Gaba Kuraa Hausa Novels

Gaba Kuraa Part 3

This entry is part 3 of 5 in the series Gaba Kuraa by Sadnaf

THIS NOVEL IS DEDICATED TO BARRISTER BILKISU GARBA

GABA KURAA

 NA SADNAF

Page 3

Kasa mik’ewa nayi tsaye saboda tsananin tsoron daya rufeni dan har fitsari na saki Ina daga kwancen

Haskeni wani yayi da cocilan Yana “Kaga yarinya fa Ina ganin lokacin data shigo kaga iirn yarinya da Madu yake San lalatawa ke tashi mana”

Ya daka min tsawa

Amma sai na kasa tashi dan jikina wani irin rawa yake

Ihuun madu kawai ke tashi dan waje suka yi dashi suka yi ta duka

Wanda ya haskeni da cocilan ya matso kusa dani shi da wani Yana “Ni dai ko Yama yi wa yarinya nan wani Abu ne naga ta kasa tashi

“Aaa ba abinda ya Mata gaskiya dan tana shigowa na ganta na fada muku kaga Yar yarinya da ko nono babu a kirjinta tashi mana naga da kafarki kika zo wajensa”

Wanda ya karbe maganar ya daka min tsawan daya sa naji kamar kirjina ya fado kasa.

Na mike zaune Ina k’ok’arin kare fuskata daga haskenin da suka yi”

Ya fusgoni waje yana cewa sauran
“Kaga karamar yarinya data zo wajen Madu ke Mai kika zo nema a wajensa”?

Kamar numfashina zai fita da naga yadda duk suka yo kaina kowa na fadar albarkacin bakinsa.

Madun da nagani kwance shame shame Kansa a fashe yasa naji kamar duniyar na juya min dan gani nake nima haka zasu min.

“Mai kika zo nema a wajen madu daddaren nan”

Wani ya fusgoni da balain k’arfi “Nazo ne ya bani kudi na siya mana abinci yunwa muke ji bamu ci komai ba tun safe”

Nace kamar zan shidde dan har lokacin karkarwa nake

“Ina iyayenki suke Ina ne gidanku”?

“Ai ba wanan tambayar zamu tsaya yi mata ba muje kawai ta Kai mu gidansu dan karka yi mamaki San zuciya ya Fito da mitsitsiyar yarinya nan ba lailai iyayen ta ma sun san ta fito ba”

Har lokacin Mai maganar na rike dani gam wasu Kuma suna kan Madu wai sai sun Kai shi wajen Yan sanda dan haka yake lalata Yara kanana”

Zubewa nayi a kasa da naga sun dage akan na Kai su gidanmu

Cikin ihuun kuka na fara rokonsu da “Dan Allah karku fadawa mama abinda nayi kasheni za tayi wallahi abinci ne bamu ci Madu yace nazo zai bani kudi”

“Wanan yarinya fa karya take ban yadda da ita ba kawai mu kaita gidansu idan ma hakane zamu ji a can”

Duk yadda naso rokonsa basu ko saurareni ba haka suka figeni Ina kuka har muka karaso k’ofar gidan su wajen hudu suka bini.

Wanda ya rikeni ya hau buga gidanmu da k’arfi.

Kafin ya sauke hannunsa Ishama ta Bude k’ofar dan idan har na fita haka take zuwa ta tsaya”

Yadda naganta a tsorace tana binsu da Kallo yasa Na fashe da wani sabon kukan.

Inda ta yo kaina da saurinta tana “Siyama Mai ya faru”?

Ke jeki kira mana Babanku”

Wani daga cikinsu yace.

Nidai kuka kawai nake dan nasan Mai kwaceni a hannun mama yau sai ya shirya.

Ji nake kamar na ciji Wanda ya rikeni na fita da gudu

Koma ina ne gwara na tafi kawai ma na huta

Amma ba zan iya ba saboda Ishama da Hisham

“Dan Allah kuyi hakuri idan laifi ta muku abinci ta fita nemo mana dan Allah”

Kamar an watsa musu ruwan zafi haka suka yi dan kallon Kallo suka koma yiwa juna su Kalli juna su Kalli Ishama su dawo da kallonsu Kaina

Daya daga cikinsu ya fara magana da “Ikon Allah ni kamar ma nasan Mai gidan nan mun tab’a gaisuwa dashi toh Ina Babanku da mamanku da zata fita nemo muku abinci daddaren nan”?

Ishama na k’ok’arin magana muka ji muryar mama da ta Bude k’ofar ta fito tana “Hayaniyar me nake ji haka Mai yake faruwa”?

“Ishama Siyama mai kuke yi a waje innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah yasa lafiya”

Mama tace tana dafe kirjinta.

Wanda ya rikeni ne ya hau magana har lokacin Yana rike da hannuna “Hajiya wanan yarinya yarki ce”?

“A yata ce lafiya”?

“Yanzu nan muka ga taje shagon wani Mai ruwa wai taje ya taimaka mata da kudi yunwa suke ji basu ci abinci ba banda Allah yasa ban shiga gida da wuri ba Ina zaune a waje da tuni ya lalata ta”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun innalillahi wa inna ilaihi rajiun wallahi karya take a kwance fa suke a dakinsu sunci sun koshi taya zan bar yarana da yunwa har kasa cinye abincin suka yi bari na dauko ragowar ka gani”

Mama tace duk hankali a tashe tana k’ok’arin juyawa ta shiga ciki wani dake tsaye da alama Sam bai yadda da maganar da tayi ba yace “Gaskiya yaran nan ba yayanki bane ba domin muna zuwa itama wanan yarinya ta bamu hakuri akan abinci taje nema musu da alama ba kece kika haife su ba dan da ke kika haife su ba yadda za’ayi wai har ta fito baki san ta fito ba Mai kamar yarinya nan ma za ta yi da kudi idan har ba yunwar ya fito da ita ba”

“Wallahi Bawan Allah karya yarinya nan take san zuciya kawai ya fita da ita Amma a koshe suke ke Ishama ban baku abinci kunci ba”?

“Kin bamu”

Ishama tace da sauri tana gyada Kai

Wanda ke rike dani yace “Hajiya yaran nan yayanki ne”?

“Yaran mijina ne yaran mijina ai Yaya na ne Kuma Allah yasan Ina k’ok’arin kula dasu kawai so suke su jawo min zagi Siyama yanzu abinda Zaki min kenan ni kike so ki sa a bakin duniya duk k’ok’arin nan da nake akan ku idan har zamu iya bawa wasu abinci kune ba zan bawa abinci ba”?

“Bawan Allah ba yadda za’ayi na cuci yayan mijina nidai Allah bai bani haihuwa ba kaga ba yadda za’ayi na cutar dasu.

Yau maganin mura nasha Sam banji motsin fitar ta ba Amma wallahi karya take yi ba yunwa ya fita da ita ba”

“Toh yaro dai baya karya hajiya tunda kin dage ga ta nan Kiji tsoron Allah ki rike amanar da aka baki Yaya na kowa ne Koda baki haifa ba bai dace ki cutar da yayan wasu ba yanzu Banda Allah ya rufa asiri da an lalata yarinya nan tunda Kuma haka ya kasance zamu na sa ido akan yaran Allah ya kyauta”

Daga haka ya saki hannuna Yana cewa sauran su tafi.

Dayan kuwa da bai yadda da mama ba yace “Ina mahaifin nasu yake ne”?

“Baya gari ai matafiyi ne”

Mama ta bashi amsa idonta a kaina

“Toh hajiya a taimaka a Kara wa yaran abinci kila koshine basu yi shi yasa ta fita Kuma Dan Allah Karki daketa dan naga kamar tsoro take ji”

“Ba abinda zan Mata Bawan Allah wallahi ina kula dasu bansan Mai yasa ta fita daddaren nan ba”

Ji nake kamar na bisu da suka tafi jikina rawa kawai yake dan nasan yau mama sai ta min mugun duka daga kallon ma da take min.

Ciki ta koma bayan ta gama min kallon da na Ke Jin kamar na juya nabi bayan wayanda suka dawo dani.

Kasa ma shiga nayi sai Ishama ce ta rike hannuna tana “Siyama zomu shiga ciki wajen wa kika tafi Neman kudin”?

Kuka kawai nake batare da nace Mata komai ba Koda ta ja hannuna cogewa nayi dan tsoron shiga nake

Ta Kara Jan hannuna na Kara cogewa cikin kuka Ina “tsoro nake ji Ishama mama dukana za tayi”

“Ba zata dake ki ba zan roketa ta dakeni akan ta dake ki”

Dak’yar nabi bayan Ishaman dake Jan hannuna da k’arfi.

Sai da ta kulle kofar muka shiga ciki inda muka nufi dakin mu da sauri da muka ga mama bata tsakar gidan.

Sai dai Muna shiga dakin muka ga mama a tsaye idonta ya kada yayi jajjur

K’ok’arin fusge hannuna nake daga na Ishama dan guduwa kawai zanyi dan gani nake mama kasheni kawai za tayi.

Ishama kuwa ta rike hannuna gam ta tsugunna akan gwiwarta ta hau bawa mama hakuri.

Mama Kallona kawai take ni kuwa sai kuka nake Hisham Kansa kuka yake yi.

Sunan Ishama mama ta kira

Ishama ta ansa cikin rawar murya

Mama ta fara magana tana “tun yaushe Siyama ta fara fita daddare nemo kudi dan ta siya muku abinci”?

“Yau kawai ne mama”

“Ni zaki yiwa karya Ishama kinsan Allah rashin fadamin gaskiya ne zai Saka na hadaku gabadaya na muku duka nace yaushe ta fara fita daddare bansani ba”?

“Wallahi mama kwana uku kenan da take fita Kuma tana fita take dawowa Dan Allah mama kiyi hakuri ba zamu sake ba”

“Ke wajen wa kike zuwa idan kika fita Siyama ki gaya min gaskiya wallahi kika min karya ballaki zanyi”

Kuka nake da iya karfina Ina yarfa hannuna nasan wacce mama idan har na mata karya zata iya ballanin dan tunda ta tab’a konani da iron nasan ba abinda ba zata iya yi ba idan har tace za tayi din.

Cikin kuka duk na bata labarin fitar da nake zuwa wajen Madu ba abinda na b’oye mata na Kara da “Dan Allah mama ki yafe min ko yunwa zai kashe mu wallahi ba zan Kara fita ba”

Ta Dade tana Kallona bata ce komai ba

Har lokacin nida Ishama a durkushe muke a kasa

Ni da Wanan kallon gwara ma kawai ta min hukunci na samu kwanciyar hankali.

Sai da ta Dade bata ce komai ta nufi wajen k’ofa da alama so take ta fice daga dakin sai naga kamar duka take so ta kawo min sai na mik’e da sauri Amma ko Kallona ba tayi ba sai ji nayi ta cewa Ishama

“Zoki karbi bredi kuci zuwa da safe tunda kun fara k’ok’arin tona min asiri”

Ishama mik’ewa tayi tabi bayan ta har lokacin a balain tsorace nake ban ma shiga dakin ba dan gani nake mama zata dakeni so take kawai na saki jikina.

Ina tsaye Ishama ta dawo da katon bredi har da butter baki sake na zubawa Ishama ido har sai da ta shiga dakin mu Nima nabi bayanta”

Nidai gani nake mama so take mu saki jiki shi yasa ta bamu bredin

Hisham ne kawai yaci bredin ni har lokacin na kasa samun kwanciyar hankali

Ita Kuma Ishama sai tambaya ta take Mai yasa nake zuwa wajen Madu Mai yasa na b’oye mata bansan mugun Abu Madu yaso yamin ba

A takaice a ranar bacci bai zo kusa dani ba yunwar ma daina ji nayi saboda rashin kwanciyar hankali dan gani nake mama zata dawo dakin

Ishama kuwa bacci barawone ya sace ta bayan itama taci bredin kadan.

Da ace nasan Yan uwan Abba da Basu fiye zuwa ba da suma banga alamar suna San mu ba da mun gudu munje wajensu.

Haka na kwanan zaune a tsorace ko Yaya naji motsi sai na zabura.

Balaraba

Tunda ta koma daki ta hau safa da Marwa tana tunanin matakin da ya kamata ta d'auka akan Siyama da take ganin itace zata fi bata matsala  acikin yaran Jafar.

Tsanar da take wa yaran ba karama bace dan gani take Jafar yafi fifita su akan komai.

Bata manta yadda ta dage wajen yiwa Jafar biyayya dan kar ya tab’a tunanin yi mata kishiya saboda haihuwar da ba tayi sai gashi tana zaune ta saki jiki ta gama Shirin tarbarsa daga tafiyar da yayi sai ganin shi tayi da matar da take ganin koda kasheta tayi ba lailai ta hucce ba.

Akan ta sai da aka yanke mata igiya biyu dan kawai tana d’auke da ciki ita kuma bata haihuwa.

Kwanciya tayi ta tafi Tunanin irin rayuwar da tayi da kudirat da tasan ta karfin tuwo ta raba ta da mijinta.

Waiwaye

Jafar.

  Ido ya zubawa kudirat dake rike da ledoji niki Niki ita da mamanta da alama daga kasuwa suke.

Dan yanzu sau uku kenan Yana ganin kudirat.

Bai San mai yasa tunda ya ganta yaji ta kwanta masa ba a karo na farko da yaji San wata ya mace bayan balaraba.

Da harshen turanci ya gaishe da maman kudirat data daura zani biyu fuskarta taji tsagun bibiyu Koda baa fada ba yasan Suma yarabawan ne.

Amsa masa tayi kudirat ita kuma sai ta gaishe shi cikin fara’a tafi Mahaifiyar ta kyau sosai ba Kuma fara bace ba amma tana da haske sosai itama da tsagun a fuskarta amma bai Kai na Mahaifiyar ta tsayi ba sai ma ka kura mata ido zaka gane tana da tsagun.

Da ido ya bisu har sai da suka bacewa ganinsa

Ta Inda ya kama gidan nan ne wajen hanyar wucewar kudirat din.

Wasa wasa sai gashi kudirat tayi Kane Kane a ziciyarsa har Allah Allah yake ya dawo daga aiki ya fito ya zauna a waje ko zai ga wucewarta.

Turanci tafi ji hausar da alama ba wani ji take ba.

Wajen karfe hudu na yamma Yana zaune ya hango kudirat din daga nesa ita da wata karamar yarinya

Daga shigar da suke yi ya gane ba lailai musulmai bane su.

Daga nesa ya gane itama satar kallonsa take.

Sai da ta zo dab dashi ya mik’e tsaye cikin fara’a da broken din da aka Fi yi a garin ya hau tsokanarta akan ta kawo ledar ya rike mata.

Cikin Jin kunya ta rufe bakinta tana ce masa uncle daya bari.

Shi kuwa ya saki murmurshi yana shi dai ta kawo ledar ya rike mata rakiya zai mata Amma fir tak’i

A takaice a ranar yasan sunanta kudirat inda shi kuma yace mata sunansa Jafar aiki aka turo shi garinsu.

Idan ba zata damu ba zai so ya ringa zuwa gidansu su ringa gaisawa.

Anan ta nuna masa tsoron ta akan kar yazo zaa mata fada

Budar bakinta sai cewa tayi ai da gani shi musulmi ne ita kuma zaa mata fada idan ta kula shi daga maganar da ta masa ya gane kamar gidansu nada tsauri akan kula ma Wanda ba addininsu daya ba uwa Uba Kuma Wanda yarensu ba daya ba.

A lokacin tana secondary school.

Yaso ya hakura kodan bambancin Addini da kabila dake tsakanin su Amma sai ya kasa dan sosai yaji ya kamu da san kudirat din har ma yaji yana sha’awar ya aureta ko Allah zai basu haihuwa a tare dan Yana balain san haihuwa ba zai iya zama da iya balaraba da suka yi shekara kusan biyar a tare da zuwan da suke Asibtin aka tabbatar masa da matsalar daga wajenta ne ba zata iya haihuwa ba.

Koken koken da balaraba ke masa yasa mi shi tausayinta inda ya hau kwantar mata da hankali ta hau rokonsa akan kar ya Mata kishiya akan bata haihuwa inda ya biye mata kawai dan ya kwantar mata da hankali amma har ga Allah Yana mugun San haihuwa.

Duk da an ce mata ba zata iya haihuwa ba haka take sa shi kashe kudi,daga taje can neman maganin haihuwa sai ta tafi can har kauyuka take zuwa wai ayi mata addu’a ta samu haihuwa.

Shi dai yasan haihuwa na Allah ne idan da rabon zata haihu a gidan duniya Koda bata je Ko’ina ba zata haihu.

Yan uwansa kuwa sai tallan mata ake masa akan ya Kara Aure,amma saboda kar balaraba ta ji ba dadi yak’i amsa tayin da ake masa dan ba laifi ta masa hallaci tun lokacin da bashi da komai har Kuma ya fara dan samun yan canji.

A duk lokacin daya so cire kudirat a ransa sai yaji kamar Kara masa Santa ake

Da alama itama kamar ta fara San shi dan musamman take tsayawa idan bata ganshi ba ta kwankwasa har sai ya fito waje.

Dabiunta duk na musulmai ne idan ba dan cross din da ke wuyanta ba ba Mai yadda ba musulma bace ba

Gidansu Kuma duk lahadi zai ga sun zo sun wuce sun tafi coci.

Yasan ya shiga tsaka mai wuya dan so yake wa kudirat bana wasa ba har sai da ta Kai shi ga fada mata irin san da yake mata.

Inda itama ta nuna masa tana san shi kawai dan dai ita ba musulma bace ba Kuma gidansu ba zasu yadda ta kula shi ba.

A cikin wata guda suka yi wani irin shakuwa na ban mamaki dan sosai take San shi har tana nuna masa ba zata iya rabuwa dashi ba.

Inda yayi amfani da wanan damar wajen cewa idan zata yadda ta musulinta shi kuma zai aureta.

Anan Kuma yaga hankalinta ya tashi inda take cewa iyayenta zasu iya tsine mata idan har ta musulunta Kuma ba lailai ma su yadda ta aure shi ba amma ita zata roke su idan har ya yadda tayi addininta.

Nan shi kuma yace mata Yan uwansa ba zasu yadda ba da dai ta daure ta musuluntar.

San da take masa yasa tace zata yadda idan har zai aureta

Ita dai iyayenta take ganin ba zasu yadda ba

A haka ya kwantar mata da hankali akan zai samu wasu su je su samu iyayenta.

Duk a tsorace take da maganar zuwa wajen iyayenta dan tasan dak’yar su tab’a yadda.

Kamar yadda kuwa ta fada ranar da yaje wajen iyayenta da wasu yarabawan da yake mutunci dasu da itace Mahaifiyarta ta biyo shi.

Irin masu akida dinan ne akan yaransu.

Silar haka har duka kudirat ta ringa Sha a hannunsu suka hana ta fita.

Ba Karamin gargadi suka masa akan rabuwa da ita ba

Har ya fara tunanin hakura da ita

Kudirat ta saci jiki ta zo ta same shi akan su gudu ita zata musulunta ya aureta Kuma.

Ashe sun ga lokacin da ta saci jiki ta fito.

Yana k’ok’arin magana yaji ana buga gidan da k’arfi.

A takaice har station aka Kai jafar akan rabuwa da kudirat.

Kudirat kuwa itama ta dage ba zata iya barin Jafar a station ba sai dai a kulle su a tare.

Ba Karamin tashin hankali aka yi ba dan babanta da maman dagewa sukayi akan idan har bata rabu da Jafar ba zasu tsine mata su cireta daga cikin yaran da suka haifa.

Su ba zasu tab’a yadda jininsu ta auri musulmi bahaushe bama balle har tace zata karbi musulunci.

Kudirat idonta ya rufe duk sharudan da suka gindaya mata da duka haka ta sa kafa ta Shure akan ita dai tana san Jafar.

Jafar matakin da iyayen ta suka d’auka ba Karamin daga masa hankali yayi ba inda ya so nunawa kudirat ta hakura kawai shi ma zai hakura da ita.

Amma kudirat ta dage akan tana san shi ita dai indai zai riketa ya rike alkawari.

A takaice da haka iyayenta suka yi fushi da ita suka koreta ta dawo wajen Jafar kasancewar kusan duk Yan unguwar sun San abinda ya faru.

Haka suka ringa k’ok’arin ganin sun sasanta su amma Ina firr suka ki.

Jafar ba dan ransa na so da yadda ta Zabe shi akan iyayenta ba ya kaita wajen Mallamai aka musuluntar da ita aka sa mata suna Fatima aka Kuma daura musu Aure.

Haka aka ringa rokonsa akan ya rike Amana idan an kwana biyu haka kila idan ta haihu su dawo kila zuwa lokacin iyayenta sun sauko.

Da wanan Jafar ya taho da kudirat arewa a matsayin matarsa.

Koda suka duro gidansu ya fara yi da ita dan so yake yasan yadda zai shawo kan balaraba kafin ya Kai kudirat din gidansa.

Sai dai Koda suka iso irin tarb’ar da mahaifiyar sa ta masa ya fara daga masa hankali dan Yana fada mata tsakanin da da kudirat da dalilin daya sa ya aureta ta mik’e tsaye tana Yana da hankali kuwa duk Matan dake cikin arewa ya rasa wacce zai aura sai yaje can kudu ya d’auko musu arniya……

Series Navigation<< Gaba Kuraa Part 2Gaba Kuraa Part 4 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *