Kwarya Tabi Kwarya Hausa Novles

Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 3

This entry is part 3 of 6 in the series Kwarya Ta bi Kwarya by Sadnaf

*PAGE 3*

Past

Hanne ce kawai take dokin komawa gidansu Zinatun dan Sule har ga Allah baya san zaman gidan Habun,a bai je neman abu ma a wajensa ba Yana wulakanta shi Ina ga ya koma cikin gidansa ya zauna,yasan sai abinda ya gani dan Zinatu bata da mutunci ko Habu bai wulakanta shi ba yasan Zinatu sai ta wulakanta su.

Gwaggo kudin da Habun ke dan bata ta d’auko gabadaya ta bawa sule tana “Yanzu kaje ka siyo muku kayan abinci kar ma ku tsaya wai neman wani abu a wajen sa duk ranar da Habu ko Zinatu suka muku wani abu sule ka tabbata ka fada min dan kallon Zinatu kawai nake duk abinda take yi na sani bana so na tab’a magana a dauka sa mata ido nayi dan tatse Habu kawai take ita da Yan uwanta.

 kudin da Habu yake kashe wa Yan uwanta ko rabinsa baya yi wa nashi Yan uwan.

A  baya ba haka Habu yake ba amma Zinatu ta canza shi gabad’aya dan da ya kashewa mutum biyar dinsa gwara ya zubar,ko ni nasan a babu yadda zai yi yake bani kudi dan nima kaina Sanin halinsa yasa ko bani da abu bana tab’a tambayarsa idan ka duba zaga ka har yanzu Ina kananan sana’a a cikin gida bana so na dora muku nauyina dan nasan duk kuna da iyali,duk Wanda ya d’auko ya bani na karba Wanda bai bani ba kuma shikenan”

A yanzu zama kawai zaku yi na wucin gadi har zuwa lokacin da Allah zai hore ma ka gyara gidan ka Hanne karki sake ki shiga harkar Zinatu dan nima nasan halinta”.

Gyada Kai Hanne tayi dan bata Jin zata aikata wani abu da zai hadata da Zinatun tunda har sun taimaka musu akan su zauna a gidan su.

Kafin su tafi gwaggo ta d’auko wani Karamin rishonta ta bawa Hanne akan su ringa sa kalanzir suna girki dashi tunda kamar ba zai yu su ringa amfani da itace a gidan Habun ba.

Har bakin kofa ta raka su tana kar su sake su b’oye mata duk abinda ake ciki su fada mata.

Haka suka baro gidan Hanne na murnar canjin wajen da suka samu Sule Kuma na tunanin canjin da zai na kawo masa b’acin rai dan yasan dole sai ransa ya b’aci.

A yanzu dagewa zai yi wajen neman kudi Yana samun kudin kwanun rufin zai fara siya ya rufe  gidansa yayi  daben kasa na tsakar gidan su koma haka.

Kudin da gwaggo ta bashi ba Karamin Dadi ya masa ba dan kayan abinci ya dan tsinta musu na kwana biyu dan da zai samu ba abinda zai na fito dasu daga bangaren nasu kar ma ace sunyi ba daidai ba, makaranta ne kawai zai na fito da su Ameera.

Koda suka isa gidan lokacin ana kiraye kirayen sallah Ishai.

Sai da suka kusa minti talatin a tsaye suna buga gidan dan Babu Mai gadi a lokacin.

Har sule ya fara tunanin su koma gidan Gwaggo dan yasan sun san sune sai sun wulakanta su zasu bude k’ofar.

Takun tafiyar da suka Jiyo yasa ya gyara tsayuwar sa ana Bud’e k’ofar yaga Habun ne da Kansa yazo ya bud’e k’ofar fuskar sa a hade ko magana bai musu ba ya juya ya koma ciki.

Sule kuwa haka ya taushi zuciyarsa suka shiga ciki da kayan abincin su,ganin bai san wajen da ya basu su zauna ba yasa ya hau kwallawa Habu kira dake ta zabga Sauri.

Fuska a hade ya juyo Yana kallon Sulen har ya karaso wajen da yake a tsaye.

Sule shi ma cikin hade rai ya fara magana Yana “Ni fa bani nace gwaggo ta ma magana ba Yaya Habu wallahi a Babu yadda zanyi zan zauna a gidanka Kuma in Sha Allah zaman namu ba Mai tsawon bane zamu bar ma gidanka in Sha Allahu “

“Sule kenan kaji nace maka wani abu Kafin kaje ka Kai karana wajen Gwaggo kace na hana ka zama nidai kazanta ne bana so ka fadawa matar ka gidanan tsaf yake kar azo a lalata min gida wancan part din zaku zauna da mukulli a jikin k’ofar”

Daga haka Habu ya juya ya bar shi atsaye.

Sule haka ya tsaya  har sai da ya b’acewa ganinsa har ga Allah da ace akwai yadda zai yi ba zai tab’a zama a gidan Habu ba, gwaggo dakunanta biyu bai san mai yasa ta hana su zauna acan ba.

Haka ya koma wajen su Hanne ya na  addu’ar shi ma Allah ya kawo masa yadda zai yi.

Hanne kuwa sai kalle kalle take tana washe baki dan Babu ko fitila a gidansu amma wanan gidan kuwa da haske su Ameera kuwa sai tsalle suke suna Anne kinga kaza kinga kaza dan ba yadda ba tayi su ringa kiranta da Umma ba amma sun saba da kiranta Anne tasan Hanne da Sule ke kiranta dashi yasa Suma suka taso da kiranta da Anne a madadin Hannen.

Suna shiga ciki Ameera Suka Fasa Ihun murna dan palon duk da ba komai tsaf yake ga haske ko ta Ina.

Hanne kanta kamar tayi ta tsallen haka taji,ko a mafarki bata tab’a kawowa kanta zama a cikin irin wanan gidan ba,bata manta yadda suke Yan guje guje da beraye da jaba ba daddare,bata manta yadda suke Yan guje guje da kadangaru da Rana ba dan dakin nasu ko filasta Babu.

Sule kuwa dakin da aka sawa katifa ya shiga da kayan nasu ya ajiye ko kadan bai ji wani farin ciki ba dan yasan ba gidansa bane ba.

Hanne kuwa kasa ma b’oye farin cikinta tayi ta bi sule cikin daki tana “Abban Ameera gani nake kamar mafarki nake wai yau mune a  irin wanan gidan kaga Saman kwanun ma ado aka masa babu alamar zai yi yoyo yanzu zamu iya baccin mu cikin kwanciyar hankali yanzu mun daina fargabar komai fa Ina ma yayanka ya ce mu zauna anan har abada ai da na kare rayuwata a bauta musu”

“Hanne nan ba gidana bane gidan yayana ne kuma zaman na wucin gadi ne ki daina mafarkin wai akwai abinda zai saka mu dawwama a gidanan in Sha Allah zan dage da addu’a ko wata guda ba zamu yi ba zamu bar gidanan dan haka dan Allah kiyi k’ok’arin godewa Allah a halin da muke ciki karki fara mafarkin kai kanki inda Allah bai Kai ki ba,Hanne idan ba makaranta ba bana so naga kafar su Ameera a waje tsakanin ki da mutanen gidanan gaisuwa ne ko ashana ne babu ban yarda kije ki karba ba”

Hanne kifta ido kawai take tana Jin zuciyarta ba dadi daga yadda Sule ke magana tasan ba wasa maganarsa.

A yanzu da suka samu waje dole su raba daki dasu Ameera dan daga ita har Sulen ba’a san ransu suke kwana dasu ba.

Dan sai su Ameera sun tafi makaranta suke iya samawa kansu nutsuwa.

Katon bargonta ta shimfidawa su Ameera a daya  dakin  ta zuba musu Abincin da gwaggo ta basu da suka taho dashi tare duk suka ci abincin dan daddare a faranti daya suke cin abincin sule ne dai yace ya koshi a yadda yake tasan Yana cikin damuwa bata san dalilin daya sa yake ta hade rai ba dan ba wani sanin abinda ya ke damunsa tayi ba gani take shine baya son taimakon da Habun ya musu.

Sai da su Ameera Suka kwanta har da Sadeeq ta tofe su da addu’a ta fito ta tadda sule a kwance idonsa a rufe gidan har wani kamshi yake mata tasan tana saka kanta a pillow bacci mai balain dadi da nutsuwa zai kwasheta.

Sai da ta kwanta a gefen sule take tambayar sa ko da abinda yake damunsa .

Sule girgiza mata Kai kawai yayi dan Sam baya san ma magana.

Hanne kuwa haka ta kwanta tana shakar iska mai dadi ko minti biyar ba tayi ba bacci mai balain dadi yayi awon gaba da ita.

Sule Shima Kansa ji yake Ina ma bangaren mallakinsa ne dan zuciyarsa ta sosu da ganin Hanne dasu Ameera nata murnar da yasan ba mai dorewa bace sai dai idan Allah ya canza musu kaddarar su ya Buda masa hanyar samu,Wanda yasan duk inda ya kai da kudi ba lailai ya iya gina irin wanan gidan ba.

Shima Kansa bai san ya akayi bacci ya sace shi ba.

Sai gashi sai da garin Allah ya waye suka Bud’e idonsu tsabar nutsuwar da suka samu dan da ace gidansa ne tun uku na dare sun tashi saboda guje gujen beraye.

Kasancewar asabar ce ba makaranta su Ameera zasu tafi ba,basu leka wajen ba suna ciki suka karya da kayan shayin da Sulen ya siya musu suna ta washe baki saboda shayin da suka Sha Ameera kuwa sai cewa take “Abba mun zama masu kudi ko”?

Murmushin yake yayi Yana “zamu yi kudi Ameera idan kinyi sallah ki ringa mana addu’a Allah ya bamu kudi”

Sai wajen goma ya shirya ya d’auki buhun kayansa na lebura Yana “Hanne anjima kadan ki shiga wajen Zinatu da su Ameera kina gaishe su sai ku dawo dan Allah daga ke har yaran nan kar kuyi abinda zaa mana magana dan a dofane muke a gidanan sun mana gargadi akan basa san kazanta ki sa ido a kan yaran nan”

“Zamu kiyaye Abban Ameera in Sha Allah”

Daga haka sule ya fito yayi hanyar waje a harabar gidan ya hango Habu a tsaye Zinatu taci kwalliya ta jingina da motarsa da alama wata maganar suke dan har Nuno bangaren Zinatun ke yi da hannu.

Can gefe Kuma Amjad da su Amrah ke ta wasa suna Yan guje guje.

Sule kuwa sam bai so haduwa dasu ba dan Yana gudun abinda zai Sosa masa rai sanin a gidansu yake cin arziki yasa ya karasa wajen su da sallama.

Zinatu kau da kanta tayi sai Habu ne ya amsa ciki ciki Sule kuwa ya gaishe su Habun ya amsa kamar ana masa dole Zinatu kuwa bata ko kalle shi ba bai bari bacin rai ya nuna a fuskar sa ba ya kalli Habun Yana “Na fita Aiki”

Kai kawai ya gyada masa yasa Kai yayi tafiyarsa Yana mamakin yadda Habun ke masa ba mai yarda shi ya Sha nono ya bar masa ba mai yarda wai Dan uwansa ne yake wulakanta shi haka dan kawai ba shi da kudi.

Hanne kuwa Sule na fita ta sa su Ameera a gaba suka nufi cikin gidan bayan tayi wa su Ameera gargadi akan kar su mata rashin Ji Sadeeq na rike a hannunta.

Musamman ta d’auko musu Sabin kayansu dan kar ma aga kazantar su ita kanta kayan kasan akwatin ta ta d’auko.

Koda ta shiga palon Amjad ne kawai ya gaisheta har Yana yiwa su Ameera wasa  Amrah Sultana da Bashir ido kawai suka zubo musu dan ba kowa a palon sai iya su kafin ta tambayi Amjad inda Zinatun take Amrah ta fara magana tana “Yaya Amjad su waye wanan”?

Murmurshi Hanne ta saki dan Su kan hadu da Amjad da Habu a gidan gwaggo yasan su yasan su Ameera sune ma dai basu fiye zuwa wajen Gwaggon ba shiyasa basu san su ba

Amjad ne ya bata amsa akan ita matar uncle sule ce su Ameera kuma cousin dinsu cikin fara’a yace “Aunty Kun dawo nan da zama ne”?

Hanne cikin sakin fuska da kaunar Amjad ta gyada kanta tana “Mun dawo nan Amjad Ina  umman ku take ka mana magana da ita”

Da saurin sa ya shige wani corridor Amrah kuwa dasu sultana suka turo baki suna musu wani irin Kallo duk da kankantar shekarunsu sun san kallon banza.

Abin ka da yarinta Ameera zagaye palon ta hau yi tana “Anne kinga wani katon abu Anne har da tv irin na gidansu Bala”

Ta Kai hannu ta fara shafawa Hanne na k’ok’arin daka mata tsawa Zinatu ta fito daga dakin tana “Cire min kazamin hannun ki da ga tv Ashe ku kuka shigo shiyasa nake shako wari tun dazu ni dai Ina ganin jarrabawa Ina zaune kalau an kwaso mana tarkace matsa min daga nan kafin na sumar dake”

Zinatu tace a tsawace wanda tsawan da ta daka wa Ameera yasa ta firgicewa ta saki ihu

Hanne da ta so zama akan kujera ta tsaya tana Jin zuciyarta ba dadi jikinta duk yabi yayi sanyi da irin tarb’ar da Zinatun ta musu su Amrah kuwa suka hau mata tambayar wai suwaye su Hannen

Hanne kuwa jiki a sanyaye ta hau magana tana “Kiyi hakuri maman Amjad Yarinta ne zuwa kawai muka yi mu gaishe ki”

“Baiwar Allah zuwan ki gidanan ya takurani ta takura yarana har ga Allah bana miki wani maraba da zuwa gidanan dan masifa duk cikin dangi ku rasa wajen Wanda zaku nemi zuwa gidansu sai nan gidan,ni duk abinda zai takura nida yarana sam ba kaunarsa nake ba da gangan mijinki yaje ya hada munafirci dan kawai ace ku dawo gidanan da zama har ga Allah ba zaku ji dadin zaman gidanan ba dan bana kaunar takura bangaren nan da kuke zaune kaji nake so na zuba dan haka idan kin koma ki kwashe muku kayanku ku koma dakin dake wajen gate dan gidan da kuka baro dai bai Kai shi ba balle kice zai muku kadan nan din zai ishe ku zama har zuwa lokacin da zaku bar gidanan”

Hanne da kanta ke kasa tana k’ok’arin Maida hawayen dake zubo mata Kai kawai ta gyada mata a daidai lokacin da Farida itama ta nufi wajen wani dan flawer Dan bata fi shekara hudu ba lokacin tana k’ok’arin tab’a flawer Sultana ta tureta Farida kuwa ta saki ihu dan ta bugu.

Ameera kuwa tayi waje da gudu dan gabad’aya ma tsorata ta suka yi.

Amjad kuwa ya hau yiwa Sultana fada Zinatu ta daga masa tsawa a daidai lokacin da Hanne ta daga Farida suka yi waje.

Sai a yanzu ta gano dalilin daya sa sule yake cikin damuwa idan har irin zaman nan zasu yi a gidanan dole su takura dan itama ba zata so a ringa wulakanta su ba.

Tuni taji zaman gidan ya fice mata a rai dan ba dan gwaggo ce tace su zauna ba da sai itama ta gwammaci ta koma gidan Gwaggo su zauna.

Tana kuka ta ringa jiddar Yan kayansu tana kaiwa dakin dake wajen gate din,dakin bashi da wani girma sai wani dan Karamin bandaki daga ciki.

Tana gama kwashe kayan Zinatun ta rufe part din ta galla mata harara dan a duniya ta tsani wani ya rabe su.

Hanne haka taci kukanta ta gode Allah ta dora Musu girkin Rana suka ci da su Ameera da suka yi tsuru tsuru ba kamar jiya da suke murna da zuwan su ba ta zuba musu abinci kenan Amjad ya shigo dakin lokacin bai Fi shekara goma Sha biyar ba cikin damuwa ya bata hakuri ta saki murmurshi tana babu komai ya Kara da zai gayawa Abbansu idan ya dawo girgiza masa kai kawai tayi akan ba sai ya fada ba kar ya wani damu.

Koda Sule ya dawo yaga wajen da Zinatu tace su koma ransa yayi mugun b’aci ji yayi kamar su tattara su bar gidan tuna idan har gwaggo ta san abinda Zinatun tayi hakan na iya jawo musu matsala yasa ya danne zuciyarsa yacewa Hanne kar ta damu zaman nasu na dan lokacine.

Ya d’auka idan Habun ya dawo zai magana sai yaga bai ce komai ba haka sule ya dage da neman kudi suka ringa zaman takura Babu alamar wani soyayyar Yan uwan taka sam a tare da Habun.

Dan idan su Ameera Suka shirya zasu tafi makaranta shi yake Kai su dan wani dan Karamin private mai balain saukin kudi ya Saka su biyun idan suka fito haka Habu zai fito da motar sa ya d’auki su Amrah da ke zuwa makaranta mai balain tsada ya wuce batare da ya musu tayin ragin hanya ba.

Gabad’aya daga shi har Hanne zaman takura suke a babu yadda zasu yi suke zaune.

Ba dama su Ameera su fito sai su Amrah sun zanne su har sukan musu Gori.

Amjad ne kawai yake kaunar su dan Zinatu har dukansa take saboda zuwan da yake wajen su yana wasa da su Ameera nama kifi su biscuit haka zai sato ya kai musu Hanne idan taki karba sai  ya nemi yin kuka.

Su Ameera kuwa dashi kawai suke sakin jikinsu dan sun san Amjad na kaunar su tasu ta zo daya da Ameera Zinatu ta rasa yadda zata yi dashi dan ko ta dake shi sai ya sake komawa wajen su.

Wulakanci kuwa da take wa Hanne ko kare ba zai d’auka ba.

Haka yaran nata Suma suke musu rashin mutunci Habun Kuma ko a jikinsa.

Sule kuwa bai bata fadawa gwaggo komai ba dan kudi kawai yake nema ya kuma kusa samun kudin dan yafi kowa san ya bar gidan.

A irin wanan lokacin watarana Gwaggo ta duro cikin gidan batare da sun san zata zo ba a lokacin Su Amrah na ta wasa a tsakar gidan su Ameera na daga gefe suna kallonsu kamar wasu marayu

Can gefe kuwa Zinatu ce a Zaune tana karkada kafa tana kallon yaranta cikin nishadi.

Shigowar Gwaggo gidan yasa gabanta yayi balain faduwa dan Sam bata San zata zo ba.

Bata San ya akayi Fareeda taje cikin su Amrah da tace suna zuwa kusa dasu suyi ta  jibgarsu ba dan so take azaba yasa su barin gidan.

Ihun Farida da sultana ke jibga yasa Ameera yin wajen su da gudu  gwaggo kuwa tayi turus tana kallon su a daidai lokacin da Hanne ta fito daga daki wajen gate din a guje dan Sam bata San ma sun fito ba.

Hankali a tashe Zinatu ta  hau dakawa sultana tsawa dan gwaggo kallonta kawai take Sultana kuwa ta hau cewa “Mummy kin manta kince idan sun zo cikin mu muyi ta dukansu har sai sun bar gidanan ba”

“Innalillahi sultana ni nace Miki haka”?

Hanne kuwa Farida ta dago tana “Ba na hana ku fitowa waje ba bakwa Jin magana ko ai ga irinta nan kin Sha duka Maza ku wuce mu tafi”

Da dan gudu su Ameera Suka yi wajen dakin gate din sai a lokacin Hanne ta lura da zuwan gwaggo ta washe baki tana ” gwaggo yaushe kika zo”?

Zinatu kuwa da duk ta rude ta hau sosa Kai tana “Gwaggo shigo daga ciki sannu da zuwa”

Gwaggo Hanne ta kalla da jajjayen idonta tana “Hanne mai kuke yi a wancan dakin”?

Present

Jiki na rawa Yar aikin ta zubo shinkafar Anne kuwa ta hau Jan hannun Ameera tana “zo mu tafi Ameera”

Ameera kuwa ta tsaya cak ba tare da ta motsa ba a daidai lokacin da Hajiya Zinatun ta karaso wajen su tana “sultana karbi shinkafar nan ki kifa Mata akanta kamar yadda ta kifa miki akan ki”

Sultana jiki na rawa ta sa hannu zata karbi shinkafar Amjad kuwa ya daka mata wani uban tsawa Yana “wallahi sai na sumar dake idan kika gwada zuba mata shinkafar nan Ameera kuyi tafiyar ku”

“Yaya kaga fa abinda ta min taya zaka ce ta tafi batare da na rama ba”?

Ameera tsaki taja ta juya tayi wajen dan Anne ta dade da yin waje.

Hajiya Zinatu kuwa cikin tsananin b’acin rai ta fara magana tana “Amjad Anya mutanen nan ba asirce ka suka yi ba kana cikin hayyacin ka kuwa?yarinya nan tazo har gida ta kifawa kanwarka shinkafa kace kar ta rama”

“Hajiya bansan yaushe zaku gane abinda kuke yi ba daidai bane karki manta arzikin nan ba mu muka bawa kan mu ba,a ganina ko wasu ke musu haka ke mai hana wacce”

Daga haka ya juya a fusace ya bar palon ko da ya fita bai ga alamar su Ameera ba.

Hakane yasa ya hau motar sa ya bi bayansu Yana Jin zuciyarsa Babu dadi…

Series Navigation<< Kwaya Ta bi Kwarya Chapter 2Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 4 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *