakan ne kawai zai iya karya lagonta harta saki jiki dani. Kuma Alhmdllh naga hakan yana tasiri sosai akanta . Taya kake tunanin yanzu na tunkareta da wannan sigar ai babu zaman lafiya”.

   “Humm kaifa na manta ashe sunanka namiji ɗaya tilo a tsakkiyar ƴaƴa mata shiyyasa. Mawashi na yarda da yanda ka tsara ɗin kuma hakan ma hanyar maslaha ce mai ƙyau da anan gaba ita kanta sai tayi alfahari da kai. Amma kai ya kamata ka memo hanyar da zakabi ta amince maka da kan nata ku zama ɗayan. Mudai fatan mu ai ayi shukar dan shi kaɗaine nake ganin zai hanata kowane irin motsi musamman daya kasance a yanzu tanada defenders a gefe kuma masu ƙarfi.”

    “Na yarda da kai, amma kuma tayaya zanyi hakan batare dana ɓata abinda na fara ginawa a zamanmu ba?”.

   Dariya sosai Ahmad ya shigayi har sai da Smart ya fara ƙuluwa sannan ya sassauta. Ya ce, “Shiyyasa nace kaifa gata yay maka yawa na kasancewarka ɗa namiji ɗaya tilo a tsakkiyar mata shiyyasa abubuwa da yawa kai hoto ne. Karka damu wannan aikina ne. Kai dai yanzu tashi ka koma gida ka maida komai ba komai ba. Amma yaran nan data cika gida da su ka tattarasu gobe su koma gida”.

      Cikin ɗan taɓe baki Smart yace, “Dama zasu koma goben ne ai saboda school. Amma ka faɗamin mi zakayi?”

   “Babu ruwanka da abinda zanyi, ai kasan dai bazan cutar da kai ba.”

  “Na sani, amma dai ya kamata ace na sani ko”.

     “Karka damu zaka sani, nima sai nayi mazari”

  Daga haka suka fito anan massalacin ƙofar gidan su Ahamd sukai salla. Ya amshi key ɗin motar Ahmad ya wuce gida. Yanzu kam ya samesu su duka a falo suna kallo. Sannu da zuwa suka shiga masa a zatonsu isowar kenan. Ya zauna yana amsa musu da tambayar lafiyarsu. Lulu na zaune a ƙasa tana shan fruits da aka yayyanka a bowl. Ta sauya kaya alamar wanka tayi, dan wando ne da riga marasa nauyi a jikinta. Kan babu ɗan kwali ya dai sha gyaran da sukayo yau sai ƙyalli yake yi. Idanunsa ya ɗan lumshe da sake lafewa cikin kujerar zantukan Ahmad na dawo masa a rai dalla-dalla. Shi yasan akwai ƙura, dan ko za’a kaisa jail sakinta bazai taɓayi ba koda a mafarki ne. Maryam ce data kawo masa abinda yace a masa cikin hikima ta janye su Amrah suka koma ɗaki tunda acan ma akwai tv. Lulu ta bisu da kallo tana faɗin, “Ku kuma ina zaku muna hira?”. Da dariya Maryam tace, “Aunty muna zuwa sirri zamuyi mu dawo yanzun”.

    “To ALLAH dai yasa bani za’a ƙullawa ba”.

  Dariya suka shige sunayi, yayinda Smart ya sakko ya zauna a ƙasan kusa da ita. Hannunta ya riƙo ya kai apple ɗin data ciro jikin cokalin bakinsa. Juyowa tai ta hararesa. Yay murmushi da ɗan kashe mata ido ɗaya. “Idan ma ke zasu ƙullawa ba gani a kusa da ke ba sai na kunceki tsaf na maida igiyar kansu Madam”.

    “A’a Granny ƙarewar Madam”. Ta faɗa tana sake balla masa harara. Dariya yayi yanzu kam fararen haƙoransa na bayyana da ƙyau. Sai da taji wani zuuu cikin kanta amma tai azamar ɗauke idanun cikin basarwa. Shiko ya cigaba da faɗin, “Ai ki godema ALLAH da baki zo a kakar tawa ba. Gaskiya da Kinga takanki dan sai na addabeki”.

    “Sai dai ko mu addabi juna. Dan kaima kasan Lulu ƙamshi ba kanwar lasa bace.”

   “Niko nasan haka”.

 Ya faɗa cikin ɗage gira. Kankanar data tsiro ta tura masa a baki tana harararsa. Ya shiga shan abarsa yana murmushi. Itako ta maida hankalinta a kallon da sukeyi dan tana matuƙar son film ɗin duk da horro ne. Shima gyara zamansa yayi ya matsa jikinta sosai ya jingina bayansa da kujera kamar yanda tayi. “Wai sai sha kike baƙya bani ALLAH sarki autan Ammah akwai haƙuri”. Ya faɗa a mararairaice. Juyowa tai ta kallesa, sai kuma ta kalla fruits ɗin. “Oh kace kwaɗayi ya zaunar dakai nan ɗin ba kallo ba ashe?”.

    “To kusan haka”.

  Ya bata amsa yana shafar sumar kansa da bata da yawa can sosai, sannan tafi saisaye kuma. “Kwaɗayi dai mabuɗin wahala ne” ta faɗa tana tsiro abarba ta miƙa masa. Maimakon ya amsa cokalin sai ya riƙe hanunta ya kai abarbar bakinsa a haka da nata hannun. Batace komai ba ta janye hanunta daga nasan. Sai ta koma idan ta sha saita tsira ta miƙa masan, shi kuma ya riƙe hannun nata ya kai bakinsa. Harda ɗan kwanto kansa a kafaɗarta kaɗan. Shagala datai a kallon yasa bata maida hankali ba duk da tabbas tana jin kan nasa a kafaɗarta sai dai ba sakar mata nauyi yay ba sosai.

     “Wai ko ki tambaya inda naje, da zan tafi baki tambaya ba. Ina can munyi waya baki tambaya ba. Na dawo ma haka. Anya zaman tare yace haka Mawaddatan’warahmah”.

   Yanda ya kirayi sunan nata sai da taji zuciyarta ta motsa. Duk da kuwa Uncle Yousuf kan kirata da sunan lokaci zuwa lokaci. Kansa da ke a kafaɗarta ta ture da faɗin, “Mi haɗina da tafiyarka da dole zan dage sai naji. Ko salan a kirani mai gulma kuma”.

      “Haka ne kuma fa”.

   Ya bata amsa cikin rashin damuwa. Sai kuma ya jawo tray ɗin da Maryam ta ajiye ya buɗe ƙaramin flaks da ta saka kunun madara a ciki ya zuba a cup, kaɗan yasa suga. Ya fara sha ya lura tana kallonsa. Kofin ya miƙa mata batare da yayi magana ba. Sai ta ɗan yamutsa fuska tana girgiza kanta.

      “Da akwai daɗi fa, ɗan-ɗana kaɗan kiji”.

   Kamar bazata amsa ba sai kuma dai ta amsa ɗin, kaɗan ta ɗibo a spoon ɗin takai baki. Sai ta ƙara ɗibowa tana kallonsa. “Akwai fa daɗi, ni dana ga tanata haɗa-haɗa sai na ɗauka jagwalgwali ne kawai”.

    Murmushi yay mata da amshe spoon ɗin yana faɗin, “Karkuma ki shanye min to daga tayi”.

   “Oh ashe ba daɗi ni ka shanye mun fruits ɗina.”

       “Tofa gori ne abun? To shikenan musha”. Ya faɗa yana miƙa mata. Amsa tai ta sha ta miƙa masa itama, haka suka dingayi yanzun ma dai da spoon ɗaya suna kallo. Ya ƙare ya sake ƙara musu wani. Sai gashi sun shanye kunun flaks ɗin duka. Farfesun dake cikin kwanon kuma bai ciyu ba. Suna a falon har sai da Film ɗin ya ƙare. Shi ya kwashe kayan ya kai kitchen tare da kashe komai ya rufe ƙofar. Ita kuma ta tattara kayanta ta wuce ɗakinta ko sai da safe babu. Da kallo kawai ya bita yana girgiza kai, shima sai ya nufi nasa ɗakin. Sai da ya kammala komai na al’adarsa kafin kwanciya sannan ya canja kayansa zuwa na barci yasa turare yay brush ya fice. Lulu na zaune a tsakkiyar gadonta tana aiki a system ya shigo. Kallonsa take da mamaki daga sama har ƙasa. Kafin cikin ƙarfin hali ta ce, “Lafiya kuwa?”.

     “Ƙalau”.

   Ya faɗa a taƙaice yana hayewa gadon…….✍️

    😜Wace gulma ta kawoshi ka to🚴

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣4️⃣

…….Sai da ya kai kwance duk tana kallonsa sannan ya cigaba da faɗin, “Zan kwana anan dan karma yaran can su fahimci wani abu daban har su faɗa a gida. Bazan so Ammah taji abinda bashi take fata ba a rayuwar gidana”.

        Duk da maganar tasa ta ɗan zabureta a zuciya sai ta kanne da tureta gefe ta ɗauke kanta. Sai kuma ta juyo da tura masa bargo ta ce, “To ga duvet nan koma sofa. Dan wlhy ban iya kwana da mutum biyu a gado ba, a cikin ɗaki ma kowa da makwancinsa ko yara ne takura nakeyi. Balle ma kai ƙato da kai ai saika sakani firgita”.

    Dariya maganar tata ta bashi, amma sai ya kanne baiyi ba yay ɗan murmushi kawai da kai hannunsa kan tarin fillos dake a gadon ya jawosu. Ita ya kalla da faɗin, “Kinga ɗan matsa gaba”. Matsawar tai shi kuma ya shiga jera fillos ɗin a tsakkiyarsu. “Gashi nan nikam an raba basai kin korani saman sofa ba dan bazan iya barci acan ba nima.”

    Harararsa tai da sake faɗin, “To nifa wlhy zan iya tsorata?”.

  “Saboda mi? Bayan kin san dai ni ne kuma bazan kawo wani hari ba inma yaƙin ƙasa da ƙasa kike tsoro”.

    Ba fahimtarsa tai ba ita kam. Dan haka kai tsaye ta ce, “Kawai dai bana son namiji kusa dani, dan yana tuna min abinda bana son na tuna?”.

   (Anzo wajen) ya faɗa a zuciyarsa. A zahiri kam sai yace, “Ai komai nada dalili. Miyasa hakan?”.

      “Humm manta kawai”.

   Ta bashi amsa tana maida hankali ga laptop ɗin tata. Shiru yay dan baya son nuna mata zaƙuwarsa na son ji. Sai ma ya lumshe idanunsa kamar wanda yay barci. Itama aikin ta cigaba da yi zuciyarta dai na wasuwasi akan kwanansa a ɗakin, wata kuma na ƙoƙarin nusar da ita na yau ne ai kawai. Bashi da wata manufa kuma tunda bai taɓa gwada makamancin hakan ba sai yau da yaran nan ke a gidan. Haka dai ta cigaba da saƙawarta da kwancewa har aikin ya nema gagararta, da ga ƙarshe dole ta kashe system ɗin da tattare takardun data baza. Juyawa tai tana kallon Smart da ke sauke numfashi a hankali, da gaske yanzu kam yayi barci dan a gajiye yake matuƙa. Sai ta samu kanta da sauke numfashi mai nauyi itama. Sauka tai a gadon ta nufi bayi, bata jima sosai ba ta dawo. Kasancewar dama wutar ɗakin ba wata mai haske bace can sosai ya sata ɗan tsayawa tana kallonsa da alama dai har yanzu zuciyarta na rawa, dan kallon da take masa bawai kallone irin na ka ɗauki hankalina ba, a’a kallone irin na nazari akan son yanke hukuncin na yarda ko kar na yarda?. Ta jima a wajen tsaye har ƙafafunta suka fara mata dayi sannan ta jasu da ƙyar ta koma saman gadon dai ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya a jere. Addu’ar barci da yakan gargaɗeta ta dinga yi wanda Alhmdllh ta yi nisa kaɗan a koyansu ta fara, sai dai bata zaton takai ko rabi ba barci ya kwasheta. Dan itama ɗin dai akwai gajiya tattare da ita, sannan da rana bayan dawowarsu ta sha syrup kwalba ɗaya. Gaba ɗayansu kamar wasa duk sai barcin yay musu nauyi sosai, kusan gabannin asuba Smart ya farka, jin abu a jikinsa da ɗumin da baiyi kama dana bargo ba ya sashi buɗe idanunsa da ke cike da nauyin barci da ƙyar. Akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta ya sauke cikin ɗan hasken ɗakin, barcinta take hankali kwance lafe a jikinsa kamar wata ƴar mage. Sai da ya ɗan waro ido na mamakin yaya akai hakan ya faru? Juyawa yay ya kallesu su da gadon, sai yaga tabbas shine ya ture filos ɗin tsakkiyarsu da ya jera ya dawo inda take. (Ɗan Ammah kaika fara kawo wannan harin na tsakanin ƙasa-da-ƙasa fa kenan) ya ayyana a zuciyarsa. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yay ɗan luuu da idanu yana maida kansa ga filonta da ya dawo kai. Kamata yay ace ya koma inda yaken kafin ta farka dan kuwa dai yasan zai sha cara, to amma yana yin wani motsi fa zata iya farkawa matsalar da yake gudun ta afku saboda a jikinsa take sosai, sai kawai ya zaɓi zubama sarautar ALLAH ido tunda akwai sauran daren, shima sabo da tashi yin nafilfilin daren ne ya sashi farkawar. Gashinta da duk ya zazzame da ga cikin ribbon da aka ɗauresa yasa hannu ya gyara mata, sai ƙyaƙyƙyawar fuskar tata ta sake fitowa fes da ƙyau. Kwanciyarta tai ƙoƙarin gyarawa da sake mamuƙesa a cikin barci batare data sani ba, dan ta kasance mai ɗabi’ar rungume filos idan tana barci, a yanzun ma dai da alama hakan take tunanin tayi, batasan baban filos bane gaba ɗaya😂. Ba shiri Smart ya rumtse idanun da ƙarfi yana cije lips, (Wayyo ɗan Ammah itamafa ta kawo hari wlhy, shike nan ƴan tada zaune tsaye sun fara tattaro makamai) ya sake faɗa a zuciyarsa yana matse jikinsa a waje guda sai dai ina a jikin nasa take ma gaba ɗaya, ta kuma cigaba da barcinta hankali kwance. Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da buɗe idanun da ƙyar a kanta. Wannan fa shi ake kira siye da kuɗi yafi siye da bashi, dan fuskarta ta sake matsowa kusa da tashi sosai ga numfashinta da ke sauka masa a kan fuska na sake rikita masa lissafi. Maida idanun kawai yay ya rumtse, sai dai zuciyarsa da gangar jikinsa sunki yarda da wannan lallashin, har takai baima gama yanke hukuncin abinyi ba kawai ya sauke lips ɗinsa akan nata, tun yanayi cikin shakka-shakkar karta farka har ya dake kawai abinsa yama ɗaura hannunsa sosai a jikinta ya sake turata ciki. Sam Lulu bata da nauyin barci, dan haka ta farka kuwa jin baƙon al’amari a gareta, sai dai nauyin da idanunta sukai da ma jikin nata ya sata jan sakanni kafin ta fahimci mike faruwa. Wannan ma wata dama ce ga Smart dake shagulgulansa batare da yasan ƙasar da ya kaima harin ta farka ba. Lokacin da ya kamata ta ɗauki mataki itama jikin nata ya fara amsar harin nasa, sai ta samu kanta da ƙoƙarin maida murtani. Rikicewa Smart ya sake yi illahirin jikinsa ya shiga rawa, sai ya nema canja salo akan fiye da abinda yake yin. Anan ne fa Lulu ta dawo hayyacinta, jikinta daya fara rawa ta fisge taja baya, sai kuma ta shiga kallon gadon da sauri, cikin ƙarfin hali da dafe kai shima Smart ya tashi zaunen. Masifa take son masa, amma bata da wani ƙarfin yinta, sai kawai ta sakar masa kuka.

    (Ya ALLAH) ya ambata a zuciyarsa da janye hannunsa da ya dafe goshi ya ɗago idanunsa da sukai matuƙar kaɗawa ya zuba a kanta. Lips ɗinsa na ɗan rawa ya ce, “Mawaddat…” yama kasa ƙarasa abinda yake son faɗar, sai kawai ya sake dafe kan tare da komawa ya kwanta..

      Hakan da yay sai ya sa wani irin takaici sake mamaye zuciyar Lulu wato ma kenan yayi hakanne dama da shiri. Tattaro dukkan ɓacin ranta take a maƙoshi, amma ta kasa furtawa, sai kawai ta tura kanta cikin ƙafafunta ta sake sakin kuka. Har cikin tsakkiyar ransa yake jin kukan nata, ga bala’in daya ƙulle masa ciki ya sashi kasa koda iya motsawa, jin ta sauka a gadon ya sashi buɗe idanun nasa da ƙyar, dai-dai nan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita tare ba banging nata da ƙarfi har sai da ya rumtse idanunsa. Har aka kira asuba ya kasa tashi saboda halin da yake ciki, ita kuma bata dawo ba, addu’a kawai yake ALLAH yasa ba ɗakin yaran ta tafi ba, duk da baya jin zatai hakan. Duk da halin da yake ciki shi ya cancanci tausayi amma shi ita yake tausayawan, dan yau ya sake tabbatar da akwai wani abu a ranta da yasa take ma tsanar maza da ƙara ƙaimi wajen son ɗaukar mataki akan masu fyaɗe. Hakan kuma nada alaƙa da cin kashin da takema ƴan aikin gidansu, dan tun a wancan karon dama ya lura tafi taka mazan fiye da matan. Da ƙyar yay dauriyar sakkowa ya nufi bathroom ɗin ɗakin, ko kayan bai cire ba ya sakar ma kansa ruwan sanyi, ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jajjere, yafi mintina goma kafin ya kashe shower ɗin ya zame kayan jikinsa, dole ya tsaftace jikinsa sannan ya fito, har yanzu dai da alama cikin nasa bai saki ba, a haka yay dauriyar fita a ɗakin ɗaure da towel ɗinta. Falo ya fara dubawa ko tana nan, amma bai ganta ba, sai kawai ya yarda wajen yaran taje. Lips ɗinsa kawai ya cije ya koma bedroom ɗinsa, sai kuma a mamakinsa ya ganta kwance anan. Dan yana buɗe ƙofar tana miƙewa zumbur cikin ɗan barcin da ya figeta bayan ta gama shan kukanta a dalilin abubuwa da yawa na rayuwarta da suka shiga dawo mata wanda bazata taɓa mantawa da su ba.

    “Nan ma biyo ni kayi? Aliyu ni zaka shiryama tuggu kamin fyaɗe! Wlhy ka sani nafi ƙarfinka kai da ma duk ire-iren ka, kuma da ga yau idan ka sake tunanin raɓata sai na ɗauki mataki a kanka dan zan iya maka illa, dan haka ka kama kanka kwanakin nan su cika batare da ka rasa wani sashe na jikinka ba!”.

    Sororo Smart yay kawai yana kallonta, yanda take maganar da dukkan gaskiyarta ga hawaye tanayi kuma, kalmar “Zan iya illataka Aliyu! Wlhy zan iya illata ka kamar yanda na kashe wancan tsinannen” ta sashi dawo hayyacinsa. Sai kuma ƙirjinsa ya shiga bugawa, amma sai yay jarumtar dannewa wajen faɗin, “Mawaddat relax ni fa mijinki ne, ki sani ni ba irin waɗancan da kike tunani bane, ALLAH ya halatta min ke duk abinda zan miki bada nufin cutarwa bane. Mawaddat aure yanada tarin abubuwa da suka banbanta da abinda zuciyarki ke iya hasaso miki. Dan ALLAH ki bar kukan nan haka ki nutsu bayan munyi salla muyi magana”.

    “Bazanyi magana da kai ba Aliyu, bakuma zan sake ganin mutuncinka ba wlhy, ban san haka kake ba ai kaina da ban ɗauke ka a yanda na fara ba….” fuuu ta fice a ɗakin nan ma tai banging ƙofar da ƙarfi har sai da ya ɗan zabura. Ya jima shiru abubuwa da yawa na masa kai da kawo a zuciya har aka fara ƙoƙarin shiga salla. A gaggauce ya shirya sai dai bazai iya fita massalaci ba dan cikinsa yay masifar ƙullewa dole a gidan yay salla. Bayan ya idar yana son zuwa inda take amma yana gudun kar yaran can su fahimci mike faruwa. Dole ya haƙuri akan har sai sun wuce, dan haka ya hau gado ya kwanta. Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai zazzaɓi ne mai zafin gaske ya lulluɓe Smart harda su rawar sanyi………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣5️⃣

………Lulu duk da ranta a dagule yake tayi dauriyar dannewa saboda yaran, kasancewar Maryam akwai hankali tunda daddare ta tsara musu su tafi yau suba ma’auratan waje, sai kuma akai sa’a har su Amrah suka fahimceta. Koda gari ya waye sukaga basu fito ba basu damu ba suka gyara gidan tsaf sukai break fast. Nasu sukaci suka shirya musu nasu a table. Sun kammala kenan Lulu ta fito. Gaisheta sukai su duka cikin haɗa baki, ta amsa musu tana murmushin ƙarfin hali, dan girmamawa na ɗaya da ga cikin abinda Lulu keso gana ƙasa da ita. Wannan kuma shine mataki na farko da dangin Smart suka kama mata zuciya da shi, yau gashi har ƙannenta sun kwatanta abinda bata taɓa gani ba. Kamar yanda suka tsara Maryam ce ta sanar mata zasuje gidan ƙunshi su taho da mai ƙunshi da tace tana so. Lulu bata kawo komai a ranta ba ta ce, “Da sassafen nan kuma Maryam. Ku bari sai anjima ni ƙunshin ma kamar na fasa kuma”.

    “Kai aunty dan ALLAH karki fasa. Ai zamuje ne dan ta sani inma tanada wani aiki kinga ta kammala da wuri bawai yanzu zata zo ba”.

   “To shike nan, amma har ku duka zakije?”.

  A tare suka amsa mata da eh. Key ɗin motar ta dake a falon ta miƙama Amrah dan sun iya driving duk da dai ba basu mota ake ba sai ta kama. Cikin gargaɗi tare, “Banda ganganci Please”. Dariya kawai su Afrah sukai dan sun san dai aunty Lu.. ɗin su indai tuƙin ganganci ne ita ɗin master ce. Sallama sukai mata suka fice, dama sun fidda kayansu tun ɗazun..

   Kwanciya tai a falon batare da neman abincin da zata ci ba duk da kusan goma ne yanzun. Tana a wajen kwance ba barci take ba har sha biyu, tunanin abubuwa kawai take daban-daban, babu alamar su Maryam dan haka ta ɗaga waya tai kiran su Amrah. Cikin dariya suke sanar mata ai su suna ma gida, sai da suka fara ajiye su Asma’u ma sannan. Shiru kawai tai da mamakin wai ita yaran nan zasu yaudara, sai kawai tai ƙwafa ta yanke kiran. Ɗan jimm tai saboda abinda take jiyowa kamar ƙaƙarin amai, kamar zata share sai kuma ta miƙe da sauri jin abin na ƙaruwa. Sam batai tunanin Smart na gidan ba, ɗakin nasa ta shiga dan anan take jiyowa, nan ɗinne kuwa a cikin toilet, mamaki ya kamata duk da matsanancin haushinsa da take ji na abinda ya faru sai ta nufi bayin. Sosai gabanta ya faɗi, har bata ma san sanda ta afka bayin ba inda yake.

    “Lafiya kake kuwa?”.

  Bai iya bata amsa ba dan ya gama galabaita da aman, dole ta ajiye komai da ke ranta kuma ta shiga taimaka masa ya wanke bakinsa da fuska, da taimakonta ya fito ya sake hawa gadon ya kwanta.

      “Please lulluɓe ni”.

    Ya faɗa da ƙyar. Lulluɓe san tai hankalinta a tashe, dai-dai nan kiran Ahmad ya shigo wayarsa, har ya lumshe idanunsa ya buɗe, ita ya kalla yayinda ita kuma take kallon wayar. “Waye?”. Ya faɗa a hankali. Wayar ta miƙo masa da faɗin, “Besty kasa”. Sake maida idanun nasa yay ya lumshe da faɗin, “Ahmad ne ɗaga”. Kafin ta ɗaga ɗin wayar ta yanke, tana ƙoƙarin kira Ahmad ɗin ya sake kira. Ɗagawa tai ta saka a Hansfree da faɗin “Hello”. Daga can Ahmad ya amsa mata duk da yayi mamakin jin wayar a hannunta. Gaisheshi tai da sanar masa bai da lafiya.

     Hankali tashe Ahmad ya ce, “Ya ALLAH gani a ƙofar gate ai”.

  “Okay to bara ina zuwa”.

Tai maganar tana yanke kiran. Wayar ta ajiye ta miƙe, Smart da ke saurarensu ya buɗe idanunsa a kanta, a hankali ya furta “Please kar ki fita a haka kisa hijjab”. Harararsa tai batare da tace komai ba ta fice. Samun kanta tai da shiga ɗakinta ta ɗauka hijjab ɗin ta saka sannan taje ta buɗema Ahmad ɗin. Ita tai masa rakkiya har ɗakin Smart ɗin ta fito ta barsu.

     Bayan Ahmad yay masa sannu ya ce, “Tashi zakai mu tafi asibiti”.

Kai Smart ya girgiza masa yana ɗan buɗe idanunsa, “Basai naje asibiti ba zai bari da kansa in sha ALLAH. Tunda ma na samu nayi aman shike nan”.

   Ahmad ya riga da yasan miye matsalar Smart ɗin. Dan haka yay shiru kawai. Dai-dai nan Lulu ta shigo ɗakin da sallama. Amsa mata Ahmad yayi. Ta ajiye tray data haɗo abincin tana faɗin “Ya sanar maka abinda ke damun nasa kai ko?”. Murmushi Ahmad yay da bata amsa. “Kin san mutumin naki ai, yanzu ma fama nake da shi muje asibiti yaƙi”.

     Kallonta takai kan Smart, ganin shima ita yake kallo ƙasa-ƙasa saita janye nata da ɗan taɓe baki. Shi Ahmad ma sai suka bashi dariya. Dan haka ya miƙe. “Inaga bashi abincin ni bari naje na samo masa magani, dan tunda yace bazaije asibitin ba to bazai je ba”. Bai jira cewarta ba ya fice. Ɗan hararar Smart Lulu tayi, a taƙaice ta ce, “Ka tashi”. Sake buɗe idanun nasa yay ya zuba mata su na kusan minti ɗaya, ita kuma ta kauda nata dan tun ɗazun yanda idanun nasa launinsu ya sake canjawa suka fito a sak na macizan da take kiransu taji bata son ya kalleta. Hannu ya miƙa mata alamar ta kamashi. Kamar zata share sai kuma dai ta kama dan ya ɗan bata tausayi kuma. Harya faɗa kamar wanda ya kwana biyu yana ciwon. Shayin data haɗo masa ta miƙa masa, babu musu ya amsa tare da motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Thanks”. Koda ta miƙa masa soyayyan doyan sai ya girgiza mata kai alamar bazai ci ba. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta maida doyar ta ajiye. Tana zaune ta ɗan juya masa baya tana latsa wayarta har ya kammala, kofin ya miƙa mata ya koma ya kwanta, ta tattare kayan ta fita da su, a lokacin kuma Ahmad ya dawo, ruwan da ya buƙata da Smart ɗin zai sha magani ta ɗakko masa, da ga haka ta koma falo tai zamanta…

   Ahmad bai bar gidan ba sai da Smart ya samu barci, bayan wucewarsa Lulu ta leƙasa, ganin yay barci ta ɗan sauke ajiyar zuciya da hararsa kamar yasan tanayi. Ɗakinta ta nufa ta ɗan kwanta itama dan shirun gidan kuma duk sai yay mata babu daɗi. Kusan a tare suka tashi bayan la’asar, tai wanka tai salla dan yanzu kam Alhamdullah, idan ma tai kamar zatai sakaci lokaci ya wuce sai taji duk babu daɗi har sai ta tashi tayi sallar take samun nutsuwa. Cikin skert dogo baƙi da ƙaramar top baƙa itama datai mata ɗas a jiki ta fito, kanta babu ɗankwali sai gashin da ya sha gyara yanata walƙiya. Wayar da take dannawa tana charting da aunty Naja’atu yasa bata lura da shi ba har sai da takai zaune. Shiko tun fitowarta ya zuba mata idanu, murmushin da take yi ya matuƙar ƙawata ƙyawunta da motsa rauninsa. Hakama kwalliyar tata ta ɗauki hankalinsa duk da ita hakan normal ne a gareta badan wani birge miji ko wani abu ta saka ba tunda dai sune kayanta na koyaushe fiye da atamfa. Ƙaramin gyaran murya da yay ya sata farga da shi, dariyar da takeyi a hankali ta haɗiye ta ɗago idanunta da sukai wani tar-tar da su da haske mai ɗaukar hankali kasancewar duk yau da ba’asha komai ba.

   “Dama haka ake jiyyar mara lafiya Madam?”.

   Hararsa ta ɗanyi da taɓe baki. “Ka dai san mai jiyyarka ba dai Mawaddat ba”.

     “Uhm hakane ashe Ahmad ne kuma fa”.

    Ya faɗa yana danne dariyarsa.

  Sake taɓe bakin tai taƙi cewa komai. Da ga haka shiru ya ratsa falon, yana tunanin faɗa mata zancen tafiyarsa da ya taso ne, dan abinda ma ya kawo Ahmad kenan, amma sai yaga bari dai ya bari ta sake nutsuwa ko zuwa gobe in sha ALLAHU. Kusan mintuna goma ya sake takalota da faɗin, “Ba abinci gidan ne? Ina kuma yaran nan banji motsinsu ba?”.

      Yanzu kam kai tsaye ta bashi amsa da “Sun wuce”.

   “Abincin fa?”.

“Na daina girki a gidan nan”.

“Miyasa?”.

   “Ba sai da dalili ba, dama can ra’ayi nayi, yanzu kuma na daina sai ka bari sai ka auro matar da zata maka”.

      “Kishiya kike sha’awa kenan?”.

   Kamar bazata tanka masa ba sai kuma tai murmushi. “Sai dai idan yau zaka aurota ko gobe kafin cikar jibi da zan ƙara gaba maybe wasu su kalleta a matsayin hakan”.

    Murmushi kawai ya saki, maimakon cewa wani abu akan batun nata sai cewa yay “Bani furar da Ahmad ya kawo Please dan yunwa nake ji”. Kamar bazata je ɗin ba sai kuma ta miƙe. Babu jimawa ta dawo da furan da kofi ta ajiye masa ta koma inda ta tashi. Television ta kunna shi kuma ya zuba furar ya fara sha.

  “K mi kika ci?”.

 “Ba buƙata”.

Ta faɗa a takaice.

   “Okay amma da kinsha furan da ga gidan Ammah ya amso ta”.

   Ɗagowa tai ta kallesa. Sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.

      “Gama ka bani kofin bana jin sake tashi”. Ta faɗa tana maida kanta ga wayarta. Bai sake magana ba har ya gama ɗin ya zuba mata, sai dai bata da yawa dan haka ya miƙe da kansa yaje kitchen ya sake ɗakko wata ya ƙarasa cika kofin ya miƙa mata. Hankalinta nakan waya take shan furar harta shanye, sake ƙarawa tai. Sai da ta shanye ta biyun yay ƙaramar dariya da faɗin, “Babu wata furar Ammah da kika sha yarinya a titi ya sayota”. Da sauri ta kallesa tana yamutsa fuska, ya sake sakin dariya da nuna mata 8-10. Filo ta ɗauka ta jefa masa da yin ƙwafa tana harararsa, sai kuma ta fara ƙaƙarin amai shiko ya cigaba da dariyarsa. Kofin takai kitchen ta wanke dan bata ƙaunar ƙazanta, duk da kuwa aikin na cimata rai dan ma yana ƙoƙarin taya ta ne, tun tana ƙorafin mai aiki har ma ta bari tunda dai taga kwanakin sun ƙare mata a gidan. Falon ta dawo ta cigaba da ɗan kallon abubuwa a TikTok. Shiko yana kwance shiru ya zuba mata ido ta ƙasa kawai yana kallonta. Kiran sallar magrib ne ya tadasu su duka. Smart ya wuce massalaci ita kuma ta tafi ɗaki. Bai jimaba ya dawo gidan saboda abinda ke damunsa ba wai ya gama sakinsa bane gaba ɗaya, jarumtar da ya saba ce kawai ta dannewa. Bai samu Lulu a ɗakin ba dan itama tana nata ɗakin a cikin makamancin irin nasa yanayin koma ace wanda yafi nasan. Dan wani abu ne ke faman ratsa mata jiki mai ban mamaki. Ga tsigar jikinta sai faman tashi take kamar mai jin sanyi. Al’amarin kamar wasa sai ya fara neman fin ƙarfin Lulu, dan da ƙyar ta iya tashi tai sallar isha’i……..✍️

   😵‍💫Lulun mu muya hwaru kuma🥲?

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣6️⃣

……..Tana idar da salla falo ta koma a daddafe, a ganinta ko zata samu sassaucin abinda takeji ɗin, sai dai kamar ma ana ƙara iza mata wutar masifa ne a cikin jininta. Saman 3sitter ta haye tare da dunƙule jikinta waje ɗaya tana jin hawaye na ciki mata ido. Ta rasa wannan wace irin masifa ce haka mara daɗin kwatance.

    Ana idar da salla shima Smart gidan ya nufo, dan har yanzu ba wani ƙarfin jikinsa yake ji ba, tunda ya shigo falon idanunsa suka sauka a kanta, ya ɗan yi jimm yana kallonta kafin ya ƙaraso ciki sosai yana ambatar sunanta. Bata motsa ba, hakan ya sashi fahimtar babu lafiya. Har inda take ya ƙarasa, ya kai zaune a kujerar da take yana mai leƙa fuskarta. Hankalinsa ne ya tashi ganin tana hawaye.

       “Ya Salam kuka kuma? Baki da lafiya ne?”. Yay maganar yana riƙo hannunta data dafe cikinta, gaba ɗayanta ya ɗago zuwa jikinsa, sake shige masa tai cikin yanayin kamar mai rawar sanyi. Hakan sai ya bashi mamaki dan ba halinta bane hakan sam kusanta kanta da shi, sannan bai manta da gargaɗinta na ɗazun akan karya sake taɓata ba. Jin yanda tama kanannaɗe masa a jiki tana shashshekar kukan da ke ratsa masa zuciya ya sashi kasa iya cewa komai. Kusan mintina uku suna a haka kafin ya ɗago fuskarta dake kwance saman ƙirjinsa hawayenta na sauka masa, itama ɗagowa tai a hankali suka zubama juna ido cikin wani yanayi mai wahalar fassara. Hannunsa ya ɗaura saman fuskarta cikin ɗan lumshe idanu da buɗewa ya furta, “Mawaddatan’warahmah!”.

       “Uhhmyim”.

    Ta amsa shi acan ƙasan maƙoshi tana lumshe idanunta hawayen da suka sake cikashi suka zubo. Jiyay gaba ɗaya hankalinsa ya sake tashi, cike da damuwa ya ce, “Har yanzu kina fushi da ni akan abinda ya faru shiyyasa kike kuka ko?”.

      Idanunta da sukai mugun canja launi ta sake buɗewa sosai a kansa, fuskarta a ɗan taɓe kamar mai son sakin kukan shagwaɓa ta girgiza masa kai.

    “To mike damunki? Ko baki da lafiya?”.

   Maimakon bashi amsa sai ta kamo hanunsa ta ɗaura a saman cikinta. Kallon cikin yay da sauri, sai kuma ya dubeta da faɗin, “Yana miki ciwo ne”. Kamar ba Lulun nan da ya sani masifaffiya ba, ta ƙara manna hannunsa akan cikin nata muryarta data koma can ƙasan maƙoshi na ƴar rawa-rawa ta ce, “Hydar yan….” sai kuma ta kasa ƙarasawa kawai ta sakar masa kuka. A karo na farko gabansa ya faɗi, ya kamata zai tayar yana faɗin, “Kinga tashi muje asibiti”. Girgiza masa kai tayi da sake nannaɗewa a jikinsa tare da kai hannunta saman gashin da ke kwance a fuskarsa luf-luf ta zubawa lips ɗinsa idanunta da sukai matuƙar juyewa fiye da yanda idan tasha kayayyakin ta sukeyi. Sororo yake kallonta, dan wannan kam shi shaida ne ba ɗabi’a ce ta ta ba. Yanda ta motsa ƴan yatsunta cikin gashin sajensa ya saka tashi tsigar jikin yamutsawa, tare da harbawar zuciya, abinda ke ƙoƙarin lafawa da ya girgiza ƴan maza a yinin na yau na ƙoƙarin zaburowa. (Anya ba wani abu daya fi ƙarfin kan yarinyar nan ta sha ba?) wani sashe na zuciyarsa ya ayyana masa, sai kuma yaji hakan bai kama hankali ba… (To mike faruwa?) Ya sake ayyanawa, sake ji yay zuciyarsa ta motsa, dan kuwa kalaman Ahmad na daren jiya ne suka shiga maimaita kansu a kwakwalwar sa, sai kuma furar da suka sha, tabbas akwai alamar tambaya… Saukar lips dinta saman nasa a bazata ya katse tunaninsa, sai riƙon da tai masa mai lafiya daya sakashi yin baya gaba ɗayansa ya zube a kujerar…..

   Dama mai neman kuka ne aka jefa da kashin awaki, kuma kamar Lulu ta kawo kuka ne gidan mutuwa. Sai ya kasance ita da aka saka a tarko ma ya fita rikicewa. Ganinfa ƙurar yaƙi na neman fara tashi a muhalin da bai kamata ba bai ma san lokacin da ya bar falon da ita ba zuwa bedroom ɗinta ba…..

   Sai da ya gama tabbatar da ta shiga hannu fiye da yanda yake buƙata, duk da harga ALLAH bada saninsa ta sha abinda ya kaita ga miƙa wuyar ba cikin sauƙi. Gashinta da ke cikin ribbon ya wargaza tare da duƙo fuskarsa gab da tata suna kallon juna, murya can ƙasa kamar zai saki kuka ya furta, “Kin yarda Aliyu Hydar ya zama Mawaddat? Mawaddat ta zama Aliyu?”.

   Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta ɗan buɗe idanunta data lumshe a kansa itama, so take tai nazari akan maganar tasa amma ta gagara samun kowace irin dama daga gangar jikinta zuwa ƙwaƙwalwa, sai ma hannunta ta ɗaura akan nasa tana girgiza masa kanta. Itama acan ƙasan maƙoshi ta ce, “Ina jin shakku”.

     “Kar kiji shakkar komai, Aliyu na *_SONKI_*, yana kuma buƙatar ki matsayin uwar ƴaƴansa abokiyar rayuwa ta har abadan Mawaddatan’warahmah. Na miki alƙawarin bazaki taɓa dana sanin zama mallakin Aliyu ba, in sha ALLAH sai na nunama duniya Mawaddatan’warahmah ba Lulu da suke kallo kawai bace akwai wani babbar nagarta tattare da ita”.

    Murmushi ta saki mai ɗan sauti ta buɗe idanunta data sake rufewa suka zubama juna ido. “Mi kake nufi Aliyu?”.

   “Baki LABARI kawai zai baki, amma gangar jiki tabbatar wa zatai kafin zuciya ta amayar da sirrin da ke cikinta. Alƙalamin ƙaddara ya jima da bushewa Mawaddat, hakama takardu sun daɗe da ɗaguwa. Miya rage garemu? ƙarasa zuwa filin yaƙin da zai bayyana Aliyu mijin Mawaddat ne kawai domin hutar da zukata masu farautar igiyar da UBANGIJI ya riga ya gama ƙadarta ƙulluwarta tun kafin haihuwar mu…..”

   “Bana gane zance a curkuɗe ka buɗemin kawai Aliyu, kana saka ni a duhu da dogon nazari a duk sanda ka ɗauki wannan tsagin na curarrun kalamai”.

      Goshinsa ya kai saman nata, hancinsa na gogar nata suna shaƙar numfashin juna. Ya saki murmushi mai sauti. “Ki bani damar baki gaba ɗayan kundin curarrun kalamai na, ni kuma zan kasance miki malami mai fassara miki su feji bayan feji a mabanbanta zangunan da masu neman ilimin kan jima basu cimmawa ba Please Mawaddatan’warahmah, na fara gazawa, ni kuma bana buƙatar shiga makarantar da babu shaidar samun damar ɗaukar darasi a cikinta, dan zata kasance min tamkar ɗan yawon buɗe ido ne kawai”.

     “Mi kake buƙata da ga gareni?”.

   “Yarda”.

  “Karka zama bahagon malami”.

“Ki zama ɗaliba mai kaifin basirar ƙarɓa da haddacewa, domin ranar amsar sakamakon jarabawa ki ɗauki first class”.

    “Jarumta da kaifin basira a jinina suke”.

    “Ni mai yarjewa ne ga dukkanin furucinki, domin tabbatar miki da hakan muje matakin farko na tabbatarwa *_ALJANNAR DUNIYA TA_*”.

   Saukar lips ɗinsa akan nata ya hanata damar furta abinda ta so faɗar, hannu biyu ta amshesa kasancewar ita a karan kanta bata sana wacece ita a wannan fagen yaƙin ba. Abinda kawai ta sani gangar jiki da zuciya duka sun karɓa saboda hakan ne mafi ƙololiwar miradinsu a wannan gaɓar bisa tirsasawar abinda tasha batare da sani ba. Al’amari fa kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan su duk biyun cikin mata kai kowa ya fara kaima ɗan uwansa hari irin na ƙasa da ƙasa. Kafin kace mi sun birkice ma juna daga haka fa labarin ya canja a yanda su duka ba haka sukai tunanin rubutuwarsa ba, dan kuwa dai tabbas wannan daren yazo ne a bisa rubutun alƙalamin ƙaddarar da basu isa canjata ba koda ace sun so hakan. Lokacin da al’amari yay nisan zango Lulu ta fara dawowa a hayyacinta da fahimtar mike shirin faruwa. Sai dai me, Smart ya kai matakin da _Uranium_ ya ke shirin jefawa fa a ƙasarta ba nuclear bomb kawai ba.

    “Aliyu! Aliyu!! Hydar!!” ta shiga ƙwala kiran sunansa a matuƙar firgici na fita a hayyaci numfashinta na barazanar barin ƙirjinta saboda tsabar shiga firgici, sai dai ina wannan yaƙin na bashin gaba ne ba na kece raini kawai ba. Kuka ta fashe da shi da cigaba da kwala kiran sunansa da magiya kai harma da tabbatar da zata halakashi amma ina, turnuƙun ƙurar yaƙi ta lulluɓe ji da ganin idanu da kunnuwa sa, yafayi alƙawarin yau sai ya kai duk wani shegen tsageran kafiri ƙasa ko shima a lissafashi a jerin manyan jaruman mayaƙa da suka amshi turar ƙasa data MUSULUNCI a hannun dama. Wannan da shi ake kira TURNUƘU faɗan ibilisai, yaro bai gani ba balle ya raba🚴….

   A wannan turnuƙu duk wani wanda Lulu kema kallon defender a rayuwarta harma da ƴan koron abi yarima a sha kiɗa irinsu Deen sun sha kiran kawo ceto sai dai da alama ko fankar ɗakin tsoron ya hanata iya juya kanta balle su da ke nesa da jinta maybe ma wasu suna can a cikinsu suna mafarkin aljanna da naman kaji da madara😁.

     (ALLAH kasa munada rabon zuwa ba’a mafarki kawai ba mu da masoyan mu baki ɗaya💫. Amma fa safiyar gobe dole a sake maimaita ƙaramin yaƙin basasa kona wucin gadi ne tsakaninmu da Smart team sai sun mana dalla-dallar yanda akai aka kawo mana wannan yaƙin sunƙurun haka🚴🚴)

     ____________★

   Zaune take hakimce uwa wata sarauniya a makeken falonta tana ma ƴaƴan itatuwa tsinci ɗai-ɗai. Mai aikinta na daga ƙasa tana tausa mata ƙafafu. Kamar wanda aka jeho da ga sama ya faɗo falon, zaburar da mai aikin tata ta ɗanyi ne ya saka Dada janye idanunta da ga kan tv ta dubeta, masifar tata tai shirin balbaleta da ita, sai kuma tai tsit saboda gyaran muryar da yayi. Gaba ɗayanta ta juyo ta dubesa, sai kuma ta saki baki alamar mamaki.

    “Sulaiman? Kai ne?”.

  Murmushi yayi a karo na farko, sai kuma ya cigaba da takowa cikin falon. Kafin ma wani a cikinsu yay magana mai aikin Dada ta miƙe zumbur dai-dai yana kaiwa zaune a kujerar kusa da Dadan da faɗin. “Ni ne fa Dada. Mun sameku lafiya?”.

    “Sulaiman bakai fushi ba kenan?”.

  Ƙaramar dariya yayi da kamo hanunta cikin nasa, cike da sauke murya ya ce………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣7️⃣

………“Dada wane ɗa ne zai yi fushi da iyayensa. Balle ma ke nasan baki da laifi akan wannan al’amarin sam.”

     “Naji daɗi da ka fahimci haka Sulaiman, dan babu ta yanda zan goya bayan bare sama da jikana. A yanzu haka koda akai min katanga da bibiyar halin da kuke ciki ban zauna ba, kuma nayi alƙawarin sai Mawaddat ta dawo hanun Tajuddeen matsayin mata dan bazan taɓa amsar waninsa ba”.

   Wani irin farin ciki ne ya ratsa Alh. Sulaiman, dama shi yasan Dadarsa na tare da su. Dada dake murmushin itama ta ƙara ƙasa da murya da faɗin, “Labari ma mai da ɗi……” Tsaf ta kwashe yanda sukai da Lulu ta sanar masa. Baima san sanda ya lailayo wata ashariya ya dire ba a gaban mahaifiyar tasa. Ya ce, “No wander naga yaron nan Yousuf nata rawan kai, ashe shegen shine ya ƙulla komai”.

     “Wlhy kuwa, nima abin ya girgizani Sulaiman. Amma ka kwantar min da hankalinka jibi da kaina zanje na ɗakko Mawaddat ko yaron nan na yawo da ubansa a baya sai ya saketa”.

   “ALLAH ya barmin ke Dada ta”.

Ya faɗa cikin wani irin matsanancin farin ciki. Gaba ɗaya damuwarsa ta shafe ma. Bai iya dogon Zama ba a gidan bayan sun ɗan tattauna akan abinda ya samu Baba da ta bashi labari ya wuce gida kasancewar dare ya fara yi, yana tabbatar mata gobe idan ALLAH ya kaimu Tajuddeen zai zo ya gaidata, da dai ya ɗauki fushi bazai sake zuwa wajensu ba, amma yanzu zai lallasoshi, dan zai sanar masa ƙoƙarin da take masa. Sosai Dada taji daɗin hakan, dan ita kam ALLAH ya jarabceta da shegen ƙulafucin ƴaƴanta da ma jikokin duka. Sai dai kuma matan ƴaƴan nata da babu wanda ta ɗagema hula a rashin mutunci, juyasu take san ranta kamar waina a tanda kamar yanda ta kame ƴaƴan nata ram a hannu sai yanda tace musu, Alh. Sulaiman ɗin nema dai kan botsare mata a wasu lokutan dan shima dai halayyar tata ce ya ɗebo tsaf. Shiyyasa takanji shakkarsa duk da kasancewar itace ta haifesa, san nan tana sonshi sosai wannan a bayyane yake a wajen kowa ma, dan sam idan rashin mutuncinsa ya tashi ba raga mata yake ba tun ma yana ƙaraminsa, balle yanzu da yake jin ya gawurta da tumbatsa a gidan ta fanin dukiya da yin suna a cikin ƴaƴan nasu. Amma a kullum Dada bata ganin laifinsa sai ma bashi goyon baya da takeyi….

     __________★

    Matuƙar tashin hankali Smart ya shiga a lokacin da ya fahimci halin da Lulu ke ciki. Ta sanƙame masa babu alamar rai tattare da gangar jikinta, da ƙyar tunanin zuba mata ruwa yazo masa a rai, sai dai koda ya shafa mata ruwan ma shiru kake ji. Gaba ɗaya ruwan ya zazzage mata zuciyarsa na wani irin dokawa tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito waje. Wata irin zaburowa tai jikinta na jijjiga. A tsahon rayuwarsa baya jin ya taɓa fuskantar makamancin farin ciki da tashin hankali masu gogayya da juna irin haka. Duk yanda yake tunanin iya shawo kan matsalar hakan ya gagara, dan yanayin nata ya wuce dukkan tunani. Yasan idan yace zai ɗauketa zuwa asibiti a wannan halin bazai ma iya driving ba, to yama manta motar su Amrah sun tafi da ita gida, dan haka ya shiga neman wayarsa. Da ƙyar ya iya samota a ƙasa harta fashe. Bai damu ba ya shiga neman Ahmad dan shine kawai yazo masa a rai.

     Shigowar kiran ta saka Ahmad kwashewa da dariya, amma daya ɗaga sai ya dake dan shi duk tunaninsa Smart ya gano ne. Sai dai kuma jin muryarsa ta saka gabansa faɗuwa. Da sauri ya ce, “Mawashi Are you okay?”.

   “I am not Ahmad. Ina cikin tashin hankali ka taimakeni kazo mukai Mawaddat asibiti, Ahmad akwai matsala wlhy na saka yarinyar mutane a masifa….”

    Sosai zuciyar Ahmad ta jijjiga, amma sai yay saurin tarar numfashin Smart da faɗin, “Kaga Aliyu dan ALLAH ka kwantar da hankalinka, ka faɗamin mike faruwa ne. Ka sakani a tashin hankali nima….”

   Cikin ƙaraji Smart ya katsesa da “Mi kake son sani ne Ahmad!! Ina faɗa maka kazo muje asibiti kana gaya min na kwantar da hankalina na sanar maka mike faruwa?. Ahmad ka taimakeni karna rasata, bazan iya yafema kaina ba idan hakan ta kasance”. Ya ƙare maganar cikin sanyin murya hawaye masu zafi na gangaro masa a karo na farko…

       Kaɗan ya rage Ahmad yin aman zuciyarsa. Muryarsa na rawa da daburcewa ya ce, “Ka.. ka yi haƙuri gani nan zuwa.” baima jira amsar Smart ɗin ba ya miƙe tare da figar jallabiya ya saka. Karo suka kusan ci da Coach da ke ƙoƙarin shigowa ɗakin nasa, da mamaki ya ce, “Ahmad kana lafiya kuwa? Ina zaka haka?”.

    “Yaya babu lafiya, na aikata babban kuskure wlhy.”

   “Kai miye haka wai, nutsu mana”.

 Coach ya sake faɗa yana riƙo Ahmad da ke ƙoƙarin turesa ya fita.

     “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri idan na dawo zan maka bayani. Aliyu ne ya kirani…”

  “Kai bana son shashancin ka nutsu kamun bayani mana”.

    Rasa mi Ahmad zaice yayi, sai kawai cikin matuƙar gundura ya ce, “Asibiti yaya. Asibiti zan kaisu, na tabbata koma minene yanada alaƙa da abinda na aikata wlhy. Dan girman ALLAH ka barni naje”.

      Hankalin Coach ya fara tashi shima, dan Ahmad yana magana ne kamar zai yi kuka.

   “Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un. Ahmad Please ka faɗa min mike faruwa? Miya samu Aliyun ne? Mika aikata masa kuma?”.

      “Yaya nayi kuskure, abu na saka musu a fura, bana raba ɗayan biyu koma miya tada hankalin Mawashi nada alaƙa da abinda na aikata ɗin. Yaya kamarfa kuka yakeyi da tabbatar min zai rasata. Yaya ka barni naje dan ALLAH”.

    Kai Coach ya dafe domin ya samu amsar abinda ya kawoshi sashen ƙanin nasa dama. Dan dama matarsa ce ta bashi maganin da Ahmad ɗin ya yarda ɗazun batare da ya sani ba kuma an ɓalla maganin, kasancewarta likita yasa hankalinta tashi fahimtar maganin datai kona minene. Taso danne zuciyarta ta binciki Ahmad ɗin ita kaɗai amma saita kasa haƙuri ta tunkari mijin nata da batun shine dalilin fitiwarsa zuwa inda Ahmad yake. Yanzu kuwa jin zantukan Ahmad ɗin ya tabbatar masa su Aliyu ya bama maganin ke nan. Ba lokaci bane na dogon tunani, dan haka ya ciro wayarsa da ga aljihu yana faɗin, “Kaga bari Khadijah tazo kuje tare, yanzu dare yayi duk asibitin da zakuje zaku iya fuskantar matsalar ganin doctor.”

    Tuni Lulu ta sake fita a hayyacinta wa Smart, zuwa yanzu kam koda ya zuba mata ruwan ma batako motsa ba. Sai kawai ya dafe kansa dake wata irin masifar sara masa. Ya auna kiran Ammah sau shuri masaƙi zuciyarsa na gargaɗinsa. Hakama Abba. A wannan halin ya tsinkayi horn ɗin da yake ƙyautata zaton na Ahmad ne. Zumbur ya miƙe ya fito, dan yasan dole sai ya buɗe masa gate ya shigo. Doguwar riga ya samo ya saka mata, dama shi tuni ya suturta nasa jikin. Yana buɗe gate ɗin bai jira ƙarasa shigowar Ahmad ɗin ba ya juya cikin gidan da sassarfa. Fitowa aunty Khadijah tai tabi bayansa, yana ƙoƙarin shigewa bedroom ta kirayi sunansa. Da sauri ya juyo dan shi idonsa ma yay rufewar da bai kula da ita ba, sannan ya manta ma ita likita ce har sai da tai masa bayani. A tare suka shiga ɗakin, ta ajiye ɗan akwatin dake hannunta ta haura gadon ta ɗagota Lulu zuwa jikinta….

   Smart da gaba ɗaya dauriyarsa ta gama ƙarewa cikin sarƙewar murya ya ce, “Aunty mun rasata ko?”.

     “A’a Aliyu da ranta. Dan zuciyarta na harbawa suma tai kawai. Amma miya firgitata haka? Dan irin wannan sumar mai nauyi mummunar firgici ko tsorata mai tsanani akan abinda mutum baya so ke kawota”.

    Kasa bata amsa yay dan tana cikin mutanen da a rayuwa yake matuƙar ganin girma da jin kunya. Itama fahimtar hakan ya sata cewa, “Shike nan ɗan bani waje mugani”. Babu musu ya fita, inda ya samu Ahmad a falo na faman kai kawo. Da sauri ya taresa da tambayar “Ya ake ciki?”. Zaune Smart ya kai cikin kujera dan ji yake jiri na ɗibarsa kamar zai zube a ƙasa shima. Ya dafe kansa da duka hannayensa kamar bazai cema Ahmad ɗin komai ba. Sai zuwa can ya furzar da zazzafan numfashi ya ɗan kallesa ya girgiza kansa, dai-dai nan Aunty Khadijah ta leƙo ta sake kiransa. Ta shi yay cikin ƙarfin hali ya nufi ɗakin. Batare da aunty Khadijah ta kallesa ba tace, “Kaimin ita Bathroom ka sakata a ruwan dana haɗa, ka riketa da ƙyau dan zata iya zabura”.

   Duk yanda tace masan hakan yayi, sai ko gashi Lulu tai wata gigitacciyar zabura lokacin da yake sakata a ruwan. Da ƙyar ya iya rirriƙeta ajiyar zuciya mai nauyi na suɓuce masa yayinda wanin sashe na zuciyarsa ke matuƙar jin tausayinta da jin haushin kansa mai tsananin gaske. Sai da ta shafe kusan minti biyu tana fisge-fisgen kafin ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya tana mai ambaton sunansa da kausasashiyar muryar ta data gama ɗashewa cikin roƙo da magiyar ya barta, karya aikata. Kalamaine data dinga roƙonsa da su a lokacin da ya gaza amsa mata dan yakai fagen da bazai iya fahimtarta ba a lokacin. Goshinsa ya haɗe da nata yana ambaton, “Kiyi haƙuri Mawaddat kiyi haƙu……”

    Bai kai ƙarshen kalma ta ƙarshen biyar ɗin ba ta ƙwalla wani masifaffen ƙara da zabura……..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣8️⃣

………Aunty Khadijah bata ma san sanda ta afko bayin ba. Da ƙyar suka iya riƙe Lulu su biyun, alamar ya fita aunty Khadijah tai masa, badan yaso ba ya fitan ita kuma ta shiga cikin ruwan ta riƙe Lulun da jikinta ke karkarwa sosai. Ta gama fahimtar minene matsalar Lulun, ko muryar Smart ɗin bata son ji sam dan firgitata take sake yi, dan haka ta fara mata magana cikin lallashi da kulawa, sannu a hanakali yanayin nata ya shiga canjawa, ta koma laƙwas sai kuma ta saki kuka da riƙe aunty Khadijah. Cigaba da lallashinta Aunty Khadijah tai da canja mata ruwa har sai da ta tabbatar ruwan zafin yay mata ratsawar da zai iya bata nutsuwar da take buƙata sannan ta fito ta ɗaukar mata kaya. Smart na zaune ya dafe kansa bayan ya gama ƙarfin halin yaye bedsheet ɗin saman gadon ya canja da wani. Shiya ɗakko kayan ya bama aunty Khadijah ta koma bayin, babu jimawa sosai sai gata ta fito riƙe da Lulu da ke takawa da ƙyar tana hawaye. Ya nufosu da niyyar taimaka musu aunty Khadijah ta girgiza masa kai, dole yaja ya tsaya badan yaso hakan ba. Sai matsanancin tausayinta da ke ratsa shi ganin yanda take tafiyar a wahalce duk da dama rabin jikinta a jikin aunty Khadijah yake. Saman gadon ta kwantar da ita sannan ta ɗaura mata ruwan data riga ta haɗama alluran barci a ciki masu ƙarfi. Cikin sa’a ruwan baifi mintuna bakwai da fara shiga jikinta ba barci mai nauyi ya ɗauke ta, ajiyar zuciyar da take saukewa a jajjare kawai kake iya ji.

    Aunty Khadijah ta sauke numfashi da ajiyar zuciya tana kallonsa, yanda ta kafesa da idanun ya sashi kasa jurewa yay ƙasa da nasa. Zama tai a bakin gadon da masa nunin ya zauna shima. Zaman yay kamar yanda ta buƙata.

      “Aliyu ka kwantar da hankalinka abinda ya faru bashi bane dalilin shigarta a wannan halin.”

  Da sauri ya ɗago ya kalleta, cikin nuna mamaki ya ce, “Amma aunty kafin yau ban taɓa ganinta a irin wannan yanayin ba”.

    “Bazaka gantaba dama, saboda ba’ai mata abinda zai kaita ga shiga irin yanayin bane. Dan akwai ɓoyayyen al’amari a rayuwarta. Yanayin da ta tsinta kanta a ciki yayi kama da na mutanen da aka taɓa ma fyaɗe….”

   “Fyaɗe!..”

  Ya maimaita kalmar da wani irin yanayi mai kama da almara. Ko ruɗani.

      “Tabbas fyaɗe Aliyu, shiyyasa a wannan gaɓar abinda ya faru a baya ya shiga tariyo mata kansa, dalilin da yasa ta firgita kenan har tana neman rasa tunaninta”.

    Kai ya shiga girgizawa da sauri. Duk da yau ne karansa na farko da fara mu’amulantar mace bazai yarda da hakan ba. Shi mai ilimi ne, sannan mai zurfafa bincike akan abubuwan da yake buƙatar sani tun bai kai haka ba. Ya nema sani matuƙa akan mace da suffofinta. Taya ma zai yarda waninsa ya aikata abinda shi shaida ne akan zama na farko a yau ɗin nan bayan wasu awanni kaɗan. Sake girgiza kan nasa yay da janye idanunsa da ya zuba akan Mawaddat ya maida su ga Aunty Khadijah. “Aunty mudai yi wani tunanin ba wannan ba, Mawaddat she is virgin hundred percent”.

     Cikin mamaki ta ce, “Aliyu kasan mi kake faɗa kuwa?”.

   “Tabbas wannan shine gaskiya. Na baki kowace irin dama kuma ta tabbatarwa ta hanyar aikin ki”.

   Sosai hakan ya nema saka Aunty Khadijah a ruɗani, amma kuma tabbas ta san Aliyu akan gaskiya da furtata, sannan ita kanta a yanayin data ga Mawaddat ya tabbatar mata yau ta fara sanin ɗa namiji a rayuwarta, dama tana son sake tabbatarwa ne. Miƙewa tai tsaye ta fara kaikawo kusan na minti guda, sannan ta juyo tana kallon Smart da ya sake zubama Mawaddat dake barci da sauke ajiyar zuciya har yanzu idanu. “Aliyu indai hakane kuwa akwai ɓoyayyen al’amari ƙunshe da rayuwar Mawaddat. Tunda har ka tabbatar min na yarda da kai, amma tabbas an taɓa harar rayuwarta da wannan siffar kuma lamarin bai kasance ƙarami a gareta ba, dan ta ajiyesa a zuciyarta da har takai yake iya firgitata irin haka. Ba kowa ne ake kai masa harin fyaɗe ya ke tsintar kansa a irin matsanancin firgicin nan ba har sai ya tabbata an aikata masan. Shiyyasa kaji nace maka an aikata matan da farko”.

     Kansa yake jinjinawa cike da nazarin kalamanta. Tare da haɗasu waje guda da wasu ɗabi’un Lulu da mabanbanta kalamanta a wasu lokuta. Idan ya ɗauki kalamanta na safiyar yau da ta tabbatar masa zata iya halakashi kamar yanda ta kashe wancan, hakan na nufin abinda Aunty Khadijah ta faɗa tabbas dole ne ya zama gaskiya, sai dai ba’a cimmata ba. Idan aka ɗauki yanda take kallon maza, da yanda ta tsani duk wani da ya aikata fyaɗe da tsaiwar da take akan case irin hakan cikin zafi da zafafawa. Waɗan nan duk hujjojine abin kallo da dubawa. Maganar Ammah a randa ya kaita gidansu da take ce masa ya kusanta kansa da ita ya fahimci damuwarta, dan akwai ɓoyayyen al’amarin data fahimta game da ita a cikin hirarsu. Anya kuwa ma shaye-shayen yarinyar nan baida alaƙa da wannan al’amarin? “Oh my God!” ya faɗa a zahiri yana furzar da iska mai zafi.

    Aunty Khadijah ta ce, “Ka kwantar da hankalinka Aliyu. Wannan damar gareka take na bincika ainahin gaskiya a yamzu. Dan inhar ta iya faɗar duk abinda ke a ranta tamkar mun yaƙi kaso sittin ne cikin ɗari na halin da take a ciki, in ba hakaba zakuyita fuskantar matsala ne kai da ita matsayin ma’aurata dan kaima zata dinga kallonka ne da wannan siffar a duk sanda ka raɓeta. Dan al’amarin ya matuƙar taɓa brain ɗinta da rayuwarta.”

     “Insha ALLAH Aunty zanyi iya bakin ƙoƙarina akan hakan. Sannan ni kaina ina son sanin kowanne tsinanne ne wannan domin ɗanɗana masa fiye da azabar daya dasama ruhinta na tsawon lokaci. Sai dai ina roƙon alfarmar kar wanda yasan wannan zancen dan ALLAH”.

   “Karka damu Aliyu aikina ne hakan. Akwai amana tsakanin likita da majiyaci, balle ma abinda ya shafeka muma ya shafemu. Kallon ɗaya daga cikin ahalinmu nake maka tamkar Ahmad. Haka itama Mawaddat tana da alaƙa damu mai ƙarfi. Dan haka in sha ALLAH a duk sanda kake buƙatar wani taimako ka nemeni”.

      “Insha ALLAH aunty Nagode sosai, ALLAH ya saka da alkairi”.

   “Amin. Sai kuma kayi haƙuri dan yanzu koda ta farka gaskiya akwai daru, dole sai ka kauda kai dan itama ba daga gareta bane tun farko an dasa mata tsoron hakanne a zuciya. Dan ma kayi matuƙar yin farar dabarar kiran Ahmad ɗin kuje asibiti, da ace kace sai har zuwa safiya brain ɗinta zai iya birkita fiye da hakan. ALLAH dai ya rufa mana asiri yay mana maganin azzaluman mutane”.

   Ya amsa mata da amin zuciyarsa na masa ƙuna. Da ga haka ta ajiye masa magunguna suka fito falon inda Ahmad ke zaune cikin damuwar daɗewar tasu. Dan a ƙalla sun samu cikakkiyar awa guda a ciki. Suna fitowa ya miƙe zumbur idanunsa akan Smart. Aunty Khadijah batace masa komai ba ta nufi hanyar fita tana kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunta. Smart zaiyi magana Ahmad ɗin ya taresa da faɗin, “Please Mawashi ka gafarce ni!”.

    “Akan me? Ahmad kaida ka taimakeni ka kawo min aunty Khadijah akan lokaci, ni ya kamata na nema afuwar taso ku da nai a daren nan”.

    Kai Ahmad ya girgiza masa da cewa “Aliyu laifina ne, na aikata kuskure”.

  Sosai ƙirjin Smart yay masifar bugawa, dan abinda Ahmad ke nufi daban shi abinda zuciyarsa ta kawo masa daban. Sai kuma yay saurin ture hakan a ransa ya zubama Ahmad ɗin idanu. “Mi kake son faɗa Ahmad, ka bani abuɗe kasan bana son kwana-kwana”.

   Hannu Ahmad ya kai saman kansa ya shafa, sai kuma ya furzar da huci mai ƙarfi. “Na zuba abu a cikin FURAR nan ɗaya. Saboda ma an tabbatar min maganin nada ƙarfi yasa na saka ɗaya kawai, sai dai zuciyata taita angizani akan na ƙara ta yadda zaka kasa control ɗin kanka har sai ka tabbatar da abinda muke fata.”

      Shiru kawai Smart yay yana kallon ƙasa hannayensa duka a cikin aljihun dogon wandonsa. Kamar bazaice komai ba sai kuma ya ɗago ya dubi Ahmad ɗin yay ƙaramin murmushi da sai ka ƙura masa ido zaka tabbatar yayi. “Baka jin magana Ahmad sam wlhy, ban san mi kake nufi zakai kenan ba ai da ban yarda munsha furar da ka kawo ɗin ba. Amma ka rubuta ka ajiye zan rama nima”.

   Ba haka Ahmad yay zaton ji ba dan haka ya zuba masa idanu kawai yana kallonsa. Ɗauke kai Smart yay gefe da sake faɗin, “Ban san kallo malam kaje ka kai aunty Khadijah gida ta huta”.

    Yanda Smart ɗin yayi duk sai Ahmad ya sake jin jikinsa yay sanyi. Sai dai dole suka fito dan dare yaja kusan ƙarfe biyu. Godiya Smart ya sakema aunty Khadijah tare da harar Ahmad da ke kallonsa har yanzu dan shi gani yake tamkar Smart ɗin ya shanye komai ne kawai a ransa dan ganin aunty Khadijah. Bayan wucewarsu ya rufe ko’ina da kashe komai. Ɗakin ya koma inda Lulu da aka sakama ƙarin ruwa take. Ya jima tsaye yana kallonta wasu abubuwa masu girma game da ita na sake hauhawar farashi a zuciya da ɓargonsa. Kafin ya lumshe idanunsa tare da ramƙwafawa kanta ya sumbaci goshinta da idanun nan da suka sha kuka yau da bakin tsiwar da ya tabbatar kona dare ɗaya ne dai ya mutu murus yau. “ALLAH yay miki albarka _Noorun Nisaaa_” ya ɗan ja sunan da hura mata iska akan idanunta yana murmushi mai sanyi ƙasan zuciyarsa cike da ɗunbin tausayinta…

     Da ga haka ya miƙe ya nufi bedroom yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Jikinsa ya tsaftace. Koda ya fito maimakon kwanciya sallaya ya shimfiɗa ya fiskanci alƙibla domin miƙa godiyarsa ga UBANGIJIN talikai mai rahama mai jin ƙai. Sai gabannin asuba da ya fuskanci ruwan daya saka mata na biyu da Aunty Khadijah ta bari ya ƙare ya je ya cire shi ma. Zama yay kawai ya saka hannunta cikin nasa ya zuba mata ido, yanda take barcin da sauke numfashi a hankali lokaci zuwa lokaci takan saki ajiyar zuciya. Abubuwa da yawa yake nazarta a kanta. Tun daga randa ya fara ganinta a airport da yaje ɗakkota har zuwa masifar da ya dinga ci a wajenta, aurensu da zaman sati uku da kwanaki huɗu yau cikon na biyar. Ya bata sunan HAWAINIYA da kan canja akowane lokaci da kuma kowane irin yanayi. Kai tsaye baka yanke mata hukunci akan kanta dan sanin ainahinta sai ALLAH. Wato duk bawan da kake kallo yana rayuwa akan kuskure ashe kai tsaye yanke masa hukunci da abinda idonka ya gani a kansa tamkar son zuciya ne. Duk wanda zai baka amsa a kanta zai ce maka she is bad girl ne kai tsaye, domin da wannan siffofin take bayyana kanta wa duniya. Dalilin shine haka aka raineta, haka ta tashi, da hakan kawai tai imani a matsayin gaskiya. “Lokaci yayi da zan san wacece ke Mawaddat? Wace irin turnuƙun ƙura kika tsallake a baya data gina miki rayuwa kamar haka? Wanene yaso lalata miki rayuwa? Miyasa mahaifinki ya nuna miki soyayya amma ya gagara tsayawa akan tarbiyyarki? Miyasa ahalinki sukai sakacin fuskantar rayuwarki na cikin wani ƙulli tun a gaɓar da ya dace ace sun fuskanta ɗin? Ina son sanin waɗan nan amsoshin da ga bakinki MATATA. na miki alƙawarin sake gina nagartacciyar rayuwar da zata fahimtar da ke tsakanin fari da baƙi koda sun gauraye a mazubi ɗaya da izinin ALLAH. In sha ALLAHU zan share miki dukkanin hawayenki na zuci dana bayyane da tafukan hannayena na maye gurbinsu da tarin farin ciki Mawaddatan’warahmah”. Motsawar da tai ya bama hannunsu damar sake matsewa cikin na juna tamkar mai jaddada masa ta amshi dukkan kalamansa itama. Hakan ya sakashi lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya………..✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 8️⃣9️⃣

…….A ɓangaren Alh. Sulaiman Garko yana barin wajen Dada Alh Baita ya kira a waya. Wanda ya shaida masa yana gida yau kam bai fita ko’ina ba. Ya tabbatar masa yana buƙatar ganinsu su dukansu a daren nan dan magana ce mai muhimmanci da shi. Babu musu Alh. Baita ya amsa masa tare da bashi address ɗin inda zasu haɗu. Sannan yay kiran su Hon. Nakowa suma. Cikin abinda baifi awa ɗaya ba suka haɗu a gidan hutawar Hon. Misau dake anguwar Farawa. Tsaf ya zayyane musu komai da suka tattauna da Dada, su kansu sun girgiza da jin wannan ƙulli. Hon. Nakowa ya ce, “Wato su waɗan nan na kula makirci a cikin jininsu yake. Yanzu shima shegen Yousuf ɗin nan ashe tsagerane a haka kamar na ALLAH yana wani sim-sim da kai. To anya kuwa Isma’il bai sanar masa sirrin dake a tsakaninmu ba kuwa?”.

        “Abinda nai tunani kenan yasa ni nemanku da gaggawa. Dan in har zai iya irin wannan ƙulle-ƙullen kamar haka dan kada yarinyar nan ta auri ɗaya daga cikin kai da Tajuddeen to inaji a raina wannan taƙamar da hura hanci da Isma’il keyi nada alaƙa da ya sanarma yaron nan komai kuwa. Dan haka nake ganin plan B dole ne mu canja labarin da ga Isma’il zuwa Yousuf, hakan zai bamu damar jifan tsuntsu ɗaya da dutse biyu, sannan zamufi gigita rayuwar Isma’il ɗin da haukatashi”.

         “Su kuma yarinyar da yaron fa?”.

    Cewar Hon. Nakowa cikin zumuɗi. Duk da Alh. Sulaiman ya fahimci inda ya dosa, amma sai bai nuna masa a fuska ba, sai ma murmushi da ya saki kai tsaye ya ce, “Wannan aikin Dada zata ƙarasa mana shi. Bayan ta ɗauke ta daga wajensa sai muje plan c akansu ita da yaron, dan dama akwai tawa da shi a ƙasa”.

    Nan ma sun gamsu matuƙa. Daga haka suka cigaba d tattauna abinda ya shafesu, musamman game da sabuwar alaƙar da suke shirin sake ƙullawa akan business. Har gabannin asubahi sannan suka watse…..

       __________★

   Yanda Smart yaga rana haka yaga wannan dare ko sau ɗaya bai rintsa ba har akai kiran sallar asubahi. Da kyar ya iya dauriyar fita massalaci. Ana idar da salla ya dawo gidan. Inda Lulu take ya sake komawa. Har lokacin tana a yanda ya barta bata farka ba. Yana tsaka da tunanin tadata ko ya barta har sai ta tashi da kanta kira ya shigo masa a waya. Yayi mamakin ganin Coach, amma sai ya ɗaga. Jin muryar aunty Khadijah saɓanin wanda yay tunani ya sashi sauke ajiyar zuciya tare da gaisheta cikin girmamawa.

        Tambayar data jeho masa akan Lulu ya sashi kallonta, sai da ya ɗan furzar da iska sannan ya bata amsa da “Har yanzu bata farka ba dai”.

    “Alhamdullah to karka tada ita, inasha ALLAH ina nan zuwa yanzu nan. Dan a yanayin da take a ciki bamu da tabbacin bazata sake tashi a firgicen ba. Hakanne kuma ba’aso da ga gareta”.

            Ya gamsu, dan haka yayma Aunty Khadijah godiya ya na yanke wayar. Kwanciya ya ɗanyi a kan sofar ɗakin ya faɗa duniyar tunani, hakan ya Bama barci damar dinga figarsa kaɗan-kaɗan. Tsakanin wayarsa da aunty Khadijah baifi mintuna arba’in ba sai gata tazo. Sosai yaji daɗi da ƙara jin kimar waɗan nan bayin ALLAH. Bayan sun ƙara gaisawa ya fita ya basu waje. Cikin hikima ta tada Lulu wadda ta farka a firgicen kamar yanda Aunty Khadijah tai hasashe, sai dai Alhmdllh cikin ƙwarewar aiki ta nutsar da ita, tare da taimaka mata zuwa bathroom ta sake haɗa mata ruwa mai ɗumi. Shawarar sake gasa jikinta ta bata ta fito. Lulu da komai ke dawo mata dalla-dalla batai musu ba ta shiga ruwan zafin, sai da taji ya ratsata tako ina ta sake samun nutsuwa sannan ta tsaftace kanta ta hanyar wankan tsarki da shi da kansa ya koyar da ita a cikin karatunsu duk da dai dama tanayi makamancinsa bayan period, amma ko randa ya koya matan yasha harara dan yay mata bayani dalla-dalla ne. Ji take jikinta ya mata nauyi sosai, ga tauna da ƙasusuwata keyi. Bata son tuna abinda ya faru saboda ƙunar da zuciyarta ke mata. Da taimakon aunty Khadijah tai salla, bayan ta idar ta jima zaune shiru tana nazarin tushen faruwar komai na daren jiyan.  Kamar wadda aka tsikara ta miƙe da sauri dan ta manta yanayin nata. Komawa tai da sauri ta zauna tana dafe kanta ta cije lips. Ƙaramar ƙarar da tai ya saka hankalin aunty Khadijah dawowa kanta. Ta nufota da sauri tana faɗin,

        “Mawaddat yi a hankali banda garaje kinji”. Bata iya cema aunty Khadijah komai ba sai hawayen da suka silalo mata masu zafi. Cikin muryarta da ke a disashe har yanzu ta ce, “Aunty dan ALLAH ina son ki kaini gida”.

      “Gida kuma Mawaddat?”.

  “Eh aunty, dan na tsani gidan nan da komai na cikinsa. Wlhy idan na cigaba da zama komai zai iya faruwa”.

    “Ki kwantar da hankalinki Mawaddat. A cikin wannan halin da kike ai wannan gidanne yafi cancanta da ki zauna fiye da ko ina. Karki ruɗar da kanki, domin yau ɗinki tanada banbanci da jiyanki. Aliyu mijinki ne, abinda ya faru tsakaninku kuma yanada banbanci da wanda zuciyarki ke kallo a baya. Bawan ALLAHn nan tun jiya hankalinsa a tashe yake da ganin halin da kika shiga, bana jin ko rintsawa yayi a daren jiya, dan ALLAH ki sakama ranki haƙuri ku fuskanci juna wataran zakiyi alfahari da hakan”.

         Kuka Lulu ta sake fashewa da shi tana mai girgiza kanta, “Aunty dan baki san miya faru bane….”

     “Ba sai na sani ba Mawaddat, ki adana wannan sirrinkine. Ni dai fatana ki kwantar da hankalinki ki saurari mijinki. Aliyu mutumin kirkine fiye da yanda kike zato ko tsammani. Ke da kanki zaki bama wani labarin hakan wata rana…”

            “Aunty shi azzalumi ne, macuci ba mutumin kirki ba. Kuma wlhy saina ɗan ɗana masa fiye da abinda ya ɗanɗana min, ni zai yaudara ya sakama disere tablet acikin abu na sha ya min fyaɗe. Natsanesa aunty, bana son sake ganin fuskarsa a rayuwata. Kuma wlhy sai na shayar da shi mamaki, dama sai da Dada ta faɗamin amma na kasa fahimtarta. Yayi hakane saboda yasan gobe zamu rabu. Bazan yafe masa ba, kuma a yau ɗin nan komai ma ya ƙare, ya kuma saurari abinda zai biyo baya”.

       A bazata suka tsinkayi deep voice ɗinsa cikin kunnuwansu dan basu san da shigowarsa ɗakin ba. “Ni ban saka miki komai kisha domin samun biyan buƙatata ba. Sannan aure nayi kamar kowane aure mai daraja da fatan mutuwa ta raba. Amma kiyi haƙuri ki bani dama na miki bayani maybe ki fahimceni kuma ki yarda” ya ƙare maganar yana ajiye tray ɗin hannunsa mai ɗauke da kofin shayi da plate da aka saka soyayyan ƙwai.

        A zafafe Lulu dake masa wani irin kallo na tsantsar tsana tace, “Har abada babu yarda a tsakaninmu. Baka da abinda zaka fahimtar da ni Munafuki, azzalumi, maƙaryaci, mayaudar…”

       “Mawaddat!!”.

    Aunty Khadijah ta kira sunanta cikin daka tsawa. Yayinda Smart ya lumshe idanunsa har cikin rai kalmomin guda huɗu da suka fito da ga bakinta na ratsa shi. Ƙoƙarin matsawa yay gaban gadon da kofin shayi a hannunsa yayinda aunty Khadijah ke cigaba da mata faɗa. Bai gama tabbatar da takai maƙurar tsorata da shi ba sai da yay ƙoƙarin riƙota tai wata irin zabura, sai dai azaba da rashin isashen ƙarfi ya sata kasa yin kowane irin yunƙuri face sake fashewa da kuka ta furta, “NA TSANEKA ALIYU!!”.

        “INA ƘAUNARKI MAWADDATAN’WARAHMAH”. ya amsa mata da tashi disashshiyar muryarsa yana tsayawa cak, kofin shayin ya ajiye a bed side drawer duk tausayinta sai ya sake mamaye masa zuciya. So yake tai haƙuri ta kwantar da hankalinta ya jera mata kalaman yabo da jinjinar ban girma, sai dai yasan bazasuyi tasiri ba a yanzu gareta, dan haka ya tattarasu ya adana a wani killataccen sashin adana manyan sirrikansa a zuciya.

          Ganin Lulu na neman sake rikice musu aunty Khadijah tace yaje falo ya jirata. Kusan mintuna biyar da fitar tasa sai gata ta fito. Kallonsa tai cike da tausayawa. “Kayi haƙuri Aliyu ba laifinta ban itama. Wlhy gaba ɗaya a ruɗe take. Dan ma a hakan fa jiya an taimaka mata da wuri shiyyasa al’amarin yazo da sauƙi. Ni yanzu ina ganin mafita ɗaya ce, ka samo wadda zasu zauna tare, sannan dole kayi haƙuri na samu ko Maman Ra’is ce (Aunty Saliha) tazo ta ƙara lallashinta. Dan yanzu ni zanje asibiti ne inada theatre. Insha ALLAH komai zai dai-daita da zarar ta daina jin raɗaɗin a ranta. Sannan ka ɗanyi nesa da itan na ɗan lokaci koda yinin yau ne haka zuwa gobe”.

       “In sha ALLAHU aunty Khadijah. Nagode sosai da ƙoƙarin ki kuma”.

     Sosai aunty Khadijah taji daɗin yanda ya fahimta ɗin. Yayinda tausayin Lulu ke cigaba da ratsata itama harma da shi kansa Smart ɗin. Dan yarinyar tana cikin wani yanayi ne mai ban tausayi. Bayan wucewarta ɗaki ya nufa ya canja kayansa, koda ya fito sai yay tunanin bari ya ɗan leƙata kafin ya wuce, dan gidansu yake son zuwa ya ɗakko mata Maryam ko Asma’u. Kamar zai fice sai kuma dai ya nufi ɗakin nata, ya samu tana toilet, sai books guda buyu da ya gani a saman gadon da pen. Juyawa yay ya fita saboda so yake yaje ya dawo da sauri. Maganar aunty Khadijah na cewar zatai magana da Aunty Saliha tazo yasa shi bai rufe gidan ba, dan yasan sun fisu kusa da nan zata iya yiwuwa ta iso kafin shi ya dawo.. Da’ace bawa yasan gaibu ko abinda zai iya faruwa a bayansa da Smart bazai yi wannan fitar ba. Da bai bar ƙofar gidansa a buɗe ba. Da ya bari har aunty Saliha ta iso kafin ya tafi…….✍️

*_Tofa masu karatu. Mizai faru? Mike shirin faruwa? Amsoshin na a FURAR DANƘO book 2 in sha ALLAHU 👌_*

_Kumin afuwa wannan karon rubutun duk yazo a yanayi na shiririta sai dai godiyar ALLAH. Yau da gobe kenan dan na fiku son naga na kammala gaba ɗaya😭. Amma in sha ALLAH muna gab da hutawa baki ɗaya. Zamu koma part 2 ne dan in numbers na nisa rubutun gundurata yakeyi wlhy🤦.  Amma insha ALLAHU zamu ƙarƙare akan lokaci._*

 _Akwai ƙura fa ta gaske a book 2, dan duk wani abinda muke san sani na ƙunshe ne a cikinsa. Kudai kuyi addu’a ALLAH yasa mu koma pages goma goma mu kammala a kwana goma. Kun san fa ina matuƙar son goma😂😂._

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

Furar Danko Book 2

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 1️⃣

*_UK (LONDON)_*

……..Kwance yake rai-rai a madaidaicin gadon nasa da mutanen Nigeria ke kira da 6-by-6. Sai dai wannan yaji katifa mai shegen laushi da bedsheet fari tas shima mai laushin gaske da ko’a ido ka kalla zaka shaida hakan. Yanda yake ɗan furzar da numfashi sama-sama da huttai ga zufa da tai ma jikinsa jagab zai tabbatar maka da ga training ya fito. Dan wandone na jc ƙarami da ya tsaya masa a fin rabin cinya da rigarsa. Sai takalma da aka san ƴan ƙwallo da su a ƙafarsa. Jikinsa ne a saman gadon ƙafafun zube a ƙasa. Iska mai nauyi ya sake furzarwa tare da buɗe idanunsa da launinsu ke a surke. Sam babu fara’a a tare da shi, dan fuskar nan ɗam take fiye da yanda kowa ya sanshi da rashin walwala acan baya….

          Cikin kuzari da ke nuna cikakkiyar lafiyar gangar jiki ya tashi zaune da ƙyau, ƙaramin tsaki ya ja tare da yamutse fuska ya fara saɓule takalman ƙafar tasa. Anan ya zubesu tare da miƙewa gaba ɗayansa ya kama rigar jikinsa ya cire cikin kamar yanayin jin haushi ya jefar da rigar ƙasa. Dogon glass ɗin da ya kasance kamar bango guda a haɗaɗɗen bedroom ɗin nasa ya nufa. Ya kai hannu ya danna wani ɗan maɓalli green. A hankali glass ɗin ya shiga raba kansa biyu har ya bada ƙofa. Shiga yay nan ma kamar a ɗan fusace, lafiyayyen toilet ne ya bayyana da ni kaina na zama baƙauya a kallo, kai tsaye ƙarƙashin shower ya nufa ya sakarma kansa ruwa yana mai jan wata nannauyar ajiyar zuciya…

       *_Aliyu Mika’il Idris Mawashi_* kenan da ke amsa sunan _Smart Mawashi_ a duniyar ƙwallon ƙafa. Duk da dai kwata-kwata watanninsa uku kenan da dawowa ƙasar ta UK a London yay signing a club ɗin Queen City. Du da kasancewar ƙaramin club ne muna fatan ya zame masa wani tsanin kaiwa inda ba’ai zato ba. A yanzu Smart da muka sani na baya mai shiru-shiru da rashin sakewa da jama’a ya sake zarce hakan. Dan yanzu ba shiru-shiru ba, har miskilanci ma ya koyo. Hakan kuma ta faru ne a sakamakon faruwar shuɗaɗɗun abubuwan da suka faru a cikin watanni ukun nan da suka wuce. A gaɓar da tafi kowace gaɓa muhimmanci a tarihin rayuwarsa. A lokacin da ya gama shiryawa da tsarawa kansa gina rayuwa mai ban sha’awa da birgewa tare da matarsa. A lokacin da yay shirin ɗaukar dukkan yarda da amanar kansa data rayuwarsa domin damƙa mata. Sai labarin ya canja da ga yanda ya rubuta shi a zuciya zuwa rubutun ƙaddara.. Matarsa ta kufce masa a yayinda da burinsa na zama ɗaya da ga cikin ƴan ƙwallo a wata ƙasa ya cika. A hankali komai ya dinga dawo masa a zuciya dalla-dalla tamkar a yanzu ne yake faruwa. _(Bayan fitarsa gida a waccan ranar ya nufi gidansu cike da damuwar halin da ya jefa Lulu a ciki. Ya samu Asma’u taje aikan da Ammah tai mata gidan Aunty Bilkisu. Sai Maryam kawai da Ammah. Ko zaman kirki baiyi ba a daddafe suka gaisa da mahaifiyar tasa ya sanar mata yazo ɗaukar ɗaya daga cikin su Maryam ne dan Mawaddat babu lafiya. Hankalin Ammah ya tashi, ko neman Abba bata tsaya yi ba tace ya ɗauki Maryam suje idan Abban ya dawo zata sanar masa, dan ita a nata zaton ko ciki Lulun ta samu. Cikin sauri Maryam ta kimtsa tare da ɗibar kunun gyaɗar da sukayi domin tafiya da shi can su karya dan itama ko karyawar basu yi ba. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso kasancewar safiya ce babu yawan go slow a hanya. Sai dai me tun a yanayin da sukaga ƙofar falon a buɗe da littafin da ya gani ɗazu a saman gadon Lulu yashe a ƙofar shiga falon alamar an yarda bisa kuskure gabansa ya faɗi. Amma sai ya dake cikin ƙarfin hali suka shiga, a falo Maryam ta zauna shi kuma ya nufi bedroom ɗinsa yana faɗa mata taje ɗakin Lulun yana zuwa. Maryam ta amsa masa da to, yayinda shi kuma ya nufi ɗakin nasa. Bai wani jima ba sai gashi ya fito. Ɗan turus ya tsaya ganin Maryam kamar a ruɗe tana kai kawo. “K lafiya? Ba canai ki shigaba ina zuwa”. Da sauri Maryam ta juyo gareshi tana bashi amsa da “Yaya ai Auntyn bata nan ciki fa. Har toilet na leƙa babu kowa a ciki, hakama kitchen, sai dai duk an harmutsa wadrobe ɗinta an ɗiba kaya harma da akwati guda da aka bari kamar sauri ya hana a ɗauka”. Wani irin duka ƙirjinsa ya dinga yi, sai kuma ya nufi ɗakin da sauri shima. Kamar yanda Maryam ɗin ta sanar masa haka ya gani, sai dai shi nashi idon ya ƙara masa ganin duk wani abu mai amfani a ɗakin ma babu shi. Ƙafafunsa ne suka fara rawa, sai dai cikin dakewa ya cigaba da ƙarfafa kansa. Takardar da idonsa ya sauka kanta a bisa gado ya ƙarasa ya ɗauka. *_Na tsaneka Aliyu, bana son sake ganinka a rayuwata, amma kaje na barka da ALLAH azzalumi. Ashe wa’azin naka duk na yaudara ne kaima baka aiki da shi. Ka manta da ni har abada, dan ko’a hanya nai maka tazara irin ta sama da ƙasa, gabas da yamma. Idan ka wahal da kanka a nemana kai ka so, dan babu wanda ya isa sakani sake zama da kai koda Uncle Yousuf ne._* jiyay jiri na nan ɗibarsa yay saurin kaiwa zaune yana ambaton sunan ALLAH. Ya jima a wajen zaune kansa na yamutsa masa har Maryam ta gaji da jira ta shigo ɗakin. Hankalinta ya tashi da ganin yanda Yayan nasu ya birkice cikin ƙanƙanin lokaci. Kansa tai tana ƙwala masa kira amma sai ya ɗaga mata hannu da ƴar tsawa-tsawa yace ta fita ta bashi waje. Ta tsorata dan haka ta fita da sauri. Kamar an saita batafi minti ɗaya da fita falo cikin ɗaurewar kai ba sai ga kiran Ahmad ya shigo mata. Da sauri ta ɗaya ta kai kunneta. Ko gaisawar kirki bata tsaya sunyi ba ta shiga faɗa masa abinda ke faruwa. Gaban Ahmad ya shiga faɗuwa shima da ga can, cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a gidan. Tambayar duniya Smart yaƙi cemasa komai har sai da ya nuna fusata sanan a taƙaice ya ce masa, “Tabar gidan”. Duk da abin ya daki zuciyar Ahmad ɗin. Sai ya shiga kwantar masa da hankali akan yana zuwa ya tabbatar bazata wuce gida ta tafi ba. Wayar Uncle Yousuf yay kira, da ƙyar ya samu ta shiga. Bayan ya gaishesa bai wani tsaya kwana-kwana ba ya sanar masa halin da ake ciki. Hakan ya ɗan ɗimauta Uncle Yousuf ɗin shima amma sai ya yanke kiran yace yana zuwa. Gidansa ya fara kira Aunty Saliha dake tsaye itama cikin tashin hankali ta ɗaga wayar da sauri. Dan dama nemansa take tun ɗazun ta gagara samunsa. Kafin ma yay mata tasa tambayar ita ta jeho masa abinda ke bakinta. “Abban Ra’is wlhy akwai matsala babba. Yanzu nan Khadijah tai kirana akan na shirya naje gidan Mawaddat babu lafiya na lallasheta da kwantar mata da hankali, banyi ƙasa a gwiwa ba nai shiri dan na shiga tashin hankalin bayanin Khadijahn. Sai dai muna kan hanya sai ga text massege ɗin ta ya shigo wai karmu nemeta, dan tayi nesa damu, na faɗa maka a kira Aliyu ya bata sakinta ta arziƙi inba haka ba zata sashi ya bada ta wuya. Duk da saƙon ya bani mamaki nacema driver yay sauri mu tafi gidan nata. lokacin da muke shiga street ɗin mun haɗu da wata baƙar mota mai tinted glass suka wuce muka wuce. Mun samu gidan buɗe da wani makwafcinsu tsaye a bakin gate ɗin, driver na ƙoƙarin shiga ya dakatar da mu cewar aiko baijin gidan nan da kowa. Dan yanzu yaga wata mata ta rirriƙo matar gidan tana kuka sun shiga mota sannan a loda akwatina a Hilux ma, shima ganin sun bar gidan buɗe ne ya sashi fahimtar babu lafiya, shine fa naketa nemanka ka kira Aliyu koka turo min Number sa amma na kasa smaunka”. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un” Uncle Yousuf ya shiga maimaitawa. Nan ɗin ma baice komai ba ya yanke kiran. Mommy ya kira, itama bai tsaya sun gaisa da ƙyau ba ya jeho mata tambayar ko Lulu taje gidan. Da mamaki tace bata zo ba gaskiya, kuma batajin zatazo ɗin, dan yau tanada Shari’a. Jin haka Uncle Yousuf ya ɗan samu nutsuwa ya yanke kiran. Ahmad yay kira yace su maza court dan tana can zai turo Aunty Saliha yanzu su riƙeta. Da sauri Ahmad ya miƙe, shima Smart sai ya miƙe. Har Maryam basu bariba suka kulle gidan. Sai dai me koda suka isa can ɗin ma babu Lulu, an kuma basu tabbacin bata zo ba. Sosai yanzu kuma hankalinsu ya fara tashi, dan kowa yasan duk rintsi fa Lulu akaran kanta bazatai sakaci da aikinta ba, musamman idan akai la’akari da yanda take matuƙar son al’amarin. Sai dai yanda aka ɗibi kaya yayin barinta gidan na hargitsa ma kowa lissafi. Gidan ƴan uwa da duk aka san zata iya nufa aka fara bubbuga waya, gidan Alhaji Garko ne farko, amma sai cikin tashin hankali Dada tace batazo ba, ba cikin Kano ba har wajen Kano amma dai amsa ɗaya ce Lulu fa bataje ba. Tun kowa na ɗaukar al’amarin wasa harya fara shan hankali, zuwa yamma dole aka shigar da report police station. ALLAH sarki Smart, yini guda baici komai ba sai ruwa, dolene a kallo ɗaya ya baka tausayi, sai da Coach ya tsaresa bayan sallar magrib yasha shayi, yana gamawa kuma sai amai, sai zazzaɓi mai zafi. Dole ranar Ahmad da Abdull na gidansu sai anan suka kwana, dan suma dai tuni sun san mike faruwa Ammah duk kawaicinta a ranar sai da ta taka gidan Smart da ga ita har Abbah. Umma kam wani shegen daɗi takeji, dan a ganin ta in har wani abu ya samu Lulu iyayenta sai sun ɗaure Smart na tsawon rayuwa.

         Al’amarin kamar wasa tuni ƙaramar magana ta zama babba, dan kwana ɗai-ɗai har uku babu labarin Lulu Daddy da Uncle Yousuf tuni sun wancalakar da ayyukan gabansu sun dawo Nigeria. Hakama su twins duk suna Kano. Smart yay wata irin zabgewa, bawan ALLAHn ko murmushi baka gani a fuskarsa, ya duƙufa kawai gayama UBANGIJI, dama Abba ya kai islamiyya da masallatai a taya addu’a, hakama ƴan sanda nata faman kai kawo da bincike. A cikon kwana na biyar ne fa Addu’a bata faɗuwa ƙasa a banza sai ga binciken ƴan sanda ya fara maida akalarsa kan Dada, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai dalilin ganin sanda aka fita da Lulu da maƙwaftansu yayi, dan ƴan sanda basu barshi ya hutaba shima. Yana ganin Dada yace ma ƴan sanda “A’a to ai wannan Maman ce na gani da yarinyar a waccan ranar, tare da wani saurayi haka mai ɗan kammani da su”. A take kowa ya dubi Dada da duk ta daburce, sai kuma ta hau borin kunya. Ran kowa a wajen sai da ya ɓaci idan ka cire Alh. Sulaiman da Tajuddeen da suka san komai. Smart kam wani irin kallo yakema Dada kawai, ji yake yau da ace bata da alaƙa da Lulu wlhy duk da tsufanta sai ya koyama matarnan hankali, dan sai ta tabbatar da ainahin Aliyu Hydar. Daddy ma dai da duk ya zabge a tsaye harda ciwo akan ɓatan Lulun a wani irin rikice yake kallon Dada da Alh. Sulaiman a karo na farko, shikam dama ya zargi Alh. Sulaiman, sai dai Uncle Yousuf ya kwaɓesa akan hakan. ALLAH sarki Uncle Yousuf sarkin dattako, da ya fahimci faɗan na cikin gidane sai ya sallami ƴan sandan kawai, da ƙyar suka tafi dan sun ce dolene Dada ta fuskanci shari’a. To abinka da manyan mutane, a take akai kiran cp ya basu umarnin tafiya. Bayan wucewarsu ne fa gida ya hargitse, dan Dada tace bazata taɓa faɗar ina Lulu take ba sai Smart ya saketa. Karan farko da tun faruwar al’amarin ya saki wani shegen murmushi mai ƙona zuciya a baɗini mai kuma hasala abokin gaba a zahiri……..✍️

     _Alhamdullah barkanmu da sake dawowa a book 2. Yanda muka fara a Sa’a ALLAH yasa mu kammala da nasarori. Ina godiya da jirana da kukayi tare da fatan alkairi 😘😘👏._

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2️⃣

……..Iyayensa ya kalla cikin nutsuwar data ratsashi a yanzu najin tabbacin ina matar tasa yake, cike da girmamawa ya ce, “Abba ku tashi muje gida kawai”. Abba da tausayin ɗan nasa ya ƙara mamaye masa zuciya ya ce, “Aliy ba tafiya gida ne masalaha ba, ka bari dai a sasanta muji miye dalilin aikata hakan”. “Abba bata da wani dalili face na son zuciya. Ina son cigaba da ganin girmanta a matsayinta na uwa kamar yanda kuka tarbiyantar dani girmama kowace irin furfura, tun farko ma ita ya kamata na zarga, amma banyi hakan ba saboda shi zargi bashi da amfani. Sai dai amsa ɗaya zan bada a yanzu har gaban Abada *_BAZAN SAKI MAWADDAT BA_*. Sai dai ayi ɗayan biyu. Ko na MUTU tamun TAKABA, ko ni na mata wanka na sallaceta zuwa kabarinta. Wannan dalilan guda biyu ne kawai zasu iya raba wannan auren da izinin ALLAH!!”. Ba su Dada ba hatta Abbah da Ammah sai da Smart ya girgizasu, dan magana yake a dake, a fusace, a kuma kausashe, hatta da Ahmad dake a matsayin aboki zai iya rantsewa bai taɓa sanin Smart ɗin yanada irin wannan zafin ba. Harara Dada ta watsa masa da faɗin, “Oh burinka kenan dama ta mutu kaci gadon dukiya. Sheɗani to ALLAH ya fika, sakin Mawaddat kuwa idan bakai ta arziƙi ba zakayi ta wuya dan bazamu taɓa haɗa zuria da jinin tsiya jinin talauci ba. dama koda ka aureta ai asiri kai ma iyayen nata matsiyaci”. Murmushi Smart ya saki da taɓe bakinsa cikin halin ko’in kula da zancen Dada. Sai ma ƙoƙarin barin falon da yake yi batare da ya bata amsa ba . Alh. Sulaiman da ya kai maƙura a kan Smart ɗinne ya miƙe a fusace yana nunashi da yatsa. Sai dai kafin ma yace wani abu Smart ya nunashi shima cikin gargaɗi, “Kai! Karka kuskura shiga ramin da zai bizne rayuwarka ta har abada ya barka da gangar jiki kawai da idanun kallo. Sunanka ƙanin uwa ne ba uba ko ƙanin uba ba. Ni da kake gani na nan Sulaiman na fika fiye da abinda ka iya wlhy. Idan kace zaka saka ƙafar wasa da ni sai na gigita rayuwarka ta yanda kai a karan kanka bazaka taɓa morarta ba balle waninka. Magana ake ta mutane ba irinku riɓɓaɓu ba okay…” da ga haka Smart ya sa kai yay ficewarsa kafin ma Alh. Sulaiman da jikinsa ke rawar ɓacin rai dana firgita ya iya furta komai, da gaskiyar Lulu idanun Smart sun cancanci kowane irin suna, musamman a yau da ransa ke a ɓace dan Alh Sulaiman idanun Smart na ɗaya da ga cikin abinda ya razana shi. Fitar Smart ɗin ta saka falon zama tsit, yayinda Alh. Sulaiman ke nuna ƙofa cikin rawar baki data hannu. Daddy ya sauke wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya a karo na farko, sai kawai yaji hawaye sun cika masa ido, dan tunda Smart ya fara magana yake kallonsa harya fice. Uncle Yousuf ne ya tashi yabi bayan Smart, haka ma Ammah da Abbah. A gate suka sami Smart yana waya da Coach, dan a gobe ya kamata ya wuce dama, sai dai da yayi aniyar haƙura dan bazai iya tafiya wata ƙasa batare da anga Lulu ba. Amma a yanzu ya gama yanke shawarar wucewa babu fashi. Uncle Yousuf da ke kallonsa da murmushi yay masa nuni ya shiga mota inda Abba da Ammah suke, bai musa ba ya shiga. Har gida Uncle Yousuf ya kaisu, inda ya samu zama na musamman da Abba da Ammah. Shi ya lallashesu akan su kwantar da hankalinsu dan ALLAH a zubama su Dada ido aga gudun ruwansu, dan ya tabbatar sun aikata haka ne dan Alhaji Garko baya nan. Sosai Abbah ya gamsu da bayanin Uncle Yousuf ɗari bisa ɗari tare da ganin shawarar itace dai-dai. Bayan wucewar Uncle Yousuf Abba da Ammah suka sake zaunar da Smart sukai masa nasihar ya cigaba da shirinsa na tafiya kawai kamar yanda Uncle Yousuf ya faɗa da masa faɗan abinda yay ma Alh. Sulaiman da Dada. Haƙuri ya basu da alƙawarin bazai sake ba. Wannan shine sanadin tattara al’amarin Lulu ya haɗa kayansa a washe gari shi da Uncle Yousuf da Coach suka nufo ƙasar UK a London. Inda yay signing da wani ƙaramin team Queen City. Su Uncle Yousuf sun sake masa nasiha akan ya kwantar da hankalinsa kan al’amarin da kanta zata bijirema su Dada. Shi dai cikin dauriya da dakiya yake amsa musu da to kawai. Amma a cikin ransa shi kaɗai yasan irin ƙunar da yake ji da matuƙar kewar matarsa. Sai dai ƴan mazan sun ɗauki aniyar da jarumtar a wannan karon na sai ya tabbatar ma family ɗin Lulu gaba ɗaya da ita kanta shi ɗan halak ne, sannan talauci ba hauka bane ba. Duk da dai yanayin yaso taɓa shi da son maidashi sanyi-sanyi a watanni ukun daya samu kansa, sannan sam yanzu baka ganin fara’a a fuskar Smart, ya sake zama shiru-shiru a yanzu ma harda miskilanci zamu iya cewa ya ƙaro. Dan bai shiga sabgar kowa, abinda ya kawosa kawai yake yi sai bautar ALLAH. Baya zuwa ko ina da ga gida sai idan yana buƙatar sayen wani abu ya ɗan fita ya sayo ya dawo sai wajen training ɗinsu. Burinsa shine ya manta da komai kamar yanda Uncle Yousuf a koda yaushe ke bashi shawara, dan har yanzu Dada taƙi faɗin inda ta kai Lulu. Duk da yanda aka so yin ɓatacciya tsakanin Daddy da Alh. Sulaiman, dan Daddy yana ragama Dada kodan darajar sunan uwa, amma tunda ya fahimci da haɗin bakin Alh. Sulaiman akai komai sai hankalinsa yay masifar tashi, yasa a nemo masa Smart, Uncle Yousuf da ke nuna shi al’amarin bai damesa ba a zahirin dan yana son Daddy ya maganantu a wannan karon yace masa ai baya ƙasar. Zancen ya girgiza Daddy duk da bai san ina Smart ɗin yaje ba ko abinda ya tafi yi. Da ga baya ma sai Dada ta tattara ta bar ƙasar itama zuwa jiyyar mijinta….)

  Wannan shine abinda ya faru kafin tahowar Smart England.

    Ɗaure da guntun towel ya fito a ƙugu, sai ƙarami yana tsane jikinsa da sumarsa da ya jiƙe da ruwa. Mai ya shafa sama-sama tare da shiryawa ciki ƙaramin wando da riga armless. Gadon nasa ya sake hayewa yay kwanciyarsa dan barci yake ji sosai. Sai dai kafin barcin ya ɗaukesa tunani ya jasa tsahon lokaci….

   Wannan kenan.

____________________★

    *_CANADA_*

  Amai take sosai cikin galabaita da fitar hayyaci, a kallo ɗaya zaka fahimci yanda duk jikinta ya saki sai huttai take da ƙyar. Cikin tausayawa mai aikin da suka taho tare tun daga Nigeria ta ke jera mata sannu. Bayan ta gama aman ruwa ta sakarma kanta daga inda take zaune tana hawaye. Haka take tun can da ma bata da juriyar ciwo, a yanzu kuma da take jin ciwon tamkar ya bambanta da duk wanda ta sabayi ne ke sake galabaitar da ita da raunana mata zuciya, har tana jin anya bazata bijirema kakar tata ba ta bayyana kanta kota koma gida Nigeria. Tsahon watanni uku kenan da barowarta gida Nigeria bisa taimakon kakarta Dada. _(Dan a waccan ranar bayan fitar Smart da ga gidan ta fito toilet da taje yin fitsari, duk da tai masa kurarin barin gidan ba’a ranar tai niyyar hakan ba, sannan batai niyyar sanarma wani nata abinda yay matan ba kamar yanda aunty Khadijah ta bata shawara. Saman gado ta koma ta ɗauki book nata da take adana muhimman sirrikanta ta fara rubutu tana hawaye, bata kai ƙarshe ba ya cika dan haka ta buɗe sabo ta cigaba. Tana tsaka da rubutun ne taji sallamar Dada a bazata, kafin ma ta farga har ta shigo bedroom ɗin nata kai tsaye. Hawayen da Dada ta gani a fuskarta ya sata nuna tashin hankali da fara jera mata tambaya, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya ta sakarma Dadan kuka kawai. Komai Dada bata tsaya tambayarta ba ta hau haɗa mata kaya, bayan ta kammala drivern da ya kawota ya shigo har ciki ya dinga kwasar kayan, yana kammalawa ita kuma ta ce Lulu ta tashi suje, da farko Lulu taso tirjewa akan ta bari Aliyu ya dawo, amma Dada ta balbale ta da masifa. Dole badan taso ba tabi umarninta ta sako. Sai dai tanayin taku biyu uku Dada ta rabga uban salati da antayo ashariya mai kawuna bakwai ta dire. Balbale Lulu tai da masifa irin wadda bata taɓa mata ba, tare da tambayoyi masu tsaurin gaske da suka saka Lulun ɗan jin nauyi harta gagara cewa komai. Sai da taga ta takura mata tace faɗuwa tayi. Hakan ya ƙara harzuƙa Dada ta fisgeta suka fita, sai dai zafin da take ɗan ji ya sata tirjewa dole Dada ta kamata suka fita cikin lallaɓawa. Anan ne makwafcinsu ya gansu, sai dai ita Lulu bama tasan maƙwafcin nasu bane ba. Lulu ta roƙi Dada suje Court akan case ɗin yarinyar nan da take so a ƙarƙare a yau, inda suka samu alƙali suka juye masa kuɗaɗe akan ya cigaba da riƙe mata mutumin a gidan yari zata bar ƙasar dan bata da lafiya. Da ga court hanyar airport suka ɗauka, suna isa basufi minti arba’in da biyar ba jirgin zuwa Abuja ya shirya tashi, dama Dada tasa a tanada mata ticket tun barowarsu gida. Ita kaɗai ta wuce Abuja Dada ta koma gida. Maimakon gidan Uncle ɗinta Khamil wata mata ce tazo ta tareta, tasan matar tare da Dada da daɗewa, suna kiranta Hajiya Shuwa. A ranar gaba ɗaya ta yini kwance ne da zazzaɓi a gidan Hajiya Shuwa, hakama washe gari dai duk gata nan ne dai babu isashen lafiya tare da ita. A kwana na uku Dada tai kiranta a waya ta tsara mata zance cewar ai Aliyu na nan nata zaginta da cewar wai ta tafi yawon banza ne, dan haka sun saka ƴan sanda sun kamashi a yanzu haka ma kotu zasu kaisa ya bata takardar sakinta. Ran Lulu ya ɓaci matuƙa dajin wai Smart na zaginta har da dangantata da karuwa, dan haka tacema Dada tana son ƴan sandan nan su ƙara wajiga rayuwasa kuma ya saketa. Kwana biyu bayannan da ke zama biyar da barowarta Dada ta kirata nan ma ta sanar mata Aliyu wai ya saketa. Duk da abinda take fata ke nan sai taji wani iri, daga ƙarshe ma ranar yini tai babu lafiya zuciyarta a cunkushe. A ranar ta sanarma Dada tana so tabar Nigeria zuwa America, amma sai Dadan ta bata shawarar taje gidanta na Canada tunda babu wanda yasan da shi, dan Uncle Yousuf yay ikirarin ɗaukarta da kansa ya maida gidan Aliyu ko tana suma tana mutuwa ne. Ran Lulu ya sake ɓaci, ta kuma sake jin ƙwarin gwiwar nisantar ahalinta baki ɗaya. Wannan shine dalilin tahowarta Canada tare da mai aikin da aka haɗota da ita mai suna Ummita. Sai dai tunda sukazo zuciyarta taƙi nutsuwa waje ɗaya, abubuwa da yawa tsakaninta da Smart a ɗan zamansu sun zame mata barazana a barci da ido biyu, wannan ya sata sake buɗe babin shaye-shayen ta sosai-sosai. Ko abinci bai dameta ba da ga shaye-shaye sai barci. A kwanakin da bazasu wuce sati biyun nan ba ne abubuwa suka fara canjawa, idan tasha kayan shaye-shayen ta tana kammalawa zatai amansu, tun tana ɗaukar al’amarin wasa har takai bata son warin kowane irin ƙwayar magani, amma cikin ƙarfin hali take daurewa ta sake gwada sha, ta kuma sake aman nasu. Wannan dalilin ya sata ɗaga ƙafa kwana biyu, sai kuma hankalinta ya fara dawowa jikinta har salla da lokaci yayi kamar wadda aka zabura sai ta tashi tayi. Kwana uku da suka wuce kuma sai zazzaɓi ciwon kai da kasala, ga yawan mafarkin Aliyu kamar wani magic a gareta. Sai duk randa tai mafarkin nashi takan tashi da ɓacin rai har taji buƙatar shan kayanta ko zata manta da shi. Sai kuma dai ta daure taƙi sha dan ko tunawa tai da su sai taji amai. Yau kuwa wayar gari tai cikin wata irin damuwa da kewar wani abu data kasa canka a ranta, sai zuciyarta daketa faman ƙuntata, cikin son kauda yanayin ne ta samu ƙwaya tasha amma ta rantse bata zama a cikinta shine take amayar da ita a yanzu)………✍️

  Wannan kenan.

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 3️⃣

…….Dole da taimakon Ummita mai aikin nata ta gyara jikinta ta kamota ta fito da ita bedroom. Cikin wando dogo da sweater ta shirya tare da Safa mai kauri sosai, ta haye gadon cikin rawar ɗari taja bargo har saman kanta. Tare da bama Ummita umarnin ƙara mata gudun room hitter ɗin ɗakin. Dan wani irin rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa waje guda. Ga hawaye sun gagara tsayawa (yau fa an taɓo manyan mata🤣🙏).

    Yanayin da Lulu ke ciki ya tada hankalin Ummita, number da suke waya da Dada jefi-jefi ta lalubo ta kira, kamar baza’a ɗagaba ma sai kuma aka ɗaga, cikin ladabi Ummita tai sallama da gaida Dada, daga can ta amsa a gadarance da tambayar ina Lulu. Cike da damuwa Ummita ta sanar mata gata kwance babu lafiya, dama kusan kwanakin nan haka take ganinta sama-sama, sai dai rashin tabbatarwa yasa bata faɗa mata ba sai yau. Rai a ɓace Dada ta shiga zagin Ummita ɗin, duk ta rikice dan tana bala’in son Lulu, zamu iya cewa soyayyar mahaifiyarta ce ta dawo kanta. Ita dai Ummita haƙuri kawai take bama Dada kawai. Dan ta tabbatar masifar tsohuwar original ce.

   Ba’a rufa mintina goma da katse wayar Dada ba alerm ɗin gidan ya kaɗa, miƙewa Ummita da ke falo tai ta nufi ƙofar, bata buɗe ba kai tsaye ba, ta danna numbers dake jikin ƴar computer ɗin kusa da ƙofar dake manne a bango dan ganin wanene. Baturiyar mace ce tsaye, cikin nuna alamar tana ganin Ummitan da ga wajen itama ta ce, “Hy” cikin ɗaga hannu. Amsa mata Ummita tai itama da “Hy” ɗin. Cikin murmushi matar ta cigaba da magana cikin harshen nasara. “Sunana Doctor Olivia, Nazo nan ne bisa umarnin Mrs Garko”. Yanda ta kira kalmar Garko ɗin taso bama Ummita dariya, amma ta dake da ƙyar sai murmushi da tai mata tare da ɓuɗe ƙofar. Sun sake gaisawa da Dr Olivia, Sannan tai mata rakkiya ɗakin da Lulu ke kwance.

     Ganin yanda jikin Lulu yay zafi sosai yasa Dr Olivia cewa dole suje asibiti, a take tai kiran ambulance cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu. Lulu na rawar sanyi da faɗin su barta ita bazataje ko ina ba su Dr Olivia suka ɗauketa a ambulance ɗin tare da Ummita suka wuce. Suna zuwa babu ɓata lokaci aka shiga da Lulu ciki tare da rufuwa bata gudunmawar gaggawa.

     *_UK_*

  Hankalin Dada da ke jiyyar mijinta ya tashi sosai, amma tanata ƙoƙarin dakewa dan kar Alhaji Garko da ya fara samun sauƙin jikinsa Alhmdllh ya fahimta tare da sauran yaransu da sukan zo dubashi. Idan wannan tawaga ta wuce sai wata kuma tazo, abinka da masu hannu da shuni, kallon fita ƙasar ake kamar barin Kano a shiga Katsina ne. Alhaji Garko da bai san halin da ake ciki ba har yanzu dan babu wanda ya sanar masa saboda halin da yake ciki ya zubama matar tasa ido cikin tausayawa, dan shi ya fassara yanayin nata ne da gajiyawa musamman da yake akwai tsufa. Cike da kulawa ya ce, “Hajarah kina buƙatar hutu, ya kamata kije gida haka nan tunda jikina da sauƙi nima, har ma muna sa ran sallama nan da ƙarshen watannan”.

     “Haba dai Alhaji ya hankalina zai kwanta kana nan ina can, duk da dai jikinka Alhmdllh amma har yanzu kana buƙatar kulawa. Danni ko sallamarka sukayi bana son ka koma gida Nigeria yanzu har sai ka sake hutawa anan magana ta gaskiya.”

   Murmushi yay irin nasu na manya da faɗin, “Hajarah rigima kenan. Yanzu ni da abubuwa ke jirana tari-tari tunda ALLAH yasa da sauran kwanana a gaba mizai sa na kuma sake sabon zama anan ai gara na koma gida ko?”.

     “Humm Alhaji wlhy wannan gaskiya ce ba rigima ba. Gara dai ka sake hutawa dan muna komawa can hayaniya ma ta isheka musamman ta ƴan siyasar nan da ba gajiya suke ba. Dan haka dan ALLAH ka yarda kawai sai ka sake hutawa, nima yanzu inaga maimakon tafiya Nigeria bari na ɗan je Canada na huta na kwana biyu kafin a sallamekan ko.”

   Ɗan jimm yay na alamar tunani, sai kuma cikin nuna fahimta ya ce, “Shike nan idan hakan kike so uwar garke na. Yanzu yaushe zaki wuce Canadan?”.

     “Eh to ko zuwa yamma haka tunda ga su Khamil da iyalansa nan sun iso ko, auta ma yace min zai baro Saudiyya shi da matarsa gobe in sha ALLAH. Kaga dai ai ka sake samun masu kulawa”.

    Murmushi yay mata cikin nuna gamsuwa. Dan Dada kam a wajen bama miji kulawa jaruma ce, tsaye take kan abinta ta kankane ko ina tunda ƙuruciya har girma babu wata mace data taɓa raɓar mata miji da sunan kishi. Wannan tsananin kishin nata yasa hatta matan ƴaƴanta take jin kishinsu akan ƴaƴan nata da suma take matuƙar so da ƙauna tamkar ubansu. Babu ɓata lokaci ta hau shirin wucewa Canada, dan ji take kamar ta rufe ido ta isa taga hanlin da ƴar jikarta take a ciki, saboda a nata bahagon tunani babu abinda zuciyarta ke raya mata sai kodai Smart, ko Uncle Yousuf wani ya sakema Mawaddat asiri ne.

     Dai-dai lokacin da Lulu ke cika awanni goma sha ɗaya a asibitin su Dr Olivia Dada ke isowa ƙasar ta Canada. Tunda ƙuruciya an riga da an san lungu da saƙo na ko’ina, dan a duk ƙasar da suke yawan zama suna da gidansu na kansu musamman manyan ƙasashen nan masu ji da kansu irinsu England, America, France Chaina, Saudiyya, Dubai, dan da gasken gaske wannan family sunada dukiya, bayan wadda mahaifinsu ya gada a wajen nasa mahaifin ya kuma tara nasa na kansa, su kansu yaran kowanne ba ƙyalan bane wajen kuɗin, dan babu wanda ke zaune kaf ɗinsu a neman na kansu suke. Ko marigayiya Mawaddat mahaifiyar Lulu data kasance mace ɗaya tilo a cikinsu sanda tana raye tsaye take akan neman na kanta saboda haka aka gina musu rayuwa, duk da yana da dukiya kuma ya gada ne shima a wajen mahaifinsa bai yarda yaransa su zama cima zaune ba, suna ayyuka a cikin gwamnatin ƙasarsu da na wasu ƙasashe, suna kuma Business ƴaƴa da iyaye har ma da jikoki. Cab ta ɗauka tun daga airport zuwa asibiti kai tsaye, dan a ƙage take da son ganin halin da jikar tata ke ciki. Wadda har yanzu ana kan tafka rigima akan ɓoyetan da tai dan bayan ita sai Alh. Sulaiman kawai suka san ina Lulun take. Hatta da Tajuddeen sunƙi sanar masa. Ita Dada zuciyarta ɗaya ce game da ɓoye Mawaddat dan kawai ta rabata da Smart ne matsayinsa na talaka jikanta Tajuddeen ya samu. Yayinda shi Alh. Sulaiman ba haka kawai bane a tashi zuciyar, dan a yanzu haka bai fara aiwatar da plan ɗinsa bane akan Lulun sakamakon rasa inda Smart yake da yay shi kuma. Dan tun washe garin da Smart ya baro 9ja yasa malami binciko masa shi amma ƙasa ko sama babu labarinsa. Amsa ɗaya suke samu a bincikensu shine ya ɓoye kansa dan kar ya saki Lulu. Duk da dai suna zargi Uncle Yousuf ne ya ɓoyesa amma a ɗan tsukunnan sun ƙara tsananta bincike kasancewar har yanzu basu sami wani point ba akan hakan. Dan shi Uncle Yousuf ɗin ma ya sake baro Nigeria ɗin zuwa harkokinsa da ya bari bayan yayma Daddy tas da tabbatar masa da cewar ya zare hannunsa akan al’amarin Lulu, dan ya fahimci goyon bayan da Daddyn ke batane a baya ya bata lasisin biyema Dada tabar gidan aurenta. Saboda ya tabbar da babu haɗin kan Lulu Dada bazata taɓa iya ɗauketa a gidan aurenta ba harta ɓoyeta gashi ana neman wata uku kamar wasa.

   *_NIGERIA_*

  Sosai Daddy yana cikin wani hali na azabtuwar zuciya game da abubuwa da yawa. Na farko shine ɗan uwansa dake fushi da shi. Ƙaunar da yakema Yousuf a zuciyarsa daban ce a wannan duniyar, dan zai iya rantsuwa ko ƴaƴansa baya musu irin wannan ƙaunar har Lulun da ake kallo ya fifita. Na biyu rashin sanin inda Lulu take har yanzu, tun yana ɗaukar al’amarin wasa Dada zata dawo da ita bayan wasu kwanaki har lamarin ya fara bashi tsoro. Lokacin da yaje UK duba Baba Garko har roƙonta yay akan tayi haƙuri Lulu ta koma gida koda bazata koma gidan mijin ba, dan tabar aikinta da mutane ke matuƙar buƙatarta. Amma sai Dada ta murje idanu tai masa tas dole yaja bakinsa yay shiru dan yana ɗaga mata ƙafa kodan darajar sunan uwa da take amsawa. Sannan fa Daddy dama can Uncle Yousuf ya fishi zafi, shi dai barsa da zuciyar tsiya kamar ɗan kuturu. Abu na uku wani salon rainin wayo da Alh. Sulaiman ya ɗan fara kawo masa da nuna shi yanzu a shirye yake da shi akan komai, sai zuciyarsa ta fara bashi anya kuwa bada haɗin kan Alh. Sulaiman ɗin Dada ta ɗauke Lulu ba kamar yanda yay zargi tun farko. Idan ko haka ne to tabbas a wannan karon ya shirya duk wacce ma za’ai ayi shima. Wannan tunanin ne ya zaburar da shi yau daga gida daya fito yace driver ya wuce da shi office ɗin Alh. Sulaiman Sufi Garko. Sanda suka iso ma shi bai kai ga isowar ba, dan haka sukai zaman jiransa. Baifi mintina bakwai ba a tsakani sai gashi shima. Sai da ya shiga da kusan mintina huɗu drivern Daddy ya shiga ya nema musu iso. Alh. Sulaiman da tun shigowar Daddy cikin Companyn aka sanar masa, yana shigowa kuma ya shaida motarsa yay wata dariyar mugunta da bama sakatariyarsa umarnin shigo da shi.

   Tunda Daddy ya shigo Alh. Sulaiman da yay wata kishingiɗar iskanci a kujera yana jujjuya kansa ya saki murmushi mai ma’anoni da yawa. Yi Daddy yay kamar bai gansa ba, sai ma ya kai zaune duk da ba’a bashi damar hakan ba. “Ina fatan kana lafiya?”. Daddy ya faɗa a takaice. A gatsine Alh. Sulaiman ya amsa masa da “A office ka sameni ai ba’a gadon asibiti ba”.

    “Kuma haka” cewar Daddy a gatsine shima. Batare da ya jira cewar Alh. Sulaiman ɗin ba ya cigaba da faɗin, “Sulaiman ina kuka kai min yarinyata?”.

      “Ka shirya ganinta yanzu kenan?”.

    Idanu Daddy ya tsurama Alh. Sulaiman cikin ɓacin rai, sai dai kafin yace wani abu Alh. Sulaiman ɗin ya ƙyalƙyale da wata dariyar mugunta yana miƙewa tsaye. Takowa yay inda Daddy yake ya ja kujerar dake kallon wadda yake zaune shima ya zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Fuska ya tsuke ya zubama Daddy dake kallonsa cike da tsana idanunsa shima. “Isma’il Ibrahim Jiƙamshi! A da kana ɗaukar duk zantukana matsayin kurari ko? Kana tunanin bazan iya illata rayuwar Mawaddat ba dan kawai tana ɗiyar ƙanwata?. To kayi kuskuren sanin waye ni, dan zamanka da ni na tsawon shekaru bakwai bai maka amfanin komai ba kuwa. Bari kaji wlhy wlhy da ace na san da wannan sirrin a hannun Mawaddat ƙanwata kafin mutuwarta, ni da hannuna zan kasheta bayan na amsa, sai ALLAH ya taimaketa ta mutu a karan kanta kafin na sani ɗin, amma duk da haka bata tsiraba ta barma ƴarta gadon laifinta. Dan haka Isma’il ina maka gargaɗi na ƙarshe, ka bani camara ɗin nan, ka kuma saka a ranka baka taɓa sanina ba har abada, in ba hakaba, a wannan karon saina wargaza rayuwar kaf family ɗinka bata Mawaddat kawai ba. Dan haka zaɓi ya rage naka….”

    Murmushi Daddy yay mai ma’anoni da yawa duk da yasan duk abinda Alh. Sulaiman ɗin ya faɗa zai aikata fiye da hakan. Amma cikin nuna halin ko in kula idonsa akansa kyam ya ce, “Sulaiman kenan. Ka manta ni Isma’il ɗin wanene nima. Sannan banda haukarka a tunaninka baka camara na nufin gogewar abinda ka tafka da in kaf family naka sukaji sai sun maka tsanar da sai ka gwammaci mutuwa da rayuwa. To idan ka manta bari na tuna maka, bayan abinda Mawaddat ta ɗauka nima ai nasan komai, ko toshewar basirar taka takai ka manta cewar komai na sani tunda da bakinka ka kirani ka sanarmin abinda kayi kuma na gani da idona, hasalima tare dani ka ɗauki yarinyar ka kai ƙasan gotter ka jefar. ai ba abinda Mawaddat ta ɗauka bane kawai hujjar. Sannan na biyu Sulaiman kada ka manta a tafin hannuna kuke kai da su Alh. Baita, idan yanzu na sanarma duniya su waye ku a ƙasar nan wlhy wlhy ba dukiya ko matsayi ba sai anyi faca-faca da namanku da taimakon mahaifinka dan kafi kowa sanin irin tsanar da yay ma abinda kuke aikatawar. Ai dama na sanar maka tun a waccan ranar, sai na ɗan ɗana ma zuciyarka rayuwa cikin fargaba da zullumi fiye da yanda ƙanwarka ta ɗanɗana min a tsahon shekara ɗaya dana rayu da ita…..”

    “Nima ai na tabbatar maka sai dai mu rayu a tare cikin zullumin da fargabar ko ka manta”. Alh. Sulaiman ya faɗa a zafafe cikin katse Daddy. Sai kuma ya ƙyalƙyale da dariya da faɗin, “Isma’il kenan a tunaninka kaima ban san a yanda ka rayun bane, ko cakake ban san kaima kana rayuwa bane cikin irin yanda kake tunanin ka sani a tsahon waɗan nan shekarun. Ka gaya min inba tsoro ba miyyasa ka ɗauke ƴarka daga Nigeria da ga randa na tabbatar maka saina hukunta rayuwarta bisa laifin mahaifiyarta? Miyasa kaketa kaffa-kaffa da ita fiye da sauran ƴaƴanka?. Amsar itace Tsoro ne! Kana jin tsorona Isma’il!! Hhhhh tabbas wannan tsorone!!”.

    Da ƙarfi Daddy ya buga decks tare da miƙewa a zafafe………✍️

   Tofa fagen na manya ne yau🚴🚴🚴

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 4️⃣

…….“Kai ɗin banza da zanji tsoronka Sulaiman. Ka sannni kaima ai, ni na wuce maka kanwar lasa, sannan ni ƙadangaren bakin tulune a rayuwarka data abokanka ta yanda kuka rasa yanda zakuyi dani. Ƙarshen target ɗinku shine ku kasheni dai, kuma na tabbatar muku a randa kuka kasheni wlhy ko minti ɗaya bazan cika ba da ɗaukewar numfashi kuma duniya zatai muku zafin da sai kun gwammace mutuwa kamar ni, dan sai mutanen duniyar sun san suwaye ku. Idan ba tsoro kuke ji ba miyya hanaku aikatawar a tsahon shekarun nan. Miyasa kuka kasa bayan kunada kowacce irin dama? Miyasa baku aikata bane sulaiman? Ku kashenin mana? Maza ku kashenin idan kun cika ku tsagerane dan ALLAH!!”.

      Matuƙar razana Alh. Sulaiman yayi da kalaman Daddy, cikin ɓacin rai da zafafuwar zuciya ya nunashi da yatsa lips ɗinsa na rawa. “Haka kace ko?”.

          “Haka nace Sulaiman, idan kuma bakaji ba na sake maimaita maka. Kuma wlhy na baka daga nan zuwa ƙanƙanin lokaci ɗiyata ta dawo gareni inba hakaba sai na sakaka nadama irin wadda sai ka gammaci mutuwa da rayuwa. Dan duk inda kasa ƙafa ka sani ni Isma’il ƙaddararka biye nake da kai. Plan ɗinku na gaba shine sakama Yousuf cocaine a kaya yayinda da zai baro ƙasar Chaina zuwa Nigeria. Bance ku fasaba dan ALLAH, amma ku sani wannan shine mabuɗin farko na kiran mutuwarku. Ni Isma’il kallon kitse kukema rogo kawai, dan ko poisining ɗin Baba da kukayi na barku ne kawai bisa wani dalilina na tarkon dana ɗanama rayuwarku. FURAR DANƘO NAKE, A SHEKARA ANA DAMU BANI FARAU-FARAU. Mawaddat kuwa bazan sake cemaka ina take ba, in dai har ita ɗin jinina ce da kanta zata maido kanta gida bisa bigiren bijire muku. Ku muje zuwa wasan a yanzu na shirya masa….”

          Har Daddy yabar office ɗin Alh. Sulaiman da yay sumar tsaye bai iya dawowa a hayyacinsa ba. Sai da Daddyn yay banging ƙofar ne ya zabura wata zufa na feso masa a illahirin jikinsa. Bai ma san sanda ya since hular kansa ya hau fifita da ita ba jikinsa ma wata irin rawar shiga ruɗani da tashin hankali. Ji yake kamar mafarki yakeyi, shin Isma’il da ya sani ne haka wai shin ko canja shi ankayina? wagga al’amari haka kamar a mahwalki. Shiy yasan Isma’il nada zuciya kam tabbas batun yanzu ba, amma bai taɓa tabbatar da zai iya wani yunƙuri ba bayan kafiyar daya sanshi da ita kawai musamman da yaga tunda suka fara ƴar tsamar nan Daddyn nayi tamkar yana shakkarsa a koda yaushe, lallai ya yarda bakatsinan mutum abin tsorone yau. Da ƙarfi ya hankaɗa kayan saman table ɗin nasa da nuna ƙofa a kausashe ya furta “Isma’il You really are playing with fire!!!….”

       (😂Daddy ni kaina ka shayar dani mamaki, ashe jinin katsinawan dai na aiki a jininka) 

       *_CANADA_*

       Sosai hankalin Dada ya sake tashi ganin yanda Lulun tai wani masifar ɗashewa ta ƙara haske sosai, ga komai nata ya ciko musamman ƙirjinta. Dan ma zazzaɓin daya tasota gaba ya ɗan saka jikin nata girgiza ƙasa kaɗan kwana biyun nan. Tambaya bayan tambaya Dada ta shiga jeroma Dr Olivia akan mike damun jikar tata haka. Kai tsaye Dr Olivia ta sanar mata Lulu na ɗauke da ciki wata uku da kwanaki biyu. Tamkar an fasa irin ƙaton dutsen nan mai girgiza yanki da gidajen wajen gaba ɗaya haka maganar Dr Olivia taima Dada saukar aradu a tsakkiyar ka. Cikin razani da zabura ta maimaita kalmar “Ciki!”  ɗin zuciyarta na bugawa. Dr Olivia ta sake tabbatar mata da hakane. Wata muguwar ashariya Dada ta lailayo ta dire akan Smart. Tare da faɗin, “ALLAH ya tsinema wannan shegen yaro dangin talauci dangin jaraba. Yanzu nan sai da dai ya ɗirka mata ciki. Amma Mawaddat kema ƴar banzar yarinya ce. Randa na ɗakkoki da ga gidan yaron nan har tambaya naita jera miki akan yanayin dana ganki amma kikace min faɗuwa kikayi ashe-ashe miƙa masa jiki kikai ya lalube”. Sai ga hawaye suna cika idon tsohuwar nan dan ɗaurama kai masifa. Kasancewar da Hausa Dada tai maganar duk sai hankalin Dr Olivia ya tashi ta shiga tambayarta ko lafiya. Rai ɓace Dada tace mata ba komai tana zuwa. Cikin rawar jiki ta fito tana neman lambar Alh. Sulaiman ɗanta…

        *_LONDON_*

       Iya ƙoƙari yana yi wajen ganin ya ajiye matsalolinsa gefe ya fuskanci rayuwarsa ta yanzu da cigaban da ya riskeshi. Sai dai hakan ya gagara matuƙa duk da akoda yaushe yay waya da Ammah ko Abbah ko Uncle Yousuf da Coach shawara suke bashi akan ya dai ƙara daurewa. Ammah kan masa nasiha mai ratsa jiki da tabbatar masa in sha ALLAH komai zai zama labari, kuma in har Mawaddat matar da zai rayu da itace duk abinda za’ai sai ta dawo garesa. Wannan ƙwarin gwiwar da mahaifiyarsa ke bashi kan ƙara ƙarfafa masa gwiwa. Sai dai hakan bai hanashi kasancewa cikin mafarkin Lulu ba a duk sanda zai kai kwance da sunan barci. Al’amarin ma har yana neman zame masa jiki akoda yaushe a koda yaushe cikin wanka yake. Ya kasa manta dare mafi daraja da muhimmanci da ya zama wani babban jigo a cikin zamansu na kwanaki ashirin da shidda. Tunashi kansa yay murmushi ko ƙaramar dariya harma da tausayawa. Duk da ashi kansa yasan darene da bazai iya tantance komai yanda ya kamata ba illa dai yasan a shi kansa yasha wahala balle ita. Amma sambatunta ko neman agaji zai ce na wannan dare ya kasa manta komai.

         Yau ma kamar kullum cikin shiri fita wajen training ya fito daga dogon ginin estate ɗin da masaukinsa yake zaune mai hawa kusan ɗari da hamsin, a hawa na tamanin da biyar yake dan haka ya sakko ta lifter har zuwa block A, sanye yake cikin dogon wando na sport da riga mai dogon hannu itama dai irin wandon ce. Sosai ya canja gaba ɗayansa tamkar wanda dama tun farko yake rayuwa anan ɗin. Fatarsa ta sake gogewa ya sake yin haske da kwarjini da cikar kamala a cikin wata uku kacal tamkar wani baƙin bature. Yawan training da sukeyi ya sake buɗe masa halittun gaɓɓai da sake kasancewar sa tsayayyen mutum da za’a iya kallo a jarumi. Kunnensa manne yake da bluetooth yana magana a hankali kamar baya so alamar waya yake amsawa. Ba kowa bane face Ahmad da yay kiransa, duk da yanayin da yake a yanzu na sake zama shiru-shiru da rashin son magana idan Ahmad ɗin yay kiransa yakan ɗan sake suyi hira. Da ɗan gudu-gudu ya fara tafiya jefi-jefi yakan ɗagama wanda suke ɗan wucewa kamar shi a hanya hannu. Yayinda yake cigaba da magana da Ahmad ɗin. Da ga estate ɗin nasu zuwa inda suke training ɗin akwai ƴar tazara sai dai ba wata mai yawa ba sosai, amma duk da haka yakan jure tafiya a ƙafa koma cikin ɗan gudu-gudu kamar yanda yake yi a yanzu domin fara motsa jininsa kafin ya isa. Hakan na ƙara masa ƙarfi da zaburarwa a yayin da ya shiga fili sai karsashinsa ya ƙaru. Sosai sabon baturen Coach ɗin nasu ke yaba ƙwazonsa da jin cewar za’a mori yaron matuƙa idan aka ƙara tsayawa akan al’amarin sa zai zama babbar kaddara, shiyyasa akoda yaushe yake sake jan Smart a jikinsa da ƙara masa dabaru kala-kala dan Smart irin mutanen nan ne masu shiga ran mutane a komai nasu, ga shi baida hayaniya sam, yanayin da yake ciki ma ya sake maida shi miskili a yanzu duk da hakan ba halinsa bane a baya. Amma hakan bai hanashi zama abin so ga wasu ba hatta a cikin teammate ɗin nashi. Alhamdullah yana ƙoƙarin maida hankali tare da ajiye gyambon dake mamaye a zuciyarsa gefe domin fuskantar abinda yaje yi a yanzu, wannan ne karo na farko da zai tunkari babban wasa link na ƙasar da za’a fara, Yana alfahari da hakan duk da team ɗin nashi ƙarami ne. Cikin zafin nama ya iso inda sauran team mate ɗinsa suke. Babu ɓata lokaci suka shiga abinda ya tarasu, sosai yake nuna ƙwazo dake firgita al’amarin wasu a cikin abokan nashi bisa dalilai masu yawa. Na farko shi kaɗaine baƙar fata ɗan Africa a cikinsu, na biyu musulmi, na uku baƙon da har yanzu bai wuce watanni uku da kwanaki ba a cikinsu, amma yana taka leda da sunan training mai firgita zuciya. Ga yanda Coach ɗin nasu yay masifar maida hankalinsa kansa a ɗan ƙanƙanin lokaci na basu mamaki. Yau ɗin ma dai mamakin daya saba basu ya basun, dan har aka tashi babu alamun gajiyawar raunin jiki dana gaɓɓai a tattare da shi. Sai dai su a zahirine kawai suke ganin haka, shi a karan kansa can ƙasan zuciyarsa cike take da rauni. Ga wani irin faɗuwar gaba da ya tashi da ita yau tamkar wanda wani mummunan abu ke neman faruwa da shi. Amma yanayinsa na dakewa da rashin walwala yasa sam su basu fahimci komai ba.

      Cikin huttai ɗai-ɗai irin na wanda yasha kai kawo ya samu waje ya kai zaune yana kwankwaɗar ruwan dake hannunsa. Sharkaf yake da zufa tamkar wanda yay wanka. Yanda yake shan ruwan kai a sama ya bama Adams apple ɗinsa damar motsawa cikin kaikawo haɗiyar ruwan da sauri-sauri. Sai da ya shanye ruwan tas ya sauke bottle ɗin yana furzar da nannauyar numfashi. A hankali ya zame jikin kujerar ya kwantar da bayansa yana mai lumshe idanunsa da kai hannunsa saman ƙirjinsa dai-dai zuciyarsa dake cigaba da bugawa ya dafe yana karanto addu’a da fatan koma minene ke tunkarosa ALLAH ya sauƙaƙa masa shi ya kuma bashi juriyar ɗauka…..

            *_NIGERIA_*

   Alh Sulaiman na tsaka da kai-kawon tashin hankalin abinda ya faru tsakaninsa da Daddy kiran Dada ya shigo masa. Kasancewar wayar a hannunsa take yana son kiran Hon. Nakowa yaja ɗan tsaki. Kamar zai share kiran mahaifiyar tasa sai kuma dai ya ɗaga tare da kaiwa kunnensa batare da ko ya gaisheta ba a daƙile ya ce, “Dada ina ɗan wani uziri yanzu idan na kammala zan kiraki”.

        Da sauri Dada ta ce, “Sulaiman muna cikin tashin hankali ka tsaya muyi magana dan wannan ma uziri ne babba”. Ɗan tsammm ya dakata da ga yunƙurin yanke kiran da yay yace “Uhumm” alamar saurarenta. Cikin rawar muryar ɓacin rai da tsufa Dada ta cigaba da faɗin, “Sulaiman ina Canada yanzu haka. Yarinyar nan dake tare da Mawaddat ce tai kirana wai gata babu lafiya tanata amai. Na ɗauka kawai normal fever ne nai kiran Dr Olivia ta dubata, amma sai ta kirani tana faɗa min zasu wuce da ita asibiti dan jikin yay zafi sosai. Hankali tashe na taho bayan nama Babanku dibara. Daga airport asibin kawai na is…..”

      Cikin ƙosawa Alh. Sulaiman ya tare Dada da faɗin, “Dada bar wannan dogon bayanin kawai faɗi mike damunta?”.

           “Wai tana da ciki har na wata uku”.

       “What! To ubanwa yay mata shi?”.

   “Sulaiman wazai mata banda ɗan iskan yaron nan”.

Wata irin zafafaffiyar iska Alh. Sulaiman ya furzar ransa na ƙara dagulewa. Batare da wani tunani ba murya a kausashe ya ce “Zubar da shi za’ai Dada. Ki haɗani da Dr Olivia ɗin muyi magana”.

        Ɗari bisa ɗari Dada ta amince da maganar ɗan nata, dan dama itama wannan shine a ranta. Alh. Sulaiman yay magana da Dr Olivia sun kuma gama ƙarƙare komai akan zubda cikin jikin Lulu kafin ma ta dawo hayyacinta tasan da shi. A wajen bature wannan ba komai bane ba, amma sai dai Dr Olivia ta tabbatar masa sai sunyi gwaje-gwajen da ya dace kafin cire cikin bawai zasuyi kai tsaye bane kamar yanda yake so shi. Yana yanke wayar Dr Olivia ta shiga yin abinda ya dace game da abinda zasuyi kan zubda cikin na Lulu ta hanyar gwada ƙarfin jininta da wasu abubuwa irin nasu na likitoci da su kaɗai suka san su………✍️

      🚴🚴🚴🚴uhhhmmm bazance komai ba nidai.

_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_

*KINSAN SUNAN LABARAN?,…..GASU KAMAR HAKA*

FURAR DANKO

Billyn Abdul

-ZAFIN KAI

Mamuhgee

-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma

-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣

……..Basuyi mata allurar zubda cikin ba kamar yanda Alh. Sulaiman da Dada suka bada umarni har Lulu ta farka, an gama dai duk wani shirye-shirye har Dada ta saka hannu. A hankali ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi sosai tana bin ɗakin da kallo, sai da hankalinta ya gama dawowa jikinta sannan ta fahimci a asibiti take. Yunƙurawa tai da niyyar tashi sai hakan yay dai-dai da shigowar Dada ɗakin. “Sunahanallahi Mawaddat kin tashi?” cewar Dada tana nufota. Ita ta taimaka mata ta ƙarasa tashi, tare da kaiwa zaune a kusa da ita. Hakan ya bama Lulu damar kwantar da kanta a jikin Dadan tana hawaye. “Yaushe kika zo?”. Ta tambaya cikin raunin murya irin ta mara lafiya. Cike da kulawa Dada ta sake rungumeta a jikinta da faɗin, “Tun ɗazun dear. Ya kike jin jikin naki yanzu haka?”.

      “Dada ko ina namun ciwo, ga yunwa ina ji sosai”.

     “Ba dole kiji yunwa ba kina ɗauke da jinin yunwa. Shegen yaro da bai wuce saiti abu yi guda ya ɗiraka miki ƙunshi ya barki da jidali”.

    Da mamaki Lulu ta ɗago ta dubi Dada saboda rasa gane ina zantukanta suka nufa. Dada ta ƙyaɓe baki cikin hasala tana yin ƙwafa. “Dada wai mi kike faɗi ne?”.

           “Mtsoww ba komai tashi muje na kaiki ki wanke baki kizo kici abincin”. Duk da Lulu na son jin fassaran zantukan na Dada sai batai musu ba ta tashi a jikin nata, da taimakonta ta wanko bakinta da fuskarta suka dawo. Apple da tace tana so ta bata ta sha, takai kusan rabi ta ajiye ta ce ta bata yugut. Shi tasha sosai dan kaɗan ta rage a babbar robar da yake ciki. Sosai Dada ta saki baki tana kallon Lulun kamar wadda ke’a cikin yunwa. Ɗan gumin da ya tsatstsafo mata na ƙoshi ta kai hannu ta share tare da komawa jikin Dada ta lafe. Shigowar Dr Olivia ya sakata miƙewa zaune. Sannu Dr Olivia ke mata cikin fara’a da jin daɗin ganin ta tashi da daɗin rai, bayan ta ɗan tsokanarta ta ciro allurar da zatai mata. Lulu bata wani damu ba, dan ta ɗauka normal allura ce, dan haka babu musu ta yarda akai mata doctor na cigaba da tsokanarta.

          Minti talatin dai-dai dayin allurar nan wani irin ciwon mara na azaba ya tasoma Lulu. A take jikinta ya fara vibration, tai wani irin dunƙulewa waje guda tana kiran “Wayyo ALLAH na Dada marata”. Yanda ta saki siririyar ƙararar sai da zuciyar Dada ta harba, hankali tashe tai amfani da wayar landline dake a ɗakin tai kiran doctor Olivia. Tamkar dama a kusa take babu jimawa sai gata ta faɗo, zuwa sannan jini ya ɓalena Lulu abin babu daɗin gani….

      Iya wahala da azaba Lulu ta Shashi, inda da ƙyar aka samu jinin ya tsaya, akai mata allurar barci tare da gyarata, barcin wahala ne ya ɗauketa sai wata irin tagwayen ajiyar zuciya take saukewa a cikin barcin. Dada da duk ta shiga damuwa ta shiga tambayar doctor yanda ake ciki, Doctor ta tabbatar mata da aiki yayi ƙyau, dan yanzu haka dai ciki ya fita sai kuma ɗan jiyyar jiki da Lulun zatai na kwana biyu. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyin gaske Dada ta sauke, a take tai kiran Alh. Sulaiman, a lokacin yana tare da su Hon. Misau suna tattauna batun Daddy. Kamar yaƙi ɗauka sai kuma dai ya ɗaga yana kaiwa kunne. A ɗan daƙile ya ce, “Dada nafa sanar miki inada uziri, mi kuma ya faru yanzun?”.

         A ɗan ɗokance da ture maganarsa ta farko Dada ta ce, “Ai an kammala aiki yanzu haka ciki yabi gottern turawa kuma”. Ajiyar zuciya Alh. Sulaiman yayi da faɗin, “To maddala, na san zasu sallameku yau ku koma gida, zuwa anjima idan na samu nutsuwa zan kiraki”. Daga haka ya yanke wayar batare da ya jira tace wani abu ba. Hakan ya bama Dada haushi dan bata gama maganarta ba, amma sai batace komai ba bayan jan tsoki. Kamar yanda ya faɗa zuwa dare da Lulu ta sake farkawa aka sallamesu. Duk da Lulu najin jikinta cikin rashin ƙarfi kwata-kwata ga jiri na ɗinarta bata kawo komai a ranta ba. An basu magunguna suka hau cab zuwa gida. Sun samu Ummita ta gama gyara ko’ina sai tashin fresheners masu ƙamshi da gidan keyi, cikin ƙarfin hali Lulu ta ce ma Dada tana son tai wanka first, amma ta taimaka mata. Dada da kanta ta cuccuɗa Lulu tare da taimaka mata suka fito, kaya ma da taimakonta ta saka, tana gama sawa tasha tea ɗin da mai aikinta Ummita ta haɗa mata bisa umarnin Dada. Sosai ta sha shayin har ma abin yaso bama Dada mamaki, ita dai cikin sauke numfashi ta koma ta kwanta dan barci takeji har yanzun.

       *_BAYAN KWANA UKU_*

  Yau kawani uku kenan da zubar da cikin jikin Lulu da batasan da shi ba ba kuma tasan an zubar ba. Ta ɗan ƙarasa jiyyarta ta kwanaki biyu yayinda Dada ke kula da ita a duk motsinta. Yanda ta miƙe da wuri zai baka tabbacin zuwan Dada yay mata daɗi, dan akoda yaushe tana nane da ita. Duk da tana jin kewar ƴan gidansu musamman Daddy, Uncle Yousuf, Da Ammah sai take ƙoƙarin dakewa da sakama ranta haushinsu akan basa sonta. Ga kuma Dada a kaikaice tana sake cusa mata laifinsu hadda sharri. A duk sanda kuma Dada ta ɗakko zancen Smart sai Lulu taja tsaki da yamutsa fuska cikin shagwaɓa tacema Dada bata son ji, ita a daina mata koda zancensa. Hakan nama Dada daɗi da sake zaburar da ita cusa ma Lulu ƙiyayyar Smart a zuciya har ma da su Uncle Yousuf. Tun ma abin baya tasiri a ran Lulu har ya fara a randa take cika kwanaki biyar da samun lafiya a bazata sai ga Alh. Sulaiman da Tajuddeen. Lokacin tana kwance a falo tana kallo. A zahiri ta warke ragal. Sai dai tana jin wani irin kasala da son shan fruits, dan rigima ma yau sai cewa tai a mata kunun gyaɗa. Da Dada tace ina za’a samo wata gyaɗa anan sai ta sanya musu kuka na gaske. Dole Dada tai kiran wani saurayi ɗan ƙawarta da suma suke nan Canada ɗin amma asalinsu ƴan Nigeria ne ya bazama nemawa Lulu gyaɗa. Sai ko gashi ya samo, Ummita ta amsa ta haɗa mata kunun data buƙata sannan aka samu lafiya. Wannan kunu shine a gabanta har zuwa yanzu lokaci-lokaci takan zuba tasha abinta har sai taji yakai mata sannan ta ajiye. Sororo tai da ganin Uncle ɗin nata da Tajuddeen, dan ita dai ganin nasu yazo mata a bazata. Yanayinta babu yabo babu fallasa ta tashi zaune tana musu sannu da zuwa. Sai kuma ta ɗan dubi Tajuddeen a yatsune tare da balla masa hararar kallon ƙurillar da taga yana mata. Sanye take da doguwar riga kalar ja da tabi jikinta ta lafe, sai rigar sanyi data ajiye gefenta kasancewar gidan akwai hitter dake ɗumama ko’ina. Rigar ta fisga ta sanya tare da komawa kwancenta kamar yanda take da. Sai dai ta danna wani ɗan maɓalli dake gefen kujerar ya bada ƙara sai ga Ummita da sauri ta fito da ga wani ɗaki tana faɗin, “Aunty kina buƙatar wani abu n…” ta kasa ƙarasawa saboda ganin baƙi. Batare da Lulu ta kalleta ba ta ce, “Ki sanarma Dada anyi baƙi”. Ummita data zube tana gaida su Tajuddeen ta amsa da to tana miƙewa ta nufi ɗakin da Dada da Lulun ke kwana.

     Ta wutsiyar ido Alh. Sulaiman ke kallon Lulu da nazartar ta, ba yau ya fara fahimtar girman kai da izzar yarinyar ba irin ta uwarta da ma shegen ubanta ce. Dan duk da yake amsa sunan yayan mahaifiyarta bata wani sakewa da shi, hasalima a duk sanda suka haɗu takan dinga acting like tana jin haushinsa. Hakan yasa yake zargin ko mahaigunta ya sanar mata wani abu a kansa ne. Wata ƴar ƙaramar ƙwafa yayi ciki-ciki a ransa yana faɗin (Zan dawo dake cikin hankalinki ai yarinyabke da ubanki dama duk mai daure miki ƙugu). Tajuddeen kam kai tsaye ya kafe Lulu da kallo, itako duk da tana jin idanunsa a kanta tai biris da shi tamkar bama tasan ALLAH yay zamansa a falon ba da ga shi har ubansan. Laifin Tajuddeen ne ya shafi mahaifinsa Alh. Sulaiman a wajen Lulu, dan bama shi ba, duk wasu ƴan gidan su Tajuddeen Lulu ta tsanesu a dalilin Tajuddeen ɗin ba kamar yanda shi Alh. Sulaiman ke tunanin Daddy ya faɗama Lulun sirrinsa bane.

      Cikin nuna mamaki Dada dake fitowa ta ce, “A’a wai dama da gaske ne kuna tafen ashe dai?”.

          Murmushi Alh. Sulaiman yayi da amsa ma mahaifiyar tasa da “Wlhy kuwa Dada ai na tabbatar miki babu abinda zai hanamu zuwa. Idan muka gaisheki sai mu wuce mu duba Baba kuma duk da shi Tajuddeen zai dawo nan Canada ɗinne akwai aikin da zaiyi”. Dada bata samu damar bama ɗan nata amsa ba saboda miƙewar da jikanta yay Tajuddeen yaje ya rungumeta. Lulu da duk ke saurarensu gabanta ya faɗi jin wai Tajuddeen yazo aiki ne nan Canada. To lallai dolene kam tabar ƙasar nan kenan a wannan gaɓar. Dan bataga haɗin kifi da kaska ba tsakaninta da Tajuddeen bazasu taɓa kasancewa a inuwa guda ba. Tsam ta miƙe cike da izzar nan tata sai dai rashin ƙarfin jiki na ciwo duk ya cinyeta a tsaye ta ɗauki flaks ɗin kunun gyaɗarta ta bar falon. Su duka da kallo suka bita kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa. Dada ta katse shirun da faɗin, “Bara yarinyar nan ta shirya muku abinci ko. Sannunku da hanya”.

    Bakin Tajuddeen a washe yana sauke nannauyar ajiyar zuciya da ga dawowa hayyacin bin kallon Lulu da yay da ido ya kalli kakar tasu. Ido ya kashe mata tare da mata nuni da ɗakin da Lulu ta shiga da baki. Dada tai ƙaramar dariya da faɗin, “To Alhaji zumuɗinka kadai bi komai a hankali, dan bamu san wane kalar barbaɗe shegen yaron nan yay mata ba, maybe bata gama dawowa cikin hankalinta ba ta kuma butsare mana a karo na biyu kadai san halin taurin kai irin na Mawaddat da shegen fitina”.

        “Karki damu Grandma, komai zai tafi dai-dai kamar yanda aka tsarashi. Indai ni ne a wannan gaɓar babu garaje. Bamma san tasan komai har sai an ɗaura auren”.

     Ƙaramar dariya Dada tayi, yayinda Alh. Sulaiman ya kura musa ido kawai, sai dai baice dasu komai ba…….✍️

       _🤔To an taɓa aure akan aurene? Yau naga lukutar masifa Dada da Alh. Tsule fa babu man kai zasu iya ɗaurawa…🚴🚴🚴_

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣

……..Lulu bata sake fitowa falon ba tana a ɗaki, sai in lokacin sallah yayi ta tashi tayi, dan tunda ta dawo asibitin nan kuma sai hankalinta ya dawo jikinta sosai. Da lokacin sallah yayi kamar wadda ake zabura sai Smart yazo mata a rai, miƙewa take cikin jan ƙaramin tsaki da son kauda al’amarin sa tai sallarta. Alhamdullah game da shan kayan shaye-shayen ta ma tunda suka dawo asibitin tamkar wadda aka tsawatar mawa bata sake sha’awar shan wani abu ba dan sun gagareta. Hasalima data tuna sai zuciyarta tahau tashi kamar wadda ta tuno wani abinci. Wannan dalilin ne ya zare mata duk wani tunanin ɗaukar wani abu tasha ya bugar da ita. Sosai wannan zuwa na su Tajuddeen da jin zaiyi zaman aiki anan yasata shiga dogon tunani, bata sha’awar tunkarar Nigeria sam, dan harga ALLAH wani sashe na zuciyarta na tsoron haɗuwa da Uncle Yousuf, sannan kuma bazata iya cigaba da zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya da Tajuddeen ba. Dolene tasan mafita na barin ƙasar zuwa wata ƙasa daban ta karasa dogon hutun data ɗauro ɗammarar yi har sai sanda taso ta waiwayi gida Nigeria sannan. Kasancewar anan ba wani an damu da dare ko rana bane dan akoda yaushe ba fasa sabgoginsu suke ba sai in sanyin gari ya hana hakan yasa Lulu tunanin ɗan fita yau tasha iska. Miƙewa tai duk da yanayi rashin ƙarfin jikin da take ji ta sake sabon shiri cikin wando da riga da jibgegiyar rigar sanyi mai hula. Turare taɗan ƙarama jikinta ta ɗauki ƙaramin ledan chocolate ɗinta ta saka a aljihun rigar bayan ta ɗaure igiyar takalmanta ta fito. Tajuddeen kawai ta samu zaune a falo yana daƙilar waya. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shiko da sai da taɗan gittashi ƙamshinta ya dakar masa hanci ya sashi farga da ita da sauri ya ɗago. Ganinta da shirin fita ya sashi miƙewa da sauri yana faɗin, “Ƴammatan ina zuwa haka ba neman abokin rakkiya?”.

       “Ba buƙata”.

    Ta faɗa a daƙile tana ficewarta, kafin ya iso ƙofar ta maida ta rufe da sanya security ta baya tana hararar ƙofar da jan tsaki tai wucewarta. Sororo Tajuddeen ya tsaya bayan ya gama mummurɗa handle ɗin ƙofar ya tabbatar da ta kulle ta baya. Lips ɗinsa ya ciza da yanayin rashin jin daɗi ya koma ya zauna a inda ya taso. Itako Lulu cikin tura hannayenta dake sanye da Safa suma a aljihun rigarta ta fara tafiya bisa lafiyayyen titin street ɗin nasu a hankali dusar ƙanƙara na ɗan sauka mata a jiki ɗis-ɗis kaɗan-kaɗan. Duk da akwai sanyi sosai yanayin ya mata daɗi, dan rabonta da irin wannan fitar haka tun bayan gama jiyyar jikinta da Smart ya murza, tana kuma ɗan fara samun walwalar ta kwana biyu sabon yanayin ciwon nan ya sake kwantar da ita shima. Tayi nisa sosai da gidan ta samu wani shagon shan coffee ta shiga, coffee ɗin tasa aka kawo mata, sai dai tana kaisa bakinta taji zuciyarta ya fara tashi, a take ƴan cikinta suka shiga hautsinawa. Babu shiri ta baro gurin cikin tashin hankali bayan ta biyasu, duk yanda taso riƙe aman ya gagara dole ta koma cikin restroom nasu ta dinga sheƙasa har ɗan kunun gyaɗar da tasha a gida sai da ta zazzagar. Cikin galabaita ta samu ta wanke fuskarta ta fito dajan ƙafa. Can gefe ta samu ta sake zama tana maida numfashi ɗaɗɗaya zuciyarta a cunkushe da tunanin wai mike damunta haka ne?. Ita dai tunda take bata taɓa fuskantar kalar ciwo haka ba da amai. (Ni dai nace Hummm). Ta jima a shagon coffee ɗin kafin ta miƙe cikin ƙarfin hali ta sake nufo hanyar dawowa gida dan wani irin sanyi mai shiga jiki da ƙashi take jin na ratsata duk da yanda ta rufe duk jikinta da kariya harda su Safar hannu da facemask amma bata tsira ba. Da ƙyar ta iya kawo kanta gida, ta cire security ɗin data sakama ƙofar saboda Tajuddeen ta shigo cikin tangaɗi. Babu kowa a falon da alama Tajuddeen ya shige, gudun karma wani yazo ya sake damunta ya sata nufar bedroom ɗinta dan yau tayima Dada yaji akan bazata sake kwana a ɗakinta ba. Dan dama da nata zuwan Dadar ya sata komawa inda ta sauka kasancewar bata da lafiya. Gaba ɗaya hankalin Dada da Alh. Sulaiman da suka haɗe kansu a bedroom ɗin Lulun da tunanin bazata shigo nan ba koda ta dawo yanzu baya kan ƙofar, tattaunawa suke game da zancen cikin da suka saka aka zubar mata batare da tasan ma da cikin ba. Wani irin bugawa ƙirjin Lulu yay da ƙarfin gaske. Ta tsaya cak tamkar wadda aka dasa matsayin gunkin tarihi ba mutum mai numfashi ba tana cigaba da saurarensu. Kanta ne ya fara juyawa sannu-sannu ta fara ganin hajijiya babu zato sai jin faɗuwar abu sukai ƙasa yifff. A tare suka zaburo tare da kallon ƙofar cikin waro idanu…..

        Bayan kamar awanni biyu ta dawo a hayyacinta, zuwa lokacin hatta da Tajuddeen na a ɗakin zaune a gefenta cikin damuwa dan har fuskarsa ta gagara ɓoyewa. Ɗaya bayan ɗaya ta gama binsu da kallo tamkar mai son tantancesu kafin ta maida idanun nata ta lumshe kawai batare data nuna alamar ta tashin ba. Hirar kakar tata da kawun nata ne suka shiga dawo mata dalla-dalla, ita Mawaddat ce keda ciki, ciki na haihuwar ɗan mutum, amma suka saka aka zubar da shi. To minene dalilinsu nayin hakan. Duk da a karan kanta bazatace son cikin take ko akasinsa ba, amma tanaji a ranta kamar ya kamata ace kafin su aikata zubar da shi a bari ta sani da kuma jin ta bakinta ai. Hannunta dake ajiye a saman cikin nata ta motsa a hankali, tare da sake matsar da shi ƙasa sosai ta shafa cikin. Wannan ne ya fargar da su Dada cewar ta farka. Gaba ɗayansu sukai kanta da sannu musamman Tajuddeen da Dada. Dan Alh. Sulaiman dai idanu kawai ya zuba mata batare da yace komai ba. Cikin damuwa Tajuddeen ke jera mata tambayar mike damunta? Ko zata tashi suje asibiti ne? Yanzu ina ke mata ciwo?. Idanun nata ta ɗan sake buɗewa ta kallesa, sai kuma ta maida abinta ta lumshe. Sake jera mata sannu da roƙon ta bari ya kaita asibitin yayi. Amma sai ta girgiza masa kanta kawai. Zai sake magana Alh. Sulaiman ya katseshi da faɗin, “Tajuddeen relax mana”. Shiru yay badan yaso ba, hakan yasa ɗakin komawa shiru. Lulu da gaba ɗaya take jin wani irin yanayi mai kama da jin zafi da ɗaci a zuciya ta sake buɗe idanunta da sukai ja akan Dada. Muryarta irin ta mara lafiya a dake ta ce, “Dada nice na samu ciki aka zubar?”. Ba Dada ba hatta Alh. Sulaiman sai da furucin nata ya razanashi. Kusan a tare suka kalli Tajuddeen da ya furta “Ciki kuma Mawaddat?!”. Maimakon amsa Tajuddeen ɗin Dada take kallo alamar jiran amsa daga gareta. Dada data ɗan daburce cikin inda-inda ta ce, “E… E… Eh hakanne Sweet heart. Mun…m…munji tausayinki ne da ganin halin da kike a ciki na wahalar ciwo. Sannan minene amfanin haihuwa da wancan sankaran shashashan yaron da ko kansa bai iya riƙewa ba sai baƙin talauci, ke akaran kanki ma baki isa haihuwar ba ai shekarunki nawa ma duka. Na biyu inaji a jikina bada yardarki aka samu cikin nan ba, sai dai in asiri yay miki tare da fyaɗe. Dan ke da bakinki kin tabbatar min baki taɓa bashi kan ki ba. Ki faɗa mana gaskiya, fyaɗe yayi miki ko?”.

         Kai Lulu ta kauda tana mai lumshe idanunta batare data bama Dada amsa ba, dan wani irin zafinsu takeji kamar ta shaƙo ɗaya a cikinsu ta maƙure kawai, a mamakinsu sai ganin hawaye sukai na zirara ta gefen idonta yana sauka saman filon da take kai har a cikin kunnenta. Gaba ɗayansu babu wanda bai kasance a yanayin zama turus ba, musamman Tajuddeen da ke jin jikinsa na tsuma. So yake kawai yaji Lulu tace fyaɗe Smart yay mata, shiko ya ɗauki alwashin koda uwarsa yake yawo sai ya yagalgala masa rayuwa. Amma abin mamaki sai gashi iya lallaɓa Dada taima Lulu dan tace wani abu game da samuwar ciki taƙi tace komai. Da tagama zasu dameta sai taja bargo har saman kanta ta rufe kawai da faɗin “Not your business! Please live me alone”.

          Wannan abin da tai ya ƙara sakasu a wasi-wasi, amma sai Alh. Sulaiman yace su manta da batunta tunda dai an ɗauki mataki, yanzu kawai abinda zasu maida hankali shine binciko inda Smart yake ya saketa a ɗaura aurenta da Tajuddeen. Sun gamsu da hakan, sai dai daga ƙarshe Dada ta bada shawaran in har fa anƙi ganin Smart dole ne su nufi Nigeria su makashi a kotu ta bama Lulu takardar saki kawai ko su nemoshi su dole ga amsa kiran kotu yazo ya bada ai. Nan ɗin ma sun gamsu, dan haka suka tsaya a bisa shawaran nan guda biyu…

        Tun daga wannan magana Lulu ta koma musu shiru-shiru a gidan, dama ga yanayin rashin jin daɗin jiki da take fama da shi, wanda zuwa yanzu take kallon hakan a matsayin zubar mata da cikin da akayi ne. Su kuma su Dada ke fassarawa da asiri Smart yay mata kawai. Duk yanda Tajuddeen ke son shigema Lulu taƙi bashi fuskar hakan. Dole ya koma baya-baya da ita amma hakan na damunsa. Bama shi ba hatta su Dadan ta tattara ta watsar kamar bata san da su a gidan ba. Ummita kawai take kulawa dan yarinyar nada hankali da nutsuwa. (Ummita ta taɓa aure harda yara biyu, sannan zata iya girman Lulu kaɗan, wahalar da tasha wajen mijinta yasa bayan ya saketa iyayenta sukace bazata zauna musu a gidaba ta tafi wajen ƙanwar mamanta a Abuja. Karatu ta koma, bayan ta kammala rashin samun madogarar aiki ya sata amsar wannan aikin zuwa Canada ta hanyar Hajiyan Shuwa maƙwafciyar ƙanwar mamanta).

      Duk da abinda Lulu ke musu duk abinda tace tana so sai Tajuddeen ya fita neman mata shi a cikin garin koda yana tunanin bazai samu ba. Duk da dai ma babu abinda tafi nacemawa a yanzu kamar kunun gyaɗa da fruits. Ita kanta har mamakin kanta take akan shan kunun gyaɗar nan na ƙaddara daya sarfaceta. Dan ita a baya ba gwanar shansa bace ba, zama ta iya rantsewa a ɗan zaman datai gidan Aliyu ne ta koya shansa. Sunan Smart da yazo mata a zuciya ya sata jan ƙaramin tsaki. Ɓal-ɓal taji cikinta ya bada har sai da takai hannu samansa ta dafa. Sai kuma akai shiru. Bata kawo komai a ranta ba ta watsar da batun Smart gefe da kan faɗo mata a rai musamman idan tayi wani abu haka daya tuno mata da zaman nasu. Sannu a hankali jikinta kuma sai ya fara sauƙi, zuwa lokacin Alh. Sulaiman da Tajuddeen sun wuce wai duba Baba Garko, sai dai a baɗini shi Alh. Sulaiman nashi zuwan akwai manufa. Ganin Lulu ta samu sauƙi ta murmure sosai sai ma wata ƴar ƙiba da murjewar jiki da ta fara. Dan tayi wani irin ƙyau na farat ɗaya da haske tare da ƴar ƙiba. Zuwa yanzu babu abinda ke damunta sai ɗan zazzaɓin dare. Da zaran ance sha biyu tayi zazzaɓi zai rufeta, zuwa gabannin asubahi kuma sai ya sauka ta wayi gari garas tamkar komai bai faru ba. Shan kunun gyaɗa kam sai abinda yay gaba. Tana nan tana abunta. Tun Dada na maganar wannn shan kunun gyaɗa data laƙama suna na fitina har ma ta kawo ido ta zubama Lulun kawai………✍️

𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲

  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆’𝙊…..!!🫗

           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

      𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔

𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 7️⃣

……..Kwanan Dada goma sha ɗaya ta fara shirin komawa wajen mijinta. Lulu ko ta maƙale tace ƙafarta ƙafarta dan bazata sake zama ita kaɗai anan Canada ba ciwo ya halakata. Cikin lallashi Dada ta nuna mata bazai yiwu ba, ta kwantar da hankalinta ai Tajuddeen na dawowa nan ɗin duk da ba’a gidan zai zauna ba. Tsaf ta tubure cewar ai ita ko ƙasa ɗaya ma bazata zauna da shi ba. Tunfa Dada na lallashinta harta birkice mata da masifa cikin ɓacin rai. Amma hakan baisa Lulu ta yarda zata cigaba da zama a Canada ba. Sai ma cewa tai ita gida Nigeria zata koma to. Tofa babbar magana, hankalin Dada ya tashi, dan tasan taurin kai irin na Lulu sarai. Alh. Sulaiman tai kira ta sanar masa. Washe gari sai gashi ya sake dawowa Canadan. Shima balbale Lulu yay da bala’i tare da zageta tas ita da Daddy sannan ya saka Dada tattaro masa passport ɗin Lulun da komai da zai iya taimaka mata fita a ƙasar ya wuce da su harda na Ummita ma. Wannan abu ya tada hankalin Lulu, hakama Dada sai al’amarin ɗan nata ya fara bata mamaki kuma. Dan sai take ganin ya zafafa da yawa, miye na ɗauke passport kamar wasu masu son kidnapping yarinya?. Amma ta kasa iya masa magana dan harga ALLAH tana shakkar ɗan nata kasancewarsa ba kanwar lasa bane ba.

      *_NIGERIA_*

    Alh. Sulaiman ya koma Nigeria bisa matsawar Tajuddeen dole yakai kotu akan alƙali ya saki Lulu, amma sai ya bashi amsa da cewar sai ma’aurata duka sun gurfana a gabansa zai iya aikata hakan. Zancen ya matuƙar bashi haushi ya yayyaɓama alƙalin magana duk da kuwa suna mutunci. Shiko yay biris da shi dan yace bazai aikata abinda ya saɓaba, taya zai kama kashe aure ma babu masu alaƙa da auren kamar a garin da babu shari’a, to yace yamawa hukunci kenan. Kusan alƙalai biyu ya sake tunkara bayan na farko amma amsar duk iri ɗaya ce suma since