Gishrin Zaman Duniya Chapter

Gishirin Zaman Duniya Chapter 1

This entry is part 1 of 6 in the series Gishirin Zaman Duniya by Badi'at Ibrahim

*GISHIRIN*

       *ZAMAN*

*DUNIYA*

   _Daga Al’kalamin_

_Badi’at Ibrahim_

( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

GAWURTATTU BIYAR 🤚🏻 TAKUN FARKO

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa  ga al’umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin zamantakewar Aure.

Kashi na farko

Babi na 1~2

Shinfi’da📖

Kano 7/2/2010 gidan cike ya ke dam da ‘yan Uwa da abokan arziki, wanda su ka amsa gayyatar biki na, daga gari gari. ‘Yan uwan  mahaifina  da su ka kasance su ne jigon bikin, kab ‘dinsu sun halarci wannan biki nawa. Daga ‘bangaren maza a waje ‘yan daurin  aure kuma, Kawu Sulaiman wan mahaifina  shine mad’aurin aure na. An cika ma’kil a k’ofar gidan mu dan gudanar da wannan ‘daurin  aure. Ni kuwa ina cikin kawayena da su ka kasance manyan mata. Dan kab kawayena babu budurwa, daga matan aure masu yara, sai zawarawa. Kasancewar na samu jinkirin aure. Shekaruna talatin da biyar a duniya. Daga gari gari a ka halarci wannan biki dan na yi gayya sosai. Abokan aikina na asibiti ma duk sun hallara, kasancewata  ma’aikaciyar kiwon lafiya, bangaren anguwar zoma. Farin cikin da na ke ciki a wannan ranar bai da abun misali. Sanye na ke cikin riga da siket na atamfar Soso, mai kalar  green da wani ganye  ganye mai ruwan madara a jikin atamfar, na yi kyau sosai, sai busa  kamshin turaren humra na ke yi. Kawayena sai tsokana ta su ke ta faman yi. Aminiyata  makociyarmu Amina ce ta shigo d’akin da mu ke ni da kawayena ta na haki. Dubanta nai da mamaki nace.

Ke kuma lafiya ki ke ta haki  kamar wacce jaki  ya ka da ita?” Ba ta ce da ni komai ba, hannuna kawai ta ja, tare da kirawo kawata Hadiza wacce ta zo bikina daga katsina. Fita mu ka yi zuwa bayan gidan mu, in da akwai rangwamen taron  mata. Ta ce da ni.

“Sadiya akwai fa gagarumar matsala a wannan karon ma.” Murmushin ya’ke na yi, domun zuchiyata har ta gama yi mun hasashen abunda amina ta ke so ta ce.”

An fasa  auran wannan karon ma ko Amina?”  Murmushi na sa ke sakar  ma Amina, amma cikin zuchiyata ci take da wuta babababah. Hadiza ta ce.

“Amina dukkan mu ba yara bane. Ina tunanin kwakwalwarmu za ta iya shanye komai. Ki sanar da mu abunda ke faruwa.” Yawu Amina ta ha’diye ta mi’komun wata kalanda. Hannu nasa  na amsa jikina na rawa. A hankali na warware wannan kalandar. Abunda na gani shi ya tsananta bugun da zuchiyata ta ke ta faman yi, take hawaye su ka gama wanke mun ‘yar fuskarta. Kalanda ce mai d’auke da hoton  Ahmad mijin da zan aura yau, tare da kawata Fatima. Ko da na duba date sai na ga the same date da nawa daurin  auren yau. Amina na duba na ce. Ina ki ka samu wannan kalandar Amina, Ahmad d’in dama soyayya su ke yi da Fatima ban sani ba, tare zai ha’da ya aure mu ko kuwa ita ka’dai zai aura, ni ya fasa  aure na?” Dukka Wa’dannan tambayoyin a gigice na jeroma Amina, cikin dimuwa da tashin hankali mafifici. Sau uku ana kawo sadaki na, ana fasa  auran, sabida kawai na yi ilimin boko mai zurfi har ina d’aukar albashi daga asusun gwamnati. Amina jiki a mace ta ce.

“Maman mu ce, ta je bikin jiya. Shine aka rarraba kalandar, yau da na zo sai na soma shiga gida kafin in shigo nan, sai na tarad da mama bata nan, ta na nan  gidan. A kan gadon ta na ga wannan kalandar. Sadiya iyakar abunda na sa ni kenan.” Lumshe idanuna  na yi, ina jin son Ahmad na ninka  kanshi a zuchiyata. Na ce.

Babu komai nagode. Koma mai Ahmad ya ke nufi ai  zan ji zan gani, tunda yau ne daurin  auran, kuma ma yanzu. A wajan na barsu na shiga ciki, ina ta gauraye hanya dan ba na jin da’di sam, zazzab’i me mai zafin gaske ya ke shirin kwantar da ni. Kwanciya na yi a d’akin da kawayena su ke. Sai liyafar cin abinci da shan lamon kwalba su ke yi. Ni kuwa na zama kurma sai duba siririn  agogon fatan da ke manne  a tsintsiyar hannuna na ke yi. Zainab kawata ta ce.

“Sadiya ta wajajen ina gidan da Ahmad zai sa ki ya ke?” Duban  ta na yi a sanyaye na ce.

Ta wajajen D’orayi  gidan ya ke, amma bansan layin ba gaskiya.” Hadiza ta ce.

“Rabu  da ita Sadiya, bayan anjima anjimannan tare da ita za mu je jere, ko wannan dinma mai gidan na ki bai barki bane?” Ta jefa ma Zainab tambaya. Dariya Zainab ta yi tace.

“Ahh haba dai, shima bazai hana ba, ya fa san yanda mu ke da Sadiya. Shima ya na waje cikin maza ‘yan daurin  auren ai.” Ni dai sai bin su da kallo na ke yi. Kanwar  umman mu ce Goggo Hansatu ta le’ko d’akin da mu ke tace.

“Kawayen  amarya da su wa da su waye za su je jere ? Dan Allah ku fito ga iyaye can a wajan mota ku ake jira.” Gabana  ne ya sa ke sabon bugawar da sai da na runtse idanuna. Su Amina, da Hadiza, da Zainab, ne su ka mi’ke tare da bin bayan Goggo Hansatu. Ni dai ina kwance ina jiran tsammanin abunda zai je ya zo.

Su Goggo su na wajan motar kayan da zata kai kayan amarya. Kawu Sulaiman da kawu Bala ne, su ka iso wajan Motar. Goggo Safiya, da Goggo Mariya ‘kannenshi ya ce da su.  Su shiga gida ya na da magana.

Bin bayan su, su ka yi zuwa cikin gidan ‘dakin da ke zauran  gidan, in da anan su ka sauka su maza mazan. Sawa ya yi a ka kirawo Yaya Asabe Babbar yayarsu a mata, da kuma mahaifiyar Sadiya, da kanwarta Goggo Hansatu.

Bayan duk sun hallarane, Kawu Sulaiman yace.

“Toh al’amuran daurin  auran yarinyar nan komai ya jagule ya damalmale. Aisha kin cuce  mu da ki ka bar mana yarinya a gida harta ri’ka  ta ri’ke. Ki ka k’i  fur ki ba mu yarinyar nan lokacin da ‘dan  uwanmu Adamu ya rasu. Amma Aisha ki ka yi fur ki ka hana, wai  ke ‘yar ki karatu za ta yi, Adamun  ya baki wasiccin ki bar yarinyar tai zurfin karatu. Toh yaro dai iyayenshi sun gama bincike sun ce ‘dan su bazai auri yar boko ma’aikaciyar gwamnati ba, ‘yan bariki masu budadden idanu. Shine ni da Bala wan mahaifin Aliyu ‘dan gidan Yaya Asabe, mu ka yanke shawarar a ‘daura auran da shi Aliyun kawai ‘dan wajan ki Yaya. Kuma Alhamdullah, Malam Bala shi ya amshi Auren har da sadaki nera dubu uku ga su.”

Yaya Asabe ta soma rabka  salati  tare da fashewa da kuka tace.

“Shikenan ni Asabe na shiga uku. Sai da yarinya ta zama ‘yar duniyar da a Birni ma ta kasa auruwa, sau uku wannan ne na hu’du ana fasa  aurenta. Shine Bala za ka cuce  ni ka Aura ma K’usar  Yaki ita? Aisha fa sai da ta tabbatar ta raba  Adamu da kab danginsa  da asirinsu irinna mutan  katsinawa, wacce iriyar azaba ce ba ta bamu ba, amma yanzu k’usar Yaki aka aura ma Sadiya? Wallahi bazan yarda ba.” Kawu Sulaiman ya ce.

“Yaya ki yi hak’uri, ni kai na na ji abun. Kuma kinga Sadiya ta girmi  Aliyu da kusan shekara biyar. Goggo Safiya tace.

” Ai  juya shi za ta yi, tai ta yi mai wayo. Ni na tabbatar sai abunda Sadiya ta ce da Aliyu. ‘Yan boko fitsararru da ba zaman aure su ke yi ba. Sun fi so a barsu sakaka sui ta cu’danya da maza wai  abokan aikinsu. Kawu Bala ya ce.

“Yanzu dai bakin alk’alami ya bushe, ni ne dai Wan mahaifin Aliyu kuma ni ne madaurin Auran shi, ni kuma na amshi Aurannan  domun a rufa ma Adamu asiri, shi da ya mutu ya bar baya da k’ura. Yarinya ta yi kwantai  kowa na gudun na shi ya aure ta. Asabe hak’uri za ki yi dan Allah. Goggo Asabe ta ce.

” yaronnan fa, da rana a kan shi. Daya dawo da wata d’aya za’ayi auran shi da Khadija ‘yar gidan mai gari, yarinya ga mai dambu Aminiyata. Wallahi aure kuma ba fashi.” Kawu Sulaiman. Ya ce.

“Wannan ba zai gagaraba yaya Asabe, yaro zai yi auran shi duk macen da ya ke son Aure.” Goggo Asabe tace.

“Shikenan yaya zan yi, cuta ce dai an riga da an cutar da ni. Yaro sai da ya zama mutum tukunna, duk wata kadarata, da gadon da shi kan shi yaron ya samu, duk ya k’are a wajan naiman ilimin addini shine har Madina. Amma zai dawo ya samu mummunan labari, wallahi bazan yi wuyar renon Kusar  yak’i, da gina  shi, Sadiya ta hanani cin arzikinshi ba. Tunda Adamu ya fa’di ya mutu, Aisha ita da ‘diyarta ne ka’dai su ke amshe ku’din pension d’in nashi da garatuti. shikenan na yi  Allah ya sanya alkhairi.” Cikin kuluwa da takaici Goggo Hansatu tace.

“An d’aura auran yarinya, babu wani shawara. Toh ya maganar aikinta da take yi na asibiti, daga can kauyan za ta dinga tawowa  ko yaya? Sannan ya yarinya zata rayu a maraya, wayayya, mai ilimi, ma’aikaciya, sannan ita ba yarinya ba. Kawai a d’aura auranta da wani Wai shi Aliyu. Ai  ta na da hakki  ya kamata aji ta bakinta, koma meye sai a yi daga baya. Sannan Sadiya ba yarinya bace, ta girmi  Aliyu nesa ba kusa ba, wanne irin zaman aure za su yi to? Aure ba soyayya, kuma a kaita kauye shikenan a dur’kusar da rayuwarta, ba za’a barta ta amfanar da al ‘umma da ilimin data karanta ba? Wai me yasa ake ganin illa ne mace ta yi ilimin boko ta yi aiki, dan ta kare  martabarta ta mace, da martabar  k’asar ta. Mu gidanmu ‘yan boko ne, kuma dole Sadiya za ta ci gaba da aikinta.” Kawu Sulaiman yace.

“Ke dakata Hansatu, wannan ba huruminki bane, ko Aisha bata isa ta tanka mun ba kan batun Sadiya. Domun ni ne uban Sadiya, duk duniya bata da gatan  da ya wuce mu. Yarinyar nan zumunci mu ka yi ma, har aka ba ma shi Aliyun domun naga anan taki auruwa, ga shi sai girma take yi, shakaru  takatin  fa da biyar ai  ta gama tsofewa a gida. Maganar aiki ma ajjiyeshi  za ta yi, mu abunda muka sani shine ‘d’akin mace shine darajarta. Mu daraja mu ka ne ma mata.” Yaya Asabe ta cabke  cikin daga murya tace.

“Zancan kauye kuma da kuke yi, ai  Adamu daga wannan kauyan ya fito kuma Aisha ta aureshi ta raba mu dashi, ko san zuwa ganin gida ba yayi. Itama dole ta je ta yi zaman aure.” Goggo Hansatu za ta yi magana Aisha ta d’aga mata hannu, dole ta yi Shiru, zuchiyarta na yi mata k’una. Cikin raunin murya tace.

“Yaya sulaiman Sadiya ‘yar ku ce, kuma kune gatan  ta. Ni ba ku da matsala dani, Allah ya sanya albarka a wannan auran, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare mu baki d’aya.” Ta na kai wa nan ta fice a d’akin. Goggo Hansatu kuwa ba karamin rikici su ka yi da su Goggo Asabe ba. Har sai da ‘yan Uwa aka shiga zancan sannan fa aka yi sulhu. Kawu Sulaiman yace.

“Safiya ina ga kuje  ku tafi kai kayan Sadiyan  ko? Kawayen  ita Sadiyan  suna wajen motar su na jira. Hansatu kuma ki kirawo ta ku tafi tare. Barayin Dauda daya gina  zai sa amaryar sa nan da wata biyu shi

Za ku yi ma Sadiyan  jere  in yaso shi Dauda ya gina  wani. Kui maza rana na yi.” Goggo safiya ba ta ce komai ba ta bi umarnin Kawu Sulaiman. Goggo Hansatu ta dubi kawayen  amarya tace.

“Toh

Su waye ‘yan kwana domun in fa mu ka je acan  za’a kwana waje ba kusa ba?” Hadiza ta ce.

“Ai  ina ga ni ka’dai ce zan kwana, sai Amina ko?” Zainab tace.

“Gaskiya kam ni kam sai dai gobe ma bi ayarin ‘yan budar  kai mu zo ganin d’akin amarya.” Goggo Hansatu ta yi ma su Hadiza jagora cikin motar da za su ta fi. Da ita sai Goggo Safiya, sai Hadiza, da Amina. A gaban mota kuma daga direba  sai Anas  wan Aliyu. Motar su Goggo Hansatu na gaba. Motar kaya na biye da su a baya.

Mahaifiyar Sadiya na dakinta, hawaye kawai ta ke ta faman sharcewa  wa. Hankalinta yai matuk’ar tashi, shin wacce rayuwa Sadiya za ta yi a kauye, gashi an aura mata miji yaro, maganar aikinta kuma fa, shin karatun da su ka da’de suna wahala domun samuwarshi, yanzu gashi ya samu har ta kai matsayin ma’aikaciyar asibiti, shikenan dangin mahaifinta sun dakatar  mata da cikar burinta da manufarta kan karatun d’iya mace?.

“Ya Allah kai ne ubangijin kowa da komai, ya Allah ka saukar ma da Sadiya nutsuwa da dangana, ya Allah ka sa aurannan  na ta ya zame mana alkhairi, ya Allah ka raba  Sadiya da makiyanta masu son ganin bayanta, Allah ka kawo mata sauyin  alkhairi.” Sauke hannayenta da ta ‘daga tayi, ta na zubar da hawaye. Ta rasa dalilin da yasa dangin mijinta su ka tsane ta. Dan kawai ta zama ‘yar boko kuma ma’aikaciyar gwamnati. Shin shi ilimin Mace laifi ne, ko kuwa kasancewarta  ma’aikaciya  zunubi ne?” Mi’kewa ta yi, ta share hawayenta. Cikin dakewar  zuchiyata ta tura d’akin da Sadiya take a kwance.

Sadiya

Idanuna  na runtse domun har zuwa lokacin a cikin fargaba da taraddadin abunda ka je ka zo na ke. Bansan me ke faruwa ba, kuma bansan a wanne matsayi na ke ba a yanzu, matar auran da igiyoyi uku su ka rataye  rayuwarta, ko budurwar da ta gaji da kwanciya a gado ita ka’dai, cike da matsananciyar sha’awa da shaukin jin dumin mijin halali a tare da ita?”

“Sadiya!!! Ki sa me ni a d’aki yanzu.” Juyawa ta yi ba tare da ta ji amsar da zan bata ba. Jiki a mace tamkar kazar da ta taka wu’ka haka na mi’ke.kawayena su kuma sai aikin zolayata su ke yi. Wai tun kamun a kaini har na riga da na karaya. Da dariyar  ya’ke kawai na bisu. Ahankali na dinga ratsa jama’ar biki ina bin sawun mama. Kallon da jama’ar bikin su ke bi na da shi, sai na lura ya wuce gaban misali. Take zuchiyata ta shiga kokawar fitowa da k’arfin tsiya.

Series NavigationGishirin Zaman Duniya Chapter 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *