Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 6

Zakaran Da Allah Yanufa da Chara Chapter 1

This entry is part 1 of 6 in the series Zakaran Da Allah Yanufa da Chara by Nuceeyluv

( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai Yayi_)

Na

*Nuceeyluv😘*

*Alhamdulillah Allah ya sake dawo Dani a sabon littafi na me suna a sama👆🏻, Bayan dogon hutun zango da mukaje💃🏻 yaudai gamu tsundum mun dawo, Ina masoyan Dangin Na fulani😂 kun gane ai😉 @SIRRIN ZUCIYA😜 da fatan Baku manta ba🤣 toh yanzun ma Nuceeyluv batayi kasa a gwiwa ba Dan ta sake zuwar muku da Wanda yafi SIRRIN ZUCIYA😋 karki Bari a baki lbri ‘yar uwa💃🏻 karki Yi sake a barki a baya💃🏻 masu iya mgn kance sawun giwa ya take na rakumi🏌️‍♂ï¸? toh wollah haka abun yake dokin Wannan littafin ya take SIRRIN ZUCIYA nesa ba kusa ba😍 haba madarar dadin ma ai sai mun luntsuma cikin lbrin…*✍ðŸ?

1….

Tafe yake cikin takun sa na kasaita Yana me kokarin zare labcoat dinsa cikin wani irin salo me matukar birgewa, *DR. UMAR SALEES* kenan matashin Dr. Me jini a jika Yana da cikar sura irinta mazanta, Idan Yana tafiya sai kace basarake kazalika idan Yana mgn tamkar Jinin saura Kai kace Dan sarki ne, Jajir yake idanunsa dara-dara lumsassu Wanda suke yanayi da kamar yanajin bcci, kwayar idanun sa fara ce tass tamkar Madara Dan haske yyinda bakin dake tsakiya ya Kara kawatu, Yana da saje irin na isassun ‘yan gayu da hancin sa Wanda ya dace da kyakkyawar fuskar sa, a takaice dai UMAR Yana da kyau da cikar sura shiyasa dayawa Mata ke kware masa, maza ke jin kishin sa, toh da Allah yasa shi bana matan bane sai ya kasance bema San sunayi ba Dan Abinda ke gabansa ya ishe shi, Wani abun mamakin shine Koda yaushe fuskar Umar a dinke take is hardly aga Yana dariya saita kure idan abin yakai dole yyi dariyar kaga yadan murmusa kadan, hakan ma sai idan tare yake da abokin sa Sadeeq,

 Sadeeq shine kadai best frnd dinsa tun yarinta har kawo yanzu tare suke, Bayan shi baya yiwa kowa dariya fuskar San Nan a dinke take, shiyasa dayawa ‘yan Mata saidai su kware masa daga nesa badai a kusa dashi ba Dan kowacce ganin sa take tamkar Namijin Zaki. Huh! Kada na cika ku da surutu domin idan nace Zan zayyano Sura da Kamala irinta Umar Zan rubuta littafi guda ban gama ba#lol😜.

Cikin sauri ya Isa cikin office dinsu direct inda ake rataye labcoat ya nufa Nan ya rataye tasa a wajen, a gurguje yyi sallama da Prof Sa’idu dake kan kujera Yana duba system, Prof Sa’idu ya dago Kai Yana duban Umar hade da kokarin zare glass dinsa yace,

“Saurin me kke haka Umar?”

Umar yadan Sosa keyar sa cikin girmamawa yace,

“I’m sorry an kirani a gida ne emergency before mu shiga theater room”

Prof ya girgiza Kai Dan yasan Umar Kai tsaye zai Gaya maka gsky komai dacin ta, shiyasa ya yadda dashi Dan yasan karya ba dabi’ar sa bace,

“Okay you can go, But u make sure ka dawo akan lkci kasan yanzu zaku koma school”

“Insha Allah I will try best”

Girgiza Kai Prof Sa’idu yyi, yyinda Dr. Umar ya juya da sauri yabar cikin office din, budewar kofar sa keda wuya daidai lkcn Dr. Sadeeq ya taho office din shima, Kadan ya rage basuyi Karo ba, Dr. Sadeeq ya dubi Omar da mmki yace,

“Kai lpy?”

Ya tmby Yana wara ido, dafa goshin sa Omar yyi Yana me dawo da hannun ya hade su waje daya👏🏻 yyima Sadeeq haka bece masa komai ba ya raba zai wuce, da sauri Sadeeq yasha gaban frnd din nasa yace,

“haba Omar wani lkcin fa wulakanci ne dakai wlhy, tmbyr ka fa nake Amma ka wani hade min hannu kamar wani ba’indiye”

yyi mgnr cikin tsokana Dan ya Saba fada masa hakan sbd kamar Al’adar sa ce mgn wahala take masa gara yyi maka nuni da hannu, Dan cije lips dinsa yyi Yana me shafa lumsassun gashin kansa cikin nutsuwa yace,

“sorry Sadeeq Ina sauri ne”

cikin kulawa Sadeeq yace,

“Ina zakaje haka kke sauri?”

Sake shafa sumar sa yyi yanaji kamar ya make Sadeeq din Amma ya Sansa da naci idan be Gaya masa ba yanzu zai Dame shi da tmby, cikin nutsuwa yace,

“Abba ne ya kirani before mu shiga theater room yanason gani na Dan yanada wani muhimmin zance dazai Gaya min,  a lkcin naso na fasa shiga sbd yadda yake min mgn nasan serious issue ne, sai yace min tunda na riga na fda masa inda zamu shiga na Bari idan muka fito sai na same shi a gida tunda mukayi mgnr naji zuciyata ta kasa nutsuwa hankali na ya kasa kwanciya kaga kuwa Dole nayi sauri”

Sadeeq ya sa hannu a Aljihu Yana zaro keys sannan yace,

“ga Wannan key din sai kaja mota ka tafi Dan kafi sauri”

girgiza Kai Dr. Omar yyi Yana Dan dafa kafadar Dr. Sadeeq yace,

“Karka damu Aboki Zan Isa gida da wuri Insha Allah”

rage fara’ar fuskar sa Sadeeq yyi Yana me duban Omar daya juya ya fara tafiya cikin takunsa na kasaita, shidai ya rasa gane kan Omar besan wanne irin mutum ne shi ba me tsananin gudun abun hannun wani, to Amma by now ya kamata ace abotar su ta wuce hakan, da sauri yabi Bayan Omar din Dan harya fara taka harabar hsptl din, ba xato Omar sai ganin Sadeeq yyi a gaban sa hakan yasa yaja baya da sauri, Sadeeq cikin bacin Rai yace,

“A tunanina Omar kayana naka ne haka zalika kayan ka nawa ne, karka manta mun wuce a kiramu abokai saidai ‘yan uwa to meyasa kke da tsanani ne Omar? Kodai har yanzu baka daukeni kamar yadda na dauke ka bane? Karka manta yadda Abba yake mahaifi a gareka Nima haka na dauke shi tamkar uba kazalika iyayena sun dauke ka tamkar dansu meyasa har yau ka kasa sakin jiki da mu ne?”

 Hmmm….! Sadeeq Yaja ajiyar zuciya Yana cusa masa keys din Aljihun gaban rigar sa yace,

“ko badan ni ba kahau motar kaje domin Amsa Kiran Abba cikin gaggawa”

ya fada Yana me bar masa wajen da sauri danma karya dawo masa da key din. Girgiza Kai Dr. Omar yyi Yana Dan cija lips dinsa badan yaso ba haka ya canja akalar tafiyar tasa zuwa parking space cikin Jerin motocin da akayi parking ya zaro wata zazzafar BMW me tsananin daukar ido da haske ya Buda cikin Nutsuwa ya shiga ciki, wohoho kaiii..! Gsky Omar karshe ne kamar Dan shi akayi motar tayi matukar dacewa dashi, kafin wani lkci harya bar cikin hospital din.

*****

….gwalalo ido tayi tana me sake Mirza idonta dgske shine kwance cikin jini male-male

“Na shiga uku ni Saratu”

Ta fada tana rufe bakinta kar makota suji, babban tashin hankalin ta kada ace mlm Sale ya mutu Nan take cikinta ya duri ruwa tunowa da tayi dazu fa da tayi masa laben taji Yana waya da MARU idan Bata manta ba taji yace yazo, Tabbas zaizo ta fada tana Kara Tabbatar wa da kanta hakan, a sukwane ta shige dakinta ta debo kudin napep cikin hanzari ta saka hijab dinta a karkace kafin wani lkci ta zari jakar ta kamar ta wanzamai ta jawo kofar ta rufe Fadi take,

“bansan wanne tsautsayi ne ya dawo Dani gidan Nan ba a Wannan lkcin”

 da sauri ta zura takalmin ta wari da wari ta sidado tabar gidan Dama unguwar baki daya Allah ya sota ta faki idon mutane Babu Wanda ya lura da ficewar ta.

Barinta unguwar keda wuya Dr. Omar ya sanyo hancin motar sa cikin unguwar, daga bangaren gidansu yyi parking sbd yasan motar bazata karasa jikin kofar gidansu ba dalilin Kwata data biyo ta wajen, cikin sassafar ya bude kofar tasu Yana me yin sallama cikin nutsuwa.

Shiru gidan ba kowa be wani damu ba Dan ya Saba da hakan shi da mahaifin sa mafi akasari sune suke jire gidan Yana takaicin Wannan Aikatau din da mahaifiyar su takeyi babban Abinda ke jefashi cikin kunci da damuwa kenan uwa uba idan ya tuna yadda ta tsane shi kamar Arne da kafiri sai yaji gaba daya duniyar tayi masa zafi, idan ya hango yadda ta maida mahaifin su tamkar wani sakarai duk ta shanye shi sai yaji kamar beyi sa’ar zuwa duniya ba gefe guda kanwar sa Data maida ta tamkar wata jari abin na ci masa tuwo a kwarya, Ya rasa inda xaisa ransa yaji Sanyi damuwa da tunani sunyi masa yawa ainun ya rasa Kama asalin bakin zaren…..

Tunda yaji shiru yasan da alama ko Abba Yana lazimi ne gyangyadi ya dauke shi tunda 11am yanzu da alama ya shiga yin walaha ne, a nutse ya yaye labulen Yana me sawo kansa cikin dakin Abban nasu,

kyammm….. Dr. Omar ya kame bakin kofa bakinsa a hangame sallamar dayayi niyyar Yi ta makale a makoshin sa, jikinsa ne ya fara kyarma labban sa na motsi saidai ya kasa furta komai, dakyar da sidin goshi ya samu hada kalmomin da zasu bada sauti cikin rudani ya furta A…a…a..b..bbb..A…bba…! Dr. Omar ya furta hankalin sa a matukar tashe ya Isa gaban Abban nasa dake kwance cikin jini male-male.

*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA….🐓*

( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Na

*Nuceeyluv😘*

Series NavigationZakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *