Kwaya tabi kwarya Hausa Novels

Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 5

This entry is part 5 of 6 in the series Kwarya Ta bi Kwarya by Sadnaf

*PAGE 5*

            Past

Hankalin Habu ba Karamin tashi yayi ba da yaga alamar Gwaggo da gaske take so take ya saki Zinatu da yake jin ba zai iya rayuwa batare da ita ba,dan Yana balain Santa kamar ya Ciro ransa ya bata,dan bai kawo ma zai tab’a iya aurenta ba dan  a cikin samarinta shine ma talaka san da yake mata yasa duk abinda take so jiki na rawa yake mata,da kuwa ya aureta sai ya cigaba da samun budi ko ta Ina hakan yasa ya Kara rike Zinatu gam Yana ganin kamar ita ce abokiyar arzikin sa,tana tambayarsa abu jiki na rawa yake mata.

Kamar zai yi kuka ya fara magana Yana “Gwaggo akan Sule zaki rabani da matata?akan sule zaki saka na saki uwar yarana”?

“A akansa zaka saketa Habu tunda har zata iya rabaka da dan uwanka,ai ba ita kadai ce autar mata ba balle kace idan ka saketa ba zaka samu wata ba,zaka iya canza ta amma baka isa ka canza Sule ba,dan Sule jininka ne shi,Har ace mace ita zata na juyaka tana dora ka a hanyar da bai dace ba,Ina Mahaifiyar ka nazo har cikin gidanan nace a bawa sule wajen zama bayan na tafi ta Kore ta ce Hanne ta kwashe kayan su ta  ta Kai su dakin waje ko almajirin ka ka bawa dakin waje ya  zauna Habu? da gaske nake rabuwa za kayi da Zinatu tunda har take san ruguza zumuncin dake tsakanin ka da Dan uwanka dama na rantse mata sai na nuna mata cewar ni na haifeka”

“Gwaggo dan Allah kiyi hakuri ba zan iya sakin Zinatu ba ki fadamin yanzu duk abinda kike so wallahi zanyi,ni daya Karamin gidan ma zan bar wa sule”

“Habu duk abinda kake yi nasani kallon ka kawai nake ban taba ma magana ba dan bana so ka d’auka ido na saka ma akan gidanka,bana so ka d’auka wai abinda kake dashi ya tsone min ido,Habu duk hidimar da kake yiwa Zinatu da Yan gidansu na sani,sarai har gidan da ka bawa dan uwanta yake zaune na sani,ban taba magana ba ban taba nuna Maka na damu ko kar kayi mata hidima ba,sai dan kanin ka zai ci arzikin ka sai ta hana ko kasan ba Sule kuka wulakanta ba ni kuka wulakanta Har wai tasa yaranta dukan yaran sule wai idan sunje wajensu,kasan Allah Habu ba abinda zaka fadamin ka rike gidanka karma ka bayar dan tun lokacin da na nemi ka bayar din baka bayar ba sai wai da kaga nace ka saki Zinatu shine wai zaka ce min zaka bawa Sule gida,toh ka rike gidanka ka ka bata takardar ta ta tafi gidansu idan tayi hankali ta gane darajar Yan uwanta ka  sai ta dawo”

Habu na k’ok’arin magana Zinatu ta Katse shi tana “Baban Amjad  ka sakeni kawai na tafi gidanmu Dan ba zan zauna a ringa nuna min kiyayya Kiri Kiri ba, ni banga wani abu da kake  yiwa Yan uwana  da za’a nemi goranta min ba,kaima kasan daga gidan da ka auroni,muna da namu rufin asirin, har mai nayi da za’a ce ka sakeni,idan ba tsana ta dama da aka yi ba,har ka kawo sule gidanan ban tab’a magana ko nace ma dan me ba,kawai hanya ce ake nema dan ka sakenin tunda dama can ba san aurena da Kai din ake ba anfi san Hanne sai ka sakeni ta aura ma wacce take so”

“Zan aura masa wacce tasan darajar zumunci,zan aura masa wacce zata nuna masa Mahimanci Yan uwansa zan aura masa wacce zata na dora shi akan turba ta gaskiya dan haka ki kwashe kayan ki ki tafi”

Zinatu dakin ta nufa a fusace har tana neman bangaje gwaggon.

Habu kuwa ya zube a kasa ya cigaba da bawa Gwaggo hakuri Yana “Gwaggo kina ganin kinyi min adalci yanzu akan sule zaki rabani da matata, gwaggo ko kinsan bambanci kike nunawa a tsakanina da sule,wato kinfi san farin cikinsa a kan nawa? Gwaggo duk abinda kika ce nayi sai da nayi ban tab’a bijirewa umarnin ki ba, Gwaggo duk da nasan zan takura da zaman sule a gidana amma haka na hakura nake zaune dashi iya haka bai Isa ba sai an sa na saki matata dan kawai an Kai shi dakin waje”?

Gwaggo da ta bala’in hade rai dan gani take ba abinda zai shiga kunneta sai fa Zinatu ta bar gidan dan ta dade tana tarata

Gwaggo na k’ok’arin magana sule ya fado palon kamar an jefo shi,ya nufi wajen Gwaggon ya zube a gabanta Yana “Gwaggo ki rufa min asiri karki sa Yaya Habu ya saki matarsa gwaggo abin nan da kike Shirin yi shi zai haddasa kiyayya a tsakanin mu dan zai ga kamar nine silar rabuwarsa da matarsa,gyaran Kuma da kike so ki samu kiyi sai dai ya lalace dan ba zai tab’a ganin farina ba,Wallahi ko sau daya ban tab’a damuwa da abinda Yaya Habu yake yi ba dan nasan komai lokacine ba abu dawamame da baya wucewa,duk da ni talaka ne Ina godewa Allah da niimar da yamin dan yamin arzikin da dubu suka rasa gwaggo fatana ki tayani da addu’ar tsawon rai da nisan kwana dan idan da Rai da rabo na shi rabon a kusa yake,kila nawa Yana nesa kowa da nashi kaddarar da arzikin dan haka gwaggo dan Allah karki raba shi da matarsa.

Nan da wani satin ma in Sha Allah zan gyara nawa gidan na koma”

Gwaggo shiru tayi tana nazartar maganar Sulen dan ya dawo da ita hankalinta dan idan har ta dage ya saki Zinatu kamar ta kawo hanyar rabuwar kansu ne da ayanzu ma gani take a raben yake tunda Habun baya iya jawo sule jiki,bata San wane irin haline da Habu ba,dan ba Karamin hidima yake yiwa mutanen waje ba sule ne dai ba zai iya taimaka wa ba,har ga Allah tana balain tausayin sule dan duk a yaranta ba mai tausayinsa,da san sadaukar da farincikinsa dan ya farantawa Yan uwansa,ya sha hakura da abincinsa suna Yara ba Dan ya koshi ba sai ya hawa Habu akan ya Kara dan Habu na da balain ci da hada musu ma abincin take ganin yadda yake handamewa yasa ta koma raba musu kwanu,Sule ba shida rowa ko kadan taso ace shi ne yake da kudin da habu ke dashi,tasan ba iya ita ba har makotan ta sai sun ci arzikinsa.

Ajiyar zuciya ta sauke ta Kalli Sulen da ke durkushe a kasa tana “Tashi Sule”

Sule mik’ewa yayi gwaggo kuwa tayi waje tana su biyo bayan ta tana san magana dasu.

Habu kuwa da ke balain Jin haushin sule shi ya fara yin wajen sule ya bi shi a baya.

Dakin su Hanne gwaggo tayi tana zuwa ta tsaya daga bakin k’ofa tana karewa dakin Kallo,dakin Karamin ne sosai dan katifar kawai ta cinye dakin da wadrobe din da ka sa ba wani space sai dan wajen da ta ga an shimfida sallaya.

Hanne kuwa da su Ameera suna daga bakin k’ofar dakin sun dan shimfida tabarma.

Gwaggo kuwa duk inda ta Kai da ta daure sai da ta rushe da kuka a daidai lokacin da ta zauna akan sallayan Habu da sule suka zauna a kasa duk hankalin su a tashe da kukan da Gwaggo take yi,Habu kuwa ya fara magana Yana “Gwaggo dan Allah dan Annabi kiyi hakuri yanzu nan zan Maida kayan wancan bangaren”

“Habu wai sule kake wulakantawa haka dan kawai ba shi da kudi,yanzu sule ka kawo sirrin dakin nan dan kawai bashi da kudi,Habu karka manta arzikin nan na Allah ne,Allah daya baka zai iya bashi shi ma duk girman gidanan da manyan dakunan cikin gidanan wai ka rasa wajen da zaka bawa Sule ya zauna da yaransa har su uku sai daki daya jal karami Anya kana da Imani kuwa?sule fa dan uwanka ne uwa daya uba daya,yanzu ko wani kaga Yana so ya wulakanta shi ba sai inda karfinka ya kare ba amma habu da kanka kake wulakanta dan uwanka,ka manta yadda kuka taso da san juna da hadin kai,yanzu macece zata sa ka juyawa dan uwanka baya dan kawai bashida kudin da bashi ya hana Kansa ba,tun Ina rayye kenan habu Ina ga na kwanta dama ko kasan wanan rarrabuwar kan naku zai iya kaini kabarina da wuri?ko kasan babban burina naga Kun taso kanku a hade waje daya, yaran ku Suma su taso a haka,yanzu ba zaka iya rufawa dan uwan ka asiri ba kenan”?

“Dan Allah gwaggo kiyi hakuri nayi kuskure zan gyara wallahi rashin zama ma da bana yi yasa ban lura ma nan din suka dawo ba amma in Sha Allah zan gyara gwaggo idan Yan uwana basu ci arzkina ba suwa zasu ci”?

“Yan uwan matarka habu su suke cin arzikin Kuma su zasu ci,dan da ace dan uwanka zai iya cin arzikin ka ba zaka ajiye shi anan ba”

“Gwaggo dan Allah ki daina dagawa kanki hankali wallahi ba abinda Yaya habu yayi da zaki damu kanki dan wallahi ban ga laifinsa ba dan tsakani da Allah akwai takura zaman wani a gidanka tunda har na samu kudin yanzu saura kadan dan Allah ki bar maganar nan Gwaggo”

Gwaggo hawayenta ta share tana “Habu ko koyi kyautatawa Yan uwa saboda arzkinka yayi albarka Habu baka da sama da Yan uwan ka zaka iya canza mata baka Isa ka canza Ibrahim Sule da dan bature ba duk lalacewa duk talaucin su Yan uwanka ne idan ka wulakanta su tamkar kanka ka wulakanta Habu dan Allah karka bawa matarka k’ofar da zata raba kanku wallahi zan iya mutuwa idan kanku ya rabu Ina so zumuncin ya dore a tsakanin ku har yaranku su girma su taso da hadin kai da zumunci Ina so yaran ku su taso da kaunar junansu har aka sa  gane waye ya haifi wani”

“In Sha Allah Gwaggo zan gyara sule ba rowa nake ma ba da gaske lokacin da gwaggo tace na baka gida na siyar ba kuma ni da kudi amma yanzu na samu kudi zan iya baka wani abu ka dan gyara gidan”

Gwaggo da Sauri ta fara girgiza kanta tana “A yanzu bana so sule ya bar gidanan anan gidan nake so ya zauna saboda wani dan dalilina idan lokacin barinsa gidan nan yayi da kaina zan zo na ce su kwashe kayan su,amma a yanzu anan nake so Sule ya zauna da iyalinsa,Ina so yaranku su taso da kaunar junansu dan matarka ta cusawa yayanka kin yaran sule a gaban idona wanan yarinya nan Mai kama da babarta ta hau doke takwara ta wai matar ka tace suna zuwa kusa dasu a dake su,Sule dole kayi min biyayya ka jingine batun gyaran gidanka a gefe a yanzu ka cigaba da neman kudin da zaka sauke nauyin iyalinka  dake kanka,Habu wanan karon naci damara wallahi duk ranar da na dawo gidanan naga an wulakanta Sule da iyalinsa wallahi a ranar sai Ka rubutawa Zinatu saki uku kaga na rantse,kana da kudin da zaka iya daukewa sule nauyin kayan abinci kana da kudin da zaka iya bashi jari shi ma ya tsaya da kafafunsa amma ba zan ma dole ba dan Sule Yana da zafin nema In Sha Allah watarana zaa dace”

Habu a Babu yadda zaiyi yaja bakinsa yayi shiru dan har ga Allah yaso sule ya bar masa gidan dan Zinatu ba ranar da garin Allah zai waye ba tayi maganar zamansu sule da tace ya takura ta ba,ya d’auka idan yace wa gwaggo zai bawa Sule gida zata bada goyon baya sai gashi ta dage akan a gidansa zai zauna.

Sule ne ma yayi ta magiya akan gwaggo ta barshi ya gyara gidansa shi ma sai yafi samun nutsuwa amma gwaggo Fir taki tana zaune tace Hanne ta fara kwashe Kayansu tana kaiwa bangaren da aka fara basu itama sai da tayi Jim dan har ga Allah bata San wulakancin da Zinatu ke musu tana zaune aka kwashe komai har habu na taya su.

Gwaggo kuwa ta tilastawa Habu kwaso kujerun da ta gani a lungun gidan,dan sababi ya sauyawa Zinatu tsabar rowa da su bayar gwara su ajiye ya lalace, Gwaggo kuwa sai da ta sa  habu ya jiddo kayan abinci bayan an jera kujeru a palon ta zauna ta Kara yiwa habu da sule nasiha,kafin tace habu yaje ya kira Mata Zinatu tana so suyi magana.

Habu kuwa sai da ya Sha wahala kafin ya samu Zinatu ta tafi Kiran Hajiyar dan dagewa tayi ita gidansu ma za ta tafi dak’yar Habu dake neman yi mata kuka ya shawo kanta,duk da kasan zuciyarta murna take da baa saketan ba,dan hankalinta ya tashi da sakin da gwaggo tace habu ya Mata.

Gwaggo kuwa fuskarta d’auke da murmurshi ta ringa kallon su Ameera dake murna da kujerun dake jere a palon sai tsalle suke suna hawa Kai.

Shigowar Zinatu palon yasa gwaggo dan rage murmurshi da fuskarta ke d’auke dashi sai da Zinatu ta zauna Hanne itama tana da ga daya barin kanta a kasa, Gwaggo ta fara da bawa Zinatu hakuri akan abinda ta mata ta Kara da ranta ne ya b’aci shiyasa ta mata barazanar saki.

Dan ba uwar da hankalin ta ba zai tashi ba idan taga kan yaranta sun d’auko hanyar rabuwa.

Nasiha sosai Gwaggo tayi wa Zinatu da Hanne akan su taimaka wajen hadin kan su Habun.

Zinatu kuwa tunda taga tsofafin kujerun ta a palon da zaman da akace zasu yi na ba ranar barin gidan taji kanta na Sara mata,duk abinda ma gwaggo ke fada ba jinta take yi ba.

Har sai da taga alamar Gwaggo na Shirin tafiya ta dawo hayyacinta suka raka har wajen motar Habun da yace shi zai kaita gida, gwaggo kuwa ta dage da kar taji kar ta gani.

Habu da Zinatu akan dole suke zaune dasu sule dan Zinatu kamar ta dauko fetur ta Kona su haka take ji.

Canja takun ta kawai tayi amma sai ta kori sule daga gidanta cikin ruwan sanyi.

A haka su Sule suka ringa rayuwa a takure dan Habu Kara nesanta kansa yayi da Sulen,dan fa tunda akansa Gwaggo taso ya rabu da Zinatu yake Jin haushinsa.

Amjad ne kawai yake shiga wajensu dan shi Yana balain san sule da su Ameera tun Zinatu na dukan sa har sai da ta hakura ta daina dukansa.

Su Ameera kuwa yanzu basa ma gangancin zuwa part din su Zinatun dan sau daya tsautsayi ya kaisu shiga da suka Jiyo karar tv,suna da san Kallo hakane yasa suka shiga palon ganin iya Amjad ne a palon yasa Ameera saurin zama a gefen sa ta tankwashe kafa ta zurawa tv ido.

Ball din da akayi da ita ya sa ta sakin ihu.

Amjad kuwa ya juya da sauri yaga Zinatu ce tayi ball da ita cikin hucci ta fara.magana tana “duk ranar da kika Kara taka kafarki kika shigo min Palo sai na ballaki shegu mayyu kawai”

Ameera a guje ta fita tana kuka Amjad kuwa ya mik’e Yana “mummy bana san Abunda kike wa su Ameera wai mai suka miki haka kika tsane su”?

“Amjad bace min da gani dan baka da hankali da kana da hankali ba zaka tsaya min tambayar nan ba”

Tunda ga ranar Ameera bata Kara zuwa part din Zinatu ba Sultana Amrah kuwa ba karamar kiyayya suke gwada mata ba dan ko Yaya tsautsayi yasa suka hadu sai sun kirata mayya sunce musu su bar musu gidan uba,tun Ameera bata ganewa har sai da tazo tana ganewa.

Ta Sako sule a gaba da Hanne akan su bar musu gidan nan ita bata san abinda su Amrah ke musu.

Sule murmurshi kawai yayi ya hau bata hakuri akan kar ta damu.

Ameera kuwa duk da ba makaranta private mai balain tsada aka saka ta ba wani irin kwakwalwa Allah ya bata dan masifar k’ok’ari ne da ita.

Idan ta zauna da Amjad suna dan karatu haka Amjad zai ta mamaki dan su sultana Zinatu tasa sun lalace ba wani k’ok’arin da suke dashi sama da shagwaba gashi makaranta mai balain tsada suke zuwa.

A haka suka ringa rayuwa a gidan duk a takure.

Gwaggo taso Habu ya d’auki nauyin karatun su Ameera amma yayi ta kwana kwana har sai da ta hakura.

Kiyayyar da Zinatu ke gwadawa su Hanne kuwa Kara gaba yake yi dan Yar aikinta taso Maida Hanne haka kawai zata tura a kirata akan tazo ta mata shara ko ta wanke kayan su sultana.

Da farko Hanne bata kawo komai ba da zuciyarta daya tayi aikin da ta bata, daga baya da ta gano dan kawai ta wulakanta ta yasa take sa ta aiki yasa ta daina zuwa ba kuma ta taba fadawa sule ba dan tasan zai iya Jin haushi.

Shekarar su daya wata rana da yamma wajen shidda na yamma a irin lokacin sule yake dawowa gidan.

Zinatu na labe ta labule ta ga ya dawo zai yi part din su,da sauri ta tura Amrah akan taje tace yazo injita ta Saka gudu.

Amrah a guje tayi wajen Sulen da ke dab da isa bangaren nasu.

Zinatu kuwa tayi sauri ta koma dakinta ta gyara daurin kirjinta tana girgiza kai cikin mugunta.

Sule kuwa cikin mamaki ya Kara tambayar Amrah Yana “Umman taku ce tace nazo?

“A Itace tace kayi Sauri”

Sule cikin daurewar Kai  ya nufi part dinsu Zinatun Yana mamakin Kiran da take masa.

Yana Isa bakin k’ofar palon ya fara Jiyo Ihun Zinatu daga daki tana rafka sallati a taimaka mata miciji.

Sule da balain sauri ya nufi inda yake Jiyo muryar ta ganin dakin a Bude yasa ya dan daga labulen Yana “Zinatu a Ina micijin yake”?

Bai gama rufe baki ba yaji an jawo shi ciki Zinatu ta danna mukulin k’ofar ta saki zanin kirjinta ta fara kwalla ihu tana  a kawo mata agaji sule zai mata fyade,a daidai lokacin da Habu ya shigo palon muryar Zinatu da yaji yasa yayi dakin a guje Yana Kiran sunan Zinatu…

Series Navigation<< Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 4Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 6 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *