Kwankwasan Jimina part 2

Kwankwason Jimina Part 2

This entry is part 2 of 3 in the series KWANKWASON JIMINA!!

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

NA

NANA HAFSATU
MX

ZAFAFA BIYAR 2024

Free page :02

Join our WhatsApp group here

__

  “Ba kiji ciwo ba ai ko?… Ki dai na tsalle tsalle Amna..” Ta karasa fada tana mai tambayar ta da hannu alamar menene?

Amna ta bude dan karamin bakin ta tana furta sunan yafendo a hankali. Ai kuwa bata karasa rufe bakin nata ba yafendo ta karasa dakin tana dogara yar sandar ta.

“Ah yafendo…” Cewar Nawra tana mai danne gefen katitar data zura littafin ta zauna akai.

“Amna tace baki da lafiya ko?”

Nawra ta kakaro murmushi tana kada kanta.

“Da sauki amma..”

“Tun dazu nake cewa kina ina ne duk su Layla suna nan.. Bake kwata kwata. Kwanakin nan na rasa gane kan ki. Na tambayi mahaifiyar ta ki tace zata miki magana. Sai Amna ce danasa Adam ya kirawo ki tace ai baki da lafiya “

Nawra dai kanta a kasa tana lankwasa yatsunta. Tace,

“Uhum… Amman da sauki ai. Nagode sosai”

“Sannu kinji?. Allah ya baki lafiya Nawrah. Kwanta ki huta”

“Tohm yafendo.. “
Nawra ta haye Kan katitar sosai ta kwanta tana mitsitsika idanu..

Yafendo ta mike dakyar tana dafe bango ta fice daga dakin

Nawra ta sauke katuwar bahaguwar zuciya ganin yafendo ta fita. Tadaga gefen katitar da saurin gaske ta zaro littafin, ta bankada kasan akwatin ta ta saka.

Amna na gefe tana kallon ta. Nawra ta riko hannun kanwar tata tace,

“Nagode sosai Amna tah.. Yau da yafendo taga Ina rubutun nan ai sai an kusa yankani. ” Ta karasa fada tana kada Kai.

Amnah tayi murmushi kawai. Tana Wasa da zaren jikin rigar ta.

“Ungo biyar dinnan na baki jeki sayi wani abun”

“Nagode” Amna ta karba cike da farin ciki ta fice da sauri.

Nawra ta kwanta akan katifar ta ta lumshe idanun ta…. Fuskar ta ta gauraye da murmushi. A zuciya take karantowa. idanuwan ta na hasaso mata rubutun haruffan da zanen su. Ya yinda labbanta ke matsowa ahankali tana karanta su…

“Nawra…. Nawra …. Nawra” Layla ta kwada mata kira. Ta shiga dakin nasu.

Nawra ta mike da sauri tana duban ta tace,

“Kai Kib katse ni wallahi”

“Dalla aiken mu akayi…”

“Ina aka aike mu ?”

“Gidan bappah Auwalu.”

“Tam. Bari nasaka hijabi”

“Dalla muje a haka kaman wasu manya zamu saka hijabi?” Cewar Layla ta fada tana yiwa Nawra nuni da kanta.

Nawra ta girgiza kai tache,

“Zan saka.. Ammi tace da hakan ake dorewa har girma. “

“Shikenan sai ki saka ai”

Nawra ta girgiza kai. Ta bude wardrobe din kayan su ta dakko hijabin ta ta zura… tana duban kanta a wani madubin su karami dake jikin dressing mirror dinsu..

Tsaf da ita kamar wata babbar budurwa ta dubi Layla dake nannade kasan zaren hannun rigar ta tace,

“Muje”

“Yauwa.”

A tare suka futa daga cikin dakin sukayi hanyar fita daga gidan yafendo na daga can runfarta ta hango su tace,

“Nawra kinji sauki me? Layla ba ke kadai aka aika bane sai dakika taso ta?”

“Wai ba…” Bata karasa ba Nawra ta saka hannu ta gwabe wa Layla baki. Da Sauri tace,

“Na ji sauki yafendo yanzu…”

“Mashaa Allahu. To kuyi sauri ku dawo”

“Tohm” suka hada baki..

Fita sukayi daga cikin gidan. Layla ta dubi Nawra cike da mamaki tace,

“Ina tsoron ranar da su bappah zasu Kama ki…”

“Ba zasu Kama nI ba inshaa Allah.. “

“Toh Allah yasa… Ni kam Dadi nakeji bama yi, karatun nan ba fa wani Dadi ne dashi ba kinaji yan maza na fada”

“Ni dai inaso”

“To ai shikenan…”

Suna tafe suna hira hadi dawasa a hanya Suka karasa gidan bappan na su.

Basu dawani nisa sosai. Don hakan bazasuyi wata tafiya can ba Sika karasa.

Bakunan su dauke da sallama suka shigaa cikin gidan.

A zaure Suka ci Karo da shi Yana tafe Yana duban goro a hannun sa.

“Ahh..” Ya fada Yana kallon su

“Bappah Ina kwana?”

“Bappah Ina kwana?”

Suka shiga gayshe da shi. Ya amsa musu Yana duban su da Karin bayani.

“Bappah Wai Kai ake jira..” Layla ta fada tana duban sa.

“Ai gabi Nan dama candin zani ai. Muje ko?”

Ya nuna kofa.. suka matsa ya shige suka bi bayan sa suka futa .

“Zo mu biya dangaki…. (Dangaki shine sunan babbar gonar data mamaye rabin garin BUNZA. Gona ce data fi wani garin girma. Itace ake yankawa samarin garin idan zasuyi sure. Kowanne sai a shata masa wani yanki nadaga ciki ya nome. Shi daya ba dan tayi. Idan ya nome ita kuma amaryar dazaa hadasu sure. zata dinga ebo ruwa sawu goma daga Rafinrau (sunan babban rafi ne da wasu ke Kira da teku. Ance duk shekara ma ya kanci mutane sama da dari. To Nan amaren ke zuwa suna ebo ruwa daga rafin da take can bayan garin zuwa gidajen surukan su wato gidan iyayen mazajen. Su Kai su koma har sawu goma. Shikenan sai a daura musu aure. Gwarzon da gwarzuwa kenan. Amfamin noman da angob yayi shikenan sai suyita ci agidan auren nasu. Ruwan nan kuma haka za aita bawa amarya tana girki ko aikin abinci har adadin data evo Kafin aure. .. wannan wata babbar al’adace da Yan yankin BUNZA ke gudanarwa shekara da shekaru…

‘Yau farisu ke nome gonar auren su da fiddau.. zo muje kinji?”

Nawra ta girgiza kanta ,

“Jeki ke kadai “

“Kinsan fada zaa mun agidaa idan ba ke. Idan mu biyu ne kuwa fadan kadan ne bama lalle ayi ba.”

Nawra badan taso ba. Tabi bayan Layla suka nufi dangaki don ganewa idanun su noman karshe da farisu angon fiddau zai yi…

Bappah Muhammad sani ya karasa cikin gidan bakin sa dauke da sallama. Yayi hanyar sashen mahaifiyar su

Ya durkusa har kasa ya gayshe da ita. Ta amsa kanta a gefe cike da kunyar dan fari.

Duk yaran nata sun hallara. Bappah sani, Bappah Auwalu shine na biyu amman yaci sunan Auwalu Lawan, Bappah salisu da bappah Junaid sai kuma mace guda daya yakunbo aminatu. Wadda itace ta biyun karshe. Bappah Junaid ne autan Dadaa (yafendo)..

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖

ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

Join our WhatsApp group here


KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

NA

NANA HAFSATU
MX

ZAFAFA BIYAR 2024

Free page :03***Hajiya Fanta… Wato Dadaa mahaifiyar su Bappah Auwalu kuma kaka ga su Nawra dake kiran ta da yafendo…

Tana a zaune ne akan babbar kujerar parlorn.. parlor ne matsakaici dauke da saitin kujeru dai dai misali.

Yayinda yaran nata ke zazzaune daga kasa kowannen su yana fuskantar ta.

Dadaa tayi gyaran murya tace,

“Dalilin daya sa na kirawo ku nan gaba daya akan wannan taron abubuwa uku ne zuwa hudu… Kuma dukkanin ku nan babu wani dayasan dalilin hakan sai Allah mahaliccin mu. Sannan bana bukata wani acikin ku ya nemi bijerewa ko ince kawo wata shawara ta daban ga zantukan da zanyi. Ina fatan Kuna saurara?”

“Muna sauraron ki Dadaa” suka hada baki wajen amsa ta..

Dadaa ta kada kai ta cigaba da cewa,

“Allah ya muku albarka duka…Allah ya hade kawunan ku ya kauda fitnah a tsakani. Allah ya raya muku zuri’ah ya albarkace su.. Aamin”

“Aameen Dadaa”

“Aaameen”

“Yauwa ku saurari abunda Zan fada da kyau. Ku Kuma nazarci zantukana a kwakwalen ku. Kada wani yayiwa maganganu na fahimta a baibai ce. Sannan duk abunda na fada Ina fatan ya kasance mafi alkhairi agare mu baki daya”

“Aameen”

“Allah ya kara Miki lafiya Dadaa”

“Aameen… Maganar fitar da ni waje don gano menene gundarin wannan rashin lafiyar tawa ni Fanta na soke ta… Babu ita”

“Amma Dadaa…

“Ya isa karkace komai…sai da na ce muku da fari bana bukata wani acikin ku ya nemi bijerewa ko ince kawo wata shawara ta daban ga zantukan da zanyi. Ku ma kuka amince ko baa ayi hakan ba?”

“Anyi Dadaa.”

“Tuba muke”

“Yauwa wannan magana ta futa na soketa. Dukkanin abunda Allah ya kadarta wa bawa na rashin lafiyar kai komai ma da sauran su. Allah ne kadai zai magance maka a duk sanda yaso.. sa’annan wannan lalurori nawa sunci kudaden da cikinmu basu ci ba. Garuruwa nesa dana kusa bawanda baa zaga da Ni asibutin sa ba don gano gundarin ciwo. Don hakan na hakura ni. Wannan ciwo bana warkewa bane .. Allah ne kadai zai mun maganin sa.”

“Dadaa ki dai na cewa hakan”

“Me ake jira ne? Dukkanin munan kowa fa tasa yake jira… Mutuwarnan sai ta dauki kowa babba dayaro kowa ba Wanda zata Bari. Don hakan a kyale ni na zauna da ciwo na. Kankarar zunubai ce. Idan Kuma lokacin tafiyar ne yayi Allah yasa mu cika da Imani”

“Ki bar fadin hakan Dadaa”

“Magana ce ta gaskia… Allah ya sa mucika da Imani”

“Aamin Dadaa”

“Aamin”

Suka amsa mata dukkanin su. Dadaa ta Dan dubi fuskokin su.

Bappah Auwalu ita yake kallo, Bappah sani ma itan yake kalla data kalle shi sai ya sadda kansa kasa. Ya yinda bappah salisu kansa ke akan agogon dake daure a wutsiyar hannun sa yana saita lokaci. Bappah Junaid Kuma kansa a kasa.. Sai yakunbo Aminatu dake lankwasa yatsunta tana duban mahaifiyar tasu Dadaa.

Dadaa ta sauke katuwar ajiyar zuciya tace,

“Allah ya hade kawunan ku…ya kauda fitnah a tsakani. Amin”

“Aamin Dadaa”

“Aamin”

“Sai magana ta gaba akan yaran wajen ku mazan… Wadanda ke makarantar boko yanzu… Tun ba yau ba ahali da yawa na yankin bunza ke aibatar mu kancewa mu muna qafafa muna fatali da al’adar kaka da kakanni. Bama koyi da sauran mutanen gari… Ku dubi ibtila’in daya saukarwa yar wajen ku kalatacciyar al’adar jigilar ruwan Rafinrau zuwa ga gidan surukan ta akan hanyar ta rasu a sawu na bakwai… Wannan munanan al’adu naki jinin su bana kaunar su.. Don hakan tun kafin rasuwar mahaifin ku muka gama magana dashi muka yanke shawara.. Zamu tarkata komai namu mu bar musu yankin nan. Zaman mu acikin sa babban ibtilai ne musanman da zuriyar mu ce kadai ke da kadarorin zinarai ragowa na dutsen bunza…”

“Mashaa Allah Dadaa… Wannan zance naki haka”

“Hakan shike Dadaa.. Allah ya amince”

“Amma Dadaa kina ganin Mutanen Nan zasu kyale mu mu bar yankin nan? Kinsan mugayen alkadarin su akan zuriyar mu”

“Babu abunda suka Isa suyi Mana Wanda Allah bai rubuta ba. Mu mayarda komai gare shi sai ya buda Mana kofa masaukakiya. Don hakan Kar ku wani damu da su. Idan aka sauya yanki sai a kyale yarannan maza suci gaba da karatun su. Matan Kuma a kyale su har zuwa sanda zasu tasa a aurar da su… Duk dai yadda ta kasance din..Kar a tsaurara akan matan nan”

“Inshaa Allah hakan zaai Dadaa.”

“Wannan zance naki haka shike Dadaa”

“Toh Allah ya Mana muwafaqa”

“Aamin Yaa Rabbi

“Sai magana ta karshe…. Dukkanin dukiyar data ragemun a duniya na hadeta waje daya na kasata kashi uku. Kashi daya zaa ajiyeta ayiwa Yara aure idan sun tasa… Su Sameer, Khaleed, Ashiir da ashfeef, Ahmad, Kashi daya zaa bawa miskinan yankin nan wajen mararrabar Ballo Mai sardii.. kashi daya na rabata tsakanin sani, salisu , Auwalu da Kuma ke Aminatu…..

Duk sukayi shiruu suna sauraron ta. Ta daga Kai ta dora akan autan ta Bappah Junaid da kansa ke a kasa tace,

“Kason daya rage na karshe kuma na barwa junaidu shi kadai…. A nan na kawo karshen maganganun da zanyi. Ina fatan Kuma zaku dauki zantuka da nayi kuyi amfani da su. Ko bayan rai na bana fatan wani acikin ku ko zuriyar sa da ya tada wata husuma ta daban. Kudi shirme ne karewa zasuyi su barku. Amman jinin Yan uwantaka na zumunta zumunci ne Mai karfi na har abada. Dan girman Allah kada ku yanke zumuntar dake tsakanin ku. Kada ku yanke alakar da kuka taso tare da ita. Kada ku bari duniya taji kan ku…kada ku bari ayi muku dariya ana zundar ku. Ku hade kawunan ku sai Allah ya shigaa lamuran ku… Hamidniyya Lebanon kada ku bari sunan zuriyar nan ya tagayyara Allah ya muku albarka”

“Aaamin suka hada baki wajen amsa ta.

Tana karasawa ta mike tana dogara yar sandar ta ta bar wajen ta koma daki.

Donma kada wani ya kawo mata wata maganar ta daban data shiga dakin sai ta sakaya kofar ta turo ta.

Ganin hakan yasa daya bayan daya suka bar wajen. Kowanne da zancen da yake azuciyarta sa.. musnaman akan jimilar kadarorin ta da tayi…

Hamidniyya Lebanon….

Mai karatu zai so yaji asalin tushen wannan zuri’ah dake cikin yankin bunza mai tarin albarka…

Ku biyo ni a next page don jin kanun labaran🏃

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

Join our WhatsApp group here


KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

NA

NANA HAFSATU
MX

ZAFAFA BIYAR 2024

Free page :04

__
HAMIDNIYYA LEBANON

Hamidniyya Lebanon wata zuri’ah ce mai karfi dake shiyar sansanin yankin bunza. Yankin bunza na dauke da yarika kala kala. Mafi yawa acikin su Fulani ne, Fulani dai kabila ce da tarihi ke turke asalinta tun karni na 15 daga wasu manyan yankuna biyu da ke kasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jalloh… Sai mafi karfin ciki wato wadanda sukafi tarin dukiya zuri’ar hamidniyya ne wadanda usulin usulin su larabawa ne yan kasar Lebanon..

Daga su sai barebari, Yarabawa, Idoma, Igbira da sauran su. Kusan dukkanin wasu yarirrika dake kunshe cikin kasar akwai su a yankin garin na bunza..

ASALIN SU

Tarihi yazo da cewa usulin zuriyar hamidniyya yan kasar Lebanon ne, Lebanon kuma kasa ce a Western Asia..

Tarihi ya nuna cewa Marigayi Hamidniyyah Mohannad Lebanon Wanda sunan sa ne zuriyar ta samu asali. Ance sunzo kasar ne yin wani bincike. Jiragen da suka zo da su suna da dan yawa. Dan haka sansanin inda ake ajiyar jirgin sai a ka samu ibtila’in gobara jiragen duk suka kone… Sai jirgin su Marigayi Hamidniyyah Mohannad wanda shi Marigayi da cikin daga cikin manyan kasa alokacin sun fita yawon bude idanu a gajimare da jirgin daga nan suka biya wata kasar..

Labarin gobarar jiragen ya koma kunnuwan can kasar inda sukayi koke koken su. Ance dukkanin jiragen sun kone da Mutanen su dake ciki. Baa banbance gawa da karfen jirgin aka tarkata aka wanke aka sallace su a haka aka birne…

Ko da ragowar jirgi daya ya dawo wato nasu Marigayi Hamidniyyah Mohannad. Sai suka samu mummunan labarin abunda ya faru..Gashi babban lefi ne ya koma kasar su shi da sauran wadanda basu rasun ba. Su ce dalilin daya faru sun bar kasar hakan ta faru to akan me zasu tafi yawon bude idanu su bar sauran mutanen su da aiyukan da aka turo su suyi? Wannan dalilin ne yasa suka yanke zama anan kawai. Domin idan suka koma kasar su ma hukuncin kisa ne za’ayi musu.

Anan suka kafa sansanin su suka auri junan su.. su da fulanin wajen suka zama mutane daya…Suna daya daga cikin manyan kabilun da suka taimaka wajen sama wa kasar ‘yanci daga turawan mulkin mallaka.

Baya ga zaratan sojoji na Fulani da suka yi gwagwarmaya, akwai kuma fitattu da suka taimaka wajen sama wa kasar ‘yanci.

Daga nan ne suka ci gaba da bazuwa cikin kasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa.

Ko da yake babu tsayayyen adadi na yawan Fulani a duniya, amma kiyasi na nuna yawansu ya kai akalla miliyan 45, kuma sun fi yawa ne a kasashen yammacin nahiyar..

Kamar yadda Fulanin ke da masarautu da dama haka ma kuma suke da karin harshe kala-kala wanda masana tarihi suka kasa kashi shida.
Wannan ne ma ya sa ba lallai ne wasu Fulanin Najeriya su fahimci fulatancin wasu ‘yan uwansu da ke kasashe kamar Senegal da Gambiya ko kuma Burkina Faso ba. Ko da a Najeriya, akwai wani karin harshe da wasu Fulanin ba su fahimtarsa.

Akwai aminta sosai tsakanin fulanin yankin bunza da zuriyar Hamidniyya Lebanon.. Tun shekarun baya ya zuwa yanzu. Kuma Allah ya sanya musu wata albarka ta tarin dukiya. Basu da wani yawa. Dan sun rarrasu da yawan su. Sai ‘ya’yan ‘ya’yayan su da sukayi aure sika hayayyafa suma suka tada tasu zuri’ar amman duk da haka basu da wani tarin yawa sai tarin dukiya .

Danma dukiyar ta babu koda kwatan rabin ta yanzu. Hakan ya samo asali ne kuma alokacin da yankuna suka hada karfi da karfe suka ci garin na bunza da yaki. Suka kwashe musu tattalin arzukan su da tarin dabbobin su sai wadanda ba’a rasa ba. Wanda suka fita kiwo hatsarin bai auku akan su ba..

Dan tattalin arzikin zuriyar ta hamidniyya kuma wadda ta ragu ce na daga abunda mahara yaki basu kwashe ba a babban dutse mai suna bunza. Wanda shine duk tarin zinaran cikin sa dama na zuriyar hamidniyya ne. Da mayakan suka raba dutsen biyu suka kwashe abunda zasu kwasa. Sai Allah bai basu ikon ganin sauran zinaren dake gefen dutsen ba daga daya bangaren.. wannan zinare shine zuriyar suka raba aka fitar wa Yafendo (Dadaa) kaso daya mafi yawa acikin . Kasancewar ta itace uwa datayi ragowa. Duk sun rasu sai ‘ya’ya’ye da jikoki…

Tana dauke da rashin lafiyar hauhawar jini da sukari. Sai ciwon kafafu suma da sukarin ne yayi silar su da Kuma girma na shekaru. Wannan dalilin ne yasa zaa kaita kasar waje afura da ita Domin duba lafiyarta sosai acan din.

Ita kuma bayan tayi wasu tunani nata na daban. Ga ganin girma daya zo mata sosai.gashi an talauta zuriyar tasu ba kamar a baya ba. Domin rabin rabin rabin dukiyar tasu ta baya basu da kwatan kwatankwacin ta a yanzu.

Hakan yasa ta tara yaran nata take sanar dasu tayiwa dukiyarta rabo gida uku bisa hudu.

Kamar yadda na zayyano muku a shafin baya… Inda dadaan ke kasafce dukiyar ta… Gata kamar haka,

Sai magana ta karshe…. Dukkanin dukiyar data ragemun a duniya na hadeta waje daya na kasata kashi uku. Kashi daya zaa ajiyeta ayiwa Yara sure idan sun tasa… Su sameer, khaleed,Ashiir da ashfeef, Kashi daya zaa bawa miskinan yankin nan wajen mararrabar Ballo Mai sardii.. kashi daya na rabata tsakanin sani, salisu , Auwalu da Kuma ke Aminatu…..

Duk sukayi shiru suna sauraron ta. Ta daga Kai ta dora akan autan ta Bappah Junaid da kansa ke a kasa tace,

“Kason daya rage na karshe kuma na barwa junaidu shi kadai…. A Nan na kawo karshen maganganun da zanyi. Ina fatan Kuma zaku dauki zantukan da nayi kuyi amfani da su. Ko bayan rai na bana fatan wani acikin ku ko zuriyar sa ya tada wata husuma ta daban. Kudi shirme ne karewa zasuyi su barku. Amman jinin Yan uwantaka na zumunta zumuncii ne Mai karfi na har abada. Dan girman Allah kada ku yanke zumuntar dake tsakanin ku. Kada ku yanke alakar da kuka taso tare da ita. Kada ku Bari duniya taji kan ku…kada ku bari ayi muku dariya ana zundar ku. Ku hade kawunan ku sai Allah ya shigaa lamuran ku… Hamidniyya Lebanon kada ku bari sunan zuriyar nan ya tagayyara Allah ya muku albarka”

“Aaamin suka hada baki wajen amsa ta.

Tana karasawa ta mike tana dogara yar sandar ta ta bar wajen ta koma daki.

Donma kada wani ya kawo mata wata maganar ta daban data shigaa dakin sai ta sakaya kofar ta turo ta.

Ganin hakan yasa daya bayan daya suka bar wajen. Kowanne da zancen da yake azuciyar sa.. musanman akan jimilar kadarorin ta da tayi…

Anan mun karkare ASALIN tushen zuriyar hamidniyya Mohannad Lebanon dake a yankin birnin bunza..

Sai kuma SHAFI na gaba zamu dora daga inda aka tsaya…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

Join our WhatsApp group here

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

NA

NANA HAFSATU
MX

ZAFAFA BIYAR 202

LAST FREE PAGE: 5


Suna kan hanyar layin su zasu koma gidah suka hadu da Hammah Ashfeef ..

Yana hango su ya yafuto su da hannu da sauri yana dafe kansa saboda yadda rana ke dukan goshin sa..

Karasawa sukayi wajen nasa.. Ashfeef ya dube su duk sunyi futu futu yace,

“Tun dazu nake neman ku… Yafendo tace daga aiken data muku ku Kira Bappah ba a sake ganin ku ba. Hankalin ta ya tashi sosai. Saboda tace ke bakida lafiya ashe ko? Wai ko jikin naki ne ya tashi a hanyar dawowa? ” Ya karasa fada dan yatsantsa na yin nuni ga Nawra dake kikkifa idanu

Nawra ta bude baki zatayi magana Layla tayi saurin cewa,

“Eh kanta ne yake ciwo shine muka shiga gidan su Nano umman su tabata magani “

Ashfeef ya kada Kai Yana kallon Nawra yace,

“Ya jikin naki to?”

“Da Sauki naji Sauki …Amma”

Bata karasa fada ba Layla ta saka hannu ta mintsino hannun ta,

Hakan yasa tayi shiru tana mai duban Layla ta wutsiyar idanu. Sam batason halin Laila nayin karya akan abunda ba haka ba.

“Allah ya sawwake ya kara sauki. Muje gidan. Don yafendo hankalin ta atashe ganin ba kudawo ba an je har gidan bappan ko kuna can bakwa nan.”

Yayi gaba. Suna biye da shi a baya.

“Toh Yayaa..”

Nawra ta juya ta dubi Layla cike da takaici kasa kasa yadda Hamma Ashfeef ba zai juyo ba tace,

“Me karya fa dan wuta ne…kina ji dai malam Yana fada mana Kuma ma yafendo tana mana tuni akai”

Layla ta tabe baki tace,

“Fada zamu sha idan ba haka na fada ba”

Nawra ta girgiza kai kawai tayi gaba abunta. Layla tabi bayanta tana Kiran sunan ta a haka suka karasa gidah..

  Da yafendo suka fara cin karo a zaune ta zabga uban tagumi tana kallon babbar kofar da Zata sadaka da wajen gidan da shigowar sa.

“Assalamu alaikum..” suka hada baki wajen yin sallama..

“Waalykm Salam… Ina kukaje ne haka iye? Nawrah Layla tun dazu ake tsumayin ku shiru. Ko jikin ne?” Ta tambaye su cike da kulawa.

“Wai kanta ne ashe yake ciwo…” Ashfeef ya amsa yafendo.

“Shine mukaje tasha magani ta kwanta agidan su …….

Layla bata karasa fadar abunda Zata karasa ba Nawra ta yi hanzar cewa da yafendo,

“Dandagi muka biya ganin noman farisu angon Fiddau.. Bamu ma gama kallon Fiddau dake daukar ruwa daga Rafinrau ba..”

Tana karasa fada tayi shiru kanta a kasa tana lankwasa hannuwan ta. Duk da karancin shekarun ta hakan bai sanya ta dinga karya ba…

“Kiyi hakuri yafendo…” Ta sake fada kanta a kasa.

Layla dake gefenta kirjinta ya cika fal da tsoron abunda zai biyo ba. Dama tun ba yau ba Nawra tasaba kwafsa musu. Don haka itama ta sadda kanta a kasa cike da muryar ban tausayi tace,

“Kiyi hakuri yafendo”

Ashfeef yayi kansu zai dake su yafendo ta hana shi,

“Kyale su….Ai Nawra kamar ko da yaushe ba itace me laifin ba. Ni nasan yau dinma kece Layla.. Allah ya shrya mana ku…”

“Kiyi hakuri yafendo bazan sake ba. Allah so nake kawai naga yadda farisu zai noman.” Layla ta tsugunna tanata bawa yafendo hakuri

Nawra ma ta tsugunna agaban yafendon suka shiga bata hakuri a tare.

“Ku tashi kuje.. Allah ya muku albarka ya yafe mana baki daya”

“Aamin Aameen”

Kowaccen su tayi bangaren su sumi sumi.

Nawra cike da madaukakin farin ciki ta shjga sashen su. Don Sam batason ta dinga karya akan abunda ba hakan bane. Gwara kowane lefi ne ta fadeshi awuce wajen. Domin malaman islamiyar su suna koya musu haramcin karya da illolin ta…

::::::::::::::

Ranar wata jumuah. Yanayin damuna ne dama. Garin yayi sanyi ya Kuma yi shiru ba hayaniya. Ni’iimar Allah a ko’ina, ciyawa tayi kore gaba daya. bishiyu nata kadawa. Ga kamshin kasa dake tashi..

A ranar ne Kuma ahalin zuri,ar hamidniyya suka tsinci kansu cikin tashin hankalin da suka Dade basu tsammaci kansu aciki ba.

Wannan tashin hankalin Kuma shine na babban rashin bango majinginar su ne wato yafendo… Daadaa.

Allah ya karbi ran yafendo da asubahin ranar bayan an idar da sallah.

Kuma a satin ne sun gama shirya komai tsaf don yin hijra daga garin bunza zuwa yankin gaban sa..

Abunda yasa basu koma din ba ma.. jira suke su karasa sayar da kadarorin su gaba daya sai su bar garin na bunza.

Allah cikin ikon sa da kudurar sa da hikimar sa Domin shidin mamallakin kowa da komai ne.. Kuma kowanne rai sai ta dandani zakin mutuwa. Domin Allah daya halicci kowane dan Adam yafu kaunar sa akan komai..

Yafendo ta cika ne alokacin tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkhar. Daman jikin ya sake tsananta. Har ya Kai ga sallah ma azaune take yi. Idan zata mike ma sai an taimaka mata. Haka idan zuwa bayi ne nanma haka.

Hakika alokacin da rashin lafiyar yafendo ta Kara tsanani. Ahalin sun shiga madaukajin rudani Mai wuyar fassarawa. Domin ko menene sai da yafendo. Itace a tsaye akan kowannen cikin su.

Don haka rasuwar yafendo ta taba dukkanin su. Manya da kananan cikin zuriyar.

Lungu da sako sai koke koke suke yi…. Hakika yafendo bango ce majinginar bayi.. ita din itace tsintsiya mai daure da zumunci, temako , dattako, tausayi, kyautata wa gaba ki daya na ahalin zuriyar hamidniyya.

Ba zuriyar hamidniyya kadai rasuwar yafendo ta taba ba. Ciki harda yarika daban daban na zuri’ah da dangi na mutanen birnin bunza.

Sunji mutuwar yafendo sosai. Garin yayi shiru. Anata koke koke. Haka aka wanke yafendo. Alhamdu Lil Laah yafendo tayi cikawa Mai kyau da kalmar shahada. Ta Kuma rasu tana kan sallayar da take ibadah. Da asubah sannan kuma a cikin babbar Rana Mai tarin albarka da alkhairai wato ranar jumuah…

Bayan an gama mata wanka. Aka Kira dangi Kashi Kashi na ahalin hamidniyya don yin sallama da yafendon.

Kowannen sai da ya zubar da hawayen babban rashin jigo da sukayi na yafendo.

Suka yiyyi mata addua. Aka nannade ta aka zura a makara… Aka sallaceta aka tafi kaita gidan ta na gaskiya..

Acan dinma iyalan nata Maza sunsha kuka. Musanman Dan autan ta Bappah Junaid. Wanda banbare shi akai daga kan kabarin yana ta rusa Kuka tamkar karamin yaro..


Hakika rashin yafendo ya haddasa rabuwar kayuwa da dama na daga cikin ahalin zuriyar hamidniyya…

Koda wajen gado ma sai da aka samu dan hargitsi Kafin dai daga baya Kuma su sulhunta. Duk kuwa dawasun su ne daga ciki suka kawo husumar.

Sai da sukayi kwanaki hamsin da biyu… Sannan suka tashi baki daya kwansu da kwarkwatar su daga yankin na birnin bunza suka koma can babban birnin Naduka………

….
Anan karshen shafukan free pages suka tsaya…zamu shiga kundun labarin a cigaban paid pages Inshaa’Allah

shin wacce iriyar rayuwa ahalin Hamidniyya Lebanon zasuyi a birnin Naduka?

Ya labarin zai kasance mai dauke da suna mai tafiyar harshen damo … KWANKWASON JIMINA!! MAI WUYAR SHAFAWA…. !?

Hamidniyya Lebanon family

Dr. Abubakhr Dollars family..

Alhaji Yusuph Family

Twist of fate, Destined lovers#Life-partners#Al-Hub-Hayaat#Rich vs poor….

✔️✔️
INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

Click here to join our group

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

vip pages na arewa👇

paid page:06

__

BABBAN BIRNIN NADUKA
(FEDERAL CAPITAL TERRITORY)

NADUKA: Karamar Hukuma ce. Area kuma Babban Birnin Jihar NADUKA a Arewacin Najeriya. Naduka tana da nisan 160 miles (260 km) gabas da birnin, BUNZA da 84 miles (135 km) arewa maso yammacin Galko, kusa da kan iyaka da hez Jamhuriyar…

Hakika Birnin shi ne cibiyar yankin noma da ke samar da gyada, auduga, fatu, gero da masara ta Guinea, sannan kuma yana da injina na sarrafa man gyada, da karfe, ya kasance cibiyar kiwon shanu, awaki., tumaki da kaji.

Mafi yawan al’ummar Birnin musulmi ne musamman daga al’ummar Hausawa da Fulani.

Marigayi Shugaban Najeriya Nande ‘Yar’kuwatua ya kasance dan asalin birni rike da sarautar gargajiya a Naduka..

Gwamnan jihar Naduka mai ci a yanzu shi ne Mal. Harisu Yusha’u PhD, wanda aka rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga Mayu shekara ta alif …., wanda ya gaji Dantekan..

Birnin kewaye yake da bango mai nisa kilomita 21(mil 13) a tsayi, an yi imanin cewa an kafa Naduka tun kusan shekaru sama da 1100. A zamanin da, idan aka samu Sarkin na Naduka da mulki na rashin sanin yakamata ana yanke masa hukuncin kisa. Daga karni na 17 zuwa na 18, Naduka ta kasance cibiyar kasuwanci a kasar Hausa, kuma ta zama mafi girma a cikin jihohin Hausa

Fulani sun mamaye Naduka a lokacin yakin Fulani a shekarar 1807. A shekarar 1903, Sarki Bakri Yarzm ya karbi mulkin Birtaniya, wanda ya ci gaba har zuwa lokacin da Nijeriya ta samu ‘yancin kai daga kasar Ingila a shekarar 19…..

A lokacin cinikayyar yankin kudu da hamadar sahara, an san birnin Naduka na daya daga cikin manyan wuraren kasuwanci da karin iko, kuma an yi imani da cewa ita ce mafi karfi daga cikin masarautun kasar Hausa ta fuskar ilmi na addini da kasuwanci da sana’o’i. Bajamushe mai binciken frankis Hon ya isa Naduka, Bature na farko da ya yi haka, a farkon karni na 19..

Tarihin birnin na ilimi irin na yamma ya samo asali ne tun farkon shekarun 1950, lokacin da aka kafa makarantar sakandare ta farko a Arewacin Najeriya ( Kwalejin Malamai ta Naduka ). Yanzu haka akwai manyan makarantu da dama da suka hada da jami’o’i uku: Jami’ar Naduka university, da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Naduka da kuma shaharariyar Jami’ar Al-Haramein Naduka(mai zaman kanta) Makaranta ce ta kudi da yayan masu hannu da shuni suke zuwa, kasashe da dama na zuwa don samun gurbin karatu a makarantar saboda tsananin kyawun ta komai da komai makarantar ta hada musanman fannin karatu tamkar a kasar waje .sai Makarantar Fasaha ta Hun Naduka Polytechnic da Kwalejin Ilimi ta Tarayya, da Kuma Makarantar koyon jinya(School of nursing) wadda ke cikin babbar asibitin Naduka . Haka nan birnin Naduka yana da wani masallaci da aka gina a karni na 18 wanda ke dauke da Hasumiya,mai tazarar kafa 50 (mita 15 ). Hasumiyar da aka yi daga kasa da rassan dabino….

Hakika birnin Naduka ya hada dukkanin wasu tarin alkhairi na rayuwa da Dan Adam zai bukata. Sai dai birnin ya rabu Kashi biyu

Akwai yankin talakawa masu dai dai karfi. Da Kuma yankin masu farcinan Susa Wanda suka tada Kai da kudi…

Don haka sai ya zamto masu kudin sun ware wajen su daban…sunyi wa layikan su gate gate suna rufe su da daddare.

Kuma akwai yar tazara sosai tsakanin Naduka crescent (Apple island). Da Kuma Naduka zone .

Naduka crescent shine matattarar inda masu kudin suke. Kama daga kan masu rawani na sarauta, da Yan siyasa ciki harda bangaren gwamnan birnin da sauran su.. hadadden yanki dai daya tunbatsa da naira ake Kuma gogawa da ita. Wannan Yana bani waje… Kowa da kudin sa wani yafi wani…

Sai Kuma bangaren yaku bayi na marasa karfi …. Ana kiran wajen da Naduka zone..

Sai birnin ya zamto tamkar kauye da Kuma cikin babban birni. duk kuwa da unguwa ce kowacce daban.. Amman akwai tarin bambamci Mai matukar yawa a tsakanin su.

Duba da yawan gidajen masu tsaunika na benaye, manyan masallatai, wuraren shakatawa, wuraren siyayya na tafka tafkan shagunan more rayuwa na kayan alatu da sauran su…

Kuma babbar jami’ar garin ta kudi wadda a kasa akeji da ita Wanda dalibai da yawa na manyan kasashe da garuruwan suna zuwa karatu makarantar. Makarantar kudi ce Bata gwamnati ba sai ‘ya’yan wane da wane ne kawai ke zuwa …

Don haka makarantar a babban yankin Naduka take na Naduka crescent da a kewa laqabi da (Apple island) saboda tsabar haduwa da kawatuwar sa. .. birane dadama da wasu kasashen na zuwa hutun yawon bude idanu birnin Naduka.. yanada manyan koramu da suke da ruwa an Kuma gyare su sosai wajen ya zama tourist attractions spot..

:::::::::::::::::::::::::::::

Sai yamma likis zungureriyar motar bus dake tafe da su da kayayyakin su ta sauke su a kofar wani gidah Mai bene da wani a gefen sa shi Kuma na kasa ne ba bene..

Dukkanin su suka firfito daga cikin motar a matukar gajiye saboda sun Sha tafiyar hanya don akwai lokaci /tazara Mai tsawo tsakanin yankin bunza da birnin Naduka..

Nawra ta tsugunna tana bubbuga Yan yatsun kafafunta dake mata ciwo saboda azabar zaman da tayi na tafiyar mota..

“Sannu Nawra…” Cewar abbiey mahaifin su..

Ya fada cikin kulawa… Nawra tayi murmushi tana daga kanta ta gyada shi da sauri tace,

“Nagode abbiey……..”

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

vip pages na arewa👇

paid page:07

__

   Ya riko hannun ta suka nufi hanyar shiga gidan na su. Ya yinda mahaifiyar su ke dauke da Amnah a hannun ta tayi baccin gajiya…

Sai su Hamma Ashir da Hamma Ashfeef da ke baya…

Gidan bene maidaidaici karami sama da kasa shine Wanda yake a matsayin na Bappah junaidu mahaifin su Nawra.

Sai dayan Kuma flat shima Mai kyawu maidaidaici bana bene ba shine na Bappah Auwalu da iyalin sa..

Yakumbo Aminatu ita mijin ta bai samu gidah a birnin Naduka ba.. don haka suka samu wani gari daga gabas suka mallaki nasu muhallin..

Bappah salisu Kuma ya samu sauyin wajen aiki… Ma’aikatar da yake aiki sun yi babban kamfanin su mai hade da gidajen maaikatan da zasu zauna aciki har lokacin da zasuyi ritayar aiki ko kamfanin ya sauke su. Don haka shi da iyalan sa suka tattara suka koma can…

Bappah sani kuma sun tafi kasar Oman don jinyar Mai dakin sa da ke dauke da lalura..

Don haka a birnin Naduka kawai gidan bappah Junaid ne da bappah Auwalu sai iyalan su..

Cike da maduakakin murmushi marar misaltuwa suka shiga gidan nasu bayan bappah junaidu yasaka mukulli ya bude shi.. ko’ina tsaf tsaf a Kuma gyare mashaa Allahu..

Falo ne maidaidaici daka shiga gidan Mai duake da setin kujeru mashaa Allah. Sai daki guda daya a kasan Wanda yake a matsayin na su Hamma Ashir da Hamma Ashfeef.

Sai kitchen maidaidaici da store dinsa aciki. Sai Kuma bandaki a kasan guda daya. Sai matattakalar da Zata sadaka da saman gidan

Dakuna ne kawai guda biyu a saman sai bandaki guda daya da wani dan corridor da aka shimfidah Masa sallaya da hijabi a ninke da Kuma charbi. Sai wani dan katako an jera alqur’ani akai da littafin adduoi ..

Daki daya daga hagu shine Wanda iyayen nasu zasu zauna aciki. Sai daki Mafi kusa da shi Wanda dama guda biyu me kawai dakunan a sama yayinda kasa keda daya da parlor
Baki daya gidan dakuna uku ne..

Biyu a sama da bandaki daya… Dayan dakin su bappah junaidu da maidakin sa mahaifiyar su nawra.sai dakin kusa da shi na su Nawra da Amna. Da bandaki a tsakiyar dakunan…

Bandakuna biyu, dakuna uku, sai kitchen da store dinsa.. sai kofar da Zata sadaka da gidan…

Daga gefen su kadan Kuma gidan bappah Auwalu ne da matar sa da ‘yayan su…

Nawra na shiga dakin su ta bude baki tana duban dakin nasu cike da tsantsar kyawu da yayi mata. Dauke dakin yake da katifa babba wadda zata dauki mutane uku..

Sai drawer din su da aka zuba musu kayan sawar su itada Amnah. Tun ta gidah ce Amman aka zamanantar da ita akayi mata fenti…

Sai labule me kyawu shima .. Da dan mudubin su da aka kafe musu shi. Gefe daya kuma dakin malale yake da ledar daki sabuwa gadaagal da ita .

Nawra ta zauna akan katifar Tasu ta saka hannuwanta biyu akan katifar dake dauke daw filallika har biyu da bargo babba guda daya ya Sha zanin gado . Ta shiga shafawa tana kumshe idanu ba karamin kyau dakin nasu yayi mata ba..

Ta kwantar da kanta ajikin pillow tana duban saman ceiling..

Cikin tunanin data fara lulawa ne ta jiyo muryar mahaifiyar su tana Kiran sunan ta.

“Nawra kina ina ne?”

“Na’am ammiey… Ga ni nan”

Ta amsa da sauri ta fita daga cikin dakin zuwa kasa inda parlon gidan yake.

Dukkanin su suna parlorn sun hallara.har Amnah data fara bacci dazu itama ta tashi tana kan cinyar mahaifiyar ta su..

Muje gidan bappan ku a gaysa ko? Sai a huce gajigar gaba daya idan muka gayshe su.”

“Toh abbiey”

Tashi suka yiyyi da ga kan kujerun da suke zaune suka fita daga cikin baki daya suka nufi gidan bappah Auwalu..

Yar tafiya kasan daga cikin bappah Junaid zuwa gidan bappah Auwalu akwai wani karamin daki da yake a matsayin na baki ko da anyi idan sunzo sai su kwan anan..

Amma bisaga rashin Yan uwa a kusa kowanne garin daya ke daban da sauran su. Hakan yasanya bappah Auwalu ya nemi shawarar bappah Junaid kan yadda zasuyi da wajen

Inda bappah Junaid ya sheda masa Cewar duk yadda ya yanke yayi. Kuma kasancewa sa babba ya rike dakin kawai don shine babu isassun waje agidan sa.

Hakan kuwa akayi. Bayan bappah junaid ya babbawa bappah auwalu baki ya amince ya karba dakin

Inda Mai dakin sa ta hora Masa kashin bacin ya bar mata dakin ta zuba kiwon da take. Dakyar ya amince shi ma sai da su bappah Junaid suka saka baki.

Ta zuba kaji dakin ya koma akurkin kaji.. kasancewar ba wani shahararren girma ne da shi ba..

…….. Ta a tsaye gaban labule data dage ta hango su a jere suna tahowa gidan su

Sun tsaya gaban dakin akurkin kajin Junaid ya saka hannu Yana musu nuni da dakin Yana magana.

Alokacin Kuma Amna ce da tambaye tambaye ta ta tsare shi tana jefa Masa tambayoyin shi Kuma Yana Bata amsa dai dai da tambayar da take Masa. Yadda zata Gane kasancewar tana da karancin shekaru..

Tabe baki tayi ta sake labulen tana jan dogon tsaki.,cike da Takaici su .

“Menene ummy?”

Hanyar daki tayi tana daga mata hannu hade da karkada mata su tace Layla,

“Idan sunzo kice bacci nake yi”.

“To”

Daki ta shige zuruf tanata kananun mita. Dai dai lokacin da bappah Auwalu ya futo daga kitchen ya shiga parlorn Yana sallama..

Layla na amsawa sai ga sautin bugun kofar su Nawraah..

“Waye?”

“Layla bude, Mu ne”…

Da sauri har tana tuntube taje ta bude musu kofar…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024


paid page :08

__

   A tare suka shiga ciki baki dayan su, bakunan su duake da sallama. Kana shiga gidan parlor zaka fara cin karo dashi.

Dake dauke da kujeru da karamar tv da kayan kallo. Daga hannun daman ka kuma dakuna ne biyu daya Yana kallon daya. Sai bandaki dake tsakiyar su..

Daga can kofar corridor Kuma kitchen ne da karamin store dinsa aciki. Sai yar farfajiyar tsakar gidan su mai shuke shuke da wasu kujeru guda biyu tsofi ne na gidan da suka taso da wani dan teburi a tsakiyar su. Sai wajen ya hadu ya bada ma’ana sosai.

Daki daya daga ciki duake yake da gado da drawer harda mudubi. Nan ne yake a matsayin dakin bappah Auwalu da Mai dakin sa.

Sai daki Mai kallon sa Kuma na Ahmad ne yayan layla Wanda tsaran shekarun nasu ba yawa. Kasancewar dukkanin su Yara ne basu mallaki hankalin kansu ba. Hakan yasa bappah Auwalu Cewar dakin ya zama na Ahmad Amma yar katitar Layla na gefe sai ta runga kwana.

Mahboub yace yaci girma ya bar mata dakin. Shi zai rika fito da katifar sa parlor Yana kwanciya. Domin shi yafu kaunar parlorn ma acewar sa…

“Nawraah”

“Uhm.. Layla”

Kamo hannun Nawraah Layla tayi suka shiga parlorn suka zauna…

Kawu Auwalu yafuto daga kitchen daya shiga Shan ruwa Yana murmushin ganin su. Fuskar sa akan Dan uwan nasa yace,

“Junaidu ne? Ku karaso ku zazzauna mana”

Bappah junaidu ya durkusa har kasa Yana gayda yayan nasa. Bappah Auwalu ya amsa fuskar a sake

“Ka koma kan kujerar ka zauna Dan Allah. “

Daya bayan daya su nawrah suka shiga gayshe shi ciki harda mahaifiyar su data durkusa itama sosai cike da ladabi da biyayya ta gayshe da wan mijin nata.

Ya amsa musu fuska a sake duka…

“Layla Ina umman na ku?”

“Tana daki “..

“Je kice mata ga bappan ku nan sunzo da su nawrah kice ta taso su gaysa.”

“Ah idan ta kwanta a kyale ta . Ma sake dawowa mu gaysa a tsanake inshaa Allah”Cewar malama Hindu.

“Aa ataso ta dai… Yanzun ta tashi daga nan anan na barsu dasu Layla.. jeki kirata ke”

Layla ta mike tana yamutsa yatsunta ta nufi dakin mahaifiyar tasu.

Ta Dan bubbuga kofar Kafin ta saka Kai ta shiga bakinta dauke da sallama,

Tana shiga ta tarar da ita akan gado tana zaune tana kallon kofar,

“Ummy bappah ne ke Kiran ki yace kizo su bappahn nawrah sunzo..”

“Naji … Kema can daya Mai abun haushi sai kice Mai Kai na na ciwo haka ba sai an taso ni ba”

“Yo hakuri”

“Je ki”

Layla ta fita tana kakaro murmushi tace,

“Wai tana zuwa”

“Ko a kwance take ne na shiga na dubata?” Malama Hindu ta tambayar,

“Aa fa “

Fitowa tayi daga daki tana bude baki tamkar gonar auduga tache,

“Gajiya ce ta mamaye ne shine na Dan kwanta ko zan ji dama. Bappan su Ina wunin ku? “

“Dama nace ko jiki ne? Sannu ya kike ji yanzu?” Malama Hindu ta tambaye ta,

“Alhamdulillah naji dama sosai ..”

“Sannu Allah yakara afuwa”
Cewar bappah junaidu

“Aamin bappan su “

Daya bayan daya su nawrah ma suka gayshe ta cike da ladabi Kai kace wasu sabbin baki ne daga wajen bayan dazu suka rabu amman saboda tsananin tarbiyya tun sanda suna yankin bunza ma haka suke gaisuwar safe da ta rana data dare daban cike da ladabi da dinbin biyayya…

Ki nunnuna musu yadda akayi jeren ko nusaiba? Cewar mijinta bappah Auwalu.

“To bappansu Mai zasu gani anan gidan. Amma dai muje. Nan din fa iya kasa ne bamu da sama” malama nusaiba ta fada tana mikewa tsaye

Basuyi mamakin kalamanta ba don ba ranar ta fara ba. Don haka malama Hindu tace,

“Haba bappah ai munsan gidan kamanta duk tare mukai komai? Ai ana tare muma komawa zamuyi mu Dan sake kikkintsa inda ya kamata”

“Yo ai dake musanman tunda ku gidan sama ne daku. Ga bene ko’ina fala fala babu matsatsi ba kanara Nan ba da dakuna biyu ne jalllin jal”

Malama Hindu batayi magana ba murmushi kawai tayi ta mike tana kamo hannun Amna autar ta.

Bappah auwalu kunya ta sake dabaibaye shi tamkar kasa ta tsage ya fada haka yake ji.

Cikin kakaro murmushi dayafi kuka ciwo yace,

“Junaidu kaga an zuba tumakin da Yan kajin fa mashaa Allah. Allah ya saka maka da alkhairi ya kara arziki. Nusiaba kin sake Masa godiya kuwa?”

Malama nusaiba tana soso kasan gashin ta ta cikin dankwali tace,

“Sosai ma. Mungode kwarai . Nan gaba ma kawak sai a bige a shigo da shi cikin nan gidan muma ya zama dakuna uku kamar su”

Bappah A. ya saka yatsa a baki ya ciza Takaici ya sake gauraye Masa wuya da ilahirin jikin sa baki daya ji yake tamkar ya hau nusaiba Mai dakinsa da bugun tsiya ya bude kofar Yana cewa,

“Muje ka gani junaidu… Allah dai ya bar zumunci ya saka maka da alkhairi”

“Aamin** suka amsa baki daya Banda nusaiba da ke tabe baki

Dan dakin abun kiwon sika nufa. Dauke da tumakin biyu da akuya daya sai kaji zasuyi goma.

“Kagani ko ? Wallahi kamar Dan su aka Gina shi komai da komai ya yi mashaa Allah”

“Gashi nan kam Allah yasa albarka Amin”

“Aamin Aamin”

“Laaa ga kwai Ina so…” Amnah ta fada Hadi da shiga cikin dakin ta dakko Kwan kajin har biyu.

“Jeki ajiye*

“A bar mata Mana ai na uwar ta ne” bappah Auwalu ya fada Yana wa nusiaba murmushi.

Ta kakaro murmushin yake tana cewa,

“Dauki mana Amnah… A soya Miki Kona dafa Miki kici kinji?”

“Nagode” Amnah ta fada da sauri tana gudu

“Sannu da miskri Allah ya bar zumunci ya kara arziki su zama garke” malama Hindu ta dubi malama nusaiba tana mata godyar kwai data bajwa Amnah

Daga nan kuma suka koma nasu gidan bayan sun musu sai da safe. … Malama nusaiba tabu bayan su da kallo tana Mai tabe bakin ta ta koma cikin gidan nasu tana jera tsaki..

“Kul kika sake daukar abunda baa baki ba baa ce Miki gashi ba kinaji na ko?”

“Eh… Bazan sake ba ammeiy kiyi hakuri” Amnah ta bawa mahaifiyar tasu hakuri

“Ya wuce… A dafa Miki ko a soya? “

” A soya”

“Yauwa… To jeki parlor ki zauna kinji idan aka soya sai a kawo Miki”

Amnah ta koma parlor da sauri ta zauna akan kujera tanata murna. Malama Hindu ta nufi wajen kwanuka ta dauki wani Dan karamin mazubi ta fasa Kwan aciki

Kallo daya zakai nata kasan ita din mahaifiyar su nawrah ce duba tsananin kamar da suke yi da yaran nata duka. Duk kuwa da sun dauki kamannin mahaifin na su ma ciki harda tsawon sa da gashin hirar sa Zara Zara masha Allah…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

vip pages na arewa👇

paid page: 09

__

  Muhammad Junaid hamidniyya shine cikakken asalin sunan mahaifin su Nawraah… Kuma shine ‘da na karshe ga marigayiya yafendo. Haka zalika karamin kani ga su Bappah Auwalu.

Hindu Musa shine sunan mai dakin sa kuma mahaifiya ga su nawrah da sauran yan uwanta.

Hindu da Junaid yan uwane wanda ke karkashin inuwa daya ta zumunta. Kuma aka hada auren su auren zumunci wanda yayi dadi. Don shekaru da yawa kenan tunda aka yi hadin auren su gashi har sun Tara iyalin kansu. Baa taba jin fadan su ba ko cacar baki.

Auren su ya kasance Mai Dadi Mai tattare da sirri domin ko yaji Hindu Bata taba yi ba. Duk kuwa da kowanne aure ana samun sabani don tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa don haka Koda sunyi fadan babu Wanda ke jin kansu ko da kuwa iyayen su. Su kan shirya kansu su sulhunta. Hakan yasa Ko a dangi ake kwatance da su idan zaa kulla auren zumunta ko idan ana jan kunnen sabbin ma’auratan akance da su suyi koyi da iyayen su Yakumbo Hindu da Bappah junaidu…

Da mahaifiyar Hindu Marigayiya Yagwalgwal Fatime Domin ita ta Dade da rasuwa tun ana goyan Nawraah, da Kuma  Marigayiya yafendo mahaifiyar junaidu yar wa da yar kani ce..

Don haka iyayen su Kanwa da Yaya ne wadanda iyayen su suka fito tsatso daya…

Kasancewar tsatson na su larabawa ne na yankin Lebanon gefe daya kuma suka hada zuri’ah Mai tarin yawa daga fulanin yankin bunza ta hangar auratayya. Hakan yasa zuriyar tasu ficewa gaba saboda tsananin kyawun su da dabi’unsu na nagarta. Masu dinbin tarin arzuka Kafin mahara su Kai wa yankin sumame suka kwakushe masu tattalin arzikin su cikin Kashi uku ba Kashi biyu…

Allah ya azurta Hindu Musa da Junaid hamidniyya da Yara Kadan masu tarin albarka,

Ashir shine babban Dan su, Sai mabiyin sa Ashfeef , Sai Kuma Nawrah sai autar su Amnah shikenan su hudu. .Maza biyu mata biyu

Hakika junaidu da Hindu sunyi wa yaran na su tarbiyya sosai da sanin yakamata Dan ko a yaran dangi ana yabon su saboda tsananin biyayyar su da sanin yakamata..

Suna kiran yan uwan iyayen nasu wasu da Bappah wasun su Abu kaza, idan bangaren mata ne sukan Kira su da yagwalgwal kaza ko yadukko, ko Maamaa tamkar yadda larabawa ke kiran iyayen su.

Wani abunda zai Kara kayatar da zuciyar Mai karatu shine akwai biyayya sosai tsakanin Yan uwan. Kowanne Yana bin Mai bi Masa a shekaru. Babban want nasu kuwa wato ashir sun dauke shi tamkar mahaifin su junaidu.

Domin duk kuwa da shekarun sa shima Bai wani manyanta can ba. Amman duk da hakan Yana tsaye akan Yan uwan nasa tamkar mahaifin su.

Da aljihun sa da karfi sa Yana kokarin killace Yan uwan nasa musanman matan tana basu tsark sosai da kulawa ta musanman dubada mata na da rauni. Ga su Kuma kanana ba masu shekaru ba..

Duk kanin yaran na su sun dauka tsatson iyayen na su. Sunada matukar kyawu mai Sanya a sake kallon suakaro na baadadi.

Dogaye ne dubada shekarun su ba su njsa ba duka.amman kowanne yayau tsawon kafa acikin su tubarkallah..

Sirara ne basu cika kiba ba.. Amman ranar batai musu nuni ba ainun ba. Gashin su duka mazan da matan wani irin kanannade ne awaraare juma bakukkirin da shi na larabawa usul.

gashin a cike yake a Kuma chure Mai tsananin santsi da laushi ..gaban gashin girayr su a kwance baki sidik da shi a Kuma cike. Domin girar kowannen su tsabar cika ta kusa hadewa ma..

Kyawawa ne sosai Wanda alkalami yayi kadan wajen zayyano irin kalma kyawun yawon da Allah ya halitta akan su. Ba abunda zance sai dai mu bisu da cewar tubarkallah don kwarai matuka Allah yayi halitta..

Dawowar su ba dadewa sosai aka Sanya yaran Maza a makarantar boko da islamiya. Haka ma matan suma an Sanya su a islamiyar kadai ba bokon dubada al’adar yankin bunza inda suka tashi tun taletale mata basa karatun boko saboda wani labari Mai raba zuciya daya taba aukuwa akan wata yarinyar da malamin makarantar yayiwa fyade har ta mutu. Kuma malamin irin masu visiting dinnan ne daya aikata abunda zai aikata sai ya gudu ya bar yankin baa sake sanin inda yake ba.

Wannan abune ya dasa tsoro Mai tasiri a zukatan iyaye mata da dattikai na yankin bunza . Inda aka yanke shawara bayan anyi gangami anyi taro aka Sanya dokar Hana Yara mata karatu gabw daya na boko sai dai islamiya wadda makarantar Yan cikin yankin ne kowa ya San su…

Duk kuwa da abunda ya farun yayi shekaru da shudewa Amman ko sau daya baa taba cewa yakamata acire dokar ba. Kowa ya hakura Yara mata suka Dena karatu. Tun kafin a haifi Nawraah. Don shekarun bayan ashiir ne kawai sai Ashfeef Sai sauran yan manyan yaran dangi..

Nawraah ta kasance maabociyar son karatun boko. Don haka takan labe a kofar ajin tana sauraron karatun da ake koyarwa su Ashfeef a makarantar. Har ya kasance tana daukar littafin Ashfeef din tana koyin rubutu tana Kuma karantawa. Tun Bai sani ba har ya kamata yayi yayi bai hanata ya kasa saboda yadda taketa rokon sa tana kuka haka ya jyaketa daga baya ma sai ya zamto yakan koya mata a boye kar iyayen su Gani ko ya Bata littafin sa ta koya. Harr dai ya saya mata Dan kirraci take koyan rubutu da karatun acikin sa da dan fensurin da ya bata..

Duk abunnnan babu Wanda ya sani sai Ashfeef da ashir daya sani daga baya sai Kuma autar su Amnah data kana yayar tata nawrah tana karatu inda nawrahn ta zaunar da ita ta gaya mata komai tana rikon ta duk kuwa dakankancin shekarun amnan da basu taka kasa sun karya ba.

A boye take koyan karatun da rubutun. . Ba Wanda ya sani daga wajen Yan uwa bayan yayyaun ta da kanwata Amnah Amnah sai Layla yar gidan bappah Auwalu wadda suka taso tare aminan juna. Don wata uku ne tsakanin su kawai Layla tabawa nawrah . Shekaran n su daya gashi komai tare suke yi.. Haka dai nawrah ta rike su bisaga Amana Kar su fadawa iyayen nasu don zaa hanata a Kuma mata babban hukunci. Suka rike mata amanar kuwa basu taba fada ba ita ma Kuma nawrahn ta Ina takunta ba a taba kamata ba sanda take rubutun, take Kuma karahrawar…

Haka Sika cigaba da rayuwa a sabon yankin da suka dawo … Bappah junaidu da iyalan sa su Nawraah da Kuma bappah Auwalu da nasa iyalan..

Nusaiba itace Mai dakin bappah auwalu.. ita ba auren zumunci bane gari daya ne kawai ya hada su na bunza. Amman itama tsaton fulanin bunza ce.

Allah ya azurta su da yaran su su biyu jachak, Ahmad shine na fari Wanda saan Ashfeef ne yayan nawrah, sai Kuma Layla din da take tsaran nawrah..

_

Haka rayuwar ta cigaba da garawa da Dadi ba Dadi … Bappah junaidu Yana aikin kera karfe zuwa na zamanj a wata masana’anta. Ya zuba dukiyar sa baki daya ya sassayi ahubbun amfani inda ya bawa matar sa jari na tafara awarar sayarwa

Nan da Nan kuwa Allah ya sanyawa kasuwar albarka. Burni da kewayen yankin zuwa ake ana saya har layi ake yi

Rayuwar sai hamrala kawai, don Ashfeef da Ashir ma sukan je masaaniyar mahaifin nasu su tayashi aikin fenti da sauran su .. da wannan sike rufawa kansu asiri musanman da yanzun babu tarin dukiyar da suke da ita a baya Kafin a yiwa yankin bunza hari……

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

paid page :10

__

BABBAN BIRNIN NADUKA
(FEDERAL CAPITAL TERRITORY)

NADUKA ZONE!!

__
     Kasancewar yanayin damuna ne, babban birnin Naduka sun samu rahamar ruwan sama sosai tamkar da bakin kwarya…

Domin ruwan har gyara yayi awasu wajajen…. Wasu daga cikin gidajen Naduka zone da ke na kasa wasu sun zube, Wasu barin su ya rushe. Wasu Kuma ruwan ya mamaye gidan. Alhamdulillahi.

Ruwan yayi gyara sosai don kwatoci ma sun cika makil. Sai samari da dattawa mazan ne suka hada karfi wajen gyara unguwannin. Aka furfuto masu shanya nayi masu kwalema nayi .

Garin yayi matukar sanyi mashaa Allah abunda zaa iya cewa kenan… Bishiyu sai kadawa suke, Iska Mai Dadi na ratsa ilahirin birnin da kewayen sa. Ciyayi sun Kara zama koraye shar.

Alhamdulillah ni’imar Allah ta sauka a ko’ina…

‘Ashir ne tsugunne agaban murhu yanata fifitawa da mahuci, Sanadin ruwan da akayi yayi gyara baki daya itatuwan mutuwa sike saboda danshi.. Sai anyita fiffitawa..Haka ya gwaggwafe Yana fifita wutar sosai tamkar wata mace… Sanye yake cikin kananun Kaya na gidah.

Mahaifiyar su malama Hindu ta fito daga cikin gidah hannunta dauke da katon tray da awara sai turiri take da alama yanzun ta sauketa a wuta.

“Sannu Hamma (dake haka take ce mai kasancewar sa dan fari a gare ta) sannu da kokari.. kawo Nan na tayaka”

“Aa Ummy ai tama kama Ina man yake?”

“Gashi can bayan Kofa. Laa tabbas ta kama Allah ya shi maka albarka”

“Aameen ummy”

“Ina Ashfeef ?”

“Nace Masa yaje ya huta ummy. Dan Allah karki ce komai”

Malama Hindu tayi murmushi, Zancen dai kenan kamar ko da yaushe. Ta dube shi tace,..

“Ba zaka dena jika kannen naka ba ko Hamma?”

“Ummy idan ban jika su ba wasuke da shi bayanni?” Yakarasa fada Yana murmushi.

Itama murmushin tayi ta gyada kawai tace,

“Toh Allah ya muku albarka gaba daya Aameen”

“Allahumma Aameen”

Nan da nan ya dakko man ya dora akan wuta tuni daman sun rage hanya ta hanyar soyashi da lawashi sai kamshi ke tashi.

Yana fara zafi Ashir yaja kujerar tsugunno wajen murhun ya shiga tsoma awarar cikin ruwan kwai daya Sha kayan hadi yanaa saka ta amai.

Mahaifiyar ta su na gefe tana shi Masa albarka. Nan da Nan kuwa aka fara yin layin awarar wasu da kulolin su na abinci wasu Kuma a Leda zaa saka musu wasu Kuma a takeway pack zaa sa musu a nade da kyauro.

Cikin haka su Nawraah suka dawo daga islamiya itada Layla..

“Sannu da aiki Yakumbo” Layla tace da Malama Hindu

“Ummy sannu da aiki… Laa icen ya huru? Sanu ummy sannu Hamma” Nawraah ta fada tana zare hijabin makarantar islamiyar kalar ruwan omo..

“Sannun ku duka Allah yabada ladan karatu .. ungo Layla kuje ku hada da abinci”

Layla ta saka hannu ta karbi bakar ledar da malama Hindu ta Mika mata cike da awara sai kamshin yajin tafarnuwa ne ke tashi ga coleslaw shima a gefe da kayan su tumatir.

“Angode”
Ta nufi gidah da sauri tana murna, Don dama Koda yaushe sai malama Hindu ta aika musu da awara fal ko saya bappah Auwalu ya Aiko ayi hanawa take tace a mayar masa da kudin ta zuba musu kyauta.

Kamar ko da yaushe don kusan kullum ita take kaiwa saboda da yamma ake farawa wani lokacin da rana don haka da sun taso islamiya malama Hindu zata bata tace ta Kai gidah..

Ta shjyga cikin gidan nasu da sauri bakinta dauke da sallama,

“Umma gashi”

Ta mikawa mahaifiyar su nusaiba ledar awarar, bappah Auwalu na daga gefe Yana duban su,

“Meye wannan din dalla kina baromin Abu a Ido”

“Awara ce inji yakunbo”

Mtscew taja tsaki tana hararar ta,

“Awarar ce kika tsaya kerere a akai na sai kace wani babban Abu nazo mu gani ko na nama haka? Matsa daga nan Kafin na Kai Miki gula aciki na hanbare ki” ta karasa tana sake dankara mata harara,

“Kawo nan Layla. Je ki cire kayan makarantar kinji?”

“Toh Bappah” Ta nufi wajensa ta Mika amsa awarar jikinta a sanyaye ta nufi daki.

Ya dubi matar tasa ta sauke kanta tana hada yatsunta yace,

“Ba Zaki dai na wannan halayen na ki ba ko nusaiba! Awarar ajiya muka basu da kullum sai sun Aiko mana kyauta?”

“Yo ai sunada kudin ne. Don sun tsinnana mana da awara da me Allah zai rage su”

Tsaki yaja shima Yana karkada mata hannu yace,

“Dakin da kike kiwon ki kudi kike biya ko kyauta sukutum junaidu ya dauka ya baki iye? Ko wani abun ki saya ki basu na karamci amman kin ki”

“Kyauta ce mana.. yo wancen akurkin dakin ai sai da ya tabbatar Dan Adam ba zai iya kwana aciki ba ko da kuwa Rai daya ne bare yace zai ci moriyar sa shine ya jefe ni da shi. Su kansu kiwon Dakyar suke nunfashi saboda azabar zafi da dubu ba wundo ba a dakin haba haba Dan Allah. “

Mikewa bappah Auwalu yayi Yana girgiza kai cike da Takaici Mai tattare da dinbin bacin ran dake fitowa daga bakinta yace,

“Tunda hakan be Miki ba kyautar tazo da sakayya Mai cin mutincin to ki tattara ki kwashe kiwon ki ki mayar musu da mukullin dakin su”

Dariya ta saki tana tabe haba Hadi da tada hannuwa tana shewa tace,

“Lalle Auwalu wallahi ni dariya ma kake bani wai daki . Wancen akurkin ne daki? Wancen Dan ficicin wajen kamar bandakin kaji zaka ce mun daki? Koda yake banga laifin ka ba duk wata Yana sanmaka sadaka fisabilillahi ai shysa idanuwanka sika rufe baka ganin lefin su. Batin na mayar musu da mukullin na kwashe kiwon na Kuma ba zan ba. Nace bazan kwashe din ba. Raba Arne da makami ibada ne. Don sun dau wancen shirme wajen cikin tarin dukiyar su ta Ina Allah zai rage su? “

Bappah auwalu yayi kwata Yana cije kasan labban sa yace,

“Wadatar zuciyaa ce kawai da junaidu da iyalin sa alhamdulillah. Domin kowa sheda ne junaidu ya sayar da sauran kadarorin sa da sukai ragowa ya fara harkar kasuwancin Nan da ita ya sanwa Mai dakin sa take awara suka taru suke rufawa junan su asiri. Nan danacee maki ga dubu uku ki fara sanaa kema ai kikayi don haka karki sake kawo mun sukar Yan uwan kinji na gaya Miki” Yana gama magana ya saka Kai ya shige kitchen tabi bayansa tana sakee fashewa da dariya tana harara tana mita,

“Dubu uku… Allah ya kwashewa dubu ukun Nan albarka. Wallahi Auwalu nafi karfin dubu. Wacce sanaar Zan fara da dubu. Har da wani mun gori wai kar na karar kawo sukar Yan uwan ka. Yo ai ba sai kamin gori ba. Abunda naka gajiya da fada kullum nasan junaidu da Hindu Yan uwanka ne na jini dukkan su. Mtscew aikin kawai”

Ta shige daki ta tana bugo kofar garam. Bappah auwalu ya tabe kansa kawai yana juye awarar ababban tray…

::::::::

Wata hadaddiyar luntsumemwniyar mota ce ta faka a daidai kofar gidan… Sliding mirror din bayanta tayi na owners corner tana hangar dandazon layin awarar..

“Hajiya kinga layin ko! Yasin Kuma duk Wanda na roka abani basa yadda Yan taurin Kai ne Mutanen dake layin”

Agogonta ta sake kalla lokaci na gogawa. Cikin ta sai kugin yunwa yake gashi awarar kawai take son ci.

Batace masa komai ba ta bude kofar motar ta futa…Kallo daya zakai mata kasan wannan daga jinsin masu farcinan Susa tafito. Dubata kayan dake jikinta kadai ma abun kallo ne tabbas kudi yayi kuka awajenta.

Agogon dake daure awutsiyar hannunta Rolex ne latest design na shekarar. Jakar hannunta samfurin hems. Fara ce sosai tamkar baturiya, fatar ta sai sheki take duk kuwa da katon sunglasses din prada designer dake sakale a idanunta…Kai tsaye ta shige cikin gidan tamkar ta San masu gidan…….

WANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

paid page :11

__

::::::::::::::::

  ***Bakinta dauke da sallama a gayance ta shiga cikin gidan har yar rumfar da Malama Hindu da yaran nata ke zauna suna ta tuyar awara har kasake biyu manya. Ga layi mashaa Allah anata shige da fice na sayan daddadar awarar…

Saboda awarar na da matukar dadi ga laushi mai tattare da kwai daya lullubeta. Tasha kayan hadi. Ga tumatir da albasa cucumber a yanke a gefe da Kuma yajin tafarnuwa sai kamshin kayan kamshi yake yi…

Babban al-muhim Kuma awarar akwai tsafta. Komai a tsaftace idan kaje saya. Harta abun daukar awarar aware yake a gefe da ledar hannu ta dauka itama. Don haka Yan hayu masu kudin birnin Kai har ma da talakawan ma siya sukeyi… Ga faraa da karanci da malama Hindu da yaranta ke nunawa masu sayar awarar ta su….

Wannan yasa da karfin addua da istigfari da shimfidar fuska da Kuma kyautatawa irinta Hindu da ahalin ta yasa baki daya mutane ke kaunar awararta. Don kullum sai ta kare idan anzo saya babu duk yawanta….

   Ta lumshe idanun ta ta bude a lokacin data karasa inda suke suyar awarar. Malama Hindu ta daga Kai da sauri duk suka juya suna kallonta hadi da amsa sallamar da tayi Kafin daya bayan daya su shiga gayshe ta.

Ta amsa fuskar ta a sake. Malama Hindu ta mike da sauri tana cewa

“Hajiya shigo ciki”

Murmushi tayi cike da mamakin bata taba zuwa ba, Amman tamkar sun Santa har da cewa ta shiga cikin gidan?

Bakinta dauke da sallama ta shiga parlorn malama Hindu ta amsa tana daga tsaye .

“Ga wuri ki zauna, mu Kara gaisawa . Barka da yammaci? Iyalin kalau?”

“Alhamdulillah.” Ta amsa ta tana duba parlorn dan karami madedeci, Amman a killace ko’ina tsaf tsaf a gyare sai kamshin turaren wuta ne ke tashi…

Lalle suna da tsafta . Ganin ba wani baki dake ciki ko masaaniyar zuwan ta balle tace shiryawa sukai .

“Ma shaa Allah” malam Hindu ta fada…

“Kinsan gidan Dr. Abubakhr dollars?”

Malama Hindu ta girgiza kai da sauri tana mai him ta da kallon Karin bayani,

“bansan shi ba gaskia”

“Hakane kam ba lalle ki San shi ba. Dubada bangaren ku daban namu damu. To shi Dr. Abubakhr din miji na ne. Ni Kuma sunana hajiya qibdiyya. Kusan kullum ai Ina aiko a saya mun awara a wajen ki”

“Allah sarki. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Da ke mutanen da yawa bazan waye wanene ke zuwa ba”

“Hakane kam…” Hajiya qibdiyya ta fada tana murmushi hadi da duban agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta tace,

“Yanzun ma shine mun fito tare da shi tun dazu yacemun layi yayi yawa Dakyar idan zaa samu..”

Malama qibdiyyah ta kada Kai Kafin tace,

“Eh wallahi.. masha Allah Nan da Nan da anyi take karewa. An goggode muku baki daya masu saya Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa. Aameen”

“Aameen”..

“Shysa na fito da Kai na .. naji zan iya samun awarar ko kuwa. Wallahi wannan ne shi ya saka ” ta yi shiru bata karasa ba.

Malama Hindu na nazarce da ita daman tun shigar ta gidan dazu a farko ta hango cikin da ke jikin ta. tayi murmushi tace,.

“Allah ya raba lafiya hajiya. Ba matsala wallahi. Zaki ci anan ko a zuba Miki a pack ki tafi da ita?”

“Aah mashaa Allah, Nagode kwarai. Gashi” ta Mika mata Yan dari biyar guda biyu.

“Ta dubu biyu kenan? Har zaki cinye ta dubu biyu?

“Karki damu. Zubamin a plate kawai na ci anan. Kamar guda takwas ta Isa”

“To bari a kawo. Amman dan Allah ki rike kudin nan wallahi zan baki kyauta. Uwa uba Kuma kudin sunyi yawa “

“Ahh yar uwa banason musu “

“To shikenan nagode Allah ya saka da alkhairi Amin”

Malama Hindu ta nufi wajen babbar food flask da suke saka awara ta dakko plate ta zuba awarar fal da kayan hadi da yaji aciki..

“Gashi ranki ya dade… Bari a kawo ruwa”..

“Kakk takura kanku bari na ce driver din waje ya kawo”

“Aa dan Allah . Ki bari nima na sami lada tukun”

Hajiya qibdiyya tayi murmushi kawai hadi da kada Kai tace,..

“To shikenan tunda haka kikace. Nagode kwarai “

Malama Hindu ta sake fita tana Kiran Nawraah. Nawraah dake zubawa wani coleslaw acikin kwanon abinci ta mike da sauri,

“Naam ummy”

“Ungo rike. Ki sayo lemo daya karami da ruwa babba shima daya. Kiyi sauri banda wasa akan hanyar”

“Tohm ummy” ta fada da sauri harda hadawa da gudu. Malama qibdiyya ta koma wajen su Ashfeef dake tuyar auren Ashfeef ya hanata ta hanyar rcewa,

“Ummy kin har bakuwa ita kadai fa. Ki koma zamu karasa Allah”

“Hamma kaji abunda yace ko”

Ashir yayi murmushi Yana sosa keyar sa yace,

“Kije ummy ku cigaba da hirar ku aii sauran kasko daya daya mu karasa”

“Tohm sannun ku da kokari. “

“Yauwa ummy”

Komawa parlorn tayi wajen hajiya qibdiyya. Hajiya qibdiyya dai sai zura lomar awara take. Tamkar zaa kwace mata saboda yadda ta gigice tana wani lumshe idanun

Hajiya qibdiyya ta saci kallon malama Hindu. Jikinta a tsaftace ba akanta irin masu sayar da awara ba shadda suke tashi idan kaje kusa da su sai hamamin wari ne ke tashi. Amman malama Hindu daga ita har yaranta tsaf tsaf suke. Uwa uba ko’ina a killace musanman parlorn da take a zaune…

Ga plate din da aka zuba mata shima tas a wanke yake…tana cikin ci sai ga nawrah ta dawo rike da lemo da ruwa a hannun ta,..

“Ummy gashi”

“Yawwa an gayshe ki. Mikawa anty qibdiyya abincin”

“Tohm ummy”

Nawraah ta karasa wajen hajiya qibdiyya ta ajiye mata lemon da ruwa. Hajiya qibdiyya ta daga Kai da sauri ta kallo malama Hindu tace

“Ruwa kawai fa nace. Don Allah a mayar da shi. Kinji?”

“Ki dubi girman Allah ki amince kinji? Hindu ta fada mata.

“Ai shikenan … Bata ta shanye naga wata karama awajen. Dake bana shan Zaki yanzu sosai Ina kan dieting ne”

“Allah ya bada sa’a. Shikenan, dauki kije ku shanye”

Amnah ta durkusa har kasa ta karba da hannu biyu. Hajiya qibdiyya na kallon ta dakyau kwarai matuka ta birgeta. Yar karamar yarinyar da bata shekara biyar ba amman take ladabi haka! Lalle iyayen ta sun bata kyakkyawar tarbiyya, ta Kuma luraa dukan su yaran nada hankali da biyayya. Ta kasa hakura bayan ta dangwali yaji ta afa a baka tana taunawa tace,

“Wannan ma yar kice ko?”

“Eh…Amnah ce”

“Mashaa Allah su nawa kenan kaman uku ko?”

“A’ahh su hudu, Biyu mata, Biyu maza…. Akwai Ashir shine wancen nawaje me tuyar awarar .sai Ashfeef sai sai nawraah wadda ta kawo lemon nan da ruwa. Sai kuma autar mu Amnah..”..

“Mashaa Allah Allah ya raya su ya musu albarka”..

“Allahumma Aameen”..

Ta matso da robar wankin ruwan da aka kawo gabanta ta wanke hannuwan ta..

“Nagode sosai.. Allah ya kara kasuwa mai albarka Amin”

“Aameen” ,

“Bayan awara sai mai kike sayarwa?”

“Awarar ce kawai ba wani abu”

“Mashaa Allah… Idan ba takura ko zaki dan dinga zuwaa kina tayani wasu aiyukan na gidah ? Mai aiki na ce tatafi. Itace mewa yara girkin abunda suke so. “

Malama Hindu tayi shiru Kafin ta daga Kai tace,

‘”To zanyi shawara da abbiey dinsu. Idan ya amince zaki gani.”

“Ga number wayata nan. Ki bani taki. Idan har kin amince zaki dinga zuwa to seki Kira a aiko driver ya dauke ki”

“Tom shikenan babu damuwa. Nagode sosai hajiya Allah ya raba lafiya”

“Ni ce da godiya sosai. Allah yabar zumunci Amin”..

Har kofar gidah malama Hindu ta rakata tana mai kambama dattako irin nata.

Wajen suyar ta je tuni har sun gama ma an saye tas bata ma kai daren ba ranar. Duk dadi ya mamaye su ganin yadda ake tururuwar zuwa sayen awarar tasu..

Nan ta sheda musu yadda sukayi da hajiya qibdiyya ta karkare musu da,

“Idan abbiey dinku yazo zan sanar Masa duk hukuncin da ya yanke sai ayi amfani da shi. Ga katin data bani da number wayarta a baya. Ta saka tawa number a wayarta. “

Duk sukai mata fatan alkhairi da kuma hukuncin da abbiey dinsu zai yanke…

_

DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING:HOME/RESIDENCE)

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

1
AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

KKJ

12

✍️:MX

Ahankali cike da nutsuwa da kwarewa direban ke tuka babbar motar da hajiya qibdiyya ke ciki a baya mazaunin owners corner….

Kallo daya zaka yiwa motar kasan ba karamin kudi aka sa aka saye ta ba. Mota ce mai nishin kudi. Kyau da kuma tsananin kawatuwa..

Baka ce irin bakin nan mai sheqi a idanu.. babbar mota ce mai kama da land cruiser . Irin Saharan mota dinnan ce wadda ke tafiya ko acikin guguwa ne da tabo. Uwa uba kuma motar bullet proof ce. Ko harbi aka saki akan ta ko gilasan ta babu abunda motar zatayi.

Unguwa ce data amsa sunanta ta manyan masu kudin birnin Naduka… Kaama daga masu rawani na sarauta, Manyan siyasa, Manyan yan boko , Ma’aikatan asibiti wato likitoci, Yan kasuwa da sauran masu farcinan susa..

Wani hadadden daular gidah tamkar a kasashen ketare. Nan direban ya nufa da hancin motar ta su. Hadadden gidah ne fari tas kalar sa. Yayinda gate din gidan jijjigagge shi kuma baki wuluk ne… Tafkeken gidah ne yayi wata unguwar a kauye. Kai ka rantse ba a Nigeria bane gidan. Ganin yadda tun awaje ba ma a shiga cikin gidan ba amman gidan ya hadu kwarai matuka ..

Ga famfuna nan anyi su awaje. Talakawan Naduka zone sunzo sunata dibar ruwan a manyan bokitai da jarkuna..

Hajiya qibdiyya ta dube su ta window yadda suke jere a layi sunata dibar ruwan . Ta sauke ajiyar zuciya kawai cikin zuciyar ta tana mai nanata,

“Allah ka horewa kowa….”

Suna karasawa camerar dake jikin gate din tayi zooming tana scanning motar kafin daga bisani gate din ya bude da kansa. Direban ya shiga da motar ciki.

Mashaa Allahu…. Mai karatu ai kawatuwar gidan ba daga waje yake ba kadai. Ashe akwai sauran kallo a gaba.

Wato cikin farfajiyar gidan ma kadai wata daular duniyar ce. Habawa. Jamaa Allah yayi mana arziki mai amfani wato kudi suna inda suke ..

Wajen motocin gidan ya nufa.. kowacce motar an tanadar mata wuri acikin wata katafariyar katuwar rumfar data hadu fiye da yadda kalmomi zasu bayyana…

Manyan moticine a jere a Kuma fake. Wannan tana bani wuri. Kowacce mai tsananin tsada ce da Kuma kudi Mai yawa.

Direban ya nufi kofa zai bude mata tayi saurin budewa ta futa tana mai daga masa hannu.

Murmishi yayi kawai ya koma baya… Domin ko da yaushe idan sun fita hakan ce take faruwa ko da ya bude mata sai ta saka hannu ta rufe ta kara budewa da kanta. Ta kance masa ya kyaleta ta dinga budewa tana rufewa da kanta ai ba aiki bane. Sangartar Kuma sai tayi yawa. Har mamaki da daure Kai lamarin yake bashi musanman idan suna magana da yan uwansa direbobi dake aikin tuki awasu gidajen yadda matan gidan ke sarauta mai cike da izza. Shi kuwa ko sau daya sai dai bacin rana shima ba fada take yi ba. Amman tunda yake arayuwar sa bai taba ganin mai saukin kai da sanin yakamata ba irin hajiya qibdiyya. Sam batada wulakanci duk kuwa da tarin arzikin da take da shi.

“Sannu hajiya akwai wani aiken ne?”

Ta grigiza masa kai tana mai duba jakar hannun ta. Ta kirgo kudi ta dunkule ta mika masa yasa hannu biyu ya karba,

“Na menene hajiya?”

“Naka ne.,… Aciki na ci awarar dana shigaa kaga ban fito maka da ita ba ka nemi wata awani wajen idan ka gani ka saya hakki ne.”

Ya girgiza kai da sauri Yana mika mata kudin yace,

“Hajiya wahalar ta Isa wallahi, bugu da Kari ma kuma wallahi a koshe nake nak. Kuma kudin da kika bani da safe ma ban Ida kashe su ba wallahi. “

“Rike rabon ka ne. Nagode…”

“Ni ne da godiya hajiya Allah ya saka Miki da mafificin alkhairin sa. Ya biya Miki bukatin ki na alkhairi duniya da lahira Amin”

“Aamin… Jam’an…” Har tayi gaba zata shiga cikin gidan sai Kuma ta juya,

“Malam Liti….”

Da sauri ya amsa Yana takawa inda take,

“Naam hajiya…”

“Wannan matar me awara…”

“Eh hajiya Ina sauraron ki”

“Yan Ina ne su? Dama can tana awara bamu sani ba?”

Malam Liti ya girgiza kai da sauri cike da girmamawa yace,

“Gaskia ba Yan nan Naduka bane ance daga baya suka dawo. Amman basuda matsala yadda naji mutane na maganar. Kusan matar da mai gidan nata ma anfi yabon su kwarai matuka. Ance sudin mutanen arziki ne. Wani abun ne hajiya?”

Tayi saurin girgzia Kai tana murmushi tace

“A’ahh ba komai malam Liti. Tanada kirki ne sosai. Ga yaranta masu tarbiyya sosai wallahi..”

“Mashaa Allahu.. haka akace kam”

“Tohm dama. Kaga tafiyar Indo me aiki an dau lokaci. Yaran nan basa cin abincin malama Talatu. Basariya Kuma tayi kankanta. So na dai yi kuskuren harshe zance ko ko gandoki ne”

“Idan na fahimta kina nufin me awarar ta dinga zuwa tana yiwa su junior abinci?”

“Eh”

“Kuma har kin gaya mata?”

“Eh… Nayi sauri ko?”

“Eh to Amman insha Allahu nasan babu matsala zata amince..”

“Wallahi na yaba da hankalin ta ne. Ga shi tanada tsafta mashaa Allahu”

“Allah yasa adace hajiya”

“Aameen Yaa Rabbi. To sai gobe In shaa’Allahu “

“To hajiya ahuta lafiya. Allah ya saka da alkhairi “

“Aameen ” ta amsa kasan makoshi .

Ta shige cikin gidan ta cikin wata babbar kofa mai nauyi da ado ajikin ta. Harda madanni na kararrawa da yar camera dake haska fuskar wanda yazo.

Bakinta dauke da sallama. Ta shiga ciki tana mai zare mayafin jikin ta,

“Wash Allah na…” Ta furta ahankali tana dafe kugunta,

“Sannu da zuwa Mami…” Cewar wata yarinyar daga gani maai aiki ce… Ta Sha uniform fari da dankwali baki.

“Yauwa sannu basariya. Kina lafiya?”

“Alhamdulillah Mami… A kawo ruwa?”

“Eh maza kawo mun. Nagode”

Yarinyar tatafi dasauri ta dakko ruwa da kofi akan tray ta ajiye agaban Mami.

“Amatsa kafafun naki yanzu”

“Yauwa yar kirki. Basariya tah. Allah ya miki albarka kinji”

Basariya tayi murmushi cike da jin dadi ta kamo kafafun hajiya qibdiyya tana matsa mata kafafun da har sun dan kunbura ma saboda tsananin ciwo. …

“Su Hayfa sun dawo kuwa?”

“A’ah ai da sauran lokaci.”

“Okay eh Allah ya dawo dasu lafiya” ta fada tana kallon agogon hannun ta. Ta tsiyayi ruwan a kofi tana sha..

Yayinda basariya ta cigaba da matsa mata kafafun ahankali tana mata sannu…

NADUKA ZONE

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

__

1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

13

NADUKA ZONE

**Malama Hindu ta haye sama don watsa ruwa, Ta sauya kaya zuwa doguwar riga marar nauyi…

Sauka kasan tayi tana tafe da carbin ta a hannu tana ja…. Ba kowa a kasan sai Amnah da tayi bacci akan doguwar kujera an lullube ta da zanin gadon Ashir…

Wajen ta futa. Tas tas ko’ina tamkar baa taba aikin wuta ba wajen. A gyare a kuma tsaftace tamkar ko da yaushe ..

Ashfeef na wanke takalman ball dinsa, Yayin da Nawraah ke taje wa yartsanar Amnah gashi tana mata kalba yan kanana,

“Sannun ku da aiki….” Malama Hindu tace dasu tana mai cigaba da kallon tsakar gidan. Ranta fes…

“Ah ummy…” Ashfeef ya amsa ta yana duban ta.

“Ummy nema na kike?” Cewar Nawraah ta mike tsaye.

“Aa ba neman ki nake ba Nawraah.. Ina Hamman ku?”

“Ya fita ba dadewa. “

“Okay”

Komawa tayi ciki ta gyarawa Amnah kwanciya ta zauna tana mai cigaba da jan carbin ta.

Can ba dadewa Ashfeef ma ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama malama Hindu ta amsa. Sai kuma Nawraah itama ta ajiye yartsanar Amnah a gefen Amnan.

“Su maman baby anyi bacci.” Nawrah ta fada tana dariya. Ta gyara zaman yartsanar Amnan.

Ummy da ashfeef sukayi dariya. Can bayan mintoci Kuma sai ga dawowar Ashir rike da jakar abbiey dinsu na wajen aiki

Ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama. Abbiey din nasu na biye dashi a baya…shima yayi sallamar

Duk suka hada baki wajen amsa musu. Amnah ta mike daga baccin da take tana mutstsika idanu

Da gudu ta nufi wajen Hamma Ashir ta rungume shi. Ya dagata yana mata Wasa bayan ya ajjye jakar abbiey dinsu akan yar kantar da suke ajiye abubuwa.

“Sannu da zuwa abbieyn su. Hamma ashe Kai ma baka nan na fito su Nawraah ke cewa ka futa ba dadewa.”

“Eh wajen aikin su abbiey naje muka taho tare”

Malam junaid yayi murmushi Yana dafa kafadar Hamma Ashir yace

“Aiki ya tayamu wallahi. Inata ya barshi ma baya gajiyawa a dole ya nace na hakura na bashi… Allah ya maka albarka. Allah ya muku albarka baki daya Amin”

“Aameen suka hada baki wajen amsawa.”

“Abbiey akai ruwan wanka ko abincin zaka fara ci?”

“A koshe nake yanzun dai kan saboda na sai fura na sha. Sai dai wankan”

“To shikenan bari a Kai bandakin.”

Kitchen ta nufa ta janyo bokitin data tafasa ruwan zafi ta rufe ta haye dashi sama ta zuba a bokitin bandaki na wanka.

Ta dauki soson sa da sabulu ta sanya masa su kusa da bokitin. Kana ta dakko tiraren ruwa ta dan yayyarfa a rariyar bandaki da lunguna. Ta janyo buta itama ta cikata ta taf da ruwa ta rufe..

Ta sauka kasan ta mayar da bokitin kitchen.

“Abbiey an hada suna bandaki”

Mikewa yayi Yana nannade hannun rigar sa yace,

“Sannu da kokari Ummy …. Allah ya saka miki da alkhairi”

“Aameen abbieyn su .. Allah ya saka mana baki daya. “

“Aameen..” yaran suka amsa baki daya..

Bandakin ya haye sama ya shiga bakinsa dauke da addu’ar shiga bandaki.

Ya shiga yin wanka yana mai sake baje kofofin hancin sa yana shakar ni’imantaccen kamshin tiraren toilet mist na kamfanin yerwa incense and more 08095215215… Sam ba karni ko bashi bashi da wasu bandakunan kanyi. Kamshi dadda’da ne kawai ke tashi tamkar ko da yaushe..

Murmushi ya saki tattausa, cikin zuciyar sa yace,

“Hindu kenan…. Sarkin tsafta, Allah ya miki albarka… Aamin”

Ya cigaba da yin wankan Yana jin sa cikin wata ni’ima. Domin yayi dacen matar kwarai da zuriah dayyiba.

Ya dan jima a bandakin don bayan da yayi wanka sai da ya rage cikin sa sannan ya dauro alwala. Dakin su ya nufa ya sauya kayan zuwa aikin da wata jallabiya da yafendo ta kawo masa tsaraba alokacin dataje makka wata shekara..

Tsayawa yayi Yana duban kansa agaban mudubin… Ya saka hannu Yana shafa aikin jikin jallabiyar. Yafendon sa kawai yake tunowa alokacin data kawo masa jallabiyar ta bashi a boye tace gashinan tsarabar sace tasa ta daban kasancewar sa dan auta.

Don duk girman sa. Da iyalin sa dake karkashin sa. Yafendo kallon dan karami take masa. Jika shi take tamkar yadda akewa yan kananan auta..

Samun gefen katifar yayi ya zauna. Ya daga kansa sama Yana Mai tare hawayen dake kokarin zuba daga idanun sa.. ya tuna ana’i jibi zata rasu ta kamo hannun sa lokacin ya shiga da asubah ya gayshe ta tace,

“Allah yayi maka albarka junaidu. Allah ya raya maka zuri’ah junaidu. Allah ya bunkasa ahalin ku baki daya ya muku albarka… Junaidu baka taba mun lefi ba. Idan ma kayi akan sani ko rashin sa na yafe maka junaidu. Allah yayi maka albarka. Allah yayi maka albarka Allah yayi maka albarka. “

Hankincinsa ya zaro ya goge dan hawayen daya fara diga. Cikin haka malama Hindu ta shiga dakin bakinta dauke da sallama bayan ta kwankwasa kofar,

“Oh har ka fito abbieyn su?” Ta tambaye shi tana karasawa inda yake ta zauna…

Ta janyo kafafun sa ahankali ta dora akan cinyar ta tana matsa masa har zuwa dunduniyar tasa.

“Abbiey yanata hawaye .. meya faru?”

Yayi azamar gogewa da sauri Yana girgiza kai yace,

“Me kika gani! Hawaye Kuma? Abune ya fada idanu na shine na cire” ya fada Yana kakaro murmushi.

Itama murmushin tayi masa kawai. Tabbas ta gani kuka yayi. Amman tasan daman ba zai Fadi kukan menene ba kasancewar inde abun damuwa ne wani lokacin ya kan dannewa baya fada mata…

“Sannu da dawowa….” Ta fada tana murmushi,

“Nagode Hindu na…..”

“Ya aikin to?”

“Alhamdulillah komai kalau…”

“Mashaa Allahu abbiey . Allah ya jara tsarewa ya kareku daga sharrin masu sharri. Allah yakara buda muku yasanya albarka a nema. Allah Kuma ya amince maka a duk kanin abubuwa daka saka a gaba”

“Aameen Hindu.. tare da ke. Nagode sosai . To ya yau din? Fatan komai kalau ?”

“Alhamdulillah fa. Ta bangaren awara ma an samu ciniki yadda ya kamata fiye da tunanina mashaa Allah.”

“Alhamdulillah haka ake so. To Allah yakara sanyawa nema albarka Amin”

“Aameen… Sai kuma wata bakuwa da mukayi yau din… Duk da dai tache tana aiko direba ya saya ko da yaushe. Nache mata bazan san shi ba saboda mutanen na da yawa masu zuwa a abun hawa ..”

“Eh… Ina sauraron ki”

“Ta sayi awara ta dubu biyu… Tace abata guda takwas kawai ta isheta nayi nayi ta bar kudin ma taki wallahi. Nasa Nawrah ta sayo mata lemo da ruwa. Ta sha ruwan lemon tace Amnah ta dauka suka raba da Nawraah..”

“Ina jin ki…”

“Yauwa da fari tacemun wai nasan wani dakta wanene?… Oh kaji sunan ya bace mun,”

“Wanene?”

“Wani sananne ne a yankin su na masu kudin nan na tabbatar. Don tayi mamaki nagani danace bansan shi ba. Inaga sananne ne sosai”

“Dan uwanta ne mutumin?”

“Aa Mai gidan ta ne … Tace dai an San gidan gaskia… Wani abu dollar daga karshe”

“Ah ..gidan Dr. Abubakhr dollars???” Abbiey ya karasa fada cike da tsantsar mamaki daya gauraye ilahirin fuskar sa. Yana bun ummy da kallon Karin bayani don tabbatarwa…

Malama Hindu itama cikin son sanin taya ya ya san shi ta kada kai da sauri tace………

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

14

:::::::;

   “Ka san shi ne abbieyn su?” Ta tambaye shi, Fuskar ta dauke da son sanin karin bayani…

Malam junaid ya kada mata kansa cikin tabbatarwa yace,

“Na san shi….. Amman ba wai sanayya sosai ba. Aminin mai gidan mu ne nan inda muke aiki a maqera. Alhaji Sambaso. Abokai ne kwarai da gaske. Don wadanda suka dade suna aiki a wajen ma suka ce kullu yaumin tare suke. Daya yana wajen daya… Suka ce mutanen kwarai ne sosai. Kuma yanada kyauta ainun shi Dr. Abubakhr din domin nima kwanaki da na aiko Ashir da dubu biyu ya kawo miki wanda nace miki awajen aiki aka bamu kyauta ai shine wanda ya mana kyautar. Dubu biyar biyar… Ko da na tambayi abokanan aiki na awajen sukace mun sunan sa Dr. Abubakhr dollars… Aminin Alhaji Sambaso ne. Don da sukace daloli yake rabawa ma da su yake kyauta. Anan ya gado sunan nasa. Ana ce masa Alhajin dollar.” Ya kai karashen zancen yana kada kansa cikin tabbatar da maganganun da yayi.

“Mashaa’Allahu….. Lalle mutanen kwarai ne…”

“Ba lefi kam… A dai yadda mutane suke fada. Kuma nima da zai babbamu kudin hannu biyu ya karbe ni har yake tambayar shi uban gidan namu yana ce masa ya sunana? Amma ni sabon dauka ne ko dan bai sanni ba. Alhaji Sambaso yace masa eh daga baya na dawo Naduka da iyalina…”

“Mashaa Allahu, Allah sarki… To Allah yasaka musu da alkhairi duka damu baki daya”

“Allahumma Aameen … Ina sauraron ki. Meya faru?”

“Yauwa to ashe mai dakin sa ce. Tace sunan ta hajiya qibdiyya kuma ita mata ce agare shi. Wai ko da direban yace mata akwai laayi ba lalli su samu ba shine ta kasa hakuri kasancewar batada lafiya tana Kuma son taci awarar sosai. Shine tashi go ciki kanta tsaye tana sallama baiwar Allah…”

“Allah sarki. Allah ya bata lafiya yasa kaffarane”

“Allah ya sauketa lafiya”

“Aameen”

“Don daman tana shigowa Ina duban yanayinta kasancewar saitin wajen Kwan lantarkin nan ta tsaya hasken ya haske ta nan na hango mashaa Allah. …”

“Allah sarki…. Ina sauraron ki sai meya faru?”

Malama Hindu ta sauke numfashi tana murza yatsunta tace,

“Catai idan ba damuwa dan Allah ta yaba da hankali na da tsafta ta idan zan iya girkawa yaranta abinci mai yi musu tatafi… Ta bani wani kati da number wayarta ta karbi tawa..”

Bappah junaidu ya kada kansa kana ya numfasa ainun tukun yace,

“Sai kika bata amsar me?”

“Ina ni Ina yanke hukunci abbieyn su? Ai sai abunda kace. Kaga yaran nan suma haka suka fada sukace duk hukuncin da abbiey ya yanke Allah sa shine mafi alkhairi Amin”

Bappah junaidu ya sake numfasawa ya daga kansa tamkar mai tunani sai Kuma ya sauke yace,

“Wane irin aiki kenan?”

“Abinci…. Na yaran ta, meyi musu tatafi ita kuma tayi nauyi”

“Tohm banyi niyyar amincewa ba gaskia dubada ba sanin hallayar ta mukai ba sai dai dan kin ga wasu daga ciki datazo din .. Kuma mai gidan nata ma ance bashida matsala. Babban abunda yasa zan iya amincewa Kuma shine dalilin wannan nauyi da kikace tayi Allah ya sauketa lafiya Amin”

“Aamin ..abbiey ka amince kenan?”

Bappah junaidu ya kada Kai Kafin yace,

“Eh to…. Bazan hanaki ba. Ban Kuma gama amincewa da barin ki kije ba saboda banyi magana da Hamma ba naji hukuncin dashi zai fi dacewa duk kuwa da nasan babu matsala … Amman zan same shi yanzu inshaa Allah. Duk yadda muka tattauna muka yanke zan gaya miki.”,

“Toh shikenan abbieyn su. Allah ya zaba abunda yafi alkhairi a rayuwar mu gaba daya Amin”

“Allahumma Aameen…”

“Azubo abincin yanzu?”

“Eh azuba.. Amman akai wajen su Bappahn su zanje muchi da shi daga nan sai mu tattauna abunda zamuyi idan na dawo zakiji komai”

“Toh Allah yasa muji alkhairi Amin, bari a zuba.”

“Aameen… Allah ya miki albarka”

“Aameen abbieyn su… Duk hukuncin daka yanke na aminta da shi wallahi. A har kullum amincewar ka nake so a dukkanin lamurana. Kasani har a raina ban yanke hukuncin komai ba sai wanda ka zabar mun. Hasalima bansa zanyin ba. Dubada aikin awara da mukeyi muma anan din.”

“Nasani Hindu…. Kada ki damu kinji? Mu Mika lamuran mu wajen Allah baki daya. Badan rayuwa ma data sauya mana ba Hindu ai munfu karfin duk aiyukan nan abaya… Sai dai ma mu mu kyautar ba dai abamu ba. To ruwa ne ya daki babban zakara. Allah yasamu dace”

“Allahumma Aameen…”

Kasan suma sauka a tare. Bappah junaidu ya fice zuwa gidan bappah Auwalu.

Ya yinda malama Hindu ta nufi kitchen cikin babban tray ta jera komai na abincin dede cin su ta hada da plates biyu da cokula,

“Ashfeef…”

“Naam ummy”

“Ungo bi abbieyn ku dashi ka Kai musu gidan bappan ku acan zasu ci”

“Tohm” Ashfeef ya karbi tray din ya fita ya nufi gidan bappah Auwalu.

A barandar kofar gidan ya hango su a zazzaune su biyun akan tabarma. Ya kai musu ya ajjye agaban su bayan yayi sallama ya gayshe da su.

“Sannun ka Ashfeef . Allah yayi albarka” Cewar bappah Auwalu

“Aameen Bappah…”

“Tashi kaje ko? Magana zamuyi”

“Tohm abbiey. Bappah a huta lafiya”

Mikewa yayi har zai nufi hantar gidah yaci karo da Ahmad tsaransa wato yayan Layla. Abokin sa ne kuma dan uwan sa ne. Wata biyu ne a tsakanin su. Don haka suna aminta sosai.

“Waje na kaje ne?” Ahmad ya tambaye shi Yana nuna kofar gidan su

Ashfeef ya girgiza kai yana sosa kasan keyar sa yace,

“Wajen su Bappah naje na kai abinci”

“Okay… Ya za’ai ball fa da Argentina zo muje mu kalla. Ana haskawa a gidan kallon ball dinnan. “

“Tohm bari na tambayi ummy tukun. “

“Ga bappah nan ka tambaye shi mana”

“Abinci zasuci Kuma magana zasuyi shi yasa. “

“Okay muje ka tambaye ta”

Suka mike suka tafi gidan su Ashfeef din suna tafe suna hira. Suka shiga cikin gidan bakin su dauke da sallama.

Ahmad ya gayda su ummy ya zauna a bakin kujera. Ashfeef ya tambayi ummy tace,

“Kuje amman karku dade ana tashi ku dawo gidah”

“Inshaa Allah ummy”

Ashir na zaune yana sauraron labarin da Amnah ke bashi na yara ya saka hannu a aljihun sa ya zaro nera hamsin ya mikawa Ahmad

“Ungo ku sayi wani abun”

“Mungode Hamma”

“Godia muke Hamma”

Suka fice sunata murna. ..ummy ta dubeshi tayi murmushi kawai… Kyawawan halayen Ashir sunada wuyar misaltuwa….

__
Bappah junaidu da bappah Auwalu sun jima sosai suna tattauna sun Kuma yanke shawara maganar aikin ummy na gidan Dr. Abubakhr dollars..

Don haka Kai tsaye ya nufi gidah bayan sun gama maganar. Ya shigaa parlor bakinsa dauke da sallama ba kowa yaran duk sunyi bacci sai malama Hindu data saka radio a kunne tana sauraron wa’azin da akeyi…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

15

::::::::

Ya sake sakin sallama a karo na biyu yana Mai zare takalman dake kafafun sa…

Sai a sannan ummy ta jiyo sautin sa. Ta zare rediyon daga kunnenta tana mikewa tsaye,

“Sannu da zuwa abbieyn su”

“Sannu kade… Yi hakuri na shagala munata hira ashe dare ya kule haka .. duk sunyi bacci ko?”

“Wallahi kuwa… Kowa yayi bacci”

“Ayyah… Yi hakuri na shiga hakkin ki. Wallahi sai da Nusaiba ta leko tana cewa ya shigar mata da tabarmar idan mun gama na duba agogo nace kai haka dare ya wuce bamu sani ba? Astagfirullah.”

Malama Hindu tayi murmushi tana jijjiga kai tace,

“Kai Nusaiba…. Halinta sai ita”

Bappah junaidu yayi murmushin shima yace,

“Allah yasa mu dace”

“Aameen…”

“Muje ko?… Mayi maganar a sama”

“Tohm abbiey.”

Ta rurrufe ko’ina sannan suka haye sama dakin su .. sai data fara lekawa dakin su Nawrah suna bacci sannan ta shige nasu dakin bakinta dauke da sallama…

“Ko kana bukatar wani abun abbiey?”

Bappah junaidu ya matsa kusa da ita ya kamo hannuwanta cikin nasa yana murzasu ahankali. Idanuwan sa cikin nata yace,

“Bana bukatar komai Hindu…. Ke kadai kin ishe ni… Ke kadai nake bukatar kasancewar ki matata agare ni a Koda yaushe .. kin zarce matsayin duk wani abunda kike tunanin zai kere ki…. “

Tayi murmushi kanta na mata girma ta dashare hakora sosai tace,

“Godia nake abbieyn su…”

“Ki fadi sunana mana daga ni sai ke ne fa… Junaidun naki Kuma?”

Hindu ta sake sakin wani tattausan murmushin da ta saka bappah junaidu Kai hannunsa kan kumatun ta yace,

“Kinji……?” Yaja ji….. Din sosai ta yadda Hindu sai data kasa danne yanayin daya sakata tace,

“Junaid …. Junaidu…. Junaidu na…”

Bappah junaidu dadi ua sake mamaye shi. Sunayen datake Kiran sa kenan lokacin suna saurayi da budurwa da aka saka ranar auren su kafin ayi auren idan yaje zance yana ce mata,

“Hindu… Hindunah…. Hindatuna tawa ni kadai …” Ya tuno bayan yana mai sake fada ahankali a kuma rarrabe

Ta sake murmushi tana cusa fuskar ta a akan cinyar sa tace,

“Kai abbieyn su har kasa na fara kunyar ka..”

“Kunya….? Ni Kuma yau?”

Ya tambaye ta yana daria sosai.

Itama dariyar tayi …ya saka hannuwan sa biyu ya dago fuskar ta. Ya tallabo fuskar sosai yana duban ta,

Ya kai kansa saitin fuskar ta dab da dab suna shakar numfashin juna .. Ya samu kansa da Kai bakinsa kan saitin tsakiyar gashinta ya sakar mata sumba..

“Allahumma barik …..”

“Wa iyyakum ….”

“Hindu…..”

“Naam….”

“Da farko Kafin na baki amsar hukuncin da muka yanke akan maganar aikin ki zuwa gidan Dr …. Inaso ki bani nutsuwar ki sosai ..”

“Ina sauraron ka Junaid… Allah yasa muji alkhairi”

“Tohm aameen ya rabbi…. Alkhairi nema.. da farko dai kinga a kudaden da yafendo ta babbamu anyiyyi guzuri akazo Kuma kashin kudin nan garin ba irin na bunza bane.nan birni ne sosai kudin komai anan Naduka ya ninka na bunza sau uku… Ko ba haka bane?”

“Haka ne abbieyn su..”

“Dukkanin ku kunsani ke da Nusaiba da sauran matan su bappah sani. Kudin da yafendo ta bari don ayiwa yarannan kidimar karatu da Wanda zaa musu idan sun tashi aure sun Kare anyi haka?”

“Hakane abbiyen su”

“Tohm… A dawo kan namu kasafin kudin. Kinga anawa kudin da gado na da Wanda yafendo tabani ta karamun dasu nayi gidan nan na Kuma tattara nake harkar kasuwancin nan da su ciki sune dai na tsakura ba yawa na baki kike awarar nan. yaran nan maza Kuma suke fenti idan an samu dama. Ake biya musu kudin boko da arabi matan ma ake biya musu kudin islamiya ko?”

“Wannan haka yake abbiyen su. Ai kowa ya sani Allah dai ya saka maka da alkhairi…”

“Aameen dukkan mu .. To kinga a abunda ake samu kema da Wanda kika bayarwa da Wanda yaran nan musamam Ashir ke kawowa duka kokari muke a taru a rufawa juna asiri. Abunda ya rage mun na boye kawai wannan ajiyar ce… Zaki dakko mun ita da safe inshaa Allahu… “

“Allah dai ya kara horewa Amin… Amma abbiyen su me zakayi da wannan ajiyar dakace ka tanade ta ne saboda nan gaba idan da rai idan auren Yara ya tashi…”

Bappah Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya mai turiri ya sake kamo hannuwanta yace,

“Babban uzuri neya taso… Kuma ba aro zan bada su ba kyauta zan bayar. Inshaa Allah Allah zai hore mana agaba… Kinji?”

Taso tambayar sa menene sai Kuma ta danne kawai ta daga masa kai. Don tasan koma menene tsakanin sa neda dan uwan sa. Don haka batasan shiga lamuran yan uwantakar su inde ba ance mata gashi gashi ba…

“Hindu …..” Ya sake kiran sunan ta..

“Naam..”

“Tunanin me kike ne?”

“Bakomai abbiey…”

“Kinga ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane. Gidan bappah Auwalu ne yake yoyo sosai baki daya katangar sai an canza ta .. wasu kofofin suma sun lalace sai ya sauya. To kinsan Nusaiba ta saka shi agaba wallahi. Ransa ba dadi sai dana tilasta masa sannan yake fada. Yace na tayashi neman inda zai samu bashi. Kuma kinga Hindu hannun ka baya rubewa kace zaka yanke ka wullar ko? Dan uwana ne bazan iya zuwa wani wajen na aro masa kudi ba bayan ni inada shi ni ne zan share masa hawaye tunda ni ne dan uwansa dake kusa yanzu… Shi yasa nace zan duba Masa acikin mutane zuwa da safe.. Amman ni ba aro zan bashi ba kyauta zan bashi. Nasan Allah bazai hana mu ba nan gaba. Dama shi ya bamu… Ko kuwa?”

“Hakane abbiey ka gama magana. Allah ubangiji ya saka maka da aalkhairi.. Allah yabar zumuncin ku. Ya biya maka dukkanin bukatin ka duniya da lahira. Allah Kuma ya kara arziki ya bude maka kofofin alkhairi Amin… Hakika Kai dan uwane na gari ne mai share hawayen nasa Yan uwan ko da kuwa shi nasa idanun rufe suke da damuwa. Allah ya iya maka abbiey. Amin”

“Aamin Hindu … Tare da ke .. Allah ya Miki albarka. Nayi dacen mata tagari a duk halin dana tsinci Kai na Hindu bazan taba mancewa da alkhairin ki gare ni ba… Allah ya saka Miki da gidan aljanna. “

“Aameen abbiey…”

“Sai maganar zuwa gidan Dr abubakhr dollars… Shin againiki ke akan kankin kanki babu takura kiyi aiki a karkashin wasu tunda ba taba yi kikai ba? Kada kiga ko sabuwar rayuwar da muka tsinci kanmu aciki a haka zamu dauwama kike tunanin kaskantar da kanki kiyi aikatau a biya ki.. don rufin asirin mu”

“Ko kadan abbiyen su… Kuma kasan ni Ina son dukkanin abunda ya danganci fannin girki. Da ba girki bane bama bana tunanin zan karbi aikin gaskia”

“Hakane…. Kuma mun yi magana da bappah Auwalu. Shima yace a nemi yarjewar ki tukun dukkanin yadda Kika yanke yayi. Idan kin amince zamuyi to muna murna idan bakyaso nanma muna murna da fatan alkhairi.. me kika zaba? Wanne hukuncin ne yayi miki”..

Malama Hindu ta dan nisa can tache,

“Na amince abbieyn su ….zanyi aikin”

“Toh Allah yasa hakanne nafi alkhairi , Allah ya dafa Miki yasa ki fara a sa’a”

“Allahumma Aameen abbiey”

Haka sai adaren ranar suka kusa raya rabinsa da hira. Daga nan sukayi alwala sukayi sallar dare kana sukabi lafiyar katifa suka kwanta bacci ya dauke su…

Sai da malama Hindu ta dauki kwanaki biyar tukun sannan ta kira hajiya qibdiyya tace mata ta amince. Hajiya qibdiyya tayi murna kwarai matuka tace mata zata aiko a dauketa da safe inshaa Allahu .. ai kuwa haka akayi da safe wata zungureriyar mota hadaddiya tazo ta dauki malama Hindu har kofar gidah zuwa gidan da zata fara aikin abinci na iyalan Dr. Abubakhr dollars…..
INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

16

:::::::::

16

:::::::::

Dr. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING/RESIDENCE:

  Malama Hindu na bayan mota, Ya yinda kanta ke kallon window na mota tana duban gidajen layin masu matukar kyawu Ma shaa’ Allah ..

Malam Liti ya karya kan mota ya shiga gidan, Yayin da malama Hindu taga gate din ya bude da kansa motar ta shiga ciki….

Kasa boye mamakinta tayi har sai da ta waiwaya ta bayan motar ta sake duban gate din ya koma ya rufe da kansa…

Ta bude murfin motar ta futa bakinta dauke da addua… Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa mai dogon hannu… Ta saka wadataccen hijabi kalar kayan na ta.

Hannunta rike da yar karamar jakarta da wayarta me torchlight aciki sai charbi da take ja..

“Yauwa, Bismillah! ga kofar da zaki shiga nan…” malam Liti ya nuna mata kofar da zata shiga ciki

“Tohm, Nagode.” Ta dan kakkalo harabar gidan cikin ranta tana yaba kyawu da tsaruwar komai na wajen tun ma bata shiga cikin ba. Don a iya motar da aka zo daukar ta kadai tasan ba karamin gidah zata jebah..

“Mashaa Allah ..!” Ta fada ahankali alokacin da ta zare kafafunta daga cikin takalman data saka ta taka wani lallausan welcome carpet da kafafun ta suka lume ciki saboda tsananin laushin sa.

Ta sadda kai kasa ta dubi dan karamun carpet din da ke shimfide a bakin kofa an rubuta masa welcome da manyan baki..

Sake doka wata sallamar tayi bayan wadda tayi ta karasa shiga ciki tana mai nanata wa a karo na uku .

“Waalykm Salam” wata dattijuwar mata ta amsa mata daga wani daki data leko da fuskar ta.

Malama Hindu ta kakaro murmushi tache,

“Ina wuni?”

“Lafiya kalau… Ina zuwa”

Malama Hindu ta nemi jikin bango ta tsaya tana dan kallon cikin babban parlorn da mai karatu zai iya fasalta shi da aljannar duniya.

Ya hadu karshen haduwa, Domin babu ce kawai babu a parlorn nan duk inda hadadden parlor ya Kai na manyan attajiran masu kudi parlorn nan ya kai. Don ko acikin manyan masu kudin ma ba kowanne bane zai yi dace da gidan sa ya samu kayan dake cikin parlorn .

Wasu irin Royal chairs ne ainihin royal na sarauta. Kirar oman kalar golden da white. Ya yinda curtains din parlorn ma royal ne design din kujerun suma.

Kai harta marikin labulayen da tv stand da dinning area da sets dinsa da ke gefe duk royal ne. Komai da komai na parlorn royal design ne. Lamarin sai dai ache tubarkallah kawai.

Dattijuwar matar tafito daga cikin dakin da take tana gyara zaman dankwalin data daura akanta.

“Baliwar hajiya ce ke”

“Eh…Ina kwana ?”

“Lafiya kalau Alhamdulillah. Bari a gaya mata”

“Tohm shikenan”

“Ki zauna ga waje nan bari na kirata”

“Tohm godia nake”

Malama Hindu ta nemi waje ra zauna a kasan carpet jikin wata kujera, ta hango dattijuwar ta nufi wajen wata waya dake manne a bango ‘intercom’ ta danna wasu number ta kira waya.

“Assalamu alaikum… Eh tazo to shikenan” ta mayar da wayar ta shiga wata kofa dake kallon daya bangaren inda dinning area yake. Wanda zaka tabbatar kitchen ne

Tray ta fito dashi ta ajiye agaban malama Hindu. Dauke tray din yake da lemo da ruwa da snacks da kofi na tangaran,

“Bismillah tana zuwa”

“Nagode… “Malama Hindu ta fada tana gyara zaman tray din

Matar ta koma cikin kitchen ta rufo kofar. Malama Hindu na zaune shiru shiru sai dube dube take

Cikin haka sai ga sakkowar hajiya qibdiyya daga bene sanye cikin doguwar riga bubu ta material marar nauyi ta daura dankwalin kayan a kanta.

Ta dashare hakora a lokacin da suka hada idanu da malama Hindu

“A kasa? SubhanAllah… Tashi tashi ki koma kan kujerar dan Allah”

“Ah wallahi nanma ya Isa hajia. Ina kwana”

“Dan Allah banason musu ki hau ki zauna please. Mama Talatu, mama Talatu”

Malama hindu ta haye kan kujerar ta tsakure kanta a kasa.

Dattijuwar ta fito daga kitchen da alama itace malama talatun.

“Hajiya ga ni..”

“Mena ce miki idan bakuwar nan tazo?”

“Kikace nache kina zuwa. Na Kuma kawo mata ruwa da lemo da su cake.”

“Bance ki ce ta zauna ta jira ba”

“Na gaya mata hajia”

” A kasan carpet saboda Allah? me ze hana kice ta hau kujera haba mama Talatu”

“Kiyi hakuri hajiya nayi kuskure”

Malama Hindu da sam bata dauka abunda hajia qibdiyya zata ce bane da sauri ta g girgiza kanta tana daga hannu,don sam batason daga zuwanta sanadiyyar ta mutanen da suke zaune da ita su bata Kuma ace ta dalilin ta. Cike da sauri tace

“Wallahi ta jatbte ni hannu biyu, Muka gaysa ta kawo mun su lemo. Allah ni ko tace na zauna akan kujerar ma bana zama hajiya. Nafi kaunar zaman kasan . Mama Talatu ba ruwanta wallahi”

Mama Talatu kanta a kasa ta ce,

“Ayi hakuri hajiya.”

“Je ki….” Cewar hajia qibdiyya.

Jikin malama Hindu yayi sanyi. Gaskia sam batajin yadda hajia qibdiyya ta yiwa mama Talatu ba. Tamkar kuwa ta ga zuciyar ta. Tache da ita,

“Karfa ki dauka Ina da faada …. Wannan dinma kamawa tayi. Kinsan lokacin abu ka gyara shi kawai ba daga baya idan bata nan ba nazo inayi da ita ban kyauta ba. Haka nake ni a duk sanda kowane yayi Abu alokacin zan wankeshi awuce wajen . So wallahi wannan abun ma ya wuce. Kakki damu ai muna tare. Mama Talatu yar uwa ce ta zarce yar tayin aiki ba ita kadai bama harda sauran maaikatan.. kinaji na?”

“Ina sauran ki hajia”

“Ita wanan da tabar nan sunanta Mama Talatu. Babbar Mai aiki ce dake abincin gidan gaba daya idan zaa ma Mai gidan ma ita ke tayani, yanada diabetes so ba komai yake ciki ba”

“Allah sarki Allah yabashi lafiya Amin”

“Aamin Yaa Rabbi… Ni sunan ki nema ke kwatanin wlh”

“Sunana Hindu…”

“Mashaa Allah.. sunana hajiya qibdiyya kamar yadda na gaya Miki a baya. Alhaji abubakhr dollars shine mijina, Kuma babban maikacin lafiya ne da kasa keji dashi baki daya. Don har number yabo ta duniya aka bashi watanni uku da suka wuce. Na zangon farko kan mukamin gwarzon dayafi kowane likitan iya tiyatar haihuwa “,

“Mashaa Allahu hajiya. Allah yakara hazaka. “

“Aamin… Ni yar kasuwa ce. Ina saye da sayarwa na manyan dilolii ke kaiwa manyan yan kasuwa Kaya suna Kuma zuwa su Sara awaje na cargo cargo. inaga foundation na tallafawa marayu da marasa karfi Mai taken,

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

17

:::
17

     Malama Hindu ta jinjina Kai tana sauraron hajia qibdiyya har ta karasa maganar da take yi.

“Mashaa Allah. Allah ya raya su baki daya ya inganta su ya Kuma tsare musu kuruciyar su har girman Amin “

“Aamin Aaameen godia nake …. Hindu, Allah Kuma ya saka da alkhairi da kika amince da rokon da nayi Miki….”

“Bakomai hajiya. Ni ceda godiya”

“Ni dai x…. Kinga me musu girkin tatafi kauye ne ganin gidah wai. To Kuma sai ta Kirani ma take cemun bazawarin da zai aure ta ya matsa yanaso ayi auren kawai. Nace mata babu komai wallahi ai auren shine gaba da komai. Allah yasa albarka. To yaran Kuma basa cin abincin da ake wa baban su Wanda mama Talatu keyi saboda akwai Abubuwa da yawa da baa saka masa a abinci kasancewar ciwon sukarin da yake da shi…. Wannan wadda tazo nan itace malama Talatu. Itace babbar mai aikin mu. Sai basariya tana Ina ne.? Basariya” hajiya qibdiyya ta kwadawa sunan basariya kiraa da karfi

Basariya ta sakko daga sama da sauri,

“Naam! Ga ni”

“Zo..”

Tazo har wajen su. Ta tsugunna ta dubi malama. hindu tace,

“Ina kwana?”

“Lafiya kalau basariya .”

“Itace basariya… Je ki”

“Mashaa Allah Allah ya rayata Amin”

“Aamin Aameen ” direban daya dakko ki sunan shi malam Liti. Direba na ne shi.. Sai emeka direben Alhaji ne. Ana Kiran sa da oga emaka….. Da Ribado direban Yara ne. Ya kai su makaranta da.sauran su. Sai su Mudi, Barau… Masu gadi ne. Sai Samuel gateman, wato security in charge of the inspection da sauran su.. sai Ghali da dahiru masu wanki da guga. Bilal Mai share share. Nuhu gardener ne. Sai latifa ita ba kwana take ba jeka ka dawo take. Tana zuwa ta share ko’ina na cikin gidan nan ta gyara ta wanke da dakuna da sauran su. “

“Mashaa Allahu…Allah yakara arziki ya biya ku baki daya”

“Allahumma Aameen…. Hindu .. dama already kin gaya mun yaran ki hudu ko da sunayen su”

“Eh duk da dai ban buda sosai ba. Sunana Hindu. Mijina sunan sa junaidu. Mu mutanen yankin garin bunza ne zama ne ya dawo da mu Nan Naduka. “

“Bunza dai ta gabas?”

“Eh ita..”

“Allah sarki. Nasan bunza farin Sani. Akwai matar kawu na yar garin ce muna kanana an Sha zuwa da mu sosai ita bafulatanar ce kinsan garin naku ya Tara yarika kala kala”

“Allah sarki..eh haka nekam .donmu kan mu zuriyar tamu ta rabu gidah biyu”

“Mashaa Allahu. Tabbas kala kala qabilu kam naga harda larabawa lokacin muna kanana”

“Eh tsatson zuriyar mu ne. Larabawan. Kuma mun hada fullanci”

“Kai mashaa Allahu. Ai ina ganin ki da yaran ki nace Kai tubarkallah mashaa Allahu. Tamkar larabawa ashe ashe akwai jinin su atare daku”

Malama Hindu tayi murmushi. Hajia qibdiyya itama murmushin tayi tace,

“Ku kadai ne anan garin kenan?”

“Aa akwai yayan miji na da iyalin sa anan. Da duk ma anan din zamu zauna to Kuma sai kowanne aiki ya mayar shi wani wajen shi da iyalin sa. Allah vai amince ba sai mu biyu kawai. Mu da iyalan yayan baban yarana”

“Mashaa Allahu… “

“Tare muke da su… Gidan su na gaba da mu bamu da nisa sosai”

“Allah sarki Allah yabar zumuncin ku, Hindu … Me yaran ki ke Kiran ki saboda yaran nan din su dinga Kiran ki da haka?”

“Ummy suke cemin”

“Mashaa Allah .. tohm Ummy su Anees zasu dinga Kiran ki da shi inshaa Allahu. Sai wani hanzari ba gudu ba. Naga kina sana’a Kuma banason na tauye Miki Taki sanaar da kike… “

“Babu komai hajiya duk ba zai gagara ba inshaa Allahu wannan ma ai sanaa ce”

“Duk da haka Hindu… Karfe nawa kike farawa”

“Da rana muke farawa. Wani lokacin yamma zuwa dare inshaa Allahu. “

“Mashaa Allahu. Tohm dama abinci ne kawai Zaki dinga dafawa Yara. Indo itace meyj musu Kuma aure zatayi. Da niyyar ganin gidah taje Kuma manemin aurannata ya matsa kan lalle shidai ayi auren kawai ta kirani tana neman sharawa nace mata Indo kiyi auren ki kinji? Shi yafi komai.”

Malama Hindu ta Kada Kai tache,

“Hakane kam Allah ya basu zaman lafiya amin. Ni Kuma Allah yasa na iya irin abincin da take yiwa yaran naki”

“Weekends sai 12 suke breakfast so kaman 10 haka kinzo Kafin 12 kin gama musu, da rana snacks suke ci already munada frozen ones a freezer sai dare Kuma muna fita dinner da babansu muci abinci awaje.”

“Kenan idan na fahimce ki ranakun hutu na azabar da lahadi abincin safe kawai akeyi nazo karfe 10 na gama na ranar shikenan darana suna cin snacks da dare kuna ci awaje ko hajiya?”

“Eh haka nake nufi Hindu… Sannan ranar litinin zuwa alhamis su zaki dinga zuwa karfe 12 na rana ki gama Kafin 2 haka zuwa uku shikenan. Da safe mostly toasted bread ko sandwich suke ci. Abincin da kika girka da rana Kuma shi zasuci inshaa Allah da daddare yawanci indomie suke dafawa da sausage da kansu.”

“Mashaa Allah Allah ya raya su ya tsare kuruciyar su har girman su Aamin.”

“Aameen Yaa Rabbi Hindu..Aameen”

“Hajiya ranar jumuaah fa banji kin ambata ba?”

“Duk ranar Fridays gidan mu nake zuwa acan muke wuni yawanci da yaran da su mama Talatu idan Kuma yaran sun tsaya lesson toh sai su samenu acan din dai. Ranar jumuaah duka Yan gidan mu muke hallara gidan mu duka acan ake cin abindi a sada zumunci”

“Mashaa Allahu lalle kuna sudaa zumunci kam. Allah yabar zumuncin Amin”

“Aameen Yaa Rabbi wataran zamuje dake ai inshaa Allahu kiga Gwaggon mu”

“Mahaifiyar ki?”

“Eh…”

“Mashaa Allahu Allah yakara mata lafiya da Nisan kwana Amin”

“Aaameen Yaa Hayyu ya qayyum nagode kwarai. Naku iyayen suna can bunza kenan ?”

“Aa sai dai Yan uwa da abokan arziki na nesa. Domin duk ahalin duk sun rasu”

“SubhanAllah Allah sarki Allah ya jikan su ya rahamshe su yabaku daya Amin”

“Aameen Yaa rahbi. Dake gaskia zuriyar tamu ana samun rashe rashe duk dangin yawanci babu sun tafi.”

“Kowa tasa yake jira. Allah ya kyautata namu zuwan Hindu”

“Aaameen hajiya…”

“Sai maganar kudin…nawa kike ganin zai isheki?”

“Hajia ki bada abunda Allah ya hore kawai”

“Ki dai fada Hindu”

“Bantaba aikatau ba hajia saboda bansan nawa ake biya ba wallahi ” tafada tana lankwasa yatsun hannuwan ta.

Hajiya qibdiyya tace,

“Dubu hamsin ya miki?”

“Hajiya yayi yawa ki rage”

“Bai yi ba ai kinada iyali Hindu. Kuma zama dasu Hayfa sai hakuri musanman Anees…”

“Dan auta?”

“Eh fa kamar kin sani … Amma ba wai karamin dan auta bane kamar Amnah dinki don ya kai dayan yaron ki dinnan”

“Mashaa Allahu wanne daga cik? Babban Ashir ? Ko na biyun sa Ashfeef?”

“Yauwa na biyun”

“Ah mashaa Allahu kam. Toh Allah ya raya su duka Amin. Nagode hajia Allah ya saka Miki da mafificin alkhairin sa ya kara arziki Amin”

“Aameen Yaa Rabbi muje nanuna Miki kitchen dinki?”

“Toh hajia….”

Hajia qibdiyya ta mike. Ya yinda malama Hindu tabi bayan ta….

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

18

18

      Wani hadadden kitchen suka shiga… Kana shiga na’urar sanyin ac zata bugo sanyin ta jikin ka…

Katoton kitchen ne wanda ke luntsume da hadaddun kitchen cabinets green and yellow… Dukkanin kitchen utensils din dakin girkin nan kalolin sa kenan guda biyu kore da yalo….

Ga wani dankareren fridge mai kofofi biyu da zaa iya bude su. Yayinda kasan sa kuma freezer ce sai water dispenser daga gefe.  Da wasu madannai ajikin sa da remote controller. malama Hindu ta dauki mintinan tana kallon fridge din. Azuciyar ta tana nanata mashaa Allah tubarkallah.

Ga wani daki karami shi Kuma dankali da doya da albasa ce kawai acikin sa a zube gaba ki dayan dakin.

Da manyan freezers tafka tafka guda uku ajere. Daya kayan Miya, daya snacks, daya kaji da nama fal.

Sai wani baskets Mai hawa hawa da yawa cike da plantain da crates na kwai ajiye dasu tafarnuwa da su spices.

Da manyan jars na daddawa, kuka, Yajin daddawa na tafarnuwa dana daddawa. Gishi, maggi da sauran su.

Sai gallons na farin mai da manja da su olive oils da sauran su… Komai da komai daya danganci kayayyakin abinci na alfarma Kama daga basmati rice da shinkafar tuwo data dafawa, spaghetti, garin tuwo, indomie, noodles da sauran su buhu buhu cartons cartons gasinan jibge a store..

Harda su kayayyakin shayi suma gasinan a kwali da gwangwanaye manya manya nasu mayonnaise, cream salads, waken gwangwani da nasarar sa, su ruwan robar da lemuka birjik kai da sauran su dai komai dai akwai babu ce kawai babu…

“Kinga komai na abincin ko Hindu?”

“Nagani hajia mashaa Allahu”

“Akwai abunda kike bukata da babu?”

Malama Hindu tayi hanzarin jinjina kai da sauri tace,

“A’ah fa hajia, ai babu abunda babu anan gashinan mashaa Allahu kamar shagon siyayya. Allah yakara arziki”

“Aameen Hindu. Amman ba zaa rasa ba. “

“Hakane kam. To gaskia dai a iya abunda na sani ko ince wadanda zan iya amfani dashi dai duk gasinan sai dai ko Nan gaba idan an tashi idan babu.. Don naga wasu daga cikin spices dinmu ma kuna da su. ” Ta karasa tana nuna wasu spices na labarawa

“Mashaa Allah kina amfani dasu? Oh haka fa ku da jinsin ku.. girki da su akwai dadi ga nara dandano mashaa Allah”

“Sosai kam”

“Tohm bari na barki kiyi musu Abu Mai saiki kawai. “

“Su uku kikace ko hajia?”

“Eh su uku ne… Ga tukwanen Nan ga oven ga grilling machine, ga gas cooker nan. Da sauran su dai duka”

“Mashaa Allahu…. Sai dai wannan sai an koya mun amfani da su. ” Ta fada tana nuni da wadanda vlbata gane ba

Hajiya qibdiyya ta gyara tsayuwarta ta shiga nuna mata aikin kowanne da yanda aje kunne su da kashe shu. Zaai mana
.

“Ga waya anan intercom ce idan kina bukatar wani abun sai ki Kira ki danna wadannan madannan. Ga ruwa Nan da lemo ki dauka ki sha duk sanda kike so. Ga rigar girki Nan idan bakyaosn kayan ki suyi kamshin girki sai ki sauya. Ga Kuma daki Nan na hutawa wanna kofar da ke kallon ki idan kin fita akwai sallaya da carbi da hijab da toilet aciki ..”

“Mashaa Allah sannu da kokari hajiya. Allah yakara arziki”

“Aameen Hindu. Allah ya jara mana baki daya “

“Aameen Yaa Rabbi”

“Toh bari naje na yo wanka Nima. Sai na sakko ko. Dukabunda kike bukata dai ko Karin bayani wannan number jikin takardar Dana baki uta Zaki Kira ta wannan wayar. Idan abunda Kuma ya kulle Miki Kai nema Zaki iya tambayar mama Talatu . Idan dakko Abu ne Kuma ki saka basariya. “

“Tohm hajia sannu da kokari. Allah ya saka da alkhairi. Aamin Yaa Rabbi”

“Aameen Yaa Rabbi. Allah yasa ki fara a sa’a”

“Aameen”

Ficewa yayi daga kitchen din. Ya yinda malama Hindu ta sauke katuwar bahaguwar zuciya tana karewa kitchen din kallo. Harda TV tanata yi ga kujerar zama har biyu.

“Wannan ba zaka Kona girki ba kana kallo?” Ta tambayi kanta

Ashe mama Talatu ta shigo ta jita. Tayi dariya tana dubanta tace

“ba zaka Koma ba Hindu indai ka mayar da hankali. Koma kallon na debe kewa sai kiga duk daddawar da zakai a kitchen baka ganin dadewarr”

“Mashaa Allahu .. Allah yakara arziki Amin”

“Aameen Yaa Rabbi… Sunana na yanka Asma’u amma ana Kirana da Mama Talatu.”

“Mashaa Allahu sunana Hindu .kema anan garin kike?”

“Aa a daga kauyen kusa da Nan din nazo dai. Amman ni anan nake a zaune aikin kwana nake. Na Dade anan gidan”

“Mashaa Allahu. . Ni Kuma daga baya muka dawo Nan birnin Naduka. Da a bunza muke”

“Mashaa Allah ai kuwa kinyi kama da Mutanen bunza mashaa Allah tubarkallah “

Malama Hindu tayi murmushi… A nutse tace,

“Nagode .. Allah yasa mu fuskanci juna. Dan Allah duk abunda zanyi ba dai dai ba ki gyara mun nagode”

“Inshaa Allahu… Bakida damuwa. Matsalata daya dama reni abundna ke hadamu da indo kenan data tafi. Amman ke naga zubin kima na muminai ne don haka banjda matsala da ke inshaa Allahu.”

“Inshaa Allahu Zaki sameni me biyayya mama Talatu. Nagode kwarai”

“Allah ya bamu sa’a.”

“Aameen Yaa Rabbi…Mama Talatu idan ba takura zan iya samun abincin da kowannen su yafu so?”

“Wia ai tsurfar su Hayfa ce sai su wallahi. Kawai ki dafa abunda Zaki iya. Zasuci a hakan.  Wancen yace kayan fulawa wancen kayan ganye wancen Abu me yaji. Haka suke ki dafa duk abunda zai fi Miki guda daya zasu ci”

“Allah sarki bayin Allah… Nagode sosai mama Talatu”

“Ba damuwa… Nima bari natafi nawa kitchen din girkin gidah gaba daya na oga zan fara sai namu “

“Okay ba anan kike ba akwai wani kitchen din!”

“Eh akwai kitchen har uku ne ai. Nan abincin Yara ake ko Mai sauki da daddare haka. Wancen na barandar Kuma shine ake na gidah gaba daya da gayshe gayshe idan da yawa zaai. Sai abincin azumi Dana sallah Dana sadaka Kuma a kitchen din waje wajen gate anan akeyi”

“Mashaa Allahu komai dai a tsare to Allah ya jara dafa musu Amin”

“Aameen..”

Mama Talatu ta nufi nata kitchen din donyin girkin bangarenta. Yayinda malama Hindu ta zare hijabibta ta zura rigar girki da aka bata.

Ban da Nan ta shiga sarrafa girkunan da ta saka zatayi.

‘Tayi Naan bread da chicken wings sauce, Sai spaghetti mai veggies, da sauce na Hanta sai ta hada fruit salad da madara ta saka flovor ya bada wani hadadden kamshi da gardi. Ta Kai musu kan dinning duka ta ajiye ..

Nan da Nan ta gyara dukkanin abubuwa da ta bata. Ta shiga dakin da hajia qibdiyya ta nuna mata dazu. Tafkeken gado da setin sa da kayan sallaya da hijabi da Qur’an da Kuma bandaki aciki tsaftatattce.

Watsa ruwa ta yi ta kodauro alwala Dan anata kiraye kirayen sallar azahar dama. Tayi sallah tana zaune akan sallaya hajia qibdiyya ta kwankwasa ta shiga dakin tana sallama.

Malama Hindu ta amsa. Hajian ta zauna a bakin gado ,.

“Har kin gama? Sannu da kokari”

“Na kammala gidah ma zan tafi”

“Ah ki tsaha kici abinci “

” A mozge nake hajia”

“Ai ko ba Zaki ci ba sai kin tafi dashi kwanon ma zan saka maki kullum sau kin tafi abinci Allah. Dama na gayawa mama Talatu ta zuba Miki.”

“Nagode Allah saka da alkhairi”

“Aameen.”

Har bakin kofa ta rakata ta shiga mota direban ya mayar da ita har gidah tanata yaba karamci da dattako irin na hajia qibdiyya….

Hajiya qibdiyya na shirin komawa sama ta jiyo karar horn din ribadu driver yadakko su hayfa daga school sun dawo. Ta kallii agogo lallek lokaci i har yayi.

Komawa tayi kasan ta fasa hawa. Kamshin dake tasowa yasa tayi wajen wajen dinning ta fara bude warmers din…

Sukayi knocking ta saka basariya ta bude musu kofar. Hayfa ce ta fara shiga ciki ranta a matukar bace…….

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

19

Hajiya Qibdiyya ta juya tana duban kofar. Ganin yanayin Hayfa yasa ta kira sunanta,

“Meye haka kika shigo kina zunburo baki gaba, ba sallama?. koma ki sallama”

Komawa tayi baya ta shigo tana sallamar ta zube akan kujera tana mayar da numfarfashi.

Junior ma ya shiga bakin sa dauke da sallama ya saqala earpiece a kunnen sa.

“Waalykm Salam…. ” Hajia qibdiyya ta amsa sallamar ta su tana duban su tache,

“Ina Anees?”

“Yana baya Mami…. Woahh kamshin meye haka?”

“Oh abincin ku ne da aka dafa.”

“Ai kam nima naji kamshin mai dadi”

“Meye kika dawo da fari fuskar ki akumbure ke kuma”

“Ko ba Yaya junior bane Mami. Ya kwace lipgloss dina a school na Kylie dinnan”

“Ke meye na zuwa da lipgloss school saboda Allah Hayfa?”

“Tohm Mami ba ita kadai aka karbewa ba classes da yawa duk an kwace ai ba zanyi favoring nata ita daya ba ko?” Cewar junior.

“Eh hakane… Kuje ku zuba abincin. Anees!!” Ta wuce ta nufi wajen tana kiran sunan sa.

“Naam Mami….” Ya amsa ta ahankali yana shafa magen sa dake zagaye shi tana kuka.

Hajia qibdiyya tayi murmushi. Ashe dashi da magen sa ne.

“An bawa Vanessa abinci kuwa?” Ya fada kansa akan magen tasa dake ta zagaye shi tana’ meow meow’

“An bata dazu basariya ma na saka ta zuba mata an bata ruwa na. Madarar ta kuwa sai zubarwa akai aka wanke kwanon nata.”

“Okay” ya amsa mahaifiyar ta su yana mai mikewa tsaye daga tsugunnawar dayayi.

A tare suka shiga parlorn shi da ita bakin su dauke da sallama..

Hayfa ta zuba nyaan bread da miya. Junior ya debi spaghetti.

“Kamshin meye haka?”

“Abincin new cook dinmu ne. Mami macace ko namiji?”

“Macece sunanta Ummy …haka zaku dinga kiranta kuma bata dade da tafiya ba.”

“Mashaa Allah gaskia she’s a great cook. “

“Wallahi kam dan words aren’t enough to express how delicious abincin nan yayi Mami. Kai gaskia she’s talented. Duk alokaci daya tayi kaman tasan kowa da abun da yake so?” Cewar Hayfa.

“Wallahi kam . Don ni banma gaya mata abubuwan da kuke so ba. Amma bari na tambayi mama Talatu. Mama Talatu! Mama Talatu”

Mama Talatu tafito daga daki da sauri tache

“Naam hajia “

“Ni ke kika gayawa Hindu abincin da zata dafawa yaran nanne ?”

“Aa wallahi. Nasan dai ta tambaye ni me yaran ke so? Nace kawai ta dafa abunda zata iya. Don kusan kowannen su da abunda yake so. Ban kuma lissafa mata nace wancen da wane abu kaza suke so ba. Nasan dai nace mata akwai me son taliyah da kayan fulawa da kuma abinci marar nauyi ma akwai me so acikin su. Wani abun ne ya faru?”

“Kai amma gaskia an gayshe da Hindu. Wannan kokari haka? Kinga tayi Naan bread da sos din chicken wings tayi spaghetti da veggies shima da sos na hanta ga fruit salad da madara shima bakiji yadda ko’ina ya gauraye da kamshi ba wallahi”

“Ga kamshin nan kan da an shigo. Gaskia tayi kokari abubuwa da yawa haka cikin kankanin lokaci. “

“Mashaa Allah kam. Kin zubawa su basariya da kowa a kwanon sa?”

“Eh na zuzzuba musu na Alhaji ma na kai masa bangaren sa. “

“Yauwa sannu da kokari”

“Yauwa hajia bari na je idan shikenan”

“Eh shikenan mama Talatu.”

Anees ya ebo fruit salad sosai ya koma gefe yana sha. Sai lumshe idanu yake,

“Da dadi shima?” Hajia qibdiyya ta tambaye shi

“Beyond words”

“Mashaa Allah… Bari dai na zuba naci nima” ta fada tana mikewa tsaye

“Mami kar ki cinye mana please”

“Da yawa ai tayi gashinan. Ai daga yanzu har ni zata ringa dafawa zan yiwa girkin mama Talatu bankwana”

Suka kyalkyale da dariya baki daya banda anees da ya mayar da kansa kan TV dake nuna shirin labarai a tashar larabawa ta aljazeera….

“Auta ya school?”

“Alhamdulillah Mami …”

“Mashaa Allah..Allah ya temaka kaji.? Akwai abunda kake so yanzu?”

“Banason komai Mami. Thanks a lot”

“Allah ya maka albarka”

“Aameen Mami… Wa iyyakum”

“Mami school Alhamdulillah mu da baki tambaye mu ba” Cewar Hayfa

Junior yayi dariya yana girgiza kai kawai. Hajia qibdiyya itama murmushi tayi tace,

“Toh Hayfa ya school? Junior ya school?”

“Alhamdulillah Mami Amma Ina bukatar abubuwa gaskia”

“Kai Hayfa…” Cewar junior

“Yaya ai gaskia ne”

Mami dai bata ce ya school din ba sai ma dariya da tayi kawai tace,

“Idan Baban ku ya dawo ki same shi ki gaya masa.. Allah ya muku albarka Amin”

“Aamin Mami”

“Aameen duk da dai kinfi kaunar autan ki ..”

Mami tayi murmushi tana mikewa tsaye ta Isa wajen wanke hannu dake gaban dinning din ta tatsi hand washing mist ta wanke hannun nata.

Daya bayan daya kowanne ya tashi. Hayfa dakinta a sama yake . Yayinda dakin anees, daban dakin junior ma daban kowanne da parlorn sa da kayan kallo da saitin kujeru hakama dakunan su da kayan kallo ..

::::::::: ::::::::::

Sai da akayi sallar isha’i zungureriyar motar Dr. Abubakhr dollars ta kunno da kan hancin ta mai nishi gate din gidan ..

Oga emeka driver dinsa ne ke tuka babbar motar da alkalami yayi kadan wajen bayyana maku adadin kyawun ta da tsadar ta. Ta matukar haduwa fiye da yadda kalamai zasu bayyana muku ita.

Kalar ruwan bula ce mai turuwa amma turuwar sheki take bayarwa. Masu gadi da security suka taso kan motar duka suna yi masa sannu da zuwa.

Da sauri suka bude masa gidan gaba inda yake zaune ba abaya ba kamar yadda da yawan masu kudi kan zauna a owners corner. Shi din agaba yake zaune tare da direban sa dake tuqawa .

“Sannu da dawowa yallabai…. ” Cewar Mudi ya karbi brief case din hannun Dr.

Yayinda sauran ma suka shiga doka masa sannu da zuwa.

“Sannun ku dai…. Nagode kwarai. Ga wannan aje wajen nai tsiren can aci.” Ya mika musu kudi a dunkule yace su raba ya shiga ciki bayan ya karbi brief case dinsa

Sukayi ta doka masa addua suna masu shi masa albarka.

Sashen sa ya wuce… Wanda zaa iya shiga ta bangaren hajia qibdiyya ma.

Babban parlor ne mai matukar girma da dinning area. Sai dakuna manya guda biyu.

Komai da komai na rayuwar masu kudi an tana deshi abangaren sa kai harda abubuwa da yawa ma da wasu masu kudin basu samu iko ba..

Bandaki ya shige yayi wanka. Ya sauya kayan sa zuwa jallabiya. Yana fitowa ya iske matar sa hajia qibdiyya.

Itama taci ado cikin wata atamfa riga doguwa samfurin a shape. Cikinta ya dan tillo kadan ya kara mata kyau sosai.

Tayi daurin ture kaga tsiya. Wadataccen gashin kanta yazubo har kafadar ta.

Sai kamshin turaren kaya na kamfanin yerwa incense and more ne ke tashi a jikin ta. Ga na gidah data kunna a burner shi ma na kamfanin tiraren yerwa incense and more ko’ina sai tashin kamshi yake uwa uba ga na’urar ac dake sanyaya wajen .

Ya sauke idanun sa akanta…suka sakar wa juna wanj tsadaddan murmushi .. ba kadan ba tayi masa kyau kamar ko da yaushe cikin cin kwalliya take. Da yawa wasu matan idan suna da ciki zaka gansu da daurin zani kansu a taje ba kitso da leda ko gwangwani suna zubar da yawu aciki ..

Ita kuwa ko da yaushe tana kokarin zama tsaf tsaf cikin cin uban su ado juma. Duk kuwa da rabin zaman mai gidan nata a asibuti yake yi, Amma hakan be hanata gyara kanta ba

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

20

Ya karasa kusa da ita yana mai riko hannuwan ta cikin nasa, Yayinda kofofin hancin sa ke shakar ni’imantaccen khumrar kamfanin yerwa incense and more da ke tashi daga jikin ta…

Har ta kai sai da ya kai hancin sa gefen wuyan ta ya sinsina… Cikin kunnenta ya saka bakin sa ya shiga mata magana tamkar mai yi mata rad’a yace,

“Kinji kamshin da ke tashi daga jikin ki? Kayan ki? Kai dama baki dayan parlorn… Mariya tahhh kullum kuma da kalar kamshin da kike bayarwa .. wannan kamshin da me da me ye ne? Uhm?” Ya karasa fada yana sunbatar gefen kumatun ta…

“Sannun ka da dawowa mijina mai tarin albarka… Kuma dan aljanna inshaa allahu… hakika nasamu babban rabo a wannan rayuwar kasan meyasa?”

Dr. Abubakhr dollars ya girgiza mata kansa tamkar karamun yaro yana sake langaba kansa akan kafadarta…

“Saboda nasami miji tamkar amini, mai kula dani, mai sani farin ciki, yana kaudar mun da bakin ciki. Hakimin dake tare da ni yafi mun komai a wannan duniyar…. Ina kaunar ka doctor na.. Allah yabar mun kai”

“Hakika nayi dacen mata ta gari matar kwarai, Tamkar aminiya,Mai kula da ni, Mai yaye mun bakin ciki, tana sanyani cikin annushuwa, hakimar dake tare da ni tafi mun komai a wannan duniyar. Ina kaunar ki Mariyatah. Allah yabar mun ke..”

“Aameen Nawan… Har abada”

Ta matse shi sosai a jikinta. Yayinda shima ya riketa gam yana cigaba dashakar niimattacrn kamshin da ke futa daga jelar gashin ta…

“Kai Mariyatah sarkin tsafta sarkin ado, Kuma sarkin kamshi. Har gashin ki na kamshi yake kullum kuma kamshin ko’ina na jikin ki ya banbanta da na baya da kike sawa different scents”

“Zinare na kenan…. Kawai hadaddun hadin kayan turaren kanfamin yerwa incense and more ne… Kaga na turara jiki na, na saka khumrah na shafa mukammaria na shafa perfume oils dinta again na kuma turara kayan jikina sannan na fesa kabbasine spray na fesawa a kayan kafin a turara su, sannan kuma na fesa man gashin ta na fesawa mai kamshi na gashi dana shafawar sa., and na shafa kulaccam dinta ta oudi “

“Kai tubarkallah… Allah ya saka mata da alkhairi da take baki wannan dadadan kayan kamshi haka. Kinsan kullum naje asibuti harda patients na tambayana kamshi da nake? Saboda wannan turaren gadon da kike fesa mana a zanin gado dana labule dana mota dinnan dana drawer da kike sakawa . Wallahi kamshin ya zauna ajiki na. “

“Mashaa Allahu.. ai turaren su bana banza wallahi. Ga rike waje”..

“Gaskia.. cuz wannan da kika saka kiga sai yi yake yana futar da kamshin har yanzu” ya karasa fada yana nuni da burner …

“Haka kayanta suke .. worth buying wallahi. “

“Mashaa Allahu.. she’s blessed”

“Sosai ma….ga abincin ka a dinning muje kaci”

“Tam”

Mikewa tayi ta riko hannun sa ya bii bayanta tamkar rakumi da akala. Taja masa kujera ya zauna ta dauki plates tayi serving dinsa komai..

“Bismillah”

“Godia nake Mariyatah….”,

“Haa bude bakin”

Murmushi yayi ya bude bakin nasa ta debi abincin ta zura masa a baki ya karba yana taunawa,

“Nagode sosai”

“Anytime…”

Haka ta cigaba da feeding dinsa har ya koshi. Ta kira mana Talatu a intercom da basariya suka kwashe kwanukan bayan sun debi gaisuwa awajen Dr. Abubakhr dollars.

“Uhm ni na manta ma ban gaya maka ba. ” Ta fada tana janyo tray din data rage Naan bread din dazu tana ci da miyar

“Meya faru?” Ya tambaye ta cike da kulawa..

“Matar nan fa tazo ta fara aikin ta. Kaga sauri kuwa? Tayi Naan bread da sauce, spaghetti da veggies da creamy milky fruits salad. Mashaa Allah komai superb”

“Mashaa Allah haka akeso… “

“Wallahi bakaga ba yara nata santi fa. Kuma ba wanda ya gaya mata ga yadda zatayi. Ita tayi komai da kanta. And it turns out perfect “

“Gashi nan kam sai kamshin abincin ne ke tashi. “

“Sosai …. So ya aikin asibutin ya patients din naka da komai?”

“Alhamdulillah… Komai kalau fa. Sai ma wani abu mara dadi daya taso”

“SubhanAllah… Meya faru Kuma?” Ta tambaye shi a gigice

“Calm down ba wani abu bane thou. Amma dai ni ne ban aminta da shi ba”

“Ka lullube ni a cikin duhu …. Meya faru?” Ta sake tambaya da cike da kulawa.

Dai dai lokacin da yaran na su sukayi sallama suka shiga su biyu… Hayfa da junior…

Suka amsa musu sallamar. Hajia qibdiyya kanta na kan Dr abubakhr tana son jin menene matsalar,

“Kai ku koma magana muke”

“No su zauna ai ba wani abu bane ya kamata su sani….Ina Anees?”

Hayfa ta juya baya tana duban junior

“Dama bai taho ba?”

Junior ya girgiza kansa, Yana daga kafadar sa.

Wayar sa Dr abubakhr ya janyo ya Kira number Anees bugu uku ya dauka yace yazo bangaren sa yanzu yanzu

Ba jimawa kuwa sai gashi ya yi sallama ya shiga sanye cikin riga da wando na bacci ya sakala airpod a kunnen sa .

“Babaa barka da dare, Mami barka da dare”

“Barka kadai”

“Barkan mu…. Wato da ban Kira ka a waya ba anees ba zaka zo ba kenan? “

Anees ya saka hannun sa ya sosa keyar sa kansa a kasa yace,

“Ina assignment ne. Tuba nake”

“Well ya wuce… ALLAH yasa mu dace. Abunda Zan fada ba wani abun tashin hankalin bane awajen ku so Mariyatah please clam down. Ki duba condition dinki baa san damuwa please. Ba wani abu bane masarauta ce take ta bibiyata tun watanni biyu da suka wuce”

“SubhanAllah wane lefi kayi musu?”

“Dan Allah ki sawa kanki salaama. Ba wani abun tashin hankali bane. Dalilin daya saka naki karbar neman da suke mun ba komai bane fyace rashin son karbar mukamin da suke so su bani . Har ga Allah banaso. Amma yanzu abun yakai har gwamna ma ya nemi gani na naje mun gana yace sako daga mai martaba satin sama ba dagawa lalle na amince abani sarautar Talban Naduka wato hakimin waje”

“Mashaa Allah! Mashaa Allah! Wannan ai abune mai kyau labari ne mai madi. Allah yasa albarka”

“Congratulations baba”

“Allah shi tayaka riko baba”

“Mashaa Allah…” Cewar Anees.

Dr. Abubakhr dollars ya kada kansa ya dubi hajiya qibdiyya yace,

“Kina ganin na amince kema?”

“Mu cigaba da addua kuma kayi istikhara, Don neman zabin Allah idan alkhairi ne Allah zai amince a nada ka idan ba alkhairi aciki ba zaai ba inshaa Allah inason ka sakawa ranka haka kawai”

Ya sauke gwauron numfashi, Yana sake kada kansa yace,

“Toh shikenan Allah ya tabbatar da abunda yafi alkhairi Amin”

“Aameen ” suka amsa baki daya…

Haka dai suka cigaba da tattauna lamarin. Kafin yaran suyi musu sai da safe kowanne ya tafi daki don kwanciya kasancewar dare yaja.. Nan sukabar iyayen na su. Hajia qibdiyya na dada tausasar zuciyar mai gidan nata Dr. Abubakhr dollars….

NADUKA ZONE

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE.


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

‘K’J
(M/W/S)

✍️:MX

21

NADUKA ZONE

Malam Liti ya sauke Malama Hindu har kofar gidan su dake unguwar Naduka zone.

Ta bude kofar ta sauka tana yi masa godia,

“Nagode sosai”

“Yauwa sai da safe” Ya amsa ta yana mai juya kan motar…

Cikin gidah ta shiga bakin ta dauke da sallama ta zare hijabin ta ninke ta ajiye akan kujera tayi kitchen tanata sauri. Ta ajiye Kwanon akan kanta ta fara kokarin daukar food flask zata wanke taji shi da nauyi. Sai a sannan ta lura kwanukan baki daya an wanke su tas.

Ya yinda food flask din data daga taji nauyi ta bude murfin sa… Tururin shinkafa da wake ya daki fuskar sa ta karkade murfin gumin ya tsatstsafe sannan ta rufe

Ko a Ido sunyi washar washar. Ko data saka abun diba ta debi kadan ta saka a baki taji lugif kowanne ya dahu.

Ta taba bokitin ruwan wanka ma taji shi taf an cika shi da tafashasshen ruwan zafi.

Gaba daya dukkanin aiyukan da zatayi anyi. Ga awara nama tanata turiri an yayyanka.

Ta fito daga kitchen din tana dokawa Nawraah Kira,

“Nawraah.. Nawraah”

“Naam ummy..” ta sakko daga bene da sauri,

“Kin dawo?”

“Na dawo Nawraah. Waye yayi aiyukan nan.?” Ta tambayeta tana nuni da kofar kitchen da yatsa.

Dai dai lokacin da Ashfeef ya fito daga dakin su yana rufe bakinsa da tafun hannun sa sakamakon hammar data taho masa,

“Sannu da zuwa ummy”

“Sannun mu… “

“Hamma ne yayi ummy.. shi yayi komai nima nace zan taya shi wanke wanke yace aa yaji Ina mura na barshi”

“Yana Ina?” Malama Hindu ta tambaye su tana mayar da hawayen da keson ya tsiyayo daga idanun ta

“Yaje baya shanya”

“Shanyar me?”

“Kayan abbiey ya wanke da naki. Yace muma gobe zai daure nanu ni da Amnah…

Ai bata karasa sauraron Nawraah ba ta fice daga cikin gidan tayi baya inda suke wanki suke shanya a igiyar wankin da suka daura a bayan

Alokacin har ya kammala shanyar, Yana katse gumin da ke zuba daga goshin sa saboda ranar dake tsananin dukan goshin nasa.

“Hamma” ummy ta kira shi tana girgiza kai

“Ah ummy har kin dawo?”

“Na dawo …. Haba Hamma duk Kai kadai?” Ta fada tana kallon sa cike da tsananin tausayi. A duniya batasan me zata sakawa da babban dan nata ba. Hakika shi din babban jigo ne acikin rayuwar su baki daya.

“Wane aiki ummy? Dan dauraye kayan nannayi fa kawai. Sauran aikin bani nayi ba”

“Kai kayi mana… Ashfeef yanzu ya tashi daga bacci. Nawrah ta gaya mun duk Kai ne kayi komai kamar ko da yaushe. Aiyukan nan sun maka yawa Hamma ka dinga bawa kanka hutu dan Allah “

“Ummy idan banyi ba wa zeyi musu uhm?”

“Sai a rarraba aiyukan kowa yayi. Kuma ba zama zan dingayi ba acan inda na samu aikinn Ina gamawa zan dawo inshaa Allah . Kaji ko?”

“Tohm ummy”

“Allah ya maka albarka. Allah ya maka albarka. Allah ya maka albarka. Ya inganta rayuwar ka Allah ya daga ka ya buda ka ya sanya tarin alkhairi a dukkanin abunda ka saka a gaba kaji?”

“Aamin ummy… Jam’an inshaa Allahu”

Cikin gidah suka koma. Abincin data taho dashi tace yaci rabi ya bar wa yaran sauran yace aa yayi cokali biyu ya bar musu.

Ya tashi ya futa ya hada murhunan awara nan da nan ya hada komai. Ya koma kitchen ya dakko abubuwan da zasu bukata ya Kai wajen.

Ummy ta sauya kaya taje ta zauna suka fara tuyar atare. Nan da nan aka fara tururuwar layin awarar. Malam Liti ne a farko farko da food flask din hajia qibdiyya.

Ba yadda ummy batai ba ba zata karbu kudin awarar nan ba malam Liti yace hajia qibdiyya tache inde bata karba kudin awarar ba to ya barshi kar ya sayo mata. A dole ummyn ta zuba masa awarar ya tafi..

Bappah Junaid ya dawo daga wajen aiki a matukar gajiye. Ashir ya yi sauri ya karasa ya tare shi ya karbu jakar aikin sa ya shiga da ita cikin gidah yana doka masa sannu.

Ya kai masa ruwan wanka mai zafi bandakin sama. Sannan ya koma wajen awarar yana taya ummy . Yayinda ita Kuma ta tashi ta nufi wajen Mai gidan nata

Ya karasa wankan ta zuba masa abincin a plate tana bashi ya cinye ras Yana shi mata albarka.

Suka shiga hirar Ashir da irin kyautatawar da yake yi musu sosai sun dade suna shi masa albarka da sauran yaran na su baki daya

Alokacin ne Kuma bappah Junaid yake gayawa ummy ya kaiwa bappah Auwalu kudin nan daya ce masa shi ya bashi sai bappah Auwalun yaki karba kan shi lalle bashi yake so idan ba zai karbi bashi Wajen wani ba to ya barshi.

Dakyar bappah Junaid ya tausashi ran dan uwan nasa yace masa ba kudin sa bane bashi ya karbi masa dama da niyyar shi zai biya nasa idan ya samu kudin. Amman tunda baya so shikenan ya rike bashin sanda ya samu ya bayar.. Ya karkare mata da,

“Yanzu dai dama sheda nake nema… Kuma ga ki. Ko bayan rai na kudin nan dana baiwa Hamma Auwalu.. kyauta na bashi ba bashi ba. Dan Allah kada ku manta saboda halin mantuwa”

“Abbieyn su ai babu wanda yasan gawar fari. Ka dai na cewa haka ma. Sannan wannan batu tsakanin ka ne da dan uwan ka. Ni nasan nan gaba idan ka gaya masa ai kudin ka ne ka bashi kyauta ka tausashe shi zai amince ya bar batun bashi ne ala dole sai ya biya .. Amman yadda kache hakan zaai abbiey”

Bappah Junaid yayi murmushi yayinda ya saka hannun sa kan kumatun ta yana shafawa ahankali yace,

“Hindu na kenan …. Kyakkyawa Mai kyakkyawar zuciya, dabiah, nutsuwa, biyayya, hankali, tausayi, Kai komai kin hada hindu. Ubangiji Allah ya shi Miki albarka. Ya raya Miki yaran ki Amin”

“Aamin abbiey tare da Kai Allah ya raya mana su baki daya ya musu albarka..”

“Aameen…Ni kuwa ya gidan aikin naki?”

“Yauwa daman yanzu nake shirin cewa baka tambaye ni ya yau takasance da ni ba….”

“Maza.. Maza bani na sha…”

Malama Hindu ta gyara zama tana duban mai gidan nata cike da murmushi ta shiga labarta masa dukkanin abunda ya faru tundaga lokacin data shirya tayi wanka direba ya dauketa ya kaita gidan har ya zuwa sanda ya dawo da ita. Komai da komai sai data gaya masa.

Kuma bappa Junaid yaji dadi da irin karbar da tace sunyi mata. Ya Kuma sake aminta da aikinta agidan sosai. Yayi musu addua sosai hadi da fatan cigaba da samun nasarar rayuwa marar yankewa..

Sunata hira har awara ta kare yaran suka karasa gyara wajen komai da komai… Sun samu ciniki sosai mashaa Allahu..

::::::::

Farin ciki lullube a fuskar sa, yayinda hannuwan sa ke rike da ledar mai baki da yellow dake dauke da kudaden da kanin sa junaidu ya aro masa ya shiga gidan nasa bakinsa dauke da sallama. Ya yinda daya hannun na sa buredi ne ya saya da ganyen shayi da sukari ya tura kofar gidan nasa bakinsa dauke da sallama………..

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

22

::::

Tana kaame akan kujera ta harde kafafu tana kuma karkada su atare. Kanta a sama. Yayinda hannuwanta ke dunkule daya cikin daya. Kana kallon ta kasan tunani ne takeyi da alama kuma tayi nisa ainun a abunda takewa tunanin..

“Salamu alaikum…” Ya sake yin wata sallamar a karo na uku..

Girgiza kai yayi ya karasa shiga ciki ya daki hannun kujerar da take Kai. Ta girgiza da sauri cike da firgice. Ganin shine yasa ta ja dogon tsaki tana wulkita masa harara,

“Meye haka dan Allah?”

“Bansani ba. Sau nawa Ina sallama kinyi kunnen uwar shegu? Sai kache ba musulma ba wai ke ba zaki wa kanki fada ba ko Nusaiba?”

“Ah menayi? Ko kuwa Kai baka tunani? Akwai dan Adam din da baya tunani ne balle ni dake cikin matsatsi da kuncin rayuwa. A wannan tsurkun gidan mai cike da ban haushi? Har a tambaye ni tunanin me nakeyi? “

Dogon tsaki yaja yana girgiza kai ya dubeta cike da takaici yace,

“Zakaran ka dai rakumin ka Nusaiba. Ki dai na Kai kan ki inda Allah be Kai ki ba fa..”

“To kaji ka. Astagfirullah irinku ne masu janyowa mutum masifa yana zaman zamansa. Yanzun wani abun sab’on nache? Yo ai zama da Kai shine babban tashin hankali idan ba kasani ba yau ka sani”

Murmushi yayi Wanda yafi kuka ciwo Yana karkada hannu yace,

“Tun safe nake neman Abu daya.. tun safe ko karyawa banyi ba na futa nema. Tun safe ko iyali na bansaka su a Ido ba na futa garari nema, Amman kice mun haka Nusaiba? Wai ni yaushe Zaki hakalii ne? Kullum girma kike amman tamkar kina cin kasa”

Mikewa tayi ta saki guda hadi da daga hannu sama ta nana a cinyarta tace,

“Auwalu kenan.. inbanda matsalar gida data fara bada matsala idan baa gyaraba damuna zatai gyara shine kake tunanin tun safe ka fita nema? to namiji ai da nema aka san shi ba zama agidaah ba kamar mace. Mace ce akasanta agidah. Dole ne namiji ya fita ya nemo ya bata. Duk mazan kwarai haka suke idan ka tsame kan ka. Har ni zaka cewa yaushe zanyi hankali Auwalu? Ai babu mai hankali da zata zauna da Kai wallahi kaji rantsuwar Allah. Duk nace mai hankali ishasshe data san mutinci da daraja ta ya mace wallahi ba zata zauna dakai a matsayin matar ka ba. Domin kuwa ta gama tabewa. “

Mtsceww, Tsceww, Mtw… Ya saki tsaki har Kaso uku a jere. Ya dubeta cike da tsananin bacin rai yace,

“Duba kiga ni… Kaf birnn nan kadan ne inda ban zagaya ba Ina neman rance na kudi da zanyi wannan gyaran na rasa. Har sauran yan uwa na Kira a waya kowannen ya bani uzurin sa kan babu. Wanda dai banason gayawa din saboda kowane hali yake zaije ya nemo wallahi kafin nace ya samomin ma don munyi maganar gyaran amman bance inaso ya nemo mun ba wallahi sai gashi yazo da kansa dauke da kudin ya kawo mun fiye da adadin yadda nake bukatar ma. A duniya idan ban godewa junaidu ba wa zan godewa! Kaf Yan uwana babu Wanda keda zuciyar Yan uwantaka da dinbin zumunci irin junaidu..” ya karasa fada yana mai zama akan kujera hadi da dafe kansa da hannuwan sa biyu ya tallabe.

Leka ledar tayi idanuwanta suka sauka akan farare kal bugun Abuja .. Ta silale ta zauna a kusa da shi hadi da saka hannu ta janyo ledar sosai ta buda ta hango bandir din dubu dubu mash tarin yawa.

Jikinta har rawa yake ta dau bandir daya tana gwalalo idanun . Bappah Auwalu ya wafce kudin ya rike ledar a hannun sa yana kallon ta

Nusaiba akwai makirci nan da nan ta kwabe fuska ta rausayar da Kai tana jan kasan jelar gashin ta tace,

“Naga ranka ya baci akan maganganun dana fada . Kayi hakuri kuskuren harshe ne… Bazan sake ba”

Bappah Auwalu yayi murmushi kawai ya gano ta sarai. Amman saboda tsabar sonta ya rufe masa idanu kawai ya girgiza kai,

“Allah yása mu dace Amin”

“Aamin..yanzu yaushe zaai gyaran gidan”

“Ko gobe ma inshaa Allahu..”

“Auwal……” Ta Kira sunan sa irin yadda take Kiran sa tun suna saurayi da budurwa.

Yana jin sanda ta kira shi ya sake murmushi kawai, don Sam bata Kiran sa da haka sai idan ya samu kudi tanason ya bata wani abun. Don rabon data kira shi haka tsakani da Allah tun suna saurayi da budurwa da Kuma farkon satinnai na auren su

“Auwal magana nake maka”

“Auwalu nake Nusaiba “

“Nusaiba gatsal? Kai ma kadan saya mana… Nusyn Auwal… Ko ka manta wakar tamu ne da muna saurayi da yammata?”

Mikewa yayi zai tashi ta mike itama tana riko hannun sa

“Ka tsaya kaci abinci mana Ina zaka?”

“Wanka zanyi Nusaiba. Ki kyale ni”

“Aa bari adan kashe sanyin ruwan yanzu. Sai kayi kaci abinci kaji. Zauna mana”

Komawa yayi ya zauna Yana grigiza Kai. Nusaiba akwai ta da salo kala kala duk yadda yask yaki biye mata hakan yaci tura.

Don bayan da ta dafa ruwan yayi wanka. Ta zuba masa abinci yaci. Haka ta dinga jansa da hira har yaran su da ta aika siyo gawayi suka dawo. Su kansu Layla sunyi mamakin ganin iyayen nasu zaune suna hira.

Nan suka zauna suma anatayi da su. Yake gaya masu ya samu kudin da zaa gyara musu gidan sunata murna.

Har lokacin kwanciya bacci yayi Layla ta nufi daki ta kwanta. Nusaiba ta tasa bappah Auwalu suka tafi daki. Yayinda Ahmad ya dakko katifar sa ya saka a parlor ya makala net ya kwanta…

Duk yadda bappah Auwalu yaso zillewa haka ya hakura ya bada kai bori ya hau. Dole sai da Nusaiba tasaka ya saya mata waya da ake latsa ta wato torch screen ta yan gayu.

Sai wani yauki take tana rike da wayar duk inda zata.. Yan layin nasu kowa ya sheda tayi wayar masu kudi

Har gidan bappah Junaid ta shiga tanata fiili da wayar a hannunta. Lamarin ma daria ya bawa Malama Hindu. Don sarai tasan da kudin da aka bawa bappah Auwalu ne zata tursasa shi tasa ya saya mata wayar adole…

============

Toh haka rayuwar ta cigaba da kasancewa. Kowanne bangare ana samun cigaba musanman gidan bappah Junaid.

Su Nawrah sunyi sauka mashaa Allah. A Kuma shekarar ne su Bappah sani zuka ziyar ce su

Inda bappah sanin ya Kira meeting duka Yan uwan suka taru. Akayi magana kan matsayar karatun yara matan na boko.

Lalle burin Nawraah ya cika duk kuwa da makaranta ce ta gwamnati zaa saka su tayi murna kwarai matuka don har hawayen farin ciki tayi.

Dakyar aka shawo kan bappah Junaid daya ki amincewa kan wasiyyar yafendo ce yara mata kar suyi boko. Nan yan uwan nasa suka wayar masa dakan ba haka tace ba. Tace dai ga yaran nan kar dai amatsa Idan Kuma rayuwa ta sauya to sai abita da yadda tazo akuma yi addua…

Don a rayuwar da suka samu kansu Idan Yara matan basuyi bokon ba Koda kadanne to akwai natsaloli da zasu fuskanta masu tarin yawa musamman da yanzun sabuwar rayuwa ce suke ginata wadda suka shiga ta zama a birnin Naduka garin yan boko da wayewar kai….

Lamarin ya cigaba da tafiya yadda ya kamata Alhamdulillah lalle Allah qadirun ne ala manyashau.

Su Nawraah an fara zama yammata yanzu sosai cikar budirc ta fara bayyana atattar da su. Wani irin musulmin kyau ne ke kara haskakata.

Wanda wani lokacin saboda tsabar maza samari dake cewa ana sallama da ita gata da kananun shekaru hakan yàsa ummyn ke cewa ta dinga saka niqab idan zata futa.

Unguwa ma sai aka dena zuwa da ita ba kowacce ba. Don hajia qibdiyya ma tayi tayi taga yaran, ummy tace zasu zo mata In shaa Allahu nan da wani lokacin idan komai ya dai dai ta…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

23

DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING:

Bakın ta dauke da sallama ta shiga cikin gidan bayan Malam Liti direba ya sauke tah.

Ja tayi ta tsaya alokacin da basariya ta bude mata kofar parlorn ta shiga, Sakamakon manyan akwatinan data gani a parlorn an ajiye su.

“Hajiyan na sama ne?” Malama Hindu ta tambayi başarıya mai aiki

“Tana bangaren baba yanzu zata dawo amma ai tafiya zasu yi ma.”

“Ah tafiyar ta tabbata kenan? Mashaa Allah Allah yasa aje a sa’a. Kafin ta dawo bari na rage wani abun” kitchen ta shiga ta zare hijabin ta ta rataye shi a maratayi, ta dauki rigar girki ta zura ajikin ta.

Nan da nan ta shiga hada girkin su Hayfa, kasancewar yanzu ta gane kowannen su abincin da yafu so dan haka Kowanne tana dafa masa daga cikin cimar sa iyakar bakin kokarin ta. Kuma yaran suna yabawa sosai suna jin dadin girkin ta..

Tana çıkın aikin ne Hajia qibdiyya ta dawo sashen nata bakin ta dauke da sallama.

Malama Hindu ta fito daga kitchen tana goge hannunta da tissue kafin ta jefar acikin dustbin ta tsugunna tana gayshe da ita.

“Da Allah tashi Hindu. Nace ki dai na tsugunnawar nan Allah. Yaushe kikazo? Ina wajen baban su ne.”

“Ban jima can ainun ba dai. Eh haka başarıya tace mun da nazo ta bude mun kofa. Har na dubi akwatinan ma nace Allah sarki Hajia tafiyar ta tabbata kenan?”

“Wallahi kuwa Hindu. Tafiya ta tabbata inshaa Allah. Sai gobe da daddare ne amma jirgin mu zamu tashi yanzun dai nace akai akwatinan booth na mota kar mu wasu abubuwan manta”

“Hakane kam gaskia don tafiya tagaji haka. Toh Allah ya tabbatar da alkhairin sa yasa kuje a sa’a yasa ki sauka a sa’a Amin”

“Aameen Yaa Hayyu yaa Qayyum. Godia nake kwarai Hindu. Dan Allah Idan kin gama aikin ma zan aike ki gidan wata kawata ko ince yar uwata ma don mun zama yan uwa, matar aminin mijina ce. Malam liti zai kai ki please”

“Tohm Hajia bari na kammala. Yanzu”

“Yauwa eh zan baki daya wayata ma sai ki tafi da ita ki dakko samfarin kayan hotunan su. Kaya ne ta kawo zamu zuba a store . To wasu sunyi extras haka double shine zaku daddauka da kuma rubuto jerin samples “

“Toh Hajia amman dai daukar hotan ne dai da duk ma abunda za’a iya miki ta wayar wallahi ban iya ba kasancewar bana rike da babbar waya. Amman Idan ba damuwa sai mu biya na dau matar yayan mijina taşan kan waya Idan kuma Nawraah sun dawo daga makaranta ma sai muje da ita”

“Toh shikenan duk yadda kukai ba damuwa. Ai kuwa yakamata ace kin fara amfani da babbar waya Hindu. Daman wayar ba wani amfani nake da ita ba sosai saboda inada ipad da ita nake amfani. Inshaa Allah Idan kika dawo na kwashe komai na kai sai na bar miki. Ma dinga vedio call Idan na tafi inshaa Allah”

“Nagode Hajia, Nagode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya biya miki dukkanin bukatun ki na duniya da lahira Allah ya saukeki lafiya Allah kuma ya raya miki yaran ki ya iya miki ya daga ki amin.”

“Aameen Yaa rabbi Hindu. Jam’an inshaa Allahu”

“Bari na karasa girkin sai na zo”

“Tohm Hindu. Nima bari na cire rigar nan na saka marar nauyi….”

“Tohm Hajia”

Hajia qibdiyya ta haye sama dakin ta. Ya yinda Malama Hindu ta koma kitchen ta cigaba da girki.

Nan da nan kuwa cikin ikon Allah ta karasa duka girkunan abincinnan data yi na Junior da Hayfa da kuma Anees.

Ta jere musu kulolin abincin akan dinning ta dakko plates da serving spoons da fork da komai dai ta jera musu kowanne sannan ta shiga dakin hutawar su tayi wanka hade da dauro alwala ta mayar da kayanta. Sannan ta hau kan sallaya jin ana kiraya kirayen sallar azuhr ta yi sallah hadi da addu’oin ta..

Sannan ta mike ta gyara zaman hijabin ta ta fita… Ta nemi gefen carpet ta zauna tana jiran sakkowar hajia qibdiyya.

Bata jima sosai ba da zama hajiya qibdiyya ta sakko daga saman sanye cikin kaya marar nauyi.

“Hindu har kin kammala?”

“Na gama hajiya. Ya jikin?”

“Alhamdulillah Hindu”

“Zaa karbi sakon yanzu ne?”

“Eh, Amma kinci abinci ne? Kici abinci tukun ko?”

“A koshe nake hajia”

“Wane irin a koshe. Ki ce dai idan kika dawo zaki ci banason musu Hindu”

“Tohm hajia inshaa Allahu… Nagode Allah ya saka da alkhairi “

“Ba godia a tsakanin mu Hindu. Yauwa ga wayar na cire password”

“Tohm” ta saka hannu biyu ta karbi wayar tana riketa da kyau

“Wayar ki ce fa atoh ki kalleta da kyau”

Malama Hindu tayi murmushi tana jujjuya wayar a hannun ta. Hadaddiyar waya kallo daya zakai mata kasan me kyau ce da tsada kuma.. Samsung ce latest design.

“Nagode sosai hajia. Allah ya biya miki dukkanin bukatin Ki. Yadda kike faranta mana Allah ubangiji ya faranta Miki. Ya sauke ki lafiya Amin”

“Aameen Yaa Rabbi Hindu”

‘B’it pi’pi’ pit B’it’ Malam Liti ya nata danna horn ta motar.

Malama Hindu ta fita da sauri tana rufe kofar parlorn ta shiga motar da sauri malam Liti yaja suka futa daga gidan,

“Mu biya ta gidah zamu dau Nawraah da zata dakko hotunan sakon da hajia ta ce”

“Okay tohm”

Naduka zone ya nufa da motar tasu. har kofar gidan su malama Hindu ya sauke ta.

Ta shiga da sauri tana kiran Nawraah. Nawraah da bata jima da dawowa daga makaranta ba tana zaune a parlorn su tana karanta wani littafi na ‘computer science’

“Naam ummy”

“Ina Amnah?”

“Sun fita da Hamma”

“Okay! Maza shirya ki mun rakiya zaki dakko wa hajia qibdiyya wasu hotuna. Da wayar nan rike ta ma tace ba password.”

Nawraah ta karbi wayar tana zura hijabi,

“Tohm ummy “

A tare suka fito daga cikin gidah sukayi kicibus da Nusaiba tana tafe tana yamutsa da wayarta a hannu. Suka tsaya suna gaysawa tana daga wayar hannun ta ummy dai tayi murmushi kawai…

“Fita zakuyi a motar can?” Nusaiba ta tambaye su tana kallo motar da malam Liti ke tukawa hadaddiya sai sheki takeyi.

“Eh futa zamuyi “

“Ungo Nawraah dan dauke ni anan wajen motar haka ki tabbatar ta fito”

Nusaiba ta karasa fada tana gyara tsayuwar ta ajikin motar.

Nawraah ta karbi wayar ta yiyyi mata hotunan. Ta mika mata. Nusaiba ta karba tana duba hotunan tana murmushi.

Suka bude motar suka shiga ciki ita Kuma ta koma cikin gidah tana sake zooming hotunan tana murmushi musanman da motar ta dache da ita kamar ta ta..

Ta daga Kai ta dubi gidan su ranta ya sosu sam bata kaunar zaman ta agidan dan tafi son gidan nasu kudi inama ace ita mayar mai kudi ce, ta fantama inda take so acikin shiga ta alfarma da hawa manyan luntsuma luntsuman motoci da masu aiki suna take mata gaba da bayan ta…

“Nusaiba Ina kokon?” Ta jiyo muryar Auwalu ta doki dodon kunnen ta
.
Ta yamutsa fuska tamkar yana ganin ta cike da kufulewa tace,

“Dan Allah ni kakka ishe ni. Koko! Koko! Koko sai kace a karkara” ta tabe baki ta shiga cikin gidan…

:::::

Babu nisa ainun suka karasa unguwar da gidan aminiyar ta hajia qibdiyya. Dankareren sign board ne an rubuta da manyan baki…

ALHAJI SAMBASO AVENUE

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

‘K’J
(M/W/S)

✍️:MX

24

:::::::::

ALHAJI SAMBASO AVENUE

*Wani * tafkeken gidah suka nufi gate din sa.. Manyan masu gadi majiya karfi a mummurde su biyu ne suka taso sukayi kan motar da malam Liti ke tukawa ganin ya tunkari gate din..

Ja yayi ya tsaya da motar. Masu gadin suka leka suka saka ya bude har booth dinsa tukun sannan dayan ya janyo wata aba kamar rediyo baka ya koma gefe Yana magana. Can ya dagawa dayan me gadin hannu ya koma ya zauna

“Ku shiga” Ya fadawa malam Liti Yana rufe masa murfin booth.

Malam Liti yaja motar Yana zakin siririn tsaki yace,

“Na tsami zuwa gidan nan yadda kikasan gidan gwamna wallahi tsare tsaren su yayi yawa. Sun san nafi shekara nawa ko muzo da hajia ko ta aiko ni ni kadai amman masu gadin nan sai sun tsayar dani…”

“Kayi hakuri. Inaga yanayin aikin nasu ne yazo da tsauri haka” malama Hindu tace da shi

“Allah ya kyauta kawai. Abun nasu ne yayi yawa kam”

“Ayyah”

Ita dai nawrah na zaune tana raba idanu. Ta saba ganin hadaddun gidaje a dramas da labari idan ana basu. Amman bata taba ganin gidah me kyawun wannan ba..

“Allahumma arzuqniy” ta fada tana sake duban gidan alokacin da suka shiga harabar gidan da mota

Malam Liti ya nemi wajen parking ya faka motar. malama . Hindu suka fita da ga ciki ta riko hannun Nawraah dake kalle kallen gidan.

Murmushi malama Hindu tayi tace,

“Ai gidan hajia qibdiyya yafu wannan kyau fa? Su gate dinsu da kansa ma yake budewa Nawraah”

“Mashaa Allahu sunji dadin su”

“Mashaa Allah! Kuma Allah ya Kai ku inda zakuje ku huta sa kwanciyar hankali Amin”

“Toh Aaameen.. Amma ummy samun irin wannan gidan kan nasan ko a mafarki”

“Yi sauri kitchen astagfirullah. Waye me azurtawa?”

“Astagfirullah Allah ne”

“Waye me talautawa?

“Allah ne”

“Waye me bayarwa”

“Allah ne”

“Waye mai rayawa”

“Allah ne”

“Waye me kashewa? Ya bayar asan da yaso ya hana asanda yaso”

“Allah ne”

“To ki yi maza ki roki gafarar Allah mumini baya yanke rai ga rahamar ubangijin sa. Allahn daya basu bai manta da mu ba kina ji na?”

“Astagfirullah… Eh Ina jin ki ummy “

“Shysa a har kullum ake son ka kalki na kasa da Kai kada ka kallo na sama da kai lalle idan ka kalla na kasa da Kai Wanda ka fishi komai tanan zaka Kara godewa Allah da rahamar da yayi maka. Nawraah wasu suna nan basu da matsugunin da zasu zauna Ina nufin gidah.. wasu basu da abincin da zasuci bara suke. Nawraah wasu suna nan kayan da zasu saka ma basu da shi sutura tayi karanci Nawraah. Wasu Kuma suna asibuti ma sai dai a kwantar a tayar basusan Wanda ke kan su ba. Wasu ma hankali ne basu da shi a zare suke suna kwana a bola. Nawraah lafiya kadai ma idan Allah ya barka da ita wallahi babban arziki ne. … Ki kasance cikin hamdala ga mahaliccin ki shi Kuma zai ninka maki bukatin ki inshaa Allah”

“Inshaa Allahu ummy”

“Yauwa Nawraah,,, mace ce ke sai kiga Allah ya daga ki ya Kai ki gidan wani hadadde Wanda baki taba zaton samu ba Allah ne kadai yabar wa kansa sanin wayasan gobe. Kuma inshaa Allah khair”

“Hakane ummy.. nagode sosai da tunatarwa”

Suna tsaye a bakin kofar tun da suka danna door bell dai baa bude musu ba sai da Nawraah ta sake saka hannu ta danna madannin tukun sannan bayan yan mintina wata matashiyar budurwa kamar Nawraah tazo ta bude musu kofar

Ta sakala earpiece a kunnenta kana jiyo karar sautin wakar da take ji.. Sanye cikin kananun Kaya riga da wando kanta ba dankwalii ta yi parking gashin nata.

Wani hadadden babban parlor ne mai girma sosai yana dauke da saitin kujeru har biyu . Yayi matukar kyau parlorn kudi yayi aiki agidan domin komai Mai tsada ne sosai.

Yarinyar data bude musu kofar wadda kallo daya zakai mata kàsan yar gidan ce dubada wani zama da tayi akan doguwar kujera ta cigaba da karkada kafa tana bun wakar da take sauraron ta earpiece.

Can sai ga wata mata fara irin fararen ne don yarinyar ma data bude irin farar nance haka. Sunada kyau ba lefi . Irin buzayen nanne yan nijar

Matar ta dashare baki tana duban su tace,

“Dan Allah ku zauna… Malama Hindu ko?”

“Eh ni ce ce. Barka da rana mun same ku kalau?”

“Alhamdulillah…”

“Ina wuni?”
Nawrah ta gayshe ta

“Lafiya kalau yammata”

“Uhm lily kawo musu ruwa please”

“Mommy ni fa ba Mai aiki bace. In kawo musu ruwa Ina Dela take takawo musu mana?”

“What nonsense coman get up. Ki dakko harda lemo ki kawo”..

“Wallahi a koshe ma muke hajiya”

“To kinji sun koshi ma” yarinyar data kira da lily ta fada. Hadi da komawa ta gyara zamanta tana harde kafafun

“Bari a kawo kayan. Ah ai dole kusha ruwa malama Hindu…takanas daga gidan kawata ai dole a karramaka . Sunana Dr. Bintu… Ke dama nasan naki hajia qibdiyya ta fada wannan ce bansan sunan taba. Yar ki ce?”

“Eh yata ce… Nawraah”

“Mashaa Allah… Sunan Mai Dadi Mai kyau kamar jta tubarkallah. Ga yata can Ilham muna ce mata Lily . Sai babban ‘dana Marwaan… Lily zo ga kawa na Miki”

Lily ta juya ta dube su duka a shekeke ta tabe baki tana girgiza kai,

“Not my type…. “

Dr. Bintu ta mike ta shiga wani daki tana kwada sunan,

“Dela.. Dela”

Da alama Mai aikinta ce don da sauri ta futo daga kitchen,

“Naam hajia”

“Zo ki fito da kayan nan duka please ..”

“Tohm hajia yanzu kuwa”

Suna dai zaune suna kallon sarautar Allah dela ta fito da wasu manyan buhubuna dauke da kaya kaka kala.

“Kunzo da wayar ki? Ku fara dauka*

“Eh. Nawraah daukar mata”

Nawraah ta mike tana daga kayan daya bayan daya tana daukar hotunan su wasu budiyoyin su take yi.

Dela aiki ya kachame mata tamkar zatai hauka tazo tana cewa Dr bintu tuwo yayi ruwa gashi ko miyar bata hada komai ba.

Malama Hindu dake jin su tace,

“Bari na zo na kama Miki ko miyar ce”

“Kai harda wahala ayi haka?”

“Bakomai hajiya”

Malama Hindu ta futa tabu bayan dela suka je kitchen din. Nan da nan dama miyar kuka ce.

Malama hindu ta hada komai da zata tanada gata da saurin aiki ta fara hada miyar nan.

Baa dau wani lokaci Mai tsawo ba kitchen din ya fara tashin kamshin Miya. Nan da Nan ta gama ta ta zuba a food flask ta dauraye hannun ta ta koma inda Nawraah ke daukar hoto da bidiyo din . Suka kammala daukar

Yayinda suka lissafa Hadi da irga kayayyakin da suka haura guda biyu iri daya suka rarraba su Kashi biyu. Kowanne nawrah ta rubuta ta wayar ta ajiye.

Suna gamawa sukai mata sallama zasu tafi.. Ta bawa Malama hindu dubu biyar ta Kuma bawa Nawraah riga da skirt na cikin kayan sabbu.

Suka mata godia suka tafi. A mota malama hindu ta curo dubu daya tabawa malam Liti Dakyar ya karba yana shi mata albarka.

Nawraah ta saka aka sauketa agidan su Kuma suka wuce. Malama Hindu ta kaiwa hajia qibdiyya wayar ta Kuma nuna mata alkhairin kayan da Dr bintu ta baiwa Nawraah. Da ita kanta data Bata dubu biyar ta nuna nata ta Kuma karin tabawa malam Liti dubu daya.

Tayita yiwa hajia qibdiyya godia. Dakyar ta tsaya taci abinci aka Kuma zuba mata wani a kwanon ta.

Hajia qibdiyya ta dauki wayar bayan ta kwashe komai ta hada da chajar ta mikawa malama Hindu Wanda saboda tsabar farin ciki har kukan dadi ta saki…

:::;

Washegari malama Hindu dataje yiwa hajia qibdiyya sallama Nan take sheda mata ai Dr bintu ta kira waya tanata yaba mutinci da iya girkin malama Hindu ta kuma roki alfarmar tunda futa qibdiyya zata tafi haihuwa waje yaranta biyu Kuma zasu yi jamia. Zatayi hutu acan sosai Kafin ta dawo tana rokon Dan Allah malama Hindu ta rika zuwa tana mata abinci saboda Mai gidan ta ya yaba kwarai da miyar da tayi yanata santi..

Dakyar malama Hindu ta amince dubada yadda hajia qibdiyya keta rokon ta…

Nan sukayi sallama da su har yaran na ta da zaa Kai makaranta, junior da Hayfa. Yayinda anees Kuma zaiyi hutu tare da hajia qibdiyya zasu huta idan ta haihu har zuwa wani dan lokaci Kafin su dawo.

Har hawaye malama Hindu da hajia qibdiyya sukayi saboda tsananin sabon da sukai da juna, malama Hindu tana katse hawayen ta tace,

“Nagode hajia .. da dukkanin tarin alkhairin ki gare ni Allah ubangiji ya saka Miki da mafificin alkhairin sa ya bude Miki kofofin albarkar sa. Ya raya Miki zuri’ah ya shriya su tundaga kuruciyar su har gidan su. Allah Kuma ya sauke ki lafiya Amin. Dan Allah idan na Miki wani lefi Wanda nasan da Wanda bansani ba dan Allah ki yafe mun.Allah ya KADDARA saduwar mu ya hada fuskokin mu da alkhairi Amin”

“Ni ce da godia Hindu Allah ya daga Miki yaran ki duk kuwa da kin mun rowar ganin su Kuma bakimin lefi ko daya ba Hindu. Sai ma ni da nasan tabbas na Miki Dan Allah ki yafe mun”

“Ku gafarce ni hajia.abubuwan ne sai ahankali, Amma inshaa Allahu har sai kin gaji da ganin su ma. Ni ke Zaki aurar da su ma. Saboda ki yafemun “

“Inshaa Allahu Hindu. Allah ya yafe mana gaba daya”

Hajia qibdiyya ta rungume Hindu jikinta sukai sallama suna daga mata hannu suka shiga mota direba oga emaka yaja suka tafi.

Yayinda ita Kuma ta shiga motar malam Liti ya sauketa agidah.

Satin ta daya agida Kafin daga bisani Dr bintu ta fara Aiko direban ta yana daukar malama Hindu tana zuwa tana abinci Yana dawo da ita…

Da wannan suka cigaba da rayuwar su.sabo sosai ya shiga tsakanin malama Hindu da Dr bintu. Itaxe yiwa mijin Dr bintu abinci Kuma ya aminta da abincin sosai yana masa Dadi don har kyautar kudi yake bayarwa ayiwa malama Hindu

Wanii lokaci takan tafi da Nawraah don ta tayata wasu aiyukan na gidan aikin nata…

Ranar wata asabar da yammaci…..

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

25

:::::::::

Ranar wata asabar da yammaci… Malama Hindu nata sauri kasancewar Dr. Bintu tace mata kada tazo da safe ta bari da yamma tazo tayiwa mai gidan nata girki zai ci da daddare ba zai samu cin na ranar ba saboda wani meeting da yake da shi,

Don haka malama Hindu ta karasa aiyukan da zatayi a gaggauce.. Ta zura hijabin ta tanata sauri ta sauka kasa.

Duk yaran suna nan har da Layla yar gidan Bappah Auwalu tana zaune a kan kujera mai cin mutum biyu tana yiwa Amnah kalaba kanana a kanta.

“Ummy tafiyar za ki yi yanzu ji rani.?”

“Eh Nawraah kilama na so na makara.”

“Bari na saka hijabi na nazo”

“Ai Nawrah baki gaji ba? Da kin zauna yau”

“Aa zanje”

“Tohm.shikenan shiryo da sauri”

Malama Hindu ta karasa fada tana zama akan hannun kujera ta dubi Ashir tache,

“Hamma dan Allah idan abbiey dinku ya dawo ga abincin cin sa nan a food flask na saka a kasan kantar kitchen. Idan yanason shayi kuma akwai ganyan shayi acikin kwanon nan na kan freezer.”

“Tohm ummy inshaa Allah.”

“Allah ya muku albarka baki daya… Ashfeef naga ka wanke takalman ball dinnan dan Allah dai karkayi dare kar ka dinga dare ma dai kaji ko?”

“Ummy kwana zaki acan ne?” Ashfeef ya fada Yana kallonta Jin tamkar kwana zatayi tana bashi sallahu

“Aa inshaa Allah komai dare da zan Kai a gidah zan kwana… “

“Tohm Allah yasa”

“Amnah banda wasan ruwa kinji? Kinga mura kike yi”

“Tohm ummy”

“Zo nan”Ta fada tana duban ta

Amnah ta mike daga kalbar da ake mata daman saura daya. Ta karasa wajen ummy . Ummyn ta rungumeta tsam a jikin tana shafa gadon bayan ta

“Allah ya miki albarka Amnah. Allah ya raya ku ya tsare kuruciyar ku har girma Aameen”

“Aaameen.. “suka amsa ta baki daya

“Layla bappah Auwalu Yana nan ne?”

“Eh Yana gidah”

“Okay. Idan nawrah tafito kuce ta sameni agidan Bappah Auwalu.”

“Tohm ummy,”

Fita tayi da sauri ta nufi gidan Bappah Auwalu… Ta kwankwasa kofar nusaiba ta bude tana mita ta dauka Layla ce,

“Dan uban ki kinje kin zauna. Marar zuciya kawai. Kullum bini bini kina hanyarr gidan su dan uban ki. Uwar taurin Kai”

“Kai Nusaiba…. ” Ummy ta fada tana girgiza kai ta Kara da cewa,

“Assalamu alaikum ga bakuwar yammaci”

“Waalykm Salam Hindu ce Ashe. Na dauka Layla ce”

“Uwar Layla ce wannan. Kai Nusaiba kiyi waa kanki fada dan Allah ki dinga shan ragowar ruwan alwala ance Yana saka hakuri ya tausasa zuciya”

“Fada mata dai Hindu.”

“Ah Bappahn su ashe kana ciki,? Barka da yammaci?”

“Barkan mu dai. Ina ciki . Duk Ina jiyo ku Ina jin maganganun da take yi ai kinsan mai hali baya fasa halin sa” ya fada yana hararo nusaiba.

Ta gatsina fuska tana juya baya tace,

“Maganar gaskia ce ai. Layla kaman taci kafar kare saboda yawo,kullum tana gidan su haba ai da gajiya “

“Gajiyar me Nusaiba? Kada ki manta da nan da can din duk tsatso daya ne. Ko yau Layla ta tattara kayan ta ta koma can wallahi gidan su ne, Haka zalika idan Nawrah ta dawo nan ma gidan su ne, Nusaiba ke fa uwa ce. Maganar dama da nazo miki kenan nace miki ke uwa ce. Ta iya yiwuwa agaba ke zaki zama mahaifiyar su gaba daya ke zaki aurar da su. Ba wai sai bayan rai na ba ko a yanzu. Yanzu ace idan rai yayi halin sa Nusaiba ke ce mafi kusantakar zama uwa agare su wadda zata share musu hawayen maraicin su Nusaiba.”

“Haba Hindu maganganun me ne haka kikeyi? Ai babu Wanda yasan gawar fari sai Allah. Kuma ‘yayan ki ko taki ko ta so ‘yayanta ne. Haka zalika nata ‘yayan naki ne”

“Kwarai dagaske baooan su. Don ni anawa rashin hankalin wallahi gani nake ko ba rai na ba zasuyi kukan maraici ba saboda Ina da ku”..

“Bar ma wannan zancen ta iya yiwuwa ma duk mu mutu mu bari ki. Yaran namu ma ke zaki cigaba da renon su . “

“Sai dai idan kai ne zaka mutu ka barta Allah . Inshaa Allah sai na zama mai uban kudi na tara dukiya na zagaye kasashen duniya , na taka nera na bada dollar na lika yan dubu dubu da kyautar motoci sai na zama babbar attajira tukui” Cewar nusaiba tana murmushi da girgiza kafa

“Toh Allah ya kyauta…” Bappah Auwalu ya fada

Malama Hindu tayi murmushi ta mike tsaya jiyo muryar nawrah tana cewa ,

“Ummy na gama ki fito mu tafi”

“Bari muje bappan su. Dama gidan aiki nazan leka. Allah ya kaddara saduwar mu”

“To masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya”

Sa kayi ta fita. Nusaiba taja dogon tsaki tana bankawa kofar da malama Hindu tabi ta futa da harara. Ta mike tamkar jirgin sama kamar zata tashi sama ta shige dakinta tana rufo kofar da karfi ji kake ‘kauuuu’

Malama Hindu ta fita suka jera sika nufi titi kasancewar direban da zai dauketa ma ba zai samu damar zuwa ba. Don haka titi suka fita ta saka sika tsaya awajen aikin kai gidan nata wato bappah junaidu.

Nawrah na daga can gefe ta basu waje tana wasa da kasan hijabin ta.

“Hindu na….”

“Naam junaidu na….. Ya aikin naku ?”

“Alhamdulillah… Ai na gaya miki mai gidan dakike aikin ogan namu sun shiga meeting dazu ai yace mu taya shi da addua wasu manyan kadarori yake so ya mallaka inde ya samu dama zai mana manyan kyauta sosai . Kinga sai mu sake gyara gidan nan sosai”

“Oh shi ya saka mai dakin sa tace ya shiga meeting kar nazo da safe sai dai da yamma kenan. Allah sarki to Allah ya amince. Amma abbiyen su ai gidan mu babu abunda ya same shi kasa ka wani damu kanka Allah “

“Shagon awara nake son na bude miki daga gefen baya dinnan zaa tada shago a dingah sayar da awarar da sauran abubuwa.”

” Allah sarki junaidu. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Hakika bani da bakin godia agare ka. Ka a sani har kullum ba zan taba dai na godewa Allah da kasancewa mata agare ka ba. Allah yabar mun Kai har gaban abadan abbiyen su. Allah ya hada fuskokin mu da alkhairi yasa ko a aljanna mu kasance atare da juna. Nagode kwarai… “

“Wadannan kalaman fa Hindu? Sai kace wadda zatayi tafiya. Toh Allahumma Aminn ai komai na miki ban fadi ba Hindu. Domin duk inda matar kwarai ta Kai kin Kai kin zarce ma”

Murmushi tayi ta dan kallo gefen Nawraah taga ta juya baya tana danna wayar ummyn dake hannun ta yayinda ba maaikaci ko daya awajen. Ta rungume da shi da sauri ta sake shi tana goge hawayen dake neman zubo mata,

“SubhanAllah kukan meye wannan,?”

“Kuma dadi ne.. kukan farin ciki ne, kuka ne mai dauke da tarin ma’anoni. Kasancewa ta mata agare ka. Kasancewar uwa ga yarana. Kasancewar suruka ga su bappah Auwalu. Abubuwa da yawa. Nagodewa Allah da samun zuri’a ta gari wato hamidniyya Lebanon. Allah ya biyaka da aljanna Junaid .. Allah kuma ya cigaba da bude maka kofofin alkhairi ka cigaba da kula da yaran mu. Gasunan amana ne Allah yabamu. Kaga nj dai bana nan yanzu aiki zan tafi. Ka Kula da su don Allah..”

“inshaa Allah Hindu… Wannan kalamai haka? Yanzu zan koma karki ji komai Allah. Nasan dama saboda su kiketa maganganun akai kwantar da hankalin ki kinji?”

“Inshaa Allah. Abincin ka Yana can na bawa Hamma sallahu. Bari mu tafi kar lokaci ya kure”

“Sai kun dawo Allah ya bada sa’a ya miki albarka “

“Aameen abbieyn su . Komai dare ai inshaa Allah gidah zamu dawo”

“Tohm Allah ya amince Hindu”

Daga masa hannu tayi shima yana daga musu suka nufi tasi suka shiga ta Kai su can unguwar ta su Dr bintu

Gidan sika shiga bakunan su dauke da sallama suka gayshe da ita tana parlor itada mai gidan nata

Kitchen suka zarce nan da nan ummy ta fara hada abubuwan abincin da zata dafa yayinda nawrah ke tayata.

A haka har suka kammala komai. Ummy da nawrah suka nufi parlorn suka jera komai akan dinning

Dr bintu da Alhaji Sambaso mijinta sunata magana a parlorn dauke da wasu takardu agaban su…

Ya yinda tashar talabijin ke nuna wakar Maher Zain ta rahamatun lil alamin

Nawrah na son wakar don haka ta danna recording ta ajiye wayar daga can gefe don ta tariyo mata muryar Maher Zain da ke raira baitin

Waya Alhaji Sambaso ya daga ya gama amsa kiran ya saki Kara da karfi Yana jijjiga Dr bintu yace,

“Alhaji ateeks ya amince…. Plazas dinnan din sun zama mallaki na. Harda estates din mejesa da guzare dana Gpo da na bayan Maduki., shikenan nayiwa Dr abubakhr warwas matsiyaci duk tarin arzikin sa da sannu sai sun zama mallaki na…”

“Alhamdulillah…. Dama naki jinin munafukar matar sa sai uban izza da iyayi. Allah yasa su mutu acan duka kowa ya h…

Ji kake taratsats malama Hindu dake tafiya tana jinsu zata ajiye tray din jikinta sai rawa yake jin maganganun da suke kafafunta suka fara rawa tray din ya kufce daga hannuwanta ya fadi..

A matukar razane suka jiyo gaba dayan su suna kallon ta. Duk sai suka sha jinin jikin su,

“Me kike anan Hindu?” Dr bintu ta fada da karfi

“Ba abunda naji Dr.. Dan Allah kuyi hakuri santsi ne ya kwashe ni”

“Bangane ba abinda kikaji ba me kike nufi.?”

Nawrah na daga kitchen tana jiyo su ta fito da sauri ta janyo wayar ta,

“Menene wannan din me kike da waya?”

“Wayar ummy ce na ajiye” ta fada tana futa daga wajen recording din”

“Hajia sai da safe” malama Hindu ta fada tana kamo hannun nawrah

Dr bintu ta juya ta kalli mai gidan nata. Ya saka yatsa a hannu yana ciza shi.

“Hindu… Hindu?”

“Naam hajia dare yayi tafiya zamuyi”

“Ai baki gama ba, dama mana kunu” ta fada tana nuna mata kitchen

Jikin malama Hindu ya cigaba da kakkarwa tana yarfe yatsa tace

“Dan Allah hajia”

“Banason musu jeki dama mana kunu nace”

“Toh”

Komawa tayi kitchen ta janyo hannun nawrah jikinta na rawa suka futa tsakar gidan ta zaro nera dari ta mika mata,

“Maza maza tafi gidah”

“Ummy meyasa?”

“Ni dai nace miki ki tafi gidah ko? Tafi da wayar tawa ma “

“Idan aka kira ki fa”

“Baa wanda zai kira ma jeki yi sauri karki juyo ki, tafi gidah ki wuce kar ki dawo. Ki kashe wayar ma me kikayj awayar ne”

“Recording wakar Maher Zain nayi”

“Lokacin duk suna wadannan maganganun?”

“Eh bansani ba ni dai tun dazu na ajiye ta”

“SubhanAllah to tafi gidah dai ki kashe wayar idan kinje gidah ki bawa Hamman ku ya ajjye idan na dawo zan karba “

“Kai ummy?”

“Nawrah nace ki tafi ko?”

“Tohm shikenan. Ga tawa ki rike” ta mika naga wayar me torchlight ta ummyn ta da da ta bar mata ,

Ummyn ta girgiza kai tana kakaro murmushi tace,

“Ai dole sai kin saka na karba Kai nawrah dadi na dake KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA… Je ki Allah ya miki albarka…”

Ummyn ta karba tana cusa ta a jakarta ta hannu … Tana kambama jarumta irin ta Nawrah tun tana karama. Lalle idan ta girma za’ai mace mai kamar maza….

Nawrah ta futa daga gidan taje titi ta hau mota ta koma gidah. Yayinda malama Hindu ta koma cikin kitchen din duk abunda da suke ashe Dr bintu na hango su… Ba dai ta jiyo maganganun da suke..

Jikin malama Hindu na rawa ta shiga aikin data sakata ta dama kunun tazuba a flask

“Hajia na karasa”

“Hindu”

“Naam”

“I don’t care da rantse rantsen da kike Amma Allah idan naji magana daya ta fita wallahi sai kinyi mamaki”

“Wace magana hajia nace ba abunda naji”

“Ni dai na gaya miki”

“Inshaa Allah hajia. Ni ba zamma Kara aikatau ba wallahi daga yau da yardar Allah, na tuba dan Allah kiyi hakuri ki gafarce ni” ta durkusa kasa tana hada hannuwan ta

“Shikenan jeki sai da safe”

Hindu ta mike dasauri jikinta na rawa ta zura takalman ma wari da wari ta saka..

Tana futa Alhaji Sambaso ya mike zai fita shima,

“No Alhaji please “

“Kin aminta da ita.. ba ita ce mai aikin su ba kafin tafiyar su waje”

“Dan Allah ka kyaleta nasan ba zata fada ba”

“Okay ni ba wajenta zani ba”

“But am…

“Nace miki ba wajenta zani ba. Refreshing brain na kawai zanyi zan dan fita yanzu ba nisa zanyi ba ita kuwa ai nasan ta hau mota ta tafi ma”

“Shikenan sai ka dawo”

Fita yayi wajen gidan ya dau motar sa ya fita daga cikin gidan a hankali yake tafiya yana hango malama Hindu tana tafe tana waiwaye tana tafiya atsorace…

Tunani dankare cikin kirjinta, wannan wace iriyar rayuwa ce haka? Dama zaman cin amana suke da su? Lalle duniya abar tsoro ce… Wayar dake gurin ta ce ta fara kara mai gidan ta ne wato bappah junaidu ta dauka muryarta na rawa ta saisaita kanta tace gata nan zata dake yanzu inshaa Allah…

Daman titin yayi dubu ba street lights sun mutu..Salati ta fara yi tana karanta la’ilaha illa anta subhanaka jnni kuntu minazzalimin..

Alhaji Sambaso ya kara gudu zuciyar sa na kuna,, wato har ta fara kiran waya tana fada kenan? ya tashi kanta tana komawa gefen bishiya ya hadata da bishiyar ta daga sama can ta fado kasa tim kamar ba mutum ba ..

Ya arce dagudu ya hau babban titi. Sai bayan yan mintina tukun sannan mutane sika taru tana numfashi dakyar,..aka lalubo waya ajikinta aka Kira number data amsa Kira karshe ta bappah junaid da nawrah tayi saying da abbiey ban da nan suka kira shi suka gaya masa hankalin da ake ciki.
.
Suka nufi gidan da ita wani mutumi ya temaka aka kaita kasancewar ummyn tanata magana da kyae kan akaita gidah

Ana kaita baki daya yaran sukai kanta sunata ife ife da adduoi. Daga na suma rankaya asibiti

Likitoci sukai kanta aka saka mata oxygen kasancewar numfashin ta ya fara sarkewa.

Likitocin sunata kokarin bata temako, Bayan wani lokaci, Likita on duty ya fito daga emergency ward yana zare facemask dinsa ya dubesu kansa a kasa .

Ashir ya karasa kusa dashi yana girgiza kafadar sa,

“Ya jikin ummyn wani abun ake bukata? Jini? Kudi? magani? Me kuke so?”

Likitan ya girgiza kansa bayan ya sauke katuwar bahaguwar zuciya yace,

“Sai dai muyi hakuri Allah ya mata rasuwa…babban dadin kuma ta cika da kalmar shahada Alhamdulillahi….

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

26

:::::::::
    Dukkanin su a tare ji da ganin su suka dauke na ‘yan wasu daki’kai…

Ji ka ke timmmmmm… Bappah junaidu ya fadi wanwars a kasa sumamme ..

Likitan yayi kansa. Ashir ya shiga bubbuga kansa a bango… Yayinda Amnah ke duban su duka tana hawayen itama duk kuwa da karama ce ainun. Ashfeef ya rike hannun ta shima yana rera kukan sa ahankali

Nawraah ta sulale daga jikin bango ta yi zaman dab’as na yan bori…Ta saki marayan kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara….

“Ummy…. Wayyo ALLAH na ummy” Ta shiga maimaitawa tana bubbuga hannuwanta a kasa.

Bappah Auwalu yana tsaye daga bakin kofar dakin bawa marasa lafiya na gaggawa temako inda aka shigar da Bappah junaidu da yayi doguwar suma suna bashi temako don ya farfado.

Nusaiba na gefe tana girgiza kai… Mutuwar Hindu kwarai matuka ta girgiza ta. Hawaye suka shiga zirarowa daga idanun ta ..

Su Layla suka karasa asibitin itada Ahmad… Ganin su suka yi cikin yanayi marar dadi…

Jikin su yayi sanyi. Layla ta karasa wajen Nawraah dake kuka sosai kamar ranta zai fita ta zauna a kusa da ita tana kallon ta,

“Nawraah….. Meya faru? Meya samu ummy? Operation ake ma ta? Ko ciwon ne ya kara tsamari?”

Nawraah ta girgiza mata kai tana zubar da hawaye. Ta saka hannun ta ta share hawayen tace da ita, cikin rawar murya,

“Ummy ta rasu”

“Inna Lillahi wa inna ilaihi raji’un… Ummyn?”

Fashewa tayi da kuka sosai itama ta saka tafukan hannuwan ta akan bakin ta. Ahmad ma ya fara hawayen yana girgiza kansa cikin dimaucewa,

Har tsakiyar dare Bappah Auwalu ya futa ya kawo musu burodi dakyar ya tsawatar musu suka sha da ruwa. Wasa wasa har akayi asubah sukaci sauran burodin…

Wata nurse ta futo daga ciki tana duban su… Kowanne cikin tashin hankali. Bappah Auwalu ne kawai yake kokartawa yana kukan zuciya,

Ta karasa kusa da shi tana masa sallama. Ya amsa ta yana sharce hancin sa da hankici,

“Mashaa Allah an samu ya farfado mun masa allura saboda ya samu nutsuwa . Ita kuma marigayiya idan akwai motar da zaa sakata aciki to idan babu munada kurkura mota ta haya sai a sakata aciki, dubu biyar ne kudin kaiwa”

Ya kada kai yana sanya hannu acikin aljihu zai zaro kudin Nusaiba dake gefe tana duban su ta karasa da sauri,

“Menene ?”

“Kudin motar da za’a saka Hindu aciki ne zan biya meya faru?”

“Har nawane kudin?”

“Menene haka sai? Dubu biyar ne mana “

“Yanzu dubu biyar din zaka kwasa ka bayar?”

“Bakida hankali Nusaiba wallahi bakida hankali “

“To ai gaskia ne. Shi ya bayar mana…. Dubu biyar dinnan idan ka kwasa ka bayar ya zamuyi da sayen taliyar…?”

Dogon tsaki yayi ya girgiza kai cike da takaicin maganganun ta yace,

“Zaki matsa ko sai na hanbare ki?”

“Hanbareni halin naka zaka nuna a bainar jamaa hanbare ni Auwalu”

Kudin ya kirga da sauri ya mikawa nurse din ta koma ciki.

Ya bar Nusaiba a tsaye tanata banbamin mita. Ya nufi wajen Ashir ya riko shi

Ashir din ya fashe da kuka. Bappah Auwalu ya riko shi ya rungume shi tsam a jikinsa

Ashir ya shiga rusgar kuka tamkar karamun yaro yana kiran sunan mahaifiyar ta su

“Ummy… Ummy”

“Dan Allah ku dai na mata kuka, ku dai na zubar mata da hawaye. Addua take bukata yanzu ba zubar hawayen ku ba. Soyayyar kadai da zaku nuna mata yanzu addua ce. Sai tafi bukatar ta. Kuyi hakuri dan Allah. Uhm munyi rashi kam . Allah ya gafartawa Hindu ya kyautata namu zuwan. Bar kuka Ashir dan Allah kaji? Alhamdulillah jikin mahaifin naku ma ya farfado yanzu nurse ta fada. Kuma zamu kai gawar gidah don a sallace ta.,”

“Wayyo Allah na. Ummy na wayyo Allah ” Nawraah ta shiga nanatawa tana cigaba da hawaye.

Bappah Auwalu ya shiga wajen da aka rufe gawar malama Hindu da wani yadi shudi baki daya ya rib’e ya koma kalar jini. Saboda tsananin jinin dake futa daga jikinta har yanzu. Tun sanda aka kawo ta. Daman bayan likitocin sun yi gwaje gwajen su angani ta samo karaya takwas. Hudu a kwibi. Biyu kafafun ta daya hannun ta. Yayinda dayan Kuma gefen wuyan ta. Sai internal bleeding shima data samu. Sai Kuma jini daya taru a kwakwalwar ta. Sai ciwo a gefen goshin ta da aka mata dinki har zuwa lebenta. Domin fuskar ta ma ta rabe gidah biyu. Da sauran ciwuka Wanda ba zasu kirgu ba don da tayi rai ma ba lalle ta cigaba da moruwa ba, kasancewar spinal cord dinta ma ya tsinke.

Bappah Auwalu ya saka hannu ya toshe bakin sa da tafin hannunsa alokacin daya shiga dakin yaga an lullube Hindu har kanta. Dankwalin data saka a kanta shi aka rufe fuskar ta. Tabbas kayan data saka ne dazu da ta je gayshe su.

Kwakwalwar sa ta shiga tariyo masa ashe dama bankwana take musu na tafiya tamkar wasiyya? . .

Wani siririn hawaye ya silalo masa ya sharce da bayan hannunsa sa.

Tsayawa yayi aka gama cike ciken da zaai na takardu kasancewar irin wannan idan aka kawo marasa lafiya ranga ranga haka magashiyan, To police na shiga cikin case din.

Don haka anyi dikkanin abunda ya dache daga karshe maaikatan suka Kai gawar malama Hindu cikin mota yar kurkura aka saka ganye agaba da bayan motar

Ballah Auwalu ya tattara kan su baki daya yaje su tafi gidah zaa yiwa malama Hindu wanka a sallace ta…
.
Bappah junaid da allura ta sake shi ya dubi Karin ruwan da ake masa ya fizge shi da karfi ya mike Yana dafa bango ya fita

Likitocin sukai kansa suna kokarin mayar dashi dakin hutun na marasa lafiya atafau yaki yace shi gidah zashi shima a sallaci malama Hindu da shi.

Ba yadda sika iya haka suka kyale shi bayan sun bada maganin da aka saya masa.

Akayi hayar mota ta debe su baki daya suka koma gidah

Ko da suka koma gidan ma sabon shafin alhini sika bude. Masu kuka na yi masu surutai nayi masu dukan kansu nayi.

Aka Kira yaran nasu baki daya lokacin da aka gama yiwa marigayiya malama Hindu wanka aka nadeta cikin likkafini fuskar ta kawai aka bari abude saboda yaran su gana da ita na karshe suyi mata addua. Fuskar ta takara kyau tamkar tana murmushi .

Ataree suka shiga baki daya har bappah Junaid kowanne da addu’ar da yake suna sake bude babin wani kukan mai kuna

“Allah ya jikan ki da rahamar sa Hindu Allah ya yaye Miki dukkanin zunuban ki ya sadaki da ajnabin rahama . Rabbi ya karbi bakuncin ki yasa karshen wahalar kenan. Ba abunda kikai min Hindu idan ma da akwai na yafe miki duniya da lahira Allah ya gafarta miki” bappah Junaid ya karasa fada har yana dora kansa akan gawar bappah auwalu ya fita dashi dakyar.

“Ummy … Ummy Allah ya gafarta miki Allah ya yafe mi ki, Allah ya sa aljanna makoma agare ki ummy. Ummy na rike alkawarin ki dayardar Allah zan cigaba da rike yan uwana har karshen rayuwata ummy” Ashir ya fada shima ya tashi ya mike ya fita kamar yadda bappah Auwalu yace kowanne idan yayi sai yabar dakin

“Ummy Allah ya jikan ki Allah ya jikan ki ummy Allah ya jikan ki ya gafarta miki ya shayar da ke ruwan alkausara” Cewar Ashfeef ya mike da kyar ya fita yana boye hawayen sa

“Ummy…. Ummy na… Ummy Allah ya jikan Ki da rahama Allah ya gafarta Miki Allah ya kyautata makwancin ki Allah ya sa aljannatul firdaws makomar ki ce, ummy inshaa Allah indai har Ina raye da raina da yardar Allah sai na kwato Miki hakkin ki da dik Wanda yayi Miki wannan mummunan hukuncin . Ubangiji Allah ya dafamun ummy. Inshaa Allah, Allah sai ya tozarta su ya wulakanta su ya d’ai d’aita su. ” Mikewa tayi dakyar ta futa tsna sake fashewa dakuka… Nusaiba ta bi bayanta da kallo tana nazari akan kalaman ta na karshe… Suwaye suka kàshe Hindu? Nawrah tasan wani abu kenan? Lalle akwai sauran kallo a gaba idan da rai. Domin Nawraah KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA….

“Bappah… Ummy ta mutu yaushe zata dawo eh?” Amnah ta fada tana rike kafar wandon bappah Auwalu .m

“Allah ya miki albarka Amnah Allah ya raya ki ya tsare ki kinji?” Ya fada mata yana kokarin mayarda kukan daya tayo masa

Waje ya futar da ita bakin kofa. Nusaiba dawasu mata makota suka sake rufe gawar malama Hindu har zuwa fuskar ta suka daure.

Aka sanyata a tabarma aka kullubeta da wani zanun aka sanyata a makara. Bappah Auwalu ya kira su Ashir aka sallaceta aka kaita gidan ta na gaskia

Kafin a fitar da ita daga gidan sai da akayi dagaske yaran ta gaba daya da bappah Junaid sika birkice suna riko makarar suna hawaye kowanne yana surutai kamar mahaukata. Dakyar aka banbare su aka fita da ita zuwa makabarta aka binne ta

Ta samu yabo sosai daga bakunan jama’ar da suka santa. Takuma samu mutane sosai da suka halarci jana’izar ta aka sallaceta suka kaita gidan ta na gaskia.

Sannan aka dawo gidah akayi cirko cirko unguwar tayi tsiit. Yayinda zuriyar hamidniyya Lebanon tamkar ruwa ya cinye su saboda alhini . Hakika baa taba musu mutuwa data grigiza su bayan ta yafendo ba sai wannan ta rasuwar malama Hindu, Mai dakin bappah junaidu, Kuma mahaifiyar su Ashir, Ashfeef, Nawraah da kuma auta Amnah…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

27

:::::::::
Haka rayuwar ta cigaba da garawa…. Bayan kwanaki arba’in da rasuwar malama Hindu. Dangi na kusa dana nesa duk sun Kokkoma inda suka fito. Yayinda kowanne ya cigaba da rayuwar sa idan ka cire ahalin na malama Hindu da mutuwar ta dake su kwarai matuka…

A Kwanakin ne Kuma hajia qibdiyya dake kasar waje ta kira wayar malama Hindu dake hannun Ashir.

Ya amsa mata bayan sun gaysa ne data tambayi malama Hindu yake sanar mata cewar ai Allah ya mata rasuwa tun kwanaki…

Hakika mutuwar ta daki hajia qibdiyya ji tayi tamkar da Wasa ko Kuma waswasi kunnenta yake mata sai data sake tambayar sa har sai uku Yana tabbatar mata sannan ta amince.

Kuka ta fashe da shi tun awayar tana sallallamin wallahi batada masaniya. Don kwana biyu itama wayar tata bata hannunta sakamakon ta haihu dan ba rai kuma ciwon ta ya tashi na hauhawar jini sai da mai gidan nata ya sake zuwa yayi ciku ciku ya sake canza date din ranar da zasu dawo zuwa dogon zango mai nisa.

Ashir sai ya koma bata hakuri jin tana kuka sosai mutuwar ta dake ta. Dakyar ta iya kashe wayar bayan ta bashi mai gidan ta Dr. Dollars ya musu gaisuwa. Ta Kuma bawa yaranta daya bayan daya sunyi musu gaisuwa ta wayar. Ta kashe wayar jikinta asanyaye

Sai datayi kuka ta koshi sosai har sai da zazzabin ya tasar mata ta kira Dr bintu a waya don tasan Kila batada masaniya bata gaya mata ba bayan sunyi waya jiya da su .

A handsfree ta saka wayar bayan sun gaysa. Murya a cike da alhini tache,

“Baki da labarin rasuwar da akayine Dr bintu ko kuwa mantawa kike baki sanar min?”

“Rasuwa kuma? Rasuwa fa kikace? Waye ya rasu? Kinganni a zaune Kinsa na mike a tsaye. Bangane ba waye ya rasu eh?”

“Hindu dai mai aikina da ke maki aiki a yanzu”

“Innnalillahi wa Inna ilaihi raji’un. Wallahi bansani ba. Yaushe ta rasu? Rannan tazo da yamma kamar yadda nace mata tazo da yamma tayi abinci wlh har take cewa zata dena aikatau. Naceto shikenan. Dama inata cewa kwanaki biyu shiru idan nakira wayar ta ma a kashe nache to inaga hutawar take bari nan da kwanaki kadan sai na kirata ko naje da Kai na na Kai mata kudin sallamar ta wannan watan meya sameta ? Zazzabin nan da akeyi ko Kuma tana da wani ciwon ne! Astagfirullah ko mutuwa ce dai tazo lokacin ta? “

“Ashe baki sani ba. Har anyi arbain dinta? Wallahi sai yau dana kira saboda Nima kwanaki biyu dinnan kinsan saboda rasa babyn da nayi Dr yasa na dau hutun komai harda rike waya. Bashine mukai waya dake ba aranar dana fara amfani da waya”

“Anyi haka ya jikin naki kuwa?”

“Alhamdulillah da sauki.”

“Kwana arbain har anyi. Allah sarki Hindu Allah ya jikanta wallahi bansani ba. Kai banji Dadi ba wallahi. Don Allah ki gayamun kwatancen gidan ko Kuma driver ya Kai ki ni ai yasani tunda shi ke dakkota ya komar daita.”

“Wallahi bintu . Bakiji rai na ba Kai Allah ya gafartawaa Hindu. Wallahi bantaba ganin mace irin taba na Dade banga mutum Mai saukin kai da Bai dau rayuwar duniya da komai ba irin wannan matar. Inshaa Allah aljanna makoma ce agareta “

“Tabbas tanada hakuri wallahi. Batada lafiya ne?”

“Aa yace min accident ne irin hit and run dinnan?”

Dr bintu na tsaye sai ta zauna jin kafarta ta fara rawa ta gaza daukar nauyin jikinta. Ta dafe kirjinta idanuwanta suka furfuto waje cikin tashin hankali tace,

“Mota ce kenan ta kasheta ta gudu? Innnalillahi wa Inna ilaihi raji’iun “

“Wallahi kusan haka yaronta yacemun. Yace police sun shiga case dinma, Amman dai an kasa gano Wanda yayi. Kasancewar dare ne Kuma ba haske awajen da aka kashe ta. Wai yaushe kikace tazo aiki last?”

Gaban Dr bintu ya buga fuss. Tsabar tashin hankali sai harbawa yake kamar zai fado daga jikinta tace,

“Kwanaki ne can kamar ranar larabaa date din…….. Tazo da yammaci ta tafi da dare”

“Exactly a ranar ne to daga gidan ki take wlh aka samu wani Wanda yake sauri kamar zai tashi ya bugeta ya gudu saboda rashin Imani. Ai addua nake Allah ya waiwayo damu ayi mai yiwuwa a nemo koma waye da karfin ikon Allah inshaa Allah da dakarun taro. Dole suyi dubada na issue din”

Jikin Dr. Bintu asanyaye tache,

“Kwarai ma kuwa …. Kai amma banji dadi ba Allah ya jikanta da rahama”

“Toh aamen dai. Nima bari na je na kwanta dare yayi anan mu”

“Shikenan kawata. Sai da safe agayda yaran”

“Zasuji inshaa Allahu. Ki gayda mun da su Lily”

“Inshaa Allah.” Dr bintu ta zare wayar daga kunnenta ahankali ta daga kai ta dubi makeken hotan mai gidan nata Alhaji Sambaso dake jikin frame tamkar shi take ganu agaske tana girgiza kai tace,

“Ko kaffara ba zan ba. Wannan aika aikan nakane Alhaji .. bayan rokon ka da nayi nace ka kyale matar nan, Ashe ashe abunda kayi kenan.. innalillahi wa Inna ilaihi raji’un yanzu ya zamuyi kenan .?”

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

K’K’J
(M/W/S)

✍️:MX

28

:::::::::
Zagaye parlorn ta shiga yi taje ta dawo tanata safa da marwa cikin tsananin tashin hankali. Jikin ta ya fara kakkarwa sosai, Baki daya tsoro ya cikata ya gauraye ta.

Tabbas idan hajia qibdiyya da mijinta Dr abubakhr dollars suka dawo suka karbi ragamar case din to lallai sai an gano su, sun kwashi kashin su a hannuwan su.

Tamkar zararriya ta shiga magana ita daya tana girgiza kai,

“Sai da na roke ka nache dan Allah kada ka mata komai . Amman ka aikaita wannan mummunan hukuncin? Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un.”

Jikinta na rawa tamkar mazari ta dauki wayarta ta kira shi har sau biyu bai dauka ba. Nanma ta masa message tace tanason magana da shi urgently ba reply.

Mayafinta ta zura ta fita daga cikin gidan zuwa parking lodge. Wajen mai gadi ta nufa dake rike da makullayen motocin gidan,

“Hajia ranki ya dade”

“Barkan mu… Bani mukullin Glk”

“Tohm gashi hajia. Allah ya dawo dake lafiya”

“Amin”

Direban ya taso da sauri ya gayshe ta ya karbu mukullin ya bude mata ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga ciki…. Baki daya bata cikin nutsuwa..

“Da gudu zaka tuka yau”

“To hajiya.. Ina zamu je?”

“Wajen Alhaji”

Suna tafe tana dukan bayan kujerar gaba, kasancewar a owners corner take, Idan ta tuno mummunan hukuncin da ya zarce ya aikata musu,

Cikin bacin rai da fargaba data gauraye ilahirin jikin ta har suka karasa kanfamin direban ya ajiye motar ta a ma’adanar motoci

Ta shiga cikin kamfanin bayan ta gyara facemask din data saka acikin mota.

Wasu maaikatan suka gane ta. Duk da facemask din data saka suka shiga gayshe da ita ladabce cike da girmamawa ta amsa tana tambayar daya daga cikin su,

“Yana ciki?” Ta nuna kofar ofishin sa dake kallon su

“Eh yana ciki hajia”

“Okay nagode”

Kofar ofishin ta nufa ta tsaya. Ta saka hannu tayi kicking har sau uku.

Yana daga zaune akan doguwar kujera makeken ofishin nasa dake dauke da bangaren desk da kujera da computer da mini fridge da kayan kallo

Sai kuma daga gefe set din kujeru ne suma da makekiyar tv da dispencer.

Sai wani drawer kuma da murfin ta garai garai ana hango komai na ciki. Su plates da cups ne da tissue da sauran su.

Shiga tayi ciki bakinta dauke da sallama. Ya daga kwalbar sugar free lemo yana sha

Dubanta yayi ta gefen idanu, ya sake karkata kwalbar cikin bakinsa ya shiga zuka ahankali yaki ajiye kwalbar,

Zama tayi a kujera mai kallon sa tana masa wani irin kallo tace,

” Ko shekara zakai kana shan lemon nan cikin kurbar tafiyar kunkuru da yardar Allah zan jira ka gama sha ka amsa mun tambayoyi na. Ko ince ka mika kanka ga jami’an tsaro bisaga mummunan ta’asaf d akai”

Ya shanya lemon ya ajiye kwalbar yana duban ta. Ya dakko wani lemo a gefen sa daya ajiye ya mika mata yana murmushi,

“Ungo sha… Haba rabin rai na”

“Ba maganar wasa ce ta kawo ni ba” ta hade rai tana amsa shi

“To fa menayi? Wait ko dan ban miki sallama ba na futa dazu? Sauri nake zamu shiga meeting. Kiyi mun afuwa”

“Kaga Alhaji ka dena wani kwana kwana . So nake ka fito a mutum ka gaya mun dalilin ka na aikata abunda kayi jiya”

“Jiya? Menayi jia?”

“Kafini sanin abunda kayi ai. Ka kyauta kenan haba Alhaji wane irin roko ne ban maka ba kan ka kyale matar nan wallahi nasan ba zata fada ba. Amman Alhaji kaje ka…

“Kinga ni bansan maganganun da kike magana akai ba. Wace mata kikace na kyale? Shin me na aikata?”

“Har kanada bakin magana ? To bari na fito maka a mutum tunda Allah yasa kaki magana… Mena ce maka akan mai aikin mu Hindu? “

“Me kike nufi ne? Wace mai aiki?

“Mai aikin gidan Dr dollars da mu kai magana. “

“Oh mai akai! Kudin ta zaa bata kome?”

Dr bintu taja dogon tsaki cike da takaici ta mike tsaye ta karasa daf da shi tace,

“Ni renin hankali ne wataran banason sa wallahi. Kayi abu ka nuna kai atafau bakai bane. “

“Bintu me ya sake samun ki ne wai eh? Idan kudi kike bukata ga atm din kinsan pin ai je ki spoiling kan ki”

“Banason kananun maganu wallahi. To tunda kaki amincewa Kanata nuna bakasan me kake nufi ba. Matar da ka buge a mota kana sane akan sani. Ta mutu … “

“Wace mata? Wane buge? Bangane me kike nufi ba”

Murmushi tayi tana girgiza kai tace,

“Ni ce ba wata ba… Yusuf” ta karashe maganar ta cikin fadar ainihin sunan sa na yanka

Ya dubeta yana maze fuska. Domin duk sanda ta kira ainihin sunan sa to lalle babban lamari ne Kuma cikin fushi take fada . Su kanyi haka daman idan yan fadan sun tashi..

“Magana nake maka”

“To me kikeson nace bayan tambayar danayi mi ki?”

“Yusuf a ajiye maganar raha a gefe. Tunda kaga na tako da Kai na nazo kasan ba karamin abu bane. Kai kanka kàsan akwai abunda kake boyemun. Sau nawa Ina kiran ka kaki dauka? Ga wayoyin ka nan, daya agaban aljihun ka dayar gatanan a kusa da Kai. Amman kaki dauka. Don haka duk wani boye boye da kake banaso ka fito ka gayan gaskia “,

“Wai maganganun me kike haka ne? Ba Kai ba …

“Yusuf dan Allah banason jayayya. . Ka futo ka gayamun gaskia boye boye ba naka bane. Case yana nan yana nisa awajen iyalan marigayiyar, Yusuf. Kai kanka kasan sai kanada babban issue ne kake zama a office baka dawo gidah ba. Kaki daukar waya da sauran su. Matar ka ce ni nasan halayen ka bari na fito maka a mutum . Hajia qibdiyya ce take sanar da ni, Rasuwar Hindu case din hit and run exactly ranar datazo mana ta karshe ta taafi da daddare dinnan. Daman Kuma na gaya maka nace wayar ta bata shiga a kashe ko yaushe idan na kirata saboda hakkin ta na kudin aikinta na wannan watan… “

“Ni menene hulda ta da rasuwar ta yanzu? Allah ya jikan rai”

“Yusuf boye boye ba naka bane. Case hana kokarin komawa hannun su hajia qibdiyya kasan su da hin diddigi da dakarun tsaro na kasa. Ka dena wannan kunbuya kunbuya din ka fito ka sanar mun komai musan yadda zaai maganar nan ta bata”

” Ke menene damuwar ki aciki ne?

“Yanzu ka amince kenan. Yusuf meyasa zaka kashe ta?”

“Kisa fa kaman na chaka mata abu ko na tura an kasheta . No ko daya. Kawai dai na bige ta da mota hoping ta samu karaya da sauran su”..

“To ta mutu Yusuf ta rasu. Case din hit and run ne yanzu. . “

“Ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru”

“Yaya zan kwantar da hankali na Yusuf! Ya Yaya! Sai da nache maka dan Allah karkayi mata komai matar nan ba zata fada ba na sani. Ka amince kace ba abunda zakayi iska kawai zaka sha haba yusuf”

“To nj dai ban kasheta ba na dai bige ta da mota tabbas, wait yanzu me kike so ayi tsoran me kike ne?”

“Yusuf itace fa as head of her family. Itake shiltering yaran ta da sauran su”

“Kakki damu. Everything is under control. Zan saka a aika musu da kayan abinci. “

“Dan Allah kayi kokari kaji? Ko Kuma zanje da Kai na store din na karba komai”

‘karki damu”

“Zanje na Kai kudin aikinta na”..

“okay ba damuwa”

Mikewa tayi ta gyara zaman gilashin fuskar ta ta zura takalman ta ta bar kamfanin….

Gidah suka koma tanata sauri ta sauya kayanta cikin wasu kayan da suka sha duwatsu da ado masu matukar kyau da tsada .

Ta sake shiga mota suka dau hanya,

“Muje kamfanin Alhaji na kayan abinci, daga nan zamuje gidan Hindu mai aikin nan nawa da kake Kai wa da dakkowa, Allah ya mata rasuwa”

“Hindu ta rasu? Kai Kai Kai duniya, mace mai kamala da kirki. Allah ya gafarta mata.”

“Aamin”

Suka dauki hanyar babban katafaren kayan masarufi na Alhaji sambaso. Wato,

SAMBASO PRODUCTIONS

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA’ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?

YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI… DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR…WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE

GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR… CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE


1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

iri ya fara na tafiya Nasarawa tareda sakawa Akai masa booking na hotel da komai.

Series Navigation<< Kwankwason Jimina Part1Kwankwason Jimina Part 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *