Kwarya Tabi Kwarya Hausa Novles

Kwaya Ta bi Kwarya Chapter 2

This entry is part 2 of 6 in the series Kwarya Ta bi Kwarya by Sadnaf

*PAGE 2*

Present

      Ameera yi tayi kamar bata ji shi ba ta cigaba da tafiyarta zuciyarta na san tilasta mata juyawa ta kalleshi a zahiri ba mafarkin da ta saba ganin sa ba.

Tana dab da tura k’ofar taji Anne na kwalla mata kira akan “Ameera baki ji Yayanki na magana ba”?

Sai da ta hade rai ta juyo fuska ba wani faraa har ya karaso wajen da take tsaye fuskar sa a washe Yana “Kanwata kina kallona kika d’auke kanki baki gani bane”?

“Yaya Amjad Ina wuni ya taro”?

Ameera tace kanta a kasa zuciyarta na bugu da ganinsa a gaban ta rabonta da shi tunda ya fita waje karatu

Murmurshi ya saki ganin Anne ta shige yasa ya dan matsa kusa da ita Yana “Ameera mai yasa baki tab’a nemana ba”?

A yadda yayi maganar yasa ta dago suka hada ido ta Kara Kau da kanta da sauri ta tura k’ofar tana “Bari na shiga ciki Yaya Amjad dan ba dade wa zamu yi ba”

Ameera da jikinta ke rawa ta shige da sauri tana Jin Yana kwalla mata kira da dan gudu ta tadda Anne dake dab da shiga cikin gidan.

Harabar gidan a cike da motoci kamar wajen siyar da motoci kaf gurin babu karamar mota.

A cikin sakani ta karewa gidan Kallo tana tuna irin rayuwar da suka yi a gidan duk da sauye sauye da canji da aka samu na zamanantar da gidan da akayi.

Tamke fuskarta tayi a lokacin da suka samu wawakeken palon da manyan mata ke zaune leshi na dukan leshi kamar gasar gwal ake dan duk kawayen Hajiya Zinatun sai walwali suke.

Anne jikinta rawa ya d’auka dan Sam bata ga kalarta a wajen ba sai taji ta muzanta ma da zuwan da suka yi ganin duk suna zaune akan kujera tuna Kuma wacce Hajiya Zinatun yasa ta fara k’ok’arin samu waje a kasan kafet ta zauna daga can gefe dan kadan da aikin Hajiya Zinatun ta ce su sauka kasa su zauna.

Ameera kuwa da sauri ta rike mata hannu tayi kasa da murya tana “Anne ya naga kina neman zama a kasa”?

“Ameera nima ban manta Hajiya Zinatu ba kar tazo ta disgamu a gaban mutane tace an hau mata kujera dan haka mu zauna a kasa idan ta fito muka mata Allah ya Sanya alheri sai mu tafi”

Ameera girgiza kanta tayi da sauri tana “Anne ba zai tab’a yuwa ba wallahi ba zamu zauna a kasa ba shi yasa tun farko da kika matsa min ke da Abba akan mu zo nace ba zan zo ba dan gudun irin wanan wulakancin dan haka tunda har muka zo wallahi Anne a saman kujera zamu zauna duk Wanda ya nemi ya wulakanta mu wallahi nima sai na wulakanta shi dan Allah ki zauna a saman kujera”

Ameera tace tare da samawa kanta wajen zama Anne sai da tayi Jim ta zauna a gefen Ameeran tana wurga ido da karewa palon Kallo dan itama ta jima rabonta da gidan Kuma gidan ya canza sosai ba kamar sanin da tayi masa a baya ba.

Daga ita har Ameera kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa duk sun tafi Tunanin rayuwar da suka yi a gidan.

Fitowar Amrah Amarya daga wani daki yasa Anne washe fuskarta dan idonta kyar a kansu ta Sha ado da wani material tana ta zabga kyalli gefenta wata ce itama da alama kawarta ce.

Ameera kuwa d’auke kanta tayi da ta mata Kallo daya duk da ta girme mata nesa ba kusa ba fuska a balain hade tana ta tunanin rashin kunyar da zata mata dan gani take ko Alhaji Habun  ne ya takata ba zata bar shi ba.

Suna zaune wajen Kujerar  dake bakin k’ofa.

Amrah kuwa wani irin Kallo ta musu kamar taga wani abin kyama ta d’auke kanta tana tunanin ko waye ya gayyace su.

Duk da tasan Anne tamkar uwa take a wajenta bata ko kalle  su ba ta sa Kai zasu fice daga palon tana dab da ficewa Anne ta tsayar da ita ta hanyar cewa “Amrah ki dan yi mana magana da Hajiya dan Allah ya Taron Allah ya Sanya alheri”

Ameera wani irin cije lebbe tayi saboda tsananin takaici dan Sam bata so Anne yi mata magana ba a ganinta duk lalacewa Anne matar kanin mahaifinta ce ko Yaya ne ta cancanci ta bata girma amma saboda wulakanci ta nuna Anne ma bata ishe ta Kallo ba”

Ameera wani irin dogon tsaki taja Amrah kuwa ta mata kallon sama da kasa tana “Ke wa kike wa tsaki”?

Ameera bata ko kalleta ba balle ta nuna ta san da ita take

Anne kuwa ta dan saki murmurshi tana “Amrah ba tsaki tayi ba kira mana Hajiyar”

“Tsaki nayi Anne idan akwai abinda za’ayi sai ayi”

Amrah gaban Ameera taje ta tsaya cikin mamaki tana “Mai kika ce”?

Ameera tsaki ta Kara ja Anne kuwa tana k’ok’arin magana wayar hannun Amrah ya d’auki Kara.

Kawarta dake bakin k’ofa tayi waje tana “kizo mu tafi tun dazu suke Jiran mu”

“Bari na dawo naji da abinda Kike takama da lokacin da na zama sa’ar ki”

Amrah tace ta zabgawa Ameera harara kamar wata sa’arta tayi waje ko kallon Anne ba tayi ba

Tana fita Anne ta rufe Ameera da fada  tana “Ameera bana san haka karki sake ki jawo min magana har mu bar gidanan mai amfanin abinda kika yi yanzu”?

Ameera bata ce komai ba a daidai lokacin da Autar  Zinatun ta fito Yarinya Sam bata da kunya duk da bata fi shekara goma Sha biyu ba.

Itama ta sha kwalliya da gwalai gwalai da less mai tsada kawayen Hajiya Zinatun kuwa sai washe baki suke suna kwalla mata Kiran “Samha Autar mummy kinyi kyau”

Baki ta turo irin na sangartattun yara ta nufi wajen wata da aka jera mata kalolin abinci daban daban a gabanta a dan zaman da Ameera tayi ta fuskanci yanayin kudinka yanayin tarb’ar da za a ma dan masu kudin ma da yadda aka tarb’e su.

Ji tayi duk ta gaji da zaman barin gidan kawai take so suyi.

Anne tayi wa magana tana “Anne dan Allah ki tashi mu tafi kina kallon ma kallon tarb’ar da muka fara samu da zuwan mu wai har ace kamar  Aunty Amrah bata San ta gaishe ki ba kina ta mata magana ta share ki ni bansan Mai yasa Abba ya matsa mana muzo ba bayan yasan daga hajiyar har yaranta ba mutunci ne dasu ba”

“Tunda har muka zo bai dace mu tafi ba tare da mun ga Hajiyar ba ki bari mu Jira ta fito bari na kira samha ta kira mana ita”

“Aaa Anne karki kira mana wancan yarinya dan wallahi dukan tsiya zan Mata idan ta mana rashin kunya”

Anne na k’ok’arin magana wasu Yan aiki suka fito da faranti cike da nau’ikan abinci da Lemo kala kala gaban wata suka ajiye abinci dayar na k’ok’arin komawa kitchen din Anne ta mik’e ta isa wajenta tana “Dan Allah ki yiwa Hajiya Magana kice Hannatu ce tazo matar sule”

Yar aikin kanta sai da ta dan kare mata Kallo kafin ta gyada mata Kai ta nufi Karamin palon da nan aka sauke manya manyan baki da a tsakiyar su Hajiya Zinatu ta baje dan su din na daban ne na palo Basu Kai su kudi ba.

Yar aikin na isa gabanta ta zube tare da kasa da murya ta sanar mata zuwan su Hanne din

Sai da ta yamutsa fuska ta fara magana tana “ita Hannatun ce tace ki zo kice min tazo na gayyace ta ne kaji mata zata zo ta bani kunya taga kalarta a gidanan ne?hmmm jeki Rabi idan ta gaji da zama zata tafi Ina ga Alhaji ne yaje ya gayyace su”

Rabi mik’ewa tayi ta bar Karamin palon.

Ameera da Anne haka suka yi zaman dirshan suna ta Jira dan Yar aikin bata dawo ta ce musu tana zuwa ba.

Ameera kuwa sai jera tsaki take dan Anne ta hana ta magana

Ganin sun tafi awa daya a zaune kamar ba Wanda ma yasan da wanzuwar su a Palon yasa Ameera ta fara magana tana “Anne dan Allah dan Annabi ki tashi mu tafi gudun iitn wanan wulakanci yasa nace miki kar mu zo kika dage sai mun zo gashi mun kusa awa daya a zaune ba Wanda ya bi ta kanmu ,tasan Kuma min zo fitowar ne kawai ba za tayi ba”.

“Baki da hakuri Ameera baki ga taro ake ba kila sallamar mutane take shi yasa bata fito ba idan muka tafi yanzu mai akayi kenan bayan zuwa mu kayi mu mata Allah ya sanya alheri”

Ameera a ba yadda za tayi taja bakinta ta tsuke yau banda Anne ce wallahi bata ga mai sawa tayi ko da minti biyar a gidan ba tasan Hajiya Zinatun ta san sun zo dan Yar aikin ta sanar mata fitowar ne kawai ba za tayi ba dan Matan dake zaune a palon sun fara mik’ewa daya bayan daya suna shiga Karamin palon dake d’auke da k’ofar glass.

Yan aikin kuwa sai Kai da kawowa suke suna direwa wayanda suka zo daga baya abinci su ko Kallo basu ishe su ba,ba Karamin tsana tayi wa familyn Alhaji Habu ba.

Sultana ce ta fado mata a rai ta dan wurga idanun ta tana tunanin ko Ina ta shiga dan kaf gidan idan akwai wacce take gwada mata mugun tsana sultana ce da suke kusan Sa’a daya kaf gidan ba mai girman kanta da wulakanci fitowarta daga wani corridor dake palon da tsinin takalminta yasa katse mata tunanin ta suka hada ido da ita.

Cingum kawai take taunawa tana yamutsa fuska itama sanye take da wani uban less mai tsada ta Sha awarwaron gwal har lokacin kallon juna suke kallon da Sultana ke mata na kaskanci yasa Ameera galla mata shegen harara taja tsaki tare da Kau da kanta tana addu’a Allah ya sa ta shiga sabgarta ta rama Marin da ta mata a baya.

Sultana kuwa wani irin murmushin mugunta tayi tana mamakin karfin halin Ameera da har take tunanin mai ta taka haka da  ta mata irin wanan kallon ta balain tsanar Ameera tunda ta fita komai bayan ita din kaskantaciya ce.

Wajen su ta nufa Anne kuwa ta saki fuskarta da ta ga sultana da murmurshi a fuskarta tana Isowa gabansu Sanin ba gaisuwa za tayi ba yasa ta fara magana tana “Sultana Ina Hajiyar ne tun dazu muka zo mun tura a mata magana ance tana zuwa”

Sultana sai da ta saki wani irin murmushin ta kama kugunta bayan ta harde kafarta tana “A tana sallamar Manyan baki ne da suka zo daga Abuja kinsan dole sai ta sallame  su zata fito”

“Aaa ya naga ba’a kawo muku Abinci ba dole ku gaji da jiranta tunda baa kawo abinci ba bari na sa a kawo muku ta hau kwallawa Yar aikin Kiran da ta iso gabanta da sauri Sultana cikin bada umarni tace ta kalli su Ameera ta je ta d’auko musu abinci

Ameera kuwa sosai ta ringa tausar zuciyarta wajen ganin ta taushi zuciyarta bata so ta biyewa zuciyarta dake ingizata akan ta tashi ta kwashe Ameera da mari dan tasan duk da biyu take wanan magana ganin so take ta nuna abincin da baa kawo musu ba yasa suka gaji da Jira yasa ta juyo a fusace Anne kuwa tayi saurin girgiza Mata Kai.

Ameera kuwa ta Kara Kau da kanta tare da Jan wani dogon tsaki dan har hannunta kaikaiyi yake tana addu’ar sauke wa Sultana yatsu biyar a fuskarta.

Sultana kuwa sai danne wayarta take ba jimawa sai ga Yar aikin ta dawo da farantin abinci tana k’ok’arin ajiyewa sultana ta daga mata tsawa dan abinci mai rai da Lafiya ta d’auko har da Rabin kaza.

Musamman tasa Yan aikin suka kwaba jollof da zasu rabawa duk talakawan da suka zo musu gida dan ta balain tsanar talaka a rayuwarta,balle da biyu za ta so wulakanta Ameera idan ta tuna abinda ta mata.

Umarni ta bawa aikin akan ita ba Wanan abinci tace mata ta d’auko ba ta mayar ta debo wani take Yar aikin ta dau haske ta koma da farantin   ta debo jollof din da nama yanka daya da robar zobo guda biyu ta kawo Sultana kuwa cikin murmushi ta sa hannu ta d’auko abinci ta ajiye a gabansu Ameera da robar zobon fuskarta fal da murmurshi tana “Ga abinci nan ku ci kafin ta fito”

Ameera jikinta rawa kawai yake da taga irin wulakancin da sultana ke Shirin Yu musu jiki na rawa ta mik’e ta Suri robar shinkafar kafin sultana ta ankara Ameera ta kifa Mata robar  akanta tana hucci

Sultana kuwa ta saki wawan Ihun konata da shinkafar yayi Ameera cikin hucci tace “Talauci ba hauka bane ba kinji ko ?duk da mu talakawa ne mun Fi karfin wanan abincin da kika sa aka kawo mana”

Sultana hannu ta daga cikin zafin nama dan ta kwashe Ameera da Mari taji an rike mata hannu ta baya.

Ameera kuwa tsaki taja tana “da tsautsayi yasa kin taba ni wallahi da sai kinyi nadamar zuwan ki duniya Anne tashi mu tafi Ameera tace cikin hucci a daidai lokacin da muryar Hajiya Zinatu ya ratso palon tana “Kizo min har cikin gida ki Kona min yarinya kiyi tunanin barin gidanan salin alin?Kai Kuma rike mata hannun da kayi na mene Amjad ka sakar mata hannunta a debo mata abinci itama ta kifa Mata akanta dan wallahi sai sultana ta rama abinda ta mata tunda ba ita ta dora Musu talaucin ba da zata hucce akan ta”

“Hajiya bai dace kice haka ba”

Anne tace cikin rawar murya Amjad kuwa da ransa yayi mugun Baci da abinda hajiya Zinatun ta fada na goyon bayan abinda Sultana tayi ya yarfa hannun sultana Yana “Hajiya wanan wane irin magana kike yi halan kin manta yadda muke da su”?

Tsaki Hajiya Zinatu tayi ta kalli Rabin da jikinta ke rawa tana “Ke jeki debo abincin nan ki kawo min yanzu nan wallahi sai sultana ta rama abinda ta mata”

“Hajiya karki ce haka”

“Hannatu na gayyace ku bikin nan ne”?

Past

Sulaiman duk yadda ya so hana gwaggo Kiran Habun da ya san ba zai tab’a bashi wai gidansa ya zauna na wucin gadi ba, yasan wulakanta shi zai yi amma gwaggo haka ta kafe har sai da aka kira Habun da ya shigo Yana kada mukullin motarsa.

Su Hanne na cikin dakin gwgago dasu Ameera gwaggo Kuma na zaune a falo da sule daya kame a gefe ya zauna dan ba abinda zai ce gwaggo zai zubawa ido yaga yadda zasu kwashe da Habu har yanzu Yana Jin haushin wulakanci da Zinatu ta masa zuwan da yayi,sallamar da Habun yayi kawai ya amsa sam bai yi niyyar mik’a masa hannu ba amma ganin gwaggo na zaune yasa da ya bashi hannu suka yi musabiha Habun ya samu gefe ya zauna Yana “Allah dai yasa lafiya gwaggo dan naga sule shi ma a gidan nan”?

“Lafiya lau Habu ba wani abu da yake faruwa, Habu a burina kullum naga yarana suna cikin farin ciki sun taso Kuma da hadin kai da zumunci da zai dore har karshen rayuwar su,ba abinda ke faranta min rai sama da ganinku tun bayan da mahaifin ku ya rasu”.

“Habu da Kai da sule da Ibrahim da Kabiru (Dan bature”

Dukan ku yarana ne duk ciki daya kuka fito damuwar mutum daya a cikin ku damuwa ta ce farin cikin mutum daya a cikin ku farin cikina ne.

“Habu nasan kana da kudi Allah ya ma arizkin da Kai kanka kasan ba ikon ka ko dabarar ka bace yasa Allah ya zabeka a cikin Yan uwanka yayi Maka wanan niima a cikin yarana Kai Allah ya rufawa asiri Wanda Ina ganin kamar duk mu Allah yayi wa rufin asirin nan,ba zan tsaya dogon turanci ba na dade Ina ma maganar jari akan ka bawa dan uwanka saboda kasan buga buga yake sai kace min baka dashi ka dan dora shi a hanyar da zai na samun kudi nan ma kace min baka da hanya naji ban damu ba dan shi sule ba rago bane har gobe bai tsaya Jiran sai ka bashi ba Neman na kansa yake a yanzu abinda yasa na kira ka rufin gidansa ya fita Kuma gidan na bukatar gyara a cikin gidajenka kananun nan Ina so ka bawa sule guda daya ya zauna kafin Allah ya hore masa ya gyara nasa gidan tunda duk arizkin ka ka kasa taimaka masa wajen gyara na shi gidan”

Habu shiru yayi Ya zubawa gwaggo ido har ta idda maganar ta sule kuwa Kansa na kasa bai ce komai ba dan idan har Habun da ya sani ne ba zai iya bashi Aron gida ba wani karyar zai yanko kamar kuwa ya sani dan Habu magana ya fara yi Yana “Gwaggo wallahi ba wani samu nake ba kema kinsani buga buga nake Yi akan me zan ki yiwa Sule hidima Ina da niyyar idan na samu kudi zan bashi wani abu dama amma a yanzu bani da kudi gwaggo,gidan haya Kuma da kike magana wallahi duk na siyar dasu na tura kudin dan akwai kayan da za’a kawo min daga can kasar china da ace kafin na siyar ne da gidan ne zan iya bashi Aron gidan ya zauna har zuwa lokacin da zai gama nashi gidan Kuma gwaggo duk abinda nayi wa nawa ai ban fadi ba”

Murmushi sule yayi ya dago ya kalleshi ya maida kallonsa kan gwaggo da ta zubawa Habu ido dan tasan bai siyar da tagwayen gidan da yake cewa ya bada hayan su ba dayan ba komai a ciki dayan ne aka kama tasan Yana da rowa bata San rowar na shi har ya kai haka ba”

Girgiza kanta tayi tana “Yanzu kana nufin gidan naka duk ka siyar kenan”?

“Ba karya nake ba gwaggo”

“Toh shikenan tunda har ka siyar da gidan naka yanzu abinda za’ayi Sule zai koma gidanka da zama tunda Yana da girma wanan bangaren da baka sa komai ba kasa a share a goge gobe zasu kwaso kayan su su zauna ko shi ma ka siyar da bangaren”?

Gwaggo tace ranta a balain bace tare da tsare Habu da ido sule na k’ok’arin magana ta daka masa wani mugun tsawa tana kar ya sake ya Mata Magana.

Ta cigaba da magana tana “tunda a yanzu baka da kudin da zaka bashi ya gyara gidansa gidan da zaka bashi Aro ya zauna shi ma ka siyar toh a gidanka zai zauna shi da iyalansa Kuma umarni nake baka kar naji kar na gani kasan dai nasan tsarin gidan naka Sule zai yi rayuwarsa da iyalinsa a cikin gidan har sai Allah ya hore masa ya gyara na shi gidan”

A yadda gwaggo ke hucci yasa Habu kasa magana dan duk abinsa Yana shakkar gwaggo dan arzikinn da yayi bai sa tayi wani rawar jiki a Kansa ba idan ya kuskure sai ta masa fada tun suna Yara ma sun fi shakkarta akan mahaifin su dan ta fi shi zafi,bai tab’a kawowa zata ce masa sule ta koma gidansa ya zauna ba da ya bar shi ya zauna a daya daga cikin gidan hayan nasa.

Yana Ji yana gani ya fito yana Allah ya kaimu goben zan sa a gyara dakin da zasu zauna.

Yana fita sule ya dago cikin sanyin murya Yana “Gwaggo ni zan nemo kudi na siyi kwanun a satin nan dan Allah ki bar maganar komowa gidan Yaya Habu wallahi ba zamu sake a gidan ba nasan halinsa na san halin matarsa gwaggo wulakanta mu zai yi”

“Na riga da na bada umarni sule gyara nake so na kawo a tsakanin ku duk ranar da Habu ya muku kallon banza ka zo ka fadamin ba yadda za’ayi Ina Raye na kawo ido na zuba muku kuna abinda ranku ke so tunda shi din marowaci ne nasan hanyar da zan bi dashi”

Sule a Babu yadda ya iya ya hakura dan kawai yayi wa gwaggo biyayya amma yasan zaman gidan Habun ba mai yuwa bane.

Hanne kuwa murna kawai take dan gidan Habun gidan masu kudi ne zata huta da kwanan fargaba da kwasar ruwa.

Gwaggo ce tasa aka tsinto musu dan abinda baza’a rasa ba ta tisa mai kurkura a gaba suka nufi gidan Habun washegari dan ba wani nisa ne dasu ba.

Zinatu kuwa kamar ta haukace a lokacin da Habu ke sanar mata dawowa gidansu da sule zai yi da iyalinsa dagewa tayi akan ba zata tab’a yarda kaninsa da matarsa har da Yara su zo su zaunar mata a gida ba taya ma zasu dawo gidan da zama”

Habu kuwa sai tsarata yake tana rantsuwar ko zasu zauna baa part din dake kulle ba sai dai Karamin dakin dake wajen gate.

Habu ce mata yayi ya yarda amma ta bari sai daga baya sai su tsiro da wata maganar.

Kamar zata fashe a lokacin da gwaggo tazo da kurkura ta karbi key daga hannunta ta bud’e daya part din tasa aka shigar da wadrobe da Yan kayan su Sule a ciki Palo daya ne da daki biyu kitchen da bandaki biyu a kowane daki.

Fuska a hade gwaggo ta rufo kofar ta isa part din Zinatun da zuwanta ta fara magana tana “Zinatu ke kika canja min Habu baa haka yake ba Zinatu ba zan bari ki raba min kan Yara ba wallahi duk ranar da kika daga kika wulakanta Sule da matarsa a ranar sai na baki mamaki kar naji kar na Gani Zinatu dan idan har zaki zama silar rabuwar kan yarana ba Abunda zai sa na zama silar mutuwar Aurenki kinsan dai Ina da Iko da karfin da zan saka Habu ya sake ki toh kar naji kar na gani”

Daga haka gwaggo ta juya ta bar palon Zinatu kuwa da ta cika tayi fam ta hau magana kasa kasa tana “Da kafar su zasu bar gidanan kuwa baki isa ki raba mu ba”….

Series Navigation<< Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 1Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *