Gaba Kuraa Hausa Novels

Gaba Kuraa Part 4

THIS NOVEL IS DEDICATED TO BARRISTER BILKISU GARBA

GABA KURAA

 NA SADNAF

Page 4

     Hankalin Jafar ba Karamin tashi yayi ba dan mahaifiyarsa Hajiya Gaje dagewa tayi akan sai ya saki kudirat dan ba ta yadda zai rasa wacce zai aura sai arniya ita bata ma yadda da ta musulunta ba.

Kudirat kuwa duk da ba hausar take ji ba daga yadda Mahaifiyar Jafar ke Magana tana nuna ta ta gane akwai matsala da dukan alamu itama bata yadda da Auren ta da yayi ba.

Hawaye kawai ta fara sharewa dan tasan ta tsinci kanta a tsaka mai wuya har taji ta fara Neman yin nadamar biyewa san zuciyarta da wajen gujewa iyayenta akan Jafar.

Haka tayi jugum a Palo tana Jin tashin muryarsu a daki.

Jafar kuwa yadda Mahaifiyar sa ta dage akan bata yadda ma da Auren sa da kudirat ba balle har wai ta zauna a gidanta ba hasali ma dagewa tayi akan ya saketa ga mata nan birjik sai wacce ya zaba ya dirza idan har Karin auren yake so.

Jafar kuwa akan dole ya yanke tafiya da kudirat gidansa tunda har Mahaifiyar sa tak’i amsar ta.

Hasali ma da kyar da magiya ya samu Yan uwa suka sa baki ta janye sakin da ta dage a yiwa kudirat.

Gabad’aya Yan uwan sa ba Wanda ya so auren kudirat da yayi.

Shi Kansa sai ya rasa da bakin da zai rarrashi kudirat dake ta kuka da ya gane cewar duk ta fahimci abinda ke faruwa .

Kansa sai Sara masa yake dan bai san Kuma tarb’ar da zai samu a wajen balaraba ba ga yunwa da gajiya da suka kwaso.

Balaraba tasan yau zai dawo dan suyi waya ta landline ya sanar mata da dawowarsa yaso ace sai ya samu ya shawo kan balaraba kafin ya tafi da kudirat gidansa.

Kunyar ma kudirat din yaji Yana Ji dan ya cika mata baki akan Yan uwansa basu da matsala sai gashi suna isowa Mahaifiyar sa ce ta fara nuna mata tsana karara.

Gidansa dakuna uku da Palo baba.

Daki daya nashi daya na balaraba dayan kuma idan sunyi baki suke zama a ciki.

Daya part din Kuma fili ne Kato da bai gina ba dan gidan nasa babba ne .

A yanzu Kuma da ya auri kudirat ya fara tunanin Gina part din Amma kafin lokacin dakin bakin zai dan gyarawa kudirat ta zauna.

Wajen goma na dare suka iso gidan sai ya tsinci gabansa da faduwa ya dai bawa kudirat baki da har lokacin bata ce masa komai ba.

A yadda ya karanci kudirat din za tayi balain hakuri.

Tausayinta yake ji lura da ta rabu da kowa duk saboda san da take masa.

Buga k’ofar ya hau yi a hankali Yana tunanin karyar da zai yiwa balaraba ya samu nutsuwar zuciya tukunna kafin ya fada mata kudirat matarsa ce.

Balaraba da gudunta ta rungume shi cikin ihuu a lokacin da ta Bude k’ofar.

Idonta ya rufe da murna Sam bata lura da kudirat dake rabe a bayan Jafar itama tana Jin gabanta na faduwa ba dan bata san itama kalar tarb’ar da Balaraban zata mata ba.

Duk Ashe dadin baki Jafar ya Mata da yace Yan uwansa basu da matsala zasu karbeta hannu biyu,dama ana ta fada mata cewar idan har ta musulintar zata fuskanci kalubale daga wajen musulmai kadan ne suke karbar mutum da hannu biyu kasa kawai tayi da kanta tana Jin tsananin tausayin kanta da rayuwar da so ke neman jefata a ciki.

Jafar kuwa k’ok’arin janye balaraba daga jikinsa kawai yake dan kar kudirat taji ba dadi.

Dak’yar ya yakice balaraba da har lokacin take Kankame da jikinsa tana ihunn muran dan kusan wata takwas kenan baya nan.

Sai da ya janye balaraba daga jikinsa ta Ankara da kudirat dake rabe a bayansa

Take gabanta yayi balain faduwa murmurshi da murna da ta zo dashi na tarb’ar Jafar ya Kau daga fuskarta.

Jafar kuwa Sam baya so balaraba ta Kara dagawa kudirat hankali hakane yasa ya fara magana dan yasan kudirat ba zata ji Mai yace ba”

“Tare muke fa da Yar magidana gobe zai biyo ya d’auketa su tafi”

Ya tsinci Kansa da sharo karyar da bai san ma ya akayi ya hadata ba

Balaraba kuwa duk da haka sai ta kasa sakin fuskarta dan dak’yar ta basu hanya suka shigo.

Kudirat kuwa cikin harshen turanci ta dan duka wajen gaida balaraba.

Balaraba kuwa ta amsa mata ciki ciki da hausa

Suka shiga palon gabaki daya

Yadda kudirat ke ta sunne kanta a kasa Jafar Kuma nata Yan kame kame yasa balaraba taji Sam maganar da Jafar ya Mata bai shigeta ba.

Dak’yar ta taushi zuciyarta wajen Kai kudirat dakin bakin kamar yadda Jafar ya umarceta ta zuba mata abinci ta fito.

So kawai take Jafar ya gama cin abinci ta hau jefa masa tambayoyin dake ranta Sam bata ji hankalinta ya kwanta da kudirat ba.

Tana tsoron ma Jafar yace Yana Santa ko Mai gidansa ya bashi ita kullum fargabarta bai wuce ranar da zata wayi gari taga Jafar ya Kara aure akan bata haihuwa ba.

Ko a yanzu ita kadai tasan kudin da ta kashe wajen nemawa kanta magani dan ta samu ciki.

Ji take dama ana fashin ciki da tayi saboda itama ta haihu ko dan kar Jafar ma yayi tunanin Aure duk da tasan ya Mata alkawarin ba zai mata kishiya dan bata haihuwa ba.

Jafar shi Kansa yasan akwai magana a bakin balaraba baya so Kuma ya fada mata komai a Daren nan yafi so ya kwanta ya samu bacci Mai kyau kafin ya fadawa balaraba gaskiya.

Duk yadda balaraba taso masa maganar kudirat sai da yasan yadda ya d’auke mata hankali daga yi masa tambayar a daren.

Idan ya tuna alkwarikan da yayi wa balaraba da yadda balaraba ke San shi sai yaji jikinsa yayi balain sanyi.

Ko baccin bai iya yi ba balaraba ce kawai ta ringa sharar baccinta a kirjinsa

Ji yake kamar ya je ya duba kudirat din da yake Jin kamar tana cikin damuwa yaso ace da ita ya kwana yau Koda ya rarrasheta ta samu nutsuwa a zuciyarta dan yanzu kamar shi kadai ne a duniyarta.

Idonsa biyu har aka kira assallatu ya shiga bandaki yayi wanka ya daura alwala dan ya tafi massallaci har lokacin balaraba bata motsa ba.

duba kudirat yake so yayi shi yasa bai tashi balaraban ba har ga Allah gangar jikinsa ne kawai a wajen balaraban amma zuciyarsa na wajen kudirat.

Sheshekar kukan kudirat daya ji yasa shi yin dakin bakin da saurinsa.

A hankali ya tura k’ofar dakin dan kar balaraba ta juyo shi.

Ya nufi wajen kudirat da ke zaune a tsakiyar katifa ta hada kanta da gwiwa tana ta kuka.

Abincin ma da balaraba ta kawo mata bata ci ba baya Jin ko kwanciya ma tayi.

Fuskarta ya dago Yana Jin kamar ya rushe da kukan shi ma dan tsananin tausayin ta da yake ji,kila da bai shiga rayuwarta ba da duk bata fuskanci wanan matsalar ba.

Bata bar shi yayi magana ba ta fara magana cikin sheshekar kuka tana yace mata Yan uwansa zasu zama Yan uwanta ba zasu kyama ce ta ba,yanzu gashi ta ga alamar Mahaifiyar sa ma ba Santa take ba.

Duk maganar da take cikin harshen turanci take yi.

Yadda kukanta ke dan tashi yasa ya jawota jikinsa dan ya rarrasheta shap ya manta da batun zuwa wani massallaci.

Sallatin da Balaraba ta gwada da k’arfi ya sa shi Jin kamar kirjinsa ya fado ya juya ya Kalli Balaraba dake tsaye a bakin k’ofa tana kallon shi.

Ranar wanka ba’a b’oyen cibi dole dai ya fadawa Balaraba Kudirat matarsa ce.

Mik’ewa kawai yayi ya nufi wajen Balaraba da ya ga jikinta na rawa da karkarwa tama kasa magana

Kudirat kuwa tsoron Balaraban ma taji ya shigeta dan ta girmeta sosai a lokacin baza ta Fi Shekara goma Sha bakwai ba.

Dan ko secondary bata gama ba tana ss 1 lokacin.

Hannun Balaraba kawai ya rike dan yaga alamar kudirat a balain tsorace take baya so balaraba ta Kara tsorata ta.

Wani irin fusge hannunta balaraba tayi cikin wani irin murya ta fara magana tana “Jafar Mai nake gani haka? Mai kake nema a dakin nan?riketa naga fa kayi?Mai tsakanin ka da ita”?

“Balaraba muje daki muyi magana ko sallah banyi ba kiyi sallah Nima nayi sai muyi magana”

“Taya zanyi sallah na kama ka a daki da wata da bansan tsakanin ku ba Jafar cin amanata kake yi da wata ka Kuma kawo min ita har gida”?

“Duk cikin ihuu balaraba ke maganar tana kallon kudirat dake raba ido”

Jafar kuwa ya fara k’ok’arin janye balaraba daga bakin k’ofar Yana “Muje daki nayi magana”

“Ba abinda zaka cemin Jafar ba abinda zai shiga kunnena wanan karuwar da ka kawo min ta bar min gida kawai kafin na lahanta ta”

“Karki Kara ce mata karuwa Balaraba Kudirat matata ce”

Ido balaraba ta gwallo kamar kirjinta zai fado kasa ta zubawa Jafar ido dan ta tabbatar da maganar daga bakinsa ya fito.

Sam Jafar tasan bai tab’a Mata irin wanan wasar ba.

Baki na rawa ta nuna kudirat tana “Kana nufin wanan da nake ganin kamar yare matarka ce?Jafar kana nufin kishiya kamin?Jafar ka manta alkawarin dake tsakanin mu akan ba zaka min kishiya ba?yanzu dan bana haihuwa ka Kara aure Jafar?

“Ina bukatar haihuwa Balaraba har ga Allah ba zan iya zama ba haihuwa ba ba zan tab’a canza miki ba dan na Kara aure ko wata ta haihu dani ba ya kamata kimin adalci Nima kamar yadda nayi Miki”

Balaraba Ihuuu ta sa kamar mahaukaciya tayi kan Kudirat da gudunta.

Tana ba zata tab’a yadda ba sai dai ta kashe su duka.

Fadar haukar da balaraba tayi a ranar bata bakine dan a karshe kudirat kulle kanta tayi a bandaki saboda tsananin tsoro dan har wuka balaraban ta d’auko.

A garin Jafar ya kwace ta yayanke shi hauka dai tuburan ta hau yi tana fashe fashe

Jafar kuwa sai da ya zuba mata Mari biyu ta dan dawo hayyacinta ta hau rusa ihuun kuka.

Jafar kamar shi ma yayi haukan saboda daga masa hankalin da balaraba tayi.

Shi da Kansa yasa mukulli ya kulle kudirat saboda kar balaraba ta ma yi mata komai dan har ga Allah ban da baya so ayi tunanin ya saki balaraba ne saboda bata haihuwa da ya saketa saboda barnar da ta masa da hauka.

Wajen iyayenta yaje ya Kai kararta har ya nuna musu hannunsa da ta yanke.

Iyayenta dattawan arizki ne dan biyo shi suka yi gidan.

Baban balaraba har da dukan balaraban sai da ya kwace ta kuma a hannunsa.

A karshe sai shi ya koma bawa iyayenta baki dan dagewa suka yi tunda bata da hankali ya Mata saki daya idan ta shiga hankalinta sai ya dawo da ita.

Dak’yar da magiya iyayenta suka hakura suka tafi bayan sun yiwa Balaraban nasiha.

Bai wani samu nutsuwa ba dan balaraba bata fasa kuka da daga masa hankali ba ga kukan kudirat da yake jiyowa daga bandaki.

Tattara balaraba yayi ya ajiyeta a gefe ya shiga dakin da kudirat take ya bude bandakin

Ya hau Kuma aikin rarrashin kudirat dake rokonsa ya bata kudin mota ta koma garinsu ita ta hakura da Auren sa ba zata iya ba”

Dak’yar ya samu ya shawo kanta ta daina kukan bayan ya Mata Lodin alkawarrukan akan riketa da Amana ba zai tab’a bari wani ya cutar da ita ba.

Da wanan ya samu kudirat ta dan kwantar da hankalinta inda sai da ya fita ya Nemo mata abinci ya tsaya akanta taci kadan

Tayi wanka ta fito ya jasu sallah

Yana Jin balaraba na kuka a dakinta bai ko bi ta kanta ba

Dan da Wanan damar zai samu ya kwana da kudirat din duk da duk hankalinsa baa kwance yake ba saboda abubuwan da suka faru.

A takaice duk yadda yaso rarrashin balaraba dan ta karbi kudirat a matsayin kishiyarta ki tayi,akan dole ya tsaya ya zama namiji saboda ya musu adalci su biyun

Kudirat kuwa bai ga alamar matsala a tare da ita ba tana da balain saukin Kai ga biyayya.

Da haka ya siya Mata sabon gado komai da komai ya sa mata a dakinta.

Ya raba musu girki.

Har lokacin Balaraba ji take kamar ta samu fetir ta Kona kudirat da bata fitowa waje Sam kullum tana cikin dakinta dan duk wani abu da take bukata tana dashi a cikin dakinta.

Jafar kuwa gajiya yayi da rarrashin balaraba ya kawo ido ya zuba mata.

Wata biyu a tsakani sai ga kudirat da ciki dan rashin lafiya da amai ta ringa yi sosai sai da ya kaita asibiti

Koda aka fada masa juna biyu gareta

Sumewa ne kawai bai yi ba dan murna.

Fadar farin cikin da ya tsinci Kansa a ciki bata bakine dan kamar zai Goya kudirat haka ya ringa ji

Tsabar murna da farin cikin da yake ciki suna dawowa ya nufi dakin Balaraba cikin tsananin farin ciki ya hau gaya mata kudirat nada ciki idan ta haihu ita zai bawa komai kudirat din ta haifa.

Balaraba ko auren da yayi bai matukar girgiza ta ya daga mata hankali kamar yadda cikin da kudirat ta samu ya daga mata hankali ba.

Rawar jikin da ta ga Jafar nayi akan kudirat yasa taji kamar zata zauce.

Jafar kuwa shi yake yiwa kudirat komai ko motsawa baya so kudirat tayi.

Duk wani Abu da yagani sai ya siyowa kudirat

Wanan rawar jikin da yake yasa Balaraba kusan mutuwa dan yanzu Jafar ko ta kanta baya bi.

Jingineta ma kawai yayi dan ko itace da girki haka zai ta leka kudirat din har sai gari ya waye.

A gaban idonta zata ga Jafar ya zage Yana yiwa kudirat girki wai duk dan tana d’auke da ciki.

Idan har dan kawai tana d’auke da cikinsa yayi haka Ina ga ta haihu tasan hoto kawai zata zama a gidan.

Idan akwai wacce ta tsana a rayuwarta bai wuce kudirat da cikin da ke jikinta da take ganin da biyu ma take wasu abubuwan dan kawai ta kunsa mata bakin ciki.

A haka watarana tana zaune a Palo bakin ciki kamar zai kasheta ko baccin kirki bata iya yi.

Kudirat ta fito da dogon cikinta da daurin kirji wai nan zafi take ji

Ta gaisheta da harshen turanci har da dan rusunawa ta samu waje ta zauna

Balaraba kallonta kawai take abaubuwa da dama na darsuwa a ranta

Gani take ba wani zafi da kudirat ke ji ta fito ne kawai dan ta nuna mata Jafar ya kwanta da ita ya Mata cikin da ta kasa dauka.

Mik’ewa tayi ta nufi wajen kudirat din tana ta tasar mata daga kan Kujera.

Kudirat da bata gane mai Balaraban ta fada ba ta tsaya kallonta

Balaraba kuwa ta wanketa da Mari tana ta tasar mata a kujera tace.

Kudirat kuwa cikin harshen turanci ta hau tambayarta Mai ta mata

Balaraba da zuciyarta ke ingiza ta da wanan damar kawai take dashi da zata shaketa ta mutu har shegen cikin da take d’auke dashi.

Ta rufe kudirat da duka tana naushi da iya karfinta cikinta kawai naushi take kawai cikin kudirat dake ta zabga ihuu.

Balaraba kuwa duka kawai ta cigaba da yi dan burinta kawai cikin kudirat din ya zube.

Sam bata San Jafar ya shigo ba sai ji tayi an fusgota an watsar da ita.

Kudirat kuwa sai ihuun cikinta take dan har jini ya fara zubo mata

Jafar a gigice ya kwashi kudirat yayi asibti da ita har da kukansa dan gani yake kamar cikin kudirat ya gama zubewa.

Allah cikin ikonsa cikn kudirat bai zube ba

Koda aka salleme su.

Suna zuwa gida ya shiga dakin Balaraba dake ta addu’a akan Allah yasa cikin kudirat din ya zube.

Jafar kuwa mugun duka ya rufe balaraba dashi ya hada da Mata saki daya.

Sam bai bari ta kwana a gidan ba.

A takaice dak’yar ya Maida balaraba dakinta saboda nauyin iyayenta da yake ji.

A lokacin saura wata biyu kudirat ta haihu

Balaraba kuwa kafin ta koma gidan Jafar ta shirya hanyar da zata biyo wa kudirat da Jafar.

Dan a garin Neman maganin haihuwa ta sansan Mallamai da haka ta fara jifan kudirat akan inta zo haihuwa kar abinda ke cikinta yazo da rai.

A haka ta ringa kananan barbade barbade har lokacin haihuwar kudirat tayi ta haifo ya mace.

Inda hankalin kudirat Dana Jafar ya tashi da su ka ga jaririyar Kamar kafarta daya a shanye yake siriri ba Kuma tsayin kafar daya ba.

Jafar kuwa godiya ya ringayi wa Allah dan yadda yake san haihuwa ko makaho Allah ya bashi Yana so.

Ba Karamin murna ya ringa yi ba.

Balaraba kuwa mutuwa ne kawai ba tayi ba dan ta dauka jaririyar zata zo babu rai.

Akan dole ta boye bakin cikinta aka Sha shagali inda aka sawa jaririya sunan Mahaifiyar Jafar da ta rasu wata hudu da suka wuce a hanyarta na zuwa kauyensu tayi hatsari

Inda ake Kiran jaririyar da suna Ishama.

Balaraba ta ga alamar idan bata Ari fuska biyu ta yafa ba Jafar zai iya yanke duka igiyar dake tsakanin su akan kudirat.

Hakane yasa ta cigaba da asirce asirce Dan raba Jafar da kudirat.

Ko arbain kudirat ba tayi ba ta Kara samun wani cikin.

A ranar da Balaraba ta gane kudirat na d’auke da wani cikin sai da taji kamar zata mutu dan da alama kudirat ta shirya rabata da Jafar gabaki daya.

Kuma taga Jafar yanzu kamar akan dole yake zaune da ita ta kudirat da Ishama kawai yake

Har wai Yana fatan Allah yasa cikin da take d’auke dashi namiji ne.

Balaraba da tsananin mugunta da ciwon Kai ta Isa wajen wani mallamin da tasan ya kware a harkar asiri.

Tayi zaman dirshan da kudin da ta siyar da gadonta dan kawai ta samu cikar burinta akan raba kudirat da Jafar…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *