Samarin Bana Chapter 6

Samarin Bana Chapter 1

This entry is part 1 of 6 in the series Samarin Bana na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele

[10:45PM, 02/11/2016] Rahamat Nalele: 👯👯👯👯👯

*SAMAREEN*

        👯  *BANAH*

       👯👯👯👯

*TASU SALAN SOYAYYAR*

*Na Rahamat Muh’md Rufa’i Nalele*

Part 1…..

*Nutsu da kyau me karatu ka karan farkwan labarin nan da kyau kuma kar kayi gigin mantawa. Dan xai temakema wajan gane ya abin xai kasance nan gabah*

Sunana  SAILUBAH KASIM.

Ina garin KANO da xama awata unguwa da akekira fage

Ina da shekara ashirin da biyar aduniya wato 25 years

 Na kasance mace mace kyakkyawa san kowa in wanda ya rasa

Ni farace soll doguwa me kyan bafali

Ina da hq da breast na ‘daukar hankali

Bancika qibaba sannan baxa’a kirani siririya ba

Komai nawa ya ha’du kamar yanda kowace mace takeso ta kasance

Idan na kalli kaina a mirror hmmmmmmm

Dole najah numfashi anan

Dan ni dake da kai bana buqatar kufitoh kuce

       Ya SAILUBAH kin ha’du

Na sauke alqur anin me girma inada ilimin  addini daidai gwargwado dan baxa’a kirani jahila ba

Ayanxu ina U:J ina fannin san kasancewa cikakkiyar doctoh

Sai dai bawani damuwa nayi da karatun bah dan inada burukan da suka shige min gaban karatun

Na kasance mace mesan ku’di

Mesan na mallaki gida da mota

Sannan ku’di su ratsani

Inasan namiji ‘dan gaye ‘dan kwalisa me ilimi wayayye me hankali

Sannan ya kasance miskili ya kasance ni ka’daice xan mallaki dariyarsa da komai na halittarsa

Ya kasance nika’daice tasa abin dubawarsa  amma in aka cire iyayansa da qannansa

Ya kasan me hakuri sannan me kishi akaina 

Ya kasance naxama nice madubin dubawarsa. Shikuma yaxama shakallo agareni

Ina da burin Auran Attajirin Alhaji me ku’di da nera

Irin Alhazawan garin abuja nan

Maso ku’di da albaxaranci

Bana burin Auran qaramin yaro kamar wanda ya girmeni da irin shekara uku haka

Na fisan na Auri wanda yabani akalla shekara goma sha biyu

haka na saka araina baxan ta6ata auran qaramin yaro bah. dan na raina qarfinsa da jarumtarsa

Acikin unguwarsu akwai wani gida me kyau da ‘daukar hankali wanda ya kasance gidan xuwana ne ako da yaushe naga damar xuwa

Inada aboki RAMADAN wanda shine ya kasance wanda yakejin sirrina

nayi matuqar shaquwa da RAMADAN irin shaquwar nan da akekira da inbakai baxan iya rayuwa bah

Ina san RAMADAN dan ya kasance yaro memin ladabi da biyayya duk da shi ‘din miskiline

Amma ya ha’du tako ta ina dan  ina qaruwa dashi tako ta ina

Dan yafini ilimi yafini hankali sannan ya fini nutsuwa

Duk shawarar da nanema agun  RAMADAN idan yace min iyi kasa bar kaza nabarshi har abada

Yaro ne qarami ‘dan shekara ashirin  cif ba qari ba rage ayau

Idan me karatu ya koma baya toko xai gane naba RAMADAN shekara biyar kenan

Saidai RAMADAN funannan yaro ne. Xaki gane waye shi idan tafiya tai tafiya

Tunda natashi banta6a ganin idan mahaifiyata bah 

Dan tada’de da rasuwa tun ina jaririya

Ayanxu dai ina hannun matar babana ko ince muku Kakata

Ba lefi suna kula dani sosai saidai matar babana tana da san ku’di ba nawasa bah

Amma duk da san ku’din nata nafita

Babana dacan yayi ku’di Sosai daga daga baya ne karayar arxiqi tasa meshi

Ayanxu bashi dashi Saidai bama rasa na sawa abakin salati

Abu ‘dayane ya bari adukiyarsa. shine gidanmu.

Gidanmu babban gidane kuma ginin xamani

Dan a unguwarmu in kacire gidansu Ramadan akyau toh cika saka gidanmu

Inada qawaye masu bu’dad’dun ido da wayewa fiye da tunanin me karatu

Wannan shine labarina akataqaice

👯👯👯

Sunana RAMADAN Nasir yaro ‘dan 20 years

Na kasance ina da buri ‘daya arayuwata shine

 natashi da maseefar san wata mace me kyan sura. Da komai

Tayi tako ta ina

Ina santa

Ina santa

Ina santa

Ina da abokana ye biyu Fawas da Khamis

Duk ra’ayinmu ‘daya yake dasu

Amma mutane da dama suna cewa nafisu nutsuwa da hankali

Na kasance ‘dan gaye me san tsafta da qamshi

Duk unguwarmu ni ka’daine nafita xakka a iya wanka

Dan nayi xaman jos anan nasamo Sirrin

Inada kalamai masu tsayawa  arai

Sannan Auntyna Tace ni futunanne ne

Ya ta6e baki sannan yaci gaba da cewa

Idan hakane Ku da kanku xaku sheda hakan idan kuka cigaba dabin Aunty Rahamat Nalele

Suna na KHAMIS

Inada shekara ashirin daidai yau

Ban tsaida wani buri araina ba tukunna

Sai dai inada san mata saboda Suna sani nisha’di. mata abin farin cikine kowane ‘Da namiji ne

👯👯👯👯

Suna na FAWAS

Inada shekara ashirin daidai yau

Ina da San mata Sosai kuma inada burin Auran mace wacce ta xarce shekaruna da kamar shekara biyar haka ko shidda

Kuma bana san Auran wacce ta Waye nafisan Auran ‘Yar qauye me halin yarinta

Tab😳

👯👯👯👯👯

Suna na Zainab Amma ana kirana da XEE dan nafisan akirani da hakan

Inada shekara ishirin da biyar.

Ina da saurayi Surajo ina matuqar sanshi da kishinsa

  Sannan ni ta hannun damar SAILUBAH CE dan duk acikin qawayanta nice babbar qawarta

👯👯👯👯

Suna na Hameeda Ya’u ina xaune a qauyan takai Babana ya rasu Mamana mah haka

Ina hannun qanwar babana Innah Hansai

Ba qaramin ganamin axaba take bah

Duk aikin gidan ni nakeyi duk wani aika ni nake xuwa mata haka duk wani Girki ni nake yi

Duk da ko tanada yara Amma Sam bata sakasu sai ni

Sosai nake hango tsanata acikin idanta

Bata sona bata qaunata

Ta hana duk wani saurayi tsayawa dani wai tafiso na xauna inta yimata bauta

Ayanxu shekatata ishirin da hu’du 24

Bani da wani buri araina sai na kallan cigaba da bautar da nakeyi

*Toh Madallah masu karatu kunji tushen kowa acikin wannan littafi nawa. dan haka sai kugyara xama kusha karatu*

SAILUBAH yarince maisan ku’di kamar yanda tafa’da

Amma duk ku’din da xata samu basa rufe mata ido

Dan ko yanxu SAILUBAH tasamu ku’di xata iya kyautarsu gabaki ‘daya dan Allah yayota da San temakwan mutane

Tana da kyauta Sosai ba ‘dan ka’dan ba da tausayi

SAILUBAH ‘Yar gayece Sosai

Duk unguwarsu ba’ayi yarinya me wankanta bah

Zama na musamman samarin layin nasu suke dan kawai suga fitowarta

Duk unguwar ba  wanda baisan SAILUBAH da halinta ba

Kyauta San Mutane San ku’di fa’dar Gaskiya…………..

Koda ko kar sa’an babanta ne kayi abunda bai dace ba  toko ba shakka saita wanke ka da soso da sabulu

Duk unguwar ba Wanda baisan sha’kuwarta da RAMADAN ba

Suna San junansu Sosai dan shi’din abokinta ne

Mutane da dama idan sukaga SAILUBAH da RAMADAN xasu skull dake skull ‘dinsu ‘daya ba qaramin sha’awa suke basu ba

Fa’di suke tsakanin SAILUBAH da RAMADAN wayafi kyau ne

RAMADAN Yarone me hankali da nutsuwa

Sam baya shiga sabgar daba tashi ba

Komai xaiyi anutse yake yinsa

Baya ‘daukar raini

Yarone me farin jinin jama’a musamman mata

RAMADAN na kowa ne dan Allah yayoshi da kwarjini

Duk inda kika kai da abinki idan kikayi toxali da RAMADAN sai kinso Ki mallakeshi a matsayin mijin Auranki

Ya ha’du ne tako ta ina RAMADAN yayi

Yana da da’din murya haka kallo ‘daya xaki mai kisan anyi balaraban yaro

RAMADAN cikakken ‘dan rainin wayone

Sam baxa ki gane inda yasa gaba ba

Yana ji da Auntynsa SAILUBAH. Sam baya San 6acin ranta

Duk Wanda yake tare dashi yasan da xaman wannan

Sai dai fah ahakan baqamin takurama SAILUBAN yake ba akan samarinta

Shi ka’daine namiji agidansu

Kuma Wanda kamanninsa yafita daban dana kowa

Sam RAMADAN bai ibo Komai na iyayan nasa bah

Mutane na mamakin wannan yanayi yanda RAMADAN ya futa xakka agidan nasu

Kome yasa hakan

(Tabbas kwakwalwa tana buqatar caji agun🤔)

Su ukune agun mahaifan nasu

Akwai yayar RAMADAN Saudat wacce ta kasance qawar SAILUBAH

Sai shi RAMADAN ‘din

Da qanwarsa Khairat

Mahaifinsu Alhaji Naziru me ku’dine Sosai

Ya shagwa6a Su da ku’di Sosai

Haka ba qaramin SOO sukema RAMADAN ba

Kome yasa haka🤔

RAMADAN Yana da San karatu Sosai gashi da ilimi tunda ya taso ya fara xuwa makaranta bai ta6a fa’duwa akan Komai bah

Yanxu haka saura bai fimai 1 year ya gama kammala karatunsa ba

Inda yake san xama cikakken likita wato doctor

Yaxama kenan ra’ayinsa ‘daya da Auntyn Sa SAILUBAH

Idan Nace muku RAMADAN ‘dan rainin hankali ne karku musa min

Haka KHAMIS iyayansa Suna da ku’di Sosai shima an shagwa6a shi Sosai da ku’di

Su biyu iyayansa suka Haifa

Ianada Yaya Rahamat tayi Aure tana garin Abujah da xama

Ganin hakan KHAMIS shi ‘daya shiyasa shi abinda yakeso kuma iyayansa suka biye nasa

KHAMIS Yanada San karatu inda yakeso yaxama cikakken loya Wato ya karanci low

Shiko FAWAS iyayansa shi ka’dai suka Haifa

Ba qaramin ji dashi suke bah

Sun shagwa6a shi da ku’di Sosai

*To Madallah me karatu gyara xama*

Yau take talata kuma antashi da ruwan sama yaf yaf yaf gwanin sha’awa

SAILUBAH sauri sauri gudu gudu takeyin Komai dan sunada karatu qarfe tara

RAMADAN ya shigo falan hannunshi ‘dauke da Wasu takaddu Yace Auntyna lokaci ya fara tafiya fah

Da sauri tajuyo xatayi magana sai kuma tatsaya kallansa kamar alokacin ta fara ganinsa

Ya ‘daga mata gira tare da qarasowa kusa da ita ya kar6i ‘dan kunnan hanunta Yace in saka miki ko

Tayi saurin ‘dagamai kai Tace kayi kyau Sosai Qanina

Yayi Murmushi Yace Nagode Auntyna

Gyarawa Sosai tayi  ya saka mata ‘dan kunnan ta’dauki gyalanta da ‘yar jakarta tamaqala

Idan RAMADAN na kanta yana qare mata kallo. Ta ‘daga mai gira

Yayi murmushi Auntyna tsaya na  photo

Wayanka saita cika da pix ‘dina

Yace in bake acikinta Wlhi bata da amfani

Tace kayi breakfast kuwa

Ya ‘dan Sosa qeya Yace nayi

Tabishi da kallo ka’dan hmm bakayi ba

Yace toh Kinga lokaci yayi……..

Cire gyalanta tayi tashiga kitchen kawai. RAMADAN yaja numfashi tare da kallan agogo yana tsaki

Bai ankareba sai gata qatan faranti ahannunta.  Wanda ke ‘dauke da lafiyayyan tia da kuma  soyayyan dankali da kwai

Ta dire a gabansa Tace nabaka minti uku kayi Maza

Yace Aunty banajin yunwa…

Ta katse shi da jefa mishi wata muguwar harara

Bashiri ya fara ci   

Yayinda ita kuma ta xauna tana amsa waya

Hello Alhajina ina kan hanyar xuwa makaranta

Yace Amma naso inxo in ganki yanxu. Plx Ki bani ha’din kai yanxu naganki

Aini takace. Kabari ina dawowa xaka ganni.

Yace toh Allah  ya dawomin dake lafiya

AmEEn Nagode. Tafa’di hakan da kashe wayan

RAMADAN najinta Yace Auntyna dawa kikayi waya

Ta gallamai harara cikin ‘daure fuska Tace ban sani bah

Yayi Murmushi Yace pls gayamin Wlhi ba’abinda xai faru

Tace hmm yama faru Wlhi saina baka mamaki idan kayi sanadin da Alhaji Jamilu ya dena xuwa gareni

Ya kalleta ka’dan dayin murmushin rainin hankali Yace baxanyi Komai bah Auntyna Amma dan Allah gayamin yaushe kuka ha’du da har ya kasance ban sani bah

Tace jiya muka ha’du a jifatu yaje siyayya

Amma shine ko  jamishi aji bakiyi ba kika amsheshi daga ganin farko

Ta gallamai harara Tace ban jah mishi ajinba

Yace me yasa

Cikin maseefa Tace saboda shi me ku’dine yayimin tun kallan farko dana masa

Yace Amma………

Tayi saurin katse shi da cewa. Wlhi RAMADAN ba wani abu daxaka fa’damin inji inbar mutumin nan dan yana da ku’di Sosai

Kyautar farko daya min jiya dubu ‘dari uku ya ban 

Yace haba Auntyna……

Na rantse da Allah ka cikani da surutu xakasha mari

Shuru RAMADAN yayi yaci gaba dacin abincinsa

Can ya kammala Yace toh mutafi ko. Yafa’da da ‘daukar Wasu takaddunta

Suka fitoh ya bu’de mata gaban motarshi tashiga shima ya shiga da jansu suka ficce daga gidan

Direct gidansu XEE sukayi Suna parking tana fitowa

Tayi kyau Sosai cikin shigar riga da siket ‘yan kanti

Ta shiga motar ta xauna tana mita wai basuxo da wuri ba

RAMADAN Yace lefin Auntyna ne fah

Tace aina sani tasaka gaba kayi breakfast ko Yace ko shakka babu.

SAILUBAH Tace hmm kema kisan inba ni’din nasashi gaba ba baci xaiyi ba

Haka dai sukayi B;U:K university.

Sunayin parking wata kyakkyawar budurwa tayi saurin isowa garesu

Cikin rashin kulawa SAILUBAH da XEE suka fito dayin department ‘dinsu

RAMADAN yafitoh da Murmushi akan fuskarshi Yace ha’a kaga kyakkyawar yarinya. Tauraruwa me dishashe hasken taurari. Gayamin me ya tsaidake a wannan lokacin da yadace ace kina can kina ‘daukar darasi

Cikin jin da’di da dariya akan fuskar Amina Tace baxan iya fahimtar Komai ba inhar banganka ba

Tunda naxo idanuna suke min ra’da’di dan rashin ganinka da basuyi ba

Yace toh gani sun ganni sai hankalinsu ya kwanta

Tayi Murmushi. Xanso muje shan iska anjima

Ya kulle motar tashi yana fa’din xanfi kowa farin cikin hakan. Maxe jeki kar darisa Su wucceki da yawa

Ba musu Amina tabar gun cikin jin da’din Ganin masoyinnata

Gab da RAMADAN xai shiga department ‘din nasu

wata ta tareshi da sauri

Ya dafe kai cikin Murmushi Yace yane Asma’u

Xuciyata bugawa take in bata ganka bah

Amma na lura Sam xuciyarka bata damu dani ba Sam

Haba nutsuwata abin kwanciyar hankalina. Wlhi dake natashi araina

Meyasa toh kakasa nemana

Kin sanni da karatu banasan nayi missing ‘din Komai. plx nutsuwata Ki lamince min nashiga na miki alqawarin yau xan baki lokaci na musamman dan kimallaki kalmomina

Tace toh Allah yasa ina maka fatan alkairi

Ya shigeta yana cewa tare dake……..

Karatu ne Wanda sukayin shi cikin nutsuwata ahaka suka tashi inda SAILUBAH ta kalli RAMADAN Tace Amma fah abubuwa da dama na kasa fahimtarsu

XEE tayi dariya Tace aike Kullun a haka kike

Tayi Murmushi dacewa ai banda matsala tunda gani ga Qanina.

RAMADAN Yace aikuwa ammafa Auntyna  kidinga lura saboda wata ranah.

Taturo baki da cewa toh naji muje gida nafara jin yunwa ba sai mun jira KHAMIS ba …….

KHAMIS ‘dinne ya katsesu da fa’din dawai tafiya xukuyi kubarni bayan yasan yau ban fitoh da mota ba.

XEE ta kafeshi da ido Tace ya fa’da mana

Ammma fah kayi kyau sosai  Tafa’da da shigewa motar Ganin SAILUBAH da RAMADAN sun shige.

Yayi Murmushi Yace kai Aunty XEE ina wani kyau anan. Yafa’da shima yana mai shigewa cikin motar

Cikin nutsuwa RAMADAN yake tuqin motar

KHAMIS Yace Kasan wani abu

Sai ka fa’da

Wlhi fitowata ‘daxo na ha’du da wata xanka’daxiya……

Ta ha’du Sosai dan tatara duk wani abinda kowane ‘da namiji yake buqata awajen mace

Dana kai agoge min motata tsayawa nayi daniyar agama goge min natafi da ita

 lokacin ko wanka banyi ba

Sai gata tayi parking motar tata akusa dani

Ta fitoh tana wani yauqi da rangwa’da. dan Allah Malam motata nakeso a wanke min nanda 10 minutes

Ba sai ta cillamin key nata bah

RAMADAN Yace kut😳

Wlhi ina gayama sai kawai naxuba mata ido kusan na 2 minutes

Ka katsaya kana kallona ko baka ‘daya daga cikin masu wankin ne

Ta katsemin tunanina da fa’din hakan…..

Kan nayi magana wanda yake goge min motar tawa Yace tab Hajjiya shima kawo tasa yayi. Baki lura da hutun da yake tare dashi bane

Kasan dake ‘Yar iskace saita juyo da kallanta. Ayya am sorry

Na watsa mata wani  kallo Nace Karki damu xan wanke miki aikin kai wajan kinma wucce

Tayi Murmushi Tace ba qarya ka ha’du ga muryarka tayimin da’di Sosai dama kana tare dani dana saka agaba dan kawai nadinga jin kalmominka…..

Kan na bata amsa yaran ya gama gogemin tawa

Saina bata kina Nace taje ta aiwatar da ‘quxirinta xan kawo mata tata motar har gidansu

Tayi dariyar jin da’di toh Nagode Sosai Allah ya saka

toh bara namaka kwatancan gidanmu…….

Na katseta da fa’din bana buqatar sani dan inaso in baki mamaki wajan kawo miki gidanku batare dakin gayamin bah

Baka fah sani ba

Nace karta damu

Haka tatafi da motata tabarmin akwalar tata

Kasan yanxu damuwata bansan gidansu bah

 kuma kamar xuciyata takamu dasanta

Dan Wlhi yau nakasa fahimtar Komai na karatu. sai San ganinta da xuciyata dake kwa’dayin qarayi

RAMADAN ya kalli Su SAILUBAH ka’dan Yace Auntys suna nan fah. Dan haka ka ankare.

Sam KHAMIS ya manta Suna tare dasu

Cikin yanayin sanyi ya kallesu Yace am sorry my Auntys

SAILUBAH ta gallamai harara Tace ‘yan yara daku sai San mata yanxu idan aka baku su ya xakuyi dasu. Ta’ina xaku fara sarrafasu

Ina ja muku kunne Wlhi kufita daga harkar mata dan sunfi qarfin Ku

 kubari Ku qara shekara goma nan gaba saiku nemesu

KHAMIS da RAMADAN suka kalli juna

Inda sabo sun saba shan fa’dan Auntyn tasu

Cikin ‘daure fuska RAMADAN Yace toh munji

KHAMIS Yace 20 years fah Aunty

XEE Tace eh baku kai soyayya ba. Na roqeku kubar kula mata……

Dai-dai nan RAMADAN yayi parking a’kofar gidansu XEE

Tafi toh tana cewa Qawata saimun ha’du anjiman

SAILUBAH Tace wane Kaya xamu sane aciki

Tace eh toh musa let ‘din nan mana

Tace red ‘din Tace eh shi

Kana takalli KHAMIS Tace toh kuhuta samari

Yace toh Aunty XEE sukayi gaba

Ita mah tayi gidansu tana tunanin KHAMIS itadai tana sanshi yaran na burgeta ga iya wanka kamar RAMADAN

Gashi hancinta baya manta qamshinsa

Maman ta kalleta Tace ya dai naganki kina Murmushi

Tace Wlhi mamah KHAMIS ne yake birgeni

Tace ayya KHAMIS ai yanada hankali

Tashige toilet tana cewa ba lefi kam

Hakama suka sauke KHAMIS agidansu

RAMADAN Yace karka damu abokina akwai mafuta

KHAMIS Yace nasan bama rasata. Xan nemi FAWAS mah

RAMADAN na parking a farfajiyar gidan nasu SAILUBAH

Yace Auntyna

Na ‘danga wayarki

Tamiqa masa da ficewa daga motar tayi falansu

Annan tatarar da Abbanta yana cin abinci Umma na gefanshi Wato matar Abban nata dake haka suke kiranta Tace sannu da gida Abba

Yace sannu kundawo lafiya Tace lafiya lau

Yace toh Madallah in kin gama cin abincin naki kixo kisa meni

Gabanta ya fa’di Tace toh

Wanka tayi ko cin abincin batayi ba taje gunsa

Yace dama xan da’da tuna miki ne akan batun tsaida Miji

Wlhi kika cikamin ciki xan aurar dake ga wanda naga dama

Tace kayi hakuri Abba ka qaramin lokaci

Yace ke kika sani nidai na qara miki lokacin

Dan yana wuccewa baki kawomin Wanda kike so ba Wlhi kinji na rantse saidai kawai kiji Nace kitashi kibi mijinki

SAILUBAH ta sunkuyar da kanta cikin ladabi Tace insha Allahu hakan baixai faru bah xan kawo Wanda nake so

Yace Allah yasa jeki

Nan Tatashi xuciyarta cike da tunani kala kala

RAMADAN ko gidansu yayi direct yayi part ‘dinsa. Dan gidan nasu acike yake tam da mutane ‘yan biki

 yaune walimar yayarsa Saudat gobe ‘daurin Auranta

Ya baje a gado yanata bincikar wayan SAILUBAH.

Har yasami abinda yake nema watoh number Alhaji Jamilu Wanda SAILUBAH tayi waya dashi ‘daxo

Nan ya kirashi ringing biyu ya ‘dauka cikin sauri yana fa’dan Allah yaja da xamaninki tauraruwa

RAMADAN ya runtse ido Cikin kamilalliyar murya Yace ba ita bace na kiraka ne in gaya maka wani abu

Alhaji Jamilu Yace toh ina jinka

Yace Kasan  da cewa tarayyarka da ita haramun ne

Dan babu kyau Nema acikin Nema

Dan da sadakin wani akanta yanxu haka baifi watanni bane bikinta

Cikin muryar tashin hankali Alhaji Jamilu Yace Wlhi ban san An kawo sadakinta  ba

RAMADAN Yace toh yanxu nagaya ma danni qaninta ne

Yace Nagode Sosai yaro Allah ya maka albarka

RAMADAN Yace AmEEn da kashe wayan

Sannan yayi blocking ‘din number Sa da delete ‘dinta

RAMADAN kenan ya tsani yaga kowa da Auntyn nasa. Shiyasa yake koran mata samarinta sanranshi. Tayi fa’dan tayi maseefar Sam bayaji. Iya kacinsa da ita shine ya bata hakuri

SAILUBAH ko daqar taci abincinta burinta tagama taje gun Qanin nata suyi shawara

Hakako akayi. Data gama Komai saitaje tasamu kakarta Tace kakane bara naje gidansu RAMADAN

Tace har lokacin walimar yayi ne

SAILUBAH Tace wai walimar walimar Saudat

Tace eh mana. Taxoma nemanki ‘daxo keda XEE wai kimata lalle ne kome tacene oho na manta

Girgixa kai SAILUBAH tayi Tace sai qarfe hu’du walimar da sauran lokaci

Tana fa’din hakan tafito daga falan nasu

Tafi toh kenan idan ya sauka alungun Gidansu wata Baraka dake kusa dasu

Saita dinga jin kamar kukan yarinya. Cikin qarfin hali tayi lungun

Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un. Tafurta hakan da qarfi. Dan Ganin wani narkeken qatan garde a’kalla xaiyi shekaru arba’in 40 Ya danne wata yarinyar makwaf ciyarsu ‘Yar miciciya batafi shekara goma ba

Aiko SAILUBAH me xatayi inba kurma ihu ba. tana fa’din jama’a kuxo ga wani axxalimin mutum yana San 6atama yarinya rayuwa…….

Kan kace me😳 tuni gun ya cika da jama’a Suna tafi da Allah wadai da shi da mamakinsa

mutumin ya saka wandansa SAILUBAH ta cukume masa riga Tace Amma kai kam Allah yayi tsinannan tsowo

Fasiqi axxalimi me mumunar xuciya ‘dan iska

Kalli yarinya qarama kana san 6ata mata rayuwa

Idan iskancin kakeji mexai hana kaje gidan karuwai kayi da wacce ta dace dakai. Tunda xuciyarka tamace da son abinda Allah bayaso

RAMADAN Wanda yafito dan rahotan da qanwarsa takai masa.

Xuciyarsa tacika da takaicin Auntyn tashi yayi dabarai kwatan mutumin ahannunta……..

Kan yayi magana sai gani sukayi

Iyayan yarinyar sun rufe mutumin da duka Sosai

Mutane na fa’din gwanda aci ubansa Suna tayasu dukansa

SAILUBAH takai hannu xata tayasu itama…..

RAMADAN yajah hannunta sai Gidansu

A farfajiyar gidan yasake mata hannun nata

Yace haba haba Auntyna meya kaiki aikata haka. Kamata yayi da kika gansa kimasa wa’axi tsakaninki dashi. Amma bai dace kitara mishi jama’a haka ba

Tunan asiri bashi da kyau ai

cikin maseefa ta hayyaqu miki tace banyi hakan da kaso ba.

Irin sune ‘yan iskan da in ba haka akayi musu bah baxasu dena abinda suke ba

Yace toh wai ke ina ruwanki meya shafeki kawai kinje kintara jama’a maxa da mata kowa yana kallanki harda wani kai hannunki jikin qaxamin mutumin. kin dai kwafsa kawai kiyarda da hakan

Yafa’da kamar xai rufeta da duka

Tace baxan yarda da hakan ba

danni abindayi dai-dai ne

Kana maganar abarsa ya6ata mata rayuwa kenan ko

dan ba kasan xafi da ra’da’din da iyayanta xasu shiba

Tafa’di hakan dasan ficcewa daga gidan

Yayi saurin kamo hannunta dan yafi kowa saninta sarai yanxu xata qara hurama wutar fetir .

Cikin sanyin Murya Yace toh yi hakuri Auntyna gwara da Allah yasa kika gansa

muje im baki wayanki pls👏🏻

Ta’daure fuska xata kawo mishi matsala yayi saurin janta part ‘dinsa

‘Yan biki suka saki baki Suna kallansu har sanda suka qule Sannan suka cigaba da har karsu Suna tuno ‘Yar cacar bakin nasu

San da ta xauna kan kujera. Cikin lallami Yace am sorry Auntyna bana san 6acin ran nan naki.

pls ki temaken Kisake min fuskarki ko nasamu nutsuwa araina dan Allah

Ta harareshi dayin  kwafah.

Ya marairaice mata tamkar xaiyi kuka

Tace najini dan Allah

Sai kace wani yayana ka wani rufeni da fa’da wai na kwafsa……

Saurin rufe mata baki yayi da hannunsa…..

Xirrrrr taji

Ita dai akowane lokaci idan RAMADAN ya ta6ata saita tsinci kanta cikin wani hali kome yasa oho

Yace ina miki addu’ar Allah yabaki miji me ha’kuri da halinki Auntyna

Da Takaici Tace AmEEn. Wai kai baka jin wani abune idan ka ta6ani

Ya ‘danyi jim can ya ta6e baki Yace banajin Komai

Tajah tsaki ako wane lokaci ka riqeni jin xirrr nakeji tun daga Kaina har babban ‘danya tsana

Yayi Murmushi da qara kama hannunta Yace qila ko danni Yarone.

Tace ko

Yace ba mamaki

Kasan miye matsalata

Ya girgixa mata kai alamar aa da kuma kafeta da ido

Wlhi Abba ne yaqara min tuni akan Aurena

Yace toh miye

Tace da matsala mana

Yace ba wani matsala kawai kifitoh da wanda ya kwanta miki arai

Ta gallamai harara

Kana barina ne da samari

Da xakace in fito da wanda ya kwanta min arai

Yayi murmushin jin da’di tare da murxa hannunta cikin wani salo Yace xan soki da qaramin yaro

Cikin ‘daure fuska Tace dawa kake….

Kan ya bata amsa taci gaba wajan fa’din. Kafi kowa sanin tsarina da ra’ayina bana san naqara jin wannan kalmar daga bakinka

Ina ganin xan janyo Alhaji jamilu jikina musaba kaga sai kawai na gabatar dashi matsayin mijina ko

tunda ya ha’du

Murmushi RAMADAN yayi Yace duk da ban gansa ba Amma hankalina ya kwanta dashi kifito dashi ‘din kawai

Ta sauke ajiyar xuciya xatayi magana wayarsa tafara ringing…….

Sake hannunta yayi ya duba wayar

Amina ya gani

meenat ya akayine

Tace lpy lau my luv

Yanxu haka ina kwance a gado naci kwalliya Sosai dan xuciyata tacika dasan ganinka muje shan iska. Allah yasa baka manta bah

Ya dafe goshi cikin marairai cewa Yace am sorry farin ciki na

Naso in cika miki alqawarin danayi miki Amma kaxai yuhuba

Xanso kiqara bani dama akaro na biyar

Amina taja numfashi cikin rashin jin da’di Tace Ashe kana sane ba yau kasaba yimin hakan ba. Da gaske yau shine karo na biyar………

Wani shegen tsaki SAILUBAH tajah da gallama RAMADAN harara

Yayi Murmushi da tsaida idanshi akan le6anta

Cikin sauri Yace eh kimin hakuri ina da wani babban uxiri ne xan kira pls

Yana fa’din haka ya kashe wayan batare da Yaji cewarta bah

Kamar yanda lamarin yasa ba faruwa mishi hakance tasake faruwa SAILUBAH taqara kai mishi harara Tace Wato kai baxaka fita aharkar mata bako

Qanqanin yaro dakai Kasan kadinga yaudarar mata ko

RAMADAN ya xuba mata ido da fa’dawa tunin wai sai yau she ne Auntyn tashi xata dena kiransa da yaro

Da ‘daure fuska Yace shekarata ishirin xaki dinga kirana qaramin yaro

Haba dan Allah yanxu inda agaban budurwar tawace shikeban kinsa tarainani dan Allah kidena kirana qaramin yaro

Tayi dariya dan ganin yanda yayi kicin kicin da fuska tunba yau ba

 tasan RAMADAN baya san  araina shi shiyasa yake ganawa Khairat axama qanwarshi dan baqaramin tsoranshi take ba

Gashi dasan girma Sam baya SO ace wane ya girmeshi

Ita ka’daice xatace mishi qaramin yaro baxai CE mata Komai ba. Toh yau gashi yayi kicin kicin da fuska

Tashi tayi taje gabansa ta manna masa kiss a kumatu kamar yanda tasaba yimai idan ta 6atamai rai Tace sorry ‘dan Qanina kai Babban yarone

Xaka kaimu walimar Saudat kajiramu.

Yace aa

Dan Allah

To naji

Tatashi xata fita Yace Auntyna yunwa nakeji

Tace toh bara na kawo maka abinci. Tafita

Yabita da kallo

Bata ‘dauki lokaci ba sai gata da plate da drink ahannunta

Tadiremai a gabansa

Taliyace Momy tayima Dady dakai ‘daxo

Yafara ci yana cewa idan baku shirya da wuri bah tafiyata xanyi

tashi tayi da ‘daukar wayarta tana cewa bara nagama Amaryar

Ka’dan yaci ya kora da drink kana yayi wanka Cikin qananan Kaya yakira FAWAS da cemai Su ha’du a gidansu KHAMIS dan shi KHAMIS ‘din yayi wani banxan kamu. Yace OK

Tunda ya fitoh qawayan Amarya yayar tasa suke kallansa

Cikin maseefar sha’awarsa dan yayi kyau Sosai ya fitoh a bature sak

Dan yanayin shigar tasa sai qamshi yake

Ya shiga falan Momy nashi annan yaga SAILUBAH tanata xuba cikin sanyayyiyar muryarta

Tanajin qamshin turaransa taja numfashi da lumshe

Yace momy ina xuwa yanxu

Tace da fatan kaci abincin da yawa Yace eh. da maida kallansa ga SAILUBAH Yace Auntyna bara inje yanxu xan dawo

Ta shagwa6e fuska Tace pls karka shanyamu Yace Karki damu my Aunty. Yafita da sauri hotan fuskarta na manne cikin kwayar idansa yana hango shagwa6ar tata

‘Yan matan suka bashi da kallo dan shi’din yayi

Wata Salma Tace nikam ina san yaran nan SAILUBAH….

Harira ta katseta da fa’din ai yayine tako ta ina

Saudat Tace ai shegen yarone yasan kan Komai daya dace dashi.

Haka kowa Yata fa’dar albarkacin bakinsa akan RAMADAN

SAILUBAH tayi shuru kawai tana jinsu

Ashe har qawayan Momyn nashi sunyaba da shi

Shiko yana fitowa daga gidan nasu idan shi ya sauka akan Jamila

Wato Jamila wata ‘Yar unguwarsu CE tana MASEEFAR son RAMADAN

Tarigada tasan duk wani motsinsa dan haka kanya fitoh daga gida take kafawa ta tsare akan wani dakali da yake fuskanta gidan nasu. Tun baya ganewa har ya ganota suka fara gaisawa

Yafara sakar mata da kalamai. Shikenan fah ya hargitsa mata tunaninta

Kowa yasan soyayya suke

Ya sakar mata Murmushi cikin sanyin murya Yace Jamis tauraruwata yau baxa abari naxo bane

Series NavigationSamarin Bana Chapter 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *