Kwaya tabi kwarya Hausa Novels

Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 6

This entry is part 6 of 6 in the series Kwarya Ta bi Kwarya by Sadnaf

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*

*PAGE 6*

            Present

Amjad kamar Abba sule ya buga masa gudumma haka yaji cikin rawar murya da tashin hankali hana shi Ameera da yake neman yi ya fara magana Yana “Abba karka manta kace duk abinda nake so idan har bai fi Karfinka ba zaka min shi,karka manta kafin na tafi karatun nace ma Ina san Ameera kace min kar na damu bata da miji sama dani,Abba na taso da kaunar Ameera a matsayinka na mahaifina ban b’oye ma ba,kayi min alkawari zaka bani ita mai yasa yanzu zaka hana ni ita saboda wani dalilin da nasan bai Isa ya hana ni auren Ameera ba idan ba Allah ya rubuta Ameeran ba matata bace Abba a yanzu da na dawo so nake na auri Ameera dan Allah kar kace dan su daddy ba zaka bani auren ta ba”

Abba sule girgiza Kansa yayi cikin tausayawa Amjad dan ya amsa mi shi ne a wancan lokacin dan kawai ya kwantar masa da hankali ya kuma d’auka da wasa yake kila yarinta yasa yace Yana san Ameera sai gashi ya dawo da maganar San auren Ameeran da yasan ba mai yuwa bane

Sunan Amjad ya kira Yana “Amjad ba abinda ba zan iya Maka ba saboda Kai Dana ne idan kaga na kasa ma abu toh ka tabbata yafi karfina ne,auren ka da Ameera ba  mai yuyuwa bane Wanda Kai ma kasan dalilina a yanzu da muka dan dawo da zumuncin mu da Yaya Habu bana so wani abu ya sake hadamu dashi,Kafi kowa sanin wacce Mahaifiyar ka ka kaddara Yaya  Habu ya yarda ka auri Ameera Kai ma kan ka kasan Mahaifiyar ka ba zata tab’a yarda ba.

 nasan duk da wayonka duk kasan mai ya faru taya zaka iya auren Ameera kayi hakuri ka bar maganar nan zaka samu wacce tafi Ameera in Sha Allah.”

“Ba zan iya Rayuwa batare da Ameera ba.

 Abba idan har Ameera bata haramta a gareni ba ba Wanda zai iya hana ni aurenta,  Daddy da Hajiya ba zasu min Auren dole ba,dole su so abinda nake so,saboda wani dalili nasu ba zan ki auren wacce na taso da kaunar ta ba akan Ameera na fara Sanin so.

Abba Ina san Ameera da Aure ka riga da kayi min alkawari na Kuma yarda zaka bani din idan kaga Daddy yazo nema min Aurenta.”

Murmurshi Abba sule yayi dan yasan Yaya Habu ba zai tab’a taka kafarsa yazo gidansa nemawa Amjad auren Ameera ba zai biyewa Amjad kawai dan kar ya d’auka matsalar da ga wajen sa ne a fili kuwa sai yace  ” idan har su da kan su suka amince ma akan ka auri Ameera ni kuma zan baka Aurenta,sai dai kafin ka fada musu  kana santa  ai Ina ga ya kamata ka fara fadawa Ameera kana Santa ko? kar tana da Wanda ita take so”

“Abba tana fita zance ne”?

“Akwai wani Yaro Sahar Yana zuwa wajenta sai da ya zo ya nemi iznina kaga ba zan iya hana Ameera zance ba tunda ta kai munzalin auren”

“In Sha Allah Ameera bata da miji sama dani Abba zanyi k’ok’arin magana da ita kafin daddy yazo.”

Murmurshi Abba sule yayi Yana “Toh Allah Ya muku zabin da yafi alheri Amjad”

Daga haka suka dan tab’a hira Amjad ya masa sallama ya fito daga dakin yaso yiwa Ameera magana a ranar sai dai Kuma ya fasa saboda baya so yayi gaggawa.

A  yanzu zuciyarsa cike take da fargaba,dan tunda yaji akwai wanda yake zuwa wajen ta zance yaji hankalinsa ya kasa kwanciya,Yana tsoron Ameera ta k’i amsa tayin soyayar sa duk burinsa a rayuwa na Auren Ameera ne,kafin ya tafi wani irin shakuwa yayi da ita, tun lokacin yaso sanar mata Yana santa,sai yaga kamar bai dace ya fada mata ba a wanan lokacin tunda bama ta gama secondary ba,kalar Shakuwar da suka yi da Ameera yasa yake ganin zata so shi dan har dan hannunka mai sanda ya ringa mata,shekara biyar daya diba a can Yana karatu ba Karamin takuruwa zuciyarsa tayi ba,dan zuciyarsa na nan a makale da kaunarta burinsa ya gama karatu ya dawo,wayar da yake dan yi da ita jefi jefi ke dan kwantar masa da hankali, hotunan ta kuwa kusan duk shi ya cike masa  waya,baya Jin akwai macen da zai so kamar Ameera.

Koda ya Isa gida mutane sun ragu sosai dan a ranar za’a Kai Amrah dakinta da alama ma an kaita dan sai tsirarun mutane.

Sai da ya fara shiga dakinsa yayi wanka yayi sallah ya fito palon gidan da Yan aikin gidan nasu suka gyara tas Kamar ba’ayi taro a gidan ba.

Alhaji abubakar na zaune da Hajiya Zinatun da alama wani tattauna suke Samha tayi matashi da cinyar Hajiya Zinatun da take shafa gashinta.

Ganin sa da suka yi yasa suka yi shiru har sai da ya karaso ya zauna a Kujerar dake fuskantar su ya dakawa Samha tsawa Yana “Maza tashi zaune kafin na gaura miki Mari kin d’auka ke yarinya ce”?

Samha mik’ewa tayi tana turo baki cikin shagwaba har ta mik’e Hajiya Zinatu ta maida ita ta zauna ta galla masa harara

Alhaji Abubakar kuwa kallon Amjad kawai yake Yana Jin wani irin farin ciki dan a rayuwarsa ba wanda yake balain so bayan Zinatu sama da Amjad,wani irin so yake masa da zai iya masa komai shiyasa sai da ya zabi makaranta mai balain kyau da tsada a can kasar wajen ya tura shi can da yayi degree dinsa da masters.

a  yanzu ma haka ya dankara masa wani katon gida  ya bud’e wani sabon plaza da sunansa shine gudummawar da yake so ya bashi a matsayin sannu da dawowar da yayi daga waje.

Amjad  kuwa cikin takaicin maida Samha cinya da Hajiya Zinatun tayi  ya fara magana Yana “Hajiya ke kike shagwaba yaran nan  shi yasa suke duk abinda ransu ke so”

“Na shagwaba su Amjad kaima sai da ka girma ai ka daina shagwabar,

kar ka sake ka takura min Yara daga dawowar ka ma ka fara akan Sultana

Da aka zo har cikin gida aka watsa mata shinkafa ka hana ta ramawa wallahi dazu banda taro ake yi Amjad da kayi kadan ka hana sultana Rama abinda Ameera tayi mata”

Hajiya Zinatu tace tana jin wani sabon b’acin rai hana sultana da yayi rama abinda Ameera ta mata dazu.

Amjad kuwa magana ya fara  yi Yana

“Hajiya har tsawon wane lokaci za’a cigaba da tafiya a haka?shikenan yaran nan basu da wani aiki sama da su ci mutuncin Yaran Abba sule,ko Aunty Hanne basu bari ba?karki manta fa Abba sule da Daddy uwarsu daya ubansu daya karki  manta Ameera tamkar yayanki ne tunda daddy yayan Abba sule ne, akan me zasu ringa dora musu Karan tsana kema kina nuna musu kiyayya Karara,ke kanki kinsan irin rashin mutunci da su sultana suke yiwa su Ameera Hajiya baki tab’a tsawatar musu kin Hana su ba sai dai ki ringa goyon bayan abinda suke yi, duk Wanda yazo taya ka murna ai abin ka tarbe shi ne da hannu biyu,amma daga zuwan su Sultana sai ta tare su da rashin mutunci.

Wani irin tsawa Hajiya Zinatu ta daka masa tana “Amjad ka rufe min baki kafin na gaura ma Mari ni na fito nace ma na tsani kanin mahaifinka da matarsa ni da kaina na fada ma haka?

Ban tsane su ba halinsu na tsana Kuma su ne suka dora mana Karan tsana saboda arzikin da Allah ya mana ba mu muka dora Musu Karan tsana ba na d’auka zaka san ciwon kanka idan ka dawo ashe har yanzu baka san ciwon kanka ba toh wallahi Amjad ka shiga hankalin ka”

“Ya isa haka Hajiya

Amjad tashi ka tafi dakin ka”

Alhaji Abubakar yace dan  yanzu Yana nuna goyon bayansa akan maganar Amjad Hajiya zata birkice masa.

Amjad na k’ok’arin magana Alhaji ya ce ka  tafi dakinka nace”

Amjad mik’ewa yayi ransa a b’ace ya nufi dakinsa da zuwansa ya zube akan gado,Yana Jin wani sabon tashin hankali na rufe shi dan a yadda yake ganin Hajiya Zinatun na gwadawa su Ameera kiyayya kafin ta yarda da Auren Ameera za’a Kai ruwa rana.

Amjad na shigewa Alhaji Abubakar ya fara magana Yana “Hajiya halan kin manta dan naki tun yana yaro haka yake da taurin Kai ai duk abinda zaki Fada masa ba zai tab’a ganewa ba,ki bi shi a hankali karki manta yanzu lallaba sa muke so muyi mu samu ya auri Jawaheer”

“Ai Alhaji idan ba taka masa birki nake ba haka zai cigaba da min wanan haukan ace kamar Amjad Sam bai San kishin Yan uwansa ba har gobe Ina tuna disga min yarinya da yasa  aka yi a makaranta akan Ameera wallahi sai naji kamar na rufe shi da duka,bansan Mai yasa yake san shishige musu ba duk ya manta abinda suka mana”

Hajiya Zinatu ta karashe cikin hucci da tsanar Ameera da taji Yana Kara darsuwa a ranta da ta tuna ranar da aka kira sunan sultana a matsayin wacce tazo na daya tana washe baki tana kallon sultana da ta taso sai kawai muryar Amjad ya ratso ta lasifika Yana ba sultana ce tazo ta daya ba Ameera ce”

Wani dogon tsaki taja dan tamkar a lokacin abun ya faru ta mik’e ta shiga daki tana tunanin hanyar da za ta bi wajen Raba Amjad da gidan sule gabadaya.

Ameera

       Tana taka keken ne kawai ba dan zuciyarta na wajen dinkin ba,dawowar Amjad ya taso mata da abinda take so ta binne a zuciyarta sai da taji ya tafi ta bar kan keken taje ta zub’e akan gado dan tana ta taka keken ne saboda yaji dinkin take kar ya sake kiranta dan,gani take tana zama dashi na Yan mintuna zai gane halin da take ciki.

Bata san wasan Yara take duk a baya ba sai da ta ga Amjad a Yau a hankali ta furta “Allah ka yaye min wanan masifa ka cire min san abinda ba zan tab’a samu ba”

Shigowar Anne dakin yasa tayi saurin goge hawayen da bata san dalilin zubowarsa ba.

“Yanzu Amjad din ne ya zama bakon ki har kike wani shigewa daki ki b’uya”?

“Dinki fa nake Anne”

“Ke kika sani kije Abban ku na kiranki”

Anne tace tana k’ok’arin juyawa

Ameera kuwa ta mik’e da sauri tana “Allah yasa ba laifi nayi ba”

Anne bata kulata ba ta fice daga dakin.

Ameera kuwa ta jawo hijabinta ta saka tayi waje tana Jin faduwar gaba dan kila maganar  Sahar zai mata”

A zaune ta ganshi akan daddumar sa da fura a gabansa

Sai da ta tsugunna ta gaishe shi ya amsa, gabanta sai dukan uku uku yake sai da Abba sule ya gama shanye furarsa ya ture kofin gefe ya dago ya kira sunan Ameera Yana “Amjad yazo ya sameni wai Yana sanki da Aure, nace masa bazan hana shi ba idan har iyayensa suka yarda ya aureki amma kafin ya tari iyayensa ya fara fada miki”

“Ina so idan ya tare ki da maganar kice kina da Wanda kike so dan kema Kinsan Aurenki dashi ba Mai yuwa bane kinsan komai kinsan duk Abubuwan da suka faru kin kuma san halin su,yanzu kina amsar tayin soyayar sa tashe tashen hankula ne zai biyo baya yanzu za’a ce kwadayi yasa kika ce kina San shi dan haka ki bashi hakuri yaje ya nemi Yar uwarsa mai kudi ya aura,Ina ga lokaci yayi da zaki bar Sahar ya turo manyansa dan Ina ga sai yaga haka zai yarda cewar kina da Wanda kike so”

Ameera dagowa tayi tana “in sha Allah Abba zan yiwa Sahar magana akan ya turo magabatansa dan ko nima ba zan tab’a iya auren Yaya Amjad ba”

Gyada Kansa Abba sule yayi Yana zata iya tafiya.

Ameera mik’ewa tayi kirjinta na dukan uku uku jikinta sai rawa yake tana shiga daki ta kulle k’ofar ta zube a kasa ta fashe da mugun kuka dan bata tab’a tunanin Amjad na Santa kamar yadda take San shi ba,da hoton Amjad take kwana har bata so ta tashi daga bacci saboda mafarkin da take dashi da tasan itama yaudarar kanta take Amjad ba zai tab’a Santa ba dan yafi karfin ajinta ko da ma ya sota babu yadda za’ayi su iya Aure saboda irin kiyayar da iyayen sa ke gwada musu,ko ita kanta ba zata tab’a iya aurensa ba ko dan Abubuwan da suka faru a baya.

Har wani zazzabi ne ya rufeta saboda kukan da ta sha tana kallon Kiran Sahar amma ta kasa d’auka tuna zata Auri Sahar ba dan tana san shi ba yasa ta Kara rushewa da wani sabon kukan.

Past

      Ihu Zinatu ke ta gwadawa da k’arfi tana “ka cikani Sule dan Allah karka min fyade”

Duk Ihun nan da take tana tsaye nesa da Sulen tana ta tsalle ita kadai dan tana Jin yadda Habu ya haukace da buga k’ofar.

Sule kuwa cak ya tsaya Yana kallon Zinatu jikinsa na balain rawa da Sharrin da take neman Kulla masa Yama kasa motsawa sai hawaye dake zubo masa.

Muryar Hanne da yaji tana “Abban Ameera ka Bude k’ofar mana innalillahi wa inna ilaihi rajiun fyade Kuma”

“Zinatu mai na miki da zaki min irin wanan Sharrin, Zinatu gwara ki sameni kice na bar miki gida da wanan cutar da kika min kimin sharri kimin kazafi dan kawai ki rabani da dan uwana Allah ya Isa tsakanina dake Zinatu ba zan tab’a yafe miki wanan  sharrin da kika min ba”

Sule yace Yana Jin dakin na juya masa da dafa bango ya murza key din Zinatu kuwa tayi saurin ta zube a kasa tare da sakin zaninta”

Habu kuwa da naushi ya Maida sule ciki Yana “Matata zaka yiwa fyade sule?har daki ka biyo matata zaka mata fyade”?

“Ina daki Ina wanka naji kamar an shigo dakin na fito kenan na ganshi a dakin Kafin na koma ciki ya jawoni wai ya Dade Yana sha’awata na bashi hadin kai dan nafi matarsa kyau kar na bari ka sani wallahi har dakina yazo zai min fyade”

Zinatu ta karashe cikin Ihun kuka

Habu kuwa bai wata wata ba ya rufe sule da duka da naushi

Hanne tayi Kansa tana “Wallahi karya take masa hanya take nema da zata kore mu daga gidan wallahi Abban Ameera ba mazinaci bane ba halinsa bane ya kamata ace kasan waye kaninka har ace Kafi yarda da matar ka akan kaninka wallahi sharri take masa dan Allah ka cika shi karka kashe min shi”

Hanne tace cikin Ihun kuka tana k’ok’arin ture Habu daga kan sule.

Muryar Gwaggo cikin wani irin murya yasa suka juya gabad’aya suna kallonta banda sule dake numfarfashi a kasa.

“Kinyi nassara wajen Raba min kan Yara Zinatu yadda kika cusa min bakin ciki a zuciyata kika raba min kan yarana Allah ya tusa Miki bakin ciki ya raba miki kan naki yaran,Ban haifi mazinaci ba amma tunda har kika bi yarona da irin wanan kazafin in Sha Allahu sai Allah ya min sakayya da gaggawa na rike ki da hannu biyu ban tab’a cutar dake ba,amma sakayyar da zaki min shine ki jefi dana da kazafin zina Nagode Zinatu.

“Habu daga min sule yanzu nan Hanne jeki kwashe kayanku mu tafi”

Habu a haukace ya daga sule Yana “Kiri Kiri ki ga sule a dakin matata kice sharri Zinatu ke masa, Gwaggo wanan wane irin kiyayaya kike gwadawa min idan sharri Zinatun ke masa ya akayi ya shigo dakin har da rufe kofa,k’ok’awa fa naji Yana yi da ita haba gwaggo wanan rashin adalci ne kenan duk abinda sule yayi goyon bayansa kike kenan”?

“Sule taso mu tafi”

Gwaggo tace a hankali a daidai lokacin da ta zub’e a kasa……

*PAGE 7*

Past

         Kan Gwaggo Habu yayi da sauri Hanne ta saki ihun kuka,kafin Habu ya kai ga tab’a Gwaggo dake ta sallati ,ta daka masa wani mugun tsawa tana “Karka Sake ka tab’a ni Habu,karka sake ka matso kusa dani.

Gwaggo tace cikin hakki dan kafafunta rawa suke sai da ya Kai ta ga zubewa a kasa ga numfashi da taji Yana mata wahala shakka, bata tab’a tunanin Zinatu zata iya hada irin wanan makircin dan ta Kori sule daga gidan Habu ba.

Kwana biyu kenan sule bai leka ta ya gaisheta ba,idan har bai zo gaisheta ba yau zata ganshi washegari,dan karfin halinsa ma duk da bashi da kudin sai ya dan tafar mata da wani abu addu’a na musamman take masa,tasan zai bala’in takura kansa wajen gyara gidansa shiyasa ta dage ya zauna a gidan Habun, shekaranjiya ta samu ta d’auki adashen da take yi da dan yawansa duk da itama tana da Yan bukatun da baza’a rasa ba amma haka ta yanke bawa Sule kudin tasan zai ishe shi siyan kwanun rufi da simintin plaster,duk da bai tab’a nuna mata su Habun na wulakanta su ba tasan baya Jin dadin zaman gidan biyayya kawai yake mata.

Ganin bata ganshi ba jiya ma bai je ba gashi ta kwana da mumunan mafarki a Kansa yasa ta yanke zuwa ta duba shi taga ko lafiya.

Tana kallon lokacin da Habu yayi parking a k’ofar gidan,har ya shiga gidan tana biye dashi ko Hanne da ta fito daga Bangarensu a guje bata ankare da ita ba,itama takawa tayi da dan gudu da taji Ihun Zinatu,cak ta tsaya da taji kalmar da Zinatu keyi akan sule nasan mata fyade.

Jikinta rawa ya d’auka ta hau zabga sallati,tana Jin Allah ya Isan da sule yayi wa Zinatu,har zuwa Bude k’ofar da yayi Habu ya Maida shi da naushi.

Bata san Zinatu za tayi tunanin kalawa sule sharri dan kawai Yana zaune a gidan Habu Yana cin arzikinsa ba.

Habu kuwa magana ya fara yi cikin ihuu Yana “Gwaggo yanzu Mai laifina ni fa aka yiwa laifi kema fa yanzu ganau ce ga sule nan a cikin dakina Mai ya kawo shi dakina idan ba fyade ya zo yiwa Zinatu ba,haba Gwaggo Kiri Kiri kike nuna bambanci a tsakanina da sule.

 Kiri Kiri kike nuna min kinfi san sule akaina.

 Yanzu da kashe Zinatun ma yayi cewa zaki yi sharri aka masa haba gwaggo wallahi ba’a yimin adalci wallahi Sule ya gama zama min a gida”

Sule  dak’yar ya iya tashi dan har lokacin dakin juya masa yake,ya kasa ma tsayawa dan yana tashi tsaye zai zub’e a kasa dan jikinsa wani irin rawa yake,  fadar halin daya tsinci Kansa a ciki bata bakine dan ji yayi gwara ace Zinatu kashe shi tayi da wanan Sharrin da ta masa Yau da’a ce Hanne ko gwaggo sun yarda akan zai iya mata fyade da ba abinda zai hana zuciyarsa bugawa.

Zinatu kuwa sai kuka  take har da shesheka sai da yaje bakin k’ofa ya juya ya Kara kallon Zinatun da ta sakar masa murmurshi a sace ta kuma cigaba da Kuka.

Sule kuwa ya Kara furta mata “Allah ya isa tsakanina da Ke Zinatu ba zan tab’a yafe miki sharrin nan da kika min ba”

Wani irin fusgo shi Habu yayi ya watsar da shi waje Yana “Har kana da bakin magana Sule kabi matata har daki ka nemi yi mata fyade Kuma kazo kana borin kunya”

Sule na Shirin magana gwaggo ta daga masa hannu dan  har lokacin ta kasa dawowa daidai a hankali tace “karka ce komai Sule karka yi k’ok’arin kare kanka ko ka wahalar da kanka wajen wanke kanka a wajensa Habun da ka sani a baya bashi bane wanan,na dade da rasa Habu tun lokacin da ya tafi neman kudi wanan Habun na gabana ba nawa bane, dan Habuna ba zai bari mace ta hada shi da dan uwansa ba”

Sule mik’ewa yayi shi da Hanne suka taimaka wajen tadda Gwaggo tsaye Zinatu kuwa ta fito tana Jan majina tana “Gwaggo wallahi ba zan tab’a hada Baban Amjad da kaninsa ba,mai ribana idan na masa sharri akan me zan masa sharri,idan gidan nake so ya bari ai zan fito na nuna masa kararara akan ya bar gidan har daki ya shigo zai min fyade ba sharri na masa ba”

“Ai ko mai zaki ce Gwaggo ba zata yarda ba,dan bata san laifin Sule ni bansan mai yasa ta tsaneni har haka ba”

Gwaggo kuwa ko kallon su biyun ba tayi ba suka bar palon ko da suka koma part din su kuka sule ya fashe dashi Yana “Wallahi tallahi ita ta aiko yarta da na shigo wai a kirani nazo,Ina zuwa sai naji tana Ihun miciji yadda take ihu yasa na nufi dakin a gigice ban kawo sharri zata kulla min ba”

“Sule ka daina wahalar da kanka wajen rantsewa nasan wacce Zinatu kawai ban kawo har zata iya Maka wanan Sharrin ba ni na haifeka nasan halinka nasan abinda zaka aikata da Wanda ba zaka iya aikatawa ba,dan kawai baka da kudi taci mutuncinka taci zarafinka,Sule zaka yi kudin nan idan har kana da rabon yi,ko Ina rayye ko bana rayye lokaci na zuwa da Habu zai gane wacce yake Aure,lokaci na zuwa da Habu zai san darajar ka,lokaci na zuwa da Habu zaiyi nadamar Abunda ya maka Sule.

A yanzu kudin da yake dashi ya rufe masa ido baya gane daidai ba abinda ya sani sama da matarsa ni kaina a babu yadda zai yi dani ne,bana so na masa magana a yanzu dan zan iya masa kalmar da bata dace ba abinda kawai zance Allah ya ganar dashi gaskiya ku hada kayan ku mu tafi ka bar kuka haka kaga yaranka Suma kukan suke”

Gwaggo tace tana goge nata hawayen

Hanne kuwa kayansu kawai take hadawa a wani babban bacco itama tana sharar hawayen.

Sule kuwa yadda gwaggo ke numfarfashi yasa shi daurewa ya mik’e ya fita waje ya samo musu  abin hawa.

  take duk suka kwashe tarkacen su.

Yace Hanne suyi gaba zuwa gidan gwaggo zai Kai gwaggo chemist a dan duba ta,duk yadda Gwaggo taso hana shi ki yayi sai da ya samo musu wani abun hawan ya nufi wani Karamin chemis da ita sai addu’a take kwarara masa.

Ta dauka ko yayane Habu zaiyi tunanin biyosu sai dai har suka koma gida bata ga keyarsa ba.

Magungunta kawai ta Sha tayi sallahrta a zaune shawarar likitar tabi wajen hana kanta tunani dan Jininta yayi mumunan hawa.

Dak’yar sule ya yarda akan zai kwana dan ce mata yayi zai je ya kwana a gidan wani abokinsa gobe zai je ya nemi rancen kudi gwaggo kuwa tace ya kwana da safe zasu yi magana.

Sule zaman dirshan da tsakar dare ya hau kuka kasa kasa dan yaji ciwon Sharrin da Zinatu ta masa.

A Karamin dakin da gwaggo ke ajiye kayan abinci ya sa tabarma ya kwanta su Hanne Kuma suna daya dakin da Yar kanwar gwaggo suna kwance su Ameera kuma tare suka kwana da gwaggon.

Motsin bude k’ofar yasa yayi saurin komawa ya kwanta.

Ta dan hasken daya shigo ya gane Hanne ce ta shigo dakin.

Hanne waje ta samu ta zauna a gefensa tana “Abban Ameera Ina can na kasa bacci nasan kaima ba zaka iya baccin ba shiyasa na ce bari na zo wajen ka ban tab’a tunanin Zinatu zata iya Maka wanan Sharrin ba”

“Hanne naga bani na dorawa kaina talaucin nan ba,naga Allah shi yake azurta Wanda yaso ya talauta Wanda yaso shikenan dan bani da kudi matar Habu ta dora min Karan tsana har da min sharri, duk da bana neman wani abu a wajensu tafi so sai ta rabani da dai dan uwana,Taya Yaya  Habu zai yarda zan iya neman Zinatu”

“Kayi hakuri Abban Ameera wallahi komai lokacine Allah da ya musu arzikin muma zai mana in Sha Allahu dan Allah kar ka sa damuwar nan a ranka ya zame maka ciwo Muna nan da Kai wallahi watarana sai sunyi nadamar wulakancin da suka mana.

Hanne ce ta ringa kwantarwa da sule hankali Wanda kalaman nata kuwa sunyi tasiri sosai wajen rage masa damuwar da yake ciki bata baro dakin ba sai wajen hudu.

Koda gari ya waye wajen bakwai sule ya tashi idonsa duk ya kumbura saboda kukan da ya Sha har wani dan rama yayi.

So yake ya Nemo rancen kudi a gurin wani da yake wa aikin gini ko Allah zai sa ya dace da samun kudin dan ya tab’a masa kyautar kudi Mai Dan yawa abinda ko rabinsa Habun bai tab’a masa ba kuma Habu yafi shi kudi.

Zai Nemo kudin rufin gidansa ko ba plaster su koma nan din sai yafi masa kwanciyar hankali a hankali idan Allah ya hore masa sai ya cigaba da gyara gidan,kudin da ya Tara kwanaki yayi hidimar makarantar su Ameera a da iya littafin rubutu kawai yake dan iya siya Mata amma wanan term din aka kira shi akan ya dan hada mata da text book dan Ameeran tana da kwakwalwa ko shi Kansa yakan yi mamakin yadda take da k’ok’ari dan bata tab’a daukar na biyu ba daga islamiya har boko duk na daya take zuwa shi yasa ko bashi da kudi ana neman wani abu Daya shafi karatun ta zai mata,ba kuma iya ita kadai ba har kannen nata sai dai Ameeran duk tafi su k’ok’ari.

A palon ya tadda Gwaggo a zaune,su Ameera kuwa sun sa kayan makaranta suna Shan koko da kosai.

Har kasa ya tsugunna ya gaishe da Gwaggo ta amsa cikin sakin fuska tana jiya kukan ka cigaba da yi bayan na  hana ka ko”?

Dan murmurshin yayi Yana “gwaggo ai duk Wanda aka yiwa irin wanan Sharrin dole Yayi kuka banda ma ina da jajjirtaciyar uwa Ina ga da yanzu Ina gadon asibiti”

Murmurshi Gwaggo tayi tana “karka damu Sule komai Mai wuce na idan Allah ya yarda Ina nan Ina Maka addu’a Kuma dan Allah karka sake ka kullaci Habu dan ya hadu da shu’umar mace ne duk rantsuwar da za’a masa akan sharri matarsa ta kala ma ba zai tab’a yarda ba,dan haka karka sake ka rike shi a ranka kaji ko”

“In sha Allahu gwaggo sai dai Zinatun ce wallahi gwaggo ba zan tab’a yafe mata ba har sai ta fito ta wankeni a wajensa”

“Ko bata fito ta wanke ka ba Sule Ina addua Allah yasa Habu watarana ya gane halin matar sa”

“Zan fita Gwaggo akwai wani mutum da nake masa aikin gini  zanje na same shi na ga ko zan samu aron kudi a gurinsa”

“Ba sai kaje ko Ina ba sule wanan dai Ina ganin zai ishe ka ka siyi kwanun rufin har da plaster din gidan”

Gwaggo tace tare da daga pilon dake gefenta ta d’auko bakin ledan da ta daura kudin a ciki.

Koda ta mik’awa sule kasa karba yayi ya zubawa ledar  ido.

Gwaggo kuwa tace “Ka karba mana Sule ni tun shekaranjiya nake zuba idon zuwan ka dan akwai adashen da na shiga na karbi nawa dama dan kai na shiga adashen  ka karba ka siyi kwanun rufin ka siyi siminti Ina ga zai ishe ka ka karba ka gani”

Sule idonsa cicikowa yayi da hawaye hannunsa na rawa ya karbi kudin Koda ya kirga ma Rabin kudin zai ishe  shi siyan kwanun rufin dakuna biyun har da plaster da dab’en kasa.

“Allah ya ara miki tsawon Rai Gwaggo Allah ya bani ikon biyanki”

“Burina kullum naga yarana cikin farin ciki Sule Idan da Ina da hanyar da zaka samu kudi da na samo ma kudi saboda wulakancin da Zinatu ta ma Ina fatan watarana Allah ya d’aukaka ka a gaban idonsu”

“Ameen Gwaggo”

Sule yace cikin tsananin farinciki ya kirga iya kudin da zai ishe shi,ya saka a Aljihunsa ya mik’awa Gwaggo sauran yana “Gwaggo kudin da na d’auka sun isheni ga ragowar nan”

“Da Ina da kudi kara maka zanyi Sule kayi amfani dashi idan har zai isa ka siyawa su Ameera katifa Suma a saka musu a daya dakin”

Godiya sule yayi ta kwarara wa Gwaggo kamar zai goyata.

A cikin kwana uku aka rufa gidan aka yi plaster da dab’en kasa har da dan fentin dakuna biyun bandakin ma ya siyi kofa second ya sa an rufe har kitchen din dan a lokacin kayan gini na da balain araha.

Ragowar kudin ya dan siya musu kayan abinci ya karasa biyawa su Ameera kudin makaranta.

Koda suka tashi komawa har da gwaggo a Yan rakiya ta kuma ji dadin ganin yadda aka dan gyare gidan yanzu.

su Ameera nada dakinsu komai dai tsaf na iya zaman talaka.

Hanne da su Ameera kuwa sai murna suke dan nan din yafi musu kwanciyar hankali da gidan Habu da suka yi zaman takura kwakwaran motsi ma ba sa iya yi.

Zinatu kuwa tsabar makirci kuka ta cigaba da sharba bayan fitar su gwaggo dan taga alamar Habu hankalinsa ya daga da ganin fushin da gwaggo tayi,kukan da take ya  hana Habun bin bayan Gwaggo.

Ya hau rarrashin ta Yana “ki kwantar da hankalinki Sule ba zai Kara kwanar min a gida balle yayi tunanin yi miki fyade.

“Yanzu banda Allah ya jefo ni da yanzu ya tab’a min ke wai kuma duk abinan Gwaggo taki yarda sai kare Sulen take”

“Ai Gwaggo ta tsane ni burinta ta gani a cikin bakin ciki Kiri Kiri taga sule a cikin dakin nan amma sai ta juya maganar wai so nake na Kori sule daga gidanka ni dai Baban Amjad na gaji da abinda Gwaggo take min ka sauwake min kawai na tafi gidanmu tunda bata san zamana da Kai tunda wancan lokacin ma ai so tayi ka sakeni albarkacin su naci shi yasa ta hakura da sakin da take so kamin”

“Ba abunda zai raba mu Zinatu ban ga Mai rabani da ke ba har akan sule gwaggo take min haka amma ba komai nasan mai zanyi kiyi hakuri ki bar kuka haka”

Zinatu kuwa har aka kwana Biyu Kukan munafirci ta ringayi tana magangunan dake tunzura Habun da ya so bin bayan Gwaggo dan baya san fushin ta,amma idan Zinatu na Yan maganganu sai yaji bama zai je wajen Gwaggon ba dan ya yarda da maganar Zinatun akan tafi san sule akansa ta Kara da sule ma ai bakin ciki yake masa da rufin asirin da yake dashi shiyasa yake ta san hadashi da Gwaggon.

A yanzu wani tsanar Sule yake ji a ransa dan ba dan Gwaggo ba har kulle shi sai yayi.

Zinatu kuwa zuciyarta fess da ganin Sule sun bar gidan,sau biyu tana nadawa Amjad duka saboda ya matukar damuwa da barinsu sule gidan har da yajin cin abinci.

Har Gwaggon ma bata so Habu ya ringa zuwa wajenta shiyasa take zugashi cikin kirsa da alama kuma ta samu cikar burinta dan ba abinda Habun ke b’oye mata ko gidan gwaggo yaje sai ya fada mata sai gashi an tafi wata guda bata ji yace mata yaje wajen Gwaggon ba.

A duniya ba abinda take so sama taga yaranta sunfi na kowa,ko makarantar da suke zuwa shine Mafi tsada a garin dan tasan sai ka tadda wuya zaka iya Saka yaronka a makarantar kawayenta kan Koda ta akan Allah ya bata dan duk abinda take so jikii na rawa ko da Habun baya so sai yayi mata.

A yanzu Amjad  na Ss1 Amrah na Jss 2 ,Umar na primary 5 sai Sultana dake primary 3 lokacin kusan ajinta daya da Ameera”.

Hanne

         Ameera ta ringa kwallawa kira dake can kulle a cikin daki.

Ameera  dinkin Yar tsanar da take ya d’auke mata hankali bama tasan Hanne na kiranta ba.

Idan har ta dawo daga makaranta ta gama home work dinta bata da aikin da ya wuce dinkin Yar tsana ko zanen flower a takarda hana ta da Hanne ke yi yasa take dinke dinken ta a b’oye.

Hanne kuwa dakin ta nufo a fusace dan tasan tana nan tana sanaar dinke dinken har mamakin Ameeran take dan har da tsakar dare zata iya farkawa ta ganta a zaune tana Zane  a bayan takardarta ko dinkin pieces din kyalle da take samowa a wajen tela ta daga labulen dakin kenan Amjad ya fado cikin gidan da uniform a jikinsa.

Anne cikin farin cikin ganinsa ta tsaya tana “Amjad ya akayi kasan gidanan”

“Anne Ina wuni”

Tana k’ok’arin amsawa Ameera ta fito daga dakin da gudu tana “Yaya Amjad”

A guje taje ta rungume shi cikin murna Shima cikin tsananin farin ciki ya rungumeta a daidai lokacin da su Fareeda Suma suka fito duk suka rungume shi.

Dan Amjad shi kadai ne Wanda ya gwada musu Kauna a lokacin da suke zaune a gidansu.

Duk wani kayan kwalam da kayan dadinsa su yake bawa a b’oye idan zasu tafi makaranta.

Har naman cikin abincinsa yake kawo musu su ci.

“Shine kuka gudu kuka barmu”

Amjad yace Yana zungure keyar Ameera da ta saki dariya tana “Ba guduwa mu kayi ba Korar mu a kayi”

Amjad na k’ok’arin magana Anne ta daka musu tsawa tana ya isa haka su bar Amjad ya shigo ya Sha ruwa.

Sai da ya Sha ruwa ta zubo musu abinci tare da su Ameeran dake ta murnar zuwan sa.

Sai a lokacin yake sanar mata gidan gwaggo yaje ta kwatanta masa gidan nasu.

Cikin damuwa ya nuna rashin Jin dadinsa na barin gidansu da suka yi.

Anne kuwa murmurshi tayi tana kar ya damu ai yaga gidan yanzu sai ya ringa zuwa amma kar ya bari Zinatu tasan yana zuwa dan tasan sai ta Zane shi.

Sai da Anne tayi da gaske Amjad ya tafi a ranar.

Tunda ga ranar kuwa Amjad yaga waje ana tashi daga makaranta zai zo anan zai ci abinci yayi wasa dasu Ameera ya kawo musu duk tarkacen da aka bashi ya tafi dashi makaranta Zinatu lokacin har kudi take bashi.

Kafin ya tafi Ameera zata d’auko takarda ta suyi karatu a tare duk da a primary take masifar k’ok’ari ne da ita dan ta iya maths sosai.

Wani irin shakuwa Amjad yayi da Ameera duk lokacin da bai zo ba itama Ameeran haka zata wuni sukuku.

Anne kuwa tun tana dukanta akan dinke dinken da take har sai da gwaggo ta mata fada akan ta bar dukan ta bata san baiwar da Allah ya Mata a dinke dinke da zanen nan da take ba.

Habu sai da ya share kusan wata hudu bai waiwayi Gwaggo ba sai da Ibrahim ya zo da iyalansa gaida gwaggo, Gwaggo ke sanar dashi duk Abubuwan da suka faru ta Kara da “A yanzu addua kawai nake bin Habu dashi dan Zinatu ta raba shi da kowa”

Yadda gwaggo ta nuna tsananin damuwarta har da kukanta yasa Ibrahim ce mata kar ta damu zai nemi Habun da Kansa,dan shi ba sule bane idan ya kawo masa raini hankali tattaka shi zai yi.

Gwaggo kuwa ta ce kar yaje ta fada masa ne kawai a matsayinsa na babba ita dai burinta su hada kansu bata san abinda zai raba kansu.

Wajen hudu na yamma Ibrahim ya isa gidan Habun,bai tsaya neman ayi masa iso ba ya shiga Kansa tsaye.

Fuska a hade ya shiga cikin palon Zinatu na hakimce da remote a hannu su Amrah na tsakar palon suma da alama dukansu Kallo suke.

Zinatu kuwa tana shakkar Ibrahim dan sau daya ma ta tab’a ganinsa bashi da fara’a Sam, mik’ewa tayi da sauri tana “Yaya Ibrahim kaine kake tafe sannu da zuwa”

Bai ko kalleta ba ya kalli su Amrah ya yafito ta Yana “Jeki kira min Babanki ba maula nazo yi a wajensa ba tunda naga fargabar uwarku shine wani nashi yazo wajen sa”

Amrah tsayawa tayi tana kallonsa dan ita ba wani sanin shi tayi ba gashi duk basu iya gaisuwa ba, Ibrahim kuwa ya daka mata tsawa Yana “Wuce ki kira min Babanku nace yayan marasa tarbiyya ko  gaisuwa baku iya ba”

Da gudu Amrah tayi dakin Habun ba jimawa ta dawo tana zungura baki.

Zinatu kuwa ta hau matsar kwallan sharri.

Koda Habun ya fito washe baki yayi Yana “Yaya Ibrahim yaushe ka shigo garin nan”?

“Na d’auka ka manta sunana ai iya sunan matarka kawai ka sani wai so nake naji ko Zinatu ta zama uwarka  shiyasa na zo naji wai daga kanka aka fara kudi ne?Habu kana da hankali kuwa?har nawa kake dashi da yasa matarka tace karka rabe mu”?

“Dan Allah Yaya Mai ya kawo maganar nan”

Ibrahim fada ya rufe Habu dashi ya masa kaca kaca ya hada da Zinatu dake ta  sharar kwalla.

Habu kuwa bai iya magana ba har Ibrahim ya juya ya tafi.

Habu kuwa jikinsa ne yabi yayi sanyi da Ibrahim yace Gwaggo na fama da hawan jini,jiki na rawa ya d’auki mukullin motar sa ya nufi gidan gwaggo,sai a yanzu Shima yake ganin rashin kyautatawar sa na kin zuwa duba  Gwaggon tunda ba ita ce ta masa laifi ba sule ne.

Duk kudinsa da komai nasa baya san fushin gwaggo

Koda ya Isa gidan sai da ya tadda sule da Ibrahim din ganin Sule Yasa shi hade rai.

A takaice silar zuwan Ibrahim Habu da sule sukayi Shirin ganin ido,dan gwaggo kuka ta Saka musu dan bata San abinda zai raba kansu.

Amma a bayan idon gwaggo Habun ko kallon Sulen baya yi kamar yadda Sule shi kuma ya ringa baya baya da Habu dan ba zai manta abinda suka mi shi ba idan suka hadu a gaban gwaggo zasu gaisa kamar ba komai.

A haka rayuwa ta ringa tafiya Sule na iya k’ok’arinsa wajen Neman halal dinsa wajen tsayawa iyalansa.

Shi Kuma Habu arziki sai gaba yake Zinatu na fantama wa duk da ba wani Abunda ya taka ka Kara ya karya yake wa gwaggo ba amma ji take dama tana da yadda zata hana shi yi mata hidima,daga sule har Hanne bata Kara Saka su a idonta ba,bata san Kuma Kai su Amrah cikin dangin Habu tafi Kai su cikin danginta.

Ameera kuwa tana da shekara goma Sha daya tayi saukar Qurani a lokacin yayi daidai da gama primary dinta.

A ranar bikin saukar nasu manyan mutane duk sai da suka samu halartar walimar saukan dan kusan dalibai Dari biyu zaa yaye,a cikin wayanda suka samu halartar walimar saukar har da mataimakin govnor  Jihar.

Duk a cikin masu saukar Kuwa Ameera ce mai Karamin shekaru  a cikinsu,dan makarantar kansu suna ji da ita.

Sule na daga gidan gaba Yana ta washe baki kamar zaiyi kuka ganin Ameera Yar karama a cikin manyan da zasu yi sauka.

Gwaggo da Hanne Suma suna wajen da Mata ke zaune sai washe baki suke.

Sule ya dan yi k’ok’ari wajen yiwa Ameera Abubuwa har da dan Abubuwan da za’a raba.

Amjad shi ma sai murmushi yake Yana kallon Ameeran Yana Jin dama shine yayi saukan,dan Zinatu bata da zafi Sam ta bangaren islamiyya tafi Maida hankali a boko.

A hankali aka fara gudunar da walimar saukar.

Ameera ce ta fara  fitowa  cikin sirrin muryarta da kiraa mai dadin gaske ta bud’e Taron da addu’a ta gyara murya ta fara karatun Qurani cikin kira’a mai dadi daya sa Rabin wayanda suka samu zuwa Jin Ina ma kar ta daina karatun.

 tsigar jikinsu kuwa sai tashi yake da yadda take karatun kamar wata balarabiya.

Sule kuwa sai share hawaye yake dan ko Iya wanan ilimin da Allah yayi wa Ameera arziki ne da kudi bai Isa siyansa ba.

Kabbara kawai ke tashi ganin Yadda duk wani kyauta da aka bayar Ameera ce kan gaba wajen karba gata Yar karama.

Wani Mai kudi dake zaune a cikin wayanda suka samu halartar walimar ya mik’ewa yayi dan Ameera ta gama burge shi gyaran murya yayi Ya fara jinjinawa Ameera da irin hazakar ta ya hau yabon iyayenta da suka jajirce wajen ganin ta samu ilimi dan haka Yana yiwa iyayenta albishir da zai biya musu Kujerar zuwa Hajj zai Kuma bawa Ameera kyautar miliyan daya”

Ai kamar ya bude k’ofar yiwa Ameera kyauta haka aka ringa mik’ewa ana zubawa Ameera kyauttuka da yasa Sule kifa goshinsa a kasa tare da rushewa da wani irin kuka.

Gwaggo kuwa sai kirari take yiwa Allah dan har kyautar gida wani ya bawa iyayen Ameera.

Amjad kuwa sai ihu yake dan ji yayi kamar shine.

Zinatu  dake zaune a can baya da ita kawarta ce ta gayyace tazo waleemar saukar kanta taji Yana juya mata da ta ji irin kyautar da aka ringa yiwa Ameera Sam bata kawo Ameera tana cikin wayanda ma zasu yi saukar ba sai da tazo,Sam bata kawo Ameera ma makaranta take ba,ba kuma taga su gwaggo ba dan a wajen da masu maiko maikon ke zaune ta zauna dan tafi karfin zama cikin talakawa.

Kamar zarrariya ta mik’e tana “wallahi saukar zuku tayi karyane ba wani saukar da tayi……

*PAGE 8*

 Kawar Zinatun hannunta ta jawo ta mai data ta zauna tana “Zinatu mai haka zaki tara mana mutane kamar ya saukar zuku tayi kinsanta ne”?

Zinatu da bama tasan ta mik’e tsaye ba tsabar tashin hankalin da ta shiga da ganin wai Ameera akayi ta zubawa wanan uban kyautatukan,tama d’auka a zuci tayi maganar bata san a fili tayi magana ba.

Kanta har wani Sara mata yake tana cigaba da Jiyo kabbarar da ake daga gidan gaba da kyautatukar da Ameeran ke ta samu.

 yaushe har aka haifi Ameera da ta isa sauke Qurani gabad’aya,har wai a ringa zuba mata wanan kyautatukan idan kunnenta daidai ya Jiyo mata kamar Kujerar Hajj taji za’a biyawa Sule da Hanne,bayan ita ko zuwa ba ta tab’a yi ba.

Ganin idan ta cigaba da zama zuciyarta na iya tarwatsewa yasa ta mik’e tayi wajen da tayi parking din motar ta,hararo sule da Hanne kawai take a jirgi bayan ita bata tab’a hawa ba.

Kawarta kuwa sai kiranta take amma ko ta kanta bata bi ba.

Tana tuki tana yarfa gumi,canjin rayuwar da Sule ke neman samu da Hanne ya matukar daga mata hankali,ko kusa ko alama bata san su samu wani hanyar cigaba tafi so duk dangi ace Babu kamar ita da mijin ta,tafi so ace duk dangi ba wayanda suka je kasa mai tsarki sama da ita da mijinta,babban burinta shine taga taje saudiya ta ganta da fararen hakoran macca guda biyu, tasan tana zuwa ta gama zama hajiyar da take so ta zama,sai gashi wayanda ta raina bama ta kawo su a sahun mutane da zasu tab’a Jiyo kamshin Airport balle har wai suje saudiya a gaban idonta aka ce zaa biya musu ba iya su ba har da Ameera.

Har fadawa Rami tayi tsabar tunanin da ta tafi tana yi.

Ko da ta isa gidan a gaban tv ta tadda Su Amrah suna Kallo kamar yadda suka saba aikin kenan idan har suka dawo daga boko,a sati bai fi sau biyu suke zuwa islamiyya ba.

duk Kuma bata damu ba dan gani take boko shine kan gaba akan islamiyya dan sai kayi karatun boko zaka iya zama cikakken mai kudi kamar yadda take hasaso Amjad a matsayin babban likita,Amrah a matsayin wata lecturer, Yaranta gabadaya dai da wani babban Matsayi.

Sai gashi wai Islamiyya da Ameera taje silarsa wai su Sule zasu tafi saudiya ga kyautar kudi da gida dan sauran ma bata iya jiyowa sosai ba saboda tashin hankalin da ta shiga.

Sam basu san da ta shigo ba sai labartawa juna labarin film din suke.

Sultana da take kusan sa’ar Ameera ta kurawa ido tana hararota a bainar jama’a tana zuba karatu cikin kira’a mai Dadi kamar yadda Ameera tayi dazu.

 sultana tafi dacewa da wanan kyautatukan ba Ameera ba.

 yanzu Ameera tafi sultana ta wani wajen kenan bayan su din suna da kudi.

Kamar wacce aka yiwa duka haka ta karasa kan kujerun.

 kanta, zuciyarta komai na jikinta ciwo kawai yake mata tana jiyo muryar Wanda yake bayanin zai biyawa Sule da Hanne Kujerar Hajj a kunnenta.

Sai a lokacin su Amrah suka lura da ta dawo.

Bata sabar musu da gaisuwa ba shi yasa suka d’auke kansu.

A wani irin tsawace tace “Ku kashe min kayan kallon nan kuzo nan gabad’ayan ku”

Ido suka zuba mata dan bata sabar musu da haka ba

Sai da ta sake daka musu tsawa suka kashe kallon suna turo baki da tambayar su mai suka yi ne.

Sai da suka jeru a gabanta ta tuna bata ga Amjad ba tun safe

“Ina Amjad yake”?

“Baya nan tun safe daya fita bai dawo ba”

Amrah ta bata amsa

Zinatu kuwa shiru tayi tana tunanin yawan fitar da Amjad keyi ya fara yawa dan  kwana biyun nan Yana   dawowa  daga makaranta zai fice daga gidan.

 baya dawo wa sai wajen Isha.

Ko ta tambaye shi zai ce Yana wajen ball bata wani damuwa dan bata san taga tana takura musu tana so taga suna duk abinda ransu ke so.

amma yawan fitar Kuma ta fara yawa dole idan ya dawo ta taka masa birki.

Amrah,Umar da  Sultana ta kalla dan lokacin bata samu cikin Samha ba

Kamar Mai mura tace “Wai ni izunku nawa a islamiyya”?

Yamutsa fuska suka yi kamar basu san mai take fada ba

Ganin basu gane ba yasa tace “Ina nufin a wane sura kuke a islamiyya”?

“Mu karatu kawai muke bamu san surar da ake karanta mana ba na iya karanta fatiha da izaja”

Amrah tace cikin murmushi

Zinatu kuwa bakin cikin yadda tayi magana kamar tayi abin arziki yasa ta kwashe Amrah da Mari tana “Ga kanwar kanwarki can tayi sauka Amrah,har kuna me zaku bari Ameera tafi ku wani abu.?

Maza kuje ku sako hijabin ku dan wallahi Kuma sai kunyi saukar nan Kun ciyo mana kyauta kamar yadda Ameera taci kyauta,wai har Yar gidan sule da bashi da komai itace da sauke Qurani ana zuba mata kyautatuka,Maza ku shiga ku sako hijabin ku duk a shekarar nan wallahi sai Kun sauke”

Zinatu tace duk bakin ciki na sake rufeta da ganin wai wai a haka Amrah ce ma mai k’ok’ari akansu,idan ta tuna yadda Ameera ke zuba karatu cikin kira’a Mai dadi sai taji kanta ya Sara mata,tana fargabar ma wani mai kudin yace zai d’auki nauyin karatun ta dan hakan na nufin zata goga da yayanta.

Ko da ta Isa makarantar islamiyar su Amrah da Shima kamar private yake dan sai da ta tabbatar da Makaranta na masu hannu da shuni ne tasa Habu ya karbar musu foam

Suna gama gaisawa da shugaban makaranta ta fara “Mallam so nake yarana suyi sauka da gaggawa zan bada ko nawa ne”

Sai da shugaban makarantar nasu yayi mata  kallon tsaf ya tabbatar da a hayyacinta take ya saki murmurshi Yana “Hajiya dama karatun da kudi ake siya?dama da kudi ake siyan saukar Qurani? Dama nemanki nake dan da baki zo ba ma zan aika muku takardar sallamar har gidanki.

Hajiya tsarin makarantar mu ba’a yin fashi batare da wani kwawaren dalili ba.

 Hajiya duka yaranki basa zuwa makaranta sai sun ga dama.

makarantar mu ba wajen wasa bane ba.

 yaranki a wata bai fi su zo sau hudu ba,zaki iya siyawa yaranki karatun Boko amma ba zaki iya siya musu islamiyya ba yaranki duka idan kika d’auke namijin ba wanda ya iya Karatu zuwa izu daya.

Gashi  basu da k’ok’ari da mai da hankali shekara uku suna maimaita aji daya wai kuma a haka kike so suyi sauka.?

 Girgiza Kansa yayi ya cigaba da

“Hajiya shawara zan baki idan kin Saka su a wani makarantar ki jajjirce,

 wajen tsayawa karatunsu dan taimakon da zaki musu kenan a matsayin ki ta uwa,kamar yadda wata baiwar Allah ta tsayawa yarta da bata fi shekara goma Sha daya ba ta sauke Qurani mai girma da ta zama abin alfahari ga kowanne musulumi,nasan silar saukar da tayi a Karamin shekaru zai zaburar da iyaye da dama wajen ganin yaransu Suma sun dage wajen maida hankali a karatun su.

Kamar yayyafin ruwan zafi haka Zinatu ta ringa Jin maganar Shugaban makarantarsu Amrah.

Ameera da ya Kara mata misali da ita yasa taji office din na juya mata idan har tace zata cigaba da tsayuwa zata iya yanke jiki ta fadi.

Haka ta baro makarantar dasu Amrah tana Jin wani zazzabi na neman rufeta gani take kamar a mafarki wai yanzu kowa da Ameera yake kwatance.

Wani Karin bakin ciki tana zuwa gidan Habu ya tareta cikin fara’a Yana labarta mata Saukar da Ameera tayi ya Kara da yanzu haka daga gidan gwaggo yake sai shiga ake ana taya ta murna

Yadda take Jin zuciyarta idan ba kuka ta fashe dashi ba zuciyarta zata iya bugawa.

Kuka ta fashe dashi tana “Baban Amjad Yar Dan uwanka kake wa murna bayan ga naka yaran nan a zube ba Abunda suka iya Ameeran da ta sauke ita Kai biyune da ita?

Kai da zaka fara tunanin hanyar da zaka bi wajen ganin Suma sun samu ilimin wai kaine ka tareni kana bani labarin saukar da Yar wani tayi ko kishin kanka baka yi,yanzu haka daga makarantar su nake amma sallame su dan haka sai kasan makaranta da zaka nemo musu da zasu yi saukar Suma”

Daga haka ta wuce dakinta tana Jin tsanar komai dan tana ji tana gani su Sule sun fi su da wani abu.

Sule kuwa ganin komai yake kamar a cikin mafarki a lokacin da mutane suka yi ta zuwa suna musabiha dashi da kalaman jinjina a gare shi na zama jajirtacen Uba ga yarsa.

Ko kusa ko alama bai tab’a hango musu wanan nii’momin da ya ga sun mamaye su lokaci guda  wani na bin wani ba.

A  rayuwarsa bai nema da yawa ba bai roka da yawa ba fatansa da burinsa bai Wuce ya iya fita hakkin iyalinsa ba wai sai gashi silar Ameera yar cikinsa yar shekara goma Sha daya ana ta musu kyautatukan da yake ganin kamar dai mafarkin yake,sai dai bai ga alamar mafarki ba da ya ga sun zama abin San kowa burin kowa ya ga mahaifin Ameera ya gaisa dashi burin kowa yaga yazo kusa dashi.

Har sai da taro ya watse suka isa office din hukumar makarantar da manyan mutanen da suka musu kyautatukan suke,

Suna fada musu yadda zasu Karbi kyautar nasu ya fara kukan farin ciki.

a duk abinda aka musu kyautar shi Kujerar hajjin da aka biya musu ma gabadaya dashi da yaran nasa yafi jijjiga shi,dan bai kawo Yana cikin Wanda zai tab’a zuwa ko da airport ba,dan yasan zai yaudari Kansa ya dorawa  kansa burin da sai dai a mafarkin ba dai a gaske ba,sai gashi Mai kowa mai komai  ya nuna shi din Mai azurta bawansa ne a duk lokacin da ya so.

Yadda yake kukan farinciki haka gwaggo da Hanne suka ringa kukan farinciki

Gwaggo sai hamdala take da suka koma gida dan gidanta suka wuce gabad’aya sai cewa take “Sule ka gani ko?kaga abin Allah ko?Na fada ma in Sha Allah sai Allah ya ma arziki na ma addu’a sai Allah ya d’aukaka ka a idon duniya wallahi ko a yanzu na fadi na mutu burina ya cika,Sule Allah ya ma arziki ta hanyar da duk bamu tab’a kawowa ba.

“Gwaggo mafarki nake yi ko dan na kasa yarda Gwaggo”

Sule yace Yana Jin farin cikin ya masa yawa kallon Ameera da yake ganin kamar jiya akayi Taron sunanta wai yau ta silarta suka samu wanan nii’momin.

“Ba mafarki kake ba sule ka tashi kaje kayi alwala ka godewa Allah dan ya gama maka komai”

Sule mik’ewa yayi Rabin kyautatukan da aka yiwa Ameera da aka nannade na daga gefenta kananan kudi duk a wajen aka bawa Ameera manyan kudine aka basu check.

Ya na cikin alwala Habu ya kwada sallama ya shigo sule kuwa amsawa yayi fuskarsa fal da fara’a dan gani yake ba lokacin da zai share Habun bane.

Habun kuwa d’auke Kansa yayi dan Zinatu ta gama tusa masa tsanar Sulen a zuciyarsa a yanzu ma tace masa yayi taka tsan tsan da Sulen bakin ciki yake masa da arzikin da yake dashi.

Cikin dan mamakin ganin palon a cike ga Ameera da Hanne a gefen gwaggo ga allon ta da sauran tarkace.

Har kasa ya gaida gwaggo ta amsa tana “Habu kaga abin Allah ko Ameera yarka ta zame mana silar arziki”

Gwaggo cikin farin ciki ta kwashe labarin komai ta bashi

Sule kuwa da bai wani ji haushi ba ya kuma tsinci Kansa da murnar abinda Sulen ya samu cikin murmushi ya ce “Gwaggo Ameera za tayi sauka shine baa fada min ba saboda baa d’auke ni da Mahimanci ba,yanzu da ban zo ba bazan san ma tayi sauka ba kenan”?

“Ai ko na fada ma matarka ba lailai ta barka ka zo ba,Kun d’auki sule da mahimanci ne ma da zai taka yazo gidanka ku d’auka wani maular yazo yi.

“Allah dai ba mutum bane .

Habu yau dai ga sule shi ma Allah ya mishi arziki ta silar yarsa ka sanar da matarka ta wulakanta min yaro Allah ya d’aukaka shi kuma a yanzu ya fara ganin budi da Izinin Allah”

“Gwaggo komai ya hadani da sule Ina murna da abinda ya samu nima Ameera yata ce, gwaggo ki daina nunawa Zinatu tsana haka,bana so a maida hannun agogo baya.

Daga haka Habu ya mik’e Yana bari ya tafi

Sule shi dai Yana tsakar gida goshinsa a kasa Yana tayi wa Allah godiya.

Har aka tafi sati daya Ameera na dan samun kyautataka  har gida aka kawo musu mukullin sabon gidan nasu dake can bakin titi a unguwar masu kudi.

Har rasa bakin godewa Allah yayi dan Allah ya masa abinda ko a mafarki bai san zai samu ba

Ko da suka je sukayi passport din tafiya har da Ameera sai da ya tambayi nawa ake zuwa hajjin dan duk kudin da Ameera ta samu na wajensa da Kuma yawa kudin.

Gwaggo ya biyawa Kujerar itama da Rabin kudin da Ameera ta samu duk bai sanar mata ba dan yaga ba Abunda zai yiwa Gwaggo sama da ya biya mata itama

Dan bai manta ba kullum shine burinta,har wani zubin takan ce Ina ma Habu ya biya ta taje da taji dadi.

Sai da yazo ya d’auki Gwaggo ya kaita aka mata Paspo suka dawo yake sanar mata da ita zasu tafi.

Gwaggo kuwa kallonsa kawai take hawaye na zubo mata tana “Kayi min abinda habu ya kasa min,ban taba tunanin Allah zai amsa min addu’a da mafarkina ba sai gashi Wanda nake sa rai nake addu’a akan ya kaini bashi yazo ya kaini ba,Kaine Allah ya bawa ikon kaini Allah yayi wa rayuwarka albarka sule budi da arziki yanzu ka fara samu in Sha Allah.

“Gwaggo ba abinda ba zan iya Miki ba tun lokacin da kika d’auki adashen da kika d’auka kika damka min gabadaya nake addu’a Allah ya kawo hanyar da zan iya faranta Miki kwatankwacin yadda kika faranta min yau Allah ya cika min burina gwaggo nima nayi abinda na saka ki farinciki adduarki tayi tasiri a kaina sosai Allah ya Kara Miki tsawon Rai da nisan kwana.

Gwaggo addu’a ta cigaba da masa tana share hawayen farinciki

Hanne kuwa duk shirye shiryen tafiyar da suke gani take kamar a mafarki dan Fareeda da Sadiq gidansu ta Kai su.

Kamar wasa kamar a mafarki sai gasu su hudu  Sule,Hanne, gwaggo da Ameera sun daga zuwa kasa mai tsarki har da Amjad a masu rakiya sai dagawa Ameera hannu yake cikin tsananin murna dan yaji dadin Abubuwan da ta samu,kasa ma hakuri yayi yayi zaman dirshan Yana labartawa Zinatu duk abinda su sulen suka samu ya Kara da “Ni ba Dan kyauta zan mai da hankali zuwa islamiyya ba,mummy duk Wanda ya samu ya sauke Qurani Allah zai bashi kwakwalwar da zaiyi karatun Boko dan a yanzu na gane sirrin Sanin karatun Qurani kafin na Boko ko ni Ameera zata iya kureni”

Zinatu abubuwa Hadar mata suka sake yi dan Sam bata San ma Amjad gidansu Sulen yake zuwa ba sai da yazo Yana bata  labari.

,yadda ya labarta Mata kyaun gidan ya Kara daga mata hankali dan a yanzu bata ga Kuma da abinda suka Fi su sulen ba.

Duk yadda taso Habu ya biya mata taje itama hajjin kar Hanne ta riga ta zuwa.

Bata samu ya biya mata ba dan hakuri ya bata akan yanzu duk ba kudi a hannunsa sai kayan kudi,kayan kudin Kuma mutane sun ki siya dan haka tayi hakuri ta bari wani shekarar.

Da biyu ta bar Amjad ya cigaba da zuwa gidansu Sulen Yana Kai Mata rahoto duk abinda ake ciki har zuwa tashin nasu.

Su sule kuwa Tunda suka isa,

 ibada kawai suka dage dayi dan ba zasu bari wanan damar da suka samu ya subuce musu ba sun gama yanke wa idan suka dawo zasu tare a sabon gidansu da shi ma ba su kawo sun Isa mallakar gidan ba dan gidan yayi balain kyau ba Abunda kuma Babu a ciki.

Satinsu uku suka fara shirye shiryen dawowa Hanne sai gata da hakoran maccanta biyu

Dukansu ba Wanda bai yiwa Ameera addu’a da d’aukaka ba acan ma sai da Ameeran tayi farin jini dan dan fitar da suke bata da aikin da ya wuce karatu cikin kiraarta mai dadin gaske.

Koda suka dawo ba Wanda basu kawowa tsaraba ba dan har makota Suma sun samu nasu rabon tsarabar.

Sule kuwa da Kansa ya kaiwa Habu nashi tsarabar dana Yara Habu kuwa ba yabo ba fallasa ya karba cikin dan Jin dadi dan har ga Allah bai wani ji bakin cikin niimar da sule ya samu ba,burgesan da yayi bai wuce uwar tsarabar da ya yowa Amjad ba,sai da yazo tafiya yake sanar masa jibi zasu koma sabon gidansu, Gwaggo ma a gidansu zata zauna dan yanzu so yake ya bawa Gwaggo kulawa tunda ta kawo girma ba komai Yar kanwarta ke iya yi mata ba.

Habu da Allah ya taimaka kawai ya bishi dan shi bai Isa cewa gwaggo ta dawo gidansa ba dan yasan zai haura da Zinatu.

San da yake mata yasa baya ganin laifin ta a duk abinda tayi masa.

Ana gobe Su Sule zasu koma sabon gidansu da yamma mummunan labari ya iske su akan sabon gidan nasu ya kama da wuta an rasa mai ya haddasa wutar.

Duk da hankalinsu ya tashi tuni suka rarrashi zuciyarsu akan Allah ne ya Basu zai maida musu Wanda ya fishi.

Agaban idon sule gidan ya konne kurmus kafin ma zuwa lokacin da Yan kwana kwana suka zo ma ya gama ci da wuta.

Kalmar gwaggo ne ya dawo masa da “Sule karka sake ka damu da rashin da kayi dan baka sa rai da Allah zai baka ba tunda Kuma hakan ta kasance kayi godiya a gareshi zai baka Wanda yafi wanna din.

Zinatu kuwa a lokacin da labari ya isketa akan gobarar da su sulen suka Yi wani irin murmushi ta saki tana Jin sanyi a zuciyarta.

A burinta bai Wuce taga kowa a kasan su ba,a burinta bai Wuce ace iya su ke da komai ba,har yanzu tana Jin ciwon hajjin da suka rigata zuwa.

A yanzu ta tsaya sosai akan su Sultana dan so take Suma su sauke kamar yadda Ameera ta sauke.

Kasancewar Sultana ta gama makaranta primary .

Makarantar secondary da tafi kowane  tsada ta Saka sultana dan babban burinta taga sultana tafi Ameera ta bangaren Boko.

Ta Kuma Fi maida hankali akan sultana dan itace sa’ar Ameeran.

A ranar da sultana zata fara zuwa ba tayi niyyar Kai Yara makaranta ba,amma saboda tasan makarantar ta masu hannu da shuni ne yasa ta shirya ta fara sauke su Amrah a makaranta ta wuce da sultana makaranta.

Murmurshi kawai take saki tana kallon yadda manyan motoci ke ta parking suna kawo yaransu duk wani mai kudi mai ji da Kansa makarantar yake kawo yaransa.

Tsintar kanta tayi cikin farinciki tana “Nasan duk k’ok’arin yarinya nan bata isa dai zuwa makarantar nan ba.

Ta sauko daga motar ta Sultana itama ta sauko duk da kankantar shekarunta Jin kanta take a sama.

Suna dab da shiga makarantar school bus yayi parking

Fitowar Ameera da school uniform din makarantar yasa Zinatu sakin Ashar da “Mai nake gani haka”…..

*PAGE 9*

*Past*

         Baki Zinatu ta saki tana kallon Ameeran ma da bata kula dasu ba,tana sanye da uniform da irin takalmi da kalar safar makarantar.

Jikinta har rawa yake saboda tashin hankali ganin Ameera ta nufi cikin makarantar.

Da balain sauri ta taka tana kwallawa Ameerar kira kamar wata mahaukaciya.

Ameera juyowa tayi a daidai lokacin da Zinatun ta isa wajenta.

a dan tsawace Zinatun tace “Ke uban me kika zo yi makarantar nan”?

Batare ta amsa gaisuwa da Ameera ta mata a tsorace ba, dan haka kawai take balain Jin tsoron Zinatu ba zata iya kirga  marukan da ta Sha a lokacin da suke zaune a  gidan su ba duk da ba wani shekaru ne da ita ba  tasan Zinatu ta tsane su ta tsani ganin su,duk kalaman da take jifansu dashi mitsiyata fakirai kwadayayu na kanta har ta haddace.

Tsawan da Zinatun ta sake daka mata da

“ba tambayarki nake ba”?

Makaranta nazo mummy”

Ameera tace cikin rawar murya dan haka taji su sultanan na fada mata

Sultana kuwa sai cewa take “Mummy kalar uniform dina ne a jikinta Suma sun zama masu kudine”?

Zinatu bata ko bata amsa ba dan ita kadai tasan bakin cikin da take ji a zuciyarta

“Waye ya Saka ki a makarantar nan?nan ya miki kala da makarantar da zaki zo”?

“Abba ne ya saka ni”

“Dalla rufe min baki Ina Sule yaga arzikin da zai saka ki a makarantar nan,wani tsinannen ne dai ya sake daukar nauyin karatunki tunda bai san mai ya dace yayi da kudinsa ba k’arfi da yaji sai kin fi yayana ko?k’arfi da yaji sai kin hada kanki da yarana ko? toh wallahi baki isa ba baki Isa hada kanki da yarana ba”

Zinatu tace tana kumfar baki batare da taji ko kunya ba.

 wani mallami da ya nufo wajensu yasa ta saisaita kanta Ameera kuwa tayi sauri tayi cikin Makarantar jikin ta na rawa dan ta d’auka zata kawo mata duka.

Zinatu kuwa har office din principal din ta shiga kamar zata tambayeta yadda akayi Ameera itama ta zama dalibar makarantar sai Kuma ta fasa dan bata so ta kawo wani zargin a ranta.

Zata iya mutuwa idan Ameera tafi sultana ta fanin Boko,zata so ace Sultana tafi Ameera k’ok’ari da aji,dan da alama duk Jss 1 zasu fara.

“Cikin dan sakin fuska ta fara magana tana “Principal nace ko za’a iya yiwa Sultana jumping ta tafi jss 2”?

Murmurshi principal din tayi tana “Da ma kin barta a Jss 1 dinta dan ba lailai ta iya gane darasin Jss 2 ba Hajiya saurin ma na mene naga yarinya ce Yar taki”

“Principal dan Allah Ina so sultana tafi kowace daliba k’ok’ari a makarantar nan,Ina so sultana ta zama itace kan gaba wajen cinye kowane darasi da aka basu,idan akwai wani extra lesson da za’a mata ayi mata zan bada ko nawa ne idan har zata gane abinda ake koya mata”

Murmurshi principal din ta Kara saki tana “Muna iya k’ok’arin mu wajen ganin daliban mu suna gane duk darasin da aka koya musu,idan har yarki nada k’ok’ari da saurin ganewa in Sha Allah zata iya zuwa na daya dan makarnatar nan gaskiya na hazikai ne”

Zinatu har kudi ta d’auko a Jakarta ta bawa principal din dan sai tayi duk abinda za tayi dan a Kori Ameera daga makarantar kafin ta tafi sai da ta san duk mallaman dake d’aukar ajinsu Sultana dan duk sai ta bisu ta tsara su idan har kudi na aiki ba Wanda zai kai sultana a makarantar.

Ko da ta koma gida haka ta wuni sukuku har sai da Habu ya dawo take sanar masa ai makarantar su Sultana Ameera itama take yi.

Habu kuwa cikin rashin nuna damuwarsa yace “Ina ga kyautatukan da ta samu har da d’aukar nauyin karatunta na secondary shi yasa kika  ganta a makarantar dan kema Kinsan sule bai Isa sakata a wanan makarantar ba”

Zinatu kuwa halin ko in kula da ya nuna yasa ta bar maganar dan taso ce masa ko zasu cire sultana daga makarantar dan gani take Ameera ta hada kanta da yayanta yanzu matsayin  su daya.

Kudurin da ta saka a ranta yasa ba’a kwana biyu bata je makarantar ba,har sai da tayi sabo da mallaman makarantar  dan burinta ta jawo su a jiki ta hada kai da daya daga cikinsu a Kori Ameera daga makarantar.

Sai dai bata abinda ta lura da kyar ta cimma burinta dan Ameera ta shiga makarantar da kafar dama,farin jini ne da ita kamar me mallamai balain ji suke da ita,dan da an tashi kwatance da ita ake kwatance.

Gashi ko term daya ba’a yi ba an fara mata korafin rashin k’ok’arin sultana duk da extra lesson da ake mata.

Past

   “Ameera dan Allah da gaske kike ko dai mafarki nake yi”?

Ameera yawu ta hadiye ta dago ta kalli Sahar dake jingine a jikin motarsa,ta saki murmurshin yak’e tana “Da gaske nake Sahar ba wasa nake ma ba”

Sahar hamdala ya hau saki Yana “Ameera ba zaki yi nadamar aurena ba na miki alkawari Ina zuwa gida zan gayawa Alhaji Kin ce na turo”

Ameera hawayen dake neman zubo  mata take ta k’ok’arin maidawa dan jiya ko runtsawa ba tayi ba,dan tasan Gangar jikinta Sahar zai aura amma Amjad ne a zuciyarta akan sa ta fara Sanin so,duk da so bai mata adalci daya kamu da kaunar Amjad da tasan Aurenta dashi ba mai yuwa bane ba.

Muryar Amjad da kamshin turarensa da  taji yasa ta dago da sauri “Ameera mai kike yi anan”?

Amjad da isowarsa kenan ya ganta a tsaye da wani dan so yake  ya bi shawarar Abba sule wajen fara fadawa Ameera Yana santa kafin ya sanar da Alhaji Abubakar akan Yana san Auren Ameeran

Hannun Sahar ya zubawa ido da ya miko masa dan suyi musabiha dan wani irin kishi yaji ya rufe shi,bai mik’a masa hannun ba ya Kara jefawa Ameera tambaya da ta dake tare da b’ata rai tana “Yaya Amjad wanan shine Sahar Wanda zan Aura”

“Sahar ga yayana nan Yaya Amjad ku gaisa”

Sahar hannu ya Kara mik’a masa Amjad kuwa da ya ji kirjinsa ya canza bugu har jikinsa na d’aukar rawar maganar da ya fito daga bakinta.

“Ameera yaudarar ka take yi an dade da Mata miji bansan mai yasa ta b’oye ma ba,nine Wanda zata aura ba kuma ta da miji sama dani dafatan zaka hakura da ita ka nemi wata”

Amjad ya tsinci Kansa da fada dan ba yadda zai raini soyayar shekara goma lokaci guda wani yazo sama ta ka yace zai auri wacce yake ganin ba zai iya rayuwa batare da ita ba.

“Yaya Amjad wai wane irin magana kake yi haka da gaske nake ma Sahar zan aura dan muna san junanmu”

Amjad da idonsa ya kada yayi jajjur juyawa yayi ya shiga cikin gidan Yana Jin zuciyarsa kamar ta tarwatse dan bai kawo wai Ameera zata iya soyaya da wani ba,duk da bai tab’a fada mata Yana santa ba ya d’auka,zata fahimci Yana kaunarta tunda kafin ya tafi sai da yace kar ta sake ta saurari kowa kar ta tab’a kula kowa yayi mata kalmomin da ya d’auka zata fahimci Yana kaunarta.

Jiki a sanyaye ya shiga cikin gidan da sallama

Anne da ke shanye kaya akan igiya ta saki murmurshi ta amsa tana “Amjad Kaine tafe da yamman nan”?

“Nine Anne”

Amjad yace a hankali tare da shigewa cikin palon ya zauna, ji yake kamar ya janyo Ameera ta dawo ciki,baya so Ameera ta yarfa shi a gaban saurayinta shi yasa ya shigo ciki.

Koda Anne ta shigo bayan ta gama shanyar,gaisawa suka yi Anne ta d’auko masa ruwa da lemo tana “Kaga matuniyar ka a waje ko”?

“Na ganta Anne waye wanan din daya zo wajenta”?

Murmurshi Anne ta saki tana “Sahar ne shine Wanda zai Auri Ameera”

Shiru Amjad yayi tsawon mintuna Yana Jin Anne nata masa bayanin yadda Sahar ke san Ameera kamar ya mutu,da shekarun da ya d’auka Yana bibiyar Ameera tana wulakanta shi”

“Anne na d’auka zaki fahimci Ina san Ameera,Anne na d’auka zaki gane irin Kaunar da nake mata Anne Ina san Ameera Ina santa da Aure”

Amjad yace a daidai lokacin da Ameera ta shigo bayan ta daidaita nutsuwarta ta aro jarumtaka ta yafa duk da rawar da jikinta keyi

Anne kasa magana tayi ta zubawa Amjad ido maganar da ya mata na sake maimaituwa akanta.

Daga kallon da yake mata daga maganar da yake da alama da gaske yake Yana kaunar Ameera,duk da a baya taso ganewa san Ameeran yake amma Idan ta tuna sabon da yayi da ita sai ta Kau da tunanin haka a ranta.

Ameera kuwa murmurshi ta saki tana “Yaya Amjad kenan taya zaka ce kana sona bayan ni Yar gidan talakawa ce kai Kuma dan gidan masu kudi,ai Babu yadda ma zan aureka dan Ina da Wanda nake so,ko da bani dashi ma Yaya Amjad Kai ma kasan babu yadda za’a yi na Aureka”

“Kar kiyi haka Ameera ni nasan kina sona kina so ki k’i aurena ne saboda abinda ya faru a baya,karki duba duk Abubuwan da suka faru Ameera da,da yanzu ba daya bane su kansu yanzu idan aka ce suyi abinda suka yi a baya,

ba zasu yi ba,Ina kaunarki  Ameera dole daddy ya so ki dole hajiya itama ta so ki”

Sai a lokacin Anne tayi magana tana “Amjad ba za mu iya baka auren Ameera ba kayi hakuri ka bar maganar nan kar ma ka furta suji,Amjad karka jawo mana wani cin mutunci daga wajen Mahaifiyar ka karka jawo mana wani wulakanci daga wajen Mahaifiyar ka ,karka manta irin tsanar da tayi wa Ameera taya ma zaka yi tunanin Aurenta?

Past

Ameera da karambani ta koyi dinki tun tana da shekara goma Sha uku,tun su Anne na ganin shirmenta kawai take sai da sule ya siyo mata keken dinkin da ta nace da masa magiya akan ya siya Mata.

Yadda ta dage ya sa sule siya Mata a cikin irin  kudaden da ta samu kyautar su da a yanzu kadan suka rage masa saboda idan ya fita bai samu wani kudi ba,da kudin yake amfani.

Ko Gwaggo hidimar da yake da ita cikin kudin Ameeran ne,silar Ameera asirinsa na rufe ruf da ba ranar da zai  aza goshinsa a kasa bai godewa Allah ba.

Dinkunan da Ameeran ta fara yi na Yara ya fara jawo hankalin mutane wajen ta dan ta balain iya dinki tafe tafe ta fara hadawa da na Manya,ban da kunshin da take yi.

Taso jawo sultana jikinta,duk da kankantar shekarunta tasan sultana Yar uwarta ce ta rasa mai tayi wa Zinatu da ta dora Mata Karan tsana,dan a ranar da aka basu result din makarantar su sai da ta sha Mari a wajen Zinatun da bata san dalilin daya sa ta mareta ba.

Dan na daya ta d’auka Wanda a gaban mallamai da wasu iyaye da suka zo aka bata kyautar.

Tsanar da Zinatun ke gwada mata yasa ta fara tunanin barin makarantar dan ta lura ba Karamin tsana ta mata ba dan har tsoron ganin ta take.

Anne kawai take iya fadawa Halin da take ciki gefe guda Kuma ga wani irin shakuwa da suka yi da Amjad da sai da yasan yadda yayi aka masa transfer ya dawo makarantar lokacin Yana Ss2.

Dawowar sa makarantar yasa ta fara samun sauki daga wajen Zinatun dan a yanzu ko tazo bata fiye sawa a kirata ba,ta lura Zinatun na balain San Amjad dan a babu yadda za tayi ta bar shi yake muamalla dasu Ameera.

Sultana kuwa na karshen ajin ta cigaba da d’auka har sukayi jarrabawa shiga aji biyu da sai da Zinatu tayi da gaske aka bar sultana ta tafi jss 2 din dan tsabar ma takaici sai da tayi wa sultana bakin duka dan tsabar bakin cikin ta take ji a ranta dan ji take kamar ya zuke k’ok’arin da Ameera ke dashi ta sakawa sultana.

Tana so watarana a kira daya daga cikin yaranta Suma sun tabuka abin arziki iya Amjad kawai taga yana da k’ok’ari a cikin yayanta.

A irin wanan lokacin aka hada gasa tsakanin makarantar su Ameera da wani makarantar da suma na masu hannu da shuni ne, Ameera tana daga cikin na farko farkon da aka zaba akan su shiga cikin gasa.

Duk da Sultana bata da k’ok’ari haka Zinatu ta dage da bada cin hanci aka Saka sunan sultana dan taji duk Wanda yayi nassara zuwa na daya zaa bashi kyautar kudi da wasu Abubuwan ciki har daukar nauyin karatun duk Wanda yaci gasar.

Zinatu kuwa kudi ta hau saki dan kawai a nuna Sultana ce tazo na daya ta hada baki da wata mallaman makarantar da tace za ta mata wnan k’ok’arin dan Sultana tazo na daya,duk da ba kudin da aka sa ne damuwarta ba,tana so itama ace an nuna yarta akan tayi k’ok’ari,tana so itama tayi suna kamar yadda kowa yasan Ameeran da aka buga hotonta a katon calendar akan tafi kowace k’ok’ari a makarantar.

Ameera kuwa tunda aka sa ranar shiga gasan su ta dage ba dare ba Rana wajen ganin tayi karatu Amjad har Sha daya yake kaiwa a gidansu Yana tayata da kwarin gwiwa akan ta kwantar da hankalinta Yana da yakinin ita zata ci.

Amma Ameera bata saki jiki ba haka ta dage da karatu har tana fadawa su sule su tayata da addu’a.

Ranar litinin suka hallara gabad’aya a wani filin makaranta mai girman gaske dan anan zasu gudanar da gasar da daya makarantar da aka hada su.

Su uku ne daga makarantar su Ameera,

Ameera sultana da wata nusaiba

Daya makarantar ma mutane uku ne.

Ameera sai da tayi addu’a kafin aka fara jefa musu tambayoyin tana amsawa da sauri da sauri dan idan ka San amsar kafin mallami ya rufe baki zaka bada amsa duk Wanda ya riga bada amsa yafi maki…..

*PAGE 10*

       Past

Ameera duk tambayoyin kusan ita ta amsa duka bata bawa Sultana da nusaiba damar amsawa ba duk da Sultana ba Sanin ma amsoshin tayi ba.

Haka aka samu awa daya suna fafftawa da daya makarantar da shi ma wani namiji ke da k’ok’arin,mallaman makarantar su Ameera sai murmushi suke dan sun san makarantar su ce zata ci gasar dan Ameera bata fadi ko daya ba.

Da haka aka watse akan ran litinin za’a sanar da makarantar da suka ci dan ranar juma’a suka gudanar da gasar.

 Ameera kuwa cikin farin ciki ta tafi gida  mallaman makarantar suka  ringa jinjina mata.

Zinatu kuwa tana bakin gate a lokacin da suka fara fitowa hararo sultana kawai take a matsayin wacce tayi nassara hararo kalar liyafan da zata hada kawai take.

Idan har sultana ba tayi nassara ba zata so ace itama Ameeran bata yi nassara ba.

Mallamar da ta bawa cin hanci duk yadda taso taga tayi dabaru wajen kalawa Ameera sharri akan da takarda ta shiga wajen,ba tayi nassara ba dan tun kafin ma a fadi sakamako mallamai da yawa sun san nassara ta Ameera ce ita ce ta cinye gasar.

Tana ji tana gani ranar litinin aka kira sunan Ameera a matsayin wacce taci gasar

Zinatu kuwa kamar ta mutu dan bakin ciki,dan wanan karon kyautatuka Ameera ta Kara samu tasan yanzu Sule ba zai na kukan talauci ba,ba zai na neman taimakon kowa ba iya wadanan kyautatukan da Ameeran ke samu tasan dasu zai na amfani dan wanan karon ma ta samu kyautar kudade.

Duk inda ta Kai da tayi tunanin kudin da take dashi zai iya siyawa yaranta k’ok’ari ba iya sultana ba, kudin bai siya mata ba sai da result da take iya siya musu da kudi dan results din da ake bawa Sultana ba nata bane bata kawai akeyi ba dan k’ok’arint ba.

Sai da suka tafi Ss1 Suka hadu a aji daya dan Sultana A take Ameera kuma a B.

Girman da Ameera keyi yasa ta fara mallakar hankalinta tasan Zinatu a duniya ba Wanda ta tsana sama da ita,tsanar da ta mata kamar zata kasheta,haka ma sultana ta dora mata Karan tsana ba Wanda bata gulmarta da ita,Idan kuwa zasu hadu waje daya sai ta zageta,ta gama barbadata a makarantar akan sun zauna a gidansu,su talakawa ne d’aukar nauyin karatun ta akayi.

Ameera kuwa ranar da abin ya isheta bata fadawa Hanne da bata da aikin daya wuce bata hakuri ba.  Gwaggo ta samu ta  fada mata irin abinda sultanan ke mata a makaranta.

Gwaggo kuwa da ranta yayi balain b’aci fada ta rufe Ameera dashi akan mai yasa bata tab’a fada mata ba,ai da ta dade da d’aukar Mataki, shikenan dan niimar ma da rufin asirin da Allah yayi musu bakin ciki suke kenan?

Anan ta hau fadawa Ameera ta daina tsoron sultana,sultana nayi mata ta rama idan ta kama ta zaneta ai ba girman ta tayi ba.

Duk bakin ciki suke saboda tafi su k’ok’ari.

Shawarar Gwaggo Ameera ta rike gam,daga Lokacin ta daura damara dan itama yanzu tasan ciwon kanta.

Suna fara Ss1 aka nada ta monitor.

  Wanan damar da ta samu itama ta hau rama duk abinda sultana ke mata dan Sultana bata da aikin daya wuce surutu idan za tayi sau goma sai ta rubuta sunanta a jerin noise makers,idan an tashi zanne masu surutun sai an zaneta.

Haka sultana za tayi ta zaginta itama tana ramawa.

Akwai ranar da Zinatu taje har cikin gidan dan a ranar an farfasawa sultana hannu,daidai da Habu sai da ransa ya b’aci da yaji Ameera ce tasa aka Zane sultanan suka hada da yiwa Ameera sharri.

Zinatu kuwa jikinta har rawa yake a lokacin da suka iso gidansu Ameera sultana na biye da ita.

A ranar Alhamis ne ba islamiyya.

Anne na yiwa Fareeda kitso gidan nasu ko’ina tsaf dan Hanne akwai balain tsafta.

Ameera kuma na kan Keke tana dinkin uniform da aka kawo mata daga wani makaranta akan ta dinka,dan yanzu makarantu da yawa kawo mata dinkin uniform suke.

Sule yanzu bashi da wani fargabar abinda zasu ci dan Allah ya masa rufin asiri ta silar Ameera.

Sule ma Kansa na gida a ranar dan ba shi da wani aikin da zai fita yayi.

Yadda aka banko k’ofar batare da sallama ba yasa Hanne dagowa a tsorace dan ba Karamin buga k’ofar Zinatu tayi tana hucci ba.

Ameera kuwa juyowa tayi tana kallon su Zinatu kuwa ta Kalli Sultana da ke matsar kwalla dan ita ta ringa zuzuta ciwon da hannunta ke mata da yasa Zinatu kasa hakuri suka nufo gidan.

Kallon da tayi wa sultana yasa Sultana nufar wajen da Ameera ke zaune tana kallon su.

Muryarta da Sule yaji yasa ya fito daga dakin ya tsaya a bakin k’ofa Yana Jiran yaga iya gudun ruwan Zinatun da a rayuwa ba wacce ya tsana sama da ita.

Hanne kuwa mik’ewa tayi tana “Wai lafiya kuwa Zinatu mai ya faru”?

Saukar Marin da Sultana ta kwashe Ameera dashi yasa Hanne sakin sallati tana “har cikin gidanmu ma bamu tsira ba Zinatu”?

Ameera kuwa kumatun ta ta dafa tana kallon Sultana da ta koma wajen Zinatu da sauri.

Zinatu kuwa bata ko kalli Hanne ba balle ta lura da sule dake tsaye da idonsa ya kada yayi jajjur Yana kallonta

Ta fara magana tana “Daga yau duk ranar da kika Kara shiga harkar Sultana wallahi da kaina zan b’allaki har kin isa kisa ayiwa yata irin wanan duka”

“Yanzu har gida kika taso yarki a gaba akan tazo ta Marar min yarinya a gida, Zinatu wai Mai matsalarki damu ne,yanzu a gidanki muke zaune da zaki na mana abinda ranki ke so”?

Hanne tace hawaye na cicciko mata a ido.

Zinatu kuwa tsaki taja tana “Ki fadawa yarki kar ta Kara rubuta sunan Sultana a cikin jerin masu surutu,ki fada mata ta fita daga harkar Sultana idan ba haka ba watarana sai na b’allata”

Daga haka ta jawo hannun Sultana suka nufi hanyar k’ofar fita.

Fincikar da aka mata da k’arfi yasa ta juyo Sule ya kwashe ta da wani irin Mari kafin ta dawo daidai ta sake kwashe ta da wani Marin Yana Jin kamar a yanzu ta kala masa sharri akan ya Mata fyade.

Zinatu kuwa kumatunta ta dafe tana “Ni ka Mara sule”?

Wani Marin ya Kara kwashe da shi Yana “Duk ranar da wanan tsinannen kafar taki ta Kara tako min gida da gawarki za’a fita daga gidanan,duk ranar da ko ke, ko yaranki wani ya sake tab’a min yarinya wallahi sai na baki mamaki”

“Sule ni ka wanka wa Mari har uku”?

“Wallahi zan Kara miki Zinatu dan yadda nake Jin tsanar ki zan iya kashe ki,dan har na koma ga Allah ba zan daina Jin radadin kazafin da kika min ba”

Zinatu da yatsun Sule suka fito rudu  rudu a kumatun ta idonta take jini ya kwanta dan fara ce sol girgiza kanta ta hau tana

“Wallahi Sule sai kasan ka mareni sai naga gatanka a garin nan”

Wani irin hankadata Sule yayi dan ji yayi kamar ya hau kwallo da ita.

Hanne kuwa da taji hankalinta ya tashi da marukan da sule yayi wa Zinatu ta fara magana tana “Abban Ameera da baka mareta ba,da baka biye mata ba,kana Kallon ba abinda ka mata ma ta Maka sharri Ina ga yanzu ka tab’a ta”

“Hanne har cikin gida ta taso yarta a gaba akan tazo ta mari Ameera,duk abinda take yiwa Ameera a makaranta da ita da yarta wallahi na sani ban tab’a nuna muku bane,duk ba wani abu yasa ta dorawa Ameera Karan tsana ba sai dan tana makarantar da yarta take yi,akan me zata sako min yarinya a gaba, shikenan dan ni talaka ne sai tayi tunanin takani a duk lokacin da ta ga dama Hanne duk abinda zai faru sai da ya faru amma idan har zata sake takawa tazo gidanan da zumar cin mutuncina wallahi zan Mata fiye da haka”

Daga haka sule ya nufi cikin daki Yana jin kirjinsa na masa zafi.

Ameera kuwa kuka kawai take dan yatsun Sultana sun kwanta akan fuskarta Marin da ta mata ya shigeta.

Hanne kuwa fada ta rufe Ameera dashi tana “Ai laifinki ne Ameera akan me zaki na shiga harkar Sultana,idan zata shekara tana surutu Ina ruwanki akan me zaki rubuta sunanta kamar baki san halin su ba”

Sule kuwa tsawa ya dakawa Hanne daga daki Yana kar ta sake tayi wa Ameera fada da wane Ameeran zata ji da dukan da aka zo aka mata har gida ko da fadan da take mata”

Ameera kuwa alwashi ta ringa Sha akan sai ta rama Marin da ta mata haka ta shige daki tana kukan bakin ciki.

Hanne kuwa gabad’aya hankalinta ya kasa kwanciya dan bata san mai zai biyo baya ba.

Ganin biyar tayi yasa ta mik’e ta shiga kitchen dan ta dora musu Abincin dare.

Ta d’auko tukunya kenan ta fito Habu ya fado gidan kamar an jefo shi daga yadda jikinsa ke rawa yana kwallawa sule suna yasa gaban Hanne faduwa.

Fitowar sule daga dakinsa da yasan dama za’ayi haka yasan zai zo tunda ya tab’a Yar gwall.

Da wani irin speed yayi kan sule suka hau wani irin k’ok’awa,a daidai lokacin da yan sandan daya zo dasu suka shigo Suma suna “Alhaji kayi hakuri muyi aikinmu karka masa komai”

Habu dak’yar ya yarda ya daga sulen da shima ya zage iya karfinsa Yana zuba mishi naushi a fuska.

Hararo yatsun Sule kawai yake a fuskar Zinatu da jinin da ta kwanta a idonta yanzu haka tana ta Ihun ta daina gani abinda yayi matukar daga masa hankali sai da ya biya ta wajen yan sanda ya tafi dasu,dan sai ya d’aure sule zai samu nutsuwa ko mai gwaggo za tayi ba zai sake shi ba har Zinatun sa Sule zai yiwa irin wanan dukan.

Dan Zinatu cewa tayi ruwan cikinta sule ya hau ya ringa kirba Mata naushi.

Kudin da ya bawa Yan sandan yasa suka yi ta jibgar sule har sai da suka Isa station da zuwan su suka kulle sule.

Dan Habu cewa yayi su kulle shi har sai Zinatu tace ta yafe zai yarda a sake shi.

A wajen fitowa daga gidan sai da ya watsar da Hanne da ta bugu da bango saboda rike masa kafa da tayi tana rokonsa akan ya rufa mata asiri kar ya kulle Mata sule.

Ganin an tafi da sule ana jibgarsa yasa ta zari hijabinta tayi gidan gwaggo dan gani take ita kadai ce zata iya yiwa habu magana yaji dama irin abinda take gudu kenan.

Su Ameera kuwa sai kuka suke.

Gwaggo na Shirin tada sallah Magriba Hanne ta fado cikin gidan cikin Ihun kuka tana ta shiga uku ta lalace.

Gwaggo da taji kirjinta kamar ya fado ta dafe zuciyarta cikin sallati tana “Hanne mai ya faru karki ce min wani Abu ne ya samu Sule”?

Cikin Ihun kuka Hanne ta kwashe komai ta fada mata tana “Gwaggo irin abinda nake gudu kenan nace masa da ya sani bai tab’a ta ba, Gwaggo muje dan Allah mu bashi hakuri dan nasan ba mai masa magana yaji sama dake”

Gwaggo sai da ta dafe bango saboda juya mata da gidan ke yi,sallati kawai take jikinta na rawa da taji wai Habu ya kulle Sule.

Cikin rawar murya ta fara magana tana “Yanzu Sule Habun ya kulle,yanzu akan ya Mari Zinatu ya kulle kaninsa da suke uwa daya uba daya”?

Gwaggo sallah da bata yi ba kenan saboda tashin hankali.

Ita da Hanne suka nufi gidan Habun.

Zinatu kuwa ihu kawai take tana karawa akan ta daina gani Habu kuwa da hankalinsa yayi balain tashi hannunta ya rike Yana “Ki tashi na kai ki asibiti Zinatu ba Abunda zai samu idonki in Sha Allahu”

“Ruwan cikina sule ya hau ya ringa naushina Yana harbina da kafa baban Amjad wallahi da gaske nake bana gani ya Maidani makauniya”

Ta Kara rushewa da kuka

Habu da yaji kamar ya mutu saboda tashin hankali cewa yake “Dan Allah Zinatu ki tashi na kai ki asibiti,na kulle Sule wallahi sai shima an tsiyayar masa da ido na bada kudi ayi ta jibgarsa”

“Gwaggo na zuwa zaka Saka a sake shi ni Kuma gani ya Maidani makauniya baban Amjad ba zan iya ba”

“Wallahi ba zan saka a sake shi ba Zinatu kashe min ke yaso yayi,ai Gwaggo itama kanta ba zata soma cewa ma na sake shi ba,sau biyu yana tab’a min ke wallahi ba zan sake shi ba  Zinatu dan Allah  ki tashi na kai ki asibiti”

Zinatu kuwa ihu ta cigaba da kurmawa tana bata gani Wanda hakan ke Kara dagawa Habu hankali.

Wanda sai da yayi da gaske ya iya kinkimarta Sultana sai Kara Ihun ai sule mugun duka ya Mata take dan Zinatu duk ta zugata akan ta fadawa Habun mugun duka sule ya Mata.

Yana k’ok’arin fita da motar Gwaggo da Hanne suka shigo cikin gidan.

Zinatu kuwa ganin su da tayi yasa ta Kara volume wajen kurma Ihun idonta.

Habu kuwa ya fito daga motar jikinsa na rawa ya isa wajen Gwaggo yana “Gwaggo na rantse da Allah sai sule ya kare rayuwarsa  a kurkuku,ba Abunda zaki ce min da zai saka na sake shi,kwanaki fyade yaso yi mata a gaban idonki kika ga ya fito  daga dakina,kika ce karya ta masa,yau kuwa dukanta yayi gashi ya makantar min da ita idan wancan na hakura wallahi wnan karon ba zan hakura ba Gwaggo sai naga abinda Sule ke takama dashi”

Daga haka habu ya shige cikin motarsa ya ja suka tafi.

Gwaggo kuwa sai da Hanne ta riketa dan kafafunta rawa yake dan tasan wanan karon Zinatu ta hada makircin da mai fitar da sule sai Allah,bata san mai yasa Habu ya kasa gane kudurin Zinatu shine taga ta raba shi da Kowa ba,amma san Zinatu ya rufe masa ido ya kasa ganewa.

Hanne taso su tafi gwaggo ta dage akan ba inda zata je sai ya dawo ya fada mata station din da ya kai sulen.

Dan sai sule ya fito zata samu kwanciyar hankali sai kuka take tana Jin kirjinta na mata nauyi dak’yar take numfashi.

Zinatu kuwa ba Karamin dadi  taji ba da Habu yak’i sauraran Gwaggo,sai gwaggo tayi nadamar nuna mata tsana,sai sule yayi nadamar tab’a ta dan yayi.

Duk da ba abinda ya samu idonta haka ya cigaba da kurma ihu akan ita bata gani sai da aka Kai ga bata gado dan idan ta yarda suka dubata ta koma gida zaa d’auka Karamin abu Sulen ya Mata.

Burinta yanzu duk wani abu da Sulen ke dashi ta silar Ameera tana so ya kare wajen faffutukar fito da Sulen.

Sai ta tabbatar da sun rasa komai zata yiwa Habu magana akan ya saki Sulen.

Tsoronta daya kar gwaggo tace zata tilasta masa dan ta lura Habu na gudun b’acin  ran Gwaggo.

Habu kuwa kasa zaune yayi ya kasa tsaye,wani irin tsanar sule kawai ke Kara darsuwa a ransa,a yadda yake Jinsa bai ga Wanda zai saka ya saki sule kurkusa ba sai dai idan Zinatun ce tace ta yafe masa.

Idan ya tuna yadda yaga yatsun Sule a fuskar Zinatun sai yaji zuciyarsa  na tafasa.

A takaice Zinatu haka ta cigaba da langabewa cikin sharri daga tace cikinta sai tace idonta dan kawai kar a sallameta.

Sai barazanar take wa Habu akan ya saketa ita ba zata iya cigaba da zama dashi ba watarana sule kasheta zai yi idan har aka sake shi da wuri.

Dan gwaggo ta dage akan sai ya fito  Mata da sule.

Daga Hanne har Gwaggon sunyi wani mugun rama.

Barazanar da Zinatun ke yiwa Habu da yake jin Zinatu tamkar Ransa.

Yasa ya shirya barin garin dasu Zinatu,dan ba zai tab’a sakin sule kurkusa ba yaga Kuma alamar Gwaggo ta d’auko hanyar tsine masa idan bai saketa ba.

Ko da ya fadawa Zinatu shirinsa,cikin kuka da kirsa tace gwara su tafi idan an kwana biyu sai su dawo dan a yanzu ba zata so sule ya fito ba yanzu da take ganin Hanne a zauce dadi take ji, sintirin da Ameera ke yi wajen zuwa a Asibtin tana zubewa akan gwiwarta akan ta yafe mata tasa baki a saki sule na balain yi mata Dadi.

Ranar talata da sassafe suka dau hanyar jigawa dan Habu ya fara Jin tausayin Gwaggon gani yake idan har ya sake ganinta ba zai iya bijirewa umarnin ta ba.

Amjad kuwa guduwa yayi dan haukace musu yayi akan shi ba zai bi su ba,zai zauna a gidan shi kadai.

Sun d’auka da wasa yake sai da suka zo tafiya suka ga ya gudu

Har Habu zai fasa tafiyar Zinatu tace su tafi

Har lokacin nuna masa take ita bata gani sosai

Suna tafiya gwaggo na isowa cikin tsananin b’acin rai jiya ko runtsawa ba tayi ba rabonta ma da baccin kirki ta manta,bata iya bacci idan ta tuna Sule na kulle bata iya zuwa ganinsa ba Hanne ke bata labarin yadda aka canza masa kamani da duka.

Zuwan da tayi na ko Habu ya saka a saki sule ko ta tsine masa dan duk wani kudinta da irin kudin da su Hanne suka b’oye sun fito dashi dan su fito da Sulen amma haka wani dan sanda ya karbe kudin ya kuma ce habu yace kar a sake shi dan matarsa ta makance.

Gwaggo kanta ne ya hau juya mata a lokacin da Amjad ke sanar mata cikin kuka akan sun bar garin.

Gwaggo kuwa da gefen kanta ya Sara mata sai da ya kai ta ga zubewa a kasa mafarin rashin lafiyar gwaggo kenan.

Hanne kuwa ta dawo kamar Mahaukaciya ga jinyar gwaggo da take ga sintirin zuwa wajen sule da ke fama da raunika a jikinsa saboda dukan da yake sha a hannun Yan sanda.

Biyar basa magani yanzu dan Yan sandan duk sun karbe musu kudadensu cikin yaudara.

Ibrahim da dan bature Shima yaji labarin kulle Sule da Habun yayi Suma sunyi iya nasu k’ok’arin wajen ganin an saki Sule amma abun ya gagara dan ba Karamin kudi Habu ya bayar ba.

Ibrahim kuwa  ganin sun kafe akan sai dai idan Habun ne ya musu umarnin su saki sule zasu sake shi,yasa ya nufi can jigawa  neman Habun dan a wajen Amjad yake Jin labarin jigawa suka tafi

Dan Amjad na gidansu Ameera har kuka yake na abinda mahaifinsa yayi.

Dak’yar Ibrahim ya gano gidan Habun dake can jigawan

Jikinsa har wani rawa yake a lokacin da aka Bude k’ofar da ya buga a haukace dan ji yake zai iya kashe Zinatu da shi Kansa Habun.

Da habu ya fara cin karo a tsakar gidan Yana k’ok’arin Bud’e k’ofar mota ya shiga da alama fita yake so yayi.

Ibrahim kuwa bai yi wata wata ba yayi kan Habun ya sure shi yayi sama dashi ya dawo ya Maka shi da kasa yana “Akan mace zaka kulle kaninka?akan mace zaka baro Mahaifiyar mu a kwance?

Naushi da duka kawai yake kaiwa Habu a daidai lokacin da Zinatu ta fito da taji Ihun Habun.

Ganin Ibrahim ne yasa ta ci burki ganin ya dago Yana kallonta yasa ta koma ciki da gudu, Ibrahim kuwa yayi kanta da gudu Shima Yana “Ni zan kashe ki da hannuna kafin ki kashe min uwa”……

*PAGE 11*

            Past

Habu da fashashen baki ya bi Yaya Ibrahim cikin gidan da yaji Yana jijjiga k’ofa da k’arfi

Dan daki Zinatu ta shige da balain sauri jikinta na rawa,dan haka kawai Allah ya saka mata tsoronsa,dan ko Habun ma shakkar sa yake.

Yaya Ibrahim kuwa jijjiga k’ofar yake Yana “Ki Bud’e idan kinsan kin cika cikakkiyar Yar iska wallahi sai na sumar dake inya so Habun idan yasan shi din dan Halak ne ya kuma haifu ya sa a kulleni nima”

“Yaya Ibrahim kasan mai Sulen yamin ne da zaka zo ka shigar masa har baka ji ta bakina ba ka rufeni da duka”?

“Habu Hala kudin da kayi hauka ya saka ka da rashin Hankali,da irin wanan kudin naka wallahi Habu gwara ma zama a cikin Talauci wai har akan Sule ya tab’a Maka mata zaka kulle Sule yanzu tsawon sati uku da kwana hudu,kanka daya kuwa Habu ko dai kana shaye shayene?Sule kaninka da kuke uwa daya uba daya kasa aka kulle dan kawai ya tab’a matarka?

“Kai yanzu zaka yarda na tab’a lafiyar matarka Yaya Ibrahim?sau biyu sule na tab’a min mata,na farko fyade yaso Mata na biyu Kuma ya so ya makantar min da ita,wallahi Allah ne ya takaita da yanzu Zinatu bata gani,haka kawai zai Sako min Mata a gaba,kaga dukan da yayi mata”?

“Yanzu dai ka zabi matarka akan dan uwanka,yanzu dai akan matarka ka daura damarar wulakanta dan uwanka saboda kawai kana da kudi?kana wajen a lokacin da Sulen ya daketa?,uban mai ya kai ita Zinatun gidan Sulen?duk baka yi bincike ba matarka ta zo ta tsara Maka karya ka hau kai ka zauna Habu?dan kawai kana da kudi kake tunanin zaka taka Wanda ranka keso har da dan uwanka a ciki?a kaddara a gaske Sulen ya daketa,idan matuniyar arziki ce ita zata so ka kulle shi?har wai ka gudu saboda kar ma a roke ka sake shi ko”?

“Yaya Ibrahim so kake kaima kawai ka goyi bayan Sule,amma ko Kai sule yayi wa matarka abinda yayi wa Zinatu wallahi sai ka d’auki matakin da yafi nawa,kaga fuskar Zinatun a lokacin da ta dawo zagewa yayi ya ringa dukanta kamar ya samu Dan uwansa namiji”

“Kana wajen ne Habu ka tambayi tsinanniyar matarka abinda tayi wa sule kafin ya kai hannu Jikinta”?

“Gaskiya Yaya Ibrahim Ina ganin girman ka Ina baka girman ka a matsayin ka na yayana ya kamata ka ja girmanka dan idan Kai Sule yayi wa abinda yamin wallahi sai kayi Abunda yafi nawa gaskiya ka daina tsinewa matata har cikin gidana kazo kana dukana,shikenan dan Ina da kudi Allah ya rufa min asiri zaku hada min Kai duk abinda nayi ba mai goya min baya sai Sule kuke goyawa baya”

Kallonsa kawai Ibrahim yake Yana Jin wani irin b’acin rai na Kara taso masa Yau ban da Gwaggo na cikin matsanacin hali da ba zai tab’a taka kafarsa yazo wajen habu ba,dan daga lokacin da yaga ya dorawa kansa wani girman Kai dan kawai yayi kudi ya tattara shi ya watsar,Wanda hakan da yayi na Jan girman sa yasa Habun ke shakkarsa.

Duk da ba kudi ne dashi ba Shima buga bugan yake cikin rufin asiri hakan yafiye masa da dai yazo neman wani abu a wajen Habu

Cikin wani irin murya ya fara magana Yana “Habu kayi asarar rayuwarka idan har akan mace da zaka iya canza ta sau dubu,zaka kulle dan uwanka da baka Isa canja shi ba,zaka jefa mahaifiyarka a cikin mawuyacin hali har silar abinda kayi mata ya Kai ta da kwanciya sai dai a kwantar a tayar,Kai ma kasan idan ba dan ka kulle Sule ba wallahi baka isa ka ga kafata a gidanka ba,dan ko duniya kake dashi Habu wallahi ba abinda zan zo nema a wajenka,banga kudin da kake dashi da har yasa ka dorawa kanka wani girman Kai,a yanzu rayuwarka na cikin mugun hatsari da ka hau motar da zata jefa ka cikin masifa na kudi da mace,daya daga ciki kawai idan baka dace ba zai kai ka ne ya baro balle har da ka hada biyun kana wulakanci saboda kana da kudi,ka fifita matarka akan danginka, Habu wallahi sai kayi nadamar wanan abun da kayi ka rubuta ka ajiye mu din da ka raina ka fifita tsinaniyar matarka akan mu wallahi watarana sai ka neme mu idan a yanzu ba zamu Maka amfani ba saboda kawai bamu da kudi watarana sai kudinka sun gaza maka abinda Yan uwanka zasu ma idan  har ka sa aka  saki Sule Kai din ba dan Halak bane ba”

“Ke kuma ki cigaba da halakar dashi,ki cigaba da juya shi abinda kika yiwa Gwaggo da izinin Allah sai anyi miki,abinda kika mana in Sha Allah sai an samu Wanda zai miki kema shegiya tsinaniya laaananiya naso ki fito wallahi sai na miki dukan mutuwa idan Habun har yasan shi din cikakken dan iska ne ya gwada min abinda yayi wa sule yaga ni”

Ibrahim yace cikin daga murya yadda Zinatu zata juyo shi

Daga haka yayi hanyar fita Habu ya kauce da sauri dan yasan zai iya kai masa wani mugun dukan yasan halinsa yasan dan har gobe duk da kudin da yake dashi Yana shakkar sa.

 jikinsa sai da yayi balain sanyi da maganganun da yayi.

 Halin da yaji gwaggo na ciki  ya matukar daga masa hankali.

Akan kujera ya zube ya dafe Kansa da hannu biyu.

Sheshekar kukan Zinatun  da ta fito daga dakin yasa ya dago da Kansa Yana kallonta

Gefensa ta zauna tana”Baban Amjad bansan Mai yasa duka Yan uwanka suka tsane ni ba,Yau banda Allah ya rufa min asiri da Wallahi Ina nan a makance,wai ace kaninka yayi min irin wanan dukan su cigaba da goyon bayansa,ba wanda ya nuna abinda yayi bai dace ba,Ni dai Baban Amjad Ina ga gwara kawai ka sauwake min kawai su aura ma wacce suke so”

Zinatu ta karashe cikin kuka har da majina

Habu kuwa da jikinsa ya gama macewa ya fara magana Yana “Zinatu bansan mai matsalar su ba,duk sun kasa gane girman laifin da sule ya aikata,sai laifina suke gani yanzu abinda ya fi daga min hankali wai Gwaggo na kwance yanzu so suke su nuna nine silar kwanciyar ta,duk abinda nayi sai an ga laifina abu kadan sai suce dan Ina da kudi nake haka”

“Nidai ka sa a sake shi tunda yanzu laifina ake gani,na dauka ma ka dade da sawa a sake shi shiyasa ban Kara ma maganar ba”

Habu kamar mai Jiran umarnin Zinatu ya mik’e ya Isa wajen da wayar sadarwa yake ya d’auka ya lalubo lambar Yan sandan Ya basu umarni akan a saki sule.

Koda ya kashe ya koma ya zauna cikin kirsa zinatu ta cigaba da nuna mata ya saketa kawai ita yanzu tasan bakin jini zata kara yi a wajen danginsa tunda duk goyon bayan abinda Sulen ya mata suke yi

Tasan idan ta furta saki hankalinsa tashi yake rarrashinta ya hau yi Yana ta daina maganar rabuwa dashi ,shi ba zai tab’a rabuwa da ita ba.

A Daren yaso su koma katsinar amma Zinatu ta nuna ya bari sai jibi,baa san ransa ba ya hakura dan duk da ya sa a saki sule hankalinsa na wajen Gwaggo.

Ibrahim kuwa da b’acin rai ya Isa katsina ransa a balain bace nadamar zuwa wajen Habun kawai yake Yana Jin tsanar shi da Zinatun.

Koda ya tashi gidan Sulen ya sauka dan gwaggo na gidan dan Hanne ke kula da ita.

Balain tausayin Hanne yake da yaranta,ya kasa yarda wai Habu ne ya jefa iyalan sule a cikin wanan tashin hankalin

Jiki na rawa Hanne ta masa sannu da zuwa dan tasan da zai je jigawa wajen Habun  idonta a kukumbure saboda kukan da take Sha a kullum.

Tausayinta yasa ya kasa ma amsa sannu da zuwan dan yasan ba zata ji labari mai dadi a bakinsa ba.

Dakin su Ameera ya shige dan nan gwaggo ke kwance.

Yana Jin Hanne na binsa a baya

Itama gwaggon tana ganinsa ta fara k’ok’arin mik’ewa dan ta matsu sule ya fito.

Bata iya bacci yanzu sai tayi da gaske take ma iya ibada dan jikinta ba kwari kirjinta kuwa yayi ta mata ciwo da nauyi, gargadi aka mata a asibiti  akan yawan tunani da take dan Jininta hawa kawai yake.

kaf yaranta ba mai kyaun halin sule,sai gashi shi ne mai ganin jarrabawa iri iri.

Har baki taso yiwa Habun dan zata iya cewa ma bacin rai yasa ta masa kalamai marasa dadi daga baya ta hau istigifari tana Allah kar ya amsa addu’ar da tayi masa.

Ibrahim kuwa dakewa yayi ya kira sunan gwaggo Yana “Kiyi hakuri banga alamar Habu zai saki sule kurkusa ba zuwan da nayi ma rashin kunya yamin, Habu yayi Nisa baya Jin komai zaka fada masa a yanzu ba ji yake ba,dan haka gwaggo kiyi hakuri,Hanne kema kiyi hakuri mu cigaba da Taya Sule da addu’a dan addu’a kawai shine mafita a Yanzu.

Dan yanzu kasar nan sai kana dashi kake mutum,ko da kashe mutum kayi kana bada kudi za’ayi kashe maganar a lankayawa ma Wanda bai yi kissan kan ba dan kawai shi din talaka ne,a yanzu talaka shine abun tausayi abin wulakantawa,Yau banda Habu yana da kudi bana Jin sule zai yi Koda kwana daya ne,dan Zinatu itace da laifi tunda har ita tazo gidan Sulen da kafarta.

Da yake Yan sandan yanzu ba gaskiya suke bi ba ai basu bamu damar ma da zamu fadi abunda Zinatun tayi ba maganar sule kawai suke ji ba yaren da suke ganewa sama da kudi.

Gwaggo na tsani Habu,idan har zai iya yiwa sule haka banga abinda zan yi dashi ba Habu ko mutuwa yayi ba zan je kan gawarsa ba”

“Karka ce haka Ibrahim karka manta Kaine babba ,karka manta wasiyyar da Babanku ya bar muku,Habu ya hadu da shaidaniyar mace dake san ya juyawa Yan uwansa baya ta k’arfi da yaji,Ina rokon Allah ya bani tsawon rayuwa naga ranar da Habu zai gane cewar Zinatu hatsabibiya ce a yanzu duk inda aka kai ga ganar dashi a fada masa gaskiya ba zai tab’a ganewa ba dan yayi nisa baya Jin kira,bamu da kudin Allah shine gatan sule zan dage da addu’a in Sha Allah zasu saki sule kwana kusa”

Gwaggo ta karashe tana share hawayen dake zubo mata

Hanne kuwa dake bakin k’ofa ta saki labulen dakin itama hawayen na gudu a fuskarta na tsananin tausayin Sule da jiya sai da taci kuka ta gode Allah da taga yadda  yake Jin jiki dan bama shi da Lafiya.

Bata Jin zata iya cigaba da jure ganin Sule a kullen dole tasan nayi.

Kullum take kai masa abinci Ameera ce Yar rakiyarta da Amjad.

Koda suka isa station din sai da ta dandana tuwon da ta kai aka kira sule ya fito fuskarsa a kukumbure da dingishi ya fito dan kafarsa mugun ciwo yake masa dan wani dan sanda da wanan sandan nasu ya bubbuge masa kafafu.

Yayi wani Irin rama gashi ya cika masa fuska ya kasa yarda Habu zai iya masa irin wanan zaluncin.

Hawaye Hanne kawai take a lokacin da ya fito minti biyar kawai aka bata

Yana zuwa ya kira sunan Hanne a wahalce Yana “Hanne ko gidanan zaku Saka a kasuwa ku siyar a kawo kudin ko zasu sakeni,yanzu idan kika tambaye su laifin da na musu suka kulleni har da irin wanan dukan basu da abinda zasu iya cewa Hanne Dan kawai bani da kudi yayana ya wulakantani haka?Hanne kafata ji nake kamar na cire na Yar ko bacci bana iya yi”

Kuka Hanne ta fashe dashi tana “In Sha Allah ba zaka wuce gobe ba zasu sake ka”

“Taya zasu sakeni Hanne bayan Yaya Habu bai basu damar sakina ba”?

“Zasu sake ka in sha Allahu Abban Ameera zanyi iya k’ok’arina”

“Ina gwaggo ya jikin nata”?

Tana k’ok’arin magana wani dan sanda yace lokacin da suka bata ya cika tazo ta tafi”

Haka Sule ya juya ya koma ciki yana waigen Hanne dake ta zubar da hawaye.

Hanne kuwa hawayenta ta share ta Kalli dan sandan tana tambayarsa inda ogansu yake tana so ta gan shi.

Sai da yayi shanyata, wulakanta ta kafin ya Mata iso zuwa wajen Asp muttaka.

Wani irin murmushi ya saki a lokacin da Hanne ta shiga office din nasa,har lokacin hawaye zubo mata yake,tunda Habu ya kira yace a saki Sule yaji ba zai iya sakinsa ba dan dole yaci ma burinsa kafin ya saki sule,duk da Hanne a cikin  hijabi take zuwa a mutunce mugun shaawarta yake,ba irin nacin da bai mata ba akan ta bashi hadin kai ya Mata alkawarin zai sakar mata Mijinta amma firr Hanne taki,a yanzu kuwa da ya ganta a office dinsa kila ta yarda da kudurinsa ne shiyasa.

“Ganin ki a office dina na nufin kin yarda da kudurina kenan”?

“Officer kaji tsoron Allah kar kayi amfani da damar da Allah ya baka wajen wulakantani,karkayi amfanin da damar da Allah ya baka wajen gana wa mijina azaba,karka manta ba sata yayi ba ba kissan kai yayi ba,dan kawai muna talakawa kuke cin zalinmu,ba zan iya baka kaina ba dan girman Allah ku sakar min mijina”

“Idan karatu kike biya min har haka ai Ina ga yaci ace na haddace zaki iya tafiya kar na sake ganin kafarki a office dina tunda har kin k’i yarda da bukata ta, a goben nan zan saka hannu a Kai shi kotu kila idan kinga an yanke masa zaman gidan yari na har abada zaki gane da gaske nake”

Kuka Hanne ta fashe dashi,dan duk akan taki yarda da bukatarsa  ya ringa ganawa Sulen azaba.

Kuka kawai take tana tuno irin azabar da Sulen ke ciki cikin sheshekar kuka tace “Na amince”

Muttaka kuwa ya saki murmurshi Yana “ko ke fa sai a yanzu nasan kina balain san mijinki gobe wajen karfe goma Sha daya ki zo nan zan d’auke ki muje Muna gamawa na miki alkawari mijinki sai an fara Kai shi asibti zaa Kai shi gida”

Hanne bata ce masa komai ba ta fito ta samu su Ameera dake zaman jiranta a waje suka koma gida.

Hanne a ranar bata ko runtsa ba tunani kawai take dan har ta amsa mi shi bata ga alamar zata iya wanan kazamin rayuwar dan kawai ta fitar da sule daga kurkuku ba.

Wajen biyu ta hau kan sallaya tayi ta kuka tana addu’a Allah ya kawo musu mafita dan ji tayi ba zata tab’a iya cin amanar Sulen ba,bama zata iya bada kanta ga wani ba.

Mutakka kuwa da sassafe ya nufo station din fuskarsa fal da fara’a dan jiya kwana yayi Yana mafarki da Hanne Allah Allah yake gari ya waye dan so yake yayi Abunda zai yi kafin Habun ya dawo garin dan ya masa karya akan ya sake shi.

Wajen goma Yana zaune dan yasan nan da awa daya Hanne zata iso, sai ga Habu ya shigo office din kamar an hankado shi.

Dole ya masa karya akan ya saki Sulen dan baya so ya bata masa shiri

Sai da suka gaisa Habun ya fara magana Yana “Yanzu naga matar sule tazo da abinci bata ma gani ba dama baka saki Sulen ba?ko kasan rashin sakin sa da kayi zai Kara jawo min laifi a wajen Mahaifiyata”?

Mutakka kasa magana yayi dan Habun duk ya bata masa shiri,bai ga alamar zai samu cikar burinsa ba,cikin tsananin bakin ciki ya kira wani dan sanda yace a fito da sule.

Habu kuwa ya mik’e yayi waje fuskarsa a hade.

Dan Hanne ma bata lura dashi ba

Yana fitowa ana fito da sule daga cell din.

Sai a lokacin Hanne ta lura da Habun Ashe tare suka zo da Zinatu da ta Kame akan benci,da alama itama bata gane Hannen ba.

Hanne kuwa da saurinta ta zube a gaban Zinatu ta kankame mata Kafa tana “Dan Allah dan Annabi kiyi hakuri Zinatu ki yafe mana kisa mijinki ya saki sule dan girman Allah”

Dadi kamar ya kashe Zinatu haka taji bata kai ga magana ba Hanne ta lura da Habun dake tsaye Shima ta mik’e da sauri ta Isa wajensa ta zub’e a gabansa tana bashi hakuri akan yayi hakuri yasa a saki sule.

Sule kuwa kallon habu kawai yake jikinsa na wani irin rawa ba Wanda ya tsana a rayuwarsa sama da Habu da Zinatu.

Zinatu kuwa da ke ji kamar ta taka rawa dan dama burinta taga sun kaskantar da kansu suna Neman wani abu a wajensu mik’ewa tayi tana “Baban Amjad ba dan halin Sulen ba kasa a sake shi”

“Ni tun jiya na bada umarni ai a sake shi bansan Mai yasa baa sake shi ba,kawai Abu daya nake so ayi a gaban Yan sanda Sule ya fita daga harkarki Babu shi babu shiga harkarki.

Sule rashin kwarin jiki yasa ko magana bai iya yi ba,kukan zuci kawai yake na wulakancin da Habun ya masa ya sa hannu akan bashi ba shiga harkar Zinatu.

Hanne kuwa sai godiya take zabga musu kamar zata Ari baki.

Haka sule ya dafa kafardarta da dingishi suka bar station din Hanne kuwa sai hamdala take tana fita ta sama musu abin hawa,tazo da niyyar bada kanta dan a saki sule sai gashi Allah ya rufa mata asiri yayi ikonsa an saki Sule batare tsinanen muttaka ya samu abinda yake so a wajenta ba.

 officer mutakka kuwa kamar ya fashe dan bakin ciki dan yaga samu yaga rashi.

Koda suka isa gidan rudewa yayi da murna gwaggo da bata iya tashi sai gashi ta mik’e a yadda taga sule ya dawo yasa hawaye ya hau zubo mata na tsananin tausayin Sulen.

Su Ameera kuwa sai murna suke kamar zasu kada Sulen da bashi da ko kwari.

Hanne kuwa jikii na rawa ta dora masa ruwan wanka dan ba abinda yake bukata sama da wanka,da aski idan ya huta sai suje asibiti a duba masa kafat tasa.

Gwaggo kuwa kuka ta fashe dashi sosai tana “Yanzu Habu ne ya wulakanta sule haka? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”

Kuka kawai take Sule dake zube a kasa da sai a yanzu yaji nauyin da kirjinsa ya masa na raguwa saboda hawayen da yake zubarwa cikin ciwon abinda Habun ya masa ya fara magana Yana “Gwaggo saboda kawai bani da kudi Yayana yaci zarafina,saboda kawai bani da kudi matarsa ta kala.min sharri,saboda kawai bani da kudi tazo har gidana tasa yarta ta Dakar min yarinya dan na mareta shine laifin da nayi da Dan uwana yayana ya  saka aka  kulleni aka yi ta jibgata kamar wanda yayi kissan Kai, Gwaggo wai ni zan yiwa kaina arziki ne? Gwaggo wai ni zan yiwa kaina arziki ne,shikenan shi talaka bashi da gata kenan?shikenan  talaka shine abun wulakantawa Gwaggo na kasa yarda dan uwana ne yamin iirn wanan wulakancin,akan kawai na Mari matarsa”

“Kayi hakuri sule karka karawa kanka wani ciwon in Sha Allah sai Habu yayi nadamar abinda ya maka Ina rokon Allah ya Ara min tsawon rayuwa Ina nan Ina hada Zinatu da Allah.

“Shigowar Habu fuska a hade da zinatu da ta sunkuyar da Kai ya katse maganar da gwaggo ke yi.

Ido kawai ta zubawa Zinatu tana Kallonta.

Zinatu kuwa murya na rawa ta hau gaida Gwaggo tana ” gwaggo wallahi bansan baban Amjad ya kulle shi ba wallahi sai da Yaya Ibrahim yaje dan Allah karki ga laifina bani da masaniya da na dade da masa magana”

Duk da gwaggo bata iya mik’ewa saboda jirin dake dibanta mik’ewa tayi tsaye.

Habu da hankalinsa yayi balain tashi da ganin yadda gwaggo ta rame jikinsa rawa kawai yake Yama kasa magana da yaga Zinatu na Neman jefa shi a wani masifar da zai Saka gwaggo Kara fushi dashi.

Har gobe Yana shakkar gwaggo ganin ta nufo wajen da yake a tsaye yasa jikinsa d’aukar rawa fuskar Gwaggo kawai fadar masa da gaba yake.

Gwaggo cikin wani irin murya ta fara magana tana ” Habu idan har kasan nice Mahaifiyar ka ni na tsugguna na haife ka,a cikina ka kwanta na tsawon wata tara na shayar da Kai na tsawon shekara biyu,na ci fitsarinka na sha Kashinka Ina umartaka da ka saki Zinatu a yanzu nan”

Habu ido ya zaro Yana sallati.

Zinatu kuwa da taji kamar gini ne ya ruguzo mata  aka mik’ewa tayi tsaye tana “Gwaggo mai nayi wallahi bani nace ya kulleshi ba”

“Habu zan kirga uku yanzu wallahi idan har baka saketa ba na rantse da Allah sai na Maka baki na cire ka daga cikin yarana,daya, biyu,

“Dan girman Allah gwaggo kimin kowane hukunci banda na rabuwa da Zinatu yanzu akan sule zaki Saka na saki matata”?

“Uku na rantse da Allah Idan har baka saketa ba a yanzu zan tsine Maka Habu”

Habu jikinsa rawa kawai yake ya zubawa Zinatu ido da ta zaro ido tana kallonsa baki na rawa yace “Zinatu na!!!!!

*Page 12*

Past

    Zinatu girgizawa Habu Kai kawai take cikin tashin hankali dan bata tab’a Jin tsananin tsoron Saki ba irin yau,duk burga take masa akan ya saketa,duk da gidansu nada rufin asirin Yan uwanta ma suna da rufin asirin ba dai kamar Habun ba dan a yanzu babu kamarta a cikin dangi Kuma har alfahari take da kudin Habun dan ya siya Mata mutunci a cikin dangi tana zuwa ake nan nan da ita.

Habu kuwa kasa furta sakin yayi ya Kara kallon Gwaggo kafin yayi magana, gwaggo ta d’auke shi da marin da ya sa itama ta kusa faduwar

A mugun tsawace tace “Ka d’auka wasa nake ma habu wallahi sai ka saketa kaji na rantse ma ko ka saketa a yanzu nan ko na maka baki”

“Gwaggo ki dubi su Amjad dan girman Allah karki saka na saki babarsu, gwaggo karki manta ni aka yiwa laifi”

“Akan tsinaniyar nan ka kulle kanin ka Habu?har ta taka kafarta tazo cikin gidanan ta sa a Mari Ameera dan Sule ya rama Marin da tayi wa Ameera shine zaka saka a kulle shi ayi ta dukansa kamar Wanda ya maka sata takamar ka kana da kudi zaka yi duk abinda ranka ke so,kaga yadda sule ya dawo kaga irin dukan da ka sa aka masa”

“Gwaggo tace wani sabon kuka na taso mata dan har lokacin sule a kwance yake Yana numfarfashi duk abinda ake bai dago ya kalle su ba hawaye kawai yake zubarwa

Hanne kuwa tana daga bakin k’ofa sai hakuri take bawa Gwaggo tana “Dan Allah gwaggo kiyi hakuri tunda har mun samu Abban Ameeran ya fito,kiyi hakuri ba sai ya saki Zinatu ba dan sakin da zai mata zai saka ya Kara ganin bakin mu”

“Wallahi sai ya saketa sai dai idan bani na haife shi ba”.

Wanan tsinaniyar matar bata da burin da ya wuce taga ta raba shi da kowa na shi,idan matuniyar arziki ce ita ai ba zata ja Habu su bar garin ba ai tana kallon lokacin da muke sintirin zuwa gidan saboda kar ma ya saurare mu shine taja shi suka bar garin”

“Gwaggo wallahi bansa a dake shi ba, gwaggo bansan mai yasa kike fifita sule a kaina ba,naso kiga irin dukan da yayi wa Zinatu wallahi da Ikon Allah take gani saura kiris ya tsiyayar mata da ido gwaggo ace duk Abunda sule ke min Goya masa baya kike, akansa yanzu zaki saka na saki Zinatu”

“Ka saketa yanzu Habu Raina ya fara b’aci bana so na ma kalamai Mari dadi,ka saketa nace”

Habu tauna bakinsa kawai yake Yana Jin kamar ya mutu Zinatu kuwa sai hawaye take gabanta na faduwa

Kamar mai rada Habu yace “Na sakeki saki daya”

“Uku zaka mata dan wallahi ko ka mata daya ba zata tab’a dawo maka ba sai dai idan bana rayye yadda ta shirya tarwatsa min kanku wallahi dole na mik’e tsaye wajen hana ta samun cikar burinta sai idan tana gidanka zata iya hada makircin da zata sa kayi ta hauka da rashin hankali dan da kana da hankali komai Sule ya Maka ba zaka iya kulle shi ba”

Cikin ihu Habu ya fara magana Yana “Haba Gwaggo kince na saketa na saketa yanzu Kuma sai kice sai na mata uku mai na miki haka kika tsane ni kinsan sakin nan da nayi wa Zinatu ya saka min tsanar Sule duk akansa kika saka na rabu da uwar yarana na saketan ma kince sai na mata uku wallahi ba zan iya ba kuma sai na Maida matata koman daren dadewa”

Daga haka ya fice daga dakin da balain sauri Yana Jin kamar ya shako Sulen dake kwance

Zinatu kuwa kamar wacce wutar lantarki ya jata haka taji sakin da Habu ya Mata.

Dakin har juya mata yake duk yadda taso dakewa ta nuna sakin bai dameta ba sai da ta kasa, ta fashe da kuka.

Gwaggo kuwa dake balain Jin tsanar Zinatun tace “Maza jeki tattara kayanki dan Habu ya gama aurenki idan har Ina rayye bai Isa ya dawo dake ba,tunda har ni da na haife shi,ban tab’a bakin cikin auro ki da yayi ba,ban taba nuna miki tsana ba,ban tab’a ce masa dan me ya tare a kanki da danginki ba,duk hidimar da yake dake da Yan uwanki wallahi na sani,nima nayi amfani da karfin Iko na na Mahaifiyar sa mana nace ban yarda ya miki ba mana,amma da yake ke din tsinaniya ce danginsa ne baki so su more shi,kince kar aci nashin wanda Allah ya mana kice akan me,ke gaki a lailai sai yaranki sunfi yaran sule toh bari kiji na fada miki Ameera da iznin Allah sai ta taka matsayin da yaranki basu isa takawa ba tunda har baki da aikin da ya wuce bakin ciki da hassada,dan niimar da Allah yayi wa sule ta silar Ameera kike wa bakin ciki,toh da izinin Allah yanzu Allah ya fara d’aukaka Ameera Maza fita kije ki kwashe kayanki.

“Da gudu Zinatu ta fita dan ji take kamar ta kwanta tayi ta birgima a kasa.

Koda ta fita bata san ma inda take jefa kafarta ba,sai kuka take Habun da ta hango nesa da gidan yasa ta canza hanya,dan tasan Yana balain Santa kamar ya mutu,bata manta wahalar da ya Sha akanta kafin ta yarda ta aure shi ba,dan Allah ya mata kyau,kyaunta ya ringa jawo mata manema dake layi akanta,a cikin maneman nata duk da akwai masu kudi amma Habu yafi haukatata da kudi,duk da ba wani San shi take ba haka ta yanke aurensa dan tasan zata ji dadi,shi kuwa tunda ta amince akan zata Aure shi yake ganin ai ta masa alfarma dan kamar tafi karfin ajinsa.

Sai ta wahalar dashi tasa ya juyawa Gwaggo baya, idan har ita gwaggo ta wulakanta sai ta rama ta hanyar da bata tab’a tunani ba,zata ga ta inda Ameera zata fi yaranta.

Tana Jin Habun dake bayanta Yana kwalla mata kira bata ko juya ba,har sai da ya sha gabanta idonsa jajjur kamar an watsa jini

“Zinatu goben na zan maidaki dakin ki karki daga hankalinki dan Allah ki bar kukan nan”

“Ai na gama aurenka Habu,Mai zan dawo nayi a gidanka,wanan irin tsana da mahaifiyar ka ke gwada min,ga na Yan uwanka ace duk Abunda aka min Mahaifiyar ka bata gani ba, goyon bayan ma dukan da kaninka yamin take wai har akan haka zata saka ka sakeni,tunda har ta sa ka sakeni,Kuma kaima ka sakenin ba Abunda zan dawo nayi a gidanka kaima kasan Ina gama idda zan samu mijin da ya fika idan ma tana tunanin dan ka sakeni ba zan samu Wanda ya fika ba toh ka sanar mata irin wayanda suke sona kafin ka aureni”

“Dan Allah Zinatu karki min haka ni nama Maida auren mu wallahi Gwaggo fushinta na dan lokaci ne wallahi zata sauko dan Allah ki daina daga min hankali ba yadda zan iya Rayuwa batare da ke ba Zinatu kema kinsani, Yau banda Gwaggo ce ta sa na sakeki wallahi ban ga mahalukin da ya isa yasa na rabu dake ba”

“Ba abinda zan ji a yanzu gwara ka yanke ragowar igiyar dan ba zan tab’a dawowa gidanka ba, Mahaifiyar ka ta tsaneni idan yarta aka yiwa abinda sule yamin zata yi yadda tayi shiru ne batare da ta d’auki Mataki ba,sai dan an d’auki Mataki akan cin zarafin da kaninka yamin zata sa a sakeni”.

“Ai da kana sona wallahi ba ma zaka sakeni ba hakuri za kayi ta bata amma da yake baka San darajata ba ai tana cewa ka sakeni ka sakenin”

“Haba Zinatu a gabanki akayi komai fa baki tace zata min,karki manta bakin uwa,wallahi yadda ta hasala zata iya min baki ta Ina zan iya samun kwanciyar hankali da nutsuwa idan Gwaggo ta min baki”

“Toh shikenan ai tunda kana tsoron ayi ma baki shiyasa ka sakeni kaje ta baka wacce ta dace dakai dan na gama aurenka”

Zinatu tace cikin tsananin bakin ciki yadda ya dage yake kare Gwaggo,ta cigaba da tafiyarta.

Habu kuwa kamar zai saka ihu da Karamin hauka,bai ga ta inda zai iya rabuwa da Zinatu ba,duk yadda yaso ta saurare shi ta fahimce shi ko kallonsa ba tayi ba har ta tari abin hawa ta hau ya koma ya d’auko motarsa ya bita a baya Yana Jin tsananin tsanar Sulen da yake Jin idan har Zinatu ta kubce masa shi kadai yasan abinda zai masa,taya Yana zaune da tashi matar amma gwaggo zata saka ya saki tasa matar Kuma duk akansa.

Zinatu kuwa da isarta gidanta dakinta ta nufa ta sauko da akwatin ta dan sai Habu ya sa Gwaggo tazo gidan bata hakuri zata yarda ta dawo mi shi,ta riga da tasan ba zai tab’a iya samun nutsuwa ba har sai ya mai da ita dakinta.

A haukace ya fado dakin duk yadda ya so shawo kan Zinatu bata ko saurare shi ba ta hau Jan akwatin ta tana rantsuwar ta gama aurensa tunda har danginsa da mahaifiyarsa basa sonta.

Kukan barin gidan kawai take na dan lokaci dan ji take kamar tayi zamanta tunda har yace ya mai da ita.

Yadda zata zauna a gidansu da bata iya awa daya kawai take yi.

Su Sultana kuwa sai kuka suke kamar yadda Habu ke neman kuka Yana kar ta masa haka ya mai da ita.

Zinatu kuwa ganin ya rike mata akwati gam yasa ta fara magana tana “Idan har kana so na hakura na dawo gidanka wallahi sai Gwaggo dasu sule sun zo har Gidanmu sun bani hakuri,yadda ta dage akan ka sakeni sai naga ta dage da gaske tana so ka maidani dakina na Kuma ganta a gidanmu wallahi zan yarda na dawo Maka”

Habu kasa motsawa yayi ya zubawa Zinatu ido da ta fusge akwatin ta daga hannun sa ta fada cikin taxin da ta tsayar.

Idan har sai gwaggo taje gidansu Zinatun, Zinatu zata yarda ta dawo masa yasan sai dai ya rasata dan yasan wacce Gwaggo,da a ce ma tana da san kudine sai yayi ta mata ruwan kudi har sai taje gidansu Zinatun ta ce ta dawo dakinta,amma yasan ko kwanciya yayi zai mutu a yadda take da zuciya ba zata tab’a taka kafarta taje gidansu Zinatun ba.

Hankali a tashe ya koma gida ya fara tunanin ta yadda zai samu Gwaggo ta sauko dan idan yace fushi zaiyi da zuciya shine zai cutu.

Kwana biyu kawai da yayi ba Zinatu ji yake kamar rayuwarsa ta tsaya wani irin so yake mata da yake ganin ba zai iya rayuwa batare da ita ba.

Gwaggo hawaye kawai take zubarwa a lokacin da Hanne ke dannawa Sule kafa da ya kumbure da suka dawo daga asibiti dan targade suka masa  acan,banda uban raunikan dake jikinsa ganin Sule a wanan halin yasa ta kuka da zubar hawaye,yau da ace wani ne yayi wa sule wanan zaluncin ba abinda zai hana ta Kai kararsa wajan Allah har sai  ta koma ga Allah sai gashi wai akan mace Habu yasa aka yiwa sule irin wanan dukan.

Taya zata iya barin Zinatu ta dawo rayuwar Habu ba zata tab’a barinta ta dawo ba sai dai idan mutuwa Habun zai yi ya mutu.

Sule kuwa azabar da yake ji a jikinsa ya sa ya kasa magana a lokacin da Gwaggo ta dage Habu ya saki Zinatu.

Sai da suka dawo daga asibiti ya dan ji dama dama ya kalli gwaggo dake ta zubar da hawayen tausayinsa tana gogewa a b’oye ya fara magana Yana “Gwaggo da baki saka ya saki Zinatu ba,dan na fahimci akan Zinatu ya gwammaci ya rabu da kowa tunda mun riga da mun san akanta duk yake wanan abun da sai ki kyalle shi abu daya kawai na sani Gwaggo na hakura da Yaya Habu a matsayin dan uwana,bana so ya rikeni a zuciyarsa yayi tunanin saboda ni kika sa ya rabu da matarsa abu daya kawai na sani ba zan yafe masa wanan zaluncin da yamin ba shi da matarsa,duk dan Ameera da Allah ya d’aukaka ta  taka matsayin da yaransa ke Kai zinatu ta tashi hankalinta,duk dan Ameera na makarantar daya da sultana ta tashi hankalinta,tafi so taga Ameera a wulakance tafi so tagan mu a kaskance tunda har dan Ameera na makarantar da Yar su take duk suke wanan abin Ameera ta bar zuwa makarantar zan cireta,ta cigaba da zuwa makarantar da zan iya d’aukar nauyinta idan bani da hali sai na sakata a na gwamnati tunda saura shekara uku ta gama sakandiren ba sai sun ga Ameera ba zasu ce ta musu wani abun na fita daga sabgar duk da ta shafi Yaya Habu da matarsa gwaggo dan haka kiyi hakuri ki bar shi ya maida matarsa Ina nan Ina addu’a kafin na mutu Allah ya gwada musu ikonsa akaina ni dinan da suka raina zasu san darajata watarana dan shi bawa baya fidda rai da rahamar Allah tunda har Ina rayye ban kuma mutu ba ban tab’a fidda rai ba nima Allah zai min arzikin nan in sha Allahu”

“Sule ba abinda zai saurin kaini makwancina da wuri  sama da na ga kanku ya rabu,Habu ya hadu da shu’umar mata ne da ta kware a makirci ba zan tab’a barinsa ya dawo da ita ba dan itace take san ta raba mun kanku,bana Jin dadin yadda kowa ke san fita daga harkar Habu, Ibrahim haka ya gama rantsuwa kafin ya koma akan bashi ba Habun Kai ma yanzu kazo kana ba Kai  ba Habun taya zanji Dadi Idan naga kanku ya rabu,taya zaku bari mace ta shiga tsakanin ku?

zaku shirya Sule nasan kana da zuciyar yafiya,Muna nan da Kai zaka ga canji a wajen Habu tunda har Zinatu ta bar raywuarsa,Kuma Wallahi makarantar nan da Ameera take yi shi zata gama tunda Wanda ya d’auki nauyin karatun ta na har ta gama ne,idan sunga su ba zasu iya ba su cire ita sultanan daga makarantar”.

Sule bai cewa gwaggo komai ba dan yasan ba zata gane abinda yake nufi ba,ita dai burinta taga kansu a hade,bai ga ta inda zai sake ganin farin Habu ba sosai yake Jin tsanar sa a zuciyarsa.

Zuwan Habu wajen biyar gidansu Zinatu amma fir tak’i saurarensa ta dage akan ita idan ba Gwaggo ta gani a gidansu ba ba zata tab’a dawo masa ba,sai Gwaggo tazo ta bata hakuri zata yarda ta dawo masa,ba kuma iya ita kadai ba har dasu sulen.

Habu kamar zai zauce haka yake ji.

Zinatu kuwa duk da kamar akan kaya take jinta zaman da take a gidansu dan ko baccin kirki bata iya yi tunda ta dawo gidan amma haka ta dage dan so take ta nunawa Gwaggo irin san da Habun ke mata yadda tasa habu ya saketa tafi so taga ta zo gidan da kanta dan ta bata hakuri.

Sati biyu kenan da barin gidanta amma jinta take kamar ta kwashi shekaru a kurkuku ta matsu taga ta koma dakinta,da gangan take cin kwalliya idan Habu yazo saboda ta Kara haukata shi.

Habu ganin babu sarki sai Allah yasa ya shirya zuwa gidan Sulen banda Yana balain kaunar Zinatu bai ga abinda zai saka ya taka kafarsa yaje gidan Sulen ba dan ya lura sai yayi kamun kafa da shi zai samu Gwaggo taje gidansu Zinatun da yake ganin abune da kamar wuya wai taje gidansu Zinatu da kanta.

Booth din motarsa ya cika fal da kayan abinci, gwaggo ma siyayarta daban ya Mata dan tana gidan sulen har lokacin bata koma ba.

Koda ya isa gidan sai da yasa Almajirai suka fara shigar da lodin kayan da ya kawo kafin ya shiga gidan da sallama a bakinsa Yana Jin bakin cikin saukar da Kansa da yake neman yi.

Gwaggo duk suna zaune a tsakar gidan tana shan fanten da Hanne ta mata dan sosai Hanne ke hidima da ita kamar ita ta haifeta,duk da suna halin rashi a yanzu suna iya k’ok’arin su wajen ganin sun bata kulawa,a haka ma arzikin Ameera ake ci na dinkunan da kunshin da take dan yi a gida,dan Sule ba ya iya fita dan har lokacin kafarsa ciwo take masa kudi yake so ya samu ya tafi babban asibiti.

Baki a sake suka ringa kallon Almajirin dake ta shigo da kaya Yana ajiyewa Yana  fita.

Sai da ya kawo na karshe sule yace “Yaro wai daga Ina wanan kayan Anya gidanan akace ka kawo kuwa”?

Shigowar Habu dake Saba babbar rigarsa fuskarsa a dan sake da sallama yasa Sule saurin Kau da Kansa.

Hanne da Gwaggo ne kawai suka amsa sallamar suna kallon sa suna kallon kayan da suka san shine ya kawo.

Da dafe bango sule ya mik’e dan ko ganin Habun baya so yayi.

Habu kuwa yayi saurin tare shi yana “Sule har yanzu ciwon kafar kake sannu dama zuwa nayi na Kai ka asibti wallahi Allah ban taba Saka su tab’a lafiyarka ba yanzu haka ma nayi kararsu dan sai na sa an koresu daga aiki”

Sule hannunsa da ya Rike ya fusge Yana “Zan samu lafiya karka damu ba sai ka wahalar da kanka kaini asibti ba”

Daga haka ya shige daki

Gwaggo kuwa kallonsa kawai take tana kallon tulin kayan da ya shigo dasu,zata iya cewa tunda yayi kudin nan bai tab’a zagewa ya siyi kaya mai yawan haka ba,dan sai da azumi ma yake tsintar kayan abinci ya Kai Mata,wani irin murmushi ta saki da ta ga ya zub’e a gabanta yana gaisheta kamar zai shige cikin kasa.

Amsawa tayi dan ta riga da tasan ladabin na mene cin hanci yake so ya basu dan ya Maida Zinatu.

Sai da ta amsa gaisuwar da ya mata ta kalli kayan abincin dake zube a tsakar gidan tana “Habu wanan kayan fa daga Ina na menene”?

“Gwaggo ku na kawowa mana”

“Yaushe ka fara kawo kayan abinci naga ko da azumi sai anyi dagaske kake Kai mun kayan abincin”.

Halan cin hanci ka kawo min dan ka Maida Zinatu dakinta”?

Girgiza kai Gwaggo tayi tana “Baka tab’a tunanin kyautata mana ba sai da na sa ka rabu da matarka ,yanzu ba zaka iya mana Abu ba sai ta silar Zinatu ko?toh bari kaji na fada maka idan har Zinatu itace autar mata wallahi ba zata tab’a dawo maka ba,idan har dan haka ka kawo wanan kayan ka tashi ka kwashi kayanka ka tafi bama bukatarsa,wanan abun da kayi ya Kara Saka min tsanar Aurenku Habu har ace baka san ka kyautata mutum ba sai dan ka rabu da matarka ai ko duk duniya zaka kawo Ka ajiye min ba zaka dawo da ita ba,idan zata dawo ma wallahi sai idan tayi wani auren taje ta hadu da wasu dangin mijin taga idan zasu d’auki iskanci da take mana ta fito sai ka aureta kila a lokacin zata san darajar naka Yan uwan amma a yanzu bada yawuna ba”…..

*Page 13*

         Habu mutuwar zaune kawai yayi Yana kallon Gwaggo fadar tashin hankalin da maganganun ta suka jefa shi a  ciki ba’ta baki ne.

Dan ya d’auka Yana zuwa gidan ko ba dan kayan abincin da ya kawo ba,ko dan Sule daya nunawa kulawarsa hakan zai Saka ta sauko taji sanyi a zuciyarta.

Yasan yaudarar Kansa yake idan har zai sa a ransa wai Gwaggo zata taka kafarta taje  gidansu Zinatu.

 Daurewa yayi wajen b’oye tashin hankalinsa Yana “Gwaggo wallahi ba dan Zinatu na kawo kayan abincin nan ba,na kawo ne dan na bawa Sule hakuri sai daga baya na gane kuskurena Gwaggo dan Allah dan Annabi ki yafe min Shima sule Ina so ya yafe min Sharrin shaidan ne”

“Habu ai ni ban tab’a rike ka a raina ba duk da kana b’ata min rai duk da kafi fifita matarka akaina da Yan uwan ka ban tab’a rike ka a raina ba dan nasan hatsarin fushin uwa akan danta da addu’a kullum nake binku akan Allah ya rabani daku lafiya bana so na tab’a fushi da ku dan nasan mai hakan zai haifar,duk baka san abinda kake aikatawa ba daidai bane sai da Zinatu ta rabu dakai kaga kuwa rabuwar taku ta fiye min alheri dan haka idan kana  sa rai wai zaka dawo da ita toh ka sa a ranka ka gama zama da ita.

Habu bai iya magana ba dan daga yadda gwaggo ke magana yasan da gasken take ba zata tab’a yarda ya dawo da Zinatun ma da take sa rai da Gwaggo ce zata  je har gidansu ta bata hakuri kafin ta dawo ba, ya biye mata ne kawai amma shi ma yaga rashin dacewar hakan.

duk dan ya faranta mata ya kulle Sule san da yake mata yasa duk abinda take so jiki na rawa yake mata amma ko shi bai san gidan Sule zata zo a ranar ba da ya hana ta yace ta bar komai a hannunsa sai gashi duk abubuwa sun cabe musu.

Gwaggo kuwa mik’ewa tayi ta fara k’ok’arin shiga dakin su Ameeran dan tasan mai ya kawo Habun tasan duk akan maganar Zinatun ne,haka kawai ba zai kawo musu kayan abinci ba tasan so yake ya Mata maganar dawo da Zinatu, ita kuwa ba zata tab’a yarda ya sake dawo da ita ba.

“Gwaggo dan Allah ki tsaya ki Saurareni ba Zinatu Zaki duba ba su Amjad zaki duba waye zai kular min dasu,yaran nan kullum cikin kuka suke bayan babarsu na Rayye ba mutuwa tayi ba,ni ya kamata ki hukunta ba ita ba Gwaggo,dan ni na saka aka kulle Sule ba ita ba,ko sule ne a matsayina matakin da na d’auka zai d’auka dan Allah Gwaggo karki rabani da Zinatu,tunda na aureta nake ganin haske a rayuwata kullum cikin cigaba  nake.”

Murmurshi Gwaggo ta saki a daidai lokacin da taje bakin k’ofar shiga dakin su Ameeran tana

 “banga ta inda ka cigaba ba Habu,cigaba ta hanyar raba ka da mahaifiyar ka da Yan uwanka ba cigaba bane ba.

Magana ta ta fito dama dan zinatu ka taka kafarka kazo har da kayan abincin, Habu kenan idan har tashin hankalin ka akan su Amjad ne kaje ka nemo wata  matar ka Aura amma da gaske nake ka gama zama da Zinatu”

“Yanzu akan na kulle Sule kika rabani da matata kika raba yarana da mahaifiyar su ?

 mai na miki haka kika tsaneni ni”?

Sule yace a haukace Yana bin bayan Gwaggo da ta shige daki ta kwanta batare da ma ta Kara juyowa  ta kalle shi ba.

Habu kuwa ihu kawai yake Yana Gwaggo tana nuna musu banbanci akan sule shi kam ba zai iya rabuwa da Zinatu ba.

Gwaggo kuwa tace idan ya gama Ihun yaje ya d’auki kayan abincin ya tafi dan komai zai yi ba zata tab’a yarda ya dawo da Zinatu ba.

Habu kuwa da yaji zuciyarsa na Neman fashewa saboda tsananin bakin ciki a fusace ya bar dakin ya ringa magana da k’arfi Yana “Na tsaneka Sule wallahi na tsaneka duk akan ka gwaggo ke San rabani da matata bani da makiyi sama da kai kana zaune da matarka cikin rufin asiri ba Wanda ya raba ka da ita amma kayi silar da kasa na rabu da tawa matar bayan duk Abubuwan da kamin adalcin da za’a min shine a rabani da matata na tsaneka Sule na tsaneka”!!!

Habu yayi waje kamar zai tashi sama,dan ba kowa a tsakar gidan.

Sule kuwa dake jingine da pillow Yana Jin duk abinda yake fadi ya Kalli Hanne da ta shige daki tun lokacin zuwansa dan tsoro ma yake bata yace “Hanne kinga irin abinda nake gudu ko,ni banga dalilin da zai Saka Gwaggo tace sai ya rabu da Zinatu ba,ba abinda Gwaggo za tayi yanzu wai da zai Saka na tab’a ganin farin Habu yadda ya tsaneni haka na tsane shi,Yaya Ibrahim da dan bature ne kawai Yan uwana amma Habu ba dan uwana bane idan har Ina ganin tabunan dake jikina bana Jin zan iya yafe masa abinda yamin dan haka idan har dan hadin kanmu Gwaggo wai tasa ya rabu da  matarsa gwara kawai ta bar shi ya maida matarsa dan kanmu ba zai tab’a haduwa ba”

“Idan kana fadar haka Sosa min zuciya kake Sule,bansan ka da ruko ba,ka yafewa Habu abinda ya maka bana so naga kanku ya rabu ba wai a kanka nasa ya saki Zinatu ba, Zinatu ba mace tagari bace da zai zauna da ita,bansan Mai yasa ya makance a santa ba,duk ba zai gane abinda nake hango masa ba sai Nan gaba yanzu duk fushin da yake na dan lokaci ne zai sauko idan an kwana biyu”

Cewar Gwaggo da ta tsaya daga bakin k’ofar dakin dan ta fito ne dan tace Habu ya kwashe kayan abincinsa sai taji sule na magana

Hanne kuwa cikin tsananin damuwa ta fara magana tana “Gwaggo dagani har Baban Ameera ba zamu tab’a samun kwanciyar hankali idan Yaya Habu bai maida Zinatu dakin ta ba zamu ga kamar mune Silar rabuwar su Wanda ba zamu so haka ba Gwaggo dan Allah ki yi hakuri ki bar shi ya maida ita dakinta”

“Hanne kenan ba Zaki tab’a gane gyaran da nake so nayi ba shiyasa kike cewa na bar shi ya mai da Zinatu,kila a gaba zaki gane abinda nake gudu”

Daga haka Gwaggo ta juya da dafa bango ta koma dakin su Ameera tana Jin kirjinta na mata mugun nauyi,tana iya k’ok’arin ta wajen hana kanta tunanin dake sa Jininta hawa,rabuwar kan yaranta da suka taso da so da tausayin juna na matukar daga mata hankali bata ga ta inda zata iya gangancin barin Zinatu ta dawo ba,dan tasan duka yaranta basu isa ketare umarninta ba,duk kudin da Habu yayi bata bashi damar ko fuskar da shine zai Juya ta ba,tasan bai isa maida Zinatu ba sai idan itace tace  ya maida ita.

Wani irin ciwo take ji a kirjinta har takan ga kamar idan ta kwanta bacci ba zata wayi gari ba.

 Addu’a kawai take akan Allah ya ara mata tsawon rai ta daidaita tsakanin yaran nata,Habu ya samu mace tagari da zata na dora shi akan hanya mai kyau.

Zinatu kuwa kallon Habu kawai take hankalinta a balain tashe da Habu ya gama kora mata bayanin duk yadda suka yi da Gwaggo ya Kara da “Zinatu yanzu bansan ya zanyi ba Gwaggo taki saurarata, Gwaggo tayi fushin da bata tab’a irinsa ba,Kuma duk akan Sule take min haka yanzu mai abin yi Zinatu ko zamu je dake ki bata hakuri”?

Zinatu wani irin Kallo ta masa tana “tunda kai Kuma ba zaka iya mayar dani ba kana gudun fushin ta sai ka sakeni dan nima ba zan tab’a taka kafata naje bata hakuri ba tunda ba abinda nayi mata ta tsaneni Kaninka ne yaci zarafina take goyon bayansa”

Habu kamar zai yi kuka ya fara magana Yana ” taya zan iya Maida ki tana fushi dani,a gabanki fa tace zata tsine min,idan Gwaggo ta tsine min ta Ina zan Kara samun kwanciyar hankali da nutsuwa.

 Uwa ai ba wasa bace ba dole mu bita muyi mata biyayya karki  duba duk abinda ya faru, fushi da gwaggo yanzu ba namu bane ba kila idan muka je zata iya  saukowa karki manta Mahaifiyata ce bana san fushinta,bana so tamin baki”

“Wai da anyi magana sai kace zata ma baki,Kai ma dai ba sona kake ba idan har kana sona ba zaka tsaya tunanin za’a maka baki ko baza’a maka kawai ka sakenin kaje ka auro wata dan ba zan wani je na bada hakuri ba bayan ni aka yiwa laifi bansan Mai nayiwa Mahaifiyar ka har haka ta dora min mugun tsana ba yarana hudu da kai amma wai bata yarda ka dawo dani ba ai karshen tsana ta nuna min”

Habu duk yadda yaso ya fahimtar da Zinatu ki tayi duk da ji take kamar ta bi shi suje su samu Gwaggon dan a balain takure take a gidan nasu,sam zaman gidan baya mata dadi,ta matsu ta koma dakinta,ta ma kasa fadawa kowa akan sakinta  akayi.

Duk da Habu ya maida auren nasu,amma gani take idan ba ganin ta tayi a dakinta ba gani za tayi kamar ita din sakakkiya ce.

kunya ma take ji ace kamarta ta dawo gida,tun kafin a gane halin da take ciki take so ta samu ta koma,amma idan har ta nuna wa Habu san komawarta ba zai wani damu ba, amma idan tana tuburewar sai yafi shiga tashin hankali gwaggo kuwa kwandunan tsinuwa da mutuwa ta ringa ja mata tana shan alwashin idan ta koma sai ta janye Habun gabadaya wanan biyayyar ma da yake mata sai tasan yadda tayi ya daina Mata”

Habu kuwa haka ya cigaba da sintirin zuwa wajen Gwaggo har wayanda yasan tana  ganin mutuncinsu yake zuwa  dasu wajen Gwaggo amma firr Gwaggo taki gashi Ji yake kamar ya mutu saboda rashin Zinatu a kusa dashi da ta masa dandana haukaci.

zuwan da yayi da sai da ya samu nutsuwa da ita saboda magiyar da yayi ta mata dan sosai ta birkita masa lissafi,Wanda sai da yaji dak’yar idan zai samu mace kamar Zinatu a rayuwarsa.

Bai san ya zai yi da gwaggo da ta kafe akan sai dai ya kare rayuwarsa ba aure indai sai ya dawo da Zinatu gidansa.

Duk da tsananin tsanar da yayi wa sule da yake ganin kamar duk shi ya jawo rabuwar shi da Zinatun sai da ya daure ya samu Sulen da baya iya fita dan kafarsa bata jure doguwar tafiya gashi Sulen yak’i bari ma ya kai shi asibiti.

Gani yake sule zai iya shawo masa kan Gwaggo hakane yasa ya roke shi akan ya taimaka masa wajen bawa Gwaggo hakuri.

Sule kuwa take yace masa ya dade Yana rokon gwaggo amma taki sauraran shi.

Wasa wasa sai gashi Zinatu ta tafi wata biyar a gidansu tun tana zuba ido taga Gwaggo ta sauko har sai da ta fara karaya tana jin wani azabar fargaba da tashin hankali dan taga alamar da gaske Gwaggo ta daura damarar rabata da Habun da tasan da wuya ta samu irinsa da wuya ta samu mijin da zai mace a kanta kamarsa.

Tuni ta fara nunawa Habu tashin hankalinta a irin wanan lokacin ta gano tana d’auke da Karamin ciki.

Dadi kamar ya kasheta dan tasan yanzu dole Gwaggo ta barta ta koma dakinta.

Cikin farin ciki ta sanar da Habu tana d’auke da Karamin ciki dan wata biyu kenan bata ga aladarta ba.

Habu kuwa ji yayi kamar ta masa albashir da gidan Aljanna dan gani yake yanzu idan Gwaggo taji labarin Zinatu tana d’auke da ciki dole ta barshi ya maida Zinatun.

Zinatu kuwa ta Kara tsara masa akan yace wa Gwaggon watanin cikin ta hudu kar tazo ta d’auka bayan ta dawo gida ya Mata cikin.

Da wanan shawarar Habu yaje gidan Sulen dan Sule ya dage ba zai bar gwaggo ta koma gidan ta ba,duk da baya iya wani aiki gani yake ba Wanda ya dace ya kula da ita a yanzu sama dasu,dan tana bukatar kulawar dan tana da dauriya ma tak’i yarda ta kwanta ne amma gwaggo bata da cikakken lafiya.

Sai dai ga mamakinsa ko daya gama korawa Gwaggo akan Zinatu nada ciki bai ma san da cikin ba sai yanzu Ashe da ciki ya saketa.

Budar bakin gwaggo sai cewa tayi “Allah ya sauketa lafiya idan ta haihu sai ta kawo abinda ta haifa din dan idan kana tunanin wai dan tana da ciki zan bari ta dawo ka yaudari kanka Habu”

Wanan karon har da kuka ya saka wa Gwaggon amma firr Gwaggo ta dage akan idan Zinatu ta haihu ta kawo abinda ta haifa Habu yaje ya nemi matar Aure.

A takaice Zinatu ganin babu sarki sai Allah Idan har ta tsaya girman kai sai dai  aganta da  ciki karshenta ta haihu a gida.

A Babu yadda za tayi ta fadawa yayarta halin da take ciki ta roketa akan ta Rakata suje su bawa Gwaggon hakuri.

Yayarta kuwa Aminatu halinsu Sam ba daya bane duk da Zinatu tak’i fitowa ta fada mata gaskiyar abinda tayi sai da ta mata fada kafin ta shirya wajen Magriba suka nufi gidan Sulen da Zinatun da take Jin wani irin bakin cikin saukar da kanta da za tayi wajen bawa Gwaggon hakuri.

Yanzu duk suna da damar da zasu mata abinda suke so amma idan ta koma duk sai tayi maganin Gwaggo sule da Hanne uwa Uba Ameeran da take Jin duk itace ma silar sakin da Aka fara mata.

A mutunce Hanne ta tarbe su, Zinatu kuwa sai sunkuyar da Kai take dan taji kunyar zuwan da tayi rokon gwaggo duk da ba ita za tayi magana ba yayarta  ce za tayi magana.

Gwaggo kuwa yadda ta hade rai yasa jikin Zinatu sanyi take hawaye ya hau zubo mata,Yayarta Amina kuwa sai hakuri take bawa Gwaggo akan ta dubi su Amjad ta hakura kila zama bai kare ba tunda ga wani cikin nan Zinatu na d’auke dashi”

Gwaggo sai da ta gama saurarenta tsaf bata katseta ba.

Zinatu kuwa sai sharar kwalla take tana ji Ina ma gini ya ruguzowa Gwaggon ta mutu kawai ta huta.

Gwaggo na k’ok’arin magana sai ga Habu ya shigo da Yaran gabad’aya dan bai ma san Zinatu zata zo gidan ba,a yanzu da yaran yake so ya samu ya shawo kan Gwaggon dan kila idan ya sako ta a gaba da yaran nashi zata hakura ta bar shi.

Sai dai ga mamakinsa sai ya tadda Zinatu da yayarta Wanda hakan yayi matukar faranta masa rai haka suka zauna gabad’aya har da yaran.

Gwaggo kuwa ta d’auke kanta duk daga kallon Habu da yaran nasa ta Kalli yayar Zinatun ta fara kora mata duk Abubuwan da Zinatun ke mata ta Kara da “Babu ko digon alheri a tare da Zinatu,dan da ace ita mace ta gari ce ita zata na ma nusar dashi tana fada masa Mahimanci mu a wajensa dan itama uwa ce ta haifa ba zata so ace wanan Amjad din mace ta rabata dashi Yana mata abinda ransa ke so ba,duk wani abu da Habu yake wa danginta yake mata wallahi na sani ban tab’a bakin ciki nace dan me ba,idan har kudi ma zata hana shi ya mana hidima dashi ba zan damu ba,amma me a yanzu ta daura damarar raba min kan yarana,Wanda ni kuwa gwara na rabata da Habun akan ta raba shi da Yan uwansa dan haka sai dai kiyi hakuri a gaskiya ba zan iya barin Habu ya dawo da Zinatu ba”

Yayarta Zinatu kuwa fada ta rufe Zinatu dashi a gaban Gwaggo sai da ta mata tas ta Kalli Habun da ya sunkuyar da Kai Shima ta masa fadan rashin dacewar abinda yayi ya Kara da kar ya sake ya yarda mace ta tab’a raba shi da Yan uwansa.

Daga haka ta sake bawa Gwaggo hakuri da take nazartar Aminan da ta fahimci halin ta sam ba irin ba Zinatun bane.

su Amrah kuwa suka yi ta matsar kwalla suna bawa Gwaggo hakuri dan duk Habun ne yace suyi ta kuka kila Gwaggo ta ji tausayin su.

Gwaggo sai da ta d’auki tsawon lokaci ba tayi magana ba kafin daga bisani ta fara magana tana “Har ga Allah na rantse akan ba zan tab’a yarda Zinatu ta dawo min rayuwar da ba,amma tunda har kika zo na ga kuma halinki da nata ba daya bane zan yarda ya Maida ita dakin ta da sharadi daya idan har shi Habun bai yarda da sharadin ba sai dai ya hakura da dawo da Zinatun.

“Tun kafin ki fadi kowane irin sharadi ne na yarda Gwaggo indai Zaki bar Zinatu ta koma dakinta wallahi na gama yarda”

Habu yace cikin tsananin farinciki a lokacin ya hada ido da Zinatu da ta matsu taji wane irin sharadi ne sai tsinewa Gwaggo take a ranta.

Gwaggo kuwa ta gyada Kai tace toh shikenan ta hau kwala Kiran “Shamsiyya !Shamsiyya?!

“Naam Gwaggo”

Suka juyo sirririn muryar mace ya ratso dakin.

Gabad’aya juyawa suka yi suna kallon bakin k’ofar Zinatu kuwa haka kawai taji gabanta na balain faduwa Habu shi ma cikin daurewar Kai ya zubawa k’ofar ido dan sam bai gane mai gwaggo ke nufi ba.

A daidai lokacin da Shamsiyya da baza ta Wuce shekara ashirin ba ta shigo cikin doguwar hijabi kana ganinta kaga nutsatsiya

Ta tsugunna a kasa tana “Gwaggo gani”

Gwaggo cikin hade rai ta kalli Habu tana “Ga matar da na nemo maka ka aura,Shamsiyya ce kanwar Hanne ba uwarsu daya ba ubansu ne daya gidansu Hanne suna da matukar tarbiyya da kowace uwa zata so ace danta ya auro Yar gidan dan haka kana bukatar Karin Aure,Karin auren nan kawai za kayi Kafin na yarda ka Mai da Zinatu dakinta idan kuwa ka ki auren ta toh sai dai ka hakura da dawo da Zinatu dakinta”?

Zinatu bata san sadda ta mik’e tsaye cikin tashin hankali tana “Gwaggo kishiya kike so Habu yamin”!!!……..

*Page 14*

                  Gwaggo bata ko kalli Zinatu dake rafka uban Sallati kamar warce ta rasa uwa da Uba ba har da ta shiga ukunta ta lalace

Yayarta kuwa sai cewa tayi “Indai karin Auren da zai yi  ne zai saka  ki sauko Gwaggo Babu matsala sai dai muyi fatan Allah ya Kau da fitina Babu matsala in Sha Allahu zan Kara yiwa Zinatu fada hakika bata Kyauta ba dole ki nemi ya Kara aure ni nafi ganin laifinsa ma yaushe zai biyewa mace ya juyawa nashi baya”

“Ba wai Babu matsala ba Amina nasan halin Zinatun ne wallahi idan har Habu ya auri Shamsiyya ta takura shamsiya ko shi Habun ya so wulakanta ta ta a ranar da na gano wallahi sai ya yanke ragowar igiyar,Habu Yana da hankali a baya, Habu da ba haka yake ba,amma Zinatu tasa ya zama wani Abu na daban, wallahi dan Yaran nan zan bar Habu ya maida ita amma ba dan haka ba wallahi ba zan tab’a yarda ya dawo da ita ba

Habu kuwa kasa magana yayi dan mutuwar zaune kawai yayi bai kawo Karin auren ne sharadin da Gwaggon ke fada ba.

Tashin hankali da yaga Zinatu ta shiga ya Kara daga masa hankali dan bai tab’a hararowa kansa auren wata bayan Zinatu ba,gani yake da Zinatu kawai zai iya rayuwa.

Satar kallon Shamsiyya da ta sunkuya da kanta ya Kara yi,taya ma zai iya auren kanwar Hanne.

Muryar Zinatu da ta fara magana cikin kuka ya katse masa tunanin da ya tafi.

“Gwaggo dan Allah kiyi hakuri ba zan iya zama da kishiya ba,wallahi bani nasa Baban Amjad  yake Abubuwan da yake ba,bani da hannu a duk abinda ya faru”

“Ai ba dan ke kadai aka yo Habun ba da Zaki ce ba zaki iya zama da kishiya ba,bani da wani matsala dake idan ba Zaki iya zama da kishiya ba ki zauna a gidanku ki samu saurayi ki aura,amma Habu kamar ya gama Kara Aurene duk da nasan ni ban Isa dashi ba,sai da yardarki zaiyi auren dan yafi Jin maganarki akan nawa ke kuma hakan na miki dadi,bayan kinsan kema kina da yaran abinda kika min watarana za’a iya miki”

Zinatu na k’ok’arin magana dan har Lokacin a tsaye take tana karkarwa hararo wai Habu zai Kara aure kamarta ta zauna da kishiya na neman sa zuciyarta ya buga

Wani irin tsawa yayarta ta mata tana ta musu shiru kar ta sake ta Kara magana idan bata san zama da kishiyar sai ta shirya haihuwa a gida,idan tana da hankali ma ya kamata ma ta nuna bata san Auren a gaban Gwaggo”

Fada sosai ta rufeta dashi Zinatu kuwa da ta kasa jurewa tayi waje da gudu tana bangaje Shamsiyyar dake tsugunne bata san ta yarda zata ma fara zama da kishiya ba taya Gwaggo ma zata nemowa Habu mata saboda kawai ta tsaneta ba zata tab’a yarda Habu ya auri wanan mitsitsiyar yarinyar da bama taga fuskarta sosai ba dole tasan nayi dan taga alamar sai ta b’iyowa gwaggo ta bayan gida tunda har ta fito ta nuna mata kiyayya Karara”

Gwaggo kuwa Habu kawai take Kallo dake tsiyayar gumi dan ji yake kamar an like masa baki,idan bai nunawa Gwaggo zai karbi Auren shamsiyar ba yanzu zata ce maganarta ya tabbata Zinatun ce ke juya shi.

Idan kuma ya karbi Auren yasa sai ya Sha wahala a wajen Zinatu dan yasan halinta tsaka mai wuyan da ya shiga yasa shi tsiyayar gumi.

Sai da Amina tace “Kayi shiru baka ce komai ba,Zaka bi umarnin gwaggon ko tsoron Zinatun ne zai hana ka karbar Auren?

“Aaa ba Karin Auren nake gudu ba wallahi ban san ta yadda zan zauna da Mata biyu bane ba Gwaggo dan Allah ki sake dubawa kigani Karin auren nan ba shine mafita ba ki yarda nayi nadamar duk abinda nayi na Kuma gane kuskurena zan gyara.

“Gwaggo murmurshi ta saki tana “Ai dama ba zan Maka dole ba Habu ai kaima kaji mai nace ma,shamsiya tana da Mai sonta ni naje har gidansu na roke su akan Ina san a baka ita a matsayin mata dan kana bukatar mace ta gari Mai tsoron Allah,amma tunda kace baka so ba matsala kawai ka sa a ranka cewar ka gama auren Zinatu duk lokacin da ka gaji da zama a haka zaka iya samo wata matar ka Aura”

“Na amince gwaggo na yarda zan aureta”

“Ba Ka yarda zaka aureta akan dole ba ko akan babu yarda zaka yi,Ina so ka sa a ranka Amana ce zan baka a duk ranar da ka cutar da ita ko Zinatu matarka wallahi tallahi ba zan tab’a yafewa ba,idan kaki kwatanta adalci a tsakanin su ba zan tab’a yafe ma ba”

“Zan kwatanta adalci gwaggo sai dai a tayani da addu’a yanzu tunda na yarda Zinatu zata iya komawa dakinta Kafin a daura auren”?

“Sai an daura auren Zinatu zata dawo dakinta”

“Dan Allah gwaggo tunda na yarda zan aureta ba zan tab’a bijirewa umarnin ki ba ki bar Zinatu ta koma dakinta ko dan yaranta da sukayi kewarta

Dak’yar da magiya gwaggo ta ce ta amince ya Maida Zinatun

Ta ce masa ya fara shirye shiryen kai sadakin shamsiya dan ba wani lokaci mai tsayi za’a saka ba.

Yayar Zinatun godiya kawai ta ringa yiwa Gwaggo tana mata alkawarin za ta Kara yiwa Zinatun fada.

Habu kuwa shi ma yayi mata godiya.

 yau kamata yayi ya kasance ranar farin ciki a gare shi,sai dai Sam bai ji farin cikin ba saboda auren da gwaggo ta kakkab’a masa bai san ma ta yadda zai auri kanwar Hanne da yasan kila sule ne ya hada wanan munafircin nan dan kawai ya tsani Zinatu ba.

Koda ya fita gidansu Zinatun yayi da yaran dan yasan sai ya Sha fama da zinatu kafin ta iya yarda ta  koma dakinta,dan ya tsani ta ringa furta masa rabuwar nan yasan a yanzu ma sai tace sai dai ya saketa akan ta zauna da kishiya.

Su Habu na fita Sule da Hanne suka shiga wajen Gwaggon da ta rike hannun shamsiya dake sheshekar kuka tana rarrashinta  dan Sam bata san da maganar Auren ba sai yanzu da ta kirata.

Mahaifin su yace mata kawai tazo wajen Hanne ta kwana biyu bata san dalili ba kuma Hanne ma bata ce mata komai ba sai a yanzu da taji gwaggo na maganar hadata Aure da Habun da take da labarin yadda yake bautawa matarsa.

Dan unguwar tasu da yake karamar unguwa ce duk an san labarin su Habun da yawa ma an d’auka asirce shi Zinatun tayi.

 Ba Wanda bai san halin Zinatu da wulakanci ba sau daya ta tab’a ganin ta a lokacin ma bata zama budurwa ba ita da Hanne sunje gidan yi mata barka a lokacin ta haifi Sultana tarb’ar wulakanci ta musu a ranar dan tana fitowa ta koma,duk gidansu ba Wanda baisan Zinatu bata da mutunci ba ga mamakinta sai gashi wai mijinta ake so ta aura daga maganar da gwaggon ke yi babansu ma ya yarda da Auren.

“Kiyi hakuri Shamsiya taimaka min za kiyi  ki ceto Habu daga halaka  ki kwato min shi daga hannun Zinatun dake juya shi san ranta”

Hanne da sam itama bata sani ba sai a yanzu da taji maganar su na tashi daga dakin.

Itama hankali a tashe ta fara magana har da hawayenta tana “Gwaggo dan Allah a nemawa Habu wata matar wallahi Zinatu cutar da Shamsiyya za tayi,yanzu zasu d’auka nice na kawo kanwata dan ya aura yanzu za’a ce kwadayi ne yasa na kawo kanwata dan ya aureta Gori da wulakanci haka Zinatu za tayi ta mana ba Kuma zata tab’a barin Shamsiyya ta samu kwanciyar hankali ba,ni da ba kishiyarta ba ma ta gana min azaba ina ga Kuma taga an mata kishiya”

Hanne ta karashe cikin kuka kamar yadda Shamsiyya ke kuka.

Sule kuwa shima magana ya hau yiwa Gwaggo Yana nuna mata rashin Jin dadinsa ya Kara da “Gwaggo iyayen Hanne duk inda suka kai ga ganin mutuncin ki idan har aka cutar musu da ya wallahi daina Ganin mutuncinki za suyi dan Allah ki hakura da hadin nan da kike so kiyi hatsarine ma zaman shamsiya da Zinatu”

Gwaggo duk bata katse su ba sai da suka gama magana ta hau sharar kwalla wanda hakan ya daga musu hankali a babu yadda zasuyi suka hakura suka bar maganar

Hanne kuwa ko runtsawa ba tayi ba dan ta ma fara tausayawa shamsiya da bata da magana hakurinta ma na daban ne a gidansu.

Zinatu kuwa haukacewa Habu tayi a lokacin da yaje gidansu tana rantsuwar ita ba zata zauna da kishiya ba,cikin gushewar hankali ta hau neman zagin Gwaggo sai da Amina ta kwashe ta da Marin daya jawo hankalin iyayen nasu kansu dan a Karamin palon gidan duk suke zaune.

Amina cikin tsananin b’acin rai ta korawa iyayensu duk abinda ke faruwa.

Take iyayen Zinatun suka rufe Zinatu da fada dan hankalinsu yayi matukar tashi da suka ji wai Gwaggo tace idan bai Kara auren ba sai dai ya rabu da Zinatun.

Su kadai suka san morar da suke wa Habun,kaf danginsu ba Wanda Habu bai kyautatawa ba taya zasu so ma Zinatu ta rabu da habu.

Habu suka ce wa ya gaggauta zuwa ya auri zabin Gwaggon suka Kara da ya daina biyewa Zinatu dan ba hankalinsu daya ba.

Zinatu cikin kuka ta tarkato kayanta,Habu ya ringa lodawa a cikin mota cikin rawar jiki.

Tunda kuwa ta koma ta d’aukewa habu wuta.

Har wani rama tayi saboda tashin hankalin da take ciki,hararo wata ta rabi habu da sunan matarsa na sa taji kamar zata mutu.

Ta kasa zaune ta kasa tsaye ta rasa yadda zata wargaza Auren.

Dan Habu kullum cikin bata hakuri yake akan ita kadai yake so,shi ko fuskar Shamsiya ma bai sani ba har yanzu ya mata alkawari sai dai Shamsiya ta zama Yar aikinta ba abinda zai yi da ita.

Da wanan kawai take dan samun kwanciyar hankali ji take dama zata samu mai shake mata gwaggo ya aika ta har lahira ta huta.

Habu tun Yana kaucewa maganar Auren har sai da Gwaggo ta Sako shi a gaba aka kai kudin Aure da sadaki.

Wajen hada lefe Zinatu ta kafe akan ita zata hada lefen,sai da gwaggo tace ba ta yarda ba tasa habu ya kawo kudi ta sa wata Yar uwarta ta hado wa shamsiya lefen aka kai.

Habu kuwa bai tab’a zuwa gidan su shamsiya ba bai ma san kalarta ba.

A yanzu Sam bashida kwanciyar hankali dan Zinatu daga masa hankali take akan bata yarda a raba musu gida ba dan gwaggo tace sai dai ya raba musu gida,ya rasa ya zai yi da Gwaggo ta yarda su zauna a gida daya.

A babu yadda zaiyi yaje gidansu Shamsiyyar da ya rage sati biyu daurin auren nasu dan itace kawai zata taimaka masa wajen yiwa Gwaggo magana.

Duk abunan da ake bai San shamsiya ba dan tun ranar da ya ganta daddare bai sake sakata a idonsa ba.

Ko da ta fito bai ga tana da wani Muni ba,da kyanta daidai nata Amma gani yake kaf mata Babu kamar Zinatu.

Daurewa yayi wajen cewa Shamsiya ta nunawa Gwaggo tana so su zauna a gida daya,haka yayi ta tsara ta har sai da tace ta yarda.

A yadda gwaggo ta yarda akan a hadasu gida daya kenan,Wanda Hanne da Sule sai da suka dage akan kar a hadasu gida daya amma gwaggo tace su zauna a gida dayan Zinatu bata Isa tayi wa shamsiya wani Abu ba duk ranar da ta gwada wallahi sai ta rabu da Habu.

A cikin kayan fadar kishiya har da Kujerar Umara Habu ya biyawa Zinatu da ta dorawa kanta masifa.

A ranar da aka je aka jerawa Shamsiya kaya a part din da su sule suka zauna hauka ne kawai ba tayi ba duk da sule na nuna mata tsanar da yayi wa auren Amma ta kasa samun kwanciyar Hankali.

Habu kuwa so yake taje saudiyar ko zata dan samu nutsuwa amma dan bala’i haka ta dage akan a daga tafiyar ita bama zata je ba a Yanzu.

Azabar da zata ganawa Shamsiya kawai take Hange dan sai ta sabauta shamsiya sai gwaggo tayi nadamar aurawa Habu ita.

A watarana na asabar aka daura Auren Habu da shamsiya Wanda a ranar Zinatu ta Tara yaranta gabadaya ta musu hudubar tsiiyar tashin hankalin Wanda a yadda ta karantawa yaran ma indai suka yi abinda ta Saka su din Shamsiya da kafarta zata gudu.

Har da Gwaggo aka kawo Shamsiya dake ta kuka kamar ranta zai fita dan tunda aka shiga satin bikin zuciyarta ke cike da fargaba da tashin hankali.

Gwaggo kuwa ranta sai da ya b’aci da taga ko dan fenti ma ba’a yiwa Shamsiya ba kuma akwai part din da yafi wanan din girma amma aka kawo Shamsiya nan.

Gwaggo har Palon Zinatun ta shiga tana rike da hannun shamsiya.

Zinatu kuwa ji take kamar ta d’auko wuka ta sokawa Gwaggon.

Ko gaida Gwaggon ba tayi ba Habu da yake can daki muryar Gwaggo yasa ya fito jiki na rawa dan a yanzu har tsoron Gwaggon yake.

Yana zuwa gabanta ya zube a kasa gwaggo kuwa cikin bacin rai ta fara magana tana ” Habu ya naga wancan bangaren  aka jerawa Shamsiya kayanta?Mai yasa ko fenti ba’ayi ba sanan daya  bangaren mai a ciki da ba zaa kai kayan Shamsiyyar ba”

Habu kasa magana yayi ya hau sosa Kai,dan Zinatu da dakin k’ofar gida ma tace a Kai kayan Shamsiyar da kyar ta yarda aka jera kayan a Bangaren dasu sulen suka zauna .

Zinatu kuwa wani irin vibrating take tana kallon shamsiya da ta Sha lullubi.

Maganar Gwaggon yasa taji cikin jikinta ya motsa

“Anan bangaren  Shamsiyya zata zauna Zinatu ta koma bangaren da aka bawa  shamsiyar idan ba haka ba sai dai ka hakura da aurenta ….

Na matsu na gama rayuwar baya na dawo cikin Labarin Amma Banga alamar zan iya gamawa kurkusa ba😥 Anya ba sumarizin zan yi ba?

*Page 15*

          Zinatu ashar ta narko kasa kasa tana kallon Gwaggo da ta hade rai tana kallon Habun da Shima ya dago Yana kallonta da yaji abinda gwaggon tace

Gwaggo kuwa ta cigaba da magana tana “tun yanzu so kake ka nuna min ban isa da Kai ba, shamsiyar zaka kai wancan bangaren da kamar Kara lalata shi akai,can ya kamata a gyara ko nan,ka canza komai na bangaren nan ka gyara amma saboda ka nuna min iyaka ta shine zaka kai ta Bangaren can da sunan tana amarya”?

“Gwaggo wallahi ba haka bane ba,nan din aka fara gyarawa shi yasa nace a dan Kara daga bikin saboda nayi gyaran gabad’aya ba wai zaben wajen gyaran nayi ba dama Ina da niyyar gyarawa da naga sun Kawo kayan jeren sai na bari akan daga baya sai a gyara”

“Toh shikenan tunda nan din ne a gyare shamsiya tayi zaman ta anan ita Zinatu ta koma can ta zauna idan ka gyara sai ta dawo dan shamsiya tana da gatanta ba sadakarta aka baka ita ba”

“Wallahi ba zan koma can ba haka kawai dan kin tsaneni sai kice na koma wancan Karamin part din,na rasa mai na miki kika tsane ni haka,Kinsa anyi min kishiya iya nan bai isa ba sai kin ce na bar wa wata bangarena wanan ai zalunci ne”

Zinatu tace cikin Ihun kuka tana Jin dama tana da damar da zata hau ruwan cikin gwaggo tayi ta bugunta.

Habu kuwa jiki na rawa ya hau bawa Gwaggo hakuri yana rantsuwar zai gyara bangaren

Gwaggo kuwa ta saki murmurshi da taga yadda Zinatu ke hucci kamar zata kawo mata duka tana “ba ke na tsana ba halinki na tsana,da zaki gyara zaa zauna lafiya Zinatu,Auren da na sa Habu yayi ke kika jawowa kanki,Kuma na rantse da Allah duk Ranar da Kika yiwa Shamsiyya wani Abu naji labari wallahi wallahi Habu ya gama aurenki ko sama da kasa zata hade ba abinda zai saka ya dawo dake,Yanda kike Jin Ciwon kishiyar da ya miki haka nake Jin ciwon hada shi da Yan uwansa da kika yi,ko bangaren can da aka Kai kayan Shamsiyya nasan aikin ki ne,Habu karka d’auka wasa nake ma idan har ka cutar da Shamsiyya ba zan tab’a yafe Maka ba, Ina so a kwashe kayan Shamsiyya a Kai wancan bangaren da kuka Saka tarkace dan nan yafi can din kyau da tsaruwa,kar naji kar nagani Habu”

Habu gyada Kansa kawai yake Zinatu kuwa ta Dade da barin palon dan idan ga cigaba da kallon Gwaggo da Shamsiya dake kuka kasa kasa zata iya rufe daya daga cikinsu da duka.

Gwaggo kuwa hannun Shamsiya ta Kara rikewa suka koma bangaren da aka mata Jeran dan habu yace gobe zai Saka ayi fentin daya part din dan yanzu lallaba Gwaggon yake baya so  yayi abinda zai bata mata rai ta ce sai ya rabu da Zinatun da bata da aikin da ya wuce daga masa hankali har wani rama yayi saboda Rashin kwanciyar hankali.

Shamsiya kankame Gwaggo tayi tana sheshekar kuka akan ita ba zata iya zama ba tsoron Zinatu take ji.

Habu kuwa da kansa ke kasa Yana Jin nasihar da gwaggo ke masa kafin Shamsiya ta rungume ta ya fara magana Yana “Shamsiyya ba abinda Zinatu zata miki, ba zan so fushin Gwaggo ya sauka akaina ba ki kwantar da hankalinki ba Wanda zai cutar dake itama Zinatun ba zata iya miki komai ba”

Gwaggo kuwa hannun Habun ta ruko ta hada da na Shamsiyya idonta cicike da hawaye ta sake damka amanar shamsiya a hannun Habun da   jikinsa duk yabi yayi sanyi, hawayen da ya ga  gwaggo na zubarwa ya  matukar sanyaya masa jiki gani yake ba zai iya cutar da Shamsiyya da da yayi niyyar tayi ta zama  idan ta gaji zata koma wajen Gwaggo akan tasa ya saketa.

Dan yasan ba zai tab’a iya mata kallon matarsa bayan Yana da Zinatu ba.

bai ma kawowa Kansa zai tab’a taka kafarsa yazo dakin Shamsiyyar ba,dan bai ma isa bane Zinatu hawa dokin wuyansa za tayi.

Gyada Kansa kawai ya ringa yi ya ringa kwantarwa da Gwaggo hankali

Har gida ya Kai Gwaggon  da sai da suka yi da gaske Shamsiyya ta cikata.

Har ya isa gidan gwaggo nasiha ta ringa masa akan rike Shamsiyya da Amana tana “Kasa a ranka ni ka wulakanta idan ka wulakanta Shamsiyya,Habu ko sau daya ne kabi umarnina ka nuna min na isa da Kai,ka nuna min ka haifu kai dan Halak ne ka karyata zargin da ake akanka na cewar mace ke juya ka ba,ka zama tsayayyen namiji a gidanka,mai iya sawa ya kuma hana,ka bawa Zinatu matsayin ta,ka bani matsayina,ka bawa shamsiya matsayinta ka bawa Yan uwanka matsayinsu dan Allah Habu ka faranta min ko sau daya ne kafin na bar duniyar nan”

“Dan Allah gwaggo ki bari ba Zaki bar duniyar nan kurkusa ba in sha Allah na miki alkawari zaki ga canji daga wajena zan rike Shamsiyya da Amana bazan tab’a bari a cutar da ita ba na miki alkawari Gwaggo”

Habu yace Yana Jin wani irin rauni a zuciyarsa da ya tuna yadda Gwaggo ta tsaya musu a lokacin da mahaifinsu ya rasu.

Gwaggo albarka tayi ta sa masa Yana Jin wani irin Dadi a zuciyarsa.

Akan hanyar komawar sa gida ya samu waje yayi parking Yana tunanin yadda zai tafiyar da Al amuran gidan,da gaske bai ga ta inda wata mace zata shiga zuciyarsa ba,kudin da yake dashi yasa zawarawa da Yan mata kawo kansu wajensa, amma bai ga wacce zata kai masa Zinatu ba,raba shi da gwaggon ke san yi da Zinatu yasa ya karbi Auren Shamsiya ba wai dan yaji zai iya tab’a Santa ba har yanzu ba iya gane kamaninta ba.

A yanzu da Gwaggo ta daureshi da jijjiyon jikinsa sai ya rasa mai ya dace yayi gani yake Allah ya Isan da Gwaggon ke ta jera mi shi akan idan ya cutar da Shamsiyya zai iya sauka a Kansa idan ya share ma shamsiyar,Taya Zinatu zata fahimci Allah ya Isan Gwaggon yake kaucewa ba san shamsiya yake ba.

Zai so Zinatu ta bashi hadin kai wajen sauke wanan nauyin da Gwaggo ta dora mi shi,zai so Zinatu tasan ita kadai yake so ko Mata uku aka bashi ya aura Kuma lokaci guda ba zai tab’a san wata ba idan ba ita ba.

Yanzu idan bai fita hakkin shamsiya dake rataye a wuyansa ba hakan na nufin ya cutar da ita.

Ba zai so ya ketare umarnin Gwaggo ba zai so ya faranta mata rai zai so ya nuna mata cewar shi din dan Halak ne har gobe Babu kamarta a duniyarsa duk da irin San da yake yiwa Zinatu.

Sai da ya kusa awa daya a zaune a cikin mota Yana Saka da warwara kafin ya fito daga motar ya siyi nama da Lemo  Kashi bibiyu ya nufi gidan Yana hararo tashin hankalin da zai tarar dan yasan yau bai Isa runtsawa ba duk da ya sa a ransa a dakin Shamsiyyar zai kwana dan nasihar da gwaggo ta masa ya ratsa shi,ba zai so Amjad ya girma ya bijirewa umarninsu ba,shi Kansa yasan Yana fifita Zinatu akan kowa san da yake mata duk ya rufe masa ido ya kasa ganin kowa.

Tun kafin yayi parking ya ringa juyo ihu daga bangaren shamsiya, hankali a balain tashe ya fito daga motar ko kashe motar ma bai yi ba.

Zinatu

       Safa da Marwa kawai take a dakinta tana Jin kamar ta koma palon ta sossokawa gwaggo ashar, gwaggo ta kai ta bango Jira kawai take Habu ya shigo yace ta koma part din Shamsiyya yaga yadda zata  yiwa Gwaggon hauka.

Tana Labe a jikin k’ofa tana Jin duk abinda suke fada.

Haushin Habu kawai take ji da taji Yana rawar murya da baki wajen kwantarwa da Gwaggo hankali wai zai rike Shamsiyya da Amana.

Ko da suka fita sai da ta biyo bayansu ta labe a ta bayan window tana Jin duk maganar da suke da yasa taji kanta da zuciyarta na hayaki,ji take kamar ta fada dakin amma wani zuciyar na hana ta.

Tana nan a makale taga Gwaggo ta fito Habu  na rawar jiki wajen gyara mata takalmanta.

Har suka hau motar suka bar harabar gidan duk akan idonta.

Jiki na rawa ta zagayo bakin k’ofar part din a daidai lokacin da taji motsin Shamsiya na kicin kicin da k’ofa da alama so take ta rufe k’ofar.

Ita kuwa cikin zafin nama ta Tura k’ofar da k’arfi, Shamsiyya kuwa ta saki ihu tayi hanyar dakinta dan a balain tsorace take kamar zata bi bayan su Gwaggon haka ta ringa ji dan ta cikin mayafin ta ta ringa kallon Zinatun dake jifanta da mugun Kallo kamar zata jawota ta rabata da ranta,labarin da Hanne ta bata akan irin zaman da suka yi da ita ya Kara kada mata yayan hanji.

Sai da aka daura auren ta fara kuka tana nadama da bata bijirewa Auren ba dan da Alama ta jefa kanta a cikin masifa gashi ko kadan bata san tashin hankali dan tana da balain tsoro

Ihu ta ringa zundumawa da iya karfin ta a daidai lokacin da Zinatu ta jawo rigarta ta baya ta keta mata shi har kasa dan doguwar riga ce a jikinta.

A haukace Zinatu ta kai mata shakka da taga shamsiyar bata da makusa tana samun kwanciyar hankali kyaunta zai fito sosai gata yarinya da ita hararo wai Habu Yama shigo dakinta har ya kalleta yasa ta Kara Shaketa tana “ke kin isa ki hada kanki Dani?kin Isa ki zama kishiyata?har kina da karfin halin da Zaki yarda a aura Miki mijina,kuma dan uwarki har ki yarda da Auren saboda tsananin kwadayi wanan tsinaniyar matar ta hada ki da mijina ki yarda ki Aure shi,an gaya Miki akwai wajen kishiya a gidana”?

Da ihu Zinatu ke magana tana bugun Shamsiyya da ta kankame jikinta tana ta b’oye fuskarta da Zinatu ke kawowa hari,gashinta da ya sauka har gadon bayanta da ta Sha kitso kananu kawai take ja tana kai mata duka,dan idan ba motsi taga shamsiyar ta daina yi ba ba zata tab’a barinta ba,idan ta sumar da ita da kafarta zata bar gidan.

Fusgar da aka mata da k’arfi da sallatin Habu yasa ta saki Shamsiyyar da tayi nassarar fasa mata baki,dan karfinsu ma ba daya bane dan ita kallon Yar shekara ma Sha biyar take mata

“Zinatu kina hauka ne uban me ta miki kike dukanta innalillahi wa inna ilaihi rajiun mai kika yi haka”?

Habu yace cikin tashin hankali tare da nufar wajen Shamsiyya da ba wani motsin kirki take ba,bayanta duk a waje saboda kankame jikinta tayi,sanadin yaga mata rigar da tayi ya bayyana bayanta da farin breziyar da ta Saka”

A haukace Zinatu tayi Kansa ko nauyin cikin jikinta bata ji ta fara “Kamata kake so kayi a gabana Habu ya naga hankalin ka ya tashi da dukan da na mata ko Santa kake yi?

Habu tureta yayi ya ruko Shamsiyya da jikinta ke karkarwa tana “Dan Allah ka maidani gidanmu ba zan iya zama ba wallahi na hakura da Auren ba zan iya ba,dan Allah ka sauwake min”

“Kayi gaggawar sakinta baban Amjad tunda ta nemi ka saketa komai ya zo da sauki ka saketa baban Amjad idan ba haka ba wallahi wanan sharar fagge ne,dan azaba zan ta gana mata har sai ta bar gidanan”

Duk inda Gwaggo ta kai da ta takura min wallahi hakanta ba zai cimma ruwa ba sai dai bakin ciki ya kasheta”

Marin da Habu ya d’auke ta dashi yasa ta ganin taurari,kafin ta dawo hayyacinta ya Kara kwasheta da wani Marin.

Yana hucci saboda tsananin b’acin rai,ya rike Shamsiyya gam da ta b’uya a bayansa tana rawar jiki”

Zinatu kuwa sai da ta daina ganin taurarin ta girgiza kanta ta kalli dama da hagu ta karewa dakin Kallo dan gani take ba Habu ne ya mareta ba wani ne dai ya mareta,sai dai muryar Habu dake tashi cikin tsananin b’acin rai yasa ta dawo daga shigarta da Marin yayi har tana neman yaudarar kanta akan Marin ne ya shigeta shiyasa taga kamar Habun ne ya mareta.

“Dan Ina kaunarki bashi zai Saka ki Raina min uwa ba Zinatu,dan Ina kaunarki ba shi zai saka ki Bude bakin ki ki jefa mahaifiyata da mumunan magana ba,a rayuwa ban taba aibata Mahaifiyar ki ba dan haka daga Rana irin ta yau kar ki sake ki kar jefa mahaifiyata da wani banzar magana batun Shamsiyya Kuma ba zan tab’a sakinta ba sai idan Gwaggo ce tace na saketa,a yanzu na shirya zama da ita a matsayin matata,zan yiwa mahaifiyta biyayya dan ba wacce zan bi a yanzu na samu aljanna sama da ita ba zanyi gangancn biye miki na Saba mata ba dan kawai Ina sanki,dan haka ba zan tab’a sakin shamsiya ba ki shirya zama da ita a matsayin abokiyar zamanki”

Zinatu suman wucin gadi tayi tana ganin kamar dai ba Habu ne a gabanta ba,gani take Aljannu ne suka shige shi dan Habun da ta san Yana kaunarta kamar ya mutu ba zai tab’a ma iya tsayawa a gabanta Yana zai karbi auren Shamsiya ba ballantana wai har ya gaura mata Mari”

Da ido kawai take bin Habun da hankalinsa ya koma kan shamsiya dake magiyar ya Maida ita gida ita ba zata iya ba

Rarrashin ta kawai yake Yana “Kiyi hakuri shamsiya ba zan iya Maida ke gida ba a yanzu ba zan kara barin Zinatu ta tab’a ki ba muje daki ki canza kayan jikinki”

Kukan kura Zinatu tayi kamar mahaukaciya tayi kan Habu tana “Idan ka Isa Allah ya tsine min daga gwaggo har Wanan tsinaniyar yarinyar sai Allah ya tsine musu na gane asirice ka Gwaggo tayi dan a cikin hayyacinka baka Isa ka wulakantani ba.

Habu kuwa ido ya zuba mata jikinsa na wani irin kyarma.

Shamsiya kuwa dakinta ta shige da sauri ta rufo k’ofa

Habu kuwa cikin wani iirn murya yace “Gwaggon ce tsinaniya”?

“A itace na fada tsinanniya ce ita idan ka cika!!!!!

Naushin da Habu ya kai mata baki ya katse mata maganar da take,Habu kuwa ya rufeta da mugun duka Yana “Mahaifiyata kike zagi Zinatu”?dama haka kike”

Bai ma damu da cikin dake jikinta ba ya cigaba da dukanta Zinatu da bakinta bai mutu ba ta cigaba da zaginsa tana aunawa gwaggo zagi,

Habu kuwa da yaji ba zai iya cigaba da jure maganarta ba yace “Kije ki kwashe kayanki Zinatu na sake ki saki daya da na cigaba da zama dake gwara San naki yayi ajalina!!¡!!!

*Page 16*

                  Numfashin Zinatu ne ya nemi barin jikinta a lokacin da kalmar sakin  ya sauka a kunnenta.

Kallon Habu kawai take tana ganin kamar dai kunnen ta daidai ne bai Jiyo mata ba.

“Habu sakina kayi”??

Tace kamar Mai rada

Habu da bakin Zinatun kawai yake gani,ya Isa gabanta ya damko hannunta ya hau janta da kasa dan ji yake kamar ya sumar da ita.

Yana fita da ita bai direta a ko’ina ba sai a waje yace “Zan koyi tsanarki Zinatu dan baki cancanci na soki ba,zan koyi tsanarki Zinatu dan ke din ba mace bace ta gari,idan har a gaban idona zaki iya zagin wacce ta kawo ni duniya Wanda da bata haifeni ta kula dani ba,da baki Isa ganina har ki aureni mu haifi Yara dake ba,ko wani kika ga Yana zagin Mahaifiyata ya kamata ace sai inda karfin ki ya kare, Amma Zinatu a gaban idona kike zagin gwaggo da bata tab’a miki komai ba, akan ki bana ji bana gani na gwammaci na b’ata da kowa akan na b’ata miki.

 Raina ne kawai ban cire na baki ba Zinatu,ban Kai Gwaggo saudiya ba,ban Kai kaina ba san da nake miki Yasa na biya miki saboda naga burinki kenan amma da yake ke jahila ce a gabana kike zagin Mahaifiyata dan kawai ta aura min wata, Zinatu kar na shiga na fito na ganki a k’ofar gidanan gobe zan biyoki da kayanki idan kin haihu zan zo na karbi abinda kika haifa”

Habu yace cikin tsananin b’acin ran da bai tab’a tsintar Kansa a ciki ba, gwaggo kawai yake gani a idonsa da ta rike hannunsa tana rokonsa ta masa biyayya ko da sau daya ne,Taya ma Mahaifiyar sa zata na masa magiya akan ya Mata biyayya.

Hannunsa da Zinatu ta rike da sauri jiki na karkarwa yasa ya juyo Yana mata wani irin Kallo dan har yanzu zagin da tayi wa Gwaggo yake ji a kunnensa

“Karka min haka Habu karka sakeni a lokacin da kishi ya rufemin ido har hankalina ya gushe da ganin ka auri wata karka min haka habu wallahi bansan na zagi Gwaggo ba subutar baki nayi,da bana kaunarka ba zanyi kishinka ba habu, Ina so da kaunar da kake min Habu? ka manta ka sakeni a baya taya zaka sake datse wani igiyar akan kuskuren da bansan ma nayi ba sai da na dawo hayyacina, Habu rabona da baccin kirki tun kafin ayi maganar auren nan Habu taya Saka sakeni dan Allah karka min haka”

Zinatu tace cikin tsananin tashin hankali tana ganin kamar dai ba Habun da ta sani bane a gabanta wani Habun ne,dan tasan irin Kaunar da yake mata kamar ya goyata da wuya ya iya tab’a sakinta idan ba tilasta masa akayi ba, bata tab’a kawowa zai ma iya sakinta cikin sauki haka ba,tunda take bata tab’a ganinsa a cikin irin wanan bacin ran ba daga yadda yake magana tasan idan ta tsaya Sanya rasa shi za tayi ta barwa Shamsiya gidan

Fusge hannunsa yayi Yana “Na riga da na sakeki Zinatu duk gushewar da hankalin ki zai yi ba zai Saka ki tab’a zagin uwarki ba,yau ko hauka kike idan kika ga wayanda suka kawo ki duniya kinsani,Raina Mahaifiyata kika yi Kuma yanzu na gane duk ni na jawo mata zagin da kika mata,dan da na nuna miki bana wasa da ita da baki Isa Bude wanan bakin naki wajen tsine min Uwa ba, Zinatu bana fatan ki dawo rayuwata dan ba zan tab’a manta zagin da kika yi wa Mahaifiyata da bata miki komai ba,a yanzu na fara gane duk abinda take so ta ganar dani, Zinatu ke ba matuniyar kirki bace ba kar na dawo na same ki a k’ofar gidanan Zinatu”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Habu Zinatun ka ce fa karka min haka kaga saura wata uku na haihu,zanje na bawa Gwaggo hakuri wallahi subutar baki nayi karka min haka”

Zinatu tace a haukace tana buga k’ofar dan rufo k’ofar yayi ya Saka sakata.

Zinatu kuwa ta dora hannu aka ta ringa zunduma ihu tana kar ya Mata haka.

Habu kuwa bangaren shamsiya ya koma shi Kansa jikinsa rawa yake dan Zinatu ta matukar girgiza shi,ta bashi mamakin da har yanzu bai sake shi ba,wai Gwaggo take tsinewa a gabansa.

Koda ya shiga sheshekar kukan Shamsiyya yake jiyowa daga dakinta.

A hankali ya karasa bakin k’ofar ya hau bugawa Yana kiranta.

Amma fir tak’i zuwa ta bud’e,ganin babu alamar zata Bud’e yasa ya koma part din Zinatun,dan yasan Shamsiyya ta balain tsorata shiyasa taki bud’ewa,dan ko ta bud’e sai dai ya bata hakuri ya kwantar mata da hankali dan ransa a mugun b’ace yake.

A gaban Tv ya tadda yaran gabad’aya Amjad ne kawai a gefe Yana duba littafinsa,da alama duk hayaniyar nan da ake ba Wanda yaji saboda idan suka sakae tv a gaba basa ji basa gani.

Wani irin tsawa ya daka musu da bai tab’a daka musu irinsa ba dan gani yake yaran kansu zai iya rufe su da duka.

A tsawace yace su wuce suje su kwanta ya Kara da musu gargadin kar ya sake ganin kowa a gaban Tv gidan.

Da gudu suka shige dakinsu, Sultana da Zinatu tafi shagwaba tayi hanyar dakin Zinatun tana turo baki da alama duk basu ga ma fitar ta ba.

Da Mari ya dawo da ita baya ta kuwa kwasa da gudu tayi dakinsu tana Ihun Kiran Zinatu,Amjad kuwa litattafan sa ya tattara ya nufi dakinsa Shima.

Habu kuwa ya shige dakinsa ya baje akan gadon da kamshin Zinatun ke ta tashi.

Tsaki kawai yake Yana tuno abinda Zinatu tayi  bai kawo duk rashin hankalin ta zata iya zagin Gwaggo ba.

Yau banda San da yake mata da ba abinda zai hana ya Mata saki uku,duk wanan hidimar da yake mata duk wanan kaunar da yake mata ashe zata iya zagin Gwaggo da sai a yau ya fara gane kuskuren sa,da’a ce Gwaggo ma bata da hakuri da zata iya masa baki.

Yafi awa biyu a kwance Yana tuno irin Abubuwan da Zinatun ke masa da yaci ya gane ba wani Sansa take ba,dan bai  manta yadda take tace masa tunda yana gudun ayi masa baki ba kar ya Maida ita,Abu kadan sai ta ce ya saketa,sai a yanzu yake ganin kalar rainin da Zinatun ta masa,duk idonsa ya rufe da kaunarta da yake Jin ko gezau baiyi ba da abinda ta masa,zai koyi danne zuciyarsa ne dan ya nunawa Zinatu Mahimanci Mahaifiyarsa,a hankali ya tafi Tunanin yadda take yawan kawo masa kushen Sule bama shi ba duk Wanda ya rabe shi Zinatu sai ta kawo matsalarsa.

Ko kadan bai ji yayi nadamar sakin da yayi mata ba.

Wajen Sha biyu ya Kara mik’ewa ya nufi part din Shamsiyya dan yanzu gani yake kulawar da zai bawa Shamsiyya shine kawai zai faranta ran Gwaggon da yake shan alwashin sake zuwa ya bata hakuri,yayi nadamar kulle Sule a yau yafi a kirga,sai a yanzu yake iya tunanin zata ma iya yuwa sharri Zinatun tayi masa dan ta tsani Sulen ya Kuma sani,dan da ace ma zuciyarta mai kyau ne,ai tasan Sulen dan uwansa ne ita mai b’oye laifin sa ne a wajensa amma itace kan gaba wajen zuga shi akan ya kulle Sulen da yake dan uwansa da bai manta irin Kaunar da suke yiwa juna ba.

Ganin k’ofar part din Shamsiyya ma a kulle yake ta waje yasa ya koma part din zinatun.

Ya shige dakinsa a ranar ko baccin bai iya yi ba dan yasan zai Sha wahalar rashin Zinatu shi Kansa yana mamakin irin san da yake mata.

Zinatu

        Dak’yar ta iya mik’ewa Jiri na dib’anta ta nufi bakin titi dan bata ga alamar Habu zai saurareta ba,har wani zazzabi Mai zafi ne ya rufeta tana rawar sanyi,gani take kamar mafarki take yi ba da gaske Habu ya furta mata kalmar saki ya watso ta waje ba.

Taya ma zata je gidansu akan Habu ya Kara sakinta,bata manta irin fadan da iyayenta suka mata akan yiwa Habu biyayya ba,dan kyautar da yake dashi yasa yan uwanta ke balain ji dashi, kawayenta kullum kan yi tunanin ko asirce Habun tayi,wai sai gashi akan gwaggo ya saketa,abunda yafi daga Mata hankali Shamsiyya da ta bari a gidan da take hangota a fuskarta.

Koda ta tari abin hawa gidan wata kawarta Hajiya Murja ta nufa dan a yanzu ba mai taimaka mata da wajen kwana sai ita,bata san a tab’a sanin ma habu ya Kara sakinta,tana da yakinin zai mai da ita dakinta,sakin nan da ya mata ba abinda ya Kara saka mata sama da tsanar Gwaggon da take Jin dama tana da yadda za ta kawo  karshenta ko paralyzed me ma tayi yadda zata daina sintiri tana hada mata masifa,duk wanan halin da ta tsinci kanta a ciki laifin gwaggon ne,banda taga Habu ya zuciyo da ba abinda zai hana ta ma fara dira gidan Sulen ta tsille su biyun dan tasan su suka hada munafirci da aka d’auko Shamsiyya da idan ta tuna ta sai taji kanta ta Sara mata saboda tsananin bakin ciki.

Baki sake hajiya murjan ta ringa Kallonta dan mijinta ma yafi habu kudi,ita ta nace wa hajiya murjan dan tana san muamalla da manyan masu kudi.

Zinatu kuwa da tayi zaman dirshan a kasa sai da ta shanye ruwa mai balain sanyi da aka ajiye mata a gabanta Kafin ta dan ji sanyi sanyi a zuciyarta.

“Murja taimaka min zaki yi Habu ya sakeni a cikin Daren nan ban Isa zuwa gidanmu ba tsautsayi yasa naje na zagi Mahaifiyar sa da ta sa aka min kishiya bansan Habu zai iya sakina ba sai gashi a cikin daren nan ya sakeni ya koreni Taya zan iya zuwa gida nace an sake sakina”?

Kuka Zinatu ta ringa yi sosai tana Jin kamar zata sume idan ta tuno korarta habu yayi ba ta inda ma yayi maganar zai tab’a iya maida ita

Murjan kuwa murmurshi ta saki tana “Ki kwantar da hankalinki Zinatu karki sake ki Kara zubar d hawayenki kin kawo kuka gidan mutuwa yanzu muje na raka ki daki ki watsa ruwa ki kwanta gobe sai muyi magana

Zinatu mik’ewa tayi tana share hawayen da ke zubo mata idan ta tuna kalmar da Habu ya jefata dashi akan zai Koyi  tsanarta.

Da zazzabi ta kwana dan ko runtsawa ba tayi ba har wani ihu take saki ita kadai idan ta tuna Shamsiyya na gidanta a matsayin matar Habun da ya dawo yace ya karbi Auren ta da hannu biyu a karyarsa wai Gwaggo yake san bin umarninta waya sani ma.ko yaudarar kanta ma take Yana San Shamsiyya da bata Fi girman Amrah Yar su ba”

tsinuwa da alkabai ba irin Wanda bata yiwa Gwaggo tana daga kwance ba, ta kasa yarda Habun da yake neman goyata saboda so shine ya iya sakinta haka”

Habu

     Tunda ya dawo daga massallacin Asuba ya nufi bangaren shamsiya dan ya dubata dan wani iirn nauyi yake ji a kirjinsa idan ya tuna Gwaggo da ta bashi amanarta.

Yasan Zinatu ta daketa ya kuma ga kamar dan jini a fuskarta zai so ya dubata ya hada da bata hakuri dan ba zai so gwaggo ta tab’a sanin abinda Zinatun ta mata ba duk da ko ta sani karshenta tace ya saki Zinatun da ya Dade da sakinta.

A rufe yake tun jiya ta ciki aka  kulle balle ya samu spare key ya bude.

A palon Zinatu yayi zamansa Yana ta tsaki da yaga yadda yayi ta fama dasu Amrah akan su tashi suyi sallah har ga Allah baya Jin dadin irin tarbiyyar da take basu a babu yadda zaiyi ne.

Har hararo Ameera yake a matsayin yar cikinsa dan har ga Allah ji yake dama shi ya haifeta.

Amrah yayi wa magana akan ta hada musu kayan shayin sai a lokacin ma suka gane Zinatun bata gidan.

Sultana kuwa a lokacin kusan itace auta ihu ta fara yi tana ita a kaita wajen Zinatun sai da ya bubuge mata baki ta masa shiru wani irin sangarta tayi wa yaran da kamar sai da ya saketa yake ta gane Abubuwan da take masa a baya ko kusa ko alama baya iya magana dan bashi da zafi Sam,Amma a ganin da yake yiwa yaran yanzu ba tarbiyyar da ta musu na kwarai.

Wajen goma ya Kara komawa bangaren Shamsiyya inda ya ga ta Fito da akwatin ta sanye da wani dogon hijabi idonta a balain kumbure duk da ba fara bace ba.

Habu jiki na rawa ya isa wajen Shamsiyya Yana “Ina Zaki je da akwati Shamsiyya”?

“Dan Allah kayi hakuri ka sakeni ba zan iya zama da matarka ba,kaga yadda ta kumbura min hannu kaga yadda ta  yakushe min fuska daga kawo ni jiya jiyan nan wallahi ba zan iya ba gidanmu zan tafi”

“Shamsiyya kiyi hakuri bansan Zinatu zata tab’a lafiyar ki ba da ban kai Gwaggo gida ba,so kike ki jawo min fada a wajen Gwaggo? Zinatun da kike ta tsoranta na saketa Shamsiyya dan haka dan Allah kiyi hakuri ki mai da akwatin nan kizo Ina so na miki magana kinji”

Habu yace Yana karewa Shamsiyya Kallo  da ta sunkuyar da Kai, dan sai a yanzu ya Kara ganin fukarta sosai tana da kyanta daidia nata, dak’yar ya samu ta bi shi palon Zinatun tana ita dai ya rufa mata asiri ya Maida Zinatu dakinta kar ta zo ta mata wani muguntar.

Su Amjad ya Tara gabad’aya ya nuna musu Shamsiyya da kanta ke kasa ya fara magana Yana “Wanan itace sabuwar auntyn ku Ina so ku d’auketa tamkar Umman ku,duk ranar da naga Kun mata ba daidai ba wallahi a ranar sai na Zane ku”

“Daddy Ina mummy mu take”?

Amrah tace tana kallon Shamsiya

“Umman ku tana gida bata da Lafiya sai taji sauki zata dawo Amrah dan haka kafin ta dawo ku rike Auntynku da hannu biyu ku girmama ta tamkar yadda zaku girmama ummanku”

“Abba wanan itace matar da ka aura da mummy ke bamu labarinta”?

Cewar sultana da take kallon Shamsiya tana harararta dan Zinatu ta basu labarinta ta kuma ce su ringa mata rashin kunya

Habu d’auke Kansa yayi kamar bai ji mai tace masa ba dan ba zai so su gwada wani rashin tarbiyyar a gaban Shamsiyyar ba

Ya hau rokon Shamsiyya akan ga su Amrah ta d’auke su tamkar yayan cikinta”

Shamsiya gyada kanta kawai take dan Yaran kansu wani irin harara suke mata dake fadar mata da gaba.

A takaice a ranar Habu bai ko fita waje ba,da  Kansa ya kwashe kayan Zinatun ya Kai daya part din da ke kulle d’auke da tarkacen komai nata.

Dan tunda Zinatun bata nan part dinta ya kamata shamsiya ta zauna ,ya karanci tana da balain tarbiya dan duk abinda yace jiki na rawa  takeyi dan duk da zuciyarsa ba dadi sai da yaci abincin da ya d’auka ba zai iya ci ba dan har lokacin zuciyarsa cike take da damuwa.

Kayan gadon Shamsiyya yasa a dakin Zinatun.

Duk wani abu nata sai da ya d’auko ya dawo dashi part din zinatun.

Kujeru ne kawai bai d’auko ba dan ko sati ba’ayi da canza kujerun palon Zinatun da yake ta iya k’ok’arinsa wajen ganin ya faranta mata sai gashi wai Gwaggon ce Abar zagi a wajenta.

Bai kawo zai Kara abincin da Shamsiyya tayi ba sai gashi ya Kara sawa ta zubo masa wani Dan a rayuwarsa Yana balain San abincin gargajiya Zinatu kuwa bata taba wahalar da kanta wajen masa girkin gargajiya ba dan tafi so tana mik’e ayi mata komai”

Sosai yake iya k’ok’arin sa wajen hana Kansa tuna Zinatun da yake Jin ta acan kasan zuciyarsa,ya kasa manta zagin da tayi wa Gwaggo.

Shamsiya kuwa ko kadan ta kasa sakin jikinta a part din zinatun dan gani take kowane lokaci zata iya dawowa dan tasan dole ne ma Habu ya dawo da ita dan ba Wanda bai san irin san da yake mata ba.

Yaran kuwa tasan ganin idon babansu ya Hana su mata rashin kunya dan Sultana da gangan ta ringa shigowa kitchen din tana watsar da abubuwa dan tayi magana.

Koda dare yayi shamsiya dakin Zinatun ta shige da saurinta

Kafin ta fito daga wanka ta dannawa k’ofar mukulli Sai ganin Habu tayi ya shigo da sallama.

Da sauri ta Saka hijabin ta Habu Kuma da ya dan ji wani yam a jikinsa na ganin ta da  daurin kirji kafin ta Saka hijabin ya d’auke Kansa da sauri ya juya zai fita sai ganin Zinatu yayi a bakin k’ofa tana kallonsa da jajjayen idonta kamar kirjinta zai fado.

“Habu kace min baka san Shamsiyya”?

“Ina ga ban ga wajen da nace na maidaki dakinki ba uban me kika zo nema”….??

*Aunty Zee mom mujahid katsina*

*Promo!promo!promo*

*Lokacin da kuke ta jira yazo insha Allah nakawo maku kayayyakina as promo duk dan kuciga ba da gwada wa* *kuduba Zakuga promo price*

*Page 17*

Zinatu

        Wuraren asuba bacci ya saceta dan kuka kawai take ga uban zazzabin da ya rufeta.

Jikinta da shatin bugun da Habun ya Mata kawai take bi da Kallo ta kasa yarda wai Habun da take tunanin ko shaye shaye yayi ba zai iya dukanta ba  ballantana wai har ya kai ga sakinta wai sai  gashi bayan duka sai da ya hada Mata da saki a Daren da aka kawo masa Shamsiyya da ganin da ta mata a yau ta matukar girgiza ta ,duk ba kuma wanan yafi daga Mata hankali ba sama da Shamsiyya da yace zai karbi aurenta sai dai idan Gwaggo ce tace ya saketa,bayan duk ba haka ya mata alkawari ba.

Tasan irin San da yake mata baya san b’acin ranta.

a Sanin da ta masa  yafi san farin cikinta ma akan na Gwaggo shi yasa bata kawo dan ta ma zagi Gwaggo zai ji haushi ba.

Haka ta ringa juyi tana hawaye har bacci ya d’auke.

Wajen takwas ta tashi a firgice har da ihunta saboda mumunan mafarkin da tayi wai Habu ya maida Shamsiyya bangarenta Kuma wai har ya tab’ata.

Tana tsoron mafarkin ta ya tabbata dan ta gama sawa a ranta wani Abu Gwaggo tayi wa Habun,idan har ba wani abu ta masa ba ba yadda Habu zai iya mata abinda ya  mata jiya.

Idan ba Gwaggo ce ta masa wani abu ba toh su Hanne ne suka masa wani abu kila dan su kuntata mata,har gwara ace wata aka samo masa da Shamsiyya da ta kasance kanwar Hanne matar Sule.

Palo ta fito jikinta na karkarwa duk da Yar aiki kawai ta gani a palon ba kowa dan da alama hajiya murjan ba da wuri suke tashi ba kuma mijinta na gari.

Ido a rufe ta nufi hanyar dakin Hajiya murjan dan ji take kamar ta zauce duk da mafarki tayi gani take da gaske ne.

Sai da Hajiya murjan ta fito fuskarta d’auke da mamaki ta dan dawo hayyacinta dan da k’arfi ta  ringa buga dakin kamar itace tasa ta mafarkin.

“Zinatu lafiya kuwa”?

Kuka Zinatu ta fashe dashi tana “Kiyi hakuri Murja ba’a nutse nake ba dan Allah ki taimaka min Ina neman rasa mijina”

“Yanzu tsakani da Allah da sassafe zaki zo kina buga min k’ofa? idan kika tashi Alhaji fa?saurin Mai kike yi bani nace ki bar komai a hannu na  zuwa anjima  idan Alhaji ya fita ba? yanzu wani Abu zan iya miki da sassafen nan.

Nifa bana san takura gaskiya bana san irin haka idan kinsan matsa min za kiyi sai ki koma gida idan na samu sarari zan nemeki na taimaka miki”

“Aaa Dan Allah Murja kiyi hakuri na kasa hakuri ne dan baki ga mummunan mafarkin da nayi ba zan iya mutuwa idan mafarkina ya tabbata”

“Ki koma daki ki kwanta zan shigo dakin ki wajen Sha daya dan wallahi sai goma muke tashi ni lamarina bansan gaggawa gaskiya”

“Toh shikenan Murja Nagode bari na koma dakin”

Zinatu tace tana Jin kamar ta shake murjan da take ganin wulakanci take mata yau banda tana neman taimako ai Murja bata Isa ta wulakanta ta ba.

Haka ta koma dakin idan ta kwanta,sai ta tashi zagaye kawai take a dakin tana tuna mafarkin da tayi da ya kasa barin zuciyarta.

Kallon agogo kawai take tana ganin lokacin kamar baya gudu Sam dan ta matsu murjan ta shigo ta fada mata irin taimakon da zata mata dan da ace zata samu ne da yanzu ma ta koma gidanta dan bazata tab’a iya barin shamsiya ta mallake Mata gida tana ji tana gani ba.

Kafin Sha dayan ma tayi ta fito Palo ta zauna sai da taji motsin su murjan ta koma daki tana Jin hirarsu cikin nishadi a palon da alama karyawa suke

Murja har da shagwabarta kamar yadda itama take yi wa Habun wai sai gashi ya rufe ido ya saketa akan Gwaggo.

Hawaye kawai take tana tunanin  su Sultana da kila a yanzu suna cikin damuwa da rashin ganinta,habu ko mayafi bai barta ta d’auko ba ya wurgota waje.

Habun da ta sani a cikin hayyacinsa ba zai tab’a iya mata haka ba dole juyar masa da kai akayi.

Haka ta ringa zuba tsaki tana juyo hirarsu murjan da take ganin da gangan ma take wulakanta ta yau banda kaddara mai zai kawota gidan murja har ta ringa wani bata lokacin da zata taimaka mata.

Sai wajen Sha biyu murja ta shigo dakin.

Zinatu kuwa da yake nema take haka ta hadiye b’acin ranta ta nutsu ta baje kunnuwanta tana Jin maganar da murjan ke yi bayan ta zauna a gefen gadon

“Ba’a zama haka Zinatu, Babu yadda zaki saki jiki kiyi tunanin Zaki samu duk yadda kike so batare da kin bi ta karkkashin kasa ba,iya so ba zai saka wai ki samu yadda kike so ba sai kin hada da mallaka,ni na d’auka ma kin mallake naki mijin dan har marasa kudin yanzu mallake su ake dan yawancin mazan yanzu idan ba mallake su kayi ba ka shiga uku,ka daura Aure da hawan jini da takaici,dan idan ba’a Miki kishiya ba haka danginsa zasu Sako ki a gaba amma kina mallake shi fa shikenan sai yadda kika yi dashi,dan haka yanzu taimakon da zan miki shine zan hada ki da mallamina da zai miki duk abinda kike so, matsalar ba’a samun ganinsa sai ran alhamis,kinga Kuma yau lahadi,a sati sau daya yake aiki dan haka gaggawa yanzu ba naki bane hakuri za kiyi har zuwa ranar Alhamis din”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku murja ta Ina zan iya Jira har Alhamis,kinsan mummunan mafarkin da nayi kuwa bayan wanan mallamin naki ba wani da zai iya min aiki da gaggawa”?

“Matsalarki fa garaje Zinatu,nan da kwana hudun ne ba zaki iya Jira ba ni ba Wanda zai iya taimaka Miki da nasani sama dashi dan aikinsa kamar yankan wuka ne,kina zuwa wajensa a ranar zai miki aiki,kafin ma ki baro can Habu zai haukace a nemanki”

“Ba iya Habun nake San yiwa aiki ba murja wanan Gwaggon tasa nake so ayi min maganin ta Habu ya tsani ganinta ya daina Jin maganarta ni so nake ma ya ringa wulakanta ta dan banda kar nayi kissan Kai da nace a Kau da ita gabadaya na huta,ita kuma Wanan Shamsiya a rabata da Habun ya Mata irin dukan da yamin ya saketa”

Murmurshi murja ta saki tana “Ai duk Wanda zai je wajen mallami ai bashi da wani Imani,ki Kau da ita kawai ki huta,duk Wanda zai saka ayi ma kishiya ai ya cancanci shekewa”

“Aaa murja bakin ciki dai nake so ta sheketa dan idan har an mallake min Habun wallahi sai tayi kuka duk takurar da ta min sai na rama”

“Ai fa idan kika je wajen mutumin nan fa kin gama mallake Habu sai dai ki Jira zuwa Alhamis din”

“Ina tsoron Habu ya tab’a wanan yarinya dan ni ya tsoratani jiya da naga kamar ya damu ma da yarinya nan,banda cin mutunci budurwa ce fa dak’yar idan zata girmi Amjad wai ita wanan Gwaggon zata aura masa”

“Duk karki damu ki bari ran alhamis din zan daure da na tashi da wuri sai mu tafi”

“Ina tsoron mafarkina ya tabbata murja”

Zinatu tace cikin tsananin damuwa dan hararo ma shamsiya da Habu a waje daya kila dai mafarkin da tayi da gaske ne.

Dak’yar ta ci abinci duk zuciyarta na can gida,ji take kamar ta tafi gidan kwana hudun nan da murja ta dib’ar mata gani take shekara hudu ne ba zata iya Jira ba.

Ko ta kan sallah ba ta bi ba haka ta ringa sakin ajiyar zuciya a dakin tana juyi,dan murja fitar ta ma tayi ta barta a gidan,gani take murjan ma dadi take ji na halin da ta tsinci kanta a ciki idan ba haka ba ai ko yayane ba zata rasa wani da zai mata aikin ba.

Wajen karfe shidda na Yamma bacci ya Kara saceta duk Kuma ba sallah da tayi mafarkin da tayi ta sake irinsa sak,ta tashi a firgice tana hada zufa ko da ta duba agogo sai taga wajen bakwai.

Waje ta fito da sauri ta tarar da murja da yaranta a gaban TV suna Kallo,daga yadda murja ta Dora kafa daya akan daya tana kallon tv ga yaranta a gabanta yasa su sultana Kara fado mata da tunanin itama fa shekaranjiya tana hakimce a Palo haka da yaranta sai gata a rabe a gidan murja.

“Zinatu ya dai naganki a firgice”?

“Na sake irin mafarkin da nayi dazu murja bani da nutsuwa hankalina ya kasa kwanciya”

“Dan kinsa haka a ranki ne fa shiyasa kike ta mafarki fa Zinatu”

“Bana so mafarkina ya tabbata murja zuwa gidan zanyi dan ba zan iya Jira har Alhamis ba,zanje ko ba zai Maidani ba nace masa zan zauna a dakina har zuwa na haihu dan ba zai Yu ya koreni da tsohon ciki ba Ina ga dabarar da zanyi kawai kenan murja Ina kebewa da Habu zan iya shawo Kansa ya Maidani inya so daga baya sai ya maidani ba zan iya Kara kwana anan Shamsiyya na gidana ba”

“Wanan ma dabara ce kije din komai ake ciki dai Kya sanar min”

Da sauri Zinatu ta gyada mata kai ta koma daki ta d’auko hijabin murjan da ta bata tun jiya wai tayi sallahn da duk bata da ma nutsuwar Yi sai dai duk ta rama daga baya.

Ji take kamar ta tashi sama a lokacin da ta d’auki hanyar gidan Habun.

Koda ta isa bata tsaya b’ata lokaci ba ta hau buga k’ofar dan a kulle yake.

Amjad ne yazo ya bud’e k’ofar Yana ganinta yace “Mummy kece”?

“Amjad Ina Babanku”?

“Yana Palo”

“Wancan tsinaniyar yarinya da aka kawo jiya fa”?

“Itama tana can part dinki daddy ya maida kayan ta can”

Ji tayi kamar Amjad ya buga mata guduma a kai ta saki baki tana kallon Amjad kirjinta na bugun Tara Tara da tunanin mafarkin da tayi.

Jikinta rawa kawai yake ta nufi part dinta da balain sauri.

Tana zuwa taga ba kowa a palon ido a rufe ta nufi dakinta tana hararo ganin Shamsiyya da Habu a gado,tana k’ok’arin tura k’ofar Habu ya bud’e ya fito.

Shap ta manta ma da sakinta yayi ta jefa masa tambayar “Habu kace min baka san Shamsiyya”

Wani irin Kallo ya Mata da yasa ta tuna fa ya saketa ta kasa yarda Habu ne ya canza haka lokaci guda tsawan da ya sake daka mata da “tambayarki nake uban me kika zo nema”?

“Habu shekara goma sha shidda ba wasa bane ba,babu yadda za’ayi ka sakeni da tsohon ciki ka Kara da korata,a yanzu na wuce zuwa gida da sunan an sakeni ga ciki,dan haka idan ma ba zaka Maidani dakina akan kuskuren da nayi ba wallahi sai na haihu zan bar gidanan”

“Ba dai a gidana ba Zinatu baki isa ki zauna min a gida ba,tunda har na sakeki idan Ina ganinki wallahi zan iya datse ragowar igiyar dan banga ta inda zan Kara ganin farin ki ba bayan kin zagi Mahaifiyata a gabana,ban ga ta inda zan iya zama dake har wai nayi tunanin maida ki dakinki ba dan haka Zinatu ki fitar min daga gida wallahi ba ki Isa zama a gidanan ba”

Zinatu hawaye kawai take tana kallon Habun da take hango tsanarta a idonsa,ba zata so ya datse ragowar igiyar ba duk da kankmar da yaranta suka mata suna murnar ganinta a lokacin da suka Jiyo muryarta suka fito daga daki da gudunsu haka Habu ya daka musu tsawa yace su koma ciki har da Marin sultana da ta so tuburewa.

Gani take kamar dai ba Habun da ta sani ba,yau banda cikin dake jikinta bata ga abinda zai hanata daka tsalle ta shige dakinta ta raba Shamsiya da numfashinta ba,ta tsani gwaggo da shamsiya bata San Wanda tafi tsana ma a cikin su biyun ba,bata ga akwai wani abu da za ta iya yi habu ya saurareta ba tana ji tana gani ta Kara barin gidan habu ya sawa k’ofar sakata.

Ta kasa yarda wai dakinta yanzu ya zama mallakin shamsiya da ta ji ta kulle k’ofar ta ciki a lokacin da habu ke magana yanzu sai ta ringa murna ita kadai ce a gidan tayi nassarar korarta.

Shamsiya kuwa jikinta rawa kawai yake a lokacin da taji muryar Zinatu a palon jiki na rawa ta nufi k’ofar ta kulle dan balain tsoron Zinatun take,tasan dole ta dawo shiyasa ta nunawa Habun bata san dawowa part din zinatun amma ya dage.

Tana Jin duk abinda suke daga palon har fitar Zinatu da dawowar Habun da yazo Yana buga k’ofar dakin nata.

Amma haka ta kwanta Taki bud’ewa har sai da ya gaji dan Kansa ya bar buga k’ofar.

Habu kuwa a dakinsa yaje ya kwanta da yaga Shamsiyya bata Bude k’ofar ba,ya riga da ya fahimci tana da balain tsoro,ba wai kuma tsoronsa take ji ba tsoron Zinatun take ji,da yaga karfin halinta na zuwa har da masa tambayoyi har yanzu Bai ji zuciyarsa zata iya saukowa har yayi tunanin maida ita dakinta ba kila sai a gaba zai ji zuciyarsa ta sauko duk da Shima rashin nata na azabtar da zuciyarsa dan Yana Santa kamar maraya yake Jinsa da rashinta b’acin ran da yake ciki ya hana shi ma barin zuciyarsa tayi tunanin ta,da ace ma tayi hankalin zuwa wajen Gwaggo ta kama kafa da ita zai iya ganin hankalinta ko da ba zata fito ta fadawa gwaggo abinda ta aikata ba dan Shima Kansa ba zai iya fadawa gwaggo cewar zaginta Zinatun tayi ba,amma dai da taje ta bawa Gwaggo girmanta ta bata ma hakuri akan Abubuwan da suka faru a baya Sanin da yayi wa Gwaggo sai ta sakota a gaba ta tilasta masa akan ya Maida Zinatun Kuma da tayi hakan zai iya Maida ita.

Amma tunda duk ta k’arfi take so ta dawo zai bata mamaki ko waiwayarta ba zai yi ba Koda zai mutu saboda rashinta kuwa.

Washegari wajen takwas har shamsiya ta gyara ko’ina ta hada musu Karin safe.

A kunyace ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska.

Sai da yaci ya koshi ya ce mata ya fita aiki ta masa fatan dawowa lafiya ko iya haka ya samu abunda bai tab’a samu a wajen Zinatu ba.

Ya saba da rashin karyawa a gida saboda Zinatu bata girkin safe da wuri,sai tara ma take tashi.

Rabon da haka kawai yasa kafarsa yaje gaida gwaggo batare da ita take nemansa da kanta ba har ya manta duk bai san mai ya hau Kansa da ya nemi juyawa Gwaggo baya ba.

Rabon da yayi hira da Sule na Yan uwanta ka tun kafin ma ya auro Zinatu,duk da kudin da yayi yasa ya canza amma ba canza can da zai juyawa nashi baya ba,sai da Zinatu ta shigo rayuwarsa ta ringa gano masa matsalolin sule da duk Wanda ya shafe shi,duk sai a yanzu ya fara gane kura kuran da ya tafka.

Wajen goma yayi parking a k’ofar gidan Sule da Abubuwan da ya siyo  musu ya d’auko daga bayan booth,ya shiga cikin gidan bakinsa d’auke da sallama.

Hanne ce ta amsa sallamar daga kitchen Koda ta fito Yana kallon yadda fuskarta ta dan nuna alamun kaduwa da ganinsa Wanda duk hakan bai masa dadi ba.

Gaisuwar da ta masa ya amsa Kansa tsaye ya shiga dakin su Ameera da anan gwaggo take nan Kuma yake Jiyo maganar sulen.

Sai da ya cire takalminsa ya shiga dakin da sallama Sule na zauna a kasa yana Shan Kunu da kosai.

Gwaggo itama tana daga sama karyawar take da alama hirarsu suke na uwa da d’a.

Gwaggo cikin tsananin farin ciki ta amsa sallamar sa tana “Habu auren nan da ka sake alherine a gareni yau gashi da kanka kazo gidanan ba tare da ni nake nemanka ba”

Murmurshi ya saki ya samu waje ya zauna Yana satar kallon Sulen daya hade ransa ya fara k’ok’arin Jan kafarsa da ya lura Yana masa ciwo har a lokacin.

Yayi saurin Kiran sunan Sulen da yaga har ya mik’e ya Isa bakin k’ofa”

Sule kamar ba zai tsaya ba ya kuma tsaya ya juyo Yana kallonsa

“Dan Allah dawo ka zauna kanina magana za muyi”

Gwaggo kanta mamaki take tana ganin kamar dai canza Habun aka yi bashi bane.

Sule na zama ya Kalli Gwaggo Yana “Gwaggo dan Allah ki tayani bawa Sule hakuri nayi nadamar duk abinda na masa ya taimaka ya yafe min Sharrin shaidan ya kaini a yanzu ba zan kara bari wani abu ya shiga tsakanin mu ba Gwaggo kema dan Allah ki yafemin”

“Ba zan iya manta Sharrin da matarka tamin ba Yaya Habu,har matarka ta kala min sharri akan Ina san na mata fyade,iya nan bai isheta ba ta zo har cikin gidanan tace na daketa ka yarda ka kawo Yan sanda bayan ka min duka  ka kulleni taya zan iya yafe ma abinda kayi min cikin sauki saboda kawai ni talaka ne”

“Duk banyi tunani mai zurfi ba Sule na aiwatar da duk abinda nayi.

 Kayi hakuri ka yafe min nama saki Zinatu dan na fara gane abinda Gwaggo take so ta ganar dani

“Zinatun ka saka mai ta Maka”?

Gwaggo ta jefa masa tambaya cikin tsananin mamaki ta Kara da “Ko wani abu tayi wa Shamsiyyar”?

Girgiza kai Habu yayi Yana ” Ba abinda tayi mata Gwaggo kawai tamu ce ta hado mu da ita tana gidansu idan tayi hankali sai na dawo da ita”

“Toh Allah ya kyauta”

Gwaggo kawai tace tana Jin dadin yadda Habun ke neman shiri da sule

Ganin Sulen nasan tirjewa yasa ta shiga maganar ta musu nasiha Wanda Shirin nasu yafi komai faranta mata  ta kuma gane da gaske Zinatun ke san hada kansu.

Dakyar sule ya yarda Habu ya Kai shi asibiti aka duba kafarsa da aka Dora shi akan magunguna dan kafar tasa ta tabu sosai da sai a hankali zai ji sauki dan dingisa kafar yake.

Koda suka koma Habu dagewa yayi sai gwaggo itama taje gidansa ta kwana biyu,tunda ta kwana biyu a gidan Sulen.

Silar komawar Gwaggo gidan Habun kenan da zuwanta yasa Shamsiyya ta samu saukin rashin mutunci da su Amrah suka hada kansu wajen yi mata Amjad ne kawai ke gaisheta Amma Amrah dasu sultana rashin kunya kawai suke mata da fitsara.

Habu kuwa wani daban yake Jinsa duk da tsananin kewar Zinatun da yake amma zaman Gwaggo a gidansa ya sa shi Jin wani nutsuwa na daban shamsiya kuwa tana iya k’ok’arin ta wajen kyautata masa yaso ya ringa kwana a dakinta amma kulle k’ofar da take yasa ya rabu da ita,dan baya Jin ko ya kwana a dakin nata da abinda zai iya yi matan.

Sosai ya zage wajen kyautatawa Gwaggo Wanda yaga hakan na matukar faranta mata dan a part din da su sule ke zaune nan ya sa mata sabon Katifa da komai.

Shamsiya kanta ya lura zuwanta gidan yasa ta saki jikinta dan kullum tana wajenta.

Wata guda a tsakani watarana daddare Habu ya kasa ko bacci dan a balain matse yake kwana biyu Zinatu kawai ke fado masa har da mafarkinta.

A yadda yake Jinsa yasa shi zura doguwar rigarsa ya nufi dakin shamsiya.

Bata wahalar dashi ba dan bugu biyu ta taso ta bud’e k’ofar.

Shi kuwa ya shiga ciki Yana ta rufe k’ofar anan zai kwana.

A yadda ya San Shamsiyya ya mace kenan,ya kuma gane Ashe ba da iya Zinatu zai iya samun nutsuwa ba akwai macen ma da zata iya bashi nutsuwa fiye da ita.

Sati guda da ya biyo baya wani iirn tattala Shamsiya yake kamar ya goyata.

Duk da bai zai ce Yana Santa ba Amma ta dan samu waje a zuciyarsa.

Tarbiyya da biyayyar kawai ma ya isa ya sa ta samu waje a zuciyarsa.

Cikin farin ciki yake barin gida Ya Kuma dawo da wuri duk da Zinatun ba wai mantata yayi ba amma daga lokacin da ya san Shamsiya Zinatun ta rage fado masa.

Kamar yadda Shamsiyya ta sabar masa Yana karyawa ta ke raka shi har bakin mota tayi sharr da ita dan itama kyakyawa ce ba laifi.

Sai da yayi da gaske ta rage Jin kunyarsa.

A yanzu baya kaiwa dare dan wajen biyar yake komawa gida ya fara sabo da shamsiya dan a wajen Gwaggo suke cin abinci dare sai su Kai goma suna hira kafin su mata sallama.

Sosai Shamsiyya ke bawa Gwaggo wani iirn kulawa da ke sa shi cikin farin ciki,dan komai za’ayi sai tace gwaggo kaza gwaggo kaza Yana matukar jin dadin haka abinda Zinatu bata tab’a yi ba kenan

Yana ganin irin farin cikin da gwaggo ke ciki dan kullum cikin shi musu albarka take wanda yana jin dadin addu’ar da take masa a yanzu Kuma burinsa ya jawo  sule jikinsa dake  baya baya dashi yarasa Mai yasa ya kasa sakin jikinsa dashi.

Wajen goma suka kwanta da shamsiya da ke zabga hamma akan bacci take ji,shi Kansa baccin ne a idonsa,hakane yasa Shima ya rufe ido Shamsiyya na kirjinsa kusan lokaci guda bacci yayi awon gaba dasu.

Wajen karfe uku Habu ya bude idonsa kamar Wanda aka mitsina Shamsiyya da ya gani a gefensa tayi matashi da kirjinsa yasa yayi wani Irin hankadata daga jikinsa, Shamsiyya kuwa ta bud’e idonta a hankali ta sauke akan Habun dake mata wani iirn Kallo kafin ya toshe hancinsa ya mik’e da sauri Ya fita waje.

Yana Jin kamar zai yi amai dan wani irin wari yaji shamsiya nayi gefe guda Kuma ji yake kamar ya zauce idan bai ga Zinatu ba”…….

*18*

*Page 18*

         Zinatu

Da zazzabi ta koma gidan murja a ranar ko runtsawa ba tayi ba dan a lokacin da ta koma murja har ta shige daki dakyar ta samu ma mai gadi ya bude mata k’ofa.

Haka tayi zaman dirshan a kasa taci kukanta ta gode Allah bata tab’a Jin ta karaya ba irin yau,dan bata ga alamar Habu nada muradin dawo da ita ba,bata kawo cikin sauki zai iya rabuwa da ita har ya iya kallon wata mace ba ballantana har ya Kai shi ga Maida Shamsiyya dakinta.

A yanzu ya karbi Auren Shamsiya kenan ta zama matarsa shi kuma ya rufe babinta kenan saboda kawai ta zagi Gwaggo da laifi ta mata tunda tasa aka mata kishiya yaci ya gane  cewar kishinsa ya rufe mata ido har sai da ta kai fa zagin Gwaggon da take ta tsinewa kowane mintuna.

Hararo Habu ya samu nutsuwa da Shamsiyya kawai Neman zautar da ita yake.

Habun da ta sani ba zai tab’a mata haka ba ita kanta alfahari take da irin San da yake mata,Babu boka Babu Mallam, tasan yadda yake rawar jiki a kanta idan ranta ya b’aci,dare daya kawai ya juya mata baya dan ta zagi Gwaggo.

Haka ta kwana tunani ko gyangyadi ba tayi ba kanta kamar ya fado saboda tsananin ciwo,Jira kawai take murja ta shigo ta fada mata yadda za tayi dan idan har ta samu aka mata aiki akan Habun ita kadai tasan irin abinda za tayi wa Gwaggo da Shamsiyya.

Murja kuwa bata ma san ta dawo a daren ba sai da Yar aikinta ke sanar mata a lokacin da mijinta ya fita.

Cikin mamaki ta nufi dakin da ta sauke Zinatun tana turawa ta ganta a zaune tsakar dakin kamar dai wacce ta fara Karamin hauka, Abunka da farar mace sai fuskarta tayi jawur ta kumbura saboda kukan da ta Sha.

Tambayar da ta jefawa Zinatun yasa Zinatun sake fashewa da kuka tana “Korata yayi Murja wallahi sun rabani da shi tsanata kawai nake hangowa a idonsa, mafarkin da nake ta ce miki nayi Ashe da gaske ne wallahi ya mai da Shamsiyya dakina alamar Babu ma ranar da zai maidani dakina,ya shirya zama da ita a matsayin matarsa,murja wallahi mijina na balain sona kema shaidata ce idan har ba wani abu aka masa aka rabamu ba aka cusa kiyayyata a zuciyarsa Babu yadda wai dan na zagi Mahaifiyar sa ya sakeni ya koreni wallahi an asirce min shi murja ki taimaka min ba zan iya barin shamsiya ta koreni daga gidana ta rabani da mijina ba”

Kuka Zinatu kawai take kamar ranta zai fita.

Murja kuwa tunda ta fara magana bata ce mata komai ba har sai da ta gama ta fara magana tana “Jiya kamar zan hana ki zuwa na barki dan naga ko na miki magana ba ji za kiyi ba, dama bai dace kije batare da wani shiri ba Zinatu,ni banga abin daga hankali da kuka ba, nifa nace miki ki kwantar da hankalinki wallahi Allah Habu zai dawo tafin hannunki sai yadda kika yi dashi, Shamsiyya da Gwaggo suma sai yadda kike so za kiyi dasu idan kawar dasu kike so ma kiyi cikin Sauki zai Kau miki dasu  matsalar ki rashin hakuri da garaje.

“Ta Ina zan iya hakurin rashin zaman gidana da wata macen yanzu itace a matsayina,ai minti daya kawai da za tayi a gidana tare da mijina ji nake kamar na zauce balle har wai a samu wajen sati daya nan da Alhamis da yawa zan iya mutuwa Murja dakina ya kaita daga dakin naga ya fito Ashe dama Yana sonta bansani ba,kila ma duk munafirta ta yayi suka hada baki akan Gwaggo ce tace ya aureta na shiga uku murja yanzu haka zan bari sai ran alhamis”?

“Idan fa kina gaggawa ba Zaki samu yadda kike so ba gaskiya kwana nawa ya rage alhamis din daurewa za kiyi zuwa ran Alhamis din zamanta a gidanki ai na dan lokaci ne dan bata isa dai tayi wata guda ba”

Zinatu kamar ta zauce kafin Alhamis din sai ta sha magani take iya bacci.

Ran alhamis kuwa tun asuba ta Shirya tana zaman Jiran murjan da itama ta sha kwandunan tsinuwa dan gani take dan ba itace a matsala ba shiyasa take mata abinda ta ga dama.

Ido rufe ido biyu hango Shamsiya kawai take da Habu ji take tana zuwa wajen bokan zata saka a Kau mata da shamsiyar kawai ta huta,sai ta rama duk wulakancin da Habu ya Mata akan gwaggo shi Kansa Habun sai ta gana masa azaba.

Tuki murja take amma gani take kamar da rarrafe take Jan motar dan da ta san hanya ma da ta dade da karbar tukin.

Da yake wajen mallamin wani kauye ne sai da suka Shari tafiyar awa uku kafin su Isa hau nan sauka can har suka iso wani waje kamar daji.

Mallamin bai samu fitowa wajen su ba sai da suka Kara zaman awa daya Zinatu kamar ta dora hannu a ka tayi ta kurma ihu.

A idonta dai boka ne mutumin ba wani mallami ba,murja ta riga da ta sanar mata sharrudansa shi yasa Koda ya fito ya fara surkullensa bata ce komai ba har sai da ya gama ya dago Yana “Yanzu Mai kike so ayi miki akan mijinki babarsa da kishiyarki”?

Jiki na rawa Zinatu ta fara magana tana “Ina so a mallake min mijina ya zama ni nake juya shi duk abinda nake so jiki na rawa yayi min,nafi so ayimin aiki a Kansa da ba zai iya Jin maganar kowa ba idan ba nawa ba  a tusa mishi sona yaji ba zai iya tab’a rabuwa dani ba”

“Wanan yafi komai sauki sai Kuma me”?

“Ina so ya tsani Shamsiyyar nan ya Mata saki uku ya kuma koreta”

“Banga rabuwarsu a kusa ba idan kuma aka dage toh duk sai dai ayi biyu Babu ke ki rasa itama ta rasa dan akwai rabo mai zafi a tsakaninsu sai dai ayi aikin dai da zai tsaneta”

“Yanzu ba wani abu da zaa iya yi ya rabu da ita har abada na tsani kishiya wallahi”

“Zasu rabu amma ba yanzu ba sai dai a shiga tsakanin su”

“Yanzu da rabo a tsakanin su kenan”?

Zinatu tace cikin tsananin tashin hankali kamar kirjinta ya fado”

“Kwarai kuwa akwai rabo a tsakanin su”

Zinatu ji tayi kamar ya watsa mata ruwan zafi shiru tayi tana hararo wai yaran shamsiya sun girma sun jeru da yayanta

Girgiza kai ta hau yi tana “a taimaka a duba min wallahi bana so ta haihu da mijina”

“Bake zaki koya min aikina ba Ina ga da kika zo ba abinda kika ce min na fada miki abunda ke tafe dake nasan Kuma Mai ke tafe dake dan haka idan abu mai yuwa ne zaki ji na fada”

Hakuri Zinatu ta bashi dan harararta Murja tayi ta kuma tuna gargadin da murjan ta mata ta Kara kasa da murya tana “Ina so yayi mugun tsanarta da zai ji tsanar ganinta ma Ina so ayi min aikin da ba zai iya saduwa da ita ba”

“Idan haka kike so yafi komai sauki idan har kika samo mana wandonta dashi za’ayi aikin,Ina mai tabbatar miki da wari zata na masa ko zaman minti daya ba zai iya yi da ita ba”

Sai a lokacin Zinatu taji sanyi a zuciyarta dan tasan zata samo wandon shamsiya cikin sauki

Koda tazo kan Gwaggon sai cewa tayi tana so a makantar da ita,dan ji tayi ba zata iya kashe Gwaggon ba kamar yadda murjan ke zugata akan ta Kau da ita kawai ta huta

Sai da bokan yayi dube dubensa ya dago Yana “Bata wasa da addu’a gaskiya makantar da ita ba zai yu ba”

“Toh idan ba abinda za’a iya mata Ina so mijina ya daina Jin maganarta ya ma daina waiwayrta ko zai waiwayeta duk abinda ta saka shi ya bijire mata ya daina mata biyayya”

Kai ya gyada mata dan aikin Habun mai balain sauki ne dan ba wani addu’a yake da aiki ba zai masa mumunan kamu ba.

Taso a ranar yayi aikin da Habun zai zo nemanta a haukace sai gashi yace sai Nan da sati uku zai yi aiki kafin nan tayi k’ok’ari ta kawo wandon Shamsiyar.

Duk ba haka taso ba amma ganin bokan mutum ne mai zafi yasa ta hakura batare da ta roke shi ya taimaka ya Mata aiki da gaggawa ba, dan gani take shekaru ya dib’ar mata.

Kafin sati ukun taje makarantar su Sultana a b’oye dan tasan ba wacce zata iya mata aikin sama da ita,duk ta wajen sultana take Jin duk irin zaman da ake a gidan har dawowar Gwaggo gidan duk tana da labari a wajen sultana.

Makarantar yaran take zuwa ta dubasu.

Ta matsu ta koma dakinta ta ganawa Shamsiyya azabar da zai Saka ta koma gidansu da kafafunta.

Ita ta fadawa sultana ta shiga dakin Shamsiyyar ta d’auko mata pant dinta ta kawo mata sun san gidan murjan tana yawan zuwa dasu.

Sultana kuwa bata Sha wahalar daukowa ba,dan shamsiya tana gama aikinta take tafiya wajen Gwaggo tayi zamanta wani zubin har sallah a wajen Gwaggo take yi,har ta shiga dakin ta kuma d’auko pant din shamsiya bata sani ba tana can.

A cikin jakar makarantar ta ta b’oye washegari ana tashi daga makaranta ta kaiwa Zinatu wandon.

Zinatu kuwa ta kaiwa bokan da tana zaune yayi aikinsa ya bata akan ta maida wandon duk ranar da Shamsiyya ta saka a jikinta,a ranar Habu zai mugun tsanarta a Kuma ranar Habu zai haukace saboda rashinta ba zai tab’a samun nutsuwa idan bai dawo da ita dakin ta ba.

Cikin tsananin farin ciki Zinatu ta koma gidan murjan da ta fara canza mata dan da alama ta fara gajiya da zamanta a gidan dan yanzu wani wulakanci take mata bama ta fitowa wajenta Hira abinci kuwa sai ta roka ma ake bata a wulakance.

Ji take kamar taje gidan da kanta ta Saka wandon a inda Shamsiyya zata gani ta saka.

Sanin kowane lokaci Habu zai iya zuwa nemanta idan har Shamsiyya ta saka wandon yasa ta koma gidansu ko sallama ba tayi wa Murja ba dan idan har ta koma gidanta bata Jin zata Kara waiwayar murjan tunda a yanzu itama tana da kafa ta kuma Kuma san hanyar zuwa wajen bokan.

Haka ta koma gidansu ta hau zuba idon zuwan Habu da take ganin kamar ta kwashi shekaru rabonta da shi.

Habu

        Habu safa da marwa kawai yake a dakinsa Yana Jin kamar yayi tsuntsu ya gansa a gidansu Zinatun da yaji kamar zai zauce idan bai ganta ba,bai san ma ya akayi har ya iya sakinta ba bayan irin san da yake mata kamar ya zauce.

Sai tunanin yadda aka yi ya dawo da Shamsiyya dakin Zinatu yake dan baya Jin a cikin hayyacinsa ya dawo da Shamsiyya da a yanzu yake mamakin yadda aka yi ya karbi aurenta wia har ya hada shimfida da ita bayan warin da ke busowa a jikinta.

Ya goge hancinsa da yaji kamar warin na manne da hancin nasa.

Yana dawowa daga massallaci ya nufi dakin Zinatun dan so yake ya cewa Shamsiyya ta kwashe kayanta ta koma wancan daya part din da tarkacen kayan Zinatu ke ciki da kayan dakinta,dan A yau yake so Zinatu ta dawo dakinta.

A kan sallaya ya samu Shamsiyya tana Jan carbi daga bakin k’ofar ya tsaya dan wari yaji dakin na masa sosai.

Kafin yayi magana ma ta taso da carbinta tana “baban Amjad wai lafiya ka bar dakin nan ko laifi nayi Maka”?

“Tsaya daga nan karki sake ki karaso kusa dani,wai wane irin wari kike yi haka kamar zai daukewa mutum numfashi”

Habu yace a tsawace Yana ja da baya dan sosai yaji kamar an Bud’e shadda da ta doso wajensa.

Shamsiya kuwa cak ta tsaya jikinta na daukar rawa da taji Abunda yace ta Kai fuskarta jikinta dan taji ko dai warin take,amma bata ji komai ba sai kamshi da hijabin ta keyi.

Maganganun dake fita daga bakinsa yasa taji kirjinta na wani irin bugu “kafin na dawo Ina so ki tattara duka kayanki ki koma wancan part din a yau Zinatu zata dawo dakinta”

Duk maganar da yake toshe hancinsa yayi

Kamar Wanda yaga Kashi haka ya ringa nuna kyamarsa har ya saki labulen ya fita

Shamsiyya gani take kamar mafarki take

Tasan koman Daren dadewa Zinatu zata dawo dakinta amma bata san mai yasa ta kadu da taji yace zata dawo ba,sosai taji wani irin tsoro ya shigeta daga canjin da tagani a wajen Habun da ta fara dan sakin jikinta dashi har tana Jinsa a zuciyarta.

Bata da wahalar kuka haka ta zauna a gefen gadon tana kuka da Tunanin sabon shafin rayuwar da za tayi da Zinatu da tasan wahala zata Sha a hannunta dan har yau bata manta dukan da Sha a hannunta ba.

Habu kuwa karfe bakwai a gidan su Zinatu ya masa.

Zinatu Sanin ya riga da yazo hannu yasa ta hau wahalar dashi dan sai da yayi kamar zai mata kuka dan Yama dan yi kukan kafin tace ta amince akan zata koma dakinta.

Jikinsa sai rawa yake kamar a lokacin da zai aureta.

Taso sai ya sake mata gado ya Mata fenti kafin ta koma amma ganin bata lokaci ne yasa ta shirya da Magriba ta zauna zaman jiransa dan Yana barin gidansu yace zai je ya gyara mata dakinta a yadda ya nuna mata tsanar Shamsiyya yafi komai faranta masa rai.

Sai wuraren Isha yazo ya d’auki Zinatun suka nufi gidansu

Zinatu kuwa sai alwashi take Sha na irin rashin mutunci da zata yiwa Gwaggon har Shamsiyyar dan tasan tayi wa Habu kamun da ko dukan Gwaggo tayi bai Isa magana ba.

  Gwaggo ido kawai ta zubawa shamsiya dake sheshekar kuka ta kasa yarda da maganar dake fitowa a bakinta.

Duk da tasan komai ya samu bawa daga Allah ne amma daga labarin da Shamsiyya ta bata yasa ta gane Habu ba’a cikin hayyacinsa ya nemi dawo da Zinatu ba,dan a yau ma bata Saka shi a idonta ba gabad’aya abinda tunda Zinatu ta bar rayuwarsa bai tab’a fashin zuwa gaisheta ba.

Bata so ta nuna tashin hankalinta a gaban Shamsiyya shi yasa ta hau kwantar mata da hankali akan kar ta wani damu da dawowar da Zinatu za tayi tunda har tana cikin gidan ba abinda za ta iya Mata ta bari Habun ya dawo zata masa magana akan ya gyara wancan part din kafin ta koma can.

Sai dai har suka kwanta Babu alamar Habu zai leko dakin Gwaggon duk da duk sunji lokacin da ya dawo sun Kuma Jiyo muryar Zinatun.

Abu kamar wasa sai gashi Habu ya tafi sati daya bai waiwayi Gwaggo da shamsiya da Zinatu ke iya k’ok’arin ta wajen mantar dashi su.

Dan so take ta dorawa Gwaggo hawan jini har yanzu bata Saka gwaggo da Shamsiya a idonta ba

Gwaggo kuwa zuwa yanzu ta kasa danne damuwar da take ciki dan tasan haka kawai Habu ba zai iya wanan canzawar ba,wani Abu Zinatu tayi masa da take so ya juya musu baya.

Wajen goma na safe ta fito ta nufi bangaren Zinatun Koda ta isa a Palo ta tarar da Zinatu da tsinin ciki da alama zata ma iya haihuwa yau ko gobe.

Tana ganin gwaggo ta saki wani iirn murmurshi tana mata wani iirn Kallo dan yau sai ta sake zaginta a gaban habu yadda jininta zai hau.

Gwaggo kuwa cikin hade rai tace “jeki kira min Habu kice masa yazo Ina san ganinsa”

“Bacci yake yi yace kar Wanda ya dame shi”

“Kije ki ce masa ni nake kiransa”

“Gwaggo kenan ai ki koma kawai dan ba zai fito wajenki a yanzu ba ki fadamin abinda kike so ki fada masa idan ya tashi zan fada masa”

Gwaggo ido ta zubawa Zinatu dake ta karkada kafa

Fitowar Habu daga dakinsa yasa ta zubawa habu ido da bai ko nuna alamun ya ganta ba sai da ya zauna a gefen Zinatun ya ce “Barka da Safiya gwaggo”

Gwaggo ido ta zubawa habun tana Jin kirjinta na mata wani irin nauyi dan ta gane Zinatu aikin da ta masa na har ya juya mata baya ne daurewa tayi ta fara Magana tana “Habu halan ka manta kana da wata matar”?

“Gwaggo a  gaskiya ni bana San takura yarinya da ko wanka ba tayi sai wari ke busowa daga jikinta  Mai zanyi da ita”

A takaice dan labarin nada tsayi

Gwaggo da dafa bango ta koma part dinta dan Zinatu har munafika ta kirata a gaban Habu,habu bai iya ce mata komai ba.

Wai tana.masifar auren da tasa Habu yayi dan munafirci ma a rasa wacce zaa bawa Habu sai kanwar Hanne.

Jikinta rawa kawai yake tana k’ok’arin addu’a dan tasan Zinatu da shirinta tazo idan bata Kai zuciyarta nesa ba zata iya yiwa Habu baki.

Shamsiyya kuwa duk inda Gwaggo taso b’oye mata damuwar da take.ciki har sai da ta gane.

Ita kuwa ta hau hada kayanta akan zata koma gidansu dan ba zata iya cigaba da zama watarana Zinatu ta kasheta ba, Gwaggo da kyar ta samu ta bawa Shamsiyya baki ta hakura ya zauna ta roki Shamsiyya da ta dage da addu’a ta ringa Taya habu dan duk abinda yake ba’a hayyacinsa yake ba.

 A haka Shamsiyya ta koma zama a wajen Gwaggon dake cikin tsananin damuwa dan Habu bai kara waiwayar ta ba.

A yanzu ma horar yunwa Zinatu ta fara musu,dan rashin lafiyar da Shamsiyya tayi ta gano tana d’auke da juna biyu

A irin wanan lokacin Zinatu ta haihu inda ta haifi ya mace Habu sai rawar jiki yake kamar baa taba masa haihuwa ba yama.manta da wata Shamsiyya a rayuwarsa.

Gwaggo kuwa tana kasan zuciyarsa amma ya kasa zuwa ma wajenta dan haka kawai yake ganin kamar zaman ma Gwaggon takura shi yake nadamar ma.kawota gidan yake a yanzu.

Zinatu kuwa tunda ta haihu ta fara neman hanyar da zata ci uban Shamsiyya cikin ruwan sanyi,Sanin yanzu duk abinda tace Habu Yi.mata yake jiki na rawa yasa tace masa ya je ya kira mata Shamsiyya tazo ta ringa tayata raino tana tayata girki da sauran ayyukan gidan.

Habu jiki na rawa ya doshi part din Gwaggo rabon da ya je ma har ya manta dan ko haihuwa da Zinatun tayi bai je ya fada mata ba

A lokacin shamsiya na kundundune tana rawar sanyi dan bata dade da amayar da dan abincin da taci ba,

Gwaggo kuwa sai jera mata sannu take tana tunanin Kai ta asibiti da kanta a yanzu ko bacci bata yi saboda addu’a kawai take babu dare Babu rana akan Allah ya ya dawo da habu hayyacinsa.

Da zaa auna jininta yayi balain hawa banda Shamsiya da tuni ta bar gidan Habu,ta koma gidan Sule dan a yanzu ba zata iya zama ita kadai ba tana bukatar kulawa

 Shamsiyya kuwa  sai rokon Gwaggo take akan ta barta ta koma gidansu.

Ita kuwa gwaggo ba zata so Shamsiyya ta koma gidansu asan halin da ake ciki ba

Kallon habu da ya gaisheta a tsaye kawai take shi kuwa cikin zazzare ido ya kira sunan shamsiyar dake kundundune yana ta taso taje ta dorawa Yara abinci “

Gwaggo kuwa ido kawai ta zuba masa tana kallonsa dan so take taga iya gudun ruwansa

Habu kuwa ganin Shamsiyya bata motsa ba ga wani wari daya cika masa hanci yasa ya toshe hancinsa ya nufi wajen da take kwance Yana zuwa ya yaye bargon da ta rufe kanta kafin ya ankara sai ji yayi Gwaggo ta kwashe shi da Mari tana “Shamsiyya ce zata je tayi wa Zinatu aiki”?

“Gwaggo yanzu akan wanan yarinyar kika mareni”?

Wallahi yau sai ta bar min gidana habu yace a haukace ya fugo shamsiya da ta dade da mik’ewa dan tsoron ma Habun take.

Yayi wurgi da ita Yana ta bar masa gida ya hau watsa kayan shamsiyar waje.

Gwaggo kuwa da ta fara k’ok’awa da numfashinta sai karar faduwarta yaji…

*Page 19*

Sule safa da Marwa kawai yake a harabar asibitin har sai da likita ya fito yake sanar masa Gwaggo ta farfado banda anyi gaggawan kawota asibiti zuciyarta na iya bugawa a guji bata mata rai  dan ba’a so jininta ya ringa irin wanan hawan

Sule gyada Kansa yayi Yana za’a kiyaye ko zai iya ganin Gwaggon yanzu?

Likita yace masa ya bari sai zuwa anjima idan ta farfado.

Sule waje ya samu ya zauna ya dafe Kansa Yana Jin zuciyarsa na masa wani irin kunna banda Yau yaje gidan Habun da kila sai dai ya d’auko gawan Gwaggo.

Dan kwana biyu kenan Gwaggo ta ringa fado masa Yau har da mafarki da ita, Wanda hakan yasa shi shiryawa akan yaje ya gaisheta,dan Su Ameera ma haka suke ta damunsa akan ya d’auko gwaggo ai itama ta yiwa su Habu kwana biyun.

Duk da Shirin da Habun ke nema dashi Sam ya kasa sakin jikinsa dashi,dan yasan rashin Zinatu yasa shi neman su amma Sanin da yayi wa Zinatu dole zata dawo,ko ba dan haka ba yanzu zai tsaya a matsayinsa ba zai shishige masa ba.

Koda ya shiga gidan Habun wajen Zinatun yaso yayi sai yajiyo Ihun Shamsiyya daga Bangaren da suka zauna.

Cikin faduwar gaba ya nufi part din da gudunsa inda da zuwansa yaga Shamsiyya akan Gwaggo Habu Kuma na tsaye akan Gwaggon Yana dakawa shamsiya tsawa wai ta matsa masa ya duba Gwaggon.

Bai ma san ya akayi ya Isa wajen Gwaggon ba ya sureta dak’yar dan kafarsa mugun ciwo yake masa dan ma Gwaggon irin jikin Fulani ne da ita bata da kib’a.

Bai ga wani tashin hankali a tare da Habu ba,Wanda hakan yayi matukar bashi mamaki.

Sai da ya fita da Gwaggo ya hango Zinatu ta fito daga part din ta tana yamutsa fuska.

Cak ya tsaya da Gwaggo a hannu dan ko ba’a fada masa ba yasan Zinatu tana da hannu a faduwar da Gwaggo tayi,ya riga da yasan wacce Zinatu sai dai ya bawa wani labari

Shamsiya kuwa sai ihu take tana su wuce su Kai gwaggo asibtii

A daidai lokacin da Habun ya tadda motar kamar Wanda ake wa dole ya daga murya Yana ya kawo Gwaggon su kaita asibiti.

Zinatu kuwa ta nufi wajensa tana tambyarsa Mai ya faru kamar wani yaronta ya hau bata labari.

Sule kuwa jikinsa rawa kawai yake saboda tsananin b’acin rai,dan Gwaggo na zaune a gidansa cikin rufin asiri Habu yaje ya d’auko ta.

Muryar Shamsiyya ya dawo da shi hankalinsa akan ga  Mai mota can ta  samo a waje bai ma san sadda ta fita waje ba.

Wajen ya fita da Gwaggo Yana Jin muryar Habu Yana ba zai zo ya shiga motar su tafi ba.

Sai da ya saka gwaggo. Abayan motar ya koma cikin gidan Zinatu har lokacin tana tsaye a jikin motar.

Sule kuwa da isar sa ya shako wuyan Habun dake tsaye Shima Yana “Wallahi idan wani abu ya samu Gwaggo na rantse da Allah sai na kasheka na kashe tsinanniyar matar nan taka, Gwaggo na zaune a gidana cikin rufin asiri kaje ka d’auko ta wallahi idan har wani Abu ya sameta sai na baku mamaki daga Kai har wanan tsinaniyar “

Sule ya cika rigar Habun yayi waje dan Habun bai iya magana ba,bai san mai yake damunsa ba, hankalinsa a tashe yake da halin da Gwaggo ke ciki amma ji yake kamar  zai mutu idan ya tab’a Gwaggon.

Zinatu kuwa girgiza kai tayi tana “Kabi bayan shi kuje asibitin kafin wani Abu ya sameta ace nice tunda danginka duk sun Sako rayuwata a gaba na rasa wanan masifa ko tuntube akayi a gidanku sai ace nice”

Habu da sauri ya tadda motar yabi bayan motar su sulen.

Zinatu kuwa ta koma ciki tana addu’ar Allah yasa ma zuciyar Gwaggon ce ta buga dan ko zuciyarta bata buga ba bakin cikin da zata kunsa mata kawai zai Saka zuciyarta ya buga watarana.

Sosai take Jin wani irin farin ciki da annashuwa da komai yake tafar mata yadda take so,a yanzu hankalinta ya kwanta da ta Kara tabbatarwa da kanta Habu ya tsani Shamsiyya dan har yanzu a tsorace take da Rabon da boka yace akwai a tsakanin Habu da Shamsiyya dan ba zata iya jure ganin shamsiya da jinin habu ba dan ko ta haihu sai ta Kau da komai ta haifa,dan so take idan suka rabu ya manta da babin shamsiyar gabad’aya.

Kafin su isa asibitin Sule ya ringa tambayar shamsiya abinda ya faru da yaushe Zinatu ta dawo gidan.

Shamsiyya da dauriya kawai take saboda zazzabin dake jikinta hakoranta sai haduwa suke ta hau labartawa Sule duk abinda ya faru daga lokacin da Zinatu ta dawo har zuwa yau da safe da Habun ya nemi taje ta yiwa Zinatu aiki da silar haka Gwaggo ta yanke jiki ta fadi.

Cikin kuka ta Kara da “Wallahi ba zan iya cigaba da zama da Baban Amjad ba Yaya Sule dan Allah ku sa ya bani takarda ta,dan ba zan iya ba”

Sule bai ce komai ba dan dama yasan za’a kai ga haka ba abinda bai yi dan gwaggo kar ta hada auren Habu da Shamsiyya ba ta dage,har gobe hankalin Hanne ya kasa kwanciya dan kusan kullum sai ta masa maganar Shamsiya akan hankalin ta ya kasa kwanciya gani take Zinatu zata iya cutar da ita dan tasan ba zata bar shamsiyar haka ba.

Bai ko Kalli Habu daya coge daga nesa ba aka shigar da Gwaggo, alwashi kawai yake Sha idan har wani Abu ya samu Gwaggo sai ya bawa Habu mamaki sai dai yasa a Kara d’aure shi .

Ba a kai Kuma ga fitowa ba yaga Habun ya juya yayi tafiyar sa alamar bai ma damu da halin da Gwaggon ke ciki ba.

Halin da yaga Shamsiya aciki yasa itama ya nemi a dubata inda itama aka bata gadon har da Karin ruwa.

Tunda Gwaggo ta farfado bata yi magana ba sai hawaye kawai da take zubarwa,shamsiya kawai ta tambaya akace mata itama tana kwance an sa mata  ruwa.

Tayi mamakin ganin ibrahim da Shima zuwa kawai yayi dan ya dubata isowarsa kenan Hanne ke sanar masa Gwaggo na asibiti dan Sule ya koma gida ya sanar mata halin da ake ciki,girki take dan ta kai Asibtin hankalinta duk a tashe sai ga Yaya Ibrahim nan yazo Shima.

Sule ne ya sanar da ibrahim duk abinda ya faru da ya tambaya shi silar rashin lafiyar Gwaggon

Yaya Ibrahim kuwa ya rufe sule da fada akan Mai ma ya Kai shi barin Habun ya tafi da Gwaggo dole ne sai sunyi muamalla da Habun da ya zabi matarsa akansu.

Fada kawai yake Yana Jiran Gwaggo ta farfado dan da alama sai ya karya Habu ya karya Zinatu dan tunda Habu ya kulle Sule ya Sha alwashin rabuwa dashi dan yana da balain zuciya.

Baya so ya dagawa Gwaggo hankali shi yasa ya taushi zuciyarsa har sai da aka sallame su har shamsiya suka nufi gidan Sulen gabad’aya Gwaggo kuwa sai share hawaye take,dan ita kadai tasan ciwon da zuciyarta ke Mata da abinda Zinatun tayi wa Habu,sai da ta fara murna Habu ya dawo hanya yanzu ya gane gaskiya Zinatu ta Kara juyar masa da kwakwalwa yanzu ba abinda yake mata ciwo sama da biyayyar ma da yake mata da yanzu baya  iya mata ko a baya Yana dan shakkarta Amma a yanzu bata ga alamar ma yana shakkarta ba dan bata kawo ba zai rama Marin da ta masa ba dazu, shamsiya da ke d’auke da  Karamin ciki kawai take tausayi dan a wanan gabar kulawar Habun take bukata,sai gashi Zinatu ta shiga ta fita ya tsani ma ganin shamsiyar.

Yaya Ibrahim da Sule ne suka tsaya a kanta taci abinci ta sha magani sosai take Jin wani irin ciwo a kirjinta dan ko numfashi take ji sai taji kamar ciwon karuwa yake,ba zata so ta mutu a yanzu da Habu ya koma hannun Zinatu tana juya shi kamar danta ba,tasan da wuya ma idan shine ya kawota asibitin wanan Tunanin da ya fado mata yasa ta Kalli sule ta jefa masa tambayar waye ya kaita asibiti.

Sule ne ya fada mata yadda aka yi ya ganta a kwance a kasa ya Kara da “Banda Allah ya taimaka naje Gwaggo da kila sai dai mu rasa ki dan ban ga alamar wani tashin hankali a tare dashi ba, Gwaggo Habu fa ya riga da yayi Nisa dan Allah ki rabu dashi kar bakin cikinsa ya sa mu rasaki kinsan tafiyar sa yayi ma bai tsaya yaga halin da kike ciki ba bai fa damu ba balle hankalinsa ya tashi

Yaya Ibrahim kuwa shi ma ya Kara da “Dolene sai anyi mu’amalla dashi Wanda bai san darajarki ba bai san darajar Yan uwansa ba ya fifita matarsa akan kowa  Gwaggo ki hakura ki sallama shi  dan idan shi baya sonki mu muna sanki mun San darajarki Dan Allah ki rabu dashi

“Ba yin Kansa bane wallahi juyar masa da Kai zinatu tayi”

“Wallahi ba wani juyar masa da Kai da tayi tsabar iskanci ne dan asiri ma ai Yana tada hali,Dan Allah Gwaggo ki rabu da Habu ki Zuba masa ido ki daina dagawa kanki hankali a akansa”

Cewar Yaya Ibrahim da yake mugun Jin haushin Habun da bai ko yarda asiri aka yiwa Habun ba dan gani yake tunda dai ya zama Mai kudi ya zama Dan iskan Kansa.

“Habu Yana cikin halaka sai dai nayi addu’a Allah ya Kubuto min dashi yanzu ni tashin hankalina Shamsiyyar dake d’auke da Karamin cikin da bai ma san tana dashi ba,tashin hankalina yanzu Mai zan fadawa iyayen Hanne da suka tsoraci bawa Habu aurenta,yanzu ko ganin shamsiyar baya so yayi,bana Jin akwai abinda zan iya fada masa da zai Saka yamin biyayya, Zinatu tasa dan biyayar da yake min yanzu baya iya min ballantana na tilasta masa kamawa shamsiya wani gidan wallahi yanzu wanan shine babban damuwata”

“Gwaggo dan dai bana gari ne bani da labarine kika hada wanan auren amma da Wallahi ba zan tab’a bari a d’auki kanwar Hanne a bawa habu da bashi da mutunci ba,kema idan kina san shamsiya dole ki Mata murnar rabuwa da Habun da sai yadda aka yi dashi nidai idan ta haihu ya sauwake mata kawai idan ba haka ba cutar da ita kawai zasu yi”

Gwaggo yadda suka sakota a gaba akan ta rabu da Habun yasa ta ja bakinta kawai tayi shiru dan ta san ba zasu gane ba amma tausayin Habun kawai take.

A Daren ranar haka ta kwana tana addu’a a dakin da take kwana suka kwana da shamsiya da taci kukanta ta gode Allah dan bama tasan tana da ciki ba sai da aka dubata yau har ga Allah bata so samun cikin ba dan ba abinda zai saka ta tab’a komawa habu tunda har Yana tare da Zinatun da take balain tsoranta.

Yaya ibrahim yaso tafiya da Gwaggo dan so yake ya tafi da ita ya mantar da ita damuwar da take ciki da suka san shi yake sa mata hawan jini,bai fadawa kowa ba yaje har gidan Habu ya Sha maruka biyu a hannunsa, dan yaso ya masa mugun duka ya tsere, Zinatu kuwa kulle k’ofar dakinta tayi bayan takalminsa ya sauka a gadon bayanta,yaso ya canja mata kamani idan yaso Habun idan shi din dan Halak ne yasa a kulle shi,dan kasa hakuri yayi da yaga har an kwana biyu habu bai tako yazo ya duba Gwaggo ba.

Ya kasa yarda wai asiri aka masa gani yake tsabar Isa da wulakanci yasa yake san nunawa Gwaggo bata kai yaje ya dubata ba.

Duk yadda yaso Gwaggo ta bi shi dagewa tayi ba inda zata je zata zauna a gidan Sulen a babu yadda zaiyi ya tafi bayan ya Roki sule akan idan wani abu ya taso ya kira shi ya sanar masa.

Gwaggo kuwa rashin zuwan Habu ya daga mata hankali dan ta tabbtar da ba Karamin aiki Zinatu tayi a Kansa ba,dan ko a baya idan ka d’auke rowar da Habun ke dashi yana matukar Yi mata biyayya Yana kuma shakkar ta.

Ta mugun tsorata da Zinatun da ayanzu tasan ta wuce duk inda take tunani idan har ba so take ta sabauta shamsiya ba gwara kawai ta sa habu ya saki shamsiya dan har ta fara Shirin zuwa gidan da kanta dan ta masa magana akan ma cikin da shamsiya ke d’auke dashi kila ko dan cikin ya samawa shamsiya wani gidan.

Sai Kuma ta fasa dan idan har Zinatu ta gano Shamsiyya na d’auke da ciki zata iya ma Yi mata wani mugun abun b’oyewar yafi.

A haka Hanne ta ringa kula da shamsiya dan gwaggo ta hana Shamsiyyar komawa gidansu.

Zinatu

  Tunda take Taron suna bata tab’a Taron da Habu ya kashe kudi kamar bai san zafinsu ba irin wanan,kafin ma tace tana san Abu jiki na rawa yake mata.

A yanzu juya shi kawai take San ranta baya ko yi mata maganar Gwaggo ballantana wata shamsiya Yaya ibrahim yanzu take so ta Kai sunansa ayi mata maganin shi dan ta lura yanzu shine zai kawo mata matsala.

Yanzu so take idan an kwana biyu tasa Habun ya kaiwa Shamsiyya takardata dan bazata tab’a yarda a dawo da ita ballantana har tazo ta samu rabo da Habu ba.

Gwaggo kuwa sosai ta dage da addu’a Babu dare Babu Rana,akan Allah ya karya abinda Zinatu tayi wa Habun,damuwar da ta Saka a ranta yasa jininta ya ringa wani irin hawa tana rashin lafiya da baa kwana biyu baa kwantar da ita a asibiti ba.

Sule kuwa Yana iya k’ok’arin sa wajen fita ya nemi abinda zasu ci duk da kafarsa dake Hana shi yin aikin da ya kamata dan idan ya motsa masa ma baya ma iya taka kafar.

Rufin asirinsa Allah rufin asirinsa Ameera dake SS 2 yanzu da dinki da kunshi ke shigo mata da kudin da kusan shine rufin asirinsu yanzu.

Dinki da kunshin da take bai hana ta Maida hankali wajen karatu ba,duk da har lokacin Zinatu nasa sultana ta matsawa Ameeran ba irin abinda bata yi dan kawai a Kori Ameera daga makarantar amma Abu ya gaggara dan Ameera Kara daukaka take dan yanzu kaf makarantar Babu kamar ta.

Amjad kuwa tamkar dan gidansu Ameeran dan duk abinda ake bai tab’a d’auke kafarsa daga gidansu Ameera da suke wani irin shakuwa da ita ba,a ya tsani abinda Zinatu da Habun ke yi dan Yana da wayon da yake gane duk abinda ke faruwa shi yake yawan ma bawa Gwaggo hakuri akan abinda Habun ke musu.

Dan duk kwanciyar da Gwaggo keyi Habu bai tab’a zuwa ya duba ta ba duk da Yana sanar masa da halin da ake ciki.

Tun Hanne na kirga watani akan cikin Shamsiya har sai da ta koma kirga sati zuwa kwananki,har ga Allah taso a sanar da Habu cikin da shamsiya ke d’auke dashi,dan tana tsoron ma ya nuna ba cikinsa bane tunda bai ma san da cikin ba kadan da aikin Zinatu ta zuga shi yak’i karbar cikin, Amma Gwaggo haka ta dage kar a sanar da Habu tana d’auke da ciki.

A dan kudin da take tarawa ta siyawa shamsiya dan abinda ba za’a rasa ba sule duk da ba shi da kudi sai da yayi iya nashi k’ok’arin

A haka wata rana daren laraba Shamsiya ta haifo yarta katotuwa ba ta inda ta bar Habu.

A gida ta haihu dan tun kafin ma su Nemo Mai mota ta haihu.

Habu

   Habu a firgice ya tashi daga bacci ya hau waige waigen dakin Yaga Zinatu ce a kwance a gefensa sai Samha dake gadonta dage gefen gadonsu.

Fuskar Zinatu kawai yake Kallo Yana tuno Shamsiya da yayi mafarki da ita a yanzu

Gwaggo da ya gani cikin kuka tana Mika masa abu ya matukar daga masa hankali.

Kamar wanda ya farka daga bacci haka yaji gani yake kamar dai duk abinda ke faruwa dashi mafarki ne.

Jiki na rawa ya mik’e yayi waje dan karfe wajen  uku ne na dare.

Dakin da sule ya zauna ya nufa Yana ganin kamar zai ga gwaggo a ciki da Shamsiyyar.

Kasan zuciyarsa Kuma Yana ta tunanin kamar dai mafarki yake da sun bar gidan.

Ganin bai gansu ba yasa bai tsaya bata lokaci ba ya koma ciki ya d’auko mukullin motarsa ya tayar ya nufi gidan gwaggon Yana Jin idan bai ga Gwaggo ko shamsiya ba zai iya zaucewan ganin komai yake tamkar a mafarki.

Yana barin gidan Zinatu itama ta mik’e a gigice tana hada gumi da ta tuna mafarkin da tayi wai Shamsiyya ta haihu.

Maganar bokan da ya dawo mata yasa ta mik’ewa da tsaye ba shiri

“Idan har kishiyarki ta samu ciki a duk ranar da ta haihu ta zubar da jini toh a ranar mijinki zai dawo hayyacinsa,dan haka sai kiyi k’ok’ari wajen ganin kin zubar da cikin dan kar ya dawo hayyacinsa….

*Page 20*

      Zinatu haka kawai taji hankalinta ya kasa kwanciya da mafarkin da tayi,tunda ta dawo ma bata sa Zinatu a idonta ba ballantana har ta tabbatar tana da ciki ko Babu,tana tsoron mafarkin da tayi ya tabbata.

Rashin ganin Habu a dakin yasa ta fito waje haka kawaii ta tsinci kanta da faduwar gaba idan ta tuna mafarkin da tayi dan komai na iya faruwa idan har da ciki shamsiya ta bar gidan toh yaci ta haifi cikin jikinta.

Ba inda bata duba ba amma bata ga Habu ba sai da ta ga wajen da yake parking taga Babu motarsa ta tabbatar wa da kanta baya gidan.

Mallakar da ta mi shi a yanzu komai zai yi sanar mata kawai yake ko kudi zai samu sai ya fada mata tayi matukar mamaki da ya fita batare da ya gaya mata ba.

Sai tunanin take Ina zaije da tsakar Daren da ya kasa bari gari ya waye.

Haka ta koma ciki ta hau safa da Marwa a tsakiyar palonta dan sai a yanzu tasan tayi sake wajen sakin jikinta batare da ta sake komawa boka ya duba mata halin da Shamsiyya ke ciki.

gari na wayewa zata d’auki hanyar wajen bokan dan bata ga ta zama ba wanan mafarkin da tayi yayi matukar daga mata hankali.

Habu

     Duk da dare ne haka ya ringa buga k’ofar gidan Sule da k’arfi dan haka kawai yake Jin kamar ya kwashi shekaru bai ga Gwaggon ba, Gwaggon ma tafi tsaya masa a zuciyasa akan Shamsiyya,ya dai kasa hada tunanin sa waje daya dan ya kasa tuna ma yadda aka yi ya dawo da Zinatun da ganin da ya mata tana bacci ya tuna masa da zagin da tayi wa Gwaggo

Hanne na dakin Gwaggo dasu sule a lokacin Gwaggo na rungume da jariryar da shamsiya ta haifa hawaye kawai take tun lokacin da Hanne ta yanke mata Cibiya ta gyara ta ta Miko mata ita.

Shamsiyya kuwa baccin wahala ne yayi awon gaba da ita.

Maganar da sule ke yi yasa Gwaggo saurin girgiza masa kai ” Bana so a tab’a fada masa Shamsiyya ta haihu sule, Zinatu matar Habu ta wuce duk inda muke tunani matsawar Habu yaji labarin Shamsiya ta haihu toh sai Zinatu taji labari dan juya shi kawai take a Kuma karantar da nayi wa Zinatun idan har za ta iya rabani da Habu banga abinda zai hana ta  raba shamsiya ma da duniyar gabad’aya ba dan na lura bata so wani ya rabi Habu balle wai har ace Shamsiyya ta haihu dashi”

“Gwaggo ni banga amfanin b’oye masa Shamsiyya ta haihu ba karki manta fa yarsa ce duk dai juyar masa da Kai da Zinatu tayi bai Isa yace bai san shamsiya ba taya zaa b’oye masa haihuwar da Shamsiyya tayi a gaba idan aka fada masa ya haihu da shamsiya yace karyane fa?wacce Zinatu da za’a na tsoron ta haka?Mai ta isa tayi Gwaggo,wallahi ba abinda za ta iya yi Gwaggo a ganina gwara dai yasan Shamsiya ta haihu ki bari gobe a tura a fada masa”

Gwaggo na k’ok’arin magana suka ji ana buga k’ofar da har sai da Shamsiyya ta bud’e idonta saboda bugun da ake wa k’ofar da k’arfi

Duk da sule ya tsorata haka ya mik’e ya d’auki cocilan mai haske yayi waje Yana waye

Hanne kuwa biyo shi tayi a baya tana kar ya bud’e muryar Habun da suka ji Yana shine yasa suka tsaya cak Sule ya zubawa Hanne ido dan sai yaji kamar dai muryar Habun

Hanne kuwa tayi kasa da murya tana “kamar muryar Yaya Habu”

Cikin mamaki sule shi ma yayi kasa da murya Yana mai Habu zai zo nema a gidansa uwar haka.

Dakin da gwaggo suke ya koma shi da Hanne da sauri har lokacin buga k’ofar Habu kawai yake da k’arfi

“Gwaggo kamar Habu ne yazo gidan nan fa mai yazo nema daddaren nan”?

Sule yace a lokacin da ya koma daki

Gwaggo kasa magana tayi ta zubawa Sule ido dan ta kasa yarda wai Habu ne ya taka kafarsa yazo gidan

Taya ma Habu zai zo tasan ba abinda zai kawo shi

“Ba Habu bane ba Ina ga kunnenka ne ya juyo ma muryarsa mai Habu zai zo nema a yanzu”

“Wallahi shine Gwaggo kinji muryarsa can Yana kwallawa Abban Ameera kira”

Shamsiyya mik’ewa tayi da sauri duk da bata da kwari ta karbi Jaririyarta daga hannun Gwaggo tana “Dan Allah dan Annabi karku fada masa na haihu tunda har yazo gidanan Gwaggo dan Allah ki taimaka kisa ya bani takarda ta dan wallahi ba zan tab’a komawa gidansa ba”

“Gwaggo duk da bamu san mai ya kawo shi ba dan Allah kisa ya saki Shamsiya tunda har Allah ya sauketa lafiya ya saketa kawai dan zamanta da Zinatu ba zai tab’a yuwa ba cutar da ita zata yi gwara kawai ta hakura da Auren

Cewar Hanne da dama burinta Shamsiya ta haihu a samu Mai zuwa wajen Habun ya karbawa Shamsiya takardata

“Gwaggo ba ta iya magana ba dan gani take ma kamar ba Habun ne yazo ba ta cire rai da zuwansa ballantana wai har ta sa rai da zai Kara waiwayarsu addu’a kawai take akan Allah yasa  abinda Zinatun ta masa ya  sake shi da wuri kafin  ta koma Allah.

Sule kuwa fuska a hade yayi waje yana bud’ewa Habu ya fara masifa Yana “Wane irin bacci kuke haka nakusa awa daya Ina kwankwasa k’ofa”?

“Mallam lafiya kazo min gida da tsakar Daren nan kana kwankwasa min k’ofa”

“Wajen Gwaggo nazo Sule ka bani hanya na wuce karka manta fa ni yayanka ne wai abu baya wucewa a wajenka ne”?

“Gwaggo bata san ganinka Yaya Habu Gwaggo ta sallamawa Zinatu daka fifita akanta saboda Kai ba zamu bari mu rasa Gwaggo ba,dan ba Kai kadai ta haifa ba, Gwaggo na zamanta a gidana cikin rufin asiri kazo ka d’auke ta kaje ka wulakanta ta banda naje gidanka a ranar kila da gawan Gwaggo zaa d’auko,da kana da kunya ma wallahi ba zaka iya zuwa ma kace kana san ganin gwaggo bayan duk abinda ka mata ba,aka kwantar da ita a asibiti ai tafiyarka kayi,ta gama jinyarta ka waiwayeta?tunda har akan wanan tsinaniyar da ba zata gama da duniya lafiya kake wulakanta Gwaggo, Gwaggo tace Ka koma can ta zama komai naka”

“Taya na wulakanta Gwaggo,dama Gwaggo bata da Lafiya ni Bangane Mai kake fada ba dan Allah kayi min bayani”?

Habu yace hankali a tashe dan duk ya kasa ma gane inda zancen Sule ya dosa

Sule kuwa yaja tsaki ya fara k’ok’arin rufe k’ofar Habu ya rike hannunsa Yana magiyar ya barshi ya shiga wajen Gwaggo

Sule kuwa ya dage akan Gwaggo tace ta yafe shi bata san ganinsa

Yadda ya dage sai ya shiga gidan yasa Gwaggo ta nemi fitowa dan tausayin Habun taji ya rufeta tasan duk abinda yayi baa hayyacinsa yayi ba,Hanne kuwa ta hanata fitowa tana kar taje gwara a nunawa Habu kuskurensa

Sule kuwa sai da ya hada da ture Habu da k’arfi ya kulle k’ofar.

Habu kuwa rai a balain bace ya koma cikin motarsa ya dauki hanyar gidansa

Gudu kawai yake da motar kamar zai tashi sama,maganganun Sule sai dawo masa yake,duk gani yake a mafarki yaga Gwaggo ta zube ya kuma kasa taimaka mata,duk Abubuwan da ya faru gani yake mafarkinsu yayi,har a yanzu bai san yadda aka yi ma ya dawo da Zinatu dakinta da sai yake Jin ma kamar a yanzu ta aunawa Gwaggo zagi.

Ko parking din kirki baiyi ba ya fito daga motarsa a fusace a lokacin da ya Isa gida.

A lokacin Zinatu na zaune a Palo tana dan gyangyadi dan jira kawai take Habun ya dawo ya fada mata inda yace da tsakar Daren nan.

A lokacin ana kiraye kirayen sallah Asuba

K’ofar palon da Habu ya hankada da k’arfi yasa ta Bude idonta a firgice Kafin ta gane mai ke faruwa sai saukar Mari taji da ya d’auke mata jinta na Yan dakika da juyawar Kai,kafin ta dawo daidai sai duka taji ko ta Ina.

Habu dukan Zinatu kawai yake Yana kwallo da ita dan ko ba’a fada masa ba yasan ita ta juyar masa da kai dan a hayyacinsa ma ba yanzu yaso dawo da ita ba.

Zinatu ihu take da iya karfinta dan bama zafin dukan ke sata ihu ba daga abinda ke faruwa a yanzu ta tabbatarwa kanta da shamsiya ta haihu shiyasa Habu ya dawo hayyacinsa.

Ihun bakin ciki da Tashin hankali kawai take kalmar da ya fito daga bakin Habun yasa taji duhu a gilma ma ta “Ba zan iya cigaba da zama da matar da zata Kaini ga halaka ba,bani da sama da Gwaggo a rayuwata zan iya canja ki sau dubu ban canja Gwaggo ba,ban tab’a Jin inda so yayi ajalin mutum ba Zinatu na yanke ragowar igiyar auren dake tsakanin mu na sake ki saki daya zamana dake ba alheri bane ba,a zaman da nayi dake ban taba ganin alherin da kika yiwa Mahaifiyata ba,a rayuwarki baki taba yabon wani nawa ba sai dai ki Yi duk yadda zakiyi dan kiga kin rabamu baki San darajar Yan uwana ba, amma ke so kike na kare rayuwata a bauta miki da danginki Zinatu ki shiga ciki ki kwashe duka kayanki dan bana so naga wani Abu naki a cikin gidanan”

Wani irin wawan ihuu Zinatu ta ringa saki tana “Saki uku kenan fa kamin Habu yanzu Babu Aure a tsakanina da Kai bayan yarana biyar da Kai”

Habu ko kallonta baiyi ba ya shige dakinta ya hau watso mata da kayanta waje.

Su Amrah na fitowa ya daka musu wani mugun tsawan da ya sa suka koma ciki ba shiri.

Haka ya watso kayan Zinatun waje har sai da yaji ciwo a garin watso da kayanta bai kuma ji yayi nadamar sakin da ya mata ba,sai ihu take tana birgima dan bata kawo ko asirin ya karye zai iya sakinta ba.

Taya ta saki jiki haka,yanzu duk burinta da mafarkinta na zama da Habu har karshen rayuwarta ya bi iska kenan tana ji tana gani sai dai ta zo ganin yayanta.

Ko ta kan kayanta bata bi ba duk yadda taso tafiya da samha hanata yayi ya rufe k’ofar gidan.

Kamar mahaukaciya haka ta d’auki hanyar kauyen da bokan yake duk da tasan ba abunda zai iya mata a yanzu tunda babu Aure a tsakanin su amma gani take idan taje wajensa zata samu mafita,dan ko Mai za’ayi sai ta dawo gidan Habu da k’arfinta bata ga ma Wanda zata iya rayuwa dashi ta samu duk abinda ranta Ke so sama da Habu ba.

A yanzu ba mai fada mata cewar ba Abunda su gwaggo suka Yi wa Habu ya tsaneta dan ita kadai tasan san da yake mata a lokacin da bata ma fara bin mallamai ba.

Shamsiya ta mata ba zata dan bata kawo da ciki a jikinta ba,da bata yi gangancin barinsu su bar gidan ba da tayi duk abinda za tayi wajen zubar mata da cikin,sai gashi haihuwar da tayi ya karya asirin da ta yiwa Habun

Sai a yanzu take nadama da bata bi shawarar Murja an Kau da Gwaggo da shamsiya da take ganin ba ta da makiya sama dasu.

Kuka kawai take tana kallon bokan da ke ce mata sai dai taje tayi wani auren ta fito sai a sake sabon aiki mai k’arfi a kan Habun dan a yanzu idan har ba aikin akayi ba ,ko ta fito ba zai aureta ba dan da Shamsiya zai zauna da ta fara samun gurbi a zuciyarsa.

Haka ta baro wajen bokan kamar zata zauce.

Gwaggo

Hawayen dake zubo mata kawai take sharewa tana kallon Habun dake durkushe akan gwiwarsa

Sule kuwa yayi balain hade rai kamar yadda Hanne ta hade rai.

Shamsiya kuwa tana can dakin Hanne da jaririyarta a hannu dan ba abinda zai saka ta tab’a komawa Habun rabon yarinya nan ta hannunta yasa ta aure shi.

“Gwaggo wallahi na rabu da Zinatu na har abada wallahi duk abinda nayi baa cikin hayyacina nayi ba dan Allah ki yafe min wallahi na rabu da ita,dan zan iya canza ta sau dubu ban Isa canza ki ba,nima a yanzu nasan Zinatu ba mace tagari bace da zan zauna da ita a yanzu nasan bata da burin daya wuce ta raba ni da kowa.

“Habu ka hadu da shaidaniyar mata bansan mai yasa naji tsoron rabuwar da kayi da ita ba, Ina tsoron abinda zai je ya dawo dan duk da ka rabu da ita babu Aure a tsakanin ku nasan ba zata barka haka ba,ka dage da addu’a Habu ba iya kudi zaka dage da nema ba”

Gyada Kai Habu ya ringa yi Yana zai dage da addu’a ya Kara jefo.maganar shamsiya da yaga Gwaggo nata kaucewa dan a yanzu gani yake itace matar da zai zauna da ita ta kular masa da Yayansa su samu tarbiyyar da ya kamata.

“Sai dai ka samo wata matar ka Aura Habu Shamsiya tace Ka sauwake mata tayi min biyayya wajen karbar aurenka duk da bata sonka amma a yanzu tunda ta nemi rabuwa da Kai ba zan iya tilasta mata ba”

“Dan Allah gwaggo ki bata hakuri yanzu idan dan Zinatu take tsoron komawa dakinta ai na rabu da ita a yanzu ba Abunda zai daga mata hankali”

“A gaskiya kayi hakuri Yaya Habu ka saki shamsiya dan tace ko ka rabu da Zinatu ita bata san dawowa gidanka dama rabone yasa ka aureta”

Hanne tayi subutar baki dan Shamsiyya rokonsu tayi akan ita bata so yasan ma ta haihu haka kawai take ganin zaa iya cutar da jaririyar ta,zuciyarta ma ta bar gidan Habun bata san koma masa

Habu ido ya waro Yana kallon Hanne da ta Kau da kanta tana sallati kasa kasa dan sai a lokacin ta gane tayi subutar baki

Gwaggo ya kalla da sauri Yana “Shamsiyya cikine da ita? haihuwa tayi”?

Gwaggo bata iya magana ba dan ita dai an sakata a tsakiya har ga Allah bata san matsawa Shamsiyya ne amma zata so ta komawa Habu dan ita kadai ta dace da rayuwarsa amma taga tun jiya tana kuka akan ita ba zata tab’a koma masa ba

Kukan jaririyar da ya karade gidan ya bawa Habu amsar tambayarsa

Ba zai iya fadan abinda yake ji a zuciyarsa ba ya mik’e ya fita ta ya nufi dakin Hanne da yake Jiyo muryar jaririyar ya daga labulen dakin ya hango Shamsiya a gefen gadon Hanne tana jijjiga jarirya da take ta k’ok’arin sata tayi shiru.

A gaban Shamsiyya ya zube Yana “Yanzu so kike ki b’oye min haihuwar da kika yi shamsiya”

Shamsiyya kuka ta saka masa Habu kuwa ya hau bata baki Yana rantsuwar bai san ma ya juya mata baya ba ta yafe masa ai yanzu ya rabu da Zinatu.

Shamsiyya kuwa ta dage akan ita ya saketa ba zata koma masa ba

Sai ga Habu har a gaban iyayen Shamsiya yana roko da magiya akan  su taimaka masa suyi wa shamsiya magana ta dawo dakinta,amma Suma duk inda suka kai ga bawa Shamsiyya baki haka ta dage akan ba zata koma ba.

Haka kawai take cikin tsananin tsoro sai take Jin idan ta koma gidan Habun kamar mutuwa za tayi.

Yadda iyayenta suka sakota a gaba yasa ta komawa Habun da sai da ya kaita wani gidan dan dagewa tayi ba zata koma gidan da Zinatu ta zauna ba tunda aka fara mata maganar komawa gidan ta rabu da nutsuwar zuciya.

Haka Habu ya ringa iya k’ok’arinsa dan yaga ya faranta mata.

Bai maida ma yaran Zinatu gidan shamsiya ba duka ya kwashe su ya kaiwa Gwaggo su dan wani gidan ya Kai Gwaggo dak’yar sule da Ibrahim suka bar shi ya d’auki gwgagon da ya samowa Yan aiki har biyu duk baya so ya takura shamsiya da yaran dan yanzu lallabata yake.

Sunan gwgago ya sawa Yar shamsiya da yake balain Santa a ransa yake Jin ma duk yaransa ba wacce yake Jin kaunarta bayan Amjad sama da ita imtihal ake kiranta a lokacin Samha nada shekara biyu.

Haka Shamsiya ta hade su biyun ta rike su duk Kuma abun nan ta kasa samun kwanciyar hankali sai da ta ga sun doshi shekara guda ta dan fara samun nutsuwa.

Zinatu

      Tana gama idda ta samo wani Auwal a cikin manemanta na baya da bata San ma ya yaji labarin aurenta ya mutu ba ya dawo mata duk abinda ke faruwa tana da labari game da gidansu Habun.

Tana ganin yaranta a makaranta dan can take zuwa ta gansu ita kadai tasan wutar dake cin zuciyarta da mugun shirrin da take yi a kasa.

Dan kullum a tafe take wajen bokanta.

Auren kawai take so tayi ya fito ta aiwatar da munanan kudurinta

Wata biyu da gama iddanta aka daura aurenta da Auwal da ta hada da masa asiri dan burinta kawai tayi ta fito ta koma gidan Habun.

Dak’yar ta bi shawarar boka wajen zama da Auwal din na wata biyu,kafin ta fara rura masa wuta akan ya saketa.

Auwal kuwa da ya gano da wata manufar ta aure shi ya dage ba zai saketa ba.

Haka suka ringa bugawa duk da jefa masa asirin da ta ke sai da suka tafi shekara dashi kafin ta samu nassara da aikin ta kama shi ya saketa saki daya.

Ji take kamar zata taka rawa saboda tsananin murna a irin wanan lokacin su sultana suka fara shirye shiryen gama secondary school

Sosai take iya k’ok’arin ta wajen ganin an karamma sultana itama dan idan har za’ayi bikin fitar dalibai ba Karamin taro ake yi ba a makarantar tana Kuma so tayi amfani da wanan damar wajen ganin Habun dan tasan dole zai je idan har ta hada ido dashi tasan ba zai Kara samun nutsuwa ba sai ya dawo gareta a haukace wanan karon ba zata tsaya Sanya ba.

Sosai ta kashe kudi wajen siye mallamin da zai fitar da sakamakon result din su Sultana,ta sa ya bawa Sultana na daya a d’auki result din sultana a bawa Ameera.

Ita kadai tasan bakin cikin da take ciki na kasa raba Amjad da gidansu Ameeran da shi bama a gidans Gwaggon yake ba Yana gidansu Ameera su debate da sauransu duk shi ya ringa karawa Ameera haske saboda kawai tayi nassara.

A ranar da zaa yaye daliban haka makarantar ta cika fal iyayen daliban sun hallara gabadaya tana daga gidan gaba a zaune taci ado sosai dan tana da kyan jiki ba mai yadda ta ajiye irinsu Amjad.

Wurga ido kawai take tana san taga ta inda zata hango Habun.

Sai da ta cire rai da ma zai zo taga yazo cikin shigar manyan kaya kana ganinsa kaga kudi da kwanciyar hankali sun zauna masa,har wani tumbi ya ajiye.

Zinatu wani iirin kishi ne ya rufeta,da taga yadda ya murmure alamar ma yana Jin dadin zama da shamsiya.

Girgiza kai kawai tayi Dan ita kadai tasan shirin da tayi.

Haka aka cigaba da gudanar da Shirin kamar yadda ta kawo wa ranta haka aka fara Kiran sunan Ameeran ana zabga mata kyauta ji take kamar zata mutu dan bakin ciki,kyautar na dalibar da tafi kowace kwazo,tsafta  girmamawa kyauta har da ta banza sai da aka zo kan results ta gyara zamanta dan tasan yanzu itama zaa kira Sultana tana ganin yadda habu ke ta tafawa Ameera kamar wata yarsa.

Duk da ba waje daya suka zauna da Sule ba tana hango shi acan gefe Shima Yana ta zuba murmurshi.

Amjad kuwa dagowa Ameera hannu kawai yake Yana sakin murmurshi dan yasan itace ma tayi na dayan.

Maganar da yaji wani nayi ta gefensa yaja hankalinsa ya matukar Kuma girgiza shi dan shine mallamin dake da alhakin fitar da result din Daliban.

Bai gama fahimtar Mai ke faruwa ba sai ji yayi an kira sunan Sultana Abubakar a matsayin wacce tazo ta daya Wanda ba iya Amjad din ba har sauran mallaman sai da suka girgiza makarantar ta d’auki shiru

Ameera kuwa kasa motsawa tayi sai hawaye daya hau zubo mata dan tasan cutar ta akayi

Wanda ke Kiran sunan kuwa da yake gayyatarsa aka yi ba mallamin makarantar bane ya cigaba da Kiran sunan sultana da taji ma tsoron tashi, Zinatu kuwa sai murmushi take a lokacin da sultana ta fito Habu Kansa mamaki ne ya hana shi motsawa.

Sultana kuwa tana zuwa ta Mika hannu dan ta karbi kyautar sai muryar Amjad suka ji ya ratso lasifikan akan ba sultana ce tayi na daya ba Ameera ce.

Ya dago results din da mallamin ya Yar a garin b’oyewa bai sani ba.

Zinatu kuwa ta runtse idonta da k’arfi tana sallati

Daga magana kasa kasa sai gashi an bada hakurin kuskuren da aka samu wajen fadar sunan aka fake da haka aka kira Ameera aka bata kyautar ta.

Tsannain bakin ciki yasa Zinatu barin makarantar bama ta tsaya ganin Habun da ta so su hada ido  ta samu cikar burinta ba.

Fadar tsanar da tayiwa sule gwaggo shamsiya bata bakine a yanzu ne zata aiwatar da shirinta da gaggawa dan ta matsu ta koma gidan Habun,da tasan yasan aurenta ya mutu ta kyarawa yaranta su fada masa Kuma sun fada din bai ko nuna alamun ya damu ba.

Shamsiyya

     Murmurshi kawai take a lokacin da Habun ya sake dawowa Yana “Wai ni ba Zaki rakani bane”?

“Nafa ce a dawo lafiya wallahi kafata ciwo take min”

“Karasowa yayi kan kujeran da take zaune Yana “Anya ba cikin Yan biyune dake ba”?

“Toh waya sani ne cikin dai nauyi gare shi kila ma mutuwa zanyi idan nazo haihuwa”

Toshe mata baki yayi da sauri Yana “ba zaki mutu ba Shamsiya ba yanzu Zaki mutu ba sai kin yi imtihal kanne har Sha biyu”

Murmurshi tayi tana “Toh mutuwa dai bata sallama a dai yafi juna idan rai yayi halinsa”

“Wallahi zamuyi fada dake bana so kina Kiran mutuwar nan”

Murmurshi ta sake saki bata ce komai ba sai ya fita sai ya dawo har sai da ta tashi dak’yar ta raka shi gate sai da ya tafi ta dawo ciki ta shiga dakin su imitihal da Samha,haka kawai taji hawaye na zubo mata ta hau yiwa imithal addu’a tana shafa kanta  bata san mai yasa yau take Jin wani iri ba.

Itama Samhan shafa kanta tayi dan sosai take Jin Yar a zuciyarta duk bacci suke ta fito daga dakin ta shiga dakinta ta kwanta ta rufe idonta ta hau kirga yatsunta.

Bugun da aka yiwa k’ofar yasa ta Bude idonta ta mik’e dak’yar.

Tana fitowa taji ihuuh daga waje ana gobara gobara

Jiki na rawa ta fito harabar gidan taga Saman gidan ke ci da wuta

A guje ta koma ciki tana zuwa taga kamar an jefo abu kamar gallon kafin ta gane mai ke faruwa sai gani tayi palon ya kama da wuta

Imitihal ce kawai a ranta jikinta rawa kawai yake bakinta d’auke da sallati tana zuwa taga imitihal ce kawai a kwance babu Samha.

Bata tsaya wani dogon tunani ba ta jawo imtihal ta rungumeta tana kuka dan babu ma hanyar da zata iya fita ta palon dan ko’ina ya kama da wuta.

Kamar wacce ake bawa umarni ta nufi bandakin cikin dakin ta duba taga babu ta inda zasu iya Fita duk girman cikinta haka ta taka masan bandakin

Ta Bude Karamin window dake ta waje ta hau zura imtihal sai ihu take ji daga waje a daidai lokacin da ta ji muryar wani na “Dan Allah kuzo ku fasa window nan tunda an kasa shiga ta ciki gata tana k’ok’arin jefo yarta ta window

Yuuu taji sun Yo wajen windon ita kuwa ta cigaba da tura imtihal a daidai lokacin da wani ya hau Abu ya fara k’ok’arin fasa windon dayan Kuma ya rike imitihal da Kanta ne bai karasa fita ba.

“Bawan Allah Dan girman Allah ga amanar Yata nan ko gidan marayu ne ka kaimin ita bana so asan tana rayye ka taimaka min”

Shamsiyya tace cikin hakki mutumin kuwa ya girgiza Kansa da sauri Yana “zamu taimaka Miki in Sha Allah ba Abunda zai sameki”

Shamsiya kuwa ta sulale kasa bakinta d’auke da sallati

A daidai lokacin da habu yayi parking ya fito a haukace Yana k’ok’arin shiga gidan da yaga an datsa kwado ta waje…..

*Page 21*

        Zinatu

  Ko dar bata ji a zuciyarta ba ta saki hannun Samha da ta d’auko daga dakin da suke kwance da imitihal.

Tun jiya ta gama shirinta da taimakon wani Ayuba rikakken almajiri da tayi wa alkawarin kudi dan sai da ta Dade tana bincike kafin ta samu Wanda zai iya aiwatar Mata da shirinta cikin sauki batare da an zargeta ba.

Tun takwas tana unguwar da Shamsiyya take nesa da gidan tayi parking a wani bakar motar da arowa tayi,Ayuba duk ya fada mata shige da ficen da Habu yake yi,komai a tsare take tafiyar dashi.

Dan shi zai duba mata komai kafin ta aiwatar da shirinta.

Boka yayi iya yinsa ya kasa raba shamsiya da Habu, cikin da take d’auke dashi ya fi komai tayar mata da hankali dan matsawar Shamsiya ta haihu hakan na nufin ta samu wajen zama ba ranar rabuwarta da Habu.

A duba mata da bokanta yayi sai an Kau da Shamsiya zata iya komawa Habu.

Sanin da tayi da ba kowa a wajen Shamsiyya idan har habu ya fita yasa ta yanke yin komai da kanta.

Zuciyarta a bushe take burinta kawai ta Kau da Shamsiya da ta balain tsana dan gani take ita ta zame mata katangar da ta hanata komawa gidan Habun.

Sai da Habu ya fita da Ya fita da wajen minti talatin ta fito daga cikin motar fuskarta sanye da nikaf daidai da hannunta sai da ya Sha safa da kafa.

Unguwar su shamsiya bata fiye mutane ba dan kamar ma ba kowa kasancewar Safiya ce dan wajen Sha daya ne da rabi.

Ta gama tsara yadda za tayi dan kwankwasa k’ofar za tayi idan shamsiya ta Bude mata sai ta hankadata ciki.

Ayuba kuwa cikin kwarewa dama ya haura ta bayan gidan da gallon din fetur biyu.

Sai dai tana zuwa sai taga kofar a Bude dan tura k’ofar kawai aka yi.

A hankali ta tura k’ofar ta shiga.

Ta hada ido da Ayuba dake labe ta baya Yana lekota.

Hannu ta daga masa akan ya dakata tukunna ta shiga cikin palon,dan tasan kila taga Shamsiya a Palo tasan bata Isa ganeta ba tunda ta Saka nikaf da safar hannu da kafa.

Duk da bata San kan gidan ba haka ta hau dube dube  tana Jin sanyi a zuciyarta da komai ke zuwar mata cikin Sauki.

Daki na farko da ta duba nan ta hango Samha a kwance da intihal.

Da sauri ta shiga cikin dakin ta zubawa Samha ido da ta tafi shekara uku da rabonta da ita wajen shekara kenan da watanni.

Bata kawo komai zai zo mata cikin Sauki haka ba,dan da Shirin sumar da shamsiya tazo saboda ta samu ta aiwatar da shirinta sai taga ta saukaka mata ma bata palon.

A kafadarta ta dora Samha.

Ta hau karewa imitihal Kallo tana Jin wani irin daci daci a makoshinta dan ji tayi ta tsani imitihal da ta Saka ta ganin munin Samha.

Duk yaranta bata Jin akwai wacce ta kamo imtihal din kyau taya ma zata bar wata mace ta haifawa Habu Yara

Ta fito daga dakin cikin sanda Samha a kafadarta har lokacin

Daya dakin ta nufa a hankali k’ofar ma a Bude take hakane yasa ta dan Bud’e labulen sai ta hango shamsiya a kwance idonta a a rufe ga uban cikinta a gaba sai da gabanta ya fadi da taga cikin dan kamar cikin Yan biyu haihuwa Kuma yau ko gobe.

Sakin labulen tayi ta fito daga palon kafin ta kawo wanan matakin sai da ta dade tana shawarar hanyar da zata bi wajen Kau da shamsiya idan tace caka mata wuka za tayi kila a gaba a rafkota dan tasan ko baa zargeta ba Gwaggo da itace next target dinta na iya zargin itace,Kona shamsiyar kawai yazo ranta Wanda tana ganin idan tayi haka kowa zai d’auka gobara tayi ba ma yadda za’ayi wani ya zargeta shiyasa ta gama Shirya abinda za tayi dan kar aga Samha ce kadai ta tsira.

Jikinta har rawa yake wajen Isa wajen Ayuba da yake labe har lokacin Yana Jiran ta Bada umarni kawai

Tayi kasa da murya tana “Zan fita ta k’ofa zan datse da kwado yadda bama zata iya fitowa ko wani Yazo ceton ta ba zaka iya fita idan ka gama”

Gyada mata Kai yayi da sauri Yana zai iya fita

Ita kuwa ta juya da sauri ta nufi k’ofar har lokacin da samha a kafadarta da ta Bude idonta tana “Umma ta matse ta da k’arfi dan kar a jiyota

Sai da ta lekar da kanta taga ba kowa sai wasu su biyu da ta hango zasu wuce,sai da ta dan Jira taga sun wuce ta fito daga gidan da sauri ta datsa kwadon ta yanka tayi bayan gidan ta wajen da Ayuban zai duro.

Ayuba kuwa Yana ganin ta fita ya wurga gallon din fetur din da ya Bude Saman rufin gidan ya wurga lighter dake hannunsa da ya kunna take kuwa ya kama da wuta

Da sauri ya yo wajen palon dan daki Zinatu tace ya wurga fetur din,sai dai Yana zuwa bakin kofa ya hango shamsiya sai ya wurga galoon din da ya fetur din ya Kara binsa da lighter ganin wuta ta kama yasa yayi saurin komawa ta bayan katangar ya danne kamar wani biri dan irin siraran nan ne.

Bayan gidan ba kowa shiyasa sai da ya kwana biyu Yana zuwa unguwar dan ya ga yadda ya ke ya gane mutane basu fiye wucewa ta bayan gidan ba dan gidajen unguwar irin manyan nan kamar dai sabuwar unguwa ce.

Yana dira ya hau tafiya da sauri sai da yayi gaba sosai ya hango Zinatu a tsaye da Samha a rike a hannunta

Ganin ba kowa yasa ya Isa wajenta Yana zuwa yaga samhan nata kuka ganin rigar Samhan a kone har da gashinta da aka yiwa parking nata tururi yasa ya Kalli Zinatun dan Samhan sai Kuka take.

“ni na Kona rigarta na dan k’onna mata gashi saboda gudun zargi.

Yanzu Ina tsaye anan ka koma ta gaban gidan nasan tunda gidan naci da wuta zaa samu wayanda suka taru kayi ta ihu kana nunawa kana so ka shiga cikin gidan.

Ka nuna tsananin damuwar ka tunda ba Wanda hankalinsa yasa yayo bayan gidanan sai ka zagayo ka karbi Samha ka nuna ita kadai ka iya daukowa zan Kara Maka kudi akan Wanda na baka bana so a zargi wani Abu kaga dai har dan konata nayi.

Gyada mata Kai yayi da sauri Yana jinjina rashin imaninta dan har ta fishi dan mamaki yadda ta Kona gashin Samha da rigarta kawai take dan ta dan Kuma Kona Samhan dan fara ce hakane yasa wajen goshinta ya kwaye.

Yadda ta tsara.mi shi haka yaje yayi dan har rike shi ake da ya ringa nuna zai shiga gidan

Mutane sai ihu suke suna Anya akwai mutane a ciki dan an datse da kwado ta waje

Wani yace gaskiya da wuya idan akwai mutum

Shi kuwa ya zaga baya Yana bari ya duba

Yana zagayawa Zinatu ta saki hannun Samha batare da ta ko ji darr ba,wani irin sanyi take ji a zuciyarta da taga yaddda gidan keci da wuta dan tasan shamsiya da imtihal da cikinta  sun zama tarihi.

Da sauri ta nufi wajen da ta ajiye motar ta da isarta taja motar da sauri ta bar unguwar tana shan kwanar da zai sadata da titi ta ga Habu ya shigo layin da balain gudu.

Ta tabe bakinta tana “Sai dai kaje ka tarar da gawarta Ina nan Ina jiranka”

Ayuba kuwa a a kafada ya d’auko Samha  Yana Ihun hannunsa

Yana zagayowa ta gaban gidan akayi sauri akayi Kansa.

Aka karbi Samhan daga hannunsa,wani kuwa yayi saurin zubawa Samha ruwa akai.

Ayuba kuwa ya fara magana kamar Wanda ya Sha wahala yace dira yayi kafin ya shiga ciki yaga samhan ta fito shine ya d’aukota.

Sai a lokacin hankalin mutane ya Basu suyi bayan gidan suka duru suka yi  bayan gidan

A daidia lokacin da Habu ya karaso da labari ya isar masa kafin ya karasa kasuwa.

Yadda yaga gidan na ci da wuta yasa ya ringa Ihun Kiran sunan shamsiya Yana a taimaka masa matarsa da yaransa biyu suna ciki.

Wanda ke rike da Samha daya lura Habu ba’a hayyacinsa yake ba ya dire Samha ya tab’a shi dan ririke shi akayi Yana Ihun waye ya saka masa kwado a gidan

“An samu wani ya ceto yarka guda daya”

Habu bai ko bi ta kan Samhan da ya ajiye masa a gabansa ba ya cigaba da Ihun Kiran sunan shamsiya Yana mamakin wanda ya datsawa gidan kwado.

Yadda yaga ko’ina na gidan naci da wuta yasa ya yanke jiki ya fadi.

 Bai tashi Bud’e idonsa ba sai a asibiti

Sai da ya kwashi mintuna ya tuna abinda ya faru ya mik’e cikin Ihun Kiran sunan shamsiya

Sule da idonsa ya kada yayi jajjur ga Ibrahim  da ya gani a tsaye a Kansa ya sa ka shi kwalla wani Ihun Yana “Sule Ina shamsiyar Yaya Ibrahim Kun ceto min ita kuwa dama mutuwa za tayi shiyasa ta ringa neman yafiyata waye ya datse min gidan da kwado”?

Magana kawai yake cikin fitar hayyaci sule kuwa da ya kasa jurewa yayi waje a daidai lokacin da wata nurse tazo ta sake masa allurar bacci

Ibrahim kuwa ya rike hanunsa Yana Jin wani irin tausayinsa duk da basa shiri da shi ya girgiza da mutuwar shamsiya da imtihal.

Sule kuwa wajen da aka kwantar da Gwaggo ya nufa Yana share hawayen dake ta zubo masa.

Yau yaje kaiwa Gwaggo maganin hawan jininta,dan kwana biyu jininta na yawan hawa yadda yaga tana dan fama yasa yace Hanne taje ta zauna da ita na kwana biyu dan yanzu ba zai iya d’aukar Gwaggo ba dan su sultana duk suna wajenta a dan gaban gidansu Shamsiya gidan gwaggo yake ba wani Nisa sosai.

Yan aiki biyuu ke hidimantawa yaran Zinatun da Gwaggo ke fadan rashin tarbiyarsu.

Dan ciwon Kai kawai suke bata  tana b’oyewa ne dan kar su sule su dage akan sai sun d’auketa dan a yanzu so take Habu ya samu kwanciyar hankali da Shamsiyar,itama ba zata so a Kai su sultana gidan shamsiya su zauna ba dan ko ita rashin kunya suke mata balle Amrah da sultana haka zasu yi ta cewa itace tasa aka saki Zinatu ta aurawa babansu Shamsiya wani irin banzan huduba Zinatu tayi wa yaran su ka tsani Gwaggo akan dole ma suke zaune a gidan dan sunga ma Habun baya wasa yanzu jibgarsu yake,haka yasa Gwaggo take hakurin zama dasu,jininta na hawa a Kai akai.

Zinatu Sam bata musu tarbiyar arizki ba dan sallah ma sai tayi ta kumfar baki suke yi,Yan aikin kuwa bama su isa su Saka su ko su hana su ba,irin halin Zinatu ne dasu wajen kyama da wulakanta wanda yake kasan su.

Idan har ka ga sun nutsu toh Habu ne yazo gidan tsabar makirci suna ganin yazo zasu hau biyayyar karya.

Duk kwana biyu sule ke zuwa ya duba Gwaggon.

Ameera yaso ta zauna ma da Gwaggon amma Shirin da yaga basa yi da sultana yasa ya fasa.

A zuwan da yake yaga Gwaggo kwance ba lafiya Koda aka duba jinin nata ne ya sake hawa.

Sai ya d’auka tunani ke sata hawan jinin haka yasa ya nemo maganin nata ya kai mata wajen goma.

Yaran duk sun tafi makaranta Hanne tun jiya tana gidan tana kula da Gwaggon da ta kwana kuka da Hanne ta rasa mai ya sakata kukan amma gwaggo ta kasa fadar takamaimai abinda ya sa take kukan.

Sai da sule yazo ya tilasta mata ta fara Shan kunun gyadar da Hanne ta dama mata

Hanne kuwa ta dago ta kalli Sulen da shi ma ta zubo masa  kunun tana “Jiya kwana nayi Ina mafarki da Shamsiyya bari na karasa na dubata Gwaggo dan Allah ki sake yiwa Yaya Habu maganar haihuwar shamsiya ya barta tazo gida ta haihu tunda ita kadai ce kar haihuwar nata yazo mata cikin dare”

Gwaggo na k’ok’arin magana wani makocinsu ya fado gidan cikin ihu daya gaban gwgago faduwa taji kamar ruhinta ya bar gangar jikinta k’ofa kawai ta zubawa ido tana kallon sule daya fita a guje Yana tambayar lafiya

Gobarar da taji ance gidan Habun yayi da shamsiya a ciki yasa ta yanke jiki ta fadi.

Hanne itama da ke rike da mayafi zubewa tayi a kasa a sume.

Sule duk bai bi ta kansu ba yayi waje kafa ba takalmi

Yana zuwa yaga gidan nata ci da wuta ga mutane sun rufe Habu daya suma

Da taimakon mutane ya kinkimi Habu Gwaggo suka yi asibti Hanne kuwa tunda ya watsa mata ruwa ta farfado take rusa Ihun kuka

Tunda suke basu shiga cikin tashin hankali irin wanan ba dan gwaggo bata da maraba da mataciya ko Bud’e ido ba ta iya yi numfashi da take ne yasa kake gane tana rayye

Habu kuwaa kamar Wanda ya zauce sai da aka dage da addu’a ya fara dawowa daidai

Suna ji suna gani haka aka ringa zuwa musu gaisuwa shamsiya da bama a samu ko gawarta ba dan gidan kurmus ya Kone.

Da yawan mutane nata mamakin mai ya haddasa gobarar Habu Kuma na ta tunanin ya akayi aka kulle gidan ta waje

Zinatu kuwa tana cikin Wayanda suka ringa sintiri cikin kuka sai barka ake mata akan kubutar da Samha tayi,da yawa akace saboda itace mai tsawon Ran shiyasa wani ya samu ya ceto ta

Abinci kuwa har aka yi sadakan bakwai haka ta ringa kaiwa gidan

A yadda take yi ba Wanda zai ma iya kawo zarginta dan ita ma Samhan ta dan konata ta goshi.

Sai da aka samu sati biyu da rasuwar suna dakin da gwaggo ke kwance ba umm balle umm um ido dai a rufe.

Habu yayi zuru ya kurawa waje daya ido,shamsiya kawai yake hangowa da tulun cikinta da yayi balain kwallafawa rai,bai ma san Yana Santa ba sai da ya rasata dan ji yayi kamar bai tab’a San wata ya mace ba

Abinda kawai ya tsaya masa a zuciya kulle gidan d akayi ta waje sai yake ganin kamar  gobarar ba daga Allah bace ba a fili ya fara magana Yana “Har k’ofa ta rakoni Sule sai da ta ga tafiya ta ta koma ciki abinda har yau na kasa ganewa waye ya sawa k’ofar kwado ta waje?Mai dalilin da zai saka a kulle gidan ta waje anya ba kashe min shamsiya aka yi ba?Wanda ya ceto Samha Mai yasa bai ceto imtihal da shamsiya ba,Ina bukatar na sake bincike Ina bukatar na nemo Wanda ya ceto Samha dan wallahi na kasa samun nutsuwa a zuciyata”

“Karka wahalar da kanka Yaya Habu kila gigicewar da kayi yasa kake ganin kamar datse gidan akayi duk abinda za kayi a yanzu ba zaka iya dawo wa da shamsiya ranta ba Allah yayi ta hanyar da zata tafi kenan a yanzu ba abinda zamu cigaba da Mata sama da binta da addu’a Allah yayi lokaci guda zata tafi da imtihal,ta Ina zaka soma Neman Wanda ya kubutar da Samha Taya ma zaka yi wanan Tunanin bayan itama Samhan kaga ta dan kone a yanzu addua kawai zamu cigaba da binta dashi

A yanzu halin da Gwaggo ke ciki ya kamata mu duba

Shiru kawai Habu yayi dan shi dai yasan yaga kwado a datse a gidan.

Bayan wata uku da mutuwar shamsiya Zinatu ta hau fado masa a rai,dan tana yawan zuwa duba Gwaggo baya Jin wani komai a kanta mutuwar Shamsiya yasa yaji bama ya sha’awar komai.

Daddare haka zai ta kuka dan har ga Allah yasan yayi babban rashi.

Gwaggo kuwa ba inda basu kaita ba hakan nan take kamar mataciya ta drip ake bata abinci.

Sule da Kansa ya fara tausayin Habun aka fara masa shaawar auren Koda aka masa magana cewa yayi zai dawo da uwar yayansa kawai ta cigaba da kula da yaranta.

Duk ba a san ransu ba Habu da ke Jin kamar zai mutu idan bai maida Zinatu dakinta ba yaje suka tsayar da magana da iyayen Zinatu

Ranar wata asabar aka Maida auren Zinatu da Habu

Gidan ta aka kara gyara mata aka zuba komai sabo ta tare abinta.

Aikin da tayi akan Habu yasa ya sake dawowa tafin hannunta wanan kenan.

*******************

    Sintiri kawai Babagana keyi a tsakar gidansa ji yake kamar ya fada cikin dakin.

Fitowar Yakaka daga dakin yasa shi sauran nufarta,sai da ta masa wani kallo cikin hade rai ta fara magana tana “A yanzu tunda ta haihu sai ka fadamin mai hadinka da ita”

“Alhamdulillah alhamdulillah dan Allah ta haihu”?

“Hmmm nifa Bangane  ma ba  Aure kayi a b’oye bansani ba kome”?

“Yakaka zan fada miki komai ki bari yanzu nasan halin da take ciki ta haihu”?

“Hmm ta haihu ta haifi Yan biyu Ina jinka wacece ita”?

“Kije ciki ki gyara ita da jaririran zanje waje na samo mata wani abu idan na dawo da bakinta zata fada mana wacece ita,dan akwai boyayyen Al Amari a tare da matar nan Ina wanan yarinyar”?

“Tana dakin su husna”

“Toh bari nayi sauri naje na dawo”…

“Guess who😂

*KWKWR T KWKWR*

*Page 22*

      Babagana

“Aliyu Kai yarinya nan cikin mota tunda har kaji tace a kaita gidan marayu akwai dalilin da yasa ta fadi haka karka bari a ganta tunda hankalinsu na can gabad’aya yi sauri ka dawo na rike ka ka girgiza windon nan”

Da sauri Aliyu ya d’auki imtihal wani ikon Allah duk wayanda suka zago ta wajen window sun koma wajen Habu da ya sume wasu Kuma suna ta bayan gidan

Wucewa suka zo yi ta layin suka ga gidan naci da wuta Wanda hakan ya sa suka yi parking dan suma suyi taimako.

A bayan motar ya kwantar da imtihal da ke Shirin kuka ya koma wajen yayansa Babagana da yake ta buga wajen karfen windon dan so yake ya cire karfen

Yana zuwa Babagana ya sauko daga abinda ya taka da sauri dan sosai gidan ke ci da wuta wani irin tausayin Shamsiya ne ya rufe shi da yaga yadda ta sadakar da ma mutuwa za tayi.

Daga yadda ta roke shi a akan kai yarta gidan marayu yasan akwai wani boyayyen Al amari,ba irin tunanin da bai zo ransa ba.

Aliyu da k’arfi ya girgiza karfen sai gashi ya banbaro a daidai lokacin da wuta ya kama kwanun bandakin

Hankali a tashe Babagana ya Sake dukan bangon window dan dak’yar ta iya fitowa ta wajen batare da sun sake fasa bangon window ba,da yake irin karfafa nan ne,k’arfi yasa sosai wajen dukan bangon har Yana Jin ciwo a hannunsa

Shamsiyya

Hawaye kawai ke zubo mata tana Jan istigifari,tafi sati tana ji a jikinta mutuwa za tayi,tunda ta dawo gidan Habu bata da wani cikakken nutsuwa dan haka kawai sai take ji a jikinta Akwai wani muguntar da Zinatun zata mata dan tasan ba zata barta ba,amma an kasa gane tsoron da take ji daidaikun Rana ne bata mafarki da Zinatu nasan cutar da ita,addu’a kawai take akan Allah ya kareta daga duk wani sharrinta,dan har tashin dare take,tsufar da cikinta yayi yasa ta daina iya tashin, ba Abunda Habu ba ya mata dan kawai ya kwantar mata da hankali ya faranta mata rai,amma zaune kawai take ba wani nutsuwa a tare da ita.

Ko ba’a fada mata ba tasan Zinatu ce ta haddasa gobarar gidan tunda taga ma an d’auke Samha.

Gudun irin wanan masifar yasa da taji aurenta ya mutu ta matsawa Habu ya dawo da ita, dan  kar ma ta riketa a ranta dan babu Wanda bai san yadda take san Habu ba tasan da wuya ma idan ba kashe auren nata tayi ba sai gashi akan Habu take so ta kau da ita,addu’a kawai take Allah yasa mutanen su cika alkawari wajen b’oye mata imtihal dan tasan idan har Zinatu tasan imitihal na Rayye sai ta kasheta itama.

Ji take inama Allah ya dau ranta kafin ta fara ci da wuta,kuka kawai take idonta a rufe tana hararo azabar da zata Sha.

Dan ta inda take kwance ma wani irin zafi ya d’auka bata ma Bude idonta ba dan bata so taga yadda wutan zai kama jikinta.

Muryar da taji da “Baiwar Allah taso yi sauri wuta ta kama Saman bandakin “

Ido a rufe ta bashi amsa da “Mutuwa zanyi ko na na tsira daga wutan da ta hada min ba zata fasa kasheni ba dan Allah ka kaimin yarinya gidan marayu kar ta kashemin ita.

“Zan taimaka miki ba zaki mutu ba ki daure ki taso kinji bai kamata ki bari taci galaba a kanki ba tunda har Allah ya turo mu dan mu taimaka miki”

A hankali ta bud’e idonta duk da rawar da jikinta keyi da gabanta dake bugu fiye da misali haka ta mik’e tana Jin kamar ingizata ake

Saura kiris wutan ya kamo wajen da take

Babagana kuwa ya Kara mik’a mata hannu dan windon ya dan yi sama kadan ya samu ya fasa bangon.

Bata san ma tana da ragowar kwari a jikinta ba ta taka kan masan duk da cikin jikinta da tsinin cikin haka ta kama hannun baba gana sai a lokacin taji tana balain tsoron ma wutar ta tab’a ta,sai a lokacin taji tana addu’ar tsawon rai dan ba zata so mutuwa a yanzu ba.

Zata so ganin Abunda ke cikinta

Har danne cikinta tayi a garin durowa tana durowa ta kwanta flat a kasa tana “Bawan Allah dan girman Allah ka b’oyeni bana so asan Ina rayye nafi so a d’auka Ina ciki”

Babagana da sauri ya hau waige waige ba kowa ma ta wajen window sai dai shi da Aliyun,kamar d’auke hankalin mutane akayi daga kansu.

Dan Habu kawai aka rufu a akansa wasu Kuma nata k’ok’arin kashe wutar gidan dake ta ci kamar ana watsa petrol ta bayan gidan ma suka fi maida hankali

Aliyu kuwa yayi saurin matsawa kusa da Babagana dan yaji duk abinda Shamsiya tace “Ina ga akwai dalilin daya bata so asan tana rayyen dan danaje can gidan kulle shi akayi ta waje,da alama dai gobarar nan ba daga Allah bane wani makiyin nata ke san kasheta dan haka Ina ga muyi k’ok’ari wajen taimaka mata

“Kaine ka iya mota Aliyu yanzu hankalinsu duk baya kanmu ka dawo da motar daidai nan mu samu mu taimaka mata dan kar a ganta zan ta duba mana kar a ma ganta.

Aliyu da sauri ya juyo da kan motar sa kamar irin tafiya zasu yi

Sai daya zo daidai wajen da Babaganan ke tsaye ya bude bayan motar

Shamsiya kuwa ta rarrafa daga wajen da take kwance tana Jin jini na bin kafarta da wani azababben ciwon mara.

Ta shige bayan motar batare da wani ya ganta ba.

Babagana kuwa ya rufe k’ofar da sauri ya zaga ta daya barin yana rufe k’ofar bandakin ya kama da wuta Sosai har Yana feso wuta.

Shamsiyya kuwa sumewa tayi tana daga bayan.

Aliyu kuwa ya ja motar da balain gudu suka bar layin

Imtihal kuwa ta hau tsalla kuka.

Sai a lokacin suka gane ma sumewa tayi.

Babagana yayi saurin cewa Aliyu yayi parking din motarsa

Aliyu kuwa yayi parking da sauri.

Babagana ya zaga ta bayan ya d’auko wani ruwa da ya gani ya watsawa Shamsiyya da ta ja dogon ajiyar zuciya

Imitihal dake ta kuka ya d’auko daga bayan motar ya koma gaban motar da ita ya hau girgiza ta Yana “Aliyu matar nan tana bukatar taimako naga kamar dai ciwo taji jini nata bin kafarta mu wuce mu kaita asibiti”

“Dan Allah karku kaini asibiti ku kaini wani wajen ku b’oyeni bana so asan Ina rayye ku taimaka min”

Shamsiya tace cikin tsananin azabar da take ji ko baa fada ba tasan nakuda take dan da alama tashin hankalin da ta shiga ya tayar mata da nakuda dan dama ta shiga watan haihuwarta

Babagana kuwa yace “Aliyu maza juya mu koma gida Ina ga gida kawai ya dace yanzu mu kaita matar nan da alama rayuwrta na cikin  hatsari”

Aliyu bai ce komai ba ya juya suka nufi gidan Babagana dan sun fito ne zasu kasuwa dan shi ba mazaunin garin bane daga kasuwa zai wuce shi kuma babagana ya wuce gida.

Su suka taimaka wa shamsiya wajen fitowa dan kasa ma tafiya tayi.

Yakaka da ta kasance matar Babagana dake tsakar gida tana wanke wanke ta mik’e cikin sallati da ta ga Babagana da Aliyu na rike da shamsiya dake ta zabga sallati

“Yakaka taimaka ki kaita daki bamu sani ba ko haihuwa za tayi”

“Daga Ina kuka samo ta? Wacece ita”?

Yakaka ta hau jefa musu tambayoyin basu ko kula ta ba har sai da suka shigar da shamsiya dakin suka fito da sauri

Aliyu kuwa yace “Bana Ina bukatar zuwa kasuwar nan kar mutumin nan yazo yayi ta jirana,idan na dawo komai a ake ciki sai ka fadamin”

Kai kawai Babagana ya gyada masa Aliyu yayi waje da sauri.

Yakaka kuwa ta sake jefa masa tambayar wacce shamsiya.

“Kije ki taimaka mata Yakaka yanzu ba lokacin da zaki tsaya tambayoyi bane”

“Kodai Aure kayi bansani ba mai hadinka da matar naga har da yarinya”

Babagana na k’ok’arin magana suka Jiyo muryar shamsiya na “Ku taimaka min dan Allah haihuwa zanyi”

“Kiyi sauri Yakaka kije ki taimaka mata”

Yakaka da sauri ta shige dakin nata

Halin da ta ga shamsiya yasa ta ajiye komai a gefe dan zata ma iya haifar shamsiya.

Sallati kawai shamsiya take har sai da ta saki Nishi da k’arfi danta ya fado

Cikin Yan mintuna ta sake Jin wani ciwon ya taso mata duk abun nan ba wani scanning tayi ba balle tasan Yan biyu ne a cikinta

Tunda na biyun ya fado yakaka ta sake yanke cibiyarsa take kuka tana bin Yakaka da ido da ta zaro mata mahaifar ta goge ta ta maida kafarta ta rufe

Hamdala kawai take furtawa a fili,dan ta cire rai da rayuwa Allah ya nunawa Zinatu ikonsa yau gata da Yan biyun da Habu ya kwallafawa ransa samun da namiji ganin Yakaka ta rufe su biyun da zani yasa hawaye gudu a fuskarta dan akwati biyu Habu ya cika da kayan jarirai na Maza dan ya dage akan shi yasan namiji zata haifa Kuma idan ta haihu sunansa zai saka masa.

Yadda yake san cikin jikinta kamar bai da wasu Yaran

Ashe bashi da rabon ganin yaran balle yasan Yan biyu ne a cikinta dan tsinin cikinta ke yawan Saka shi Ce Mata Anya ba Yan biyu zata haifa ba .

Kallon jariran kawai take da yakaka ta kwantar dasu ba ta inda suka baro Habu sai dai hanci kawai da suka dauko nata dan tana da hanci sosai sab’anin na Habu da yake a dan doke.

Tana Jin sadda yakaka ke fadawa mijin ta akan ta haihu yanzu ya fada mata wacece ita.

Bata ga laifinta dan tayi kishin mijinta ba,ta tuno Zinatu da akan kishi taso aikata lahira

Ba Karamin k’ok’ari Babagana da yakaka suka yiwa shamsiya ba,duk da basu Santa ba,haka suka tsaya wajen kula da ita,dan Yakaka ita ta ringa mata wanka ta dai d’auketa tamkar yarta duk da bata san ya akayi ta sauko din ba.

Duk da alama ya nuna ba wai wani wadata ne dasu ba amma haka suka siyo kaya mai araha suka kawo na jarirai.

Wani daki suka kaita take zaune,a karantar da tayi wa gidan kamar basu da Yara a gidan.

Sai da aka samu kwana uku Shamsiya ta iya basu labarin ta

Yakaka kuwa sai kuka take saboda tsananin tausayinta

Babagana kuwa Yama kasa magana dan rashin imanin Zinatu ya zarce tunaninsa sai da komai ya lafa

Ya Kalli shamsiya Yana “Yata sai nake ganin bai dace a b’oye wa iyayenki kina rayye ba,ya kamata su san kina rayye,ni a ganina tunda har kinsan abokiyar zamanki ke san kasheki mai zai hana a hadata da hukuma,kinga bai dace ki nuna bakya rayye duk saboda kishiyarki ba,mijinki ma ya kamata ace yasan kina rayye, saboda yasan kishiyarki ce ta so kasheki”

“Kishiyata ta wuce duk yadda kuke tunani,a yanzu Ina so ta d’auka na mutu nida yata,da cikina,idan har iyayena suka san Ina rayye ko mijina dole zata sani za Kuma ta sake wani sabon Shirin ta bullo ta inda bamu tab’a tunani ba,dan haka Ina so na zama mataciya a idon kowa Ina so na gudu na bar garin nan,sai yarana sun girma zan bayyana kaina”

“Kina ganin hakan zai yu zaki iya kula da yaran nan har su uku”?

“In Sha Allah zan dage da addu’a tunda har Allah ya barni da raina bayan na cire rai da rayuwar toh duk abinda na sa agabana in Sha Allahu Allah zai cika min shi”

“Akwai kanwata tana Yobe zan rakaki wajenta zan Mata bayanin komai,Allah bai tab’a bata haihuwa ba,zan roketa akan ta rike ki,dan tana dan aiki zata iya kula daku in Sha Allahu,nima Ina so kiyi wa kishiyarki ba zata ta d’auka bakya rayye”

Shamsiya kuka kawai take tana kallon Babagana da yakaka har ga Allah bata san akwai mutanen kirki irinsu ba

Ko Yan uwanta ne su sai haka.

Haka Yakaka da Aliyu suka kaita har garin Yobe dan Aliyu saboda shamsiya ya dawo daga Can maidugurin dan Shima so yake yaji labarin Shamsiyar.

Kamar wasa Yakura da ta kasance kanwar yakakan ta karbeta da hannu biyu sai ma godiya da take wa Yakaka da ta kawo mata Shamsiya da yaranta.

Dan tana da kudi mijinta na da kudi haihuwa ne kawai Allah bai basu ba.

Mijin ta ma sai ya so fin ma Yakuran murna dan ji yayi kamar ma shi ya haifi Yan Biyun da yake ji dama Shamsiya ta bar mata su.

Yakura kuwa alwashi ta sha wajen taimakawa Shamsiya da iya karfinta da taji labarin abinda kishiyarta ta mata.

Ganin shamsiya ma ba wai wani shekaru ne da ita ba yasa ta mai da shamsiya makaranta,rayuwar da shamsiya bata tab’a tunanin za ta samu ba sai gashi silar Zinatu da ta so Kau da ita ta samu rayuwar da take tunanin sai dai a mafarki, ba iya ita kadai ba daidai da imtihal da Yan biyunta da ta sawa sunan Habun da shine Hassan din Husainin Kuma ta Saka sunan mahaifinta suke kiransu da Aryan da Abyan Suma wani irin gata ake musu da ko a gaban Habun suke ba lailai su samu irin wanan gatan ba dan tun suna shekara biyu Mijin Yakuran ya saka su a makaranta mai balain tsada.

Ita kanta nan da nan ta canza idan akwai abinda ke damunta bai Wuce kewan iyayenta dasu Hanne ba,wani zubin sai taji kamar tabi dare taje sai Kuma ta fasa dan bata san ta bayyanar musu a yanzu sai Nan gaba.

Zinatu

   Duniyarta kawai take ci da tsinke dan ta samu duk  abinda take so,kamun da tayi wa Habu ba dan karami bane,dan ji yake kamar ya goyata.

Dan Shirin ma da yake da su Sulen sai da tasan yadda tayi wajen Raba su.

Gudun zargi yasa wani zubin take barinsa zuwa duba Gwaggo da har lokacin take kwance rabi a mace rabi a rayye.

Itama kanta takan je gidan Sulen ta duba Gwaggon.

Da bama Bude ido take ba balle tasan idan akwai Wanda yazo dubata.

Burinta bai wuce ma Gwaggon itama ta wula ta zama tarihi kamar yadda shamsiya ta zama tarihi kamar ba’ayi ta ba.

A irin wanan lokacin ta matsawa Habu ya nemawa Amjad makaranta a kasar waje dan ta ga alamar idan ba haka tayi ba ba zata iya nisanta shi da zuwa gidan Sule da tayi iya yinta wajen ganin ta hana shi zuwa ba Amma yak’i hanuwa.

Sai da ya bar kasar ta samu kwanciyar hankali.

Har lokacin tana nan da kiyayyar Ameera da taga ta d’aukaka ta silar dinki da kunshin da take wanda da kudin da take samu asirin su sule ke rufe Wanda duk bata so haka ba taso ace yadda yake fama da ciwon kafa ya koma bara.

A hakan ma ido take sawa Habun dan kar ya taimaka musu.

Bata Kuma san akayi ba Ibrahim ya d’auke Gwaggo daga gidan Sule.

A rayuwa idan akwai abinda ta tsana taga talaka ya rabe su.

Shiyasa duk wani mai kudi da ta sani take hulda dasu,take sa yaranta kawance da yaran masu kudi.

Kaf yaranta tafi cin buri akan sultana dan tafi duka yaranta kyau burinta kawai taga ta sama mata wani Mai mugun kudin ta aura.

A cikin shige shigenta ta samowa Amrah wani Mai kudi ta kama wa Amrah shi har ya fito ya aureta.

Amjad na daga waje ta samo masa mata  jawaheer da  itama ta  kasance Yar gidan masu kudi dan burinta kawai  taga duka yaranta sun auri masu kudi wanan kenan.

Cigaban labarin

Zinatu

Ido ta zubawa Amjad tana kallonsa kamar a ranar ta fara ganinsa.

Habu kuwa ya Kara gyara zamansa ya cire hulan Kansa Yana “Mai kace yanzu”?

“Abba cewa nayi Ina san Ameera Ina so ka shige min gaba wajen neman Aurenta”

Habu satar kallon Zinatu yayi yaga Amjad ta zubawa ido tana kallonsa

Amjad kuwa ya cigaba da magana Yana “Abba idan har kuna sona ku shige min gaba wajen nema min Auren Ameera dan na dade Ina kaunarta,zan iya mutuwa idan har ban aureta ba Abba”

“Allah ya jikanka da Rahama Amjad dan sai dai ka mutu din dan da Raina dai ba zan taba barinka ka auri wata Ameera ba,kana ma da hankali kuwa kasan Mai kake cewa kuwa?

“Haba Hajiya ya zakice gwara ya mutu da ya auri Ameera ai rarrashin sa ya kamata muyi ko ai kema ba Zaki so ya mutu ba”

Mik’ewa Zinatu tayi tsaye cikin hucci tana “Amjad idan mafarki kake ka gagauta tashi dan ba zaka tab’a auren Ameera ba, tun kafin ka dawo nace ma mun nema Maka auren jawaheer baka da wata mata sama da ita, Jawaheer ce daidai aurenka dan rayuwar yanzu KWARYA TA BI KWARYA Ake bi,dan gidan masu kudi ya auri Yar gidan masu kudi,talaka ya nemi Yar uwarsa talaka ya aura dan haka ka bar Ameera ta auri talaka dan uwanta Amma Kai kam Baka da Mata sama da jawaheer”…..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 23*

           “Ni Kuma wallahi sai na Auri Ameera ba zan auri wata jawaheer ba,wai Hajiya mai bambancin talaka da Mai kudi,Mai yasa kike so ki ringa kyamatar talaka da bashi ya hana Kansa arziki ba,kudin nan da muke takama dashi naga Allah shi ya bamu ba mu muka bawa kanmu ba,akan me zaki ce ba zan auri Ameera da ta kasance tamkar ya a wajenki tunda mahaifin ta dai kanin Abba ne,Hajiya a yanzu ko mace baa yiwa Auren dole balle namiji dan haka ni ba wata Jawaheer da zan Aura ni Ameera nake so ita zan Aura”

Amjad yace cikin ihu ya mik’e ya bar palon Yana Jin dama ba Zinatu ce ta haife shi ba,dan tun Yana yaro ya taso da kin halayyenta ba wani makusancin su da bai san kyamatar da Zinatu ke yiwa talaka ba, shiyasa duka kanennsa suka taso da kin talaka Suma da wuya ma kaga suna muamalla dasu,Karin bakin cikinsa yadda Habu baya iya tab’uka komai biyewa Zinatun kawai yake.

Zinatu kuwa dakinta ta shige ta bar Habu da ke k’ok’arin yi mata magana,dan tasan kila yace ta bar Amjad ya auri Ameera dan yana balain san Amjad yasan shi ma yana balain san yaga Amjad ya auri jawaheer,amma dan ya faranta masa zai iya hakura ya bar shi ya Auri Ameera. ita kuwa da ranta ba zata tab’a barinsa ya auri Ameera da ta bala’in tsana ba,tunda tafi Sultana k’ok’ari ta tsaneta.

Dan a zagayen unguwar su ba Wanda bai san Ameera ta Fanin dinki da kunshi ba,gata da farin jini,duk da kudin da suke dashi bakin ciki take da kudin da Ameera ke samu

Dan a yanzu dai ba wacce ke tashen kunshi da dinkin da ya amsa sunansa dinki sama da Ameera.

Sule

   “Ameera bana so Amjad ya sake dawowa gidanan batare da wata magana a kasa ba, to tun jiya nake zuba idon zuwan wanan yaron har yanzu shiru banga yazo ba,ni ko dai kema san Amjad din kike ne”?

Ameera dake durkushe a gaban Sule kanta a kasa tayi saurin girgiza kanta Hanne kuwa tace “Taya ma zata soma wanan gangancin ai sai dai so na Yan uwantaka amma itama tasan yaudarar kanta take idan har kamuwa tayi da san Amjad”

“Tun jiya nake gwada wayarsa a kashe bansan mai ya samu wayarsa ba amma a ranar da ya zo da Kansa ya tabbatar min da manyansa zasu zo Ina ga dai wani abu ya hana su zuwa”

Ameera tace tana Kara sada kanta kasa

Dan kwana biyu kenan bata iya samun Sahar a waya duk da zata amshi auren nashi ne ba wai dan tana san shi ba sai dai dan San da yake mata abinda za tayi kenan ta gujewa Amjad dake sintirin zuwa gidansu,taso ace ba dan gidansu Habun bane ba da tafi kowace mace Sa’a dan tana balain kauanrsa kamar yadda yake kaunarta,kawai ta bar kaunarsa a matsayin sirrin zuciyarta

Abba sule sallamar ta yayi yace taje a ga zuwa goben

Tana shigewa daki Abba sule ya Kalli Hanne Yana “Wallahi yaran nan suna san junansu sai dai Aure a tsakanin su ba mai yuwa bane ba,Amjad tamkar dan cikina haka nake jinsa,yaron nan bai d’auko halin Yaya Habu da Zinatu ba,shi ka dai ne ya fita daban a gidan banso ya nemi abu a wajena na hana shi ba,yau da Gwaggo kalau take nasan ita zata dage wajen hada auren nan shekara nawa yanzu Gwaggo sai dai a kwantar a tayar wallahi halin nan da take ciki na matukar damuna”

“Addu’a kawai zaa cigaba da Mata Abban Ameera tunda duk ba abinda ba’ayi ba ba kudin da baa kashe ba amma an kasa shawo kan matsalar”

“Allah ya tashi kafadun ta Yaya ibrahim yak’i bari a d’auko ta yace idan aka kawota wai bakin cikin Yaya Habu ne zai karasa Gwaggon da bama tasan inda kanta yake ba”

“Allah ya tashi kafadunta ita kuma Shamsiyya Allah ya gafarta mata”

Hanne tace idonta na cicciko da hawayen tuna shamsiya da tayi mutuwar azaba,silar mutuwar ta yasa har gobe Mahaifiyar ta ke fama da shanyewar barin jiki dan labari na isar mata ta yanke jiki ta fadi, mahaifinsu kuwa bai Kara samun cikakken lafiya ba shekara uku da suka wuce Allah ya karbi raywuarsa.

Ameera

      Sai da taci kukanta ta gode Allah ta Kara Kiran lambar Sahar da take kyautata zaton a kashe take wanan shine karo na farko da aka samu kwana biyu bai mata waya ba,zuwa yanzu sai jikinta ya fara bata ba lafiya ba.

Jin wayar na ringing yasa ta mik’e zaune dan a kwance take

Sai da Kiran ya kusa katsewa taji ya d’auka muryarsa can kasa kasa.

Ameera daurewa tayi wajen tambayarsa ko lafiya taji shi haka kwana biyu Kuma wayarsa a kashe?

Sahar kuwa dake kwance a dakinsa ya mik’e zaune Yana Jin kamar yayi ta rusa kuka yace “Bana Jin dadine Ameera sai yau ma aka sallamo mu daga asibiti”

“Mai yake damunka bansan baka da Lafiya ba wallahi ai da ko text kamin ya jikin naka yanzu”?

“Da sauki Ameera ya su Baba”?

“Abba Yana nan kalau shi ne ma yake tambayar ka ya matsa min akan na nemo ka a waya kasan na fada masa akan kace zaka turo manyanka a tsayar da magana”

Shiru Sahar yayi yana Jin zuciyarsa na masa wani irin nauyi bai san mai zai cewa Ameeran ba,sai da ta Kara cewa hello

Yace “Dama rashin lafiyar da nayi ya hana su zuwa amma tunda naji sauki zasu zo”

“Toh shikenan Allah ya baka lafiya”

Sahar bai iya amsawa ba ya kashe wayar dan ji yake kamar ya rushe da kuka,Yana balain san Ameera da bashi da burin da ya wuce na aurenta.

Ameera macece da kowane namiji zai so aurenta dan iliminta da tarbiyyar ta nutsuwa da kamun kanta yasa ya kamu da mugun santa sai dai duk abun nan da ya zayyano ba shi iyayensa ke dubawa ba,Yar gidan manyan mutane suke dubawa Wanda su din arzikin su bai wani taka kara ya karya ba,amma suke burin ya Auro Yar baban gida.

Ya lumshe idonsa Yana tuna sadda ya samu Mahaifinsa da mahaifiyar sa da maganar Auren Ameera

“Daddy Iyayen yarinya da nake so sun ce na tura manya na a tsaida magana”

Murmushi mahaifinsa yayi ya cire gilashin fuskarsa Yana “Ma Sha Allah My son Yar gidan waye ita?wanene mahaifin ta”?

Murmurshi Sahar yayi yana ” Sulaiman sunan mahaifinta daddy yarinyar tana da ilimin Arabic sosai tana da tarbiyya dan sai da nayi bincike ma a kanta”

Murmurshi Mahaifiyar sa tayi tana “Ba wanan yake tambayar ka ba Sahar tambayar da yake ma shine wanene mahaifinta a garin nan shahararen dan kasuwa ne?ko Kuma dan siyasa ne da ana Kiran sunan shi a san shi”

Sai a lokacin Sahar ya gane tambayar da mahaifinsa ke masa suka zuba masa ido suna Jiran amsar tambayar da suka masa.

Jiki a sanyaye yace “Mahaifinta shagon provision ne dashi ba wani bane”

Kallon juna suka yi sai da suka dau tsawon lokaci kafin Mahaifinsa ya fara magana Yana “Sahar Yar baban gida nake so ka nemo ka aura,yarinya da ana Kiran sunan mahaifinta zaa san wanene shi a garin nan,a rayuwa yanzu ka taimakeni ne in taimake ka,idan ka auro wanan yarinya ba abinda zata kawo ma,sai dai Kai ka kare a bauta musu da iyayen ta amma idan ka auro Yar manyan mutane zaka ga kai kana musu,Suma suna maka,dan haka ka hakura da maganar Auren yarinya nan ka nemo Yar manyan  mutane”

“Daddy yarinya tana da tarbiyya da ilimi macece ta gari Ina balain Santa”

“Na gama magana Sahar yarinyar ba ajin aurenka bace kaje ka nemo daidai da Kai ka aura ka barta ta samu dan uwanta talaka ta aura”

Sahar kwana biyu yayi Yana bin iyayensa akan maganar Ameera amma suka dage akan basu yarda ya auri Ameera ba wanda hakan ya haddasa masa zazzabi Yama kashe wayarsa dan baisan Mai zai cewa Ameera ba

Duk da yasan ba lailai su tab’a amince masa ba haka ya sake komawa wajensu Yana rokon su akan su bar shi ya Auri Ameera.

Amma suka dage akan bada yawunsu ba ya Nemo Yar manyan mutane

Ganin an tafi sati gashi Ameera ta Kara masa text akan turawa yasa ya daure Wajen yi mata text akan tayi hakuri ta nemi wani ta Aura.

Ameera

       Duk da bata San Sahar sai da ta girgiza da text din daya turo Mata ,dan a yanzu Amjad ba Karamin matsawa Abba sule yayi ba akan Yana so ya aureta,shi ba sai ma Habu sun zo nema masa auren Ameeran ba,shi ya zame masa uwa da Uba,Sule kuwa tausayin Amjad yasa yace masa shi  ba zai hana shi Ameera ba matsalar Sahar ya riga da ya turo manyansa Kuma Ameera shi take so,Kuma ko ba dan haka ba,ba ya Jin zai iya bashi auren Ameera batare da Habune yazo gidan da Kansa nema masa auren Ameera ba.

Inda Abba sule ya sako Ameera a gaba wajen matsa mata akan ta yiwa Sahar maganar turowan dan so yake ma suna zuwa yace su bada sadaki kawai a daura auren ko hakan zai saka Amjad ya hakura.

Ameera Kiran Sahar kawai take a waya dan so take ya fada mata dalilin da yasa ya fasa aurenta dan ita dai tasan Yana balain santa ba Karamin abu ne zai sa ya fasa auren ta ba Wanda rashin Sanin dalilin zai jefata cikin damuwa.

Amma duk Kiran da ta masa bai d’auka ba sai text din ban hakuri ya ringa turo Mata Yana fada mata irin san da yake mata”

Sule Kansa sai da hankalinsa ya tashi da janyewar da Sahar yayi,dan daya kasa hakuri ma sai da ya neme shi,dan ji yayi Yana so yasan dalilin da yasa har Sahar ya fasa auren Ameeran.

Cikin Jin nauyinsa Sahar ya fada masa iyayensa ne suka hana shi auren Ameera ya fada masa dalilin su

Sule kuwa duk da yaji ciwon janyewar amma Sanin dalilin ya dan kwantar masa da hankali dan ya d’auka ko wani Sharrin aka yiwa Ameera shi yasa ya fasa auren nata,bai san haka zamanin ya koma ba,ya d’auka iya Habu ke gudun Hulda da talaka Ashe wasu masu kudin ma gudun talakawan suke.

Shi ya kwantar wa da Ameera hankali yace ta sake dubawa a maneman ta ta samu wani talakan da yake daidai da ita ta aura dan yanzu rayuwar ta koma ta KWARYA TA BI KWARYA sai kana dashi kake mutum amma matsawar baka dashi gudun ka ake komai kyaun halinka kuwa.

Habu

        Ba yadda bai yi da Amjad akan ya hakura da maganar Auren Ameera ba amma  Amjad haka yak’i ya haukace musu akan shi ba zai iya hakura da Auren Ameera ba.

Abu kamar wasa sai gashi Amjad har da kwanciya a asibiti dan Sule  ya dage akan ba zai iya bashi auren Ameera ba sai dai idan Habun ne ya taka kafarsa yazo gidan da Kansa

Wanda sule ya fadi hakane dan yasan ba zai ma tab’a zuwa gidan nemawa Amjad Auren Ameera ba,dan saboda Gwaggo ma yake dan shiga harkar Habun duk da a a kwance take so yake ya Mata biyayya wajen ganin basu bar Zinatu ta raba kansu gabad’aya ba.

Habu kuwa ganin Amjad a kwance a gadon asibiti Zinatu kuwa na can ko a jikinta Yasa ya koma gidan dan duk da Shima zai so ace Amjad din a matsayin sa na dansa na fari ya auro Yar babbar gida amma haka zai Hakura dan yaga idan ba’a bar shi ya Auri Ameeran ba kashe Kansa zaiyi a banza.

Sai dai ko da ya koma gida ya tari Zinatu da maganar sai cewa tayi ita ba ta yarda ba bayan duk Abubuwan da suka faru taya ma Amjad zai auri Ameera,abinda ba Wanda Sule ya tsani ma gani kamarta,sanan taya kamar Amjad zai auri Ameera ai ba da yawunta ba.

Habu kuwa zuwa wanan lokacin sai yaji ya fara zuwa wuya dan baisan Mai yasa Zinatu ke balain gwadawa Sule kiyayya ba,shi bai ga aibun Ameera da ba Wanda ba zai so dansa aurenta ba dan ba Wanda baisan irin tarbiyyar da ta samu ba duk da ba wani shiri yake da sule ba amma Shima Jin dadinsa ne ma ace Amjad ya aureta

Cikin hade rai ya fara magana Yana “yanzu maganar lafiyar Amjad muke yi zinatu ba abinda ya faru a baya ko wani Abu ba,tunda har ya dage akan Ameeran yake so Ina ga barinsa ya auretan yafi inya so daga baya sai ya auri jawaheer din akan wani dalilin mu da bai taka kara ya karya ba bai dace muki barinsa ya auri wacce yake so ba”

Zinatu shiru tayi tana kallon Habun dake magana cikin bacin rai da daga murya dan rabon da ya ma iya daga mata murya haka har ta manta,dole ta waiwayi bokanta ta san shirn da za tayi.

Bata dubo Amjad ba har aka sallamo shi dan Habu ne ya ringa kwantar masa da hankali akan kar ya damu zasu bar shi ya Auri Ameera.

Zinatu kuwa jinsu kawai take dan ba zata tab’a barin Amjad ya auri Ameera ba ta bayan gida zata biyo musu.

Kafin Habu ya je wajen sule ta riga shi zuwa gidan dan ya sanar mata akan lahadi zaije wajen Sulen ya nemawa Ameera auren Amjad.

A lokacin da ta isa gidan Ameera na palonsu tana hada kayan wata Amarya

Hanne kuwa taje gida dan akwai wani biki da suke yi a cikin dangi.

Kannenta kuwa sunje islamiyya

Zinatu sai da ta gama karewa tsakar gidan Kallo a wulakance tana hararo yadda wai kawayenta hajiyoyi zasu zo gidanan kawo lefe

Taya ma zata bar Amjad ya auri Ameera ai sai da ta samu talaka dan uwanta ta dan yaranta ma suka Fi dacewa da Auren.mai kudi.

Rabon da ta taka kafarta tazo gidan ba zata iya tunawa ba ba ko sallama ta nufi palon da yake Jin karar keken

Ameera kuwa ganin Zinatu a bakin k’ofa ta harde hannunta a kirjinta tana Kallonta yasa ta tsayar da dinkin da take tana “Wa alaikum Salam”

“Banyi sallama ba dan bana Jin Kun cancanci ayi muku sallaman ke tashi ki kira min Hanne”

Ameera kamar zata shareta ta cigaba da dinkinta sai Kuma ta daure Wajen cewa “Ba ta nan”

“Toh Bud’e kunnenki da kyau kiji abinda zan fada miki, Ameera idan har kina san kanki da Lafiya karki yarda da Auren Amjad da zaa zo nema masa aurenki ki fito ki nuna bakya san auren kije ki nemi wani ki aura amma idan ba haka ba”

Ameera katseta tayi da sauri tana “Ba abinda zanyi da Amjad ko da shine autan maza dan bashi da tarbiyyar da zan iya aurensa har na kira shi da uban yayana,sai dai ni na roke ki ki fada masa ya daina nacin zuwa dan ba zan tab’a aurensa ba nafi karfin aurensa”…..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 24*

  Zinatu

           Kallon Ameera kawai take tama rasa mai zata ce mata

Ameera kuwa ta d’auki rigar da take hadawa ta fara k’ok’arin nufar cikin dakinsu dan a yadda take Jin zuciyarta har zagin Zinatu za ta iya yi,dan tun kan ta mallaki hankalinta ta matsa mata ta rasa mai ta mata da ta dora mata wanan karon tsanar.

Tana dab da shiga dakinsu taji ta fusgota ta baya tana “Ni kike wa rashin kunya?ni zaki kalla kice yarona bashi da tarbiyya?Har ke zaki budi bakin ki kice kinfi karfin auren  Amjad”?

Ameera fusge jikinta tayi daga rukon da ta mata tana “Idan tsoho bai ji kunyar hawa Jaki ba,Jaki bai zai ji kunyar kayar dashi ba,idan rashin kunya kike ganin na miki toh ke kika jawo na Miki Rashin kunyar da ba halina bane ba tun Ina yarinya kika matsa min kika dora min Karan tsana narasa mai na miki,a ganina ai ba ni ya kamata ki yiwa gargadi ba,Amjad ya kamata kiyiwa gargadi idan har kin isa dashi,duk da mu talakawa ne amma da gaske nafi karfin aurensa ba abinda zanyi dashi dan haka idan kinsan kin isa da shi ki gargade shi akan kar ya Kara taka kafarsa a gidanmu dan wallahi ko Maza sun kare ba abinda zanyi dashi”

Daga haka Ameera ta shige daki ta rufo k’ofar dakin nasu tana sauke numfashi dan wanan dabiar ba nata bane ara tayi Zinatu ta isheta shiyasa ta rufe ido wajen yi mata rashin kunyar,da gasken Kuma take ko da Amjad shine autan mazan ba zata tab’a iya aurensa ba duk da mugun san da take masa,dan bata ganin mutunci Zinatu baya ganin farinta bata ga ta inda ma zata ma iya aurensa ba kamar yadda Abba Sule da Hanne ke fadan suma ko Mai Amjad zai yi ba zasu iya bashi auren ta ba dan duk sun san halin Zinatun da rashin mutuncinta.

Zinatu kuwa sai da ta dade a tsaye tana Jin zuciyarta na mata zafi da ganin wai Ameera saar sultana ce ta wanketa tas haka sosai taji tana kiyasta kalar muguntar da za tayi wa Ameera Koda kuwa Amjad bai aureta ba,ta lura wanan dinki da fulawan da take yi yasa take ganin kamar ta Kai amma idan ta daina iya dinki da kunshin zata ga dame za tayi takama.

Haka ta baro gidan tana dan Jin Kuma sanyi a zuciyarta dan daga yadda Ameera tayi magana tasan ba zata tab’a yarda da Auren Amjad din ba sai dai ya gama haukansa shi kadai.

Koda ta isa gida bata nunawa Habu ma taje gidan ba

Amjad kuwa ta Dade da Daina amsa gaisuwar sa abinda Kuma ke Kona mata rai bai wani san fushi take dashi ba Yama fita san yayi zuciyar.

Koda Hanne ta dawo Ameera ta sanar da ita zuwan zinatu da yadda suka kwashe da ita mamaki ne ya rufeta dan ta d’auka Zinatun ta dan girma taya ma zata zo ta ringa sainsa da Ameera da take kamar ya a wajenta,da bata wahalar ma da kanta zuwa yiwa Ameera gargadi ba,dan itama da ranta ba zata tab’a iya barin Ameera ta auri Amjad ba Koda kuwa sama da kasa zata hade dan tafi kowa sanin wacce Zinatu,har gobe tana zarginta a mutuwar shamsiya kawai ta dai ja bakinta ta tsuke ne

Sule kuwa murmushi kawai yayi da Hanne ta sanar masa yace bai yi mamaki ba,yasan da Ameera bata shige daki ba zata ma iya k’ok’awa da ita girma ne kawai Zinatun ba zata tab’a yi ba ai ko dan Zinatun ba zai tab’a iya bawa Amjad Auren Ameera ba.

Washegari wajen goma sai ga Habu a gidan, rabonsa da gidan Shima Kansa ya manta

Amjad kuwa jikinsa sai rawa yake Yana washe baki dan gani yake tunda har Habu ya zo gidan a yanzu dole Abba sule ya bashi Auren Ameera.

Kadaran kadahan suka gaisa Habu Yana ta wani Shan kamshi dan kawai ya farantawa Amjad yazo nema masa auren Ameera amma har ga Allah Shima ba haka yaso ba.

Dole ne ma ya canzawa sule gida kafin bikin dan Shima ba zai so wayanda yake muamalla dasu suzo suga irin gidan da Amjad yazo neman Aure ba.

Sule kuwa kallonsa kawai yake Yana Jiran yaji Mai ke tafe dashi.

Sai da Habun ya gama kalle kallensa kamar ana masa dole ya sanar da Sule dalilin zuwansa ya Kara da “Amjad ya nuna nan da wata biyu yake san auren,dan haka karka matsawa kanka wajen yin wani hidima tunda itama Ameerar Yata ce ni zan mata kayan dakin inyaso sai na bada kudi a siya Mata su kayan kitchen din”

Murmurshi sule ya saki Shima sai da ya dau tsawon lokaci kafin ya fara.magana Yana “Yadda kayi magana kamar har nace ma na yadda zan bawa Amjad Auren Ameera,yadda kayi magana kamar irin dole tunda kana da kudi kai Mai kudine Kai zaka tsara min komai ka juyani yadda ranka ke so.

Idan baka manta ba a baya nace akwai lokacin da zaka nemi abu da kudin ka ba zaka same shi ba,akwai lokacin da ni dinan da ka raina zaka zo neman Abu a wajena ga Kuma lokacin yazo Yaya Habu,dan ni Sule ba zan tab’a bawa Amjad Auren Ameera ba sai dai Ameera ta kare rayuwarta a haka batare da mijin Aure ba,kaje ka nemawa Amjad Aure a wani wajen amma ni Sule ba zan tab’a bawa Amjad Auren Ameera ba”

“Sule kenan dama shi talaka ance yafi kowa ruko da zuciya Ina ganin wanan lokacin da arziki ya zo ma bai kamata kayi fatali wajen juya masa baya ba,kaima kasan banda Amjad ya nace Yana kaunar Ameera ni Habu ba zan tab’a taka.kafata nazo gidanka nema masa aurenta da har zaka tsaya min maganganun abinda ya wuce a baya,dan haka lokacin kaima da zaka dangwali arziki yayi ka ajiye girman Kai da ruko ka bawa Amjad Auren Ameera”

Murmurshi sule ya sake saki Yana “Ai ko mutuwa nayi zan bar wasiyya akan ba yadda  a bawa Amjad Auren Ameera ba,Yaya Habu wallahi yau ban da Gwaggo ba abinda zai saka na tab’a iya Kara muamalla da kai,kudin da kake takama kana dashi har nima zan dangwala din baya gabana a matsayin nan da Allah ya ajiyeni wallahi nafika kudi haka nake jina matarka jiya tazo tayi wa Ameera diban albarka abinda bata sani ba shine da bata wahalar da kanta zuwa wajen yiwa Ameera kashedi ba dan ba abinda zai saka ni da kaina na mik’a yata wajenku bayan ba shaye shaye nake ba,kaje wajen masu arziki ka namewa Amjad matar Aure amma ba dai Ameera ba”

“Sule kana da damar da zaka ma zageni banga laifinka ba dan yau da wanan yaron bai matsa min ba ai nafi karfin zuwa gidanka nema masa auren ka kila kana cikin wayanda basu da rabone a rayuwarsu kawai abinda nake so ka sani ka cutar da Ameera dan ba lailai ta tab’a samun miji irin Amjad ba”

“Fin Amjad zata samu Yaya Habu ni Sule ni na fada maka dan babann gida Ameera zata aura da suka san mutunci mutane suka san darajar mutane Ina takaici da Amjad ya ratso ta tsatson Kai da Zinatu”

Habu wani irin Kallo yake yiwa sule kamar zai kai masa shaka sule kuwa ya cigaba da kallonsa Yana zaune

Sanin idan ya kara jefawa Sule wani maganar zai yabo masa mai zafine kamar dama irin Jiran zuwansa yake yasa shi fitowa daga palon a fusace bai ko Kalli Amjad dake tsakar gidan Yana Hira da Sadeeq kanin Ameera ba yayi waje a fusace.

Amjad kuwa ya mik’e da sauri yabi bayansa

Kafin Amjad yayi magana Habu ya juyo a fusace Yana “Kaine duk ka jawo min wanan wulakanci da kaskancin,da baka dage kana san yarinya nan ba da ba abinda zai saka na tab’a tako kafata nazo wai gidan Sule ya ringa Yaba min magana ba,an nemo Maka mace ta arziki da mutunci Yar manyan mutane ka dage Yar sule kake so da bakin ciki yake ma da ganin arzikin da nake dashi,toh yace ba zai baka Auren Ameera ba Koda zaka mutu,ni Kuma ba zan iya musu dole ba dan haka sai kasan yadda za kayi”

Daga haka ya shige bayan motar yace driver yaja motar su tafi dan a yadda Amjad ya daskare a tsaye Yana kallonsa yasan ba binsa zai tab’a yi ba sosai yake Jin kamar zuciyarsa zata fashe saboda tsananin bakin ciki.

Amjad kuwa gidansu Ameeran ya koma da gudunsa hankalinsa a balain tashe dan kiri Kiri ya fara ganin samu da rashi.

A gaban Sule ya zube yana tambayarsa da gaske ne ba zai bashi Auren Ameera ba

Sule kuwa kafin yayi magana Ameera ta fito daga dakin tana “Nice nace bana so Yaya Amjad ba Abba ne ya hana Ka aurena ba,Amjad ba zan iya aurenka ba,Jiya Hajiyar ku tazo har gidanan ta zageni tas ta zage Abba da Umma tace idan har na yarda da aurenka kasheni ma za tayi,Amjad ka daina wahalar da kanka dan ba zan iya aurenka ba kayi hakuri kaje ka nemi wata”

Amjad kallon Ameera kawai yake hawaye na zubo masa Sule kuwa ya dafa kafadarsa Yana “Kayi hakuri Amjad ka dage da addu’a akan Allah ya baka wacce tafi Ameera Aurenka da Ameera ba mai yuwa bane ba”

Amjad mik’ewa yayi bai ce komai ba ya fice daga gidan

Ameera kuwa ta koma dakinta tana Jin Sule na abinda tayi yayi daidai dan baya so Amjad din yaga kamar shi ya dage akan ba zai bashi Auren Ameeran ba.

Ameeran kukanta taci ta gode Allah ta goge duk hotunan Amjad dake wayarta da zobonsa da ya bata kafin ya bar kasar dole ta dage wajen nisantar duk wani abu da ya shafe shi dan tasan auren su bama tab’a yuwa bane.

Amjad kuwa a haukace ya koma gida,kamar zai daki Zinatu haka ya ringa masifa Yana rantsuwar shi ba zai auri jawaheer ba tunda har taje gidansu Ameera tasa aka hana shi aurenta ya rantse ba zai auri jawaheer ba.

Zinatu kuwa murmurshi kawai take tana kallonsa har ya bar palon kamar zai tashi sama,fes take Jin ranta dan tasan ta riga da ta rufe Kuma babin Ameeran Koda ba zai auri jawaheer ba ba zata damu ba dan gwara dai ya auri koma wacce da dai ya auro mata Ameera.

Washegari Amjad ya hada kayansa akan kasar zai bari shi ba zai iya zama ba Habu kuwa kamar zaiyi kuka rarrashi kudi da kalamai ba Wanda bai yi wa Amjad ba dan baya so ya Kara Nisa dashi company daya Bude masa yake so a yanzu ya fara zuwa amma haka Amjad ya tubure akan shi ba zai zauna ba tunda har suka kasa nemo masa auren Ameera.

Yana Ji Yana gani Amjad yayi tafiyar sa

Zinatu kuwa ganin duk yabi ya damu yasa tace ya bar damun Kansa yanzu fushi Amjad din yayi zai sauko ne ya dawo da kafafunsa.

Shigowar Samha palon daga ita sai riga da wando yasa ya dago Yana kallonta.

Har ta iso wajen da suke zaune tayi matashi da cinyar Zinatu da ta hau sakin murmurshi tana shafa gashinta Habu kuwa daidaikun Rana ne zai ga samha bai tuna da imitihal ba,duk da baya nunawa a fili amma Yana yawan tunawa da shamsiya da imtihal har gobe yakan tuna cikin dake jikin shamsiya kafin ta rasu,ya kasa manta irin rayuwar da yayi da Shamsiya kullum cikin yi mata addu’a yake har da sadaka.

Shigowar wata kawar Zinatu palon yasa shi mik’ewa ya hau sama tare da amsa gaisuwar kawar tata.

Zinatu kuwa katin hannun ta kawai take juyawa tana “Hajiya Farida ai dole muje wajen nan matar sarki guda yanzu saboda dan nata zai dawo ake ta wanan shirye shiryen?

“Shi kadai ne fa danta ke kuwa Kuma shi kadai ne namiji dan anyi shagali a murnar dawowar sa kasar nan ai ba zaki yi mamaki ba,ke kinsan ma da yadda na samo mana Katin nan”?

“Ai ke kam kin gama min komai wallahi dan bani da burin daya wuce naga Ina shiga cikin irin wandanan mutanen”

“Ke kinga yadda mutane ke ta dokin zuwa wajen nan ai wallahi da Ina da yarinya budurwa sai na tafi da ita dan sai nasan yadda na cusa ta wajen danta ko Allah zai sa a dace ke ki duba min ace kamar dan gidan sarki Maje  yace Yana san yarki”?

Ido Zinatu ta waro ta kaiwa hannun Hajiya Faridan Cafka tana “kin manta Sultana yarki budurwa ce ai Sultana ta gama samun mijin Aure Farida”

Zinatu ta saki ihu tana hararo Sultana a matsayin sirikar Gimbiya Maimuna

Ji take kamar har Yariman yaga Sultanar Yana so

A ranar ko baccin kirki ka sa yi tayi dan hararo Sultana a gidan sarauta kawai take.

Mik’ewa ta sake yi ta sauko kasa dan ta hau sama ne kawai dan ta d’aukewa Habu hankali dan bata so ya gane ma Sultanar bata gidan.

Tun karfe uku na rana tace mata zata.je birthday kawarta amma gashi har Sha biyu na dare bata ga ta dawo ba.

A rayuwa tana so taga yaranta a waye suna Hulda da yaran masu kudi shiyasa indai wani abu ya taso take barin sultanar har wani zubin ma ta kwana duk batare da Sanin Habun ba tana so taga ta bawa yaranta freedom suna abinda ransu ke so.

Cikin sanda ta fita waje ta hau tambayar maigadi har yanzu sultanar bata dawo ba,dan umarni ta masa akan tana dawowa ya bude mata k’ofar.

Mai gadi na k’ok’arin magana taga alamar dirin mota a k’ofar gidan nasu.

Da sauri ta bud’e ta leka taga wani ne ya sauke Sultana a wani arnen mota,ya Sha kitso da sarka.

Sultana Kuma riga da wando ne a jikinta ya matseta

K’ofar da ta Bude yasa suka Kallo bakin k’ofar Saurayin kuwa ya dago mata hannu Yana “Hi mum”

Zinatu bata iya magana ba dan bata ga alamar tarbiya a tare dashi ba tana san masu kudi amma ba Yan iska ba

Sultana kuwa ta daga masa hannu ta nufi k’ofar da sauri

Zinatu kuwa ta bud’e mata kofar tana shigowa ta damke hannunta ta hau janta bata direta ko Ina ba sai a dakin sultanan

Sultana kuwa ta fusge hannunta da taji tana neman b’alla mata tana “Wai karyani za kiyi ne”

“Sultana kina da hankali kuwa daga zuwa birthday Zaki Kai karfe daya na dare waye wanan dan iskan da ya kawo ki a mota”?

“Kai hajiya saurayina ne fa kinsan waye babansa kuwa tab ai in gaya miki Don ne Shamsu”

“Wanan dan iskan daya Sha kitso shine abun so a wajenki sultana”?

“Wai baki ji mai nace ba Mai kudine fa kinga dala Dari biyar ya bani fa”

Sultana tace tare da Bud’e Jakarta ta d’auko kudin ta nuna wa Zinatun da ta zauna a gefen gadon.

Ta Kai hannu zata karba sultana ta mayar da kudin cikin jaka tana “Yana sona yace zai aureni”

“Bar maganar nan sultana wanan shamsu bai dace dake ba karki manta nace miki ke matar manya ce shi yasa Zaki ga nama fi kashe kudi akan ki,kinsan Sarki Maje ko”?

Sultana sai da ta hau wurga idonta kafin ta tuna tace “Ina dai Jin sunansa bansan shi ba”

“Toh dansa ranar juma’a zai dawo daga waje  Yarima Zayyan idan ya dawo ranar asabar za’a hada masa walimar dawowa an kawo mana Katin gayyata.

Yan Matan garin nan kaf zasu je dan kowace burinta taga taje ko Yarima Zayyan zai kyasa yace Yana so,dan gata ne kuma kema Kinsan kudinsu ba Wanda ya dace dake sama dashi sultana tunda aka kawo min katin na matsu ki dawo na sanar miki daga yau zuwa asabar dinan gyaran jiki zan sa a fara miki so nake ki samu shiga a wajensa ki gayamin yadda zanyi idan Allah ya tabbatar min”

Zinatu tace tana washe baki dan ta gama sawa a ranta da hadin nan da take so tayi

“Hajiya karki wahalar da kanki kiyi mafarkin da ba zai tab’a tabbata ba yarima Zayyan wallahi yafi karfin ajina ke kinsan yadda manyan mata masu kudi ke san sa kuwa?ai ki ma daina wanan mafarkin dan yafi karfin ajina”

Hannunta Zinatu ta ruko tana “zan kashe ko nawa ne Sultana wallahi sai ya soki kin gama samun mijin Aure fa”

Dariya sultana tasa ta hau cire.kayanta tana “toh Hajiya bari na barki ki gwada saanki idan ma takamarki wanan kwalin ne zai Saka ya Soni mafarki kike”

Dariya Zinatu tasa tana “bakisan wacce Mahaifiyar ki ba Sultana Dan Allah Karki sake fita daga gidanan har sai bayan Taron nan gobe zan sa a fara miki gyaran jiki”

Daga haka ta mik’e ta bar dakin.

Ameera

   Wayar hannunta ta zubawa ido kamar yadda Hanne dasu Sadeeq suka zuba mata ido suna kallonta bayan ta gama amsa Kiran da aka mata”

“Wai kinyi shiru waye ya kiraki ne”?

“Anne wai kinsan matar sarki ce tasa a kirani wai naje na mata kunshi sun ga wai kalar kunshi na a Instagram ni mamaki ma ya Hana ni motsawa shi yasa na sake Kiransu Ina nidin tace nazo na mata kunshi amma matar ta sake tabbatar min da na shirya gobe da yamma zaa zo har gida a d’aukeni”

“Dan Allah aunty ki tafi dani shikenan mun gama arziki idan kika je kunshin nan”

Sadiq yace cikin ihun murna

Ameera kuwa tace “tab ai ba zan iya zuwa ba gani nake bani suke nufi ba kuskuren kira su kayi Amma Ina na iya kunshin da zan yiwa matar sarki guda salon naje ma a daureni”

Murmurshi Hanne ta saki tana “Ameera ba yadda Allah baya ikonsa ba kuskuren kira suka yi ba tunda har suka kira suka ce a yanar gizo suka ga kalar kunshinki har suka dau lambarki da gaske ke din suke nema,Ameera duk inda rabonki yake sai kin same shi,dan ba ranar banzan da bana miki addu’ar nassarar rayuwa dan tun kina karama muke morarki har kawo girmanki da har yau arzikin ki muke ci,duk wani abu da zamuyi takama dashi a yanzu ta silarki muka same shi,a rayuwa burinki kiga kin faranta min kin faranta wa mahaifin ki abinda kike mana ko wani namijin ne sai haka,rufin asirin namu ta silar ki ne ba mu da abinda zamu yi a rayuwar nan sama da addu’a da godiya ga Allah da ya Kai ki matsayin da bamu tab’a kawo wa kanmu ba a yanzu dan haka karki yi mamaki dan matar sarki ta nemi ki Mata kunshi dan in Sha Allah nassara da d’aukaka za kiyi ta samu a rayuwarki”

Ameera hawaye kawai take sharewa dan wani sai ta rasa yadda za ta godewa Allah dan a yanzu wajen fili biyu Abba sule ya siya da kudin da take Samu ta kunshi da dinki,masu kudi kawai ke nemanta akan su zo mata kunshi idan kuma taje wasu har dubu dari suke daukowa su bata,dan page ta Bude a Instagram da sunan Meerah Henna and tailoring ta Saka hotunan kunshin da tayi wa mutane da dinki.

Da kudin da take samu Abba sule ya bude shago a kasan layinsu yake zama bata tab’a tunanin kunshinta ya kai ya burge matar sarki ba ta bud’e datan ta ta shiga Ig tana kallon kalar kunshin da ta dora,banda messages rututu da bata ma samu damar budewa ba”

Ko baccin kirki ba tayi ba dan sai ta tsinci kanta da fargaba wai kamarta zata taka kafarta a gidan sarkin da labarinsa kawai take ji.

Ji take ma kamar ta kashe wayar ta dan tsoro ma ta ringa ji

Bata San ya akayi Hanne ta sanar da Abba sule ba ya kirata ya dafa kanta ya Mata addu’a akan kar ta damu rabon ta ne a can shiyasa suke nemeta.

Wajen Sha biyu sai ga Kiran waya matar da ta kirata jiya tana sun iso unguwar tasu ta musu kwatance

Jikinta rawa kawai yake ta fita waje da hijabinta har kasa.

Nesa da layin ta hango katon jeep sai da ta kira taga sun nufo wajen da take tsaye.

Suna zuwa daidia wajenta wata Yar dattijuwa ta fito tana “kece mai kunshin”?

Gyada Kai Ameera tayi

Matar kuwa tace “Yarinya ki fara yiwa Allah godiya dan kakarki ta yanke sak’a dan Gimbiya da kanta tace a d’auko ki Mata kunshi”

Ameera jikinta rawa yake da taji ta Kara tabbatar mata da gimbiyar da kanta ke nemanta.

Tare suka shiga cikin gidan da matar da take kyautata zaton jakadiya ce sai da suka gaisa da Hanne da ta lura da itama jikinta rawa yake ta Kara cewa Hanne tayi wa Allah godiya kafin ta fito waje Hanne da hawaye ke zubo mata ta sake rike hannun Ameera tana “Ke Mai Sa’a ce Ameera Allah ya buda miki kwakwalwarki ki Mata kunshin da baki tab’a yiwa wani ba,kije Allah ya bada Sa’a”

Ameen Ameera tace ta rike hannun Farida suka yi waje dan ji tayi ba zata iya zuwa ita kadai ba.

Kamar mafarki haka take gani sai gasu a wani wawakeken palon da suke ganin tamkar Aljannar duniya.

Ameera bata tsaya kalle kalle ba Fareeda ce ta kasa hakuri ta ringa kalle kalle.

Ameera kuwa kanta ta sadar a kasa faduwar gaban da take ta fama dashi yasa ta hau addu’a

Daga kirarin da taji ana yi yasa ta gane gimbiyar ce ta fito da kanta

Wanan matar da ta d’auko ta ta ringa zabga mata kirari kamar zata Ari baki har sai da ta samu waje ta zauna

Ameera da Fareeda suka rarrafa gabanta suka  hau gaisheta

Ba mai yarda ma gimbiyar ce dan fuska a sake ta amsa gaisuwar ta jefa musu tambayar wacce mai kunshin

Ameera da jikinta ke rawa tace itace

Gimbiya Maimuna kuwa ganin jikin Ameera na rawa yasa tace ta kwantar da hankalinta ta nutsu ta mata kunshin

Ameera a nutse ta hada kayan kunshin nata tana Jin idon gimbiyar a kanta har ta fara mata da Jan kunshi a kafa bakinta d’auke da addu’a akan Allah yasa taga kyaun kunshin

Bama tayi Nisa a kunshin ba taji gimbiyar nata yabawa da yasa Ameera ta fara jin sanyi a zuciyarta

Sai a lokacin ta dan samu nustuwa ta dage wajen tsantsara kunshin da duk basirar da Allah ya bata

Dan gimbiyar fara ce tas tamkar wacce take zanna mata da engine haka kunshin ya ringa fitowa.

Busar dake ta tashi da dan hayaniya da ake kaure dashi yasa Gimbiyar sakin murmurshi tana “Yarima ya iso kenan”

Jakadiya dake gefenta a durkushe tana zuba mata fifita tace da alama shi ya iso.

Ta mik’e da sauri tana su Ameera su tashi su bar palon su koma can idan yareema ya fita sai su dawo su cigaba da kunshin.

Ameera da taji jikinta ya Kara kwasar wani rawan ta fara k’ok’arin mik’ewa da sauri Gimbiyar ta girgiza Mata Kai akan ta koma ta cigaba da aikinta.

Jakadiya kuwa tayi wajen k’ofar da yaji dogarai nata kirari kamar zasu Ari baki

Itama kirarin ta hau masa kafin ma ya shigo wani iirn kamshi ya mamaye palon.

Gimbiya kuwa sai murmushi take tana kallon Yarima Zayyan a daidai lokacin da ya karaso Ameera da kirjinta ke dukan uku uku ta dago suka hada ido

Ameera ta Kau da kanta da sauri ta fara k’ok’arin mik’ewa tsaye Gimbiya ta sake ce mata “Karki damu Ameera ki cigaba da aikinki kinji”

“Ranki ya dade Dan Allah bar mu tsaya daga waje idan Kun gama sai mu dawo”

Ameera tace cikin rawar murya dan sosai jikinta ke rawa

Muryarta yasa Yarima Zayyan Kara Kallonta a sace kafin ya sumbaci gimbiyar a hannunta Yayi maganar da su kansu basu ji ba yayi waje.

Sai a lokacin Ameera ta dan samu nustuwa Gimbiya kuwa ta zuba mata ido tana kallon ta dan nutsuwar Ameeran yayi matukar burgeta.

Kunshin da ta mata Yayi bala’in kyau da sai taga tama Raina duk kunshin da ake mata a baya

Ganin Ameera ta matsu ta tafi yasa tayi wa jakadiya magana kasa kasa ta daga wani lalausan Tim Tim dake gefenta ta d’auko wani kati mai balain kyau ta mik’awa Ameera tana “Ina gayyatarki waleema gobe jakadiya zata rakaki gida”

Jikin Ameera rawa yake wajen amsar Katin dan ba Karamin matsuwa tayi ta bar gidan ba.

Suna fitowa harabar gidan suka fara k’ok’arin shiga motar da jakadiya ta nufa da wani jaka a hannunta.

Kamar ance ta daga kanta sama sai taga Yarima Zayyan ya zubo mata ido Yana kallonta.

Ta kuwa shige motar da balain sauri bata samu nutsuwa ba sai da suka bar harabar gidan suka hau titi

Jakadiya kuwa ta dora mata jakar a cinyarta tana “Babarki ta iya haihuwa yarinya kinje da saarki dan wanan jakar cike take da kudi”.

Yarima Zayyan

Nifa ban iya Abubuwan sarauta sarauta nan ba sai ana min hakuri da yadda zan rubuta a beg shine fiction din dana Kara Dan labarin ya Kara siga 😂😂

*KWKWR T KWKWR*

*Page 25*

Yarima Zayyan

        Duka abokinsa fu’ad ya kai masa Yana “dan Allah ka tashi ka shirya muje wajen nan Kai kadai ake Jira fa”

“Daga dawowa ta dan Allah ba zaku barni na huta ba wallahi a gajiye nake”

“Daurewa zaka yi abokina ko awa daya ba zaka yi bafa kaga rashin zuwan naka ba dadi tunda saboda Kai aka hada Abun nan

Tsaki Yarima Zayyan yayi ya mik’e Ya fada bandaki banda kar yak’i zuwa suga kamar ya musu rashin mutunci da ba inda zai je shi bai ga amfanin wani hada partyn murnar dawowarsa da abokanansa su kayi ba,ba kuma iya su ba Gimbiya kanta itama ta hada duk bai sani ba sai dazu da ya koma wajenta take sanar masa

Mutum ne shi da baya san hayaniya amma tunda sun dage haka zai daure.

A nutse yayi shirinsa cikin wani shigar Kananan kaya da suka yi matukar amsar sa,kasancewar bakaken kaya ne sai farinsa ya Kara fitowa sosai.

Kana ganinsa kaga kudi,kyau da Jin dadi uwa Uba sarauta da ya zauna a jikinsa da ko waje ya shiga kana ganin yanayinsa kasan jinin sarauta ne shi.

Koda suka isa wajen wani katon gida ne a GRA abinka da masu kudi ba Karamin kawatuwa wajen yayi ba.

Tun kafin ma ayi parking ya fara hango Yan mata na ta kai da kawowa a harabar katon gidan da ya gaji da haduwa tamkar Rana saboda hasken gidan

Tunda suka taho bai magana ba sai a lokacin ya juya ya Kalli Fu’ad Yana “Ya naga har da Mata”?

“Ya ba zaka ga mata ba ka d’auka waleema muka hada ma,duk saboda Kai fa aka hada partyn nan sai kayi ta wani abu kamar baka waye ba”

Fu’ad kuwa ya bud’e k’ofar motar ya fita

Yarima Zayyan kuwa Sam bai san Taron da Mata aka hada ba ya d’auka iya su abokaina zasu hadu ayi murnar dawowar tasa bai kawo da akwai mata ba,ba Kuma wai sabo ne bai Saba da zuwa party yaga Yan mata ba kawai Yana k’ok’arin yaga ya kiyaye mutuncinsa a matsayinsa na dan sarki,dan yasan Yanzu Yana fita wasu har labewa zasuyi wajen yi masa video,shi kadai yasan kalar Yan Matan da ke masa magana ta yanar gizo akan suna san shi,duk da a waje duk yayi Karatunsa idonsa Kuma a Bud’e yake amma Sam baya wani sha’awar rayuwar sharholiya,dan Gimbiya tayi tsayuwar daka wajen bashi tarbiyya da Kuma haka ya taso duk kudinsa da wayewarsa baya shan sigari baya neman mata.

Idan akwai abinda ya tsana ma bai wuce yaga mace bata da kamun Kai ba duka abokanansa Yan sharholiya ne sunki Kuma yarda akan baya yi din dan rayuwar Sam bata burge shi dan shi mutum ne mai kyankyami ma.

Sai da suka Kara dawowa wajen motar Kafin ya danne zuciyarsa ya fito cikin bakin glass din daya saka dan baya so ma Yan Matan wajen suga fuskarsa dan ko a can haka suke kawo kansu har mamaki yake Yana tunani yanzu Babu mata masu kunya.

Ta glass din fuskarsa yaga Mata sun zubo masa ido, daga mai gyara rigarta sai Mai zazzago da rigarta dan na fulaninta ya fito.

Gashi duk sun matse Rabin surorinsu a waje duk Kuma sun d’auka ta hakan zasu burge shi.

Waje daya ya kame ya zauna ya d’auko wayarsa ya hau latsawa dan  bama yaso ya Kalli Yan Matan da yaji ma Kona masa rai suka yi da ganinsu.

Bai san mai yasa Yan Matan hausawan Suma suka aro wani alada da ba tasu ba suka Ara suka yafa,banda kar yayi karya zai iya cewa ya dade Rabon da yaga nutsatsiyar mace.

Dan ko ta Ig nashi ma hoton da ke bayyana surarsu suke turo masa wai Kuma a haka suke tunanin zasu iya sace zuciyarsa.

Jefi jefi ya ringa dagowa Yana kallon yadda abokanansa da suka d’auki hakan a matsayin wayewa suka ringa rawa da Yan mata.

Wasu kuwa sai wucewa suke tayi ta gabansa Yana ganin Hade ran da yayi ne ma ya hana su karasowa wajensa.

Abokanan su kuwa da suka ga Babu ma alamar zasu samu fuska a wajensa suka kyalle shi.

Dan musamman Yan mata suka ringa kamun kafa da abokanansa dan so suke ko yayane Yama kula su suji Dadi.

Amma daga yadda ya hade rai da kwarjininsa yasa suka Kasa dosar inda yake

Yarima Zayyan kuwa ganin abun nasu bana karewa bane yasa ya mik’e a lokacin da idonsa ya sauka akan wata dake can gefe ta matse cikin riga da wani skirt bai Kai Mata gwiwa ba sai wani dogon takalmi da ta saka mai igiya.

Ba yadda ma zaka yarda bahaushiya ce balle ka kawowa kanka musulma ce.

D’auke Kansa yayi da yaga ta zuba masa ido tana kallonsa

Wajen da yayi parking motarsa ya nufa dan wajen Sha daya ne na dare gashi Kansa har ya fara masa ciwo.

Hararar da ya zabgawa Fu’ad yasa bai karaso wajen sa ba,dan yaga wasu Yan mata na gefensa sun Sha ado har sun gaji da alama wajensa suke san zuwa shiyasa suka je wajensa

Dan a Nigeria dai bashi da amini sama dashi,Halinsu ne dai bai zo daya ba.

Yana k’ok’arin tada motar yaga wanan yarinyar da take neman cinye shi da ido ta nufo wajen motarsa da saurinta.

Tana zuwa ta hau kwankwasa glass din motar

Mamaki ma ta bashi dan karfin halinta ma ya gani.

Zuge glass din motar yayi sultana kuwa ta Kara gyara zaman rigarta ta ware idonta da ta Sha kwallin magani ta tsuguna yadda zai iya ganin kirjinta dan Tunda taji labarin abokanan Yariman zasu hada masa walima kafin na gimbiyar ta shiga ta fita wajen ganin ta samu mai gayyatar ta,dan Zinatu ta balain lasa mata Zuma a baki tuni taji shamsu ya fice mata a rai,kwarin gwiwar da Zinatun ke bata yasa ta balain sa rai da Yarima da tasan idan har ta auree shi bata Jin akwai Wanda zai kaita Sa’a.

Bata fadawa Zinatu zata ma zo parrtyn ba dan ta karfin tuwo ma take hanata fita ta ringa kashe kudi wajen yi mata gyaran jiki

So take tun kafin goben da zasu je walimar Yariman ya fara ganeta kar ma yak’i ganin kyaunta idan ta saka material mai balain tsadan da Zinatun ta dinka mata,amma idan ya ganta a cikin kananan kaya yaga surarta da kyaunta Kila kafin goben ta fara sace zuciyarsa.

Wani irin Kallo Yarima Zayyan ya ringa mata da yasa sultana Jin kamar an like mata bakinta dan kwarin gwiwar da ta zo dashi yabi iska.

Manyan idonsa da ya zuba mata yasa ma ta ka sa magana

“Lafiya”?

“Zuwa nayi mu gaisa Saboda mu gaisa da Kai kawai nazo partyn nan”

Sultana tace cikin dan rawar murya tana ware idonta sosai yadda kwallin da Zinatun ta karbo mata zaiyi tasiri akansa.

Sai da ya gama kare mata Kallo ya fara magana Yana “Tunda zu da na ganki na sa a raina ke ba bahaushiya bace ba kila wata arniyar dai suka gayyato ga mamakina sai naji kinyi Hausa da ga kuma yadda kika yi magana kamar dai ke din musulma ce,kin d’auka da wanan shigar da bayyana surarki da kika yi shi zai saka ki burgeni”?

Girgiza kai Yarima Zayyan yayi ya Kara jefa mata wani hararar Yana “Gwara na koma ga Allah ba Aure idan har irinku  ke yawo”

Daga haka ya ja motarsa ya bar Sultana da ta kasa Koda motsawa sai motarsa da ta bi da ido.

Shigar jikinta kawai take kallo tana mamakin mai aibun shigar nata

Ta d’auka ma shigar nata burge shi zaiyi tunda daga kasar waje ya dawo sai gashi bata ga alamar burge shin ma tayi ba sai kyankyaminta da ya nuna Yana yi.

Har ta koma gida a sace dan a sace ta fito jikinta sanyi yayi sai a yanzu take nadamar ma zuwa parrtyn dan ta bala’in kamuwa da kaunar Yarima Zayyan din tana tsoron gobe ya ganeta ma ya ce ya ba zai aureta ba.

Sule

    Jakar kudin da Hanne ta ajiye a gabansa kawai ya zubawa ido bayan ya kirga kudin ciki

Ya kasa yarda wai wanan daruruwan ta silar kunshi aka bawa Ameera,wai kamar.Ameera ce da yiwa matar sarki kunshi har tana gayyatar ta zuwa wajen Walima

Muryar Hanne ya katse mata tunanin da yake “Mallam kasan ko abinci na kasa ci tunda suka dawo wallahi na kasa yarda wai matar sarki Ameera tayi wa kunshi,na kasa yarda wai wanan ubann kudin a dare daya Allah ya bamu”

“Hanne  sai  a yanzu na gane ni din mai arziki ne ba talakan da Yaya Habu ke min Kallo ba,arzikin nawa ta hannun Ameera Allah yamin.

Yanzu mai na nema na rasa a rayuwata inama Gwaggo Kalau take taga d’aukakar da Ameera tayi wai matar sarki guda Ameera taje tayi wa kunshi.

Hanne da Sule haka suka ringa magana cikin farin cikin suna kwararawa Ameera da bata ko Bude kudin da aka bata ba ta bawa Hanne addu’a.

Ameeran

Ita kanta gani take kamar a mafarki taje tayi wa matar sarki kunshi bata tsaya iya nan ba wai har gayyatar ta tayi waliman da taji tana balain fargabar zuwansa dan gani take Sam bata  kai ma taje waleemar ba,duk da manyan ma da take wa kunshi sun Sha gayyatar ta zuwan ne kawai ba tayi dan Allah ya mata farin jinin.

Har garin Allah ya waye zuciyarta cike take da fargaba dan wajen hudu za’a fara waleemar Hanne kuwa tace mata sai taje dan rashin zuwan nata kamar tayi wa Gimbiyar rashin kunya ne banda haka da bata Jin akwai abinda zai saka taje wajen da take ganin babu mai zuwa sai Wanda ya Isa ya kuma Kai.

Tana da kaya masu kyau a matsayinta ta wacce ke dinki hakane yasa ta ringa duba kayan daya dace ta Saka har sai da ta samu wani atamfarta da aka yiwa adon less a jiki da dan tsadarsa ta siye shi ta masa dinkin doguwar riga.

Dinkin da ta masa yayi balain kyau dan bata fiye jiki ba shi yasa idan har za tayi dinki take dinka bubu saboda ta dan ciko ba kuma taso taga kaya ya matseta.

Ko da ta saka kayan ba wani kwalliya tayi ba dan kunyar ma kwalliya take ta shiga cikin jama’a sai taga kamar kowa ita yake Kallo.

Sosai tayi kyau fuskarta ta ringa sheki saboda da Sabulun Mg take amfani shekara wajen biyu kenan,da taga tallansa a cikin wani littafi kamar wasa ta gwada siya,daga fara amfani dashi ya fito Mata da asalin kalarta dan ita ba fara bace ba ba kuma baka ba sai Sabulun ya taimaka wajen fito mata da ainihin kalarta kamar irin bakaken turawan nan.

 (08062991549 Mg skin care has a package for you if you want to be glowing and you want to knw your skin type don’t hesitate to chat her up she got you a covered)

Hanne kuwa kallon Ameeran kawai take tana sakin murmurshi dan tayi balain kyau kamar irin yaran masu kudin nan haka ta fito amma Ameeran kuwa ji take kamar ba zata iya zuwa ba,dan gani take wajen waleemar yafi karfin zuwan irin ta.

Dak’yar ta d’aure wajen Samawa kanta kwarin gwiwa tayi shatar bolt din da zai kaita har can wajen da ba boyayyen waje bane dan Karamin katin dake cikin envelope din shi zata bayar da zai Saka a barta ta shiga,banda Hanne ta dage taje tasan ba ma lailai gimbiyar tasan ba ta zo ba.

Zinatu

         Musamman ta kira Mai kwalliya aka zo har cikin gida aka tsantsarwa sultana kwalliya kamar wata Amarya.

So take ya zama Babu ma wacce ta Kai sultana kyau a wajen.

Dan ba Karamin kudi  ta kashe wajen gyara Sultana ba,dan gyaran jiki tasa aka yi mata Sosai kamar wata Amarya

Abinka da fara sai sultana tayi ta wani d’aukar ido,hararo kawai ma Sultanar take a matsayin matar Yariman dan bokan ya bata tabbacin fa sultana na hada ido da Yarima  sai ya Aure ta zai samu nutsuwa,sai da ta sakarwa bokan kudi sosai har da dan turare ya bata da sultanan zata shafa.

Bata ma damu ta hadu kamar yadda ta damu a gama da Sultanar ba.

Sai da aka gama yiwa Sultanar kwalliya kamar ma ranar Aurenta

Itama ta mik’awa Mai kwalliyar fuskarta ta mata kwalliyar.

Motar Habun da yafi kowane tsada tasa driver yafito dashi suka kame a baya suka nufi wajen da aka hada waleemar.

Kamar yadda Zinatun tayi tsamani.

Manyan masu kudine kawai suka ringa parking da wasu labarinsu take ji ba wai tab’a ganin su tayi ba,sosai take Jin kanta a sama dan itama wankan gwal tayi kamar yadda tayi wa sultana.

A Kuma kallon da take yiwa Yan Matan wajen gani take duka Babu wacce ta kai sultana haduwa daga yadda Yan mata suka cika wajen tasan duk da biyu suka zo kowace so take taga ta samu Yarima Zayyan yace Yana Santa

Sanin ma duk wahalar da kansu suke saboda bokanta da ya bata kwallin da Sultana ta rambada yasa ta saki murmurshi.

Kafin Gimbiya ta fito ta samu dak’yar ta kusa hannunta cikin na sultana ta shiga wajen Gimbiyar dan gani take idan aka fara Taron kanta ya dau zafi bama zata san sunzo ba balle har taga Sultana tayiwa Yariman sha’awar aurenta

Duk da ba saninta gimbiyar tayi ba haka ta kutsa ciki ta zub’e ta hau Kai gaisuwa itama sultana na Kai wa Gimbiyar gaisuwa da ke ta daga hannu cikin fara’a dan Sam bata da wulakanci haka Kuma duk yaranta dan gani take Wanda bai gaji arizki ba shi ke wulakanta mutum amma idan har ka gaji arizki dole kasan darajar mutum.

Zinatu kuwa Yar kauye ta koma da sultanan suka hau kallon d’aula kowace da tunanin da take yi a zuciyarta

A hankali masu zuwa gaida gimbiyar suka ringa yin waje.

Jakadiya ta ware murya akan a watse yanzu Gimbiya zata fito itama

Zinatu kamar kar ta tashi haka taji amma haka ta mik’e hannunta cikin na Sultanar suka yi wajen hall din.

Sai da suka shiga ciki taji tama raina kanta gabad’aya wayanda ta dan Sanin ta zauna a gefensu sultana kuwa na daga wajen da Yan mata ke zaune tana yiwa mutane kallon daidai.

Gimbiya tare suka shigo da Yarima.

A wajen da aka tanadawa gimbiyar ta zauna fuskarta d’auke da murmurshi

Yarima da ya sha nadi Shima cikin fararen kaya ya zauna a wajen da aka tanadar masa.

Zinatu kuwa haka ta zuba ido taga ko Yariman zai Kalli Sultanar

Duk da ba lailai ta iya ganewa ba saboda nadin daya Sha.

Zinatu kuwa ji  take kamar ta d’auki sultana ta Kai ta gaban Yariman

Jakadiyar da ta hango hannunta rike da wata ya ja hankalinta dan wajen da Gimbiya ke zaune ta nufa da ita

Koda suka isa wajen Gimbiyar sai taga yarinyar ta zube tana Kai gaisuwa.

Haka kawai taji gabanta ya yanke ya fadi ido ta Kara gwalewa tana san taga wacce wanan din

Sai taga Gimbiya ta zuro hannunta ta cikin alkyabarta ta bubuga bayan yarinyar da wani abun adon dake hannunta.

Kafin jakadiya ta kara rike hannun budurwa da kanta ke kasa ta nufi wajen da ta lura manyan mutane kawai aka warewa su zauna

Zinatu har da dan mik’ewarta dan so kawai take taga waccece haka mai matsayin da zata zauna wajen manyan mutane.

Sai da ta zauna jakadiyar ta bar wajen Ameera ta dan dago da kanta Zinatu ta gwalo ido tana “Wacce nake gani haka”?

Sultana kuwa ta mik’e ta loka Ashar tana “Ameera”

Yarima kuwa ya furta magana daga bakinsa zuwa kunnensa da  “Har yanzu akwai mata masu kamun Kai haka wacece yarinya nan”?????…..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 26*

       Zinatu

      Hannunta ta Kai ta hau goge idonta tama manta da make up din fuskarta dan sai take ganin kamar dai ba Ameera yar gidan Sule ta hango ba,Sharrin make up din da aka mata kila ya sa ta ganin kamar Ameeran ta hango,dan tasan ko k’ofar wajen Ameera bata Isa zuwa ba balle wai har ta shigo da Rakiyar Jakadiya Gimbiya wai har ta Santa a kai ta wajen da manyan mutanen ke zaune ba

Sai dai har ta goge idon nata,ta cire guntun eyelashes din da ta saka dan gani take kila har gashin idon ma yasa ta rashin ganin sosai.

Ameeran ce dai a zaune tamkar Yar wani mai kudin,ta kuma saje da Yan mata masu Kyau da aji

Kanta a kasa kamar ta Saba da zuwa irin wanan wajen sab’anin Rabin wayanda ke wajen da suka waware ido suna bawa idonsu abinci.

Bama tasan mayafinta ya sauka daga kafadarta ba dan ji tayi kanta na hayaki da jikinta ke rawa da tarin mamaki da tambayoyin daya cike mata zuciya na yadda aka yi Ameera ta samu zuwa waleemar da har wai Gimbiya ta Santa ba iya nan ba aka mata wani iirn karramawa dan ta wajen dai da take hango Ameeran matar Govnor garin na zaune a wajen.

Hannunta da taji an ruko ya dawo da ita hayyacinta ta d’auke idonta daga kallon Ameera da bata ma san tana yi ba.

“Lafiya Hajiya Zinatu na ganki a tsaye kina gumi”?

Zinatu kasa magana tayi ta waiga wajen da Sultanar ke zaune sai ta ganta a tsaye itama a cikin irin yanayin da take ciki dan itama daurin da aka mata yayi nashi wajen hannunta kawai ta saka a bakinta irin na takaicii dinan duk Kuma wajen Ameeran suke Kallo bama su san abubuwan da ake gudanarwa ba.

Zinatu dak’yar ta taushi zuciyarta da taji ya kama da wuta ta zauna tana share gumi,tama kasa hada tunanin ta waje daya

Cikar da wajen yayi yasa Sultanr ta kasa Isa wajen Zinatun

Banda kar ta jawo hankalin mutane kansu ji take kamar ta isa wajen Ameeran ta tambayeta uban me tazo yi,uban waye ya gayyace ta.

Kasa hakuri tayi ta zuge Jakarta ta d’auko wayarta

Ta hau Kiran Zinatu a waya

Zinatu kuwa da kwallin idonta duk ya cabe saboda goge fuskarta da ta ringayi ta d’auki wayar sultana kuwa ta hau magana cikin dan ihu tana “Hajiya kinga wa nake gani kuwa wai ko dai idona ne ni kadai”

“Ameera ce Sultana Ameera yar gidan Sule itace dai nake hangowa a wajen manyan mutane”

“Hajiya jakadiya ce fa ta shigo da ita da alama fa Gimbiyr ma ta santa hajiya ko dai ita Yariman ke so karki manta yadda muka kwashe da ita a makaranta haka ta ringa kwace duk abinda ya dace ace na samu”

Zinatu sai a lokacin taji gabanta yayi wani Irin faduwa cikin tashin hankali tana “Sultana tofar da bakin yawu mai Yarima zai yi da Ameera?ai karatu daban Aure ma daban Taya zai auri Ameera akwai dai dalilin daya sa ta zo nan amma ba dan Yarima ba dan Yarima bashi da Mata sama dake sultana kinsan nawa na kashe kuwa ki koma ki zauna karki dagawa kanki hankali wani abu daban ya kawo Ameera wajen nan Kuma zan gano komai tazo nema,zan gano yadda a kayi tasan Gimbiya”

Duka cikin hall din suke magana.

Sultana kuwa ta kashe wayarta tana dan jin hankalinta na kwanciya

Ko su da suke da kudi Gimbiya bata san su ba taya zata san da wata Ameera dake can loko.

Yareema kuwa kallon Ameeran da hankalinta ke kan wayar kawai yake duk yadda yaso ya d’auke idonsa a kanta sai yaji ya kasa dan gani yayi ta fita daban a cikin irin Yan Matan da yake gani,Yana kallon yadda idon mata ke neman fadowa Kansa,amma tunda Ameera ta shigo bata ko Kalli wajen da yake ba,ba kuma Wanan ba kalle kallen da wasu suka ringayi da yasan wasu da yawa kan yi saboda tsaruwar guri,amma Ameera bata ko Yi wanan kalle kallen ba,wani irin nutsuwa da Aji yake gani a tattare da ita, Tun a jiya da ya ganta ya ga nutsuwa da kamalla a tattare da ita.

Bai kawo akwai Matan da suka Yarda da natural dinsu batare da sun canza hallitar fuskarsu ta hanyar kwalliyar dake Maidasu ma wani hallita na daban kamar dai yadda duka Yan Matan da suka samu zuwa Taron fente fuskarsu wasu kamar Yan tsana haka suka koma,wasu Karin gashi an bazo dashi har baya wasu farce ma suka saka duk da sunan wayewa,duk da kwalliyar da wasu suka yi kana iya ganin yadda hannunsu yayi dabara dabara na bleaching,Wanda duk Ameeran sai ta zama opposite din abinda yake gani bai kawo akwai irinta ba har yanzu.

Yaso ta dago kanta ko Yaya ya sake ganinta amma bata dago ba wayarta take dannawa ko da ta dago kanta nan da nan take mayarwa kan wayar sai ya lura kunya ce ta sakata hakan,daga yadda ma take kasan ba’a sake take ba.

Ko ruwa ta kasa d’auka ta Sha balle ta tab’a lodin Abubuwan da caterers suka dora akan tebur din.

A nutse yaga ta mik’e kanta a kasa ta Isa wajen Gimbiya ta zub’e zuwa can sai ta mik’e tayi hanyar waje.

Gyaran murya yayi dogarin dake gefensa ya sunkuyo da sauri

Yareema kuwa yace “Ina so nasan wace ce wancan yarinyar da ta zo fita Ina so na San komai a kanta”

“An gama ranka ya Dade”

Dogarin yayi waje da sauri

Zinatu

Har tuntube ta hau yi wajen mik’ewa tabi bayan Ameeran da ta ji ta gaji da zaman wajen dan duk a takure take jinta dak’yar ta iya zaman Yan mintuna batare da ta ko Kalli Abubuwan da aka jera a gabanta ba ta nufi wajen Gimbiyar ta zub’e wajen yi mata sallama.

Gimbiya kuwa ta saki murmurshi ta gyada mata Kai

Ameera kuwa tana fita taga wani dogari ya bude mata mota sai taji ma ta tsorata.

“Gimbiya tace a maidaki gida”

Hakan da taji yace yasa ta nufi bayan jeep din da aka bud’e mata tana ta mamakin kirkin da taga gimbiyar ta mata dan tana isowa ta kasa shiga cikin hall din,har ta juyo dan ta koma dan ji tayi ma ta yaudari kanta idan tace zata shiga wajen da masu kudi kawai taga suna shiga sai ganin Jakadiya tayi a gabanta tana ai yanzu Gimbiya ke tambayarta tazo su shiga daga ciki,iya nan bai isa ba gashi tasa a kaita gida.

Ta saka kafarta kenan zata shiga cikin motar  taji muryar Sultana da Zinatu sun hada baki wajen kwalla mata kira

Juyowa tayi tana kallonsu.

Taga har da dan gudunsu dan kawai su iso wajen da take,yadda fuskar su biyun ta damale da kwalli gasu kamar a firgice yasa ta sakin dariya har tana rufe bakinta da hannu

Sai da taga sun kusa isowa wajenta ta shige bayan motar dogarin kuwa ya rufe k’ofar.

Tasan rashin mutunci zasu mata bata ga amfanin ta tsaya saurarensu ba,dan tasan ko Yaya ta hadu da ko sultana ko Ameera sai ranta ta baci.

Tana Kallon su ta cikin glass yadda suka tsaya cirko cirko har motar ta bar harabar wajen.

Sultana kuwa ta saki jakar hannunta tana “Hajiya kiga fa dogari ne ma ya tafi rakata gida, kiga fa kaita gida ma za’ayi,ya zaki ce ba ita Yareema ke san Aura ba,Ameera ce zata tab’a bari nayi abin arziki ai ba zata tab’a bari ba.

a  makaranta haka ta dage sai da ta wuceni yanzu ma a mijin tace ban isa ba kiga fa saboda ta taki wani Abu kiranta muka yi ta juyo ya Saka mana dariya ta hau motar tayi tafiyarta”

Zinatu da ke Jin kamar zata zauce dan ji tayi ma cikinta na Murda mata idan har zargin da Sultanan keyi ya tabbata tace “Sultana zan iya kashe Ameera idan har hakan ta kasance dan yarinya nan tun tana karama ta ke bani ciwon kai ki barni nayi bincike”

“Ai a garin na barki kiyi bincike sai dai kiji an daura auren”

Zinatu daurin dankwalinta ta gyara ta goge fuskarta da sultana ta ringa yiwa dariya,sai da ta goge tacewa sultanar idan ta gama dariyar itama ta gyara nata fuskar.

Sai da itama ta goge fuskar nata suka nufi cikin hall din cikin Zinatu har lokacin karta mata yake.

Jakadiyar da ta hango yasa ta saki sultana ta karasa wajenta da gudu

Tana zuwa ta rike hannun jakadiya tayi kasa da murya tana ta taimaka mata tambayarta kawai za tayi

Ganin jakadiyar na mata wani irin Kallo yasa ta bud’e Jakarta hannunta na rawa ta d’auko bandir din dubu ta damka Mata a hannu tana “Dan Allah wanan yarinyar da kika raka wajen Gimbiya waccce ita”

Jakadiya sai da ta cusa kudin a jikinta ta jefawa Zinatu tambaya da wacce yarinya take nufi dan tana da balain san kudi,ko jiya sai da ta raba Ameera da wani abu

Zinatu kuwa ta hau yi mata kwatancen Ameera jakadiya ta hau gyada Kai tana “Ooo wanan yarinya ai kunshi take yi kunshi tazo tayi wa Gimbiya sai Allah ya hada jininsu ai yarinya nada hankali”

Zinatu bata iya magana ba sultana tace “Ahap ruwa ai baya tsami banza”

“Shikenan”?

Gyada kanta Zinatu tayi jakadiya kuwa ta shige cikin hall din

Zinatu da taji kanta na Sara mata ta juya sultana da ke Jin kamar ta fashe ta hau magana tana “kin dai ji da kunnenki Gimbiya tana san Ameera itace zata tallata Ameera a wajen Yareeman kiga fa yadda tasa a Maida Ameera gida ai ba iya kunshi yasa ta mata haka ba wallahi so take ta hadasu Aure,ni shikenan wanan tsinaniyar yarinya nan sai ta fini komai”

Zinatu bata ce mata komai dan tunani kawai ta tafi ta hau bayan motar da suka zo dashi,Sultanar itama ta hau driver ya jasu suka tafi.

Koda suka koma gida daga Sultanar har Zinatun kasa zaune suka yi suka kasa tsaye

Ganin sultana na neman kuka yasa Zinatu ta hau kwantar mata da hankali.

Zinatu washegari da sassafe ta nufi wajen bokanta Koda ta isa ta zayyana masa zargin da take,sai ce mata yayi ai fa yareema bashi da Matar Aure sama da Sultana,suje su san dabarar da zasuyi Sultanar ta samu hada ido da Yareeman,ba zai Kara samun nutsuwa ba har sai ya aureta shi bai ga alamar wani Aure a tsakanin Yareema da Ameera ba.

Zinatu haka ta taso tana dan Jin sanyi a zuciyarta amma kasan zuciyarta sai take ganin kamar dai zasu iya wayar gari Ameera ta auri Yareeman tunda Gimbiya na santa.

Taya ma zata bar Yarima ya auri Ameeran da ta mata rashin kunya ta Kalli cikin idonta tace mata tafi karfin Auren Amjad,idan har ta auri Yareeman hakan ya tabbata ta dai Fi karfin Amjad din kenan.

Girgiza kanta tayi tana hararo yadda zata sume idan aka wayi gari wai Ameera da Aure a gidan sarauta,wanda hakan na nufin Sule da Hanne zasu yi arziki har su hada kansu da su.

Ko abinci kirki kasa ci tayi tana ta zabga tunani,ta dai fadawa Sultana duk yadda tayi da bokanta

Sultana kuwa kamar zata ce mata tafa hadu da Yariman sun hada idon amma wulakanci ya mata sai kuma ta fasa tana tunanin kila dan daddare ne shiyasa kwallin baiyi tasiri ba.

Zinatu

   Sai da ta kira Amjad da wani layin ta samu ya d’auka dan tana ta kiransa da layinta amma yak’i d’auka

Yana dagawa ta hau masa kirari tana “Haba babana waye ya gaya Maka ana fushi da uwa yanzu akan Ameeera za kayi fushi dani?

Ganin Amjad bai ce komai ba ba kuma shi da niyyar magana yasa tace “Toh albashirinka gobe zanje gidan Sule na bashi hakuri da kaina zan nema Maka auren Ameera sai na tabbata da sun baka zan baro gidan”

“Dan Allah da gaske kike Hajiya”

“Wallahi da gaske nake ba wasa nake ma ba dan haka kama dawo gobe asubanci zanyi dan duk na gane kuskurena ya kamata ace ka auri Ameera”

Ihu Amjad ya saka cikin tsananin murna Yana jibi zai dawo Nigeria

Zinatu kuwa ta saki murmurshi ta kashe wayarta ta haye sama

A kan gado ta tarar da Habun Yana ta latsa laptop dinsa da wani zungureren takarda a gabansa.

Zinatu kuwa ce masa tayi ya bata hankalinsa magana zasuyi

Habu sai da ya karasa shigar da lissafin da yake ya rufe laptop din

Zinatu kuwa kamar gaske tayi rau rau da ido tana “Alhaji kwana biyu kenan Ina kewan Amjad na kasa yarda wai akan an Hana shi auren Ameera ya zabi ya bar kasar nan,yaron nan fushi yake dani sosai,bana Jin dadi Ina san farin cikinsa,tunda har ya dage Ameera yake so zanje gidan gobe nayi wa sule magana da kaina Ina ga idan yaga naje zai iya bawa Amjad din Auren Ameeran”

Habu wani irin murmushi ya hau saki cikin tsananin farinciki Yana “A gaskiya kin gama min komai dan nuna miki ne kawai bana yi amma Ina cikin damuwar rashin Amjad.

Duk da haushin Sulen da nake ji amma saboda Amjad zan biki muje dama Ina ga saboda ke ya dage ba zai bada auren Ameeran ba amma idan yaga munje dake dole ya yarda kin amince da Auren”

Da haka Zinatu ta kwanta tana sakin murmurshi ita kadai dan tana ganin hakan kawai za tayi ta hana auren idan ma da gaske Gimbiya ke san hada Ameera da Yareema.

Ameera

     Labari kawai take bawa su Abba sule akan yadda aka gudanar da waleemar.

Bakinsu duk d’auke da murmushi dan tun jiya Ameera ke ta basu labari

Shi Kansa Sulen  irin yadda Gimbiyar tayi wa Ameera yayi matukar bashi mamaki dan bai kawo wai bayan taje zaa kawo ta har gida ba

Zasu iya awa biyu Yana Hira da yaransa da Hanne dan sosai ya jawo yaransa jikinsa dan ya ringa Sanin halin da suke ciki

Duk da Hanne ta bashi labarin duk yadda akayi sai da ya sake tambayar Ameeran da safe bayan sun karya ta hau kuwa bashi labari cikin tsananin murna tana ita da ta sani ma bata karbi kudin kunshin ba

Sule na k’ok’arin magana sai sallamar Habu suka ji da Zinatu

Baki a sake suka ringa binsu da Kallo bayan sun amsa sallamar ciki kuwa har da Ameeran da ta gama sawa ranta wani rashin mutunci ne ya kawo su inda ta Sha alwashin a yau zata rufe idonta har Habun ta wanke dan talauci ba hauka bane

Ga mamakinta Zinatu wajen da take zaune ta nufa da zuwanta ta rungumeta tana “Ki yafe min Ameera na gane kuskurena duk shaidan ke san cin galaba akanmu ya raba kanmu ya raba zumuncinmu”

Habu ya karbe da yiwa sule bayanin abinda ke tafe dasu ya Kara da a manta da duk abinda ya wuce

Zinatu kuwa ta kira sunan Sulen idonta cicike da kwalla tana “Wallahi har a cikin zuciyata nayi nadamar duk Abubuwan da suka faru dan Allah ka bawa Amjad Auren Ameera”

Sule murmurshi kawai ya ringa saki har sai da ya ga duk sun gama magana ya Kalli Zinatu Yana “Zinatu nasanki tamkar yunwar cikina,aurenki kawai Yaya Habu yayi amma bai kaini Sanin halinki ba akwai wani babban dalilin daya sa kika zo nemawa Amjad auren Ameera da kanki akwai wani babban dalilin daya sa kika taka kafarki a gidanan akwai wani burin naki da kikeso ki cimma abinda baki sani ba shine idan zaki rainawa kowa hankali ni Sule nafi karfin rainin hankalinki kamar yadda na fada a baya “Ameera Koda ta rasa mijin Aure ba abinda za tayi da Amjad,Ameera tafi karfin Auren Amjad dan haka idan abinda ya kawo ki kenan kika taso Yaya habu gaba kuka zo zan iya cewa zaku iya tafiya dan ko a mafarki ba zan bawa Amjad Auren Ameera ba”

Zinatu kallon Sule kawai take tana Jin kamar ta d’auki wuka ta soka masa ta kasa yarda yadda ta kwantar da kanta tana Jin kamar ta rusa kuka saboda kaskantar da kanta da zata yi wajen Sule zai iya rufe ido ya wulakantata.

Habu kuwa mik’ewa yayi a fusace Yana “Har Kai ka Isa ka wulakanta mu Sule waye Kai har mai ka d’auki yarka da kake san wulakanta mu”?

“Ni Sule talaka wajena dai kuka zo nemawa danku Aure na kuma Hana yanzu sau biyu kuna zuwa nema a wajena idan kudinku duk zai muku amfani a duk inda kuka je a wajena kudinku ba zai tab’a muku amfani ba ba zan bawa Amjad Auren Ameera ba kalas”

Daga haka Sule ya mik’e ya shige daki.

Take duk suka watse daga palon suka bar iya Zinatu da idonta ya kada yayi jajjur da Habu dake vibrating shi kadai.

Gimbiya

      “Ammi kinsama min matar Aure kuma dan Allah karki min haka wallahi nima na samo yarinyar da ta kwanta min dan Allah kar ayimin auren dole Ammi”

Yareema yace kamar zaiyi kuka

Gimbiya kuwa ta saki murmurshi tana “kasan ba zan tab’a zaba maka macen da Bata dace da rayuwarka ba,sai da nayi bincike na tabbatar da hankali da nagartar yarinya nama sha’awar aurenta Yareema kai din mai biyayya ne nasani ka daure Wajen karbar zabina ba zaka yi nadama ba”

Yareema kasa magana yayi dan baisan yadda zai fahimtar da ita kamuwa da yayi da kaunar Ameeran da ya gama Sanin komai a kanta hoton da Gimbiya ta turo gabansa tana “Kaganta nan bata da aibu”

Yasa ya d’auki hoton da sauri hannunsa na rawa yace “Ammi wanan ce wacce kika samo min din”?

“Itace Yareema”

“Alhamdulillah Ammi alhamdulillah itace wacce nace miki nima Ina so din”

“Alhamdulillah zabin da kayi yayi Yareema sai dai fatan Allah ya tabbatar muku da alheri ba za’a tsaya bata lokaci ba gobe zaa je nema maka aurenta”…..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 27*

        Zinatu tsananin bakin ciki yasa suna baro gidan Sule ta rushe da kuka,dan sai da ta daure Wajen tausar kanta kafin su zo din,dan taga alamar idan ba haka tayi ba tana ji tana gani sai dai ta ji labarin Yareema ya auri Ameera,dan ta yarda da zargin da  sultana keyi akan ba iya kunshi ya kai Ameera gidan ba kila asirin dai maganin farinjinin da ta sa a ranta cewar Hanne ta karbawa Ameera tun tana yarinya shi yayi aiki akan Gimbiya.

Habu kuwa sai masifa yake Yana zagin Sule da cewa ai su taimaka musu ma zasuyi da zai hana Amjad Auren Ameera,Amma sule da alama bashi da rabon Arzikin ne idan Amjad ya dawo shi ma sai ya masa dole akan ya hakura kawai da Ameeran

Zinatu kuwa da mayafinta ta goge hawayen dake ta zubo mata na zallar bakin cikin Rashin mutuncin da Sule ya Mata,da Kuma zullumin kar ta wayi gari taji labarin Ameera ta kai inda take burin taga sultana ta Kai Allah yasan zuciyarta bugawa kawai zai yi.

“Bansan Mai yasa kanin ka yayi min irin wanan tsanar ba yanzu mai laifiin Amjad da zai ce ba zai bashi Auren Ameera ba,yanzu har akan ya bawa Amjad Auren Ameera gwara ya bawa bare kenan”

“Kansa fa yayi wa hajiya dan haka ki daina wani damun kanki idan Amjad ya dawo zan sake fada masa irin rashin mutunci da Sulen ya mana idan Yana da zuciya ai ya hakura da Ameeran da na rasa ma mai ya gani a wajenta yake so ba bayan ga Yan mata nan birjiki yaran manyan mutane yanzu mai Ameera zata fadawa Yar gidan Ambassada nan”

Zinatu hawaye ta cigaba da zubar wa.  Habu kuwa ya  ringa rarrashinta Yana Jin wani irin haushin sule da nadamar ma zuwan da yayi.

Zinatu ranar ko baccin kirki ba ta iya yi ba,dan duk Abubuwan da taso ace sultanar ce ta samu tun suna Yara Ameeran ce kawai ke ta samu,ta balain kashe kudi da kwallafa rai akan hada sultana da yareeman

Duk da wani zubin takan ji hankalinta ya kwanta idan ta tuna maganar boka akan yareema bashi da matar Aure sama da sultana,dan shekaru sama da Sha biyar duk aikin da ya mata Yana yi kawai bata san mai yasa Wanan karon zuciyarta ke cike da fargaba ba.

Washegari da sassafe taso suje wajen bokan da sultanar dan akwai ayyukan da take so ya mata da sune kawai zai saka taji sanyi a zuciyarta dan ta kasa manta wulakancin da Sulen ya Mata ta kasa manta rashin kunyar da Ameeran ta mata

Sai aka samu akasi driver nasu bai zo ba ta kuma kira wayarsa ya ce an musu rasuwa bata Jin zata iya tuki zuwa can.

Duk ranta ba dadi dai suka karya da yaran gabad’aya akan dining

Habu kuwa nata shigar da lissafi a laptop dinsa.

Yaran lokacin duk sun baje daga palon wasu ma sunyi waje.

Yadda yaga Zinatu tayi shiru yasa ya dago Yana “Hajiya wai har yanzu ba Zaki bar cire wanan abin a ranki ba”?

“Hmmm Alhaji kenan taya zan iya manta rashin mutuncin da kaninka yamin yanzu fa gobe Amjad zai dawo Mai zamu ce masa”?

“Hakuri zamu bashi mana tunda sule ya dage ba zai bashi Auren Ameera ba ana dole ne”

Zinatu girgiza kanta tayi tana ai shikenan.

Habu kuwa ya dago Yana “Kinsan wanan katoton gidan dake kallon gidanmu da nace miki ina zargin na wani dan siyasan ne na macece”

Ido Zinatu ta waro tana “Kana nufin gidanan dake kallon gidanmu na mace ne”?

“Wallahi na mace ne dan ni kinsan Ina ta so nasan waye mai gidan dan irin masu kudin nan zaka so ka kula alaka dasu,ko dan ta Fanin kasuwancin ka toh duk sai na d’auka iya iyalin nasa ne suka riga shi tarewa ko kila dai Mai gidan baya kasar wallahi sai Jiya wani ke fadamin wai macece mai gidan mijinta kuma wai ya rasu ke kinga yadda yake lissafin kudin matar yace macece kamar Maza wai yanzu haka ma gidajen manta a garin nan ba zasu kirgu ba”

“Kai Alhaji Yanzu gidanan da kyaunsa ya dakushe kyaun gidajen mu macece mai gidan”?

“Wallahi na mace ne nidai nayi mamaki nima da naji wai macece ta iya kera irin wanan gidan, ni yanzu ke zaki shishige mata kiga ko da kwangilar da zaki iya samo mana daga wajenta”

“Samha fa tana shiga gidan so nake nima idan an kwana biyu na shiga dan Hulda da irinsu akwai Dadi,aikuwa a yanzu zan fake da Samha na shiga gidan dan zan so ganinta wallahi”

Murmurshi Habu yayi da yaga yadda Zinatu ta ware ta hau hira har tana sake fita waje ta Kalli gidan da Babu kamarsa a layin ai dole ma ta samu sabuwar Kawa

Ta koma cikin gidan suka cigaba da hira da Habu.

Har ya karasa Abunda yake yi ya fito dan ya tafi.

Yana fitowa da motarsa yaga An Bud’e gidan da yake saka shi ganin munun gidansa,dan gabad’aya shekara guda kawai da gina gidan,dan gidajen mutane hudu matar ta siye aka baje shi aka tayar mata da ginin dan a yadda ma yaji labari a guriin makotan nasa da su suke bashi labarin ma ai macece ta siye gidajen nasu, duk haduwa da tsarin gidajen haka aka baje aka tashi gini mai balain kyau da ya hadiye Miliyoyin kudi, kawai yasa a ransa koma wacce mai gidan mijinta ba Karamin gaggarumin mai kudi bane kafin ya rasu kila a irin gadon da ya bari itama ta samu kudi haka.

Samha da ya ga ta Fito da wata yarinya da bata Fi shekara goma sha hudu ba yasa ya tsaya dan ya tuna Zinatu tace Samha na shiga gidan ko baa fada masa ba da alama yarinya ce kawar Samhan.

Ganin Samha na Nuno motarsa yarinya Kuma dake sanye da wani riga da skirt sai wani hula da ta saka ta kuma dan fi Samhan tsayi ta saki murmurshi suka nufo wajensa

Glass din motarsa ya zuge Yana kallon su har suka karaso Samha dake rike da hannun yarinya da tayi zubi da irin bakaken turawan nan gata da balain kyau yasa ya zubawa yarinyar ido Yana Jin kirjinsa na dan canza bugu,dan sai yaga ta masa yanayi da wacce ya sani amma ya manta koma wacce.

“Daddy kaga kawata Imiii”

“Immi here is my Dad”

Immi kuwa ta dan rusuna ta gaida Habu da harshen Turanci,Habu kuwa ya amsa cikin sakin fuska Yana ta so ya tuna wacce yarinyar ke kama da “cikin murmushi ya tambayi Samha da “da kawar taki bata  Jin Hausa ne”?

“Bata ji daddy a shekarar nan fa suka dawo Nigeria amma duk a kasar waje aka haifesu daddy baka ga kannenta ba masu kyau Yan biyu”

Murmurshi Habu yayi ya tambayi Immi da murmurshi kawai take ta saki da ya mamanta

“Immi na k’ok’arin magana yaga wasu Yara daga k’ofar gidan cikin shigar su iri daya kyawawa dasu suka hau kwallawa Immi kira”

Kallonsu kawai yake Yana Jin dama su karaso dan a rayuwarsa Yana balain San Yan biyu take suka tuna masa da Shamsiyya margayiya da yayi ta tunanin cikin jikinta na Yan biyu ne Allah bai yi zasu rayu gabadaya ba

Take yanayin sa ya canza dan idan har zai tuna shamsiya sai ya rasa mai ke masa Dadi.

Da ido ya bi Immi da ta kwasa da gudu ta nufi cikin gidan,wata dake sanye da kamar uniform tazo ta ja hannun Yan biyu Immi itama ta bisu a baya suka rufe k’ofar.

Bai ma san mai Samha ke fada ba saboda tunanin da ya tafi.

Sai da suka shige ya cewa Samha ta koma ciki shi kuma yaja motarsa ya tafi.

Zinatu

   Sultana ki daina dagawa kanki hankali zaki fa Auri Yareema sai dai idan bani ce na haifeki ba”

“Tun muna Yara Ameera ke samun nassara akaina Hajiya mafarkin nan da nayi da ta auri Yareema ni na fada Miki sai ya tabbata yarinya nan fa mayya ce Kuma na lura ni din ce bata so na tab’a finta da Komai”

“Ina da wacce na samu take min bincike akan gidansu gimbiyar duk halin da ake ciki na bata kudi akan ta ringa fada min indai akwai maganar nasan zata sanar min da wuri balle ma ba zan ma zauna zaman Jira na tabbatar ba dan nima ban manta maitar yarinya nan ba zata iya shammata ta, gobe asubar fari zamu d’auki hanyar wajen  Mallam nidai yanzu damuwata ta Ina zaki ga Yareema ku samu ku hada ido dashi”

“Anya wanan kwalin nasa na aiki kuwa Hajiya gaskiya da iya kwalli nan daya bayar bana jin zai sa Yareema yaji Yana sona ya dai sake mana wani aikin”

Da haka suka bar maganar zuwa gobe.

Zinatu wajen yamma ta shirya cikin wani tsadadden doguwar rigarta ta rike hannun Samha suka nufi gidan dake kallon gidansu dan haka kawai taji ta matsu tasan matar gidan dan ta kula alaka da ita,dan tana san Hulda da masu kudi.

Koda suka shiga gidan daga Yan aikin da suka ci uniform suna ta kai da kawowa tasan matar gidan ta kama kasa

Dan Koda ta zauna ta hau wurga idonta jikin manyan frames din dake jikin banging Palon dan so kawai take taga hoton matar kafin ta fito duk da baa ce musu komai ba dai waje ta samu ta zauna

Samha kuwa da alama ta zama Yar gidan dan sama ta haye da gudu

Bata ga wani abu mai kama da hoto ba sai frames din Surori,Sunayen Allah da sauran su.

Wurga ido kawai take ta ga ta inda zata ga matar gidan

Sai da ta samu minti ashirin  a zaune tana ta bawa idonta abinci dan banda kar tayi kauyancin da tace bata tab’a shiga irin palon ba inka d’auke palon Gimbiya da suka samu suka shiga dak’yar.

Motsin wata karfaffa dake sanye da uniform ya katse mata tunanin da take cikin harshen Turanci ta jefa mata tambayar ko madam din tasan da zuwanta”?

Zinatu kuwa ta girgiza kai itama cikin harshen Turancin tace acewa madam din makociya ce ta shigo dan su gaisa.

Matar kuwa ta girgiza Mata Kai akan madam bata fitowa wajen mutane sai tana da appointment da mutum dan haka tayi hakuri ba zata samu ganinta ba

Zinatu kamar zata rushe da kuka haka taji ta mik’e Jiki a sanyaye Samha ta sauko suka tafi.

Suna fita ta hau tambayar Samha ko tasan matar gidan.

Samha tace ita bata Santa ba iya yaran kawai ta sani sai Yan aiki

Zinatu kuwa taja tsaki har da aunawa matar zagi dan gani take wulakanci ne da ita tunda sai tana da appointment da Kai take ganinka anan ta Kara jinjina arizkin matar tana shan alwashin nace Mata har sai sun zama kawaye.

Hutu da Jin dadi da shekarun da ta Kara ya matukar canza ta,ta tashi daga siririya ta koma Yar duma duma, murmurshi kawai take yi tana kallon Laptop din gabanta daga lokacin da ta shigo har zuwa zamanta a Palo kallonta kawai take tana sakin murmurshi sai da ta fita daga gidan ta rufe laptop dinta tana “Not so soon Zinatu amma saura kiris “

Zinatu

Washegari da sassafe suka d’auki hanyar wajen bokan tafiyar awa biyu da rabi ya karaso da su wajen bokan.

Zinatu kuwa ta gyara zamanta ta hau zayyana masa Abubuwan da take so ayi mata “yarinya nan tun tana karama take bani ciwon kai,boka,duk wani abu da naso ace sultana ce take samunsa yarinya nan itace take samunsa.

Silar wanan dinki da kunshin da take suka Yi kudi har take haduwa da manyan mutane

Ina so ayi min aiki akanta ta daina iya dinkin da kunshin,idan tazo yi taji kamar zata mutu,Sanan Ina so ayi min aikin da zata dawwama a gidansu tafi ma mujiya bakin jini.

Ina so Kuma a sake min wani aikin akan Yareema ya fito wuta wuta ya auri Sultana”

Bokan dube dubensa ya hau yi na tsawon lokaci kafin ya fara magana Yana “Wanan yarinya fa tana da addu’oin tsarin jikii a jikinta aiki akanta zaa Sha wuya amma zan yi iya k’ok’arina naga abinda zan iya yi”

“Yareema Kuma sai an samo mana gashin Kansa zaa masa aiki mai zafi da zai auri Sultanar duk da ko baa kawo gashin ba Yareema fa shi zai auri Sultana”

Washe baki Zinatu tayi kamar yadda Sultanar tayi Zinatu kuwa tace a duba mata dai ko dai akwai wani abu a tsakanin Yareema da Yareeman ta fada masa zargin da suke

“Boka kuwa ya gama dube dubensa yace “Gimbiyar kadai ke san Ameera amma Yareeman kuwa ko a kafa aka daura masa Ameera kuncewa zaiyi Banga wani Aure a tsakaninsu ba”

Da farin ciki Zinatu da Sultana suka baro wajen bokan.

Koda suka iso wanka kawai sultana tayi taci abinci sallah kuwa sai daddare ake hadawa Gabad’aya ayi

Taci kwalliya ta rambada kwalli ta fito da mukullin motar Zinatu dan wani zubin da motar Zinatun take fita.

Ta d’auki hanyar wajen garden din da take haduwa da kawayenta wayyayu farincikin da take ciki yasa take Jin ba Abunda ya dace da ita sama da yau ta dandana zukar Shishan da kawayenta ke ta mata kwadayi yau zata fesa hayakin sama dan tasan ta zama Sarauniya Gimbiya.

Sule

      Hannun Gwaggo ya rungume fuskarsa cabe cabe da hawaye Yana “Gwaggo dan Allah ki Bud’e idonki ko sau daya ne kiga tasirin da adduarki tayi a kaina, Gwaggo dan Allah ki Bude idonki kiga abinda rabbi yamin Gwaggo ki Bude idonki kiga wai dan sarki ke san Auren Ameera, Ameerar da kike yawan yi wa addu’a wai ita yaron sarki yazo neman Aurenta Gwaggo”

Kuka kawai sule keyi dan har yanzu gani yake kamar a mafarki motoci sukayi parking a k’ofar gidansa da Rakiyar dogarawa da manyan mutane wai sun zo neman Auren Ameera.

Duk yadda abubuwa suka wakana gani yake kamar mafarki yake har sai da suka tafi da ya amsa da ya bawa Yareema auren Ameeran.

Suna tafiya yayi sujjadar shukr bai tsaya bata lokaci ba ya fito ya nufi tasha ya d’auki hanyar garin katsina dan duk da gwaggo bata iya magana ita zai sanarwa wanan abin farincikin

Hanne kuwa ya barota a can daki tana ta rizgar kuka

Ameera kuwa kamar ma dai dan gajeren Suma tayi na wucin gadi

Ya Ibrahim kuwa Yana daga can gefe Yana ta rafka hamdala dan yasan ba iya Sule ne ya warke ba har shi kila ta silar Sulen zai yi arizkin dan yasan sule ba kamar Habu yake ba

Ihunn da sule yasa da “Wallahi ta motsa hannunta ya Ibrahim yasa shi mik’ewa da gudu ya nufi wajen da Gwaggon ke kwance Sule na kankame da hannunta.

*KWARYA TABI KWARYA*

*28*

*KWKWR T KWKWR*

*Page 28*

          Ya Ibrahim kurawa Gwaggo ido yayi da ke kwance kamar yadda ta kwashi shekaru din ba motsi abinci da sauran abubuwa ta drip ake bata.

Bata Kuma tab’a motsawa ba

“Gwaggon ce kaga ta motsa hannunta”?

“Wallahi ta motsa ya Ibrahim ta motsa hannunta”

Sule yace Yana Kara kankame Hannun Gwaggon cikin tsananin farin ciki tamkar har Gwaggon ta samu saukin.

“Zanso Gwaggo taga arzikin daya shigo gidanmu zanso Gwaggo ta ga niimar da Allah ya mana Ya ibrahim ya kamata mu sa ayi mata sauka mu Kara dagewa wajen addu’a”

“Ana yi Sule sai dai a Kara Allah ya tashi kafadunta”

Haka suka zauna a gaban Gwaggon suna ganin kamar zata Kara motsawan a ranar a dakin Gwaggon suka kwana suna hirar bikin Ameera da suke ganin kamar a mafarki dan Sule har lokacin gani yake zaa iya tashinsa ace mafarki yake yi.

Bai san akwai wasu masu kudin da suka san darajar mutane har suka san darajar talaka ba sai yanzu,dan ya d’auka duk masu kudin halinsu guda ne lura da Abinda Suma gidansu Sahar suka yi na kwarya tabi kwarya,Wanda tun a lokacin yaji duk masu kudin sun fice masa a rai addu’ar miji nagari kawai yake yiwa Ameera dan yasan indai ta samu na gari shikenan tana da abinda zata rufawa kanta asiri,sai gashi, zuriar Sarki Maje sun bashi mamaki duk da suka zo din ya nuna musu shi fa talaka ne tukuf zai hau bayani sai yaji wani a cikin manyan mutanen ya dakatar dashi akan sai da suka san ko shi waye kafin suka zo nemawa Ameera Auren Yareema,sai da suka san komai a Kansa suka zo nemawa Yareema Auren Ameera tarbiyyar da ya bawa Ameera kawai da nutsuwarta ta siye zuciyarsu ai Wanda ya gaji arziki baya dagewa akan sai gidanku na da arziki zaa aureka su Nasabar mutum suke dubawa

Kai kawai ya ringa gyada musu dan sun fa kashe shi da mamaki, daga zuwa tambayar da bayarwar da yace anyi,haka aka ringa ajiye jakunkuna suka mik’e da maganar dawowar da zasuyi zasu zo da komai nasu ba b’ata lokaci Kuma an nemi da a b’oye neman a bayyana samu dan baa so mutane su san wa Yareeman zai Aura saboda yadda mutane da yawa ke san suga su suka samu damar da Ameeran ta samu.

Sai yaji kamar sun shiga zuciyarsa dan shi ma ba zai so asan Wanda Ameera zata aura ba,duk da yasan idan Allah yace sai anyi sai anyi din

A ranar haka ya kwana sallah da godiya ga Rabbi Mai yi a lokacin da ya so dan ko a mafarki aka ce Wai Yar cikinsa zata taka irin wanan matsayin karyatawa zaiyi.

Kafin ya tafi ya d’auko kudin da Ameera taje kunshi gidan sarkin da duk basu tab’a ba ya damkawa ya Ibrahim dan ba Karamin kudi suka ajiye ba daga zuwa tambaya.

Hanne

       Fadar kukan da ta Sha bata bakine dan daga ita har su Ameeran kuka suka sha suka gode Allah,Hanne kukan ban zata ba farinciki da komai take yi ita kuma Ameera sai ta kasa gane mai ya sakata kukan,dan bata ma san mai take ji ba a lokacin,gani take tamkar mafarki take yi, wanda sai da ta Kai da ta shiga Ig dinta tayi searching din sunan Yareeman da Rabin followers dinsa Yan mata ne,gani take ba ita Ameeran ake nufi ba,dan da ace ya ganta sosai ba yadda ma zai ce Yana Santa dan idan a kyau da aji ne Yan Matan da suke rububin sansa sun dameta sun shanye,manyan Yan mata yaran masu kudi ba ita da take lungu take zuba kunshi da dinki, banda Sule da bakinsa yace mata ance Yareema ne ya ganta yace Yana so da tace kila Gimbiya da tayi wa kunshi ce taso ta hada Auren da mutuncinta ya zarce Tunaninta.

Sam bata yarda wai da gaske bane ba gani take kuskukre aka samu dan Abu ne da take ganin kamar da wuya shi yasa ba zata saka ma rai ba,yau da ta na da dama da Amjad zata aura da Sansa ke manne a zuciyarta har lokacin.

Dan a Kansa ta fara Sanin so amma tasan sai dai suyi hakuri dan balain tausayi yake bata,bama ta iya Bude texes din da yake tura mata dan tasan karya mata zuciya zai yi.

Kafin ma akawo kaya sai ga Sako daga gidan sarki akan sule ya zabi a gyara gidan ko Kuma su tashi su koma wani gidan.

Sule kuwa ganin daga gidan sarki aka zo yasa yace sai dai a gyara gidan dan shi da ta shine ma da an bar masa gidansa haka dan shi bai aibun gidan ba balle abin gyara,abinka da kudi,sai gashi sun Kawo ma’aikata,Da zasu canza fasaalin gidan

Hanne kuwa hakan da ta gani ne yasa ta tattara su Ameera Suka koma gidansu.

Shi kuma Abba Sule sai ya koma tsohon gidan Gwaggo dan gyaran da ake bana wasa bane ba abinka da masu kudi.

Hanne

   A zaune a dan tsakar gidansu da bai fiye girma ba tsaftar da gidan ke dashi yasa gidan yin kyau.

Tana zaune kusa da  Mahafiyar Shamsiya tana dan mata fifita, mahafiyar ta kuma na can wajen kitchen suna dan tab’a hira.

Ameera kuwa na can cikin daki tana waya da Yareeman da ta kasa Koda furta A,dan ta true caller ta gane shi yake kiranta sai da tayi da gaske kirjinta na dukan uku uku ta iya d’aukar wayar.

Bayan gaisuwa bata iya magana ba dan shi ma maganar tasa daidai yake yinta.

Sai a lokacin ta tabbatar da shi din ne dai aka zo nemawa aurenta.

Muryar Amjad da taji a tsakar gidan yasa ta mik’ewa tsaye murya na dan rawa tace wa Yareema tana zuwa za tayi wani abu zata sake Kiransa.

Zinatu

     Hannun Amjad ta ruko dake k’ok’arin yin Waje bayan ta sanar masa zuwan da tayi gidansu Ameeran Sule ya dage akan ba zai bashi Auren Ameera ba,dan Amjad ko minti ashirin bai yi da dawowa ba ya fara tambayarta yadda suka yi.

Zinatu kuwa ta karanta masa yadda Sulen ya musu rashin mutunci wanda da biyu tayi dan Amjad ya tsani sule da yake ganin mutuncinsa da akan sa wani zubin ya gwammaci bacin ranta akan nasa,daya barin Kuma zata so ya sake komawa gidansu Abba Sulen ko Allah zai saka su bashi Ameeran da ta tanadarwa abubuwan tashin hankali idan har ta auri  Amjad din,dan da dai Ameera ta Auri Yareema da taji hankalinta ya kasa kwanciya har lokacin gwara ta Auri Amjad.

“Ni bansan mai yasa Sule baya so ya baka Aurenta ba,babu yadda banyi ba a ganina ka hakura kawai ka karbi Auren Jawaheer din”

“Abba sule ba zai hana ni auren Ameera ba tunda yace min sai yaga kin taka kafarki kinje gidan da kanki zai yarda da cewa kin amince da Aurena da ita zanje gidan da kaina naji dan Alhaji shi ma yace min kinje Sanin da nayi wa Abba sule baya magana biyu ya kamata ya bani Auren Ameera”

“Toh shikenan Amjad jeka ka dawo amma Sule kam da wuya ya baka Aurenta dan ya dage wai sai wanda yafika arziki ma zai bawa Ameeran

Amjad bai ce mata komai ba ya fice daga palon Koda yaje gidansu Ameeran sai ya kasa gane gidan dan wani tsarareren gida yake ganj bene.

Sai da ya karasa shagon Abba Sule dan a layin shagon nasa yake.

Wani ke fada masa ai gyara ake a gidan dan shagon Abba Sule a rufe yake anan yake fada masa su Ameera na gidansu Hanne .

Ba irin tunanin da bai zo masa ba na kodai siyar da gidan su Abba sule suka yi.

A gaban Hanne ya zub’e ya hau gaisheta.

Hanne kuwa ta amsa cikin sakin fuska tana Jin tausayin Amjad din,dan har kunyarsa ma take ji,tasan yaron Sam bai d’auko halin iyayensa ba,tana ta tunanin abinda zata fada masa idan ya tambayeta game da Auren da Ameera za tayi dan gani take ya ma sani sai ga Abba sule shi ma ya kwada sallama ya shigo.

Sai da suka dan tab’a hira kamar yadda suka Saba da Abba Sulen har suka ci abinci Ameera na labe a jikin labule tana kallonsa

Amjad ya hau magana Yana “Abba kace idan har Hajiya da Alhaji suka zo da kansu nema min Auren Ameera zaka bani,akan zuwan da suka ce za suyi na dawo Abba na Kuma dawo Hajiya ke sanar min wai kace ko a mafarki ba za ka iya bani Auren Ameera ba”

Abba sule hannun Amjad ya ruko ya hau masa nasiha Yana bashi hakuri akan ya hakura da Ameera dan Ameera ma ta samu mijin Aure har zai fada masa Wanda zai Auri Ameera sai Kuma ya fasa dan bama yaso Zinatu ta tab’a sanin wanda Ameeran zata Aura.

Fusge hannunsa Amjad yayi daga rukon da ya amsa idonsa jajjur kamar an watsa borkono dan har ga Allah yaji ciwon abinda Abba sulen ya masa.

So yake ya yarda da Maganar Zinatun akan Abba sule shi ne kawai baya so ya bawa Ameeran ba wai dan wani dalili ba.

A halin da yake ciki ko magana baya Jin zai iya yi,dan ya kasa yarda duk murnar da yake na Ameera zata zama mallakinsa ya Kara zama mafarki

Waje yayi Yana Shan alwashin hakura da Ameeran

Koda ya koma gida yanayinsa kawai Zinatu ta gani ta tabbatar da Sule dai da gaske ba zai bawa Amjad Auren Ameera ba

Zama bai kamata ba dakinta ta koma ta sake Kiran jakadiya a waya da ta siye da kudi akan ta ringa fada mata duk halin da ake ciki yanzu haka ma itace ta sanar mata wajen da Yareeman yake tasa Sultana ta rambada kwalli akan taje can ko Allah zai saka su hada ido.

Jakadiya tabbatar mata tayi akan ba wanu Abu dai dake faruwa a yanzu ai tana Jin wani labari zata kirata

Da haka ta dan samu nustuwa tana Jin da wuya ma Yareema yaso Ameera tsorata kawai sukayi da maitar Ameeran da ke ta samun duk Abunda take so tun suna Yara.

Har dakin Amjad ta je ta rarrashe shi akan ya hakura da Auren Ameera ya karbi Auren Jawaheer da kyakyawa ce bata da laifi.

Amjad kuwa da ya gama turawa Ameera text na nuna rashin Jin dadinsa akan abinda Abba sule ya masa ya Kara da ya d’auka tana san shi Ashe zata iya auren wani bayan duk irin san dayake Mata dan haka shi ma ya hakura da ita din.

Ya dago ya Kalli Zinatu muryarsa kasa kasa yace ya yarda da Auren Jawaheer din.

Zinatu ji take kamar ta taka rawa dan murna

Sai ma idan sultana ta dawo gidan ta mata albishir da ta samu ganin Yareema gani take zama ta iya suman Dadi.

Sai dai da kuka sultana ta dawo akan Mari ta Sha a wajen Yareeman

Ta hada da Ihun tafa ji labari kamar Ameera zai aura.

Zinatu da taji kamar ruwan zafi take watsa mata tace tayi saurin tofar da bakin yawu amma Yareema ba zai tab’a auren Ameera ba.

Washegari da sassafe suka Kara dira wajen boka Zinatu cikin tsananin damuwa ta zayyana mishi duk Abubuwan dake faruwa.

Boka ya Kara cazar su kudi yace zai yiwa Sultana wankan magani da zai Saka Mata wani irin haske a idon Yareema.

Sultana kuwa ganin ya mik’e a wani mulmule dashi yasa ta dage akan ba ta yarda ayi mata wani wankan magani ba balle da taji tubewa za tayi su kebe da bokan.

Duk yadda Zinatu taso shawo kanta haka sultana ta tubure boka kuwa yace ba kuma hanyar da zata samu Yareeman sai ta hanyar wankan da zai mata.

Sultana kuwa tuni tayi wajen motar ta haka suka baro kauyen tana aunawa bokan ashar Zinatu Kuma na ta fadan kin yarda da tayi.

Sultana kuwa ta ringa zuba mata rashin kunya tana ita taje ayi mata wankan maganin ai da alama ba abinda bokan ya iya gwara su nemi wani.

Sai a lokacin hankalin Zinatu ya kai akan ya kamata su nemi wani din ya musu aiki.

A cikin kwana biyu wata kawarta ta hada ta da wani hatsabibin boka da ya sanar musu da ai Yareema yanzu haka ya samu matar Aure amma kusa yin auren.

Zinatu da Sultana kuwa hankali a tashe suke mik’e tsaye wajen tambayar wacce matar da zai aura.

Boka yace musu wata  ya samo bai San ko wacce ba,amma zai iya aikin da zaa wargaza auren a karkato da hankalin Yareema kan sultana.

Haka Zinatu ta saki uban kudi boka ya basu tarkacen abubuwa yace sultana taje tayi amfani dashi na kwana uku zata ga aiki da cikawa

Hanne

    Ido ta waro tana kallon Ameera dake rike da bandir din Dalla da Mahaifiyar ta ta d’auko da wasika,ciki kuwa buhunhunan abinci ne sai wani wasika da aka sake turowa a yanzu da suke tsakar gidan da shine silar da ya sa Mahaifiyarta d’auko bandir din kudi da wasikun da ake yawan Aiko musu ta kawowa Hanne da ta mik’a wa Ameera ta karanta musu

“A duk wasikun aike ne akeyi na kudi da kayan abinci a kasa ana rubuta sadaka fisabillahi.

Yanzu wanan wasikar da aka turo wai mai taimaka mukun na so a kai Babba Jummai  waje dan a duba lafiyarta”

“Wajen wata hudu kenan ake mana Aiken kayan abinci da wanan takardar da bansan menene ba na dai ga yayi kalar kudi

Ana kawowa ake tafiya baa fada.mana mai kawo mana shiyasa ni kuwa nake jibge duk Abunda aka Aiko dan ni tsoro ma nakeji, abinda yake bani mamaki waye mai Yi mana Aike haka har yasan da Jummai ba ta da Lafiya”?

Mahaifiyar Hanne tace cikin tsananin damuwa.

“Sultana.

     “Ni kika Mara”

“Yawu ta tofawa Matashin a fuska da Kallo daya zaka masa kasan iirn Yan dabban nan ne tantiran Yan iska dan gashinsa kitsewa yayi yankan wuka a jikinsa da yawa da yasa  fatarsa dameji saboda dinkin da ya Sha.

Wani store ta shiga dan ta dan siyi ice cream ta fito ta karasa gida dan wahala kawai taje ta sha bata samu ganin Yareema ba

Tana fitowa taga mutum a zaune a saman motar ta

Yana zuka sigari

Wani irin tsaki taja cikin nuna kyankyami tace masa ya saukar mata a mota ta fara k’ok’arin Bud’e motar tana shan alwashin Jan motar da gudu idan har bai sauka ba

 taji  ya dafata ta baya  ta juyo a fusace  ta kwashe shi da Mari

Ya dafe kuncinsa Yana ni kika Mara”

Sultana kuwa ta tofa masa yawu tana “Na mareka”

Yawun fuskarsa ya shafo da bakekkan hannunsa ga mamakin ta sai taji ya kira sunanta da “Sultana kin jawowa kanki tunda har kika mareni Banga uban da zai hana ni aurenki ba Baki da miji sama dani.

Wani irin dariya sultana ta kwashe dashi sai da ta masa wani irin mitsiyacin Kallo ta Kara tofa masa yawu ta shige cikin motar ta tayar tare da Jan motar da gudu tana Jin kamar tabi ta kan kafarsa.

Da gida zata je sai Kuma ta fasa dan haduwarta da dan shaye shayen nan ya Kona mata rai,sai ta nufi wani garden da take yawan zuwa ta Sha iska.

Zinatu

Wayar dake Rike hannun ta ne ya sulmiye daga hannunta a lokacin da tayi tozali da katin daurin auren Yareema da sunan Ameera baro baro wani irin Sara mata kanta ya ringa yi har duhu na gilma mata dan jiya bokan ta ke fada Mata an wargaza auren da Yareema zaiyi

Bata ma san mai Samha da ta fito daga kitchen ke cewa ba

Kafin ta dawo daga Karamin sumar da tayi taga wani ya fado palon Yana zazaare ido da kalle kalle.

“Hajiya kwana biyu”?

Wani irin Kallo ta fara yiwa Dan shaye shayen da ya shigo mata Palo tana mamakin Ina Mai gadi yaje da ya bar dan shaye shaye ya shigo mata Palo.

Tsabar mamaki ma kasa magana tayi ta zuba masa ido tana kallon yadda ya zubawa Samha ido kafin ya d’auke Kansa daga kallon Samha da ta koma gefen Zinatun saboda Dan shaye shayen ma tsorata ta yayi dan har da wuka a kugunsa.

“Bawan Allah lafiya Mai kake nema”?

“Hajiya yarinya nan dana d’auko a wutar nan  ce ta girma haka”??

Zinatu ido ta zaro waje cikin azabar faduwar gaba tace “Ayubaaa”

“Naam sirikata”

Ayuba yace Yana fesa sigarin dayake zuka sama

Shigowar sultana palon da ashar din da ta lafto yasa shi sakin murmurshi yana “Sirikata  sultana nake so, Ina san ta da Aure zaa bani ko Kuma dai sai na  tona”?????…

*KWKWR T KWKWR*

*Page 29*

      Zinatu

“Ga wanan na Kara maka akan kudin da na baka Ayuba har Abada baka sani ba bansanka ba Ayuba ka Nisanci garin nan wanan kudin da na baka zai ishe ka, ka dan  jari dan Allah karka sake ka tab’a dawowa garin nan”

“In Sha Allahu Hajiya yanzu garinmu zan koma ba abinda zai dawo dani”

“Muje na kai ka tasha Ayuba dan sai na ga tafiyarka hankalina zai kwanta duk da Ina da tabbacin ba Wanda ya ganka amma Ina tsoron wani abu ya taso ace za’ayi bincike”

Zinatu tace tare da shigewa cikin motar ta,Ayuba kuwa yace zai debo kayansa ta girgiza masa kai tana ba sai ya dauko komai ba ya shigo ta Kai shi tashan.

Bata bar tashan ba sai da ta ga tafiyar su,a tashar nan ta watsar da haduwarta da Ayuba dan tama rufe babinsa,tasan ba kuma abinda zai saka asirinta ya tab’a tonuwa sai dai Yau sai ga Ayuba a  gabanta  a cikin palonta Yana san yi mata barazana.

Sultana kuwa Mai gadi kawai take kwallawa kira tana rugawa  Ayuba  Ashar dake ta fesa hayakin sigarin sama

“Wai ya naga kin tsaya kina kallonsa ne Hajiya ko kin San shi ne”?

“Ta sani sarai ya ba za ta tsaya Kallona ba,ki dai iya harshenki dan ke matata ce”

Sultana kuwa ta Kara soka masa Ashar tana Jin kamar ma yarfa mata ruwan zafi yake da yake kiranta da sunan matarsa

“Mai hadin ki da dan shaye shaye dan dabba Hajiya,Yace kin san shi ke kuma kinyi shiru baki ce komai ba”

Zinatu da taji kanta na balain Sara mata da tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki har yanzu bata dawo daidai daga ganin Katin dauren Auren Ameeran da  Yareema ba sai gashi Ayuba Shima ya bullo Yana san tona mata rufaffen sirrinta da take fatan ko da mutuwa tayi ba Wanda zai tab’a sani.

“Ki shiga ciki sultana

Ayuba na ganka a waje mana”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Hajiya kin dai san shi kenan mai hadinki da dan dabba”?

Sultana tace cikin tsananin mamaki tare da bin Zinatu da ido da tayi hanyar waje

Ayuba kuwa ya sakar mata murmurshi Yana “Ayuba sunana ki daina kiran mijinki da dan dabba”

Daga haka ya bi bayan Zinatun da ta Kara kwalla masa kira  daga bakin k’ofar.

Sultana kasa ma motsawa tayi har sai da ta ga sun fice daga palon tana ta mamakin mai hadin Zinatu da Ayuba sa Kallo daya zaka masa kasan dan dabba ne,a idonta sai taga kamar ma tsoron Ayuban Zinatu ke  ji har idan ba sanin shi tayi ba taya zai samu ma karfin gwiwar shigowa har cikin palonsu ya tsaya”

Kasa hakuri tayi ta leka waje

Ta tsaya tana kallonsu daga wajen gate

“Ayuba mai ka dawo yi garin nan bayan na sallameka?Ayuba a gaban yata kake so ka tona min asiri?Mai ya kawo Ka gidana Ayuba Ina Kuma da Hadi da kaine ?Yanzu da Alhaji na nan haka zaka shigo min gida Kai tsaye?

“Ayuba sai da ya zuke guntun sigarin hannunsa ya fesar da hayakin, ya Yar da guntun sigarin ya murza da kafarsa kafin ya dago Yana “Hajiya kisan kai fa kika Saka nayi,taya za kiyi tunanin haka kawai dan kin bani wani guntun kudi kin gama sallamata,a baya har da yarinta yasa na karbi wanan Aikin,tunda nake ban taba kashe ko da bera ba,ke kika fara sakani aikata mumunan laifin da ya bud’e k’ofar da na zama kangarare yanzu,dan daga lokacin da na miki aikin nan zuciyata ta bushe na daina gane ya tausayi da Imani yake,yanzu haka ko wata uku banyi da sake fitowa daga kurkuku ba,duk abinda kike Ina sane dake dan ba zan iya manta ki ko na rabu dake ba dan kece silar gurbacewar rayuwata dan haka batun wai kin sallameni ki ajiye wanan maganar a gefe,dan a yanzu ni din bana kwarai bane a idon mutane na Kai munzalin da zan Aure amma ba Wanda zai yadda ya d’auko yarsa ya bawa Irina tunda har kinsan a yadda nake a da Kuma kece silar zama na haka toh na ga yarki sultana Ina so shi yasa nazo wajenki dan naji ya za’ayi”

Zinatu ido ta zaro tana kallon Ayuban da ke magana da iya gaskiyar sa sai taji tana neman ma rasa tashin hankalin da ta shiga akan auren Ameera,dan Ayuba yazo mata da maganar da take ganin Sam ba mai tab’a yuwa bane ba,ko bai fada ba daga irin yankan da ya Sha a jikinsa daga irin zubinsa ma kasan rikakken dan dabban ne zai iya aiwatar da komai,ciki kuwa har da tonan asirinta da idan har ya fallasu tasan ta Kade har ganyenta

Gumin daya tsatsafo mata ta goge ta daure Wajen hadiye tashin hankalinta tana “Ayuba nawa kake so yanzu na baka dan Allah dan Annabi ka manta dani ka fadi komai kake so banda Auren Sultanar da kasan ko a mafarki ma ba mai tab’a yuwa bane”

“Aiko duk kudin duniya zaki bani a yanzu ba zan tab’a karba ba Hajiya dan yanzu kudi ba zai tab’a iya gyara min rayuwata ya koma kamar da ba,karki manta kece silar dawowa ta haka Kuma wai ke kike san ki nuna kin fi kowa kyamata,Yarki nake so na aura idan ba zaki bani ita ba,dama na gaji da raywuar zan tona miki asiri ne kawai na tonawa kaina inyaso na ma kare rayuwata kawai a kullen”

“Ayuba taya zaka ce Duk Matan duniyar nan ka rasa mai aurenka, dama namiji na rasa matar Aure ne?indai matar Aure kake so karka damu indai auren kake so kayi karka damu zan nemo maka matar auren da kaina”

“Ni sultana yarki nake so ba na bukatar ki nemo min wata”

Zinatu ido ta zuba masa tana kallonsa dan taga alamar da gaske yake maganar da ta gwamaci yawo tsirara wai da ranta ta d’auki yarta da take cin buri akanta ta bawa Ayuban da take ganin ko gadin gidan Sultana aka bashi an ci mutuncinta yarinyar da take burin kaita gidan sarauta wai ita kamar Ayuba Almajiri dan shaye shaye zai zo ya tsaya a gabanta yace Yana san sultana

“Kin tsaya kina kallona zaki bani aurenta ko na tafi company mijinki da gidansu kishiyar taki dake can kasan layi na sanar musu kece kika haddasa mata gobara kika saka na d’auko miki yarki”

Zinatu zuwa wanan lokacin sai taji kamar zuciyarta zata Faso daga kirjinta dan hararo tonuwar sirrinta kawai take a idon duniya kila ta kare rayuwarta a d’aure dan tasan da yawa basu manta wanan gobarar da ya tashi da shamsiya da cikin jikinta da yarta ba,Yana cikin Labarin da aka kasa mantawa.

Ganin Ayuban yayi wajen k’ofa Yana Tunda bata da abun fade ta zuba ido taga zuwa gobe ya fado mata sunan company Habu da kwatancen gidansu Shamsiya

Da sauri ta dakatar dashi tana “Zan baka Aurenta Ayuba ka bani nan da sati biyu”

Murmurshi Ayuba ya saki Yana “nan da sati biyun Ina zuwa nake so a daura mana Aure Kuma bani da wajen zama a gidanan nake san na zauna dan naga gidan Yana da girma kinga jikokin ki zasu taso a gabanki”

Amai Zinatu taji Yana san taso mata ta danne dan dauriya kawai take idan taji Yana san hada Kansa da sultanar da ta nufo wajensu da alama ta kasa hakuri shiyasa ta taho wajensu

Zinatu kuwa tace ya tafi taji,dan kafin sati biyun tasan ta rufe babinsa ko nawa zata kashe sai ta kashe saboda ta kawo karshen sa.

Sultana kuwa na karasowa ta hau jefa mata tambayoyin Mai hadin ta da Ayuba wane asirinta zai tona”?

Zinatu kuwa bata ko kulata ba sai da taje palo Sanin halin sultanar sai ta samu amsar tambayarta zata barta Yasa ta d’auko wayarta ta budo Invitation din daurin auren Yareema da Ameera ta mik’a wa Sultana.

Sultana kuwa tana ido biyu da Invitation din ta saki wayar ta re da sakin Ihun ta hau burburwa a kasa tana “Mai nayi wa Ameera a rayuwar nan da take san kwace duk wani abu da nake so a rayuwata,mai nayi wa Ameera take san taga sai ta fini ta kowanne Fanin yanzu Yareeman da nake Shan wahala akansa ta kwace min?

“Sultana ki bar ihu haka ki kwantar da hankalin ki ai dai baa daura auren ba sai asabar mai zuwa zanyi duk yadda zanyi dan na hana Auren nan indai Ina rayye ba zan tab’a barin Ameera ta auri Yareeman da ni kadai nasan kudi da na kashe dan ki Aure shi ba,Ashe Sule yasan mai ya taka shi yasa yace Ameera ta fi karfin auren Amjad,taya zan iya barin Ameera ta shiga gidan sarauta ta miki fintinkau,ko kinsan idan har Ameera ta Auri Yareema hakan na nufin Sule ya zama mai arziki,ya shiga sahun manyan mutane da kila ma yazo yafi mahaifin ku taya zan tab’a iya barin ayi auren nan,ai idan Ameera tayi nassara wajen finki k’ok’ari a makaranta ba zan bari ta fiki da samun miji ba”

“Aikin gama ya gama Hajiya dan bokayenki duk makaryata ne maha’inta tsinanu sau nawa kike sha shan rantsuwa da Shan alwashin ganin kinci galaba akan Ameera da ta zame mana karfen kafa amma Muna ji Muna gani haka zamu ga ta Kara samun cikar burinta,nidai Ina ga wanan rashin saan da na d’auko ma daga wajenki ne”

Zinatu kallon Sultanar Kawai take tana Jin wani bacin rai na rashin iya maganar sultana dan sam bata iya magana ba wani zubin idan ya kwaba Mata magana kamar ba itace ta haifeta ba tana Jin ciwon yadda wani zubin take San Maya rashin kunya amma bata iya kwabarta saboda bata san b’acin ran yayanta.

Rarrashin Sultanar Kawai ta ringa yi tana alkawarta mata akan zata samu Yareema Koda bazata Aure shi ba itama Ameeran ba zata same shi ba,zata zagaye duka bokayen garin zata saki kudi dan ta samu cikar burinta

A haka sultana ta shige dakinta ta dauko wayarta ta Bude data nan kuwa jininta ya nemi hawa dan kasa ma kirga akwatunan da aka yiwa video tayi da aka makalla hoton Yareema a sama ta kasa Kuma hoton Ameera ce da ta Saka lafayya ta sha Nadi tayi matukar kyau

Ihun da ta fasa yasa Zinatu shiga dakin nata a guje

Zinatu kuwa irin uban dukiyar da taga an narka da sunan na Ameera da kila har ta shekara goma bata gama Sake kayan ba,yasa wani irin zazzafan zazzabi rufeta dan gani take idan har Ameera ta auri Yareeman da take burin Sultana ta aura zuciyarta zata iya bugawa,hararo sule da Hanne sun shiga sahun manyan mutane na matukar daga mata hankali ta kasa yarda  wai Ameera yar gidan Sule da ta tsana ke neman shiga gidan sarauta.

Buge bugen waya kawai take tana neman mafita kafin asabar din,dan bama ta Ayuba take ba kawai so take tayi iya k’ok’arinta wajen wargaza auren Ameera da Yareeman,bata san ya akayi bokayen da ta Saka rai da zasu mata aiki mai zafi suka kasa aikin da suka tabbatar mata da zasu yi mata ba.

Wayanda suka san alakar ta dasu Ameeran a cikin kawayenta haka suka ringa  kiranta a waya suna san suji tabbaci a bakinta dan har dan shelanta Musu tayi akan Yareema nasan Sultana.

Ganin idan ba kashe wayar tayi ba haka za’ayi ta kiranta kowa na bata labarin uban dukiyar da aka hadawa Ameera yasa ta kashe wayar ta kwanta tana Allah Allah gobe tayi ta bazama dan ji take idan ma har ta kasa samun cikar burinta zata iya aika Ameran lahira dan gwara kowa ya rasa.

Habu

      Shi kansa jiki a sanyaye ya nufo gida da katin daurin Auren Ameeran da Sule ya Kai masa har companysa da sai da ya girgiza da yaga wai Dan sarki ne zai auri Ameera,sai ya rasa mai yake ji a zuciyarsa dan har ga Allah sai yaji zuciyarsa ta sosu,bai sani ba ko dan Sulen ya hana Amjad Auren Ameeran ne ko Kuma dai k’ofar da ta bud’e masa ta d’aukaka da arzikin dake nuni da ya tado shi a yanzu yasa yaji zuciyarsa ta sosu.

Juya katin daurin auren ya ringayi Ya Kalli Sule da a idonsa ya canza a cikin kankanin lokaci yace “Na d’auka kace baka da kwadayi ya akayi ka yarda ka bawa Yareema Auren Ameera”?

Murmurshi Sule ya saki Yana “Ba nida kwadayi Ya Habu kaima kasan haka,Allah dai ya rubuta Yareema shine mijin Ameera”

“Aaa san zuciya dai yasa ka zabi bawa Yarka bare akan dan uwanta,na dauka Kai kake jajirce wajen ganin zumuncin dake tsakanin mu ya daure,na dauka Koda baka so ko dan gwaggo zaka bawa Amjad Auren Ameera Amma sai gashi saboda san abin duniya ka hana Amjad ka bawa wani Bare”

“Banso zama da Zinatu yasa ka koyi yiwa mutum Hassada da bakin ciki ba ya Habu, Ina ga ko Rana aka sawa Ameera da Amjad idan har dan sarki ya zo yace Yana Santa Kaine mutum na farko ka da zaka ce Amjad ya janye amma sai gashi wai kiri Kiri kake san nuna min Jin haushinka da niimar da Allah yayi wa Ameera ya kuma yamin,idan kana so kaga haske a rayuwarka ka cire kyashi da hassada daga ciki ka daina fatan kagani a kasan ka a kowane lokaci nima Allah ya dagani ta hanyar Ameeran karfe goma Sha daya ne daurin Auren a babban massallaci sai kazo”

Daga haka Sule ya fice daga office din.

Habu kuwa ya bi shi da ido maganganun da ya masa na dan shigarsa zurfin da yayi a tunani yasa bai San ma Amjad ya shigo office dinsa ba sai da ya karbi hadadden invitation din hannunsa yaga katin daurin Ameera ne.

Rawar da jikinsa ya d’auka Yasa shi samun wajen zama,dan bai tab’a fidda rai akan ba zai aureta ba

Habu kuwa haka ya zagayo wajensa ya ringa bashi baki Yana ya hakura kawai Allah dama yayi Ameeran ba matarsa bace ba

Amjad kuwa ya mik’e tsaye Yana “Ina so a je a nema min Auren Jawaheer ba Kuma nasan a sa lokaci Mai tsawo Nima Auren kawai zanyi ko zan rage Jin zafin da nake ji a zuciyata

Da haka suka rabu Habu na dan samun nutsuwa a zuciyarsa dan jawaheer itama ba Yar kananan mutane bace ba

Tun kafin ya karaso k’ofar gidansa ya hango gidan su Immi a dan Bude haka kawai yake  san yaga Yana kallon gidan,har wani sanyi yake ji a zuciyarsa ya kuma rasa dalili,har tambayar Samha yake Ina kawarta Immi da yaji ta shiga zuciyarsa har Yana Jin dama yarsa ce.

Motar dake k’ok’arin fitowa daga gidan kawai yake Kallo dan ya riga da ya karaso k’ofar gida Shima

Immi ya ga ta Fito da dan gudunta ta shige cikin motar da wani ya bude mata, murmurshi kawai ya ke Yana ta san tuna wacce ya sani Mai irin fuskarta, fitowar wasu Yara biyu da aka yiwa shiga iri daya ya sa shi zuba musu ido Yana addu’ar Allah ya sa su fito sosai yadda zai iya ganin su,dan a rayuwarsa Yana San Yan biyu.

Har yaran sun fito waje ta yadda zai iya ganinsu sosai sai yaga wata karfaffa ta zo ta rike hannayensu ta shige dasu ciki.

Murmurshi kawai ya ringa yi shi kadai Yana tunanin sa Samha watarana ta fito masa da Yan biyun can da yake yawan ganinsu daga nesa  yaji Dadi a zuciyarsa.

Koda ya shiga ciki kafin ma Zinatu ta tare shi da maganar Auren su Ameeran ya Mika mata katin daurin auren,ya hau mata bayani akan dazu sulen ya kai masa katin

Zinatu da ke Jin kirjinta na dab da fashewa ta hau masifa tana zagin Sule akan ai ya Munafircesu yanzu dama akan dan sarki aka hana Amjad Auren Ameera kamar mai Karamin tabin hankali haka ta ringa masifa tana Yanzu yaci kamar su a b’oye musu

Habu hakuri yayi ta bata ya Kara da kar ma ta damu ai Amjad yace ya hakura zai auri jawaheer

Da a baya yace mata haka ba abinda zai hana ta taka rawa amma a yanzu sai bata ji komai ba, Auren Yareema da Ameera kawai da zaayi shine a Kahon zuciyarta

 Da sassafe kuwa ta  dau hanya ta ringa shige da ficen yadda zata wargaza auren Ameera da Yareeman.

Ameera

  Sai da aka kawo Katin dauren Auren ita da Yareema Kafin ta yarda cewar da gaske fa Aure za tayi a gidan sarauta,gani take Sam bata dace da Aurensa ba.

Haka dai aka ringa Shirin bikin da aka kawo mata kayan da take ganin kamar dai a mafarkin ne dai dan har dasu mukullin mota aka hado a cikin lefen da aka kawo mata shawarar Hanne kawia ta bi wajen dagewa da addu’a dan tasan ba zata rasa makiya ba.

Yanzu kaf layinsu Babu kamar gidansu dan ba Karamin haduwa gidan yayi kamar ma bashi ba.

Duk da Yareeman ya zo sau daya Kuma dan zuwan da yayi sun dan tab’a hira ta kasa sakin zuciyarta akan auren.

Ana saura kwana hudu Biki tana can daki tana Jin jakadiya da tazo tafiya da ita gidan da zaa fara mata gyaran jikin taji sallamar Zinatu da Sultanar da sai da gabanta yayi wani Irin tsinkewa wanda sam bata tab’a Jin hakan ba

Addu’a tayi a zuciyarta ta fara k’ok’arin fitowa dan tasan ba alheri ne ya kawo su ba

Tana Jin Sultana na ta tambayar Hanne Ina dakinta,Hanne kuwa ta bata amsa ita kuwa sam bata San ma ta shigo mata daki hakane yasa tayi waje suka ci karo a bakin k’ofa

Sultana kuwa ta rungumeta gam tana na Miki murna Ameera

Ameera kuwa ganin ta balain kankameta ta kuma dora hannunta a wajen cikinta kamar shafawa take yasa ta hankadata

Tana “nifa bana shiri da masu fuska biyu?nifa na riga da nasan da biyu kuka zo gidanan mai kuka zo nema”?

“Murna muka zo tayaki Ameera ba wani Abu ba,karki manta fa ke Yar uwata ce abin alheri ne ya sameki Kuma muka zo Miki murna amma tunda da alama baki ji Dadi ba Allah ya baki hakuri ai mantawa mu kayi yanzu kinfi karfinmu ke matar Yareema ce guda”

Ameera na k’ok’arin magana sai ga Zinatu itama ta shigo tana kalle kallen gidan da ta kasa b’oye bakin cikinta dan a Karamin palon gidan dakin Ameeran yake.

Tayi matukar girgiza da ganin irin gyaran da akayi wa gidan Sulen da ya dame nasu ma ya shanye

Dauriya kawia take wajen hana kanta ihuu Karin wani tashin hankalin haka tazo ta tadda jakadiya a gidan da ta mugun hade rai daga maganar da take ta gane ma zuwa aka yi a tafi da Ameeran.

Dan gyaran jiki zaa mata,saboda ta samu cikar burinta haka ta danne kanta wajen nuna murntarta a fili.

Kamar jakadiya na watsa mata fetur haka ta ringa ji a lokacin da ta rike hannun Amaera da kanta ke kasa akan zaa kaita gidan gyaran jiki sai kirari take zuba mata.

Irin rayuwar da ta sowa sultana taga Ameera na k’ok’arin samu

Sai da suka ga tafiyar Jakadiyar suka yiwa Hanne sallama da taji itama hankalinta ya kasa kwanciya da zuwan da suka yi.

Koda Sule ya dawo tana sanar masa ya saki murmurshi Yana yasan da abinda ya kawo su gidan dan haka yanzu zai fita ya samu Mai masa suakr Al Qurani akan Allah ya karesu daga duk wani sharrinsu dan shi yasan Zinatu muguwa ce ba abinda ya manta daga bakin cikin da ta ringa yiwa Ameera tun suna Yara yasan ba murna suka zo taya su ba wani abun ne dai ya kawo su.

Ameera…..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 30*

      Ameera

    Hawaye kawai ke zubo mata kanta a kasa tun  ba’a daura Auren ba an fara kaita inda bata tab’a mafarkin takawa ba dan zubewa kawai aka ringa yi a kasa ana mata kirari,tana iya kallon komai daga cikin alkyabar da Jakadiya ta saka mata da Gimbiya ce ta bayar da kanta akan a Saka Mata

Bama Kuma gidan Gimbiyar aka kaita ba wani waje daban aka kaita

Duk sai taji ma ta kasa ma samun nutsuwa da taga wayanda a haife sun haifeta wai sune ma hadimanta ita dai kanta ta sadar kasa tana kallon ikon Allah dan lamarin gidan sarauta kam sai dan sarauta dan ji take kamar ta yaye alkyabar tace su rufa mata asiri su bar zub’ewa a gabanta

Taso a gida aka Kai mata Mai gyaran jikin amma ganin umarnin Gimbiya ne yasa ta hakura

Da ta motsa sai a zube a kasa bayan bama magana tayi ba

A ranar haka ta kwana juyi a wani laulausan gadon da take ganin ko shi ka samu a aljanna ka gama dace,tsarkin da bata dashi ya hanata rayya daren dan tunda aka fara maganar Auren ita da Yareema ta Kara dagewa da addu’a da godiya ga Allah dan tasan wanan auren nata yin Allah ne.

Koda gari ya waye duk sai ta kasa sakin jikinta dan wayanda a haife zasu iya haifarta su suka ringa rawar jiki a kanta abincin karyawar ma birjik a ka jera mata,jakadiya kamar ta fuskanci halin da take ciki ta Kori kowa tana daga kasa ta hau mata bayanin ta saki jikinta haka gidan sarauta yake yanzu fa matar Yareema ce ita sai ta Koyi Abubuwa dan dukansu a karkashinta suke yanzu umarninta kawai suke Jira

Ameera bata iya ce mata komai ba dan ta wanan faggen zaa Sha fama da ita dan duk wayanda suka ma gaishetan kasa amsawa tayi sai ita ta Kara gaishe su har tana dan rusunawa.

Ko abincin kasa ma ci tayi

Haka tayi zuru tana tunanin irin raywuar da za tayi a gidan Yareeman,dan ta taso da san dinki da kunshi tsoron ta ma ace zaa hanata dinki da kunshin dan tana san Sana’ar da take yi,ba kuma tayi wani zama da Yareema ba balle taji ko zai barta dan Hanne ma ce mata tayi bata da hankali Taya tana matar Yareema zata na kunshi da dinki.

Haka ta ringa dan latsa wayarta har  mai gyaran jikin da kamshinta da ya cika gidan yasa ta gane ta iso

Har cikin dakin mai gyaran jikin ta shigo sai a lokacin Ameera ta gane ta, dan kwarewar da tayi a gyaran jiki yasa tayi popular aka santa kusan itace dai wacce idan kana so kayi gyaran gaske sai ka kirawota ta ig taga handle dinta,inda har Bridal package ta siya a wajenta aka kai mata har gida.

Cikin sakin Fuska suka gaisa da ita kafin ta umarceta akan zasu fara da dilka da halawan

Inda ta tube daga ita sai wani zani Mai gyaran jikin da taji ana cewa Umsad ta fito da Sudanese dilka da iya shi kadai ya cika dakin da kamshi ta matso kusa da ita ta hau mulka mata.

Da ido Ameera ke bin duk Abubuwan da take gyara mata jikin dashi da bama aje ko’ina ba taga fatarta ta fara canzawa sai da tazo Saka Mata Wani turare wuta da taga an Saka masa Najmatashahar na tsuggona ta ce Mata bata da tsarki,Umsad din kuwa ta saki murmurshi tana kar ta damu ta hau kan turaren ta zauna zai shiga jikinta a haka.

Ameeran kanta tasan ta gyaru dan jikinta kawai ta ringa bi da Kallo dan wani irin iska ma ke shigarta,kamshi kuwa kamar a cikin turaren aka tsomata dan daidai da ruwan wankanta sai da Umsad ta zuba mata wani irin turare,ga kamshi da kyalli dan da alama Gimbiya ba Karamin kudi ta sakar mata ba.

Sai da ta fito daga wankan ta sa ta shiga wani Abu da aka hura kamar balloon nan tagane Ashe wani turaren ta Kara zubawa da zai tsane mata ruwan jikinta kamshin ya sake zama a jikinta sai da suka kusan awa biyar tana gyareta kafin ta tafi ta ajiye mata turaren shafawa a undies da panties akan ta ringa shafawa kafin ta saka.

Gani take ko a iya haka aka tsaya ma ba sai ta sake mata wani gyaran ba amma a yadda Umsad din ke sanar mata sai tayi kwana biyar curr tana gyara ta.

Ta d’auko wasu hadin Humra da kwallaca ta ajiye mata a gaban mudubi akan ta ringa shafawa.

(Ina wayanda suka san kansu suka san tasirin da kamshi yake dashi a rayuwar Aure toh fa karki bari wanan damar ta wuceki ku k’ok’arta wajen mallakar Humra ko turaren wutan Umsad dan canza kamshin gidajenku da ni na tabbatar muku da ba zaku yi nadamar siyan kayanta ba,idan gyaran jikin ma kike so ko kuma.kayan gyaran Umsad get you a covered duk Wanda ke da bukata zai iya nemanta ta  wanan layin 08028827241 siyan nagari Maida kudi gida)

Ameera kuwa murmurshi kawai take saki bayan tafiyar Umsad din dan sai take ganin kamar canzata ma akayi jikinta wani irin laushi yayi kamar ta jaririya sai taji Ina ma Amjad tayi wa irin wanan gyaran.

Take murmushin fuskarta ya bace da ta tuna text din daya turo Mata Mai karya zuciya akan yadda ya ci burin su Gina rayuwar Aurensu har zuwa ta yayansu a cikin text din ta fuskanci ya rike Abba sule a ransa ya Kara da dan yasan bashi da kudine ma Abba Sulen ya hana shi aurenta ba wai dan akwai wani abu a tsakanin shi da su Zinatun da da kansu suka sake zuwa nema masa aurenta, daga nan ya Mata fatan alheri da addu’oin da ya sakata zubar hawaye dan har ga Allah Halin Zinatu yasa ta tsani Aurensa dan tasan ganganci ma za tayi idan ta Aure shi,dan tasan kila har kasheta ma Zinatun za ta iya yi,sai a lokacin ta tuna da zuwan da suka yi gidansu da sunan tayata murna tasan ba taya murnar suka zo ba kila zuwa suka yi su ganewa idonsu gidansu da taga Zinatu nabi da Kallo wuta naci a idonta tasan basu tab’a tunanin Allah zai d’aukaka darajar ta haka ba,idan ma wani Sharrin suka Kuma zo dashi tana addu’a akan Allah ya maida musu kayansu kansu.

Hirar da  ta ringayi dasu Fareeda ta waya shi ya ringa  debe Mata kewa a ranar,ban da Aure bata ga abinda zai saka ta rabu da iyayenta da kananneta da dake Jin tamkar su din ne rayuwarta tun a yanzu ma ta fara kukan rabuwa dasu,dan tasan Hanne kwantar mata da hankali kawai take akan zata bata Fareedar da itama ta zama budurwa amma tasan ba bata fareedan za tayi ba.

sai da tazo kwanciya Ta sha maganin Sanyin mmn mujaheed da wajen sati biyu kenan tana Sha.

Zinatu

      Da zazzabi ta koma gida tana Jin kamar ta hadiiyi zuciya ta mutu da taga canjin raywuar da Sule ya samu Hanne da ko a mafarki bata tab’a kawowa sun Isa ma takawa ba.

Kanta da taji Yana ciwo ya hana ta yiwa Sultana dake ta magana tana “Hajiya wanan karon idan har Aikin nan da akayi akan Ameera bai yi aiki ba barin garin nan kawai zanyi dan zuciyta ce kawai zata buga saboda bakin ciki,Hajiya kiga fa gidansu Ameera yafi namu yanzu,kiga yadda Wanan Hanne ta canza ta dawo wata fara tayi kib’a,tun Ameera bata ma shiga gidan Sarauta ba kiga yadda ta canza nidai Allah yasa aikin nan da muka Sha bakar wahala har dasu zuwa makabarta yayi”

Sanin idan har ba magana tayi ba haka Sultana zata dameta da magana ba zata barta taji da ciwon kan dake damunta ba yasa ta ce ” Yace zai yi aiki indai bata da tsarkin Kuma a duba mana da Yayi ai munga lokacin da zata shiga bandaki da auduga a hannunta dole wanan karon aiki da muka yi a kanta yayi tasiri kamar yadda ya fada idan daya aikin bai ci ba ai na biyun yace dole zai ci”

“Ni nafi san na dayan yaci Hajiya ai ba abinda yafi naga ranar daurin Auren bayan an cika a shelanta akan an fasa auren,amma matsawar ba haka akayi ba ai kamar ma ta samu cikar burinta ne Hajiya”

Zinatu bata ce mata komai ba dan dauriya kawai take da gaske tashin hankalin da rashin nutsuwa ya saukar mata da zazzabi  lokaci guda da taga Sule na neman finsu arziki duk sai taji tama raina gidanta da taga yadda gidansu Ameeran ya dawo.

Haka ta kwanta a daki tana juyi bayan ta sha paracetamol sultana kuwa wanka tayi ta sake kwalliya ta shigo dakin ta d’auki mukullin motar Zinatun batare da ta ce Mata ga inda zata je ba ta fice daga gidan.

Baccin Yan mintuna ne yayi awon gaba da ita Wanda mumunan mafarkin da tayi yasa ta tashi a firgice tana hada gumi, Gwaggo tayi mafarki da ita ta shigo dakin tana rike da hannun Shamsiyya da duk da ba wani sanin ta tayi sosai ba a wancan lokacin amma cikin da tagani a jikinta ya sa ta gane itace shamsiyar a kwancen da take taga Habu ya nufi wajen Shamsiyar da gudu ya rungumeta wai Yana Ashe bata mutu ba, Gwaggo kuwa ta zuba mata ido tana Kallonta

A San ta mik’e ta isa wajensu ta tashi a firgice wanan shine karo na farko da tayi mafarki da shamsiyar.

Gumi kawai ke tsatsafo mata tana wurga idanuwa da san ta gane mai maanar mafarkin da tayi,take Ayuba ya fado mata a zuciyarta da kamar ma da sandar mantuwa aka bugeta tama manta da babinsa.

Da sallati ta mik’e dan sai take san fassara mafarkinta da Ayuba ke san fallasa sirrinta shi yasa tayi mafarki da Shamsiya da Gwaggon.

Bata san ya akayi ta manta wajen sanar da bokanta  ya haukata mata Ayuba ko ya kashe shi ba,bata san mai ya mantar da ita ba.

Jiki na rawa ta d’auko wayarta ta lalubo lambar sabon bokan da sai da ta Sha wahala wajen haduwa dashi,bayan nan akan aikin da tace ayiwa Ameera sai gasu jiya a makabarta wajen Sha biyun dare sun je binne wani layya dake d’auke da sunan YAREEMA DA Ameera baro baro”

Jefar da wayar tayi da taji lanbar bokan nata a kashe ta fito daga dakin tana dole ma gobe tayi asubanci tafiya wajensa dan Ayuba zai iya dawowa a kowane lokaci haka kawai tana zaune kalau yazo ya tona mata asiri, Sultanar da take ganin tama Fi karfin wasu masu kudin wai ita Ayuba zai zo yace yana so ya Aura har Yana ce mata a gidanta zai zauna jikokinta su taso a gabanta.

Ta girgiza kai tana ayyana mutuwa ce ma tafi dacewa da Ayuba ba haukacewa ba.

Mafarkin nan da tayi ya kuma d’auke mata hankali daga kan bikin Ameera da taji ya tsaya mata a Kahon zuciya da ko numfashin kirki ba ta iya yi.

Tana kitchen tana girki Samha ta shigo da yarinyar makotansu da take ta burin haduwa da matar gidan.

Sosai taji tana so taga ta Kulla alaka da makociyarta da tasan ta balain kama kasa dan daga irin zungura zunguran motocin dake shiga da fita har da su security a masu gadin gidan tasan matar mai kudi ce ta gaske amma bata ga alamar zata samu Kulla abota da ita ba dan da alama sai Wanda ta sani take Hulda da ita.

Da sauri ta ajiye cokalin hannunta ta fito daga kitchen fuskarta a washe ta Isa wajen Samha da ta gani da wani katon akwati ita kuma kawarta Immi ta zauna da wani tab a hannunta.

“Hajiya kinga kayan da Mamansu Immi ta bani wai na sa na raka Immi biki gidan Sarki wai duk zasu je”

Kinga har da pass din gidan bikin ta saka min a akwatin

Jikin Zinatu rawa kawai yake wajen Bud’e akwatin bakinta a washe bata ma ko amsa Gaisuwar da Immi ta mata da Turanci ba dan ita bama fiye gane Turancin Immi take ba dan kamar Turancin nata na waje take yi,da alama dai bama Yan Nigeria bane su.

Kayane kala uku a dinke irin kayan da ta dinka da yafi kowane tsada a cikin kayanta da su din ne a yanzu zata saka taji tayi shigar kece raini,sai gashi wai irinsa makociyarta ta siyawa yarta a dinke bama tasan lokacin da ta samu waje ta zauna ba ta cigaba da karewa kayan Kallo cikin tsananin mamaki dan kala ne kawai ya bambanta.

Kowane da kalar takalmi da jakarsa sarka da dan kunne.

Sai wani dan envelope da ke ta walwali da ta Ciro daga cikin akwatin ta zaro iv da ta ci karo da sunan Gimbiya daga sama tana gayytae zuwa dinner din auren Yareema da sunan Ameera daga gefe.

Kanta taji ya sara mata har envelope din na zamewa daga hannunta.

A daidai lokacin da Habu ta shigo palon da sallama Samha ta tafi da gudu ta rungume shi ta hau bashi labarin kayan da maman Immi ta bata ta hau Nuno masa akwatin

Habu kuwa Immi kawai ya zubawa ido Yana Jin kaunar yarinya na shigarsa da shi Kansa bai san mai yasa idan ya ganta yake Jin wani iri a zuciyarsa ba.

Bai ma lura da halin da Zinatun ke ciki ba ya  Isa wajen da Immi ke zaune da ganinsa yasa ta mik’e tsaye ta hau gaishe shi da Turanci

Ya ruko hannunta cikin murmushi Yana amsawa  da tambayarta ta makaranta da kanneta

Cikin harshen Turanci tace duk kalau suke

Samha kuwa ta hau d’auko kayan tana ajiyewa a cinyar Habun tana “daddy kaga kayan da Immi ta bani inji mamansu wai zasu je Biki ranar Juma’a zan rakasu kaga takalmin ma”

Habu washe baki yayi ya hau daga kayan da ko baa fada masa ba ba kuma Sanin kayan Matan yayi ba sosai yasan kaya ne masu tsada

Sai a lokacin ya Kalli Zinatu da yaga gumi na tsatsafo mata duk da Ac palon ya fara magana Yana “kayan Nan sunyi kyau matar nan da alama tana da matukar kirki yanzu dan Samha ta raka su biki tayi mata wanan dinkunan”?

“Kasan bikin Ameera ne da alama matar nan tasan ma matar sarki kaga IV din dan pass din da ba kowa ake bawa ba,dinner da ba kowa suke gayyata ba shi aka bawa makociyar nan tamu da kila ma pass din da yawa aka bata shi yasa ta bawa Samha,tsakani da Allah Alhaji za’ayi iirn wanan dinner amma Hanne bata san ta gayyace mu ba”

“Taya zata gayyace ku bayan Gimbiya ce ta hada dinner ko baki karanta a  takardar bane”?

“Hmm kasan rashin mutunci suka mana da muka je Yi musu Allah ya Sanya alheri Hanne ko Kallo Bamu isheta ba,Ameera tsaki ma taja da ta ganmu”

“Toh abinka da sabon shigar arizki ai dole suyi haka ai talaka bai iya samun waje ba,Kuma da baku je din ba sai suce bakin ciki ake amma tunda har kunje ai shikenan ba sai sun Kara ganin kafarku ba,nima iyakacina naje daurin aure dan yaya Ibrahim ma bansan ya zo garin nan ba sai dazu nima ban ishe shi kallo ba dan Yana ganin kamar yanzu Sule ya fini,nidai duk ki share batunsu a fara maganar Auren Amjad da Jawaheer dan jibi zaa Kai komai da komai sunje basa san a sa lokaci Mai yawa”

Ajiyar zuciya Zinatu ta sauke tana Jin kamar tayi ta rusa ihu

Ganin Immi na k’ok’arin tafiya yasa habu saurin cewa Zinatu “Ki tashi ki bita gidan kiyiwa maman nata godiya,da alama tana san Samha,ranar juma’a sai a shirya Samhan ta bisu bikin taje ta dawo”

Mik’ewa Zinatu tayi dan ko bai fada ba dama sai tabi Samhan dan yau sai taga wanan makociyar nata mai kudin,Kuma ba Samha ce zata je dinner ba itace zata je ta ganewa idonta komai,gwara taje taci dariyarta da kyau dan tasan auren Ameera da Yareema da ake San daurawa asabar da zai kama washegari ba Mai yuwa bane ba”

Sabuwar laffayarta ta nada da ta siya da dan tsadarsa

Ta rike hannun Immi suka nufi cikin gidan

Sosai ta ware idonta tana bawa idonta abinci

Suna shiga cikin palon taga wasu Yara biyu sun bata baya shigarsu iri daya suna kallon katon tv Daya kusa cike bango guda

Haka kawai taji tana san taga fuskar yaran

Waje ta samu ta zauna da harshen Turanci tacewa Immi ta cewa mamanta tazo yi mata godiya

Immi ta hau sama da dan gudunta har lokacin yaran take Kallo basu juyo ba mik’ewa tayi dan ta Isa wajensu

Sai taga wanan karfaffan matar ta budo wani k’ofa dake cikin palon ta fito fukarta a balain hade

Tana zuwa ta rike hannunsu tabi ta k’ofar da ta fito suka shige

Zinatu tsinewa matar ta hau yi mintuna a tsakani sai gata ta dawo tana tambayarta da Lafiya

Zinatu kuwa ta ce Mata wajen matar gidan tazo tana san mata godiya ace mata neighbor dinta ce gaisawa kawai za suyi”

Karfaffan matar tace mata wai Hajiyar yanzu is busy tace oda time ta dawo

Zinatu kamar ta fashe dan bakin ciki kamar ba zata tafi ba ta daure ta mike ta bar gidan tana tsinewa hajiyar da Allah ma yasa ta talauce dan taga alamar bata da mutunci sau hudu kenan tana zuwa tana ce mata ace ba za’a samu ganinta ba.

Koda ta koma b’oye pass din bikin Yareeman tayi dan tasan a ranar jumaan dole ma ta samu ganin makociyar nata tunda har zata je dinner din.

Wajen goma sultana ta dawo na dare itama da irin pass din da tace dak’yar ta samo aka buga mata irinsa dan kamar duk Wanda aka gayyata da sunansa a ciki dan ita fa sai taga duk abinda za’ayi a wajen bikin

Allah yasa ma a ranar dinner aikin nasu ya fara ci

Zinatu itama ta labarta Mata yadda makotansu ta gayyaci Samha har da dinka mata irin kayanta

Nan Sultana ta hau Ihuun da itace ba zata baro gidan ba da alama wanan makociyar tasu mai balain kudi ce ai zuciya ba nasu bane ba ta makale mata.

Ameera

     Ba mai ganinta ya iya ganeta saboda gyaran da ta Sha da ado,tunda aka fara gudanar da shagalin bikin take ganin kamar dai mafarki take yi,dan garin kawai ya dauka wani irin hadadden kamun aka hada mata da ita kanta bata Isa cewa tasan Rabin wayanda suka kira kansu da kawayenta ba sosai kowa ke burin yaga ya shigo jikinta ya nuna ya Santa kama da ga fitar da anko da tsare tsaren da akayi duk bata san Ya akayi ba.

Cikin tsari da wayewa akayi kamu,fadar irin kudin da aka kashe a wajen ma bata bakine

Washegari akayi launching da shi ma ya hada da manyan mutane.

Ba mai yarda wai Hanne da Sule su din ba masu kudi bane dan tuni suka saje da masu kudin danginsu Sule da Na Hanne duk sun samu zuwa dan shine kusan wayanda duk danginsu Ameeran zasu samu halarta.

Dinner goben na family gidansu Yareema ne da ba kowa aka gayyata ba

A duk inda mutum ya Kai ga fadi haduwar da Ameera tayi da Yareema a ranar dinner din da kamar iya masu kudin kawai aka gayyata a wajen bata bakine.

Ameera rawar da jikinta ke tayi yasa Yareema rike hannunta gam.

Zinatu

        Duk inda taso ta gano wacce makociyar tata bata iya ganewa ba dan Immi ma bata matso kusa da inda suke zaune da Sultana dake can baya kamar wasu marasa gata ba,duk san su nuna suna da kudi Suma Basu ga masu kudin da suka sani ba a awajen.

Sultana kuwa ganin hannun Ameera cikiin na Yareema yasa taji kamar zata yanke jiki ta fadi ta kasa yarda wai Ameeran da suke fatan wani mitsiyacin yazo ya aureta

Itace wai Yareema zai aura,zata iya mutuwa idan aikin su bai ci Yareema ba gobe

Duk San taga duniya da shagalin da ake kasa hakuri tayi ta bar wajen

Zinatu ta mara mata baya dan kayan ma da take takamar ta saka da babu tamkarsa a cikin kayanta shi taga an dinkawa wasu Yara a wajen.

Waje daya suka kwana da sultana ba Wanda yayi bacci a cikinsu dan ba wacce bata ji jininta ya hau ba.

Tattaunawa kawai suke har Kuma aka kira sallah asuba.

Wajen goma Habu ya shirya shi da Amjad suka bar gidan dan su nufi wajen daurin Auren da ake haskowa life a gidan tv da Sultana da Zinatu sukayi zaman dirshan suna ganin hada hadan da ake na daurin auren

Sultana rike kirjinta kawai tayi ko kifta idonta bata yi kamar yadda Zinatu itama ta kurawa tv ido suna Jiran suji an fasa daurin auren

Sai dai me karfe goma Sha daya aka hau sakin busa da sarewa ana shelanta daurin Auren Ameera Da Yareema.

Sultana kuwa ta kaiwa tv jifa da wayar hannunta tana “an daura auren Ameera da Yareema dama na fada sai an daura”

“Saura daurin aurena dake amarya ta”

Suka Jiyo muryar Ayuba daya sa 3qtr daga bakin kofa

Zinatu da ta tafi suman wucin gadi ta zuba masa ido tana kallonsa kamar yadda yake kallonta

Ya daga mata gira cikin murmushi Yana “Ba zan motsa daga gidanan ba sai an daura min Aure da Sultana hajiya”……

Masha Allah Alhamdulillahi!💃💃💃

En’uwa kubude kunnuwanku dakyau ku jini nidin Ina fada muku wannan ne direct daga zuciya ta don nima Ina cikin Wanda sukayi amfani d turarukanta tested and trusted ina sake godiya ga Allah a koda yaushe Alhamdulillahi!

Allah ka kara haska baseera mu ta kara gano in gattattun magunguna masu kyau dan gyara zaman auremmu.

Hmm yar uwa kar in’cikaki da surutu,nesar ki tazo kusa in sha Allah,kinaso ki zama shalelen oga?kinaso duk inda mijinki ya zauna agansa yana murmushi da an’tambayesa yace Matata nike tinani?.

To matso kusa zaki samu biyan bukata da yardar Allah.

Kamar kullum kamin inyi sabon book sai na bincikomuku in gantattun maganin da zai amfani lafiyar jikinki wanda sai na tantance kamin na watsama duniya shi dan ku anfana kunson ina sonku sosai.

To yau nazo muku da er baiwar Nan wato umsad incense

Ba boka ba malam! amma akwai wani sirri na mussamman da sai kinyi amfani dashi zaki faɗamun,uwa uba Karkato da  Hankali mai gida a kanki, wanda sai Duniya tasha mamaki wasuma zasuce wani abu kikemasa ba ason sirrin Haj.umsad bane ke tasiri Akan kuba.

Yar uwa karkice mijina baya bani kudi bazan sai abinda zangyara kainaba,Aa ki daure ki saya dan gyara martabaki ta yanda bazai taɓa rayuwa in bake ba.Yazama ɗumin da yake samu daga garekine kawai,Ko mata ukku zai samu Wallahi bazaiji abinda yakeji akankiba ina da tabbaci akan haka.ya jama’a

*Munada  maganin infection da ya addabi mata,Yana saukar da Ni’ima ta ban mamaki,Yana sanya ki ɗumi mai daɗi,Yana sanyaki matsi na tashin hankali,Yana magance ciwon kafa ga wayanda suka fara manyanta,uwa uba kamshi Yah Allah yah Rahman 🥰Haɗine na mutan Sudan Wlh Babu karya a cikin sa,Kunson gwarzuwarku UMSAD INCENSE takan shiga ta fita ta kutsa kasashen ketare don samo muku ingantattun kaya Wanda ba gama gari ba. Mudinne dai bama Saida abin banza ,Sai ta shiga ta fita kamin ta watsomuku shi,Nason da yawanku kunyi amfani da kayanta kuma kunji yanda suke basai nace komi ba.

Bari inbaku sunan Wani turare nata  Laila Ahlam😍 yana daga cikin turarukan tsuguno da take sayosu dg kasashen larabawa shi din na mussamman ne dagajin sunansa kunson yasamo asaline daga larabawa masana sanin sirrin Kamshi. Don wannan baiwar tata ta dabance ko iya turaren umsad kika rike to Ina tabbatr miki Zaki mallake oga tsaff abinki don mijinki ko kurma ne saiya magantu inyaji qamshin turaren UMSAD Ina Kara gaya muku nidin tested and trusted 💯 bani d haufi kudai

Karku bari a baku labari Yar uwa maza hanzarta dan neman naki kai Tsaye daga UMSAD INCENSE Dan neman karin bayani ki tuntu6e ta ta wannan layin

*KWKWR T KWKWR*

*Page 31*

Sultana dake cike fal da bakin cikin daurin Auren Ameera kamar zata kashe kowa ma haka take ji ta Kalli Ayuban da ya tara uban Jan gashi ga wani kazaman sarka daya lafta a wuya mamakin confidence dinsa take yadda yake iya shigowa gidan Kai tsaye batare da ko fargaba ba,yadda yake magana da Zinatu batare da ko tsoro ba

Kallonsa kawai take tana Jin zuciyarta na Kara tafasa da aurenta da yake cewa zaiyi

Tana k’ok’arin magana ya daga mata hannu har lokacin fuskarsa d’auke da murmurshi Yana “banda rashin kunya Amaryata ba irin wanan tarb’ar nake so na samu daga wajenki ba na kwaso yunwa ya kamata ki samo min abu na ci”

Sultana wani irin Ashar ta lailayo masa tana Jin kamar ta daka tsalle ta shake shi ga mamakinta sai taga ya wuce ta ya taka katon kafet mai laushi da ya mamaye tsakiyar palon da katon takalminsa ya zauna akan kujera ya d’auki remote yana k’ok’arin canza Tasha

Zinatu da ta rasa ma da wane tashin hankalin zata ji ta mik’e tsaye dan sam bata san mai ya Kara hawa kanta ta manta da batun Ayuban ba,duk wanan tashin hankalin bikin Ameeran ne ya d’auke mata hankali

Sultana kuwa da kanta ya gama daurewa da matukar mamaki ta Kalli Zinatu tana “Ai Ina ga lokaci yayi da ya kamata ki fadamin alakar ki da wanan dan daban dan idan har ba wani abu ne a tsakanin ku ba bana Jin ya Isa ya iya shigowa gidanan har ya samawa Kansa wajen zama kazaman magana na fitowa daga bakinsa,ranan da ya zo na tambaye ki baki bani amsa ba mai hadinki da dan shaye shayen nan Hajiya dan hakurina ya fara karewa wallahi Allah zan kira masa Yan sanda”

“Ayuba ka tashi muje waje muyi magana”

Zinatu tace tana dan Jin tsoro na rufeta kamar ba ita ta haifi Sultanar ba yadda ta tsaya a gabanta tana daka mata tsawa baza ma taso ace Habu ya dawo ya gansa ba

Ayuba kuwa sai cewa yayi

“Wane magana Kuma za muyi Hajiya bayan Wanda mu kayi ranan ai yanzu daurin Aurena da Sultana kawai nake so naji yaushe za’a daura dan a satin nan nake so a daura amma idan har wata maganar Kuma zaki min bayan wanan gaskiya ba zan saurareki ba”

“Kutumar Uba wai wacce sultanar kake ta cewa zaka  Aura”?

“Akwai wata Sultanar a gidanan ne bayan ke”?

“Ayuba ya jefa mata tambayar tare da jifanta da wani irin murmushi

Sultana kuwa a haukace ta Kara matsawa kusa da Zinatu tana “A Ina kika samo wanan Dan shaye shayen a gaban idonki yake ce wa zai Aureni baki ce komai ba,ni Sultana wanan dan daban yace zai Aura ai wallahi sai na kira masa Yan sanda ma dan yaci mutuncina har kwantan nawa ya Kai ace a rasa mai san Aurena sai dan dabba”

Sultana ta fashe da kukan bakin ciki ta nufi wajen da wayarta ke yashe  dan akwai wani dan sanda da ta sani da suke mutunci dashi sosai

Zinatu kuwa Hankali a tashe ta Isa wajen Ayuban tana “Muje daga waje ai maganar Auren Sultanar za muyi karka bari ta kira Maka Yan sanda Ayuba”

“Ni ai bana tsoron Yan sanda Dan kawai na zo gidan Sirikaina sai a kama ni”

Ayuba yace Yana wani bouncing tare da mik’ewa a daidai lokacin Sultana ke Ihun magana ta waya akan wani dan shaye shaye ya shigo gidan

Ayuba kuwa ya tab’e baki  yayi hanyar waje, Zinatu ta mara masa baya tana Jin dama tana da Ikon da zata Kau dashi idan suka fita dinan dan bata tab’a tunanin zai tab’a dawowa har yazo Yana mata barazanar fallasa sirrinta ba.

Wajen gate suka tsaya Zinatu ta fara magana tana “nan da sati biyu nace ma ka dawo ya akayi ka dawo yanzu Ayuba,kai yanzu burinka kaga ta daga min hankali kenan”?

“Ba zan iya Jira sai Nan da sati biyu ba shiyasa na dawo dan banga ma abin da zai saka ki diba min wani sati biyu ba”

“Haka ake auren Ayuba a cikin gaggawa ba tare da wani shiri ba,ko kasan sai na samu na shawo kan Sultana da babanta zaka iya aurenta,ba zaka bari na bi komai a hankali ba,ko an gaya Maka Yar tsana zaka aura ba wani shiri da za’ayi,Ina lefen da zaka yiwa Sultana Ina sauran abubuwan da ake yi kafin Aure”?

“Ai ke Zaki yi komai ni nawa kawai sadaki ne a daura aure karki manta fa rai ake magana da kudi baya iya siyan shi,kissan kai fa kika Saka nayi ai batun wani lefe koma gida ake bayarwa kafin Aure Ke zaki bayar Ina da sadakin da zan iya bayarwa Shima dan kar naji kamar sadakarta aka bani”

Zinatu kallon Ayuban kawai take tama rasa mai zata ce masa danganta Kansa da yake da sultana ba Karamin zafi yake mata ba dan har gani take gwara taga mutuwarta da taga wai sultana ta auri Ayuba

Sultana data hango ta nufo wajensu yasa tayi saurin fara magana da “Toh shikenan Ayuba yanzu naji kaje ka dawo nan da kwana uku yau zan sanar da mahaifinta akwai dai Shirin da zanyi nan da kwana ukun kana zuwa zaa daura muku Auren”

Murmurshi Ayuba ya saki Yana”dafatan ba wani shiri kike so kiyi a kaina ba dan wallahi wahalar da raywuarki kawai za kiyi ni Ayuba nan da kike gani na wuce tunanin ki dan idan kika gwada wai yin wani Abu da ni na tabbata wahalar ma da kanki kawai za kiyi zan baki mamaki kamar gobe ne ai nan da kwana ukun bana so idan na zo ki Kara tarata da wani tsatsuniyar”

A daidai lokacin da Sultana ta karaso tana rugawa Ayuba Ashar Zinatu da duk hankalinta ya tashi da taji Sultana na bawa mai gadi umarni da  ya kulle k’ofar kar ya bar Ayuba ya fita Yan sanda suna hanya.

 ta hau dakawa Mai gadi tsawa akan ya budewa Ayuba k’ofar ya fita

Sultana da take Jin ma kamar Zinatu ce ta tsaya Sanya ta rasa Yareema da bakin cikin rasa shi ga wani kazamin dan dabban da ya zo Yana zai aureta ta tsaya a bakin gate tana “Wallahi ba zai bar gidanan ba sai Yan sanda sun zo sun tafi dashi,har cikin gida yazo Yana cewa ni amaryar sa ce,Kuma kina ta kumbiya kumbiya kin ki fada min mai hadinki dashi ai idan Yan sanda suka zo suka tafi dashi suka ci ubansa ai dole ya fada mana Mai ya taka da yake iya shigowa gidanan Kansa tsaye har yake da gut din cewa ni Amaryar sa ce”

“Sultana ki matsa ya wuce wallahi zan ci ubanki”

“Wallahi ba zan matsa ba sai Yan sanda sunzo”

Sultana tace cikin ihuu

Zinatu kuwa ta fara k’ok’arin matsar da ita da k’arfi da taji Ayuba na cewa

“Aikuwa idan suka tafi dani tas zan basu labarin komai,dan ba zan kwashi shekaru Ina fama da rashin kwanciyar hankali ba idan aka kulle mu biyun da kece silar ma sawa na dawo haka zan fi samun sallama a zuciyata”

Zinatu kuwa wani irin fincika tayi wa sultana dan jikinta rawa kawai yake tana Jin kamar kirjinta ya Faso iya maganar da Ayuban ke fada ma kawai gani take Sultanar zata fahimci mai yake cewa

Sultana kuwa ta saki ihu tana ita ba zata bar Ayuba ya bar gidanan ba kar mai gadi ya sake ya bude k’ofar a daidai lokacin da suka ji dirin motar Habu

Zinatu ta saki sultana da sauri ta nufi wajen Ayuban dake tsaye kyam ba alamar wani tashin hankali a tare dashi ta hau magana tana “Ayuba dan Allah ka tafi karka tsaya kula kowa na ma alkawari zan aura ma Sultanar kaje Dan Allah bana so a yanzu baban sultanar ya gano wani Abu”

“Sai na gaisa dashi zan tafi dan ya kamata ace na fara gabatar masa da Kaina kafin kwana ukun da kika dib’ar min”

Daga haka Ayuba yayi hanyar gate a daidai lokacin da Habu ya shigo gidan Yana Saba babbar riga Amjad biye dashi a baya,Zinatu kuwa ta daure Wajen danne tashin hankalin da take ciki,dan tasan tana tsara Habu shikenan

Habu turus ya tsaya Yana kallon Ayuban da ya Sha armless da 3qtr kana ganinsa kaga irin tantiran Yan iskan nan

Amjad Kansa Ayuban yake Kallo cikin tsananin mamaki ya Kalli Mai gadi da yayi cirko cirko Yana kallonsu

Sultana kuwa ta nufi wajen Habu da gudunta tana “Daddy wanan dan daban sau uku kenan Yana zuwa gidanan har cikin palo yake shigowa Yana yiwa Hajiya rashin kunya wai akwai wani abu a tsakanin su har Yana cewa ni zai Aura,daddy ka tambaye shi wane shi mai hadinsa da Hajiya dan taki ta fada min”

“Alhaji karka bi takan maganar Sultana wanan sunan shi Ayuba a gidansu Hajiya fattu yake Aiki ta bashi Sako ne ya kawomin bansan mai matsalar sultana ba”

“Amma idan Sako zai kawo miki sai ya shigo min har cikin gida ba zai iya bawa Mai gadi ya baki ba,akan me zaki bari ya shigo min har gida”?

Habu yace rai a balain bace yadda yayi magana cikin dan tsawa ya Hana sultana karyata Zinatun ya cigaba da bambamin fada

Amjad kuwa ya bud’e kofar gate din ya nuna wa Ayuba hanya Yana yazo ya fita

Ayuba kuwa ya saki murmurshi Yana “Babban Yaya ni ban ga abin korata ba nifa zan Auri Sultana,Alhaji ya kamata Hajiya ta Maka bayani dan nine zan Auri Sultana idan Allah ya yarda Kuma har ta amince akan zata bani aurenta”

“Daddy kaji mai yake cewa ko”?

Sultana tace cikin ihu

Habu da Amjad kuwa mamakin da ya basu ya hana su magana har Ayuban ya fice Yana dagawa Zinatu hannu da sai Nan da kwana ukun.

“Hajiya waye wanan dan iskan yaron?Mai hadinki dashi wane magana naji Yana yi”?

“Alhaji kai ma da wata magana na fada maka a gidan Hajiya fattu yake aiki haka yake Abu kamar mara hankali haka nan da kake ganinsa Kansa Ba daidai yake ba gida Kuma da ya shigo laifin mai gadi ne dan da ace ya hana shi shigowa da bai Isa shigowa ba Yunusa daga yau idan ya sake zuwa karka sake barinsa ya shigo gidanan”

Amjad kuwa girgiza Kansa kawai yayi ya nufi cikin gidan dan shi kam ba wani ganewa Zinatun yake ba.

Zinatu kuwa ta wayance da tambayar Habu daurin Auren Ameeran

Sultana kuwa dakinta ta shige tana risgar kuka,dan ita kadai tasan wutar dake ci a zuciyarta

Ta kasa yarda wai Ameeran da take zagi take kusheta a wajen kawayen ta itace ta auri miji na kece raini mijin da Mata ke rububin so.

Hawayen dake ta zubo mata take sharewa tana Jin Habu na labartawa Zinatu yadda aka gudanar da daurin Auren daga nan Kuma suka fara maganar lefen Amjad dan an kai kudin Auren har an sa rana.

Zinatu

     Allah Allah take Habu ya fita ta san nayi dan idan bata yi gaggawan Kau da Ayuba ba tasan dole sai ya tona mata asiri.

Wajen Uku Habu ya fita dan bai fiye fita da wuri ba a weekends.

Yana fita ta shiga dakin sultana da ta tarar da ita tayi rub da ciki daga yadda take dan kada kafarta tasan idonta biyu

Kaf cikin yaranta ba wacce take Jin ta daban a cikin zuciyarta sama da Sultana.

Dan zata iya cewa halinta duk ta kwaso ko da suke Yara sai su yi laifi gabadaya ta daki sauran amma taki dukan Sultana.

Cikin Kuma yaran nata itace tafi kowace kyau shi yasa tun ma tana yarinya taci buri a kanta,a burinta kullum taga sultana ta samu mijin Aure na kerewa Sa’a sai gashi Yareeman da ta so ace shi ya aure ta,gasi gashi yaje ya auri Ameeran da take jinta a Kahon zuciyarta dan gani take tun tana yarinya take ta shan gaban sultana ta Fanin komai Wanda hakan ya saka mata mugun tsanarta.

A gefen gadon ta zauna ta fara shafa kan Sultanar da ya Sha kitso attach har gadon baya tana “Ki kwantar da hankalinki sultana Yareema sai ya saki Ameera karki manta abinda boka yace mana idan har baa fasa auren ba daya aikin da yayii zai yi aiki,kema Kinsan irin mutanen da Yayi wa aiki yadda suke labarin aikinsa Ina da tabbacin nan da Yan kwanaki zamu ji labarin Ameera ta zama bazawara”

“Nifa na Daina yadda da duka bokayenki dan dukansu makaryata ne maha’inta macuta,har ace baza su iya hana Auren Ameera da Yareema ba,idan har sun iya aiki ai bai kamata wargaza auren ya gaggaresu ba har yanzu kafata da na kurje a garin gudu da muka je makabarta wallahi ciwo yake min,ni na fidda rai kawai nasan Ameera ta Sha gabana a komai dan ni banga Wanda zan Aura yayi daidai da Yareema ba”

“Ki bar fadin haka Sultana indai Ina rayye sai kin Sha gaban Ameera Ina nan da ke Zaki ce ni na fada Miki,daya aikin da nace yayi wa Ameera nasan sai yayi aiki ni na fada miki”

Sultana tsaki taja tana “sai kiyi tayi ai ni ki rabu dani kawai ki daina Saka min rai da abinda ba zan samu ba zan Saka shamsu kawai ya turo.manyansa kina zaune zaki ga Ameera da ciki,ai ta k’arfi da yaji Ameera ta gagaremu”

Duk da Zinatu taji zafin yadda Sultana ke mata magana haka ta cije ta saki murmurshi tana kar ta damu yareeman ma zata aura,daga haka ta tashi ta bar dakin ta koma dakinta ta shirya ta d’auki mukullin motar ta ta fito dan a yanzu Ayuba take so tayi maganinsa kafin ta san mai ya dace tayi,tana da yakinin aikin da bokan yayi wa Ameera dole ma zai ci tunda har aka daura Auren dan dama bokan yace musu da wuya idan zaa fasa dan Shima Yareeman da danginsa ba haka suke zaune ba,amma daya aikin kam dole ma zai yi dan bai ma karbi kudin wanan Aikin ba shiyasa ta yarda akan ya iya aiki dan cewa Yayi sai aikin yayi zata bashi kudin

Wajen Magriba ta isa wajen bokan bata samu ganinsa ba sai wajen Tara.

Maganar Ameera ta fara masa ya ce mata dama ai ya fada mata auren da wuya ya fasu amma daya aikin kam zai kama Ameera wanan a zaune take

Zinatu sai a lokacin ta ji hankalin ta ya dan kwanta dan ko da Sultana ba zata auri Yareema ba zata so Yareema ya saki Ameera kowa ma ya rasa.

Maganar Ayuba ta sako masa ta Kara da “Dan Allah Mallam ayi min aikin da zan Kau dashi kawai idan ma hatsari zaa saka yayi ayi min aikin da Kawai zan Kau dashi dan barinsa ma a rayye ma ganganci ne.

Kwaryar gabansa ya jefawa wani farin Abu dan Yana jefawa Wanda kake maganarsa zai bayyana

Wanda ya bayyana a cikin ruwa tsaye da singlet Yana busa sigari yasa shi mik’ewa tsaye da sauri

Zinatu kuwa da ta tsorata da yadda ya mik’e itama ta mik’e tsaye tana “Lafiya kuwa”?

Motsin da taji a bayanta yasa ta juyawa sai taga Ayuba ne a tsaye da singlet da sigarinsa a hannu

Bokan kuwa ya hau magana Yana “Dan nawa kike so ki kawar”?

“Sirikata mai kike nema anan”?..

Ameera

      Sai da ta samu kwana biyu tana sauke baccin Gajiya dan tunda aka fara shagalin bikin bata Kara wani baccin kirki ba har Kuma aka gama shagalin Biki aka kawota wajen Gimbiyar dan bata san dalilin da ya sa baa fara kaita gidanta ba aka fara da kaita wajen Gimbiyar da wani kebabben waje aka kaita da wasu hadimai biyu bata da aiki sama da bacci idan ta farka kuwa gyara kawai take Sha daga na jiki har magunguna da suka fara isarta da akan dole take Sha.

Nasihar Abba Sule da Hanne na manne a kanta dan da aka zo tafiya ita haka ta rungume su biyun tana ta rizgar kuka,dan ba dan Aure ba bata Jin akwai abinda zai tab’a sawa ta rabu dasu,haka suma suka ringa sharar kwalla suna saka mata albarka da nasiha.

Daidai Gwaggo da ba wani motsi take iya yi ba duk da a yanzu akan ga ta dan motsa din sai da Abba sule ya dora hannunta akan Ameeran Yana “Gwaggo ki sawa Ameera Albarka zata tafi gidan mijinta”

Ko dan nasihar da suka mata zata yi iya k’ok’arin ta wajen  bin Yareema sau da kafa,ta waya kawai suke magana tunda aka kawota,dan ita bama tasani ba ko Al adar gidan Sarautar ce haka.

A ranar da ta cika kwana biyar a gidan sarkin

Da yamma aka shiryata cikin wani irin alkyabba bayan uban gyaran da Umsad ta sake  mata ta jikata da humrar da ta Kasa gane ma kalar kamshin da yake.

Gaban Gimbiya aka kaita kanta a kasa ta hau gaisheta dan ita bama ta iya irin gaisuwar da suke ba.

A madadin ta amsa sai taji ta kamo hannunta tana “tun Ranar da na fara ganinki naji kin shiga zuciyata yadda nake Jin Yareema a zuciyata haka nake Jin ki a zuciyata,Allah ya baku zaman lafiya karfe bakwai jirginku zai tashi wata uku za kuyi kafin ku dawo”

Ameera Kara sunkuyar da kanta tayi tana Jin dan Jin fargabar barin kasar da bata ma san wane kasa zasu je ba a matsayinta na wacce ko Abuja bata tab’a zuwa ba,tafiya wajen da ba kowa nata batare da tasan  kowa ba yasa taji wani iri a zuciyarta,idan akwai abinda ke sa ta mik’ewa zaune idan ta tuna bai wuce wane irin rayuwa za tayi da Yareeman da ba wani shakuwa tayi dashi ba,basu tab’a zama face to face sunyi maganar awa guda ba,wani irin nauyi da kunyarsa take ji Kuma shi da alama akwai dan sarauta a jikinsa baya iirn zakewar nan suyi hira ko ta waya.

Nasiha Gimbiya itama ta mata wajen shidda da rabi sai ga Yareema ya shigo ta cikin alkyabar ta dan saci kallonsa,sai ta tsinci kanta da kallonsa dan sai take ganin kamar dai ya aureta ne bai santa ba sosai dan gani take ya wuce ajinta ya fita komai ma,a gefenta ya zauna Shima Kansa a kasa Gimbiya ta masa nasiha ta Kara  damka masa amanar Ameeran.

Shigowar wani yasa ya mik’e  a karo na biyu kenan ya Mika hannunsa ya kamo hannunta dan a wajen dinner ya rike hannunta daya sa jikinta rawa har sai da ya cika Mata hannu sai Kuma yanzu.

Muryarsa da taji a saitin kunnenta ya katse mata tunanin da ta tafi

“Ya kamata ki rage wanan tsoron naki dan ni ba dodo bane am your husband”

Ameera yawu ta hadiye batare da tace komai ba har ya bud’e mata bayan wani katon jeep ta shiga a hankali.

Tana Jin har lokacin zuciyarta na wani irin bugu.

Ta sunkuyar da kanta kasa kamar zata hada kanta da gwiwarta a lokacin da Yareeman Shima ya shigo dan ta fahimci bai fiye San wanan abubuwan girmamawan nan ba yafi san private life.

Jikinta rawa kawai yake a lokacin da taji ya Kara kamo hannunta cikin nashi hannunta da ta damke da k’arfi ya bud’e a hankali ya hau mata tafiyar tsutsa a hannu.

Duk sanyin ac bai hana taji gumi ya rufeta ba,dan wanan shine karo na farko da zata ji ta kusa da namiji haka sosai motar ma kamar ba tafiya yake ba

Ga kamshin humrar jikinta da nashi da suka hade suka bada wani irin kamshi.

Hannunta cikin nashi ya sauko da ita daga cikin motar

Ameera rayuwar da duk bata kawowa kanta ba matsayin da bata tab’a tunanin takawa ba sai gasu jirginsu ya daga zuwa Paris amarcin ma ba zasu yi a Nigeria ba.

Tana Jin idon Yareema a kanta amma ta kasa ma dagowa ta kalle shi dan gam ya rike mata hannu….

Masha Allah Alhamdulillahi!💃💃💃

*KWKWR T KWKWR*

*Page 32*

    Zinatu jikinta rawa kawai yake tana kallon Ayuban da ya karaso shigowa dan Karamin dakin har lokacin busa sigarin yake ji tayi kamar ma numfashinta ya bar gangan jikinta

Maganar bokan ya Kara dukan kunnenta da “Dan baban nawa kike so ki Kashe”?

Ayuba dariya ya kwashe dashi daya ga Zinatu ta zube a kasa saboda rawar da jikinta ke yi

Dan sai a yanzu ma ya gano dalilin zuwan nata

Sigarin hannunsa ya karasa zukewa ya jefar dashi Yana “Sirikata yanzu ke so kike ki Kau dani saboda kawai nace Ina San yarkii da Aure?dama Shirin da kika ce zakiyi na ki Kau dani ne saboda kar ki bani Yar cikinki har na zama abin gudu da kyama a wajenki bayan kece silar ma wargaza nawa rayuwar?

“Wai ka santa ne dan Babba Mai hadinka da ita”?

Bokan yace yana jifan Zinatu da wani irin Kallo dan ko yatsa ma baya so yaga an nuna dansa guda daya tilo da yake ji dashi

“Baba ai wanan sirikita ce itace hajiyar da nace ma tasa na Kona wata Mai ciki da yarinya,itace wacce tasa na bar karatun da ka turani na koma wani wajen na dawo haka”

“Dama kece kika wargaza min rayuwar da”?

Bokan yace cikin wani irin hucci dan sai da ya kusa zaucewa saboda rashin ganin Ayuban da sai da ya kwashi shekaru kusan goma Sha bai Kara Sanin inda yake ba,dan karatu ya tura shi yayi,bai Fi shekara biyu ba kenan da dawowar tasa,inda duk da shi din hatsabibine bai so Ayuba ya zama gaggarare ba”

Zinatu da taji dakin na juya mata da ta gano abinda ke Shirin faruwa da ita ta mik’a hannunta dake karkarwa tana “Mallam dama Ayuba danka ne”?

Dariya Ayuba ya Kara kwashewa dashi Yana “Babu ko tantama Hajiya mahaifina ne Kuma ko wani wajen kika je ba Zaki tab’a cin galaba a kaina ba ai na fada miki,na Dade banga mace mai san zuciya da san kanta ba irinki,wato na gama miki amfani ko ba zaki iya bani Auren Yarki ba”

Zinatu zubewa tayi akan gwiwarta ta hade hannayenta ta fashe da kuka dan tasan babu mai kwaceta daga hannun mahaifin Ayuba,bata manta irin rashin imaninsa ba “Dan Allah dan Annabi Ayuba ka rufa min asiri dan Allah Mallam ka taimaka min ku rufa min asiri duk abinda kuke so wallahi zan muku banda Auren Sultana ba wai dan na raina ka ko Ina kyamarka ba, ba wai  bazan iya  baka Aurenta bane ba.

 An sawa Sultana rana tana da Wanda zata Aura   zan nemo ma wata budurwar Mallam kayi aiki akanta kayi aiki akan iyayenta yarinya ma tafi sultana kyau sunanta Fareeda bari na nuna muku hotonta kugani”

Zinatu tace cikin rawar murya tare da d’auko wayarta dake cikin jaka sai da tayi da gaske ta samo hoton Fareeda kanwar Ameera ta haskawa Bokan da ya zuba mata ido kamar yadda shi ma Ayuban ya zuba mata ido fuskarsa d’auke da murmurshi

“Kaga yarinya ce ma bata Kai sultana shekaru ba Dan Allah Ayuba ka taimaka min”

Zinatu tace tare da sake rushewa da kuka dan a yanzu tasan ko ta asiri ma zai iya Auren Sultanar

Bokan kuwa ya Kalli Ayuba Yana “Dan Baba ka fada min duk abinda kake so a yanzu nan zan aiwatar ma dashi”

“Hajiya sultana nake so ba wanan yarinyar da kika nuna min ba,Ina da damar da zan sa mahaifina yayi aiki akan sultana da kafarta tazo wajen da nake amma ba zan haka ba dan bada wani abu kika sa na biyewa san zuciyata naje na kashe mace Mai ciki da yarta ba,tunda har kika nuna min kiyayya Karara ni ba haifata a kayi ba wato ni a yanzu bana gari bane ba ban dace da Auren yarki ba, toh zabi biyu kacal zan baki ko ki bani Auren sultana ko na tona miki asiri a wajen mijinki na Kuma sa mahaifina ya warware duk wani aiki da ya tab’a miki dan ke din azzaluma ce muguwa”

Zinatu da rarrafe ta karasa wajen Ayuba ta kwanta a kasa ta rike kafarsa tana magiya.

Boka kuwa ya dagewa Ayuba akan ya bar shi kawai yanzu nan yayi aiki akan Sultana ta haukace akan San shi bama duk zasu tab’a samun kwanciyar hankali ba sai sun aura masa sultana

Ayuba kuwa ya girgiza Kansa Yana “kar ayi musu komai baba nafi so ta bani yarta da kanta na aura bana san wani asiri hajiya mai kika ce dan Ina da Wajen da zanje jibi su Mallam zasu zo da sadakin da za’a daura mana Aure da Sultana,idan kuma kince Aaa toh a jibin zan tona miki asiri har gidansu da aka tab’a basu kyautarsa kika sa aka Kona nasani dan Wanda ya aiwatar Miki da aikin abokina ne”

Zinatu kirjinta da take Jin nauyinsa kawai ta rike hawaye na zubo mata a kaf rayuwarta bata tab’a shiga tashin hankalin da ya Kai Wanan ba,Ayuban dake tsaye kawai take Kallo taya da hankalinta zata cewa Sultana ta auri Ayuba, kaf yaranta ba Wace taci wa burin auren shaharareen Mai kudi sai sultana,Ameera irin wanan Ayuban ta sha yi mata addu’ar samu da guzurin ma cikin shege da abin kunya,taya Ameera na Auren irin Yareema ita kuma Sultana da ta taso cikin gata ta bage da Auren irin Ayuban da har gwara talaka tukuf akansa,dan dabba dan shaye shaye da Kallo daya zaka masa kasan ya rike a shaye shaye shi ne wai zai auri Sultana.

Tuna rufaffen sirrinta da zai tona da hakan na nufin faruwar abubuwa da yawa ciki kuwa kila har da rabuwa da aurenta da take fatan a ce mutuwa ce zata raba, kila ba iya wanan ba zaa iya kulleta ma har karshen rayuwarta,ba zata so asan itace ta kashe shamsiya da ciki ba,dan tasan karfin asirin da tayi wa Habu yasa baya maganar mutuwar shamsiya dan bata manta yadda ya fice a hayyacinsa da yakin da ta Sha kafin ya Maida ita dakinta bayan mutuwar shamsiya wani zubin ma kamar asirin na dan sakinsa yayi ta maganar Shamsiya Yana Ina ma ta imitihal na rayye ya ringa ganinta Yana tunawa da ita.

Idan har ya tuno shamsiya bata sake gane Kansa sai ta koma an sake sabunta aiki akansa,tasan yanzu idan har asirinta ya tonu aikin da tayi akan Habun ya warware da Kansa ma zai daureta uwa Uba ya gano tana da hannu a kwanciyar Gwaggo da ta kwashi shekaru dan ta kwantar da ita ne saboda tasan idan ba haka tayi ba a gaba zata iya sawa Habu ya kara yin wani auren amma idan ta kwantar da ita ba yadda zata Kuma iya masa umarni,a haka wai dan kar nauyin ya Mata yawa shi yasa ta bar ta a rayyen dan gwara taji da nauyin kissan kan  da tayi wa shamsiya akan ta karawa kanta da Gwaggo da a yanzu ma ba maraba ne da ita da shamsiya ba.

Hannunta kawai ta dora akai tana risgar kuka dan tana cikin tsaka mai wuya a duk sharadun da Ayuban ya bata san wane za ta zaba ba, ganin Auren sultana da Ayuba na iya buga mata zuciya,tonuwar asirinta ma na iya buga mata zuciyar.

“Toh nidai  Ina da abin yi ba zan zauna ki ringa bata min lokaci ba a cikin biyu dole ayi daya jibin nan ko auren nida sultana ko Kuma tonuwar sirrinki”

Ayuba yayi hanyar waje Zinatu dake Jin kamar ta mutu ta sa ihu tana “Na yarda nace ma na yarda”

“Dame kika yarda din”?

Zinatu kuka kawai take kamar ranta zai fita dan sai take Jin kamar ta bari  ya tona mata asiri da ta d’auki yarta da take jinta kamar ranta ta bawa Mara galihu dan iska da mahaifinsa rikakken boka ne mushriki,amma tonuwar asirinta ma zai iya shafar Sultanar

“Na yarda ka auri Sultanar amma dole mallam yayi aiki akanta da mahaifinta dan nasan ba zasu tab’a yarda ba,dole ka zama na gari ka daina shaye shaye ka cire wanan karfunan daga jikin ka ka aske gashinka zan baka kudi ka gyara fatar jikinka”

Zinatu tace tana Jin kamar zata mutu da ta zuba masa ido ta kasa yarda wai wanan da ko wanki ba zata iya bashi ba shi ne zai auri Sultana

Da wani irin murmushi Ayuba ya dawo baya ya tsugunna a gaban Zinatun Yana “Zaluncin da kika saka nayi a baya ya isa haka ba zan Kara aiwatar da wani zaluncin ba,ba zan yiwa kowa asiri ba,dan koman daren dadewa asiri karyewa yake,karki ga nazo a dan boka halina da nashi ba daya bane ba,Ina da ragowar Imani a tare dani ba wanda zan juyarwa Kai da kanki zaki san yadda Zaki shawo kan sultana da babanta ki aura min ban damu da yadda za kiyi ba”

“Taya zaka ce ba zaa juyar musu da Kai ba taya a cikin hayyacinsu zasu tab’a yarda,ka manta iirn tsanar da sultana ta Maka?ka manta iirn tsanar da Mahahfinta yayi wa Yan shaye shaye idan baa juyar musu da Kai ba taya zasu tab’a yarda”

“Wanan fa matsalarki ce ba tawa ba,ba zan kare raywuata a firgice da rashin nutsuwa ba kamar yadda Ina ga har ki koma ga Allah rayuwarki a haka zai tafar miki a firgice dan asiri karya ne koman Daren dadewa sai ya karye,a gaba ma ya daina ci,ke zaki shawo kansu nidai jibi zan zo a daura mana Aure”

Ayuba yayi hanyar waje Zinatu ta tashi a guje ta bishi a baya

Tana “Ayuba na hadaka da girman Allah ka sasauta min zuwa jibin nan kayi min alfarma na karshe a yanzu nasan Kafi karfina ban Isa ma na sake ja da Kai ba,sai ka bani lokaci zan iya shawo kan Sultana da babanta tunda har kace kar a asirce su,Kuma a yanzu idan naje musu da maganar dole zasu dago da wani Abu dole sai na fito na fada musu dalilin daya sa nace kai zata aura dan girman Allah Ayuba ba dan halina ba”

“Nan da yaushe zan baki”?

“Nan da wata guda dan Allah Ayuba kaga za’ayi bikin Amjad baifi saura sati uku ba idan aka gama da bikin sai nayi dabaru wajen shigo da Kai Dana Zinatu zuwa lokacin ka dagawa shaye shaye kafa zan baka kudi ka gyara kanka zan Nemo kudi Mai yawa na baka kaja jari”

Murmurshi Ayuba yayi Yana “Saboda ke ba zan canja komai ba dadina da gobe saurin zuwa kafin wata dayan kije kibi wasu mallaman ki Kai musu sunana,kafin wata dayan kiyi duk yadda za kiyi wajen ganin kin Kau dani,abinda kawai zan baki shawararsa shine karki wahalar da kanki ba Abunda zaki iya yi akaina,idan kin Saba nassara akan kowa akaina ba zaki tab’a nassara ba,na baki nan da wata dayan”

Zinatu da jikinta ke rawa da taji duk ya zayyano mata Abunda ke ranta ta zube a kasa ta hau masa godiya

Bai ko bi ta kanta ba ya shige cikin gidan.

Zinatu ta tashi da gudu ta nufi wajen motar ta

Da ikon Allah ta koma gida dan kuka kawai take ta sharba dan tasan tana cikin tsaka mai wuya

Bata Kuma Isa gidan ba sai wajen Sha dayan dare.

Habu kawai ta tarar a palon cikin jallabiya ta Maza,da wayarsa a hannunta da tasan ita yake ta kira dan taga miscal dinsa rututu dan a motar ta ta bar wayar.

Karyar motarta ne ya lalace Kuma ta hadu da barayi a hanya kawai ta Masa ta Sanya masa kukan tashin hankalin da take ciki.

Habu hankali a tashe ya hau rarrashin ta har Yana Neman kaita asibiti saboda zazzabin daya rufeta.

Sai gashi kamar wasa sai da aka kwantar da ita din,inda ana auna jininta aka ce ya hau,dan Sultana ce ta Kara siyar mata da jaridar da ya hau mata da jini,ta nuna mata hoton Ameera da Yareema hannunsa a cikin na juna suna dago hannu a lokacin da zasu hau jirgi su tafi Paris honey moon

Kuka kawai take tana hararo Sultana da Ayuba kila a cikin wanan kauyen taya Ayuba zai Auri Sultana da itama ke ta kuka da ganin Ameera taje kasar da take mafarkin zuwa a rayuwarta a duk kasashe ba inda take balain burin zuwa sama da Paris sai gashi Ameera can suka tafi honey moon.

Satin ta daya a asibiti aka sallamota.

Tana daki a kwance tayi zuru tana tunanin hanyar da zata bi wajen dakile maganar Auren Ayuba da sultana da take jinsa a yanzu shine babban damuwarta da tashin hankalinta.

Halin da take ciki ya hana ta ma zagewa wajen shirye shiryen Auren Amjad da ake tayi dan saura sati biyu inda zaiyi daidai da wata gudan da ta dibawa Ayuba duk kibarta sai gashi tayi wani iirn rama.

Shi Kansa Habu sai da damuwar da take ciki ya hau Neman shafarsa.

Bata san lokacin da Sultana ta shigo ba sai da taji ta zauna a gefenta ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi

“Wai ke Hajiya ko dai wani cutar ne dake kike ta boyewa ne,kinga yadda kika dawo kuwa?

Da ido kawai take bin sultanar hawaye cike a idonta na ganin zukekiyar budurwa irin sultana wai ita zata bawa Ayuba.

“Ya kamata kan ki ware kafin bikin Yaya Amjad ke kinga Shirin da ake tayi a gidansu Aunty Jawaheer din Kai ai da biyu nake shishige musu wallahi nidai tunda bani da Sa’a a rayuwata duk abinda nake so Ameera ce take samu na hakura haka nan zan lallaba da Shamsu mun gama tsayar da magana dashi idan an gama Auren Amjad zai turo manyansa duk da bai Kai Yareema kudi ba Suma suna da nasu arzikin,nasan dama yaudarar kaina nake idan nace zan cigaba da sa Rai da mutuwar Auren Ameera da ya tafi sati uku kenan banji labarin komai ba”

Zinatu ajiyar zuciya ya sauke dan tashin hankali hawa hawa ne tuni ta manta da wani aiki ma da suka yiwa Ameeran yanzu bata shi ma take ba ta Sultanar take,yau ba dan wanan masifar daya bullo mata ba Allah kadai yasan shagalin da za tayi a bikin Amjad,dan tasan su jawaheer sun ninkesu a arziki nesa ba kusa ba auren Amjad da jawaheer kamar wani cigaba ne a garesu.

Kayan da sultanar ta karbo daga wajen dinkin kawai take nuna mata akan shamsu ne ya biya mata kudin dinki ta Kara da “Yace ma anjima zai zo ya duba ki ni matsala ta dashi fa kamar Yana dan zuke zuke”

“Ba zaki Aure shi ba Sultana ki rabu dashi”

Taji kamar an fusgo maganar daga bakinta

Sultana wani iirn Kallo ta fara mata na wasu Yan mintuna kafin ta mik’e tsaye tana ” Idan ba aure shi ba kin samo min wani mijin da zan aura ne”?

Na samo miki mijin Aure sultana idan baki Aure shi ba zan iya mutuwa,mutuwa ma zanyi”

Sultana dariya ta kwashe dashi tana “nidai hajiya tunda fa kika kwanta rashin lafiya na lura kanki ba dadi wato mutuwa za kiyi idan ba auri Wanda kika samo min ba to waye wanan din da kika samo min”?

hawayene kawai yake zubowa Zinatu tana sharewa da hannu dan bata kawo akwai ranar da Yar cikinta zata danganta ta da mara hankali ba.

Kamar wata sa’arta ta Kara daka mata tsawa tana “Wane miji kika min da idan ba aure shi ba zaki mutu”?

“Ayuba ne wanda na zaba miki ki Aura sultana”

“Waye haka”?

Sultana tace tana k’ok’arin tuno waye ma Ayuban

Zinatu sai taji ta kasa fada mata wane Ayuban take nufi

Sai da taga Sultana ta haukace mata da tambaya waye haka tace “Wanda yake zuwa gidanan da kike cewa dan dabba”

Sultana ido ta zaro tana kallon Zinatun dake ta share hawaye

Ta ja da baya tana Kallonta ta karkada kunneta tace “Sake maimaitawa naji mai kika ce”

“Auren ku na dan lokaci ne sultana ki daure kimin biyayya”

“Lailai Hajiya kin haukace kin samu tabin hankali bansan ma baki da hankali ba sai Yau”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Sultana Hajiyar kike cewa ta haukace a Kuma cikin hayyacin ki kike kuwa”?

Amjad da shigowarsa kenan da Habu suka nufo dakin dan su duba jikin Zinatun suka ji maganar da sultanar ke jifan Zinatun da shi.

Habu da yaji Kansa ya Sara masa kar jikinsa na d’aukar rawa da Jin iirn lafazin da ya fito daga bakin sultanr ya matsar da Amjad gefe Yana “Sultana Mahaifiyar ki kike zagi”?

“Tarihi ne ya maimaita Kansa dan itama haka ta zagi Mahaifiyar ka yaji kamar an rada masa a kunnensa sai yaji Kansa yayi wani Irin Sara masa da Gwaggo ta fado masa a rai”….

Birnin Paris

    Duk inda Ameera taso dakewa kar ta nuna kauyancinta sai da ta kasa dan haka ta ajiye kunyar da take ji ta ringa karewa ko’ina Kallo wani hotel suka sauka da aka yiwa ginin glass daga dakin ma da suke duk glass ne kana iya hango komai a waje sai dai idan ka zuge labule.

Yareema kuwa ganin gabadaya ta kasa sakin jikinta dashi yasa bai wani matsa mata ba ya barta har zuwa lokacin da zata dan fara sakin jikinta dashi kwana uku suka yi tana kwana akan kujera kaya ma sai ta shiga bandaki take iya sawa.

Bai san har yanzu akwai mata masu irin wanan kunyar ba dan abinci ma bata iya ci a gabansa sai ya fita waje.

Ganin idan ya biye mata haka zasu cigaba da tafiya yasa ya fara tilasta mata wajen cin abinci a gabansa,

A kwana na hudu ya dage Shima akan Kujerar zai kwana akan dole ya tilasta mata ta kwana a gadon.

Dan san da yake mata yasa yake so duk abinda zai mata ya zama asan ranta ne baya so ya tilasta mata.

Kwanan da suka fara yi a gado daya ya kuma fara hargitsa shi inda baya iya jurewa har sai ya tab’a ta,inda kamar zai zauce yake ji a bai ma Santan ba dan wani iirn siihirtacen kamshi da taushi ke tashi a fatar jikinta,duk ashe kallon tsoro yayi wa Ameera cikinta fatarta yafi ma wajenta kyau.

Idan akwai abinda ke damunsa bai wuce kunyarsa da take ji ba ya rasa yadda zai mata,ko Yaya zai tab’a jikinta haka zai ga jikinta na rawa har dasu gumi.

A haka ya ringa bawa Kansa hakuri har yaga ta dan fara sakin jikinta dashi suka tsaya a iya wasanin da nan ma sai tayi ta boye b’oyen fuska sati biyun da suka yi kawai Ameera tayi wani irin kyau ta canza kamar ba ita ba.

Ameera

A karantar da tayi wa Yareema mutum ne shi mai balain tsafta duk inda ta kai ma ga tsaftar ta sai taga ya dameta ya shanye,hakan yasa itama ta dage wajen kara tsaftar dan a rana itama tana brush ya Kai sau hudu,turaren da yake fesawa a bakinsa itama shi take fesawa a bakinta,ba abinda bashi da turarensa.

Tun bata ma iya sakin jikinta tana Jin zuciyarta cike da fargaba har sai da tazo ta fara sakin jikinta tana Jin Kuma Yareema a zuciyarta.

A ranar da suka samu sati biyu da kwana uku ya dan fita yace mata zaije ya dawo ita kuma tayi amfani da wanan damar wajen shiga wanka inda sai a ranar ta bud’e wani akwatinta da duk aka zuba mata tarkacen humrarta da sauransu.

Ta hau gogawa a jikinta

Da bayan kunneta sai da ta gama gogawa ta rufe ta maida cikin akwatin.

Ta nufi wajen da kayanta suke da duk Yareema ne ya siyo mata bai bari ma an tafi da wani kayan lefe ba.

Wani riga da skirt da wai a haka shine Mai mutuncin ciki ta saka tayi parking din gashinta da ta shafawa turaren gashi Shima ta zauna akan kujera ta nemo lambar Hanne dan wayar da take yawan yi dasu ke rage mata kadaici.

A wajen Hanne take Jin labarin auren Amjad da jawaheer da yasa taji zuciyarta tayi matukar sosuwa.

Bata ma san zata ji ta damu ba sai da aka sanar mata da Auren da zaiyi sallama kawai tayi da Hanne ta kashe wayarta.

Ta hau share hawayen da ita kanta bata san dalilin yinsu ba.

Shigowar Yareema dakin yasa ta saurin fara share hawayen nata

Shi kuwa ya nufi wajen da take ya  zauna a gefenta bai yi wata wata ba ya jawota ya rungumeta.

Sai taji tana bukatar ma hakan sai tayi lamo a kirjinsa tana Jin bugun zuciyarsa sai Jin saukar numfashinsa tayi a wajen kunnenta kafin ta gane mai yake Shirin yi sai ji tayi Yana Kai Mata sumba ko ta Ina jikinsa na rawa,ba Kuma wai yau ya Saba da mata sumbar ba amma na yau daban yake dan a haukace yake Kai Mata sumba Yana Kiran sunanta.

Ita kuwa jikinta ya d’auki rawa tana tunanin Yau fa da alama ba zai iya hakura da ita ba  ita kanta taga k’ok’ari da hakurinsa.

Wani irin sura ya Mata bai direta ko Ina ba sai kan gado Yama kasa rabuwa da jikinta hakan yasa ta sadakar hawaye na zubo mata kusan awa daya Yana haukata mata jiki da itama kanta bata Isa cewa bata karbi Sakon da yake aika mata cikin kwanciyar hankali ba.

Sanin babu gudu Babu ja da baya yasa ta nutsu dan tasan koman Daren dadewa sai hakan ta kasance

Da bby I love you da sumba yafi a kirga da ake jera mata ya hau neman hanyar sa dak’yar da kuka da tasan Yareema yayi Nisa sai dai Kuma idan ya dawo.

Koda komai ya lafa bacccin azaba ne yayi awon gaba da ita a kirjinsa dan kamar zai Maida ita cikinta haka ya ringa yi Yana jera mata godiyar da bata san na menene ba.

Bata san tsawon lokacin da ta dauka tana bacci ba a cikin baccinta dai zuciyarta cike take da nishadi tana Jin dama kar ta farka ta dawwama a haka.

Dan bubuga ta da taji ana yi yasa ta bud’e idonta a hankali zafin da taji ya ziyarci kasanta yasa ta tuno da abinda ya faru.

Ta Bude idonta a hankali ta sauke akan yareema da taga ya kura mata ido kunya yasa ta saurin rufe idonta sai taji yace “Bby ki tashi kinyi bed wetting kin jika mu”

Sai taji kamar ya buga mata guduma akai ta bud’e idonta da sauri dan tabbas a jike take jinta ta tashi zaune da sauri a daidai lokacin da Yareeman ya mik’e tsaye Yana “kinyi fitsarin kwance ki tashi ki gyara jikinki”……..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 33*

Ameera

      Kirjinta bugawa yake da k’arfi kalmar fitsarin kwancen da Yareeman yace na Kara maimaituwa a kanta

Ta kasa ma motsawa har sai da taga ya rufo k’ofar bandakin

Tayi sauri wajen mik’ewa duk da zafin da taji haka ta daure ta Kalli jikinta da taji kamar ruwa aka watsa akan gadon har wajen da Yareeman ke kwance

Sallati tasa a hankali ta kai hannunta ta shafa wajen da Yareema ya kwanta ta kai hannunta hancinta.

Sai taji gabanta ya tsinke dan zarni taji ba wai ruwan da take tunani bane ya jika katifar

Da bargo a nannade a jikinta ta mik’e har Lokacin jikinta rawa yake ta Kara shafa wajen da ta kwanta da taga abu mai yauki yauki da Kuma dan jini kadan sai jikewa da wajen yayi sosai ta kara shafawa ta kai hancinta taji dai zarnin fitsarin ne.

Ta saki sallati tana mamakin yadda aka yi har wai tayi fitsari Anya ba wani wajen yareema ya fasa mata a jikinta ba yasa fitsarin ya fito batare da ita taji alamar tana Jin fitsari ba.

Dan har lokacin kasanta wani irin zugi yake mata ko tsayuwar ma da tayi ware kafarta tayi.

Taya ma za tayi fitsarin kwance a gaban Yareema, Mai yasa bata tab’a hakan ba sai da Yareema ya sadu da ita.

Kukan bakin ciki da kunya ta fashe dashi dan har ga Allah taji mugun kunya wai da girmanta tayi fitsari a jiki

Sam bata san ma Yareeman ya fito ba sai muryarsa taji Yana “Common babe kukan na menene,may be nayi hurting dinki ne shiyasa kika saki fitsarin batare da kinsani ba muje bandaki na taimaka miki ki kintsa jikinki though nima this is my first time Ina ganin hakan ke kasancewa ga  kowacce cikakiyar budurwa da bata taba sanin wani da namiji ba Ameera am proud of you Allah ya miki albarka da kika tsare min mutuncinki”

Yareema yace a daidai lokacin da ya ruko kugunta ya rungumeta a jikinsa Ya sumbaceta a goshinta

Dan har ga Allah Idan yace bai ji dadin kasancewa da ita ba yayi wa Kansa karya Ji yayi ma a yanzu ya fara Santa

Gamsuwar da ya samu yasa bacci yin awon gaba dashi Tana rungume a kirjinsa

Ji yake kamar ya maida ita cikinsa dan Yana ma ta danne Kansa ne kasancewarta budurwa amma ji yake kamar ya Kara idan ya shako turaren dake tashi a jikinta.

A cikin daddan baccin da ya kwashe shi yaji kamar dumi ya ratso ta boxers din jikinsa lema lema haka daya sa ya bud’e idonsa a hankali Jin dumin a jikinsa sosai yasa ya raba Ameera da jikinsa ga mamakinsa sai yaga daga Jikin Ameera ruwan ke fitowa dan Babu komai a jikinta.

Mamaki ne ya rufe shi dan bai san ruwan na mene yake fitowa a jikinta mai balain yawa har haka ba inda ya kasa hakuri ya Kai hannunsa ya shafa dan ba zai yu ace wanan abu kamar ruwa niima ne,ga mamakinsa sai yaji zarni inda ya waro ido cikin mamaki ya ja da baya Yana kallon Ameeran da jikinsa da ta jike da fitsari.

Yafi minti goma Yana tunanin mai ya haddasa mata yin fitsarin,dan suna kwana a waje daya bata tab’a haka ba,sai tunaninsa ya basa kila ya wahalar da ita azaba yasa ta sakin fitsarin dan shi Kansa yasan bai mata da sauki ba,dan ya kasa controlling Kansa da yaji gardinta.

Ameera idonta kawai ta rufe gam dan ji take kamar ta nutse dan azabar kunya ta kasa yarda wai fitsarin kwance tayi duk da taga Yareema ya danganta fitsarin nata da azabar da ta Sha da itama ta sa a ranta hakane.

Kukan da ta saka masa kanta binne a gwiwarta yasa ya bar mata bandakin dan bahon bandakin cike yake da ruwan dumi daidai yadda zai iya gasata taji dadin jikinta.

Yaso ace shi ya taimaka mata amma ganin ta Saka masa kuka yasa ya baro mata bandakin.

Kyankyamin da yake dashi ya Hana shi canza zanin gadon dan yau ba dan kaunar da yake wa Ameera ba baya Jin zai iya Kara hada shimfida da ita.

Ba Kuma zai so ya kira ma’aikatan hotel su gane musu Sirrinsu ba.

Shirun da yaji Ameeran yasa yasan ba zata tab’a fitowa ba kunya ba zai barta ba

Kunya ado ce ga ya mace kunyarta na matukar burge shi.

Daga bakin kofa yace mata ta fito zai fita waje ya dan siyo musu wani abu.

Ameera tashin hankalin fitsarin da tayi da abin kunyar da take ganin ta aikata yasa ta kasa fitowa sai da da ta tabbatar da fitar yayi ta fito tana dauriya wajen hade kafarta.

Tuni kuka ya Kara balle mata da taga yadda gadon yake a jike Kuma duk sanyi freshners din dakin sai taji kamar iya zarnin kawai take ji.

Sallah ta fara yi kafin ta cire zanin gadon ta goge katifar sosai fankar da ta saki yasa nan da nan ya bushe ta Kara shimfida wani sabon zanin gadon da ta gani a drawer dan ta lura indai Yareema ya kwana sai ya Kara canza zanin gado har jibgo zanuwan gadon yake kamar suna gida

Bed spray ta fesawa gadon da kawarta ce tayi mata gudumawarta duk da ba wai wani kawance suke can ba daga mata dinki suka Saba da ita sosai.

Kamshin bed spray din kawai ya Isa yasa ka baccin da baka shirya ba

( A wajena kawai zaku samu wanan bed spray din🤨🤨🤨)

Cikin mintuna ta gyare dakin tas ta Bude fridge ta d’auko yogurt ta Sha ta kwanta.

Sam ba kunyar saduwa da ita da Yareeman yayi ke dawainiya da ita ba,kunyar fitsarin da ya kwace mata batare da taji ma alamar fitsarin ba ya dameta.

Kamar zata zura bandaki a lokacin da ya dawo da lodin abubuwa

Duk idon ta a rufe taji ya Sanya mata zobe ya sumbaci hannunta Yana jaddada irin san da yake mata.

A ranar ya Mata adalci bai nemeta ba,dan rungumeta kawai yayi ita kuwa ta kasa ma bacci tana tsoron bacci ma ya kwasheta ta saki fitsari.

Koda bacci barawo ya saceta da bata san ma tsawon lokacin da ta d’auka tana baccin ba a frigice ta tashi tana duba jikinta.

Yareema da mik’ewarsa kenan saboda alarm din sallah Asuba da ya tashe shi ya saki murmurshi dan ta balain bashi dariya duk mutsu mutsun da take Yana jinta shareta kawai Yayi.

Kan gadon ya koma ya jawota ya rungumeta yana “Haba babe dan jiya wahala ta saki yin fitsari sai ki d’auka yau din ma za kiyi dan Allah ki saki jikinki ba yau muka fara kwana a waje daya ba jiya ma akwai dalili shi yasa dan haka ki saki jikinki pls idan ba so Kike Ina dawowa daga massallaci na Kara shiga duniyar da kika kaini jiya”

Ameera kanta ta tusa a kirjinsa dan itama kanta sai yanzu ta dan ji nutsuwa dan ta yarda azaba ya sakata fitsarin da bata san tayi din ba.

Kafin ya dawo daga massallaci ta Kara gyara musu dakin

Yana dawowa suka Kara bin lafiyar gado.

Har ga Allah a yanzu ji take ba wacce ta kaita Sa’a a rayuwata dan Yareema tamkar ba jinin sarauta bane shi,sosai yake gwada mata so kamar zai Maida ita ciki.

Kwana uku da suka biyo baya iya wassani kawai suke yi da a yanzu sai ta tsinci kanta da Maida masa martani bata sani ba.

Har ji take bata so yayi nisa da ita a ranar da ta samu kwana hudu daddare ta dan watsa ruwa ta d’auko wanan humrar NAJMATUSHSHAHAR VIP KHUMRA.

Ta shafa a jikinta Sam bata kawo yana tadda mugun sha’awa ba,sai da ta ga Yareema ya haukace mata.

Sai gashi a ranar sau biyu ya nemeta ba kuma taji zafi can kamar ranar farko ba

Zuciyarta cike da nishadin albarkar da ta Sha a wajensa da sumbatu bacci Yayi awon gaba dasu.

Kamar dai wancan lokacin taji Yana tashin ta ko da ta bud’e ido bai magana ba sai gadon ya nuna mata batare da yace mata komai ba ya mik’e tsaye inda taga bayan boxer nasa a jike,cikin wani irin azabar faduwar gaba ta mik’e tama manta Babu kaya a jikinta taga wajen da take kwance ne a jike jagab gama zarnin balain na tashi har wajen da Yareema ke kwance.

Hannu ta Dora aka ta saki ihun kuka.

Dan zuwa yanzu bata san tunanin da ya kamata tayi ba.

Taya da girmanta zata na fitsarin kwance

Fitowar Yareema da zura doguwar riga a jikinsa yayi waje Yana “Babe ki tashi ki gyara jikinki kar lokacin sallah ya wuce ki” yasa ta sakin wani sabon kuka dan duk yadda Yareema yaso b’oye mata bacin ransa sai da taga alamar bacin rai a fuskarsa.

Kanta har ciwo yake mata dan ita kadai tasan tashin hankalin da take ciki,dan a tarihi ma bata tab’a ji daga saduwar Aure anyi fitsari ba

Kamar wancan lokacin haka ta gyara dakin tana kuka wanan karon sai taji ma kamar zarnin fitsarin yafi tashi akan turaren da ta bulbula.

Koda Yareema ya dawo Kara kwantar mata da hankali yayi ba kamar wancan lokacin da ya ringa nace Mata ba.

Sai bulbula freshener da taga Yana ta famin yi Wanda hakan yayi matukar Sosa mata zuciya

A ranar sai ga Yareema da kwanan kujera

A ranar bacci bai ga idonta ba da asuba taji ya yaye bargonta Yana lekata har da wani sakin ajiyar zuciya da alama so yake yaga ko tayi fitsarin kwancen

Sai gashi ya hau tashinta har da rungumeta akan ta tashi tayi sallah.

Sai da suka zo karyawa yayi gyaran murya ya fara magana Yana “Babe Ina ga matsalar ki sai mun danganta da zuwa asibiti dan ban taba ganin irin haka ba dan na lura sai an sadu dake kike fitsarin  kwancen.

Dan haka ki shirya anjima muje wajen wani likita gynaecologist ne

A takaice sai ga shi sun je asibiti likita yace musu babu iirn Wanan case din da zaa ce daga sx sai fitsari yasan dai a lokacin yin Sx idan an kaiwa mace geji ova tana squirting har ta watso namiji waje dan kamar fitsari haka squirting din yake amma ba fitsarin bane ba zallar niima ne, matsawar ba haka bane ya kasance musu toh ba yadda daga sex zaa saki fitsari dan ko fitsarin kake ji nashi wajen yake yi idan za’ayi.

Ameera kuwa sam baa cikin hayyacinta suka dawo ba dan hankalinta Yayi matukar tashi

Sai Yareema ne ma ya ringa kwantar mata da hankali

Daga lokacin idan ya kasa hakuri da ita ya sadu da ita sai tayi fitsari Mai shegen zarni

Inda zarnin fitsarin ma yasa Yareema ya raba shimfida da ita nan din ma yayi ta juyi Yana toshe toshen hanci.

A hankali ta fara ganin canji a wajen Yareeman dan a yanzu hade mata rai yake yi.

Wani zubin ma yak’i kwana a dakin sai dai da safe ta ganshi.

Ganin idan ta cigaba da b’oye b’oye itace zata cutu ga uban ramar da tayi a madadin kwanciyar hankali

Ta ajiye kunya a gefe ta kira Hanne a waya cikin kuka ta daure ta fada mata halin da take ciki.

Hanne kuwa sallati kawai ta ringa rafkawa tama kasa magana ta kashe wayar ta wajen isha sai ga Kiran Abba Sule Koda ta d’auka fada ya rufeta dashi akan mai yasa zata dau tsawon lokacin nan bata fada musu halin da ake ciki ba,kamar zai kawo mata duka ta wayar kafin daga karshe ya hau bata addu’oi yace a yanzu bata ga ta bacci ba ta ringa tashin dare idan ma asiri akayi in Sha Allah zai karye yasan aikin makiya ne”

“Yareema”

Lumshe idonsa yayi Yana Jin sallatin da Gimbiya ke ta rafkawa tana “Baka rike Amana ba Yareema mai yasa tuntuni baka fada.min ba sai yanzu har akwai abinda zaka iya b’oye min,Kai yanzu hankalin ka bai baka aikin makiya bane ba,tunda sai idan ka sadu da ita take fitsarin.

Maza Maza ku fara Shirin dawowa Nigeria karku haura jibi”

Ajiyar zuciya Yareema ya sauke Shima duk yabi ya ramen yace in Sha Allah dan har ga Allah ji yake kamar zai zauce saboda halin da suke ciki,kawai ya kasa jurewa ne shiyasa ya canzawa Ameeran dan dakin ba Karamin zarni yake ba har Ameeran a yanzu baya Jin kamshinta zarni kawai yake ji Yana busowa daga jikinta.

Zinatu

    Maruka biyu Habu ya kwashe sultana dashi kafin Amjad ya karbe da yin ball da ita suyi hanyar waje

Zinatu kuwa sai sheshekar kuka take ta d’auka zata ji Habu ya hawo gadon wajen rarrashinta sai ji tayi yace “Wato a rayuwar nan sai ka ma manta da kayi Abu,sai ka aikata Abu baka d’auke shi a bakin komai ba,sai ka manta da kama Yi sai ya dawo ma ,Yau zagin da kika yiwa Mahaifiyata Yar cikinki ta miki kin d’auka na manta ko zan iya mantawa wallahi Yana cikin abinda ba zan tab’a mantawa ba a rayuwata.

Karkiga laifin sultana Abunda kika aikata ne itama tayi sai dai nace Allah ya kyauta

Daga haka Habu ya mik’e yayi hanyar waje

Zinatu da taji iska Neman daukarta ta mik’e tsaye tana k’ok’arin sakin ihu dan gani take Habu ya gama dawowa hayyacinsa tunda har ya iya tuna abinda tayi wa Gwaggo

Tuni ta Nemi guntun zazzabin da take ta rasa washegari da asuba ta d’auki.hanyar kauyansu Ayuba da isarta ta zub’e a gabansa cikin kuka tana rokonsa akan ya sake daure mata habu dan gani take shi ya kunce shi

Ga mamakinta sai mahaifin Ayuban yace bashi ya warware Komai ba ya gwada.mata ta kwaryarsa akan ai Gwaggo ta farfado Kuma dama duk ranar da ta farfado Habu zai fara dawowa hayyacinsa dan ba Karamin Addu’a Sule ke yi ba dare ba Rana ba.

Cikin kuka kamar zata zauce a ranar sai gata da bawa boka kanta akan a d’aure mata Habu dan matsawar ya dawo hayyacinta tasan sai ya Mata Saki.uku.

Mahaifin Ayuba kuwa ya moreta san ransa yace ta kwarfa kazantar jikinta ta matse masa a miya idan har yaci ai sai Kuma yadda tayi da habu dan kamun ya wuce na da.

Da wanan ta sanar da Habu auren sultana da take so Ayuba yayi duk duk da kamun da ta masa sai da yayi mugun tirjewa kafin ya amince akan a bar maganar har zuwa lokacin da zaa gama bikin Amjad.

Da wanan ta dan samu nutsuwa aka fara bikin Amjad da gidansu Jawaheer suka kashe Miliyoyin kudi dan ita kadai ce yarsa tal,daidai da gidan da Habu ya kerawa Jawaheer rainawa suka yi mahaifinta ya gwangwajeta da wani arnen gida

Shagali kamar baza’a mutu ba,sai Zinatu taji dama sultana ce ta dace da wanan arizkin.

A dinner da aka hada na karshe da ta gayyaci manyan kawayenta taci uwar kwalliya kamar me da tawagarta dan family su Jawaheer ne suka hada.

Suna zaune a wajen da suke tana Jin kanta a sama duk da ruwa ba Sa’an kwando bane su Jawaheer sun dame su a komai taga an kira sunan wata babbar bakuwa akan ta Bude wajen da addu’a.

Daga yadda taga duk mutanen wajen na rawar jiki yasa itama ta nutsu dan barrister  Aisha taji an kira sai taga wata hadaddiyar mata ta taso cikin wani iirn shigar da zata ce kaf gurin babu kamarta ta Saka facemask

Ta ga ta nufi wajen da aka ajiye lasifakan

Ta karba muryarta daya ji hutu jikinta duk Madara tana walwalin gwala gwalai ta Bude wajen da addu’a

Haka kawai Habu ya rike zuciyarsa Yana daga wajen Maza

Ko addu’ar da take wani soje ne a bayanta.

Sam bata san an gayyaci ma su Hanne ba sai da ta hango su a high table

Dan abun na Yan boko ne

Hanne

Kirjinta wani iirn bugu yake da taji barrister da ta d’auki hankalin jamaa muryarta na ta tashi cikin larabci

Abba sule na daga gefenta a zaune dan zaman na mata da miji ne

Ta ruko hannun Habun batare da ta shiryawa haka ba tana” Abban Ameera muryar matar nan kamar na Shamsiya…….

Wallahi tallahi banida lafiya bana shelanta rashin lafiya pls include me in your prayers I need it 👏👏👏

*KWKWR T KWKWR*

*Page 34*

Murmurshi Sule yayi Yana “Na yarda kin fara tsufa Hanne shamsiya da ta manta ma da gidan duniya tana can kwance makomarta Aljanna da izinin Allah itace Kuma muryarta ke miki gizo”

Hanne ido kawai ta zubawa barrister Aisha batare da tama ji mai Sulen ke cewa ba,dan da gaske muryar Shamsiya take ji na ratso lasifikan.

Sai da Barrister Aisha ta gama addu’ar ta.

Ta ajiye lasifikan ta nufi wajen zamanta tare da gyara facemask din fuskarta ta saci kallon wajen da Zinatu ke zaune da ta saki baki da hanci tana Kallonta.

Murmushi kawai tayi ta d’auke kanta

Ta saci kallon Habun da Shima ya zuro mata ido ko kiftawa baya yi tasan duk basu isa su ganeta ba Koda bata Saka face mask ba,

Ba Kuma iya su din ke kallonta ba dayawa daga cikin mutanen wajen suma kallon nata suke.

Hawayen daya zubo mata ta share da kyallen hannunta a lokacin da idonta ya fada kan Hanne da bata san da sun zo wajen ba,zuwa yanzu sai take Jin kamar ba zata iya cigaba da b’oye kanta ba lokacin da ya kamata ace ta bayyana yayi haka nan,dan duk abinda take so ta samu din ta riga da ta same shi,a yanzu tasan tafi karfin Zinatu so take ta bi komai a hankali.

Zinatu

     Dak’yar ta d’auke idonta daga kan barrister Aisha da ta d’auki hankalinta inda nan ma sai da wata kawarta ta tab’o ta ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi dan gabad’aya Barrister Aisha ta tafi da imaninta, matar ta hadu ne iya haduwa da ko daga iya shigar jikinta kasan ba karamar hajiya bace ba,

“Wai Mai kike ta kallonta ne haka”?

Cewar wata kawarta dake zaune a gefenta

Ajiyar zuciya Zinatu ta sauke tana “Dan Allah barrister nan bata burge ki ba”?

“Ta burgeni mana amma kema Kinsan tafi karfinmu balle muce zamu yi kawance da ita ke da ganin matar nan ta ji kudi ta gaji,taji Boko ta gaji taji komai ma kiga yadda Kallo ya koma kanta ke har da mijinki gashi can ita yake Kallo”

Zinatu da sauri ta waiga ta Kalli wajen da Habun ke zaune taga da gaske barrister Aisha yake Kallo

Tsaki taja tana “A banza sai dai iya kallon kawata dan wanan matar Koda bazawara ce ma tafi karfin Aurensa sai dai maigadinta balle ma dak’yar idan bata da aure ai ni sai na Kulla kawance da ita ta karfin tuwo wallahi”

Dariya kawar Zinatu tasa tana Allah ya bada saa idan da rabo sojan dake tsaronta ya gwabjeta shikenan.

A haka aka cigaba da shagalin dinner Habun Kansa haka kawai yaji ya kasa samun nutsuwa tunda barrister Aisha ta fito ta bud’e taron da addu’a wani iri yake ji da shi Kansa ba zai iya fasalta abinda yake ji din ba,har cikin zuciyarsa yake Jin muryar barrister Aisha har ta koma ta zauna.

Hanne kuwa duk ta kasa samun nutsuwa Shamsiyya ce ta Kara fado mata a rai sosai har tana Jin kamar ta rushe da kuka dan itama tasan yaudarar kanta take mai irin muryar Shamsiyar ce ba shamsiya da wani zubin sai ta tsinci kanta da cewa “tunda har ba’a ga gawar shamsiya da imitihal ba Ina ma suna rayye Ina ma ace ba mutuwa suka yi ba”

Ta Sha yin wanan Tunanin da Kuma addu’a Wanda tana danganta hakane da kila dan ba’a samu gawar Shamsiya an sallaceta an binneta kamar yadda ake binne kowane musulmi bane shiyasa take yawan tunanin nan.

Koda aka zo liki iyayen Jawaheer dubu dubu suka fito suka yi ta manna wa Amarya da ango inda suka fi dai mannawa Jawaheer.

Inda hakan yasa Zinatu mik’ewa itama tana Jin zuciyarta na sosuwa da yadda iyayen Jawaheer ke neman nunawa sunfi su arziki,kamar tasan hakan zata kasance itama ta tanadi kudin likinta

Sai da ta fara tsayawa wajen da Habu ke zaune ya taso suka Isa filin a tare dan iyayen Jawaheer su biyune suma suka fita wajen yin likin.

Suma likin suka hau yiwa Amjad sai Habu ne ma ya likawa Jawaheer dan Zinatu ji tayi tana Jin haushin gidansu Jawaheer da Kiri Kiri suke san nuna musu basu Kai ba dan a idonta ma sai take gani kamar wulakanta su ma suke yi dan basu wani girmama su ba.

Kamshin turaren da ya daki hancinsu a ta gefensu yasa suka waiga

Barrister Aisha ce a gefen Zinatun ta mik’a hannunta ta hau Likawa amarya da ango daloli,ai kamar an zugo duk manyan masu kudin da suka samu halarta wajen sai gasu suma sun iso filin jiki na rawa a madadin su likawa amarya da ango sai suka hau Likawa barrister Aisha da ta koma kan Habu da ya daskare a tsaye Yana Jin kamar iska na masa wahalar shaka sai da ta gama da Habun ta koma kan Zinatu da jikinta ke rawa da ita kanta bata san dalilin daya sa jikinta rawa har kirjinta na bugun tara tara ba, Barrister Aisha kuwa ta cigaba da Mata yayafin daloli,Zinatu da jikinta ke rawa ta tare kudin da hannu biyu dan ba zata yi gangancin sakin kudin ya zube a kasa ba,tama manta da taron bikin danta ne daidai da dalar daya fadi kasa sai da ta je kasa wajen daukowa ta dago tana “Godiya muke Hajiya”

Barrister Aisha kuwa ta watsa mata sauran kudin da taga tana ta lalubar kwayar idonta ta bar filin Zinatu dake rungume da kudin da aka lika mata ta cikin mayafi ta nufi wajen zamanta da sauri ta d’auko Jakarta ta juye kudin a ciki batare da ta damu da masu ma kallonta ba.

Gani take ma idan ta ajiye jakar zaa iya sace mata kudin hakane yasa ta rike jakar dan ba zama za tayi ba wajen wanan barrister zata koma dan tunda har ta mata liki da alama ba zata Sha wahala wajen kawance da ita ba

Sai dai ko da ta juya sai ta hango barrister Aisha acan bakin k’ofa zata tafi hannunta rike da wasu Yara Maza biyu sunyi shigarsu iri daya daga bayansu Kuma Immi ce kawar Samha.

Da gudu tayi hanyar wajen tana Jin kanta na Neman kuncewa da tunanin da ya darsu a ranta da kodai makociyarsu ce barrister Aishan

Kafin ta Isa wajensu taga  Samha ta Isa wajen Immi  habu shima Yana tsaye rike da hannunta

Ta Isa wajensu da sauri a daidai lokacin da taji habu na cewa “Immi barrister Aisha dama mom dinki ce”?

Zinatu da sauri ta Kara matsawa kusa da Immi dan ta tabbatar da zargin da take taji Immi na “Yes she is my mom”

Zinatu da saurinta ta nufi wajen motar da taga Barrister Aisha ta shiga da Maza biyun.

Habu shima bai wani tsaya Jira ba dan haka kawai yaji shi ma Yana so yasan barrister Aishan da Ashe itace makociyarsu da yaji yarta ta shigar masa zuciya Yan biyun nan nata kuwa burinsa kullum yaga ya gansu sosai sai dai daga nesa yake iya ganinsu kamar a yanzu da hangosun da yayi yasa ya tashi da saurinsa dan ya isa wajensu sai dai kafin ya Isa yaga barrister Aisha ta riga shi Isa wajensu ta rike hannunsu suka nufi wajen motar.

Zinatu kuwa Koda ta isa wajen motar kafin ta kwankwasa glass din wani murtukakken mutum ya zagayo Yana tambayarta lafiya

Zinatu kuwa kafin ta bashi amsa shima Habun ya karaso cikin harshen Turanci yace wa mutumin suna so suyi mata godiya ne

Zinatu tayi saurin karbewa ta hanyar gyada kanta

Mutumin kuwa a madadin ya kula su sai hannun Immi ya ruko ya sakata daga gaban mota ya rufe k’ofar.

Yana “Hajiya tace bata bukatar godiyar ku”

“Kamar ya bata bukatar godiyarmu mai yasa take haka ne,makociyarmu ce fa dan Allah ki Bude k’ofa ki fito mu gaisa”

Zinatu tace tana Jan k’ofar motar wajen da shamsiya ke zaune tana kare mata Kallo ita da Habun.

Hannunta kawai ta daga driver ya figi motar ya barsu nan a tsaye Zinatu nata maganar da ba iya jiyota take ba.

Sai da suka hau kan titi shamsiya ta saki ajiyar zuciya ta cire face mask din fuskarta ta Kalli Aryan da  Abyan da suna Kara girma kamaninsu da Habu na Kara fitowa,tasan ba Wanda zai gansu  bai san cewa su din jinin Habu bane ba shiyasa take iya k’ok’arin ta wajen b’oye su har zuwa lokacin da ta san ta shirya bayyana su.

A haka taro ya watse Amjad ya d’auki Amaryarsa suka nufi gidansu da Zinatu ta tura sultana akan taje ta kwana ta gano mata komai dan dama sai da aka kai amarya aka fara dinner.

Koda suka koma Habu dakinsa kawai ya wuce yayi kwanciyarsa dan bai san mai yasa yake Jinsa wani iri tunda Barrister Aisha ta bud’e taro da addu’a har zuwa likin da ta masa  da yasa  shi san tuna shamsiya margayiya da kwana biyu kenan takan fado masa a rai.

Alhaji buba daya fado masa a rai yasa shi saurin mik’ewa ya d’auko wayarsa ya Kara lalubo wayarsa Yana Jin kirjinsa na dukan uku uku.

Zinatu kuwa bandaki ta fada ta d’auko Dettol ta zuba a ruwan zafi ta wage kafarta ta hau kwarawa dan tunda ta bawa boka kanta ta daina gane kanta,dan wani irin azabar kaikaiyi take fama dashi idan ya taso mata haka zata yi ta Susa a yanzu ma da abin ya isheta sai take ganin ba abinda zai Saka taji sauki sama da ta sadu da Habun.

A gaggauce ta watsa ruwa ta fito daga bandakin ta dan shafa turare ta dora zani akan t shirt din da ta saka ta fito daga dakinta.

Dan bama kowa a gidan nasu dan ba wani gayya tayi ba tun jiya ma ta sallami Yan kwana.

Samha kuwa tana can gidan Barrister Aisha da ta ke ta tsinewa a zuciyarta na wulakanta su da take tak’i bari su ganta.

Kaikaiyin da take ji sosai yasa ta nufi wajen dakin Habun da saurinta

Karar Bud’e kofar palon yasa ta tsaya dan wajen Sha biyu da rabi ne na dare

Sultana ce ta shigo fuskarta a balain hade ta jefar da jakar hannunta ta Kalli Zinatu dake tsaye fuskarta d’auke da mamaki tana kallonta “hmmmm Hajiya ai wanan Jawaheer din tsinanniya ce wallahi koroni tayi,kinga dai gidan sama da kasa ne ko?toh wallahi bansan ma.yadda akayi tasan Ina dakin kasa ba har na kwanta fa kawai ta sauko wai lafiya mai nake nema nace Mata kwana zanyi sai kawai ta nuna min k’ofa wai nazo na fita yanzu nan,ba sai na hau daga murya dan Yaya Amjad ya juyoni ba dan nasan shi dai bai isa korata ba,ai wallahi Koda ya sauko sai ya daka min tsawa wai banji mai tace bane hauka ake katotuwa dani nazo kwana a gidansa kwanan uban me zanyi wallahi haka wanan Jawaheer din ta rike hannuna ta wulani waje Yaya Amjad na Kallona ai Hajiya Ina ga kin debo ruwan dafa kanki dan wanan Jawaheer din kam ba matuniyar arziki bace ba”

“Yanzu Jawaheer din ce ta koroki Kuma Amjad na Kallonta”?

Zinatu tace tana Jin kanta na Sara mata har kamar zata fadi

Sultana kuwa taja tsaki ta d’auki Jakarta tana “Sai kawai nazo na zuba miki karya ko kece kika je gidan Ina ga koroki za tayi”

“Wallahi bata Isa ba tayi kadan ta koreni,har ta Isa ta koreki daga gidan dan uwanki ai wallahi idan ba tayi wasa ba sai na Saka Amjad ya saketa dan ni sai daga baya ma na fara ganewa ba mutanen arizki bane su Allah ya kaimu gobe zanje gidan naji dalilin da ya sa ta koreki ai”

Zinatu tace cikin tsananin b’acin rai ta nufi dakin Habun dan sultana ta dade da shigewa dakinta.

Ko da ta shiga dakin zarya taga Habu nayi a dakin Yana ta zuba gumi kamar Wanda aka tsamo daga Mai

A yadda ta ganshi a firgice da waya a hannu yasa gabanta dan faduwa dan bata tab’a ganinsa a irin wanan halin ba

“Alhaji lafiya kuwa ya naganka haka”?

“Zinatu na shiga uku na lalace asirina ya tonu na kashe kaina da kaina”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Mai ya faru ne Bangane ka kashe kanka da kanka ba”

“Kinga wayar Alhaji buba a kashe tun shekaranjiya nake Kiran wayarsa a kashe a yanzu nake samun labarin wai ya bar kasar damfarata yayi”

Habu yace tare da zubewa a kasa ya dora hannunsa aka

Zinatu kuwa ta saki ihuuu ta dira gaban Habun tana “Kana nufin duka dukiyar ka da takardun gidaje da companyka har da bashin banki da kaci dan kayi kasuwancin da ka fada.min ka samu mahaukatan kudi hannun dan damfara ka fada”?

“Miliyan hamsin naci na banki Zinatu daga Ina zan fara wallahi Alhaji buba damfarata yayi”

Habu yace cikin ihun kuka

Zinatu kuwa cikin Yan sakani ta hango talaucewar da zasuyi da yadda zasu zama abin tausayi wani irin duhu ne ya mamaye mata ido kafin ta yanke jiki ta fadi.

Ameera

         Ki saki jikinki dani Ameera ki d’aukeni tamkar Mahaifiyar ki idan har kina da wata damuwa ki daina b’oye min kinji ki ringa fada min da ace wanan matsalar ma Kun sanar min da wuri wallahi ko kwana uku ba za’ayi ba zaa warware ai na riga da nasan Sharrin makiya da Ikon Allah da kariyarsa duk muke rayye yau.

Alhamdulillah Mallam yayi nassarar karya asirin amma ya ce na kusa dake ne suka miki asirin a maida musu kayansu ko Kuma a barsu”

Ameera da tunda Gimbiya ta fara mata magana take zubar hawaye Jin abinda tace yasa ta dago ta sake tambayarta da na jikinta ne suka mata asirin?

Gimbiya ta gyada mata Kai

Ameera kuwa ta Kau da kanta tana “A Maida musu kayansu Ranki ya dade idan har za’a iya Maida musu a taimaka min a mai da musu”

Murmurshi Gimbiyar ta saki tana “ko dai a kyalle su dai”?

“Aaa Ranki ya dade a Maida musu kayansu Kawai”…..

*Page 35*

Ameera

      Tunda Gimbiya ta bar dakin take ta kuka dan ko ba’a fada mata wayanda suka mata asirin fitsarin kwacen da ta ringa zubawa ba tasan su Zinatu ne,dan tasan ba yadda za’ayi alheri ya tab’a kawo su gidansu,shiyasa da suka zo taji gabanta ya tsinke har Kuma suka tafi ta kasa samun nutsuwa bata manta yadda Sultana ta kankame ta ba,ta shafe mata mara,tun tana yarinya tasan basu da aikin da ya wuce jifanta da sharri ta ta rasa mai ta tsare musu a rayuwa nan,Allah kadai yasan kunyar Yareema da take ji,Allah kadai yasan halin da ta ringa shiga idan ta budu ido ta ga tayi mala mala da fitsari mai zarnin masifa da ita kanta ji take shakar da take yana damunta.

Taya ma zata iya yafe musu abinda suka mata baa irinsu Zinatu ake yafewa Sharrin da suka aikata ba shiyasa tacewa gimbiyar a maida musu kayansu tana Kuma fatan Sharrin ya koma kan sultana da tafi kowa tsanarta.

Kamshin turaren da ta shako yasa tayi saurin rufe idonta dan dama kwanciyar rub da ciki tayi.

Duk da Yana iya k’ok’arinsa wajen ganin ta saki jikinta dashi amma ta kasa sakin jikinta dashi dan kunyarsa da nauyinsa take ji wai ace kamar Yareema na Auren irinta iya haka sai ta Kara masa da fitsarin kwancen da ya hana ya more wa Aurensu.

Banda Gimbiya ta hanata fadawa kowa taso fadawa Hanne da Abba Sule amma ganin ta roketa yasa ta bari tunda suka Kuma duro Nigeria taji kamar ta budi idonta ta ganta a gida.

Hannunsa taji a gadon bayanta da sunanta da ya kira  yasa ta  bude idonta dan tunda suka bar kasar bai Kara ce mata Ameera ba da Babe yake kiranta.

Hakane yasa ta baje kunnenta dan taji mai zai ce mata

“Kiyi hakuri nima kimin uzuri am a human being bansan haka abin yake ba,sai da Ammi  ke sanar min,duk da nima wani zubin na sha kawo tunanin hakan lura da sai mun tara dake hakan ke faruwa but sai na zama confused Ina tunanin ko akwai Matan da idan aka yi sex dasu hakan na iya kasancewa bayan an gama pls ki yafe min dan canza miki da nayi acan kinsan dai Ina sanki ba ba zan tab’a iya wulakanta ki da gangan ba”

Ameera kukan da take ta san dannewa ne ya kwace mata dan duk da tasan yafi karfin ajinta amma zuciayrta sai da ta ringa sosuwa da yadda yake gudunta kamar yana kyamarta sai da ya kai ma wani zubin daga nesa yake mata magana

Yareema kuwa gadon ya hau sosai ya dago ta ya rungumeta ya cigaba da rarrashinta Yana Jin dama Gimbiya ta bar shi ya wuce da ita gidansu,dan shi kadai yasan irin azabtuwar da yayi da  kaurace mata da yayi, dan shi kadai yasan niimar da Allah ya mata,shi kadai yasan irin nutsuwar da yake samu da ita idan har ba wani larura ba baya fatan rabuwa da ita Koda na kwana daya.

Sai da ya kai zuciyarsa nesa ya iya hakura da ita dan tunda har Gimbiya tace masa asiri aka mata an Kuma karya yasan ta warke yanzu ba zai na fargabar tab’a ta ba.

Zinatu

     A hankali ta bud’e idonta da dishi dishi ta fara gani kafin a hankali ganinta  ya washe,Habun da ta gani a gefenta da dogon wandon shadda da vest a zaune da waya a hannu idonsa ya kada yayi jajjur yasa ta tuna abinda ya faru ta mik’e a firgice tana “Waye ya hada ka da wanan Alhaji buban Alhaji bamu ga ta zama ba kasan idan har da gaske kake ya gudu da duka takardu da komai naka mun talauce kenan?kasan hakan na nufin zamu rasa komai mu zama talakawa kenan,bayan kaninka ma da muka d’auka bashi da rabon arziki ya farfado Shima a yanzu baza ka gaya masa komai ba,iya ma hada Kansa da yayi da Kai bai Isa ba sai ka hadu da Yan damfara a daidai lokacin nan an yashe mu Kai Ina ba zai tab’a yuwa ba Alhaji bani wayar nan na d’auki lambarsa”

Zinatu duk tace a haukace Habu kuwa yaja dogon tsaki Yana “Kefa Zinatu wani zubin idan kika yi wani abu kamar baki da hankali haka kike, yanzu idan kina da hankali mai ya kawo maganar sule a cikin maganar nan,mai matsalarki ne ma da Sule da a rayuwarki kike so kiga kin Sako shi a maganrki har kina an d’auka bashi da rabon arizki,ke komai sai kin Sako sule ne a wanan masifar ma da na tsinci kaina ba zaki barni naji da daya ba sai kin kawo min wani magana kudin nan dai nawa ne ni nasan wahalar da na Dade Ina Sha a wajen nemansu dan haka baki Isa kifini Sanin zafin kudina ba dan haka ki barni naji da abinda ya dameni”

Zinatu kasa magana tayi dan wani iirn azabbaben kaikaiyi ne ya taso mata cikin dabara ta zura hannunta daya ta hau Susa tana lumshe ido Habu kuwa Kansa na kasa sai zabga sallati yake dan ya d’auka ma fadan da ya rufe ta dashi ne yasa tayi shiru,ya kasa yarda Alhaji buban da yaga Yana juya daloli da wani abokinsa ne ya hadasu yace su hada kudi dashi zasu d’auko kayan da ana siyarwa zai zama wani katoton miloniya,bai zura jiki ba sai da ya fara da bada dan kudin da bai taka kara ya karya ba,kafin sati aka dawo masa da kudinsa rubi wajen goma,jiki na rawa ya zura kudi da yawa cikin sati biyu Alhaji buba ya maida masa uban kudin da ya girgiza imaninsa ya rufe masa idonsa ya kwashi kusan duk wani kudinsa dake cikin bankin ya bawa Alhaji buba,ai kafin sati yaga Yana ta turo masa kudi har ya rubanya abinda ya bayar,ko baccin kirki kasawa yayi a ranar,saboda yasan da zai saka kudin daya Fi abinda ya bada din wani shahararen attajiri zai zama shiyasa Koda ya sake dawowa ya kawo shawarar ai ya rufe ido ya zuba kudade idan ma kadarorine dashi duk ya siyar a cikin wata guda sai dai ya fara hararo Kansa a matsayin dangote,jiki na rawa ya hau daga duk wani kaddara nasa har da mall din da ya siyawa Amjad komai nashi iya nan bai Isa ba sai da ya hada da rancen kudin banki iya gidan da suke ciki ne kawai bai kawar ba.

Ya juyewa Alhaji buba da ya tafi akan ya zuba ido nan da sati biyu yagani.

Sai gashi an share sati biyu shiru da ya fara Kiran Kuma lambar Alhaji buban sai yaji a kulle kamar ma ba’a tab’a amfani da layin ba Wanda ya hada su shima ya kawo mishi nashi Kukan akan ai shi ma ya damfare shi.

Sallati Habu ya karasa saki Yana “Na shiga uku na lalace daga Ina zan fara yanzu Allah ya rufa min asiri ya min sutura na tonawa kaina asiri da kaina yanzu Ina zan samo kudin da zan biya banki”

Zinatu kuwa da zuwa yanzu ji take idan ba kusantar ta Habun yayi ba ba zata daina Jin kaikaiyin ba ta matsa kusa dashi ta dafa shi tana “Ka kwantar da hankalinka Alhaji in Sha Allah karfin addu’a zai saka ya fito gobe idan gari ya waye duk wani mallamai da muka sani zamu raba musu kudi akan suyi ta jifansa da yaseen ba zai tab’a samun nutsuwa ba har sai ya dawo maka da dukiyarka  yanzu muje ka kwanta ka dan yi bacci”

“Ai nida bacci sai na samu mafita dan yanzu bata dukiyata nake ba bashin bankin da naci nake tunanin lokacin da na dib’ar musu ya kusa idan har ban samu wanan kudin ba wallahi na Kade har ganyena.

“Kafin fa lokacin idan Allah ya yarda addu’a zata yi aiki Alhaji muje dan Allah ka kwanta”

Zinatu tace tana Jan hannunsa Habu ya fusge hannunsa Yana “Wai kanki daya kuwa Ina cikin halin nan zanyi bacci idan ke kina Jin bacci kije ki kwanta dan Allah ma ki tafi dakin ki karki dameni”

“Alhaji kayi hakuri hakkina zaka bani dan Allah Ina cikin Wani hali”

Zinatu tace kasa kasa tana k’ok’arin kwanciya a jikin Alhajin a san ta ja hankalin shi

Habu kuwa da yaji wani abu ya tokare masa wuya tare da ganin bakin Zinatun Yana Jin kamar ya tashi ya rufe Zinatun da duka ya hankadata da k’arfi har sai da ta baje a kasa Yana “Zinatu bansan baki da hankali ba sai yau Ina cikin wanan halin zaki nemi hakki anya kanki daya ma kuwa baki zare ba? kinsan Mai nace Miki ya sameni kuwa ?kinsan halin da na ce miki nashiga kuwa a irin wanan lokacin zaki nemi hakkinki”?

“Kayi hakuri Alhaji kamawa tayi dan kadan kawai na dan samu nutsuwa”

“Fitar min a daki Zinatu kifita yanzu nan kafin na rufe ki da duka dan wallahi zan iya dukanki”

Zinatu mik’ewa tayi da sauri ta fice daga dakin kamar ma zai datse mata hannu dan biyota yayi ya kulle k’ofar

Zinatu kuwa da ji take kamar zata haukace ta nufi kitchen ta d’auko wani Karamin cucumber da ta gani ta shige dakinta ta rufe kofa.

Tana kuka tana “Na jawowa kaina masifa Allah ya tsinewa Natete Albarka Allah ya sa ka dawwama a wuta aikin ma da nasa kayimin baiyi ba dan gashi baya Jin maganata ga talauci na k’ok’arin shigo mana cikin gida da wane zanji ne Mai ke Shirin faruwa dani haka,yanzu wanan kaikayin da me zan magance shi dan nasan Kaine kasamin wanan balain iya warin da na shaka bai isa ba ga kaikaiyi ka samun”

Ta ringa magana ita kadai kamar mahaukaciya sai da taji gabanta ya dauki zafi ta wurgar da cucumber.

Ta shiga bandaki tayi wanka ta daura alwala sallah Isha dan duk rashin nutsuwa ma ya sa ba tayi ba sai ta gama komai take yi take sallah idan tayi akan lokaci to ba abinda take shi yasa yaran nata suka taso duk a haka Amjad ne dai kawai ya fita zakka.

Sai da ta sallame sallah ta cire hijabi ta hau gado ta hau juye juye tana tunanin ta inda zata fara magance lodin.matsalolin da take hangowa dake gabansu,na farko na arizkinsu da taga Yana Neman guduwa,a yadda ya tsani talaka ta tsani muamalla da talaka wai a wayi gari  suma su zama talakawa a Karamin gida kila ba mota sai ta tuno rayuwarsu Sule a baya sai ta mike a firgice tana “Allah Ubangiji ya kiyaye ba zamu tab’a zama talakawa ba”

Ta koma ta zauna tare da tuno Ayuban da tasan zai iya bayyana a kowane lokaci ta tafi Tunanin irin hidimar da aka yi a bikin Ameeran da taso ta samu lebura ta aura ta ringa zuwa gidan sultana ma neman taimako,wai yau Ameeran nan ce take gidan sarauta bama sa kasar duk uban kudin da ta kashe dan ta wargaza auren sai da akayi asirin fitsarin kwancen ma da aka mata dan Yareeman ya saketa da wuri nan ma shiru bata ga alamar yayi aiki ba,dan kullum cikin kasa kunne take taji labari an sakota Amma Shiru.

Tana cikin tashin hankalin Ayuba da ya zame mata karfen kafa da take ta tunanin ta yadda zata b’ullowa Sultana sai ga talauci na neman kutso musu ta k’arfi da yaji.

Kamar kanta zai kunce haka ta ringa ji dan tasan yanzu bokan ta ba kowane aikinsa ke ci ba,tunda Habun har ya warware ga Ameera itama aiki bai kama ta.

Wajen hudu bacci Yayi awon gaba da ita,muryar Samha da taji a kanta yasa ta Bude idonta taga har gari ya waye.

Wajen Tara na safe ma mik’ewa tayi tana yamutsa fuska zuciyarta duk a cunkushe ta shige bandaki batare da tabi ta kan Samhan dake bata labarin Immi da Abubuwan da Babar immin ta bata ba,sai a lokacin ta tuna barrister Aisha da take mugun Jin haushinta gani take kudin da take dashi yasa take wulakanta mutane.

Alwala tayi ta fito tayi sallah tana sallamewa ta fito waje.

A Palo ta tarar da Samha da sultanar.

Sultanar na latsa wayarta ita kuma Samha na fama da wani abin game da aka bata

Ba Wanda ya gaisheta a cikinsu ta kuma Saba shi yasa bata bi ta kansu ba ta nufi dakin Habu

Koda ta isa dakin ta bud’e sai taga Habun baya ciki da alama fitar sassafe yayi rufe k’ofar tayi ta koma palon ta zauna ta buga tagumi tana tunanin ta inda zasu fara.ma idan har Alhaji buba bai dawo ba

Ashar din da Sultana ta lailayo yasa Zinatu ta dago tana Kallonta

“Hajiya kinji wanan Jawaheer din  wai nazo tana so ta aikeni”?

Shima Yaya Amjad gashi ya turo min text wai nazo na tayata Yan aikace aikace gani Yar aiki

Jikin Zinatu rawa kawai yake ta mik’e tsaye ranta a balain bace  dan sai a yanzu tama tuna ta koro sultana daren jiya.

Dakinta ta shiga dan yadda take Jin zuciyarta bama zata iya magana ba ta d’auko wayarta dake gaban mudubi ta lalubo lambar Amjad ta hau kiran shi tana sintiri a tsakiyar dakin ta

Sai da ta masa miss cal hudu ana biyar taji muryar Jawaheer na hello “Bani Amjad ai wayarsa na kira ko”?

“Ooo wai Baby ai bacci yake bai tashi ba”

“Ke zan soka miki Ashar ni zaki yiwa bariki zaki bani shi ko kuwa”?

“Hajiya mijina bacci yake Kiran da kike masa a yanzu na menene da sassafen nan”

“Baby ke da waye ne a waya”

“Mai delivery ne da zai kawo min sako hau sama kayi kwanciyar ka”

Zinatu taji Jawaheer ta bawa Amjad amsa

“Nice Mai delivery Jawaheer ni uwar mijinki ce Mai delivery”?

“A wajenki kadai na fara ganin surukar da ta Tura yarta wai taje ta kwana a gidan danta da ya tare a ranar aurensa karmu soma haka dake dan idan kika ce zaki takurani Hajiya zaki sha wahala seriously”

“Wallahi sai ya sake ki dan bansan ke Yar iska bace ba sai yau”

“Auren zobe hajiya mutu ka raba”

Taji Jawaheer tace tare da kashe wayar

Zinatu ta jefar da wayar hannunta ta jawo hijabin da tayi sallah tayi waje tana Jin kamar zuciyarta aka cinnawa wuta saboda tafasan da yake.

“Sultana muje ki rakani gidan Amjad wallahi sai ya saki yarinya nan idan har ni na tsugguna na haife shi wai yarinya nan ni take cewa Mai delivery”?

“Bangane Mai delivery ba”?”

Muje sultana dan sai na nunawa yarinya nan ita karamar Yar iska ce

“Assalamu alaikum Sirikata Ina zaa je da sassafen nan haka aa Amaryata kinga yadda kike kyalli kuwa tun kafin ma ayi auren”…

*Page 36*

   Sultana

  Ido kawai ta zuba masa tana kallonsa zuwa yanzu sai taji ta fara tsorata da lamarin Ayuba da Zinatun dan ta tuna yadda suka kwashe wancan lokacin da ya kai Habu ga marinta,Amjad ya Mata dukan tsiya dan ranta yayi balain b’aci da abinda Zinatun tace wai Ayuba zata aura idan bata Aure shi ba zata iya mutuwa shagalin bikin Amjad ya mantar da ita maganar dan da gaske ta fara yiwa zinatu kallon mai tabin hankali dan tasan idan a hayyacinta take ba ma zata soma hadata da Ayuba wai har tace kar ta turo shamsu ba wai Ayuba zata aura ta cigaba da kare wa Ayuba Kallo da ta lura baya rabo da shan sigari

“Wanan Kallo haka Amaryata ko baki gane ni bane”?

Zinatu kuwa hannunta kawai ta dora a Kai dan a yanzu bata san da wane zata ji ba,da jawaheer da ke neman mallake mata da har tana cewa ya shiga daki ya kwanta,ko Kuma da talaucin da ya fara musu  barazana ko da Ayuba da ta d’auka ma zata iya bashi Auren Sultanar idan ta dan gyare shi da kudi suka bashi gidan zama suka bashi jari duk da bata san taya ma uwar gayyar zata tab’a yarda ta auri Ayuban a cikin hayyacinta ba,shi kuma tsinanen Ayuban ya dage ba zaa juyar mata da hankali ba,a hankali ta  saci kallon Sultanar da ta zubawa  Ayuban idon da ya nufi wajen kujera Kai tsaye ya zaune kamar irin gidan ubansa,yau ban da tana gudun tonuwar asirinta Allah yasan ba zata tab’a barin Ayuba da Rai ba,ban da Uban Ayuba yafi karfinta da komai za tayi sai tayi dan ta Kau da Ayuban da bata Jin akwai Wanda ta tsana dai a yanzu sama dashi,bata so wai tace tayi nadamar ma Sanin Ayuban dan ba dan shi ba da yanzu kila bata dawo gidan ba,da kila Shamsiya na Rayye ta mallake Habu da yayanta.

“Sirikata Yau Kuma kin kasa magana ne daga ke har amaryar tawa sai Kallona kuke kamar baku sani ba”

“Karka sake ka Kara cemin amaryarka wallahi wallahi zan saka a d’aure ka Hajiya ka sani,Kai kasan menene a tsakanin ku amma idan ma da bakinta tace ma zata baka Aurena to ka gaggauta farkawa daga mafarkin da kake dan wallahi gwara na kare rayuwata ba aure da dai ni sultana na rasa Wanda zan Aura sai kazami Dan dabba dan shaye shaye Irinka zan Aura Allah ya kiyaye Koda Maza sun kare wallahi ba abinda zanyi da Kai”

Sultana ta nufi dakinta tana Jin zuciyarta kamar zata tarwatse saboda tsananin bakin ciki,idan har ta cigaba da tsayuwa ba zata iya ganewa wai Zinatu ce ta haifeta ba zata iya zaginta,tana ganin lokaci ma yayi da zata kira shamsu akan yazo ya samu Habu akan maganar Aurensu dan a yanzu Zinatu kam ba kallon mai cikakken lafiya take mata ba lura da yadda take yawan cin burin ta auri Mai kudi tana mamakin a yadda ta iya ce mata ma ta auri Ayuban da ta san da bata bashi tabbacin zata Aure shi ba bai Isa zuwa gidansu Kai tsaye har ya ringa ce mata amaryarsa ba”

Zinatu

    Tausar kanta tayi ta nufi wajen Kujerar dake kallon Ayuba ta zauna

Tana “Ayuba ni nace ma zan baka auren sultana na Kuma ce ka bani nan da wata daya Ina ga sai wani satin wata dayan zai cika,Ayuba dan Allah ka daina daga min hankali dan Allah ka daina zuwa gidanan sadda ranka ke so,Kai ma kasan ai a yanzu dai ban Isa yaudarar ka ba,tunda Ina da babban sirrina da duk duniya ba Wanda yasani sai kai, Kuma rashin cika maka alkawarin ka zai saka ka bankadamin wanan sirrin,taya zan k’i cika maka alkawarin baka auren sultana”

Hannu Ayuba ya daga mata Yana “Dakata haka Hajiya da wanan dogon bayanin naki ai na fada miki duk ranar da na dawo ba zan saurari komai ba wallahi ba Rana kawai zaa bani naje na taho da waliyina a daura mana Aure yanzu mai ya kawo wanan dogon bayanin da kike min”?

“Ayuba a yanzu Muna cikin Wani hali bamu da nutsuwar maganar Auren sultana mahaifinta ya riga da ya yadda zai baka ita kaga bani da wani fargaba,mun fada hannun wani dan damfara yanzu bamu da nutsuwa sai komai ya daidaita,dan a yanzu idan har Wanda ya damfare mu bamu kama shi ba,bansan dame za’a mata kayan daki ba,bansan wanne kudi zan baka kaja Jarin da zaka iya kula da ita ba,bansan wane kudi zan baka ka  kama muku gida ba”

“Hajiya kenan ta nan kuma kika bullo wato hannun Yan damfara Kuka fada duk uban kudin nan da mijinki yake dashi,toh naji ni bani da matsala ai da kudinku ni mata kawai zaa bani,idan wajen zama ne kuma Muna da wajen zama a gidanmu”

Zinatu kuka ta fashe dashi tana “Ayuba dan Allah ka barni naji da tashin hankalin dake gabana taya Sultana da ta taso cikin gata da hutu ta iya zaman kauye,taya sultana zata iya rayuwa a karkara dan Allah ka barni zuwa wani satin mu warware matsalar dake gabanmu tukunna”

“Wai wacce sultanar kike ta cewa zaki bawa dan dabann nan ne,?ashe dama kece kika ce zaki bashi aurena shi yasa yake zuwa gidanan Kai tsaye yake cemin amaryarsa?dama saboda wani boyayyen sirrinki da kike tsoron tonuwarsa kika ce zaki bashi Aurena Hajiya? toh wallahi tallahi ba zan tab’a aurensa ba,Kai Ayuba idan ma wani ta kashe ka tona mata asiri itama ayi mata hukuncin daya dace da ita,ba zai Yu ita ta gama more nata rayuwar ni Kuma akan wani boyayyen sirrinta ni Kuma ta kassara min rayuwa ba Kuma da take ce maka Mahaifina ya yarda akan zai baka Aurena ai shi ba dan shaye shaye bane da zai baka Aurena dan haka ka tona mata asiri kawai dan wallahi Azeem ba zan aureka ba”

Sultana tace daga bakin kofar dakinta dan kasa hakuri tayi ma ta tashi ta labe a bakin k’ofa dan taji mai suke tattaunawa dan so take ta Kara tabbatar da zargin da take akan ko Zinatun ce ta masa alkawarin bashi aurenta ga mamakinta sai taji Zinatu na magiya har tana Kara da bashi tabbacin bashi aurenta saboda wani sirri nata da take b’oyewa.

Zinatu mik’ewa tayi kamar zata fasa ihu da ta ga sultana ta koma dakin ta banko k’ofa.

Ta Kalli Ayuban da shi ma k’ofar Sultanar yake Kallo tace “karka damu da rantsuwar da tayi bata da miji sama da Kai nidai taimako na karshe ka bari zuwa wani satin Dan Allah dan Annabi ka daina zuwa”

“Asabar mai zuwa zan zo da sadakina da Waliyina ba zan karbi wani uzuri ba a ranar ko a daura aurena da ita ko wallahi na tona sirrin ki kawai nima na huta”

Daga haka Ayuba ya mik’e yayi waje

Zinatu ta saki ajiyar zuciya tare da zubewa akan kujera ta dafe kanta da taji kamar zai tsage.

Zuwan Ayuba ya Kara mantar da ita zuwa gidan Amjad haka ta shige daki ta kulle tana Susa tana tunanin ta inda zata fara dan hankalinta yayi matukar tashi da sultana ta ji maganar ma da take da Ayuba duk da bata ji sirrin da take b’oyewa ba amma ta tsorata da  ta san cewar tana da wani sirri da take b’oyewa dan data furta ko mutum ta kashe sai da taji kamar numfashinta zai d’auke dan sai take ganin kamar har ta gano abinda ta yi tsoron ma Sultanar take ji dan bata san amsar tambayoyin da zata mata ba.

Ganin har uku Habu bai dawo gidan ba yasa ta hau Kiransa a waya amma Yana ta ringing bai d’auka ba,haka ta ringa sintirin bandaki dan  a yanzu babban tashin hankalinta ace baa kama Alhaji buba ba,bata san ya zasu soma rayuwar talauci ba burinta Habun kawai ya dawo taji ya ake ciki.

Habu

      Tunda ya fita massallaci bai koma gida ba dan tashin hankali da yake ciki na ganin arzikin daya kwashi shekaru kusan ashirin da Yan Kai Yana Shan wahalar nema dare daya Yana neman rasa komai,ba iya wanan yanzu ma ke daga masa hankali bashin bankin da a yanzu ya duba yaga nan da kwana biyar ya sa hannu akan zai biya su,sanin da Kuma yayi wa banki idan har bai biya su ba zai iya kare rayuwarsa a kurkuku.

Duk inda yake tunanin zai samu labarin Alhaji buba yaje amma Babu Wanda yasan ma kasar da ya tafi balle yasa rai zai samu sanin inda yake.

Haka ya shige cikin motarsa ya kwantar da seat din Yana tunanin hanyar da zai bi wajen nemo ma kudin da zai biya banki dan yanzu shine babban tashin hankalinsa.

Ba zai tsaya Sanya ba dan yasan Alhaji Buba ya damfara shi ba zai tsaya sa rai da zai iya dawowa ba gwara ma duk Wanda yasan Yana mu’amalla dasu na arizki ya fara nemansu saboda ya samu ko da rancen kudine yaga ko zai iya hada bashin da yaci.

Sai dai kamar hadin baki duka abokanan kasuwancin nashi haka suka hau bashi hakuri wai sun tura kudi sunyi Katt Babu kudi a hannun su.

Haka ya kifa Kansa akan steering Yana tunanin mafita a wanan gabar ba abinda yake bukata sama da addu’a karo na farko a rayuwarsa da yaji ya dace ya kaiwa Allah kukansa akan wani damuwarsa karo na farko da yaji Yana bukatar Addu’ar Gwaggo dake kwance da yasan ko hannunta ya dora akansa kila zata iya jinsa ta masa addu’a.

Sai yaji ma Yana Jin wani nauyi da kunya dan bai tab’a tsayawa addu’a na musamman akan neman biyan bukata ba,bai tab’a ware lokaci ko da sau daya ne yace bari yayi wa Allah godiya akan nii’momin da ya amsa da shi Kansa yasan bai wai dan ya cancanta Allah ya bashi ba kawai Allah na azurta wanda ya so ne kawai ba wai dan zafin addu’ar da yake dashi ba,hasali ma iyakacinsa sallah farilla ba wani Kara nafila yake ba,balle wai ya ringa  Wani tashin dare.

( Ba sai ka shiga matsala zaka kaiwa Allah kukan ka ba,ka kasance mai godiyar Allah a kowane lokaci idan ma niimar kake dashi ka roki Allah ya Kara ma idan baka dashi ka dage wajen rokonsa ya baka duk abinda muka samu ba ikon mu bane ba dabarar mu bane ba Allah shi mai yalwa ne mai Kuma azurtawa zafin addu’a na iya canza ma kaddarar ka Allah ya sa mu dace Ameen”)

Da tunanin Gwaggo ya nufi gidan Sulen dan tunda Sule ya d’aukota sau daya yaje ya ganta,wani iirn yake ji a kirjinsa idan ya tuna yadda ya watsar da Gwaggo,bai manta yadda gwaggo ta jajjirce akan su ba

Bai san ya ma akayi bai yi amfani da kudin da a yanzu yake neman subuce masa wajen nema mata lafiya ya fitar da ita har waje ba tunda Yana da damar da zai fitar da ita din.

A lokacin da ya Isa gidan Sule kasa fitowa yayi daga cikin motar ya zubawa gidan Sule ido dan sai yake ganin kamar ma gidansa ba gida bane akan gidan Sulen,da ya tab’a Neman wajen zama ya rasa ya bashi wani Karamin daki ya zauna wai yau sule ne ya mallaki iirn Wanan katoton gidan.

Jiki a sanyaye ya Fito daga motar ya kwankwasa k’ofar gate din.

Wani ya bud’e k’ofar daga shigarsa ya gane mai gadi ne

Ya hau tambayar sa waye shi

Habu kamar zai fashe da kuka haka ya ringa ji dan ya kasa yarda tun ma dai arzikinsa bai bar hannun nasa gabadaya ba an fara k’ok’arin hana shi shiga gidan Sulen da ba zai manta ba har Aikin gadi yayi.

Yana k’ok’arin bashi amsa yaji dirin mota ta bayan shi.

Gefe ya koma ya tsaya dan mai gadi da da saurinsa ya koma ciki ya wangale gate din gidan.

Bai iya gane suwaye a cikin motar ba dan da tint a cikin motar sai da motar ta shige Mai gadi ya rufe k’ofar.

Yaga Sule ya fito fuskarsa ba yabo ba fallasa yace “Yaya Habu ya ka tsaya daga waje ka dade da zuwa ne”?

“Aaa ban dade da zuwa ba Ina so dai na shiga ciki Mai gadinka ya hana ni shiga”

“Ina ga bai gane ka bane Bismillah”

Abba sule yace tare da nufar ciki Habu kuwa ya hau bin shi a baya yana kalle kalle ko a mafarki akace masa Sule zai taka wanan matsayin karyatawa zai yi.

Sai da suka wuce wani babban Palo kafin su shiga wani Karamin Palo inda habu ya tsaya cak da ya ga Gwaggo a zaune daga kasa ta jinginna da pillow gefenta Hanne ce ke bata abinci a baki, ya Ibrahim Kuma na dage Saman kujera a zaune Shima da matarsa itama tana daga gefe Hira ma suke yi.

Ya Ibrahim na ganinsa ya hade rai

Gwaggo Kuma da tayi fayau sosai ga wasu magunguna a gabanta ta zubawa Habu ido tana kallonsa kamar yadda Habun da taga jikinsa na rawa ya zuba mata ido Yana kallonta.

Gani yake kamar mafarki yake ba zai Yu Gwaggo da ke kwance rai a hannun Allah da bata da maraba da mataciya itace a zaune tana kallonsa ba.

Hawaye kawai ke zubowa Gwaggo da tunda ta farfado take zuba idon ganin Habun amma sai gashi an kwashi kusan wata guda Habu bai zo ya dubata ba.

Kallonsa kawai take hawaye na zubo mata Habu da jikinsa ke rawa ya rarrafa zuwa gaban Gwaggon Yana “Gwaggo yaushe kika farfado wallahi bansani ba Sule ya zaka min haka mai yasa baka fadamin Gwaggo ta warke ba,yanzu saboda kayi kudi kake so ka ringa wulakantani kuna wareni”?

“Ai mun d’auka ka manta kana da uwa mun d’auka Zinatu itace ta mayye Maka gurbin Gwaggo ai akan me zaa kiraka ace ma ta warke ka damu da Gwaggon ne a lokacin da muke Bauchi sau nawa kazo duba Gwaggon”?

“Ya Ibrahim mai na maka dan Allah ka tsane ni yanzu so kake ka ringa irin wanan maganar saboda Gwaggo taji haushina? Gwaggo dan Allah dan Annabi ki yafe min wallahi bansan kin farfado ba”

Habu yace tare da ruko hannun Gwaggon da har lokacin shi take Kallo bata d’auke idonta daga Kansa ba..

Ameera.

*KWKWR T KWKWR*

*Page 37*

Ameera

          Tamkar wata Amarya haka Gimbiya ta sa aka kara yi mata gyaran jiki na sati daya ban da kayan gyara da maganin Sanyin da ta sa aka ringa tilasta mata wajen Sha har gyaran ma na neman fi na farko.

Yareema kamar zai zauce haka ya ringa ji dan Gimbiya ma ta hana ya shigo wajen da take dan a yanzu ne ma take amarya a cewarta tunda bata tare a gidanta ba suka wuce Paris.

Ameera ita dai duk jikinta a sanyaye yake dan gani take kamar ko ta koma zata iya sake fitsarin kwacen.

Ko baccin kirki ba ta yi dan yanzu zagewa take wajen yi wa kanta addu’a kariya daga Sharrin makiya.

Yareema kuwa kamar ya shigo ta wayar ya d’auketa idan suna video call,har magiya yake mata akan ta faki idon mutane ta fito wajensa ya rasa dalilin da yasa Gimbiya ta ce ya bari sai an kaita dakinta kamar wasu sababin Aure.

A yau da yake Asabar tun wajen hudu Umsad ta gama mata gyaran jiki ta shiga wanka ita kanta ji take kamar canzata a kayi dan fatarta wani irin sulbi ya ringayi banda kamshin dake fita a ko’ina na jikinta.

Koda ta fito haka ta ringa zama a turaren tsugguno.

Wata mai kwalliya aka kira ta  mata kwalliya aka nada mata wani lafayya sai bulbula kamshi take.

Wajen shidda wasu manyan mata da bata san ya ma suke da gimbiyar ba suka Rakata gidanta da taji suna ta santinsa dan kanta a rufe yake Koda ma ba’a rufe yake ba ba zata iya dago wa ta kalla ba.

Da Bismillah ta shiga gidan kamshi kuwa kamar an Bud’e gidan turare.

A gefen gadonta taji sun zaunar da ita.

Duk da bata san su ba haka suka ringa mata nasiha suna fada mata dabarun zama da miji dai kowace dai ta bata shawararta kafin su mata sallama su tafi.

Sai da taji fitar su ta dago da kanta tare da sauke ajiyar zuciya ta dan yaye lafayyar ta hau karewa dakin Kallo.

Fadar haduwar dakin ma bata bakine

Bama zata iya fasalta halin da take ciki ba dan wani zubin takan ji dai kamar wata rana zata farka taga mafarki take yi.

A hankali ta koma ta zauna ta hau addu’ar Allah ya rabata da yin fitsarin kwancen dan sai take ganin kamar dai bata warke din ba.

Da sauri ta rufe idonta da taji an turo k’ofar dakin kamshin turaren Yareema ya bade ko’ina.

Tun kafin ma ya karaso wajen da take taji jikinta na dan rawa har tsigar jikinta na tashi.

A gabanta ya tsugunna ya ruko yatsunta da ya sha Jan kunshi ya sakar musu kiss kamar mai rada yace “Welcome home babe”

Runtse idonta ta sake yi da taji ya yaye lafayyar gabad’aya.

Shirun da taji yasa ta dan Bud’e idonta taga Ashe kura mata ido Yayi ko kiftawa baya yi

Har ga Allah bata so zurma jiki a kaunarsa ba amma idan tace a yanzu bata kamu da kaunarsa ba tayi wa kanta karya Yareema irin namiji ne da kowace mace zata so ace ta samu “kina da kyau Ameera Ina sanki Ameera”

Ya jawota ya rungumeta tare da sauke wani irin ajiyar zuciya itama ta rungume shi gam.

Zuciyarta cike da fargaba da addu’a a bakinta har Yareema da ya ringa ji kamar ma bai tab’a sanin ta ba sai a ranar dan sabuwa ta dawo masa dal zai iya cewa ma kamar Zuma aka Kara Mata.

Kirjinta wani iirn bugu yake da taga alamar ya samu nutsuwa dan acan Paris Yana kankameta nan ko bacci bai d’auke su ba ma zata ji ta jike su.

Har ya jawota ya rungumeta yana saka mata albarka bata ji ta samu nutsuwa ba har bacci Yayi awon gaba dashi idonta biyu.

Sai wajen uku bacci barawo ya saceta motsinsa ya sa ta farka da sauri kirjinta kamar zai fita ta shafo wajen da ta kwanta ta Kalli boxers din Yareeman taga bata jika shi ba itama bata jike ba alamar dai asirin ya karye.

Sai a lokacin hankalinta ya kwanta

Basu tab’a shiga wanka a tare ba sai gashi Yareema ya dage mata ta karfin tuwo dai ya ke san cire mata ragowar kunya daya rage Mata.

Ko massallaci bai je ba a gida yaja su sallah.

A Ranar ko waje Yareema bai leka ba kamar zai Maida ta ciki.

Sai a yanzu ma suke cin amarcin.

Daga gidansu Yareema ake kawo musu Abincin da zasu ci.

Sai da suka samu sati biyu cif kafin Yareema ya bari a kawo mata wata Yar dattijuwa da ke zuwa tayata aiki dan sam baya san rayuwar takura.

Zinatu

   A ranar Habu bai koma gidan ba sai wajen takwas na dare

Duk ta kasa zaune ta kasa tsaye dan bata san inda Habun ya shiga ba tun safe.

Dirin motarsa da taji yasa ta saurin mik’ewa tsaye taje ta tsaya a bakin k’ofa.

Duk ta kasa ma cin abinci ga kaikaiyin da ke neman haukatata tsabar Susan da take a yanzu ko fitsari za tayi ji take kamar an watsa mata barkono.

Sultana kuwa tun da rana ta fice daga gidan bayan ta mata rashin kunya.

Sau uku tana Kiran Amjad dan ma yazo gidan ko asibiti ya mikata kafin Habun ya dawo dan sam bata Jin zata iya tuki.

Amma Jawaheer Ce ta ringa daga wayar rashin Sanin halin da suke ciki game da dukiyar su ya hanata zuwa gidan Amjad din dan ta gama kudurcewa a ranta akan sai Amjad ya saketa dan Sam bata san haka Jawaheer din take ba.

Koda Habun ya shigo bai ma tsaya ba balle ya Kalli inda take yayi shigewarsa daki.

Zuwa yanzu sai taji tana fargabar ace dan kamun ma da ta masa ne ya warware gabadaya

Bata yi kasa a gwiwa ba ta bi bayansa

Inda ta same shi a gefen gado a zaune

Ta zauna a gefensa tana “Alhaji ya ake ciki ne tunda ka fita wallahi na kasa nutsuwa an samu labarin Alhaji Buban”?

“Ban samu labarinsa ba Zinatu,a yanzu bamu da komai idan nace miki komai Ina nufin a yanzu mun dawo talakawa marasa ko sisi dan bani da ko biyar a account dina ban Kuma ba wa wani ajiya ba idan akwai abinda ya rage min yanzu a rayuwa motata ce sai gidanan shi ma zan saka su ne a kasuwa na siyar naga ko kudin zai Kai na biya bashin da naci a banki”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Alhaji yanzu wanan gidan ma siyarwa za’ayi idan ka siyar Ina zamu koma”?

“Karamin gida zamu nema mu kama haya”

Innalillahi wa inna ilaihi rajiun innalillahi wa inna ilaihi rajiun mun shiga uku mun lalace Alhaji taya zamu fara  raywua a gidan haya,dan Allah ka nemo kwararrun Yan sanda su Nemo mana shi Ina abokanan ka kasa su kawo mana agaji su hada Maka kudi Alhaji”

“Zinatu ba wajen Wanda zan je neman wani taimako a wajensa ni a yanzu na karbi wanan jarrabawa da Allah yamin da hannu biyu idan kinga ba zaki iya ba zaki iya komawa gidanku”

Zinatu Shiru tayi tana kallon Habun dan sai taga kamar ma bashi bane ba dan fuskarsa sam ba annuri tana tsoron ace asirin da ta masa ne ya karye

Bata Kara ce masa komai ba ta mik’e tsaye ta fara k’ok’arin yin Waje dan Bokanta kawai zata kira a waya ta sanar dashi halin da take ciki.

Sai taji muryar Habun na “Gobe ki shirya da safe ki je ki duba Gwaggo dasu sultana dan ta farfado”

“Gwaggo ta farfado fa kace”?

Zinatu tace gabanta na dan faduwa da bata san dalili ba duk da bokanta yace mata ta farfado bata kawo da gaske bane

“Bakya so ta farfado ne”?

Habu ya jefa mata tambayar Yana tuna yadda ya baro Gwaggon dazu dan bai kawo zata yafe masa cikin sauki ba,ta ce ta yafe masa,inda jiki na rawa ya fada mata halin da yake ciki.

Itace ta masa nasihar karbar sabon shafin rayuwar da ya bud’e masa na Babu inda ta hau masa addu’a akan Allah ya kawo masa mafita da gaggawa dan kafin ta kwanta dogon jinyar bacin rai ma yasa ta tab’a masa addu’ar talaucewar ko hakan zai saka ya San darajar mutane ya kuma san yadda kowane talaka yake ji ta Kara da rokon Allah akan ta janye kalamanta Allah ya Buda masa.

Ta Kara masa da misali da Sule da suka wulakanta shi da Zinatu suka d’auka bashi da rabo a rayuwarsa yau ga Yadda Allah ya d’aukaka Sule ta hanyar Yar cikinsa.

Duk da bata masa maganar Zinatu ba yasan Gwaggo bata San Zinatu

Zinatu girgiza kanta tayi da sauri tana “Aaa Alhaji wane irin magana ne wanan ya zaka ce ko bana so ta farfado ne ni kuwa nake so ta farfado”

“Toh gobe kije da yaran nan ki dubata”

“Allah ya kaimu”

Daga haka Zinatu ta fice daga dakin.

Duk hankalinta a tashe dan har ga Allah farfadowar Gwaggon ya daga mata  hankali.

A ranar Sam bata samu bokanta a waya tama rasa tunanin daya dace tayi.

Dan a yanzu babban tashin hankalin ta yadda zasu bar tamfatsatsten gidanan su koma wani haya.

Haka ta kwana juyi tana tunanin mafita har bacci Yayi awon gaba da ita.

Wajen goma ta shirya dan Habu shi ya tasheta akan ta shirya su tafi gidan Sulen

Bata samu fuskar da za ta kawo wani magana ba hakan yasa bata iya musa masa ba.

Har ga Allah a babu yadda za tayi zata je gidan Sulen da idan ta gani sai taji kamar zata mutu dan bakin ciki.

A Palo ta tarar dasu sultana da Samha sun shirya Suma gabansu kuma ledoji ne da bata san ko menene a ciki ba.

Habu na tsaye da mukulin motar sa Babu ma alamar wani tashin hankali a tattare dashi Wanda hakan na nufin ya ma daina damuwa da dukiyarsa da ya rasa ta Gwaggo yake yi.

Ko gaisheta Sultana ba tayi ba ta mik’e tayi waje da ledojin dake ajiye a gabanta

Samha ta mara mata baya.

Ganin Habu yayi waje Shima yasa tabi bayansa.

Tafiyar minti goma Sha biyar ne ya Kai su gidan Sulen

Zinatu kuwa kamar ta fashe dan bakin ciki wanan shine karo na biyu da taga gidan Sulen sai taga.kamar ma kallon tsoro tayi wa gidan ranan da suka zo da Sultana gidan ya hadu ne a karshen haduwa.

Duk inda taso b’oye bakin cikinta kasa wa tayi haka ta hade fuska ta ringa kallon gidan tana Jin kamar ta samo fetur ta kona.

Habu kuwa tuni yayi gaba shi da Samha dake ta zuba surutun haduwar gidan.

A katon palon da ya gaji da haduwa suka zauna sultana ta ajiye ledojin hannunta.

Ganin basu ga kowa ba yasa Habu mik’ewa dan a Jiya daddare ya gane dakin da Gwaggo take

Fitowar Hanne daga kitchen cikin shigar wani less dake ta walwali ta Sha awarwaron gwal da sarka da dan kunne yasa Habu ya koma ya zauna

Zinatu kuwa ta zuba mata ido tana kallon Hanne da ta canza Gabad’aya kamar ma ba ita ba

“Yaya Habu sannunku da zuwa”

“Yauwa Hanne an tashi lafiya”?

Hanne murmurshi ta saki a daidai lokacin da ta karaso wajen su

Ta Kalli Zinatu da idonta ke ci da wuta kamar zata shakota.

Tace “Bismillah muje Gwaggon na dakinta”

Habu kuwa tuni ya mik’e yayi wajen dakin Gwaggon Zinatu kuwa ji tayi ma ta kasa mikewar dan kamar zata mutu haka ta ringa ji.

Ta kasa yadda Hanne da take sawa ta mata sharra itace yau sanye da less din daruruwa gwala gwalan jikinta kuwa sun kusa mil daya.

Dan Hayaniyar da ta Jiyo daga waje da murmushin da Hanne ta saki tana “Ba dai har ta Kara so ba”

Yasa Zinatu da sultana kallon bakin k’ofar.

Inda suka ga Ameera ce ta shigo da wata dattijuwa a gefenta tana rike da Jakarta

Ganin su da Ameera tayi yasa murmurshin fuskarta raguwa ta Kalli Hanne tana “Anne Mai suka zo nema Kuma a gidanan”??

*Page 38*

“Gaisuwar ki kenan Ameera wane irin tambaya ne wanan”?

Hanne tace cikin dan mamakin Ameeran dan duk da tasan yadda suke da su Zinatun bata san Ameera ta nuna musu wani Abu ko ta musu rashin kunya

“Anne wallahi ba alheri ke kawo su gidanan ba shiyasa nake tambaya ni nasan abinda suka min Kuma suma kansu sun sani”

Ameera wuce ciki bana san wani magana

Hanne tace fuska a hade

Ameera kuwa banda Anne ce ta ce ta shiga ciki da ba abinda zai hana ta Korar su.

Duk da asirin da suka mata ya karye har gobe tana Jin ciwon abinda suka mata taso ma fadawa su Anne amma alkawarin da tayi wa Gimbiya yasa ta hakura da fada musun

Dakin Da Gwaggon take ta nufa dan zuwanta na uku kenan,dan suna dan gama Shan amarci ta roki Yareema akan zata zo gida.

Ta d’auka zai hana ta ga mamakinta sai ya barta akan da yamma zai biyo da Kansa ya d’auke ta.

Dan gani yake ba abinda ba zai iya yi mata ba

Sai da taje gida tasan Gwaggo ta farfado anan take Jin labarin irin alherin da Yareeman ke musu.

A ranar kamar ba zata koma gidanta ba dan sai taji dama ya barta ta zauna fadar albarkar da addu’ar da ta ringa sha daga wajen Su Hanne har Gwaggon bata bakine daidai da Ya ibrahim Shima baa barsa a baya ba yanzu haka a gidansu yake zaune dan Abba sule ne ya dage masa akan ya dawo saboda gidan nasu katoto ne tunda dama can ya Ibrahim bashi da gidan Kansa yaransa Kuma duka mata sunyi Aure namijinsa guda ne shi kuma Yana karatu acan kudu,Dan bature da ya kasance kanin su Abba sule Kansa sai da ya dandani arziki ta silar Ameera duk da ba’a a garin yake Shima da iyalinsa ba.

A dakin Gwaggo ta tarar da Abba sule Habu har da Ya ibrahim

Har kasa ta zub’e ta hau gaishe su dan Sam bata kawo zata same su a dakin Gwaggon ba duk da sunfi zama dai a dakin Gwaggon dan burin kowa yaga ya farantawa Gwaggo.

Sai a lokacin ta gane Zinatu tare suka zo da Habun.

Fuska a washe Habu a hau amsa gaisuwar Ameera da tayi wani irin kib’a da haske Kai da ganin fatarta kasan kudi ya zauna.

Kunyar Sule da Ameeran ma yaji Yana ji daya tuna yace wa Sule Ameera bata Isa samun miji kamar Amjad da tun jiya yake kiransa a waya bai d’auka ba.

Sai gashi Allah daya tashi ikonnsa ya bata mijin da Amjad bai isa ma matsawa kusa dashi ba.

Daga yadda yaga Gwaggo ta washe baki tana amsa gaisuwar Ameeran ya tuna ma da su Zinatun yazo ya mik’e yayi waje.

Zinatu kuwa ganin Ameerar cikin kwanciyar hankali ba alamar ma tana da wani matsala yasa wani abu ya tokare mata a zuciya Sultana kawai take hararowa da Auren Ayuba kaskantace,duk uban wahalar nan da ta Sha tun suna Yara wajen ganin Ameera bata kamo sultana a komai ba,duk burinta na san sai dai Ameera ta hango arizki a wajen sultana duk burinta basu cika ba,da alama asirin fitsarin kwancen ma bai yi aiki ba dan da yayi aiki tasan ba zata ga Ameera fes haka.

Hawayen bakin ciki ne ya hau tsere a kumatunta ganinta zaune a gidan Sulen da tayi wa fatan zama a kasan su ya zama shi yake zuwa nema a wajen su daga shi har matarsa da Yayansa yau gasu a gidan Sulen a zaune gidan da ko a mafarki aka ce mata sule zai mallake irinsa karyatawa za tayi.

Da ido tabi Ameeran har ta shige dan corridor ta dawo da kallonta kan Sultana da ita ta zubawa ido.

Hanne a lokacin ta sake barin palon wata da alama da Yar aiki ce tazo ta ajiye musu snacks a gabansu.

Sultana ta mik’e ta isa gaban Zinatun bayan ta d’auki Jakarta da ta ajiye.

Ta sunkuya kadan tayi kasa da murya tana “Kina kallon Ameera kina kallon yadda hutu da Jin dadi suka nuna a jikinta,amma kece da kanki kike san hada Aurena da wani kazami mashayi akan wani rufin asirin ki da bansan na menene ba wallahi tallahi bazan tab’a auren Ayuba ba,Ameera da tayi Aure a gidan Sarauta fina tayi,wai har ace da kanki kike fadawa Ayuba zaki bashi aurena ki shirya tonuwar asirinki dan a yau shamsu zai zo ya samu Abba akan maganar Auren mu”

Daga haka sultana tayi waje dan bama zata iya jure ganin Ameeran da a yanzu tasan tafi karfinta ba.

Tana fita Habu ya iso palon Yana “Sai na roke ki zaki shigo ne Zinatu Ina Sultanar naga iya Samha”?

Zinatu da tana hango Habu ta hau goge hawayenta da mayafinta ta gyara zaman mayafinta tana ” Yanzu dai ta fita Kuma bamu san kan gidan ba taya zamu San wajen da Gwaggon take”

Habu waje yayi a daidai lokacin da ya hango sultana har ta kusa Isa wajen gate

Ya hau kwalla mata kira sai da ta dawo ya koma ciki yayi gaba Yana su biyo shi a baya.

Zinatu kamar zata zub’e haka ta ringa ji dan jikinta rawa kawia yake dan sai ta tsinci kanta da tsoron ganin Gwaggon,sai take ganin kamar idan Gwaggon ta ganta zata gane tana da sa hannu a kwanciyar da tayi.

Koda suka isa tafkakken dakin ba kowa iya Gwaggon ce sai Ameera dake gefenta tana bata fruit a baki.

Zinatu kuwa cikin sakani ta karewa dakin wai da aka bawa Gwaggo take zaune,dakin ya fi ma dakinta nesa ba kusa ba.

Gwaggo kuwa kadaran kadahan ta saki fuskarta tana amsa gaisuwar su sultanar dake Jin kamar ta hau kan Ameera ta rufeta da mugun duka, tama kasa b’oye bakin cikinta dan Ameera yanzu Sam baa sa’arta bace ba.

Ameera kuwa itama wani irin harara ta gallawa Sultanar ta ajiye farantin hannunta tayi waje

Ta bar iya Habu dasu Zinatu a dakin.

Inda Ameera ta tashi nan sultana ta zauna,Samha itama ta zauna a gefen Gwaggon ya zama kamar sun sakata a tsakiya

Habu kuwa ya samu Kujerar dake gefen gadon ya zauna.

Sosai yaji zuciyarsa ta masa wasai wanan nauyi da daurin da yake ji duk Babu ganin Gwaggon ma a zuane yaji ya rage masa kaso hamsin cikin damuwar da yake ciki na kudinsa da ya rasa.

Zinatu kuwa gaban Gwaggon ta zube ta hau gaisheta

Gwaggo kuwa ta zuba mata ido sai da ta dau sakani tace “Zinatu kinga yadda Allah yake ikonsa ko ban mutu ba gani nan sai lokacin da Allah yayi zan bar duniya zan tafi”

Zinatu dagowa tayi da sauri tana kallon Gwaggon kirjinta kamar ya fado dan sam bata gane inda maganar Gwaggon ya dosa ba.

Gwaggo kuwa ta saki murmurshi ta d’auke kanta

Habu da Shima bai gane inda zancen Gwaggon ya dosa ba ya dan saki murmurshi Yana “Wallahi Gwaggo ba Wanda ya kawo zaki tashi shekaru da yawa fa daga kinji labarin mutuwar shamsiya kiga fadi baki Kara Sanin inda kanki yake ba”

Murmurshi Gwaggo tayi tana “Allah sarki Shamsiya matuniyar kirki ni kuwa gwara ma da ka kawo maganar shamsiyar dan tunda na farfado Ina ta so na samu Wanda zai bani cikakken labarin yadda a kayi gidanka yayi gobara aka fito da Samha amma ba’a samu ceton Imitihal ba ya akayi haka”?

Zinatu gumin daya tsatsafo mata ta hau sharewa tana satar kallon Gwaggon da ke dan kallonta

Habu kuwa da yaji kamar Gwaggo ta fama masa ciwo ya hau bawa Gwaggo labarin duk abinda ya faru a ranar da yadda yayi sallama da shamsiya ta raka shi daga fitarsa da Yan mintuna labari ya same shi akan tayi gobara ya Kara da “Har yau Ina mamakin wanda ya kulle gidan ta waje dan kwado aka saka aka datsa lokacin da komai ya lafa naso nayi bincike su sule suka hana ni dan sai nake ganin kamar dai wani ne ya haddasa gobarar,Kuma naso na nemi Wanda ya ceto Samha a lokacin dan nima sai da na yi mamakin yadda ya iya fito da Samha batare da ya fito da Imtihal da a waje daya suke kwance ba a lokacin.

Da yanzu imtihal na Rayye da yanzu tana da shekara goma sha biyar”

“Mai ya sa a lokacin baka dage wajen bincike Dan ka gano Wanda ya kulle gidan ta waje ba,mai yasa a lokacin baka  yi bincike ka gano Wanda ya ceto Samha ya bar imtihal a ciki dan ta mutu ita da shamsiya da cikin jikinta ba”

“Gwaggo a lokacin baa nutse nake ba kuma ko da na dawo hayyacina su sule ne suka hanani Kuma ko nayi bincike ko banyi ba ai bazai saka Shamsiya ta dawo duniya da imitihal ba addu’ata kullum Allah yasa Aljanna ce makomar su”

“Banji a jikina gobara ne ya tashi a gidanka ba amma koma dai menene in Sha Allah gaskiya za tayi halinta”

Gwaggo tace tare da sakin murmurshi ta sako wani zancen.

Zinatu dake ta tsiyayar gumi jikinta na rawa ta mik’e tsaye tana “Gwaggo tun jiya nake dan fama da zazzabi zan je asibiti a dubani zan sake dawowa gobe”

“Ko dai yanzu zazzabin ya rufe ki Zinatu toh Allah ya sauwake sai kin dawo din”

Zinatu waje tayi da sauri har tana tuntube

Dan gani take idan ta cigaba da zama Gwaggo ma na iya cewa itace tasa aka kunnawa gidan wuta.

Sosai taji ta tsorata da Gwaggon dan yadda take magana sai take ganin kamar tasan tana da hannu a tashin gobarar.

Ko ganin gabanta ba tayi sosai

Ta fita waje a yadda take jinta ba zata iya Jiran ma su Habu ba Titi ta mik’a ta tari napep ta fada masa unguwar da zai kaita

Sai share gumi take tana tunanin ko dai Gwaggo tasan wani abu ne?amma taya zata san wani Abu bayan labari na isar mata ta yanke jiki ta fadi inda ita kuma daga zuwa dubata ta shafa mata maganin da zai ta sakata kwanciyar a iya saninta Gwaggo bata san komai ba ya akayi take magana kamar tasan wani Abu ko tana zargin wani abu.

Sam bata san ma sun iso ba sai da taji mai napep ya Mata magana ta dawo hayyacinta kasancewar ko jaka ma bata d’auko ba yasa ta cewa Mai gadi ya bashi dari biyar.

Ta shige ciki da sauri dan  gabad’aya ji take kamar kanta zai fashe Sam bata ga ta zama ba komawa wajen Boka Natete ya kamata dan gwara ya duba mata ko Gwaggo akwai abinda ta sani idan har ta sani din gwara kawai ta karasa ta.

Koda ta shiga gidan turus tayi tana kallon Amrah dake zaune a kasa ta mimika kafarta da ya kumbura da uban ciki a gaba,dan tsufan da cikinta yayi yasa bama tazo shagalin bikin Amjad ba dan cikin jikinta Muni ya saka ta sosai shi yasa ko fita bata san yi.

Akwatunan da ta gani a gefenta ga idonta ya kada yayi jajjur yasa gabanta wani iirn faduwa

Ta karasa wajen Amrah da Saurinta tana “Amrah lafiya ya na ganki haka? wanan akwatinan fa”?

Amrah kuka ta fashe dashi sai da tayi mai isarta ta bud’e Jakarta ta d’auko wani farin takarda tana ” Bashir ya sakeni Hajiya Bashir ya sakeni saki biyu”?

Zinatu zaman Yan dabaro tayi a gaban Amrah batare da ma tasan yadda aka yi ta tsinci kanta da zama ba ta cire dan kwalin Kanta da taji Yana Kara Mata zafi dan kanta tururi kawai yake

Kamar ma zata cire rigarta ma haka ta ringa ji saboda ko’ina na jikinta zafi ya d’auka ta fusge takardar daga hannun Amrah tana “A daidai lokacin nan da nake cikin tsaka mai wuya nake cikin tashin hankali hawa hawa Bashir zai sake ki Mai kika masa ya sake ki”?

“Hajiya sati biyu kenan idan na kwanta bacci sai dai na farka naga nayi fitsarin kwance mai zarni,tun ina dauka ciki ke sani fitsarin har sai da ya zama ido biyu ma idan Ina zaune zanga na jike da fitsari Bashir tun baya damuwa sai da ya zo Yana wulakantani ya kaurace min yace abun nawa na iskanci ne ba ciki ke saka ni fitsari ba tunda har da rana Ina sakin fitsarin

Gashi abun kullum kara gaba yake dazu kawai dan yayi baki na d’auko musu lemo na ajiye zan juya kenan naji na jike da fitsari har fitsarin na gangarawa kasa shine Bashir ya fusata ya min saki biyu ya fito min da akwatuna na yasa driver ya dawo dani gida”

Amrah ta karashe cikin sheshekar kuka

Zinatu kuwa ta dora hannunta aka tana”Aikin da muka yi akan Ameera ne ya dawo kanki Amrah innalillahi wa inna ilaihi rajiun Kuma mun jefa maganin a ruwa mai tafiya na shiga uku ni Zinatu wanan wane irin masifa ne”

Amrah cak ta tsayar da kukan da take duk nauyin cikin jikinta ma bata ji ta mik’e tsaye tana “Hajiya dama kune silar da nake ta fitsari har sai da aka sakeni”?

Zinatu ido ta zaro waje dan ta dauka a zuciyarta tayi magana bata san a fili tayi ba

A daidia lokacin da su Habu suka shigo gidan

Amrah ta fasa ihu ta fada kan Zinatu tana “kin kashe min Aure hajiya dama Ameera kika je yiwa asirin fitsarin kwance ya fada kaina”…..

*Page 39*

          Zinatu

Da k’arfi ta rufewa Amrah baki dan Wajen su Habu ya nufo yana “Lafiya mai yake faruwa mai yasa kika danne mata baki haka”?

“Alhaji Aljannu Amrah ta tayar fusge fusge da maganganu nazo na tarar tana yi wai Bashir ne ya saketa”

“Subhanallahi toh cika mata baki mana ya kika danne ta da k’arfi haka”

Amrah kuwa sai k’ok’ari take ta cire hannun Zinatu daga bakinta

Habu kuwa ganin yadda ta danne bakinta da k’arfi jikin ta na rawa yasa ya daka mata tsawa Yana ta saketa mana

Zinatu kuwa ta saki Amrah kirjinta kamar ya fado,ba zata so Habu yaji maganar tayi wa Ameera asirin fitsarin kwance ba,dan tunda har ya iya maganar Shamsiya har tana ganin ciwon da yake ji a zuciyarsa da yake bawa Gwaggo labari tasan asirin da ta sake masa da tsautsayi yasa ta bawa Boka Natete kanta ya karye

Cikin Ihun kuka Amrah ta Kalli Habu tana “Hajiya ce silar mutuwar Aurena,Abba Ashe Asiri taje yiwa Ameera na fitsarin kwance shine asirin ya dawo kaina”

“Bangane Maganar da kike yi ba wa aka yiwa asiri wacce Ameeran kike magana”?

Kukan da yaci karfin Amrah da kugunta da taji ya rike yasa ta kasa magana

Zinatu kuwa da bakinta ke rawa tace “Alhaji kaga irin maganganun da take ko Kai ma kasan baa cikin hayyacinta take ba”

Ihun da Amrah ta kwalla yasa suka yi kanta gabad’aya

Jinin da suka ga ya fara biyowa ta kafarta yasa Habu sakin sallati.

Zinatu kuwa kamar ta fadi saboda tashin hankali.

Haka suka kinkimi Amrah suka yi asibiti da ita.

Zinatu kamar zata zauce haka ta ringa ji dan Sam bata san ma da wane zata ji ba.

Har wani dan rama tayi,ko da aka duba Amrah Nakuda ne ta fara

Abinka da asibitin kudi sai da ta koma gida dan ta d’auko kudin da zasu kashe a asibitin dan Habu yace mata bashi da ko sisi Yana kuma ta Kiran Amjad a waya baya samun sa.

Kamar zata saki ihu a lokacin da ta jawo drawer dinta da ta ajiye dalolin da Barrister Aisha ta lika mata da ta kwaso tasan ko Yaya ta canza kudin suna da yawa dan itama ba Karamin kudi ta kashe a bikin Amjad ba duk dan ta nuna suna da kudi.

Wayam taga drawer ba ko sisi

Tasan ba mai daukar mata kudi sama da Sultana dan itace take zuwa ta dib’ar mata kudi Kai tsaye batare da ta tambayeta ba.

Maida drawer tayi ta rufe ta d’auki ATM dinta ta fito dan a yanzu so take ta fara samun kan Amrah kafin ta san nayi dan yanzu babban burinta taga ta koma wajen boka Nateten dan bata ga ta inda zata soma maganar Auren Sultana da Ayuba bayan asirin da ta yiwa Habu ya karye ba.

Asibtin ta koma wasa wasa sai gashi Amrah ta kwana ta Yini bata haihu ba inda aka yanke yi mata operation

Suka sa hannu bayan sun biya kudi Mai yawa.

Hanne

      “Gwaggo Yau ma kawar taki zata zo dubaki ne”?

Murmurshi Gwaggo tayi tana “Ya aka yi kika san zata zo”?

“Ai naga kina ta fara’a me Gwaggo indai zata zo sai naga kina ta farin ciki”

“Zata zo Anjima Hanne”

“Gwaggo dan Allah Mai yasa wacce suke zuwa tare da ita take san Saka nikaf ne ya take da ita”?

Murmurshi Gwaggo ta saki tana “Kai Hanne wanan tambayoyi haka yarta ce ai haka take bata cire nikaf”

“Gwaggo nidai Ina ganta duk sai naji tsigar jikina na tashi haka kawai nake so naga fuskarta”

“Zaki ga fuskarta watarana Hanne karki damu naga dai ai kuna gaisawa ko”?

“A Gwaggo Muna gaisawa”

“Toh watarana ma zaki ga fuskarta”

Murmurshi Hanne tasa ta mik’e tana “Gwaggo bari naje na karasa aikina”

Kai Gwaggo ta gyada mata ta bi hanne da ido har ta fice daga dakin

Ta Maida idonta ta rufe ta tafi Tunanin ranar da ta farfado

Idonta da ya mata nauyi ta bud’e dak’yar ba kowa a dakin ita kadai ce sai karatun Qurani dake ta tashi a dakin.

Tafi awa daya tana ta k’ok’arin hada tunanin ta waje daya dan sam ta kasa tuna inda da take balle tasan abinda ya faru da ita.

“Gobara ya tashi a gidan Shamsiya tana ciki Kuma”

Kalmar da ta fara tunawa kenan kanta ya Sara mata kafin ta runtse idonta tamkar a yanzu ta fara tuna abinda ya faru.

Shamsiya da ta tuna da cikin da take d’auke dashi da yadda ta ringa rokonta akan ba ta san komawa gidan Habu ita tsoro take ji yasa ta fara sheshekar kuka dan da ace tasan mutuwa za tayi da bata barta ta koma gidan Habun ba.

Shigowar Hanne dakin da sallatin da ta rafka da k’arfi tana ta farfado yasa ta dan Bud’e idonta,tana kallon Hanne da ta fita da gudu ba jimawa sai gata ta dawo da sule da Ya ibrahim da suka ringa Yar rige rigen zuwa wajenta

Ita dai ido ta zuba musu tana kallon yadda suke murna da ta farfado har Sule ya tafi Sujadda Yana godewa Allah da farfadowar da tayi.

Daga yadda suke magana ta gane ta Dade a kwance dan da alama sun fidda rai ma da ita.

Bayan Yan koke koken da suka yi tayi magana a hankali akan su dagata tana so ta zauna.

Sule da ya Ibrahim ne suka dagata har lokacin hawaye bai bar zubo musu ba

Gabad’aya jikinta ba kwari can kasan murya ta tambaye su inda Habu yake da dan bature.

A zaune tayi sallah zuciyarta fal da tunani da tambayoyin ko abincin da suka jera mata a gabanta bata iya ci ba da ido kawai take bin Sulen da ta ga canji a tare dashi daga gidan ma da suke zaune ta gane Allah ya rufawa Sule asiri irin rufin asirin da ta dade tana rokon Allah akan ya mi shi.

Ameera da ta tuna yasa ta sake jefa musu tambaya

Sai a lokacin Abba sule ya rike hannunta ya hau bata labarin komai tunda ga lokacin da ta kwanta har zuwa Auren Ameera.

Wani sabon kukan ta Kara kecewa dashi dan ta d’auka imitihal na Rayye

Sai da ta kwana tana kukan rashin shamsiya ganin su Sule sunyi matukar damuwa yasa ta bar kukan filin ta koma na zuci.

Jamaa da tayi muamalla dasu kuwa duk da suka ji labarin ta farfado haka suka ringa cincirindon zuwa duba ta dan ba laifi tayi zaman mutunci da mutane sosai,duk da wasu Allah ya musu rasuwa a yadda take Jin labari.

Acan inda ta zauna wacce ta zamo kamar Kawa a gareta  Maman Kamilu dan su Sule ma sunyi k’ok’arin waje rike zumunci basu manta da ita ba dan itama a kwancen da take sun bata labarin yadda take yawan zuwa dubata.

Itama tana cikin wayanda suka ringa sintirin zuwa dubata.

Duk rashin zuwan Habu ya dameta dan har dan Bature Shima yazo ya dubata amma Habu bai zo ba,ya Ibrahim Kuma yace ba zaa kira shi ba a zuba masa ido aga iya gudun ruwansa a wajensa take Jin labarin yadda Habu ya watsar da ita,da irin rashin mutunci da ya ringa yi har Ya ibrahim na ce mata ta yafe Habu kawai ta cire shi a cikin yayanta.

Tasan da gangan Habu ba zai watsar da ita ba,tasan duk abinda yake yi baa cikin hayyacinsa yake ba dan tasan wacece Zinatu,tun kafin ma ta kwanta bata da burin da ya wuce taga ta raba ta da kowa Ina ga Kuma ta kwanta.

Addu’a kawai ta ringa bin Habun da shi satin ta biyu da farfadowa watarana da Yamma tana zaune dan a yanzu Sam bata San kwanciya dan wani irin ciwon baya take yi Wanda har zaryar asibiti su Sulen ke yi da ita dan bata sani ba ko dan ta dade a kwance ne shiyasa take fama da ciwon bayan.

Farcen kafarta Hanne ke yanka mata Maman Kamilu ta shigo da wata mata dake sanye da nikaf ga hijabinta har kasa sai bulbula kamshi take

Gwaggo kuwa murmurshi ta saki da ta ga maman Kamilunn dan Sam bata kawo zata dawo kurkusa ba lura da shekaranjiya tazo ta dubata.

Maman Kamilu waje ta samu ta zauna ta nunawa Mai nikaf din waje itama ta zauna cikin wani irin murya ta hau gaida Gwaggo da Hanne

Gwaggo ta amsa cikin fara’a Hanne Kuma ta fita waje ba jimawa ta dawo da ruwa da lemo ta ajiye musu tayi waje.

Gwaggo kuwa satar kallon Mai nikaf din kawai take dan bata san Wacce ita ba kuma bata ga alamar maman kamilu zata fada mata wacce ita ba

Kamar tasan abinda ke zuciyata

Taga Mai Nikaf din ta taso ta dawo gefen gadon ta zauna

Maman kamilu Kuma taje ta rufe k’ofar har da murza mukulli

Hakan da ta gani ne yasa kanta ya daure tana k’ok’arin magana Mai Nikaf din ta daga nikaf din fuskarta.

Gwaggo ta dafe kirjinta kamar wacce wutar lantarki ya ja dan duk da ta manyanta,ta canza ba zata kasa gane ta ba.

Hawaye kawai ke tsere a fuskarta a lokacin da ta fada kan Gwaggon ta saki kuka a hankali.

Gwaggo da tayi suman wucin gadi ta tattara dan sauran nutsuwar da ya rage Mata ta dago ta tana “Shamsiya ke nake gani ko dai gizo kike min”?

“Nice Gwaggo kiyi magana a hankali ban mutu ba Gwaggo Ina rayye”…

*Page 40*

          Gwaggo

Hannunta rawa kawai yake wajen shafo fuskar shamsiyar dan gani take kamar dai gizon take mata ba ita bace ba,ta dan girgiza  kanta tana tunanin kila dai Tunda ta d’auko tsufa da tunanin Shamsiyyar dake manne a ranta da ko na Sakan daya bata tab’a barin zuciyarta ba yasa take ganin shamsiyar ce.

Shamsiya kuwa ganin yadda gwaggo ke ta shafa fuskarta jikinta na rawa yasa ta rike hannayenta ta matsa kusa da ita sosai ta kwantar da muryarta dan Sam bata san Hanne ta ganeta a duk wayanda ma take mataciya a wajensu ba wanda ta fara bayyanawa kanta sama da Gwaggo

“Gwaggo ba gizo nake miki ba Shamsiya ce kanwar Hanne ban mutu ba na samu na kubuta daga gobarar”

“Shamsiya wai da gaske kece nake gani a gabana ba mutuwa kika yi ba? Habu da sule sun tabbatar min kina cikin gidan Samha ce kawai aka kubutar Maman Kamilu ko dai kaina ya fara tab’uwa ne wai Shamsiya ce kika zo da ita”?

“Itace ba mutuwa tayi nima jiya daddare tazo min sai da na tsorata amma da ta min bayani na yarda tana rayyen ki barta dai ta miki bayani ba fatalwa bace ba ita din ce dai bansan dalilin daya sa tace bata so kowa yasan tana rayye ba ciki kuwa har da mahaifiyar ta dake kwance”

“Shamsiya”

Gwaggo tace tana Kara Kankame hannunta dan a yanzu ta yarda ba gizo idonta ke mata ba Shamsiyr ce dai a gabanta, Shamsiyyr da tunda ta farfado duk sallar da za tayi sai ta mata addu’ar rahamar Ubangiji,takan ji kamar ma itace silar mutuwar shamsiyar dan itace ta matsa mata ta koma gidan Habun har gobara ta tashi da ita.

“Gwaggo Ina rayye ban mutu ba”

Shamsiya tace hawaye na tsere a fuskarta.

Gwaggo kuwa ta saki hannun Shamsiya ta daga hannunta sama ta hau Godewa Allah tuni taji kamar nauyin da taji kirjinta na mata tunda ta farfado na raguwa

Sai da ta dade tana yiwa Allah kirari da godiya kafin ta sauke hannunta ta Kara ruko hannun Shamsiyar dake ta aikin share hawayen farin cikin kasancewa da wani na kusa da ita bayan tsawon shekaru,ba zata iya fasalta yadda take Jin zuciyarta ba.

“Bani labari shamsiya ya akayi kika iya kubuta daga gobara?Ina cikin jikinki Ina imtihal”?

Shamsiya na k’ok’arin magana suka ji ana kwankwasa k’ofar

Shamsiya tayi sauri ta matsa kusa da Gwaggo cikin muryar rada tace “Gwaggo bana san Hanne tasan nice a yanzu ke kadai ce kika San Ina rayye bana san kowa ya sani a  yanzu akwai abinda nake Jira sai dai idan na baki labari”

Gwaggo da sauri ta gyada kanta

Shamsiya ta Maida nikaf din fuskarta ta koma kan Kujerar da take zaune da Hanne ta fita ta barta.

Maman Kamilu Kuma ta isa bakin k’ofar ta bud’e tana “Sirri muke irin namu na tsofaffi”

Murmurshi Hanne ta saki tana “Ai tunda naga kun rufe kofa nace toh wani tattaunar wa kuke yi dama Faten tsakin da Gwaggo tace tana so na gama shine nace bari na kawo muku kila kema kiyi sha’awa”

“Aikuwa kin kyauta dan kamar kinsan Ina ta sha’awa ba mai yimin ne”

Maman Kamilu tace tare da karbar farantin hannun Hanne.

Hanne kuwa da idonta ke kan shamsiya da haka kawai taji tana san ganin fuskarta ta karasa wajen Gwaggon dake ta sakin murmurshi tana “Allah dai ya miki albarka Hanne yadda kike dawainiya dani Allah yasa naki yaran Suma suyi dawainiya dake haka idan kin tsufa”

“Ameen Gwaggo”

Hanne tace cikin murmushi tana “Baiwar Allah tunda kin shigo ai da kin cire nikaf din tunda nan duk mata ne”

“Kai Ai bata tab’a rabuwa da nikaf dinan barta kawai kije abinki bamu gama tattaunawa ba”

Hanne mik’ewa tayi tana “Too ai bansan baku gama ba bari naje toh Gwaggo idan kina bukatar wani abu sai ki kirani”

“Ba matsala Hanne Allah ya miki albarka”

Daga haka Hanne ta fice daga dakin tana Jin kamar taje ta cire nikaf din fuskar Shamsiya.

Sai da ta fita shamsiya ta saki ajiyar zuciya ta tashi da kanta taje ta saka mukulli ta dawo wajen Gwaggo ta cire nikaf dinta ta hau bata labarin yadda su Babagana suka taimake ta har zuwa gidan yakura da take cewa Mami da suka kaita da silar kaita gidan Yakuran ne ya canza mata rayuwa canjin da ko a mafarki bata tab’a tunanin samu ba.

Waiwaye

Alhaji Mato da Yakura tamkar Yar cikinsu haka suka d’auki Shamsiya da suke ganin kyautar ta Allah ya Basu,dan sosai suke Jin tamkar su suka haifeta.

Yaranta Kuma da suke da balain shiga rai da farin jini sai suke ganin tamkar jikokinsu ne.

Dan kamar ma zuwan shamsiya raywuarsu da yaranta sai ya Kara zama silar yin Arizkinsu dan budi suka yi ta samu ko ta Ina.

Alhaji Mato da ya kasance mijin Yakuran ya samu Karin matsayi a a wajen aikinsa inda aka mai dashi kasar waje.

A lokacin Shamsiya ta gama secondary school tana Jiran result Alhaji Mato ya zo musu da albishir din komawa waje gabad’aya.

Silar komawarsu waje kenan.

Inda Imithal aka Saka ta a makaranta mai balain tsada Yan biyu kansu makarantar da aka saka su acan wajen na masu hannu da shuni ne.

Shamsiya zata iya cewa ma haifarsu kawai tayi amma sunfita san yaran dan basa wasa da duk wani abu da ya shafi yaran.

A haka ta fara zuwa jamia inda ta zabi karantar law dan babban burinta taga ta zama lawyer idan har Allah ya ara mata tsawon rayuwa da kanta take so tayi sharia da Shamsiya

Abinka da can da nan ba daya bane ba kuma bata da burin da ta saka a gaba sama da zama lawyer sai karatun nata ya ringa zuwar mata cikin Sauki tun kafin ma ta gama karatu Yakuran da Shamsiya ke cewa Mami ta dora ta akan business siyar da wanan shiga da wanan Nigeria Shamsiya ta fara kama manyan kudin da bata tab’a tunanin kama su ba.

Alhaji Mato kuwa shi ma ariziki sai abinda yayi gaba gashi yasan manyan mutane.

Shamsiya kuwa duk abinan da ake hankalinta na Nigeria yadda Yakura taga Abunda ke jefa ta cikin damuwa shine tasan halin da Yan uwanta ke ciki a gida.

Yasa ta mata hanyar wayanda suke da kusanci da su Hannen

Inda duk wani labarin su  Hanne har zuwa rasuwar mahaifinsu duk ta silar Wanda take Jin labarin gidan nasu ta samu labari.

Taso zuwa Nigeria a lokacin amma Yakura ta hanata dan lokacin ta kusa gama makaranta Kuma Ko ta gama aiki na jiranta Mai tsoka.

Shamsiya a haka taci kukan rashin mahaifinta banda Yakura da ke ta hanata taso shiga Nigeria a sirrance taga mahafiyarta dan tasan tana rayye.

Amma tuna idan har Mahaifiyar ta tasani zaman lafiyar da suke da babbar Hanne zai sa itama ta fada mata daga nan Hanne zata iya Jin labari itama ta fadawa Abba sule daga nan Kuma zaa iya Sanin tana rayye Wanda duk burin da taci zai tashi a banza dan tana so ta bayyana ne a lokacin da shamsiya bata tab’a tunanin ba.

A haka ta gama karatun ta ta zama cikakiyar Lawyer ta samu aiki a wani babban kotu a can

Irin cases din da ta ringa nassara akansu saboda kwarewar da ta yi akan aikinta yasa ta ringa samun kudi.

Kudin da taga tana samu yasa ta shawarci Alhaji Mato akan yadda zata ringayi da kudin dan niyyarta ta ringa turawa Mahaifiyar ta.

Sai dai a ranar sai gashi Alhaji Mato da Yakura sun bata wani takarda da tana dubawa taga Rabin dukiyarsu ne suka mallaka mata Halak malak,dan sunce itace dai yarsu tunda basu tab’a haihuwa ba idan kuma rai yayi halinsa ragowar dukiyar sai su Yan uwansu su d’auka.

Yadda suka kira lawyer da shaidun sun mallaka mata dukiyar yasa ta sakin kukan farin ciki dan yau ko da bata aiki wanan dukiyar da suka mallaka mata ya ishi har jikokinta rayuwa.

Da wanan ta ringa tura kudi Nigeria ana tamfatsa mata gidajen Mai da sunan A$A Oil And Gas.

Banda gidaje da ta ringa ginawa gefe guda Kuma duk motsin su Habu tana da labari.

Har na gidansu da a yanzu take musu Aiken kudi da sadaka fisabillahi .

Da kudin da take dashi ta kula alakar kasuwanci da  wayanda suke ji da kansu a kudi,a ciki akwai gidansu Yareema,akwai gidansu Jawaheer da duk tasan suna da alaka da Zinatun da take so a yanzu ta shiga jikinta ta shamace ta

 A haka ta saki kudi Mai yawa tasa aka siye gidan dake makwaftaka da gidan Habun ta Kara da siyen gidaje biyu na jiki tasa aka baje aka tamfatsa mata gida dan so take idan ta dawo Nigeria ya zama tana makwaftaka da Zinatun.

Koda ta tashi dawowa Nigeria bayan ta ajiye aikin ta na can wajen.

Kuka taci ta gode Allah na rabuwa dasu Yakuran da suma suka shirya komawa Saudiya gabad’aya.

Bata ma so rabuwa dasu ba su suka karfafa mata gwiwar ta koma Nigeria ta cimma burinta.

Koda ta dira Nigeria gidansu baba gana ta fara sauka dan zata iya cewa sune silar da ta samu niimar da take dashi duk da tana yawan yi musu aike har gida ta Gina musu.

Alheri tayi musu sosai tabi yayansu dake gidajen auren ta musu goma Sha Tara ta arizki.

Da haka ta dawo gidanta dake kallon gidan Shamsiya inda abun yazo mata da sauki sai Samha ta fara shigowa gidanta da biyu ta jawo Samhar jikinta dan so take ta shiga jikin Zinatun sosai.

Kamar yadda tayi tsamani tasan sai Zinatu ta shigo gidan saboda kwadayinta hakane yasa ta ringa wasa da hankalin ita da Habun da ta lura Basu da burin daya wuce su san ta.

Bare ma Zinatu da ta nace da shigowa gidan.

Da biyu take b’oye Aryan da Abyan dan da Habu suke kama sosai haske kawai suka Fi Habun.

Tasan idan har Zinatu ko Habun suka gansu dole jikinsu zai iya basu jinin Habun ne dan kamaninsu yayi yawa.

Tunda Kuma ta dawo Nigeria sau biyu tana zuwa gidansu cikin nikaf da sunan gaishe su kawai tazo yi.

Duk da a yanzu idan ya bayyana tasan Zinatu ba Abunda za ta iya yi amma sai take san ta d’auki lokacinta wajen cigaba da sawa Zinatun ido.

Duk halin dasu Hanne ke ciki tana sane

Har zuwa Auren Ameera da Yareema da Gimbiya ce ta bada katin gayyata na musamman aka.kai mata dan sun ma santa saboda itama kudin da take dashi dan masu kudi sun san junansu.

Da Barrister Aisha suka Santa dan kawai tayi bada kama.

A irin wanan lokacin taji labarin Gwaggo ta farfado da tasan cewar ma aikin Zinatu ne,dan daidai da zaryar da Zinatu ke yi gidajen bokaye tana da labari dan duk wani motsinta ta sani

Farfadowar Gwaggo yasa taji kamar ta taka rawa dan babban burinta a yanzu taga wani wanda take da kusanci dashi yasan cewar tana rayye.

Dan har zuciayarta ta fara azalzalarta da taje ta samu Hanne a b’oyen amma gani take idan har Kuma Hanne tasan tana rayye murna ba zai iya barinta ta b’oye ba.

Tasan Gwaggo kawai zata fara bayyanawa kanta akan tana rayye ta kuma bata shawarar abinda ya dace tayi.

Gwaggo

Rungume shamsiya tayi da ta gama bata labarinta ta Kara da “Kwananki bai kare ba shamsiya saboda habu take so ta kashe ki bata san kwanakin bai kare ba,hasali ma kasheki da ta so tayi ya zama silar d’aukakar ki.

A yau ba sai gobe ba shamsiya ki Kai Yan sanda ki kamata lokaci yayi da zaki bayyana tasan kina rayye Ina so naga ya za tayi idan ta ganki da jikokina”

“Gwaggo saura kiris Ina ta bincike ne akan yaran da ta aika ya Saka min wutan.

Duk da nasan da wuya na iya samun sa amma Ina ta bincike na samo makarantar da yayi idan har Allah ya taimakeni na samo yaron komai zai zo min cikin sauki”

A ranar Gwaggo kamar ba zata bar shamsiyar ta tafi ba da alkawarin ba zata tab’a fadawa kowa ba suka rabu.

Koda aka kwana Biyu sai da shamsiya ta sake dawowa duba Gwaggon da maman kamilu.

Gwaggo kuwa abinda ya d’auke mata hankali daga damuwa da rashin ganin Habu kenan dan burinta a yanzu asirin Zinatun ya tonu Habu yasan waccece yake Aure.

Dan yanzu addua kawai take ba dare ba Rana akan idan akwai wani asiri ma da Zinatun tayi Allah yasa ya karye.

Zinatu

    Ihu kawai take tana “ku barni na debo kayana ya zaku watso mu waje batare da mun d’auki komai ba”

Tace a haukace tana k’ok’arin fadawa gidansu da ma’aikata da bata sani ba ko Yan sanda ne da suka zagaye gidan sai ta je shiga sai wata murtukekiyar mata tayi jifa da ita.

Wajen Habun dake tsaye can gefe Yana ta rafka sallati ta Isa tana Jin wani azabar kaikaiyi na taso mata dan a yanzu ko yaya ta shiga tashin hankali sai taji wani azabar kaikaiyi ta kasanta.

Zata je wajen boka zata je wajen bokanta dan ya sabunta mata aiki akan Habu bayan nan ya Mata wasu Abubuwan Abu ya gaggara dan rashin lafiya Amrah ta ringayi bayan anyi mata C’s kamar zata zauce haka take ji.

Ba mai kula da ita sai ita Habu kuwa Yana ta k’ok’arin hada kudin da zai b’iya banki Amma kamar an toshe masa duk wata kofar da zai samu kudi.

Iya miliyan biyar ya samu a wajen Amjad da yace masa bashi da kudi.

Da nan ma shi yaje can gidan Amjad din dan wayarsa na hannun Jawaheer

Tashin hankalin da yake ciki bai sa ya bai bi takan Amjad ba,a yanzu bashi da zabin daya wuce siyar da gidan nasa.

Sai dai kamar an kwarawa gidan nasa bakin jini duk wanda yazo sai dai Yayi wa gidan tayin wulakanci gefe guda Kuma ga lokacin biyan yayi suna Neman haukata shi da Kiran waya.

Shi Kansa bai san ta Ina zai fara ba dan gefe daya ga Amrah nata fama da rashin lafiya da jaririya.

A yau da ya kasance litinin Yana zaune Yana tunanin zuwa wajen Sulen da yasan da wuya ya iya samun irin wanan kudin a wajensa

Zinatu Kuma na kitchen tana girki tana masa mitar canzawar da Amjad yayi daga auren Jawaheer ta Kara da tana gama girkin nan gidan Amjad din zata je

Suka ji jiniya daga waje kafin su gane mai ke faruwa sai ga ma’aikata sun cika gidan har da bindigoginsu.

Hannunsa kawai suka rike suka yi waje dashi wata Kuma tayi wajen da ta hango Zinatu na lafiya daga Ina ta ruko hannunta bata direta a ko’ina ba sai waje.

Amrah da itama ke fama da kanta suka fito da ita da jariryar  da ta haifa waje,sultana dake sanye da sleeping Dress itama da daki daya suka kwance da Samha aka watso su waje Suma suna mitsitsika ido.

Daga nan  suka hau zanna gidan da wani Jan rubutu

Zinatu kuwa da ta kasa gane mai ke faruwa ta nufi wajen Habun da gudunta ta hau tambayar sa me ke faruwa ne

Anan yake fada mata banki sun kwace gidan da motoci biyun da ke ciki Kuma a Sanin da ya musu idan har baka biya su ba ko cokali basa bari ka d’auka.

Anan Zinatu ta hauakce tana akwai gwala gwalan ta a ciki akwai suturunta masu tsada a ciki tayi cikin gidan da gudu suna su bar ta kwashe kayanta.

Amma Ina ko ta kanta basu bi ba suka garkame gidan suka haye motocinsu suka tafi.

Zinatu ta zube a kasa ta hau birgima tana “wayoo Allah gwala gwalaina yanzu bazasu barni na dauki komai ba yanzu daga Ina zamu fara”

“Wai Abba Mai ke faruwa ne ya suka watso mu waje su waye su”?

“Karku Tara mana jamaa kuzo mu tafi gidan Sule tukunna”

“Bangane mu tafi gidan Sule ba taya zamu kwashi jiki dukanmu mu tafi gidan Sule wallahi ba zamuje gidan Sule ba”

“Toh gidan uban wa zakije idan ba zakije gidan Sule ba sai ki tafi gidan ku ni ki barni na wuce da yarana gidan Yan uwana”

“Haba Alhaji ai da kunya ka kwashi jiki da yaranka ka tafi gidan kaninka Ina laifi mu tafi gidan Amjad ai nan yafi mana rufin asiri kafin mu San nayi tunda gidan danmu ne”

“Kinji kunya Zinatu Yanzu dan baki da hankali gidan Amjad kike so mu kwashi jiki mu tafi da kije gidansa da kije gidan Sulen wane yafi “?

“Wallahi gwara naje gidan Dana Alhaji nidai idan zaka je kaje Kai kadai Amma nikam can gidan Amjad zamu tafi”

“Ke da wa zakuje gidan Amjad wallahi ba zanje ba ke kinsan rashin mutunci matarsa kuwa ai wallahi ba abinda zai kaini gidan ni gidan ma kawar Samhan nan zan shiga”

Sultana tace tare da rike hannun Samha suka nufi gidan shamsiyar da sauri.

Zinatu kuwa ta karbi jaririyar Amrah daga hannunta tana “Kizo mu shiga gidanan kafin na kira Amjad a waya su gyara mana daki.

Amrah mik’ewa tayi dan tunda ta haihu bata magana bata da ma aikin daya wuce kuka.

Habu kuwa ganin duk sun nufi gidan shamsiya yasa ya d’auki hanyar titi dan gidan Sule kawai zaije yaji idan zasu bashi wajen zama dan a yanzu ba inda zai Fi masa rufin asiri sama da can.

Da yake Samha ce tasan kan gidan da dan gudunta ta shiga gidan.

Sultana na biye da ita a baya

Zinatu Kuma tana daga bayansu itama tana binsu dan da wanan damar ma da ta samu na Neman taimakon zata samu ganin matar gidan.

Akan dining ta hango wasu Yara suna cin abincin palon ba kowa sai karar tv

Samha kuwa wajensu tayi da gudu tana “Aryan Abyan ina Immi da Mummy”?

Zinatu tsayawa sukayi daga tsakiyar palon suna kallon yaran da Basu juyo ba

Sultana kuwa kamar gidan ubanta tayi saurin samawa kanta wajen zama tana “Allah yasa matar nan ta rikeni.

Juyowar da Aryan da Abyan din suka yi yasa Zinatu kusan sakin jariyar hannunta dan sai taga kamar Habu aka zuke ya dawo yaro ya zama biyu……

*Page 41*

          Zinatu

Ido kawai ta kura musu tana kallon su,dan Yarinta da haske kawai Yan biyun zasu fadawa Habu amma ba inda suka baro Habun

Sultana kuwa da itama idonta ya Fada kan yan  biyun ta mik’e tsaye cikin tsananin mamaki ta nufi wajen Yan biyun tana “Hajiya kinga mai idona yake gane min kuwa kinga Yan biyu masu balain kama da Abba”

Shamsiya da fitowarta daga wanka kenan taji motsi a kasa sanin ba Wanda tasan zai zo gidan yasa ta nufi wajen da wani Abu ke ajiye kamar kwamfuta dan ta nan take ganin duk wani abu dake wakana a kasa.

Dafe kanta tayi da sauri da taga Zinatu a tsaye baki a sake ta kurawa su Aryan ido

Wani abu dake gefe ta latsa da sauri kafin ta cire hannunta wata Mata da itace take mata aiki muryarta ta ratso abin

Cikin bada umarni tace ta sauka kasa da sauri ta  hawo dasu Aryan Sama sanan ta sallami Su Zinatu su tafi.

Ta zubawa kwamfutar ido tana kallon yadda Zinatu ta fara Jan kafarta irin rukon da tayi wa jaririyar yasa ma Amrah taso wa ta karbeta daga hannunta.

Zinatu kuwa kasa ma hada tunanin ta tayi waje daya dan tayi matukar girgiza da ganin Yan biyu masu balain kama da Habun dan kamanin yayi yawa ta d’auka ko kanta ne ma ya fara samun matsala dan abubuwa da yawa da suka cushe mata Kai har magana take ita kadai.

Sai da ta ga Sultana itama taga kamanin Yaran da Habun ta fara Jan kafarta dan ta Isa wajen su Yan biyun abubuwa kala kala na zuwar mata rai,abinda Kuma yafi tsaya mata a rai shine kila Habu ya tab’a Aure a b’oye bata sani ba,idan ba aure yayi a b’oye ba to kila soyayya yayi da wanan barrister ya Mata ciki dan gabad’aya Tunaninta bai kawo mata shamsiya ba dan tasan ta rasu.

Aryan da Abyan kuwa ganin sultana ta saka su a gaba tana ta tafa hannuwa yasa Aryan fara mik’ewa dan basu da sakewa da wayanda Basu sani ba.

Aryan ya matsar da Kujerar da yake Kai cikin harshen Turanci yacewa Abyan ya tashi su koma sama

Dan Yama tsorata da yadda Zinatu ta zuba musu ido ta kuma nufo wajen su.

Ga sultana ta rike Abyan tana tambayarsu su Yan biyune ya sunayensu.

Saukowar wanan murdadiyar matar cikin hade rai yasa sultana sakin Hanun Abyan a daidai lokacin da Zinatu ta karaso kanta na duakar dumi da lodin tunanin dake kanta na ganin Yan biyu masu kama da Habu

Hannunsu Aryan ta rike ta hau sama dasu.

Sultana da Zinatu suka bi su da ido.

Sultana kuwa ganin sun haye ta Kalli Zinatu tana “Hajiya kiga wani ikon Allah wallahi yaran nan yadda kika san Abba ne ya haifesu kinga yadda suke kama dasu ni kuwa zan so ganin babarsu da babansu wallahi kila ma su Abba suna da Yan uwan da bamu sani ba shi yasa yaran ke kama dasu.

Maganar da Sultanar ta fada yasa ta sakin wani irin wawan ajiyar zuciya dan sai taji ta yarda duk yadda a kayi ma akwai dan uwansu Habun kila da shi yake auren barrister Aisha shiyasa yaran suka yi kama da Habun dan Sam ba wani sanin Yan uwan Habun tayi ba in ka d’auke wayanda suke uwa daya uba daya.

Saukowar matar nan da tambayr da ta jefa musu da  harshen Turanci akan Mai suke nema

Yasa sultana bata amsa cikin harshen Turanci akan Matar gidan suke nema is urgent wani taimako zata musu

Matar kuwa tace suyi hakuri matar gidan tayi tafiya Kuma ko tana nan sai kana da appointment da ita zaka iya ganinta dan haka su rubuta mata sunansu da lambar waya idan ta dawo zata bata.

Sultana tuni ta hade rai dan Sam ba haka taso ba gashi yadda taga matar ta hade rai gashi ta murdu da alama tana kawo wani magana zata iya watsa ta waje.

Samha kuwa dake can kujera tana Dan wasaninta ta nufi wajen matar ta kira sunanta da Aunty cikin harshen Turanci tace ai ita zata iya zama ko tunda Matar gidan ta Santa

Matar kuwa ta dan saki murmurshi tana zata iya zama matar gidan  ta Santa.

Zinatu kuwa Sam ba haka taso ba taso ganin Barrister Aisha dan a wanan gab’ar tana bukatar taimako a wajenta tana so Kuma ta ganta ta dan yi mata tambayoyi ko zata gano Wanda take Aure dan tabbas duk yadda akayi Wanda yake da Hadi dasu Habun ta aura.

Muryar matar ne ya katse musu tunanin da take  tana ko zasu ajiye lambar wayarsu su tafi akwai abinda za tayi.

Sultana tsaki taja tayi waje fuuu tana “Yau banda kaddara har akwai wacce ta Isa ta wulakanta mu har ana mu ajiye lamba kafin mu ganta.

Zinatu kuwa da taji tana balain San ganin Barrister Aisha ta karbi takardar hannun matar ta rubuta lambar wayarta da sunanta

Ta mik’a wa matar tana Dan Allah barrister Aisha na dawowa ta taimaka mata ta bata ta ce Mata maman Samha ce akwai taimakon da take so ta mata.

Matar karbe takarda tayi tana zata fada mata.

Zinatu kuwa ta juya tayi waje tana Kara waigen palon taga ko zata ga Yan biyun da suka tsaya mata a rai.

A waje ta tarar da Amrah rungume da jariryarta

Sultana kuwa sai masifa take tana zagin barrister Aisha

Zinatu kuwa ta warware dan kwalin kanta ta dan lullube kanta dan sai a yanzu ma ta tuna ko waya ma basu bari sun d’auka ba.

Kamar za tayi kuka ta Kalli Sultana tana “Yanzu dai dolenki ki zo mu wuce mu tafi gidan Amjad ko tunda dai an koremu daga gidan matar nan da bata ganuwa sai tasan mutum na rasa wacce irin mata ce ita sai kace wata matar shugaban kasa.

“Hajiya sai nake ganin dama gidan Abba Sulen muka je tunda Yaya Amjad ko sati biyu fa bai yi da Aure ba bai dace ma ace munje can ba”

Amrah tace a hankali dan wanan tashin hankalin da ta shiga na fitsari yasa ko magana ba ta san yi mugun haushin Zinatu take ji da tunda aka sallamota daga asibiti take ta bata hakuri ta ringa mata alkawarin zata samu lafiya zata sa a karya asirin da tayi.

Duk da ta tsani su Ameeran itama dan suna Yara ma Zinatu ta cusa musu kiyayyar su a zuciyarsu amma Sam bata San mugunta bata so Zinatu ta cutar dasu ba Abu daya dai kawai take so ya zama basu kamo kafarsu a komai ba ya zama dai sune a kasan su.

Sai gashi ma a garin mata muguntar abu ya dawo kanta

“Aikuwa gidan Yaya Amjad zamu je ba za muje gidansu Ameera neman taimako ba ai da kunya na kasa yarda wai yau mune muke neman wajen zama wai uban me Abba yayi ne aka zo aka kwace mana gida ina sauran gidajen da yasa Yan haya suke ina kudinsa suke ya siya mana wani gidan mana”

Sultana tace tana hararar Zinatu da ta rike hannun Amrah tana su tafi gidan Amjad din dan ba zata tsaya sauraran sultana da a yanzu zata iya kawo mata Mari ba,sultana ta balain rainata duk abinda ya fito daga bakinta yabata take yi kamar ba ita ta haifeta ba,

A yanzu ba wacce take balain tausayi sama da Amrah a yanzu so take ta dan samu nutsuwa ta je wajen boka Natete taji ko da yadda zai iya karya asirin a Kuma Yi aikin da Amrah zata koma gidanta tunda saura igiya daya.

Tunda suka dawo gida aka kira Bashir a waya akan ta haihu bai zo ba wani abokinsa ya taro da tarkacen kayan bby da dubu hamsin

Abubuwa duk sun cakude mata

Har suka hau Napep suka Isa gidan Amjad sultana masifa kawai take tana ita ba zata d’auki iskancin Jawaheer ba idan har ta mata sai ta rama.

Zinatu kuwa maganar Jawaheer da sultanar tayi ya tuna mata rashin kunyar da jawaheer ta mata har tana danganta ta da Mai delivery take tayi balain hade rai dan idan tace ba tayi nadamar hada Auren Amjad da jawaheer ba tayi karya.

Karewa gidan Kallo kawia take dan suna kwankwasawa Mai gadi ya bude musu suka shiga

Gidan ya hadu karshen haduwa ga wawakeken space a tsakar gidan banda inda akayi parking motoci wajen uku biyun na Jawaheer ne dayan Kuma na Amjad.

Gidan duplex ne tasan zasu iya kare rayuwarsu a gidan batare duk sun takura ba.

Bayan Sultana suka ringa bi dan ita tasan kan gidan

Zinatu kuwa da Amrah basu san gidan ba sai dai a hoto da suka gani.

Amrah ce kawai tayi sallama a tamfatsesen palon dan Zinatu mugun hade rai tayi dan tafi so Jawaheer tasan cewar itace ta haifi Amjad,ita kuwa sultana waje ta samawa kanta ta zauna dan Jawaheer dai a yanzu bata Isa korarta ba tunda tare suka zo da zinatu.

Ba kowa a kasan sai katon tv daya kusa cike bango guda da ke tayi.

Zinatu da Amrah Suma waje suka samu suka zauna.

Dan suna Jiyo motsi daga kitchen sun san ma Jawaheer ce dole ma zata fito ta gansu.

Muryar Amjad suka fara juyowa daga kitchen din Kafin ya fito da cokali a hannunsa ya daura apron a saman riga da wandon da ya sa yana “Habibty kina san Sauce din ko kin bar palon ne”?

Amjad yayi turus a lokacin da yayi tozali dasu Zinatu a madadin Jawaheer dake kwance akan dogon kujera tana Kallo,ko da wasa bai kawo zai kamu da matukar kaunar Jawaheer haka ba,sai da ya aureta.

Ji yake kamar kawai ya hadiyeta ya huta a babu yadda zai yi yake iya rabuwa da ita.

Shi yasa ko yaya indai Yana gida toh baya so Sam ta ringa aikin wahala daidai  da wanka dak’yar yake barinta tayi dan tare suke shiga.

Ko kadan baya san b’acin ranta

Wajen tara da rabi suka sauko kasa dan su hada breakfast shi kuwa ya dage akan tayi kwanciyar ta shi zai musu breakfast din

Inda Jawaheer tayi kwanciyar ta a doguwar kujera ta kunna tv tana Kallo

Shi kuma ya hau hada musu Abincin karyawan.

Sanin tana palon yasa shi fitowa dan ta nuna tana san sauce din albasa sai dai Yana fitowa sai yaga Zinatu a zaune har dasu sultana.

Cikin dan mamakin ganinsu da sassafe har da Amrah ba kuma su kira shi akan zasu zo ba mamakin Kuma ganin su gabad’aya yasa ya karasa wajen Zinatu da idonta ke neman fadowa saboda harararsa da take yana “Hajiya Kune a gidan namu da sassafe nan Allah yasa lafiya”

Ya zauna akan kujerar dake kallon na zinatun ya hade rai Yana amsa gaisuwar da su sultana ke masa har lokacin da cokali a hannunsa

Zinatu

Kuwa kamar an dora Mata bullo inci shidda haka ta ringa ji da taga Amjad ya fito daga kitchen da cokali a hannunsa,alamar ma baiwar Jawaheer ya zama sai yadda tayi dashi.

Kasa amsa gaisuwar da Amjad yayi mata tayi cikin tsananin b’acin rai ta fara magana tana “Lalacewar taka ta Kai har ace ka zama baiwar mace wai kana namiji ka shiga kitchen kana girki Amjad”?

“Matata ce fa Hajiya dan na tayata aiki ai Ina ga ba wani Abu bane ba yanzu dai Hajiya Allah yasa lafiya na ganku da sassafe haka har da su sultana”

“To ko zaka koremu ne”?

“Taya zan kore ku hajiya tambaya kawai nake dan ganin ki dasu sultana da sassafe haka ban da ma mun tashi yau da wuri da kila Muna bacci ma yasa nake tambaya Allah yasa lafiya”

“Amjad Kai yanzu so kake ka fifita matarka akanmu kenan,yanzu ace kasan halin da muke ciki akan talaucin da ya tunkarro mu,kasan kanwarka na kwance ba lafiya a matsayinka na namiji guda daya tal da muke dashi Amjad baka nuna ko damuwarka ba balle kasan halin da ake ciki kazo ka tare a gindin mace kamar baka da Yan uwa ka ringa bauta mata”

Amjad hade rai yayi dan a gaskiya ba zai soma d’aukar takura daga wajen Zinatu ba

Yana k’ok’arin magana takun takalmin Jawaheer da muryarta ya katse masa maganar da yake so yayi

“Hayatti baka gama bane ko sai dai nazo na taya ka”

Zinatu ido ta zubawa Jawaheer kawai tana Kallonta kamar ta shakota sanye take da wani doguwar riga ta atamfa da aka yiwa barin stones sai kyalli take.

Ta daura dankwalinta da ta turo Saman goshinta.

Ganin su Zinatu a zaune da Kuma kallon da Zinatun ke Mata kamar zata cako mata wuka yasa ta sakin murmurshi dan tasan wacce Zinatu shi yasa itama zata daura damarar zama da ita ta nuna mata itama sirikar zamani ce tunda dai ba zata ja girman ta ba

Amjad murmurshi kawai yake har da mik’ewa tsaye yana “Na gama mana Habibty bansan ma kin bar Palo ba na fito ne dan na tambaye ki sai naga su Hajiya sun zo”

Murmurshi Jawaheer ta saki tana “Ai kuwa na gansu da sassafen nan Hayatti karasa aikin ka ka kai mana sama bari mu gaisa da su”

Amjad fuskarta ya shafo Yana “Kinyi kyau Habibty”

Ganin ma Jawaheer yasa Yama manta su Zinatu na zaune yayi hanyar kitchen jikinsa na rawa

Zinatu ta saki sallati a daidai lokacin da Jawaheer ta zauna a Kujerar da Amjad ya tashi ta dora kafarta daya akan daya tana “Hajiya Sannun ku  da zuwa”

Zinatu kasa amsawa gaisuwar Jawaheer tayi ta zubawa Jawaheer ido kirjinta na bugu da yadda Amjad ke rawar jiki wajen bin umarninta

Jawaheer kuwa ganin bata amsa ba yasa ta Kalli Sultana da Amrah tana “Yan kanenna ai ya kamata ace kun gaisheni ko karku manta gidana kuke zo”

“Ba zasu gaishe ki ba Jawaheer ni kin gaisheni ne da zaki nemi su gaishe ki dama haka kike? Yanzu namijin nawa da ya a tilo kika asirce min shi kike Neman Mai dashi bawanki”?

Murmurshi Jawaheer ta saki bata yi magana ba saboda fitowar da Amjad yayi da faranti a hannunsa ya Haye sama Zinatu da jikinta ke rawa ta mik’e tsaye dan ta kasa ma jurewa taya Jawaheer zata ringa saka Amjad aiki kamar danta

Jawaheer sai da ta ga ya Haye sama itama ta mik’e tana “Yanzu dai Ina so nasan mai kuka zo nema da sassafen nan daga ke har yaranki “?

“Karyaki ta Sha karya jawaheer idan ma asirice min da kika Yi wallahi sai na karya koma me kika Yi”

“Ba fa kowa ke yin asiri ba Hajiya ni ba asirin da na yiwa danki balle na mallake shi dan idan har na masa asiri ai nasan koman daren dadewa sai ya karye ya dawo ya tsane ni bani da lokacin da zan bi wani boka kawai dai iya ladabi da biyayya zai saka na mallake mijina a tafin hannuna nidai Abu daya nake so na fada miki ba zan d’auki takura ba”

“Ni kike wa rashin kunya Jawaheer so kike kice Ina bin boka”?

“Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun wai Hajiya Dan Allah lafiya Mai ya faru ne wai kuka zo da sassafen nan”?

Amjad da ke saukowa yace fuskarsa a hade dan daga yadda yaga Zinatu na magana yasan takura Jawaheer za tayi shi kuwa ba zai d’auka ba gaskiya

Zinatu da idonta ya kada yayi jajjur ganin Amjad na mata magana a dan tsawwace yasa ta ce “Amjad zama muka zo yi a gidanan ko zaka Kore mu ne”?

” A wane gidan zaku zauna”?

Jawaheer tace tana zaro ido

Sultana kuwa da taga Zinatu ta kasa ma magana ga Amjad Shima ya zuba mata ido Yana kallonta yasa ta fara bashi labarin yadda aka kwace musu gida da dalilin daya suka zo.

Jawaheer kuwa ta ce “Tabdijam a gidanan zaku zauna Ina”

Daga haka  Jawaheer ta hau sama da saurinta

Amjad kuwa ya fara magana cikin daga murya Yana “Hajiya taya ma zaku zauna a gidana wanan ai zubar wa da Kai mutuncine dududu satina nawa da Aure za zaki dawo gidana daa zama har da su sultana.

Ai Abba ba zai rasa gidan da zaku zauna ba kuma nima zan iya kama muku haya gaskiya karki manta fa wanan gidan Jawaheer ne ma ba nawa ba taya zaki ma ce zaku zauna anan”

“Toh ka saketa ta koreka daga gidan nata idan har ba zamu zauna ba wallahi tallahi sai dai ka saketa ka taho mu tafi Kai yanzu so kake ka fifita matarka akan mu yanzu da Alhaji ba ya Raye ba zaka iya kula damu ba kenan”

Amjad bacin rai da yake ciki yasa bai ma iya magana ba ya Haye sama da sauri dan Habu kawai zai kira a waya dan  bazai tab’a yuwa ba.

Zinatu kuwa taja dogon tsaki tana idan ya Isa yazo ya fitar dasu

Sultana ta hau zugata wani daki dake kasa da dan girmansa sultana tace su shiga

Sai da suka shiga ciki Zinatu ta kwanta tana Idan har ta bar gidanan toh Amjad ya saki Jawaheer ne

Sultana kuwa da ke balain Jin yunwa tacewa Zinatu yunwa take ji Kuma tana tsoron fita Amjad ya zaneta

Zinatu kuwa ta mik’e tsaye tana suje kitchen din

Amrah kuwa da suna shiga dakin ta kwanta tayi lamo saboda yanzu sau biyu kenan tana jikewa da fitsari

Amjad

      Ka kwantar da hankalinka ina hanya zanzo gidan naka dan ni gidan makotan nan namu suka shiga sai da nace kar su zo gidanka Mahaifiyar ka ta isheni wallahi idan har ba zata zauna a gidan Sule da na samu yace mu zo mu zauna ba wallahi sai dai na bata takardarta ta tafi gidansu…..

Gwaggo

*Page 41*

      Gwaggo

Kallon Habu kawai take daya sadda Kansa kasa kamar zai kuka Yana kwarara musu bayanin abinda ya faru dashi

Da ita da Sule yazo ya tarar a dakinta Yana mata yankan farce,dan Sule da Hanne kamar su goyata haka suke yi dan Sule sosai yake kyautata Mata dan a fadarsa addu’ar da take yawan yi masa shi ya kawo shi wanan matakin da ko a mafarki akace yau zai ci karfin bukatunsa har wai ya ringa taimakawa mutane karyatawa zai yi.

A da ba’a san  dashi ma a dangi ba,bai ishi mutane Kallo ba,yadda suka taso da san zumunci yasa ko lokacin da bashi da komai ko Yaya ya samu sarari zai bi dangin babansu da dangin Gwaggo dan ya sada dai zumunci duk da bashi da komai.

Amma a dangin ma lokacin basu d’auke shi a mutum ba kowa lokacin Habu shine mutum sai su ma shigo garin su tafi daga baya sai dai yaji labarin anje gidan Habu.

Abin na matukar damun Gwaggo inda takan masa addu’a akan kar ya karaya in Sha Allah zai zama mutum watarana tunda a yanzu idan baka dashi Kai din ba mutum bane sai kana dashi.

Habu shi dangi ke ji dashi duk wani abu idan ya taso shi ake nema jiki na rawa

Sai gashi wai yau shi dangin nan ke tururruwar zuwa wajensa a yanzu bashi yake zuwa nemansu dan ya sada zumunci ba sune suke rawar jiki wajen zuwa wajensa ta waya kuwa haka zasu yi ta kiransa

Fuskar da bai basu ba yasa suka daina zagin Habu dan ba kunya suka hau ce masa ai Habun bashi da kirki ga rowa daga shi har matarsa Amma shi kam da Hanne sai dai Allah ya musu albarka dan basa gajiya da hidima da Yan uwa.

Wanda hakan ya zamewa Gwaggo abin alfahari har takan rasa yadda zata godewa Allah

(Allah kayi mana sutura ta arikzi Mai yalwa da albarka Ameen ya rabbi)

Sule kallon Habun kawai yake a lokacin da yake rokonsa zai zauna a gidansa kafin ya samu kudin kama musu haya idan kuma zai bashi rancen kudin da zai kama musu haya ya taimaka duk maganar da yake Kansa na kasa dan har ga Allah Yana Jin kunyar abinda yayi wa Sule a rayuwarsa.

Sule kuwa Gwaggo ya kala da fuskarta ke d’auke da murmurshi tana “Allah kenan Yau Habu Kaine da zuwa wajen Sule Neman taimako Allah buwayi gaggara misali Ashe Sule Yana da Rana,Ashe akwai ranar da zai zo Habu zaka taka kafarka kazo neman taimako a wajen sule da kake wa kallon kaskantace,Ashe akwai ranar da zaka zo neman taimako a wajen sule da ka wulakanta ka kulle shi akan matarka,Ashe akwai ranar da  Zaka zo neman taimako a wajen Sule da baka d’auke shi a bakin komai ba”

Habu kasa ya Kara yi da Kansa dan sai ya rasa ma bakin magana ko da ya saci kallon Sulen da bai so gwaggo ta tuna irin Abubuwan da ya masa ba a gabansa sai yaga shi ma waje daya ya kurawa ido hawaye na zubo masa.

Sule ba abinda yake tunawa sama da wulakancin da Habu ya masa akan kudin da bai taka kara ya karya ba dan ya siyi kwanun rufin gidansa Amma kememe yak’i,ya dage masa akan bashi da kudi,haka ya ringa zirga zirgan zuwa gidansa shi da Zinatu na wulakanta shi,ya tuna yadda ya zauna a gidan Habun da aka basu wani dan Karamin daki daga bakin gate a lokacin ban da ya kai zuciyarsa nesa da zuciyarsa na iya bugawa saboda wulakancin da Habu da Zinatu suka ringa musu.

Duk da ya yafe duk abinda Habun ya masa dan gani yake ko iya wanan niima da Allah ya masa a gaban Habun ya Isa ya sa ya yafe masa Amma ko Yaya ya tuna sai yaji ciwo tamkar a lokacin  Habun ya wulakanta shi har Yau kafarsa kan motsa masa da ciwo saboda azabar da Yan sanda suka gana Masa da Habun ya daure shi,akan zaman gidan Habun Zinatu ta masa Sharrin fyade.

Ya dade Yana addu’a akan Allah ya Ara masa tsawon Rai ya bashi ranar da shi ma Habu zai zo neman Abu a wajen sa sai gashi Allah ya amsa masa addu’ar sa.

“Halinka da sule ba daya bane ba,nasan halinsa ba zai duba duk abinda ka masa ba nasan zai taimaka ma Wanda banda Kai din ka gamu har da Sharrin mace duk da nasan har da halinka wallahi da na Hana sule  taimaka ma kaji irin ciwon da yaji a lokacin da ya zo neman taimako a wajen ka”

“Gwaggo dan Allah ki bar dawo da abinda ya wuce, Gwaggo dan Allah ki bar tunawa Sule abinda ya faru a baya ni kaina idan na tuna abinda na yiwa Sule wallahi Ina Jin kunya kila har da abinda na masa yasa Allah ya jarrabceni da karayar arizki,wai ace duk arizkina Gwaggo Yau na wayi gari bani da ko sisi balle wajen zama hakika nayi matukar nadamar abinda nayi wa Sule,sule dan Allah ka yafe min abinda nayi ma kaga tun ma ba’a je ko’ina ba yadda rayuwa ta juya dani”

Sule hawayen fuskarsa ya goge Yana “Ya wuce Allah ya yafe mana gabad’aya”

Gwaggo duk da halin da Habun ya shiga na a tausaya masa tsintar kanta tayi da Jin dadin Neman taimakon da ya zo yi wajen sule itama ta Dade tana addu’a akan Allah ya kawo ranar da Habu zai zo neman Abu a wajen sule sai gashi  kuwa Allah ya kawo ranar.

Tasan kila silar karayar arizkinsa zai Saka ya shiga hankalinsa.

Maganar da Sule ke yi yasa ta tatttara hankalin ta wajensu

“Akwai wajen da zaku iya zama Yaya Habu batare da kun takura ba amma Ina ganin gwara na baka mukullin wani gida da Ameera ta gina take Shirin zuba Yan haya Ina ga sai Kun Fi sakewa akan zaman ku a gidanan,bana so kuji a ranku ma ko gidana ne ba zaku iya sakewa ba,Amma duk inda ya kasance ku kadai ke zaune a gidan nasan sai Kun fi sakin jikinku akan nan”

“Aaa Sule ban yarda ka d’auki gidan Ameera ka bashi akan ya zauna ba,tunda har kace akwai wajen da za su iya zama a gidanan gwara su zauna anan din,dan nasan ba zaka tab’a wulakanta su ko ka nuna musu Kai Mai gidane a gidanka suke zaune”

Gwaggo tace cikin hade rai dan haka kawai taji tana so su zauna a gidan Sule tana so Habu da kansu su gane inda ake abin arziki.

“Gwaggo zan so ace su sake a duk inda zasu zauna bana so su kasa sakin jikinsu”

“Ban yarda ba Sule kaje ka nuna masa inda zasu zauna”

Sule sam ba haka yaso ba dan sai yake ganin kamar Su Habun zasu takura.

Amma ga mamakinsa sai yaji Habu na hakan ma ai yayi Allah ya Kara arziki.

Mikewa Sulen yayi suka fito waje.

Ya nufi part din da yake sabo dal ba komai a ciki sai robobin fenti

Dakuna uku ne da Palo daya kowane daki da bandaki a ciki sai kitchen da store.

Koda suka shiga part din Habu washe baki yayi ya ringa zabgawa Sule godiya kasan zuciyarsa kuwa tuna Karamin dakin da ya Kai sulen a shekarun baya kawai ya ringayi bai kawo sule zai iya bashi waje mai kyau har haka ba.

Sule  sai da ya nuna bacin ransa ya hakura da masa godiyar.

Yace yaje ya d’auko su Sultana kafin su karaso zai saka a share parrt din a goge.

Zinatu

      Ba kunya ta juyo indomie da ta dafa a faranti da dafaffen kwai ta fito suka shige daki.

Dan Jawaheer tayi kadan ta hanata zama a gidan,dole Amjad ya zaba a cikin biyu ko su zauna gidan ko Kuma ya saki Jawaheer da ta balain tsana take nadamar nema wa Amjad Auren ta.

Zarnin fitsarin Amrah daya cika dakin daga shigar su yasa sultana mik’ewa bayan taji ta koshi ta hau magana tana “Gaskiya Hajiya zama da Amrah a waje daya da akwai takura wallahi dan Allah yanzu haka zamu cigaba da rayuwa tana zabga wanan uban fitsari Mai zarni,wallahi duk mallamanki shegu ne Hajiya Ameera fa akace yayi wa aiki amma sai gashi aikin ya dawo kan Amrah”

Kukan da Amrah ta fashe dashi yasa Zinatu saurin matsawa kusa da Amrah tana “karki bi ta kan maganar Sultana anjima zanje wajen Wanda yamin aikin in Sha Allah zaki samu sauki kinji”

Zinatu tace duk hankalinta a tashe da taga yadda Amrah ke kuka tasan da ace aikin kan Sultana ya fada da ko numfashin kirki bata Isa yi ba.

Mik’ewa tayi bayan ta samu Amrah tayi shiru itama ta goge   nata hawayen dan sai da ta dan nutsu ta hau tuna tarin matsalolin dake gabanta

Ayuban da ta tuna da zai iya duro mata a kowane lokaci yasa ta mik’ewa duk da basu d’auko kaya ko daya ba saboda watso su da aka yi waje haka zata shirya taje gidan daya daga cikin kawayenta ta karbi kaya ta saka ta d’auki hanyar gidan Bokan dan tana bukatar ya Mata ayyuka da yawa duk da  jikinta ya fara sanyi da boka na teten dan duk aikin da ya mata da ta sa Rai da zasu ci duk kusan ya warware.

Yanzu wani iirn farin ruwa ke fitar Mata a jikinta Mai warin gaske kaikayin Kuma ya ragu.

Amjad

            Dak’yar ya samu ya shawo kan Jawaheer da ta tubure masa akan bata yarda Su Zinatu su zauna mata a gida ba,taya ma Zinatu dasu sultana zasu zo su tare mata a gida bayan ko sati biyu ba tayi ba

Ita kam Sam ba zata tab’a yarda su zauna ba Ina laifin a kama musu Haya.

Amjad rarrashinta ya ringa yi Yana Ta kwantar da hankalinta a yau zasu bar gidan ba zasu kwaana ba.

Sam bai ji Yana Jin haushin Jawaheer da ta nuna bata San zaman zinatun a gidan ba hasali ma sai yake balain Jin haushin Zinatun Yana ganin takura masa kawai take so tayi amma idan ba haka ba dan dai kudin da zai kama musu haya ba zai gaggare shi ba

Har a yanzu bai daina mamakin yadda akayi  arzikin da suke dashi ya kare a dare daya ba.

Motsin da yaji a kasan palon da karar Tv yasa shi saukowa kasa dan dakinsa ya shiga dan ya shirya ya tafi aiki abincin ma da ya dafa musu kasa ci yayi Jawaheer ma dak’yar ya samu ta ci kadan.

Kusan lokaci guda suka sauko kasa da jawaheer da ta bala’in Hade rai

Koda suka sauko sultana suka gani a kan 3 seater a kwance ta bararraje da remote a hannunta.

Ganin Amjad a fusace da jawaheer da ta mugun hade rai yasa ta mik’e tsaye.

Dan tana balain tsoron Amjad dan indai taje hannunsa tana balain dakuwa.

“Ke mai haka”?

“Yaya Amjad Kallo nake”

“Kashe min tv na yanzu nan”

Jawaheer tace tare da fusge remote din hannunta a daidai lokacin da Zinatu ta fito daga dakin fuskarta a balain hade.

Ta nufi wajen su Amjad din da zuwanta ta fara magana tana “Amjad kaji kunya wallahi baka ji dadin rayuwar ka ba Kai yanzu akan mace kake so ka wulakanta kanwarka,yanzu har zaka yarda mace ta rabaka da Yar uwarka,ko kasan zaka iya canza wanan fitsarariyar yarinya amma baka isa canza Sultana ba toh wallahi ba zan zuba ido Ina kallonka ka fifita matarka akan Yar uwarka ba,ba zan zuba ma ido naga ka wulakanta mu akan wanan yarinyar  ba Amjad na yarda zamu bar gidanan ka saki yarinya nan yanzu idan har na isa dakai ka saki yarinya nan yanzu”?

“Kinyi Asara Zinatu wallahi baki ji dadin rayuwarki ba,kisa ya saketa a yanzu kema sai ki shirya karbar naki sakin,dan wallahi Yana sakinta kema sai na sakeki…..

*KWKWR T KWKWR*

*Page 43*

Jiya nayi mistake bansa 42 ba na Kara Saka 41 so zamu tashi a 43

Zinatu

   Ido ta zubawa Habu dake tsaye a bakin k’ofa Yana hucci Sam bata ma san sadda ya shigo ba saboda idonta ya rufe sosai burinta kawai taga Amjad ya saki Jawaheer da take Jin dama tana da dama ta zare ranta

Ta kasa yarda Amjad zai iya fifita Jawaheer akan ita da take Mahaifiyar sa har Yana gwammatar bacin ranta akan nata,har akan sun zo gidan dan su zauna ya rufe ido yake san ya wulakanta ta.

Kallon Habu kawai take tana Jin wani daci daci a bakinta daga irin kallon da yake mata ta gane asirin da ta masa ya karye rugu rugu,bayan aikin da ta Sha wahala wajen yi akansa da silar ta mallake shi da sai yadda tayi dashi taje ta bawa Boka kanta ta jefa kanta a bala’in infection Mai warin gaske dan ko ita da take da jikinta wani zubin tana shako warin.

Ko wata daya cikakiya ba’ayi ba wai har asirin da ta masa ya karye.

Daga irin kallon da yake mata tasan zai iya sakin nata idan har ta tilastawa Amjad sakin Jawaheer.

Hawayen bakin ciki ne ya hau zubo mata ta d’auke kanta daga kallon Habun da jawaheer ta Isa gabansa ta zube tana gaishe shi ya hau amsawa tare da bata hakurin zuwan da suka yi.

Ya dakawa Sultana tsawa akan yanzu nan su fito su tafi taje ta kira Amrah yanzu Yana jiransu.

Sultana tayi dakin da suke da gudunta dan bata tab’a ganin Habu a cikin irin wanan b’acin ran ba.

Zinatu kuwa hawayen bakin ciki kawai ta cigaba da zubarwa tana kallon Amjad da yak’i kallonta.

Hasali ma idonsa na kan Jawaheer da ta mik’e ta Haye sama

Habu kuwa sai daya ga ta hau sama

Ya fara magana Yana “Sule ya bamu wajen zama a gidansa dan haka idan kinga dama kizo ki wuce mu tafi idan baki ga dama ba sai ki san nayi amma wallahi baki isa zama a gidan Amjad ba,dan ba zan manta ba lokacin da nace gwaggo tazo ta zauna a gidan mu haka kika ringa bakin ciki kina kunci kamar zaki Mutu toh yadda kike ganin kamar takuraki Gwaggo tazo yi a lokacin sa miki ido tazo yi haka itama Jawaheer din take ji dan haka zo ki wuce mu tafi”

“Wai Habu taya zamu koma gidan Sule da zama bayan duk abinda ya faru a baya wanan ai gwara mu zauna a ko’ina da dai zaman mu a gidan Sule.

So kake su wulakanta mu ko suyi tunanin Kai mu boys quarters wallahi ba zan iya ba”

“Ba inda nake dashi da zan zauna Zinatu tunda har kanina ya bani wajen zama wallahi can zani na zauna dan Sule da ace bashi da zuciyar yafiya wallahi ban kawo zai ma iya Kallona ba, hakika mace tagari tana taka rawar gani a rayuwar da namiji dan yau da ace ke din ta gari ce a lokacin da na so wulakanta kanina ke din mai hana ni ne sai gashi kece ma kan gaba wajen zugani akan na wulakanta sule da yau zai min rana,kika Saka na kulle Sule na biye miki na ringa wulakanta kanina, yau gashi duk wulakanci da na masa ya yafe min har ya bani wajen zama a gidansa Zinatu a yadda nake jina a wuyan nan kafin na kirga biyar ki zo ki fice daga gidan nan,dan na lura baki san abin kunya ba idan ma ba zaki bimu gidan Sulen ba sai ki tafi gidan ku ki zauna,a yanzu baki isa ki Kara rabani da wani nawa ba”

Zinatu kukan bakin ciki ta fashe dashi tana “Sai da na kawo tsufa a yanzu zaka ringa wulakantani kana min barazanar saki,taya kamar ni zanje na koma gidanmu da zama wa zan samu a gidan da zan zauna.

Har talaucin namu ya kai ace sai mun koma kasan kaninka mun zauna kamar wasu mara sa gata, nidai idan har wajen zama ne zai Saka mu koma gidan Sule wallahi zan Nemo mana kudin haya mu kama gida,kar ka manta Kai fa yayan sule ne ba kaninsa ba,ai ba girmanka bane ace ka koma kasan kaninka ka zauna.

“Sultana zo ku wuce mu tafi dan idan na biyewa wanan Babar taku zuciya zata debeni na saketa”

Sultana da sauri tayi waje tana rike da jaririyar Amrah

Amrah Kuma tana biye da ita a baya rigar jikinta a dan jike

Habu kuwa bai ko Kara kallon Zinatun dake ta rusa kukan bakin ciki ba yayi waje Amjad yabi bayansa.

Sai da suka je bakin gate Amjad ya fara magana Yana “Abba wallahi nima tunda nasan halin da ake ciki nake ta iya k’ok’arina wajen ganin na samu kudi amma bansamu ba banji dadin abinda ya faru ba”

“Amjad ni kaina na kasa samun kudin balle Kai arizki ai na Allah ne dama aro Allah ya bani ya kuma karbi abinsa Allah dai ya bani ikon cinye wanan jarrabawa tunda har suka karbe komai a yanzu zan na samun dan baccin dan ko baccin kirki bana iya yi saboda kudinsu a yanzu zan dage wajen nema dan bana so na dorawa Sule nauyin komai Ina ma Ina da damar da zan Maida hannun agogo baya wallahi da ban aikata abubuwa da yawa ba ciki kuwa har da wulakanta wayanda Basu dashi.

“Naji Dadi Abba da kasan Allah shi yake azurtawa ya kuma talauta,naji dadin tawakalin da kayi nace ta bakin Hajiyan baka ganin ya dace ace haya aka kama da zamanku a gidan Abba sule sai nake ganin kamar zaku takura ba zaku na sakewa wajen yin abubuwa ba.

Ina da kudin da zan iya kama muku Haya Abba

“Karka damu Amjad halina Dana sule ba daya bane ba,sule ba zai tab’a wulakanta mu ba Kai Mai bawa wani labari ne,a gidan Sulen zamu zauna batare da naji fargabar wai gidan wani nake zaune dan nasan sule dan uwana ne kaima kanka kasan halinsa.

Ina ga da wanan kudin hayan gwara ka bani na Kara nema naja jari dan ba zan iya zaman haka ba Neman kudi ba

“Hakane Abba,Abba sule ba zai tab’a wulakanta ku ba dama dan naga Hajiya ta damu ne shiyasa nake san a kama Hayan”

“Rabu da ita idan ba zata zauna ba sai ta nemi wajen zama wallahi banda su sultana da na bata takardarta ta kawai na huta dan a yanzu idan na tuna Abubuwan da ta saka na aikata ciki kuwa har da wulakanta Mahaifiyata wallahi sai naji kamar na hadata da bango nayita duka”

“Kayi hakuri Abba hakuri zaka cigaba da yi da Hajiya tun a baya ya kamata ace ka gane haka dan kai ne ya kamata ka ringa nusar da ita bamu da wanan ikon amma tunda a yanzu Allah yasa ka gane kaima  zaka taimaka wajen yi mata nasiha in Sha Allah zata gyara Abba ka daina zancen rabuwar nan”

“Shiga kace ta fito dan ba zan bar gidanan ba sai naga ta fito daga gidanan”

“Abba dan Allah ka rabu da ita nasan zata zo ka kyalleta.

Dak’yar Sule ya yarda dan dagewa yayi akan sai Amjad ya kira Zinatu sun tafi.

Amjad kuwa ya d’auko mukullin motarsa ya fitar da motarsa waje ya bawa Habu mukullin akan ya ringa hawa tunda motar Jawaheer biyu ne zai ringa hawa dayan

Ya bashi ATM dinsa akan ya Ciri kudi su danyi kananan Abubuwan kafin yazo gidan Abba Sulen

Da haka Habu yaja motar  ya tafi dasu sultana da bakin ciki yasa ta kifa Kanta ta hau kuka dan ji take kamar zuciyarta zata fashe da taga wai gidansu Ameera zasu je su rabe su zauna,kila a yanzu Hanne tayi tunanin wulakanta su.

Kamar tayi ta rusa ihuu haka ta ringa ji,taya ma zasu koma kasan su Ameera.

Koda suka iso gidan sai da Habu ya wanka Mata Marin da ya sa ta ganin taurari ta shiga gidan dan cokewa tayi a bakin k’ofa ta hau cewa Habu ita ya barta ta koma gidansu kawarta ta zauna ita gaskiya ba zata iya zama  a gidansu Ameera ba.

Amrah kuwa tana rungume da yarta ta shige gidan dan damuwar da take ciki kawai ma ya isheta.

Sule cikin gidan yasa suka shiga har da sultanar dake ta sharar hawaye

Suka je suka gaida gwaggo.

Hanne kuwa cikin sakin fuska ta tarbe su ta bawa Habu mukullin part din tace Sule ya fita.

Gwaggo kuwa sai kallon Habu take dake ta sisine Kai sai da suka je fita

Gwaggo tace

“Ina Zinatun take ko ba ita ba zata dawo gidan Sulen ta zauna ba tafi karfin zaman gidan Sulen”

“Gwaggo ban san mata ba gidan Amjad ta dage zata zauna na dai ce mata ba da yawuna ba Ina ga anjima tazo dan nace idan taga ba zata iya zama a gidan nan ba ta tafi gidansu”

Murmurshi Gwaggo tayi tana “Ai da kunya kamar ku a matsayin ku na masu kudi ku dawo kasan Sule da baku d’auke shi a bakin komai ba baku tab’a kawowa zai taka wanan matsayin ba ai da kunya kam ku dawo kasan da zama ni nagane mai take ji da kunya kam”

Habu bai ce komai ba dan har ga Allah baya san Wanan gorin da Gwaggo ke musu ba yadda zai yi ne.

Ganin Gwaggo ta kwanta yasa ya fice daga dakin

Koda ya Isa part din bayan yace wa su Amrah su biyo shi a baya.

Fes suka ga parrt din har da kujera sabo dal da labule sai kamshin turaren wuta ke tashi.

Tsakiyar palon Kuma kuloline da alama abinci aka ajiye musu.

Habu sai yaji kamar yayi kuka dan gani yake duk basu cancanci wanan tarb’ar ba.

Dakuna biyun duk katifa ne sababi,dazu sai yaga kamar Babu da alama ma Sulen siyo musu yayi dan da Leda duk a jiki

Dan karfin hali har da gado aka sa a daya dakin inda Habu ya yanke daukar wanan a matsayin dakinsa.

Sai da ya watsa ruwa ya Kara Maida kayan jikinsa yayi sallah laasar ya fito Palo yaci lafiyayyen abincin da Hanne ta ajiye musu.

Sai a yanzu yake Jinsa cikin nutsuwa dan saura kiris ya zare saboda harkar bankin nan

Allah ya rufa masa asiri da wayarsa a Aljihunsa a lokacin da suka watso su waje.

Hakane yasa ya Ciro wayarsa ya sake Kiran Amjad ya tambaye shi ko Zinatu ta tafi

Amjad yace masa ta tafi.

Daga haka Habu ya kashe wayarsa ya mik’e ya nufi wajen Gwaggo dan a yanzu zai k’ok’arin wajen ganin ya dan gyara kura kuransa ko ta kan Zinatu a yanzu ba zai na bi ba duk da baisani ba ko zata yarda ma ta dawo gidan Sulen ko ta dai gwammaci zuwa gidansu a wanan gabar kuwa ko rabuwa yayi da ita ma ba zai tab’a damuwa ba dan a yanzu sai dai kawai ya danne abinda yake ji a zuciyarsa amma tsanarta ma yake ji.

Zinatu

      Haka ta tsaya a palon tana Jiran dawowar Amjad da taji ya fita da mota waje.

Koda Amjad ya dawo cikin tsananin b’acin rai ta fara magana tana “Amjad yau ni mahaifiyarka ka wulakanta akan matarka ,Yau akan matarka ka murzawa idonka Toka kake Korar mu daga gidan ka

“Toh Wallahi Babu yawuna a yanzu a auren Kai da jawaheer na debe albarkar cikin auren,kasan dai sai ka bini zaka samu aljanna ko toh Ban yarda da Auren ka da jawaheer ba yarinya nan ba matuniyar arziki bace wai har tasan taje ta gaida Abbanku a tsugunne amma ni ko Kallo ban isheta ba,ita ta rabu da nata iyayen lafiya tasan darajar nata iyayen Kai baka San darajar naka ba ko toh wallahi babu yawuna a zaman da kake da ita “

Daga haka ta fito daga gidan batare da ta ma tsaya sauraran hakurin da Amjad ke bata ba

Koda ta fito gidan wata kawarta ta wuce hajiya hauwa.

Dan Sam bata ji zata iya komawa gidan Sule da zama ba

A wajen hajiya hauwa ta samu kudi da kaya ta canza bata zame ko’ina ba sai wajen boka Natete da sai da duhun Magriba ta Isa.

Bata samu ganinsa ba sai wajen goma

Inda da shigarta dan dakin dake ta bugawa ta rushe masa da uban kuka dan tama rasa da wane matsalar zata fara

Boka Natete kuwa kallonta kawai yake da idonsa daya da sha kwallin.

Sai da ta gama kukan ta fara da masa bayanin asirin da yayi wa Habu ya karye bayan akan mallake mata Habu ta bashi kanta gashi yanzu ruwa Mai wari na fitar Mata.

Ga asirin da yayi wa Ameera ya komawa Amrah tana ta zabga fitsari har da Rana.

Ga Gwaggo ta farfado ga talaucewar da suka yi.

Ita bata san ma ta inda zata fara ba ga Ayuba da ya Sako rayuwarta a gaba

Sai da ta gama zayyane masa tsaf.

Ya jawo kwaryarsa ya fara magana Yana “abinda yasa asirin da akayi wa mijinki ya karye da wuri ai yanzu Yana ibada sosai Kuma Mahaifiyar sa itama hana idonta bacci take wajen yi masa addu’a dan ta gano kin mallake mata da.

“Asiri Kuma da aka yiwa Ameera karyewa yayi aka maida kan Amrah abinda zai saka a karya asirin sai Kun nemo wanan layyar da kuka jefa a ruwa zan warware abinda nayi

Talaucewe kam kunyi shi sai dai a ringa taimaka muku a yanzu

Zancen Kuma dan baba Aure Babu fashi ranar asabar dinan Babu gudu Babu ja da baya.

Kuma a dubawar nan da nayi komawar da kuka yi gidan kanin mijinki toh mijinki fa zai sake Aure,zai auri wata babbar mace Zaki zama abin tausayi

Zinatu kafar boka Natete ta kamo ta ringa rusa ihu tana ya taimaka mata da wane zata ji,ita a yanzu babban burinta a Kara mallake mata Habu ayi mata aikin da Amrah zata warke.

Ayi mata aiki akan Gwaggo ta mutu,ayi mata aiki akan sule su talauce ayi aiki akan Yareema ya saketa.

Zata yi komai idan har zai mata aiki ta yarda Ayuba yazo ya auri Sultanar.

Murmurshi Boka Natete yayi yace duk zai Mata aikin amma sai ta kwana

Haka Zinatu ta kwana a wajen boka Natete duk da warin da boka Natete haka ta Kara Bude kafarta ya dirjeta San ransa har sai da taji numfashinta na Neman d’aukewa.

Kafin ya fita ya barta sai wajen bakwai na safe ya dawo wajenta dan Tama kasa tashi

Ya bata wani ruwa a buta akan ta wanke gabanta ba zata najin kaikaiyi ko wari ba.

Ya bata wani Abu akan ta matsa a can kasanta akan idan ta Isa gida tayi duk yadda za tayi Habu ya kwanta da ita idan har Habu ya sadu da ita

Ko wuta tace ya shiga sai ya shiga

Ya bata wani laya yace ta sawa Gwaggo a kasan pillow indai ta dora kanta akan pillow sai taji kamar ana buga mata guduma akai har sai ta mutu

Sule Kuma nan da Sati zai talauce zaa saki Ameera.

Amma fa Asabar suna tafe da Ayuba akan daurin auren shi da sultana.

Zinatu tabbatuwar Abubuwan da ya zayyana mata kawai take tana washe baki sai da tazo tafiya ta tuna Jawaheer tace Yayi mata aiki akan Jawaheer ta ringa warin jaba har sai Amjad ya saketa

Boka Natete yace kar ta damu ta samo wandon Jawaheer zai Yi aiki akan  wandon indai ta Saka sai ta ringa warin jaba.

Shap ta manta ma da zancen Amrah sai da tayi Nisa ta sake dawowa wajensa ta masa maganar Amrah akan ayi aiki akan mijin ya Maida ita tunda bata san ta inda zasu samo layyar ba

Boka Natete yace a samo gashin mijin Amrah zaiyi aiki akansa.

Da haka Zinatu ta baro wajen boka Natete zuciyarta fal da farin ciki.

Sai da ta tsaya a gidan Hajiya hauwa kawarta tayi wanka ta Kara canza kaya har da kwalliyar ta ta nufi gidan Sulen dan so take ta dan ja ra’ayin Habun a yau dai ya kwanta da ita ta fara dai da mallakar shi.

Tasan Idan ta mallake shi bai isa yin wani Aure ba.

Sosai ta danne zuciyata wajen danne zuciyata ta saki fuskarta ta  fara shiga wajen Hanne suka gaisa kafin ta karasa wajen Gwaggo tana addu’ar Allah yasa ma bata dakin ta saka mata layyar a kasan pillon.

Sai dai Koda ya shiga a zaune ta tarar da Gwaggo da farin glass a idonta

Da wani littafin addu’oi a hannunta gefenta Kuma Samha ce da Immi sai Habu dake zaune akan kujera

Cikin dan mamakin ganin immin da a yau sai taga ta mata kama da Habun ta zubawa Immi ido

Gwaggo kuwa ta gyara zaman glass dinta tana Kallonta fuskarta d’auke da murmurshi tana “Zinatu ai na d’auka kinfi karfin zuwa gidan Sule ki zauna Ashe zaki zo ya naga kina ta kallon Immin ne ko kinsanta ne”?

Murmurshi yake Zinatu ta saki ta karasa wajen ta ta zube a kasa ta hau gaisheta

Gwaggo ta amsa cikin sakin fuska

Zinatu kuwa ta dago ta Kalli Samha tana “Tare kuka zo da immin”?

“A dazu Abba ya d’auko mu daga gidan dan gwaggo ce tace a d’auko ni”

Shine Immi tace sai ta biyoni

Murmurshin yak’e Zinatu tayi batare da tace komai ba ta saci kallon Habun da ya mugun hade rai

Gwaggo kuwa sai murmushi take tana Yaba mata magana.

Daurewa tayi ta cigaba da zama sai da taga Samha ta mik’e tana bari ta d’auko Nurr Yar Amrah ta tashi ta bi Samhan da sauri dan bata san part din da aka basu su zauna ba.

Sai da suka Isa part din taga yayi kyau ba laifi ta tab’e baki ta shige dakin data ga gadon tana ai dadin abun Suma sun kusa talaucewa.

Haka tayi zaman dirshan ta ringa Jiran shigowar Habu dan yau ko fyadene sai ta masa.

Bai kuwa shigo part din ba sai wajen goma bata ma ga sultana ba dan Amrah tace   mata tun jiya daddare ta fice bata dawo ba har yanzu.

Koda Habun ya ganta cikin kwalliya har da sleeping Dress tana ta kamshi bai ko kalleta ba ya shige bandaki ya daura alwala ya fito Yana “Nan fa dakina ne daya Kuma nasu sultana

Wancan na gefen ne naki dan haka tashi ki tafi dakinki Dan Allah bana san damuwa

Zinatu mik’ewa tayi batare da tace masa komai ba ta iso inda yake tsaye ta ruko hanunsa tana “Haba Alhajina wai har yanzu fushi kake dani baka hakura ba dan Allah ka bar fushi dani haka kaji”

Habu fusge hannunsa yayi yana “Naji”

Daga haka ya Isa wajen da ya shimfida sallaya ya tadda sallah shafii da wtr da Gwaggo ce ta fada masa tarin ladan dake ciki dan iya sallah farilla kawai yake yi baya wani Kara nafila.

Sai da ya Kai Sha daya akan sallaya Yana Jan carbi Zinatu kuwa sai zabga hamma take tana kallonsa dan ta matsu ya zo suyi abinda zasu yi ya dawo tafin hannunta.

Koda Habun ya iddar da jallabbiyar jikinsa ya hau gadon ya kwanta Zinatu ta matsa  kusa dashi da sauri ta rungume shi

Habu kuwa da ya gane manufarta ya zuba mata ido Yana kallonta

Ganin kila tana da bukata sosai shi yasa take yawan nuna bukatarta yasa ya daure dan ya biya mata bukatar ta sai dai sai da ta zama ba komai a jikinta yaji wani irin wari na busowa daga gabanta kamar an Bud’e shadda.

*Page 44*

Zinatu mik’ewa tayi jikinta na wani irin rawa dan ita kanta ta shako warin bata kawo daga jikinta bane ba.

Dan dazun nan ma kafin Habun ya shigo ta shiga bandaki ta Kara gyara jikinta bata ko ji wari ba.

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun yanzu gabanki ne yake wanan warin Zinatu”?

Habu yace Yana Kara toshe hancinsa

Zinatu kuwa da zuwa yanzu ta jike da uban gumin tashin hankali ta rarumo zaninta dake gefe ta daura fadar tashin hankali da take ciki bata bakine.

Sanin bata san ma amsar ma da zata bawa Habun ba yasa ta nufi bandaki

Da zuwanta ta tsugguna ta zaro abinda ta tusa a gaban nata sai taga shi din ne yake balain doyi kamar zai d’auke Mata numfashi.

Bata san ya akayi ya fara wari haka ba dan kafin ta sa ba warin da yake kuma Boka Nateten yace dole ta bar shi a jikinta dan shine zaiyi aiki akan Habun.

Kukan bakin ciki ta fashe dashi dan da alama wahalar banza ta sha jiya a hannun Natete dan tasan  Habu  ba zai iya kusantar ta tana wanan uban warin da duk da ta cire Abin tana Jin warin na busowa daga gabanta.

Sabulu ta samu ta wanke abin duk da azabar da take ji a kasanta na tun jiya da sai da tayi ruwan zafi sosai ta dan samu sauki dan Natete kamar wani Doki haka yake.

Sabulu ta sa ta dan wanke gabanta shi ma sai da ta goge jikinta ta Kara shinshina abin ta ji baya warin kamar dazu.

Gabanta ma haka ta Kara Maida abin jikinta sai da ta kwashi mintuna dan taji ko zata ji warin taji Babu.

Ta fito daga bandakin dan ba zai yu ta Sha uban wahalar nan jiya bata samu biyan bukatar ta ba.

Bata ga Habu a dakin ba.

Hakane yasa ta bud’e k’ofar ta fita inda ta hango shi a kwance akan kujera har da lulluba da bargo.

Ji take kamar ta daure shi ta afka masa dan babban burinta a yanzu shine ta mallake shi ya dawo tafin hannunta.

Dan idan ba haka ba duk abinda yace dole tayi ciki kuwa kila har da cigaba da zaman gidan Sulen da take Allah Allah sati ya zagayo ta banka masa wuta idan aikin ma Nateten bai yi ba

Dan a yanzu ji take ba wayanda ta balain tsana take ganin sune ma suka musu asirin talaucewa sama da Su Sulen.

Duk da Hanne bata nuna Mata komai ba dazun gani take wani gani gani take mata da biyu ta jera zobunan gwala gwalan da suka ci uwar nata data rasa wai kamar Hanne ma.yanzu manyan atamfifo take sawa a gida bama fita unguwa ba.

Ga Gwaggo itama wai yanzu habaici take mata tana wani ji da Hanne dan kawai suna da kudi.

Bargon jikin Habun ta yaye.

Taga ya yamutsa fuska da alama bacci ne ma ya fara d’aukarsa.

Kafin ma ta zauna a gefensa ta dan hillace shi ya fara magana a dan tsawwace Yana “Zinatu Dan Allah ki rabu dani bacci zanyi,na kasa yarda wai wanan warin daga jikinki yake fitowa mai ya same ki haka Zinatu”?

“Tusa ne ya kwace min Alhaji ba daga gabana warin da kaji yake busowa ba a yanzu da na samu nayi Kashi shikenan dan Allah ka tashi mu shiga ciki Ina da tsananin bukata kasan ba mai sama min nutsuwar sai Kai”

“Zinatu ni Zaki cewa warin dana ji.yana fitowa daga jikinki tusa ne?Kinsan warin da naji kuwa?Taya warin nan zai zama tusa da ya gume ma dakin,har yanzu ma warin naji Yana busowa daga jikinki, Zinatu bansan mai ya sameki kike wanan warin ba ki gaggauta tafiya asibiti gobe a duba ki dan bai kamata ace ta samun nutsuwa kike ba dan wallahi ba warin tusa bane wanan daga gabanki warin nan ya ringa busowa”

“Wallahi tusa nayi Alhaji a yanzu ba wani wari muje kaji”

Habu hancinsa ya toshe da ta Kara matsowa kusa dashi tana k’ok’arin Jan hannunsa ya fusge hannunsa da hannu daya Yana “Zinatu wallahi wari naji kina Yi dan Allah ki rabu dani ki tafi daki karki sa numfashina ya d’auke innalillahi wa inna ilaihi rajiun Zinatu kinji warin da nake ji na tashi a jikinki kuwa”?

Zinatu mik’ewa tayi ta koma dakin Habun ta hau shinshina jikinta hankali a tashe amma ba warin da taji Yana tashi dan har sunkuyawa tayi ta dan Kai fuskarta jikinta bata ji warin komai ba.

Jakar da Hajiya hauwa ta bata ta d’auko wani body spray mai balain kamshi da ta d’auko dazu a gidan Hajiya hauwa ta hau feshe ko Ina na jikinta da turare har da cinyoyinta.

Dan ta k’arfi da yaji yau sai Habu ya kusance ta ko da ma dambe zasu yi

Sai dai ko da ta fito kafin ta karasa ma wajen Habun ya daka mata wani uban tsawan daya sa ta tsayawa cak Yana “Karki sake ki matso kusa dani wanan wane irin jarraba ne ko kin fara samun tab’in hankali ne taya kina buso irin wanan warin kike tunanin yin wani abu daban Zinatu idan Allah ya kaimu gobe ki tafi asibiti”

Daga haka Habu ya mik’e wajen biyun dare a lokacin ya fice daga palon

Zinatu ta zube a kasa ta rushe da uban kuka dan a yanzu sai tunanin ta ya fara bata wani muguntar Natete ya Mata take warin idan Habu zai kusance ta

Da rarrafe ta koma dakin ta tana Jin wani zazzabi na neman rufeta.

Ta kasa yarda duk durzar da Natete ya Mata jiya daya kusa sumar da ita duk akan ta mallaki Habu ya tashi a banza.

A yanzu ganin da take yiwa Habu tana dan yin wani Abu zai ma iya rabuwa da ita karin tashin hankalinta Auren da Natete yace mata zai Kara da tunanin ta ya bata ba mai Saka shi auren ma sama da Gwaggon da ta san ta tsaneta dan daga yadda ta ringa kwaba Mata magana dazu tasan a yanzu zata daura damara wajen wulakanta ta.

Dole tayi asubanci tafiya wajen Natete dan ba zata Sha wanan uban wahalar ba biyan bukata ba.

Shamsiya

      Gilashin fuskarta ta gyara fuskarta d’auke da murmurshi ta cigaba da magana tana “kice kallon Immi ta ringayi ko jikinta ya fara bata yar Yaya Habun ne”

“Ai sai da na jefa mata tambayar ko ta Santa ne sai bata bani amsa ba”

Nikam b’oye b’oyen nan ya isheni haka shamsiya lokacin da ya kamata ace ki fito haka yayi tunda abin yanzu ya zo da sauki suna zaune a cikin gidanan kin ga agaban kowa da kowa asirinta zai tonu matar nan ta tafka zalunci da yawa”

Gwaggo tace tare da b’allar goron da Shamsiyar ta kawo mata dan wajen goma na dare tazo gidan lokacin su Hanne sun kwanta bama kowa.

Duk tana waya da Gwaggo akan komai dan har zuwan su Zinatu gidan sai da ta sanar da Gwaggo.

Inda ta nunawa Gwaggo bata san tayi gaggawa so take ta fara da musu wasa da hankali

Inda da biyu Gwaggo tace Habu yaje ya dauko Samha ko da yaje ya tura Mai gadi

Sai Shamsiya tace Imtihal ta bi Samhan suje .

Koda suka fito Habu sai ya  tsinci Kansa da farin ciki da yaji Immi tace mamanta tace tabi Samha tayi kwana biyu.

Yana matukar san Immi da bai san dalilin daya sa yake jinta a ransa ba

Yakan dan bugi cikinta dan yaji wani abu game da mahaifinta da Barrister Aisha amma baya Jin komai daga wajen Immin.

Koda suka isa gidan

Hanne haka ta ringa bin Immi da ido dan taga kamaninta da shamsiya sosai inda ta kasa hakuri ta bi su dakin Gwaggon dan nan suka shige gabad’aya

Tana shiga dakin taga Immi da Samhan a zaune a gefen Gwaggon.

Habu Kuma na zaune akan kujera suna magana da Gwaggon

Shamsiya kuwa da zuwanta ta zauna a Kujerar dake kallon na Habun ta ruko hannun Immi ta hau tambayarta sunanta.

Immi ta mata gurgurarran hausarta da sunanta Immi

Gwaggo kuwa ta wayance dan sai take ganin kamar Hanne zata iya ganowa jinin shamsiya ce itama ta hau jefawa Habu tambayar a Ina ya samo immin

Anan Habu ya hau mata bayanin ai Yar makociyarsu ce barrister Aisha ya hau tunawa Hanne ita wacce ta bud’e taron bikin Amjad da addu’a wanan Barrister Aishan

Hanne ta gyada.kanta tana “Gwaggo wallahi sai naga yarinya nan tamin kama da shamsiya ki kalleta sosai Zaki ga kamaninsu itama barrister Aisha a ranar wallahi sai naji muryarta kamar na Shamsiya har Abban Ameera sai da na fadawa a ranar yace min gizo muryarta ke min”

“Kai Hanne ta Ina yarinya nan suke kama da shamsiya ai duk da na tsufa Ina da ido gaskiya bata kama da ita”

Habu kuwa ido ya kurawa Immin tunda yaji abinda Hanne tace kamanin Shamsiya yake gani a jikin immin sai a yanzu da Hanne ta fada ya fara tuna dalilin daya sa idan yaga immin sai yaga tana masa kama da wata wacce ya sani amma baisan wacce ba

“Gwaggo da gaske Hanne take wallahi Immin nan kama da shamsiya ko dai kuna da wata Yar uwa mai kama da shamsiya ne baku sani ba Hanne”?

“Kaima kaga kamanin nasu ko”?

Hanne tace tana cigaba da kallon Immin da ta rike hannunta gam dan har tsayin hanci da girar irin na Shamsiya ne har yatsun hannunta.

“Nagani Hanne a yanzu da kika fada wallahi naga kamaninta da margayiya”

“Lailai na yarda duk nafiku gani taya wai yarinya nan take kama da shamsiyar yo ko tana kama da shamsiya shikenan sai ya zama tana da Hadi da shamsiyar da ta dade rasuwa ita da cikin jikinta da imtihal,ai dama ana samun haka sai kaga wani ba dangin iya Babu na baba amma sai kaga kamaninsa da wani idonku ne kawai ma ni banga kamar da suke ba.

“Hakane Gwaggo kama ce kawai amma zan so naga Mahaifiyar ta wallahi har muryarta fa irin na Shamsiya ne”

“Ai barrister Aisha bata ganuwa  amma nima zan so na ganta dan gaskiya naga kamanin yarta da shamsiya”

“Ai sai kuyi tayi Kuma Samha jata ku fita waje kuyi wasan ku”

Cewar Gwaggo dan sai take ganin idan suka cigaba da kallon Immin zasu gane ma jinin shamsiya ce.

Da wani  Hirar suka dan bar zancen

Hanne ta tashi ta bar dakin ba jimawa su Immin suka dawo dakin inda mintuna a tsakani sai ga Zinatun.

“Karki damu Gwaggo so nake na kama Zinatu da kyau ta hanyar da ma zata tonawa kanta asiri da kanta batare da ta wahalar da mutane ba.

“Toh ba dai yanzu kin samu komai kike so ba mai ya rage Kuma?

Murmurshi Shamsiya tayi ta mik’e tsaye tana “Gwaggo gobe zan turo Yan biyu gidnan Ina so na fara dan dagawa Zinatu hankali.

Idonki ya zama Yana kan Yan biyun ke a gobe kice kin ga kamaninsu da Yaya Habun.

Akwai Shirin da nake Yi a gobe zan fara aiwatar wa Ina mai tabbatar miki sai kan Zinatu ya kusa zarewa”

Murmurshi Gwaggo ta sa tana “ki Aiko min jikokina da wuri Shamsiya dan na Matsu na gansu”

Da haka shamsiya tayi mata sallama ta fito da nikaf dinta batare da kowa ya ganta ba.

Zinatu.

       Baccin daya d’auketa wuraren asuba yasa bata tashi Bud’e idonta ba sai wajen Sha biyu na safe

Da balain sauri ta tashi ta fada bandaki ta daura alwalar da Sallah kawai take yi ba wai dan tama san mai take yi ba dan sallah kamar ma na dole take yinsa a haka ma ba wai cikakiyar sallah take yi ba.

Tana iddarwa ta shirya ta yafa mayafinta dan bata ma ji motsin kowa ba da alama Habun dai Tunda ya fice bai dawo ba

Koda ta fito a Palo ta tarar da Habu a tsakiyar kafet suna karyawa da Amrah da ta dora yarta a cinya da Samha.

Yadda Habun ya hade ransa yasa gabanta dan faduwa jiki a sanyaye ta Isa wajen kafet din ta zauna tana k’ok’arin magana Habun ya jefo mata tambaya da “Ina Sultana take”?

“Alhaji bansan inda take ba yanzu shiryawan nan da kaga nayi nemanta zan tafi yi gidan kawayenta kasan batare muka zo gidanan ba shekaranjiya ballantana nasan lokacin da ta fita”

“Zinatu wane irin tarbiya kika bawa yaran nan wai har ace sultana zata iya fita wani wajen taje ta kwana?Kuma jiya da kika dawo kinsan bata kwana a gidan ba tun ranar da Muka dawo din amma saboda rashin hankali ba ta Sultanar kike ba sai kike ta wani Abu daban Zinatu wallahi kin cuceni idan har yarinya nan ta d’auko min magana sai na baki mamaki dan Allah dubi irin tarbiyyar da yaran Sule suka samu  ke gabad’aya ma baki damu da yaran ki ba dubi halin da Amrah ke ciki bata yadda zaki kaita asibiti ta samu lafiya kike ba ta wani Abu daban kike”

Zinatu hawaye kawai ke zubar mata dan yadda Habun ya ringa mata fada abune da bata Saba dashi ba,ta Saba da itace ma mai masa fadan ya bata hakuri da rarrashi.

Bai ko Kara kallon fuskarta ba ya Kara rantse mata idan har sultana  ta d’auko masa magana zai bata mamaki.

Sai da taga yaje fita tace masa “Zanje gidajen kawayenta na dubota”

“Ban yarda ba ba inda zakije dan bake kike auren kanki ba da duk lokacin da kika ga dama Zaki fita ba tambayar izini ba komai wallahi ko bakin  gate  kika fita nidake ne a gidanan”

Idan Kun gama karyawa yanzu nan ke da yaran ku tafi wajen Gwaggo ku gaisheta umarni na bayar”

Daga haka habu ya sa Kansa ya fice.

Zinatu ta dora hannunta Akai tana ta shiga ukunta.

Dan wajen Natete take san zuwa gashi Habu ya hana ta fita

Wayar Amrah ta karba ta shige dakinta dan bata da waya ta kuma haddace lambar Nateten

Sai dai ko da ta kira wayarsa a kashe take kuka taci ta gode Allah da taga alamar  abubuwa a yanzu kwabe mata suke yi tama rasa da wane zata ji.

Abunda take gudu da tsanar na komawa kasan su Hanne gashi Yana Neman tabbata

Tunda yanzu idan suka je gaida gwaggon dole su gaida Hanne

Iya wanan bai Isa ba yanzu bata San inda sultana ta shiga ba.

Ganin Habu a wuya yake yasa ta daure ta wanke fuskarta ta fito

Ganin ba kowa a palon har dakunan jikinta ya bata sun tafi gaida gwaggon

Haka ta fito kamar zuciyarta zata fashe dan bakin ciki ta nufi part dinsu Hannen

Kafin ta karasa part din Hanne ta hango Habu a tsaye Sule da ya ibrahim.

Sai Ayuba da wasu Yan iska abokanansa su uku har da karnuka

Gabanta wani irin faduwa yayi ta tsaya cak.

A lokacin da taji Habu na “Zinatun ce tace ma zata baka Auren Sultanar Kuma a yau zaa daura muku Auren”?

“Kwarai kuwa ka kirata mana kaji”

Zinatu da sauri ta fara k’ok’arin komawa tana Jin kamar numfashinta zai d’auke saboda tashin hankali

Taji muryar Ayuba da k’arfi Yana “Sirikata ya kike k’ok’arin juyawa ne Yau fa ba gudu ba ja da baya sai an daura min Aure da sultana naga mijinki na wani magana kamar bai san zancen ba”

Sallati Zinatu kawai ta ringa ja a lokacin da Habu shi ma ya kwalla mata kira.

Karkarwar da jikinta keyi yasa ta zube a kasa Habu da zuciyarsa ke tafasa ya Kara daka mata tsawa akan tazo mana.

Gidan na juya mata ta mik’e ta nufi wajen su Habun tana bin bango.

A daidia lokacin da Gwaggo dasu Hanne har da Amrah suka fito Suma 

Gwaggo kuwa ta hau sakin murmurshi tana maganar zuci da “Shamsiya kin san kan ta tsiya iya wanan ma kawai ya Isa ya zautar da ita”

“Sirikata kamar yadda muka gama tsayar da magana dake Yau asabar ga alewa da sadaki na kawo na daurin Auren nida sultana kinsan nace miki idan har kika Kara kawo min wani magana wallahi sai na tona miki asiri,abin ma zai fimin Dadi ga mijinki a tsaye ga Yan uwansa ga kowa ma”

Zinatu kuwa hankali a tashe ta Isa wajen Ayuban jikinta na balain rawa ta hau magana kamar numfashinta zai d’auke

“Ayuba yau zaa daura ma Aure ai da sultana karka wani damu

Alhaji dama Ayuban nan sultana tace tana so akan shi ma take ta gudu dan ta ce idan har baa daura musu Aure dashi ba guduwa za tayi Alhaji dan Allah ka karbi sadakin a daura musu Auren kar yata ta shiga duniya”

Habu kallon Zinatu kawai yake kamar yadda Suma su sulen suka zuba mata ido cikin mamaki yarfa hannu da take tana dora hannu akai.

Habu kuwa da ya kasa magana tsabar mamaki ma yasa Sule karbe maganar da “Sultanar ce tace wanan Dan dabban take so Kuma akansa ta gudu Zinatu”?

“A wallahi tana balain San shi  dan Allah ku daura mata auren nan saboda ta dawo”

“Wai dama amaryar tawa guduwa tayi kan uban nan toh taya ma zaa duara auren bayan bansan inda amaryar tawa take ba.

Hajiya wai ko kin dauka wasa ne ya kawo ni.

Ina ga bari dai kawai na hakura da Auren nan na fadawa mijinki abinda muka aikata ko”

“Fadamin abinda kuka aikata Ina jinka”?

Habu yace kirjinsa na sama da kasa

Zinatu kuwa ta zube a kasa ta hau rusa ihuuuu kamar zata fasa musu dodon kunne

Ayuba kuwa ya zubawa Habu ido Yana tuna maganar da shamsiya ta masa “Barazana kawai za kayi tayi akan zaka tona asirin ba tonawar za kayi ba idan har kana so na wanke ka kenan ita kadai zan kulle”……..

Kuyi hakuri jiya wayata haukcewa tayi zan Kara yin posting zuwa can dare in Sha Allah ko ba yawa thank you an kusa dai gamawa ku huta na huta

*Page 45*

Ayuba d’auke idonsa yayi daga kan Habun daya matsu yaji Mai zai ce dan ba fadan zai yi ba satinsa daya kenan a wajen Shamsiya data sa aka kamo shi.

Ya dauka irin kamen da aka saba mi shi ne, shi  yasa bai ko wani damu ba dan yasan zai fito ba jimawa dan har an gaji da kama shi.

Sai dai a madadin da aka kama shi a Kai shi station kamar yadda aka Saba sai yaga an kai shi wani tamfatsesen gidan da ke kallon gidansu Zinatun.

Mamakine ya rufe shi da hakan yasa ya kasa magana har sai da suka kwashi mintuna a zaune a tamfatsesen palon Yana kalle kalle ba Abunda yake tunani sama da Mai ya aikata da za’a kawo shi wanan gidan

Fitowar Shamsiya da bai santa ba yasa ya zuba mata ido Yana kallonta har ta karaso ta zauna idonta na kansa.

Da harshen Turanci tace wa wayanda  su ka kamo shi su bata waje na Yan mintuna

Suka fita waje ya rage daga ita sai Ayuban dake ta zare ido Yana “Wai Mai nayi aka kawo ni nan ne”?

Murmurshi Shamsiya ta saki tana “Karka damu zaka san dalilin da ya sa nasa aka kamo ka”

Ayuba kallonta kawai yake kamar yadda take kallon shi ta cikin farin glass din dake sanye a idonta.

Ganin tak’i magana yasa Ayuba fara nazarin ko dai aiki zai Mata ne tunda wayanda suka kamo shi kamar ba Yan sanda bane bai gansu da kayan Yan sanda ba.

“Hajiya idan aiki zan miki ki fada min mana”

Murmurshi Shamsiya tayi ta gyara zamanta tana “Aiki zaka min irin Wanda kayi wa wata a shekarun baya Ina wanan gidan dake kallon gidana gidan nake so ka Kona min da mutanen ciki”

Ayuba ido ya zaro waje har gabansa na faduwa

Dan har gobe idan akwai abinda ya aikata da yake hana shi rashin nutsuwa da nadama bai wuce aikin da Zinatun ta bashi ba matar da ya kona gidanta da ciki da yarta ya tsaya masa a rai da hakan yasa ya sha alwashin yadda ba shi da nutsuwar zuciya haka zai hana Zinatu zaman lafiya

“Hajiya ba zan iya wanan Aikin ba sai dai ki nemi wani”

“Mai yasa ba zaka iya ba baka tab’a Kona gidan mutane bane da mutane a ciki”?

Shamsiya tace tana Cire glass din fuskarta saboda taga ko Ayuba zai ganeta duk da tasan da wuya ma ya santa dan ta Sha wahala sosai wajen samo shi.

Ayuba haka kawaii ya ji tsoron shamsiya ya rufe shi yadda ta kure shi da ido sai yake ganin kamar daga yadda take jefa masa tambaya tasan ya tab’a k’ona gidan Mai ciki da yarta

“Kayi shiru baka tab’a Kona gida mutane na ciki bane”?

“Hajiya Wacece ke dan Allah kinsan wani abu akaina ne”?

“Nice wacce ka konawa gida da yata a ciki”

Wani irin mik’ewa Ayuba yayi yaja da baya Yana kallon Shamsiya da ta dora kafarta daya akan daya ta jingina bayanta da kujera tana kallon Ayuban dake karkarwa Yana Nuno ta da hannu

“Kina nufin kece wacce Hajiya Zinatu tace na Kona gidanta da yarta a ciki”?

“Nice wacce aka baka kudi ka Kona ni da Yata”.

Ayuba ja da baya ya sake yi ya hau girgiza Kansa yana “Aaa bake bace ba wacce na Kona gidanta ta rasu da cikin jikinta da yarta ban tafi ba har sai da gidan ya zama toka ba Wanda ya fito daga gidan”

Ayuba ya karasa cikin rawar baki.

“Dawo ka zauna kwanana bai kare ba gani nan da raina”

Shamsiya tace tana nuna masa wajen da ya tashi.

Ayuba da kirjinsa ke bugu fiye da misali ya dawo ya zauna har lokacin bai yarda shamsiyar bace ba dan bai ga ta inda aka fito da ita ba

“Ka daina mamakin ganina a rayye rayuwa da mutuwa ta Allah ce akan kudin da bai taka kara ya karya ba aka baka akan ka Kona ni da cikin jikina da Yar yarinya da bata fi shekara biyu ba”

Ayuba jikinsa rawa kawai yake da zuwa yanzu ya yarda shamsiyar ce take magana akan gwiwarsa ya tsugunna ya hau bata hakuri Yana “ban Kara samun nutsuwa ba tunda na Kona gidanan da nake tunanin kina ciki,nayi nadamar karbar aikin da Hajiya Zinatu ta bani dan silar abinda na aikata na zama kangarare zuciyata ta bushe na fara aikata manyan laifuka Wanda sanadin haka yasa na dage nima ba zan barta ta samu nutsuwa ba sai ta bani Auren yarta”

“Bani labarin komai har zuwa neman yarta da kake yi”

Ayuba da sauri ya zauna Yana Jin nauyin da ya ke ji kirjinsa na tsawon lokacin da ya dauka ya kashe shamsiya da cikin jikinta da karamar  yarinya na raguwa a kirjinsa.

Ya hau bata labarin yadda Zinatu ta nemo shi ta bashi kudi da galan din fetur biyu akan ya Kona gidan,da yadda Zinatu ta shiga gidan da kanta ta d’auko Samha har zuwa kulle gidan da tayi ta waje ta dan Kona Samha saboda kar a zargi komai.

Har zuwa b’acewar da yayi daga garin dan kar a gano shi zuwa dawowar da yayi raywuar Zinatu ya dage akan sai ta bashi Auren Sultana  Yanzu haka ma asabar suka tsayar akan zai je a daura masa aure da sultana ko ya tona mata asiri

Murmurshi Shamsiya ta saki dan duk ta riga da ta sani tabbacin take so dadin daddawa ma Ashe Ayuba ya fara mata barazanar tona mata asiri idan bata bashi Auren sultana da tasan Habu dai a cikin hayyacinsa dai ba zai tab’a bawa Ayuba auren sultana ba sai Zinatu ta fada masa dalilin da yasa take so ta aurawa Ayuba sultana.

Ayuba kuwa hakuri ya cigaba da bata akan yayi nadamar ma karbar aikin

Shamsiya kuwa bata ce masa komai ba ta mik’e tayi waje ta kira wayanda suka kamo shi akan su tafi dashi su cigaba da tsare shi awajensu.

Sai da Ayuba ya samu kwana shidda a hannunsu duk hankalinsa a tashe Yana tunanin kila Shamsiya kulle shi za tayi.

A  jiya ta sa aka kara Kai shi gidan inda take sanar masa aikin da zai mata idan har Yana so ta yafe masa batare da ta kulle shi ba.

Ya ringa zuwa Yana dagawa Zinatu hankali Yana mata barazana dan so take ma kafin ta bayyana kanta Zinatun ta tonawa kanta asiri da kanta.

   “Na fada ko kuwa zaki Nemo min amaryata?

Zinatu da numfashinta ya fara k’ok’arin barin jikinta saboda tashin hankali tona mata asiri da Ayuba ke san yi agaban Habu da Yan uwansa ciki kuwa har da Gwaggo

Ta mik’e cikin wani irin rawar jiki da baki tana “Zan Nemo Maka Sultana Ayuba a yau zan Nemo Maka ita kaje kawai”

“Idan har na dawo gobe bata dawo ba a gaskiya zan tona kawai”

Ayuba yace Yana k’ok’arin juyawa piton da yayi yasa abokanan sa juyawa da karnukan da suka zo dashi

Habu kuwa ya sha gaban Ayuba cikin zafin nama Yana “Ni mahaifin Sultana da hankalina ba zan tab’a baka yata ba kasan dai ba Wanda yake da Ikon aurar da ita sama dani toh dan haka a yanzu ka gaggauta fadamin abinda kuka aikata Kai da ita dan idan har Dan rufin asirinta zata baka Auren Sultana wallahi ba zan tab’a baka Aurenta ba.

“Alhaji wallahi ba wani Abu da muka aikata da zai tona yanayinsa zaka duba ai Ina biye mi shi ne kawai amma ba daidai yake ba”

“Idan kika Kara magana Zinatu wallahi zan baki mamaki Ina jinka mai kuka aikata”?

Habu yace tare da cakumo wuyan rigar Ayuban dan yazo wuya duk da bai san wane sirri Ayuban ke san tonawa ba yasan gaggarumin Abu Zinatu ta aikata daga yadda hankalinta ya tashi har wai yadda yasan tana ji da sultana zata iya bawa Ayuba aurenta akan dai ya tona mata asiri

Ayuba murmurshi ya saki Yana “gaka ga ta nan ka tambayeta zata fada maka da bakinta abinda ta aikata,ni yanzu Ina fada ai kamar nayi wa kaina mugunta ne tunda Ina san yarka ko Kai kake da Ikon bani ita koma itace ba abinda ya shafeni nidai zan zo a daura mana Aure Ina nan zan dawo gobe”

Ya fusge rigarsa daga rukon da Habun ya masa

Habu kuwa ya Kara Kai hannu zai damko shi, Gwaggo ta dakatar dashi tana “ka rabu dashi ai bashi ya kamata ya fada ma abinda ta aikata ba ita ya kamata ka tambaya mai ta aikata haka da har take so ta d’auki yarta ta bawa dan dabba dan rufin asirin ta”

“Wallahi Gwaggo ba abinda na aikata ki yarda dani shaye shayensa kawai yayi yazo Yana maganganu”

Zinatu tace cikin tsananin tashin hankali dan ta gama sadakarwa a yau asirinta zai tonu.

Habu ido ya zuba mata kawai Yana kallonta.

Ya ibrahim kuwa ya girgiza kai Yana Allah ya kyauta ya nufi part dinsu dan duk yanzu a gidan Sulen suke Dan bature ne kawai baya gidan.

Sule Shima ciki ya koma Yana sakin murmurshi dan yasan duk nisan jifa kasa zai dawo karshen alewa kuwa kasa.

Iya Gwaggo ke tsaye a bakin k’ofa sai Habu da Zinatu da tayi zaman dirshan a kasa

“Mai kika aikata haka Zinatu,wane irin abu kike b’oyewa da baki san a sani akan a sani gwara ki dauki yarki ki bawa dan dabba”?

“Wallahi ba abinda na aikata Gwaggo ki yarda dani,sultana ce duk ta jefani a cikin wanan masifar dan itace ta kawo shi tace tana so to Yana da dan tabin hankali idan Yana abinsa biye mi shi ake yi idan ba haka ba sai haukansa ya motsa”

Wani irin ashar Habu ya lailayo ya maka mata Ya fara k’ok’arin yin kan dan ji yake kawai Shaketa kawai zai yi har sai ta fadi abinda ta aikata da bakinta

Gwaggo kuwa ta Kara dakatar dashi tana ya rabu da ita ai idan ma wani Abu ta aikata take ta b’oyewa dole dai watarana asirinta ya Tonu dan ba Mai bawa Ayuba auren sultana idan har Ayuban yaga haka dole shi ma ya tona mata  asirin.

Daga haka Gwaggo ta koma ciki

Ta barsu anan Zinatu kuwa sai rusa kuka take Habu na rantsuwa idan har ya gano abinda ta aikata wallahi sai ya bata mamaki.

Daga haka shi ma yayi hanyar wajen Yana Jin Kansa na daukar dumi da abhbuwan dake faruwa dashi,a yanzu ya fara ganewa Zinatu akwai abubuwan da ta aikata munana da take b’oyewa.

Duk sai a yanzu yake ganin kamar baa cikin hayyacinsa ya bar Zinatu ta ringa abinda ta ga dama ba ciki kuwa har da rashin bawa yayansa tarbiya da silar haka yasa wai Sultana ta iya barin gidan batare da sun san inda take ba.

A dakalin k’ofar gidan da ya zauna Yana ta Saka da warwara dan bai san ma abinda ya dace yayi ba akan Zinatu da yake Jin tsanarta a zuciyarsa.

Wajen awa daya Yana zaune a k’ofar gidan yayi zurfi a tunanin matsalolin da yake ciki bayan na talaucewar da yayi,ga larurar Amrah da bai san dalilin fitsarinta ba,ga Sultana da bai san ma inda take ba.

Muryar Zinatu da yaji kasa kasa a ta gefensa ya katse masa tunanin da yake.

Koda ya juya wani irin wari yaji ya buso daga jikinta da ya tilasta masa toshe hancinsa

Zinatu kuwa da idonta ya kada yayi jajjur saboda kukan da ta Sha da ta koma daki ta zaro ido tana kallon Habun da ya mik’e Yana “Zinatu wai warin Mai kike yi haka ne tun jiya”?

“Wari Kuma Alhaji”?

Zinatu tace cikin faduwar gaba ta hau shinshinar jikinta taji ba wani warin da take hasali kamshin turaren da ta fesa take yi

Yadda taga Habu yaja da baya  ya dage wajen toshe hancinsa da hannu yasa ta fashe da kuka tana “Alhaji yanzu salon da ka bullo dashi kenan wajen wulakantani,Mai na Maka haka da zafi da zaka ringa cewa Ina wari idan kusa da Kai ne baka so nazo ai gwara ka fadamin akan me zaka ringa cewa Ina wari,mai yasa ba Wanda yake Jin  Ina warin sai Kai” ?

“Zinatu kije ki binciki kanki wari kike yi tun jiya nake Jin Wanan warin na busowa a jikinki”

Zinatu jikinta ta Kara shinshinawa cikin tashin hankali amma bata ji warin da take ba

Ganin idan ta dage da surutai ba zata samu fita zuwa wajen Nateten da take Jin kamar tayi tsuntsu ta ganta a wajensa ba yasa tace “Ina so naje asibti a dubani bana Jin dadi”

“Ba inda zaki je Zinatu ni yanzu Sam ban yarda dake ba,ki koma ciki,kuma ba zuwa za kiyi ki kwanta ba wajen Hanne Zaki shiga ki taya ta aiki dan ita ba baiwar mu bace da zamu mik’e.kafa tayi ta dafa abinci tana bamu”

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Alhaji yanzu Hanne zanje nayi wa aiki sai kace wata Yar aiki karka manta fa Kai yayan mijinta ne yanzu saboda kawai Muna zaune a gidansu sai naje na zama Yar aikinta”?

“Toh ai ita ba Yar aikinmu bace ba,haka kawai ba zamu zauna mu zuba ido ta ringa komai ba dan haka umarni na baki yanzu ki tafi bangaren Hannen idan kinga ba zaki iya ba toh sai naji”

Zinatu ido kawai ta zuba masa tana kallonsa kamar kirjinta zai fado saboda tsananin bakin ciki Kuma har lokacin hannunsa na bisa hancinsa.

Juyawa tayi ta koma ciki sai da ta je part dinsu ta d’auki wayar Amrah ta sake gwada wayar Nateten dan ji take kamar zuciyarta za tayi bindiga babban tashin hankalinta a yanzu rashin mallake Habu dake takata yadda ransa ke so har Yana hana ta fita,idan har bata mallake shi ba dole asirinta ya tonu dan bata ga ta inda zai tab’a yarda ya aurawa Ayuba sultana ba,tasan Kuma idan har hakan ta kasance dole Ayuba ya tona mata asiri.

Kamar zata yi tsalle ta shiga cikin wayar haka taji a lokacin da taji wayar Nateten ya shiga

Koda ya daga da sauri ta fara magana tana “Aikin da kayi akan Mijina baiyi ba dan abin wari ya sani ya kasa kusantata asirina Yana dab da tonuwa Natete ka taimaka min dan Yau saura kiris Ayuba ya tona min asiri Ina so nazo Yanzu ma ya hana ni yanzu Abu kadan sai yace zai sakeni ka taimaka.min Natete yanzu ya zanyi da wanan warin da nake ya zaayi na Samu ya kusanceni”?

Natete tumbinsa ya ringa shafawa Yana sakin murmurshin mugunta tuna ganimar da ya kwasa a wajenta yasa shi lashe lebbensa  Dan shi ya sa mata warin dan baya so ma mijinta yanzu ya ringa kusantar ta yafi so shi kadai ya ringa morarta “Ai na fada Miki yanzu mallake mijinki sai anyi gaggarumin aiki yanzu abinda za kiyi k’ok’ari kizo ki kwana zaa  mi shi aiki Mai balain zafi”

“Taya zan zo na kwana bayan ba biyan bukata”?

“Kizo a sace ni na tabbatar miki zanyi aiki akansa a yau zai dawo tafin hannunki”

Zinatu kuwa toh kawai tace masa ta kashe wayarta

Dan ko da tsakar dare ne sai taje wajensa ba yadda zata zauna gobe Ayuba yazo ya tona mata asiri.

Daga haka ta fito ta nufi wajen part dinsu  Hannen .

Koda ta isa a Palo ta tarar da Hannen da wata Hajiya suwaiba da ta so suyi kawance da ita amma firr  tak’i matar masu kudine sosai ganinta da Hanne yasa taji kamar zuciyarta zata buga.

D’auke kanta tayi ta nufi dakin Gwaggon

Ga mamakinta sai taga Ameera a zaune tayi jajur da ita cikin shigar wani bubu sai walwali take.

Tana gefen gwaggo a zaune bata ma san lokacin da Ameeran tazo ba

Amrah Kuma tana takure a gefe kamar mabaraciya, Zinatu kamar ta saki ihu haka ta ringa ji ta kasa yarda wai Ameeran da ta raina yau itace a sama ta zama Abar Kallo Amrah yarta Kuma na daga kasa kamar Yar aiki.

Waje ta samu ta zauna a gefe ta danne zuciyata wajen gaida gwaggo, Gwaggo ta amsa cikin sakin fuska dan a yanzu dariya ma Zinatun ke bata duk tabi ta firgice.

Ameera kuwa ciki ciki ta gaisheta ta d’auke kanta

Zinatu kuwa ta zabga Mata harara tayi kamar bata ji ba sai tsinewa Ameera take a zuciyarta tana Allah yasa tayi hatsari a hanyarta ta komawa gida.

Gwaggo hirarsu suka cigaba da yi da Ameera Zinatu kuwa sai girgiza kafa take kamar zata fashe dan bakin ciki.

Shigowar Habu da Sule har da Hanne yasa suka Kalli k’ofar gabad’aya

Dan da biyu Gwaggo tace a kirasu dan tana so ya zama suna dakin Yan biyun zasu shigo.

Ameera har kasa ta zub’e ta hau gaishe da Habun da ke washe baki da ganinta.

Hira suka cigaba da yi gabad’aya har su Ameera zasu bar dakin Gwaggo ta Hana su.

Dan jijjigar da Amrah ta fara yi yasa suka.maida hankalinsu gabad’aya kanta fitsarin da ya hau gangarowa daga jikinta Mai yawa da zarni yasa su Sule sakin sallati dan basu tab’a gani ba.

Zinatu kuwa kanta tayi kasa dashi hawaye na cicciko mata a ido kamar yadda Amrah hawaye ya wanke mata fuska

Habu kuwa sallati kawai ya ringa yi ciki ciki dan zuwa yanzu hankalinsa ya Kara tashi dan abin Amrah kamar gaba.yake Yi.

Gwaggo ce tayi karfin halin tambayar Amrah lafiya ta saki fitsari tana zaune.

Ameera zarnin kawai da ta shaka yasa ta gane asirin da suka mata da tace a Maida musu kayansu kan Amrah ya koma ba sultana da itace ta shafa.mata Abu a ciki.

Amrah kuka kawai take ta kasa magana.

Sai Habu ne ya bawa Gwaggo labari cikin rawar murya ya karashe da ya rasa wane irin Abu ke damun Amrah dole ya Kara Mai da ita asibiti.

“Abba ba sai ka wahalar da kanka zuwa asibti ba asirin da aka min akan na ringa fitsarin kwance shi nasa aka min addu’a aka karya asirin nace a maidawa duk Wanda yamin asirin fitsarin kwancen.

Amrah da sauri ta dira gaban Ameera ta tsugunna a gabanta tana “Wallahi bani na Miki asirin fitsarin kwance ba su sultana ne suka miki duk da bana shiri dake ba zan iya cutar dake ba dan Allah kisa Wanda ya dawo da wanan asirin kaaina ya karya shi ko ya mayar kan wayanda suka yi”…..

*Page 46*

       “Amrah kanki daya kuwa su wane sultana ne suka mata asirin fitsarin kwance ya dawo kanki ko kema kin fara samun tab’in hankali ne”?

Zinatu tace cikin dakiya duk da ji take kamar kirjinta ya fado saboda tsananin tsoron tona mata asiri da Amrah ke Shirin yi

Amrah kuwa bata ko kalli Zinatu ba ta cigaba da bawa Ameera hakuri.

Su Hanne da maganar da Ameeran tayi yayi matukar daure musu Kai suka zuba mata ido suna kallonta take Sule da Hanne suka gane inda maganar Ameeran ya dosa, Gwaggo ce kawai da Habu basu gane kan zancen ba

Inda Habu da Kansa ya gama daurewa da maganar da Amrah tayi yace “Amrah Bangane Maganar da kika yi ba Yanzu Ameera ki fahimtar dani su waye suka miki asirin  fitsarin kwance?

Gwaggo murmurshi ta saki dan ta fahimci komai daga fitar da taga Hanne da Sule suka Yi daga dakin.

ta fara magana tana “Hmm dadina fa da sharri shi dan aikene a rayuwa duk Wanda yace tukunyar wani ba zai tafasa ba nashi ba zai tab’a tafasa ba Ameera tun tana yarinya ba irin sharri da baa bita dashi ba amma da yake ita din kainuwa ce dasheen Allah ba Wanda ya Isa yaga bayanta.

Ameera da baki yi haka ba ai ko iya niimar da Allah ya miki ya d’aukaka ki akan makiyanki yaci ace kin yafe batare da kin maida Sharrin da aka miki ba dan haka idan kina da hali Wanda ya karya asirin kice ya sake karya asirin kinji Yar albarka”

Ameera kanta ta gyada Amrah kuwa ta hau mata godiya .

Habu kuwa da ya fara daukar haske daga maganar da gwaggo tayi dan Zinatu gumi kawai take tana wurga idanu yace “Ameera Waye ya miki Asiri”?

“Ka bar maganar nan Habu ko ka sani ai ba abinda zaka iya yi akai yanzu ba ga Ameera kana Kallo garau take ba ba abinda za’a iya mata ai sai abinda Allah ya hukunta zai sameta Allah ya kyauta ya shirya”

“Dan Allah gwaggo ki barta ta fadamin taya za’a ayi ta tafiya haka a cikin duhu gwara idan abinda zan iya d’aukar Mataki ne akai na d’auka”

Murmurshi Gwaggo tayi tana “kana da gajen hakuri Habu bani nace a bar maganar ba ka bar shin kawai”

Habu na k’ok’arin magana Aryan da Abyan suka shigo bayansu Kuma su Hanne ne har da sule da ya ibrahim da tsananin kamanin Yaran da suka gani da Habun yasa suka Kasa hakuri suka biyosu driver ne ya sauke su ya wuce.

Basu ma san daga Ina yaran suke ba

Da harshen turanci suka gaishe su suka tambaye su inda Gwaggo take.

Gwaggo murmurshi ta saki tana kallon Aryan da Abyan da suka yi shigar su iri daya ba inda suka baro Habu ta mik’a musu hannu tana “Oyoyo Yan biyuna sunanun ku da zuwa”

Wajen Gwaggon suka nufa dan sun ganeta ta hoton da shamsiya ta nuna musu ta kuma fada musu kakarsu ce.

Zinatu kuwa tunda suka shigo ta daskare akan kujera kirjin ta na bugu da ganin Yan biyun da taga kamar Habun aka zuke,kamar wacce ta samu tabin hankali haka ta ringa juya kanta ta Kalli Habu ta Kalli Yaran.

Habu kuwa hannunsa ya dafe kirjinsa dashi dan tunda Yan biyun suka shigo yaji bugun kirjinsa ya sauya kallonsu kawai yake Yana Jin tsigar jikinsa na tashi.

Da hannu biyu Gwaggo ta rungume su.

Hanne da ta kasa hakuri tace “Gwaggo yaran waye wanan masu balain kama da Yaya Habu”?

“Jikokina ne Hanne”

Gwaggo tace cikin tsananin farin ciki ganin Yan biyun da Zinatu taso kashewa.

“Jikokinki kuma Gwaggo Bangane jikokin ki ba”

Zinatu ta tsinci kanta da fada batare da ta shiryawa haka ba dan har mik’ewa tayi tsaye kanta na daukar wani irin zafi dan ta kasa hada tunanin ta waje daya.

Ganin Yan biyun yau kusa da kusa da Habu a waje daya yasa taji hankalinta Yayi bala’in tashi dan sai take ganin kamar yaran Habu ne take ta fara tunanin ko dai Aure Habun yayi a b’oye bata sani ba

Habu kasa hakuri yayi ya ruko hannun Aryan da Abyan ya tsugunna a gabansu ya cigaba da kallonsu.

Sule da ya ibrahim kuwa da har lokacin mamaki bai sake su  da Gwaggo tace jikokinta bane Suma suka hada baki wajen jefawa Gwaggo tambayar taya Yan biyun suka zama jikokinta yaran waye

Murmurshi Gwaggo ta sake saki ta Kalli Zinatu da ta kurawa Yan biyun da habu ya rike gam Yana kallonsu kirjinta kamar ya fado tace

“Jikokina ne dai kamar yadda kuka ji na fada muku”

“Gwaggo dan Allah ki bar wahalar da mu ki fada mana yaran waye dan Yaran nan kamanin su yayi yawa da Habu tamkar Habun ne ya haife su”

“Toh ai baku yi karya ba yaran Habun ne shi yasa nace muku jikokina ne”

“Yaran Habu Kuma tayaya suka zama yaran Habu dama Habu yana da wata matar ne bayan ni”?

Zinatu tace cikin rawar baki tana Tunanin  kila Barrister Aisha ce ma matar da Habun ya aura bata sani ba”

Habu mik’ewa yayi ya zubawa Gwaggo ido kamar yadda duk wayanda suke dakin suka maida hankalin su kan Gwaggon suna Jiran Karin bayani daga bakinta.

Zinatu kuwa da bata ma san yadda aka yi ta Isa gaban Habun da Yan biyun  ta fara magana tana “Habu yaran nan yayan waye dan Gwaggo tace yaran ka ne Aure kayi a b’oye bansani ba ko ya akayi yaran nan suka zama yayanka dan a iya sanina yaran nan yayan barrister Aisha ne  makociyar mu aurenta kayi ko zaman daduro kuka yi ta haifo ma yaran nan kamin bayani yanzu dan na kasa gane maganar da gwaggo take”

“Gwaggo dan Allah yaran waye wanan kin bar mu a duhu a iya Sanin mu tunda shamsiya ta rasu bai sake wani auren ba, taya yaran nan suka zama yaran Habun?

Ya Ibrahim yace cikin zakuwar San yaji yaran waye dan duk kansu ya kulle sun kasa ganewa.

Gwaggo murmurshi ta saki da taga yadda jikin Zinatu ke rawa  taso ace a yau ayita ta Kare,taso ace Shamsiya ace da Yan biyun tazo amma ta dage ba yanzu zata bayyana ba ta kusa.

 yadda taga duk sun matsu suji daga bakinta yasa tace

“Jikokin Maman Kamilu ne wasa nake muku kawai”

“Gwaggo yaran nan jinina ne ba da wasa kike ba Gwaggo taya yaran nan zasu zama jikokin Maman Kamilu bayan ga kamanina dasu Gwaggo ya nake Ji a jikina kamar yaran shamsiya ne”?

“Wacce shamsiyar”?

Zinatu ta zaro ido cikin azababen faduwar gaban da ya hade Mata da murdewar ciki

“Taya zasu zama yaran shamsiya bayan shamsiya mutuwa tayi da cikin jikinta”?

Gwaggo tace cikin dan mamakin yadda Habu ke Shirin ganowa yaran shamsiya ne Wanda idan har hakan ya kasance dole Zinatu zata gane Shamsiya na Raye.

“Gwaggo yaran nan jinina ne wani zubin sai na ringa ji a jikina shamsiya bata mutu ba,dan ba Wanda yaga gawanta.

Rashin ganin gawanta yasa sai na ringa Jin kamar ta tsira daga cikin gobarar nan Gwaggo yaran nan kamanina dasu yayi yawa,Ina bukatar nayi bincike Ya ibrahim Sule ku duba min yaran nan har dan bakin dake gefen wuyana gashi nan a wuyan su.

Koda shamsiya bata rayye kila sai da ta haifi cikin jikinta ta rasu.

“Wai taya ya zaka ce yaran nan jinin shamsiya ne bayan gidanan kurmus ya Kone tana ciki wallahi shamsiya ta mutu ni na tabbata”

Zinatu tace cikin tsananin tashin hankali

A yadda tayi magana a firgice cikin tashin hankali tana rike zaninta kamar dai zata fara Karamin hauka yasa Gwaggo Sakin murmurshi tana “kika ce kin tabbata ta mutu taya kika tabbatar da ta mutu”?

“Gwaggo gidan fa kurmus ya Kone ba Wanda bai sani ba taya zaa ce yaran nan yaran shamsiya ne kawai dai Habu so yake ya wayance kila Aure yayi a b’oye bansani ba ko Kuma ciki yayi wa wanan barrister Aisha dan yaranta ne Habu ka fito ka fada mana gaskiya”

Zinatu tace tana Kara kallon Yan biyun da ganinsu ke Saka ta faduwar gaba kamar kirjinta zai fado.

Hanne kuwa dasu sule gwaggo kawai suke tayi wa magiya ta fada.musu gaskiya yaran waye dan Suma Basu yarda jikokin Maman Kamilun bane.

Habu dake rike da hannun Aryan da Abyan gam bai ko Kalli Zinatu ba ya nufi hanyar waje da Yan biyun Yana “Ina bukatar ganin Barrister Aisha Ina so ta fada min inda ta samo yan biyun nan da nake Ji a jikina jinina ne”

“Kama riga da kasan jininka ne asirinka ya tonu karya kawai kake yi wayancewa za kayi ni zaka yiwa bariki ka dirkawa barrister Aisha ciki ta haifo ma Yan biyu kazo kana lankayawa margayiya shamsiya wallahi sai na bika naje.

Gwaggo kuwa duk Kiran da take wa Habu bai ko juya ba sai da ya fita.

Yana fita da Yan biyun ya nufi wajen motar Amjad ya bude bayan ya Saka Yan biyun batare da ya kalli Zinatun da bai ma san mai take cewa ba

Burinsa kawai ya gansa a gaban Barrister Aisha

Yana fita daga gidan Zinatu ta fita da gudunta taje ta hau Napep  kamar wata zararriya tana hararo irin dukan da zata yiwa barrister Aisha idan har zarginta ya tabbata.

Gwaggo

      Dafe kanta tayi tana Jin duk tambayoyin da su Sule ke ta jefa mata akan Yan biyun sai magiya suke akan ta fada musu.

Gwaggo kuwa ta dago tace wa Ameera da Amrah su fita su basu waje.

Sai da ta ga sun fita ta daga kasan pillonta ta ciro karamar wayar da iya shamsiyrr kawai suke  waya da wayar.

Ta kira lambar shamsiyar tana d’auka tace “Habu Yana hanya zuwa gidanki Zinatu kuma ta biyo shi dan haka sai kisan Shirin da za kiyi Ina ga yau ya kamata ayi ta ta kare”

Daga haka Gwaggo ta kashe wayarta.

Ta dago ta Kalli su Sule da suka kura mata ido suna kallonta

Ta Kalli Hanne da taga ta dafe zuciyarta tana k’ok’arin magana taji Hanne tace “Gwaggo Shamsiya tana rayye ko?shamsiya ce take zuwa wajenki ta Saka wanan dogon hijabi da nikaf ko”?

“Tana rayye Hanne shamsiya tana rayye Yan biyun nan yaranta ne ita ta haife su”…..

*Page 47*

     Hanne dafe kirjinta tayi ta samu waje ta zauna saboda rawar da jikinta ya d’auka,bata kawo zaton da take da hasashen da take gaskia  bane,tunda ga lokacin da Mai nikaf dinan ta tsiri zuwa da maman kamilu Shamsiya ta hau fado mata dan duk da ba ganin fuskar Mai nikaf din take ba indai zata ganta sai taji gabanta ya fadi har tsigar jikinta take ji Yana tashi haka zata tayi ta kallonta tana Jin dama ta iya zuwa ta bud’e nikaf din fuskarta,sai da Sule ya nuna mata bacin ransa sosai ta bar masa maganar shamsiyar da a yanzu take yawan mafarki da ita.

Sai take Jin kamar Shamsiya ba mutuwa tayi ba,sai take Jin kamar Shamsiya tana rayye duk da gidan ya Kone kurmus basu samu ganin gawanta ba haka kawai sai zuciyarta ya ringa raya mata Shamsiya na rayyen inda kwana biyu kenan shamsiya ta tsaya mata arai har bata tashi tunanin ta sai taga Mai Nikaf din da take ganin kamar Shamsiyar ce.

Daga lokacin da ta dan fara Shan jinin jikinta daga yadda taga Gwaggo na kulle k’ofa dakin idan Mai nikaf din tazo da a yanzu ma ita kadai ke zuwa wajen Gwaggon bata zuwa da maman kamilu.

Kwana uku da suka wuce suka ci karo da ita a bakin k’ofa inda a ranar ta ji muryar Mai nikaf din da ya sa gabanta balain faduwa dan hakuri ta bata ta saka takalminta da sauri ta fice daga gidan.

Har ta fice jikiinta bai bai daina rawa ba dan idan har ba tab’in hankali ta samu ba muryar shamsiya taji,inda ta taka da saurinta tabi bayanta dan sosai taji tana so taga fuskar Mai nikaf din  sai dai tana zuwa bakin gate din taga har driver yaja motar sun tafi.

Jiki na rawa ta nufi wajen Gwaggo inda tana shiga Gwaggo ta kashe wayar da take da sauri takan yi mamakin yadda gwaggo ke san yin waya a b’oye da ta rasa da wa za tayi waya haka.

Tunda ga ranar ta ji ta fara dasa zargin ko dai shamsiya ce Mai nikaf din.

Sai gashi Gwaggo ta tabbatar mata da shamsiya tana rayye Yan biyun da ba inda suka baro Habu yaransa.

Ya ibrahim da Sule suma kasa tsayawa suka yi sai da suka samu waje suka zauna

Gwaggo kuwa ta zuba wa Hanne ido da itama Hanne ita take Kallo

Sam bata so ita ta fara sanar musu da shamsiya na Rayye ba amma a yadda taga abubuwa na tafiya sanar da Su Sule da Hanne gani take shine mafita dan tasan idan har tace kar su tab’a nunawa kowa shamsiya na Rayye ba zasu sanar da kowa ba.

Babban burinta itama kullum bai wuce shamsiya ta bayyana kanta asirin Zinatu ya tonu kowa ya huta ba

Koda shamsiya bata bayyana kanta ba abubuwa duk sun riga da sun kwabewa  Zinatu dan asirinta ma ya riga da ya tonu ko da iya Ayuba aka barta.

“Kuyi hakuri da ban sanar muku da wuri ba wasu dalilai yasa na b’oye muku duk da ku din ba wayanda ya kamata na b’oyewa bane,amma shamsiya ta rokeni akan bata so kowa ya san tana rayye dan ni kadai nasan tana rayye.

Gwaggo ta hau basu labarin yadda Shamsiya tazo gidan da Kuma dan gajeren labarin yadda ta tsira daga gobarar,da Kuma dalilin daya sa ta b’oye kanta.

Tunda Gwaggo ta fara basu labari Hanne ke ta zabga kuka Ya ibrahim kuwa sai sallati yake Sule kuwa bai wani yi mamaki da Gwaggo tace Zinatu ce ta haddasa gobarar ba dan yasan wacce Zinatu ko a lokacin sai da ya kawo zarginta kawai bashi da shaidan da zai zargeta ne shiyasa bai tab’a nunawa Yana zargin sa hannun Zinatu a gobarar da ya faru ba.

“Mai yasa shamsiya zata b’oye min kanta Gwaggo Mai yasa zata min haka ko dan ba uwar mu daya da ita ba,duk tsawon shekarun nan ace Shamsiya tana rayye amma ko sau daya bata tab’a tunanin neman mu ba,ko da bata nemeni ba mai yasa bata nemi Mahaifiyarta dake kwance da silar rashinta take kwance,silar rashin shamsiya mahaifin ya samu ciwon barin jiki har sai da ya koma ga Allah duk dan rasa shamsiya da yayi da tunanin duk laifinsa ne saboda shi ya Mata dole a auren ita da Yaya Habu,Amma Gwaggo ace Shamsiya duk tana rayye bata tab’a bayyana mana kanta ba tana da wayanda suka fi mu ne”?

Hanne tace cikin tsananin kukan bakin cikin abinda shamsiya tayi dan duk ba Wanda bai kamu da hawan jini ba a rashin shamsiya Amma sai gashi tana sane ta b’oye musu kanta sai gwaggo ta bayyana wa kanta”

“Idan Kuma kika yi haka Hanne ba zanji Dadi ba,ni a ganina dalilan da na fada Muku ya Isa yasa shamsiya b’oye kanta sai dai idan baki ji dadin da ni ta fara bayyanawa kanta ba,ba ke ba yanzu so kike ki nuna ban cancanci na fara Sanin tana rayye ba ko”?

“Ba haka bane Gwaggo tashin hankali da ta jefa mu da tsawon shekaru muke fama da bakin cikin rashinta da ciwo Gwaggo ai ba yadda za’ayi mu tab’a tona sirrin da take so ta b’oye batare da an sani ba amma tunda yanzu tana rayye Alhamdulillah”

“Yauwa Hanne ko kefa dan Allah bana so ku tab’a nunawa Zinatu komai Ina so mu bar maganar nan a tsakanin mu, Zinatu ta dade tana aikata Abubuwan da ya kamata ace asirin ta ya tonu amma dai yanzu komai ya zo karshe,shamsiya da take tunanin ta kashe tana rayye har da Yan biyun da take tunanin da cikinsu shamsiya ta mutu,ni da nake Mahaifiyar Habu ma taso kasheni Allah bai yi ba gani nan a rayye Ina addu’a tafiyar nan da tayi shamsiya ta bayyana mata kanta Ina addu’ar Allah ya kawo karshen duk wani makircinta”

“Ai Gwaggo komai yazo karshe Kuma dan tun kan asirin nata ya tonu ta fara zarewa ni zan so asirinta ya tonu a gaban kowa Gwaggo”

Cewar sule

Ya ibrahim kuwa da har lokacin yake sallalami yace “Ni fa har yanzu mamaki bai gama sakina ba wai a Ina Habu ya samo shaidaniyar matar nan ne?nifa banda kince a dan Jira Gwaggo wallahi ta dawo gidanan sai na sumar da ita na mika ta wajen yan sanda”

“Duk ba sai an Kai ga haka ba a bi komai a hankali ke kuma bar kukan haka nasan kila Shamsiya zata bayyana musu kanta yau idan kuma bata bayyana kanta ba komai dai ya kusa zuwa karshe”

Daga haka suka cigaba da tab’a hira har sai da sule ya bawa Gwaggo labarin asirin fitsarin kwancen da Zinatu tayi wa Ameera da bama su san cewar Ameera ta sa an maida wa Amrah ba,ya Kara da bai san mai ya tarewa Zinatu a rayuwa ba duk da duk abinda take koma mata yake amma ta kasa daddara.

Habu

          Yana tuki Yana kallon Yan biyun da yake Jin wani irin kaunarsu na ratsa shi,abubuwa da yawa sun tsaya masa a zuciya da sai yaga barrister Aisha zata warware masa komai, dan ba mai ce masa Yan biyun nan ba jinin sa bane, abinda ya kasa ganewa shine ya  aka yi shamsiya ta tsira daga gobarar da agaban idonsa yaga gidan ya Kone kurmus Wanda hakan ya Kai shi ga sumewa,a idonsa bai ga ta inda shamsiya zata iya tsira daga wanan gobarar ba,bai ga Kuma akwai Wanda ya shiga gidan ba.

Iya Samha dai wani ya ceto da ya ringa ji dama shamsiya ya ceto ba Samha ba,Wanda banda su Sule sun hana shi a wanan lokacin yaso neman Wanda ya ceto Samhan,yakan zargi wani ne ya hada masa gobarar lura da yadda aka kulle gidan ta waje amma ya rasa Wanda zai zarga din lura da ba wani yake fada dashi ba har ita shamsiya ba ta da wani abokin fada.

Bai dai san tunanin da ya kamata yayi ba Barrister Aisha ce kawai zata warware masa komai.

Yana Isa k’ofar gidan yayi parking duk ma tambayoyin da yake wa yaran dan yaga ko zai gano wani abu ba wani amsa suke bashi ba.

Sam bai ma lura da Zinatu da itama Napep ya ajiyeta ba ta cire mayafinta ta daura damara.

Hannunsa cikin na Yan biyu ya hau buga gate din gabansa na faduwa dan har zuciyarsa ta fara rayya masa  ace Yana shiga yaga Shamsiya.

Isowar Zinatu bakin gate din yayi daidai da bude k’ofar da Mai gadi yayi.

A yanzu ba lokacin da zai biyewa Zinatu bane shi yasa bai ko bi ta kanta ba ya shiga ciki,duk da ba ciki ya so shiga ba yaso ace Mai gadin ya cewa yayi wa Barrister Aisha magana amma ganin Yan biyun sun shige ciki da dan gudunsu batare da sun saki hannun sa ba,yasa Shima ya bi bayansu inda tunanin sa ya bashi kila dan mai gadi ya ganshi da Yan biyun shi yasa bai hana shi shiga ba.

Yana Jin muryar Zinatu na “Cin Amana Kiri Kiri wallahi ba zan yarda ba”

Koda suka shiga palon ba kowa sai katon tv dake kunne.

Wand yake kyautata zaton shine Hassan din ya saki hannun sa yayi sama da sauri,shi kuwa ya sunkuya yace wa Abyan ya kira mi shi mominsa.

Abyan kuwa shi ma ya Haye sama da sauri.

Tun kafin ma yaga barrister Aisha yaji gabansa na faduwa.

“Ai ba zata tab’a yarda ta fito ba saboda tasan asirinta ne zai tonu, Ashe duk tsawon lokacin nan Habu cin Amanata kake da wanan matar da take ta b’oye kanta,har Mai na rage ka dashi da zaka min irin wanan cin amanar har Kuma ka ringa raina min wayyo kana nuna min baka Santa ba.

“Zinatu kafin na kirga biyar ki bar gidanan Zinatu kin fara kaini bango”

Habu yace cikin tsananin b’acin rai

Zinatu kuwa ta gyara tsayuwarta tare da Kara gyara zaman mayafinta a kugunta dan yau bata ga uban da zai hana ta jibgar barrister Aisha ba,dan ko bata nan sai ta Jira ta balle a yanzu ta gano dalilin da yasa barrister Aisha ke b’oye kanta soyayya take da Habu shiya sa take b’oye b’oye.

Kawai mamakin da take har a wane lokaci Habu ya hadu da barrister Aisha?Aurenta yayi a boye ya Mata ciki ko Kuma dai soyaya suka yi yayi mata cikin shege dan ita kanta tasan wanan Yan biyun yaransa ne.

Wani dogon tsaki taja tana “wallahi ba inda zanje sai dai duk abinda zaka yi kayi har ka haihu da wata bansani ba dan asirinka ya tonu kazo kana min borin kunya”

Habu da zuwa yanzu ransa ya Kai kololuwa wajen b’aci ya nufi wajen Zinatun dan yadda yake Jin zuciyarsa da tsanata in ya Shaketa sai ta daina numfashi zai saketa.

Takun tafiya da yaji ya sa shi tsayawa bai Kai ga Isa wajen Zinatun ba.

Ko da waiga wanan murdadiyar matar ce ta sauko

Cikin harshen Turanci ta hau tambayar su wa suke nema

Kafin Habu yayi magana Zinatu tayi caraf wajen cewa “karki sake ki mana karyar Turanci asirin madam dinki ya riga da ya tonu ni nasan tana ciki kice ta sauko idan ta Isa ta daina wani b’oye ‘b’oye”

Matar bata ko kalli Zinatu ba dan shamsiya na ta mata magana ta airpod din dake sakale a kunneta akan kar ta bi ta kan Zinatun.

Fuska a sake ta cewa Habu wa yake nema

Habu kuwa yace mata shi ma cikin harshen Turanci akan ta taimaka masa ta cewa Barrister Aisha Yana San ganinta.

Matar kuwa tace mi shi barrister Aisha bata gari tayi tafiya sai lahadi zata dawo amma zata sanar da ita idan ta dawo

Habu cikin magiya ya Kara cewa ta taimaka masa tayi wa barrister Aisha magana yasan tana nan dan Yan biyun ma sun sanar masa da tana nan

Matar kuwa ta girgiza kanta bisa umarnin da shamsiya ke ta bata akan barrister Aisha bata gari sai dai idan ta dawo.

Habu kuwa dafe Kansa yayi da yaji ya fara masa ciwo dan zuwa yanzu ya fara gasgata zarginsa akan akwai wani boyayyen Al amari game da Barrister Aisha dan duk yadda a akayi tasan wani abu bai san mai yasa take san b’oye masa ba.

Ji yake kamar ya hau Saman benen da Kansa amma daga yadda murdadiyar matar ta tsaya fuska a hade ba zata tab’a barinsa ya hau Saman ba.

So yake ya Kara ganin Yan. Biyun da suka hau sama amma bai ga alamar zasu sauko ba

Zinatu kuwa sai ihu take tana “Munfika tana nan wallahi saukowa ne ba zata yi ba wallahi ba zan bar gidanan ba har sai ta fito ni zaa gwadawa munafirci”

Habu kuwa cewa matar yayi zai dawo ranar lahadin ta fadawa barrister Aisha akan Yana so ya ganta.

Daga haka ya fara k’ok’arin yin Waje

Zinatu kuwa ganin da gaske barrister Aisha ba saukowa za tayi ba yasa ta nufi wajen matattalar benen da gudunta dan ta k’arfi da yaji sai taga Barrister Aisha sai dai ko Mai zai faru sai dai ya faru.

Habu da yaje bakin k’ofa ya tsaya cikin tsananin mamaki Yana kallon Zinatu da ta kusa Isa wajen da murdadiyar matar ke tsaye dan bata Kai ga saukowa ba.

Shamsiya dake gaban laptop dinta tana ganin duk Mai ke faruwa a kasa

Ta saki murmurshi cikin harshen Turanci tacewa Lydia tayi wa Zinatu dukan tsiya.

Lydia kuwa tuni ta cafe Zinatu da take ganin karfin halinta

Tayi ball da ita ta gangara kasa

Habu kuwa ya sa Kansa ya fice daya ga Lydia na zuba mata naushi da ball

Dan Lydia ta masa daidai shi ma Jira yake Zinatun ta zo hannunsa ya Mata mugun duka.

A yanzu ya Kara tabbatar wa Kansa bai yi dacen mata ba,dan da tana da hankali ba kishi ya dace ta sa a gaba ba, sultana da tayi batan dabo da basu san ma ta inda zasu fara nemanta ba zata dage wajen nema,amma saboda rashin hankali ta haukace da kishi har take da karfin halin zuwa gidan Barrister Aisha.

Har yanzu idan ya tuna warin da ya shaka daga jikinta daren jiya sai yaji yawu ya taru a bakinsa.

A yadda yake ji ma ba zai iya cigaba da zama da Zinatun da yake zarginta da aikata abubuwa da yawa ba ciki kuwa har da asirinta da Ameera taso tonawa dazu

Da Kuma Ayuba da taje tayi wa alkawarin auren sultana saboda kawai kar ya fallasa sirrin da ya matsu yasan ko mai ta aikata haka da ta gwammaci bawa Ayuba auren sultana da dai asirnta ya tonu,dole ma ya nemo Ayuba dan zai so Sanin Mai Zinatu ta aikata har haka.

Da haka yaje ya hau motar da Amjad ya bashi ya nufi gidan gwaggon dan da alama itama gwaggon akwai abinda take b’oyewa dole tasan Barrister Aisha tunda har ta turo Mata yaran

Ba zai ma iya hakurin zuwa lahadi ba idan har Gwaggo bata fada masa komai ba sai ya dawo gidan Barrister Aishan.

Lydia kuwa sai da tayi wa Zinatu lilis ta watsa ta waje da kumburareen baki tana zuba musu Allah ya isa da alkawarin sai ta rama

Shamsiya kuwa ta rufe laptop dinta tana gobe Kya sake dawowa.

Sam ba haka taso ba,yau da ace iya Habun ne yazo da ta bayyana masa kanta.

Amma da Gwaggo ta kirata akan Zinatu ta biyo shi a baya shi yasa ta sake boye kanta dan a gidan Sule take san bayyana tunda kusan duka zuriar Gwaggon na gidan

Dan bature ne kawai baya nan a gaban kowa zata tona asirin Zinatu.

Zinatu kuwa dak’yar ta mik’e da kumburaren jiki tana shan alwashin yadda zata ga bayan barrister Aisha da tsinaniyar matar da ta ajiye a gidan ta mata duka.

Gidan kawarta ta nufa da ta d’auka ma hatsari Zinatun tayi,duk da canja mata fuskar da kawar tata tayi haka ta shanye wulakancin da ta mata ta sake rokonta kudi ta ci abinci ta nufi wajen Natete dan mafitar  kawai da ya rage Mata kenan,taga alamar idan ba tayi wasa ba asirinta sai ya tonu.

Koda ta isa wajen Nateten  cikin kuka ta Kara Zayyano masa yadda asirinta ke neman tonuwa da sakota da Gwaggo tayi a gaba da Kuma Yan biyun da suka bullo na Habu da bata san lokacin da ya nemi barrister Aisha ba,cikin kuka ta hau fada masa duk irin Abubuwan da take so  ya Mata ciki kuwa har da kawo karshen barrister Aisha da Gwaggo sai mallake Habu da take so ta sake yi da k’arfi  ayi mata aiki  akan sultana ta dawo gida a rufe bakin kowa yadda ba mai iya magana idan zaa daura auren ta da Ayuba,tana Kuma so ayi asirin da zaa raba Ameera da Yareema dan Ameera ta zame mata masifa duk wasu mugayen abubuwa da Babu ko alheri daya ta zayyana akan Natete ya Mata da ya dage da Zane a cikin kwarya.

Sai da ta gama tsaf yace aikin duka mai sauki ne karfe daya na dare zai mata aikin.

Zinatu kuwa ta mik’e da saurinta tana “Ni wallahi ba zan kwana ba,ni na daina gane Maka gaskiya sau biyu Ina baka kaina dan duk na samu cikar burina amma duka a banza hasali ma kamar ma asirin ma da nayi duk warware wa yake, Taya ban samu biyan bukata ba zan sake bari ka tab’ani,kiri Kiri naso mijina ya sadu dani ya ringa toshe hancinsa saboda warin dake fita a jikina a gaskiya Natete sai Aiki yayi zan sake yarda dakai idan dai duk abinda nace kayi min yayi ni na Maka alkawarin yin sati ma amma bazan Kara yarda ka durjeni ba biyan bukata ba”

“Toh shikenan sa takalmin ki tafi, aikin ne baki so ga tonuwar asirinki kaca kaca ma na gani ciki kuwa har da kulleki da za’ayi a kurkuku”

Natette yace cikin mugun hade rai

Zinatu kuwa ta koma ta zauna da sauri ta sawa Natete kuka tana ita dai ya taimaka mata bata so asirinta ya tonu.

Haka Natete ya sake mata wayo ya dirjeta a daren Koda garin Allah ya waye sai ma ta kasa tashi duk yadda taso ma tafiya a washegarin bata iya tafiya ba sai da ta sake kwana nan din ma Natete ba daga Mata kafa yayi ba dan daina ma kula masu zuwa wajen sa yayi kamar dai Wanda yayi sabon aure.

Sai tsine masa take a zuciyarta dan ya azabtar da ita a ranar da ta kwana na biyun wajen karfe biyu ya hada Mata tarkace na binnewa na turarawa da sauransu akan duk aikin da tace ayi mata zai ci.

Tabbatar mata da yayi da ya mallake mata habu ta tafi gidan batare da tayi ko fargaba ba yasa ta nufi gidan Sulen ba tare da tayi fargabar komai ba.

Sultana

       Bugun da taji an kai mata a baya da k’arfi yasa ta dan Bud’e idonta dak’yar dan tun jiya bata san inda kanta yake ba,tsananin bakin cikin rayuwar da za tayi a gidansu Ameera da taso ace itace a kasanta yasa ta kasa jurewa Habu Yana nufar Bangaren su Hanne ta fito itama dan sam ba zata iya zama a kasan su Ameera ba.

Koda ta fito bata zame ko’ina ba sai wajen Saurayin ta shamsu da dama tasan gidansa tunda tana dan zuwa wani zubin.

Koda ta je bata same shi ba sai da ta zauna zaman jiransa sai wajen goma na dare ya dawo a buge,tasan dai Yana Shan shisha da sigari dan saboda shi ma take dan tab’a Shan Shishan.

Buguwar da yayi yasa bai wani ma ganeta ba sai washegari dan a Palo ta kwana shi kuma ya zube a kasa.

Sai da ya wartsake ya ganeta ya kuma nuna Jin dadinsa da ganinta Koda ta fada masa abinda ya kawota akan ita dai ya fito ya aureta ita ba zata iya zaman gidan kanin babansu ba dan har labari ta bashi tama nuna masa auren dole ake so ayi mata.

Shi kuwa shamsu yace kar ta damu idan iyayen sa suka dawo kasar zai sanar dasu.

Da haka shi ma yayi wa sultana wayo ya rabata da budurcinta.

Suka koma zama kamar mata da miji,iya nan bai Isa ba sai da ya hada da koya mata yadda ake Shaye shaye,tun sultana na dan janye jikin ta har sai da itama ta Koyi shaye shayen aikin kenan su Sha suyi makil su aikata Al fasha.

Shamsu kuwa da yaga ya gama samun Abunda yake so gashi Yan sanda yanzu suna nemansa saboda safarar kayan mayyen da yake ya rubuta mata wasika daddare ya tattara kayansa ya gudu dan Jininta bai fiye k’arfi ba indai ta sha haka zata bugu tayi ta bacci zata iya kwana biyu tana bacci.

Sai da ta wartsake sosai ta ga Yan sanda ne wajen su biyar a tsaye  akanta.

Rashin kwarin jiki yasa tana mik’ewa ta Kara koma wa ta zube a kasa cikin tsananin tsoron ganin su cikin muryar mayye tace musu lafiya.

Ba Wanda ya bata amsa wani ya figo ta ya sa mata ankwa suka Yi waje da ita.

Kuka ta fashe dashi ta Dora hannunta a ka tana ta shiga uku a haka har suka Isa wajen Yan sanda anan ta gane shamsu suka je kamawa da manyan laifukan da ya aikata a rashinsa suka kamata suka Kuma dage sai ta kira wani nata yasan halin da ake ciki

Ganin idan har bata kira ta sanar da halin da take ciki ba haka zasu cigaba da tsareta.

Tana ji tana gani ta Bada Lambar wayar Habu.

Zinatu

       Tana Isa gidan Sule ta tsaya a k’ofar gidan ganin ba mai kallonta tayi sauri ta tsugunna ta binne layya hudun da Natete ya bata akan ta binne a k’ofar gidan Sulen a yanzu babban burinta ma anjima ta kawo karshen Gwaggon.

Sai da ta Kade kasar dake hannunta ta shige cikin gidan.

Ba Wanda taci karo dashi har ta Isa part dinsu.

Sai da tayi wanka ta dirje jikinta dan duk bata samu tayi wanka ba ta daura alwala ta fito.

Sallah ma a gurguje tayi duk baa nutse ba dan babban burinta taga Habu taga ko aikin da aka masa yayi.

Koda ta fito daga daki ba kowa a bangaren nasu hakane yasa ta nufi part din Hanne dan tasan kila  Amrah na can zata so yau ta sa layar da ta b’oye a zaninta a pillon Gwaggo Yau ko zata kai Sha biyun dare sai ta saka mata layan dan ta lura Gwaggo ta fara ganota.

Koda ta isa cak ta tsaya daga bakin kofa dan gabad’aya su Hanne na palon a zaune suna ta hira har da Gwaggo da hakan yayi matukar bata mamaki dan bata tab’a ganin gwaggo a palon ba sai dai a daki.

Duk fuskarsu d’auke da murmurshi suka zuba mata ido Habu ne kawai yake mata wani iirn Kallo da ta kasa ganewa.

Yan biyun da ta gani a gefen Habun da Immii yasa gabanta wani irin faduwa.

Ido kawai ta zuba musu tana kallon su.

Muryar Gwaggo ne ya dawo da ita tunanin da ta tafi

“Ya kika tsaya daga bakin kofa ki shigo mana”

Kamar umarnin Gwaggo take Jira ta shiga cikin palon tuna zargin da take da Yan biyun yaran Habu ne yasa ta nufi wajen Habun tana “Habu yaran nan dai sun tabbata yayanka kenan mai na Maka da zaka min irin wanan cin amanar”?

Habu hannunsa ya Kara damkewa da k’arfi ya sunkuyar da Kansa dan wani irin tafasa yake dak’yar idan zai iya cigaba da dannewa batare da ya hada Zinatu da bango ya rabata da ranta ba.

“Wai toh ki samu waje ki zauna mana daga dawowarki zaki hau masifa”

Hanne tace tana sakin wani irin murmushi

Zinatu kuwa ta kwasheta da wani iirn harara ta Kalli Gwaggo tana “Gwaggo ki tambaya min Habu taya ya hadu da barrister Aisha har ya Mata ciki ta haifa masa yaran nan”?

“Wai kina so kice baki gane yaran nan ba yaran shamsiya ne fa ba Barrister Aisha ba”

Kamar wacce aka bugawa guduma haka Zinatu taji ta Kalli Habu daya dago da kansa Yana kallonta cikin jajjayen idonsa.

Ta Maida kallonta wajen Gwaggon tana “Bangane yaran shamsiya ba wacce shamsiyar kike magana”?

“Shamsiya dai matar Habu da kika sani yaranta ne”

“Ta Ina shamsiya ta haihu bayan ta mutu da cikin jikinta taya yaran nan zasu tab’a zama yayanta Gwaggo”

“Aikuwa dai Yan biyu yaran shamsiya ne ga imtihal nan ma a gabanki  ko ita baki gane ta ba”

Zinatu zubewa tayi a kasa ta hau girgiza kanta tana “Gwaggo karki haukatani shamsiya ta mutu a cikin gobara nan da cikin jikinta da imitihal na tabbatar da haka dan bata inda zata ma iya fitowa daga cikin gobarar nan dan Samha kawai nasa Ayuba ya d’auko min”

“Allah cikin ikonsa Kuma gani nan da raina baki samu nassarar kasheni ba Zinatu”

Taji muryar daga bakin k’ofar dakin Gwaggo…..

Masoyana abin Al faharina ngd kwarai da addu’oinku da kulawar ku a agareni ngd da soyayar da kuka nuna min ta hanyar yiwa kanwata margayiya addu’a Allah ya Saka muku da mafificin alheri ngd da so da kauna Allah ya bar mu tare ngd ngd

*Page 48*

Habu

      Tunda ya isa gida ya nufi part din su ya kwanta tunanin da ya matsawa Kansa da shi ya sa mi shi ciwon kai da hakan ne ya hana shi zuwa bangaren su Hanne  dan ya samu Gwaggo da tambayoyin da ke ciciyar zuciyarsa.

Ya rasa ma tunanin daya dace yayi akan Yan biyun da yake Jin su a zuciyarsa bai ji Dadi da bai samu ganin Barrister Aisha ba dan ita kadai ce zata warware masa komai dan bai san ma tunanin da ya dace yayi ba idan har Yan biyun nan jininsa ne hakan na nufin shamsiya ta tsira daga gobarar  da bai san ta inda ta fito daga gidan ba,abinda bai gane ba taya ta haifi Yan biyun, hakan na nufin shamsiya na Rayye kenan? Mai hadin Barrister Aisha da Yan biyun da yaji suna ta kiranta da momi,ko dai ma kamani ne kawai suke da Yan biyun ba jininsa bane ?duk a wajen Barrister Aisha zai samu amsar tambayoyin sa,dan yadda yake Jin Yan biyun a ransa ba yadda ma za’a ce ba jininsa bane su.

Haka ya kwanta da tunani sallah kawai ke tashin sa dan ko massallacin ya kasa zuwa.

Rashin dawowar Zinatu bai ko wani dame shi ba dan ya gama sawa a ransa sakinta zai yi dan sosai yake Jin tsanar Zinatun Yana tuna Abubuwan da duk ta aikata abaya ciki kuwa har da zagin Gwaggo da tayi har ji yake ya aka yi ma ya dawo da ita rayuwarsa.

Rashin Sanin inda sultana take da rashin damuwar da Zinatu ke nunawa ya Kara Kona masa rai da tsanar Zinatun.

Tunanin nan ya sa shi mik’ewa ya fito daga dakinsa ya nufi dakinsu Amrah da yanzu ita kadai ce da Samha sai jariryarta.

Lokacin wajen tara na dare.

Kallo ya tarar dasu suna yi a  dan Karamin tv dake  dakin.

Shigarsa dakin yasa suka rage volume din tv suka hau gaishe shi dan da alama ma basu san ya dawo ba.

Amsawa yayi ya jingina da jikin bango ya hau tambayar Amrah ko akwai kawayen sultana da tasani da zai iya zuwa a duba ta a wajensu.

Amrah kuwa ta girgiza kanta akan ita bata san kawayenta ba.

Nan ma ya tambayi Samha itama tace ba ta sani ba.

Cikin yarinta Samha tace kar ya damu da sultana idan ta gaji da yawon ai dole ta dawo gida.

Bai ce musu komai ba ya fito daga dakinsu ya samu waje a palon ya zauna ya buga tagumi,har ga Allah ba irin raywuar nan ya sowa Kansa ba.

Ya so ace yaransa sun samu tarbiyya sosai kamar yadda su Ameera Suka samu.

Idan har zai ga Fareeda kanwar Ameera da kaninsu sai yaji dama yayansa ne.

Yasan banda Allah ya rufa masa asiri Amrah ta ma yi Aure da wuri da kila itama haka zata na yawo batare da Zinatu ta ko damu ba, Zinatu ta bangaren tarbiyyar Yara kam ta cutar dashi bai san mai yasa a lokacin baya iya d’aukar Mataki ba.

Larurar da Amrah ke fama dashi na fitsarin ma bai ko dameta ba daga maganar Kuma da aka yi dazun kamar Zinatun na da hannu a abinda ya samu Amrah bai san mai yasa Gwaggo ta ringa hana shi binciken da ya kamata yayi akan Zinatu da kararar ya gane akwai mugayen Abubuwan da take aikatawa a b’oye.

Duka yaransa ma ba Wanda ya sauke Qurani.

A massallaci haka zai ta kallon Kaninsu Ameera cikin sha’awa Yana karatun Qurani.

Da kila Shamsiya na Rayye da kila yaranta sun taso kamar yadda su Ameeran suka taso cikin tsananin tarbiyyar.

Girgiza Kansa yayi ya daga Kansa ya Kalli agogo yaga karfe Tara da rabi na dare,tunani kawai yake inda Zinatu tayi har lalacewarsa ta kai haka wai ace matar da yake Aure lokacin da taga dama zata fita lokacin da ta ga dama zata dawo.

Shi kuwa zai zauna yaga iya gudun ruwanta.

Da haka ya runtse idonsa ganin tunani na neman Kara tayar masa da ciwon Kai yasa ya mik’e ya nufi part dinsu Gwaggo  Yana addu’a akan Allah yasa ba tayi bacci ba zai ta mata magiya ko zata fada masa wani abu game da Yan biyun.

Daga shi sai jallabbiya ta Maza ya nufi part din  Koda ya Isa ba kowa a palon an ma kashe fitila mai haske sai mai duhu da aka bari da ya dan haske palon.

Da alama su Hanne sun kwanta Kansa tsaye ya nufi dakin Gwaggon.

Yana zuwa bakin k’ofa yasa hannu dan ya tura k’ofar yaji muryar Gwaggo na ” Ni dai ba zan cigaba da biye miki ba gaskiya ki fito haka nan mai ya rage Kuma da kike Jira nifa na fadawa su Sule dazu ma dan yadda suka tsareni da tambayoyi ba zan iya kauce musu ba”

Muryar wata yaji kasa kasa ba kamar yadda yake Jiyo na Gwaggo ba,mamaki kawai yake wacce tazo wajen Gwaggo a irin wanan lokacin batare da tunanin komai ba ya tura k’ofar dakin Yaga kuwa ta bud’u.

Gwaggo da Shamsiyya suka waiga da sauri,

Shamsiya tayi kasa da kanta cikin bugun zuciya Mai k’arfi.

Gwaggo kuwa tace “B’oye B’oye Kuma ya kare ai”

Habu kallon Gwaggo kawai yake Yana kallon Shamsiya da bai ga fuskarta sosai ba tayi saurin kasa da kanta duk da bai san ko wacce ba sai da ya Tsinci Kansa da faduwar gaba.

Kalmar da Gwaggo tayi da b’oye b’oye ya kare ya tsaya masa ya fara k’ok’arin hada ma’anar maganar tata.

Shamsiya kuwa sallati kawai take dan har ga Allah ba haka taso ba.

Bata so Habu ya ganta bama a yanzu sai gobe da ta gama sawa a ranta zasu zo da yaran gabad’aya.

Dan a gobe ta yanke tonawa Zinatu asiri.

A yadda take san ta tsara yadda komai zai kasance yasa ta zuwa wajen Gwaggon dan ta riga da tasan lokacin da su Hanne suke kwanciya.

Sanin da mai gadi ya Mata yasa tana zuwa yake Bud’e mata ta shiga ciki har ta gama magana da Gwaggo ta fito ba mai ganinta a zuwan da tayi take labartawa Gwaggo dukan da tasa Lydia ta yiwa Zinatu.

Inda suke Hira Gwaggo na fada mata ta gaji haka nan ta fito ta ta tonawa Zinatu asiri ko minti goma ba tayi ma da zuwanta ba Habu ya shigo dakin.

“Idan kin gama sallatin sai ki dago ai ya ganki”

Gwaggo tace tana Jin farin cikin ritsa Shamsiya da Habun yayi dan tasan yanzu dole shamsiya ta bayyana kowa ma yasan tana rayye ta kuma matsu taga asirin Zinatun ya tonu habu ya saketa kowa ya huta.

Habu kallon Shamsiya kawai yake kirjinsa na wani irin bugawa so kawai yake ta dago ya ganta

Ganin tak’i dagowa cikin dan rawar murya da fargabar ma Sanin koma wacce ya Kalli Gwaggo Yana “Gwaggo wacce wanan”?

“Ba zaka Ji a bakina ba ka karaso kawai ka ganta”

Kamar Mai Jiran umarnin  Gwaggo ya nufi wajen su Gwaggon kirjinsa kamar ya fado kwakwalwar sa ma tak’i bashi hadin kai balle yayi hasasheen wacce zuciyarsa ke rayya masa.

Shamsiya kuwa rike zuciyarta tayi dan jikinta har rawa ya d’auka itama bata san dalilin da yasa taji tana tsoron dago da fuskarta ba.

Ganin bata da yadda za tayi dole Yau dai Habu ya ganta ya kuma san tana rayye yasa ta dago da kanta.

Habun da ya kasa zama ya kura mata ido Yaja da baya cikin Ihun sallati dan ko a duhu yaga Shamsiya sai ya ganeta,duk da ta manyanta ba kamar shekarun baya da take yarinya ba,sai ya ganeta.

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Gwaggo Shamsiya nake gani fa ko idona ne”

Dariya Gwaggo tasa dan dariyar ya bata da taga yadda ya ja da baya ya kurma sallati jikinsa na rawa.

Shamsiya kuwa hawaye ne ya hau zubo mata tana kallon Habun da jikinsa ke rawa.

Ita kanta bata san dalilin zubar hawayenta ba

Habu Kansa ya girgiza ya Kara goge fuskarsa da bayan hannunsa yaga sai Shamsiya ce dai a zaune take kallonsa  ba wai gizo ta masa ba.

Yana k’ok’arin magana shamsiya ta katse shi ta hanyar cewa “Nice Yaya Habu ba mafarki kake ba shamsiya ce dai da ka sani Ina rayye ban Mutu ba”

Habu daskarewa yayi a tsayen yama kasa motsawa da yaji maganar shamsiyar dan kallon wancan ma shamsiyar yake mata da ya sani a baya.

Hannunsa ya daga ya nunata a daidai lokacin da take share hawayen dake ta zubo mata

Yace “Shamsiya baki mutu ba kina nufin kece nake Kallo a gabana”?

“Nice Yaya Habu ban Mutu ba kwanana bai kare ba”

“Kazo ka zauna mana ko baka yarda ita din bace”?

Gwaggo tace tana kallon Habun da har lokacin jikinsa rawa yake.

Sai da Gwaggo ta sake masa magana ya zauna daga wajen da yake zaune har lokacin ya kasa d’auke idonsa daga kan shamsiya gani yake kamar mafarki yake ba ita din bace ba.

“Shamsiya a gaban idona gidanan ya Kone kurmus Banga ta inda aka fito da ke ba taya kika tsira daga gobarar nan,yanzu duk tsawon lokacin nan dama kina rayye shamsiya”?

Shamsiya Kai ta gyada masa.

Itama ta sauka kasa ta hau bashi labarin yadda su Babagana suka taimake ta har zuwa haihuwar da tayi da yadda suka taimaka mata a karshe ta Kara da “Bayan na samu duk abinda nake so na fara k’ok’arin dawowa gida Nigeria duk halin da kuke ciki Ina sane.

Bana so a tab’a gane ni shi yasa na sawa kaina Aisha nice nan Barrister Aisha wacce gidanta ke kallon gidanka.

Da biyu na bar imitihal take zuwa gidanku na ringa b’oye Yan biyu dan nasan duk Wanda ya gansu sai yaga kamanin da kake dasu dalilan da na Zayyana ma shi ya hana ni bayyana kaina sai a yanzu duk da na samu yadda nake so na yanke zan bayyana kaina dan nasan da ace Zinatu tasan Ina rayye ba abinda ba za tayi dan taga ta Kau dani ba duk da a yanzu nafi karfinta ba abinda zata iya min amma duk Wanda miciji ya Sara sau daya idan yaga tsumma zai ga kamar micijin ne amma yanzu komai ya zo karshe asirin Zinatu ya riga da ya tonu.

Tunda ta fara magana Habu ya kura mata ido Yana kallonta bai ma san hawaye na zubo masa ba inda tace itace Barrister Aisha sai da ya mik’e tsaye bakinsa yake so ya bude ma ya Mata tambaya sai ya kasa hakane yasa ya cigaba da kallonta har ta Kai Aya sai ya rasa ma mai zai ce mata.

Gwaggo kuwa da taga Habun ya girgiza da duk labarin da shamsiya ta bashi ta kira sunansa akan ya koma ya zauna.

Mai Kuma abin mamaki

Habu da ya rasa ma abinda zai cewa shamsiya da ya gano itace wanan hamshakiyar Mai kudin da yake kwadayin ganinta dan ya dan yi muamallar arziki da ita ya kasa yarda muguntar Zinatu har ya Kai ta iya hadawa shamsiya gobara dan ta kashe shamsiya a labarin da shamsiya ta bashi ya gane Ayuba ne ya hada gobarar.

Fadar halin da ya Tsinci Kansa a ciki na bayyanar shamsiyar da ya d’auka ta rasu da cikin jikinta da imitihal bata bakine,fadar farin cikin da ya Tsinci Kansa ma bata bakine dan kuka yaci ya godewa Allah har da Sallah rakaa biyu a dakin Gwaggon na godiya ga Allah dan bai kawo shamsiya zata iya wanan namijin k’ok’arin ta rike igiyar aurensa har zuwa wanan lokacin batare da ta sake wani auren ba.

Sai da ya sallame kuma suka hau hira su ukun suna tsaara yadda za’a biyowa Zinatun.

Habu kuwa har da Kara komawa part dinsa dan ya duba ko Zinatu ta dawo yaga dai har karffe biyun dare bata dawo ba da alama ma baa yau zata dawo ba.

Gwaggo kuwa ganin Habu da shamsiya sun barke da hira ana ta bawa juna labari sun ma manta da tana dakin Babu alamar shamsiya zata tafi da alama a gidan zata kwana ta mik’e tayi waje taje ta kwankwasa wa su Hanne k’ofa.

Hanne na fitowa Gwaggo tayi kasa da murya tana ga shamsiya can a dakinta.

Kafin Gwaggo taa rufe bakin ta hanne tayi dakin da gudunta.

Sai gashi kamar ba dare ba gidan ya kacame da koke koke da murna

Cikin kuka shamsiya ta Kara basu labari gabad’aya.

A dakin duk suka tsara yadda zasu biyowa Zinatun.

Sai da aka kira sallah asuba su Sule suka bar dakin

Suka tafi suka duara alawala hannne da taci kukan farin cikinta ta gode Allah itama ta daura alwala a bandakin dakin Gwaggon sai kallonn Shamsiya take tana ganin kamaar mafarki take.

Bata San irin farin cikin da yaan gidansu zasu ji ba idan suka ga shamsiya Ashe duk wanan Aiken da ake zuwa gidansu Shamsiya ce ke wanan Aiken.

Ashe daai shamsiya itace Barrister Aisha.

Wajen shidda shamsiya tayi saurin barin gidan dan bata so zinatu ta dawo ta sameta.

Habu ne ma ya ja motar dan dama Allah Allah yake gari ya waye yaje yaga yaransa.

A gidan Shamsiya ya wuni suna Kuma ta waya da su sulen dan suji ko Zinatu ta dawo sai dai bata dawo din ba.

Sai washegari da suke tunanin zata dawo din shamsiya da yaran suka zo gabad’aya.

Kamar yadda suka yi tsamani sai ga shamsiya na cilla kafa suna kallonta ta ccctv cameran dake waje.

Ido sukka waro gabad’aya suka sa sallati a lokacin da suka ga ta sunkuya tana binne layya.

Habu girgiza Kansa kawai yake duk inda ya so ya danne zuciyarsa ya hau zubar da hawaye.

Dan gani yake Zinatu ce kaddararsa.

Gashi ya kasa ma fadawa kowa akan an kiraa shi sultana na kulle.

Shamsiya da sauri ta shige dakin Gwaggo ta labe.

Tana Jin duk maganar da Zinatun take har zuwa subutar bakin da tayi.

Zinatu……

*Page 49*

  Zinatu

               A hankali ta mik’e tsaye cikin wani irin tsoro da faduwar gaban da bata tab’a ji ba dan rawar da jikinta ya d’auka yasa ta zube a kasa da taji Gwaggo tace Yan biyun da take wa kallon yayan barrister Aisha wai yaran shamsiya ne.

Jikinta wani irin rawa ya d’auka da tayi tozali da Shamsiya da ta gaji da haduwa da kyau ko a duhu ka ganta kasan hatimin nassara ya zauna,duk da shekarun da aka d’auka ba zata kasa gane ta ba,dan tsanar da ta mata yasa fuskarta ya zauna a kwakwalwarta.

Murmushin da shamsiya ta sakar mata tana ” Wai ko dai baki gane ni bane Zinatu?Nice dai Shamsiya da kika sa Ayuba ya Kona ni da ciki da imtihal,kika shigo kika d’auki Yarki kika dan konata a Kai saboda kar a dago ki.

Zinatu gani a rayye da imitihal da Yan biyun da kika so kar su shaki iskar duniya,yau gamu nan a gabanki”

Zinatu girgiza kanta ta hau yi da sauri ta fara ja da baya tana mursika idonta dan gani take tab’in hankali ta fara samu ba yadda za’ayi ma shamsiyar da ta kulle a cikin gida ta samu fitowa, tana kallon yadda gidan ke ci da wuta da ta tsaya a bayan gidan.

Bata ga ta yadda Shamsiya ma zata iya fitowa ballantana har wai ta haifi cikin jikinta ba.

A haukace ta fara tsalle tana ihuu “Wallahi wanan fatalwar shamsiya ce,shamsiya ta mutu ita da cikin jikinta da imtihal,sai da na kulle k’ofar ta waje,yadda ma ba zata iya fitowa ba,na koma bayan gidan a gaban idona gidan ya Kone kurmus bata yadda ma zata fito,wallahi shamsiya ta mutu wanan  fatalwar ta ce.

Zinatu tace cikin ihu ta manne a jikin bango tana matse kafarta dan sosai taji cikinta na Murda mata ga fitsari da taji yana neman kwace mata,bata yarda ma shamsiyar bace duk yadda aka yi ma shamsiyar fatalwa ta fara mata kila ma ita kadai ce take kallonta.

Muryar Habu da taji Yana “Zinatu dama haka kike?Yanzu kece da bakin ki kike fadar kin kulle gida saboda kar shamsiya ta samu hanyar da zata fito?Zinatu Yanzu har rashin imanin ki ya kai haka”?

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku na lalace wallahi karya nake bani bace ba”

Zinatu tace cikin ihu da ta gano ma tayi subutar bakin tonawa kanta asiri dan shap ta manta ma da mutane a palon ta hau tonawa kanta asiri.

“Kull karka sake ka tab’a ta koma ka zauna”

Gwaggo tace da taga Habu ya mik’e cikin zafin nama dan yadda yake Jin tsanar  Zinatu gani yake ba abinda zai saka ya ji sanyi a zuciyarta sama da ya rabata da numfashinta,Kuma yadda yake gwara ya kasheta kawai a kulle shi,dan cutar da Zinatu tayi mi shi yayi yawa.

Duk sai a yanzu ya gane wasu Abubuwan da yake ta aikatawa duk ba’a cikin hayyacinsa yake ba,yau da Allah bai bashi jajirtaciyar uwa kamar Gwaggo ba kila  da ta zuciya wajen yi masa baki,da kila yanzu ba shi da ma wajen zama dan bada iya Gwaggo ta hada shi ba har da Yan uwansa da Allah ya sa basu da ruko,jiya haka ya zauna ko runtsawa bai yi ba Yana tunanin duk Abubuwan da ya aikata a baya ciki kuwa har da wulakanta Sule da yake jininsa,da ayanzu arzikinsa yake ci.

“Dan Allah Gwaggo ki barni na kasheta ta cutar dani Gwaggo,Koda bata samu nassarar rabani da ke da Yan uwana ba sai da da tayi nassarar rabani da matata,da ta so kashewa,sai da ta sa yarana suka taso tamkar wayanda basu da Uba,suka kwashi shekaru ba tare da sun sani ba Gwaggo mai nayi wa Zinatu da zafi da zata min irin wanan muguntar”?

“Ba zaka kasheta ba Habu,in Sha Allahu ba zaka tab’a kisan kai ba,yanzu godiya zaka yiwa Allah da ya haska ma wacce ita,godiya zaka yiwa Allah da bai bata nassara wajen kashe shamsiya da yaranta ba,yau silar kashe shamsiya da ta so yi yasa shamsiya ta kai matsayin da duk bamu tab’a tunanin zata kai ba ko iya wanan kadai ma ya Isa yasa ka rabu da ita, Abubuwan da ta aikata kawai ma sun isheta,kaga da bakinta ma tazo tana tonawa kanta asiri ko wajen Yan sanda ma aka kaita ba zata wahalar dasu ba”

Tunda Gwaggo ta fara magana Zinatu ta zubawa shamsiya ido har lokacin gani take mafarki take yi zata iya farkawa daga mummunan mafarkin da take ta kasa yarda wai Shamsiya da take tunanin ta shafe labarinta tana rayye ba ita kadai ba har da yaranta guda uku ras,a Sanin da tayi mata a baya ko secondary ba tayi ba,bata da wayewa ko ilimi abinda yasa take ta kwowanton anya Shamsiyar da ta sani ce ita,maganar da taji Gwaggo tayi akan silar abinda ta aikata yasa shamsiya ta taka matsayin da Basu tab’a tunani ba yaja hankalinta,ta fara k’ok’arin hada tunanin ta waje daya,inda taji gabanta yayi wani Irin faduwa da taga shigar dake jikin shamsiya da gwala gwalan hannunta,tsintar kanta tayi da nuna shamsiya da hannu tana “Shamsiya kece barrister Aisha”?

Murmurshi Shamsiya ta saki tana “Bari na baki gajeran labarina dan ya kamata na warware miki komai dan naga kallon da kike min har yanzu kin kasa yarda nice”

Shamsiya sai da ta dora kafarta daya akan daya.

Ta hau bawa Zinatu labarin yadda ta kubuta daga gobarar da silar arzikinta da komai ma ta Kara da “Tun Ina yarinya na taso da san na zama likita idan Allah ya bani dama,sai dai saboda abinda kika min na zabi karantar lawyer dan da kaina nake so na tsayawa kaina wajen sharia da ke,baki wahalar da ni ba,duk maganar da kika yi kin ga nayi recording”

Ihuu Zinatu tasa ta zub’e a kasa ta hau birgima tana Shamsiya ta rufa mata asiri ta yafe mata.

Habu da ke tsaye har lokacin Yana Jin zuciyarsa na tafasa da tsananin tsanarta ya daka mata wani irin tsawan da yasa ta mik’ewa batare da ta shiryawa haka ba yace “Wallahi sai kin kare rayuwarki a kurkuku sai na tabbata da an yi miki hukuncin kissa ta hanyar rataya na!!!!

“Ya Isa haka Yaya Habu akwai abinda nake so na tambayeta idan har ta fadi gaskiya zan roke ku akan ku yafe mata”

Sule yayi wa Habu ido da ya harzuko kamar zai daki Sulen da yaji Yana kawo maganar yafe mata

A ba yadda zai yi Yayi shiru.

Ya koma ya zauna

Sule kuwa ya Kalli Zinatu da ta dora hannunta aka tana kwada sallati yace “Zinatu idan har kika fadi gaskiya yau a gaban kowa zan k’ok’ari naga baa kulleki ba,abin nan ya kasa goguwa a raina,abin nan ya zame min ciwo a cikin zuciyata da idan har zan tuna sai naji tamkar a lokacin abin ya faru”

“Zinatu a shekarun baya kin ce na shiga dakin ki da zumar na miki fyade tsakanin ki da Allah na ni na kawo kaina dakin ki?Kuma nayi yunkurin yi Miki fyade”?

“Wallahi ko bata fada ba Sule nasan sharri ta maka wallahi daga baya dana zauna nayi tunani nasan sharri ta maka”

“Aaa Yaya Habu a duk abinda ta min wallahi ba Wanda ya kasa goguwa a zuciyata sama da wanan duk da nasan duk Wanda ya sani yasan sharri tamin nafi so ta Kara fada a gaban kowa”

Daga haka sule ya Kara Maida kallonsa wajen Zinatu dake tsiyayar gumi kamar an tsoma ta a ruwa tana yarfa hannuwa dan tasan yau duk wani asirinta ya tonu,tunda shamsiya ta bata labarin itace barrister Aisha taji kamar an caka mata wuka a Kahon zuciya,yau da ace tasan shamsiya kudancewa za tayi da bata ma tura Ayuba ya Kona ta ballantana har ta fada hannun Wayanda suka taimaketa ta zama hamshakiyar Mai kudi, Karin tashin hankalinta ma Barrister ce ita,yanzu zata iya sawa a daureta ko a kasheta.

“Zinatu tsakanin ki da Allah nake so ki fada nayi yunkurin yi miki fyade?

“Dan Allah Sule ka yafe min Sharrin shaidan ne,a lokacin na tsani na budi ido na ganka a gidanan na rasa ta hanyar da zan sa ka bar gidan Habu ya koreka wallahi shi yasa na Maka wanan Sharrin dan girman Allah ku yafe min”

Zinatu tace tana rusa Ihun kukan ta shiga uku

Ihunta kawai ke tashi a palon Sule kuwa haka kawai yaji hawaye ya cicciko a idonsa dan sai yaji tamkar a yanzu ta masa Wanan Sharrin da ya masa nauyi a zuciya,duk da Gwaggo da Hanne a lokacin basu tab’a yarda ya aikata hakan ba,amma sai yake Jin ba mai wanke shi yaji dadi a zuciyarsa sama da Zinatun.

Kuma a yanzu da ta fada sai yaji zuciyarsa ta rage masa nauyin da yake ji tun tsawon shekarun nan da aka d’auka.

Habu kuwa ya sunkuyar da Kansa kasa kamar mace ya hau kuka Yana “Allah sai ya tsine miki Zinatu Allah sai ya Kona ki Zinatu ba zan tab’a yafe miki Abubuwan da kika sa na ringa aikatawa ba,Ina Jin kunya idan na tuna fifitaki da nayi akan Mahaifiyata da Yan uwana,har na kasa yadda da dan uwana na biye miki Zinatu wallahi ba zan tab’a yafe miki ba Zinatu”

“Dan Allah ka yafe min Habu a lokacin gani nake,an dora Maka nauyi shi yasa na aikata abinda nayi sanka duk shi ya kaini ga aikata abinda nayi dan Allah ka dubi yarana ka yafe min Gwaggo dan Allah dan Annabi ki masa magana ku yafe min Allah Yana San bayinsa masu yafiya”

“Kinsan Allah ne Zinatu”?

Gwaggo ta jefa mata tambaya tana tuna shekarun da ta kwashe a kwance batare da tasan inda kanta ma yake ba

“Nasan Allah wallahi Gwaggo Allah shi ya hallice mu dan mu bauta masa”

“Baki San Allah ba Zinatu dan da kinsan Allah ba Zaki tab’a tunanin rabani da dan da ni na tsugunna na haife shi na Raine shi har ya zama mutum kika gan shi kika aura ba,dan kawai Ina k’ok’arin ceto dana daga halaka kika shiga kika fita kika kwantar dani Zinatu tsawon shekara goma Sha Ina kwance ni baa mace ba ni baa Raye ba,Zinatu duk akan Ina san na dawo da dana kan hanya mai na miki a rayuwar nan Zinatu,laifina shine haifar Habun da nayi kika gan shi da hakoransa tallatin baki san wahalar da na sha akan sa har ya kawo wanan matakin da ya zama mutum ba,kika ce ni din ma baki da burin da ya wuce kiga kin Kau dani mai na miki”?

“Gwaggo bansan zaki Dade har haka ba wallahi bansan zaki Dade a kwance ba a lokacin gani nake kin takurani baki da burin daya wuce kiga kin rabani dashi,a lokacin gani nake baki da burin da ya wuce kiga ya min kishiya shi yasa nayi abinda nayi “

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun innalillahi wa inna ilaihi rajiun yanzu dama kina da hannu a kwanciyar da Gwaggo tayi”?

Habu yace cikin tsananin tashin hankali tare da mik’ewa tsaye.

Gwaggo kuwa da ta rufe fuskarta da tafin hannunta ta hau sheshekar kuka dan zargin Zinatun kawai tayi take so ta tabbatar da zarginta bata kawo da gaske Zinatu zata iya mata wanan zaluncin ba.

Habu kuwa da yaji ya kasa jurewa ya Isa gaban Zinatun da balain gudunsa ya Shaketa Yana rantsuwar sai ya kasheta.

Sai zuba mata naushi yake da dayan hannun Yana ta cuce shi Allah ya Isan sa bai yafe ba ya saketa saki uku

Bai saki Zinatu ba duk da k’ok’arin da su Sule ke tayi dan ya saketa sai da yaga ta daina motsi

Ya saketa yana fatan Allah yasa ma mutuwa tayi.

Gwaggo kuwa sai fada take masa akan yanzu idan ya kasheta fa bashi da hankaline.

Sai da Hanne ta jika Zinatu da kyau ta farfado daga sumewar da tayi.

Ta hanyar sheshekar kukanta suka gane ta farfado

Gwaggo kuwa dakinta ta shige Habu Kuma ya fice daga palon dan bama ya palon ta farfado Koda ya fita Yan sanda ya kira a waya ya kulle gate din dan idan ba kulle Zinatu aka yi   ba ba zai tab’a samun kwanciyar hankali ba.

Bai koma ciki ba sai da Yan sanda kuwa suka zo yayi musu jagora zuwa ciki.

Zinatu kuwa sai ihuu take tana a yafe mata.

Shamsiya kuwa ganin Habu Yama fita daukar zafi shi yasa bata Kara k’ok’arin yin wani Abu ba,dan ita har ta d’auki shawarar Gwaggo na a rabu da ita ma ba sai an kulleta ba,iya tonuwar da asirin ta yayi ya Isa ya hanata samun nutsuwa.

Zinatu kuwa tozalin da tayi da Yan sanda yasa ta mik’ewa da sauri ta fara k’ok’arin Neman wajen buya,dan idan akwai abinda take tsoro bai wuce wai yau taga taje hannunsu ba.

Habun da duk akan sa ta aikata duk abinda ta aikata shine kan gaba wajen kamota ya kawo ta wajen yan sandan suka Saka Mata ankwa suka yi waje da ita tana ji tana gani aka jefa ta a bayan mota ganin dai da gaske dai station zaa kaita.

Cikin wani irin zafin nama ta faki idon yan sandan ta duro daga bayan motar dake sharara gudu,wani mota dake biye dasu yayi sama da ita…..

*Page 49*

  Zinatu

               A hankali ta mik’e tsaye cikin wani irin tsoro da faduwar gaban da bata tab’a ji ba dan rawar da jikinta ya d’auka yasa ta zube a kasa da taji Gwaggo tace Yan biyun da take wa kallon yayan barrister Aisha wai yaran shamsiya ne.

Jikinta wani irin rawa ya d’auka da tayi tozali da Shamsiya da ta gaji da haduwa da kyau ko a duhu ka ganta kasan hatimin nassara ya zauna,duk da shekarun da aka d’auka ba zata kasa gane ta ba,dan tsanar da ta mata yasa fuskarta ya zauna a kwakwalwarta.

Murmushin da shamsiya ta sakar mata tana ” Wai ko dai baki gane ni bane Zinatu?Nice dai Shamsiya da kika sa Ayuba ya Kona ni da ciki da imtihal,kika shigo kika d’auki Yarki kika dan konata a Kai saboda kar a dago ki.

Zinatu gani a rayye da imitihal da Yan biyun da kika so kar su shaki iskar duniya,yau gamu nan a gabanki”

Zinatu girgiza kanta ta hau yi da sauri ta fara ja da baya tana mursika idonta dan gani take tab’in hankali ta fara samu ba yadda za’ayi ma shamsiyar da ta kulle a cikin gida ta samu fitowa, tana kallon yadda gidan ke ci da wuta da ta tsaya a bayan gidan.

Bata ga ta yadda Shamsiya ma zata iya fitowa ballantana har wai ta haifi cikin jikinta ba.

A haukace ta fara tsalle tana ihuu “Wallahi wanan fatalwar shamsiya ce,shamsiya ta mutu ita da cikin jikinta da imtihal,sai da na kulle k’ofar ta waje,yadda ma ba zata iya fitowa ba,na koma bayan gidan a gaban idona gidan ya Kone kurmus bata yadda ma zata fito,wallahi shamsiya ta mutu wanan  fatalwar ta ce.

Zinatu tace cikin ihu ta manne a jikin bango tana matse kafarta dan sosai taji cikinta na Murda mata ga fitsari da taji yana neman kwace mata,bata yarda ma shamsiyar bace duk yadda aka yi ma shamsiyar fatalwa ta fara mata kila ma ita kadai ce take kallonta.

Muryar Habu da taji Yana “Zinatu dama haka kike?Yanzu kece da bakin ki kike fadar kin kulle gida saboda kar shamsiya ta samu hanyar da zata fito?Zinatu Yanzu har rashin imanin ki ya kai haka”?

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku na lalace wallahi karya nake bani bace ba”

Zinatu tace cikin ihu da ta gano ma tayi subutar bakin tonawa kanta asiri dan shap ta manta ma da mutane a palon ta hau tonawa kanta asiri.

“Kull karka sake ka tab’a ta koma ka zauna”

Gwaggo tace da taga Habu ya mik’e cikin zafin nama dan yadda yake Jin tsanar  Zinatu gani yake ba abinda zai saka ya ji sanyi a zuciyarta sama da ya rabata da numfashinta,Kuma yadda yake gwara ya kasheta kawai a kulle shi,dan cutar da Zinatu tayi mi shi yayi yawa.

Duk sai a yanzu ya gane wasu Abubuwan da yake ta aikatawa duk ba’a cikin hayyacinsa yake ba,yau da Allah bai bashi jajirtaciyar uwa kamar Gwaggo ba kila  da ta zuciya wajen yi masa baki,da kila yanzu ba shi da ma wajen zama dan bada iya Gwaggo ta hada shi ba har da Yan uwansa da Allah ya sa basu da ruko,jiya haka ya zauna ko runtsawa bai yi ba Yana tunanin duk Abubuwan da ya aikata a baya ciki kuwa har da wulakanta Sule da yake jininsa,da ayanzu arzikinsa yake ci.

“Dan Allah Gwaggo ki barni na kasheta ta cutar dani Gwaggo,Koda bata samu nassarar rabani da ke da Yan uwana ba sai da da tayi nassarar rabani da matata,da ta so kashewa,sai da ta sa yarana suka taso tamkar wayanda basu da Uba,suka kwashi shekaru ba tare da sun sani ba Gwaggo mai nayi wa Zinatu da zafi da zata min irin wanan muguntar”?

“Ba zaka kasheta ba Habu,in Sha Allahu ba zaka tab’a kisan kai ba,yanzu godiya zaka yiwa Allah da ya haska ma wacce ita,godiya zaka yiwa Allah da bai bata nassara wajen kashe shamsiya da yaranta ba,yau silar kashe shamsiya da ta so yi yasa shamsiya ta kai matsayin da duk bamu tab’a tunanin zata kai ba ko iya wanan kadai ma ya Isa yasa ka rabu da ita, Abubuwan da ta aikata kawai ma sun isheta,kaga da bakinta ma tazo tana tonawa kanta asiri ko wajen Yan sanda ma aka kaita ba zata wahalar dasu ba”

Tunda Gwaggo ta fara magana Zinatu ta zubawa shamsiya ido har lokacin gani take mafarki take yi zata iya farkawa daga mummunan mafarkin da take ta kasa yarda wai Shamsiya da take tunanin ta shafe labarinta tana rayye ba ita kadai ba har da yaranta guda uku ras,a Sanin da tayi mata a baya ko secondary ba tayi ba,bata da wayewa ko ilimi abinda yasa take ta kwowanton anya Shamsiyar da ta sani ce ita,maganar da taji Gwaggo tayi akan silar abinda ta aikata yasa shamsiya ta taka matsayin da Basu tab’a tunani ba yaja hankalinta,ta fara k’ok’arin hada tunanin ta waje daya,inda taji gabanta yayi wani Irin faduwa da taga shigar dake jikin shamsiya da gwala gwalan hannunta,tsintar kanta tayi da nuna shamsiya da hannu tana “Shamsiya kece barrister Aisha”?

Murmurshi Shamsiya ta saki tana “Bari na baki gajeran labarina dan ya kamata na warware miki komai dan naga kallon da kike min har yanzu kin kasa yarda nice”

Shamsiya sai da ta dora kafarta daya akan daya.

Ta hau bawa Zinatu labarin yadda ta kubuta daga gobarar da silar arzikinta da komai ma ta Kara da “Tun Ina yarinya na taso da san na zama likita idan Allah ya bani dama,sai dai saboda abinda kika min na zabi karantar lawyer dan da kaina nake so na tsayawa kaina wajen sharia da ke,baki wahalar da ni ba,duk maganar da kika yi kin ga nayi recording”

Ihuu Zinatu tasa ta zub’e a kasa ta hau birgima tana Shamsiya ta rufa mata asiri ta yafe mata.

Habu da ke tsaye har lokacin Yana Jin zuciyarsa na tafasa da tsananin tsanarta ya daka mata wani irin tsawan da yasa ta mik’ewa batare da ta shiryawa haka ba yace “Wallahi sai kin kare rayuwarki a kurkuku sai na tabbata da an yi miki hukuncin kissa ta hanyar rataya na!!!!

“Ya Isa haka Yaya Habu akwai abinda nake so na tambayeta idan har ta fadi gaskiya zan roke ku akan ku yafe mata”

Sule yayi wa Habu ido da ya harzuko kamar zai daki Sulen da yaji Yana kawo maganar yafe mata

A ba yadda zai yi Yayi shiru.

Ya koma ya zauna

Sule kuwa ya Kalli Zinatu da ta dora hannunta aka tana kwada sallati yace “Zinatu idan har kika fadi gaskiya yau a gaban kowa zan k’ok’ari naga baa kulleki ba,abin nan ya kasa goguwa a raina,abin nan ya zame min ciwo a cikin zuciyata da idan har zan tuna sai naji tamkar a lokacin abin ya faru”

“Zinatu a shekarun baya kin ce na shiga dakin ki da zumar na miki fyade tsakanin ki da Allah na ni na kawo kaina dakin ki?Kuma nayi yunkurin yi Miki fyade”?

“Wallahi ko bata fada ba Sule nasan sharri ta maka wallahi daga baya dana zauna nayi tunani nasan sharri ta maka”

“Aaa Yaya Habu a duk abinda ta min wallahi ba Wanda ya kasa goguwa a zuciyata sama da wanan duk da nasan duk Wanda ya sani yasan sharri tamin nafi so ta Kara fada a gaban kowa”

Daga haka sule ya Kara Maida kallonsa wajen Zinatu dake tsiyayar gumi kamar an tsoma ta a ruwa tana yarfa hannuwa dan tasan yau duk wani asirinta ya tonu,tunda shamsiya ta bata labarin itace barrister Aisha taji kamar an caka mata wuka a Kahon zuciya,yau da ace tasan shamsiya kudancewa za tayi da bata ma tura Ayuba ya Kona ta ballantana har ta fada hannun Wayanda suka taimaketa ta zama hamshakiyar Mai kudi, Karin tashin hankalinta ma Barrister ce ita,yanzu zata iya sawa a daureta ko a kasheta.

“Zinatu tsakanin ki da Allah nake so ki fada nayi yunkurin yi miki fyade?

“Dan Allah Sule ka yafe min Sharrin shaidan ne,a lokacin na tsani na budi ido na ganka a gidanan na rasa ta hanyar da zan sa ka bar gidan Habu ya koreka wallahi shi yasa na Maka wanan Sharrin dan girman Allah ku yafe min”

Zinatu tace tana rusa Ihun kukan ta shiga uku

Ihunta kawai ke tashi a palon Sule kuwa haka kawai yaji hawaye ya cicciko a idonsa dan sai yaji tamkar a yanzu ta masa Wanan Sharrin da ya masa nauyi a zuciya,duk da Gwaggo da Hanne a lokacin basu tab’a yarda ya aikata hakan ba,amma sai yake Jin ba mai wanke shi yaji dadi a zuciyarsa sama da Zinatun.

Kuma a yanzu da ta fada sai yaji zuciyarsa ta rage masa nauyin da yake ji tun tsawon shekarun nan da aka d’auka.

Habu kuwa ya sunkuyar da Kansa kasa kamar mace ya hau kuka Yana “Allah sai ya tsine miki Zinatu Allah sai ya Kona ki Zinatu ba zan tab’a yafe miki Abubuwan da kika sa na ringa aikatawa ba,Ina Jin kunya idan na tuna fifitaki da nayi akan Mahaifiyata da Yan uwana,har na kasa yadda da dan uwana na biye miki Zinatu wallahi ba zan tab’a yafe miki ba Zinatu”

“Dan Allah ka yafe min Habu a lokacin gani nake,an dora Maka nauyi shi yasa na aikata abinda nayi sanka duk shi ya kaini ga aikata abinda nayi dan Allah ka dubi yarana ka yafe min Gwaggo dan Allah dan Annabi ki masa magana ku yafe min Allah Yana San bayinsa masu yafiya”

“Kinsan Allah ne Zinatu”?

Gwaggo ta jefa mata tambaya tana tuna shekarun da ta kwashe a kwance batare da tasan inda kanta ma yake ba

“Nasan Allah wallahi Gwaggo Allah shi ya hallice mu dan mu bauta masa”

“Baki San Allah ba Zinatu dan da kinsan Allah ba Zaki tab’a tunanin rabani da dan da ni na tsugunna na haife shi na Raine shi har ya zama mutum kika gan shi kika aura ba,dan kawai Ina k’ok’arin ceto dana daga halaka kika shiga kika fita kika kwantar dani Zinatu tsawon shekara goma Sha Ina kwance ni baa mace ba ni baa Raye ba,Zinatu duk akan Ina san na dawo da dana kan hanya mai na miki a rayuwar nan Zinatu,laifina shine haifar Habun da nayi kika gan shi da hakoransa tallatin baki san wahalar da na sha akan sa har ya kawo wanan matakin da ya zama mutum ba,kika ce ni din ma baki da burin da ya wuce kiga kin Kau dani mai na miki”?

“Gwaggo bansan zaki Dade har haka ba wallahi bansan zaki Dade a kwance ba a lokacin gani nake kin takurani baki da burin daya wuce kiga kin rabani dashi,a lokacin gani nake baki da burin da ya wuce kiga ya min kishiya shi yasa nayi abinda nayi “

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun innalillahi wa inna ilaihi rajiun yanzu dama kina da hannu a kwanciyar da Gwaggo tayi”?

Habu yace cikin tsananin tashin hankali tare da mik’ewa tsaye.

Gwaggo kuwa da ta rufe fuskarta da tafin hannunta ta hau sheshekar kuka dan zargin Zinatun kawai tayi take so ta tabbatar da zarginta bata kawo da gaske Zinatu zata iya mata wanan zaluncin ba.

Habu kuwa da yaji ya kasa jurewa ya Isa gaban Zinatun da balain gudunsa ya Shaketa Yana rantsuwar sai ya kasheta.

Sai zuba mata naushi yake da dayan hannun Yana ta cuce shi Allah ya Isan sa bai yafe ba ya saketa saki uku

Bai saki Zinatu ba duk da k’ok’arin da su Sule ke tayi dan ya saketa sai da yaga ta daina motsi

Ya saketa yana fatan Allah yasa ma mutuwa tayi.

Gwaggo kuwa sai fada take masa akan yanzu idan ya kasheta fa bashi da hankaline.

Sai da Hanne ta jika Zinatu da kyau ta farfado daga sumewar da tayi.

Ta hanyar sheshekar kukanta suka gane ta farfado

Gwaggo kuwa dakinta ta shige Habu Kuma ya fice daga palon dan bama ya palon ta farfado Koda ya fita Yan sanda ya kira a waya ya kulle gate din dan idan ba kulle Zinatu aka yi   ba ba zai tab’a samun kwanciyar hankali ba.

Bai koma ciki ba sai da Yan sanda kuwa suka zo yayi musu jagora zuwa ciki.

Zinatu kuwa sai ihuu take tana a yafe mata.

Shamsiya kuwa ganin Habu Yama fita daukar zafi shi yasa bata Kara k’ok’arin yin wani Abu ba,dan ita har ta d’auki shawarar Gwaggo na a rabu da ita ma ba sai an kulleta ba,iya tonuwar da asirin ta yayi ya Isa ya hanata samun nutsuwa.

Zinatu kuwa tozalin da tayi da Yan sanda yasa ta mik’ewa da sauri ta fara k’ok’arin Neman wajen buya,dan idan akwai abinda take tsoro bai wuce wai yau taga taje hannunsu ba.

Habun da duk akan sa ta aikata duk abinda ta aikata shine kan gaba wajen kamota ya kawo ta wajen yan sandan suka Saka Mata ankwa suka yi waje da ita tana ji tana gani aka jefa ta a bayan mota ganin dai da gaske dai station zaa kaita.

Cikin wani irin zafin nama ta faki idon yan sandan ta duro daga bayan motar dake sharara gudu,wani mota dake biye dasu yayi sama da ita…..

*Page 50*

Zinatu

      “Amjad idan mafarki nake ka tasheni dan Allah,Amjad nice yau aka yankewa kafa biyu?Yanzu shikenan na zama gurguwa Amjad?

Amjad kace min mafarki nake Babanku ba sakina yayi ba akan shamsiya.

Amjad kace min mafarki nake ba shamsiya na gani a rayye da yaranta har guda uku ba

“Amjad kace min mafarki nake ba Shamsiya ce Barrister Aisha ba,kace min mafarki nake ba itace ta zama attajira ba?

“Ka tasheni daga Wanan mumman mafarkin Amjad”

Zinatu tace cikin Ihun kuka kafafunta biyu yanke ya Sha bandeji

Amjad da ya buga tagumi a gefenta yabi ya fita a hayyacinsa saboda zirga zirgan da yake daga wajen aiki zuwa asibiti wajen duba Zinatu da ke cikin comma tsawon wata daya sai yau ta farka tayi tozali da kafarta dake yanke banda dinkunan da ta Sha a fuska da hannayenta dan ba Karamin kudi ya kashe a asibiti ba dan raga raga motar tayi da Zinatu da ba ma kawo zata rayyu ba.

Jawaheer ya kalla dake can gefe tana latsa wayarta cikin hade rai da yasan dalilin hade ran nata wai ta gaji da zuwa ta zauna a asibti wajen Zinatun Wanda har ga Allah zuwa yanzu ya fara Jin haushin Jawaheer din.

Sati biyu kenan da komawar Amrah gidan Bashir bayan Mahaifiyarsa tazo ta bawa Habu hakuri akan bata kasar ne shi yasa bata san mai ke faruwa ba.

Habu kuwa cikin tsananin murna yace mata ba komai a satin aka maida Auren Amrah dake ji kamar an mata bushara da gidan Aljanna dan bata da burin daya Wuce dama ta koma dakinta tunda har Allah ya taimake ta ta warke da sai da taje har gidan Ameera ta mata godiya dan Gwaggo ta fada mata cewar Ameera ce ta roki mallamin akan ya karya asirin da aka mai da mata.

Bayan godiyar da ta mata sai da ta hada da Neman yafiyar Ameeran dan tasan sun musu abubuwa a baya da a yanzu take Jin kunyarsu idan ta tuna.

Tun suna Yara Zinatu ta koya musu tsanar su Ameeran har zuwa girmansu haka suka tashi da tsanar ganin su Ameera na walwala daga d’aukakar da Allah yayi wa Ameera zuwa canjin rayuwar da iyayenta suka samu da duk ma cikinsu ba Wanda ya samu niimar Ameeran da suka taso da burin ta wulakance sai gashi Allah ya tsaya mata yau su din da suke Jin sun fi su yau basu isa ma taka matsayin da suke ciki ba dan sune ma suke cin arzikinsu.

Koda ta zo tahowa haka Ameera ta hada mata goma Sha Tara ta arziki bata duba duk abinda ta mata a baya ba.

Kamar a mafarki Kuma sai ga Mahaifiyar Bashir tazo akan komawarta dakinta Wanda bata sake cikakken bacci ba saboda murna har sai da aka maida Auren ta da Bashir da yazo daukarta.

Habu da sule suka hadu suka musu wa’azi suka tafi.

Inda ta yanke zata ringa zuwa duba Zinatun dake asibitin dan Ji ta ringa yi ma a ranta Zinatu ce ta ringa jefa su a masifa bata shiga wani damuwar tashin hankali da halin da take ciki ba dan a yanzu duk ta gane Zinatu ce ta jawo musu wanan masifa ta Kuma jawo mata.

“Ba mafarki kike ba Hajiya da gaske ne duk abinda ya faru yau ga irin abinda na dade Ina fada miki Hajiya wai har ace zaki iya kashe mutum,yanzu dan Allah wa gari ya waya.

Tun Ina yaro nasan duk Abubuwan da kike yi ba daidai bane ba Hajiya,yanzu banda wanan hatsarin da kika yi wallahi da kina can a kulle”

Amjad yace cikin kasa da murya saboda kar Jawaheer taji dan har ga Allah Yana Jin kunyar Abubuwan da Zinatu ta aikata a matsayinsa na dan cikinta.

Habu har ikirari yayi akan zai tsine masa idan ya Kara masa maganar Zinatun da yake so yayi ta nema mata yafiya a gurinsu dan har ga Allah uwa ba wasa bace ba.

Gwaggo da shamsiya da bai tab’a tunanin zasu ce sun  yafe wa Zinatun ba sun ce sun yafe dan a iya halin da Zinatun ke ciki idan har kana da Imani dole ka tausaya mata dan zuwan da Gwaggo tayi da shamsiya dubata sai da suka girgiza da ganin yadda ta rasa kafafunta biyu ban da dinkuna da ta Sha.

Gwaggo kuwa sai sallati take tana tun a gidan duniya kenan Ina ga anje lahira lailai Allah tun a gidan duniya  yake hisabi idan aka ce akwai ranar da za’a wayi gari aga Zinatu ta dawo haka ba mai yarda.

Sule Kansa baa bar shi a baya ba dan sai da yazo da Hanne asibitin ya dubata,halin kawai da ya ganta a ciki yasa shi cewa ya yafe mata duk abinda ta masa daya zo tafiya ya bawa Amjad kudi mai yawa dan shi ne ke tsaye akan Zinatun

Habu kuwa ko sunan Zinatu baya so yaji an kira ma,saboda tsananin tsanar da ya mata duk da   shamsiya tana ta k’ok’arin kwantar masa da hankali tana jawo shi jikinta dan ya rage damuwar da yake ciki  Na sultana da aka samu aka saketa dak’yar bayan an damko shamsu saurayinta.

Sai dai dawowar sultana da sati biyu Suka gano tana d’auke da ciki.

Gashi da tsakar dare sai sun ganta da kayan shaye shaye.

Gajiya da Habu yayi yasa ya watsa sultana waje dan duk sun koma gidan shamsiyar da sai da aka yi da gaske Gwaggo ta sa baki ya koma dan sai yake Jin banbarakwai wajen komawarsa gidan shamsiyar Wanda hakan da Shamsiyr ta gani akan Yana baya ne saboda bashi da kudi yasa ta nuna masa bacin ranta.

Sai a lokacin ya saki jikinsa a cikin manyan gidajen manta ta bashi ragamar kula da guda daya da akasan ranta mallaka mi shi tayi so take sai an kwana biyu sai ta bashi takardun gidan man.

Duk yadda Shamsiya ta so shawo Kansa akan Korar sultanar da kullum a buge take, ki yayi yace ba zai iya da abun kunyar da sultana ke jawo masa ba,gwara ta shiga duniya.

Shamsiya kuwa ganin sultana ma bafa wani daidai take ba dan kamar baa abinda ke ma sama mata nutsuwa sama da kayan. Shaye shayen.

Da sai daga baya ma ta gane satar mata kudi take wajen siyan kayan mayen.

Inda ta sa sultana agaba suka je gidan Sule.

Ta fada musu Korar da Habu yayi wa sultana.

Gwaggo kuwa na k’ok’arin magana sule ya ce mata kar ta damu su zasu rike sultana ai sultana Yar sa ce.

Yadda sultana ta koma gidansu Sulen kenan.

Shi da Hanne suka tsaya tsayin daka wajen ganin sun hana ta shaye shayen

Amjad kuwa hakan da ya gani yasa ya roke su akan su bar shi ya kai ta asibiti a zubar mata da cikin jikinta dan indai ta haifo musu shege a zuria zata bata musu Suna.

Sule da Gwaggo kuwa suka ce ba zasu yarda ya zubar da cikin ba ta hanyar da Allah ya kaddara zata samu cikin kenan.

Zinatu rufe idonta kawai tayi ta cigaba da sheshekar kuka

Ba Abunda take hararowa sama da shamsiya da a yanzu ta mata nisa ta Fi karfinta ko ta Ina.

Duk zuwan da take wajen Natete bai tab’a duba mata yace mata shamsiya na Rayye ba.

Ta tuna irin kudaden da ta kashe da irin morar da Natete ya Mata da tunda ya fara saduwa da ita ta daina jinta daidai.

Kuka ta Kara rushewa dashi tana “Amjad Natete ya cuceni ya yaudareni ba zan tab’a yafe masa ba duk inda na kai ga na Kashe kudi dan ya mallaka min Babanku yak’i min aiki,haka ya sani a gaba ya ringa saduwa dani Yana yaudarata wallahi!!!

Amjad hankali a tashe ya rufe mata bakinta da hannu biyu har gabansa na faduwa da irin maganganun da ke fitowa daga bakin Zinatun

Sallatin da jawaheer ta kwada tana tafa hannuwa yasa shi kallonta da jajjayen idonsa.

Jawaheer kuwa ta cigaba da tafa hannuwa tana kallon Zinatu ganin Amjad na kallonta da jajjayen idonsa yasa ta furta Allah ya kyauta ya shirya.

Zinatu kuwa ta cigaba da mutsu mutsu da Kai saboda matse mata bakinta da Amjad yayi.

Amjad da ke Jin maganar da Zinatu tayi na manna a kansa har lokacin ya matsa kusa da Zinatun Yana “Bani kadai ne a  dakin nan ba Hajiya ki daina tonawa kanki asiri ki daina magana.

Fusge hannun Amjad tayi daga bakinta ta bud’e idonta tana “Wane asirine ya rage min da zai rufu tunda har asirina ya tonu a gaban makiyana ai gwara kowa yasan mai na aikata ke Jawaheer karki sake ki tab’a yarda da bokaye wallahi duk makaryata ne sau uku Natete yayi amfani dani amma ban ga wani biyan bukata ba

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun innalillahi wa inna ilaihi rajiun

Amjad ya Kara kaiwa bakin Zinatun Cafka ya matse Yana Jin kamar zuciyarsa ta tarwatse saboda tsanin bakin ciki.

Cikin rawar murya ya kalli  Jawaheer Yana “Dan Allah ki kira min likita ya Mata allura duk maganar da take a yanzu baa hayyacinta take ba”

“Karka wayance da baa hayyacinta take ba wallahi kalau take abinda ta aikata take fada dan ba Wanda bai san biye biyen da take ba,har wai ace saboda ka mallaki miji zaka bawa Boka kanka gaskiya Baby na tausaya muku wallahi baku yi dace da uwa ta gari ba gaskiya ban da Ina sanka wallahi da sai na rabu da Kai tirkashi.

Daga haka tayi waje A daidai lokacin da hawayen daya cika idon Amjad suka zubo ya saki bakin Zinatun da ta cigaba da maganganun kamar dai wacce ta samu tabin hankali dan sai tonawa kanta asiri take,yau banda yasan darajar uwa da sai ya Nisanci Zinatu kamar yadda kowa ya gujeta.

Amma ba zai iya ba dan ko Yan uwanta ma ba Wanda ya zo tunda duk ba uwa da Uba gareta ba sai Yan uwa,a matsayin sa na babban danta ba zai iya juya mata baya ba a daidia wanan lokacin.

Ganin idan ba alluran aka mata ba haka zata ta fadar maganganun da ke neman tarwatsa masa zuciya dan ma Allah ya rufa masa asiri Jawaheer ta bar dakin,yasan daga Rana irin ta yau ba lailai Jawaheer ta Kara wani mutunta shi ba.

Haka yaje ya kira likita yazo ya Mata alluran bacci.

A ranar sai Samha wata nurse ya bawa kudi dan ta kula da ita dan ya gaji sosai Yana bukatar wanka da hutu.

Koda yaje gida a ranar bai ishi Jawaheer Kallo ba inda zuciyarsaa tayi matukar sosuwa

Koda yayi wanka yayi sallah kwanciyarsa kawai yayi a dakinsa Yana tunanin abinda ya dace yayi akan lamarin Zinatu.

Dan yasan dole a sallameta daga asibiti koman daren dadewa Kuma daga yadda yake gani ba mai iya riketa sai shi.

Inda matsalar take tun yanzu Jawaheer ta canza masa akan rashin lafiyarta Ina ga yanzu da Zinatu ta Kara tonawa kanta asiri a gaban Jawaheer din.

Haka ya kwana Yana juyi da tunanin ko dai gidan Sulen zai je ya roki arizki akan su riketa ya ringa daukar nauyin duk wani abu da ya shafeta.

Sai Kuma yaga rashin dacewar hakan dan abun zai yawa tunda suna rike da Sultanar ma da suke fama da ita idan ya Kara da Kai musu Zinatu abin zai yi yawa.

A haka ya bar wa zuciyarsa rike ta ya cigaba da zuwa duba Zinatun da ya lura ta dan samu tabin hankali dan haka kawai sai ta kece da dariya ta hau rantsuwar shamsiya fa ta mutu a gaban idonta gidan ya kone.

Kafin ya samu likita ma da maganar maganin da zaa bata ta bar wanan kananan maganganun likita ya bashi takardar sallama ya Kara da bashi shawara akan ya kai Zinatu asibitin mahaukata.

Haka Amjad ya tattaro Zinatu ya dawo da ita gida dan ba zai iya kaita asibitin mahaukata ba dan yasan kila idan ya kaita ta Kara haukcewar.

Sai dai Koda ya iso gida Jawaheer murzawa idonta toka tayi tace ba dai a gidanta Zinatu zata zauna ba sai dai ya nema mata wani wajen.

Amjad duk da bakin cikin Rashin mutuncin da Jawaheer ke ta gwada masa daga lokacin da Zinatu ta kwanta a asibiti haka ya danne zuciyarsa dan a yanzu sosai ya fara nadamar ma yarda da yayi ya zauna a gidanta dan da ace bai zauna ba da bata isa ma Yi masa Iko da gidan ba.

Haka ya Kara kinkimar Zinatu suka bar gidan Jawaheer nata zuba kananan maganganun da suka ringa Sosa zuciyarsa.

Bai zame ko’ina da Zinatu ba sai gidan wata yayarta inda ya roketa akan nan da kwana biyu zai zo ya d’auketa.

Nan ma yayar sai da ta tubure akan ba zata karbeta ba,dan Zinatu ba Karamin rashin mutunci tayi mata ba,akan tana auren Mai kudi,ba kuma ita kadai ba Rabin dangi ma ba Wanda take zumunci dashi saboda kawai suna da kudi a wanan lokacin.

Amjad sai da yayi ta hada ta Allah da Annabi kafin ta yarda da kyar tana ya tabbata nan da kwana biyu yazo ya d’auketa.

Kansa kamar zai fashe dan ciwo dan bai Kara samun nutsuwa da kwanciyar hankali ba tunda Zinatu ta kwanta.

Koda ta tashi gidansu Abba sulen ya nufa,dan har gobe dashi yake iya shawara sosai dan har ga Allah ya gaji da rashin mutunci Jawaheer.

Sai da yaci ya koshi ya huta suka dan tab’a hira da Gwaggo da awajenta yake Jin labarin iirn hidimar da shamsiya ke yi danginta da dangin su Habun.

Dan tunda ta bayyana dangi suka san tana rayye aka gama koke koke da  murna Shamsiya ta biya kudi aka Kai Mahaifiyar ta waje ita da mahaifiyar Hanne akan a duba lafiyarta idan ta samu sauki Kuma su wuce umara su huta.

Dangi kuwa na kusa da na nesa duk Wanda dai yazo ganin shamsiya sai Shamsiya ta musu babban kyauta.

Daidai da makota sai da suka ci arizkin shamsiya.

Sai addu’oi take Sha ko ta Ina.

Ayuba Kansa jarri ta bashi da haka ya ringa zuwa mata godiya dan ta canza masa rayuwa.

Sai da gwaggo ta gama bashi labari ta kuma hau tambayarsa lafiyar Zinatu.

Anan Amjad ke bata labarin halin da yake ciki game da jawaheer akan Zinatun.

Gwaggo kuwa ta hau masa fada akan kar ya sake ya tab’a biyewa Jawaheer ya wulakanta mahaifiyarsa uwa ba wasa bace ba ta bashi shawara akan kar ya sake ya tab’a biyewa Jawaheer.

Amjad kuwa ganin gwaggo bata nemi ma a kawo Zinatu gidan ba yasa ya yanke shawarar abinda ya dace yayi

Sai da yazo tafiya yaga sultana da cikinta tana ta cin tuwo ga Hanne a gefenta da alama ma Hira suke

Sai yaji wani irin sanyi a zuciyarsa dan ba zai iya fadar dadin da yaji da irin rukon da Su Sule suka yiwa sultana ba dan a yadda yaga sultanar ma har ta nutsu dan yaji ma yanzu Fareeda ke koya mata karatu itama ta nemi yafiyar su Ameera dasu Hannen.

Kwana biyu a tsakani ya samu gidan haya ya kama Mai kyau ya zuba furnitures da komai dan shamsiya ta bashi babban aiki a wani companyta ban da kudin da ta bashi Mai yawa.

Sai da yaga ya zuba duk wani abin bukata ya nufi gidansa fuska a hade.

Koda ya Isa Yana dab da shiga palon yaji yo muryar Jawaheer tana gulmar Zinatu da wata Jin iirn zagin da take wa Zinatu yasa ya kasa jurewa Ya shiga ciki fuskarsa a balain hade bai ko Kalli Jawaheer da suka firgita da ganinsa ba ya wuce dakinsa ya hau hada kayansa a akwatinsa.

Sai da ya gama kwashe iya kayansa.

Ya yagi wani takarda ya rubutawa Jawaheer saki daya.

Ya ajiye akan gadon

Ya hau kinkimar akwatunan Yana kaiwa mota bai ko Kalli Jawaheer da ke ta tambayar sa Ina zai Kai kayan ba sai da yaje duakar na karshe yaci karo da ita a bakin k’ofa.

Sai yaji kamar bai tab’a Santa ba,duk da yasan Mahafiyarsa ta aikata abubuwa ba Wanda ya Kai shi Jin ciwon abinda tayi amma ba zai so ace wata Kuma ta ci mutuncinta ba.

Kan gadon kawai ya nuna mata ya sa Kansa ya fice daga dakin

Dama Habu ya Dade da Maida masa motarsa dan sabuwar mota shamsiya ta siya masa

Ba wani abun Jawaheer da ya d’auka balle ta masa gori.

Yana kallon sadda ta nufo wajensa aguje tana ita zai Saka Mai Tai masa.

Shi kuwa Yaja glass din motarsa sama ya ja motar ya fice daga gidan.

Ameera…

*Page 51*

Ameera

       A katon makarantar da ta bud’e na koyar da dinki  Yareema yayi parking din motarsa da sai da tayi da gaske Yareema ya barta ta Bude makarantar koyar da dinki dan gani yake bai kamata ace matarsa na abinda zai wahalar da ita ba,ganin ma Allah ya rufa musu asiri ba  wani Abu suka nema suka rasa ba.

Ganin Ameera bata da buri da mafarkin da ya wuce ta Bude makarantar koyar da dinkin tunda ya hana ta Dinkin bayan ta biyo ta hannun gimbiya da itama ta roke shi akan ya barta ta bud’e din tamkar tana so ta taimakawa Mata ne wajen samun koyar Sana’ar hannu da zasu taimaki kansu dashi.

Da wanan Yareema ya kera mata wani katon Makarantar koyar da dinki.

Ameera kamar ta Goya shi haka take ji dan tana so taga itama an karu da baiwar da Allah yayi mata da silar dinki da kunshi yau ta kawo wanan matsayin da take.

Wajen Bud’e makaranta koyar da dinkin manyan mutane da yawa sun halarta har da gudumawar su da suka ji Ameera zata kwashi dalibai wajen Dari biyu kyauta.

Nan ma idan za’a yaye daliban  za’a basu  kyautar keken dinki.

Ba Wanda bai samu halarta bikin Bude makarantar ba a cikin dangi.

Yanzu Ameera sai ta zama abin alfahari a wajen kowa ciki kuwa har da Gimbiya da shi Kansa Yareema da bai kawo abin zai burge mutane haka ba.

Dan da gaske ta taimakawa marasa k’arfi wajen koya musu Sana’a duk da ba keken zata na hawa tana koyar da dalibai ba,ta samu ma’aikata da suka kware a dinki maza da Mata da albashin da zata na biyansu duk karshen wata.

Ita kuma zata na rubutu suna koya kafin ma’aikantan su  Koya musu practical.

Sosai take Jin dadin yadda take Shan addua a wajen mutane.

Ta Kai hannu zata Bude motar bayan ta manna wa Yareema kiss a kumatunsa na sai ta dawo.

Ya ruko hannunta ya kura mata ido Yana kallonta kamar a ranar ya fara ganinta.

Murmurshi ta sakar masa cikin dan Jin kunya tana “Ko dai na hakura da shiga ne mu juya mu koma gida”?

Girgiza Mata Kai yayi Yana “Daliban ki Suma suna bukatar ki kije kawai sai nazo d’aukar ki”

Ya dan yamutsa fuskarsa Ameera kuwa ta Kara damke hannunsa da ke cikin nata tana “Wai ciwon kan ne har yanzu”?

Gyada mata Kansa yayi ya kai hannunsa wajen mararta Yana “Kema Kinsan nayi hakuri wata wajen guda rabona dake”

Murmurshi  Ameera tayi cikin Jin kunyar Yareeman da a yanzu ne ta dago kananan rashin lafiyar da yake wajen wata uku ta fara ganin canji a jikinta ta hanyar kib’a da kanana laulayi da kwadayi.

Inda Yareema ya hau murna ya dauka ciki ne da ita.

Dan ta lura Yana da san Yara tun ma da komai ya daidaita a tsakaninsu ba shi da maganar da ya wuce samun cikinta.

Sai dai yadda take ganin jini na mata wasa yasa ta San ba cikine da ita ba.

Dan tasan mace Mai ciki bata fiye period ba.

Bata dai fada masa ba tayi test a b’oye taga ba cikin ne da ita ba.

Inda ta hau mamakin mai ke sata kwadayi haka alamomi dai na masu ciki.

Dan sosai take kwadayin Abubuwan da Yareema take sawa ya siyo mata inda shi kuwa komai take so sai ya samo mata duk ya d’auka ciki ne da ita.

Sai ta shiga damuwa dan ita kanta tasan ba lafiya ne da ita ba a haka ta yanke zuwa asibiti dan a dubata sai dai ko da ta je asibitin magunguna kawai suka hada mata basu fada mata takamaiman abinda ke Saka ta kwadayi kamar Mai ciki ba.

Ko da ta zo Kuma tana amfani da maganin sai jini ya hau mata wasa a haka Yareema ya gano ba cikin ne da ita ba.

Ganin an tafi wata biyu tana fama har dasu rashin bacci yasa ta fara tunanin ko dai larurar tata bata asibiti bace ba har gabanta na faduwa da ko jifanta aka sake yi.

Dan yanzu Yareema Yana cikin damuwar halin da take ciki tunda baya iya b’oyewa.

Ameera taji dadin haduwarta da Nurse Nasiba dan itace ta dora ta akan Abubuwan da za tayi dan ta magance cutar.

Allah cikin ikonsa kuwa ta fara ganin canji sosai a jikinta.

Yareema Kuma tunda ta fara magani ya daga mata Kafa duk da ba wai jinin take ba a yanzu Al adarta ma ya daidaita.

Ita kanta yanzu bata da burin da ya wuce ta ganta da cikin ko dan farin cikin Yareeman.

“Nasan kayi hakuri ai bansan abinda ke saka ka  zazzabi kenan ba da tuni na baka magani bari na dawo”

Ameera tace tare da kashewa Yareema ido daya saki murmurshin Jin dadi ya jawota ya rungumeta ya mata radda a kunne da ya sa Ameera rufe idonta da sauri dan taji kunyar abinda ya rada Matan.

Kullum sai ta godewa Allah daya bata Yareema a matsayin miji,dan bata Jin zata samu miji mai Santa kamar shi ba Abunda baya mata na kyautatawa gashi bashi da girman Kai kamar bai hada jini da sarauta ba.

Har ta shiga Aji ta koyar da Dalibanta murmushi bai yanke a fuskarta ba.

Taso sai hudu ta baro makarantar amma farantawa Yareema da take so tayi yasa ta koma gida inda ta fara Shan maganin Sanyi mmn mujaheed kafin ta turare jikinta da turaren Umsad gidan Kansa tashin kamshi yake banda maganin gyaran da ta dirkawa kanta dan ita kanta tayi kewar Yareeman sosai,kunya ce take hanata nuna masa bukatar ta.

Irin shigar da yake so yaga tayi na kanana kaya  tayi.

Wajen karfe hudu ta kira shi a waya dan tasan kila zai iya zuwa makarantar d’aukarta

Yana kuwa d’auka yace mata Yana hanya zai zo ya d’auketa tace masa ya taho gida ta dawo.

Kamar wani ango haka ya shigo da kaya niki niki a ranar sai da suka tuna Daren amarcinsu.

Wata daya tsakani Ameera ta fara laulayi Mai zafi Yareema kuwa har da tsallensa dan shi da ya kaita asibiti da kansa likita ya tabbatar masa da ciki ne da ita.

Abin nema ya samu,duk da cikin yazo wa Ameera da laulayi Mai zafi haka Yareema ya ringa lalabata kamar kwai,sosai ya kwallafa rai da cikin Ameeran inda cikinta na cika wata hudu ya fara siyan kayan jarirai yana yasan namiji zata haifa Kuma sunansa zai sa masa.

Murmurshi kawai Ameera ke yi dan har Hira Yareema ke yi da cikin wai Yana magana da dansa.

Gimbiya kanta hidima kawai take da ita duk wani abu da masu ciki ke so cikin yi mata aikensa take.

Ameera kam bata wani ci buri ba kullum fatanta Allah yasa ta haihu lafiya dan ko da su Hanne suka tafi Hajji gabadayansu har da su Abba Ibrahim sai da tace su mata adddua sauka lafiya.

Cikinta na shiga wata biyar Daren Alhamis Yareema ya tashi da wani irin ciwon ciki da ya daga mata hankali dan karfe ukun dare  ya tashi ya ringa sallati Yana cikinsa.

Har suka Isa Asibiti Yareema sallati kawai yake,kafin kace me an cika asibitin dan Labari yaje wa Gimbiya.

Ameera kuwa dauriya kawai take dan zazzabi ma taji Yana Neman rufeta banda wani irin tsoro da taji Yana shigarta,Dan kwana biyu kenan Yareema na ce ma ta Anya Yana rayye zata haihu.

Lafiya lau suka kwanta daren jiya wajen daya da rabi na dare ya tashi yayi nafilar da ya Saba ya koma ya kwanta.

Duk da likita yace musu ya samu bacci sun shawo kan matsalar bata ji hankalinta ya kwanta ba.

Gimbiya kuwa sai ta dage akan ta koma.gida ta huta ai tun ma Yana Saurayi yana fama da irin wanan ciwon cikin.

Dak’yar ta yarda ta koma bayan Yareema ya farka ya daura alwala a gaban idonta sai da taga ya tadda sallah tabi bayan jakadiya dan su tafi gida dan Gimbiya ta dage akan ta tafi gida.

Koda ta isa gida ma sai taji wani sabon zazzabin ya sake rufeta gabanta sai faduwa take.

Dak’yar ta daura alwalar azahar tayi sallah ta zauna akan sallaya ta hau Jan carbi ita kanta bata san me yake damunta ba.

Haka nan take Jin zuciyarta ba Dadi.

Duk yadda jakadiya taso taci abincin da ta zuba mata kasa ci tayi rawar da taji jikinta nayi yasa ta kwanta akan sai ta sallaci sallah la’asar sai ta Kara komawa asibiti.

Karfe uku da minti ashirin daidai taji gabanta yayi wani Irin faduwa da yayi daidia da lokacin da taji yo kukan ambulance.

Bata ma iya mik’ewa ba taga wata kanwar Gimbiya ta shigo da jajjayen idonta da zuwanta ta ruko hannunta ta fara k’ok’arin tayar da ita tsaye dan ta kaita daki dan a Palo take zaune.

Kukan da ta Jiyo daga waje kasa.kasa da gawar Yareema da aka shigo dashi yasa taji dakin na juya mata sai da ta zube a kasa still ganinta bai dawo daidai ba taga an wuce da Yareema Karamin palonsu ta Jiyo muryar wani na ” Mai kaunar Yareema ba zai kuka ba dan ya mutu a babbar Rana ta juma’a Kuma gashi a cikin halin sallah Allah ya d’auki ransa”

Abinda kunnenta Suka Jiyo mata kenan kafin hankalinta ya gushe.

Mutuwar Yareema ta girgiza dubanin mutane.

Da ba ma makusancinsa ba.

Duk wanda zai budi baki sai dai ya fadi alherinsa.

Gimbiya kuwa sai Allah ya bata jarumtaka ita ta koma kwantarwa Ameera hankali

Ameera kuwa har aka yi arbain gani take mafarki take zaa tasheta ace mafarki take yi yareeema ba mutuwa yayi ba,ta kasa yarda yadda ya kwalafa rai akan cikin jikinta ba zai samu ganin jininsa ba.

Kamar zata zauce sai da karfin addu’a da su Sule da gimbiyar suka dage dayi  ta dan fara dawowa daidai, tuni Ameera ta zama wani irin  shiru shiru,duk da bata gidan Yareeman ta koma wajen Gimbiyar da itama tayi wani iirn rama  da alama ita damuwarta ta ciki ce.

Daga Gimbiya har Ameeran sai ka rasa Wanda zaka tausayawa a cikinsu biyun.

A haka cikin Ameera ya cika wata tara ta haifo katon yaron da ba inda Ya baro yareeema kamar anyi kaki an ajiye.

Haihuwar da Ameera tayi da tozalin da tayi da Yareema Karami da aka maida masa sunan yareema ake kiransa mufeed ya fara rage mata damuwar da take ciki.

Gimbiya kuwa sai take Jin kamar Yareeman ta ne ya dawo.

Mufeed sai ya zama Dan gata gabada baya

Ameera bata kaunar abinda zai sa tayi nisa da mufeed da Allah yasa wa farin jini,Gimbiya kuwa gani take kamar tafi ta san ma mufeed din,haka za tayi ta bata labarin yadda margayi yayi kaza lokacin da yake kamar mufeed.

Gadon Yareema kuwa da aka raba,sai da Ameera ta samu nutsuwa ta kasa rabonta gida uku dan Yareema ya bar dukiya Mai yawa da kusan duk mallakin mufeed ne,a Wanda aka batan ta raba uku ta dau Kashi daya,ragowar Kuma ta gina katon massallaci da rijiya da sunan Yareema

Dan gani take shine kawai abinda zata iya yiwa margayin da tsawon zaman su bashi da burin da ya wuce yaga ya faranta mata.

Musamman take ware lokacin Yi masa addu’a dan har itama ta koma ga Allah bata Jin zata tab’a iya manta shi.

(Yauwa bari na tuna muku a baya na fada muku wajen yareema fiction ne,wani Ameera ke Aura ba Yareema ba,na sa ko harkar sarauta ne haka saboda labarin yayi Zaki,Amma wani daban Ameera ta aura mutuwa ta raba su karku zo kuce Mai yasa na kashe Yareema tsohon mijin ma Ameeran rasuwa yake yi)

2 years later

 Gidan Sule cike yake da mutane dake ta Kai da kawowa dan Yau ake daurin Auren Fareeda da wani Saurayinta.

Can dakin Gwaggo Ameera ce a zaune cikin shigar wani arnen less tana cin pankaso Sultana Kuma na zaune can gefe da Karamin cikinta da bai Fi wata uku ba dan wata shidda da suka wuce tayi Aure,dan tunda ta haifi cikin shegen da Ciro mata shi ma akayi a mace a cikinta ta nutsu sosai,dan Sule da Hanne sun taimaka ainun wajen shiryuwarta inda sai a yanzu ta gane duk rayuwar da tayi a gidansu cikin duhu tayi,ba abinda ta tab’a yi da Zinatu zata kwabeta tace tayi ba daidai ba sallah ma Sam bata matsa musu akan suyi,Dan ilimin da ta samu ta silar Makarantar da sule ya sakata yasa ta gane rayuwar da tayi a baya duk a cikin jahilici tayi shi bata samu uwar da zata dorata akan hanya ba.

Irin rukon da Su Sule suka mata da itama tasan a baya a karamin shekarun ta ta musu rashin kunya ta zagesu duk bisa zugar Zinatu.

Cikin kuka ta Kara neman yafiyar su,ta nemi yafiyar Ameeran da take ganin hassadar da suka ringa mata ne ya zame mata Taki har ta Kai matsayin da Basu tab’a tunanin zata Kai ba,yau ba Wanda ba arzikin Ameeran yake ci ba idan ka d’auke Shamsiya da itama Kau da ita da Zinatun ta so yi ya Kai ta ga wanan matsayin.

Habu kuwa sai a yanzu yasan ya auri mace ta gari duk kudin shamsiya bata tab’a wulakanta shi ko ta masa Iko da dukiyarta ba.

Burin Gwaggo ya cika na San ganin kan yaran nata a hade dan daidai da dan bature shi ma ya dawo da iyalinsa gidan Sulen kowa da part dinsa.

Habu ne kawai baya gidan.

Amjad kuwa ba yadda Jawaheer bata yi akan ya Maida ta dakinta ba yak’i,dan gani yake Jawaheer zata iya zama kamar Mahaifiyar sa wajen san taga ta juya shi kila har ta Kai shi ga halaka.

Dangin Zinatu ma kansu kin riketa suka Yi duk da yace zai Basu kudi,Yana Ji yana gani ya tattara Zinatun ya Maida ta gidansa.

Ya samo Yar aiki da sultana suke kula da Zinatun da tabin hankalinta ma sai abinda yayi gaba,dan sai da ya Kai yanzu sai an daure mata hannu dan har jiwa kanta ciwo take tana rantsuwar sai ta kashe shamsiya ta kashe boka Natete.

Amjad idan akwai abinda ya rage masa Jin dadi bai wuce larurar Zinatu ba dan a yanzu Yana samun kudi sosai,auren yake so ya sake yi Amma ya rasa wacce zai aura dan sultana ta samu mijin Aure yasan idan har tayi auren ba lailai Mai aikin ta iya kula da Zinatun ita kadai ba.

Tunda Ameera ta gama takaba ta yaye mufeed ya fara sintirin zuwa gidansu dan har lokacin Yana balain Santa har addua yake akan Allah ya mallaka masa ita.

Sai dai bai ga a alamar fuska a wajen Ameera  ba, ya rasa yadda zai tunkareta dan har kishin margayi yaji Yana yi.

Gwaggo da ke fama da ciwon suga ga tsufa dan ma an sama mata maganin gargajiya a wajen Aunty zeem da ya taimaka ainun wajen kwantar da ciwon ta Kalli Ameeran da ta gaji da haduwa tana ta cin fankason ta kamar bata da wani damuwa.

Hira suke da sultana sama sama Amrah ta shigo itama da goyanta a baya dan ta sake haihuwa.

Gwaggo kuwa ta kira sunan Ameeran tana “Ameera ya maganar da muka yi dake jiya”?

Ameera tuni murmurshin fuskarta ya bace da ta tuna maganar da Gwaggon ke nufi akan Auren Amjad da aka sakota a gaba akan tayi.

Dan har Abba Sule da Hanne sai da suka roketa akan tunda an tafi shekara biyu har an kusa na uku ga manema nata sintirin zuwa wanan karon ta taimaka ta auri Amjad ta tausaya masa.

Ameera kuwa sam a yanzu ba auren take so ba,dan gani take ba zata samu miji irin Yareema ba,gani take ma san da tayi wa Amjad na shakuwa ne,Wanda ta so Yareema ne.

Tasan dole za tayi Aure amma gani take Yayi kurkusa Kuma har lokacin tana kin auren Amjad ne saboda Zinatun.

“Kinyi shiru kin manna min hauka Ina ta magana ni kadai”

“Gwaggo dan Allah ya nemi wata ya aura dole sai ni zai aura naga ma Mahaifiyar sa ta nuna tun a baya bata so har tsine masa tace za tayi dan Allah ya nemi wata ya aura ni ba yanzu zanyi Aure ba sai mufeed ma ya girma”

“Yanzu zumuncin ne baki so a Kulla ko Ameera yanzu ace ba zan iya rokanki abu kimin ba?toh Babu damuwa Ameera nasan idan na mutu sai kinyi zo kina da kinsani kin faranta min ko sau daya ne ba komai ai lokacina ma ya kusa”

“Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun Gwaggo yanzu Dan naki Zaki fara maganar mutuwa toh naji na yarda kafin ace ni na kashe ki ma”

Murmurshi Gwaggo ta saki dan shine Kuma babban burinta taga Yaran Sule da na Habu sun Kulla wani zumunci tun lokacin ma da Amjad ya saki Jawaheer taso a hada auren Amjad da Fareeda.

Amjad ya dage akan baya so dagewar da yayi yasa ta hakura.

Sai Kuma gashi Allah yayi Amjad din dai zata aura.

Wata biyu da Auren Fareeda aka daura auren Amjad da Ameera,fadar murnar da Habu yayi bata bakine,dan babban burinsa yaga zumuncinsu ya Kara kulluwa.

Ashe dai da Rabon Aure a tsakanin Amjad da Ameera.

Wani katon gida Shamsiya ta basu kyauta.

Gyara kuwa har yafi na auren ta na fari.

Dan burin kowa yaga ya gyarata

Gimbiya kuwa itama ta taka rawar gani sosai dan har da kayan gyara ta Aiko mata.

Ameera kuwa ita dai gata nan dai bata farin ciki bata bakin ciki,hasali tunda aka daura auren rayuwarta da margayi ke dawo mata har Kuma aka kaita din.

Sai taji mutuwarsa ta dawo mata sabo.

A madadin amarcin da Amjad yaci buri da dokin Yi da wacce ya fara so a rayuwarsa yake Kuma so har gobe sai ya koma rarrashin Ameeran da dama lallabata yake.

Ameera kuwa ganin yadda Amjad ke lallabata har tsawon sati biyu yasa ta fara k’ok’arin rungumar Amjad a matsayin mijin aurenta.

A cikin wata biyu San Amjad ya fara dawowa zuciyarta dan Yana kwatanta Abubuwan da margayi ke mata Sosai.

Duk da Zinatu tana gidan a wani part din da wata Yar aikin dake kula da ita ta kasa zuwa wajenta Amjad ma ya hanata zuwa din.

Wata shidda da Auren ita da Amjad ta samu ciki.

Banda arizkinsu dake ta bunkasa da suka hada hannu ita da shamsiya suka Bude gidan marayu.

Wata ranar Alhamis da yamma ta Jiyo Ihun daga part din da aka ajiye Zinatu da duk dare sai Amjad ya shiga wajenta tana so taje ta duba ta amma Amjad sai ya hana ta zuwa ta rasa dalili.

Nan kuwa Amjad dalilin daya sa yake hana Ameera shiga wajen Zinatun

Bai wuce Haukan da Zinatun keyi tuburan ba,dan har lokacin tana Ihun Natete ya cuceta ya kwanta da ita sau uku,yanzu shikenan Hanne ta fita duk yadda taso ganin bayan sule bata cimma burinta ba,duk yadda taso Ameera a ce itace a kasan sultana hakan bai yu ba,gabad’aya haka take Ihun tonawa kanta asiri Wanda Amjad kuwa ba zai so Ameera taji ba.

Da dan gudu ta Isa part din da take Jiyo Ihun Yar aikin.

A daidai lokacin da Amjad shi ma ya dawo gidan da gudunsa shi ma ya karasa part din da shigarsa yaga Ameera a tsaye a bakin k’ofa

Zinatu kuwa ta shake Yar aikin Taki cikata tana “Nace ki kaini wajen Natete ko akan me zaki daureni.

Duk abinan da take bata ga Ameera da ta tsaya cak tana kallon Zinatun da kamaninta suka canza da sai da gabanta ta fadi da ganinta ba.

Indai ba daure Zinatu akayi ba haka za tayi ta Jan duwawu tana watsa abubuwa tana k’ok’arin fita daga dakin.

Shigar Amjad dakin da saurinsa yasa ta dago har lokacin tana shake da wuyan Yar aikin

Ameera da ta gani a tsaye a bakin k’ofa yasa ta tsaya cak ta kura mata ido batare da ta motsa ba,kallon da take.mata tana tuna irin Abubuwan da taso yiwa Ameera da ta ringa tsallakewa da irin duakakar da tayi Sultana taso wa wanan rayuwar ba Ameera ba,har Amjad ya cire hannunta daga wuyan Yar aikin bata sani ba.

Sai da Amjad ya fara k’ok’arin hade hannayenta dan ya d’aure ta ta fusge da k’arfi ta fara Jan duwawu dan ta Isa wajen Ameera dake tsaye har lokacin jikinta na rawa dan sallati kawai take a zuciyarta da taga yadda Zinatun ta dawo.

“Mai kike yi a gidanan uban me kike nema,bayan kinfi sultana komai ke dai Allah ya tsine Miki !!!

Amjad rufe mata bakinta yayi da hannu daya ya fara k’ok’arin daure hannayenta.

Zinatu kuwa ta gartsa masa cizo Mai zafi da ya sa ya cikata batare da ya sani ba.

Dan ganin Ameeran da take yasa taji idan ba shaketa tayi ba ba zata tab’a samun nutsuwa ba

Da Jan duwawu ta Isa wajen k’ofar Ameera kuwa tayi baya da sauri.

Zinatu kuwa da idonta ya fada kan heater da aka jona batare da tunanin komai ba ta tsoma hannunta da zumar d’auko heater daga ruwan zafin dan ta watsa mata ruwan zafin kamar wacce aka shafewa kwakwalwa tana rike heater ta hau vibrating dan wutan janta yayi sosai Amjad kuwa ya hau Ihun sallati.

Sai da suka samu minti uku Zinatu na vibrating kafin yaga kamar an watsar da ita gefe tayi fari fatttttt kamar an zuke Jinin jikinta,Dan taurin rai Ameera kawai take Kallo tana k’ok’arin magana kafin bakin cikin idonta ya koma sama

Ta daina motsi.

Ameera kuwa da ta gigice waje tayi da gudunta dan Zinatu ta tsorata ta ba kadan ba.

Amjad Sam bai kawo ta mutu ba sai da suka je asibitin aka tabbatar masa da ta rasu.

Bai so a yanzu Zinatu ta mutu batare da ta tubarwa Allah ta nemi yafiyar wayanda ta zalinta ba yaso ace ta dawo hayyacinta ta gane kuskuren da ta aikata amma Allah bai nufa ba.

Haka yaci kukansa ya gode Allah.

Kasancewar dare ne

Baa samu binneta ba a ranar sai washegari da tsiraran mutane ne suka samu zuwa janaizar ta (Allah kasa muyi kyakyawan karshe ka sa mufi karfin zuciyarmu Ameen)

Shekara daya da rasuwar Zinatu itama Gwaggo ta amsa kiran Allah wasiyyar da ta bayar na rike zumunci su Sule suka Kara rikewa da k’arfi.

Dan daidai da su Amrah dasu Ameeran sun hada kan yaransu wajen zumunci.

Ameera na zaune lafiya da Amjad da yaransu biyu yanzu haka.

Mufeed Kuma Yana wajen kakarsa da ake kawo shi wajen Ameera duk lokacin da yayi hutun makaranta.

Boka Natete kuwa Shima mutuwar wulakanci yayi dan mota Ce tayi kwatsa kwatsa da namansa a hanyarsa ta zuwa yiwa wata Mai kudi aiki.

Allah ya raba mu da kyashi hassada da rowa Dan duk shi ya Kai Zinatu ga halaka  anan na kawo karshen littafin KWARYA TA BI KWARYA Kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafe min darasin dake ciki Allah ya bamu Ikon karuwa dashi.

Na saudaukar da littafin nan ga margayiya Laweesa kanwata dan Allah duk Wanda ya karanta littafin nan yayi mata addu’a Allah ya Kai haske kabarinta da ita da Al ummar musulmai da suka riga mu gidan gaskiya idan tamu mutuwar tazo Allah ya bamu ikon cikawa da kyau da Imani.

Series Navigation<< Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 5
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *