Nayi Nadama Chapter 6

Nayi Nadama Chapter 5

This entry is part 5 of 6 in the series Nayi Nadama na Aysha Ali Garkuwa

[4/9, 1:48 PM] 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 MI,WASMITI…..page 5⃣

Na Aysha Ali Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Gaba dayansu suna cike a porlon cikin shirin komawa

Sunyi sit dan bppa Yaya zai musu Nasiha da Addu,a kamar yadda yake musu ko yaushe in sunzo komawa i dan da wani mai buqata ko uzuri ko umurni toh duk a wannan lokacen yake bawa yayanshi damarsu

Shiru sukayi cikin maida hankali kanshi

Sadiq ne yayi slm tare da shigowa da sauri Aysha ta juyo gunshi cikin harara tace Allah Sadiq ka kawomin kayana ko baka dinkaba ni gsky Na gaji Amira tace gsky kam kaya kusan shekara baka dinkasuba Usman dake gefenshi ya kaleshi a yatsine yace gsky dai Sadiq ka shiga tara tunda Sam baka da cika alqawari duk halayen teloli kai ka hada ga shegen son kudi Kaine dinkin yan mata kaine dinkin samari har Na tsofaffi baka bari….

Innayi ta amshe zance da cewa ai Sadiq kam sai a hankali wlh nima tun bayan sallahn bara Na bashi fatarina ya dinkamin aljihu a jikinsa Na samu gun ajiye yan canji da woyata Amman har yau bai baniba

Mixxixx Rabi,u ya ja tsaki sai da duk suka juyo gunshi yace kajifa kaji shirmanta ko ana mgnan kaya masu rai kekuma kina mana mgn bujenki Duk sukayi dry Adam yace tab innayi kawai ya batar miki da fatari .

Tab tace aiko sai ya biyani shidai Sadiq sai dry yake Abdul ya kalleshi yace ai ba dry kakeba biyan fatari zakayi

Ya dan gyada kanshi ya ajiye wata qatuwar leda yace toh kudai ga naku dan wlh dama nasan su Aysha Anty masifa jiya ko bacci banyiba saida Na gama hada muku ya kalli su Usman yace Yaya Usman kuma ga naku.

Abba ya danyi gyaran murya yace toh Ku saurara ai mana Addu,a Bappa Yaya ya rinqa musu nasiha da sanya musu albarka daga qarshe ya musu Addu,a

…….. Duk suka fito suka shishshiga mota a hankali Yusuf ya yafito Sadiq da hannushi da sauri ya iso gunshi cikin kulawa yace kai Sadiq anya kuwa kana maida hankali kan kara tunka ? Cikin girmamawa yace sosaima Hamma Yusuf nama kusa try Universityn zariya yace ka dai kula dan naga gaba daya so kake ka zama mai dabi,ar mata shiyasa bansoka da dinkin nanba dan mafi akasari telolin mata da masu daukan photo dabi,ar mata suke dauka haka dai ya dan mai nasiha

Suka tfy suna kewar juna

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Yau kusan satinsu 3 kenan da zuwa mambila amma Yusuf bai kuma zuwa ba kuma duk weekend sai sun je yau jumma,a bayan sunyi sallan la.asar duk suna hallare a babban palonsu suna ta hira bb bello ya dan gyaran muraya yace toh Yusuf kunsan gobe Saturday ko dan haka duk Ku shiyarya da wuri dan tfyar sassafe nake son muyi..

Ya dan tura hularsa qeya kadan yace hmm baba nifa ina da taya goben Ummi ta dan kalleshi cikin jin haushi tace wai kai kam wanne iron mutum ne kai Sam bakason shiga yan uwanka kowa mararin zuwa yake Amman banda Kai su kullumu basu da mgn sai taku Amman a fili kake nunawa Baka damu da suba Duk baqin haline hakan da mugun mishkilanci wlh bakaji dadin rayuwarka ba..ta qarishe mgnar cikin fada

Nenne ta dan kalleshi tace ina zakaje ne Yusuf ?.

Ya dan yamutsa fuska yace Yola zamuje dan tunda nazo bamu jeba gashi har klcin komawata ya fara matsowa Goggo jiyama saida ta kirani tana ta fada bamu jeba

Adam ya kalleshi da kyau yace wai kai ban ganeba fa kanata xakuje bakujeba kai dasuwa kenan zaku ? Ya dan harareshi ta wutsiyar ido yace toh da dasuwa nake zuwa ? Atoh nikam bazaniba ban saniba wataqil Ahmad zaije

Ya kalleshi a yatsine yace wlh sai kaje dole kaje mutum baison jiharsa ta aihuwa ko kadan

Ahmad ya danyi murmushi yace toh Abba mu dai gobe Yola zamu Abba da su Nenne su kace toh Allah ya kaimu lfy

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Haka kuwa akayi Adam badon yaso ba suka tfy Adamawa

bayan sallah azahar kada suka isa A hankali Ahmad yayi parking a harabar gidan hydar da Maryam dake qoqarin fitowa da sauri suka qarasa gunsu cikin jin dadin ganinsu hydar ya karbi briefcase en Yusuf da miqamar hannu suka gaisa Maryam ko da sauri ta fada jikin Adam tana welcome ya Adam sai yau kuka zo ya dan subbaci goshinta yace ya zafin garinku tai dry dai dai lkcin da ta fada jikin Ahmad ta dan dago kanta ta kalli shi tace kajifa ya Ahmad wai garinmu wato shikam bandashi murmushi kawai ya iyayi yana dan tureta daga jikinshi dan wani mugun Abu yaji yana yawo a jinshi  abinda bai tabajiba dan ya runqumi su Amira ga kuma Yusuf dake ta watsa musu harara

A hankali ta nufi jikin Yusuf tana Hamma Yusuf yaus…..

Da sauri ya katseta ta hanyar daga mata hannu da murtuqe fuskarsa tamkar sojan dake filin daga Atake  tasha jinin jikinta

***********

Bayan sun gaggaisa gogga ta cika musu abinci a gabansu suna ci suna dan hira ba laifi yau yadan sake Amman dai baici Abinciba har baba Umar ya dawo ya jasu palonshi sukai ta hira yana musu da nasiha ya kallesu da kyau cikin qaunar yaran nasu yace Ahmad kunci abinci kuwa ? Alhamdulillah baba munci mukam Amman biyaye baiciba ya fada yana nuna shi OK yace ya kwallawa Maryam kira yace ta kawo mishi abinci ..

da kanshi ya zuba mishi ya bashi yana maza cinye banason dabi,arkannan ta zama da yunwa da gyar ya danci kadan  ya kalli Goggo yace Goggo nonofa mai dan sanyi tana dry ta dauko mar mai sanyin gsky toh nanne ya danci

Haka sukai ta hira kashe gari suka dan zaga dangin babansu Adam

Da a zahar suka kama hanya sai jaligo

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Aysha kam tunda tasan yana dan zaman palon ta daina fita da zaran tasan yana gun bata fita duk da bawai mgnarsa take jiba qamshin turarensa ke fadamata yana palon

Dan gudun bala,inshi da duka

Yau tunda safe suke ta dan girke girken dan yau babban soja xai diro daga Abuja ya Abubakar kenan sosai take farincikin zuwansa dan yana gwada mata kauna ta haqiqa

Qarfe 2 dai dai ya dira a babban palonsu tana tsaye gefen dining area tana ta shirya mai abinci Sam bata lura tare suka shigoba da qarfi tasa dan qara ta fada jikinshi yako tallabota yana dan juyawa da ita a tsakiyar palon sai dry take sosai tana miss U ya Abubakar juyi yake da ita sosai tana maqale a jikinshi Ahmad dake gefensu farinci yake sosai a ransa ganin ayshansa Na cikin happy aduniya duk abinda zai sata farinciki to shima zai sashi farin cikin

Muje zuwa masu karatu aiki Na gaba Na Gode da kulawarku da qaunarku gareni Nina kuna raina 😍😘

Series Navigation<< Nayi Nadama Chapter 4Nayi Nadama Chapter 6 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *