Kwaya tabi kwarya Hausa Novels

Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 4

*PAGE 4*

Present

       Anne fada ta rufe Ameera da shi a lokacin da suka hau Napep tana “Da ace nasan haukar da zaki je kimin kenan wallahi ba zan tafi da ke ba sai naje ni kadai na dawo,akan me zaki kifa Mata shinkafa akanta tunda kinsan dan ta wulakanta mu ta kawo abincin ba sai mu ki kallon abincin ba akan me zaki zuba mata shinkafar?har wani abu suka Yi mana akan Wanda suka mana abaya,kina tunanin kin Isa ki rama wai duk abinda suka mana?shikenan duk sai mu zama daya dasu”?

“Anne a baya da suka wulakanta mu dan ban san ciwon kaina bane ba amma a yanzu wallahi ba zan tab’a iya jurewa ba Rashin taka musu birki yasa Muna haduwa dasu sai sun san yadda suka wulakanta mu duk da ba wani abu yanzu ake nema a wajen su ba can bayan ma ba tab’a nema akayi ba Anne da ace ni kadai suka yi wa wallahi ko kallon su ba zan yi ba amma tunda har dake suke so su wulakanta wallahi ba zan d’auka ba dan ko hajiyar ce da kanta wallahi sai na nuna mata baya da yanzu ba daya bane ba,naso d’auke sultana da Mari dan Ina nan sai na rama Marin da ta min a makaranta”

Ameera tace tana share hawayen da take ta k’ok’arin hana su zubowa dan har gobe ta kasa manta wulakanci da cutar da suka musu,abu ne da take ganin da wuya ta iya mantawa dan wani zubin sai taji dama su din ba jinin su bane.

Amjad daya fado mata a rai yasa taji bugun kirjinta ya canja.

Sam bata san sun ma karaso gidan ba sai da Napep ya tsaya a k’ofar gidansu.

Anne ta d’auko kudinsa ta bashi ita kuma ta fara k’ok’arin shiga cikin gidan a daidai lokacin da bakar mota ta tsaya a gaban gidan nasu,a sace ta Kalli motar take ta  gane Amjad ne ya biyo bayan su.

Gidan ta shige da sauri da ta ga Anne ta tsaya tana biyo su yayi?

Ameera kuwa ta k’arfi ta fara k’ok’arin danne abinda ke san taso mata dan har Amjad take so yaga canji daga wajenta.

Tana Jin muryar Anne na ce masa ai da ba sai ya biyo su ba ya kwantar da hankalinsa ba wani abin b’acin rai da aka musu,Anne ta hau bata laifin ma rashin kyautatawar da tayi akan da bata biyewa sultanar ba.

Ameera kuwa runtse idonta kawai tayi tana Jin tashin muryarsa da yake nuna rashin Jin dadinsa na halin kannensa da Hajiyar sa ya kara da “Na d’auka tunda shekaru sun ja duk zasu gane gaskiya su daina abinda suke yi wallahi bana Jin dadin abinda ke faruwa Kuma Abba yak’i tsayawa ya kawo gyara a tsakanin su yau fa idan ya fadi ya mutu Abba sule ne zai mayye mana gurbinsa, wallahi saboda irin wanan dabiar na Sha addu’a akan Allah ya kawo silar rugujewar arzikin idan har hakane zai saka su gane abinda suke yi bai dace ba”

“Karka wani damu kasan rayuwar ce yanzu duk ta canza wani zubin idan har kana da wanan kudin zaka ga Yana kada Maka gangar rashin gaskiya dan zaka d’auko wani hali ne mara kyau ka yafawa kanka bayan arzikin ma aro Allah ya bamu lokaci na zuwa zasu gane hakan da kansu dan akwai abinda kudi ba zai iya Samar Maka shi ba,rayuwa ce ta juya yanzu wai sai kana dashi kake mutum,amma matsawar baka da wanan kudin Kai da babu duk daya tunda na gane haka wallahi Amjad na daina damun kaina bama Kai kanmu inda Allah bai kaimu ba,zumuncin da gwaggo ta jaddada rukonsa yasa Muka je muku Allah ya Sanya alheri duk da ba Wanda ya gayyace mu iya Abban Ameeran aka kawowa kati amma muka ga dacewar zuwan namu muma”

“Anne dan Allah kuyi hakuri”

“Haba Amjad karka wani damu wallahi ko kadan banji haushi ba hasali Ameeran ce ma ta bani haushi dan na dauka yaci ta Saba da halin su,yaushe ka dawo ne”?

“Shekaranjiya na dawo Anne Ina Ameeran ne Ina so na ganta dan naga tayi fushi Anne”

Murmurshi Anne tayi tana “Tana daki bari na kira ma ita”

Ameera kuwa mik’ewa tayi da sauri ta shige bandaki dan ji tayi Sam bata san taga Amjad din duk da zuciyarta dake bugu da san ganin sa a zahiri ba kamar a mafarkin da ta saba ganinsa tana rayuwa dashi da tasan sai dai a mafarkin ba mai tab’a yuwa bane.

Bandakin Anne ta buga tana “Ameera kizo yayanki na kiranki”

“Anne dan Allah kice masa sallah nake Anne ni duk haushin sa nake ji kar nazo na masa rashin kunya”

“Ameera zan d’auki komai amma banda wulakanci idan kina da hallaci ma ko wani ke san wulakanta Amjad sai inda karfinki ya kare kafin na kirga biyar Maza fito ki same shi Yana Palo Yana jiranki”

Daga haka Anne ta fice daga dakin.

Ameera kuwa jikinta rawa kawai yake tana tsiyayar gumi kamar wacce zata je gaban dan sanda bayan shekara wajen biyar sai yau zata Kara tsayawa a gaban Amjad wanan karon wani daban take jinta ba kamar a baya ba.

Sai da ta saisaita kanta ta hade fuska tana dan Jin faduwar gaba ta fito daga dakin.

Ba kowa a palon sai shi kadai ya kuma kurawa dakin ido,d’auke kanta tayi da sauri da suka hada ido,dan bata ga alamar zuciyarta zata bata hadin kai wajen canzawa Amjad ba.

Dan nesa dashi ta zauna ta sunkuyar da kanta ta fara wasa da zoben azurfa da aka yiwa Harafin AA a hannunta

Amjad kuwa sai da ya dau tsawon lokaci Yana kare mata Kallo kafin ya kira sunanta

Ameera dagowa tayi ta kalle shi.

Amjad ya sakar mata murmurshi Yana “Na d’auka sai kin fi kowa farin ciki da ganina,amma sai naga baki wani nuna damuwar ki da ganina ba na miki laifi ne”?

“Laifin me zaka min Yaya Amjad ba laifin da ka min tsalle kake so nayi da na ganka ai nasan dole zaka dawo tunda bikin Aunty Amrah ake shi yasa ba zan mamaki dan na ganka ba.

Ameera tace cikin dakiya tare da Mai da kanta kasa

Amjad kallon Ameeran kawai yake cikin mamakin yadda ta canza mi shi kamar ba wacce da zai tafi har da kukan ta ba, ba dan bikin Amrah yazo ba saboda ita ya dawo dan yayi balain kewarta,duk sai yaji jikinsa ma yayi sanyi dan kwarin gwiwar da ya zo dashi ya gudu ya bar shi.

Sunanta ya Kara Kira ta dago ta sake kallonsa ta sake Mai da Kanta kasa dan idan har zata cigaba da kallon cikin idonsa  zata wargaza abinda ta shirya da take ganin shi ne mafita a gareta”

“Ameera banji dadin tarb’ar da kika min ba Ina ta dokin zan dawo na ganki sai gashi kin sage min gwiwa”

“Wai Yaya Amjad sai na goya ka kake so kasan nayi murnar ganin ka ai kasan yanzu na sake girma da hankali ba zai yu nayi ta wani tsalle Ina murna da ganin ka ba wai dan banyi murnar dawowar ka ba,Kai ma kasan ba zan tab’a manta hallacin ka a gareni ba kayi min abinda ba zan tab’a mantawa ba a rayuwa ta tsakanina da Kai sai fatan alheri”

“Laifin su Hajiya ne yake San shafata ko Ameera? Kema Kinsan ba haka kike ba kin canja din”

“Ba canja maka nayi ba Yaya Amjad Ina nan a yadda ka sani”

“Girgiza kai Amjad yayi ya na Jin wani fargaba a zuciyarsa gani yake Ameera ma saurayi tayi shi yasa ta canza mi shi duk da bai tab’a gwada mata wani alama da zai nuna yana santa ba”

Ajiyar zuciya ya sauke Yana Kara kallon Ameeran da ya ga ta mugun canza masa gabadaya kyaunta ya Kara fitowa sai glowing take ba kamar yadda ya tafi ya barta ba,dole ma Maza su sota idan har bai yi da gaske ba Yana ji Yana gani wani zai riga shi.

Ameera kuwa mik’ewa tayi tana “Yaya Amjad zan shiga ciki wallahi Ina da dinkuna da zanyi da gobe za’a karba”

“Na d’auka tunda kika gani ba zaki bi ta kan dinki ba”

“Yaya Amjad Mai kuwa zai hana ni bi ta kan dinki ,ko ka manta rufin asirin da dinki yamin”?

Murmurshi Amjad yayi Yana “Jeki kiyi dinkin ki Ameera ba zan tafi ba har sai Abba ya dawo mun gaisa”

Ameera da jikinta ke dan rawa tayi sauri ta shige ciki tana sauke ajiyar zuciya dan ta d’auka zata tonawa kanta asiri ya gano halin da take ciki.

Amjad kuwa hannun Sadeeq yaja ya Kai shi waje ya hau bugar cikinsa akan ko Ameera na da samari akwai masu zuwa sallama da ita”?

Sadeeq kuwa murmurshi yayi ya hau bawa Amjad labarin yadda Maza da yawa ke zuwa neman Ameera har kudi yake samu sosai ta silar Ameera dan kowa burinsa yaga ya bashi cin hanci ya kira masa Ameera ya bashi labarin wani daya nacewa Ameera ya Kara da kullum sai yazo”

Amjad hankalinsa ba Karamin tashi yayi ba idan har ya tsaya nauyin baki zai cutar da kansa.

Hajiya Zinatu da ta fado masa yasa gabansa faduwa daya tuna maganar da ta masa “Amjad na samo maka mata Yar babban gida wacce ta dace dakai kana dawowa zamu nemo Maka aurenta,bana Jin akwai wacce zata Kai ni farin ciki idan naga ranar  auren ka da jawaheer kasan silar auren nan zamu Kara suna mu shiga jerin manyan masu kudi”

“Hajiya Ina ga dai sai Ina so zan aureta ko”?

“Ko baka so Amjad wallahi sai ka aureta baka San mutuncin da zaka kankaro mana idan ka auri Yar gidan Ambassada ba”

“Hajiya ban miki alkawarin zan iya aurenta ba dan na lura ba dan Allah kike so na aureta ba dan wani biyan bukata kike so na auri Yar gidan Ambassada”

“Amjad zan Maka dole ne dan ban ga wacce zaka aura sama da jawaheer ba tunda har ita ta amince dole ka aureta”

Ajiyar zuciya ya sauke daya tuna maganar da suka yi da Hajiya Zinatu da ya zama tamkar karatu a wajensa dan kullum sai ta jadadda masa auren Jawaheer da ko kadan bata masa ba bai ma ga ta inda ta dace dashi ba.

Jiki duk a sanyaye yayi sallah Magriba ya ci tuwon shinkafar da Anne ta zubo masa dan Yana balain Jin dadin abincinta tun ma lokacin da suka zauna a gidansu.

Yana Jiyo karar keke daga dakin Ameera tun tana shekara goma Sha uku ta koyi dinki da karambani gashi yanzu ta zama expert.

Wajen bakwai da rabi Sule ya dawo daga shago Yana ganin Amjad ya washe baki Yana “Yaushe ka dawo Amjad dan dazu da naje daurin aure ban ganka ba”

“Ban samu zuwa ba Abba tun shekaranjiya na dawo”

Sule kuwa cikin tsananin farin cikin ganin Amjad ya zauna Ya hau tambayarsa Karatunsa.

Duk da yaci abinci sai da sule ya Kara tilasta masa ya Kara cin abinci.

Sai da suka gama Amjad ya fara magana Yana “Abba a yanzu da na dawo Ina so na Kara Maka tuni maganar da muka yi da kai abaya Ina nan akan bakata”

Sule kuwa take murmushin dake fuskarsa ta hau raguwa da yaga yadda Amjad yayi maganar da ya d’auke shi a matsayin wasa a lokacin

Ganin ya sake magana Yana “Abba kayi shiru”

“Wai kana nufin dama da gaske kake da kace kana san Ameera”

“Abba da gaske nake  Ina san Ameera da Aure”

“Amjad Kafi karfin Ameera Aurenka da ita ba mai yuwa bane ka barta ta auri daidai da ita Kai ma ka samu daidai da Kai a yanzu rayuwar da ake ta KWARYA TA BI KWARYA CE talaka ya samu Yar uwarsa talaka ya aura,Mai kudi ya samu Yar uwarsa mai kudi ya aura,Ina ga Kai ma Kafi kowa sanin iyayenka Kafi kowa sanin yadda suka tsani talaka ba zan iya baka auren Ameera ba kayi hakuri Amjad”.

Past

      Zinatu hankali a tashe tayi wajen Gwaggon tana “Gwaggo ki zo mu shiga daga ciki mana kika tsaya anan”

Ko kallonta gwaggo ba tayi ba ta cigaba da kallon Hanne da tayi kasa da kanta tana tunanin amsar da ya dace ta bata Gwaggo kuwa ta sake daka mata tsawa tana “ba tambayar ki nake ba mai kuke yi a dakin can”?

“Nan suka bamu Gwaggo anan muke zaune”

Hanne tace a hankali

Zinatu kuwa da duk hankalinta ya tashi da rutsa su da gwaggo tayi ta fara magana tana “Gwaggo wancan bangaren da aka basu yoyo yake Yana bukatar gyara shi yasa Baban Amjad yace su dawo nan kafin a gyara can din”

Gwaggo da jikinta ke balain rawa saboda bacin rai cikin wani irin murya ta Kara kallon Hanne tana “Hanne tun yaushe ta dawo daku dakin nan dan nasan Habu yayi kadan ya ketare umarni na kimin magana yanzu kafin ranki ya baci”

“Gwaggo washegarin da muka dawo gidanan da zama Abban Ameera yace na shiga na gaisheta da Yara,da muka je gaisheta shine tace na kwashe kayan mu na dawo dashi nan dan kiwon kaji za tayi”

“Innalillahi Hanne Mai na miki Zaki min irin wanan Sharrin ba Baban Amjad ne yace ku dawo nan din da zama ba”?

Hanne na k’ok’arin magana gwaggo ta daga mata hannu tana “Jeki Hanne”

Hanne kuwa ta nufi wajen dakin nasu da dan gudu Gwaggo kuwa ta zubawa Zinatu ido dake kikifta idanu tana soshe soshe

Rai a b’ace Gwaggo ta fara magana tana “Kin d’auka wasa nake miki da nace zan d’auki mumunan Mataki akan ki idan kika sake kika wulakanta Sule dan kawai Yana zaune a gidan dan uwansa,har nazo gidanan da kaina na karbi mukulli daga hannunki ki Kara karba ki korasu daga bangaren da Habun ya basu kice wai kiwon kaji za kiyi wato kaji sunfi su daraja a wajenki ko”?kin d’auka duk hidimar da Habun ke yi da gidanku bansani ba,?kin dauka bansan ya bawa dan uwanki kyautar gida ba”? Zinatu wai har dan Sule shi ma zai ci arzikin Habu kice ba Isa ba ki dauko kaskantacen daki ki bawa yarona kice ya zauna nan din gidan ubanki ne ko da kudin ki aka gina gidan”?

“Gwaggo karya Hanne ke min wallahi bani nace ta dawo dakin nan ba Baban Amjad ne”

“Sanin halin ke da mijinki yasa ban sanar muku da zan zo ba dan nasan dole sai Kun wulakanta Sule da matarsa,tunda har bakin ciki kike da arzikin da sule zai ci Habu ya gama aurenki a yau Zaki tattara ki koma inda kika fito dan nasan a gaba ma ni zaki sa ya juyawa baya wai har kice yaranki su ringa dukan yaran sule idan suka matsa kusa da su Zinatu?

Zinatu hankali a tashe ta hau rokon gwaggo tana rantse rantse,Hanne kuwa da ke tsaye tana Jin duk abinda ke faruwa ta dawo wajen Gwaggo da saurinta tana “Gwaggo dan Allah kiyi hakuri karki koreta karki rabata da yaranta akan mu iya wajen ma da suka bamu ya ishe mu gwaggo dan Allah kiyi hakuri”

Gwaggo kuwa tsaki tayi ta nufi cikin gidan tana rantsuwar sai Habu ya saki Zinatun.

Koda ta isa ciki har dakin Zinatun ta shiga ta hau watso mata kayan waje dan Zinatu ta Kai ta bango ko da Habu zai mutu sai ya rabu da ita dan sam Zinatun ba matuniyar arziki bace.

Tana tsaka da watso kayan Zinatun Habu ya dawo

Zinatu kuwa ta fashe da kuka da taga tashin hankali ya bayyana a fuskarsa da ganin gwaggo a cikin gidan

Yana k’ok’arin magana gwaggo ta daka masa tsawa tana “Habu a yau ba sai gobe ba ka rubutawa Zinatu takardar sakinta,dan ba’a yi macen da zata zo ta raba min kan yarana ba.

Habu har sule zaka Kai dakin waje da iyalinsa,?ka manta yadda kake da Sulen ne habu wai har ka fifita.matarka da Yan uwan ta akan dan uwanka”?

“Gwaggo dan Allah kiyi hakuri karki raba Zinatu da gidanan idan kika ce na saketa wa zai zauna min da yaran idan har akan sule ranki ya b’aci haka kiyi hakuri zan bashi mukullin Karamin gidana ya zauna da iyalinsa har zuwa lokacin da zai gyara na shi gidan”

“Ka riga da ka makara Habu idan har Dan nace ka saki wanna matar kace wai zaka bawa Sule mukullin Karamin gidanka ka bar shi ni Sule zai koma gidana da zama Amma wallahi sai ka saki Zinatu ko na tsine Maka”….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *