Gudun Kaddara Part 2

Gudun Kaddara Part 2

This entry is part 2 of 2 in the series GUDUN ƘADDARA

GUDUN KADDARA

HUGUMA

PAGE 02

Wani irin kuka da gigitacciyar qara sultana din ta saki tana riqe bibi data qaraso gurin. Tallafe sultana din tayi tana fadin

“Ashsha,ashsha,haba maina,me ya hadaku da zafi har haka?kai da nace maka baka ta lafiya?” Ta qarashe maganar idanunta saman fuskar sulatana da tayi jazur. Har cikin tsakiyar ranta takeji kamar ana fusgarta,saboda yadda zallar madarar zafin marin ya ratsata yadda ya kamata. Kai tsaye zata iya cewa ta manta da wani abu mai suna mari bare yadda zafi da radadinsa yake,sai gashi yau ya zama mutum na farko da ya tuna mata da wannan

“Ta gaya miki yaushe tabar dakin nan ta tafi gurin raye raye a tsakiyar maza ba tare da saninki ba” abinda ya furta kenan yana nunata da yatsa,ya sauke hannun ya juya yana fita a dakin cikin tsananin qunar rai.

Fuskar sulatana din bibi ke shafawa tana qoqarin rarrashinta,saidai ko a jikinta wai an mintsini kakkausa,kuka take sakewa kamar wadda aka yanki naman jikinta

“Wallahi radadi fuskata takeyi bibi,Allah bazan yarda ba,bazan yafe masa ba” sosai maganar ta daki zuciyar bibi din,tabi sultana da kallo wadda ruwan hawaye ya dade da gama jiqa mata fuska

“Sultana,mainanki ne fa?”

“Shi din bibi,mugu azzalumi,kawai don naji ana kida na tsaya rawa sai ya biyoni ya mareni?,me nayi masa?” Sosai jikin bibi ta mutu,bata taba tsammanin akwai ranar da zata zo da wani sabani me kama da wannan zai gilma tsakanin maina da sultana ba,sultanar da ko ita ba kasafai yake bari tana yi mata fada ba,bare duk da batasan yaushe ne lokaci na qarshe da aka daketa din ba. Sultana din da bata cin abinci ba tare da maina ba,bata iya bacci ba tare da maina ba,komai ma na rayuwarta maina ne,yau rana tsaka kamar wadanda aka yiwa farraqu suke neman sauya halayya ita da shi gaba daya

“Amma dai sultana sau nawa ina jan kunnenki akan zuwa wannan gurin?,saboda gujewa rana irin wannan?,ranar da maina din zai san kina zuwa?”

“Wallahi bai isa ya takuramin ba,shi waye ya takura masa?,kawai don yaga ina masa biyayya?,ai ba tsoronsa nakeji ba” ido da baki gaba daya bibi ta bude tana kallon sultana din. Mainan da ya zamewa kowa dodo cikin gidan?,koda a boye basu iya hirarsa bare a zahiri irin haka amma ita take sake masa magana?.

“Anya sultana?,me yake cikin kanki?,kina girma kina cin qasa?”

“Ki rabu dani tunda goyon bayansa kikeyi kema” ta fada tana ture hannun bibi dake cinyarta,sai kawai ta nufi toilet dinta ta shige ta maida qofar ta kulle,ta zauna a toilet seat taci gaba da rera kukanta kamar wadda sautin yakewa dadi.

Baki sake tabar bibi a zaune a wajen,cikin matuqar mutuwar jiki ta dauke kallonta daga bakin qofar toilet din,tasan halin sulatana da tsananin kafiya da kuma taurin kai,duk yadda taso ta fito a yanzun idan ba niyya tayi ba zata bata bakinta ne kawai

“Allah ya kyauta,yayi mana maganin wannan sabuwar matsalar kuma” bibi ta fadi ta yunqura tana miqewa. Sai a sannan taga jakar makarantarta dama doguwar rigar uniform da hijabinta a yashe a qasa. Tasa hannu ta kwashesu ta juya tana barin dakin.

Tsaye tayi gaban mudubin bandakin nata tana kallon fuskarta,sosai fuskar takeyi mata radadi,tasha ji a bakin su lamira cewa yaa maina din yana da zafin hannu,amma bata taba tantancewa ba sai yau,tunda bai taba kai hannunsa fuskarta ba. Hannu ta sanya ta sake shafar kuncin nata da yayi jajur,abinka da farar fata

“Dama haka zafin mari yake?” Ta tambayi kanta da kanta can qasa,saboda iya rayuwarta da kuma wayonta ba zata iya tuna lokacin da aka daketa bama bare a mareta

“Allah ya isa na” ta fada qasa qasa wasu sabbin hawayen suna zubo mata. Da baya da baya ta koma,tayi zamanta saman toilet seat tana ci gaba da fitar da sheshsheqar kuka. A iya marin da yayi mata yau kawai sai takejin wani mugun haushinsa irin wanda bata taba ji ba. Yaa maina din,shalelenta itama shalelensa,ba wanda ke tabuwa a wajen dan uwansa,amma yau sai taji ko fuskarsa bata son kalla.

Da zazzafan ruwa sosai yayi wanka bayan ya gama dukka uzururrukansa na ranar,da dan wuri yaso shigowa gida saboda yanayin sanyi da ya fara busawa,amma kuma daukan karatun da ya tsaya yi a zawiyya yasa lokacin shigowarsa gidan ya dan ja. Yana shiryawa yana bin tsarin dakin nasa da kallo,yaja tsaki lokacin da ya bude wardrobe dinsa yana bin shirin kayan da kallo.

Hannu ya saka ya zaro wata turtle neck sweatshirt me dogon hannu baqa,wadda ta fidda zallar hasken fatarsa da kuma narkakken kyau da yake shimfide a fuskarsa,wanda ke cakude da qyalli da sheqin samartaka.

A nutse ya shirya,idanunsa saman agogon dakin nasa ya dauki wayarsa yana shirin ya fita. Kamar jira wayar keyi ta dauki tsuwwa,sai ya dakata ya maida hankalinsa kanta.

‘BIBI NA’ shine sunan dake yawo saman screen dinsa. Daga wayar yayi yana ci gaba da shirin fitar.

Muryar Dijama ce, cikin d’ari d’ari da takatsantsan take gaya masa saqon bibi

“Okay” kawai ya fadi a taqaice yana katse kiran. Iska me zafi ya furzar daga bakinsa

“Me ya faru ne bayan tafiya ta?” Ya yiwa kansa da kansa tambayar da shima neman amsarta yakeyi. Gaba daya sauyin halayya da dabi’u yake gani daga yarinyar. Yarinyar da ya bata dukkan wani minti da awa dake cikin rayuwarsa wajen ganin ya raineta rayuwa me kyau,ya bata tarbiyya da tasha banban da ta kowa,ya kuma killaceta fiye da yadda ake killace kowacce diya mace dake jahar maradi,sai gashi tafiyarsa da waiwayo gida da yayi komai ya kwabe ya canza.

Iskar ya sake fesarwa,sai ya soma fita a dakin a gaggauce,can qasan ransa cike da tunani tare da son gano ina matsalar take?.

Zaune ya sameta cikin parlor din nasu,sanye da sassauqar doguwar riga me gajeran hannu,kantan nan yasha gyara qwarai,hannayenta dake sanye da wasu siraran warwaraye riqe da jarida tana dubawa. Farar ba’abziniya,wadda ke tafe da tsaho da qiba dai dai gwargwado. Tana da wani kyau na musamman wanda shekarunta basu kai ga boye shi ba.

Sallamarsa ya sanyata daga kanta ta dubeshi,sai ta sauke qafafunta da suke a harde a dazun ta gyara zamanta sosai tana amsa masa sallamar.

A gefe ta ajjiye jaridar tana dubansa har ya qaraso. Cikin girmamawa ya zame ya tsugunna a gabanta

“Barka da wuni”

“Barkanka,tun dazu nake maka aike ka fito kaci abinci amma hakan ya gagara” agogo ya sake kalla,tabbas yana toilet yaji shigowar almu har sau biyu

“Wanke nakeyi,ina kammala shiryawa kuma na fito”

“Saika qarasa kaci abincin ko?” Ta fada tana miqa hannunta da nufin daukar jaridarta.

“Zanje sashen bibi,yanzu zan dawo sai na zauna gaba daya” tsaiwa tayi da abinda takeyi,ta kalleshi yanayin fuskarta yana canzawa

“Me kuma zakayi a sashen bibi bayan na tabbatar tun safe bakaci komai ba?” Cikin lanqwasa murya da salon lallashi irin wanda ita daya yakewa duk duniya yace

“Yanzun zan dawo AMA,zanyi magana ne da sultana”

“Sultana?……kai dawo ka zauna” ama din ta fada tana sake sauke qafafunta qasa.

Yadda ta buqata haka ya koma ya zauna sosai yana lanqwashe qafafunsa,zama tayi sosai ta zuba masa idanu tana jin wani zafi yana ratsa zuciyarta,ME YASA TAKETA GUDU AMMA KAMAR K’ADDARA NA BIBIYE DA ITA?.

“Wai sai yaushe zaka san cewa ba ahalin su NAFEESA na haifawa kai ba?,sai yaushe zaka daina bautawa abinda ya shafi nafeesa da rayuwarta gaba daya?” Maganar ta sauka a wani muhalli me girma na zuciyarsa,ta kuma taba masa wani gurbi da bayason ta taba masa din har sai da ya dan lumshe idanunsa kadan ya bude,wanda yayi dai dai da sake magantuwar ama

“Tunda na haifoka ruhinka ke walagigi a hannunsu,tun kana da shekara sha biyar ka fara fuskantar qalubale duk don saboda su,da jajircewata da tsaiwata akan rayuwarka na kawo qarshen komai,a yanzun bayan komai ya shude da shekara kusan goma shine kakeson dorawa daga wata bautar da wahalar?” Tayi masa tambayar data sanyashi sake lumshe idanunsa kawai. Cikin tsakiyar zuciyarsa yake bawa kansa qwarain gwiwa,ya saisaita kansa zuwa harshensa sannan cikin tarin nutsuwar da tun yana qanqaninsa ta sanshi da ita

“Ni da nafeesa da sultana duka abu guda ne yayi mu,idan ba jinin nafeesa a jikina ama akwai jinin sultana,ita din qanwata ce halak malak,uwa daya ce kawai bata haifemu ba,amma uba daya muke ni da……..”

“Aliyyu!” Ta kirayeshi da ainihin sunansa

“Banason kaci gaba da gayamin wannan labarin qanzon kuregen……”. Yankewa maganar tata tayi sakamakon shigowar kira wayarta.

BIBI ta gani,sai ta dauke dubanta daga kan wayar ta maida akan maina,sanann ta sake kallon wayar a karo na biyu kafin ta daga

“Okay” kawai ta fada a taqaice,sai ta sauke wayar sannan ta maidata gefe ta ajjiye

“Maina” ta kuma kiransa,ba tare da ya amsa ba yayi qas da kansa

“Duka duka shekarunka ashirin da hudu ko da biyar a duniya,karatu nakeso kayi,ka zama mutum kamar kowa,banaso ka harmutsa rayuwarka cikin matsalolin da ba naka bane,bakai bane tilashinsu,kabar masu matsala suji da matsalarsu,so nake kayi karatu,ka zama wani,domin kaine madubin qannenka,kuma kaine gobe na” Yadda tayi maganar kadai zai fahimtar dakai zallar qauna da soyayyar da zuciyarta ke gwada masa. Ya sani,ama tana masa wata soyayya ta daban,wadda tasha banban data qannensa ma,bai sani ba,shin ko soyayyar ɗan fari daban take da a zukatan iyayensu?.

Wani qaunar ama ne ya sake saukar masa,tabbas duk abinda takeyi yasan tana yine saboda soyayya da qauna irin ta ɗa da uwa,to amma shi ɗin ta yaya zaya zuba ido ya bari tarbiyyar sultana ta samu rauni?,yarinyar da tunda sanarwar haihuwarta ya shiga kunnuwansa yakeji a jikinsa kamar shine mahaifinta?,kamar rayuwarta da haƙƙin kula da ita ya hau kansa kacokam.

“In sha Allah zan kula iya bakin ƙoƙari na,ba zaki sameni da wani abu da bakiso ba”

“kaje bibin tana kiranka” ta faɗa da sautin da zai nuna maka akwai hushi danƙare cikin ranta.

ZAFAFA BIYAR FAMILY🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba

ZAFAFA BIYAR❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥

❤‍🔥 SABUWAR SHEKARA

❤‍🔥 SABON TSARI

❤‍🔥 SABBIN LABARAI

❤‍🔥 TSUMAMMIYAR SOYAYYA

❤‍🔥 CAKWAKIYA

❤‍🔥 LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO

❤‍🔥 SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA

❤‍🔥 LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_

KWANTAR DA ZUCIYA

CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA

QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA

KWANKWASON JIMINA ME WUYAR TABAWA (miss xoxo)

TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE (Billynabdul)

AMEENATU (Mamuhghee)

GUDUN K’ADDARA GUZURIN TARAS DA ITA (Huguma)

KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI.

THANKS FOR CHOOSING US🫂🫂🫂🫂

Join our WhatsApp group here


GUDUN KADDARA 🏃🏽‍♀️

HUGUMA

PAGE 03

Har ya kusa fita ya dakata,ya waiwayo yana dubanta. Kallon jaridar kawai takeyi amma da alama bata iya ci gaba da karanta komai ba

“Don Allah ama almu ko atta,wani yayimin kiran najma ta dawo ta sake gyara dakin nan baiyi ba” fararen idanunta ta daga ta kalleshi dasu

“Ba d’iyar wadda zan kira ballantane ayimin gorin rashin diyoyi mata,ko wannan gyaran ma atta na saka yayi maka,suma a hakan zasu koya,tunda ko yanzun ma wasu abubuwan sukeyi min,banga abinda diya mace zatayi wanda zai gagari namiji yayishi ba” Dan qaramin miskilin murmushin nan nasa da yafi kama da motsa baki yayi. Abu guda daya tal da yasan ya jima yana ciwa ama tuwo a qwarya shine rashin haihuwar ‘YA MACE,shi kuma ya jima da ciwa kansa wani alwashi game da hakan,alwashin da ita kanta bai sanar mata ba har yanzun

“Kiyi haquri zan saka a turota tazo ta gyara” kai tsaye ta sake dubansa

“Ka wuce ka tafi,kafin ka dawo zan shiga na gyara maka da kaina” kansa ya girgiza da sauri

“Karkiyi wahala,zan sake gyaran”

“Nidai iya abinda nace maka kenan” ta bashi amsa a taqaice tana maida kanta ga jaridarta.

Har ya isa sashen bibi zuciyarsa bata huta da tarin tunani da son gano laifin da nafeesa ta yiwa ama ba wanda har yake shafar SULTANA a wajenta,nafeesar da har tabar duniya bata da abokin fada,nafeesar da har ta gama rayuwarta badai kaji ance an kawo qararta ba,nafeesar da har tabar duniya ko musu bata iya ba bare sa’insa da wani. Laifin nafeesa daya ne LALURARTA indai har lalura da ciwo suna iya zama laifin dan adam……indai har suna iya zama kuskuren mutum da har Allah ya zabi ya dora masa ciwon,banda wannan shikam bazai iya adar da komai ba.

Kaf tunaninsa ya yanke lokacin da ya isa dakin sultana din,ya samu masu aikin gidan da su lamira sun cika dakin suna mata magiyar ta fito. Ransa ya baci lokacin da yaga bibi zaune a gefe,itama tayi magiyar tayi magiyar har ta gaji. Shigowarsa kadai ta sanya muryoyinsu daukewa,kowa ya shiga taitayi da nutsuwar sa. Shurun kuma shi ya isarwa da sultana cewa tabbas maina dinne ya shigo,shi daya ke da wannan fitinanniyar kwarjinin dake karya lagon kowa.

“Ni wallahi bazanji tsoronka ba” ta fada qasa qasa tana jan qwafa hadi da hararar qofar bandakin tamkar shine tsaye a wajen

“Duk ku fita” ya basu umarni yana takawa zuwa bakin bandakin.

“Anyi magiyar anyi lallashin amma taqi ta bude,tunda ta shiga take zaune a ciki,kamar wadda ta samu dakin gyatumarta” bibi ta fada hankalinta adan dage tana kallon maina da ya sanya wani dan scissors yana qoqarin warware lock din qofar. Kanzil bai ce da bibi ba. Sultanan na zaune daga ciki,amma tana iya jin kusur kusur dinsa jikin qofar. Sake hararar qofar tayi,don ta tabbatar bai isa yace zai bude qofar ba muddin idan ba itace tayi ra’ayi ta bude ba.

Kadawa hantar cikinta tayi sanda taga ya tura qofar ya bude,ya kammala warwareta tas kenan.

Tsam ta miqe daga saman toilet seat din tana kallon qwayoyin idanunsa data jima da sanyawa suna da LION EYES,ta fada ta sake fada,a duk sanda yake kallonka irin haka,idanun nasa basa mata kama da idon kowa sai idon zaki sanda yake kallonka cikin fusata,tun ranar da sukaje zoo tace wai ta tantance hakan. Tun su chafa’atu na mata dariya har suma sukayi amannar hakanne.

Yadda ya qureta da kallo ya zuba mata ido itama hakan tayi masa,abinda kaf rayuwarsa yafi tsana kenan,kayi laifi sannan ka tsare mutane da kallo kamar sa’anninka?. Duk wani yaro da ya girma ya taso a gidan yasan baya son wannan dabi’ar,sun kuma kiyaye,abinda ya zaunar dashi da su lafiya kenan

“Zo ki fita a gurin” ya fada mata a tsawace,tsawar da taji kamar zata tarwatse da kwanyarta,ta gigitatata har sai data kulle idanunta gaba daya hadi da qanqame jikinta guri daya. TSAWA na daya daga cikin abinda ta tsana,saboda muddin kayi mata ita ka gama birkitata kenan. Duk da kafiya taurin kai da zafin zuciyarta kuwa.

Idanunsa ya lumshe had’i da budesu,yadda tayi din ya tuna masa da naffeesa,abinda ya sassauta ranshi da zuciyarsa kenan,ya kuma sassauta muryarsa

“Fita nace tun kafin na sake kai hannuna kanki”

“Taho muje,ya isa hakanan” muryar bibi ta ratsa toilet din. Ita ta sanya hannu ta jawota ta fito da ita daga bedroom din,ya tako a hankali ya biyo bayansu yana sake karantar canjin halaye matuqa daga gareta. Musu,taurin kai,tsiwa,rashin kunya da rashin tsoro

“Saketa bibi,ta canza kayanta ta fito taci abinci,kuma wallahi kika wuce minti goma sai na zane miki jikinki,dukan da ban taba kwata yi miki shi ba” ya fada yana juyawa yana fita a dakin.

Da jiqaqqun idanunta ta bishi da harara tana jin kamar zata hadiye da zuciyarta

“Wai shi me nayi masa?,daga dawowarsa yabi ya takura mutane?,kuma ai da ba haka yake ba,salon muguntar da aikin sojin suka fara koya masa kenan?” Dafe goshinta bibi tayi,gaba daya sultana din ciwon kai takeson bata

“Ke bakiga kin canza ba,kin zama mara kunya,ana gaya miki kina musu?,idan akace ki bari ba zaki bari ba,to na godewa Allah da dawowar tasa,shi kadai ne maganinki ai” wani baqinciki ya mamayi zuciyar sultanan,kamar ita za’a ce wai wani zaiyi maganinta?.

“Ki gaya masa ya fita a hanya ta to,ai zama yaya da qanwar ba dole bane,kuma bai isa yayi maganina ba Allah,saidai muyi maganin juna” ta fadi tana soma zare kayan jikinta. Zata shirya taje din bawai don tana tsoronsa ba,saidai don kawai bata qaunar duka,bata qaunar abinda zai taba lafiyarta sam,daga lokacin daka saka hannu a jikinta to ta daura da kai kenan,ba ita babu komai,saidai kuma ka shiga uku a gurinta.

Bibi tana tsaye har ta gama shiryawa abinta,riga da wando ta sanya,skinny jeans mara nauyi,sai shirt dinsa me gajeran hannu,sako sako lallausar sumarta da tsahonta ke sanyawa saidai ta lanqwasa ta sau biyu tayi,don ribbon din dake kantan saboda bala’in da takeji bata ko tsaya gyarashi ba.

Light blue ne kayan,sun yi masifar yi mata kyau,sun haska jar fatarta qwarai,idan ka kalleta zaka dauka ta fito ne daga yankin india ko qasashen larabawa. Tun asali kyan sultana na dabanne,wanda akayi ittifaqin ita daya ce tal ta dauko ainihin kamannin LAILA babar kakanninsu. Har yanzu daidaikun tsofaffi da manyan dake cikin unguwarsu dake tushen jaharsu ta AGADEZ basu manta da LAILA ba,tarihinta bai goge ba,macen data zuba kyau daya banbanta da kyawun kowacce ‘ya mace da tayi rayuwa ƙarni guda da ita.

A saman kujerun dining din suke zaune,biyu cikin masu aikin gidan na kaikawon shirya abincin daren a samansa. Ysatsunsa cikin na juna,idanunsa zube fes akan fuskar bibin. Cikin nutsuwar da tun yana mitsitsinsa ta zame masa dabi’a kuma halayyarsa yake magana

“Amma why bibi?,me yasa za’a bari halaye da dabi’unta su canza?,ya akayi sultana ta canza?,ba haka na tafi na bar muku ita ba” ya fada har tsakiyar ransa yana jin radadin rushewar tubalin ginin tarbiyyar da ya fara yi mata,wadda tasha banban data qasarsu.

“Duk wani iya bakin qoqari inayinsa mainassara,to amma kasan komai yana da alaqa da muhalli da kuma abokan mu’amala na yau da gobe” kansa ya girgiza yana furzar da iska me zafi daga bakinsa

“Bibi,goumar ya fara fadamin,mais(but) na dauka kawai surutu ne irin nashi,certainement(definitely)banji dadin abinda idanuna suka tarar ba”. Ajiyar zuciya bibi ta saki,itadai ta sani,babu ta inda tayi sake ko saakcin tarbiyyar,tun daga kan uwayensu ma ballantana su,kwadayi da son samun cikakkiyar tarbiyya ya sanya ta yiwa hamidou magana,suka tattara suka bar niamey izuwa maradi,maradinbda take kallo da hangen sunfi kusa,alaqa ta qut da qut da nigeria. A nutse take masa bayanin iya abinda zai iya fahimta. Kansa a duqe yana latsa wayarsa tare da sarrafa maganganun bibi cikin kansa,yana kuma son lanqwashe bakin matsalar da kuma yadda zai bullo mata. Nunfashi ya zuqa yana daga qawatattun idanunsa wadanda suke da wani irin shape,idanun da sultana din ta sakawa suna da yeux de lion(lion eyes) ya zubesu kan tafkekiyar TV plasma din dake maqale a bango,suna haska labaran dare a channel din niger 24tv. K’aramar yarinya ce da bayanta ya mamaye fuskan tv din,tana bayanin yadda wani matashi yayi mata fyade(rape). Kasuwa hankalinsa yayi gida biyu,fiye da rabin hankalinsa yana kan labaran,yayin da wani kaso dan kadan kunnuwansa ke ga bibi.

A hankali wani abu ya soma tsaya masa a rai,bacin rai ya fara sauka a hankali saman zuciyarsa yana mamayeta. Maqurar bacin ran da hatta bibi dake zaune a wajen sai data fahimci hakan.

Wani dogon tsaki mai matuqar sauti ya fidda,dai dai sanda tani shugabar masu kula da sassan bibi ta kawo tray na qarshe ta ajjiye

“Miqo min télécommande(remote)” cikin girmamawa ta rusuna ta juya ta isa ma’ajiyarsa ta dauko ta miqa masa.

Channel ya canza gaba daya,zuciyarsa na wani irin quna da zafi,babu abinda yafi tsana a duniya a yanzu irin kalmar FYAƊE. A duk lokacin da aka haska wani mutum dauke da laifin fyaɗe,yakanji inama za’a bashi damar hukuntashi,tabbas idan har ace zaya samu irin wannan damar,zaiyi masa hukunci ne mafi tsanani,wanda ko mace akace masa gata zai yanka da gudu ne ya gusa daga wajen,sakamakon azabar da shi daya yasan yadda take da zai ɗanɗana a hannunsa. Harshensa har ɗaci yakeyi sanda ya buɗe baki yana magana da bibi

“majorité ire iren wadan nan abubuwan akwai sakacinmu dake haifar dasu”

“ƙwarai kuwa,wasu abubuwan kuma ƙaddarar bawa ce daga sarkin mabuwayi” gama maganar bibi yayi dai dai da fitowar sultana. Da ido bibi ta bita tana kallon yadda fuskarta tayi jazur,sai kawai ta miqe a hankali tana sauka daga gurin dining din,abinda ya sanya sultana tsaiwa cak tana kallon bibi din,don ita ba zata yarda ta barsu a wajen daga ita saishi ba,ya sake taba lafiyarta ba gaira ba dalili

“Ina kuma zaki tafi bibi?” Ta tambayeta tana karya wuya,hawaye nason taruwa cikin idanunta

“Qaraso ki zauna” maina da idanunsa yake kanta ya fadi,fuskarsa a matuqar hade,abinda zai alamta maka babu wasa ko misqala zarratin a tattare da shi. Duban cikin idanunsa tayi,niyyarta tace ba zata zauna din ba,to amma kuma sai kalmar ta maqale mata saman harshenta. Kamar ba zata qaraso din ba,amma yadda kaifaffun idanunsa suka ritsata ya sanya ta sauya akalarta zuwa inda yake mata umarnin,zuciyarta kamar zata fashe,duk wani qaunar da take masa taji ta fara raguwa sosai cikin ranta,sai wani haushinsa da takeji. Tana matuqar qaunar lafiyarta,hakanan bata qaunar duk abinda zai taba mata lafiyar. Karo na uku kenan ana sauya mata makaranta saboda attempting din dukanta da aka taba yi sau daya a kowacce makaranta.

Tsaki yaja dai dai sanda ta zauna saman kujerar,ta dafe hannunta tana saman kujerar tana gyara zamanta sosai saboda qafafunta ba zasu kai qasa ba,duk da tana cikin sahun yara masu tsaho. Tsakinsa ya sake qular da ita tare da bata haushi sosai,sai ta juyar da kanta gefe tana murguda bakinta tare da sakin qananun surutai qasa qasa.

“Duba nan” ya fada yana tattara dubansa a kanta. Tilas tabar kallon hagunta ta dawo da kallonta zuwa gareshi

“Wannan kayan…….ban hanaku sakasu ba?,kun dauka a french muke?” Ya tambayeta a kausashe,har cikin ransa yana jin haushi da takaici. Zuwa lokacin alamomin girma sun fara bayyana a jikinta,tana da girman jiki wanda yake da saurin bayyanar da girman d’iya mace,hakan kuma yasan yana da alaqa da rayuwar jin dadi da tsantsar kula da jikinta ke samu na dukkan wani abu da zai inganta lafiyar jiki data fata ya kuma tabbatar da girma na dan adam a lokaci qanqani. Ya sani kusan da madara aka raineta,har ya tafi akan shan madara ya barta,duk da bashi da tabbacin har yanzu tana sha?,yana ji a jikinsa ma lokaci yayi da zata ajjiye duk wasu dabi’u na quruciya,ta fuskanci girma wanda yake dab da iso mata.

“Last zuwan ama Nigeria na qarshe ta kawowa kowaccenku wadatattun atamfofi da zata dinka,sannan dukkaninku kuna da abaya wadatacciya,wannan shine gargadi na farko kuma na qarshe,kada na sake ganinki da irin wadan nan kayan a jikinki” ya fada yana kallon idanuwanta.

ZAFAFA BIYAR FAMILY🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba

ZAFAFA BIYAR❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥

❤‍🔥 SABUWAR SHEKARA

❤‍🔥 SABON TSARI

❤‍🔥 SABBIN LABARAI

❤‍🔥 TSUMAMMIYAR SOYAYYA

❤‍🔥 CAKWAKIYA

❤‍🔥 LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO

❤‍🔥 SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA

❤‍🔥 LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_

KWANTAR DA ZUCIYA

CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA

QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA

KWANKWASON JIMINA ME WUYAR TABAWA (miss xoxo)

TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE (Billynabdul)

AMEENATU (Mamuhghee)

GUDUN K’ADDARA GUZURIN TARAS DA ITA (Huguma)

KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI.

THANKS FOR CHOOSING US🫂🫂🫂🫂

Join our WhatsApp group here

Haushi kamar zai kasheta,wai shikam yaa maina yana kallonta ne har yanzu a little sultana da ya bari shekara hudu baya?,itafa ba zata dauki ire iren wadan nan abubuwan ba bayan tana kallon yadda sauran qawayenta na makaranta ke rayuwarsu cikin ‘yanci. Kaf cikinsu ma bataga me saka wata aba wai atamfa ba,meye hadinsu ma da ita?,sai ita zai bullowa da sabon tsarin doka?.

“Ni ban iya daura zane ba” ta amsa masa tana turo baki manyan fararen idanunta na kallon shinfidadden gilashin dining din,ji takeyi kaman ta mangareshi,har yanzu tana jin radadin marinsa akan fuskarta.

‘Dan dukan table din yayi da tafin hannunsa

“regarder(look),ki iya ko baki iya ba duka zaki koya ne,muddin kinaso kiga ainihin mainassara kici gaba da yimin musu da kuma dan banzan kafiya da taurin kan da kika koyo”

“Kai kuma shegiyar masifa da bala’i da baqinciki da bacin rai kamar tsohon kuturu” ta fada cikin ranta. Baiji abinda tace ba,amma yaga sanda jajayen lips dinta suke motsawa

“Me kika ce?” Ya jefa mata tambayar data kusa sakata fadowa daga kan kujerar da take zaune akai din. Da sauri ta daga fararen idanunta ta kalleshi dasu tana motsa baki

‘”ni?,ni bance komai ba” idanunsa ya lumshe kadan ya budesu. Ya tabbatar tayi magana,akwai abinda tace,amma cikin sabon halin da ya fuskanci ta sake kota koya harda iya fadin qarya kanta tsaye. Bayajin zaiyi wuya ya sake tafiya niamy haka ya zauna,gwara duk sati ya dinga tahowa maradi yana hutun qarshen makonsa a nan.

“Dauki abinci kici” ya fada yana nuna mata tsadaddun warmers din dake jere saman dining din

“Mari!,mari!!” Ta fara qwala kiran sunan kamar zata saki kuka. Da kallo ya bita yadda ta narke kamar me ciwo tana kiran sunan mai aiki,tana nufin ita zata zuba mata kenan,zubawar ma bata iyawa?.

“Ya isa haka karki kashemin dodon kunne” ya fada yana wurga mata wata iriyar harara wadda bata taba ganin ya mata irinta ba. Da kallo ta bishi ranta yana baci,sai taji idanunta na marmarin juyewa itama ta mayar masa da hararar da yayi mata din,to amma yana kallonta ta dauke kanta gefe,zuciyarta tana sakeyin zafi,haushinsa na sake cikata

“Nidai wallah ba zai takuramin ba,mutum ba ubanka ba ba komi ba” ta fada qasan ranta.

Plate din ya tura mata maimakon ya jawoshi gabansa ya dinga bata a baki har sai tace ta qoshi kamar yadda ya sabar mata a shekarun baya. Cikin ransa da zuciyarsa yakejin dole ya janye ya kuma rage dukkan wata kulawa da damuwa da yake nuna mata,domin ya fahimci aiki ne jajur a gabansa wajen maido sultana din kan hanya. Don girma ta fara girma,jikinta ma ya nuna hakan,a wannan gabar idan bai tsaya mata sa zafi zafinsa ba a haka zataci gaba da girma a sangarce,bayan kuma gidan wani za’a kaita,ya yiwa nafissa adalci idan hakan ta faru?.

“Oya bismillah” ya fada yana sake turbune fuska,idanunsa akan wayarsa dake ringing. Zai daga ta katse,sai kuma sautin sallama daga can bakin qofa.

Matashin saurayine wanda shekarunsa ba zasu haura sha biyar ba,dogo ne fari,kansa dauke da nannadaddiyar sumar nan ta abzinawa. A fusge yake kama da maina,saidai kuma idan ka kalleshi da kyau zaka fahimci akwai banbacin kamannin.

“Ya maina,ama tana kira” ya fada idanunsa akan fuskar sultana wadda ke kallon abincin gabanta kamar taga wani abun tsoro,fuskar nan a dagule da bacin rai

“D’accord,allons-y(alright, let’s go)” miqewa yayi yana gyara shirt dinsa data tattare yana kuma sauke hannun rigarsa da yayi rolling up zuwa gwiwar hannunsa

“Kada na dawo na samu komai a ciki” ya qarashe maganar yana sauke mata kallonsa sai kuma ya dauke kai yana sauka daga dining area din ya nufi qofa.

Da idanu yaron ya bishi,kamar shima jiran fitarsa yakeyi ya dawo da dubansa kan sultana,ya saki dariya yana tattakowa da hanzari zuwa wajenta. Kafin ya iso ta miqe tsaye ma tana shirin barin wajen ba tare da ta sakawa abincin koda yatsarta ba

“Albishirinki,examens lundi(exams monday)” ya fadi yana dariya saboda sanayyar da yayi mata da tsantsar gabar da takewa makaranta.

Harara ta watsa masa kamar zata fiddo fararen idanunta waje

“Kada ka sakemin maganar examens,bazanyi ba,bazanje école(school)din ba munafuki” ta qarasa fada tana murguda masa baki. Dariya ya sheqe da ita sosai,SADDI mutumin sultana ne qwarai,saidai kuma zaman nasu ayi fada ayi dadi. Yasan duk abinda takeso shi yasa suke shiri,hakanan yana da tarin tsokana da calikanci wanda shike hadasu fada da sultana,saboda ita ba kasafai takeson tsokana ba,saidai akwai dan banzan surutu kamar yadda saddi yake da shi,shi yasa tasu tazo daya da ita sosai.

Waqe ya fara yi mata na gobe ranar makaranta ce cikin harshen farasanci,bata waiwayo ta dubeshi ba bare ta kulashi,saboda bacin ran maina kawai yau ya isheta takaici.

Dakinta ta shige ta kulle abinta tayi kwanciyarta,ko madararta data zame mata qa’idar sha duk dare bata nema ba a yau,don batason ma yazo ya isketa ya sake shiga rayuwarta ya bata ranta.

Tana jin tanja me kula da ita ta musamman da aka ware mata na buga qofa tayi banza da ita. A qalla ta kusa minti talatin tana bugu akan ta bude mata zata shigo ta shirya mata uniform da sauran tarkacen kayan tafiyarta makaranta kamar yadda ta saba duk ranar Sunday war haka amma tayi kunnen uwar shegu da ita har ta gaji tace

“Idan ma bakison zuwa makarantar ne to ki tashi ga láit(madara)dinki,ki kuma yi wanka ki canza kayan kwanciya” hararar qofar tayi ta sake juyawa abinta tana riqe game dinta da kyau tare da sake shiga next level na game din.

Game ce da tayi mugun shiga rayuwarta,muddin kanason ganin nutsuwarta da walwalarta to idan tana yin game dinne,tana bata lokaci da nutsuwarta irin wadda karatunta bai samu koda rabin rabinta ba. Ganin da gaske ba zata bude ko ta magantu ba ya sanya tanja ta haqura. A hanya sukaci karo da bibi

“Ta kwamta ne mutunniyar?” Bibi dake fitowa a kitchen ita da ammara ta fadi tana duban tanja

“Wallahi bibi ta qiya ta bude koda qofar ma,ni zato ma nakeyi fa tayi bacci,da maina zan kira ko zata bude idan ta jishi”

“A’ah,barshi tanja,dama yau sun hau sama sun fado da ita” ido tanja ta zaro,ba ita bama hatta da ammara sai data zare idon itama,kowanne mamaki yana ratsashi.

“Dama akwai ranar da yaa maina zai sab’a da sultana?” Ammara ta riga tanja tambayar bibi. Kai bibi ta kada tana yin gaba,ita kanta ta jinjina al’amarin,koda fada bata zaci maina zai iya daukewa a yiwa sultana a gabansa ba,sai gashi har shine da sanya yatsunsa guda biyar saman fuskarta,abinda ba’a taba yiwa sultana din ba.

Yadda bibi tayi gaba bata amsa musu ba yasa suka kalli juna

“Tabdijan” ammara ta fada,sai ta soma takawa tabi bayan bibi riqe da plate din appale din da aka wanke aka dora siririyar wuqa a kai. Dole tanja taja qafafunta cikin tsananin mamaki itama tana bullewa zuwa babban boys quaters din da ya kasance muhallin ‘yan aikin gidan.

ZAFAFA BIYAR FAMILY🫂🫂🫂🫂🫂

🔥 me kike jira ne da har yanzu baki shige ahalin zafafa ba

ZAFAFA BIYAR❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥❤‍🔥🔥

❤‍🔥 SABUWAR SHEKARA

❤‍🔥 SABON TSARI

❤‍🔥 SABBIN LABARAI

❤‍🔥 TSUMAMMIYAR SOYAYYA

❤‍🔥 CAKWAKIYA

❤‍🔥 LABARAI NE MASU RATSA ZUKATA DAKE TAFE DA WANI IRIN SALO

❤‍🔥 SALON DAKE DAUKE DA ZALLAR GOGEWA DA QWAREWA WAJEN SARRAFA ALQALUMA

❤‍🔥 LABARANSU NA MUSAMMAN NE DAKE DAUKE DA WANI IRIN SALO ME RATSA JIKI_

KWANTAR DA ZUCIYA

CIRE DAMUWA DA SABUNTA SOYAYYAR MASOYA

QAWATATTU KUMA TSARARRUN LABARAN 2024 DIN SUNE KAMAR HAKA

KWANKWASON JIMINA ME WUYAR TABAWA (miss xoxo)

TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE (Billynabdul)

AMEENATU (Mamuhghee)

GUDUN K’ADDARA GUZURIN TARAS DA ITA (Huguma)

KOWANNE LABARI NA DAUKE DA SUNA ME HARSHEN DAMO,KAMAR YADDA GUNDARIN LABARIN KE DAUKE DA SALON DA ALQALUMAN ZAFAFA BIYAR NE KADAI ZAI WARWARE MUKU SHI.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

GUDUN ƘADDARA🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️

H U G U M A

PAGE 05

MONDAY

Cikin katafariyar harabar qawataccen gidan fara sol din school bus din yaran gidance me tsaho,wadda ke dauke da rukunin mazaunai a cikinta har kashi hudu banda mazaunin driver. Lausasan gurin zama shimfidar lallausan carfet daga qasan motar gami da wasu qananun curtains a kowanne window dake cikin motar,wanda shine zai bayyana maka ainihin nauyin kudaden da aka narka domin mallakar motar da kuma sadaukar da ita domin jigilar karatun yaran gidan.

Daga waje kuma a rubuce baro baro hannun hahu da dama na motar rubutu ne da manyan baqi kamar haka MAYAK’i BUS SCOLOIRE.

Daya daga cikin dabi’unsu a kowacce safiya,hayaniya ce zaka sameta fal cikin motar,fadace fadace da juna da kuma sauran rigingimu da baa raba yara da shi,har zuwa sanda za’a sauke kowannensu. Amma a yau din akasin wanann dabi’ar itace ta maye gurbin waccan. Shuru motar take,kowa ya kama mazauninsa cikin nutsuwa da kamala,wasu daga cikinsu ma litattafansu ne a hannunsu suka sake dubawa saboda exams da zasu fara a yau din. Duk kuwa da cewa kowa bakinsa cike yake da magana da kuma qorafi amma ba wanda ya iya tankawa saboda gudun daga murya.

Dukka hakan yana da nasaba da wanzuwar Aliyyu maina a wajen. Qasan daya daga cikin bishiyun da suka zamewa harabar gidan ado. Saman wata kujera ta itacen bamboo da aka qawatata da cushion masu laushi don samun dadin zama.

Sanye yake da wasu baqaqen pyjamas da suka fidda samartaka da kuma tashen quruciyar dake tattare dashi. Sassanyan kyawun da quruciya da kuma tashen girma ke sake haskashi. Hannunsa riqe yake da wani qaramin littafi da ba lallai ka iya tantance na meye ba yana dubawa. Kusan wannan din dabi’arsa ce a duk sanda ya dawo daga motsa jikinsa daya zamar masa al’ada kowacce safiyar duniya. Sadai a yau din da biyu yayi zaman nasa,ya karbi key na school bus dinne zaya kaisu makarantar da kansa,yanaso a qalla ya zaga gari ya samu kyakkyawar iskar da safiyar litinin din ke fesarwa.

Kaman yadda tarin abokai basa cikin tsari da dabi’arsa,hakanan yawa ba dabi’a tasa bace,wannan ya sanya lokaci lokaci yakanyi sha’awar zagaye garin na maradi bisa rad’in kansa.

Najma ce mutum ta farko data fara sauke qaramin curtains din jikin motar tana sauke ajiyar zuciya

“Gaskiya muna gab da makara fa,babu wanda zai gayawa yaa maina zamu makara ne?,kuma sultana ma bata fito ba?”

“Waye yake da jarumtar tararsa ya gaya masan?,ko ke zaki iya wannan shahadar?” Aminata dake seat din gaba ta gada tana waiwayowa hadi da jifan ammara da tambayar.

“Ke ba zakije ba sai ni?,na rasa kuma qarar waye zankai sai ta sultana?,qarar sultana a wajen yaa maina saboda ganganci?” Najma ta furta tana nuna kanta,akwai alamun girmamawa maganar daga harshenta zuwa baki.

“Kuna tunanin yaa maina da sultanan da ne?,kunsan jiya jiya naji bibi na masifan yaa maina din ya mari sultanan?” .

Waiwayo sukayi kowa ya zuba mata ido,wasuu baki bude suna kallon yasmine,maganar na shiha kunnuwansu tamkar labarin qanzon kurege.

“Ah lallai na yarda,bibi ta fara rikicin tsufa,ya maina dinne zai mari sultana,sultana fa?,bibi anzo gangara…….” Maganar kaltoum kenan ta fada cikin jinjina maganar,abinda ya sanyasu sakin dariya gaba daya,dariyar kuma data dauke dif lokaci guda sanda aminata dake a gaba gaba tayi musu alama na tahowar maina,sai dukkansu suka shiga nutsuwarsu.

“as tu fini?(kun gama?’ ya jefa musu tambayar cikin tataccen faransancin nan dake saman harshensa,wanda yayi mugun gwanancewa kai kace yaren uwa da uba ne yake yarawa

“Sultana ce kawai……” Yasmine tayi namijin qoqari hadi da qarfin halin furtawa. Saidai ita dinma kasa qarasawa tayi sanda ya watso mata idanunsa.

Duk da ta kasa qarasawar amma tuni ya hasaso me takeson fada. Sakin murfin motar yayi yaja baya a hankali

“vous êtes très stupide,saboda baku kishin kanku ba kuma damu da karatun ba shi yasa kuka kasa sanarmin” Ba wanda ya iya tanka masa a cikinsu,shi dinma ba jiran amsarsu yakeyi ba,sai kawai ya zube hannuwansa ga aljihun wandonsa ya fara takawa zuwa cikin gidan a nutse.

Bisa hanya yake sarrafa abun cikin ransa. Daga zuwansa kawo yau ya fahimci ita daya ce tal take makarar dasu a makaranta,kullum case din nata ne,da gasken da akace masa bata qaunar karatu ko qanqani haka ne?.

Karo na kusan shida tanja ta sake shigowa dakin,takai dubanta ga lunch bag da sauran tarkacen kayan makarantar sultana din dake ajjiye yana jiranta.

Kai ta girgiza tana sakin qofar gami da qarasa shigowa dakin. Wata baiwa zata iya cewa ko meye zata kira hakan?,har yau bata tabajin da haushin sultana ba,kokuma taji ta qosa da halayyarta ba ko guda daya.

“Sultana” ta kirayeta cikin lallabawa. Shuru babu amsa kamar yadda ta zata,duk da tayi imanin idanunta biyu,saboda tana hango hasken mayatacciyar game dinta data jinginar a jikin NINI dinta tana yi. Sake kiran sunan nata tayi a karo na biyu,wannan lokacin bata damu data amsa ba tace

“Kin sandai lundi(monday)yau,sannan kuma examine zaku fara,yanzu haka nasan kowa yana can ke yake jira” sosai ta tura baki gaba tana ji har cikin ranta tanja ta dameta ainun ta kuma uzzura mata,saidai bata tankawa tanja din ba sai shura qafafunta da tayi taci gaba da game dinta

“Sultana”

“Don Allah tanja ki barni,na riga na gayawa bibi bani da lafiya,kuma nasan zata gayawa kowa haka,bazanyi wani examine ba ni”

“Ai shikenan” tanja ta fadi tana miqewa. Iyakar qoqarinta itama din tayi,tana jin sultana kamar jininta dukka silar nafessa,ba zata tabawa mantawa da nafessa ba kamar yadda batajin zata gajiya da sultana da kuma dabi’unta.

Tana jan qofar taku biyar kacal maina ya sanyo kai. Tadan rabe gefe suna gaisawa. Ba ma’abocin son gaishe gaishe bane, gaisuwa daya tak ya tambayeta

“Ina sultana?”

“Tana ciki,amma bata da lafiya” bai qarasa jin statement dinta ba ya zare idanunsa daga kanta ya doshi qofar dakin,saboda a cikin jikinsa yakejin bai gamsu da rashin lafiyarta ba.

Cikin zumudi ta qara speed na game din nata,saboda tana stage na qarshe a game din data dauki dogon lokaci batakai wannan stage din ba,mintuna qalilan ya rage mata takai gidan qarshe.

Tayi mugun nisan da bataji shigowarsa ba,ba kuma lallai da idanu ta ganshi ba,saboda ta nutse sosai cikin comforter tana buga game dinta hankali kwance.

Gyara tsaiwarsa yayi sosai yana kallon yanayin kwanciyarta cikin comforter din. Yana da wani irin kaifin ji da kuma kaifin gani,saboda haka yana iya hangen haske ta cikin comforter din. Mamaki yaso saukar masa,me yakai haske cikin abun rufarta?, tambayar da ta sanyashi miqa hannu yana yaye comforter din,dai dai sanda motsin bargon yayi silar faduwarta a game din,cikin sakannin duka ta hasala ta bude bakinta cikin tsaiwa zata sauke kwandon bala’i dukka a tunaninta tanja ce

“Wai nikam ana dole tanja?,nace bani zuwa meye ne naki a ciki idanb……..” Gaba daya maganar tayi wani irin juyi ta tsaya mata a maqoshi. Dukka idanunta biyun dake wani irin haske da sheki cikin taqaitaccen hasken dakin ta zuba masa su cikin matuqar tsoro da razanar yadda ya risketa.

Sauke idanunshi yayi ga gadon,ba komai saman bedsheet din sai tarin ledojin madararta bila adadin. Biscuit da chocolate masu dan banzan zaqi da suka raineta da su kuma har yanzu suke ci gaba da bin jini da kuma rayuwarta.

Zare idanunsa yayi daga ‘yar kallo kallon da sukewa juna tsakanin idanunta zuwa shinfidarta wani bacin rai yana lasar zuciyarsa ya maida kan tanja dake shigowa dakin kanta a qasa,tana jin nata laifin na idar da abinda ba haka bane zabi ne na sultana din kawai

“Na bata minti biyar kacal ta fito,ki bata lunch bag dinta ta fito da ita kamar kowanne yaro” ya qarasa fadin maganar yana fita a dakin ba tare daya waiwayo ta ba.

Wani uban tsalle ta daka tana direwa tsakiyar gadon nata

“Ke kika kiramin shi,kuma Allah ko meye zaiyi bazanje ba,ni ba tsoronsa nakeyi ba” abinda sultana din ta sake fadi kenan tana juyawa zata koma gadon. Tarota tanja tayi,cikin lallashi hilata ta samu ta shawo kanta da qyar ta watsa ruwa tunda already tun asuba take nata wankan,ta fara shiryawa tanayi tana mita,baki abun magana,abinka da mutum me baki kwata kwata taqi yin shuru.

“Sultana,kinfini sanin halin kawunki,idan yayi magana baya canzata,kibar ganin yana sonki yana nuna miki fifiko cikin yaransa,to amam kada ki manta ainihin halayyarsa tana nan fa,bashi da sauqi muddin akan harkar karatu ne” ita kanta ta dade da haddace wannan saidai ta yiwa wani tuni. Amma a yau din maganar ta zama kamar tunasarwa ce a gareta,tilas ta gama shirin ta kuma dauki lunch bag din da tsabar gata kullum kwanan duniya sai an rakata da ita,amma yau yaa maina din yace baison ganin wannan. Gaba daya a taqaice maina din yana son zame mata wata barazana kenan?. Ta yiwa kanta tambayar dai dai sanda ta isa gaban motar.

Yadda kowa ya tsirata da idanu ya sake hassalata,wannan ya sanya tana sane tabi takan qafafunsu ta kuma tsallake kowa sannan ta zabi seat din da yayi mata. Kowa a cikinsu yanason yayi qorafi amma hakanan yaja bakinsa ya kulle saboda maina din,wanda ya tashi motar ya kuma figeta da gudun nan nasa dake sawa mutum nutsuwa koda bai shirya hakan ba.

Yar uwa kinsan illar dake tareda infection kuwa?,*to bari kiji kadan daga cikin illar da infection yake da ita,kinsan cewa infection

yana hana haihuwa

yana hana ma’aurata jindadin mu’amala

yanasa warin gaba kowane irin tirare kika sa bazai hana wannan warin fita daga jikin kiba

fitar farun ruwa

kaikayin gaba

tusar gaba duk suna daga cikin illar da infection yakewa lfyr ki

Ina masu fama da ulcer,Asthma,sickle,ina matar dake fama da fibriod,matsalar rashin haihuwa ko bushewar jiki da fata shin kiba kareki kikeso ki koma yar chas chas ko tumbi ne ya hanaki gayu ku garzayo kuma ku kwada ku gani da ikon Allah da izinin Allah,munada blood circulature machine vip chais kedai kira number nan domin karin bayani ku tuntubeni kai tsaye ta nan

Masu tambaya muna maraba daku

Mun gode.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 06

Sai da ya ajjiye kowa,ita kadai tayi saura cikin motar amma yana ankare da ita sam babu damuwa a tattare da ita bare gudun kufcewar lokaci ya dameta. A nutse cikin sassanyan muryarta ma take bin waqar dake fita ta radion motar wadda suka sako bayan kammala labaran safiya daga radio alheri.

A hankali ya sanya hannunsa ya kashe radio din gaba daga. Sai tayi d’if tamkar me nazarin wani abu,kafin daga bisani ta tabe baki ta kuma maida dubanta kan titunan da suke wucewa wanda ke da qarancin zirga zirgar jama’a ainun.

Da kallo ya bita sanda ya sauketa,har zuwa sanda ta shige sashen gine ginen ajujuwansu. Janye idon nasa yayi,kana ya sanya hannu ya zare belt din jikinsa sannan ya kashe motar ya kuma bude murfin ya fito.

Hakanan kawai yaji yana da buqatar bincikar motsinta da duk wani performance nata na makaranta.

Kyakkyawar tarba ya samu daga office din principal din saboda sunsan waye shi daga kuma wanne gida ya fito. Cikin ban girma principal din ya gabatar masa da document na sultana kamar yadda suke da tsarin ajjiye document na kowanne dalibi tare da rubuta abubuwa da suka shafi rayuwarsa cikin makarantar,sannan ya dauki wasu takardu ya fice don ya bashi damar dubawa a nutse.

Tun kafin ya kammala dubawa ransa yayi qololuwar baci,ya sauke document din daga fuskarsa yana ajjiyeshi saman table din. Tsai yayi a wajen tamkar bazai tafi ba sai kuma ya soma takawa yana fita a office din ba tare da ya jira ko ya nemi kowa ba.

A gaggauce yake tuqin saboda zuciyarsa da ta motsa. Baiga komai na kirki cikin karatu da shaidar da sultana ke samu a takardunta ba,komai nata poor,babu wani abu da yake EXCELLENT idan ka dauke tsaftar uniform dinta.

Sanda ya isa gidan kai tsaye sassan bibi ya wuce. Baiko kula da gaisuwar hadiman bibi din ba ya zarce dakin sultanan.

A hankali ya murda qofar dakin ya kuma turata. Duk da haske bai wadaci dakin ba amma yana iya kintacen yadda aka gyare dakin tsaf kamar ba shine dakin dake hargitse dazu dazun ba. Hannu ya sanya ya kunna fitilun dakin,haske ya gauraye ko ina.

Wannan dakin na sultana wanda shi da ita suka rayu tsahon shekaru tara a ciki yana kula da ita,yana rainonta,yana mata ginin da yake da tabbacin zata zama cikakkiyar mutum kamar kowa,cikakkiyar mutum data banbanta kuma da kowa din,amma a yanzun yana ganin take take na idan baiyi da gaske ba tabbas mafarkinsa zai gushe ne ba tare da ya maidashi cikin zahirinsa ba,burin nafessa kuma zai shafe kamar yadda a yau ya shafe daga doron qasa.

A nutse kuma a hankalce yake qarewa dakin kallo. Cike yake da teddies tako ina tamkar don su take rayuwa. Baby doll kala kala. Daga can wani table din kuma tarin games ne iri iri,tab da spare din wayar hannu.

Qarasawa yayi qaramar drawer dinta ya sanya hannu ya bude. Tarin biscuit da chocolate kamar wani qaramin store. Ya matsa yana buda fridge dinta qarami dake dakin. Madara ce kamar ko yaushe danqare a fridge din tun daga sama har qasa. Tamkar wata ruwan sha,tamkar ba madara bace me tarin daraja da tsada wadda sai anyi takakkiya tun daga niamy an kawota ba.

Rufeshi yayi,ya qarasa ma’adanar litattafanta ya fara saukesu a qasa. Zaman dirshan yayi saman lallausan carfet din dakin yana bitarsu daya bayan daya

“Ya salam…….ya ilahee” shine abinda bakinsa dake motsawa kadan kadan yake furtawa.

Kusan za’a iya cewa ba komai a cikin litattafan nata me bare a iya ganin me ta shuka,tabbacin bata note bata assignment bata kuma homework ko class work. Shafukan da ya dace da samun rubutu kuwa ba wani rubutun arziqi bane a ciki. Komawa yayi kan litattafanta na islamiyya. Nan ma dai duka sammakal,sai ya tattara litattafan ya jayesu gefe yana dafe da goshinsa zuciyarsa na wani irin bugawa cikin zallar bacin rai. Wato tana rayuwa ne a duk yadda taso kenan?,babu wani me monitoring dinta?.

Kamar Bibi tasan tambayar da yake yiwa kansa kenan ta murda handle din qofar ta shigo. Idanu ya bita da shi kamar yadda itama.ta bisa da nata idanun

“Tanja tacemin kana ciki tun dazun” kansa ya gyada mata a sanyaye yana lumshe kyawawan idanunsa da suka dan sauya launi kadan. Daya daga cikin alamun dake nuna yana cikin bacin rai kenan

“Bibi….” Ya kirayeta yana tusa kalaman da zaya gaya mata kada zafin dake ransa yasa yayi maganar da bai dace ba,don ba kasafai ya fiya control din kansa akan dukka issue din da ya shafi sultana ba

“Lafiyarka Aliyyu?” Bibi ta tambayeshi tana kiransa da ainihin sunansa

“Anya zamu iya sauke amanar sultana dake wuyanmu?” Yayi mata gajeriyar tambayar me dauke da tarin abubuwa masu yawa.

Da idanu ta tsirashi tanason warware maganar tasa

“Kamar yaya maina?” Ta tambayeshi tana sauqaqewa kanta dogon nazarin da kwanyarta ta tafi yi

“Komai na sultana ba daidai yake tafiya ba bibi,komai ciki harda karatunta” ya fada yana miqa mata daya daga cikin litattafanta da yafi bata mata rai. Ta zauna shafi bayan shafi ta rubuceshi da waqar wani shahararren mawaqi a nan nijer dake waqar hip-hop da harshen faransanci.

Bin littafin tayi da kallo don ba karatun boko tayi ba,saidai tana da ilimin muhammadiyya sosai

“Tabbas sultana batason makaranta bata kuma qaunar karatu nasan wannan,amma ina dukka bakin qoqarina wajen ganin tayi karatun tunda nasan wannan shine burinku daga kai har nafessa” shuru yayi na wasu daqiqu,iya qoqarin tarbiyya da saita yara gidansu ya samu wannan shaidar,amma jarrabawar iyayensu yana kyautata zaton akan sultana take.

Bai sake cewa komai ba ya miqe ya fara tattara dukka wasu teddies da games nata dake dakin. Sai daya rabata da dukkan wasu kayan wasa ya kammalesu guri guda sannan ya fita a dakin.

Nannauyar ajiyar zuciya bibi ta sauke zuciyarta tana karyewa. Batasan me yasa duk sanda ta yunqura da nufin yiwa sultana hukunci me tsauri take kasawa ba,tana jin yarinyar har tsakiyar zuciyarta da wani irin zallar tausayi da soyayyar da batajin cikin jikokinta akwai wadda ya rabauta da kwatankwacinta.

Kamar yadda take mutum ta qarshe dake fitowa ta shiga motar makaranta,hakanan ita ke kasancewa mutum ta farko dake fara fita a motar duk sanda aka iso gida. Tamkar motar tana cizonta haka take bude motar a gaggauce ta fice tana waqe waqenta,bata damu da qafar waye ta taka ko ta buge ba,saboda duk wanda yayi qorafi ko wani abu makamancin haka bakinta baya mutuwa,koda kuwa ita ke da laifi ba zatayi shiru ba sai inda qarfinta ya qare. Bata da wani qarfi ko na sisin kwabo,amma dukka qarfinta da qoqarinta ya tuqe ne a zuciyarta. Tana da wani irin taurin kai da kafiya wadda da qyar ake iya tanqwarata ko juyata.

Yau dinma itace ta farko data diro daga motar,ta kuma wuce cikin gidan sassan bibin hankalinta kwance tana janye da jakarta. Tun daga falo kamar ko yaushe ta fara jefar da jakarta da qanqanin qanqanin hijab din da suke saqalawa. Cireshin kuma ya bawa lallausar sumarta da sam bata kitsuwa damar warewa.

Takalmi zuwa socks dinta ta salube suma ta wurgar,ta zare rigarta da wandon duka,ba abinda ya rage mata sai vest dinta data kawo har cinya da kuma wandonta da ya tsaya iya gwiwa.

Fridge ta bude ta dauki madararta me sanyi ta fasa ta fara sha sannan ta wuce dakinta bayan ta kalli agogo ta kuma qiyasce mintunan da suka rage da za’a dameta da batun tafiya islamiyya. Islamiyyar da ayau ta haqqaqe ko dambun namanta za’a yi yau din ba zataje ba,don haddarta ta jiya da shekaran jiya duka babu wadda tayi. Ba abinda ta tsana irin a bata haddar,a duk sanda malamin ya shigo ita kuma nata karsashin ya qare,ta gwammace ta nade cikin hijabi ta hau baccin qarya,ciwon kai ciwon ciki duka nata ne,tun malamin na tunanin hakanne da gaske har ya fahimci akwai lauje cikin nadi,duk wata hikima da hukunci ba wanda baiyi mata ba amma sam ba abinda ta sauya. Batason karatun shi ya sanya ta sakawa ranta bata ganewa wannan yasa bata ganewar.

Cak ta tsaya sanda ta tura qofar dakin nata tana bin dakin nata da kallo. Taku biyu baya tayi tana mutstsuke fararen idanunta tana sake kallon kowacce kusurwa ta dakin da kyau.

Sakin labulen tayi sannan ta bude dukka siririyar muryarta ta soma kwarara sunan

“Tanja!……tanja!……tanja!” Tamkar wadda sukayi kacibus da mutuwa.

Kusan lokaci daya suka saki dukkan abinda sukeyi din suka durfafi dakin da wani mugun sassarfa. Daga tanjan da aka kira har bibi da ba’a ambaci sunanta ba a rude suke matuqa da kiran tanja da sultana keyi babu qaqqautawa. Zuciyarsa a tsinke da tunanin mugun abu ya sameta.

Birki suka ja dukkansu suna kallonta,ta yaye zanin gadonta gaba daya ta kuma wargaza kayan closet dinta gaba daya

“Ina nini na tanja?,ina games dina?,waye ya shigo ya sacemin kayana?” Ta fada idanunta na rau rau da hawaye,zallar tashin hankali ya bayyana saman fuskarta

“Yanzu fisabilillahi saboda wannan ya sanya kika dinga qwalawa tanja kira?,dukka falukan gidan nan sai da suka amsa?” Bibi ta fada tana tsuke idonta akan fuskar sultana,tana ganin wani tashin hankali da muraran kan fuskarta,kai kace an sace mata wasu abubuwa masu matuqar muhimmanci ne ga rayuwarta. A wajentan masu matuqar muhimmanci ne,domin ninin na daya daga cikin abubuwan da tafi so cikin abubuwan data mallaka,hakanan games dinta suna a mazaunin manyan abokai cikin rayuwarta.

Duk yadda take da surutu rawar kai da tarin tarkacen qawaye hakan bai hanata qin shiga shirgin kowa tare da ware kanta haka kurum idan taso cikin dakinta. Zata iya kashe awanni ita daya,rungume da nini dinta da kuma games dinta.

Kai kawai bibi ta girgiza ta juya tana barin dakin

“Waye ya daukemin nini na?” Sultana ta fada muryarta na rawa tana shirin fara sakin kuka. Itakam bibi ma bata waiwayo ba,sai tanja dake qoqarin kintsa dakin ta amsata

“Mainasara ne sultana”

“Maina?” Ta furta cikin cika da batsewa tana jin masifa fal zuciyarta. Da gaske dai rayuwartata yakeson shigar mata,qarfi da yaji yakeson shiga abinda take ganin bai shefeshi ba tunda tuni ya zare kansa daga sahun mutanen dake qaunarta har zuciyarsu

“Wai shin me yayi ruwansa da kayana tanja?” Ta jefawa tanja tambayar cikin kaushi da zallar bacin rai

“Karatu mana sultana?,maina yana miki sha’awar karatu ne”

“To bazanyi ba,nace bazanyi ba,wani banzan maina bai isa ya takuramin ba bayan shi din ba ubana bane” ta fada cikin tafasar zuciya.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 07

Maganganun sai suka kwancewa tanja kai,koda cikin mafarki tayi mafarkin sulatan zata iya gayawa maina hakan lallai zata daukarwa ranta cewa gundumemiyar qarya ce mawai shaidan ya wassafa mata a mafarki don yayi wasa da tunaninta. Maina da sultanan da suka zama wani kyakkyawan madubi da kowanne uba zai kalla game da diyarsa?,yau itace ke furta masa hakan?.

Ko kafin tanja ta sauke tunaninta sultanan ta fice a dakin a gaggauce.

A falo taja tunga,don dama bibi take nema kuma ta ganta. Da jiqaqqun idanunta da suka gaza boye hawayen da taketa son shanyewa ta dubi bibi,don duk yadda taso ta shanye bacin ran maina amma ta kasa,saboda zuciyarta ta gaya mata nini dinta da games dinta sun tafi kenan,tafi kowa sanin shi din kaifi daya ne,kuma ya aikatashi zaiyi shi ne gaba gadi,babu kuma sauyi ko canji a hukuncinsa

“Bibi ki gaya masa ya dawomin da kayana” ajjiye cup din hannunta bibi tayi,daga tsayen da take ta maida dubanta kanta

“Zai dawo miki dasu,amma saifa idan kin maida kai ga karatunki,na tabbatar idan yaga hakan ko bakice ba zai dawo miki da kayanki gaba daya koda kuwa ba’a ce masa ba”

“ni kawai ki gaya masa ya dawomin da kayana tunda dai ba shine ya siyamin ba” tayi maganar da alamun kuka yana son balle mata.

“Ai sai kije ki karbo da kanki” bibi din ta fada cikin gatse. Bibin na direwa sultana tayi hanyar falon cikin dakiyar zuciya,cikin zuciyar tata tana fadin

“Aiba ubana bane,ba kuma mala’ikan mutuwa bane da zanji tsoronsa”.

Kaman ko yaushe,ma’abocin rashin son hayaniya ne da kebe kansa guri guda a mafi yawancin lokuta. A yanzun ma hakan take. Shi daya ne a farfajiyar gidan,yana sanye da wata lallausar shirt da trouser dukkansu royal blue ne da dan ratsin blue din kadan a jikinsu. Ma’abocin karance karance ne sosai,yana daya daga cikin hobby dinsa. Ko yanzun ma littafin wani shahararren marubuci ne a hannun nasa dan qasar faransa.

Idanunta a kansa tun daga nesa ta tsareshi dasu,sannu a hankali take qara kusanci a tsakaninsu. Wani irin kwarjininsa ke dukan zuciyarta yana neman cire mata dukka wani qwarin gwiwa da ta fito da ita,saita ta lumshe zuciyarta na sake bata qwarin gwiwar tunkarar nasa ta kuma zazzage masa dukka bacin ranta da abinda ke cikin zuciyarta.

Maimakon ci gaba da samun qwarin gwiwar isa gareshi din,a duk sanda tayi taku daya sai qarfin gwiwarta ya ragu da wani kaso me yawa. S hankali ta tsaya cak kamar wadda aka yiwa burki sanda take dab da isa gareshi,kwarjininsa gaba daya ya gama cikata,tayi imanin tayi kadan ta isa inda yake din duk da confidence din da ta fito da shi a dazu,wannan baqincikin ya sanyata juyawa da sassarfa me hade da gudu tana komawa sassan bibin.

Sam baisan da tsaiwarta a wajen ba,don shi din mutum ne da bai fiya mai da hankali da idanu akan abinda bai shafeshi ba,yaji motsi da taku duka lokaci daya,ya daga shanyayyun idanunsa yana bin hanyar da kallo. Baici nasarar ganinta ba,saidai yaga shigewar mutum sashen bibi,sai ya dauke kansa ya maida ga abinda yakeyi.

Da kallo bibi dake zaune cikin lafiyayyun kujerun falon ta bita. Ta sake baki kawai sanda ta zube saman daya daga cikin kujerun tana sakin qarfaffan kuka

“Oh…..oh ni maryamu,yau naga abinda ya isheni”

“Alla……Allah sai ya dawomin dasu,Allah bibi kiyi masa magana” abinda sultana din ke maimaitawa kenan cikin kuka. Ta tafasa sauke bibi bata sake cewa da ita ba sai maida kanta da tayi ga abinda takeyi,saboda tayi imanin zata bata bakinta ne kawai,don babu abinda zatace da sultana da zai sanyata tayi shuru.

Kuka sosai tayi cikin kujerar kamar wadda aka yiwa mutuwa,irin kukan data jima batayishi ba,har ranta bibi kejin kukan amma tayi banza da ita,saboda ita kanta ta tabbatar dauke kayan shine maslaha. Tanja ce ta dinga fama hade da jelar lallashin sultanar amma babu abinda ya canza. Zuwa wani lokaci tayi shuru,shurun da ya tabbatar tayi bacci.

Blanket tanja ta dauko tana jan qafafunta ta gyara mata kwanciya,zuwa yanzu sultanar tayi girman da ba zata dauketa ba,ba kamar shekarun baya ba da idan ta gama rigimarta kamar haka tayi bacci tanja din ke daukarta ta kaita dakinta ta kwantar da ita.

Wannan abun da ya farun ya sanyata tsirar fushi da kowa cikin gidan,gefe daya kuma ta sake fakewa da wannan ta aske zuwa islamiyya. Hatta bibi batasan bata zuwa din ba,tanja kawai tasan da hakan,ita dinma kuma bata gayawa kowa ba,saidai tanata qoqarin lallabata da hikima da dabara akan batun zuwan.

Cikin kafiya da taurin kanta tayi kunnen uwar shegu da tanja din,duk da hakan tanjan bata fasa hilatarta ba.

Kwanaki uku kenan ya karanci kowanne yaro na fita islamiyya amma banda ita. Tun a kwanan farko yaso yiwa tufkar hanci,amma sai ya fasa ya zuba idanu yaga iya gudun ruwanta. A iya nata hasashen da gajeren tunanin tana tunanin kamar ya fita sabgarta ne,hakan ya sanya baya gane duk wani motsi nata kenan.

L A H A D I

Kimanin qarfe uku na yammacin ranar lahadin,ranar da kowanne yaro na gidan ke tafiya tahfeez,tun sha biyun rana sai qarfe biyar da rabi na yammaci suke dawowa cikin gidan.

Dai dai lokacin da sultana ke cikin dakinta,tayi game yau din har ta godewa Allah cikin wata wayarta da uncle inoussa ya taba bata gift na birthday dinta. Shekara guda kenan wayar na ajjiye bata taba amfani da ita ba,sai a yanzu da maina ya talautata ya kwashe mata dukka abokan debe kewarta.

Qishirwa ce ta dameta,ta bude fridge dinta babu ruwa,madararta ma sauran kadan ta qare. A kwanakin ta sha madarar sosai zaman da takeyi a dakin na awanni har batasan adadin guda nawa ta sha ba. Maida murfin fridge din tayi ta rufe,ta sauke lausasan siraran yatsunta qasa ta miqe tana daure gashinta dake da tarin yawa tsaho da santsi,baqi sidik da shi na asalin buzaye.

Cikin takatsantsan take takowa zuwa falon don kada suyi kacibus da bibi,taji dadi sosai data fuskanci babu kowa cikin falon,wannan ya sanya kanta tsaye taci gaba da takawa zuwa ga babban freezer dake girke a wata kusurwa ta musamman dake cikin falon.

Cikin nutsuwa jerin gwanon motocin ke kutso kai cikin tafkekiyar harabar farko ta gidan,wadda a nan aka tanadi wani tsararren parking lot da aka gina shi bisa tsari da kuma dacewa.

Lafiyayyun motoci ne da suke lashe manyan maqudan kudaden da kai zaiyi ciwo wajen lissafin yawansu. Kowacce mota kuma mallakin hamshaqin attajirin dan kasuwa ne wato MUHAMAT MUHAMMAT MAYAK’I. Dan kasuwar da sunansa yayi wani irin fice yayi tambari ya kuma shahara cikin qasar NIJER dama nigeria din gaba daya.

A nutse suka gama tsaiwa,mota ta qarshe a cikinsu seat din gaba suka bude. Wani farin matashi me tsaho da kuma kauri ya fito ya dawo set din baya ya bude murfin motar.

“Bismillahir rahmanir raheem” shine abinda mutumin ya fada yana sako dogayen qafafunsa yana fita a motar.

Tsayayyen ingarman ba’abzine fari sol sol dashi,giant ma’abocin tsaho da kuma qiba wadda tsahon ya tafi da ita,wannan dalilin ya sanya kai tsaye zaka iya kiranta da murjewar jiki. A duba na farko kawai zaka yi masa kasan cewa yana cikin jerin samarin da suka zuba kyau da kuma qasaita a zamaninsa. Dai dai lokacin maina ya qaraso gurin. Qarasawarsu kusa da junan ta haifar da wani kyakkyawan kallo na kyawawan halittu guda biyu masu dan shigen kamanni da juna. Maina din ruwa biyu ne,wani lokaci kamanninsa sukan juye zuwa na ABA,wani lokaci kuma sai kaga kamar kaga AMA.

Isowar tasa ta fidda murmushi saman fuskar mutumin,bai iya jurewa ba ya miqawa maina din hannu

“Likita bokan turai mainassara” siririn miskilin murmushi ya walqa saman fuskarsa,cikin matuqar girmamawa ya furtawa aba din kalmomin maraba da shiryayyu kuma taqaitattun kalmominsa,sannan ya matsa gaba kadan yana karbar briefcase din aba din daga hannun daya daga cikin yaransa.

“Ka shaidawa bibi isowata” aba ya fada don yasan abinda maina din ke son fara yi kenan.

Kansa tsaye ya tunkari sashen bibi din yana takawa cikin nutsuwar nan tasa data girmewa shekarunsa. Yana bude qofar tana sakin gorar ruwan hannunta,hantar cikinta tayi wani mugun kadawa lokacin da idanunsu suka gauraya waje daya,tsoro ya bayyana sosai cikin idanunta,yau kam tasan ta kade,batasan kuma me qwatarta ba bayan ubangijinta.

Shanyayyun idanunsa ya zube mata yana fara hukuntata da kallonnan nasa da a baya su kadai suna iya fahimtar da ita umarninsa ko haninsa. Ya raineta da irin wannan sigar da ta sanya basai ya furta komai ba take iya gane me din yake nufi. Duk taurin kanta da dakiyarta a yau jikinta ya kasa shanye wannan tsoron daya kwanta saman zuciyarta. Dukka jikinta yadan soma rawa,ya ajjiye briefcase din aba ya goye hannayensa a qirjinsa ba tare da ya dauke idanunsa a kanta ba ya jefa mata tambayar

“Ina islamiyya?,me kikeyi a gida?” Kwata kwata dukka wata amsa ta dauke a bakinta,musamman sanda idanunta suka hangi bibi tsaye daga bayansa baki sake tana mamakin ganin sultana din itama a gida

“Ina islamiyya nace miki!” Ya sake fada cikin tsawa,tsawar tasa data kusa ruguza ragowar nutsuwarta.

Cikin harshensa daya gauraye da hausa faransanci da kuma yaren buzanci yayi sallama a falon,sallamar tasa da tayi dai dai da saukar rahama da wani irin farinciki a zuciyar sultana. Dayan madogarartata ya dawo,bango abun jinginarta,wanda a yanzu tana da yaqinin shine ya maye gurbin matsayin yaa maina din a ranta da zuciyarta,ta tabbatar kuma a yau ta kubuta daga dukkan wani hukunci da muguntar da maina ya tanadi yi mata. Bata qara koda second biyu ba ta qarasa gareshi da hanzarinta. Kaman wadancan shekarun ta tarbeshi,saidai a yanzun ita kanta taji kunyar fadawa jikinsa sai hannunsa data kama,qwayar idanunta dake da wani irin maiqo koda babu hawaye a cikinsu sun sake sheqi saboda qwallar data tara a cikinsu.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 09

Yana shiryawa bayan ya fito daga wanka tana taimaka masa amma yana karance tsaf da ita. Walwalarta ta ragu ainun,kuma dukkan alamu sun nuna shaguben da yayi mata dazun ya taba zuciyarta kamar kullum.

Tsaf ya gama shirinsa sannan ya samu gurin saman sofa bed ya zauna yana dubanta

“Nu’aima” yayi kiranta da sunanta na ainihi. Dara dara kuma farare sol din idanun nan nata da ya santa dasu. Tun daga quruciya har kawo girma suna nan basu canza ba su ta dago tana dubansa

“Why?,me yasa kowanne hali naki a bayyane yake amma kin kasa canza halinki akan duk wani abu da ya shafi nafissa,me tayi miki ne?” Sosai tambayar tayi mata tauri a ranta,ta gaza gane me ya sanya suka kasa fahimtar ta ne?,me yasa kowa ke mata bahagon kallo da kuma bahaguwar fahimta?,bayan sunfi kowa sanin wacece ita?.

Sai data gyara zamanta sosai sannan ta dubeshi,sai kuma ta kauda kanta gefe

“Har yanzu kun gaza fahimta na ne aba,nidai na sani iya iyawata,nayi abinda ya dace ne kawai da rayuwarmu gaba daya wanda nayi imanin inda an samu akasin hakan a yanzun ba wanda yake da guarantee na halin da duka ahalinmu ke ciki” nannauyar ajiyar zuciya aba ya saki,sannan ya saki wani siririn murmushi

“Amma kinsani bawa baya taba GUDUN K’ADDARARSA?” Tambayar tasa tazo mata wani iri,kamar ma zata iya cewa bata fahimci ainihin saqon da yakeson isar mata ba

“Kamar yaya kenan?”

“Kamar yadda ya faru” ya sake dilmiyar da ita ta hanyar bata amsar da ba ita take da buqata ba a sannan.

Iska me sanyi ta furzar a bakinta,sannan ta sake juya kanta gefe

“Na fada xan kuma sake maimaitawa,bana qin nafissa da tuni ta jima da gushewa cikin duniya,kamar yadda sultana batayimin komai ba da zan qita,inda ina qinta ne,da babu yadda za’a yi na bari maina yayi ruwa da tsaki cikin lamuranta……abu daya zan gaya muku,ku ajjiye komai ku dora rayuwarta bisa siradi da turbar da ya dace”.

Tsam ta miqe ta fara hada kayayyakin da ya gama amfani dasu. Murmushi ya saki qarami,wannan kusan itace amsarta ta qarshe a duk sanda magana irin wannan ta hadasu,bata taba canzawa ba. Ya jima baiga tsayayyar mace me kamar maza irin nu’aima din ba,ba gudu ba ja da baya,bata kuma tsoron duk abinda ta tunkara.

Cikin qawataccen parlor din mallakin hamshaqiyar ‘yar kasuwar HAMDIYYA ABDU ME KANO su biyu ne rak zaune a cikinsa. Sassanyar la’asar ce maras hayaniya dake busa sanyi kadan kadan maras shiga jiki sosai. Saidai duk da hakan hakan bai hana matashin ba’abzinen Aliyyu maina sanya wata lallausar baqar zipper hoodie sweater ba wadda ta fidda ainihin sassanyan kyawun fuskarsa,siriri kuma dogon hancinsa ya fita dodar saman miskilar fuskarsa dake a yanayi na babu yabo babu fallasa,dukka a hakan saboda yana tare da AMA dinsa.

Cikin takardu suke kaca kaca shi da ita,kyawawan zagayayyun idanunsa suna saman takardar hannunsa,ya tsareta dasu tsaf tamkar meson banbance ainihin launin dake jiki.

Baya yaja a hankali ya zauna yana miqe dogayen qafafunsa dake taka muhimmiyar rawa wajen zamtowarsu dogo kuma tsayayyen namiji,ya furzar da iska kadan daga bakinsa yana lumshe kyawawan zagayayyun idanunsa. Furzar da iskar da yayi ita taja hankalin hajiya hajja hamdiyya. Ta daga idanunta a nutse tana ajjiye kyakkyawan abun rubutun hannunta idanunta a kansa

“Yaya dai?,idan ka gaji a kawo maka haleeb mana” kansa ya girgiza a hankali ba tare da yace komai ba. Shurun itama tayi tana ci gaba da dubansa,ya motsa kadan ya ajjiye takardun hannunsa gefe

“Kina tara lissafi da yawa ama,wannan duka kafin wannan satin ya kamata ace kin fidda komai” qafarta tadan kada kadan tana dubansa

“Ka manta bani da mataimaki?” Ta jefa masa tambayar kai tsaye cikin salon son titsiyeshi.

Kansa yadan kawar,don yasan ya dauko maganar da zata janyo masa tarin qorafi dake wajenta

“J’ai besoin d’aide(ina buqatar matemaki)” ta fada da harshen faransanci,wanda ya kama bakinta da kyau fiye da zato,ba zaka taba tsammanin akwai wani yare saman harshenta ba bayan wannan. Cikin shi da ita din ba wanda ya sake cewa komai,sai ta jawo wayar dake saman wani qawataccen table na glass dake daura da ita ta fara danna numbers din da zata sadata da sashen kitchen dinta.

A taqaice ta bada umarnin abubuwan da take da buqata ta maida wayar ta ajjiye tana duban maina din. Tana da tarin tsaruka masu yawa a kansa,kasancewarsa dan fari a gareta da take masa hangaen kyakkyawar makoma. A dukka tsarinta da burinta maina din daga secondry school ya gama duk wani karatu a duniya,burinta shine ya fuskanci dukiyarta,tunda tarin dukiyar da mahaifinsa ya mallaka yana da tarin amintattu dake kula masa da kowanne sashe nata. Duk da hakan taso ace ya kasance shine shugaba a garesu gaba daya. Burinta akan rayuwar yaran nata qwalli biyu kacal me zurfi ne,tanaso ta basu gata da rayuwa me kyau fiye da wadda suka samu daga wajen nasu mahaifan ita da ‘yaruwarta nuwaira.

“Me da me ka samu hadawa?” Ta sake tambayarsa tana kallon wayarta dake haske da idanunta ba tare data kai ga dauka ba,da alama bata shirya dauka din ba. Cikin nutsuwa da melodic voice dinsa ya dara fidda mata bayani dalla dalla.

A nutse take gyada kanta tana saurarensa,ba shakka ba qaramin alfahari take da maina din ba,yana da wata irin sharp brain,lissafinsa har tsoro yake bata,ba shine ke juya mata dukiya ba,ba kuma shike mata business din ba,amma kusan kaman ya fita sanin yadda kudadenta ke gudana tare da jujjuyawa,asara faduwa inda za’a samu riba da inda aka tafka kuskure.

A hankali tare kuma da wani irin qaqqarfan sound qarar kida ya ratsa muryar maina,lokaci guda kuma ya ragewa muryarsa kaifi da karsashi.

A nutse ya daga kansa yana duban Ama cike da mamaki,yana daha daga cikin nau’in mutanen da basa qaunar hayaniya kwata kwata. Itama ama din shi take kallo,tsaf ta karanci qwayar idanunsa da kuma tarin tambayoyin data karanta a cikinsu.

“Waye da wannan aikin Ama?” Yayi tambayar a nutse yana ajjiye document din hannunsa.

Bakinta ta mele kadan sannan ta amsa masa tana hade yatsunta guri guda

“Waye a cikin gidannan ya isa yayi wannan abun idan ba sultana ba?”

“Sultana?” Ya tambaya fuskarsa da sautin muryarsa cike fal da alamu na mamaki. Bata sake amsa masa ba sai jawo takardar data ajjiye dazun da tayi taci gaba da dubawa.

Kansa a qasa yana murza hannunsa cike da bacin rai,yana tunanin zai iya jure tashin sautin kidan har zuwa lokacin da wani cikin gidan zai tsawatar ya dakatar da kidan amma sai ya gaza jurewa. Saboda cikin qwarewa da wani irin salo yake tsinto muryar sultana din tana biye da waqoqin turawan qasar faransa din,tamkar tare da mawaqan suka rubuta waqar,abinda ya bayyana masa zallar tadda take saurarr tare da biyar waqiqinsu kenan sau da qafa.

Sake ture documents din yayi ya miqe fushi na soma cin zuciyarsa har ya soma tasiri saman fuskarsa.

“Ina zuwa ama” ya fada yana ficewa daga falon.

Baki ta sake tabewa tana girgiza kai. Yana daya daga cikin abubuwan da sukayi mata tsaye a rayuwa yadda mainan yayi tsaye cikin rayuwar yarinyar. Yarinyar da kaf gidan babu wani yaro da yayi miqewar qafar da tayi. Ko meye ne zatayi ba wani laifi nata fitacce da ake iya gani,ko yaushe tana da immunity,maina din kadai ne yake iya keta wannan immunity din. To amma me yasa shi din bazai sanya idanu kamar yadda kowa ya sanya ba?.

“Saboda nafissa” wata zuciyar ta bata amsa,sai ta saki siririn tsaki ta ajjiye takardar ta dauki wayarta.

Idan daga nesa kake ka kalli wajen zakayi tunanin wani gagarumin dinner party akeyi a wajen.

Dukka kusan tsararrakinta ne a wajen,wadanda sukayi shekaru dai dai da nata,sai kuma wadanda suka dara shekarunta da kadan. Abun ban mamakin da kuma daure kan shine,kusan dukkansu maza ne tsararrkin nata,sai mace qwaya daya a cikinsu.

Bayan tsananin baci da ranshi yayi harda tashi da hankalinsa yayi. Ba sau daya ba ba sau biyu ba indai idanunsa dai dai suke ganin yana ganin yaran kusan duk yammaci a farfajiyar gidan,saidai bai taba kawowa wai suna taruwa cikin gidan bane da zummar sunzo wajen sultana. Gaba daya tunaninsa na bashi gurinsu almu saddi da su atta suke zuwa. Yanzun kenan duk taron yarannan maza suna abota ne da sultana?.

Tambayar data sake tunzura bacin ransa,ya qara sassarfar tafiyarsa,fatansa kadai ya isa ga gungunsu da basusan ma da tahowar tasa ba. Yayin da shugabar tawagar sultana tayi nisa cikin wata irin rawa data sake bashi mamaki.

Yadda take lanqwasa jikinta zakayi tsammanin babu qashi ko daya cikin jikinta. Yadda kuma take rawar cikin karsashi kadai zai tabbatar maka hakan yana mata nishadi qwarai.

Tsaiwarsa guda daya ta dakatar da tarin hayaniyar da sukeyi a wajen. Kaf dinsu ba wanda hantar cikinsa bata kada ba. Sanda yasa hannu ya yiwa mp din nata wani wawan duka ta dauke dif saida kowa cikinsu yaji kamar yayi layar zana ya bace.

“Ku fice!” Ya fada da gigitacciyar fusatacciyar muryarsa.
Babu shiri har wani na ture wani suka soma laluben babbar katafariyar qofar data iyakance harabar farko ta gidan da haraba da biyu,inda ainihin ginin gidan yake da kuma muhallin da suke a zaune din.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

Page 10

Yadda ya rakasu da kallo haka sultana ma. Saidai kuma abinda ke zukatan kowa tsakanin shi da ita ya banbanta da na danuwansa.

Zallar fushi da bacin ran yadda ya wargaza mata dabarta data saba hada musu dukka qarshen sati ita da abokai da qawayenta. Suci su sha su kuma cashe ba tare da kowa ya matsa musu ko ya adabba musu ba. Sai gashi yau rana guda daya tak,daga fara zuwar musu hutun tsakiyar karatu yana neman ruguje mata abinda ya kusan zame mata al’ada,akan meye?,ba wanda ya taba yi mata hakan a gidan sai shi?.

Ta gefan maina kuwa nashi fushin yasha banban da nata. Wani bahagon kallo yake jifanta da shi cike da zallar bacin rai dake cin zuciyarsa ainun. Abubuwa iri daban daban zuciyarsa ke qiyasta masa ya aikata mata da zai zama makwafi na daukan mataki ko kuma hukuntawa a gareta. Saidai kuma ta wani fannin ta qarfin tuwo yake danne zuciyar tasa,tare da sake gayawa kansa wacece sultana a garesa,sultanan nafissa ce,sultanan kamar d’iya take a wajensa.

“Wuce cikin gida tun ban tattakaki a wajen nan ba” ya fada a mugun tsawace. Har tsakiyar kwanyarta taji sautin qaqqarfar husky voice din nasa dake cakude da fushi,fushin da zuwa yanzu ta shiga sahun jerin mutanen da suka sakan qarfinsa da kuma illarsa.

A nutse kuma a hankali ta juya zuciyarta na wani irin raurawa. Kuka takesonyi na yadda ya bada ita gaban friends dinta,amma dakakkiyar zuciyarta na gaya mata

“Akul kada ki fara,kada ki yarda yaga lagonki kamar yadda yaga lagon su lamira”

Da idanu ya rakata daga nan inda yake tsaye yana hadiyar bacin ranta,tabbas inda yasan tafiyarsa da kuma yin nesansa da gida haka zata sake tabarbara al’amuran sultana…….haka zata sake maida sultana……haka komai zai sauya da ya haqura da tafiyar,da ya nemi afuwa daga wajen aba,yaci gaba da roqarsa ya barshi yaci gaba da lallaba karatunshi a haka.

Sai data fara nisa sannan ya ankare da shigar dake jikinta,shigar qananun kaya trouser da shirt inner da top. Sosai kayan suka zauna mata a jikinta wanda yake a murje tsaf…..zallar hutu da kwanciyar hankali sun bayyana muraran a tattare da ita,ko ina nata ya soma cikowa alamun da hasken gaske dai girma ne yake cuso kai cikin qananun shekarunta da duka duka basu haura sha biyu ba.

Duk yadda yaso ya daure don kada sanya baki akan lamuranta su yawaita amma ya kasa,saboda shiga ce da ya haramtata baki daya cikij gidan,ba kuma yanzun abun ya faro ba,tun zamanin da nafissa kawai ke rayuwa cikin gidan a matsayin diya mace,har kawo yanzun da diyoyi matan cikin gidan suka sake yawaita.

Sake quluwa tayi ta cika fam sanda taji yana qwala mata kira sunan

“Ke!” Sunan da duk duniya tafi tsanar ka kirata dashi.

Bai umarci tazo ba,da kansa yake takowa inda take tsayen. Sai ta samu zuciyarta da bugawa cikin tsananin tsoron wanne laifin kuma tayi?,saidai kuma taurin kanta da zuciyar nan tata maras tsoro na sake qarfafar dukka gabbanta akan bata aikata masa laifin komai ba.

“Sau nawa zan gaya miki na hanaku irin wannan shigar?,ina atamfofin da AMA ta raba muku?” Yayi mata tambayar yana tsareta da lion eyes dinsa da a yau suke cike da fushi.

Baki takeso murguda masa ko ta maida masa amsa me ciwo,don dai ita zuwa yanzu tuni ta cireshi daga sahun mutanen da take jin nauyinsu take kuma ganin kima martaba da darajarsu

“Ni ban iya sakasu ba,kuma ma zafi garesu”

“Kalleni nan” ya fada cikin zallar tsare gida. Kasa duban idanun nasa tayi,duk kuwa da yadda takejin a yanzun bawai kallon idanunsa ba,har zagi tanajin zai iya fita a bakinta a yadda takejin ya matse rayuwarta haka da yawa.
“duk ranar da na sake ganinki da wadannan kayan ki tabbatar saikin raina kanki,abu na biyu muddin na sake ganin qafafun wadannan cikin gidan nan a tare dake……basai na gaya miki abinda zanyi ba,bacemin a gun” ya fada a kausashe kuma a tsawace.

Wani irin fushi da tarin haushinsa takeji kamar tayi me?. Me zatayi masa ne ta huce wannan abun da yayi mata?,me zatayi masa ta rama?,kawai sai ta bude zazzaqar muryarta ta fara jera waqoqinta hankali kwance tana wucewa zuwa sashen bibi

Bamu damu da kowa ba kar wanda ya damemu……baka bani ban baka to hushin na menene?,ashe zaman duniya iyawa ne

Da mugun sassarfa ta soma tafiya me hade da gudu da kuma sauri,saboda ta tabbatar abinda tayi din babu wani makawa da zai hanata karbar hukunci mafi muni daga hannunsa.

Cikin kunnen nasa dukka baitocin waqoqinta suka sauka. Wani irin mamaki ne ya kasheshi,zuciyarsa tayi wani mugun yunquro masa,har a cikin ransa yakejin yau din dole ya ajjiye duk wani dubayya da yakeyi ya hukuntata yadda ya kamata.

Kusan lokaci guda suka isa parlor din bibi. Daidai lokacin da take zaune saman daya daga cikin qawatattun kujerun turkey da suka sake daga darajar parlor din har set biyu mabanbantan kaloli da suka dace da juna. Hannunta na dauke da tasbaha da bata rabo da ita tana ja,musamman lokutan da take ita daya irin wannan,yayin da rabin hankalinta yake kan tv france dake gudanar da wani shiri dake nuna ainihin zallar al’adun gargajiya na qasar nijer din. Lallausar rigar wani farin zaren ulu ne a jikinta,wanda yake da adon ja jefi jefi,budaddiyar rigar ta asalin saqar qabilar abzinawa. Tun daga yanayin jikinta zuwa suturarta zaka fahimci sukunin rayuwar da take ciki da kuma zallar kulawa da take samu.

Bata kawo shigowar kowa a cikinsu ba a lokacin,don haka a dan firgice ta daga idanunta tana saukesu daga bakin glass door din parlor din nata.

Tun kafin ta gama rarrabe tunaninta akan abinda ke faruwa sultana din ta fado,kafin takai ga dauke idanunta a kanta ko kwanyarta ta warware mata komai maina ya biyo bayanta.

Taku daya tak ya sakeyi ya cimmata,wanda duka duka tazararsa shi da ita da kuma bibi din baikai taku biyu ba.

“Kul maina!,menene haka?” Muryar bibi ta dakatar dashi daga saukewa sultana zaratan hannayensa da yayi niyyar yi saman farar fuskarta.

A hankali ta sauke kallonta daga kan dogayen yatsun mainan ta maida kan fuskarsa

“Zauna maina” Ta fada cikin wani irin mode dake nuna tsoro da fargabar da suka cika zuciyarta.

Ji yayi sam bazai iya zama din ba,sai ya sauke hannayensa ya xubesu zuwa cikin aljihunsa,ranshi a mugun bace yana jin yadda jijiyoyin jikinsa ke harbawa saboda tsananin bacin rai.

Bibin ta sani,koda ta tambayeshi ba’asi a yadda fushinsa ya hau zuwa matakin da tasan ya kusa kaiwa qarshe,koda zata dige tana tambayar nasa ba zaya ce komai ba,don haka ta waiwaya ga sultana data dade da yin garkuwa da bayanta,ta dunqule ta kuma cure a bayan nata,manyan idanunta na runtse gam,abinda ke bayyana ainihin asalin tsoronta

“Me kikayi kuma sultana?” Tambayar da bibi ta jefo mata ya bata tabbacin ta samu tsira daga hukuncin ya maina din,wannan din ya sassauta tsoratarta da kuma fargabarta,ta zame ta zauna sosai tana kallon bibi kamar ba itace ke boye a bayanta da razananniyar fuska ba

“Nima bansan abinda nayi masa ba bibi,hakanan kawai ya biyoni zai bigeni” kyawawan idanunsa ya hada ya lumshesu guri daya yana furzar da iska daga bakinsa. Wani baci ransa yake sakeyi,bayan zallar rashin kunya harda qarya?,abar da yafi tsana kayi masa?

Yana daya daga cikin abinda yasa wasu ke masa kallon tsatstsaura,saboda shi din yana cikin jerin sahun mutanen da kwata kwata basu iya qarya ba. Kome dacin abu,komai girman abu idan zasu fada zasu fadi maka ne kansu tsaye kuma iyakacin qarshen gaskiyarsu,ko tayi maka dadi ko batayi maka ba. Daya daga cikin abubuwan dake tunzura fushinsa shine qarya,kusan duka yaran gidan sun sani,samun sassaucinka idan kayi masa laifi ka amsa kayi,wannan kawai na iya sanyawa ka wanke dukka laifinka a wajensa.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 12

,zuciyarta ta tsinke da tsoro amma wannan tarin kafiyar tata gami da taurin zuciya ya sanya batayi ko gezau ba a fili bare ta nuna hakan.

A nutse ya qaraso wajen yana dubansu a nutse

“Ku saketa” ya fadi a nutse. Sakin nata sukayi hakan ya sanya fa silalo daga jikin motar ta tsaya da qafafunta. Baibi ta kanta ba ya waiwaya ga tanja yana neman ba’asin abinda yake faruwa,inda inda tanja din ta soma yi masa,wannan ya sanya ya maida tambayar tasa ga lamira dake dab da window din.

Cikin nutsuwa da takatsantsan tayi masa bayani da harshen da zai fahimci komai. Sanda ta kammala maganar watsawa sultana wani kallo yayi yana hadiye bacin rai. Kullum sake lalacewa takeyi abun nata kuma yana qara gaba ne. Bayason ya fiddo mata da ainihin kalarsa gaba daya,saboda yayi imanin hakan bazaiwa kowa dadi ba a gidan. Yana da wani irin fushi zuciya da kafiyar da shi kansa yasan girmanta,wannan ya sanya yake yawan kaucewa dukkan abinda zai bata ransa

“Kada na bude idanuna na sake ganinki a tsaye a nan wajen stupide(shashasha)” yadda yayi mata maganar da kuma yadda kowa ya zuba mata idanu yana kallon fadan da yake zazzaga mata sai taji abun baiyi mata ba,kaman ya tozartata ne,abinda yasa taji zuciyarta ta wani quntace guri daya,sai kawai ta saki kuka iyakar qarfinta tana rufe fuskarta da hannuwanta.

Sake baci sosai ransa yayi,saboda shikam baiga uwar da akayi mata ba,uwa uba ma hukuncin da zaiyi matan baiyi mata shi ba. Wannan ya tunzurashi ya taka a zafafe ya finciko hannunta yana tambayarta cikin tsawa kan abinda akayi matan.

Wani ihu ta qwala kai kace ya karyata ne gida biyu. Ihun nata da yaja hankalin aba dake tattaki ta bayan gidan.

“Lafiya?,ke sultana meye?” Ya kuma jefa mata tambayar yana isa gareta hadi da kamo hannunta. Kai kawai maina ya kawar yana hadiyar wani abu me cikin wuyansa,iya yadda take kukan kawai yana sake bata masa rai da tunzurashi.

“Don nace bazan hau bus scoloire ba shine yakemin fada zai dakeni,ya kamamin hannu inajin ma ya karyani” ta fada tana miqawa aba hannun nata.

Hannun ya kama yana dubawa da kyau hadi da jujjjuyashi,sai ta saki ‘yar qaramar qara

“Wayyo Allah na” ta fada hawaye shabe shabe saman fuskartata,kai kace da gaske karyata din yayi

“Sannu sultana,ya isa,sannu” aba din ya fada fuskarsa na nuna alamun abun ya tabashi

“Ina modu” aba ya fada yana duban sararin gurin

“Gani ranka ya dade”

“Jasu ku tafi makarantar,kai hassane……”

“Yallabai” ya fada yana matsowa cikin girmamawa

“Ka fiddo wancan motar,a wanketa a duba lafiyarta,daga yau ta zama ta daukan sultana” a dan hanzarce maina ya daga kansa ya dubi aba din,ransa yana motsuwa. Da gaske dukkan abinda takeso sukeyi mata kenan?,ya daga tayi hukunci irin nata sai a biye mata. Idanunsa suka hada da aba din,sai ya jefa masa harara abinda ya sanya maina sake kauda kansa kenan. Akan sultana babu abinda ba zasu iya yi ba kenan?.

Ransa a matuqar bace ya soma barin wajen. Yayin da sultanan ta bishi da kallo dariya can fal qasan ranta,tana fatan inama zai waiwayo ta samu damar yi masa gwalo,ko ba komai yau ya gane matsayinta a wajensu aba din.

Ya jima zaune cikin sofa din falonsa yana jujjuya abubuwa. Yayi dukka iya lissafinsa amma ya kasa bashi dai dai,ba haka yakeson rayuwar sultana ta tashi ba,to amma ta yaya zatayi saiti kamar yadda yakeso?,bayan wadanda yake da buqatar dafawarsu dukka su dinma idanunsu a rufe yake. Idonsa ya lumshe yana fidda iska daga bakinsa,yana qoqarin kawar da zuciyarsa daga yunqurin fara jin haushin yarinyar. Makaranta yakeson komawa,amma tunanin abinda zai bari idan ya tafin shike taka masa burki.

Knocking yaji anayi,amma har aka kwashe wasu sakanni ya gaza bada umarnin a shigo din. Sai bayan da ya tabbatar ba za’a daina masa knocking din ba sannan ya motsa bakinsa yana tambayar waye

“Goumar ne” ya amsa masa daga wajen

“Entrez(shigo)” ya amsa shi yana sauke qafafunsa qasa tare da qoqarin saita yanayinsa.

A nutse ya murda qofar yana shigowa,goumar baqin buzu kamar yadda sultana ke kiransa kai tsaye,sunan kuma ya soma bin bakunan wasu ‘yan gidan. Shine d’a na farko ga Oncle bashar qani ga aba wanda shike binsa.

Kusan shine wanda yabi maina sawu da sawu,ya dauki dabi’unsa da yawa bawai ta siffar kwaikwayo ya siffantu da dabi’ar haka kawai ba,a’ah bibiyace ta jini kamar yadda ake iya samu daga kowa cikin kowacce zuri’a.

“Ama tana kiranka,tace votre petit déjeuner est prêt(abincin safenka ya kammalu)” qafafunsa dake saman dan table din mulmulallen katakon ya sauke yana dan sake ciki da idanunsa tamkar bayason budesu gaba daya

“Zauna goumar” maina ya buqaci haka daga gareshi. A nutse ya samu seat ya zauna,sosai mainan ya gyara zamansa yana kallonsa

“dites-moi(ka gayamin)iya lalacewan da sultana tayi” a dan rude kadan goumar ya daga kansa yana duban maina din

“Frère(haka yake kiransa wasu lokutan) lalacewa kaman yaya?” Qaramar Ajiyar zuciya ya sauke idanunshi akan goumar

“Eh,na fara tsorata da tarin halayenta,ina tsoron kada ya zama maza sun hure mata kunne……” Kai goumar ke girgizawa

“Ban taba ganin abu mai kama da wannan ba frère,banajin kuma haka” gyara zama maina yayi yana dan jin nutsuwa kadan

“Amma ka gayamin,wanne kallo za’a yima mace me irin halaye da dabi’un sultana?,idan a nan qasar ba aibu bane a sauran wasu qasashe fa?” Shuru goumar yayi ba tare da yace komai ba. Halayen sultana suna bashi mamaki ta yadda sukayi matuqar shan banban da na sauran yaran gidan,to amma kuma fadin hakan ga maina kamar qarawa fetur wuta ne.

Shurun goumar ya sanyashi miqewa kawai. Sai da ya biya ta bedroom dinsa ya zare takalman qafarsa ya maida gurbinsu da slippers sannan ya fito.

Har kullum sassan Ama din nasa daban yake da sassan sauran matan gidan ba,bawai don tana mahaifiyarsa ba a’ah,zai iya cewa kaf duniyarsa,a kuma ‘yar taqaitacciyar rayuwarsa bai taba katari da macen da tayi tsananin sanin ciwon kanta irin ama din ba.

Masu aikinta ne qwara hudu rak da bata tana sauyasu ko ragesu ba keta kai kawo suna sake gyara tsarin dining din. Kai tsaye za’a iya kiran ama din da ruwa biyu,’inda ana tsotsar boko to tabbas za’a iya cewa ita kam ta tsotsi boko daga jinin mahaifinta. Ta wani kuma idan kace bafaransiya ce shima bakayi kuskurenba,saboda yadda abubuwa da yawa na qasar haihuwar mahaifiyarta ya kama jikinta ya kuma zame mata jiki.

Kamar kowanne lokaci yau ma tana saman qawatattun kujerun da aka kewaye falon da su har rukuni uku. Hankalinta ya tafi sosai kan system dake kan cinyarta,ya kuma tabbatar abinda ya shafi business dinta ne.

Fararen idanunta ta daga tana amsa sallamarsa gami da dan binsa da kallo,har cikin ranta tana jin wani abu mara dadi yana motsa ranta. Damuwarsa bata taba boyuwa a wajenta koda kuwa yayi qoqarin yin hakan. Duk abinda ya faru dazun saman idanunta akayishi,ta kuma tabbatar yana daya daga cikin abinda ke damun ransa yanzu hakan.

“bonjour ama(barka da safiya ama)”

“matin” ta amsashi a taqaice tana gyara zaman eye glasses dinta. Sai da ya zauna sosai sannan ta dauki qaramar wayar dake gefanta tayi kira zuwa kitchen,magana tayi na mintuna qalilan sannan ta ajjiye wayar. Sake maida dubanta tayi a kansa

“petit-déjeuner(breakfast)naka wa ka barwa?” Bai amsa mata ba sai shafa lallausar sumarshi kawai da yayi da daya hannun nasa yana jin damuwa cikin qirjinsa

“Ba kowa ama” dan shiru ya ratsa tana danne dannenta a laptop kafin ta sake magana

“Yaushe zaka koma bakin karatunka?” Tayi masa tambayar tana zube masa idanunta. Qaramin murmushi ne ya subuce masa,ya gyara zamansa yana cewa

“Yau kuma ama?” Kai ta gyada cikin basarwa

“Oui(eh)……” Ta fada kai tsaye

“pourquoi?(me yasa?) Ama,ko kin gaji da nine?” Yayi tambayar cikin salon tsokanar da ba kasafai ya fiya yinta ba a tsakaninsu,duk kuwa sa cewa akwai sakewa qaunar juna da kuma fahimta,amma halinsa na miskilanci ya sanya ba komai yake iya yi ba

“Eh……na gaji da ganinka a haka kana ragaita tsakanin abinda ba zaka iya gyarawa ba……ba sultana ce ba?, itace ta tsaidaka ko?” Tayi masa tambayar idanunta tsakiyar nasa.

Zare idanunsan yayi sannan ya motsa labbansa a hankalin cikin son kare sultanar,kada ta sake baqi cikin idanu da zuciyar ama din

“Non ama(a’ah ama)”

“To menene?…..sultana ce haka sukeson su ganta,haka suka tsara mata ta taso ta kuma rayuwa,to kai a suwa?. Don kawai kana yaya ga mahaifiyarta?,duka duka shekarunka nawa maina?,tu as beaucoup à faire dans ta vie(kana da abubuwan yi da yawa cikin rayuwarka) ka fuskancesa ka barta tayi rayuwa yadda suka tsara mata,ne perds pas ton temps(karka bata lokacinka)” ta qarashe fada cikin zafi zafi.

Shuru yayi yana sauraren sautin muryarta,zuciyarsa na sake motsawa,gaba kura baya sayaki,ta yaya zai iya bari sultana ta taso a haka?,duk kuwa da cewa abune da da yawa daga cikin al’umarsu suka taso suna ganinsa,kusan ya zame musu ruwan dare,ba kuma komai bane,amma kuma shi cikin jininsa ya tsani wannan tarbiyyar tasu sam,yana qyamatarta qwarai da gaske,da kuma gasken turawan France sun musu illa qwarai,sun shiga tarbiyya al’ada da kuma dabi’unsu

“suis désolé(am sorry)” ya fada kawai a taqaice don bashi da wata kalma da zai iya furtawa bayan wannan a yadda yaga ran aman ya baci.

Wannan duka ya hadu ya dinga damunsa cikin rai. Duka duka abincin bai iya ci me yawa ba ya tashi,abinda ya sake bata ran ama kenan. Tana ganin duka ya tattara damuwar sultana ne a ransa,wanda koda shine ya haifeta iya abinda zaya nuna kenan. Yayin da shi nasa damuwar tafi karkata ga yadda soyayya da zallar gata da su bibi ke nunawa sultana keson zamewa tarnaqi cikin samuwarta da maidata cikakkiyar mace wadda yakeson ya raina. Cikakkiyar macen da duk mijin da Allah ya bata zaiyi alfahari da zamowarta matarsa. Mace daya tamkar da dubu da tarbiyyarta zata fita daban da sauran mata cikin al’ummarsu.


A nutse bibi ta shafa addu’arta kan fuskarta da dukkan tafukan hannayenta guda biyu. Can qasan ranta abun yana ci gaba da tsinkular ranta,fargabarta tana sake qaruwa kan sha’anin sultana da maina. Ta gaza fahimtar ina ainihin matsalar take?,sai ya dafa qasa da dukka hannuwanta tana tashi daga saman lallausar farar dardumarta.

Babban falonta ta fito cikin nutsuwa da kamalar data cika fuskarta. Akwai dattako sosai akan fuskarta da kuma cikar dattijantaka. Hakanan tsarin halittarta yake,tana da nutsuwa qwarai cikin komai nata,SULTANA CE kadai rauninsu.

Tanja kadai ta samu zaune cikin falon tana kallo. Lokaci ne na hutu ga dukka ma’aikatan gidan,bata kuma tsawwalawa ga kowanne ma’aikaci dake qarqashin sashenta,suna walwalarsu tamkar kowanne mutum cikin gidan. Kusan ma’aikatan sashenta ma sunfi na kowanne sashe samun ‘yanci.

“Sannu da fitowa” tanja ta fada tana lanqwasa qafafunta

“Yauwa tanja,ko zakiyimin kiran maina don Allah?”

“Maina kaman ya fita shi da alhossain”

“Indai tun dazunne na tabbatar zuwa yanzu ya dawo” bibi ta fada tana zama saman daya daga cikin kujerun hadi da ambatar sunan Allah

“To” tanja ta amsawa bibi tana miqewa ta gyara dankwalinta sannan ta nufi waje.

HUGUMA👑👑👑

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 13

Waya ta sameshi yana yi. Dogon wando ne fari qal a jikinsa da singlet fara itama,sai ya ajjiye wayar yana duban tanja data tsaya nesa da falon

“Mainasara bibi ce take kira”

“d’accord” ya amsa can qasa da muryarsa me sanyi.

Ko daya baiyi niyyan shiga sassan bibi din ba,ya sanyama ransa ma sai tayi cigiyarsa kafin ta sake ganinsa,saboda yana ganin cewa suna da tagomashi wajen lalacewar ginin da ya fara yiwa rayuwar sultana. Saidai kuma bibi din ta wuce ta kirashi yaqi zuwa,don haka ya sauke qafafunshi dake saman table qasa yana ajjiye wayarsa saman kujerar ya wuce zuwa bedroom dinsa.

Kaftan abaya budaddiya ya zura navy blue,kalar data fidda sigar kyawunsa matuqa,haskensa ya fito sosai,ainihin zallar hasken cikakken ba’abzine.

Kamar yadda yake dabi’arsa hannayensa zube a aljihun kaftan abaya din yana qissima abubuwa da dama cikin ranshi. Iskar bayan azahar tana kadawa kadan kadan me cakude da sanyi maras tasiri. Ire iren wannan yanayin suna masa dadi sosai kasancewarsa mutum ras son zafi ko kadan. Hatta da sutura ba kowacce yake sanyawa ba saboda baison abinda zai takura jikinsa.

Da nutsatstiyar sallamarsa ya shiga parlor din bibi. Ta amsa masa tana karantar nazarinsa sanda yake basarwa ba tare daya kalli fuskarta ba,daya daga cikin alamun fushinsa kenan.

“Samu waje ka zauna” bibi ta bashi umarni kai tsaye,ita dinma yau fuskarta ba’a sake take kamar yadda ta saba ba.

Kaman bazai zauna din ba sai kuma ya matsa sofa din gefanta ya zauna a kai bayan dukka wadanda ke zirga zirga a falon sun kau,don basu waje.

“Aliyyu” bibi ta kirashi da sunansa na asali kai tsaye. Sexy eyes dinsa ya daga ya kalli Bibi sannan ya motsa bakinsa

“Kada kace komai maina,mamaki kurum yanzu kake bani” ta fadi tana qare masa kallo tamkar tanason hange meye abinda ya canza a tattare dashi da ya sauya launin mu’amalarsa da sultanan tashi

“Gaba daya ka canza maina,kamar ba kai ba,ka tashi daga mainan sultana ka koma aliyyu haidar,ka tashi daga frèren sulty ka koma wani abu na daban,kana neman zamewa yarinya kamar wani dodo,kamar ba kaine ka raineta da hannunka ba?,kamar ba kaine kaci kashi da fitsarinta ba?,kamar ba kaine kake hana idanunka bacci saboda sultana na kuka ko tana rigima ko bata da lafiya ba,dukka ina wannan kulawar?,tsakaninka da ita yanzu sai kyara sai hantara sai tsangwama,sama da tsangwamar da kakewa kowa cikin gidan nan” bibi ta qarashe fada tana sauke maganganun nata hade da fitar sirrin numfashi,da alama daga qasan zuciyarta maganganun suke fita

“Me yasa bibi?” Ya jefa mata tambayar,idanunta kadan ta qanqance tana dubansa alamun neman ba’asin tambayar da yayi matan

“Me yasa bibi zaku barta ta sangarce bayan kowa cikin gidan nan tarbiyya bai daya ake musu,waye tafi cikin yaran gidan nan bibi?,sai abinda sultana ke so?,sai abinda ya kwanta mata a rai yayi kuma dai dai da raayinta?,bibi wannan ba soyayya bace sam ba qauna bace,ita din diya macace,gidan wani zataje,baki tsoron ta tashi a haka taje masa da dabi’ar da bazai iya ba a dawo muku gida da ita?,wala’alla ni din bana kusa da ku,kune zaku fini jin ciwon hakan,kuma kafin ni na gani ku zaku fara gani kune zaku fara karbar sakamakon”

“Auzubillah……haidar me kake cewa haka?” Bibi ta fada fuskarta na nuna girman da zancan yayi mata. Ba komai saman fuskarsa kaman ma baisan me dame ya cewa bibin ba ya dage dukka girarshi biyu

“Oui(yes)”

“Dukka maza ne zasu iya daukan halin banzanta?”

“Subhanallahi,da gaske ka sauya maina,ka canza,na tabbatar frèren sultana bazai taba fadin haka a kanta ba……to bari kaji,kai din yaro ne da har yanzu bai wuce shekara ashirin da biyar zuwa da shida ba,a dukka matakan tarbiyya banjin kasan wani abu me yawa,bata haka ake yiwa yaro tarbiyya ba,tsanani da matsi basa kintsa yaro ko kadan,ka sanyawa sultana zafi da yawa,kana amfani da irin zafinka na halitta,ita diya mace kwata kwata bata buqatar zafafawar namiji,bare kuma yaran mata da yanzun suke tasawa tarbiyyarsu nada matuqar sulbi da santsi,don Allah maina…..banajin dadin canzawarka kwata kwata,ka koma frère din sultanansa na baya”.

Idanunsa ya lumshe sannan kuma ya budesu, muryarsa a lanqwashe yace

“Bibi na fiki jin rashin dadin dabi’un sultana,na kuma taras da ku ba masu goyon baya na ba wajen maidata hanya,bazan canza ba indai sultana ba zata canza ba,dole ta koma kamar kowanne yaro dake gidan nan” kai bibi ta gyada,tun ba yau ba tasan irin nasa halin. Yana da tarin kafiya da taurin kai akan dukkan abinda ya sanya a gaba ko ya furta zai aikata. Fadin zaiyi abu yana da wuyar ji daga bakinsa,amma muddin ya furta din to babu sauyi,komai dadi komai wuya.

Sake gyara goyon school bag dinta tayi dake bayanta,tana jin kamar ta fada dakin ta rufe yaa maina da duka,ai ita batasan haka yayi nisa wajen qinta ba,batasan haka zuciyarsa tayi zurfi wajen son quntata mata ba,lallai Allah baya bacci da har kunnuwanta suka jiye mata komai. Indai yana tunanin iya tsare gidansa,daci da baqin ransa,fada da hararraminsa zai bashi abinda yakeson yaga ta koma din to tabbas zata tabbatar masa ita din ba tsoronsa takeyi ba,kuma bai isa tabuka komai ba

“Sultana kibi a hankali,kinfi kowa sanin waye frère” wani sashe na zuciyarta ya gaya mata sanda take qissima da irin salon da zata shiga falon

“Idan garwashi ne shi ni wuta ce” ta baiwa kanta da kanta dama zuciyar dake gargadinta amsa,bata kuma sake tsayawa sauraron kowacce shawara daga zuciyarta ba ta sanya kai falon da waqar data zame mata madadin sallama.

Idanunta saman fuskarsa tana nazarin furucinsa daya bayan daya,dai dai sanda siririyar muryarta dake cike da tsiwa ta isa ga kunnuwansu tana rera waqar ado isa gwanja

Allah ka aika munafukinmu qarshen nesa,tafiyar qasa koda lafiya ko babu,kaishi garin da ko kuyanga babu,barshi a can da arziqi ko babu,ni nasha tabara nasha yasin,kuma nasha rigakafin alatsine . Sai ta juya zuwa waqar wani mawaqin qasarsu ta nijer

Munafuki Alla kasheshi,koda safe koda rana ko ma dare ne

Tana maganar ne kanta yana kallon lobby na dakunansu tana kuma nufar can,tamkar batasan da zaman mutane a wajen ba.

Mutuwar zaune bibi tayi,ana kukan targade ga karaya ta samu,ana neman gyara ga sabon ruwa ya ballo. Ko waye kai,komai girmanka muddin ba iyayensa ba baka isa ka ratsa waje bakayi masa sallama ba,kamar yadda duk yadda yake da buqatar shiga guri muddin ba’a amsa sallamarsa an kuma masa izini ba yana juyawa ne ya koma inda ya fito. Wannan ya samu asali ne daga cikakken karatu da tarbiyyar daya samu daga islamic school din da yayi masu kyau a Nigeria.

Har ta kusa shigewa ya kirayeta cikin tsawa,kaman ta wuce ciki sai narkakken tsoronsa dinnan da take qoqarin binnewa ya motsa mata. Tunga taja ta tsaya kana ta waiwayo tana dubansu ba tare data iso inda suke ba

“Koma ki yima mutane sallama” idanunta masu kama da digon zaiba ta dan juya tana bata fuskarta,ta motsa qaramin bakinta dake cike da tsiwa tace

“Nifa na riga nayi sallamata ehe” daga wannan ta juya tana shirin wucewa dakin tare da sake maimato waqoqinta a sarari sosai saboda saqon ya isa gareshi.

Wata baqar zuciya ce ta motsa masa,tabbas sultana dashi take,shi takewa wadannan waqoqin. Uwa uba yau shine zaiyi mata magana tasa qafa ta shure?,tama maidashi mahaukaci?.

Daga sultana har bibi babu wanda yasan lokacin da ya isa dakin. Dai dai sanda take wurgi da komai na makarantarta kamar yadda ta saba tana sake sakin waqoqinta cikin harshen faransanci,ranta fes tana jin ta fara samun nasarar rage haushinsa cikin ranta.

Cire hijabinta yayi daidai da dauketa da marin da yayi,babban dukansa shine marin,bai iya wani duka ba idan ransa ya baci bayan shi. Sanin darajar da fuska take da shi ya sanya bai cika yin dukan ba,zaiyi wuya kaga ya daki wani cikin qannensa,amma wajen iya bada horo su kansu sun tabbatar babu na biyunshi kaf cikin family.

Wata irin gigitacciyar qara ta saki tana dafe kuncinta da hannayenta bibbiyu ba tare data fuskanci meye ya sameta ba. Sautin muryarsa saman kanta kwanyarta tayi saurin ingizo mata me yake faruwa da ita,saidai kafin ta gama daidaita tunaninta ya sake aje mata wani Marin hade da qatotuwar tambayar da batasan da wanne zataji ba,marin ko amsa masa tambayarsa

“Saikin gayamin wanene munafukin cikin gidan nan” yayi maganar yana zare belt din dake jikinsa. Dukka jikinta rawa ya fara yi,saboda ganin fushi muraran saman fuskarsa,uwa uba tunda take bazatace ga ranar da aka sanya madoki aka daketa ba,shine ma mutum na farko kaf fadin rayuwarta da ya taba taba lafiyarta tunda tazo duniya,wannan ya sanya take matuqar razana duk sa’ilin da ya shimfide mata dogayen yatsunsa saman fuskarta

“Waye munafukin nace?!” Ya maimaita tambayarsa yana ware mata lion eyes dinsa da suka sake gigitata,sai ta ware dukka muryarta tana qwalawa bibi da tanja kira

“Wayyo Allah na bibi,zai kasheni,zai kasheni,wayyo na shiga uku”

Yatsansa ya dora saman lips dinsa yana sake fidda mata idanunsa dake danqare da bacin rai

“Kika sake buda bakinki a nan sai na miki dukan da ba zaki qara iya daga yatsarki ba,tais toi idiot(shut up idiot)!” Ya qarasa fadi a tsawace. Dole qanwar naqi ta sakaya ihunta,duk da tana jiyo bibi na bugun qofar hadi da kiran sunanshi da bashi umarnin ya bude,saidai kuma bata da ikon cewa komai.

Stool dinta ya jawo ya zauna a gabanta,ta qanqame jikinta guri daya tamkar me jin sanyi. Ba sanyi takeji ba,tsantsar tsoro ne ya sanya jikinta ke shivering,amma batason yaga hakan daga gareta,hawaye kwance saman fuskarta,ilahirin fuskar tata radadi take mata

“A frère dinki kika sanni ko?,to daga yau ki saka a ranki maina nake a wajenki kamar yadda nake a wajen kowa na gidan nan,zan fiddo miki ainihin kalata tunda na fuskanci kin zama graduate a fannin rashin kunya.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 14

“Dago kanki ki kalleni!” Ya gaya mata da wata a tsawace

“Baki isa kifi qarfin kowa a gidan nan ba,idan ma kinfi qarfin nasu ne ni bakifi qarfina ba,zan iya tattakaki nayi miki dukan da ba’a taba yi miki irinsa ba kuma babu abinda zai faru,daga yau zan kafa miki dokokin da idan kika tsallake guda daya a cikinsu ki tabbatar da kin shiga uku” ya fada yana murza yatsunsa. Idanunta ta runtse tana jin sautin yatsun nasa,wani sabon hawayen ya balle mata,yau ita ya maina yake yiwa haka?,ita ya sanya a gaba yake yiwa wannaj tijarar?,ita ya yiwa irin wannan titsiyen da babu mahalukin da ya taba yi mata irinsa?.

Kimanin minti talatin yana gindaya mata sharudda da qa’idoji,sultana din tana zaune a gabansa ba tare data motsa ko ta furta komai ba. Duka maganganunsa basuyi tasirin komai a ranta ba face wani mugun qulli data yi masa,haushi da tsanarsa na ratsata.

“Kinji dukka abinda nace?” Ya tambayeta da kakkausar muryarsa. Kai ta gyada masa idanunta suna mata wani mugun radadi

“dis-le plus fort(ki daga murya ki fada)!” Ya fadi a kausashe

“Eh” ta amsa da dakusashiyar muryarta.

Da wani mummunan kallo tabi bayansa,tana jin kamar ta bishi tayi masa mugun duka, idanunta tamkar zasu fado har ya fice. Hannuwanta biyu ta saka tana shafar fuskarta. Maruka hudu cikin qanqanin lokaci?,bata taba sanin haka mari yake da tsananin zafi ba sai yanzu tunda baby wata halitta data taba dora mata hannunta saman jikinta da sunan duka sai shi.Dama haka mutumin da aka mara yakeji?,tambayar ta taho mata da tawagar hawaye suka zuwa saman fuskarta.

Daga tanja har bibi taqi kula kowa,juyin duniya amma funfurus taqi tace komai,sai hawaye da taketa yi babu qaqqautawa. Duk wani abu da bibi keyi mata ita ta yiwa kanta shi. A wannan yanayin lokacin tafiya islamiyya yana yi ta shirya. Yana daya daga cikin dokokin da ya kafa mata,bata jira kowa ba ta yiwa driver dinta magana yayi gaba da ita. Saidai ko da suka isa makarantar babu abinda ta tsinana sai kwanciya,har akayi karatun aka gama babu abinda ta maida hankali ta fahimta.

K’arfe takwas na dare tana nade cikin blanket saboda busawar sanyi da aka fara samu lamira ta shigo dakin. Dan kallonta tayi ranta yana mata sanyi da yadda yaa maina din ya sanya sultana din tayi laushi a yau

“Kije ya maina yana kiranki a parloir” sai data hadiye wani abu cikin wuyanta sannan ta bude dara daran fararen idanunta tana kallon lamira da kyau,tanason zazzage masa masifa da tsiwar data cika mata qirji tun safe to amma batason dogon magana a yadda take a fusacen.

Har lamira takai qofa sultana batace komai ba,sai lamira din ta dakata

“Yace ki taho da manuels et cahiers d’exercices naki” faduwa taji gabanta yayi a karon farko,sai ta kauda kai still dai babu abinda tace din har lamiran ta fice.

Kaman ba zata tashi ba sai kuma ta miqe. Jakar makarantarta ta jawo dukka biyun islamiyya da boko ta fara zazzage litattafan ciki gaba daya.

A sanyaye ta bisu da kallo daya bayan daya tamkar yau ta fara ganinsu. Akwai qura tabbas! Shine abinda zuciyarta ta raya mata.

DA ALAMA YAU AKWAI TONON SILILI😂

Cikin qwarin gwiwar nan da taurin rai da zuciyarta ke bata a ko yaushe ta miqe da littafan cikin kyakkyawar handbag dinta,wadda tsara ba cikin tsarabar da aba keyi mata duk sanda zaiyi tafiya kamar babu gobe.

Har ta kusa da bakin qofa ta tuna da kayan da suke jikinta. Kallon kanta tayi,shirt ne da wandon leggings da suka bi lafiyar jikinta,suka kuma yi mata matuqar kyau kamar baby doll. Tana da wata irin qirar kyakkyawan jiki da shape me kyau tun tana da qananun shekaru sosai. Tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,tana jin kamar ta yita dukan maina a yau din nan,ta juya ta koma dakin tana qunaquni

“Haka kawai a wani dameka,tsabar rainin wayo,ko meye na tare masa oho” tayi maganar tana zuge closet dinta.

Lalube lalube ta shiga yi saboda batasan ainihin muhallin da kowanne kaya nata yake ba,tunda ko meye zata saka tanja ke ciro mata,hakanan idan aka kammala wanki da gugansu ita dince dai ke sake zaman shiryasu fes. Kafin wani lokaci ta gaji tubus,sai ta koma bakin gado ta zauna tana haki kamar zata fashe da kuka

“Tanja!” Ta bude siririyar muryarta tana kiranta,abinda ta kwana biyu batayi ba kenan,don tun wancan ranar takejin haushinsu,ta kebe kanta daban,a cewarta sunaji sanda maina din ya tsintstsinka mata mari,ya kuma sanyata a daki zai kasheta,amma ba wanda ya qwaceta har sai da yayi iya yinsa ya qare.

“Tanja….tanja…..tanja” ta sake jero sunayenta a jere.

“Na’am na’am uwaddaki” ta amsa tana shigowa da dan saurinta.

Closet sultana ta nuna mata da yatsa

“Ina jilbab dina suke?”

“Na’am?” Tanjan ta tambaya cikin mamaki,saboda ita dai iya tsahon zamanta da sultanar shine abinda bata taba tambaya cikin sutura ba,ko da mayafi ma yana iya qare zamaninsa a cikin kayanta bata waiwayeshi ba, za’a iya siyoshi ya gama zamansa yakai lokacin badawa a bayar dashi yana sabo

“Allah tanja kin jini sarai,ku dama kullum kunfison baqincikina” ta fada qwalla na cika shiny eyes dinta.

Tanja batace komai ba ta matsa ga closet din ta bude. Sai gata ta fiddo jilbab din sabo kar onion color ta miqa mata,sai tayi tsaye tana dubanta.

Kasa sakawa tayi saboda gaba daya ya dabaibayeta,ta yita juyashi cikin jikinta tana sakin tsaki,tanja na tsaye dariya tana kamata amma ta kanne.

Da gasken ta kasa sakawa,sai kawai ta yageshi ya wurgar tana sakin kuka gami da komawa ta zauna

“Allah sai Allah ya sakamin tsakanina da ya maina,duk shi ya jazamin wannan aikin,Allah ka sakamin” ta fada cikin rawar muryar kuka.

“Tashi ki gani kinji” tanja ta fada tana dauko hijabin. Kamar ba zata tashin ba to amma idan ta tuna qarawa kanta mintuna takeyi daga mintunan da yasa akayi kiranta sai ta miqe din.

Tsaf tanja ta saka mata ta kuma daure mata kan

“Ma sha Allah,fatabarakallahu ahsanul khaliqin” tanja ta fadi tana murmushi. Wani mugun kyau fuskarta tayi cikin hijabin,tanjan tana iya cewa bata taba ganin tayi mata kyau cikin sutura ba irin haka. Tamkar wata diyar larabawa,kyakkyawar fuskarnan dake dauke da quruciya da qarancin shekaru ta fita sosai tsakiyar hijabin.

“Uwaddaki,ya miki kyau wallahi tallahi” tanja ta fada tana dariya. Harara sultana ta jefa mata,sannan ta tura baki gaba tana kwasar litattafanta ta fice,a zuciyarta tana jin cewa tanja tana mata ba’a ce kawai zaginta takeyi,ina wani kyau a nan?.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 15

Tana riqe da litattafan da takeji kamar ta watsar da su tayi ta sanya kai falonsa. Da sauri ta koma da baya sannan tayi sallama tana jin ranta yana baci.

Kansa ya dago daga duba wani littafi dake riqe cikin hannunsa suka hada idanu. Gabanta ya fadi,nutsuwa da tsoron da batasan daga ina suke ba suka saukar mata.

“Wa’alaikummus salam” ya amsa mata yana maida kansa ga littafin. A nutse tattako ta qaraso ta nemi waje ta zauna,cikin sanda ta ajjiye litattafan tana satar kallonsa. Sai data kusa minti biyar a zaune sannan ya ajjiye littafin a gefe,ya miqa hannu ya jawo litattafan nata ya fara dubawa.

Tun da can yasan ba wani abun arziqi zai taras ba,amma abinda ya gani na yau din ya zarce na kullum muni

“Ba arabi ba boko?” Ya daga kai yana jefa mata tambayar da wani irin yanayi dake nuna bacin ransa da kuma mamaki

“Gaskiya mana,dole kije ki zauna kiq zuwa da wuri” ya sake maimaitawa yana jin kamar ya tashi ya zaneta da kyau.

Sake maida dubansa yayi yana sake nazartar littafan,assignment homework harma da classwork kowanne mark dinta zero ne. Littafin haddarta ta islamiyya ba komai akai sai tsalli tsallin ayoyi. Littafin assignment na islamiyya kam blank ne ma,ga question a rubuce amma babu digon amsa ko daya sai sararin gurin.

Wani bahagon tsaki yaja ya maidasu ya rufe,ya tabbatar idan yaci gaba da dubawar sanda zai tsinka mata mari ka bai sani ba,mafi alkhairi shine ya rufe din.

Tambayoyi ya fara jero mata daya bayan daya,saidai bata da amsar kowacce tambaya daga islamiyya har bokon,cikin tambaya ashirin da qyar take iya amsa daya

“Ya rahman” ya fada yana lumshe kyawawan zagayayyun idanunsa da suka soma kadawa. Gaba daya babu komai a kanta,duk wani gini da ya fara mata a baya babu shi. Ta zama bata gane komai a yanzun,lallai wani sabon aikinne a gabansa. Sai yaji gaba daya komawa niamy tanason ta sake barin jiki da ransa,saidai kuma shi kansa yasan hakan bame yiwa bane, karatunshi ya riga ya fara nisa,karatu me wahala da tsada,a gefe guda kuma daukar irin wannan mataki dai dai yake da shiga rigima da ama,gwara aba zai iya fuskantarsa ya bashi uzuri,amma baijin amma zata fahimta kwata kwata,musamman da zai zama batun akan sultana ne.

Zama yayi sosai ya bata lokacinsa ya zana musu jadawalin karatu,lokutta ya zaba na daban da yake available a gida,itama kuma bata komai a sannan. Sanda ya gama ya bata takardar karba tayi kawai ta kalla

“Kan bala’i” ta fada tana jinjina qoqarinsa. Ita zaiwa wannan tsarin karatun?,don ya hanata walwala ko meye?,itakam ba zata taba lamunta wai wani karatu ya shiga rayuwarta ba,akan meye?,bayan ba wani abu da karatun zai tsinana mata,haka ta miqe ta tattara littattafan nata da tarin assignment jingim da ya bata.

Ko takan litattafan bata sake bi ba ta shiga sabgoginta,a tsakanin juma’a zuwa asabar ya bata ayyukan,kuma ba zasu sake zama karatun ba sai litinin. Bata tashi tunawa ba sai ranar lahadi da daddare,a take idanu ya raina fata,ta dauko litattafan amma ta kasa gane komai,sai taja tsaki tana watsar da littafan ta koma ta kwanta,cikin ranta tana qissima yadda zata kaucewa zaman karatun a washegari.

Lallabawa tayi ta fice dab da magariba data fuskanci yaa maina din yana nan,kuma tayi imani sai anyi zaman karatun,wannan ya sanyata ta shirya abinta ta sulale ta fice ko bibi bata sani ba.

Gidansu muhsee ta wuce,daya daga cikin abokanta da gidansu ke bayan layinsu. Ranta fes ba wani fargaba ko tunanin girman laifin data aikata take wucewa kai tsaye zuwa gidan.

Kidan dake tashi a harabar gidan nasu shine ya baxu har wajen gidan. Ta saki murmushi tana jin dadi cikin ranta,ta kwana biyu batayi rawa ba yau zata motsa jikinta yadda ya kamata. Qafafunta har qaiqayi sukeyi mata. Yaune birthday din muhsee,sanda ya tura mata invitation bata taba tsammanin zata samu halarta ba saboda yadda yaa maina din ya matse komai,ya hanata sak ya hanata rawar gaban hantsi,daga islamiyya sai boko,sai kuma tarin assignment din da ya hadata dashi wanda ko yaya ya ganta zaune bata komai tambaya ce akan

“Shin kin gama duk ayyukanki da kika samu guri kika zauna kina raba ido?” Wannan kusan itace tambayarsa ga kowanne yaro ma gidan duk sanda ya ganshi a zaune,muddin yana daukan karatu a hannunsa.

Tana shiga gurin ya barke da ihun murna,dukka qawayensu ne maza da mata cike a gurin. Sosai kanta ya fasu da yadda suka nuna murnar zuwa gurin,tuni ta ware a cikinsu aka shiga hidima da sabgogi ba tare da tana duba lokaci ko tuna cewa laifi zata aikata dingimeme ba.

Tun kafin lokacin karatunshi da ita ya cika ya kammala komai ya sallami su najma da yakewa lesson kaman yadda ya saba duk sanda yake nan,musamman subjects din da yafi qwarewa akai su kuma suke basu wahala.

Tun yana duba lokaci har ya sauke qafafunsa qasa yana jawo wayarsa. Momma ya kira matar oncle bashar yace ta turo saddi yayi masa kiran sultana. Minti uku kacal saddi din ya nemi izinin shigowa sashen nasa ta hanyar yin knocking

“Entrez(shigo) ya fada yana gyara zamanshi. A nutsen ya shigo yana duban maina.

“yaa maina….bata nan” idanunsa akan fuskarsa saddi

“Bata nan?,da darennan a lokacin karatu?,ita da wa suka fita bayan time ne na karatu?” Kai ya girgiza

“Ba’a sani ba,bibi dinma batasan bata nan ba” idanu ya qanqance yana jin zancen banbarakwai

“comment ça se fait?(garin yaya ya faru?)”

“je ne sais pas(ban sani ba)” ya fada a ladabce. Wani iri yaji maganar tayi masa,kaman yaya za’a ce ba’a ga sultanar ba?,kuma ba’a san ina take ba?,duk girma da fadin gidan da yawan security din dake cikin gidan?,idan bata nan ina taje da daren nan?,lokacin da kowa ke cikin gidan.

“Jeka” ya fada yana miqewa daga zaman da yayi,ya lalubi wayarsa ya saka a aljihunsa ya zura baqaqen slippers dinsa yana ficewa a sashen nasa.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

Page 16

Carko carko ya samu bibi da tanja da sauran masu aikin sashen bibi din,harma da su momma dake sassansu. A nutse ya qaraso falon yana duban fuskokinsu,kanshi tsaye ya tura tambayar ga bibi

“Garin yaya aka rasata?”

“Bana ce ba maina,don taci abinci da yamma bayan sun taso a makaranta,ta shiga daki tace zata kwanta kafin ayi sallar magariba,tanja ta shiga tada ta saboda ta samu sallar ta tarar ba kowa a ciki” Shuru ya biyo bayan bayanin bibi,yayin da maina ke nazari kadan kadan cikin kwanyarsa

“Inaga koda oncle umar a kirayeshi a shaida masa,dare yana yi kada ta fada wani hannun” mommy matar oncle umar din ta fada fuskarta na bayyanar da tashin hankalin da take ciki

“Non(a’ah),basai kun kira kowa daga cikinsu ba,zaku daga musu hankaline tunda har yanzu babu tabbacin wani abune ya sameta”

“Wani abune mana maina?, yarinyar na cikin dakinta a nemeta a rasa?” A nutse ya zubewa bibi kallonsa,bayason yayi doguwar magana ne cikin mutane,amma cikin jikinshi yakejin bawai wani abu bane ya sameta ba

“se détendre(relax)elle est en sécurité in sha Allah(lafiya qalau take in sha Allah” ya fada yana daga mata hannunsa

“Ina goumar?” Yayi tambayar yana wuwwulga idanunsa cikin falon.

Babu shi a wajen,don haka ya aika saddi yayi masa kiransa. Ba jimawa suka shigo tare don shi din bame yawo bane,mayen karatu ne,duk inda zashi baya wuce farfajiyar gidan ko garden na gidan,yayi nisa shine ka sameshi qarshen layinsu cikin wata qaramar majalisa da sukanyi duk yammaci,ita dinma ba kullum yake fita ba

“Karbo key din mota wajen bibi ka fito muje” ya fadi yana fita a parlor din ya barsu a nan a tsaye.

Goumar din Bai tambayi komai ba har ya tada motar suka fice a gidan. A nutse motar ke ratsa layin nasu har suka kai qarshensa. Yana qoqarin hawa kwalta sai ya canza shawarar yabi ta layuka,wannan ta sanya ya dan rage gudun yabi ta layin bayansu

“Ka sakamin ido kawai akan hanya goumar”

“Toh ya maina” ya amsa masa yana gyara zamansa cikin motar.

A slow motar ke tafiya,zaka tsammaci gurin tsaiwa take nema,dukka fitilunta ya kunna ya bada full light yadda zasu samu damar ganin abinda ke bayansu da gefen da gefansu da kuma nesa da su,daga shi har goumar babu me iya cewa komai. Kowa yaja bakinsa ya tsuke,amma kuma kowa da tunanin dake cikin zuciyarsa.

Tun daga farkon layin kidan ke tashi kadan kadan,kana natsowa ta wajen gidan yana sake qarfi a kunnuwanka. A tare suka kalli juna shi da goumar,sai kowa ya dauke dubansa ba tare da yace komai ba.

Sake rage saurin motar yayi. Dai dai sanda yazo qofar gidan sai yayi kaman zai tsaya amma sai ya fasa

“Gidansu waye wannan?”

“Gidansu sultee,gidan alhaji mamman bashar” kai mainasara ya gyada,sai ya fara neman gurin tsaiwa daga qarshen katangar gidan. Haka kawai yaji yana buqatar tsaiwa a wajen hakanan kuma haka kawai din yaji kaman sultana din zata iya kasancewa cikin gidan.

Ya kammala parking ya kashe motar,ya fara kwantar da kujerar,sai a sannan goumar ya kalleshi

“Yaa mainasara……ya muka tsaya?, ba tafiya zamuyi bane dare yana sake yi”

“Ka kula da me shiga da kuma wanda zai fita” maina ya fadi masa yana kwantar da jikinsa a kujerar gami da lumshe fararen idanunsa. Da mamaki goumar ya maida dubansa a kansa

“Amma……kana tunanin zamu samu sultana a nan wajen ne?”

“peut être(wataqila)” ya amsawa goumar tare da maida idanunsa ya lumshe kamar wanda ke shirin yin bacci

“Banda abin yaa maina mu da muka fito neman yarinyar da ta bace sai ka kawomu nan?,sannan kuma har ka kwanta kace zakayi bacci” goumar ya fada cikin ransa. Duk da haka sai ya maida kansa ga window din motar don yin abinda ya sanyashi.

Tana tsaka da rawarta hankali kwance,bata ma wani tuna yadda zata koma gida da kuma irin qurar da ka iya tashi sai taji kaman fitan wani abu daga jikinta. Gabanta yayi mummunan faduwa,a hankali ta sauke hannunta dake sama tana jujjuyashi zuciyarta na bugawa. Kada dai ace wannan abun da tanja tace mata zai dinga dawowa duk kowanne wata ne ya sake dawo matan.

“Na shiga uku” ta fada qasa qasa. Daga yadda taji dumi yana ratsata tabbas shine,babu komai a jikinta banda pant da dogon wandon dake jikinta,ta yaya zata fita a wajen ba tare da sun tsaidata har jikinta yakai ga baci ba?. Akwai qawayenta wajen,hasalima cikin gidan nasu akwai qawarta,to amma ta yaya zatace musu ga abinda takeyi?,bayan kuma babu wadda ta taba ce mata tana menstruation?.

Cikin dabara ta fara zame jikinta daga wajen a hankali a hankali. Bata tsaya ba sai data tabbatar ta zamewa ganinsu sannan ta doshi qofa. Ranta a jagule yake sosai,ita harga Allah batason wannan abun da tanja tace mata kowacce mace data gani tana yinsa,ita inda za’a bata magani ta daina yinsa kwata kwata da tafison haka,gani ma takeyi ‘yan iska ne suke yinsa,kwata kwata ma shekararta nawa da zai dinga zuwa yana takurata?.

Cak ta tsaya sanda ta isa bakin gate din gidan,sai a sannan tunaninta ya dawo mata dai dai. Ta yaya zata koma cikin gidan ba tare da kowa ya ganta ba?,tasan zuwa yanzu zaiyi wuya idan ba’a fara nemanta kusfa kusfa cikin gidan ba.

“Ki basar kawai kiyi shigewarki,ko ‘yan guards kada ki kalla” wata zuciyar ta bata shawara

“Ya maina fa?” Wani sashe na zuciyarta ya tambayetan iya tambayar kawai sai data sanyawa gabanta faduwa,sai ta cije lips dinta ta furzar da Iska tana qanqance idanu.

“Idan kika shiga dakinki kika kulle kikaqi budewa ai dole ya haqura” wata zuciyar ta sake gaya mata. Kai ta jinjina cikin gamsuwa da wannan shawarar,sai ta soma takawa tana fita daga gidan tare da baiwa kanta qwarin gwiwa,ta wani gefen kuma tana takatsantsan da takunta gudun kada jikinta ya baci.

“SULTANA MAYAK’I” aka ambaci sunanta daga cikin motar dake sako kai layin. Kanta ta daga tana duban motar da aka sauke glass dinta. Yarane matasa su biyu,wanda dukkansu ba zasu haura shekaru sha hudu zuwa sha biyar ba. Kowannensu kansa dauke yake da sassalkan gashi irin na ainihin buzaye,farare qal suna diban kamanni da juna. Koda ba’a gaya maka ba zakasan cewa yaran gata ne kamar yadda sultana take ‘yar gata kuma sangartacciya. Akwai alamun hutu me yawa a tattare dasu.

“Tsaya a nan zamuyi magana da wancan babe din,saura kuma ka matsa daga inda kake,ko parking wallahi bamuce ka gyara ba” daya daga cikin yaran dake cikin wani lafiyayye kuma tsadajjen trouser da shirt ya fada,sanann yayi tsalle yana saukowa daga cikin motar dayan ma ya biyo bayansa.

Tana tsayen tana kallonsu har suka iso inda take tsayen. Da wani banzan kallo take kallonsa,batasan ma sun gayyaceshi ba da duk yadda take da son zuwa irin wadannan wuraren ba zata zo ba. Duk da rawar kai tsiwa da tarin surutunta,amma ita din mutum ce da ba da kowa takeson mu’amala ba,hakanan komai sonka da jama’a sukeyi idan bakayi mata ba sam ba zata taba shiga shirginka ba.

“ma petite amie(budurwata)” daya daga cikinsu wanda yayi warning driver dinsu ya fada yana murmushi

“ma petite amie?” Sultana ta fada cikin tsantsar mamaki tana masa wani kallon banza haushinsa yana cikata. Ya maidata ‘yar iska da har zai kirata budurwarsa?.

“Kaga fa bata gane ba,yau dai ga dama ta samu kawai ka gaya mata” kai ya jinjina alamun gamsuwa,har yanxu yana murmushin yace mata

“Sultana Je vous aime(sultana ina sonki)” idanu ta zaro dukka waje saboda ba wanda ya taba cewa wai yana sonta din sai abdul din, hasalima ko hira me kama da wannan ita da qawayenta basu taba yi ba,iyakarsu hirar waqoqin da sukayi dadi da sababbi,wace zatayi birthday ko ta hada musu picnic,yaushe zasuje shan iska da sauransu

“je quoi ??” Ta tambayeshi galala tana masa duban sakarai zuciyarta tana quna

“Je vous……” Bata barshi ya qarasa maimaitawa ba ta daga hannu ta shareshi da mari tana huci

“Ashe mahaukaci ne kai?,dan iska kawai dalla matsa ka bani waje na wuce,banza” shafa gurin yakeyi marin da zagin nata suna hasalashi,sai ya miqa hannu gareta daidai sanda maina yayi wata zabura ya miqe ya zauna sosai,bai kuma bata lokaci ba ya kama murfin motar ya balle ya fice da wani mugun zafin nama.

A tsorace goumar ya bishi da kallo,ashe duk abinda ke wakana yana kallo kenan?,tun daga fitowarta har xuwa yanzu,a yadda ya jishi shuru idanunsa kuma kaman a rufe bai taba kawowa yana kallon komai ba,sai shima ya bude murfin motar ya mara masa baya.

Baya taja a zafafe cikin hasala ta fara auna ma abdul din zagi

“Ka sake ka tabani ka gani,banza dan iska,kana sona?,to ni ba ‘yar iska bace ma nemi irinka ‘yar iska kuyi soyayya,soyayyar banza soyayyar wofi,to idan baka sani ba bari na gaya maka soyayya iskanci ce,ni kuma ba ‘yar iska bac……..” Maqale mata maganar tayi a maqoshi saboda ganin yaa maina din da tayi a gabansu. Duk wani dakiya da taurin zuciyarta sai ya gagara ko ina na jikinta ya dauki rawa,ta soma ja da baya da baya qafafunta suna shaking.

Kallo daya ya yiwa su abdul suka arta zuwa motarsu har suna gware da juna. A idanunta suka kai ga motar tasu,sai ta juya da wani bahagon sauri tana lalubar hanyar gida.

Fincikarta taji anyi,kafin kuma ta gama gane abinda yake faruwa har ya soma janta ya watsata cikin mota. Seat din driver ya koma ya tayar da motar ya figeta yana fita a layin.

Tsamo tsamo tayi cikin motar jikinta yana rawa,goumar ne keta surfa masifa kamar zai ari baki. Idan yayi da.hausa ya koma France sai ya koma yarensu na buzaye har suka isa gida.

Qaton hon ya dinga danna musu babu qaqqautawa har sai da ya taso dukka security na gidan. Suka bude qofar ya shiga da motar ya tsaidata tsakiyar harabar gidan ba tare da ya isar da ita parking lot ba

“Dukkanku baku da amfani,meye amfanin ku da bazaku tsare shiga da fitar kowa ciki da wajen gidan nan ba,duk yawanku kuna meye da har yarinya qarama zata iya ficewa akan idanunku ba tare da kun sani ba!” Ya qarasa fada maqogwaronsa kamar zai fashe saboda fushi da bacin rai. Duk wata jijiyar kansa ta tashi rada rada. Waiwayawa yayi ga motar ya bude ya saka hannu ya finciko sultana,cakewa tayi tsaf tana riqe hannun motar cikin nuna kafiyar shiga cikin gidan.

“Ka sakeni zan shiga da kaina” ta fadi cikin ranta tana tabbatarwa yau asirinta ya gama tonuwa,kuma lallai yau sai kowa yasan tana menstruation,don a yadda takeji a jikinta ta riga da tayi stain(tache) wannan ya sanya ta sake kafewa taqi motsawa gudun tonuwar abun boye da zai iya sanyata ta kunyata.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 17

Taurin kai da zallar kafiya kawai ya hango cikin idanunta,wannan ya sake zafafarshi ya daga hannu zai wanke fuskarta da mari,abu daya da yake sanyawa ya samu sasaauci akanta. Har ta runtse idanunta tana jiran jin saukar marin,zuciyarta na ayyana mata muddin ya sauke tafukan hannunta saman fuskarta babu makawa sai ta haifar masa da dana sani,wannan wani alqawari ne data daukarwa ranta. A duk ranar da yayi kuskuren sake taba lafiyar fuskarta ya maretato a ranar sai ta sakashi yayi nadamar aikata hakan,wannan alqawarinta ne,muddin tana numfashi.

“A’ah,ya haka maina?,kul……” Muryar bibi ta dakatar da shi tana takowa gurin tana daga qafarta da qyar saboda ciwon qafa da yake dan damunta lokaci lokaci. Hannu ta sanya tana karbarta daga hannunsa

“A ina kuka samota?” Bibi ta fada tana riqeta da kyau tashin hankalin kan fuskarta yana bayyana qarara

“Bibi bansan na fita ba nima,ciwon mara na dinga yi ni kadai cikin dakin,sai na dinga jin bazan iya zama ba shine na fita nasha iska” qaryar data sambado tayi daidai da sauka da idanunsa sukayi kan dogon wandon jikinta ruwan toka wanda da kadan top din jikinta ta rufe mazaunanta dake da wani irin shape da yake fita yanzu da kadan kadan saboda girma da ya fara zuwa.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kawai ya fada yana kauda kansa. Ranar da nafessa ta fara menstruation ya tuna. Tana kwance a dakin bob cikin sutura da rufin asiri,kaf gidan babu wanda yasan da hakan ma,shi ta fara gayawa kuma shine ya fara mata tunin karatunsa da akayi musu a islamiyya. Har tayi nisa da farawa bibi ko (mamma/mahaifiyarta) basu sani ba. Yau ga diyar nafessa nata ya sameta tana gantali bisa kwalta,ya rabbb…… sultana kuwa idan akace zakka ce za’a ce anyi kuskure ko an fadi ba dai dai ba.

Kasa jurewar tsaiwarsu a wajen yayi ga masu aiki,idan yanzun shi kadai ya gani waye da waye next da zasu iya gani?,wannan tunanin ya sanya ya warceta daga hannun bibi yayi gaba da ita,bai ko tsaya sauraren bibin dake faman qwala masa kira tana son tsaidashi ba.

Tsoro ya sanyata kukan da bata shirya ba,tasan yau din ta shiga uku ta lalace. Abinda ya bata mamaki,duk yadda tayi zaton dokuwa zatayi ba haka bane,don dakinta ya wurgata ya juya yana barin sassan nasu.

****Karfe goma harda kusan mintuna ashirin da bakwai ta isa qofar dakin nasa. Sanye take da wani material me azabar tsada da daukar idanu,kamar yadda yake sunnarta ce sanya suturu masu tsada da daraja,ba kuma wai don alfahari ko fariya ba, a’ah ta isa ne ta kuma kai ta sanyasun. Tun asali da kuma tushenta ta fito ne daga gidan arziqi da kuma wadata,wadatar da taso ta zama sanadiyyar rushe aurenta da ABA. Karin maganar MATAR MUTUM KABARINSA itace tayi tasiri,ta kuma yi ruwa tayi tsaki wajej tabbatuwar aurensu,yau gashi harda zuri’ar samari uku a tsakaninsu. Kalar yadin ruwan sararin samaniya ne da aka yiwa ado da gold color,wannan ya sanya ta yane gashinta me santsi da golden mayafi. Kyawunta da ajinta ya fita sosai,hakanan adonta ya sake boye shekarunta.

Sau biyu kawai tayi knocking qofar ya taso ya iso bakin qofar yana budewa,don qamshinta kawai ya isar masa da wacece

“bonjour(barka da safiya)” maina ya fada yana fitowa zuwa falon nasa

“Ka tashi lafiya?” Ta amsa masa tana takawa zuwa falon itama

“Me yake damunka maina?,jiya bakaci abincin dare ba,yau lokaci yana neman gotawa baka fito ba” ta tambayeshi tana kallon idonsa.

Hannu yasa ya murza goshinsa yana jin bacin ran dake ransa tun jiya har yanzu yana taso masa

“suis désolé(am sorry),zan fito yanzu naci zan shirya” boyayyar ajiyar zuciya ta saki tana juyawa

“Ka shirya gaba daya don zaka kaini gidan dezatou,conducteur na(driver)baya nan”

“d’accord(okay)” ya amsa mata yana dubanta har ta fice daga falon. Ajiyar zuciya ya sauke me qarfi yana komawa ya zauna saman kujerar falon,jiya kwana yayi zuciyarsa na gaya masa ya bar sultana da su bibi suyi duk yadda sukaga dama,tunda hakannan suka tsarama rayuwarta,bashi kuma da wani mataimaki a cikinsu din da yake gani sune dukkan wani jigo kuma ginshiqi na rayuwarsu gaba daya.

Idan yayi kamar yayi na’am da hakan kuma sai zuciyarsa ta tuna masa da NAFESSA,anya idan yayi hakan ya kyauta?,ya kumayi adalci?,hannunka yana rubewa ne ka yanke ka yar?.

“Kada ka sake saka hannu kace zaka daketa,diya macace ita” Maganar aba kenan da suka zauna da shi bayan ya dawo gida a daren jiya

“Zata daina,wani abun akwai quruciya a ciki,amma da sannu zata daina,tsanani baya tarbiyya mainassara” Kalaman aba ya sake dawo masa.

Kadan yadan daki hannun kujerar da yake kai sannan ya miqe yana komawa bedroom dinsa.

Yaja lokaci a falo yana tariyar abinda ya farun jiya,don haka a yanzun adan gaggauce ya shirya cikin wata shadda gezner da aka yiwa dinkin zamani,ya zauna masa das a jikinsa ya kuma yi masa kyau,duk da cewa shi din ba ma’abocin sanyasu bane. Sassanyan turarensa na ko yaushe ke tashi a jikinsa,ya tsaya gaban madubi ya gyara sumarsa me santsi da baqi ya kuma gyara gashin fuskarsa. Fuskar ta fita sosai,ta bayyanar da zallar kyawu irin na buzun asali.

Yana tafe yana daura agogon hannunsa tare da duba lokacin da ya kashe. Dab da zai gifa sassan bibi wanda tun jiya bai sake komawa ta can ba,daidai lokacin da sultana ke fitowa hannunta dauke da sabuwar game dinta tana nufo harabar gidan,da alama tana neman me saita mata ne.

Kallonta yayi sama da qasa da wani bahagon kallo. Vest ce a jikinta me siririn hannu da iyakacinta gwiwa,sai wando ta ciki wanda bai qarasa sauka idon sawunta ba. Kanta a bude babu koda hula bare ayi batun mayafi,sai sassalkan gashinta dake reto har dokin wuyanta wanda yake daure cikin siririn ribbon. Tsaiwa tayo cak qirjinta yana bugawa. Duk tsaurin idanunka idan ya saka maka lion eyes dinnan nasa sai ya cire maka duk wani qwarin gwiwa taka. Taku biyu tayi baya saita juya da sassarfa tana komawa ciki.

Qwafa yaja zuciyarsa na sake zafafa akan zafin jiya. Duk wani abu da za’a hanata ita kuma shi takeyi. A age dinta sam bai kamata tana fitowa koda veranda dinsu a haka ba bare ta kawo farfajiyar gidan. Ga security zaratan qatti dake kai kawo a wajen.

Da wannan qarin takaicin ya jefa qafansa falon ama din nasa. Ya sameta tayi nisa a breakfast dinta don har ta kusa kammalawa. Kujera yaja ya zauna,daya daga cikin masu aikinta data fara tattara abinda aka bata a wajen ta matso da zummar serving nasa sai ya daga mata hannu yana dakatar da ita.

Abu biyu kadai ya buda a ciki,sai ya bari ya soma zuba Black tea,sam bakinsa bakinsu babu wani dandano. Shi kansa yasan damuwa ce qasan ransa,ya sani yana da fushi sosai da zuciya,shi yasa yake yawan kaucewa abinda duk zai bata masa rai.

Duk yadda yake cakalar abincin ama tana ankare da shi,taso kawar da kai tayi banza da lamarinsa amma ta kasa jurewa,wacce jaraba ce ne wai irin haka?,har yanzu jinin nafessa baibar wahalar da rayuwarta ba?,wai sai yaushe?.

Mug din tangaran din hannunta ta ajjiye,banguls din gold guda biyu dake hannunta suna bada sauti

“Inaso ka shirya cikin kwanaki uku ka koma makaranta,bana kuma buqatar zuwanka a nan kusa” ta baiwa maina umarnin kanta tsaye tana kafeshi da kallo. Shima ita yake kallo kafin ya janye dubansa. Wanne irin umarni ne haka na kai tsaye daga wajen ama din?. Kamar tasan tambayar dake Kai kawo a zuciyarsa kenan ta dora da maganarta ba tare data damu da yadda yayi sak da jin maganar tata ba

“Bana son ganin gilmawarka cikin gidan nan maina,ka fita a harkar ‘yarsu,haka sukeson ganinta shin kai meye naka?, nafessa dai ko?,duk yadda kakai ga son nafessa ma wanda ya fika sonta ya dauke abarsa,ka rabu da nafessa ma bare sultana?…… abu na qarshe da zan gaya maka shine,nima ban yarda ka sake kai hannunka fuskar ‘yarsu ba,diya macace data soma girma,banaso kada na sake ji ko gani” ta qarasa fada tana nunashi da yatsa kafin ta sauke hannun nata ta miqe tana tura kujerarta baya sannan ta fara sauka daga dining area din tana cewa

“Zan shiga mu gaisa da bibi,ka dauki key din farar Ferrari na” daga haka tayi gaba taba qwalawa me aikinta kira kan ta dauko mata hand bag da mahadin shoe dinta.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 18

Dezatou din na daya daga cikin manyan abokan business na ama,sannan kuma qawa a gareta ta hannun damanta. Mansion House ne da ya cancanci wannan sunan,me dauke da manyan katangu da kuma gini na alfarma tsakiyarshi. Gate na biyu suka zarce kai tsaye bana sun samu tsallake gate din farko, already tasan da zuwansun,don haka maina yana tsaida motar tana isowa wajen.

Gwanar fara’a ce da son mutane,don haka fuskarta wasai da fara’a take cewa

“Wai wai,yau maina nake gani hamdee…….da kin gayamin tare kuke ai da na shirya tarbar baqo na musamman” dan murmushi ama tayi,tana jin dadi sosai akan yadda dezatou ke nuna qaunar maina a fili. Tadan kalleshi kadan,tasan cewa kawai ya kawota ne saboda fushinta na jiya.

Har sunyi gaba dezatou ta juyo

“Shigo mana maina,ya zaka tsaya a nan,kaimafa nan din gidanku ne” kansa ya girgiza kawai yana dan sakin fuska kadan

“Zan jira nan cikin mota,akwai wayar da xan amsa”

“Bazai shiga bafa dezatou,rabu dashi” ama ta fada tana yin gaba

“Shikenan,zan turo meena ta kawo maka ruwa” ta fada tana bin bayan ama.

Cikin motar yayi zamansa yana latsa wayarsa,shige shige kawai yakeyi cikin Instagram yana bibiyar pages din da yakeso yake kuma bin labaran da suke dorawa kullum.

Wani dogon tsaki yaja ya sanya tafin hannunsa yana dafe goshinsa kamar wanda goshin nasa ke masa ciwo,sai ya maida kansa ya jinginar ga kujera yana lumshe idanunsa yana jin zafin abinda ya gama karantawa a wani page yanzu yanzu. Labari ne akan fyade da aka yima wata budurwa,sau da dama yakanyi dana sanin daukar wayarsa aduk sanda yaci karo da labari makamancin wannan,ba kalmar da ya tsana ya kuma qi jininta irin kalmar FYADE din.

Knocking din glass din windown qofar da aka fara yi shi ya sanyashi bude lumsassun idanunsa a hankali.

Tana tsaye daga gaban window din,hannunta riqe da wani kyakkyawan vanish tray me kyau sosai samanshi wani irin cups ne qananu da gorar ruwa data lemo,sai wani qaramin tray din dake dauke da wasu nau’ikan snacks.

Farar buzuwa ce tas,doguwa sosai,fuskarta dauke da fara’a,sanye cikin riga da wando jeans,kanta wani siririn dan kwali ne da yafi kama da yadi wanda ta daure gashinta da ya sauko kafadarta ta hagu. Budurwa ce da duka duka ba zata wuce shekaru sha takwas ba. Fuskarta shimfide da murmushi take dubansa. Sai ya dauke kansa sannan yasa hannu ya sauke glass din,a maimakon ya bude mata cikin motar kamar yadda take da buqata

“Yaa maina,ta yaya zan saka maka tray din.” Ta tambayeshi tana narke wuya cikin shagwaba. Kanshi ya sake daukewa ransa yana baci. Baisan me ya sanya dabi’ar saka qananun kaya da rashin damuwa da hijab ko babban mayafi ta zame musu al’ada ba. Kaman meenatun a yanxun yana ganin ta wuce munzalin yawo da irin wannan suturar,amma su a wajensu basu ga hakan ba,hasalima dai dai ne.

“Na gode,zaki iya maidawa ciki” ya amsata ba tare da ya waiwayo ba.

Dukka gwiwarta ya kashe mata da Maganarsa,tunda mommy dinta tace mata maina dinne yazo takuma kai masa ruwa da snacks hankalinta ya dauku. Ya jima yana burgeta,ta dade tana qissimashi cikin ranta a matsayin miji,saidai tana mugun shakkarsa,yana kuma yi mata matuqar kwarjini sosai,don koda taje gidansu daga gaisuwa babu abinda yake sake hadasu. To yau din tana ganin ta samu wata babbar dama da ko yaya zatayi wani motsi da zata isar masa da saqon zuciyarta,sai gashi shi din kuma ya katsi hanzarinta.

A sanyayen ta juya tana komawa cikin gidan,wanda da shigarta da kadawar wayarsa duka ba’a yi minti guda ba. Ama ce,sai ya daga yana saka wayar a kunnensa

“Aliyyu”

“Na’am” ya amsa mata

“Wanne irin shashanci ne wannan?,ya yarinya zata kawo maka ruwa ka maidota bakasha komai ba?,wannan ba maida alkhairi baya bane?”

“Afwan” ya fada a gajarce

“Gatanan dawowa,koda ruwan kasha ladan kyautata makan da tayi”

“In sha Allah” ya sake amsawa ama din sannan ta kashe wayar.

Iska ya furzar daga bakinsa yana kallon wani guri na daban. Ta cikin madubi yaga tahowarta,don haka kafin ta iso ya bude side din da yake,abinda ya yiwa meena din dadi sosai ta saki murmushi sanda ta iso tana miqa masa ruwan.

Hannu ya sanya ya dauki gora daya yana cewa

“Na gode” sai ya maida qafafunsa cikin motar yaja murfin ya rufe a hankali. Dan saroro tayi kafin kuma ta juya a hankali tana sake komawa cikin gidan,ranta duka a jagule babu dadi, wato kisan mummuqe yayi mata ruwa ne ya dauka kuma yayi godiya,ya yiwa amansa abinda takeso ba wani qorafi kuma da zata kai.

Sun dan jima suna waya da sultan kafin ama ya iskoshi. Tare suka fito da hajja dezatou din da meena dinma kanta. Tanayi tana satar kallon maina din har suka gama sallama,sai ta matso saitin window dinsa cikin siriryar murya take magana bayan ta miqa masa ledar turaruka

“Yaa maina…..ka gaida gida mun gode sosai da ziyara”

“Au yama gaida gida shi daya meena abun ‘yar haka ne?” Ama ta fada tana kallonta cikin dariya. Dariyar tayi itama tana dan sunne kai

“Kiyi haquri ama,ki gaida gida kema mun gode”

“Banaso,sai dana roqa” ta fadi cikin dariyar tsokana maina yana tayar da mota.

Shuru ne ya fara biyo baya cikin motar kafin ama tayi magana

“Kaga meena ko?,yarinya nutsatsiya me hankali,kullum daga makaranta sai gida” ama din ta fadi

“Uhmmm” mainan ya amsa mata

“Ba ruwanta ba surutu ko hayaniya ko rawar kai,shekararnan zata gama karatunta,hajiya dezatou so takeyi ta bada aurenta ko kudinta a kawo idan yaso saita dora karatunta”

“Uhmmm” maina din ya sake fadi

“sanda zataci rabin karatun sai ayi auren,kafin takai ga haihuwa ma qila ta kammala karatunta”

“Hrmmmm” ya kuma fadi idanunsa suna kan titi. Wani kallon takaici ama ta bishi da shi

“Hala kam kurmantaka ta sameka maina?” Ta jefa masa tambayar cikin hasala. Kadan ya waiwayo ya dubeta sannan ya maida dubansa ga titi

“Me ya faru ama?”

“Ya ina baka labari kaman me ciwon baki?,daga hmmm sai hrmmm?” Dariya taso qwace masa amma ya daure,ya fuskanci inda ama din ta dosa tsaf,saidai kuma shi sam baiga macen data dace ya aureta ba kaf fadin niger da maqotanta,a yanzun dai bai gani ba,shi ko kusa ko alama meena batayi masa ba,baiga wani abu tattare da ita na musamman ba,shi da yakeson macen da ilimin addini suka ratsata ainun,ilimin boko dinma ya samu mazauni a wajenta,macen da shigarta ta banbanta da shigar matan qasar nijer ma gaba daya,shidai a yanzu cikin qasarsu baiga matar aurensa ba,kaf cikin matan da yake gani baiga wadda ta taba burgeshi koda kuwa sau daya ba

“Kiyi haquri ama,ai labari kike bani,bazaiyiwu kuma na katseki ba”

“Kaji dashi dai……ni meenatu banga ta dace da kowa ba saikai,ita nake maka sha’awa,saboda haka ka maida hankalinka,zaka saka rana ka koma ku sake ganin juna kai da ita”

“Allah yayi zabi mafi alkhairi” kawai yace da aman. Babu wani zafafawa,shi yasan halin ama,a yanzun rigima kawai takeji,shi yasa ya lallabata aka bar maganar a haka. Yanzun banda rigimar ama shi daketa kiciniyar ganin ya zama cikakken likita kuma soja wa yake ta wannan batun?,baijin yanzun zai kalli ma wata diya mace,har sai ya kammala cika mafarkinsa da tun yana yaro qanqani yakeyi.

Suna parking harabar gidan suka taka zuwa haraba ta biyu qasan rumfar da aka tanada saboda hutawa ya hanga cike da matasan yara,koda ya duba still dai sultana ce gang leader. Agogon hannunsa ya kalla ranshi yana baci,dai dai lokacin da ya dace ace tana islamiyya amma ta tara mutane ana buga game ana ihu.

Dole ya dauke kansa ya kuma taushi zuciyarsa yayi wucewarsa ciki,amma na ankare da shi,hakan kuma da yayin ya kwantar mata da hankali,ko banza tasan aliyyu din me biyayya ne.

Ta gabansu ta wuce,kusan hada baki sukayi suka gaidata. Wani abu guda daya dake bawa kowa mamaki cikin gidan. Yadda sultana din ke ganin girman ama ainun cikin gidan,tana cikin jerin sahun mutum ukun da ko meye sukayi mata bata iya maida musu martani.

Ita dinma kadaran kadaham ta amsa musu tana wucewa ciki.

**** To cikin kwanakin ukun da ama tace masa a cikinsun ya shirya ya koma makarantar. Abinda ya sake baiwa sultana dama tayi wata irin sakewa,komai nata gaba gadi take yinsa,koda bibi ta soma fada yanzu zata saki kuka,kukan da yake mugun raunata bibi din.

Hankalinta kwance ta baje kolinta,koda akayi hutu ma,dogon hutun da yakan dauki dalibai a qalla wata uku tafiya tayi yawan hutu abinta cikin dangi da ‘yan uwa da suke abun arziqi tasu tazo daya. Abinda ya sake taka muhimmiyar rawa wajen koyon abubuwa da yawa a tattare da ita,saboda kusan duk gidan da taje din gida ne da yaran gidan basusan wani abu waishi takura matsi ko sanya takunkumi ba

(Kira a nan a gareku iyaye,bawai yara sunyi hutu ba a dauki kuma dabi’ar zuwa hutu gidajen ‘yan uwa,a kula da inda yaro zayaje,a tabbatar inda zaije din saidai ya koyo wasu zababbun kyawawan halaye bawai ya sake bankada ko azama cikin nashi dabi’un da akeson rabashi da su ba).

Duk da maina din ya zare hannu da jiki da yawa daga cikin sha’aninnikanta amma hakan bai sanya a boye ya zare hannu daga kanta ba,a duk sanda yazo gida hutu yana biye da komai nata,abun da yake sake bata masa rai na rashin ci gaba akan dabi’unta saima koma baya da ake sake samu. Tuni a islamiyya dukka yaran gidan da suke aji daya sukayi gaba suka barta. Don su najma da lamira yanzun haka suna ajin sauka,watanni kadan zasuyi khatama. Ko a boko dinma don kawai tsarin makaranta ne na ‘ya’yan masu dashi,abinda ya tseratar da ita kawai kenan,amma a matakin karatun dake cikin kanta duka duka bai wuce ace a sannan tana primary ba.

Abun yana daga masa hankali ta yadda kowa ya gaza hango abinda shidin yake hangowa,ko kuma yace me ruwa da tsaki da kuma damar sakata ko hanata suka gaza gano hakan. Ba abbansa kadai ba,hatta oncle bashar da oncle umar din suma duk sammakal. Wata irin soyayya ce gaba daya ta uwarta da kakanta wato dan uwansu suka aza mata,wani irin gata da ko quda basuso ya cutata mata.

Ama dinsa ce kadai yake hangen tana hangen abinda yake hange din,zuciyarsa ta jima tana gaya masa zata iya tallafa masa wajen taro sultana. Yana shakkar tararta da maganar,amma ranar da abun ya cishi tura dole ya isketa da batun.

Wani babban album ne a hannunta amma saita rufeshi tana kallonsa

“Maina,ka cireni daga wannan batun kwata kwata,ba hurumina bane,kai kafi kowa sanin haka,ni zan taba diyar nafessa?,a wanne matsayin kenan?,hatta da ubanka ka manta kallon da yakemin a kan sultana?” Kansa ya mirgina gefe,wannan maganar ta tsahon shekaru kudan sha uku zuwa sha hudu ta gaza mutuwa

“Karki duba wannan duka ama”

“A matsayina na wa?” Ta jefa masa tambayar

“Yarki ce ama jikarki ce kema”

“Kaine kaga haka,tashi ka bani guri maina,ni bana sanya kaina a abinda bai shafeni ba ko zai taba mutuncina”

“Sultana bata tana miki rashin kunya ba,bazata miki ba ama”

“Ka bani guri nace ko?kaidai da kaga zaka iya sai kayita yi….” Dauke kanta tayi tana qwalawa saddi kira

“Dauko remote ka canza min channel” ta fada tana sake bude album din nata,saidai can qasan zuciyarta itama wani abu yana tsunkulinta amma tana qoqarin kautar da kanta da tunaninta daga kai. Haka ya qaraci zamanshi a gabanta ya miqe jiki a sanyaye ya fice a falon.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 19

THE DESTINY |

Su hudu ne zaune cikin falon bibi da babu kowa sai tanja dake kai kawo ita da biyu cikin masu aikin bibi.

Su biyar ne a falon,hanan maama rachida bilkissou sai kuma sultana din. Dukkaninsu su biyar din kowacce idan ka kalleta akwai alamu na samun cikakken gata a tattare da ita,cikin duba na biyu kuma zakasan kowacce ta fita ne daga gidan da sukunin rayuwa ya samu muhallin zama. A tsakanin su biyar kowacce shekararta tsakanin sha biyu ne zuwa sha uku,saidai tarin iyayinsu da rawar kai zakayi tsammanin sun tasamma shekaru sha takwas takwas ne. Sosai halinsu yazo daya,shi yasa abota a tsakaninku keda matuqar qarfi da tasiri,duk wanda yasan daya a cikinsu yasan daya,kowaccensu tana ji da gata da kuma sakewa,duk da cewa a cikinsun babu kamar sultana,wadda bayan fifikon gata data samu,ta samu wani irin fifiko na kyawun sura tun gabanin ta kammala cika mace. Ta mugun iya dressing kamar yadda yaren faransanci ya zauna daram a harshenta,hakan kuma baya rasa nasaba da zaman da tayi a waje cikin turawan faransa na tsahon wasu shekaru harta kammala primary dinta.

“Ni so samu da magariba za’a fara birthday dinnan maganar gaskiya sai yafi dadi” sultana da ta qare karanta katin birthday din hanan ta fada tana maida dubanta ga fuskar rachida. Qaramar dariya rachida ta saki

“Allah ya shiryaki kedai,duk wani harkar rawa kina gaba gaba” ido sultanan ta lumshe

“Hmmm ke bakisan yadda rawa take da dadi bane,Allah ji nake kaman na fara takawa tun yanzu,ni hanan kin gama biyana,irin wannan birthday din nakeson yi qarshen shekarar nan” sultana ta fada tana tashi ta zauna sosai saman kujera,saboda tana hasaso yadda abun zai kasance

“Idan yaa maina ya bari ba” bilkissou ta fada tana zuqe madarar hannunta.

Harara sultana ta jefa mata

“Kina daga kwance kina shanyen madara kina min fatar tsiya,wanne ya maina din da yanzu baya zaman gidan nan ma,saidai munafukai irinsu goumar su gaya masa”

“Baqin buzu?,yana burgeni wallahi” hanan ta fada tana dan murmushi. Caa sukayo mata suna tsokanarta,yayin da sultana ke binsu da ido tana tabe baki. A rayuwarta haka kurum taji ta tsani koda zancan soyayya ma,duk da su din wannan ba fagensu bane dama,ba wani abu bane da sukeyin Maganarsa ba

“Meye abun burgewa a wajen wannan?,kaf halin yaa maina daidaiku ya baro” sultana ta fada tana tabe baki

“Wai ina su najma”

“Kin kuwa tunamin,basu nasu card din” idanu hanan ta zaro

“Ko kema fa lallabawa zakiyi kije baresu?”

“Kada ki damu,sun jima suna cewa a gayyacesu idan za’a yi,barema duka date din da aka saka dodon nasu baya nan,kinga nima hankalina kwance zamuje mu dawo abinmu ba wanda zaya matsa mana,wannan babban hotel da dad ya kama mana hall a ciki ai ya gama mana komai” ta fada tana dariya.

Sun jima suna hirarrakinsu suna sake tsara yadda zasuyi abinsu

“Sauran abinda m ba zamu iya ba auntie haula tace zata tsara yadda komai zai tafi mana yadda mukeso”

“Sai auntie” sultana ta fada tana dariya, tana jin dama itace cikin gidansu hanan,babu matsi babu kuma takura.

Sallama sukayi da Bibi ta rakosu makeken parking lot dinsu inda suka zaunar da driver dinsu yana jiransu. Sai da suka fice a gidan sannan ta juya ciki tana gyara card din hannunta.

Sassan uncle umar t soma shiga,ta samu mamma na sanya turaren wuta a falo. Gaidata tayi mamma ta amsa tana dubanta yadda ta shigo a wani mugun nutse

“Najma fa?”

“Suna daki ita dasu aminata” bata ko waiwayo ba ta zarce dakin da zumudinta,sai mamma ta bita da kallo har ta shige sannan ta dauke kanta tana ci gaba da zuba turaren wutan.

Cikin sa’a dukkansu ta samesu a dakin,aminata najma yasmin da lamira

“Kuzo kuga wani abun arziqi” ta fada tana rarraba musu card din. Karban nashi kowa yayi yana dubawa,najma ce ta fara daga kai

“Birthday din hanan?,haka akeji da ita aka kama mata wannan babban hall din?” Dariya sultana tayi

“Don hall kawai?,sai kinje ma kinga yadda aka tsara gurin”

“Zuwa kuma sultana?” Aminata ta fada tana zare ido. Da wurwuri sultana ta jefeta da harara

“Eh mana,hanan ce fa,kuma idan ya maina kuke tsoro ai baya nan,hasalima shekaran jiya duka duka ya tafi,shi kuma da sake dawowa sai wani satin nan da kwana goma ma,kunga hankali kwance zamuje mu dawo” shuru suka danyi suna kallon juna

“To ta yaya zamu fita su mamma basusan birthday muka tafi ba?”

“Karku damu da wannan kun manta ina da modu?” Dariya suka saki plan din nata yana musu dadi. A nan suka sake suna maida yadda abun zai wakana.

Tun daga ranar take shirya kaya da shigar da zatayi. Duk da dimbin suturunta da suka kusa kala dari biyu amma sai taga sam basuyi mata ba. Ta tashi hankali har sai da aba yasa aka dauketa taje ta siya abinda ranta yakeso da sunan wani taro zasuyi a makaranta. Ba wanda ya qaryatata tunda makarantarta daban data sauran.

THE DESTINY ||

***Wadatacce kuma yalwataccen daki ne wanda a qalla yake dauke da manyan katifu masu azabar tudu da taushi guda uku. Turkey carfet ne malale a qasan dakin wanda ya dace da curtains dake maqale jikin manyan windows da qofar dakin.

Ba wani tarkace a dakin,domin kuwa komai yana tsare ne bisa muhallinsa cikin tsaf da kuma wayewa. Akwai babbar cupboard ta jikin bango wadda daga samanta akwatune masu kyau a qalla sunkai shida mallakin samarin dakin.

Daga gaban murfin cupboard guda daya maina ne a tsaye yake dauko wankakkun kayansa dake shimfide a ciki suna fidda qamshin sassanyan mayataccen turarensa yana jerawa cikin wata kyakkyawar madaidaiciyar luggage milk color da torches na Navy blue a jikinta. Daga yadda yake zaro kayan yana jerasu a ciki zakayi tsammanin yana yine saboda tsabar yanga da kuma salo irin nasa. A’ah,a yau din ba haka take ba,domin kuwa tun daren jiya ya tashi baya jin dadin jikinsa sam,wani irin kasala da mugun ciwon kai harda tsarabar guntun zazzabi su suka tayashi kwana. Zuwa wayewar garin yau kuma yaji babu abinda yake da buqata irin yaje gida,duk da cewa suna tsakiyar karatunsu da ya soma daukan zafi da gaske.

Wani matashinne kamar shi yayi knocking qofar sannan ya turo ya shigo dauke da jakar leda dake dauke da tambarin wani gidan abinci dake nan kusa da ecole din nasu. A bayansa wani matashinne da dukkansu shekarunsu zasu zo guda.

Kadan ya waiwaya yana amsa sallamar tasu sannan yaci gaba da qoqarin zuge zip din luggage din

“Ami(aboki)Me nake gani?,ya da hada kaya cikin bagage(luggage)?” Ya fada yana neman daya daga cikin sofa da suka qawata dakin da ita ya zauna akai idanunsu dukka su biyun suna kan maina din. Idanunsa yadan lumshe kadan yana jin kansa yana dan sarawa kadan duk da yadan samu sassauci

“Gid nikeson zuwa,amma gobe ma zan dawo ko lundi(monday)”

“Kace dai kawai raki zaka nuna da langwai,kanaso kaje ama tayi jinyarka” murmushin gefen baki kawai yayi,da mahadi da sultan din dukkansu gwanayen tsokana ne,ana cewa sai hali yazo daya ake abota,to amma su a kansu abun ba haka yake ba,akwai banbacin halaye da dabi’u masu yawa tsakaninsu. Kusan dukkan abokansu dake shigowa dakin mahadi da sultan ke kawosu,don ta maina kam shi daya ma zai iya qare zamanshi.

Yana jinsu sunayi masa tsiya ya wuce toilet dinsu dake manne cikin dakin,ya fiddo brushes dinsa da toothpaste da sauran kayan wankanshi ya dawo ya qarasa hada kayanshi. Order yayi na mota har cikin makarantar,ta iso bakin hostel dinsu sultan da mahadi sukayi masa rakiya har ya tashi.

Lamo yayi cikin motar,bai motsa ba har sai da kira ya shigo wayarsa. Da ya duba da kyau sai yaga meena ce,yaja siririn tsaki yana maida wayar silent ya jefata cikin jakar hannunshi da ya zuba qananun tarkacensa. Yadanbi jakar da kallo,shi da yace gobe ko jibi zaya dawo,besan me ya sanyashi debo kaya haka ba.

“Alhamdulillah” ya fada a nutse sanda ya sauka tsakiyar farfajiyar gidan yana duba yadda sassan gidan yayi shuru. Sake duba wrist watch din hannunsa yayi wanda ke dauke da sunan kowacce rana yanason ya gani ko yayi kuskuren tunanin yau din weekend ce saidai kuma koda ya kalla dai dai lissafinsa ya bashi. Bai tsawaita tunaninsa ya janye luggage dinsa kansa tsaye ya wuce sashensa,don duk cikin mutanen gidan yasan ba wanda yasan da zuwansa.

Ko yaya yaje makaranta ya dawo bai iya zama a daki haka,mafi yawan lokutta ma ama na sanyawa a gyara masa ne tun kafin ya iso din saboda saninsa da tayi da shegen tsantsami da tsaftar tsiya. Yau ba wanda yasan da zuwansa bare yayi masa wannan tanadin,don haka ya zage ya gyara dakin nashi yadda yakeso sannan ya shiga wanka.

Yaji qwarin jikinsa sosai,kamar ciwon dama yana jira ya baro makarantar ne. Wannan ya bashi damar shiryawa cikin trouser silk shirt me gajeran hannu. Ainihin cikar zati da surarsa suka fito muraran,kyakkyawan ba’abzinen matashi aliyyu haidar mayak’i.

Da salon nutsuwar nan tashi ya wuce zuwa sassan bibi. Duk yadda sukayi fada ko suka samu sabani,duk yadda sukaso share juna ita dashi amma hakan bai yiwuwa,shi yasa sam ba’a shiga fadan bibi da haidar maina,idanma ka shiga din kaine da jin kunya. Sai daya dan kalli sassan amansa kadan kafin ya shige,ya san muddin taji ya shigo gidan ba ita ya fara nema ba saita nuna masa fushinta koda da kalaman baki ne,sai ya qudirta a ransa bazai jima wajen bibi din ba,zai fito yaci abinci a wajen ama din nasa. Dab da zai shiga saqo ya shigo wayarsa,sai ya rage sassarfar da yakeyi yana dubawa.

Tailor dinsa ne yake gaya masa ya kammala dinkunansa duka,zaiyi tafiya zuwa diffa,idan baya gari ya aiko daga gida a karba masa,kada ya buqacesu shi kuma baya nan. Saqon ya rufe yana rayawa a ransa zai fita idan ya gama cin abinci ya karba,ko miqe qafarsa ya danyi qila ya sake jin qwarin jikinsa.

Baki bibi ta sake da ganinsa,abinda basuyi tsammani ba tunda duka duka wancan satin ya tafi,kuma a yanzun yakanyi sati uku ma baizo gidan ba

“Hala kewar matarka ta isheka kazo ganina ko?” Bibi ta fada tana dariya. Fuska yadan yamutsa kadan yana dubanta sannan ya nuna qirjinsa da yatsanta

“Ni maina?,Allah ya kiyaye,na barwa su saddi” wasa ne da ba kasafai suke yinsa ba ita dashi,amma duk sanda kaga ta jashi da wasan to tabbas tana cikin nishadi ne da jin dadin ganinsa.

Suna gama gaisawar bai jima ba ya miqe

“Bari na qarasa ciki”

“To,saika fito”.

Kyakkyawan falon da ko yaushe yake cikin tsafta da kyau,komai nashi bata taba bari ya tsufa ko kyansa ya disashe. Ba kowa cikinsa sai masu aiki guda biyu dake yayyafin turare suna gohe marbles din dake shimfide a qasan falon. Wannan din kusan al’adarta ce,kowacce rana sai anyima qasan falon irin wannan gugar sau biyu zuwa uku,wannan ya sanya qamshi sosai ya kama wajen.

Sun shaida masa tana samanta,sai yace su barta,ya sanya suka shirya masa abinci ya soma ci,sannan ya fidda wayarsa ya fara kiranta.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 20

Ba jimawa ta sauko tana fadin

“Wanne irin shashanci ne haka maina?,zaka taho ba zaka sanar ba?” Dan qaramin murmushi ya saki,har yanxu ama tana kallonsa ne kamar wani saddi

“Banajin dadi ne ama,hakanan naji inason zuwa na ganku”. Fuskarta tadan nuna damuwa,taja kujerar dake fuskarsa ta zauna idanunta a kansa cikin kulawa tana tambayarsa meke damunsa?.

“Zazzabi ne sai dan ciwon kai bame yawa ba”

“Subhanallah,Allah ya sawwaqe,to ya jikin yanzu?”

“Alhamdulillah,da sauqi sosai”

“Ma sha Allah” ta fadi dai dai sanda wayarta ta dauki tsuwwa. Fuskar wayar ta kalla sannan a hankali ta furta

“Mariya?” Sai ta daga kiran ta saka a kunnenta.

Sallama ta farayi sannan sauran maganganu suka biyo baya,tun tana maganar a hankali har alamun fushi suka dan fara bayyana saman fuskarta,kuma alamu sun nuna ranta ne ya far baci. Dukka maina yana ankare da ita yana diban abincin kadan kadan yana ci yana nazarinta

“Shikenan na gode,Allah ya qara zumunci” ta qarashe fada tana katse kiran.

Iska ta furzar daga bakinta tana hade yatsunta waje guda

“Lafiya ama?” Ya tambayeta yana ture kwanon abincin daga gabansa

“Wato shi zumuncin yanzu haka ya koma?,Allah ya sani ina bakin qoqarina gurin ganin na gina zumunci me qarfi tsakanina da ‘yan uwana amma kowa sai ya watsamin qasa a ido saboda Allah ya jarabceni da son ‘ya’ya mata kuma bai bani ba…..”

“Wani abu ya sake faruwa kenan?” Ya kuma fadi ransa yana sosuwa saboda yadda fuskar ama din ta sauya ta fara hada ja,alamun dake nuna inda zata samu sarari kuka ma zatayi

“Mun gama magana da mariya zata bani bintu,ina ganin kamar diyata take tunda dan uwana ya hanani ita din ‘yaruwatace mace zatafi fuskantata,har daki nasa an gyara mata an zuba furniture da nayo order dinsu daga turkey,an mata dinkin dukka kayan da zata saka,na siya mata foam zan canza mata ecole duka a nan,na ajjiye mata driver personal,na gama komai cikin satinnnan nake shirin zuwa Nigeria na daukota,shine yanzun ta kirani take gayamin wai abbanta ya hana,kakarsu tace ba zasu bada ita ba” ta qarashe maganar da alama abun ya sosa mata rai sosai.

Kyawawan idanunsa ya lumshe yana jin ciwon abun shima,bawai kuma ciwon hanasu bintu bane,tunda ko ba komai,duk da auty mariya masu wadatane sosai suma din amma basu kama qafar ama ba,ama nada son yara da riritasu,cikin gidan kaf banda sultana baiga wanda baya cin moriyar ama din ba wajen kyauta da jan mutum a jiki,ya sani bintu din zata samu gata da kulawar da babu lallai ta samu a gidan mahaifinta. Bacin ransa na ganin damuwa me tarin yawa saman fuskar ama din,inda yana da hali da ya samar mata wannan abun da zai wanke wannan baqincikin da takeji a duk sanda ta nemi riqon diya cikin diyoyin ‘yan uwanta bata samu ba.

Matsowa yayi sosai ya kama hannunta ya riqe cikin nasa,cikin tausasa murya ya soma magana

“Kiyi haquri ama,daga yau kiyi haquri kibar musu diyoyinsu daga yau,ni na miki alqawarin in sha Allah duk sanda nayi aure zanyi addu’ar Allah yayita bani diyoyi mata,zan fara addu’a tun yanxu,sannan na miki alqawarin ko diyoyi mata nawa na haifa naki ne har sai kince kin gani da riqon ‘ya’ya mata”. Wani qawataccen murmushi da ya bayyana kyau da sauran quruciyarta ta saki bs tare da ta sani ba

“Maina,ta yaya zan gaji da riqon diyoyinku koda taron arfa zaku haifa?,ai saidai naci gaba da addu’ar Allah yaci gaba da baku masu albarka ya kuma hore mana abinda za’a kula dasu” daya hannun nata itama ta dora saman nasa

“Na gode sosai,daga yau in sha Allah na haqura,zan kuma jirayi jikokina komai tsahon lokaci kafin zuwansu” Murmushin shima yadan saki yana jin dadin yadda maganarsa ta faranta mata.

Agogo ya duba sannan ya miqe yana cewa

“Zanje na karbo dinkunana ama”

“Allah ya tsare,kada ka jima kaga bakajin dadi”

“In sha Allah……Key din mota daya zaki bani aro”

“Ya kamata kayi zuciya kayi motar kanka mana” ama din ta fada tana dan murmushi hadi da miqa hannu ta dauko key din motar da dazu goumar ya ara ya fita da ita ta miqa masa

“Akwai lokaci ama,karatu,yanzun inayin mota ko banaso sai ta sanyani yawo,ko banyi ba su sultan zasu sakani”

“Wannan karatu,Allah yasa a gamashi lafiya” ya amsa mata da ameen yana kaiwa qofa.

Sai da yahau titi sosai sannan ya tuna ya cewa bibi zai dawo,don haka ya ciro wayarsa yayi kiranta

“Bibi na wuce amma yanzu zan dawo”

“To yayi,idan kana dawowa ka tahomin da tsiren yahaya,na kwana biyu banci ba” dariya tadan subuce masa

“Kicemin kawai kwadayinki ne ya tashi” dariya tadan saki itama

“Idanma shidinne ai kaine ka koyamin ko?,nidai a kawomin”

“To in sha Allah” ya fada yana murmushi,sai ya katse wayar ya ajjiye a kusa dashi,ya dora hannuwansa duka saman sityarin yana fidda qotutuwar ajiyar zuciya idanunsa bisa titi

“Kowa yabar gida gida ya barshi” ya fadi yana furzar da iska daga bakinsa.

Mintuna arba’in ya qarasa shagon telan nasa,ya samu kayan a kammale cikin babbar jakar ledar dake dauke da tambarin shagon. Ya qarasa gurin biyan kudi yayi musu transfer na balance dinsu

“Yallabai ka duba mana” auwalu tela ya fada yana dan murmushi. Daukan ledar maina yayi

“A’a,basai na duba ba a hanya nake”

“To godiya mukeyi,sai mun sake ganinka” ya fada yana masa rakiya har bakin motar.

Sanda yake dawowa cikin shagon muzammilu ya tareshi

“Da alama kudi ka samu jikin sarmayin nan naga ka kasa zaune” dariya Auwalu ya saki

“Ah na samu alhmdlh,kowanne kaya saida ya qaramun kudi akan ainihin kudin dinkin kuma yana sane,na jima banga matashi da kudi basu dameshi ba irin maina mayak’i” idanu muzammilu ya buda

“Kai……kada kacemin family din MAYAK’I ne?” Kai auwalu da ya jawo wasu kaya zai yanka ya kada masa

“Qwarai kuwa”

“Amma gaskiya baka hadu ba,kuma kai banza ne,tsakani har ga Allah mutum irin wannan yazo wajen nan koni ka kasa gayawa na yagi wani abu?,yo aiko kudin cefani na sati na samu gurinsa ina laifi” harara auwalu ya jefa masa

“Hauka nake na gaya maka ku zubar mana da mutunci?,irin wadannan basason roqo basason wargi,kai bakaga yanayin fuskarsa ba?, baya wasa,ni ban taba ganin dariyarsa ba,yana dai murmushi sa’i sa’i”

“Ba komai,zamu hade nan gaba”

“Kai ka jiyo” ya amsa masa yana zare tip na awo daga wuyansa.

A nutse yaci gaba da tuqinsa tamkar bashi da wajen zuwa. Haka kawai weather din maradi din yau take masa dadi,sanyi sanyin nan dake nuna an fara bankwana da zafi. Sannu sannu har ya isa gurin yahaya.

Gurin gashin nama ne na gargajiya sosai,mutum biyu bibi keson namansu yahaya ko yahuza. Ba ruwanta da wajen wani BBQ ko gashin engine da sauransu,takance ita tafi gane wannan,shi yasa koda cikin gida masu aiki sukace zasu gasa mata ba kasafai take ci ba,saidai ta aiko nan din ko wajen yahuza a siya mata.

Yana ganinsa ya iso gaban motar tun kafin ya fito.

“Yallabai,hala bibi tayo aike” fuskarsa adan sake ya gyada masa kai

“Saqo ta bayar takanas”

“Kayya,kuma ba’a zo da wuri ba yau,yanzu na gama hada kaya komai ya qare wallahi” ya fada cikin rashin jin dadi yana kallon bayansa

“Babu komai,Allah ya qara albarkar kasuwa” maina din ya amsa yana laluba canjin aljihunsa ya miqa masa.

Hannu bibbiyu yasa ya karba yana godiya,yana matuqar jin dadin zuwan maina gurin,koda bai siya komai ba zai cikaka da alkhairi ya barka a wajen kana godiya,yana tsaye har motar maina din tabar wajen.

Har ya dauki hanyar gida yaga bai kamata ya shigarwa bibi din haka ba,ya tabbatar ta sanya rai tunda har ta bashi sautu,don haka ya juya akalar motarsa zuwa wajen yahuza dake bakin police station.

A hankali yake gangarowa saman babban titin da ya kasance daya daga cikin manyan titunan na garin maradi din. Titine dake dauke da manyan hotels eatery da guest houses parks da sauransu. Wannan dalilin ya sanya baka rabashi da wucewar manyan motoci masu matuqar tsada da daraja saboda gurin na kai kawon baqi daga gurare daban daban,yayan masu kudi masu buqatar hutawa da sauransu,dalili kenan da ya sanya aka qirqiri police station a gurin saboda samar da tsaro da kuma wanzar da zaman lafiya.

Daga gefe ya tsaida motarsa,ya saka hannu yana dage glass din motar yana duban glass din yana jiran ya gama rufewa ya fita a motar.

Kamar gilmawar walqiya motar tazo ta gotashi,idanunsa kuma sukayi masa kyakkyawan daukan wata sura cikin motar da tafi kama da SULTANA.

Tamkar an sanya wuta an jashi haka yaji haka yayi fit ya fita a motar,daidai sanda motar ke sanya hancinta zuwa cikin katafaren hotel din dake girke a wajen,karkatawar da motar kuma tayi ya bashi damar ganin sultana din sosai zaune daga back set tana dariya.

Wani mugun bugawa zuciyarsa tayi har sai da yaji kaman zai fadi. Bai qara koda second guda ba ya soma tattakawa cikin sassarfa yana dosar gate din. Kanshi tsaye ba tare da ya tsaya kulawa da security dake bakin gate din ba ya cinna kai ciki. Daidai sanda motar ta kammala tsaiwa qofofin motar suka bude wadanda ke ciki suka fito.

‘yaran ‘yammata ne kamarta su biyu sai matasan samari su uku harda driver din.

Sanye take da wani tsadadden trouser da ya zauna daidai jikinta kamar yadda rigar tayi masifar dacewa da qirar jikinta,qafafunta saye cikin wani arnen Boot da aka siyeshi da CFA me tarin yawa. Kanta babu koda qyalle bare dan kwali,gashinta me matuqar tsaho da santsi an masa wani irin gyara da idan ka kalleta zaka rantse batasan zoka kasheni da yaren hausa ko buzanci ba,don gaba daya ta koma kamar wata balarabiya daga qasar qatar ko oman ko wadda ta fito daga qasar hindu. Iya kyau tako ina ita kanta tasan a yau ta yishi,tun sanda aka gama shiryata,su lamira da sauran friends dinta kuma suka tabbatar da hakan ta hanyar kodata.

Batasan ya akayi ba,ta sama ne ta qasa ne oho,saiji tayi an finciki hannunta. Sanda ta waiwayo taga shine sai da taji tamkar jinin jikinta ne tsaf ya qone,wata mahaukaciyar razana tayi,amma cikin qasa da minti guda wannan zuciyar ta yunquro ta kuma fara haska mata tarin tozarci da asarar da zaya janyo mata matuqar bata jajirce ba. Wannan ya sanya ta turje sanda yake qoqarin riqeta da kyau ya kuma janyeta daga cikin gurin.

“Ka sakeni mana,me nayi maka?” Ta fada tana bata fuska da turo baki gaba cikin tsiwa da rashin kunya.

Yana waiwayowa abu na farko da ya fara yi sauke mata wani zazzafan mari da tunda ya soma dora hannunsa saman fuskarta bai taba mata irinsa ba. Marin da ya sanya ta gigice gaba daya ta kuma tabbatar da cewa ashe a baya qaryar jin zafin marinsa takeyi,yanzunne ta tabbatar da ainihin abinda ake nufi da mari,yanzu ne kuma ta gasgata gaskiyar zafin da yake dashi na gasken gaske. Mari na biyu daya qara mata shine ya cisge duk wata kafiya tata da taurin kanta,bakin cewa ya saketa ta koma ya mutu murus. Ya janyeta da zafi zafi tana gurdewa saboda tsinin takalman qafarta,bai kuma saketa ba ako ina sai cikin motar sa,ya maida murafun ya rufe ya murza key ya kulleta.

Hannayensa ya zuba duka cikin aljihun wandonsa yana kallonta sanda take rusa kuka yana kuma furzar da wata zazzafar iska. Shi kadai yasan me zuciyarsa ke raya masa a kanta. Sultana a hotel?,tafiyarsa har ta sake sanyata ta kuma lalacewa haka?,me bibi takeyi?,aikin me aba yakeyi?,haka ake gata?,sudin haka akayi musu?. Qafa ya saka cikin zafin rai yadan daki gaban motar sai ya juya yana nufar wajen yahuza wanda baisan ma yazo ba,cikin ransa yana rantsuwa da Allah yau kam za’a kawo qarshen komai,duk da ama taja kunnuwansa akan sabgar sultana din,amma yanzun an fara kaiwa shingen da idan basu tsaya ba zasuyi kuka dukkaninsu da idanunsu,tunda zuwa yanzun ta fara kaiwa shekarun girma,shekara goma sha uku nan da shekaru biyu budurwa za’a yi kiranta.

Koda yaje yadan samu layi,ba mutum ne shi me take doka ba,duk da akwai sanayya tsakaninsa da yahuza ta regular customer da business owner amma sai yabi layi kaman kowa. Saman kujerar roba dake wajen ya zauna,saidai sam bashi da walwala ko sukuni,saboda wani irin zafi da zuciyarsa take masa.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 21

Kuka takeyi sosai tana murza fuskarta dake mata wani irin mahaukacin radadi,baya ga zafin marin babu abinda yake zuciyarta illa asarar zuwa birthday din dake tunkarota tunda tayi amanna zuwa yanxu sha’ani yayi nisa,kuma dukka su lamira aminata da yasmine suna ciki.

Yaushe ma yazo garin bayan kwanansa nawa duka da tafiya?. Me yasa bashi da aiki sai marinta?,abinda wani halitta be taba yi mata ba sai shi?.

Wata irin mahaukaciyar qiyayyarsa da tsana me qarfi ta sauko mata sanda taga fuskarta a jikin mirror,ta hada wani mugun ja,shatin dogayen yatsunsa kwance akan fuskarta.

“Wallahi daga yau ba zaka sake marina ba,bakaci bulus ba” ta fada a fili cikin muryar kuka

“Tome zaki masa ki rama?” Ta tambayi kanta da kanta.

Gilmawar wani dan sanda ta bakin motar yana nufar can wajen yahuza saita zame mata tamkar amsar tambayar ta,cikin sauri ta koma bakin window din,akwai sauran space da bai qarasa rufewa ba don haka ta saka kanta ta wajen ta fara sharara ihu tana kallon saitin policestation din.

“ku taimakeni!,wayyo Allah,don Allah wani ya taimakeni!!” Ta fadi tana kallon gate din policestation. Shuru ba kowa ta wajen,abun da ya tabbatar mata sai tayi da gaske,kuma tana buqatar tayi komai da sauri kafin maina ya cimmata,don haka sai ta qara bude dukka muryarta da qarfi tana fadin

“Ku taimakeni a taimakeni wayyo Allah wani ya taimakeni!!!,ku taimakeni don Allah SATO NI yayi!” Maganarta ta qarshe tayi dai dai da dawowar police din dake riqe da wata qaramar baqar leda,da alama wani abun ya siyo.

‘yan sanda ne tsayayyu da sukasan abinda sukeyi cikin kulawa da haqqin kowa,ba batun cin hanci ko rashawa burinsu dai kawai aikin da hidimtawa zuwa ga qasarsu NIJER. Da sassarfa ya nufo gurin,sai sultana din ta qara bude murya da kyau tana sake sakin ihun neman taimako

“Ke!,menene?”

“Me motarnan ne ya satoni”ta fadi cikin kukan baqinciki ya bata mata ranar gaba daya.

“Sata?” Bai gama jiran amsarta ba ya waiwaya yana qwala kiran inoussa da idrissa. Cikin qasa da second biyar sai gasu sun iso,fitowar tasu da tsaiwarsu a wajen suna cigiyar waye mamallakin motar ya fara jan hankulan jama’a ta wajen.

“A gaida hajjaju don Allah” yahuza ya fadi yana miqawa maina ledar naman

“Zataji” ya amsa da sauri don yana burin ya isa gida kan sanda aba ke dawowa.

Da mamaki yake kallon motar tun kafin ya qaraso yadda ‘yan sanda suka baibayeta

“Duk yadda akayi me motar yana ta nan baiyi nisa ba,ku bincika” gabansa ya tsinke dajin abinda suke fadi,ko wani abu ya faru da sultana dake cikin motar,wannan ya sanya ya qarasa da sassarfa yana fadin

“Gani,nine me motar” yadda dukka aka zuba masa idanu yasa yasha jinin jikinsa

“Kaine me motar?”

“Eh” ya gyada kai

“Satar mutane da ranar Allah kuma don rashin kunya ka daukota ka aje cikin jama’a kusa da hukuma saboda ka maida polisawa shashashai?……idrissa,karba maqulli ku sakata a ciki shima ku shigo dashi yayi bayani”. Gaba daya kansa ya qulle,baima fahimci komai da suke fada ba. Ta gefen sultana kuma sai taji hakan baiyi mata ba,ba ciki taso a shiga ba,a nata plan din zasu budeta ne ta fita,ita kuma sai ta samu ta koma gurin birthday din,sauran kome zai faru idan sunje gida wannan wani abune na daban.

A nutse kuma cikin zallar mamakin daga inda batun satar mutane ya bulla ya shiga motar ya kunnata ya kuma gyara tsaiwarta ya gangara da ita cikin police station din.

Su suka nuna masa inda zai ajeta ya ajjiye din kuma ya fito yana bin bayansu zuwa cikin station din.

Gurin zama yayi musu a gurin da ake daukan statement,har a lokacin tunaninta gaba daya yana wajen birthday din burinta daya suce ta tashi tayi tafiyarta ta samu cikakkiyar damar zuwa ayi sha’anin da ita

“Kikace satoki yayi daga ina?” DPO ya jefawa sultana tambayar yana kallonta. Da sauri tana kuma sharbe hawaye ta gyada kai

“Satoni yayi zaiyimin FYA’DE” Ta fada da confidence tare da nuna tsoro zalla saman fuskarta.

Wani mugun duka zuciyarsa tayi,irin dukan da bata taba yi masa irinta ba iyakacin tsahon rayuwarsa.

“Sultana!?” Ya kirayeta da wata madaukakiyar tsawa fuskarta cakude da wasu al’amura masu nauyi da suka hada da razani da kuma firgici me yawan gaske

“fermez-la(shut up)” shima dan sandan ya dakawa maina tsawa cikin nuna bacin rai qarara

“Bude mata ido zakayi ka hanata fadin gaskiya?, idan har kai me gaskiya ne ka bari ta gama jawabinta sai kayi naka” ya fadi yana muzurai idanunsa akan maina,kamar yadda shima maina din ya kafeshi da nasa idanun,maqoshinsa yana sama da qasa,idanunsa kuma sauya launi a hankali a hankali,saboda wata muguwar suya da kalmar FYA’DE ZAIYIMIN din data fada ke yi masa.

“Kin sanshi dama kenan?” DPO ya sake tambayarta yana maida hankalinsa kanta. Ga tarin mamakin maina saita girgiza kai da sauri

“Ni bansanshi ba,bansan wayeshi ba,ban taba ganinsa ba sai yau,a hanya ya ganni ya satoni,yanata qoqarin min fyade din…….”

“Sultana!” Ya kuma kiran sunanta jin tana sake yunqurin dangantashi da kalmar fyade

“vas-tu te taire ?(zakayi shuru ko kuwa?” Dan sanda da tasa budaddiyar muryar me kauri data lullube ta maina ya fada yana tashi kaman tsaye kaman zai rufeshi da duka,kasancewar ko a girme ya girme masa.

Zuciyar ‘yan maza ta motsa,ya mance sam sam wai a gaban hukuma yake, idanunsa rufe ya soma zazzagawa dan sandan masifa

“Ta yaya zaka zauna yarinya qarama ta dinga tsara maka qarya abinda bai faru ba ehhh?”

“Au qarya ma takeyi?,wannan marukan na fuskarta duk na meye?,ko ku baku gani ba?” Ya fadi yana tambayar sauran Yan sandan dake wajen

“Gaskiya ne Monsieur(sir),dama duk sanda zasu aikata hakan saisun mammare fuskar yara harda duka na rashin imani” wata police mace dake tsaye a wajen ta fada cikin hasala,da alama itama akwai adawa me qarfi tsakaninta da fyaden

“fermez-la(shut up),kina sanye da kaki amma baki iya banbance tsakanin me gaskiya da me laifi,kuna hukunci da abinda aka baku labari!”

“Zaginmu zakayi?” DPO din dake tsaye a daura dashi ya fada cikin hasala

“Bazan zageku ba amma na raina iyawark…….” Baikai qarshen zancan ba DPO din ya zuba masa lafiyayyen mari saman kyakkyawar farar fuskarsa.

Tamkar gilmawar walqiya,tamkar kuma gizo sultanar taga saukar mari kan fuskar maina. Tayi muguwar razanar da har sai data miqe daga saman kujerar da take zaune a kai

“Koma ki zauna,ai tunda kike nan tu es en sécurité,bai isa yayi miki komai ba,mara gaskiya kawai,ba daka mata tsawa da hanata tona maka asiri zakayi ba,défendre kanka zakayi kaima indai kai me gaskiya ne,ka gaya mana a ina ka santa?” Koda yana da nufin masa bayani bayajin zai iya buda bakinsa a yanzu,domin wata irin wuta ce kai kawo tsakanin qirjinsa zuwa bakinsa,wani irin kallo yake jifan DPO din dashi da idanunsa da sukayi jazur kaman an masa kwalli da borkono.

“Wannan bashi da gaskiya,ku sakamin shi a bayan kanta” ya fada cikin bada umarni. Bai hanasu yi kasa komai ba don yasan kowanne motsi zaiyi a wannan lokacin to tabbas zai iya daukan mummunan hukunci akansu gaba daya saidai duk abinda zaya faru ya faru. Takalminsa suka karba agogonsa da wayoyinsa dukka suka kashe. Yana tsaye daga dakin yana kallon yadda suka rufe sultana suna mata sannu hade da sake dubata

“Ki rakata gida aicha” DPO din ya fada

“A’ah zan iya tafiya” ta fada da sauri tana satar kallon inda suka rufe maina

“Idan aka ganni da ku kowa ma zaisan me ya faru,banason mamana ta sani hankalinta zai tashi”

“Shikenan,ku kaita bakin layi” ya fadi yana sanya hularsa gami da miqewa.

A hanya sam batajin me suke cewa sai tunanin abinda ya faru a station din. Ranta ya danyi mata rashin dadi da kulleshin da sukayi,so tayi ace tunda Allah yasa sun rama mata mare maren da tasha a hannunsa su sakeshi hakanma kadai ya isa.

A bakin layin nasu suka ajeta ta taka har zuwa gida da qafarta. Tana shiga farfajiya ta biyu ta sami su lamira. Dukkansu sukayo kanta

“Su zinnira sukace wai yayankine ya tafi dake,sunce kaman yaa maina,amma shi kuma baya nan,ina kikaje har akayi aka gama baki wajen anata cigiyarki?” Kusan a jejjere suka dinga jefa mata tambayar

“Yaaya Samaila na raka wajen budurwarsa(wani dan aminin oncle bashar ne” itace amsar data basu kenan tana wucewa sashen bibi ba tare data tsaya jiran labaran da suka qullo zasu bata ba,don babu abinda labaransu zasu qara mata ta sani sai zallar bacin rai,tunda dai maina din da basusan da zuwansa ba ya bata mata ranar gaba daya.

“Allah ya sakamin” kawai take fadi duk sanda ta tuno burin da taci akan ranar amma ya wargaza komai

“Allah yasa ya sake musu taurin kanshi su sake lallasashi yadda ko ya dawo gida zai barmu mu sarara” ta kuma fadi sanda ta tube kayanta ta shiga wanka.

Wankanta tayi abinta ta shirya tsaf kamar ba abinda ya faru taci gaba da sabgoginta. Duk sanda ta tuna ya maina din yana kulle a station sai taji dariya tazo mata,musamman idan ta tuna zafin kansa tsananin tsaftarsa da qyanqyaminsa,yau ya zaiyi dasu?.

Ba wanda ta gayawa sai lamira yasmine da aminata

“Kuma wallahi wallahi naji zancan a bakin wani ko?,ni kadai nasan me zanyiwa mutum” ta fada tana zare fararen idanunta

“To waye ma zai fada?,can tsakaninku,amma ki sani wallahi duk ranar da yaa maina ya dawo taki ta sameki kin shiga uku,don wallahi bazai qyaleki ba” cewar aminata.

Duk da maganar aminata tasan gaskiya ne ta kuma ratsata amma saita murje idanunta. Dare ya fara yi tana jin bibi ta fara cigiyarsa amma tayi kunnen uwar shegu,sai ma ta nade abinta cikin blanket din da tasa tanja ta kwaso mata daga daki.

Kasa jurewa bibi tayi ta soma neman wayarsa tana fadin

“Yau kuma ina Aliyyu ya tsaya,shi da bame yawon dare ba,ba kuma wani tarin abokai gareshi ba bare nace su suka riqeshi?” Tabe baki sultana tayi tana sake cusa kanta cikin blanket

“Yau dai shalelen naku dan baqar zuciya sai kwanan magarqama” ta fada qasan zuciyarta tana lumshe idanunta hankalinta a kwance.

Tana nan a kwance ama ta aiko itama nemansa,bibi tace bata ganshi ba tunda ya fita itama nemansa take,ga dukka wayoyinsa a kashe, ba’a rufa mintuna arba’in ba ama din ta kasa daurewa ganin dare yana yin nisa ta shigo da kanta,don itama ta gaza samunsa,ta kuma tambayi su goumar ba wanda yasan ina yake.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 22

A hankali dare ya fara nisa ba maina ba dalilinsa,sun gwada wayarsa fiye da sau shurin masaki amma ba wani respond. Tun sunayi iya su yasu har aka saka mazan gidan iyayensa. Allah yasa aba yana gari.

Abun ya dagi hanakalin kowa saboda ba halinsa bane yin nesa da gida haka,musamman idan yana gari baya wuce sallar isha’i a waje. Sai gashi yau din har ana tunkarar biyun dare ba maina ba wayarsa ba kuma motsinsa.

Tuni sultana tayi nisa a duniyar bacci abinta,hankalinta kwance tamkar ma bata da masaniyar komai akan lamarin,koda wasa bata nuna tasan komai ba,kamar yadda su aminata suka zuba idanu suga qarshen abun. Sunsan dai qila lokacin yankewa sultana mummunan hukunci ne yazo cikin gidan.

Dukkaninsu kwanan zaune sukayi a falon bibi cikin tashin hankali. Har safiyar lahadin ba wani motsinsa ko labari,abinda ya sake tashin hankulansu

“Zaman nan bazaiyiwu ba yaaya,inaga ya kamata muyi report policestation daga can mukai cigiya gidajen radio da television,wannan shirun ba na lafiya bane” oncle umar ya fada yana miqewa

“Hakan shine zaifi dacewa,zamanmu a nan ba abinda zai maganta” oncle bashar shima ya fada

“Amma sanda ya fita bibi,baice muku zaije wani gurin ba bayan karbo dinkin?” Aba ya fadi yana duban bibi

“Nace masa dai inason nama wajen yahaya”

“Bayan can fa?bakiyi saqo ko ina ba?,don mun duba yahaya din yace yaje amma bai samu naman ba ko fita a motar baiyi ba ya juya”

“Indai haka ne to wajen yahuza nasan zaice zaije ya samomin” bibi ta fada da sauri hankalinta yana kawowa

“Shikenan,bari mu bincika can din,daga nan idan bamu samu komai ba akai saimu qarasa policestation din mu bada cigiya”. Da wannan shawarar oncle bashar da oncle umar suka fice,yayin da sukaci gaba da zaman dakon jiran abinda zai faru cikin gidan. Sultana nacan kwance tana sheqa baccin safiya hankali kwance,tana jin kamar ta fidda qaya daga gidan.

Suna isa yahuza yana qoqarin wanke gurin sana’ar tasa. Duk da bai sansu ba amma yana ganinsu yasan cewa manyan mutane. Cikin rawar jiki yayi musu iso zuwa cikin ainihin rumfar tasa

“Akwai yaro Aliyyu dake zuwa wajenka siyan nama”

“Aliyyu?” Ya fada da dan tambaya

“Eh,maina ba” oncle bashar ya maimaita mishi

“Oh to….naji naji,jikan bibi…..aiko jiya ma yazo gurin nan siyan mata nama”

“Yauwa,madalla,abinda mukeson ji kenan dama,yaushe yabar wajen?,don tun jiya bai koma gida ba” zaro ido yahuza yayi cikin tsoro

“Bai jima ba na sallameshi,ya matsa kusa da policestation dincan yace zai dauki abun hawansa,duk da naga jama’a da dama a wajen,da alama wani case din aka kawo ko wata rigimar akeyi,don naji mutane na zancan an kama me fyade da satar mutane” yahuza ya zarce da bada bayanin da ba’a tambayeshi ba

“Akwai policestation kenan anan kusa?” Oncle umar ya tambaya. Jinjina kai yahuza yayi

“Gata can” ya furta yana musu nuni da ita”. Waiwayawa sukayi dukkansu suka kalleta. Oncle umar ya fara miqewa

“To ai ta kwana gidan sauqi,inaga saimu qarasa mu bada report tunda dai bincike ya nuna daga nan guraren aka rasa kuma ina yayi”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,Allah ya bayyana,Allah ya bayyanashi” yahuza ya furta cikin madaukakin jimami,duk da yanaji a jikinsa bawai bata maina din yayi ba,yafi kyautata zaton kawai ya tafi shan iskarsa ne,tunda ta yaya sankacecen matashi majiyin qarfi irin maina din za’a iya saceshi kamar wani kaya?.

Tare suka gangara a qasa har zuwa cikin policestation din suna tattauna yadda zata kasance. Sanda suka isa gurin ‘yan sanda hudu suka taras saman kanta suna hira abinsu.

“Cigiya mukazo bayarwa na yaronmu da ya bata jiya” oncle bashar ya fada yana kallon dan sandan

“To bismillah,ku zauna yallabai” ya fadi cikin girmamawa saboda kwarjinin da sukayi masa,uwa uba kuma dukka alamu sun nuna cewa su din wasu manya ne cikin nijer din.

“Kai……sanda…..zo ka taho mini da abun rubutu,oga yace wannan yaron idan aka kai azahar baice komai ba a fara tuhumarsa,don ya fuskanci girman kai aggareshi me yawa,sai an sauke mishi shi” dan sandan da ya bawa su aba masauki ya fada da qatuwar muryarsa me kauri da cika kunnuwa.

“Ya lamarin ya kasance yallabai?,inajin da kaina zan shiga na daki yaronnan yadda yakewa mutane gani gani tun jiya,yaqi bada tarho din kowa bare a nemi yan uwansa,da alama dai da gasken bashi da gaskiya”

“Ku dinga bi a hankali dai”

” Ranka ya dade?,barawon mutane kuma dan fyade za’a bi a hankali?”

“A’uzubillahi” aba ya furta yana jin laifukan sunyi girma da yawa

“Wallahi yallabai,yaro da duka duka bai wuce shekara ashirin da biyar ba amma ya iya tara manyan laifuka haka,bari ka ganshi yallabai…….kai sanda,fito da yaronnan,a sake gwada bashi abinci a waje tunda yaqi ci ata ciki kada ya mace mana ya jawo mana masifa” ya fadi yana duban hanyar guraren,sannan ya dawo da hankalinsa ga littafin statement yana qananun mitoci

“Allah ya sawwaqe,Allah ya kyauta” aba ya sake fada kawai yana sauraren statement din da oncle bashar ya fara bayarwa.

Kalaman oncle bashar ne suka maqale masa a maqoshi sanda ake shigowa da maina gurin

“Uban waye ya kawo mana yaro ya daure mana shi?,uban me yayi?” Oncle bashar ya fada cikin matuqar zafi da zafin zuciya yana duban dan sandan da wani irin kallo da ya sanyashi yasha jinin jikinsa

“Ah……yallabai ai shine barawon mutanen kuma dan fyaden”

“Rufemin baki shashasha!” Oncle umar gwanin zuciya ya fada da wata mahaukaciyar tsawa

“Ku kwance masa hannu ku bashi takalmansa”

“Yallabai…… yallabai bari a kira DPO”

“Kayi hauka ne?!” Oncle umar ya sake fadi a fusace,fusatar data tabbatarwa da dan sandan lallai akwai abinda oncle umar din ya taka

“Omar……yi a hankali mana,a hukuma kake fa” aba da ya dafa kafadarsa ya fadi cikin tausasawa,kasancewarsa mutum me nisan zangon daukar zafi

“To ‘yar gidan uban waye zai yiwa fyaden?,uban waye kuma ya sata?,wanan da alama baisan FAMILYN MAYAK’I ba” Oncle umar ya sake maimaitawa a fusace yana duban aba

“Ka bari dai ayi komai a nutse……yallabi ku kira DPO din”

“Okay sir” dan sanda da jinin jikinsa ya kusa daskarewa tunda aka furta mayak’i family ya fadi da rawar jiki yana saluting aba,don sai a sannan hankalinsa ya dauko masa hoton fuskar waye aba din.

Har dan sandan yaje ya musu iso wajen dpo ya dawo maina baice komai ba sai kansa dake qasa,duk kuwa da tambayoyin da oncle umar keta jero masa

“Ka gani ko yaya?,baya magana fa,Allah muddin wani abu ya sameshi dasu da wanda ya kawoshi nan din sai ya raina kanshi”

“Muje dai Omar ” aba ya fadi yana sanyasu a gaba.

Aba din yana shiga DPO din ya miqe cikin mamaki

“Barka da zuwa yallabai,yau kaine da kanka a office dina?,bismillanku” murmushi kawai aba din yayi,yaja kujerar ya zauna sannan su oncle bashar suka zauna,banda maina dake a tsaye bashi da ko alaman tsaiwa,don bai qaunar dogon zama sam cikin office din mutumin,shi daya yasan me yakeji a zuciyarsa,shi kansa din ma bazai iya tantancewa ba. Bayason kallon fuskar mutumin sam,saboda tana tuna masa da mummunar lafazin da suka jefeshi da shi shida sultana,tana tuna tozarcin da yayi masa irin wanda ba’a taba masa irinsa ba tunda ama ta kawoshi duniya

“Kada dai ace wannan yaronka ne?” Dpoya fada yana nuna maina

“Eh yarona ne,nazo kawo cigiyarsa kuma muka sameshi a nan”

“Subhanallahi” tiryan tiryan ya gaya musu yadda komai ya faru,sannan ya dora da cewa

“Yaqi bayani ne yaqi fadin komai,ko kare kansa wallahi yaqi yayi,bansan ba mara laifi bane tunda baiyi yunqurin bawa kansa kariya ba”

“Amma yarinyar wace a ina kuma take?”

“Bansani ba tunda baiyi bayani ba amma dai ga unguwarsu ga kuma hotonta mun ajjiye report saboda gaba” ya fada yana miqa musu wani file

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,sultana ce,’yaruwarsa ce ai,’ya take a wajensa” oncle bashar ya fadi,yayin da aba da kuma oncle umar suka bushe a wajen suka kasa cewa komai.

Shuru dakin ya dauka na wasu sakanni,a nutse aba ya daga kai ya dubeshi

“Meye ya hada haka da ita?,a ina ka daukota?” Sai a sannan yadan motsa kadan daga tsaiwar da yayi kamar an dasa itacen bishiya,rayukan ‘yan maza ne a dugunzume ainun. Dpo din ya fahimci muddin yana wajen bazaiyi magana ba,su dinma sun fahimci hakan,saboda haka oncle bashar yace

“Maganar nan ta gida ce yaaya”

“Gaskiya dai” DPO ya fadi. Dukkansu cikin mamaki da juya lamarin suke dukka su ukun,har zuwa sanda DPo da kansa ya rufe case din,ya kuma tattara musu dukkan wani document da ya shafi case din suka fice da shi.

Ba wanda suka yiwa bayanin inda suka samoshi,saidai oncle umar daketa banbamin fada kaman zai ari baki,daga qarshe kuma

“Zataci qaniyarta sultana wannan karon” har yanxun maina din bai cewa kowa uffan ba,don bayajin bakinsa zai budu har wasu kalamai su iya fita.

Jikinsa dukka radadin cizon da sauro ya kwana yana masa a jiya,uwa uba tsabar tsantsami ya sanya yake masa qaiqayi jikin nasa,don haka ya hada ruwa me zafi yayi wanka bayan ya watsa kayan jikinsa a dustbin,duk tsadarsu bayajin zai iya sake amfani dasu.

Shi daya suka bari a shiyyar tashi,don yace yanason ya kwanta ya huta,ko abinci da ama tayi masa tayi cewa yayi baici ya qoshi. Da gaske bayajin abincin zaibi ta maqoshinsa,da bibi ma ta aiko dashi sawa yayi aka maida mata,ya rufe qofofinsa ya kwanta yana fatar yayi baccin da bai samu yi ba a daren jiya.

Bayan ya kwanta din labari ne yasha banban. Duk inda ya runtse idanunsa ya juya ba abinda idanu da kunnuwansa ke jiye masa sai kalmar SATONI YAYI,FYADE ZAIYIMIN.

“la haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem” ya dinga maimaitawa. Futucin yaqi barin kunnuwansa……Ga tarin mamakin sai yaji wata siririyar qwalla na fito masa ta gefen idonsa guda daya.

Hannu ya sanya ya shafosu yana kalla,shi kam iya tsahon wayonsa da girmansa ya mance yaushe ne lokaci na qarshe da ya ga hawaye cikin idanunsa haka. Duk da ya karbi horo na sajoji masu matuqar wahala da azaba,amma basu taba sakashi dar ba bare damuwa har akai ga qwalla,sai gashi yau furucin sultana ya karya zuciyarsa har haka?.

Haka ya wuni ya kwana,saida tursasawar ama yaci abinci zuwa dare

“Wai ina ka bace?,me sameka da wannan mummunar damuwar take bayyana kan fuskarka?” Ta tsareshi da tambar tana kallon fuskarsa. Har ama din tayi ta gama itama bata samu amsa ba hakanan ta haqura tunda ta samu yaci abincin.

Sultana kuwa tunda taji yaa maina ya dawo gida ta koma tamkar kazar da aka jefa da wuqa,wato kenan tasan wa’adin kwanakin rayuwarta a duniya qididdigaggu ne. Dukka saita tsargi kanta,ta rasa dukkan wani sukuni da walwala,ta yiwa kanta iyaka da kuma shamaki iya dakinta kadai.

Tayi tsammanin games dinta da su nini zasu debe mata kewa,amma kowanne sai taji baya yi mata dadi,idan ta dauko game din sai taji batayi mata ba saita watsar,idan ta dauko nini din ta rungumeta kaman yadda takeyi a baya sai taji ta isheta itama saita ajjiye ta koma ta kwanta. Haka ta dinga juyi kafin daga bisani aminata da lamira suka leqo suna mata dariya tare da sake gaya mata tabbas ya maina fa ya dawo

“To sai me?, mala’ika ne shi?,yayita dawowa,nidai ko banza ai an rama min marina” ta qarashe fada tana murguda baki sannan ta juyar da fuskarta zuwa bango abinta.

*

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

Page 23

W A S H E G A R I*

Idan ka hango yadda ta takure a quryar bango ta kuma cukuikuye cinyoyin Bibi saika dauka mala’ikan daukan rai ne daura da ita. Idanunta sunyi tsilli tsilli sanda maina ke maimaita yadda komai ya faru da wata iriyar saryayyar murya. Dukkansu suna wajen banda aba da tafiya ta kamashi niamy da sassafen. Idanunshi basu kan kowa saboda suna cike ne da wasu al’amura da shi kansa baisan iyakarsu da nauyinsu ba. A karon farko da yaji yarinyar ta fice masa fit daga kanshi gaba daya.

Yana gama kaiwa qarshe shuru ya ratsa dakin,sai bibi dake sallalami tana qoqarin ture sultana daga jikinta

“Ashe fitinarki har takai haka sultana?,ki daure dan uwanki kiyi masa mummunan qazafi irin wannan?,sultana?,babanki maina yake fa?,shine yaci kashinki yaci fitsarinki fa sultana?,anya?” Bibi ta furta cikin wani fushi da bata taba kwatantashi ga sultanar ba.

Oncle umar kuwa waya ya ciro yayi kanta,saida oncle bashar ya tsaidashi da qyar

“Ka banni yau jikinta ya gaya mata,ta dauka duk cikin gidan ba’a iya dukanta ne?”

“Kada ku daketa” muryar maina da wani irin sauti ta cika falon. Waiwayawa sukayi suka dubeshi,har ya miqe tsaye ma abinsa

“Ba fyade tace zanyi mata ba?,to tabbas ta rubuta ta ajjiye NI MAINA SAI NA YI MATA FYADEN,zatasan me ake nufi da ainihin fyade”

“La’ilaha illa anta…….na shiga uku ni kubra” bibi ta fada da mugun qarfi tana zaro dukka manya idanunta waje,muryarta tana rawa

“Aliyyu,maina…..me kake fada!,maina!!” Ta qwala kiran sunansa sanda yake dab da ficewa daga falon. Bai dakata ba bare yaji me take cewa ya sanya kansa yana ficewa,ba daga falon ba daga gidanma gaba daya.

“Na shiga uku na lalace ni kubra,me yake shirin faruwa da iyalina?” Bibi ta sake fadi cikin rudewa da tashin hankali.

“Kinga bibi,kada ki wani dagi hankalinki fa”

“Kasan maina ne?,kasan duk furucin da zai furta yana nufin abinda ya fada din,kasan halinsa kaifi daya ne,kasan baya fada ya canza ko?”

“Ai bashi ya haifi kansa ba bibi” ama da sai a sannan ta samu fusgo tata nutsuwar ta fadi tana matsawa kusa da bibi din don ta taya su oncle bashar rarrashinta.

Duk yadda sukaso kwantarwa da bibi hankali ta qiya,hasalima kuka takeyi

“Ina tsoron halin maina na kafiya akan magana da cika magana idan ya fadeta,ina tsoron kada da gaske din ya lalata rayuwar marainiyar Allah”

“Ba zata faru ba bibi don Allah ki kwantar da hankalinki” ama ta sake fadi cikin nata tashin hankalin da rudanin.

Sun dauki dogon lokaci kafin su samu bibi ta tsagaita kukan,tace amma su nemo mata maina tayi magana dashi. Sam ranar maina din qin zama a gidan yayi,kamar yadda ya kama wayoyinsa duka ya kashe,bai kuma shigo gidan ba sai qarfe sha biyu saura na dare.

Yana shiga ama tana sanya qafafunta,tamkar dama tana biye dashi. A mamakance ya waiwayo yana dubanta

“Ama,bakiyi bacci ba?” Dubansa take da fuskarta a dinke tsaf

“Ta yaya kake tunanin mahaifiyar da d’anta yayi irin wannan mummunan furucin a gabanta zata iya kwanciya ta runtsa?” Tayi masa tambayar da salon da ya sanyaya masa jiki

“Zauna” ta bashi umarni kai tsaye. Bai musa ba ya koma a hankali ya zauna yana kallonta

“Aliyyu,ina dukka hankalinka da tunaninka suka tafi?,ina iliminka?,kasan illa da munin iqirarin da kayi?,ta yaya zaka dauki wuqa da kanka ka dabawa cikinka?” Ta dakata tana maida numfashi

“A gaban kowa kayi iqirari irin wannan?,inda kana da qanwa uwarku daya ubanka daya da ita wani ya fadi haka a kanta zakaji dadi?” Idanunsa ya runtse yana jin ciwon dukka kalaman a karan kansa

“Inaso ka janye wannan iqirarin,ka kuma baiwa bibi haquri,don banason ma zancan yakai kunnen mahaifinka,bana so kuma hakan ta sake faruwa ko da wasa”

“In sha Allah,kiyi haquri ama” ya fada a tausashe.

“Ya wuce,zan turo saddi da abincinka” ta fadi tana fita a dakin.

Ya jima zaune a wajen yana juya lafazin nasa,har zuwa sanda saddi ya riskeshi da karagar abincinsa cikin warmers na alfarma masu tsananin kyau kamar yadda yake kusan hakan al’adar ama ce,komai nata me kyau da tsada ne.

Ko kusa ko alama bata taba daukar kalmar SAI NA MIKI FYADE da ya maina ya furta din zata zame mata wani abun damuwa ko barazana ba,abinda kawai yafi mata dadi da bai taba lafiyarta ba ya juya kuma yabar gidan. Ga tarin mamakinta sai gashi a sanda dare ya fara yi kalmar tana dawo mata,ta rufe idanunta ta rungume nini da kyau ta kuma nutse a blanket dinta amma sai taji maganar tana dawo mata.

A hankali labarai akan fyade suka soma dawo mata cikin kwanya. Labaran da bata taba basu muhimmanci ba cikin rayuwarta,wasu ma ta mantasu sai gasu suna dawo mata daya bayan daya. Sannu a hankali tsoro taji ya fara shigarta. Tunda take bata tabajin tsoron kwana cikin dakin ba sai a yau,tanaso ta miqe ta fice ta tafi dakin bibi amma tsoron ya hanata motsi. Qarar rufe kitchen da tanja tayi tayi mugun kada mata ciki,sai zuciyarta kawai ta bata yaa maina ne yazo zaiyi abinda yace din,abinda ya qarasa firgitata ta saki qaramin ihu hade da hawaye

“Wayyo bibi,ki taimakeni” muryarta tanja dake niyyar wucewa taji,abinda ya dawo da ita kenan,ta murza qofar dakin ta bude,sai kawai sultanan ta sake rikicewa tana boye kanta qasan pillow.

Kallo daya tanja tayi mata ta lura a tsorace take

“Sultana,tanja ce” ta fada tana kamo kafadarta. Jin muryar tanja din ya sanyata watsar da nini din ta miqe da hanzari tana riqe tanjar

“Ki kaini wajen bibi” ta fadi hawaye yana kwance mata saman fuskarta.

Sosai abun ya bawa tanja mamaki,me ya sanya sultana kuka da razani haka?. Hannu ta saka ta daga sultanar

“Muje na kaiki” ta fadi ba tare data tsaya tambayarta abinda ya faru ba.

Bugu biyu sukaji muryar bibi din tana cewa su shigo. Tanja ta tura qofar ta saka sultana a gaba suka shiga.

Bibi din tana zaune saman abun sallah,da alama ta jima da idarwa ta zauna ne kawai qilan tana wani tunani na daban.

Da kallo ta bisu har sultana din ta qaraso,gaban bibi ta zauna tana kwantar da kanta saman cinyarta tana hawaye. Kanta bibi ta fara shafawa a hankali

“Nazo wucewa ne naji ihunta” mummunar faduwa gaban bibi yayi, zuciyarta ta harba tana fargabar jin statement din tanja na gaba

“Da na shiga sai naga kaman a tsorace take ta qudundune a blanket shine tace na kawota gurinki”

“Shikenan jeki tanja sai da safe”

“Allah ya bamu alkhairan” ta fadi tana juyawa ta fita a dakin ta basu waje.

Shuru ne ya biyo baya na wasu mintuna a dakin,har yanzu sultana tana kwance saman cinyar bibi. Zuciyar bibi din kuma tayi nisa wajen saqe saqen abubuwa da dama na dogon zango,sai daga bisani ta sauke ajiyar ta kuma kira sunan sultana din

“Me ya baki tsoro?” Tayi mata tambayar tanason tabbatar da abinda zuciyarta ke saqa mata.

“Ba komai” ta fada a sanyaye tana sake narkewa kan cinyarta,don ko maganar ma sai taji kamar tana qara mata razani ne. Bata qara tambayarta ba itama bibi din,sai data gama addu’o’inta sannan tace

“Tashi ki hau gado ki kwanta” zare jikinta tayi ta haura gadon bibi ta rakata da kallo tana kallon laushin da jikinta yayi.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

Page 24

Ko washegari wani irin sukuku ta tashi,babu wannan dan banzan surutun da rawar kan da take damun bibi dashi. Komai da takeyi bibi din tana ankare da ita,haka kawai ta dinga jin zuciyarta kwata kwata babu nutswa. Duk motsin da sultana tayi idanunta yana kai. Tare sukayi breakfast da sultana din abinda ba kasafai yake faruwa ba,bayan sun gama suna zaune dai a falon suna kallo,saidai kowa da abinda ke cikin jiki da zuciyarsa.

Da muryar nan tasa dake da wani irin zurfi me cakude da kwarjini yayi sallama cikin falon bibi din. Yau din yana sanye da wasu fararen hoodie and jogger pants da ratsin gray color. Fuskar nan na fidda tsananin kwarjininsa da haibarsa, qamshin turarensa me sanyin qamshi da bashi da damuwa ko kadan ya game ko ina.

Sallamar tasa tayi daidai da miqewar sultana cikin sauri daga saman cinyar bibi. Zumbur kamar wadda aka tsikarama wani kakkaifan abu saman qahon zuciyarta. Idanu ta kafeshi da shi gabanta na bada sautin bugu,shima da idanun ya kafeta,lion eyes dinsa dinnan dake azabar cika mata idanu. Kallon da a yau ya dasa mata wani mugun tsoronsa,kalamansa kuma suka sake dawo kata fes saman kai kamar yadda suka dinga yi mata kai komo a qwaqwalwa.

Yadda suka kafe juna da idanu haka bibi ta kafe maina din da ido. Gabanta nason faduwa zuciyarta na ayyana mata abubuwa da dama. Meye dalilin irin wannan kallo da yakeyi mata haka?. Zuciyarta yanzun bata da tabbas akan maina,duk wani motsi nasa a yanzun abun ta sanya masa ido ne.

Idonsa ya dauke daga kan sultana din yana qarasowa cikin falon. Ba abinda ke dawo masa a rai irin qarfin halinta da kuma taurin zuciyarta,ta yadda har ta iya kaishi ga kwana a policestation,wannan wanne irin hadari ne da ita?,a wadannan shekarun nata da duka duka idan aka kacaccalasu gida uku baifi ta tsira da shekaru qwara hudu ba?,me zai faru a nan gaba muddin dai tana da irin wannan zarrar?.

“Barka da safiya bibi” ya furta yana zama daura da ita,abinda ya sanya sultana sake kame jikinta guri guda kenan,ta kuma lanqwasa qafafunta tana maqalewa jikin bibi,har yanzu idanunta qur a kansa,tana jin kamar ma kowanne motsi idan yayi zai iya zama cutarwane a gareta. Bata sake kuma shiga matuqar tsoro ba saida bibi ta zaunar da ita a daxu bayan sallar asubahi tayi mata irin fadan da bata taba yi mata makamancinsa ba,ta kuma gaya mata meye ma’anat fyade da har zata yiwa dan uwanta mummunan qazafi da shi,illarsa da yadda yake taba rayuwar diya mace. A lokacin ta sakejin jikinta yayi mugun mutuwa,ta kuma sake jin mugun tsanar maina da tsoronsa. Banda haka duk da sanin illarsa shi da yayi din amma yaci alwashin sai yayi mata?,dama ashe shi din DAN ISKA ne bata sani ba?. Tayi furucin fyade ne saboda gani data taba yi wata jaruma tayi cikin shirin film,kuma ta samu kubuta daga hannun jarumin.

“Lafiya qalau” bibi ta amsa masa da salon amsa gaisuwar da ba irinta suka saba ba

“Tashi ki bamu guri” maina ya fadi yana maida dubansa ga sultana dake masa kallon Allah ya tsine uwar me qarya,kallon da yayi kama da kallon ban sanka ba, yau na fara ganinka

“Ki nemi hijabi ki saka” bibi ta fada tana bin sultana da kallo wadda ke sanye da wando da ‘yar Short sleeve shirt wadda ta bayyana santala santalan damtsenta. Maganar ta sanya hijabin sai maina ya gaza fahimtar me ma’anarta?,da bai gane ba sai ya share batun ya dubi bibi din bayan sultanan ta iske daki

“Haquri nazo na baki akan furucina na jiya,kiyi haquri,ba kuma ina nufin hakan har raina ba,kuma ba zan sake lafazi makamancin wannan ba” idanu bibi ta gwalalo tana dubansa

“Wa?,ai tsohonka kadai nake jira ya dawo yayi mana shamaki,ni zaka yaudara aliyyu?,kaman bansan halinka ba?,kafiya taurin kai da naci akan dukkan abinda kace zakayi?,ni zaka yaudara da kalaman ban haquri?, tabdi…..bazan taba yarda ba” bibi ta fada tana kada yatsanta dan manuni.

Shuru kawai yayi yana kallonta har ta kammala,sai yadan lumshe idonsa ya bude yana dubanta,can qasan maqoshinsa yana qoqarin hadiye bacin ranshi,donshi a son ranshi banda bin umarnin ama ma bazaizo wani bata haquri ba saidai aje a haka

“Ki yarda dani,da gaske nake baki wannan haqurin bibi” ya maimaita yana kafeta da ido. Dubansa tayi cikin idanu na wasu sakanni,kamar zatayi magana sai kuma ta fasa,ta juye da rufeshi da masifar da yayi imani sultanan ya kamata ta yiwa ita amma tazo shi ta balbaleshi da ita.

Har tayi ta gama bai sake ce mata kanzil ba,sai data sauke sannan yace

“A bani breakfast”

“Yau bamuyi da kai ba”

“Nasan hanyar kitchen” ya fada yana miqewa hadi da gyara zaman rigar jikinsa ya soma takawa

“Kaga,nifa yanxu ina da diya mace da nake raino nan sashen,ba kowanne lokaci ya kamata ma ka dinga shigomin ba,ko zaka shigo ma ka dinga neman izini saboda mu kintsa” cak ya dakata da tafiyar,ya waiwayo yana duban bibi din yana jin maganar nayi masa banbarakwai.

Wata irin dariya mara sauti ce ta subuce masa,sai kawai ya cije lips dinsa yana kada kai. Wai dukka akan sultana take gaya masa haka?,sultana ce wai har za’a kira budurwa?,sultanar da tasan hanyar club tasan hanyar hotel wai yanxu ita akewa kaffa kaffa?,bama haka ba…..shi tasa lalacewar ma ta rasa ina zata qare sai akan wannan qaramar halittar?,ya baro manyan mata da komai yaji a hostel,suna kiransu ma free of charge,matan abzinawa,shuwa da fulani masu shegen kyau da baijin duk kyau irin na sultana zata bude musu idanu tunda nata bai riski ‘yammatanci ba,su basu tsone masa idanu ba sai sultana?.

Har zai biyewa bibi din sai yaga ma bashi da lokaci,ya sanya kai kawai ya wuce kitchen din abinsa.

Har ya cinye asabar da lahadinsa baima sake haduwa da sultanan ba. Litinin da sassafe ama ta sakashi a gaba akan ya koma. To shi dinma dama ranar yayi niyyar komawar,don haka ya tattara ya nasa ya nasa ya koma din.

Kamar jira sultana din takeyi dama ya tafi sai ta warware ta koma halayyarta. Sau tari idan ama na veranda dinta tana hangenta ta farfajiyar gidan tana wani iya shegen saidai kawai taja tsaki

“Allah ya shirya”. Tana hangen abubuwa da yawa da yarinyar ke dashi wanda sauran sa’aninta a gidan basu dashi. Amma mugun gata da saken da ake bata a gidan ya hana komai ma tasiri.

Bata sake shiga taitayinta ba sai ranar da ya sake zuwa hutun kwanaki uku. Shi zam baima wani lura da yadda take mugun gudunsa da d’ari d’ari da shi ba sai a wannan zuwan da yayi,d’ai d’arin da shi baima fahimci akan meye takeyi ba.

A hankali bibi ta fahimci komai,rashin sakewar sultana din a duk sanda akace yau maina ya sauka a gidan,abunda ya dinga taba ranta kenan,ta dinga jin babu dadi. Hakanan zuciya ta dinga yi mata saqe saqe kala daban daban cikin ranta. Kwata kwata itama bibi din sai ta dinga rasa nutsuwarta idan yana nan din,a hankali itama sultanan saita daina kwana dakinta duk sanda maina yake gari,idan kaga ta koma dakinta to baya nan ne ya koma makaranta.

*K’arfe hudu na yammacin ranar,ranar da gidan ya kasance akwai qarancin jama’a,saboda kusan duka yaran gidan sun wuce islamiyya idan ka dauke sultana dake kitchen din bibi a dai dai lokacin. Oat takeson sha amma kuma tanja bata kusa,ita kuma baya ga tanja din bata yarda kowa ma yayi mata komai a gidan sai bibi. Bibi a lokacin bacci take,ita kuma ta matsu da tasha din,abinda ya sanya ta shiga kitchen din kenan ta dinga hada kwabarta.

A qalla babban gwangwanin oat da qatuwar gwangwanin madara ta kusa juyewa cikin bowl,ta kammala tayi tsaye riqe da qugunta tana tunanin yadda zata tafasa ruwan zafi. Tana dari dari saboda tana tsoron wuta,tana kuma iya tuna yadda ruwan zafi ke mugun tururi duk sanda tanja ta saukeshi daga saman gas.

Bacci yayi me nauyi a yau din,saboda muguwar gajiyar dake jikinsa sakamakon training da sukayi duka wancan satin babu hutu,wannan dalilin ya sanya yana samun interval na kwanaki a wannan satin yayo gida,yasan a nan dinne kawai zai huta sosai,kanshi yayi fresh yadda ya kamata,babu me takura masa,koma bayan hostel da ba lallai su sultan su barshi ya huta ba su da gayyar abokansu.

Dispenser dinshi babu ruwa ciki,don haka ya zura jallabiyyarsa me sulbi ‘yar marocco ya sauko ya fito daga dakin.

Tun azahar yasan ama bata nan,don tana da taro na musamman a qungiyarta data bude don taimakawa mata iyayen marayu da zauwara,wannan dalilin ya sanyashi wucewa kai tsaye sassan bibi.

A falo yayi sallama,tunda yaji shuru yasan bacci ne ya sace bibi din,sai kawai ya wuce kai tsaye ya kutsa zuwa kitchen yana mamakin yadda yau sam babu wulgawar masu aiki ko daya a sassan.

Da sallama ya shiga kitchen din,sallamar data sanya zuciyar sultana wani mugun bugawa,wani tsoro ya mamayeta wanda ya sanyata waiwayawa da sauri tana dubansa.

Duba biyu yayi mata ya dauke kashi yana qarasa shigowa, shigowar da ta qarawa sultana razani,ta duba hagu da dama,ba kowa a kitchen din sai su biyu rak,hasali ba motsin kowa ma a sassan sai nata da nashi,tayi wura wura kawai saita sanya gudu tana ficewa daga kitchen din. Da kallon mamaki ya bita

“Anya yarinyar bata samu motsuwar kai ba?,gudun na meye takeyi kamar wadda aka biyo?,ko wani zallar rainin wayonne?” Ya raya a ransa,sai kawai ya juya yaci gaba da takawa,takun da baiyi guda uku cikakke ba ya jiyo bibi tana doka salati,kafin kuma muryarta ta maye gurbi

“Ke!,meye hakan?,waye ya biyoki?,lafiyarki qalau?” Duka bibi ta jefa mata tambayar,tambayar da ta gaza amsa mata sai riqe bibi din kawai da tayi. Har cikin zuciyarta ita kanta tana jin yadda take gudu qwarai da gaske,bugun zuciyar da take motsawa da wani irin qarfi da batasan meye sila ba

“Matsamin ni na shiga naga wanne qaddararren abune” bibi ta fadi tana ture sultana din daga jikinta ta kuma kutsa kitchen din babu tsoro ko dis a ranta.

Cak ta tsaya saboda ganin maina da tayi a kitchen din,ita batasan ma ya shigo garin ba,dama shine ya biyo sultana din?.to me yake shirin aikata mata?, Sai ta runtse ido tana furta

“A’uzubillahi” a sarari saboda wani mummunan tunani da ya d’arsu a ranta

“Dama kaine ka biyomin yarinya?,me tayi maka?,me kuma zakayi mata?” Bibin ta fada zuciyarta tana dan bugawa.

A nutse ya waiwayo ya dubeta,cikin sakanni qalilan ya samu amsar tambayoyin da ya jima yana yiwa kansa game da kaffa kaffan bibi a kansa da yadda yarinyar ke wani guje guje. Murmushi ya subuce masa, murmushin da ya sake dada yawan fargabar bibi

“Me kuwa zanyi mata?,ko tace miki fyade nayi mata?”

“Qaniyarka aliyu” bibi ta furta tana watsa masa daquwa duk kuwa da yadda zuciyarta ke tsananta bugawa. Bai sake ce mata komai ba kamar yadda itama ta kasa ci gaba dace masa komai,saboda qafafunta sunyi nauyi kamar yadda jikinta ya sanyaya,sai kawai ta juya tana fita a dakin.

Qaramin tsaki maina din yaja,shi lamarin nasu ma sam yanzun dariya yake bashi,inda sun kwantar da hankalinsu ma sam ya fidda sha’anin sultana a ransa,duk da abun yana matuqar yi masa wani irin ciwo qasan zuciya,to amma ya ajewa ransa akwai lokacin da zai fatali da komai da kowa ya kuma gyarata koda kowa bayaso.

Tunda ta koma daki tunani iri daban daban yake bijiro mata,har ta shiga bandaki ta daura alwala ta fito duk tuntuni tayi sallar la’asar dinta sultana na maqure saman gado. Kallo daya tayi mata ta dauke kai,ai kuma shikenan,duk wani sakewa da walwala tata tayi qaura,tasan bata da wani sauran sukuni kuma.

Gefen gadonta ta zauna tana fidda numfashi. Ta soma gajiya da mugayen saqe saqen da zuciyarta keyi mata akan maina din,ta gaji da kokwanto,ta kuma gaji da bacci da ido daya,tasan kuma tunda zuciyarta ta dasa zargi akan maina ba zata taba bari ba,ba kuma zata taba bari ta huta ba.

“Gwara na kawo qarshen komai” bibi ta fada tana janyo wayarta.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 26

Bugu biyu rak ya daga wayar,daga can bangarensa cikin matuqar girmamawa yayi mata sallama

“Wa’alaikummus salam warahmatullah,ka yini lafiya ya aiki?”

“Lafiya qalau bibi,alhmdlh,kuna lafiya?”

“Lafiya muhammat,kamar yaushe zaka dawo?”

“Gobe ma nake sanya rai bibi……wani abune ya faru?” Kai ta girgiza

“A’ah babu komai,faduwa ai tazo dai dai da zama,Allah ya dawo dakai lafiya”

“Ameen ya Allah,amma ina fatan lafiya?”

“Lafiya qalau sai alkhairi”

“To Allah ya tabbatar”

“Ameen ya Allah” basuyi doguwar magana ba jin cewa yana cikin jama’a tayi masa sallama ya ajjiye wayar.

Qatuwar ajiyar zuciya ta sake saukewa tana ajjiye wayar,sai a yanxun takejin kamar nauyin dake zuciyarta ya fara raguwa,ta hade hannayenta biyun duka ta lanqwasa waje daya tana furta

“Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammad” sai ta maida dubanta ga sultana. Ga mamakinta har bacci barawo yayi awon gaba da ita,sai ta samu kanta tana me zuba mata idanu,ba abinda take tunawa sai nafessa,shin KO TARIHI ZAI MAIMAITA KANSA?,shin hukuncinta shine dai dai ko akwai gyara?,akwai ta inda ta kuskure?.

Duk ta inda ta laluba a zuciyarta da neman amsar tambayar sai taji ta gayawa kanta da kanta dai dai tayi, addu’a ta dinga yi cikin ranta tana sake tsananta neman zabin Allah,sai ta dinga jin tabbatuwar jin cewa dai dai tayi din.

THE BEGINNING

Hira sukayi a qalla ta kusan mintuna arba’in,irin hirar dake tsakanin uwa da danta. Su biyu ne rak a falon,dai dai sanda agogo ke tafiya a hankali har zuwa sanda ya nuna qarfe tara saura na dare

“Bibi” Sir muhammat mayak’i ya furta yana gyara zamansa

“Na’am” ta amsa masa tana dubansa

“Jiya kin kirani,kuma kiran da kikamin din nasan akwai babban dalili”

“Qwarai kuwa” bibi ta fada tana gyara zamanta

“Wato akwai wani al’amari da ya faru ranar da tafiya ta kamaka safiyar juma’a,washegarin ranar da akaga maina” gyara zamanta tayi ta warware masa komai sannan tayi shuru tana dubansa. Kai kawai muhammat mayak’i yake jinjinawa

“Shi aliyyun a gabanku ya furta wannan mummunar kalmar?,ashe aliyyu bashi da hankali har yau ban sani ba?”

“Na gaya maka ya shigo ya bada haquri,to amma ni gaskiya zuciyata har yau har kwanan gobe bata nutsu ba…..muhammat duk sanda naji motsin maina a sassana sai hankalina ya tashi,duk sanda naji maina yazo gidan nan bani da sauran nutsuwa har sai ya koma. Dani da kai da dukka sauran wanda ya rage cikin gidan nan mun sani,Aliyyu bai taba furta cewa zai aikata abu be aikatashi ba,ina tsananin tsoron sharrin zuciya,ina gudun halin ‘ya’yan yau,ina kaucewa faruwar mummunan abu cikin zuri’ata,ina da tsoro muhammat ina da fargaba,kuma babu abinda zai kawo mini qarshen wannan fargabar sai abu daya…..”

“Idan da raina kuma ina da iko bibi,bazan taba barin mahaifiyata cikin fargaba ba,meye abinda zai faranta miki?”

“A daura auren MAINA da SULTANA,koda har yanzu akwai qudurinsa cikin zuciyarsa,koda zai aikata din zaizo da sauqi saboda ta kasance halalinsa ce ita din”.

Jinjina kai kawai aba yakeyi cikin nazari,saidai tako ina maganar bibi ta gamsar dashi,shi kansa bazaiso ace diyan cikinsa ya yiwa ‘yar mammodu mummunar barna ga rayuwarta har haka ba.

“Juma’ar nan me zuwa nan da kwanaki hudu zan daura aurensu bibi in sha Allah,hakan yayi miki?”

“Allah ya albarkaci rayuwarka muhammat, ubangiji yadda kake farantamin yaci gaba da faranta maka kai da sauran ‘yan uwanka”

“Ameen ya Allah”

“Amma kuma hamdiyya fa?,ina gudun kada tarihi ya maimaita kansa” qanqanin tsaki yaja

“Kada ki sanyata a sahun qalubale bibi,wancan dinma RABO NE YA RANTSE shi ya kawo komai”.

Duk da ba shakka ko shayin hamdiyya ama yakeyi ba,amma haka ya dinga juya yadda zai gabatar mata da zancan,a haka har lokacin kwamciya bacci yayi,ta kawo masa tea din da duk dare saita dafa masa yasha yake kwanciya,tunda jajayen sawaye kawo yau ba tana nan da wannan dabi’a tata bata canza ba

“Allah yayi miki albarka,amma zauna zamuyi magana” ya fadi yana karbar tea din daga hannunta sannan ya kurba kadan yana ajjiyewa saman bedside drawer.

Zaman tayi idanunta bisa kansa tanason jin abinda ya sanya ya dakatar da ita a irin wannan lokacin da yace mata a matuqar gajiye yake,hutawa kawai yakeso yayi sosai

“Kin qagauta kiji meye ko?” Ya tambayeta cikin zolaya,sai ta saki murmushi tana kauda kai gefe. Tana da zafi a wasu al’amuran,ba a komai takan sanya baki ba,tana kuma da kawaici saidai a wasu abubuwan kuma bata da haquri sam ko daukan ganganci ko ba dai dai ba

“Inaso idan Allah ya kaimu juma’ar nan na daurawa danki aure” ya fada cikin halin ko in kula,kuma hankalinsa kwance kamar ba wani batu bane me muhimmanci.

A mamakance ta juyo tana dubansa,kanta yana daurewa tam

“Dana kuma?,wanne dan nawa?”

“Kina da wani shaqiqin d’anne sama da Aliyyu maina?” Ya tambayeta idanunsa cikin nata

“Maina kuma!?” Ta jefa masa tambayar ranta yana motsuwa cikin zallar shakka da mamaki

“Eh mana,amma fa kada kice zaki wani daga hankalinki,ba wani aure bane da za’a yiwa shagali ba,sultana ce kawai zan daura masa aure da ita shikenan suci gaba da rayuwarsu,sauran lamarin kuma mun barwa Allah ikonshi”.

Batasan takai tsaye ba sai da taji qafafunta suna taka qasa,tamkar wadda aka daurewa jijiyon jikinta gaba daya haka taji. Aba ya daga kai ya bita da kallon yadda ta miqe din a razane

“Ko a yanzunma bai isa aure ba kaman yadda kika yi akan nafessa mahaifiyar ta?” Motsa bakinta tayi,akwai maganganu masu yawa a ciki amma sai ya sake datsar hanzarinta

“Kayi GUDUN K’ADDARA iya iyawarka,amma ka sani matuqar tana rubuce cikin littafin KADDARARKA to sai ta iskoka…….shawara daya zan baki,koda wasa kada kice zaki kwatanta abinda kika kwatanta a baya,domin qarshen wannan karon kece ba zaiyiwa kyau ba……an zana a cikin zanen qaddarar sultana maina ne yafi dacewa a daura mata aure dashi a yanzun,bansan gaba ba,bansan kuma me gaban zata haifar ba” ys qarashe jawabin yana jan blanket zuwa qafafunsa.

Kamar wadda aka dasa haka taci gaba da tsaiwa a wajen,ta gaza furta komai saboda wani bahagon yanayi data kasa tantance launinsa dake kai kawo a zuciyarta SO KO K’I?,MURNA KO BAQINCIKI?,oho itama bata sani ba……abu daya dai ta riga ta sanyawa ranta,ta yaya zata so abinda tasan wani irin ZARGE ne me wuyar kwantuwa?,sultana fa?,kaf yaran gidan a rasa waye za’a bashi sai sultana?, sultanar da tun ba’a diga samuwarta a mahaifiyar mahaifiyarta ba ta nesanta tsakanin maina da mahaifiyartata?,ta hana UWA yanzu kuma ‘YA zata maye wannan gurbin na UWAR?,ta yaya hakan zata faru?.

Wadannan dama tarin wasu tambayoyin su ta dinga yiwa kanta ita qwallin qwal cikin dakinta. Batasan da waye zata tattauna wannan maganar me uban nauyi da tarin sarqaqiya ba,abun tana jinsa kamar a cikin mafarki ne kawai bawai a gaske ba,SULTANA?,MAINA?,to waye ya qulla?,……amsar dai daya ce,ta tabbatar bibi ce,da basu cimma nasara ba wancan karon shine a yanxun suka shammaceta?. Gwara nafessa sau malala gashin tinkiya NAFESSA tafi sultana nagarta nesa ba kusa ba,sultana din ALBASA CE wadda sam batayi halin ruwa ba,nafessa bata da wani aibu gabanta da bayan halayenta kaf,banda wani dalili guda biyu rak,bataga abun gufu ga nafessa ba,amma kuma sultana fa?,aibubbuka da abubuwan gudu gasunam birjik basu da iyaka

“Karki matsantawa kanki da yawa,ina kikaga hadi tsakanin maina da sultana?,ko hankali ya bada haka?,barsu suyi iyakar iyawarsu,idan suka sheqa suka samu babu qwaya zasu warware da kansu” hajiya dezatou tace da ita.

Daren gaba daya bata samu wani isashen bacci ba. Da safe da maina ya shigo suna breakfast kallonsa kawai takeyi tasan baisan abinda ke shirin faruwa cikin gidan ba,amma taji aba din yace idan ya kammala ya sameshi a baya ta gurin swimming na gidan,ta tabbatar zancan zaiyi masa.

TOFA MASU KARATU,AKWAI TARIN TURKA TURKA CIKIN LABARINNAN

“akwai BAZATA masu yawan gaske*

inason na jaku zuwa wata kyakkyawar gaba da zata zame mana tamkar tsani ko shimfida na labarin da zamu samu bigire me kyau bayan sallah da zamu dora

SHIN MAINA ZAI YARDA?

“SULTANA FA?*

IDAN HAR HAKAN YA YIWU ME ZAI BIYO BAYA?

AKWAI WATA MURDADDIYAR QADDARA CIKIN LABARIN,WADDA KE ZAMOWA TAMKAR WATA GUGUWA DAKE WAJIGA ZUKATANSU DA ZUKATAN MUTANE DA DAMA

AKWAI TARIN KUKA/NADAMA/SADAUKARWA/BA ZATA DA QARFIN DA QADDARA KE DA ITA CIKIN RAYUWAR KOWANNE BAWA

INA SAKA RAN GOBE NA BAKU SHAFUKAN DA ZASU ZAME MANA MURFI NA LABARIN IN SHA ALLAH,MURFIN DA ZAI RUFEMU HAR ZUWA BAYAN WATAN AZUMI

HUGUMA CE 👑👑

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

Page 27

Kamar yadda aba ya buqata,maina bai gusa daga gidan ba har sai da ya sameshi cikin balcony dinsa dake bada kyakkyawar iska tatacciya. Yana tsaye sanye da kaftan abaya me sulbi wadda yadinta ke fadin irin kudi da tsadarta. Hannunsa duke da daya daga cikin jaridun qasar nijer din yana dubawa ta cikin eye glasses din da ya yiwa kyakkyawar fuskarsa kyau,fuskar da har yanzu kyanta bai gushe ba,kyawun kuma dake bayyana adadin sharafin samartakar da aka sha a shekarun quruciya.

“Zauna maina” ya fadi yana daga tsayen ba tare da ya zauna ba yana nuna masa kujera. Komawa yayi da baya ya zauna,yayin da aba ya ajjiye jaridar hannun nasa saman wani dan table,ya kuma goye hannayensa a qirjinsa yana duban idanun maina

“Kasan me yasa na kiraka?” Kai ya girgiza a hankali,sai aba ya saki hannayensa yana gyara tsaiwarsa

“Ranar juma’ar nan me zuwa zan daura maka aure kai da sultana,nace bari na baka labari kafin kaji a wani guri gwara kaji a bakina……..don banason duk wani bore ko wani motsi na rashin amincewa,to kawai nake da buqatar ji daga bakinka” yakai qarshen zancansa yana qoqarin bude ruwan gora don yasha.

Wani yarrrr maina yaji tun daga saman kansa har yatsun qafarsa

“Sultana ‘yata aba?” Ya jefa masa tambayar cikin wata murya me cike da sanyi

“Yar nafessa dai da mamuda ko?” Ya maida masa amsa kai tsaye,sai kawai maina din ya sadda kansa qasa.

Bayajin komai akan hakan,shi kawai abunne yaji ya masa banbarakwai. Dukka shirin bibi ne wannan ya tabbatar,saboda ya gama karantar takunta fes,wai ita a lallai tsoronsa take kada ya bata mata jika. Tuna hakan da yayi ya kusa sanya dariya ma subuce masa,wannan auren ai kawai wahal da kansu su aba zasuyi,baiga ma abun tada jijiyar wuya ko daga hankali ba,ya fahimci auren fakewa ko auren jingina bibi keso ayi saboda tsabar bata sadaki da batawa mutane lokaci,shi da zai wuce makaranta ma ranar alhamis kuma sai an sake ganinsa?. Wannan tunanin ya sanyashi miqewa yana fadin

“Allah ya sanya alkhairi” kawai a gajarce. Da ameen aba ya bishi,dama baya sanya ran maina din zai wani kawo matsala me yawa,ta inda ya zaci ma zai iya taurarewa saboda sabanin fahimtar da ya shiga tsakaninsa da yarinyar da qaqqarfar rashin jituwa.

Yana saukowa ama na tararsa,tun daga qafar bene na qarshe

“Me yace maka?,kaji abinda ya ballo kuma?” Tayi maganar fuskarta kwance da muguwar damuwa da rudani. Hannunta dukka biyun ya kama a nutse ya isa da ita saman kujeru ya zaunar da ita

“Zauna don Allah ama ki daina damun kanki,wannan wani game ne kawai da bibi ta shiryashi,kada ki daukeshi wani abu me muhimmanci don Allah,ranar alhamis ma ni zan koma makaranta” ganin bai daukaki al’amarin ba shima sai taji hankalinta yadan kwanta,ta sakawa ranta salama kadan,saidai kuma abun yana damunta qasan zuciya. Wai a rasa kaf gidan da waye za’a masa wannan gantalallen daurin auren sai sultananan?,yarinyar da ta gallabi kowa?,ko su kuwa basa iya controlling nata?. Saita ajiye doguwar ajiyar zuciya tana mamakin yadda suka dauko al’amarin da bazasu iya warwareshi ba,don ko ita ina bata hango wata mafita ba sai sake dagula komai.

Shirin komawa makaranta abinsa yaci gaba dayi hankalinsa kwance,don shi a wajensa wannan abun dai dai yake da buga wasanni,koma meye suka shirya oho,shidai ko meye ma a yanzun baida lokacinsa bashi kuma da plan dinsa sam sam.

Sultana kam sanda bibi ke gaya mata wai za’a daura mata aure da maina ranar juma’a maida bibi tayi kaman wata nini dinta da take wasa da ita,ta dinga qyalqyala dariya harda buga qafa,su aminata dake zaune da yasmine sai suka fita hankali ma,su kansu kallonta suke saboda yadda ta maida lamarin wani abun wasa

“Nice matar maina” ta fadi tana wani lanqwashe murya,sai kuma ta saka dariya

“Allah ya sawwaqe,tabdijan,ni kuwa me zanyi da wannan mutumin?,dan iskan me cewa zaiyiwa mutane fyade?” Duka bibi ta kaiwa bakin sultana,ta tsani jin wannan kalmar daga bakinta,tadan sameta kuwa amma baiyi yawan da za’a zuzutashi ba,ai kuwa ta bare baki ta saki kuka

“Na sake jin kin furta wannna kalmar a bakinki fasa bakin zanyi sosai,ba irin wannan shafar mai ba”. Kuka tuburan ta zauna tana ma bibi,tun bibi din na shareta har kukan ya fara damunta,tanja tayi lallashi tayi lallashi har ta gaji,sai suka fahimci mafaka take nema saboda dama ranar Monday za’a karbo result na exams dinsu,tanja ta gama fahimtar kome,batayi abun arziqi bane shi yasa takeson ta fake da wannan.

A dole bayan bibin ta gama shareta kuma ta dawo tana lallashinta. Suna tsaka da wannan ya shigo rataye da jakarsa a baya wadda take set ce da luggage dinsa. Sultana ce ta fara barin falon da gudu gudunta ta wuce ciki bata ko waiwayi inda yake ba. Sai a yau ya sake fahimtar abinda yarinyar takeyi

“Saina koya miki hankali “ya fada qasan ransa,saboda mugun haushi abun ya bashi,dukka su aminata suna wajen,waye ta gani ya firgita haka ko ya gudu?,sai ita?. Bibi din ya yiwa sallama kamar ko yaushe

“A sauka lafiya” ta amsa masa da shi tana binsa da kallo sanda suke fita shida goumar,baki ta tabe tana jinjina kai

“Miskili kafi mahaukaci ban haushi” ta fadi a fili qasa qasa,har yanzun bai nuna mata komai ba akan batun daura auren,so ko qi duk bata fahimci komai ba.

To koma meye can ta matse masa,itadai da wata barnar gwara wata,hankalinta zaifi kwanciya idan sultana ta amsa sunan matarsa,ko mene zai biyo baya kuma me sauqi ne.

Kamar yadda suka qudurta a ranar juma’a din aka daura auren SULTANA MAHMOUD MAYAK’I da angon ALIYYU MUHAMMAT MAYAK’I. Daurin auren da yayi matuqar daurewa dangi kai,saboda muguwar ba zata da ya yiwa kowa.

“Maina din da ya raini sultana?,ya zame mata kamar uba ko wani shaqiqin yaya?,ashe shi zai aure kayarsa? Maganganun da suka dinga yawo kenan.

“Ina almurin,ashe kansa ya yiwa kiwo” wata qanwar bibi ta fadi sanda ta iso gidan. Itadai bibi murmushi kawai tayi,domin kuwa ita kadai tasan dalilin da yasa hakan ta kasance,kuma ita daya take tunanin me gobe zata haifar?,ya zata kasance musu dukkansu a gaba?.

Ga sultana kuwa a ranar ma suna sharafinsu ta sulale tayi ficewarta gurin rawar taron sunan maman qawarta da akeyi. Ranar ta jijjigi rawa yadda ranta keso,sai daga bisani wata maqociyarsu da taje taron sunan ta kamota ta jata gefe tana tsareta da ido

“Halan bibi batasan kin fito ba?”

“Eh suna can suna taro” ta bata amsa cikin halin ko in kula. Kai sosai fattu ta girgiza,batasan wacce irin zallar wauta ke damun sultanan ba

“Kinsan me ake nufi da aure kuwa sultana?,zauna dai tukunna” fattu ta fadi tana gyara mata wajen zama. Bata musa ba ta zauna saboda dama ta gaji sosai saboda rawar da tasha.

Ba abinda ta boye mata,ta warware mata komai game da abinda ake nufi da aure. Mugun baci ranta taji yayi,wato abinda bibi ke nufi kenan?,dama tasan abinda ake nufi din tace a aure mata maina din dan iska?,sun bashi damar yayi mata fyaden kenan,yama kasheta a cikin gidan kenan tunda daga yau yafi kowa da kowa dake cikin gidan iko da ita,to ita kuwa daga yau su zuba da yaa maina din,zai gani idan zai juyata yadda yakeso yake kuma buri.

Driver dinta fattu ta sanya ya maidata gidan,bata qi ta fattu ba don ranta a bace yake,hakanan kuma jikinta a sanyaye yake,ta dinga juya maganganun da fattu tayi mata a ranta sanda suke hanyar komawa gida

“Tabdijan” ta dinga maimaitawa lokaci lokaci tana gyada kai. Ita za’a yiwa irin wannan abun?,taga yadda hakan zai faru kuwa ita.

Sanda ta koma cikin gidan ba wanda ta kula,ta wurwuce abinta har zuwa quryar dakinta ta kulle ta shiga hidimar data dameta.

Ko bayan an watse fushi ta shiga yi da bibi,kusan kwana uku bata shiga sabgar bibi,saboda tana ganin ai an hada baki da ita ne za’a cuceta kawai. Saida bibi ta gaji da halin nunqufurcinta sannan ta isketa a daki ranar. Vest ne a jikinta da wandonsa iya cinya tanata game abinta,ta zare ribbon din kanta taqi ta hade sumarta waje daya,taqi kuma yarda tanja ta taje mata a gyara.

“Ke me yake damunki ne sultana?” Bibin ta fada cikin fada fada

“Ni ki qyaleni,bayan an hada baki dake za’a kasheni a gidan nan” idanu bibi ta fidda waje

“Kisa sultana?,ashe baki da hankali”

“Allah bibi,kawai sai ku auramin maina?,idan aurenne saiku bari na sake girma naga wanda nakeso ba wannan…..”

“Ya isa,kiyimin shuru haka haba” bibi ta dakatar da ita kafin ta sake ballo wata maganar,don a yanzun dole a hankali a hankali ta soma nuna mata yadda zata darajta maina din,tunda ko banza igiyar aure nauyi da girma gareta.

A nan tayi borenta ta gama suka kuma shirya da bibi,don dama tsakaninsu ba’a shiga.

Ganin bai sake waiwayar gida ba kuma babu gilmawarsa saita sake abinta sosai,taci gaba da sakalcinta cikin gidan,duk da a wannan karon abubuwa da dama bibi tana tarota,tayita zuba ido taga ko ama zata nuna wani abu ko zata dinga sanya baki cikin sha’anin sultana din amma sai tayi kaman bata cikin gidan,koda a gabanta sultana zatayi abu kaman da can baya dauke kai takeyi ta wuce abinta. Bawai don bata sane ba,tana sane da komai tana kuma biye da komai,ta watsar dinne saboda kama girma da mutuncinta kamar can baya.

FAREWELL
But
A new chapters unfold

**** Satittika har guda gudu cur yayi babu shi ba labarinsa cikin gida. Haka kawai yaji baya sha’awar komawa gidan,sai kuma abubuwa sukayita shigowa na uzururrukan makaranta da suka sake riqeshi,don haka ya fidda batun ma zuwa gida,har sai da aka shiga sati na biyar. Satin da yazo da wata GAGARUMAR QADDARA……QADDARAR da ta zama sila ta wanzuwar komai. Qaddarar da dukkanin ahalin mayak’i basu taba koda hakaitota cikin tunaninsi ba. Qaddarar da ta d’aid’aita farincikin wasu da dama ta qulla wasu alaqoqi ta wargaza wasu……..ta nesanta na kusa ta kuma kusanto da na nesa. Ta jefa ALHINI TARIN BAQINCIKI NADAMA DA TAKAICI ME TARIN YAWA A ZUKATAN WADANSU.

NAYI AJIZANCIN NAWA,A YAU NASO NA BADA DUKKA SHAFUKAN SAI WASU HIDIMOMI SUKA RIQENI,AMMA A GOBE IN SHA ALLAH ZAN BADA WANDA YA RAGE DIN

KARKI BARI A DORA TAFIYAR GUDUN K’ADDARA BAKI KASANCE DA GROUP DIN BOOK DIN NA HALAL BA

JAZAKUMULLAH.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

Page 28

***Wani irin jiki ne da ita wanda baya qaunar zafi ko kadan,wannan ya sanya take da vest da wandunansu masu yawa da takan sanyasu koda kuwa bawai zafi akeyi a garin ba. A hakanma bibi din ta kwashe wasu ta bayar saboda ta fara girma baici ace tana ci gaba da sanyasu ba.

Su hudu ne a falon,bibi din,deeja mai aikin bibi,tanja sai sultana din da tanja ta kama kan nata take gyarawa. Ana gyaran kan tana qorafi don ita sam bata son a taba mata suma. Yatsuntsa guda goman duka lalle ne aka saka mata. Idan akwai abinda takeso cikin ado kaf to jan lalle ne,shi dinma kuma bawai tana iya zama bane ayi mata qafa da hannu ba,saidai ayi mata iya yatsun qafa ko iya yatsun hannun.

Sallamarsa cikin falon goye da qatuwar jakar ‘yan makaranta ta tsaida numfashi na daqiqu daga jikin sultana,sannan tayi wani tsallen albarka tana miqewa,da sauri tanja ta riqota amma tuni ta zille,lallen kuma dake hannunta ya sabule yayi nasa guri,bata kuma tsaya ba ako ina sai daki.

Dukkansu suka bita da kallo har ta qule cikin dakin. Wani abu ya hadiye yana qarasowa cikin falon. Karon farko da ranshi ya baci akan abinda takeyi din idan ta ganshi,ya karanci abun nata harda iskanci da iya shege,banda hakan daga sallama kamar wadda taga mala’ikan daukan rai.

Bayan sun gaisa su tanja miqewa sukayi suka basu guri kamar ko yaushe. A yau din bibi ta sakar masa sosai kamar yadda suke a baya,har abun yadan bashi mamaki

“Sai yau aka tuna damu?” Ta fada tana ‘yar dariya

“Sai yau akaga damar sakarmin fuska?” Ya fadi yana dage mata girarsa guda daya fuska a dinke tsaf. ‘yar dariya tayi tana watsa masa daquwa

“Ungonan ja’iri, gidanku”

“Oho……ni gaskiya kenan na fada ai” ya fadi yana samun gurin zama sosai.

Ya kusa awa guda gurin bibi din suna hira,amma ko motsin sultana bai sake ji ba har ya fita a sassan.

Ya samu ama da baqi wajen mutum hudu,kuma dukkansu dangin aba ne,don haka daga tsaye suka gaisa ya juya zai wuce sashensa,saboda yau din a mugun gajiye yake,yanason kuma yadan fita bayan ya huta

“Bikin ni’imatu akeyi fa aliyyu” ama ta fadi tana dan murmushi saboda tunawa da tayi da irin drama din da akayi akan ni’imatu din da maina. Tayi mutuwar sonshi kamar ba gobe,shi kuma yayi matuqar qin jininta,haka nan tun suna qananu. Yana da wani irin hali, zuciyarsa me girma ce ba kasafai soyayyar wata ke burgeshi ba.

“Allah ya sanya alkhairi” ya furta a taqaice yana gyara maballin wuyan rigarsa da hannu daya

“Zaka fito ne yanzu?” Ama ta sake tambayarsa

“Eh to,bacci ne a idona da yawa,wai da inason nadan kwanta”

“To qilan kafin ka tashi ka samu gidan ba kowa,don dukka zamu gurin kamun amarya”

“Okay,sai kun dawo,amma zan dauki key daya na mota da ita zan fita” sai ya qarasa yana daukan key din da ya gani saman table yana ficewa.

Yana yin wankan kuwa baccin yayi awon gaba da shi,bai farka ba sai bayan sallar la’asar,har sallar taso kubce masa. A gurguje ya daura alwala ya fice masallaci. Sanda zai dawo din yaga sun fara shirin fita,don masu mota a cikinsu sun fidda motocinsu daga parking space.

Ya samu ama ta bada abinci a kawo masa,amma sai baici ba,ya duba lokaci,ya tabbatar idan yakai dare wajen masu mishi gyaran gashi zaya samu layi sosai,don haka kawai yahau shiri da zummar idan ya dawo yaci abincin.

Cikin wani red shirt me gajeran hannu ya shirya,yayi kyau ainun,hakanan gashin da ake cewar za’a je gyaranshi ba wani alamun buqatar gyara sam a tattare dashi. Nannadaddiyar sumar nan me santsi irin ta asalin abzinawa buzaye. Wani boot ya sanyawa qafarsa,gwanin saka boot ne sosai ko don saboda kyakkyawar alaqar dake tsakanin aikinsu da takalmin?.

A dan gaggauce ya fito,mutanen gidan har sun fara fitowa,sai ya wuce abinsa kai tsaye yana duban key din motar da ya dauko yana nufar motar.

Ita daya qwallin qwal shigarta ta banbanta da dukka shigar sauran ‘yan uwanta,cikin high tummy plazo me rawa take da wata riga mahadinsa me gajeran hannu. Wando ne me azabar kyau da tsada wanda ta hadashi da wani high Hill shoe me madauri wanda yake mahadin qanqanuwar handbag din data saqale cikin yatsunts. Wasu irin fashion earrings ta sakawa kunnenta,wanda bai zuwa da sarqa saidai abun hannu da agogo da kuma zobe. Gashintannan me azabar tsaho da santsi an masa wani gyara na musamman,wani ya duba gaban fuskarta yabi ta gefen kunnnenta,ta hade da sauran na bayan ta matseshi cikin band me kyau da qyalli. Kallon daya idan kayi mata zaka iya rantsewa da Allah daya daga cikin diyoyin celebrities na qasar india ne,don muddin ba baki ta bude tayi maka magana ba,zaka kafe ne da cewa ko zo na kasheki bata sani da kowanne yare ba idan na indiyanci ko larabci ba,don sakkk kamanninta suka alamta hakan.

Ba waje ba,iya cikin farfajiyar gidan kadai da ta tako dai data dauki hankalin kowa. Dai dai kuma sanda maina ke fiddo motar daga cikin jerin sahun motocin yana duba bayansa ta cikin madubin motar don ya fita da kyau ba tare daya taba kowacce mota ba idonsa ya sauka a kanta.

Dukkansu najma kowacce doguwar rigar atamfa ne gown a jikinta,harda siraran mayafansu,to amma sultanar ko hula bai samu arziqin sanyawa ba bare aje ga batun mayafi. Har yaja motar gaba kadan yana dauke idanunsa daga kanta wani abu daya darsu a zuciyarsa ya sanya ya tsaida motar

“Idan a baya baka da right,yanzu kana da cikakken damar da zaka hukuntata ka kuma bata kowanne kalar umarni da kakeso,babu me cewa don me,wannan abun da sukayi sun baka cikakkiyar dama ne a hannunka da zaka saitata yadda ranka keso ba tare da sunsan da haka ba” ya gamsu qwarai da wannan maganar,sai ya sanya hannu ya danne horn din motar tashi.

Dukkansu aminata dasu yasmine dake tsaye hankalinsu yayo gurin harda sultanar,amma sai sultanan ta dauke kanta. Hannu yasa ya kirayi aminata. Gabanta yadan fadi sai ta hau raba idanu,sannan kuma a hankali ta fara takowa

“Jeki kiramin SULTANA” ya fada yana bude aljihun gaban motar. Juyawa tayi da sauri ta koma gurin sultanan

“To me zanyi masa?” Ta fada tana bata fuska tare da murguda qaramin bakin nan

“Oho na sani?,sha’anin miji da mata?” Aminata ta fada cikin tsokana,uwa uba itadin tadan girme musu saboda haka ta fisu wayo a wasu abubuwan.

“Kinga aminata banason iskanci, don ni ba ‘yar iska bace,kije ki gaya masa bazanje ba” ama dake dan gaba kadan dasu maganar ta sauka a kunnenta,tasan dama za’a rina,amma sai tayi kaman bata ji ba. Idanu aminata ta fidda

“Ni bazan iya ce masa haka ba wallahi”.

“To sai kiyita tsayawa a nan” sultanar ta sake fada tana juya mata qeya.

Shurun da yaji yasan akwai walakin,don haka ya fito da kansa. Tun kafin ya qaraso suka dare daga wajen,banda sultana din dake tsaye,duk da zuciyarta nata faman bugawa amma ba zata nuna masa tsoronta ba har ya qaraso

“Ita bibi din tana kallonki kikayi wannan shigar?,wuce ciki ki saka atamfa ta mutunci kamar kowa” ji tayi duk duniya kawai ya gama raina mata hankali,ta yaya ta gama target dinta zaice ta wani canza shiga?,ita sam bataga ma ta inda zata cire wadannan kayan ba.

“Atamfa?,zafi fa akeyi,ni zafi takeyimin a jikina” ta fada tana tura baki gaba

“Zaki wuce ko sai na tattaka wuyanki a gurin?!” Ya fada cikin matsananciyar tsawar data sanya dole ama ta qaraso gurin,fon tasan tabbas akaci gaba da haka to zasu raba abun fadi a gurin,gashi akwai sauran mutane a farfajiyar gidan

“Ya isa maina,ke sultana jeki canza din kizo ku wuce,ki daina musu kai kuma ka dinga sassautawa fushinka” bata sake musantawa ba ta juya zuwa ciki din,abinda bata taba tunanin akwai wanda zai sakata tayin ba,sai gashi ta canzo atamfar. Haka kawai take masifar ganin kima da kwarjininta,tasan cewa kwata kwata bata cikin jama’ar dake takura mata cikin gidan,zaiyi wuya tace mata yi ko bari wannan ya sanya takejin ko meye tace mata tayi din zatayi shi.

Qin fita yayi kaman yadda yayi niyyar yi da farko,sai ya koma kawai cikin motar ya zauna yana monitoring dinsu,har suka kammala shigewa motocin suka fice. Haka kawai yakejin sai yayi da gaske,kuma babbar dama ce tazo hannunsa na saita komai,don haka ya kunna motar ya tasheta yabi bayansu.

Babban event ne me tsada girma kyau da kuma tsari,akwai babban majigi daga waje da zaka iya ganin dukka abinda ke faruwa a ciki. Sai ya samu gurin parking cikin motocin al’umma dake wajen ya ajjiye motar tasa,ya kuma sauke dukka glass din ta yadda zai iya ganin dukkan abinda yake faruwa da kai kawo a wajen.

Jinsa yake a takure gaba daya a gurin,kasancewar sam baya son hayaniya,kuma irin wadannan guraren ba wajen zuwansa bane. Kujera motar yadan kwantar kadan ya maida bayansa jiki,ta qasan ido yake ci gaba da kula da komai,har zuwa wani lokaci da yaji ihu sowa da kuma tafi sun cika wajen.

Dubansa ya maida ga allon majigi din dake waje,idanunsa kuwa sukayi kyakkyawan gani. Sultana a tsakiyar fili tana ta cashar rawa,mayafin da ya tilasta mata sakashi ma baya ko a hannunta bare kanta. Tsam ya tashi ya zauna yana dubanta,family and friends sun rude dayi mata tafi,masu liqi kuma sunyi,sai step din ya fara cika da mutane saboda ita. Wani irin salon rawa da tunda yake bai taba ganin irinta ba,bai kuma taba tunanin ta iya rawa haka ba.

Daga gefe ya hangi isowar ama,ta saka hannu a dabarance ta janyeta daga gurin. Hannunsa ya nutsa saman sumarsa yana rufe idanunsa,wani takaici yana cika mishi zuciya. Iska me zafi ya furzar yana ji har cikin ransa lallai tabbas dole ya dauki mataki tsatstsaura a kanta,matakai take buqata masu tsauri,baiga ta inda sassauci zai gyaro sultana ba,bayan kullum qara girma takeyi kuma sake sangarcewa takeyi.

A zafafe ya tayar da motar yana barin wajen ransa yana sake dugunzuma. Da irin wannan bacin ran ya isa wajen askin. Dama can bame yawan magana bane,don haka har akayi aka gama yabar wajen ba maganar da ta hadashi da kowa.

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

PAGE 29

Guraren tara da rabi na dare ya suka shigo gidan,yana jin sanda suka dawo gidan,yana zaune daha balcony din ama. Abinda ya qara masa takaici kowa da qafafunsa ya taka ya wuce ciki,amma ita sai da tanja ta rirriqeta saboda gajiya da bacci,ya dauke kansa yana jan tsaki sannan ya miqe yana sauka daga wajen.

****K’arfe sha biyu na rana ya fito daga sashensa,sunata shige da ficen tafiya kamun amarya anjima kadan. Wadanda ba’a yiwa qunshi ba su najma suna sassan bibi ana musu.

Falon ciki ya wuce ya zauna,sai bibi din ta fahimci kaman yanason yin magana ne da ita,don haka koda ta fito daga kitchen sai tabi bayansa.

“Meye da meye yau za’a yi a gidan oncle issoufou?”

“Kamun amarya ne yau din ai,da dare kuma su wuce dinner,shikenan an gama don gobe zasu wuce ghana da mijin,babu batun rakiyar amarya” kai ya jinjina

“Koda ba’a gama bama,bana buqatar SULTANA ta sake fita ko ina,bawai bikin gidan oncle issoufou kawai ba,kowacce unguwa ma daga yau,daga makaranta sai gida……..” Bai dire ba ihun kukanta ya ratsa gurin.

Sam bai ma kula tana wajen ba,ya waiwaya yana dubanta,shigowarta kenan sai ta watsar da abinda ta shigo dashi din ta shiga kuka da gaske kamar qanqanuwar yarinya.

“Wallahi sai naje Allah sai naje” ta dinga maimaitawa bakin fal da tsiwa da rashin kunya

Idanu ya zuba mata zuciyarsa tana tafasa,tabbas idan yaci gaba da zama a wajen zai mata mugun duka ne wataqila,kuma ama ta gargadeshi akan hakan,don haka sai ya miqe yana barin falon,amma cikin zuciyarsa yana tabbatarwa kansa tabbas yau zai mata gargadin da ba zata sake mararin maida masa magana ba.

Babu irin kukan da magiyar da bata yiwa bibi ba amma dukka suka taru suka bata haquri,tana kuka cikin falon bibi din tana jin tashin motocinsu suka fice suka barta,aka barta ita daya daga tanja sai deeja.

Da gudu ta diba tayi dakinta tana sake rusgar kuka,cikin zuciyarta fal tsana da haushin maina. Na meye zai hanata sakewa kaman kowa?,me ta tsare masa ne?,yabi ya damu rayuwarta cikin gidan sama da rayuwar kowanne mutum?. A duniya batajin akwai wani mutum data tsana sama da yaa maina a yanzu.

Tun tana kukan da sauti tanja na bata haquri har tanja dinma ta gaji,don bakinta kaman zaiyi ciwo,sai kuwa ta sauqaqe mata ta hanyar cewa

“Ki fitarmin daga dakina,ai harda ke aka kada baki,kuma wallahi bai isa ya hanani fita ba,ai ba ubana bane” ta fada da qarfi cikin zafin zuciya kaman tana gabansa. Juyawa kawai tanja din tayi tabar dakin,ta sani idan ranta ya baci komai ma zata iya fadi indai sultana ce.

K’arfe biyar saura na yamma ya dawo daga sallar la’asar da ya fita. Gidan ya dauki shiru,sai securities dake bakin aikinsu. Su dinma babu yawaitar kai kawonsu,saboda ganin yammaci ne,kuma babu yawaitar zirga zirgar al’umma cikin gidan bare unguwar da dama ba mutane ta cika ba.

Dakinshi ya koma ya aje wayoyinsa,sannan ya sake fitowa yana nufar sassan bibi da yayi imani zuwa yanxun bibi ta tsufa gidan biki.

Tun daga falon farko har na biyu ba kowa,sai na’urori dake ta faman aikinsu,ya kashe wasu ya wuce wasu har ya dangana da qofar dakin sultana,sai yadan dakata kadan,ya dage kaftan abaya dinsa ya zare belt din wandon jikinsa,sannan ya murza qofar dakin ya tura ya shige.

Tarwai dakin yake da haske,sai tarin ledojin madararta da Allah ne kadai yasan daga dare zuwa wunin yau guda nawa tasha. Yadda take bata muhimmanci sam abinci baya cikin tsarinta haka,da a rasa madararta gwara a daina girki a gidan ita a wajenta,komai nisan dare idan ta laluba babu ita to ko a ina taje sai an nemota,duk kuwa da cewa tafiyayya ce daga niamy ake jibge mata ita me tarin yawa.

Tana daga bari daya na gadon,kwance cikin kwanciyar rub da ciki wanda tayita ne daxu da tana kuka,daga kukan kuma ta zarce baccin. Hannunta daya ma ya sauko daga saman gadon,sumarta na barbaje saman filon,haka gajeriyar gown din jikinta ta tattare zuwa cinyoyinta.

Kadan yake ganin fuskarta,a hakan da take bacci zakayi tsammanin wata innocent ce,amma ba komai sai zallar fitsara rashin kunya da tarin raye raye da waqe waqe. Cikin ransa ya gama hango yadda zai firgitata,don haka ya matsa ya rage wutar dakin sannan ya tako a hankali ya tsaya a kanta.

Kamar wadda aka sanarma ko kuma taji cikin jikinta saita motsa kadan,tayi juyi zuwa hannun damanta dai dai sanda idanunta suka hango mata tsaiwarsa a gefen gado.

Razananniyar qara ta saki tana watstsakewa daga baccin ba tare data shirya ba. Ko gezau baiyi ba yana daga tsayen yana kallonta da lion eyes dinnanan nasa da suke da wani irin haske. Fuskarsa a dinke murtuk irin murtukewar da bata taba ganin makamanciyarta a tattare dashi ba.

Wani bugawa zuciyarta tayi bugun da ya kusa wucewa da numfashinta sanda zuciyarta ta raya mata wani abu,matsanancin tsoro rudu da firgici suka shigeta sanda tunaninta ya fara dawowa ta tuna cewa bibi fa bata nan,bama bibi ba,kowa na gidan baya nan,tana tunanin daga ita saishi

“Dalla malami ka fitarmin daga daki,kaga kowa baya nan ko?,to idanma FYADE kazo kayimin wallahi baka isa ba” ta fada da wani irin accent na zallar rashin kunya,rashin kunyar da take ganin itace kadai zat qwaceta

“Dalla malami?” Ya fada cikin tsananin bacin rai yana nufota

“Eh na fada din ba hak……” Bata sauke ba ya fidda hannu ya zabga mata mari. Qarar marin da a kunnuwanta suka tariyo mata kalaman wancan ‘yar sandar

“Eh ai dama kafin suyi aika aikarsu saisun mammare ‘ya’yan mutane sun bubbugesu da duka” maganar data tabbatar mata da gaske maina yazo ya aikata ne. Don haka tayi kukan kura ta miqe tsaye tsakiyar gadon ta fara ihun fadin

“Wayyo ku taimakeni,fyade zaiyimin,wai ba kowa?,tanja!…..tanja!”

“Shut up!” Ya fada da qarfi don tana neman cika masa kai da hayaniya ta kuma rudashi

“Wallahi bazanyi shuru ba,fyad……”

“Shut up stupid!” Ya kuma fada yana haurowa da zafin nama saman gadon. Kalmar fyaden idan ta fadeta yana jin kamar tana yankar zuciyarsa ne. Sai ya miqa hannunsa ya fincikota

“Shashasha mahaukaciya,bakisan fyade ba ko?,to zakisan yau me ake nufi da shi” ya furta yana ingizata saman gadon. Wani irin matsanancin fushi yakejin ya saukar masa,zuciyarsa na masa tariyar sanda ta fara jifansa da qazafin,yana jin idan ba maganinta yayi ya tabbatar mata da abinda kalmar ke nufi a aikace ba ba zata daina jifansa da mummunar kalmar ba.

Abinda yake shirin aikata matan bai sanya bakinta mutuwa ba,sai zagi data fara jifansa dashi ganin yana qoqarin rabata da gantalalliyar rigar jikinta. Yadda bakinta ya kasa mutuwa tsoro yaqi shigarta shi ya sake tunzurashi,ya kuma iza wutar fushin dake ruruwa a zuciyarsa. Sai kawai ya sanya mata dukka qarfinsa don ya nuna mata ya kuma TABBATAR mata da girman tazarar dake tsakaninsa da ita,ya fara yage rigar yana zubarwa. Nata qarfin ta sanya tana tunanin zata iya qwatar kanta dashi,saidai kuma inaaa…..wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,ba abinda dan qarfinta ke iya tabuka mata. Sake tattaro qarfin nata tayi don masa waigi daga shiga wajen da ya nufa din tana kiran masa Allah ya isa,Allah ya isan da yakejin kamar ta watsa masa wuta,hakan ya tunzurashi ya sake saka mata Mari kuncin hagu da damanta,marin da ya sanya labbanta na qasa fashewa,ya kuma dauke mata wuta gaba daya,wutar da bata tashi dawo mata ba har sai da ya soma shiga katangaggen shingen da ko kusa ko alama ba’a tsammaci budeshi ba a irin wannan lokacin.

Azababbiyar azabar da ta zarta ta marukan da tasha a hannunsa ya ratsata,tun daga tafukan qaffaunta har tsakiyar qwaqwalwarta. Kumburarrun idanunta da sukayi kwanciyar jini ta gefansu ta rintse tana jin numfashinta yana barazanar barin gangar jikinta a hankali,saidai duk da haka bakinta bai fasa fadin muggan kalamai a kansa ba,zuciya cike da tsana,gangar jikinta bata gaza ba tana qoqarin ganin ta dakatar dashi da sauran qarfin da takejin tana dashi har zuwa sanda ruhi da gangar jikinta suka gaza daukar lalurar maina,suka kuma gaza daukar girman nauyin da ya azawa qananun shekarunta numfashinta ya fara fusga a hankali,dukka kalamanta suka gaza,idanunta da ganinsu ya raunata ainun suka rufe,bakinta kuma yayi shuru kamar yadda numfashinta ya fice fit daga gangar jikinta,komai nata kuma ya tsaya cak,wanda duka wannnan maina bai lura dashi ba.

Wani irin abu da bai taba kwatanta jinsa cikin jikinsa ba yaji yana ratsashi,wani irin yanayi da bai taba cin karo da kwatankwacinsa ba,daga gangar jikinsa har zuciyarsa wasu mabanbantan al’amura ne ke tarayya cikin kowannensu,jikin da kuma zuciyar. Yayi wani ficewa daga hayyacinsa,fitar hayyacin da ta sanya yayi wata mummunar barna,wadda bai ankara ba sai bayan shudewar wani zamani.

Ya zare jikinsa daga na sultanan,hankalinsa da nutsuwarsa suna dawo masa sannu a hankali. Wani mummunan firgici ya tsinci kansa a ciki sanda ya dafa hannuwansa saman gadon ya jisu cikin damshi ainun. Koda ya duba sai yaga kalar ja,jar kalar dake alamta masa lalllai jini ne,jini kuma me yawan da ya sukurkuta masa tunani

“Jini?,daga jikin wa?” Ya fada muryarsa na wani irin rawa. Da mugun hanzari ya yaye dan blanket din da ya rufe sultana dashi,a nan ya samu ainihin amsar tambayarsa.

“Sultana!” Ya kirayi sunanta da wata razananniyar murya. Dukka hannunsan ya sanya ya dagota yana duban fuskarta.

Kowacce halitta dake fuskarta ta sauya kamar yadda gangar jikinta ya saki gaba daya. Ba wani abu dake motsi a jikinta,saima sandarewa da yaga tayi. Hancinsa da ma bakinsa yakai ga fuskarta,ba numfashi ba alamarsa,sai sanyi da fuskartata da kuma tafukan hannayenta sukayi.

“Ta mutu!” Ya fada a gigice bayan ya sanya yatsunsa biyu a jijiyar daya tabbatar a karatunsu muddin bata harbawa to batun rayuwa a tare da mutum

“Sultana!” Ya sake kiran sunanta wanda ya taho hade da gunjin kuka.

Kansa ya kifa saman tata fuskar ya saki kuka me qarfi,kukan da tsahon rayuwarsa bai taba yin irinsa,ya kashe musu sultana,da wanne ido xai kalli bibi?,da wanne ido zai kalli aba?,uwa uba da wanne ido zai kalli nafessa?. Ya kashe sultanar da ya raineta da hannunsa?,ya kashe sultanar da yaci kashi da fitsarinta?,da wanne ido zai kalli sauran mutane?.

D’il yaji harbawar jijiyar sau daya,abinda ya sanyashi daga kansa da sauri yana dubanta,ya kuma tattara dukka hanakalinsa da nutsuwarsa ko zai sakejin ta harba din amma bata harba ba. Hannunsa ya sanya ya dafe saitin zuciyarsa da qarfi wani kuka me ciwo yana sake qwace masa. Da sauri ya sauka daga gadon ya gyara mata kwanciyarta.

Cikin mintuna goma ya bata dukkan wani tallafi da zai iya sanyawa ta rayu,saidai bata dai bada wani reaction ba har ya gama. Amma kuma yana da cikakken hope akan taimakon da ya baiwa numfashinta da zuciyarta,Sai ya tattara komai nasa ya sake matsawa gabanta ya shafa sumarta yana jin kamar zuciyarsa zata fado.

Bazai iya tsaiwa yayi ido hudu da Bibi ba

Bazai iya fuskantar aba ba

Me zai cewa ama?. Sai ya sauke hannunsa da sauri ya juya yana fita daga dakin,wanda daga nan bai zarce ko ina ba sai dakinsa.

Ko minti biyar bai rufa ba a dakin ya fito,babu komai a hannunsa sai qaramar takarda daya soketa jikin qofar dakin nasa,sai wata qaramar jaka dake riqe a daya hannun nasa. Ya fara takawa yana barin ainihin ginin gidan yana dosar qofar fita a gidan. Zuciyarsa na wani irin fusgarsa,wata izuwa dawowa cikin gidan,wata kuma zuwa fita daga gidan,fita kuma da zata kawo nisan tazara me yawa,har sai ya tanadi amsoshin da zai baiwa ahalin MAYAK’I. walau SULTANA ta rayu ko kuma TA RASA RANTA,Ya tabbatar dole wataran ya fuskancesu,dole ya fuskanci abinda ya aikata a yanzun,saidai kuma a yanzunne bai shirya fuskantarsu ba.

ina Aliyyu maina ya tafi?

shin ya tafi kenan?

ya bibi ama da aba zasu kalli maina a yanzu?

meye zai biyo bayan rayuwar SULTANA da MAINA?

FAREWELL BUT A NEW CHAPTERS UNFOLD

YANZU MUKA KAMMALA SHIMFIDAR LABARIN,AINIHIN LABARIN SAI BAYAN SALLAH IDAN ME DUKA YA KAIMU

INA MUKU FATAN ALKHAIRI,TARE DA FATAN YIN IBADAR WATAN AZUMIN RAMADANA LAFIYA

INA ROQA MUKU ALKHAIRIN UBANGIJI TARE DA FATAN ZAMU SHIGA CIKIN RAHAMARSA YA SAKAMU CIKIN ‘YANTATTUN BAYINSA ALFARMAR WANNAN WATAN

KADA KI SAKE ‘YAR UWA,KIYI IBADA DA KYAU,TA YIWU WANNAN SHINE RAMADAN DINKI NA QARSHE A RAYUWA

MATATTU DA DAMA DAKE QARQASHIN QASA A YANZU HAKA SUNACAN CIKE DA BURIN INAMA ACE SUNA CIKIN WADANDA SUKA SAMU DAMAR HALARTA WANNAN LOKACIN CIKIN GIDAN DUNIYA,SABODA SUNSAN YADDA AIKIN LADA KEDA MATUQAR TSADA DA DARAJA A BARZAHU

SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASH HADU AN LA’ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA’ATUBU ILAIKA

MA’ASSALAM👑👑


Series Navigation<< Gudun Kaddara Part 1
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *