Nihad Hausa Novels

Nihad Chapter 6

This entry is part 7 of 6 in the series Nihaad by Khaleesat Hydar

~~~~~~ 6

Washegari Monday har karfe tara Nihad na ta kwance a dakinta, karfe tara da rabi aka bude kofar dakin, ta juya ganin Umma ce ta shigo ta mike xaune a hankali, Umma tace “Baxa ki makarantar bane Nihad, naga yau Monday” Nihad tace “Lectures din karfe goma ne, Nihal ta tafi islamiyya?” Umma tace “Tun yaushe, ke dai kam na san ba xa ki ba” Nihad bata ce komai ba, Umma ta juya ta fita, sauka tayi daga saman gadon ta shiga bandaki, nan ma sai da ta bata kusan minti arba’in sannan ta fito, shiryawa tayi cikin tsadadden bakar Abaya, wurin shirin ma ta 6ata kusan minti talatin, banda kamshi babu abinda ke tashi a ko ina na jikinta, sosai Abayar ta amshi farin fatarta kai kace balarabiya ce, ta dau karamin handbag ta sa flat shoe sannan ta fito daga dakin bata kulle ba don Hafsah xata shiga tayi mata gyaran dakin sannan ta wanke mata bandaki, tana tafiya kamar bata son tafiyar ta tafi part din Mumy ta bude kofar parlon, xaune ta ganta parlon tana waya, ta cire takalminta nan bakin kofa ta karasa ciki a hankali, ta xauna saman kujera fuskar nan nata babu yabo babu fallasa, har Mumy ta gama wayar sannan ta gaisheta, Mumy ta amsa mata ita ma a dakile without looking at her, mikewa tayi tace “Xan tafi makaranta” Mumy tace “Allah ya tsare” fita tayi daga parlon ta wuce part din Umma, Umma tace “Ashe dai za ki, toh Breakfast din fa?” Tace “Xan yi a makaranta” Umma tace “Toh Allah ya tsare” Kamar xata yi kuka tace “Umma ni gaskiya baxan iya shiga mota daya da wannan yaron ba” Umma tace “Toh yanxu ya xa ayi, idan na tafi na amsar maki makullin kin san anjima xa a dauko yara a makaranta” A hankali Nihad tace “Toh pls Umma zaki bani makullin motar ya Farooq” Umma ta rike ha6a tace “Farooq, to bari dai in dauko maki” cike da farin ciki Nihad tace “Yauwa Umma, karfe hudu xan dawo in sha Allah baxan wuce haka ba” Mikewa Umma tayi ta fita daga parlonta ta wuce dakin First son dinta, makullin dake jikin kofar ta murda sannan ta bude ta shiga ciki ta dauko makullin motarsa ta fito, farin ciki sosai Nihad tayi ta mashi makullin tana murmushi tace “Umma nagode” Umma tace “Toh ki tafi a hankali dai, kar ki kwarzane masa mota mu shiga uku” Nihad tace “A hankali xan tafi Umma” Daga haka tayi ma Umma sallama ta fita daga parlon cike da murna, ta fitowa compound taga mai gadi xaune tare da Khalil, lokaci daya ta wani murtuke fuska, ta nufi mai gadi tana juya makullin hannunta tace “Hey Bude min gate xan fita” Tashi yayi da sauri ya tafi xai bude gate din, ta nufi motar yayanta, ta gefen ido khalil ya bi ta da kallo, har ta shiga motar, bayan ta gama warming tayi zoom off out of the compound duk don ta tada k’uran interlock, Mai gadi ya daga mata hannu yace “Allah ya tsare Hajiya” ko kallonsa bata yi ba balle ta tanka, ta ja motar tayi gaba, kulle gate din yayi ya dawo yana kallon khalil yace “Hajiya ce xata bata motar Farooq da yake baya gari, kuma ina tabbatar maka uwarta bata sani ba, dama Umman ke daure mata tayi ta abinda ta ga dama a gidan nan ai, kai kam huta roro” Khalil yayi murmushi yace “Yanxu ina xata haka?” Mai gadi ya xauna yace “Wai Makaranta mana, kasan jami’arta shegen tsada ke garai” Khalil yace “Ita er uwarta fa?” Mai gadi yace “Baiwar Allah, ba daxu ka ajiyeta a islamiyya ba, hutun makaranta ta dawo, amma kaga kullum sai taje islamiyya abunta…” Khalil yace “Wacce makarantar take ita?” Mai gadi yace “Ba nace maka a Zaria take, Ahmadu Bello” Khalil bai kuma cewa komai ba. Nihad na driving tayi dialing number Husnah, Yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad tace “Kin shiga school ne?” Husnah tace “Me yasa kika kashe wayarki jiya bayan munyi dake kina tahowa?” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “It’s a long story, but ya na ji muryarki haka, are you okay?” Husnah tace “Partially” Nihad tace “Where are u at now?” Husnah tace “Ni’ima guest palace” Nihad tace “Really? To bari in taho nan kawai, nima I’m not even in the mood of attending lectures today” Husnah tace “Sai kin xo” Katse wayar Nihad tayi ta dau hanyar Ni’ima guest palace din. Nihad na isa tayi parking ta kirata, nan Husnah ta sanar mata room number dinta, Nihad ta sauka motar ta shiga ciki, Knocking tayi kofar dakin, Naf ta bude, Nihad ta d’an buda ido ganin Husnah a kwance ta lulluba, ta kalli Naf tace “Is she okay?” Naf tace “Shigo in kulle kofa” Nihad ta shiga ta karasa gun Husnah, ta xauna gefen gadon tana kai hannu jikinta tace “Ya dai Husnah?” Husnah ta mike xaune tana ta6e baki tace “Ashe Yaks d’an iska ne duk bamu sani ba” Nihad ta ɗan bude ido tace “Me ya faru?” Husnah tace “Kawai yaje ya sha kwayoyinsa jiya in gaya maki yayi assaulting dina” Nihad ta xaro ido tace “Really?” Husnah tace “Wllh ke dai in gaya maki, ban da abunsa ai i wouldn’t have denied him” Nihad tace “Where was Nafee then?” Husnah tace “Ita suna tare da saurayinta, kin san shi ma ya zo” Da mamaki Nihad tace “Yaks??” Husnah tace “Ai kuwa baki ga yanda ya dinga tambayarki ba, nace kina hanya duk ya damu baki iso ba, ke gwara ma da baki xo ba din, kilan rashin xuwanki ya sa haka ya faru,” Nihad tayi shiru, can tace “Tabdi, kuma a Tahir guest palace din?” Husnah tace “Wane Tahir, ai ba a can muka yi birthday din ba, ke kinga haduwar birthday din nan kuwa Nihad?? Gaskiya na jima ban ga birthday da yayi haduwar na Maska ba, it was light” Nihad tace “Ni xancen yaks ne ya tsaya min a rai, Shi yasa fa kike ganin bana kula clique dinsu, bana harka da maza marasu aji” Husnah tayi dariya tace “Ni kawai way of approach dinsa ne ya kona min rai, amma what’s there? norms ne ai, someone that i have been crushing on from day one” Nihad tace “To karfe nawa ku ka bar wajen?” Husnah tace “Kai dare yayi fa sosai, ke ni fa wllh gwara ma da Allah ya hanaki xuwa nace maki, don da ban san ya xan yi da ke ba a wajen ga uban daren da muka yi, cabb to wa ma xai saurareki, gaskiya birthday din nan yayi armashi, ai da naga daren yayi sosai shine na fasa komawa hostel kawai muka kama daki a nan ni da Surayya, ita Naf fa sai yau da safe ta xo nan ta same mu” Nihad ta kyabe baki ta ajiye handbag dinta tace “I am jet hungry banyi breakfast ba, me suke siyarwa a nan?” Husnah tace “Ke bamu dade da waya da Ayman ba xai taho mana da abinci yanxu, bari in kirasa ince plate uku xai kawo, shi ma jiya ya dawo daga Egypt” Daga haka Husnah ta kirasa ta sanar masa ya dado wani plate din, bayan ta ajiye wayar tana kallon Nihad tace “Amma jiyan me ya hanaki xuwa don Allah?” Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya irin na takaici tace “Husnah in gaya maki wani sabon driver Abba ya dauka, kin san ai ya bude ma Habibu Shago” Husnah ta gwalo ido tace “Don Allah, kina nufin yanxu babu Habibu? Allah sarki, kai amma xaki yi kewan Habibu, sau da yawa fa da shi kike hada baki, gashi duk inda kika ce ya kai ki kai tsaye yake kai ki, har ma ya jira ki” Nihad ta marairaice tace “Ke dai bari, ai ni aka yi ma da Habibu ya bar driving, sau nawa yake kai ni Tahir ko Bristol or prince hotel, kuma ya jirani komin dadewar da xa mu yi, sau nawa xa mu fita in amshi mota a hannunsa shi ya tafi harkar gabansa nima inyi tafiyata, sai na gama xan kirasa mu hadu a busstop mu koma gida, Yawanci ba shi nake aika ya siyo min duk abinda nake bukata ba, ai har kuka sai da nayi da naji Abba ya bude masa shago, Habibu ai mutum ne” Husnah tace “Amma fa ya ci kudinki ba karya” Nihad tace “I wish Allah xai ta6a xuciyar Abba ya dawo mana da Habibu kawai” Husnah tace “Toh shi sabon da aka dauka fa?” Nihad ta gyara xama tace “Ai shi xan baki labari yanxu, wato wani tatattcen d’an iska, mara kunya Abba ya dauko mana as driver Husnah, kinsan jiya a kansa sai da Mumy ta mareni har sau biyu a titi cikin jama’a? Husnah as i am talking to u now i am boiling inside, tun shekaranjiya nake cikin ɓacin rai da bakin cikin mutumin nan, daga fara aiki shekaranjiya har ya raina ni baya girmama ni, ina masa magana sai yayi min banxa ko kuma ya kalle wanda ke kusa da shi irin dai kamar ba da shi nake ba da na kusa da shi nake, ko kuma ya kara min sheggun kunnuwansa gaba, irin dai na raini da tantiranci, Husnah yayi mugun raina ni wllh, yanxu maganar da nake maki motar ya Farooq Umma ta bani makulli na fito da shi, baxan juri xama a mota ni da shi yana driving dina ba….” Tuni har hawaye ya cika idonta, Husnah dake ta sauraronta da mugun mamaki ta gyara xama tace “What?? Shi ordinary driver din yake duk wannan abinda kika lissafo min kuma kika kyalesa? Ta yaya kika basa wannan fuskar ya rainaki daga fara aikinsa Nihad? Waye shi haka, kuma a ina Abba ya samo sa?? Wai ma garin yaya kika yi creating room for this bullshit” Nihad na shessheka tace “Baxa ki gane ba, wllh irin yan iskan nan ne yaron, cikin ruwan sanyi yake raininsa da rashin mutunci, idan kin gansa ma xa kiyi xaton baya magana nan ko katon ɗan iska ne, yanda fa kika san motarsa haka yake jin kansa daga fara aiki” Husnah ta rike ha6a tace “Tabdi… to kuwa xa mu yi maganinsa, but what did Abba say about it? Ko baki kai kararsa ba har yanxu?” Nihad tace “Babu wani action da Abba ya dauka tunda Mumy ta zuzzuga sa, har Umma ma ta saka baki amma Abba yaki daukan kwakkwaran action, the painful part of it is that Mumy supporting dinsa take kamar ta ta6a saninsa, kinsan yanda take abubuwanta dai, to wllh a kansa ta gaggaura min mari jiya a tsakiyar Hotoro dalilin da yasa na fasa xuwa Tahir palace kenan, to wannan ne har xan dinga basa kudi yana kai ni duk inda nake so ba tare da yayi casting dina ba wataran? Ina ai baxai yiwu ba, bana harka da fitsararrun yara ni….” Husnah tace “Calm down besty, shi karamin kwaro ne wllh, kuma xa mu yi maganinsa, Clique dinmu kadai mun ishesa” Naf dake ta sauraronsu ta kyabe baki tace “Lallai wnn ɗan iska ne number 1, daga wani kauyen aka samo maku shi halan? Shi a yan kauyen ma shege ne fa” Nihad tace “How will i even know, wlh d’an rainin wayo ne na karshe, gashi baya wani magana nake gaya maku, yanda kuka san kurma, cikin ruwan sanyi yake rashin mutunci da raini, ga wani ji da kai, to kana aiki karkashin mutane kana driving ina wani ji da kai??” Kwankwasa kofar aka yi, Husnah tace “Ayman is here…” Naf ta nufi kofar ta bude, wani matashi ya shigo dakin rike da takeaway uku with many drinks da bottle water, Ya ajiye ledan yana kallon Nihad yace “Manyan mata, ashe dai kina kasar nan Nihad?” Nihad tace “To an zuga Abbana ya ki kai ni UK karatu ba dole a gan ni a kasar ba” Dariya yayi yace “Gaskiya ne, to ya kwana da yawa, kinsan ku manya ne ba kowa ku ke replying ma chat ba both WhatsApp and IG” Nihad tace “Not at all” Husnah ta mike ta dauko takeaway daya ta ajiye ma Nihad, Ayman na kallon Husnah yace “I think bari in kama wani dakin kawai” Husnah tace “Ohk then” Daga haka ya fita daga dakin, Naf ta ja tsaki tace “Sai shegen girman kai, wato jira yake in fara masa magana ko” Husnah tace “Ke dai kowa sai kice yana da girman kai bayan kema kina fama da naki, duk fa Salman ne ya hura maki kunne ki daina kula kowa sai ki dinga fakewa da ana maki girman kai” Naf tace “Ni fita ma xan xo in yi yanxu, amma xan dawo later” Husnah tace “Ina xa ki? Baxa ki ci abincin ba?” Tace “Idan na dawo xan ci” Husnah tace “Kar fa ki ki dawowa Naf, saboda ke naki gayyato Zully nan fa” Naf tace “Ke wllh xan dawo, wani Alhaji ne ke ta damuna da kira ya shigo kano, to yayi min alkawarin waya dama, shine xan je” Husnah tace “Ahh, to maza ki je, Allah ya sa mu ga latest iphone” Naf ta dau figigin gyalenta tace “Toh Allah ya sa bari in je, Nihad idan na dawo xa mu tsara yanda xa ayi da ɗan kauyen can shi kuma” Nihad tace “Toh sai kin dawo” Daga haka Naf ta fita daga dakin, Husnah tace “Tabdi, yau ni naga karfin hali wai barawo da sallama, wannan idan yayi wata daya a gidan ai sai dai kuma ya koma rayuwa cikin main building ya bar boys quarters kawai” Nihad tace “Sai yanzu rashin barina in xauna a hostel da Mumy tayi ke kara damuna sosai, kinsan da na hakura amma tun da aka kawo wannan drivern damuwan ya dawo sabo” Husnah tace “To ko xaki kara gwada yi ma Abba magana?” Nihad tace “Babu yanda Umma bata yi da shi ba, amma da yake Mumy da ya farooq sun hure masa kunne ya ki amincewa, sae dae kawai yayi ta bani hakuri wai there is time for everything” Husnah tace “Gaskiya in har ba sallaman driver din nan aka yi ba xaki takura sosai, gashi Abba baxai baki mota ba ko” Nihad tace “Ba fa ruwan Abba, Mumy ce matsalar gidan nan sae yaya Farooq, amma ae Umma tayi kokarin ganin an bani motar kwanaki hakan bai yiwu ba” Husnah xata yi magana wayarta ya fara ring, tana dubawa taga Ayman ne, dagawa tayi tace “Ya? Wani room number kake?” Yace “102… Pls Nihad ta bani minti goma mu yi magana mana” Husnah tace “Ohk over there?” Yace “Yeah” katse wayar tayi tana kallon Nihad tace “Ayman wants to speak to you” Nihad tace “Ohk kin katse wayar kuma” Husnah tace “No, yana room 102” Nihad tace “Ina ga ya sha kwaya, nice xan bi sa dakin??” Husnah tace “C’mon, minti nawa xa kiyi ki fito, he said just 10 mins, behave like the big girl u are mana” Nihad tace “Look, ya bar ni ma inji da damuwata i don’t have that strength to talk” Husnah tace “Don Allah kiyi hakuri ki je Nihad, minti goman nayi ko bai gama magana ba ki fito kawai, ko albarkacina ya ci mana, yana ganin idan na gaya maki xaki ji shi yasa ya biyo ta wajena, ki je ki dawo ki ji yanda xa mu yi da wancan ɗan kauyen shi kuma” Nihad ta d’an kyabe baki, sai kuma ta mike tana gyara veil din abayanta tace “Wani room ma kika ce?” Husnah ta gaya mata, daga nan ta fita xuwa dakin. Kwankwasa kofar dakin tayi, sai gashi ya bude yana kallonta da murmushi fuskarsa yace “Welcome Nihad” gefensa ta bi ta shiga dakin ta xauna saman one seater dake dakin tana kallonsa har ya dawo ya xauna gefen gado sannan tace “I am all ears” shiru yayi yana kallonta, ta langwabar da kai tace “Kayi shiru” Ɗan murmushi yayi yace “Donno where to start from, kinsan kina da wani kwarjini na daban Nihad” Ta kalli agogon dake wrist dinta, sannan tace “Then just start from d end” Dariya yayi sannan yace “Ohk, a takaice kawai ina son ki bani dama let date” Tace “Sorry but i don’t double date Ayman” Yace “What’s d big deal about double dating Nihad?” Ta girgiza kai tace “Tsari na kenan, i have my boyfriend, and yana sona kamar yanda nima nake son sa, so what’s d need of dating else where?” Shiru Ayman yayi, can ya mike ya koma kan kujerar da take ya xauna a hannun kujeran xai kama hannunta ta fixge ta matsa gefe sannan tace “I am sorry Ayman, ina da saurayina kuma duk kun sani” Yayi kasa da murya yace “Yeah i know, but pls Nihad… even if it’s once a while, i will always provide u with all ur needs, i am not talking about petty needs” Da mamaki tace “What’s that u are talking about?” The way he was looking at her directly in the eyes yasa ta mike tana kallonsa da kyau tace “Seems Husnah bata ta6a baka labarina ba ko?? Kawai kana ganin mu tare, duk inda take xaka gan ni, Ohk get this Ayman, my obstinacy have limit, it hasn’t attain to this extent, sorry” Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin ta kullo masa kofar. Tana komawa wajen Husnah, Husnah ta katse wayar da take ta ajiye, Nihad tace “Baki ta6a gaya ma Ayman wacece ni ba ko?” Husnah bata ce mata komai ba, Nihad ta nemi waje ta xauna, Husnah tace “Toh wai meye a ciki, kawai kin bi kin makale ma Aliyu da definitely kinsan yana da yan mata iri iri shi ma, ni wllh Aliyun nan haushi yake bani, ga shegen ji da kai kamar ɗan jinin sarauta, duk abinda ya daura ki a kai shi kike yi, ga samari iri iri ko wanne na sonki amma kince ke sai Aliyu, to Aliyun me” Nan da nan Nihad ta hade rai tana kallon Husnah, can ta ja tsaki ta dau jakarta ta mike ta nufi kofa, Husnah tace “Tun da an ta6a numfashin ki ba dole ki nufi kofa ba, to baxa ki tsaya ki ji yanda xa mu yi da sabon drivern naku ba” Ko sauraronta Nihad bata yi ba har ta fice daga dakin, Husnah ta ta6e baki tace “Kawai ki makale ma mutumin da yan mata ke rububi a kansa, ki dauki son duniya ki dora masa, shi kuma yayi ta yin kamar bai san kina yi ba, da ma yana baki lokacinsa yanda ya kamata ne abun baxai dameni ba” Husnah ta ja tsaki ta jawo abincin gabanta ta bude…..

7️⃣

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Sai bayan la’asar Nihad ta iso gida, bayan ta fito daga wajen Husnah school kawai ta wuce tayi attending lectures daya, mai gadi na bude gate ta shiga gidan ba tare da ta saurari gaisheta da yake ba, tayi parking dai dai inda motar take ta kashe, sauka tayi ta kulle motar tana kallon inda mai gadin ke xama ko xata ga Khalil, ai ko yana xaune, ko da wasa bai kalli inda take ba, sai ma danna torchlight phone dake hannunsa da yake with full concentration, nan da nan taji har ranta ya fara baci, wai wa yayi ma wannan mutumin hanyar xuwa neman aiki a gidansu? har ta juya xata wuce ciki sai kuma ta dawo, fuskarta daure ta nufesu, Mai gadi na ganin ta doso inda suke ya mike daga xaunen da yake yana gaisheta, Babu yabo babu fallasa ta amsa sannan tace “Aminu kuna canza ma tsuntsaye na abinci da ruwa kuwa??” Yace “Ehh Hajiya ko daxu da kaina naje wajen na basu abinci da ruwan” Mai gadi ne ke mata magana amma banda hararan khalil babu abinda take with hatred, how dare him baxai gaisheta ba ma, wani dogon tsaki ta ja tace “Aminu ka sameni wajen tsuntsayen” Daga haka ta wuce fuuu xuwa bayan gidan inda cage din birds din nata suke, Aminu ya kalli khalil sannan ya bi bayanta da sauri, sai a snn Khalil ya daga kai ya bi su da kallo, suna isa wajen tsuntsayen tace “Aminu in tambayeka mana” Yayi kasa da kai yace “Toh Hajiya” Tace “Wai waye ya kawo wancan yaron gidan nan da sunan ya nemi aikin driving?” Aminu yace “Hajiya Habibu ne ya kawosa ae” Da mamaki tace “Habibu??? Habibu dai?” Aminu yace “Kwarai Hajiya” Juyawa tayi ta wuce ta bar sa tsaye a wajen, gida ta shige, Aminu ya dawo bakin gate ya xauna yana kallon khalil dake kallonsa shi ma, yayi kasa da murya yace “Wai tambaya take wa ya kawoka, to ban san ko na kwabsa ba da nace Habibu, kasan fa Habibu mutuminta ne, har makudan kudi tana basa, to duk inda xata kai tsaye yake kai ta har ya jirata, ya sha gaya min maganganu amma yace kar in gaya ma kowa” Khalil yace “Wani magana?” Aminu ya gyara xama yace “Ae otal daddaya ne a garin nan da wajen shakatawa irin ta manya bai ta6a ajiyeta ba… Kai duk dai wani otal dake kano da ya amsa sunansa otal xuwa take, wani lkcn tun safe sae dare xae je ya daukota, Khalil dake ta kallonsa da mamaki yace “Hotel?? Me ke kai ta can?” Aminu yace “Ahaf ka ji ka da wani xance, me ake zuwa yi otal, kuma kaf babu wanda ya sani a gidan nan sae Habibu sae kuma ni da yake gaya ma, kai wani lkcn har Habuja tana xuwa kuma ta dawo a ranan, kasan sha’anin jirgi, peee ta tafi peee ta dawo ita da kawayenta, babu wanda xae sani, duk kowa tunaninsa tana makaranta, ita ce Kaduna, Ita ce legas, patacot…..kai manyan garuruwan kasar nan dai da ka sani babu inda yarinyar nan bata xuwa, babu abinda Habibu bai sani ba game da ita ai, ina ga shi yasa taji haushin barin dreba da yayi” Khalil dai yayi shiru, Mai gadi yace “Atoh ni kallonta kawai nake kyar” Khalil yace “Allah ya kiyaye” Mai gadi yace “Ameen dae” Nihad na shiga bedroom dinta ta ajiye jakarta da mayafi ta dau wayarta tayi dialing number Habibu, yana fara ringing ta nemi gefen gado ta xauna babu bata lkci ya daga hade da sallama yace “Hajjaju Hajjaju ina yini” Tace “Lafiya lau Habibu” Yace “Ya kwana biyu kuma?” Tace “Lafiya lau, Kana ji na?” Yace “Ina ji Hajiya” Tace “Wannan drivern da ka kawo ma Abba, a ina ka san sa?” Habibu yace “Wani abu ya faru ne Hajiya?” Tace “Tambayarka nake kana tambayata” Yace “Ehh Hajiya na san sa, d’an uwa na ne, garinmu daya” Nihad tace “Bana son karya ta ina ya xama ɗan uwanka kana baƙi yana fari??” Habibu yace “Ayya Hajiya ai in dai ka fito kauye daya da mutum ku ka shigo maraya dan uwanka xaka kirasa, haka abun yake ki tambayi kowa ma” Ta kyabe baki tace “Toh abu daya nake so da kai yanxu” Yace “Toh ina ji Hajiya” Tace “Ko nawa kake so xan baka Habibu, in dai kudi ne kar ka ji komai” Shi dai yayi shiru, tace “Kana ji na?” Yace “Ehh ina ji Hajiya” Tace “So nake ka kira Abba ka 6ata sa a wajensa, ka kirkiro wani babban laifi kace yayi a garin naku ashe dalilin da ya sa ya bar garin kenan, kai baka sani ba sai yanxu wani ɗan garin naku ke sanar maka” Jin shirun da Habibu yayi tace “Kayi min shiru?” Da sauri yace “Ehh ina jin ki Hajiya, ina sauraronki” Nihad tace “Good, yaushe xan saurareka?” Yace “Xuwa gobe in sha Allah” Tace “Ohkk” daga haka ta katse wayar ta mike ta nufi window tana jin wani relieve a ranta. Khalil na shigowa parlon chalet din da suke ciki dab da magrib ya dinga bin parlon da kallo, tun safe da ya fito bai sake shigowa ba sai yanxu, kuma kafin ya fita tass ya share ko ina, amma yanxu parlon wani sai yace yara kanana sun shiga sun yi wasa da rana, beside that every where is so untidy, nan kayan wanki, can kayan guga da Isiya ke yi, ga plate din abinci da cups a tsakar parlon, kofar ma a wangale ake barinsa sauro su shiga yanda suka ga dama, Ya dinga kallon Saminu, Isiya da Shafi’u da ke parlon, Kafin ya ce komai Shafi’u yace “Ana ta kiran wayarka tun daxu fa” Kallon direction din da jakarsa yake yayi, sai kuma ya kallesu yace “Amma nace ku yi hakuri ku bar barin kofa a bude sbda sauro, tunda a parlor nake kwanciya ko” Isiya yace “Baka ga fankar ya lalace jiya ba, AC dama tun da ka xo ai baya yi, shhkn sbda sauro sai mu ki bude kofa iska ya shigo” Khalil ya dinga kallonsa, Saminu yace “Haba kai tun da ka zo sai kayi ta abu isa isa da gadara don kaga muna maka shiru, mu kafin ka zo haka muka saba barin kofa gaskiya” Khalil bai kuma ce masu komai ba ya nufi gun kayansa, ya dau jakarsa da blanket, sai tsintsiya da parker da yake shara, hanyar dakuna uku dake chalet din ya nufa, duk suka bi sa da ido har da waigawa, sai da ya bude ko wani daki sannan daga karshe ya shiga na dama, ajiye jakarsa da blanket yayi, duk wani ghana must go da jaka da ya gani a dakin sai da ya cilla sa waje, sannan ya cire dukunannen zanin gadon dake kan gadon shi ma ya cilla masu waje, tas ya share dakin, sannan ya shiga bandaki nan ma ya wanke, ya fito ya bude jakarsa da makulli ya dauko Harpic da hypo ya koma bandakin, bayan ko ina ya dawo yanda yake son ganinsa, yayi wanka ya dauro alwala ya fito, har xai kulle jakarsa sai ya tuna wayarsa ya dauko ya ga miss calls din Habibu kusan 7, ya gama kare ma number kallo sannan ya ajiye wayar ya mike ya fita daga dakin ya sa makulli, ya zira makullin a aljihun jallabiyan jikinsa, babu yabo babu fallasa ya fito parlon ya nufi kofa duk suka bi sa da kallo babu wanda ya iya cewa komai har ya fita. Bayan khalil yayi sallah yana xaune gefen mai gadi sai ga Hafsah ta kawo ma mai gadin abinci, Mai gadi na kallonta yace “Shi ma ki kawo masa tasa abincin nan kawai” Tace “Toh” sannan ta juya ta koma ciki, Khalil ya mike yace “Xan dau wayata da ka sa a caji” Daga haka ya shiga dakin mai gadin ya dauko wayar ya dawo ya xauna, yayi dialing number Habibu ya kai kunne, ba a dauki lokaci ba Habibu ya daga yace “Ranka shi dade” Khalil ya gyara xama yace “Ya kake” Habibu yace “Lafiya qlau wllh, ya aikin?” Khalil yace “Alhamdulillah” Habibu yace “To madallah, kana ji na” Khalil yace “Ina ji” Habibu yace “Wani abun ya hadaku da wannan yarinyar Nihad ne?” Khalil yace “Wani abu kamar me?” Habibu yace “Aa wai ko sa’insa, ko dai makamancin hakan” Khalil yace “Ko daya” Habibu yace “Tohh, akwai fa matsala” Khalil yace “Ta me kenan” nan Habibu ya sanar masa yanda suka yi da Nihad daxu, Khalil yace “xan kiraka anjima” Daga haka ya katse wayar ya amshi abincin da Hafsah ta kawo masa yace “Nagode” Nihad ta fito daga wanka kenan da daddare Mumy ta shigo dakinta, sunkuyar da kai tayi tana goge jikinta tace “Ina yini” Mumy tace “Wa ya baki makullin motar Farooq daxu?” Nihad ta kalleta da sauri, sai kuma ta marairaice tace “Umma ce ta bani” Mumy tace “Ke yanxu Nihad duk wata hanyar da xaki bi ki sani magana shi kike nema a rayuwarki ko?? Kwata kwata baki daukeni bakin komai ba, duk abinda xai 6ata min rai shi kike rawan jiki kiyi, ki kama ki dau mota ki kama  hanyar makaranta without i and ur dad knowing ko Nihad” Nihad ta fara shessheka tace “Mumy u don’t want to be considering me, ni baxan iya shiga mota daya da wancan sabon driver din ba shi yasa na amshi makullin motar ya Farooq gun Umma” Mumy tace “A saboda meye baxa ki shiga mota daya da shi ba? Saboda shi ba mutum bane? Kawai don bai baki makullin mota kin tafi gantali ba shine kika dau karan tsana kika daura ma mutumi? He is only trying to protect his job don ai ba a basa umarnin ya baki makulli ba ko” Kuka Nihad take sosai tace “Ko me nace Mumy baki supporting dina, wllh yaron ba shi da kunya, ya raina ni kawai” Mumy tace “Wato yaro ne ma?? Me yasa ita Nihal bata complain a kansa, ina ce shi ke dropping dinta a islamiyya kullum, i even ask her ko taga yana da matsala tace min he is so friendly, me yasa ke baxa ki sauke kanki yanda er uwarki ke yi ba” Nihad ta hade rai tace “Wannan wawiyar me ta sani, ko bai mata magana ba ma ai washe masa hakora xata yi ita tayi masa, baxa ma ta jira ya gaisheta ba ita xata fara gaishesa sbda bata da hankali, pls mumy ki daina sa Nihal a cikin mutane” Mumy tace “Ki bi duniya a sannu Nihad, babban matashi irin wannan sbda yana aiki karkashin Abbanki kice baxa ki gaishesa ba sai dai ke ya gaisheki, me yasa baxa kiyi koyi da Nihal ba, me yasa kika dau duniya da xafi haka” Nihad tace “Ni dai Mumy kiyi hakuri ki bani makullin motar ki yau wllh ina da lectures karfe goma, Ni kuma baxan juri shiga mota daya da shi ba” Mumy tace “Toh xa mu gani kuwa, kuma wllh kika sake xuwa gun Hajiya kika amshi makulli sai na 6abbalaki a gidan nan” Nihad tace “Shikenan ni baxan je makarantar ba kawai” Mumy tace “Ohk ni kike gaya ma wannan ko” Ta fashe da kuka sosai tace “Toh Mumy ya kike son inyi, ni naga kamar ma kin fi son driver din nan a kaina kawai” Mumy tace “Ehh na fi sonsa a kanki, kuma wllh kar ki kuskura ki bari karfe goma yayi maki a gidan nan, sannan shi din xai kai ki, idan kuwa ba haka ba xaki sha mamakin abinda xan maki, tunda ke kin dau girman kan duniya kin daura ma kanki” Daga haka Mumy ta fice daga dakin, Nihad tayi kukanta ma’ishi, taji ta tsani wannan bawan Allah, ta tsanesa… Babu yanda ta iya haka ta tashi ta shirya, karfe goma saura minti biyar ta fito compound, atamfa ce jikinta da wata mitsitsiyar mayafi da ta rataya a wuya, hannunta rike da laptop dinta da jaka, fuskarta a daura ta nufi can inda ta hango Driver din a xaune da Aminu, tana masa wani matsiyacin kallo, cike da isa da gadara tace “Tasowa xaka yi kayi dropping dina a school idan ka ga dama, kai kuma Aminu sai ka gaya masa makarantar tamu” Daga haka ta juya ta bar wajen ta tafi can gun motar, murya can kasa kasa Aminu yace “Iko sai Allah” Mikewa Khalil yayi ya nufi motar, Har xata bude back seat sae kuma ta fasa ta xaga ta bude seat din gaba ta shiga, yanda ta hade rai sai kayi xaton ko dariya bata ta6a ba, shi ma ya shiga motar, suna fita compound Aminu ya daga masu hannu, AC din motar Nihad ta kunna, shi dai bai nuna yasan abinda tayi ba, suna hawa saman titi tayi connecting phone dinta ta kure waka a motar, shi dai driving dinsa kawai yake, bayan kusan minti talatin suna tafiya, ganin tafiyar tasa babu direction, ta wani juya ta kallesa tace “Wai malam baka san inda xaka kai ni bane, ko Aminun bai gaya maka ba?” Tafiyarsa kawai yake pretending he didn’t know she is talking duk da yana jinta, rage volume din wakan tayi can kasa, a fusace tace “Malam da kai nake” Ya kalleta yace “Ohk magana kike, wakar ki ce ta hana inji” Ta yi masa wani kallo tace “Da yake kai kurma ne ba dole waka ya hanaka ji, Aminu wai bai gaya maka inda xaka kai ni ba?” Yayi slow down sannan yayi parking yace “Ina ta sauraren kice ga inda xaki ne ai” Buda baki tayi tana kallonsa, Cikin daga murya tace “Aminu bai gaya maka bane?” Yace “Toh ai ban ga Aminu cikin motar ba” She couldn’t stop looking at him, ita ba abin ta sauka ba, dakewa tayi tace “Saboda ba kai ke xuba fetur a motar ba shi yasa kake ta yawo da ni a cikin garin kano ba tare da kasan inda xan je ba ko?” Bai bata amsa ba, bata kuma ga alamar xai ce komai ba, wani dogon tsaki ta ja, ta gyara xama tace “Dama harka da ɗan kauye ya gaji haka, idan kaga dama Maryam Abatcha American University of Nigeria xaka kai ni” Without looking at her yace “Ohk sai kin dinga min kwatance” Tace “Ban gane sai an maka kwatance ba, kai dama babu inda ka sani a kanon ka xo ka nemi driving a gidanmu?” Yace “Ehh idan aka ci gaba da nuna min wajajen xan sani ai” Tace “Amma wllh  baka da amfani” Tsaki ta ja tace “Ai sai ka juya kan motar idan dai ba garinku xa mu je ba” yace “In kince aje can din ma ai sai aje” Bude baki tayi, sai kuma tace “Wallahi yaron nan ka raina ni” Sai a sannan ya juya ya kalleta jin abinda tace, ta galla masa wani harara tace “Malam kana bata min lkci xan je makaranta” Yace “Na xata garin namu xa mu” Daga haka ya juya, rai a bace ta dinga gwada masa inda xai bi har suka iso makarantar, ganin yayi parking a waje tace “Malam tada motar nan ka shigar dani ciki, ko duk nan akwai wanda kaga anyi dropping a titi?” ya ci gaba da driving din slowly, dai dai gate din makarantar ya tsaya ya sauke glass din motar, gaishesa security din suka yi, ya amsa ya amshi pass ya shiga cikin makarantar yace “Ina?” Rudely tace “Duk inda ka ga wancan jan motar ta bi kai ma ka bi, bani da lkcn yi maka wani kwatancen” Bai ce mata komai ba, ya ci gaba da driving dinsa, Dai dai wajen da motar ta tsaya ya samu waje yayi parking shi ma, ta ciro wayarta ta kira Husnah, Husnah na dagawa tace “Kin shigo school?” Husnah tace “Ehh, ke kina ina?” Nihad tace “Ku fito parking space ke da su Naf ku sameni yanzu yanzu, ki tabbatar har da Zully xa ku taho” Husnah tace “Ke kika yi driving din yau ma?” Nihad tace “Ke dai nace ku zo sharp sharp” daga haka ta katse wayar, ta zuge zip din jakarta ta fiddo chewing gum ta jefa cikin bakinta tana tauna a hankali, Shi dae gabansa kawai yake kallo, Bayan few seconds ya kashe motar ya zare makullin ya ajiye nan kusa da ita without looking at her, ya bude motar xae sauka, da mamaki tana kallonsa tace “Heyy, meye hakan kake yi? Waye xaka bar ma motar?” Still bai kalleta ba yace “Masu shi” Daga haka ya kulle motar ya juya ya bar wajen, kasa cewa komai tayi sbda mamaki, can ta sauka motar tana bin sa da ido baki bude, sae ga Husnah da Naf with Zully da wata kawar Zully, Husnah ta karasa kusa da ita da sauri tace “Nihad what happened, ya da bude baki haka” Nihad ta kalleta tace “I don’t think this guy is okay, ji tafiya yayi ya bar min motar fa Husnah” Husnah tace “Wa??” Nihad tace “New driver din, kiranku fa nayi wai ku gansa, mu yi masa tijara…” Husnah tace “Wai wancan me bakar rigar dake tafiya?” Kasa bata amsa Nihad tayi don da gaske mamaki ne kawai ya cikata, Naf tace “Kawai haka nan ya kama ya tafi babu magana?” Nihad tace “Not at all, ajiye min makulli yayi kusa da ni, nace wa xai bar ma motar, wai masu shi…. kawai ya saka kai yayi tafiyarsa” Lkci daya Husnah da su Naf suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Nihad ta hade rai, Husnah tayi dariya me isarta sannan tace “Gaskiya wannan drivern dan duniya ne, ni ko na so in gansa wllh, ya iya bada amsa dai dai da tambaya” Nihad ta hade rai tayi locking motar ta bar su wajen a tsaye ta wuce aji, bin ta suka yi har sannan suna dariya, a lecture room suka sameta, Husnah ta xauna kusa da ita tace “Anya ba ajiye aikin yayi gaba daya ba” Nihad tace “Toh ni ya kamata ya ba makulli? Ko dama ni na basa makullin?” Husnah ta fashe da dariya har da kife kai.

💖💖 *NIHAAD* 💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

8……

Throughout the day’s lecture mood din Nihad was so dull, gaba daya she wasn’t her self, Husnah tace “Nihad mu je mu ci abinci ni dai na fara jin yunwa” A takaice tace “I am not hungry” Husnah tace “C’mon babe, wai me ke faruwa ne? Gaba daya you look dull today, don Allah ki gaya min me ke faruwa” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Wai har ni mutumin nan xai ma walakanci ya ajiye ma makulli ya wuce Husnah?” Husnah ta ja wani dogon tsaki tace “Ohh this? Wai wannan ne ya canxa maki mood throughout? Lallai ma, To wai meye abun damuwa, kika sani ko barin aikin ma yayi? Ni na fi tunani ya ajiye aikin ne, ba gashi da kika tambayesa wa ya bar ma motar yace maki masu shi ba, probably yayi quitting ne” Nihad dake ta kallonta tace “Sai ya rasa wanda xai ajiye ma aiki sai ni, me yasa bai kai ma Abba makullin ba, salon ayi xaton ni ce na koresa? dama babu wanda ke considering dina a gidan banda Umma, kawai so yake ya kara ja min bakin jini wajen Mumy” Husnah ta ja tsaki tace “Soo what? Idan ma ajiye aikin yayi ai hakan ke kika fi so, abinda kike ta so ne ya faru fa, karkari su gama surutunsu na kwana biyu su yi shiru, sannan a samo wani driver din wanda xa ki juya yanda kike so, ba shikenan ba?” Nihad ta taɓe baki ta mike tana harhada material din karatunta tace “Xan tafi gida” Husnah tace “Gida kuma? Da wuri haka? Ke da nace maki xa mu je guest inn din su Bill yanxu, Kai Nihad yau da kike da full control din mota an bar maki kiyi yanda kika ga dama shine xa ki wuce gida da wuri, haba yan mata, ki bari wajajen six ki koma gidan mana” Nihad tace “Ni kawai gida xan tafi duk raina a bace yake” Husnah ta juya ido tace “Toh ai shkkn, bari in raka ki gun motar” Tare suka isa inda motar yake, Nihad ta ajiye jakanta da kayan karatunta a bayan motar, sannan ta zaga ta shiga driver seat, Husnah na tsaye har ta tada motar ta fara tafiya….. Nihad na isa gate din gidansu tayi horn, mai gadi ya fito da sauri ya bude gate din, ta shiga gidan tayi parking, sannan ta kashe motar ta sauka, kallon inda mai gadin yake tayi, ta ga shi kadai ne a wajen, ta nufi cikin gida ba tare da ta dau material din makarantar ta dake bayan mota ba, Mumy na xaune parlor da Nihal, sai Umma dake parlon ita ma duk suna kallo, ta gaida su xata wuce, Mumy tace “Bani makullin da kika amsa wajen driver daxu” Tsayawa tayi cike da mamaki tana kallon Mumy tace “Mumy wa yace ni na amsa makullin?” Umma tace “Atoh, nima dai nace baxa kiyi haka ba, amma shi algungumin yace kin amshi makulli, kuma sun yarda” Nihad tayi narai narai da ido tace “A yaushe na amshi makulli wajensa? Wllh Umma sharri yayi min” Mumy tace “Ban tambayeki ba’asi ba, makulli nace kawai ki bani, xa kuma mu hade a daki” Nihad ta fashe da kuka tace “Ni wllh Allah ya isa wannan sharrin da yayi min, Allah ya isa tsakanina da shi munafuki kawai, ajiye min makullin fa kawai….” Throw pillow Mumy ta dauke ta jefa mata tace “Tafi ki bani waje, ga ki nan munafuka, wllh tunda haka kika xaba xa mu sa kafar wando daya dake a gidan nan, kuma daga yau kika sake driving da kanki sai dai ki canza wata uwar bani ba” Umma tace “Wai ya kike haka ne Maryam? Shikenan kai da ɗan ka baxa ka ja sa jiki ba komai ya fada maka sai ka karyatasa baxa ka goyi bayansa ba, me yasa kike fiffita bare akan naki? Wannan wace irin rayuwa ce? Ki bar ta tayi bayani ma kin ki sbda rashin adalci” A fusace Mumy tace “Bana son bayaninta, wani bayani xata min sai kace bani na haifeta ba, ko kuma ban san halinta ba, wllh daga ni har ubanki babu me irin wannan mugun hali naki don ma kiji, in har kince ke sai dai ki tuka kanki to wllh ki nemi wata uwar, kuma ai kin saba cewa a baki makullin ba wnn ne karo na farko ba, don haka babu abinda xa ki gaya min in yarda” Kuka kawai Nihad take xuciyarta na suya, ta ajiye makullin motar nan saman kujera tace “Allah ya isa karyan da ya laka min, Allah ya isa tsakanina da shi…” Tashi Mumy tayi, Nihad na ganin haka ta wuce sama da gudu, Mumy tace “Tsaya dai ki min rashin kunya” Mikewa Umma tayi ta fita daga parlon, tana fita compound ta kwalo ma Aminu kira ya taho da sauri, tace “Ina dreban nan yake?” Mai gadi yace “Ya fita ya ɗan amso abu” Tace “Toh xai dawo ya sameni” Daga haka ta juya fuu ta koma ciki. Nihad na shiga dakinta ta sa makulli ta dinga rusa kuka ta dau wayarta tayi dialing number Abba, yana fara ringing ya daga yace “Hello Dear, ina meeting i will get back to you” Ta fashe da kuka tace “Abba ni dai kawai a canza driver din nan, bana son ganinsa kuma, i can’t withstand the sight of him any longer, kawai ni dai Abba ka sallamesa” Abba ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Why did u ask him to hand over the key to you da ya kai ki makaranta?” Nihad ta xaro ido tace “Abba wllh sharri ya min, ta yaya xan ce ya bani makulli, wllh karya yake min ni ban ce masa haka ba” Abba yace “Idan na dawo gida xa mu yi magana yanxu muna meeting ne” Daga haka ya katse wayar, kuka ta dinga yi, nobody is getting her banda Umma, wato dawowa gida yayi ya laka mata wannan uban sharrin gashi kowa ya yarda, number Farooq tayi dialing, yana dagawa shi ma ta rushe masa da kuka yace “Lafiya??” Cikin kuka tace “Yaya dama Abba ne ya dau wani sabon driver, yaya tun da ya fara aiki yake laka min sharri iri iri, yana sa Mumy na kara tsanata, wai daxu ya kai ni schl shine ya ajiye min makulli yayi wucewarsa, da ya dawo gida shine ya je yace ma su Abba da Mumy ni nace ya ajiye min makullin” Farooq yace “To ai halinki ne wannan, amsan makulli a wajen drivers kiyi driving da kanki, ke ko wani driver sai kin samu matsala da shi, haka Habibu farkon da ya fara aiki a gidan nan, why are u always having issues with everybody? Me yasa ita Nihal bata ce an mata ba” Lkci daya ta hade rai, yace “Shi wannan din yaushe ya fara aiki har kika fara samun matsala da shi Nihad?” Kin cewa komai tayi, yace “Ki min magana ko in kashe wayata” Murya can ciki ciki tace “Sallah xan yi” Katse wayar yayi, ta jefar da nata wayar, wato nobody is even supporting her, then xata dau action da kanta. Tana kwance bayan tayi wanka tayi sallah wayarta ya fara ring, ta jawo wayar ganin number da ke kiranta ta mike zaune ta daga tana wara ido tace “Shine baka ce min xaka dawo ba bayan ko jiya mun yi magana” Yace “How are you?” Ta lumshe ido tace “I am fine, ya hanya?” Yace “Alhamdulillah, yaushe za mu hadu? I will be leaving for Abuja next tomorrow” Tace “Wai yau kake nufi xa mu hadu?” Yace “Toh shikenan tunda ba yau ba” Da sauri tace “Noo ba haka nake nufi ba, i only asked, okay yanxu xan shirya in fito in sha Allah” Yace “Where are we meeting?” Tace “U suggest” Yace “How about Royal park…” A hankali tace “Kasan fa an canza mana driver” Yace “Ohh really, when?” Tace “Kwanan nan” Yace “So u are not use to the new one ko?” Ta taɓe baki tace “Aa wannan dan rainin hankali ne, i don’t think we can eva get use to each other” Yace “To yanxu ya za mu yi? Sbda ke na sauka kano fa” Tace “For now pls mu hadu ko a wellcare ne, dama xan ɗan yi shopping…” Yace “Nahh, baxan iya fita don kawai in je wellcare ba, kina nufin a tsaye xan ganki sannan mu rabu?” Tace “No pls, after today i will plan where we will be meeting, ba kace next tomorrow xaka koma ba” Yace “Karfe nawa xa ki wellcare din?” Tace “Kawai shiryawa xan yi yanxu” Yace “Drivern ne zai kawo ki?” Tace “To ya xan yi shi din xai kawo ni, dama kuma Abba ya bani kudin shopping kawai dai ban je nayi ba ne har ynxu” Yace “Okay idan xa ki fito ki kirani” Tace “Tohm, i will call you” Daga haka ya katse wayar. Sosai taji xuciyarta yayi sanyi duk wani bacin rai dake tare da ita ta nema ta rasa kawai muryarsa da ta ji. Bayan ta shirya ta fito ta tafi bangaren Mumy, Tana tsaye a parlon tace “Abba ya turo min kudin shopping, cream dina da sabulu sun kare, ina son xan je in siya yanxu, sai driver yayi dropping dina a can” Mumy tace “Gobe Nihal xata je shopping xata koma makaranta, sai ki bari ku tafi tare” Nihad da gabanta ya fadi tace “Mumy bani da cream din da xan shafa ne fa, let me get even if it’s just the cream today idan ya so goben sai mu je tare, ina gama siyan cream din xa mu dawo gida” Mumy tace “Allah ya tsare, sannan kuma ki yi masa abinda kika saba, ki tabbatar tare xa ku dawo gidan nan da shi” Nihad dai bata ce komai ba ta juya ta bude kofar dakin sannan ta fita. Tana fita compound taga bata ga drivern ba, ta tambayi mai gadi yace “Yanxun nan ya bar nan, ya shiga can bangarensu…. ” Chalet din ta nufa, ta hangosa zaune saman matakalan dake wajen waya kare a kunnensa, yana hangota ya katse wayar kuma ya ki kallonta, ta karaso babu yabo bbu fallasa tace “Hey idan ka ga dama zaka ajiyeni a well care yanxu yanxu” tana fadin haka ta juya ta bar wajen. Da ido ya bi ta, sai kuma ya mike ya ciro makullin a aljihunsa ya bi bayanta, tana tsaye compound din ta kira Aliyu, ta sanar masa gata nan xata fito, bayan ta gama wayar ta karasa ta shiga bayan motar, sai da suka hau saman titi sannan yace “Kwatance xa ki yi” Ta hade rai tace “Kai ko ina sai kace baka sani ba sai an maka kwatance, baka da Google map ne??” Yace “Ban da” Tsaki ta ja, haka ta dinga gwada masa inda xa su bi har suka iso well care, parking yayi a space da ake parking din, tayi dialing number Aliyu, yana dagawa tace “Are u inside?” Waige waige ta fara yi jin abinda yace, tace “I am also outside, where did u park?” Sauke glass tayi, lkci daya ta hangosa, murmushinsa me kyau ya sakar mata yana kallonta, xata katse wayar yayi saurin cewa “Waitt” sai ta fasa kashewa tana sauraronsa, yace “What if idan an ɗan basa wani abu mu ce ya jira mu a nan, mu je eatry… i am jet hungry” Rasa abinda xata ce masa tayi, don ta ce ma Mumy baxata dade ba, can ta saci kallon Khalil ta ga idonsa a kan Aliyu yake ko kiftawa bai yi, duk da glass din a dage yake, kuma tinted ne ba me duhu can ba, a ranta tace wannan ma yayi kama da wanda xai amshi abu idan an basa, bude motar tayi ta sauka ta nufi inda Aliyu yake, shi dai Khalil bai daina kallon Aliyu ba kamar ya ga wani halitta na daban, tana karasawa gun motar Aliyu dake ta kallonta underneath his breathe yace “Waow, baby kin kara kyau fa, tell me what is d secret” Tayi masa murmushi wanda har dimple dinta sai da ya lotsa, sauke idonsa yayi kasa, can ya zaro dollar 100 a aljihunsa yace “In bashi wannan ya jira mu a nan?” Tana kallon kudin tace “Toh kasan dai ba wai mun saba da shi bane, snn bashi da kirki fa wllh” Aliyu yace “Kudi ne baki fara basa ba shi yasa baku saba ba, yana ganin wannan yanxu xaki ga kun dawo kun dai daita kun saba” Bude motar yayi ya fito, walking majestically ya nufi motar, Nihad ta bi sa da kallo, Waige waige khalil ya fara yi da sauri, as if looking for an alternative kafin Aliyu ya karaso gun motar, lokaci daya kawai yayi locking motar kafin ya iso, Aliyu na karasowa ya bude motar yaji a kulle, kwankwasa glass din motar yayi, Khalil ya kauda kai duk da Aliyun ba ganinsa yake ba, Sau biyu Aliyu na kwankwasawa kafin ya daga kai ya kalli Nihad, ta buda masa hannu alamar i told u dama, mamaki ne ya cika Aliyu ya dinga kallon motar, can ya sake Kwankwasa glass din, tace “Dear just leave him ka bar wajen kawai, ba nace maka ɗan iskan yaro bane” Aliyu da ransa ya gama baci yace “Who did he think he is, da driving din da yake yi ake biyansa yake takama ko me? Waye shi yana matsayin just driver xai kulle mota yana jin ana kwankwasawa ya ki budewa, kuma ba wai bai gan ni bane” Nihad tace “Ai ban ta6a ganin mutum me karfin hali irin yaron nan ba” Aliyu yace “Look Nihad idan kika shiga school gobe xa mu hadu, i can’t stand here any longer, mood dina ya baci seriously, ba a ta6a ci min fuska irin yau ba” Nihad tayi shiru tana kallonsa duk jikinta yayi sanyi, don kana ganinsa kasan ransa yayi mugun baci da gaske, tafiya ya fara yi kawai ya koma gun motarsa ya shiga ya tada yayi zoom off, da ido khalil ya bi sa har ya hau saman titi, Nihad ta dinga kallon motar tana jin kamar ta rushe da kuka ko xata ji sauki a ranta, mutumin da tayi wata da watanni bata gani ba, shine wannan drivern xai 6ata ma rai har ya tafi?? Ta fi minti biyu tsaye kawai kallon motar take with different thought running her mind ga wani kullutu da ya tokareta a makogwaro sbda bakin ciki da takaici, a duk abubuwan da yake mata bata jin akwai wanda ya mata ciwo ya ta6a har karshen xuciyarta irin wannan, she is trying her best not to cry, don har idonta ya cicciko, kiris ya rage ta fashe da kuka a wajen, Khalil dake ta kallon duk expression da reaction dinta ya shafa kansa, sai kuma ya sauke both glasses yace “Naga kamar kin fasa siyayyan, kuma ga hadari, ni kuma bana tuki cikin ruwa ko in baki makullin in yi tafiyata??” Wani matsiyacin shegen kallo tayi masa, ta bude back seat ta shige motar ta kulle da karfi tana kara danne kukan dake cin ta, tada motar yayi, yayi reverse ya dau hanyar gida, har suka isa gida Nihad danna kukanta take, bayan yayi parking ta bude motar ta sauka ta tafi gun driver seat ta tsaya tana nunasa da yatsa tana huci tace “Sai kayi da ka sanin abinda kayi min yau wllh, kuma ni ce sanadin barin ka gidan nan, banza mahaukaci kawai talaka” Kashe motar yayi ya sauka yana kallonta ya kara mata kunne gaba yace “Kamar kina magana?” Da wani bakin ciki ya mamayeta bata san sanda ta cakumo kwalarsa ba duk da uban tsayinsa tsaurin idonta bai sa taga hakan ba, tana jijjigasa da duk karfinta hade da kunduma masa wani mummunan zagi, mai gadi dake ganin komai ya karaso da gudu jikinsa na bari yana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Subhanallahi… ” Khalil dai kallonta kawai yake baya ko kiftawa, cikin nutsuwa yace “Cika ni” Ta buga wani uban tsawa tana dungure masa goshi tace “An ki a cika ka din, kayi uban da xaka yi in ga, kai har ka isa kana aiki ƙarƙashinmu kana matsayin Drivern gidanmu ka dinga kawo min raini? Ni ce ma zaka raina? Kasan wa ka walakanta daxu?? To wllh ko kaff zuri’arka xa a siyar idan har Aliyu ya daureka kudin da aka siyesu bai isa yayi bailing dinka ba” Nihal ta fito cikin gida da kawarta xata mata rakiya ganin abinda ke faruwa ta karaso da sauri xata ta janye Nihad tace “Nihad what’s this u are doing, don’t u have manners? Meye wannan kike yi?” Nihad na huci ta bangajeta a fusace tace “Eh ban da shi, sai ki ara min naki ke me shi, a kan matsiyacin nan xaki ce min bani da manner, kin san abinda yayi min ne?” Nihal na kallon Khalil cike da damuwa tace “Don Allah kayi hakuri” Yana warware rigarsa da Nihad ta cakuikuye yace “Ba komai… fita xa ki yi ne?” Nihal dai duk jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, yace “Ko ba fita xa ki yi ba?” tace “Aa Kawata xan raka bakin titi” ya kalli kawartata dake tsaye ita ma tana kallon abun mamaki, yace “Ohk to, ta hau sai na ajiyeta a gida, xan jira ta a waje….” Yana fadin haka ya koma motar ya tada ya bar wajen, mai gadi ya tafi da sauri ya  bude gate, Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ba, da hanzari ta shige cikin gida tana kuka sosai. Bayan ta ci kukanta me isarta ta dau wayarta ta kira Aliyu, har ya katse bai daga ba, ta kuma kiransa nan ma no response, hawaye ne ya dinga sauka idonta, bayan kusan awa daya ta mike ta gyara idonta ta fita, bangaren Mumy ta tafi sai taga kamar tana da bakuwa, hakan ya sa ta bar wajen ta tafi gun Umma, Umma tace “Lafiya me ya sami idonki Nihad?” Cikin rawan murya tace “Umma Aliyu ne ya dawo shine muka yi da shi xa mu hadu a wellcare, bayan mun hadu sai ya sauko daga motarsa yace bari su gaisa da driver ai ko in gaya maki mutumin nan yayi masa walakanci mafi muni, ya kulle motar ya kuma ki ya sauke glass, banda Abba da ya ja mana ina Driver xai ma tsaya same place inda nake balle Aliyu? Yasan waye uban Aliyu a kasar nan, kaskantar da kansa fa yayi ya tafi su gaisa maimakon shi drivern ya sauko ya taho har inda yake ya gaishesa amma ya masa wannan mugun walakancin” Umma dai sakin baki tayi tana kallon Nihad, can tayi kasa da murya tace “Wai har yanzu kuna tare da Aliyun nan ne dama?” Nihad ta gyada mata kai tana matsar kwalla, Umma tace “Ba kince min kun rabu ba kwanaki?” Nihad tace “We came back together 1 month ago” Umma tace “Ke dai bakya ji Nihad nace ki fita harkan yaron nan, ba mutunci ne da familynsu ba kin ki, nace ki rabu da shi in kina son sama ma kanki mutunci kina son ki tsira da mutuncin ki, ina ke ina Aliyu banda dai yaudaran kai Nihad? Kika san wasu irin yan mata yake hulda da? ‘ya yan shugaban kasa yake hulda da fa” Nihad taki cewa, Umma tace “Gaskiya kar ki sake kulasa ni dai na gaya maki, yana son ki ne ko sau daya bai ta6a takowa ya xo gidanku ba? Sai dai soyayya a titi da makaranta, kema kinsan yaudaran kanki kike don Aliyu ya fi karfin ki, me ma xai kawosa gidan nan? waye ubanki a inda ubansa yake, inaa ai nisan ma yayi yawa, balle ma duk yan iska ne yaran masu kudin nan wa enda idonsu ya yage har kunne, banda lalata yara da bata masu rayuwa babu abinda suke” Nihad still ta ki cewa komai, Umma tace “Kin min alkawarin xa ki rabu da shi kiyi blocking dinsa kamar yanda kika yi blocking din Ahmad yanxu?” Nihad ta turo baki tace “Ni dai ina sonsa Umma, shi ma kuma yana so na ai, da baya so na baxai dinga kirana ba har yace mu hadu a wani waje, dama ce maki xanyi xan je gidansu Baffa ko da Mumy ta tambayeni” Daga haka tayi ficewarta daga parlon Umma ta bi ta da ido ko kiftawa babu, Nihad na sauka downstairs ta fito compound, fuskar nan nata a murtuke ta nufi gate, mai gadi dai ya kauda kai da sauri don tare suke da Khalil, shi dai ya rasa kan wannan abinda ke faruwa tsakaninta da Khalil, yana mugun ganin karfin halin Khalil da baya nuna shakkarta kamar su, har ta fita gate ta dawo tana kallon mai gadi fuskar nan nata babu rahama tace “Kai in ji dai kuna kula min da tsuntsaye na? Don idan har wani abu ya samesu wllh kaf gidan nan duk sai kun raina kanku ban cire kowa ba kuma” Da ladabi yace “Ko daxu sai da naje can da kaina Hajiya” Ficewa tayi daga gate din bayan ta maka ma khalil da bai ma san tana yi ba harara, Mai gadi ya kalli khalil yace “Sai fargaba nake kar tace xaka kai ta wani waje” Khalil yayi murmushi yace “Meye a ciki, sai a kai ta ai…” Da yake babu wani nisa da kafa Nihad ta bi ta cikin anguwanni har ta isa gidan yayan Abbanta, Hamid na xaune compound tare da wani abokinsa, kallo daya tayi masu ta kara gaba abunta, Abokin nasa yace “Wannan ba cousin din nan taka bace, naga ta wuce bata ce maka komai ba, and kamar kuna good time da ita ai” Hamid yace “Noo, step sisters dinta ne muke good time, wannan ai yar iska ce” Abokin yace “Shit but sun yi kama sosai, kamar har ya wuce misali” Hamid yace “Toh wannan da kake gani ji take da girman kai da rainin wayo, sannan runz girl ce…” Abokin ya wara ido yace “Waow dai dai mu kenan, ka hadu mu to” Hamid ya masa wani shegen kallo yace “Ai da manyan mata ake runz ba kwailaye ba, kwailar ma fitsararriya irin wannan” Tuni Nihad ta shige gidan, direct part din Kakarta ta nufa, tana bude kofar dakin ta shiga, inna tace “Aa, daga ina haka, Ibrahim din ya shigo ne” Nihad tace “Ni kadai ce” Inna tace “Aa naga sai ya taso keyarki kike xuwa shi sa abun ya daure min kai, ina ce tare ku ke” Nihad ta nemi waje ta xauna, Inna tace “Baki da lafiya ne?” Nihad ta fashe da kuka kamar jira take tace “Inna wani sabon driver Abba ya dauka, yaron ba shi da kunya ya raina ni inna, ba irin rashin mutuncin da baya min” Inna da ta saki baki tace “Shi Dreban?” Nihad ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Inna tace “Ko ba wani gansameme ba yana tafiya gansan gansan?” Nihad tace “Shi” Inna tace “Toh ai Ibrahim din ya kawo sa har nan ya gaisheni, amma ni na xata ɗan arxiki ne, don har kasa ya duka ya gaida ni” Nihad tace “Wllh na munafurci ne….” Nan ta labarta ma inna abinda ya faru kamar yanda ta gaya ma Umma, Inna tace “Ba lafiya, shi dreban??”

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

9…..

Nihad na shesshekan kuka tace “Wllh shi inna, kawai an bar sa yana ta abinda ya ga dama a gidan kamar gidan ubansa, duk ya gama rena ni, ko gaisuwa bata hadani da shi” Inna tace “Duk ba wannan ba, yanxu kin kira Aliyun??” Nihad ta daura kanta gefen gadon inna hawaye na sauka idonta tace “Bayan ya ki dagawa” Inna ta dauko wayarta ta mika mata tace “Kirasa da nawa” Nihad tace “Ae idan ba shi da numberka baxa ka iya samunsa ba, ya sa layinsa a Private” Inna tace “Wai ko ba dai Aliyu ɗ’an wajen janaral Habubakar jikamshi ba?” A hankali Nihad tace “Shi…” Inna tace “To wannan dreba duk yanda aka yi tsinanne ne, ko don nace masa ya saki jikinsa yasa ya sake kamar gidan ubansa? to ai ni na xata yaron arxiki ne” Salati inna ta saki tayi tagumi tace “Yau naga dreban jaraba, ashe duk ni na ja komai da nace ya saki jikinsa, to a kira min Ibrahim din tun yamma bai yi ba ya sallamesa” Nihad ta dau wayar inna da sauri ta fara neman number Abba tayi dialing, Inna ta bude baki ta rike ha6a tace “To shi kuma Aliyun banda abunsa garin yaya xai ce sai yayi ma dreba magana mutumin da ba ajinsa ba, ai abinda bai sani ba talakawan nan haka suke da dacin rai kamar mutum ne ya doro masu talaucin, ina shi ina wani basamuden buzun dreba can? To ko a almajiri dai baxa su yarda su ajiye wannan mutumi a gidansu ba balle dreba, su da tun daga titin da ya yanka unguwarsu xaka fara ganin dirka dirkan sojoji har da motocinsu….” Nihad ta turo baki tace “Abba bai daga ba” Inna tace “Ina xai daga, ya tashi ya kawo wani kato gansameme kamar mutanen farko ya dau mota ya basa, ni wllh ranan da na fara ganinsa sai da na tsure, sai fa ya daga mutum ya nanasa da kasa sau biyar bai gaji ba, irinsu ai gadin dogon banki ya kamata a basu ba wai motar mutane ba” Nihad dai tayi tagumi don abinda ya dameta daban, ita yanxu ta ya xata fara shawo kan Aliyu, da yaya ma suka dawo soyayyar, Inna tace “To ko kin san inda ya sauka ki rakani mu je in basa hakuri” Nihad ta kalleta tace “Ji ki kuma, kawai don ki ja min raini?” Inna tace “Wani raini mutumi na nema ya kubuce, wa ke ta wani raini Nihad, idan ma baxa ki shiga ba ni ki rakani ki nuna min hanya in je in samesa” Nihad tace “Aa ke dai kawai duk yanda xa kiyi kiyi Abba ya kori driver din nan kawai” Inna tace “Yo sai ma kin fada, abu har ya kai yana korar ma jikokina samari” Hamid ne ya bude kofar dakin ya shiga yana kallon Nihad yace “Ke don uwarki ni sa’anki ne xaki wuce ni da abokina baki gaishemu ba” Nihad ta turo baki ta koma gefen Inna, Inna dai bata ce komai ba, Yace “Mahaukaciya kawai, uban wa xaki dinga daga ma kai?” A fusace Nihad tace “Kina dai gani babu abinda na masa ya xo ya fara xagina ko inna, ni fa shi yasa bana son xuwa gidan nan wllh, kowa yaje yaji da mugun halinsa” Cikin xafin nama ya nufeta, Inna ta mike ta wangale hannu tana tare Nihad tace “Dokeni to, Hamidu nace ka dokeni” Huci yake yana kallonta, Inna tace “Ai dama ka saba dukan nawa yanxun ma ka duka, ranan da ka biyo Bilkisu ai ni ka jibga ba ita ba” Nihad ko kallonsa bata yarda ta sake yi ba, Yayi wani kwafa ya fice daga dakin, Inna ta kulle dakinta tace “Kinsan korosa aka yi daga can kasar wajen wai wa’adinsa ya kare a can, to kuma sai kayi ta hucewa kan ya yan mutane” Nihad bata san lkcn da ta kyalkyale da dariya ba, Inna tace “Allah haka uban yace min, duk a booth din jirgi aka kwaso su aka dawo” Nihad dai bata ce komai ba, Inna tace “Yanxu ko kin boye number ki baxai daga wayar ba?” Nihad ta mike tace “Ni dai xan tafi inna dama anjima da daddare kice Hamid din ya kawoki nan gidanmu ki samu Abba da kanki” Inna tace “Toh shkkn ma, kawai bari inje in riskesa a gidan ba sai mun yi waya ba, idan ma ya kama ko shi sai ya kira Aliyun ya basa hakuri” Bude baki Nihad tayi, can ta kyabe bakin tace “Ni dai sai kin zo” Daga haka ta fita daga dakin, A bakin gate abokin Hamid ya tare ta da ya faki idon Hamid ya biyota, yana fara magana ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu tana yatsine fuska tace “Ina wasa da kai ne malam?” Daga haka ta ja tsaki tayi ficewarta daga gate din, ya bi ta da kallo baki bude, dama Hamid ya gaya masa ya ki ji. Nihad na komawa anguwansu ta yi ido hudu da Khalil dake xaune kan dakali a kofar gida wayarsa na kare kunnensa, yana ganinta bai sake cewa komai ba a wayar da yake kuma bai cire wayar a kunnensa ba, har ta isa dai dai inda yake, tayi masa wani harara ta ja tsaki ta shige cikin gida tayi banging gate din. Abba na tsaye balcony bayan magrib Khalil ya karaso da ladabi yana kallonsa yace “Gani Alhaji” Abba yace “Yauwa pharmacy xan aikeka ka siyo min magani yanxu” Khalil yace “Toh, ya sunan maganin?” Abba na duba wayarsa yace “Yanxu likitana ya turo min ta message bari dai in duba” Abba na shiga message din har ya fara pronouncing sunan maganin kawai ya fasa kar khalil yaje ya masa shirme, yace “Bari kawai xan rubuta maka a takarda kaje ka siyo, idan ka siyo sai….” Abba ya dakata ganin mai gadi na bude gate, sai ga motar Hamid ya shigo compound din, Abba yace “Je ka xan rubuta sunan maganin a kawo maka yanxu” Yace “Toh Alhaji” daga haka ya nufi boys quarters, Inna ce ta sauka daga motar ta nufo balcony, Abba dai na tsaye yana ta tunanin ko lafiya, Tana isowa ganin yanayinta yace “Lafiya inna?” Tace “Ina fa lafiya, mu je parlor baxan iya tsayuwa ba” Sai da ta fara shiga parlon Abba ya bi ta, kanta tsaye ta tafi parlonsa duk yana biye da ita, ta nemi waje ta xauna shi ma ya xauna yace “Ina yini Inna?” Tace “Ibrahim a ina ka samo wannan gansamemen dreban naka?” Abba yace “Wani abu ya faru ne?” Tace “Meye baxai faru ba, ya kora ma Nihad saurayi, d’an wajen Janaral Jikamshi, har yaron ya goge numberta yanxu haka da nake maka magana” Abba yayi shirui yana kallonta as if confused don ya kasa fahimtar xancen nata, Inna tace “A kara min Ac, xafi ya isheni” Abba ya dau remote ya kunna Ac din, yace “Ban fahimta ba Inna” Nan inna ta xauna tayi ma Abba tsari da abinda Nihad ta fada mata da ma wanda bata fada mata ba duk ta dire ma Abba, Abba yace “Ikon Allah, ke yanxu wa ya sanar maki wannan?” Inna tace “Har gida ta sameni tana kuka kamar ranta xai fita, hankalina yayi mugun tashi shine nace da kaina xan taho da daddaren nan, sannan a kira min dreban in ji uban da ya aikosa wajenmu, ni dama ina ganinsa na sha jinin jikina ban yarda da shi ba kawai nayi shiru ne, wa yasan adadin binne binnen da yayi maka a gidan nan yanxu? Huhuhu kana wasa da buzun mutum, Ai irinsu xuwa suke su tarwatse gida kai har ma su talauce mai gidan su saci abinda xa su sata su gudu su koma Nijar, to Ibrahim ko motar nan ma ya gudu maka da shi ai ya cuceka, to yanxu ni dai a kira min shi ko in tafi in samesa da kaina” Abba yace “Aa ba sai kin samesa ba, ai sallamarsa kawai xanyi ya tafi ba sai anyi wani tashin tashina ba” Inna tace “Aa ko xagi ne a bari in masa kafin ya tafi ai” Abba yace “Ke dai nace ki bar komai a hannuna, bari Hamid ya xo ya maida ki gida dare yayi” Tace “Ai Habubakar ne ya sa ya kawoni banda haka waye ubana Hamid xai kawoni, tun fa da aka korosa daga kasar wajen yake jin haushin kowa, to ni nasan sanda ya koma can da xama balle sanda aka korosa, kawai gani nayi ya dawo da manyan jakunkuna, ji yake kamar duk ya kashe mu yanxu haka” Abba yace “Ke wa yace maki an korosa, don Allah ki bar fadin wnn magana a xata da gaske ne” Mikewa yayi ya fita daga parlon ya kira Hamid dake main parlor yace “Zo ka maida Hajiya gida” Yace “Toh Abba” Har mota ya rakata, bata ce xata shiga wajen matansa ba shi ma bai ce ta shiga ba, don da suka fito parlor ma yace Nihal ta kirasu su gaisheta ta hana, yana tsaye compound din har motar ta fita, yana kallon mai gadi dake kulle gate yace “Kai ina Ibrahim?” Aminu bai kai ga bada amsa ba sai ga khalil da mota, Aminu ya kara bude gate din Khalil ya shiga compound din da motar sannan yayi parking a parking space Abba dai ya bisa da kallo, yana sauka daga motar ganin Abba a tsaye, ya nufesa da ledan pharmacy a hannunsa ya ɗan risina yace “Ga maganin Alhaji” Abba yace “Wani Magani?” Khalil ya kallesa yace “Da kace a siyo” Abba yace “Na gaya maka maganin da zaka siyo min ne?” Khalil ya kalli ledan hannunsa da sauri, kawai sai ya rasa abinda xai ce, Abba ya amshi ledan ya bude maganin sannan ya bude wayarsa ya shiga message din da Dr dinsa ya turo masa yaga maganin ne Khalil ya siyo, Abba ya daga kai yana kallonsa daga sama har kasa, kafin yace komai khalil yayi saurin cewa “Ai ka fada min sunan maganin, rikewa nayi a kai” Abba dai bai ce komai ba sai kallonsa yake, Khalil kam ya kasa barin su hada ido, Can Abba yace “Ban gaya maka sunan maganin fully ba” Da sauri khalil yace “Ka tambayi Habibu a can garinmu akwai wani likita da ya bude Kemist na siyar da magunguna, na fi shekara takwas ina jire masa shago yana bani wani abu duk wata, Allah ya bunkasa masa shagon sosai, rasuwa Allah yayi masa shine yaransa suka rufe shagon bayan sun bada sarin duk magungunan da ya bari, wannan dalilin ne ma har yasa da Habibu yayi min tayin wannan aikin na taho kano don ina xaune babu abinda nake, don haka babu wani magani da ban sani ba yanxu haka sai abinda ba a rasa ba…” Abba yace “Allah ya rufa asiri…. Yau kuma me ya hadaka da Nihad?” Khalil ya sunkuyar da kai yace “Bani da masaniyar na mata wani laifin yau, kawai dai abinda na sani saurayinta ya zo zai bani kudi yau da na kai ta babban shago xata yi siyayya, sai na nuna baxan amsa ba, shkkn abinda na sani kenan Alhaji” Abba yace “Kaje xa mu yi magana gobe” Daga haka Abba ya nufi cikin gida, Khalil ya koma gun mai gadi ya zauna letting out a deep breath. Washegari da safe Nihad ta leka window ya fi sau goma wai taga ko driver ya fara harhada kayansa xai bar gidan, amma sai taga ya kai su Sudais da Amina school, kuma da ya dawo taga ya ci gaba da zama bakin gate, kasa samun sunkuni tayi, ta dau wayarta tayi dialing number Inna, yana fara ringing ta daga, tace “Ina kwana inna” Inna tace “An tashi lafiya” Nihad tace “Inna wai jiya ya ku ka yi da Abba da kika xo ne?” Inna tace “Yace xai yi masa koren kare, ai shi bai san haka yake ba, da kyar ma in ya kwana a gidan ki bincika ki ga” Nihad tace “Wani bincike bayan ga mutum can a zaune ina kallonsa” Inna tace “Atoh, Kilan sai yau xai tafi, ai na gaya ma Ibrahim maganganu masu ta6a xuciya jiya, yace min in sha Allahu xai sallamesa, ina jin sai yau din xai koresa don jiya kinga ai dare yayi kar ace mutum bai da imani yayi kora cikin dare” Nihad tace “Sai anjima” Katse wayar tayi ta bude kofar daki ta fito, a parlor ta hadu da Nihal, Nihal tace “Kinsan in two days time xan koma school” Nihad ta tsaya ta kalleta tace “Toh ai baki gaya min ba” Nihal tace “Toh yanxu na gaya maki” Nihad tace “Toh yanxu da Habibu baya nan waye xai kai ki Zaria?” Nihal tace “Ni ma ban sani ba, sai Abba yayi magana” Nihad tace “Don kinga wannan drivern sallamarsa xa ayi yau” Nihal dake ta kallonta tace “Okay” Nihad tace “Ko dai har kinyi shopping din ki?” Nihal tace “Aa probably today or tomorrow, sai yanda Abba yace” Nihad tace “Okay ki min magana sai mu je har da ni” Nihal tace “Okay, baki da lectures yau?” Nihad tace “Toh ko ina da lectures ai babu driver da xai kai ni, but karfe tara nake da lectures” Bata jira cewar Nihal ba ta nufi kofar fita parlon ta fito compound, Backyard din gidan ta nufa kai tsaye gun tsuntsayenta su Saminu na gaisheta duk tayi kamar bata ji su ba, tsaye tayi bata motsin kirki tana kallon cages din birds din da duk suke a bude kuma babu birds din a ciki sai roban abincinsu da ruwa, duk cages din guda hudu a bude suke har na parrot dinta, Dawowa tayi da gudu cikin gida tana kallon Saminu dake shara Shafi’u na watering flowers din gidan cikin tashin hankali tace “Saminu ina tsuntsaye na aka kai min?” Saminu ya mike da sauri haka Shafi’u da yayi dropping watering can din hannunsa, Saminu yace “Suna can cikin kejinsu Hajiya” Ta gwalo ido tace “Wani cage din??” Duk suka nufi inda birds din suke, sai ga su sun dawo suna wuri wuri da ido, Saminu na in ina yace “Wllh Hajiya ko jiya sai da muka xuba masu abinci da ruwa….” Da sauri ta juya ta bar wajen ta nufi gun mai gadi cikin rawan murya tace “Aminu ina aka kai min tsuntsaye na?” Aminu yace “Suna can keji Hajiya” Cikin daga murya tace “Wani Cage din, abinda naje na tarar a bude babu komai ciki” Mai gadi ya mike da sauri yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, babu komai ciki?” Shi dai Khalil na xaune yana danne danne da torchlight phone, Aminu ya nufi inda birds din suke da sauri, Nihad da har kanta ya sara mata ta bi bayansa gabanta na faduwa, can ba a dau lkci ba sai ga ta ta dawo tsakar compound ta rusa wani uban ihu ta daura hannu a ka uwa warce aka yi ma mutuwa, Nihal ce ta fara fitowa a guje ta nufota tace “Nihad what happened?” Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace “Wani yaje ya bude min cage din birds dina duk sun gudu, wayyo Allah na na shiga uku, wllh har sun saba dani Nihal, Parrot din har kiran sunana yake yace good morning” Su Aminu da Saminu dai na can gefe a tsaye sai wuwwurga idanuwa suke, Umma ce ta fito compound din Mumy na biye da ita a baya, Hankali tashe Umma tace “Lafiya Nihad, me ya faru?” Nihad ta nufeta tana kuka sosai ta kamo hannunta tace “Umma wani yayi releasing din min birds dina duk sun gudu babu ko daya” Umma ta saki salati tace “Waye da wannan danyen aikin, yanxu babu ko daya wa ennan tsadaddun tsuntsayen da Abbanki ya siya maki” Nihad na gyada kai cikin kuka tace “Wllh duk sun gudu, bude masu cage din aka yi don su gudu” Mumy dake kallonta tace “Shine xa ki 6ara baki haka ki daga mana hankali Nihad?” Umma ta kalli Mumy tace “Haba Maryam, ko don ba ke kika bada kudin siyan tsuntsun ba, kinsan yanda dabba ke da shiga rai kuwa” Mumy tace “Toh waye ya budesu har suka gudu? Sannan ita me yasa bata xuwa dubasu a kai kai yaushe rabon da taje inda suke” Cikin kuka Nihad tace “Wllh ina xuwa dubasu ki tambayi Aminu, kullum sai naje dubasu” Nihal tace “Toh ko da aka basu abinci ne aka mance ba a kulle cage din ba” Nihad ta durkushe wajen tana kuka kamar ranta xai fita tace “Ni wllh ko ma wa yayi min haka Allah ya isa ban yafe ba, Allah ya tsine ma koma waye, Allah ya isa, shi ma sai an nemasa an rasa wataran yanda na rasa tsuntsaye nahhh” Juyawa Mumy tayi ta wuce cikin gida, Umma ta dagota tace “Ai ba Allah ya isa xa kiyi ba, koma uban wa yayi wannan aika aikan dole a ganosa a hukuntasa, ki bar komai a hannuna kawai” Nihad na shessheka tace “Umma wanda yayi mun haka ya tsaneni ne shi sa yayi haka kuma sai Allah ya tsine masa albarka ya daidaice, Allah ya isana” Nihal tace “Ki daina cewa haka baki san ko…” A fusace Nihad ta mike ta hankadeta har sai da ta kusa faduwa, tace “Shut up plss if have nothing good to say” Bude baki Umma tayi, sae kuma ta kalli Nihal tace “To wuce ciki” Nihal ta ta6e baki ta juya ta koma ciki, Umma ta juya ita ma ta bar wajen, Nihad ta hade rai ganin yanda ma’aikatan gidan ke kallonta, cikin tsawa tace “Uban meye kuke wani kallona munafukai yan iska, ai har da hadin bakin ku aka sakar min tsuntsaye suka bi duniya, to ku sani wllh daga yau sbda ku ni xan dinga shiga kitchen sai in ga d’an iskan da xai xubo maku abinci ya kawo maku, for one week ba ku da abinci wllh a gidan nan tunda har aka sakar min tsuntsu suka gudu” Tana fadin haka ta juya fuuuu ta wuce ciki. Da yammacin ranan Farooq ya shigo gidan daga Abuja, Nihad da abun duniya ya isheta don har sannan Aliyu isn’t picking her calls, ga kuma har yanxu bata ga Driver ya bar gidan ba, kuma babu ma wata alamar da ta nuna xai bari, yana nan a xaune tare da mai gadi, ko makaranta bata je ba sbda damuwa gashi har test Husnah tace mata anyi, ta mike daga xaman da take ta yi a parlor ta fito compound jin motar Farooq, tamke fuska tayi ganin Khalil da Aminu sun nufi Farooq, Khalil ya fara basa hannu da ladabi, suka gaisa, farooq dai sai kallonsa yake, Aminu dake ta rawar kafa yana washe baki yace “Ae shine sabon dreban gidan tun bayan tafiyar Habibu, yau kwanansa biyar ina jin a gidan nan” Farooq ya kara kallon Khalil daga sama har kasa, sai kuma yace “Driver??” Sai kuma yayi saurin cewa “Ohk maa sha Allah, ya sunanka?” Khalil yace “Ibrahim” Farooq ya gyada kai yace “Maa sha Allah….” Tuni Mai gadi ya dau jakar Farooq ya nufi cikin gida da shi, Nihad dake tsaye balcony ta hade rai tace “Toh ajiye kayi tafiyarka ko ka aikesa ne??” Aminu ya ajiye jakar ya juya sui sui ya bar wajen, Farooq ya amsa gaisuwan da Nihal ke yi masa ya nufi Nihad yace “What happened Nihad?” Kamar jira take ta fashe da matsanancin kuka, yace “Meye haka?” Cikin kuka tace “Ya Farooq wani axxalumin da baya tsoron Allah ya bude ma tsuntsaye na cage duk sun gudu har parrot din” Bude baki Farooq yayi yace “Garin yaya?” Ta karasa ta rungumesa tana kuka sosai, ta gefen ido khalil ya kalleta kafin ya juya ya bar wajen, Farooq ya dago kanta yace “But how did it happen” Tace “Kawai yau da safe naje basu abinci naga ba komai cikin cage din” Yace “Ow that’s bad, bari anjima sai mu je ki siyo wasu” Ta marairaice tace “But how will d parrot get to know me just as the old one?” Yace “Yanda wancan din ya sanki sabon ma haka xai san ki” Daga haka ya kama hannunta suka shiga gidan tana share idonta. Bayan ta amshi nata tsaraban da farooq ya kawo mata ta wuce sama xuwa dakinta, wayarta ta dauka ta sake kiran Inna, yana fara ring Inna ta daga, Nihad tace “Inna har yanxu fa driver din na nan babu inda ya tafi don ma in gaya maki” A fusace inna tace “Ke raba ni da wani shegen dreba an shigo an kwashe min yan canjina wai barin gidan da nayi jiya da magariba, kowa sai ce min yake ba shi bane, to ni na saci abina koko?” Nihad ta tabe baki ta katse wayarta, sai kuma ta ja tsaki tace “Dama ba a abun arxiki dake…” Da daddare tana dakin farooq dake kallonta yace “Toh sai in ce masa me idan na kirasa?” A hankali tace “Kawai hakuri xaka basa a kan abinda driver din yayi masa” Farooq yace “Ba kince layinsa a kulle yake ba?” Tace “Aa ya ta6a saving numberka a gabana ai, ka tuna sanda ya kiraka da baka da lafiya?” Yace “Oh, ohk” Daukar wayarsa yayi ta kira masa number Aliyu yayi dialing, a kashe suka ji wayar, yace “It’s switch off” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Ki je kawai, gobe sai in kirasa” Mikewa tayi tace “To sai da safe yaya…..”

Saura how many page free pages ya kare???

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_📖✍🏻

10……

Khalil na xaune yana waya a bakin gate mai gadi ya karaso wajen daga boys quarters, Khalil ya saka wayar a aljihunsa bayan ya gama, Aminu da har ya xauna ya mike yace “Aa bari in baka waje ka ci gaba da wayarka….” Khalil yace “Na gama” Aminu ya dawo ya xauna yana kallonsa yace “Na lura baka son kayi waya a gaban mutane saboda hayaniya ko?” khalil yace “Haka ne” Aminu yace “Ina can tare da su Saminu muna ta jajanta lamarin tsuntsayen nan da suka gudu, abun da mamaki da al’ajabi, sun kusa shekara daya da rabi fa a wajen ba a ta6a nemansu an rasa ba sai yau” Khalil yace “Ai gwara da suka gudu kar xunubanta ya dinga shafarsu su ma” Aminu ya kyalkyale da dariya yace “Wllh baka da dama, ni tashin hankalina abincin da tace xa a hanamu, in an hanamu abinci ya xa mu yi? Ba fa kanta kenan, duk da nasan uwarta baxata yarda da hakan ba, amma makira ce tana iya biyomu ta kwace idan an kawo mana” Khalil yayi murmushi kawai, Aminu yace “Amma fa kana bani tsoro da mamaki yanda kake nuna mata baka shakkarta, akwai wani littafi da na ta6a saurara a shafa labari, kaga yanda ta sa ka gaba haka? To haka ita ma yarinyar littafin ta sa mutumin gaba yana aiki a kampanin babanta ita kuma ita ce manaja a kampanin, tayi ta masa walakanci da rashin mutunci daga baya ta xurma sonsa in gaya maka, To sai….” Dakatar da shi khalil yayi yace “Me kake nufi?” Aminu ya gyara xama yana washe baki yace “Toh wa ya sani ko hakan xai iya faruwa wataran, barin taga sambalele me dogon hanci, ka fa san matan nan ba alkibla garesu ba….” Khalil yace “Ta wahala…. banda abun ka ina ita ina talaka? Sai dai kuma bata san wani talakan ma ko da kudi aka hadasa bazai saurareta ba, in dai kamar ni talakan yake wllh ko kallonta baxai yi ba” Aminu ya gwale ido, sai kuma ya tuntsire da dariya yace “Yanxu kana nufi misali yau ace maka gata nan ka aura baxa ka aura ba?” Khalil yace “Misalinka ba me yiwuwa bane har duniya ta nade, don kuwa da in aureta gwara na aura Krista, ko kuma in dauwama ba auren, kai kasan darajan da Allah yayi ma ɗan Adam kuwa? To bari kaji ko da kudi wannan yarinyar baxata tsaya inda budurwata take ba, ga ta dai yar talakawa kamar ni amma ita wannan fitsararriyar baxata tsaya inda xata tsaya ba wllh….” Aminu yace “Aa dole xaka ji haushinta wllh, nima kuma ina taya ka jin haushinta kullum, ji tijaran fa da tayi maka daxu, banda yanayin rayuwa a ina xata ganka har ta cakume kwalar rigarka tana dungure kanka tana maka munanan xagi, a ƙalla ai xaka bata kusan shekara goma na sani, amma ta maka wnn cin mutunci da tijara gaban Nihal da kawarta, ba ma wannan ba ji yanda ta dau bahon ruwa gaba daya ta juye maka a cikin jama’a” Khalil yayi wani Murmushi bai dai ce komai ba, Aminu yace “Ni dai yau ace min ga ta in aura xan yarda in aureta ko don kudin babanta da kuma halaccinsa, sai kuma in saita mata xama….” Daga sama har kasa khalil ya kalli Aminu, bai san sanda yayi dariya ba yace “Kai ta kudin kake kenan” Aminu ya washe hakora, Khalil ya girgiza kai yana Murmushi, Aminu yace “Wllh ni fa naji dadin bude kejin nan da aka yi tsuntsayen suka gudu, Allah ne ya bi min hakki na abinda ta min jiya a kan su” Khalil yace “Ku kuka bar mata tsuntsayen suka kai har warhaka a gidan ai” Daga haka ya mike ya bar Aminu a wajen xai je yayi alwala kafin a kira isha’i.  Nihad na komawa dakinta taga missed calls din Husnah da yawa, ta xauna gefen gado ta kirata, yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad ta dinga jin hayaniya tace “Kina ina haka?” Husnah tace “Mozida suite” Nihad tace “Me ake yi a nan?” Husnah tace “Wllh na manta ban gaya maki ba shekaranjiya a schl, Abokin saurayin Naf ne ke birthday, nayi ta kiranki tun daxu baki daga ba dama wai in gaya maki” Nihad tace “Toh ai tun jiya ya kamata ku gaya min, kuma yanxu kinga dare yayi” Husnah tace “Kashhh, kinga ke matsalarki kenan Nihad, karfe takwas din ne dare?” Nihad tace “Toh ta yaya ma xa ayi in taho babu me kai ni, kinsan wawan nan har yanzu Abbanmu bai koresa ba wa yasani ma ko asiri yayi ma yan gidan duk suke supporting dinsa, Umma ce kadai ke bayana a ko da yaushe, throughout na xuba ido yau in ga ko xai tafi ban ga ya tafi ba” Husnah tace “Kinsan abinda zai faru?” Nihad tace “Aa” Husnah tace “Yanxu xa mu fita mu karo wasu wine, kawai ki san duk yanda xa ayi ki fito mu hadu a wannan katon supermarket din na anguwarku” Nihad tace “Kar fa ku bar ni inyi ta jira Husnah” Husnah tace “Haba wani jira, bayan gashi nan yanxu ni da Naff da Sumy za mu fito” Nihad tace “Okay, bari a shiga masallaci sbda yan sa ido, sai in fito” Husnah tace “Sai mun hade, kar kuma kice ban gaya maki ba, A abokan celebrant din har da ‘ya yan gwamnoni, shiga ce ta kece raini xa ki yi, duk da nasan ki ba wasa” daga haka Husnah ta katse wayar. Nihad ta mike ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje jin ana kiran isha’i, ta dauro alwala ta fito da sauri, tada sallah tayi bayan ta idar ta fito da wani ubansun gown dinta ja wanda Aliyu ne ya siyo mata daga kasar waje ta saka, ko make up bata yi ba duk ta harhada kayan make up din da turarruka a wani babban jakarta da xae iya daukan hijab da takalmi da tarkace da yawa, tana jin an tada sllh sae da ta jira aka yi raka’a daya snn ta fita da sauri bayan ta sa ma dakinta makulli, tayi surveying parlor don tabbatar da babu kowa a ciki, ko wa na dakinsa, dama kuma gidan ana magrib kowa ke shigewa daki babu me shiga privacy din wani, sai kuma washegari idan an hadu wajen breakfast, yawanci da yake a bangaren Umma dakinta yake, Umma kan shigo taga ko tana waya kuma da wa take wayar, to dai ta sa ma dakin makulli ko taje xata shiga xata ji sa a kulle, da sauri da sauri ta fito compound nan ma ta ci sa’a babu kowa, duk suna masallaci, kan kace me ta bar compound din ta kama hanyar inda supermarket din da Husnah tace ta jirasu yake, tana isa wajen ko minti biyar ba ayi ba sai ga motarsu Husnah suka dauketa suka wuce, Husnah tace “Yanxu da Habibu na nan nasan da kansa zai xo ya daukeki idan aka gama partyn ko karfe sha biyun dare ne, yanxu dole kinga sai mun ajiye ki a nan after the party in ba dai saurayi kika yi a can ba” Nihad dai ta xuge jakarta ta fara gyara fuskarta xata yi light make up. Wajen partyn ya hadu iya haduwa kamar yanda Husnah ta fada ai kam ya yan manya ne suka cika wajen, very dim light ne kunne a inda suke birthday din, babu abincin da babu da abun sha tun daga ruwa, lemo, wine, alcoholic drinks, kai komai da akwai a wajen, gasassun rago biyu aka bankare wajen, ga manya manyan pepper chicken… cake din da budurwarsa tayi masa ma kadai abun kallo ne… duk hayakin cigarette ya turnike wajen, an sha shagali iya shagali a birthday din nan, abinda Nihad bata yarda da shi ba shine ta sake ma maza fuska a wajen, xata dai shige cikin kawayenta mata amma bata xama cikin maza, ko da kana ta shisshige mata ma banxa xata yi da kai tayi ta danna waya, Husnah ta kwankwade glass din wani alcoholic wine, glass na biyu kenan ta sha, su Naf da sauran yan matan wajen su ma duk wine din suke sha, Husnah na kallon Nihad dake rike da cinyar kaza da wani can drink a gabanta tace “Wllh ki ɗan dana wine din nan ya fi na wancan ranan dadi sannan shi wannan babu abinda xa ki ji idan kika sha, wllh soo cool” Nihad tace “Aa baxan sha ba drink din nan ya isheni” Zully tace “Ke dadina dake kwabsin ki yayi yawa, don Allah ki ɗan kurba idan bai maki ba sai ki bari kar ki sha, nima kinsan ai ban fiye son wines haka ba, amma tunda kika ga ina shan wannan ya kamata kisan ba karya” Nan duk suka mata caaa akan cewa ta ɗandana idan bata ji dadinsa ba sai ta bari, Husnah ta cika mata glass din gabanta tace “Kiyi sipping first ki ji” Nihad ta dauka ta kai baki ta kurbi kadan, bayan few seconds ta wara ido tana kallonsu tace “Waow its really nyc, it tastes good” Husnah ta kyalkyale da dariya tace “Ba na gaya maki ba da kin tsaya kin kwabsawa” Nan Nihad ta kwankwade wine din, Husnah ta kara cika mata glass nan ma ta shanye, Naff sai dariya take tana cewa “Wllh ki bar ta haka Husnah tam ni dai na gaya maki” Husnah tace “Toh meye a ciki ai baya wani bugarwa” Haka dai Nihad ta sha wine tayi nak, party din da ba a karasa da ita ba kenan tayi ta masu layi a wajen, banda dariya babu abinda suke mata, Husnah tace “Kaii amma jininta ma bai da karfi wllh, ɗan wannan wine din shine xai bugar da ita” Nan suka ci gaba da shagulgulansu, Nihad kuwa ta kife kai a wajen sai bacci, ba a tashi birthday din nan ba sai karfe dayan dare, Husnah ba irin tashin da bata yi ma Nihad ba amma ta ki tashi, da ta dagota xata koma ta kife kai, wani abokin celebrant din yace “Na kama daki a nan why not kawai ku barta ta kwanta ta huta” Husnah tace “Aa nasan halinta tana farkawa xa mu samu matsala da ita, kawai dai kamata yayi mu ma a kama mana dakin dama dare yayi ba lallai a bari mu shiga schl ba yanxu, idan ya so duk sai mu kwana a nan” Ba don ransa ya so ba haka nan ya kama masu dakin, suka ciccibi Nihad sai dakin suka kwantar da ita saman gado, Husnah dai na ta kaffa kaffa da Iphone din Nihad a wajen tunda ta san halin wasu daga yan matan dake wajen. Sai kusan biyu suka kwanta a dakin bayan duk sun yi wanka.    

Karfe hudu da rabi Nihad ta farka da wani axababben ciwon kai, da kyar ta mike xaune tana bin dakin da kallo, sai kuma ta sauka tana layi ta nufi kofar dake dakin wanda bandaki ne, ta kuma sani tunda sun saba lodging a wajen ita da su Husnah, tana shiga bayin bayan tayi fitsari taji wani amai ya taho mata, nan ta dinga kwarara aman tana rike da cikinta dake juya mata, da kyar ta wanke bakinta bayan ya lafa mata ta fito, bata sake komawa baccin ba sbda ciwon kai me tsanani da ya takurata, ganin biyar ya kusa ta ta6a Husnah da kyar, ta fi minti goma tana tada Husnah dake xuba minshari kamar wani kato, kafin ta bude ido cikin magagin bacci tace “Wai ya aka yi Nihad?” Da kyar Nihad tace “Don Allah wa xai yi dropping dina gida kafin yan gidanmu suyi noticing bana nan, asuba ya riga yayi” Husnah ta ja tsaki tace “Tsakar daren nan wa xai wani kai ki gida kowa na bacci, ki bari gobe kawai” Nihad tace “Ke asuba fa yayi ki duba agogo ki ga, wllh na manta yayanmu na gida zai iya xuwa bedroom dina yace xai tasheni inyi sallah, idan yana gari duk yana tashin mu….” Husnah tace “Ohh God Nihad ki barni inyi bacci mana, haba” Daga haka ta juya ta ci gaba da baccinta, tashi Nihad tayi da kyar ta bude jakarta ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita, babu kowa reception din hotel din sai tv dake aiki, ta fita haraban wajen, wani mutumi ta gani xaune yana ta xukar ta6a a waje, ganinta ya kashe ta6ar, ta nufesa tana kallonsa ganin bahaushe ne tace “Bawan Allah idan babu damuwa ina son taimako wajenka don Allah” Daga sama har kasa yake kallonta yace “Taimakon me?” Tace “Nasarawa GRA nake son ka ajiyeni pls, kawayena da muke tare da su bacci suke ni kuma ban xo da motata ba” Yace “Ohk babu damuwa, bari in dauko makullin motata” Tace “Toh Nagode, nima xan dauko jakata” Daga haka duk suka koma ciki, ta shiga dakinsu, shi ma ya shiga nasa, ta tattara komai nata a jakarta, wayarta ne kawai bata gani ba, zaro ido tayi lkci daya hankalinta ya tashi ta fara tashin Husnah a rikice tace “Husnah ina wayata??” Da kyar Husnah dake ta snore kamar doki ta bude ido, a fusace tace “Ohh my God Nihad ki kyaleni mana inyi bacci, me yasa kin fiye takura ne wai” hankali tashe Nihad tace “Dalla can ina wayata??” Husnah ta ja wani dogon tsaki ta daga pillow dinta ta zaro wayar ta ajiye mata a gefe sannan ta ci gaba da baccinta, Nihad ta sauke ajiyar xuciya sannan ta dau jakarta da wayar da sauri ta fita, Tsaye ta gansa a haraban hotel din yana jiranta jikin motarsa, bayan ta shiga motar shi ma ya shiga, suna fita daga suite din yace “Ku ne ku ka yi birthday jiya?” Gyada masa kai tayi kawai, yace “Gaskiya ne, birthday din na manya ne” Duk surutun da yake Nihad ba tankasa take ba, banda tashi babu abinda xuciyarta yake, she was so uncomfortable, a haka ta dinga daurewa tana masa kwatance har suka isa dai dai inda su Husnah suka dauketa daren jiya, yace “Ina gidan naku?” Ta nuna masa wani layi dake a rufe tace “xan karasa da kafa, kaga gate din a kulle yake” yace “Ohk amma ya sunanki?” Cike da karfin hali tace “Aysha” yace “Maa sha Allah, Aysha ki bani digit dinki mana” ta gyada masa kai kawai, ya mika mata wayarsa ta amsa tayi dialing wani old line dinta dake a kashe tace “Wayar a kashe yake sai na shiga gida na kunna” yace “Toh shkkn nagode Aysha ni sunana Mustapha” tace “Nagode, sae anjima” daga haka ta bude motar ta sauka, cike da karfin hali take tafiya don jiri ke dibanta, ta shiga layin da ta nuna masa, sae da ya ga tayi nisa sosai a layin sannan yayi reverse ya bar wajen, tana waigowa taga ya wuce, ta juya da sauri ta dawo ta fita daga layin sannan ta dau hanyar nasu layin, gani tayi kamar an idar da sallah bayan ta iso kusa da gate din gidansu, da sauri ta bude karfen inda aka xagaye da flowers a kofar gidan nasu ta shige bayan flowers din ta buya tana maida numfashi, don har an fara fitowa daga masallaci, tana jin aka shiga cikin gida aka kulle gate, Sai kuma ta sake jin an bude gate din, Muryar Abbanta taji yana amsa gaisuwa nan bakin kofar gate din, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta, ta kara yin lamo a cikin flowers din duk da ant da taji suna cizonta bata damu ba, ta fi minti bakwai a haka bata sake jin motsin kowa ba bakin gate din, hautsinewa cikinta ke yi taji amai na taho mata, kokarin fitowa take yi daga flower din don ta samu ta shige cikin gida, kawai taga mutum xaune a dakalin dake kusa da inda take labe, sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don duk xatonta ya Farooq ne don shi ma ya kan xauna a waje idan aka idar da sallah, ya daga kai jin motsi, sai kuma ya mike tsaye da sauri, komawa baya yayi yana kallonta with surprise, ita kuwa tsabar tsorata aman da take rikewa ya taho mata, ta durkusa ta dinga kwarara aman a wajen, kauda kansa yayi bayan yayi perceiving din aman da take yi, ya sake kallonta this time around da wani expression a fuskarsa, duk sae da ta amaye sauran liquor din cikinta sannan ta mike da kyar, ko kallonsa bata yarda tayi ba ta shige gate din gidan, ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, ko second ashirin ba ayi da shigarta ba sae ga mai gadi da gudu ya fito waje yana kallon Khalil yana zare ido yace “Ina me tabbatar maka bata kwana gida ba, dawowarta kenan daga duk inda ma taje wllh” Khalil dai bai ce komai ba, mai gadi ya yamutse fuska yace “Ni warin giya ma nake ji, ko kai baka ji ba don Allah?” Khalil ya juya ya shiga gate din gidan ya xauna nan saman bench dake gefen dakin mai gadi with numerous thought running his mind, mai gadin ma ya shigo ya zauna yace “Ni fa sai nake ganin ma kamar warin giya take ko kai baka ji ba?” Khalil ya kallesa yace “Amma baka wanke bakin ka ba ko?” Mai gadi ya ɗan zaro ido, sai kuma yayi yake yace “Ai shi xan wanke ma na fito yanxu…” Tashi yayi da sauri ya shige dakinsa, Khalil ya kalli hanyar gate din, sai kuma ya mike ya fita, jakanta da ya hango cikin flowers da ta bari ya dauko ya shige cikin gidan sannan ya nufi chalet dinsu, A parlor ya tadda Su Saminu sun yi dai dai duk suna bacci, ya ciro makullin daki a aljihu, ya bude dakin sannan ya shiga ya kulle kofar, xaunawa yayi gefen gado ya bude jakar, takalma heels ya fara cirowa da kayan kwalliya da turarruka, sai iphone dinta da ya gani, ya dinga jujjuya wayar don a lock yake, sai kuma ya ajiye ya ci gaba da ciro sauran kayan jakan, bai san sanda ya bude baki ba ganin kwalban Codeine, can ya ajiye a gefe, ya bude wani zip dake cikin jakar, still yayi ya dinga kallon abinda ke wajen babu ko kiftawa, ya kai hannu a hankali ya cirosu gaba daya yana jujjuyawa, prophylactics ne na maza da na mata, ya ajiye su a gefen gado ya mike ya nufi window din dakin yana kallon waje babu ko kiftawa.

Nihad na fitowa daga wanka aka bude kofar dakin, sae da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don tsoro, Umma ce ta shigo dakin ta rufe kofar murya can kasa tace “Daga ina kike Nihad?” Nihad ta daburce tace “Ni Umma?” Umma tace “Aa ban son karya ba yanxun nan naga giftawarki ba na fito daga parlon Abbanku?” Nihad tayi narai narai da ido tayi shiru, Umma tace “Gaya min gaskiyan inda kika je” A hankali tace “Wata kawarmu ce ke birthday Umma” Umma tace “Ki dai nutsu, in ma xaki birthday ae sai ji gaya min ni baxan hanaki ba, amma baxa je makarantar yau ba bacci xa kiyi ko?” Tace “Aa xan je” Umma tace “Toh sai kiyi ki shirya karki makara” Daga haka Umma ta juya ta fita, Nihad ta sauke ajiyar xuciya, sai yanxu da ta sake wani aman da xata yi wanka taji ta ɗan fara dawowa dai dai, kanta ya daina juya mata, tana gaban madubi tana shafa mai ta tuna da jakarta, xaro ido tayi ta mike da sauri ta dau hijab dinta gogagge ta saka sannan ta fito daga dakinta, downstairs ta sauka ganin Farooq a xaune dining area tace “Yaya ina kwana?” Yace “Kina jin ina Knocking ki ka ki bude kofa daxu?” Tace “Aa yaya ina bandaki ne, ai na tashi sannan ma” Bai ce komai ba, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya ta bude kofa, yace “Ina xa ki?” Ta marairaice tace “Xan je in duba ko Allah xai sa tsuntsayen sun dawo” Murmushi kawai yayi ta juya ta fita, da sauri ta nufi gate, taji dadin ganin mai gadi baya bakin gate din, sannan khalil ma baya wajen, tana bude gate ta samesu su biyu xaune kofar gidan, suna hada ido da khalil ta daburce, sai ta hau kame kame, bata amsa gaisuwar da mai gadi ke mata ba tace “Aminu a layin nan babu inda zan samu katin waya?” Aminu yace “Inaa, Hajiya ai sai an fita can supermarket” Tace “Ohk” Da gefen ido ta dinga lekan cikin flowers din dai dai inda ta buya amma bata ga alamar jaka ba, nan hankalinta ya tashi sbda wayarta na ciki, bata san lkcn da ta karasa wajen ba tana kara dubawa da kyau, Aminu yace “Wani abu kike nema ne Hajiya?” Wani shegen kallo tayi masa tace “Toh ina ruwanka?” Khalil dai na ta danna er karamar wayar hannunsa, ta saci kallonsa.

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

11

Juyawa Nihad tayi daga karshe ta koma cikin gidan don ko kallon inda take Khalil bai yi ba, to wai wa ya dau jakarta? lkci daya jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi fiye da da, haka nan ta shiga gida jiki ba kwari ta koma dakinta ta shirya, Hijab har kasa ta saka ko powder bata shafa a fuskar ba, ta fito ta tafi bangaren Mumy, xaunawa tayi saman kujera ta gaisheta sannan tace “Mumy xan tafi makaranta ina da lectures karfe takwas” Mumy ta kalli agogo ganin bakwai da rabi tace “Kinyi breakfast ne?” Tace “Xan yi idan na sauka” Mumy tace “To ko ke fa da kika sa Hijab yau, kinga yanda yayi maki kyau, amma kullum in ta maki magana daya a kan shegun mayafan nan da kike sawa ba kya ji” Nihad ta ɗan kirkiri murmushi ta mike tace “Sae na dawo” Mumy tace “Toh Allah ya tsare, kiyi addu’a kafin ki fita” Nihad ta amsa da “Toh” sannan ta fita. Gaba daya Nihad neman appetite dinta tayi ta rasa, daga karshe nan ta bar abincin tayi ma Umma dake parlor sallama ta fita gidan, mai gadi kadai ta samu xaune bakin gate, ta nufesa tana tsaye dab da shi tace “Aminu don Allah baka ga min jaka a bakin gate ba? Kamar a nan na yar jiya da daddare, ko da safe nan don Allah baka gani ba??” Yace “Subhanallahi jaka Hajiya? ae ko wllh tllh ban gani ba, kema kin san da na gani ae xan adana maki” Nihad ta rasa abun cewa tayi shiru, iphone dinta fa na jakar yanxu ta ina xata fara? Wani xufa ta ji na keto mata, can ta dake tace “Ina driver din?” Aminu yace “Ya tafi yayi wanka” Tace “Sae kaje kace masa ya fito ya kai ni makaranta ni dai” Aminu ya mike da sauri yace “Toh Hajiya” daga nan ya nufi chalet din. Bayan Aminu ya shiga har dakin da khalil ke ciki ya sanar masa abinda Nihad tace, khalil dake zaune gefen gado yana combing kansa yace “Ta saba xuwa makaranta karfe bakwai da rabi dama?” Aminu yace “Atoh dae, nima ban ta6a ganin ta fita da safe xuwa makaranta ba wai kuma ran asabar, amma kai dai kawai ka fito kaje ka kai ta kar ta kara maka wani fitsarar” Khalil ya kallesa bai dae ce komai ba yana ci gaba da combing din kansa, Aminu ya bi dakin da kallo yace “Wai!!! amma kana kokarin gyara dakin nan, dubi fa dakin kamar a can daya bangaren, ba dauda ba wari ba tarkace, wannan ai idan na kwanta a nan sai in makara al-qur’an….” Khalil ya mike yace “Mu je…” Aminu ya kasa kunne yace “Ba waya bace ke wannan rurin?” Khalil yace “Mu dai je” Aminu ya mike ya fita dakin, Khalil ya bi sa da kallo kafin ya dage duvet din da ya lullube jakar Nihad da shi a saman gado sannan ya bude jakar ya ciro wayarta dake ta vibrate alamar kira, Husnah ya kara gani for the fourth time a jikin screen din wayar, tun daxu take kira, nannade wayar yayi da duvet don baxae iya silencing dinsa ba sbda security dake jiki, ya dau makullin mota ya fita daga dakin ya kulle sannan ya fita compound. Yanda xaka san abun duniya ya taran ma Nihad xama tayi a kan bench da mai gadi da Khalil ke xama, ita dai tana da yakinin dole Khalil xai hango jakar a bayan flowers kuma ai a bude ma ta bar karfen wajen, wai to don bashi da kunya sai kawai ya kama ya dau mata jaka, yaushe ta sake masa har xai kai hannunsa kan jakarta, wato yanxu jira yake sai ta tambayesa kenan? Cabdi… tana hangosu tayi maza ta mike ta sha kunu, Khalil dai ko kallon direction dinta bai yi ba ya tafi gun motar ya bude ya shiga, bayan yayi warming mai gadi ya bude masa gate, Sai da ya fita compound sannan Nihad ta fita ita ma tana tafiya a hankali ta bude back seat ta shiga ta xauna, Aminu ya dinga daga mata hannu alamar a dawo lafiya, ko kallonsa bata yi ba, Khalil ya ja motar suka bar layin, tunani take to yanxu dai tambayarsa jakarta xata yi? Cab gaskiya baxata yi hakan ba, m ta saci kallonsa ta madubi suka yi ido hudu, da sauri ta dauke kanta ta wani daure fuska ta zuge zip din wani jakar da ta dauko ta fiddo chewing gum ta bude ta jefa baki, shi dai driving kawai yake, sai da suka kusa makarantar tayi gyaran murya tace “Malam ka bude min Ac xafi ya dameni….” A takaice yace “Ke kika san meye shi” Tayi masa wani kallo tace “kace me??” Bai tanka ta ba, ta masa wani shegen harara ta ja tsaki kasa kasa ta ci gaba da taunar chewing gum dinta, suna isa makarantar dai dai department din nasu yayi parking, tana ta sauraron ta ji ko xai yi maganar jakar amma shiru, gabansa kawai yake kallo, ganin bata sauka ba, kuma kamar bata da niyyar saukan yace “Ko yau ma xa a bar maki makullin ne?” Ta galla masa wani harara tace “Ai ba ni na kawo motar ba balle ka bar min makullin” tana gama fadin haka ta bude motar ta sauka ta ki kulle door din tayi tafiyarta, ya bi ta da wani kallo, sai kuma ya sauka ya kulle sannan ya hau motar ya tafi…. Husnah na ganin Nihad tace “Shine nake ta kiranki kike danna min busy Nihad?” Nihad ta sauke ajiyar xuciya amma ta ki bata amsa, ta nemi seat ta xauna, wato dai a takaice drivern nan ne ya dau jakar tunda gashi har Husnah ta kira ana ta danna mata busy, lallai mutumin nan raini me karfi ya shiga tsakaninsu, bayan dauke mata jaka sbda guts har bude jakar ma yayi kenan, muryar Husnah ya dawo da ita daga tunanin da take, tace “Ina magana kin min shiru, dama ba komai bane ce maki xanyi ki taho da jakar da kika je birthday jiya da shi, don akwai abubuwana a ciki” Nihad ta kalleta tace “Abubuwanki kamar me?” Husnah tace “Kwalban Codeine dina da Naff na ciki, sai prophylactics, ni ina jin kamar ma har da lingerie dina a jakar, don na duba ban gani ba….” Nihad ta zaro manyan idonta tace “Duk a cikin ina???” Husnah tace “Jakarki mana, kinsan yana da girma” Nihad bata san sanda ta mike ta dafe kirjinta ba tace “Na shiga uku….” Da mamaki Husnah tace “Kin shiga uku kuma? Me ya faru?” Nihad tayi narai narai da tace “Wayyo Allah na, Me yasa xa ki min haka ki ajiye abubuwan nan a cikin jakata Husnah? Me yasa xa ki min haka? Gashi yanxu jakar ta fadi a bakin gate ban san wanda ya dauke min ba” Husnah ta gwalo ido tace “Kaiii, garin yaya kika yarda jaka a bakin gate Nihad?” Nihad da abun duniya ya isheta ta koma ta xauna ta cije yatsa tace “Na shiga uku” Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh kinsan wa ya dau jakar ne?” Ta kalli Husnah tace “Wallahi wannan driver din nake zargi don shi kadai ya gan ni sanda na dawo da asuba don a bayan flowers dake kofar gida na fara buya as a result of people coming out from the mosque after subhi prayer” Husnah ta rike ha6a tace “Ji tsiya, Driver kuma?” Nihad ta kasa cewa komai tayi tagumi, Husnah tace “Tabb shine kika yi shiru, to me kike jira da har yanxu baki tambayesa ba?” Nihad tace “Toh me xan ce masa? Bayan ban ga sanda ya dauka ba, Har wayata fa na cikin jakar, idan ba sata yake son yi ba ai xai ba Aminu ya ajiye min” Husnah tace “Ehh lallai wannan mutumin ya rika, shi ke ta ja min busy kenan? Wato dai har ya bude jakar” Nihad ta xaro ido tace “Na shiga uku, gashi kin xuba abubuwa kika ce cikin jakar” Husnah ta mata wani kallo tace “Ke dalla to meye, koma me ya gani cikin jakar ba shi ya ga duhu ba, kuma ma bansan uban me kike jira da har yanxu baki tambayesa jakarki ba, ko tsoronsa kika fara ji? ai ba ma tambayarsa xa ki yi ba wai ko ya ga jaka ko bai gani ba, kawai ce masa xa ki yi ya baki jakar ki da ya dauka kar kiyi masa rashin mutunci, kuma kada ya sake ta6a maki kayanki ko da kuwa a titi kika yar don baki aikesa ba” Nihad dai ta rasa abun cewa tunani iri iri ke yawo a ranta, Husnah ta kyabe baki tace “Ni dai ki adana min prophylactics din nan foreign ne ba na kasar nan bane kuma tsada ke garesu, Codeine din kuma shi ma nasan ba kya sha, kar ki je ki xubar ki adana mana gaskiya” Tashi Nihad tayi ta bar mata wajen ta koma seat din baya abun duniya ya isheta, yanxu mutumin nan duk ya ga abinda Husnah ta saka mata a jaka? To amma ya ma yi mugun rainata gaskiya, waye shi da har xai bincika mata jakarta?? A daddafe Nihad ta yi lectures daya tace xata tafi gida, Husnah tace “Ke don Allah ki saki ranki, ko Abba ne ya ga jakar nan ya dauka ya bincika ai sai haka, me xai dameki akan wani shegen driver dinku ya bude jakar ki? Ae rashin mutunci mafi muni xaki masa idan kin koma gida anjima, ni abinda ya fi damu na ma wayarki ne wllh, don matsiyacin sai ya iya dauka yace xai je ya siyar bai san wayar nan sai ta siye duk yan kauyensu ba, yanxu kawai ki xo mu je police station, cikin lokaci kalilan xa ayi tracking” Nihad ta zaro ido tace “In tona ma kaina asiri kenan, kin zata na gaya ma kowa cewar na yarda jaka da waya a ciki? To har Nihal bata sani ba” Husnah tace “In kince ayi cikin sirri babu tonon asiri ai sai ayi hakan, duk fa mutanena ne, amma wllh so nake a walakanta sa idan aka ga wayar a wajensa, a nakada masa shegen duka” Nihad tace “Husnah bari in je gida ko xan ji saukin abinda ke damuna, i can’t endure anymore” Husnah ta ta6e baki tace “Wllh kina da sa ma kai damuwa, duk ki bada space din da lamarin driver xai dinga damunki haka, to wai shi wannan driver din daga ina ya xo yake abu isa isa da gadara haka?” Mikewa Nihad tayi tace “Duk yanda ake ciki xan kiraki da wayar Nihal ai tana da number ki” Daga haka ta fice daga hall din, tun da ta fara school din bata ta6a trekking da kafafuwanta har bakin titi ba sai yau, haka nan ta tsayar da adaidaita shi ma xata iya kirga iya sau nawa ta hau sa a rayuwarta, suna isa gida ta sauka ta bude jakarta ta basa kudi sannan ta shiga gidan, Aminu ne kawai bakin gate, ta ɗan bi compound din da kallo sai kuma tayi kasa da murya tace “Aminu baka tambayar min driver din can ko ya ga jakata ba kuma?” Aminu yace “Anya, don ina da yakini da ya gani xai nuna min, ai shi mutum ne me gaskiya da amana” Ta wani galla masa harara tace “Dallah Malam rufe min baki, duka duka kwananku nawa tare xaka san yana da gaskiya da amana, ashe kai dolo ne ma ban sani ba? To bari ka ji wayata ce ta kusan miliyan daya da rabi a jakar nan” Driver ya gwalo ido yace “Subhanallahi, subhanallahi….” Nihad ta saci kallon wanda ke tahowa ganin driver din ne ta daure fuska ta juya ta nufi cikin gida da sauri, xaunawa Khalil yayi gefen Aminu ganin yanda yake zaro ido kamar mara gaskiya yace “Me ya faru kake buda ido haka” Aminu yace “Ba nace maka ta yarda jakarta ba daxu har tana tambayata ko na gani, to wllh wai har da wayarta na miliyan biyu da rabi a cikin jakar” Khalil ya ciro karamar wayarsa yace “To ta huta…” Aminu yace “Atoh dai, Ta kuwa huta wllh, don yau tana sa uban a gaba ya siya mata sabo wallahi sai ya siya, sai dai uwarta ta hana amma tsaf in dai ita ce xai siya mata, kai kaji waya har miliyan uku, ni yanxu na samu irin kudin nan ai kauye xan koma in tada gini malam, inci me kyau in sha me kyau, sannan in kara mata biyu….” Khalil na kallonsa yace “Haba?” Aminu yace “Wllh tllh, albashin namu fa Hajiya ke amsowa a wajensa ta bamu, Ni dai ban san ko nawa yake bata ba amma dubu 50 50 take bamu, kuma da farkon xuwana akwai wani lkcn da ya ta6a bani da kansa wllh dubu 70 ya bani, to kilan dai har da kyautatawa ce irin tasa ban dae sani ba” Khalil dae bai ce masa komai ba. Nihad na shiga cikin parlor ta tafi dakinta direct, xaunawa tayi gefen gado ta rafka tagumi abun duniya ya isheta, tun da shegen mutumin nan ya xo gidan nan bata da kwanciyar hankali, bude kofar dakin aka yi Nihal ta shigo da sallama, Nihad ta daga kai tana kallonta, Nihal ta karaso ta xauna gefenta tace “Amma ba ki jira ku gama lectures din yau ba kika taho ko” Nihad ta yatsine fuska tace “I am tired, kawai shine na dawo” Nihal tace “Toh ki kwanta ki huta, xuwa yamma sai ki rakani shopping din, kinsan gobe sunday xan tafi fa” Nihad tace “Wa xai kai ki shopping din??” Nihal tace “Khalil” Nihad ta juya ido tace “Waye haka?” Nihal tace “Driver…” Nihad ta bude baki ta rike ha6a tace “Wai khalil? Shi uban wa ya basa wannan suna yana driver? Ni fa na xata kinyi wani saurayi ne Khalil ban sani ba, shi driver din ne yace maki sunansa khalil?” Nihal dai kallonta kawai take, Nihad ta gyada kai tace “Tabdi, ana iskanci a duniya, shi yasan ma’anar Khalil din ma kuwa?? Yau naga mutumi da karfin hali, ke kuma wawuya shine kika yarda sunansa Khalil, to wllh karya yake ba abinda ya hadasa da wannan sunan” Nihal tace “To ko ma dai meye sunan Abbanmu garesa, ko so kike in kira sunan Abba gatsau?” Nihad tace “Toh meye don kin kira tunda ba sunan Abban kika kira ba? Meye don kin ce masa Ibrahim ba shine sunan nasa ba? Wato dai ke kika makala masa khalil din kenan?” Nihal tace “Aa, yace haka ake kiransa dama, ni bani na sa masa ba” Nihad ta bude baki tace “Ji shegen karya, to karya yake munafuki, uban wa ke ce masa haka? Amma fa mutumin nan yayi mugun raina maki wayo ma dai, a kauye wa yasan wani khalil, dama Halilu yace shine xan yarda, to wai tsaya ma tukun, fira ku ke har yake gaya maki sunansa khalil??” Mikewa Nihal tayi tace “Woo na gaji da question and answer din nan, Ko ma meye sunansa ba abu bane da za mu tsaya muna bata lkci akai, ni dai anjima ki shirya mu je Sahad store din” Nihad tace “Allah ya kiyaye in dai can xaki wllh baxan je ba, ga wajaje irinsu wellcare kice min Sahad, ai kowa da kowa ke xuwa Sahad” Nihal ta juya ta kalleta, sai kuma ta girgiza kai kawai ta fita daga dakin. Nihad ta rike ha6a tace “Ji maye wai khalil, shi a lallai ya xo gidan masu kudi bari ya maida sunansa irin na yan gayu wai khalil, aa Khalo ba khalil ba” Ta ja tsaki ta mike ta shige bandaki. Ta a fitowa ta koma gefen gado da take xaune ta xauna, tunani ta shiga yi a ranta, to ko dai taje can chalet din da kanta ta duba jakarta ne? Ta kalli agogo lkci daya ta mike ta fito main parlor Umma tace “Aa har kin dawo er baba” Nihad ta gaisheta sannan ta fita balcony har sannan taga yana xaune tare da Aminu a bakin gate, komawa ciki tayi ta shiga kitchen sannan ta bude kofar kitchen din da xai sada ka da back yard din gidan wanda ta nan ma xaka iya xagawa har xuwa Chalet, ganin yanda Hafsah ke kallonta ta sha kunu tace “Ya dai da kallo haka ke kuma?” Hafsah ta kauda kanta, Nihad ta fita da sauri ta xaga ta baya sai Chalet, bata ga takalmin kowa a bakin kofar ba alamar su Isiyan ma duk basa nan kenan, a hankali ta bude kofar tana leka parlon sannan ta shiga, da sauri sauri ta fara dudduba parlon, har xuwa dining area bata ga alamar jakarta ba, har bandakin dake parlon sai da ta bude, wanda sai da ta kusa amai, ta kullo da sauri tana yatsina fuska ta yi hanyar dakunan chalet din, duk dakuna biyun dake a bude sai da shiga tana tottoshe hancinta tsabar tsami da doyi, na ta bincika kaf Ghana must go da ta gani a dakunan amma bata ga jakarta ba, dakin da khalil ke ciki ta murda ta ji a kulle, to ko dai nan dakin aka ajiye jakar nata shine har da kullewa da makulli, tunanin inda xata fara nemo spare key ta shiga yi, can ta zare key din dake jikin kofar su Isiya ta juya ta fita da sauri ta xaga ta koma kitchen, sai da ta wanke hannunta da morning fresh ta hada har key din tana yatsina fuska sannan ta shigo parlor, har wani tashi taji xuciyarta ke yi sbda warin da ta dinga inhaling, kazami irin wannan har shi xai takura mata a gidan nan ya dinga shiga gonarta, dubi wajen da suke kwana wanda ita ko pig take rearing baxata bari yayi rayuwa a irin wannan kazantaccen wajen ba, tana wannan tunanin ta faki idon Umma dake waya ta shige bangaren Abbanta, direct dakinsa ta wuce bayan ta shiga parlor, nan ta hau bude duk wani drawer da ke dakin, a bedside drawer ne ta ga bunches of spare keys na gidan, tayi murmushi ta kalli na hannunta sannan ta hau duba irinsa, kaf irinsu guda uku dake wajen duk sai da ta dauka incase of necessity sannan ta mayar da drawer din ta kulle ta mike ta fice daga dakin, kitchen ta sake bi ta xaga xuwa Chalet din, da sauri ta shiga ciki ta nufi hanyar rooms din, dakin dake kulle tayi facing, ta hau gwada makullen hannunta da sauri da sauri, lkci daya ta bude dakin, wani farin ciki ne ya lullubeta, ta shige ciki ta kulle tana bin ko ina da kallo gabanta na faduwa? Banda kamshi babu abinda ke tashi a dakin, rigarsa da ta gani saman gado ya sa ta gane shine a dakin, rike ha6a tayi…. to gidan uban wa ya samo wannan turaren da ya xuba a dakin haka, bata daina bin dakin da kallo ba ta karasa middle of the room, the room look so different kamar ba a chalet din ba, babu tarkace da kaya kamar irin na su isiya sannan everywhere looks so neat and tidy, ta kyabe baki without bothering ta hau yin abinda ya kai ta dakin, Duvet ta gani kamar an rufe abu da shi ta tafi da sauri ta daga sai ga jakarta a ajiye saman gadon, xaro ido tayi wani farin ciki ya lullubeta, ta bude jakar tana bincikawa da sauri, banda abubuwan da Husnah ta xuba mata a jakan sai nata tarkacen bata ga alamar wayarta a ciki ba, nan kuma ta marairaice tana bin dakin da kallo, a ina to ya ajiye mata wayar?? Sake jakar tayi ta nufi tasa jakar kayan dake dakin, sai bin jakan take da kallo kafin ta durkusa ta xuge zip din, ko karasa bude zip din bata yi ba tayi ido hudu da wayarta, babu bata lkci ta dauka, dai dai nan kuma aka bude kofar dakin, tsabar rudewa da tsorata da tayi bata san sanda ta mike ta saki wayar jikinta na rawa tace “Wayyoo… Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_📖✍🏻

12…..

Tsaye Khalil yayi bakin kofa yana kallonta with a weird facial expression, bata sake yarda sun hada ido ba banda faduwa babu abinda gabanta yake, sai kuma ta hade rai xata durkusa ta dau wayarta da ya fada saman jakar, yayi hanzarin shiga cikin dakin ya sa kafa yayi changing position din jakar yana kallonta, tana ganin haka ta bi jakar cike da tsiwa tace “Wai kai yaushe na fara wasa da kai a gidan nan ne da xaka dinga raina ni haka? ina ruwanka da kayana ko a saman titi na jefar da xaka ta6a min, how dare you?” Tana fadin haka ta ja tsaki ta kara dukawa zata dau wayar, ya dauke jakar a wajen, buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, sai kuma ta nufesa da nufin cakumosa yanda ta saba amma ganin kallon da yake mata sai kawai ta tsaya tana harararsa, cike da rashin kunya tace “Wallahi idan baka mika min wayata a dakin nan ba xan maka sharrin da har abada baxa ka mance ba, ka bani wayata nace…” cikin kakkausar murya yace “Idan kin fasa…” Ta kankance ido tana kallonsa da mamaki jin abinda yace, ji take kamar ta kifa masa mari, da a waje ne wllh ba abinda xai hanata marin sa, Yana mata wani kallo ya ajiye jakar a gabanta yace “Idan kin isa ki ta6a” A fusace tace “Toh wai kai idan kana sata sai ka rasa wayar warce xaka sata sai tawa a gidan nan? A kaina satarka xai kare? Idan na ta6a uban me ka isa ka min? Wllh sai na ma sharrin da baxaka ta6a mantawa da ni ba” Duk wannan babatun da take bata yarda ta ta6a jakar ba, banda faduwa kuma babu abinda gabanta yake barin da ta ga irin kallon da yake mata, jakarta dake gefen gado ya nufa ya dauka ya dawo inda take ya jefa mata a gabanta yace “Dauki ki fita… Abubuwanki dake ciki xa su fi wayar muhimmanci gare ki” Kamar xata yi kuka tace “Ni wllh ka bani wayata kar in hadaka da Abbana da yayana” Da Husky voice yace “Dauka jakar ki nace ki fita” Bata ce masa komai ba ta tafi ta dau jakarta tana jin kamar ta fashe da kuka, ta nufi kofar tana tafiya a hankali, ta gefen ido ta saci kallonsa sae kuma ta dawo da gudu ta fixgo jakarsa ta nufi kofa a guje kamar an aikota, tana shiga parlorn plate din da su Isiya suka ci abinci suka bari a wajen ta take sai da ta tafi tsuuu kamar xata tashi sama sae ga ta a kasa timm, jakarsa kuma yayi can hanyar kofar fita, nata kuma yayi wajen Tv, gwalo ido tayi tana numfashin wahala da kyar tace “Wayyoo Abbana, wayyo bayana ya karye” tsaye yayi bakin corridor din dakunan ya rungume hannunsa ya jingina da pillar din wajen yana kallonta irin dai dai kenan, ta fashe da matsanancin kuka tana jujjuya kanta tace “Wayyo Allah na a zo a taimakeni bayana ya karye, baxan iya tashi ba” karasowa cikin parlon yayi zai tafi ya dau jakarsa, tana ganin haka ta yunkura ta tashi ta nufi kofar da gudu ta figi jakar tasa, a dari da sittin ta fice ko bin ta kan nata jakar bata yi ba a parlon, bai san sanda ya bi ta ba, tuni har ta dau hanyar kitchen yace “Keeeee dau wayarki ki ajiye min jakata” haba da ya kara tuna valuable dinsa dake jakar kawai ya bi ta, tana isa kofar kitchen ta murda ta ji sa a kulle, ta gwalo ido tace “Na shiga uku, Hafsahhhh uban wa yace ki kulle” tana ganin ya nufota kawai ta ajiye jakar a kasa tana kallonsa xuciyarta na bugawa, yana isa gabanta ya duka ya dau jakarsa sannan ya bar wajen. Nihad bata san sanda ta fashe da kuka ta sulale wajen ba tana cewa “Wallahi sai na maka rashin mutunci a gidan nan, kawai mutum kamar maye ya sa min ido a gidan ubana duk ya bi ya takura ni” Sai kuma ta mike ta xaga ta shiga cikin gidan, Umma dake parlor ta kalleta daga sama har kasa tace “Lafiya?” Nihad tace “Ina Hafsah?” Sai ga Hafsah ta fito daga bangaren Mumy, Nihad ta nufeta tana huci tace “Ke mahaukaciyar wace gari ce da xaki rufe min kofa bayan kinsan na fita?” Hafsah tace “Ayya kiyi hakuri wllh ban san baki shigo ba, na xata kin bi ta gaba kin shigo” Nihad ta mata tsawa tace “Aa ta hancinki na bi na shigo” Tsaki ta ja ta juya ta bar wajen kamar xata tashi sama. Umma dai ta bi ta da ido, direct dakin Nihal ta tafi, Nihal har ta gama shiryawa tana kallon Nihad tace “Ohk baxa ki rakani din ba” Nihad tace “Nihal idan na fara yi ma wancan driver din rashin mutunci ke ce ta farko da ke fara jin haushi, wllh duk abinda na masa kar ki ga laifi na, don haka tun wuri ki je ki samesa ki amso min wayata da jakata dake wajensa” Nihal dake kallonta with confusion tace “Me ya kai jakarki da waya wajensa kuma?” Nihad tace “How will i even know?? I mistakenly dropped my bag at the gate jiya, ko sani ma ban yi ba….” Nihal ta katseta tace “How will u mistakenly drop a whole bag not even purse Nihad?” Nihad ta hade rai tace “And that is none of ur concern, kawai abinda nace maki shine ki amsar min kayana a wajensa kar in fara rashin mutunci na, don wllh idan bai yi hankali ba sai na gaura masa mari kuma ba abinda xai faru” Dariya ta ba Nihal, sai dai bata yi ba, tace “Ke yanxu wa yace maki shi ya dau maki jaka?” Nihad tayi saurin cewa “Aminu ne ya gaya min, kuma don’t forget wayana na ciki” Nihal tace “Amma ai ba yaki bane, xa ki iya samunsa politely ki tambayesa jakar, na tabbata xai baki” Nihad ta yi wani dariyar rainin hankali tace “Koh? To sannu, shi drivern xan je in sama politely sbda ina tsoronsa ko? To abinda baki sani ba, Aminu ce min yayi satar jakar yayi niyyarsa yayi shiru, bai kuma san Aminun ya gansa ba, to idan yana sata sai ya fara ta kan kayana a gidan nan? Kaii amma mutumin nan ya kara bani tsoro wllh” Nihal ta dau karamin handbag dinta tace “Yamma na yi, xan tafi shopping” Nihad ta hade rai tace “Ohk baxan raka ki ba kenan?” Nihal tace “Oh na xata kince ai baxa ki ba” Nihad ta harareta tace “Yaushe nace maki haka?” Nihal tace “Toh dauko hijab dinki mu tafi” Nihad bata ce komai ba ta juya ta fita, Nihal ta bi bayanta, babban dalilin da yasa Nihad xata shopping din nan kawai don Nihal ta amsar mata jakarta da wayanta gun khalil, Nihal na fitowa parlor Umma tace “Har kin shirya auta?” Nihal tace “Eh na shirya” Umma tace “To kar dai ki manta turarena” Nihal tace “Toh baxan manta ba” Umma tace “To ya kika tsaya, ga yamma na yi” Nihal tace “Ina jiran Nihad” Umma ta kalleta tace “Nihad? ita tace maki xata?” Nihal tace “Eh” Umma tace “Ke da xaki yi maza kije kiyi abinda xai kai ki ki dawo, meye kuma sai kun yi zuga kamar yan matan amare Nihal” Nihal tace “Aa nafi son mu je tare” Umma tayi shiru bata kuma cewa komai ba, Nihad ta fito sanye da Hijab ita ma, Tana kallon Nihal tace “Mu je” Nihal ta kalli Umma tace “Sai mun dawo” Umma tace “Allah ya tsare” Nihad tace “Umma xa a taho maki da wani abu ne?” Umma tace “Aa babu komai, Allahj ya tsare” Fita suka yi daga parlon, Nihad ta hade rai ganin khalil da Aminu, Nihal ta nufesu tana kallon khalil tace “Idan baka yin komai xa mu iya tafiya yanxu?” Ya mike yace “Ohk” Motar ya nufa, Nihad ta bi sa da wani shegen kallon tsana, duk Aminu na lura da ita, Nihal ta bude front seat xata shiga Nihad tayi saurin cewa “Me xa ki yi a gaba ke kuma?” Nihal tace “I prefer seating here” Nihad ta ja tsaki ta bude back seat ta xauna, Tuni mai gadi ya bude gate din suka fita compound din, Khalil yace “Wani supermarket din xa mu Hajiya?” Nihal tace “Ko wanda ya fi kusa” Nihad tace “Kai Malam mu tafi Sufi Mart” Khalil dai driving dinsa kawai yake, next thing kawai Nihad taga ya dau hanyar wani store din daban, ta kankance ido tace “Wai kai kurma ne baka ji inda nace ka kai mu bane?” Driving dinsa kawai yake kamar bai san da shi take ba, Nihal ta juya ta kalleta tace “But ai duk daya ne Nihad” Nihad ta galla mata harara tace “To da ke nake ke kuma?” Nihal ta dauke kai bata ce mata komai ba, A Danja Khalil ya sauke glass din motar ya amshi facemask hannun wani yaro sannan ya basa kudi ya kulle glass din, Nihad ta kyabe baki, sai kuma ta ja tsaki ba dai wanda yace mata komai a motar. Parking Khalil yayi a inda aka tanadar don parking a harabar Supermarket din, ya kashe motar yana kallon Nihal, tace “Baxa mu dade ba in sha Allah” Nihad tace “Toh da kike cewa haka wa xai dauko kayan idan mun gama siyayyan? Ai sauka shi ma xae yi daga motar ya kwaso kaya ba wai zama xae yi a driver seat ba” Nihal ta kalleta tace “But the staff in there will do that, it’s not necessary” Nihad tace “Wallahi u have a very big problem, what is then the use of him? Why then did he have to drive us here if he can’t come out and help? Sannu good Samaritan” Nihal ta kalli khalil tace “Sae mun fito” Yace “Toh a fito lafiya” Ta bude motar xata sauka yace “Amma bari in sa maki number ta idan kin gama sae ki kirani in dau maki kayan” Tace “Akwai masu daukan kayan a ciki kar ka damu” yace “Toh idan da wani abun sae ki kirani” Tace “Toh” wayarta ta mika masa yayi dialing number din sa sannan ya mika mata, amsa tayi ta kira number, karamar wayar dake aljihunsa ya fara ring, tace “Nagode” daga haka ta bude motar ta sauka, Nihad dake ta kallon ikon Allah ta ja tsaki me tsayi sannan ta sauka, ko barin wajen motar basu yi ba tace “Me ye na wani exchanging digit da driver idan ba kaskantar da kai ba Nihal? Me yasa ke kin fiye over sabi a rayuwarki? Ni ban san me yasa ke da Mumy ku ke yin haka ba wllh” Nihal taki tanka mata, Nihad tace “Though wannan ba damuwata bace, my problem is ban ji kin masa maganar jakata da wayana ba?” Nihal tace “Xan yi” Suna shiga mall din, Nihal ta fara daukan abubuwan da ta xo siya tana xubawa a cart Nihad na tura mata cart din, duk inda suka gifta sae an kallesu don babu wanda bazai ce su ba yan biyu bane, they look so cute, beautiful and adorable, kawai dai Nihad ta fi Nihal haske da tsayin hanci with more cute lips, ita kuma Nihal ta fi Nihad cika, though she isn’t chubby but ta fi Nihad warce iska me karfi idan aka yi xae iya tafiya da ita… Lol, tsayinsu daya haka ma shape din large eyes dinsu, sae dai kana kallonsu kasan Nihad tafi Nihal wayewa nesa ba kusa ba, ganin Nihad isn’t taking anything Nihal tace “But kince kema xa kiyi shopping kin fasa ne?” Nihad ta yatsina fuska tace “I won’t shop here” Nihal bata kuma ce mata komai ba, har ta gama daukan duk abinda xata bukata a makaranta, sannan ta dau ma Umma turarurrukan da tace, wani tsadadden turare da ta san Nihad na so ta daukar mata, Nihad ta amsa tace “Thank you” Daga haka ta saka shi cikin cart din, Nihal ta dau wayarta tayi dialing number da Khalil ya sa mata with the intention of asking him a question, can kuma dae kawai ta katse ta fasa kiran nasa sbda Nihad dake ta kallonta, wasu turarurrukan biyu ta deba ta sa a cart sannan tace “Shikenan na gama” Nihad ta tura cart din suka nufi counter. Suna tsaye counter din Nihad tace “Na manta xan dau Sanitary Napkin” Daga haka ta juya zuwa in da zata dauka, khalil ya shigo cikin mall din with facemask, yana hango Nihal a counter ya nufi wajen yana kallonta yace “Naga kiran ki…” Nihal tace “Oh bansan ya shiga ba” Yace “Ohk, sun gama in dau kayan?” Xata yi magana kawai wata yarinya kamar balarabiya ta nufosu tana kallon Khalil closely tace “KJay?” Juyawa yayi da sauri, Ta wara ido kafin ta ce komai yace “Ohh Nadiya, daga ina haka?” Ta kyalkyale da dariya tace “How wonderful i recognized u upon the nose mask KJay…” Ya kalli Nihal da sauri yace “erm, yi hakuri don Allah minti daya…” kawai yace “Mu yi magana a waje Nadiya” yana fadin haka ya bar wajen da sauri, Sai a sannan Nadiyar ta kalli Nihal dake ta kallonta daga sama har kasa, Nadiya ta daga mata hannu tace “Hi” Nihal tayi murmushi ta daga mata hannu ita ma, juyawa tayi ta bi bayan khalil da har ya fita mall din, Nihal ta bi ta da kallo, har gadon baya ta saki dogon baƙin gashin kanta, daga ganinta kasan half cast ce, sae ga Nihad ta ajiye Sanitary Napkin din a kan counter, tana kallon Nihal sai kuma ta kalli inda take ta kallo amma tuni Nadiya ta fita daga mall din, Nihad tace “What are u staring at?” Nihal ta dauke kanta da sauri tace “Nothing” ma’aikatan wajen ne suka kwasar masu kayan xuwa mota bayan an biya kudin kayan, Khalil na jingine jikin mota ya rungume hannunsa, ganin sun fito ya xaga ya bude booth din motar, wanda ya tayasu fito da kayan ya shigar cikin booth, Nihal ta bude handbag dinta ta dau dari biyar ta basa, yayi mata godiya sannan ya wuce, tuni Nihad ta shige bayan mota, Nihal ta xauna gaban motar, ya tada motar suka bar shopping mall din. Tunani iri iri ke yawo a xuciyar Nihal, she can’t even think straight, Nihad kuma ta kasa kunne taji Nihal tayi ma Khalil maganar wayarta amma shiru, har ta shirya rashin mutuncin da xa tayi mata suna shiga gida don dab suke da isa gidan kawai ta ga Nihal ta kallesa tace “Ina son xan maka magana don Allah” Bai kalleta ba idonsa na kan titi yace “Toh ina jin ki Hajiya” Ina a polite state tace “Jakar Nihad yana wajenka ko?” Yayi ɗan yi shiru kamar baxai ce komai ba, Nihal dai kallonsa kawai take, sai kuma yace “Eh yana wajena” Tace “Toh xaka bani don Allah idan mun isa gida” Yace “Toh ba damuwa, in sha Allah” Nihad ta galla masa wani tsinannen harara ta kauda kai, da yace baxai bada ba ya gani mana, suna isa gida yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta tsaya nan parking space babu yabo babu fallasa tana jiran jakarta. Nihal ta sauka ya bude mata booth ya saukar da kayan kasa, xagawa tayi xuwa gun Nihad tace “Ki tafi ciki, ai xan amsar maki” Nihad tace “Nooo, Baxan tafi ba, ina nan ina jira” Khalil dake jin abinda tace, ya dai kwashi kayan Nihal gaba daya ya kai mata can bakin kofar shiga main building din gidan ya ajiye, Nihal na tsaye har ya dawo yana kallonta yace “Anjima da daddare xan baki jakar idan na shiga can bangaren kenan” Nihad tace “Ban gane anjima da daddare ba, kai ko kunyan sata baka ji ba a ranka, to tun wuri ka shiga yanxun nan ka fito min da jakata kar in tara maka mutanen gidan nan, wallahi rashin mutunci xan maka don ma kaji in gaya maka” Khalil ya kalleta yace “Toh” Daga haka ya tafi wajen mai gadi yayi xamansa, a fusace Nihad ta kalli Nihal tace “Kina dai gani ko, wllh sai na nuna masa wacece ni yau kar ya fito min da jakata” Nihal tace “Ba sai da nace ki shiga ciki xan taho maki da shi ba, toh ai gashi nan kin ji” Nihad tace “Na ji me? Ai jakata baxata kara minti biyar a hannunsa ba, bari ya gani” Tana fadin haka ta juya fuuu ta wuce cikin gida, ita damuwarta kar ya ba Nihal jakar ta bude taga kayan Husnah dake ciki, Nihal ta nufe Khalil dake kusa da mai gadi ta mika masa ledan hannunta tace “Gashi nan na daukar maka kai ma, amma don Allah kayi hakuri ka bamu jakar yanxu” Yana kallon ledan yace “Nagode sosai Hajiya, Allah ya saka da alkhairi…. Bari in dauko maki jakar” Daga haka ya mike ya nufi chalet, ta bi sa da kallo sannan ta bi bayansa, da ya lura tana biye da shi, sai yayi slowing pace dinsa, tana isa kusa da shi tace “Ina son xan maka tambaya” suna ci gaba da tafiya ba tare da ya kalleta ba yace “Ohk ina sauraronki?” Tace “Tell me… who are you?” Ya ɗan yi jim sai kuma yayi saurin cewa “Ban gane abinda kike nufi ba” Tace “Nasan ka gane” Yace “Da gaske ban gane ba” suna isa Chalet din kafin tace komai, yayi maza yace “Ina xuwa in dauko jajad yanxu” daga haka ya shiga ciki ta bi sa da kallo, ba a dau lkci ba ya dawo rike da jakar Nihad, a bude zip din jakar yake, ya mika ma Nihal ta amsa, babu abinda idonta ya fara cin karo da sai kwalban Codeine da prophylactics da ke saman jakar, lkci daya ta rude apart from being shock, bata san sanda ta rungume jakar ta juya da sauri xata bar wajen ba, yace “Ga wayarta” Nihal ta juyo da kyar amma ta kasa barin su hada ido, ta dai amshi wayar da yake mika mata ta juya ta bar wajen tana tafiya da sauri, tana shiga gida direct dakin Nihad ta wuce, Nihad xata fito daga dakin kenan suka kusa cin karo, Nihad ta koma baya, Nihal ta shiga dakin ta jefa mata jakar a kasa tana girgiza kai sadly tace “Nihad meye wannan a cikin jakar ki??” Nihad ta kalli jakar lkci daya gabanta ya fadi, Nihal ta karasa cikin dakin ta xauna gefen gado ta dafe kanta, Nihad dai sai kallon jakarta take tana tunanin abinda xata ma khalil taji sanyi a ranta, ko daxu da ta bude jakar bata ga abubuwan nan a saman jakar ba, wato shi ya daura su saman jakar ya bar zip a bude don Nihal ta gani, Bayan kusan minti daya Nihad ta kalli Nihal, hawaye ta gani idonta, Nihad tace “Look Nihal wllh wllh ba kayana bane na Husnah ne, haba don’t u trust me?? kema kinsan i can neva posses such stuffs, i swear to God na Husnah ne, shi kuma munafuki algungumin da ya daura a saman jakar ya jira ya ga abinda xai faru da shi a gidan nan” Tana fadin haka ta durkusa ta hau tattara abubuwan dake cikin jakar ta kulle, Nihal dai bata ce komai ba ta mike a sanyaye ta ajiye mata wayarta a gefen gado sannan ta fice daga dakin.

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

13…..

Zaunawa Nihad tayi ta dau wayarta ta bude, nan ta ga miss calls da ya wuce misali, ta shiga call logs ta ga kiran Aliyu guda daya wanda yayi mata tun da safe, bata san sanda ta sauke wani ajiyar xuciya ba, so he did call her, wani Murmushi tayi, tayi dialing number sae da ya kusa katsewa ya daga, tayi kasa da murya tayi masa sallama ya amsa, jin yayi shiru a hankali tace “Can you hear me?” Yace “Yea ina ji” tace “You called da safe, bani da lafiya shi yasa ban samu dagawa ba” Yace “Baki da lafiya? Me ya sameki?” Ta langwabar da murya tace “Na tashi da xaxxabi ne” Yace “Subhanallah, how are u feeling now?” Tace “Da sauki shi yasa har na samu na kiraka” Yace “Since when were u sick?” Tace “2 days ago” Ya dan yi shiru, sai kuma yace “I am sorry, Allah Ubangiji ya baki lafiya” Ta lumshe ido tace “Ameen” Yace “Hope kina iya cin abinci?” Tace “Ehh daxu na samu na ci” Yace “Get well soon dear” Ta dan yi shiru sai kuma tace “Kayi hakuri da abinda ya faru few days back” Yace “Nihad” Tace “Na’am” yace “Daga ina akayi employing driver din nan?” Tace “Wllh ban sani ba i just saw him over night a gidan” Yace “Ya sunansa?” Ta gyara xama tace “Halilu” Yace “Good, yana gidan har yanxu ko?” Tace “Yana nan wllh, rashin mutunci kuwa sae abinda yayi gaba, i have just decided in dinga hawa adaidaita from henceforth idan xan je makaranta” yace “You don’t worry, i will bring an end to everything” tayi wani Murmushi tace “Trust u dear” Yace “A gidan yake permanently ko yana xuwa ya tafi ne?” Tace “Aa a nan yake permanently ba inda yake xuwa” Yace “Ohk, gobe xan shigo kano in sha Allah” tace “Toh Allah ya kai mu” Yace “Ameen, i will call u back later” Tana Murmushi tace “Alright dear” daga haka ya katse wayar ta lumshe ido ta bude cike da farin ciki, at last they will bring an end to this forsaken driver, tasan tun da har ya shiga trap din Aliyu kuma ya shiga uku. Nihal na ta xaune parlor a dining area har kusan karfe tara na dare, she her self don’t even know what exactly she is sitting down there for, har Umma sai da tayi mata magana ta tafi ta kwanta ita da xata yi tafiya gobe, amma bata bar wajen ba, Farooq ya shigo parlon ganin ita kadai yace “Me kike yi a nan?” Ta kirkiri murmushi tace “Ba komai kawai ina duba waya ne” Yace “Ohk, xo ki amshi sako ki ba Aminu” Tace “Toh” Mikewa tayi ta bi bayansa har xuwa bedroom dinsa ya dauko wani takalminsa ya mika mata yace “ki kai masa” Ta amsa tace “Toh” Yace “Gobe da yaushe xa ki tafi?” Tace “Da safe in sha Allah” Yace “Ohk” Juyawa tayi ta bar wajen, tana fitowa compound ta tafi bakin gate inda Aminu yake, Bata ga Aminu a wajen ba sai khalil, yana ganinta yace “Barka da yamma Hajiya” Ta gyada kai kawai tace “Ina Aminu?” Yace “Ya ɗan fita xai dawo yanxu” Tace “Ohk, ba nisa yayi ba?” Yace “Ehh ban san ko yyi nisa ba” Ta koma gefe ta tsaya tace “Ok i will wait” shi dai Khalil bai ce komai ba, but from all indication he was uncomfortable with her by his side, bayan kusan minti daya tayi breaking silent din tace “Daxu na maka tambaya baka ce min komai ba” ya ki kallonta yace “Ohh, yi hakuri Hajiya wani tambaya kenan?” Tace “Kawai cewa nayi, xan iya sanin ko kai waye?” Yayi shiru na few seconds, sai kuma yace “Ohk amma ina son ya kasance tsakanina da ke, don ba kowa nake ba labarina ba” Nihal tace “In sha Allah nayi alkawarin rike maka sirrin ka” Murmushi yayi ya gyara xama yace “Kinyi alkawari har yar uwarki baxa ki gaya ma” Nihal tace “Nayi alkawari” Yayi kasa da murya yace “Kamar yanda na sanar maki a baya, ni sunana Ibrahim, amma a kan kirani da Khalil, ni haifaffen garin getso ne….” Ta katse sa tace “Garinsu Malam Habibu?” Yace “Ehh, garinmu daya, har kuma yanxu iyayena na garin duk da baabata yar Nijar ce, don ta kan daukeni da kannena mu je Nijar a shekarun baya” Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba tana ta kallonsa, ya sosa kansa yace “Nayi karatun primary, daga bisanni na daura da na sakandari inda na dakata a aji na uku ban ci gaba ba har yau, Baabata ta saka ni gareji a wancan lkcn, amma Allah bai yi xan maida hankali in koyi gyaran motar ba, kawai na koma aikin plumbing tare da wani d’an kanin babana a garin, sai dai ban dau lkci ina aikin plumber ba kasancewar na iya karatu da rubutu dai dai gwargwado ya sa wani a garin namu me suna Alhaji Mu’azu ya ajiyeni shagon chemist dinsa ina jire masa shagon, na kuma fi shekara takwas ina xama a shagon har daga bisanni Allah yayi masa rasuwa, da farko na samu wani aikin wanki da guga a gidan wani commissioner nan cikin garin kano, wani yaron me chemist din yayi min hanyar aiki a gidan, to yarinyar gidan ta kan xauna tare da ni mu yi hira, idan xata yi fita ba me nisa ba ni take sa in rakata, duk wani aike nata ni ke xuwa, kuma duk abinda aka girka a gidan da kanta take debo min ta kawo min, tana da kirki ainun, kuma baxan ta6a mance alkhairinta gareni ba, ita ta karfafa min gwiwa muke turanci tare, wanda banyi dai dai ba ta gyara min, bata kiran sunana kai tsaye sae dai ta ce min Kay… Wannan kusancin namu ya sa mahaifiyarta warce ‘yar daya daga kasashen larabawa ce ta tilasta mai gidan sai da ya sallameni, a nata tunanin soyayya muke da yarinyarta, wanda kuma ba haka bane, sunan yarinyar Nadeeyah… da ita muka hadu a Supermarket daxu…” Nihal dae kallonsa take ko kiftawa babu, ya shafa kansa yace “Yauwa abinda na mance ban gaya maki ba shine ina da iyali da yaro daya wanda Allah yayi ma rasuwa ko wata biyu ba ayi ba yanxu, kuma shekarunsa biyar a duniya ya rasu” Nihal ta buda ido sosai tana kallonsa with shock, ya sauke kansa daga kallonta, he was looking sad, a hankali tace “Hasbunallah, Allah ya gafarta masa” Yace “Ameen, sunan matata Jiddah, wannan dalilin ya sa Nadeeyah kan kirani da Kay… Wani lkcn kuma ta kirani da KJay, har garinmu na kai ta wajen matata Jiddah” Nihal dai bata ce komai ba, Khalil yace “Bayan kusan sati uku da sallamata da aka yi daga gidansu Nadeeyah, shine Habibu yayi min hanyar wannan aikin a nan gidan, kin ji takaitaccen tarihi na….” Ta daga kai ta kallesa, kallonta yyi jin bata ce komai ba, a hankali tace “Allah ya taimake mu baki daya” Yace “Ameen” Aminu ne ya shigo compound din rike da leda, yana ganinta da farko sae da gabansa ya fadi don a xatonsa Nihad ce, sae ya ga ba ita bace, Aminu ya washe baki yace “Barka da dare Hajjaju” yana fadin hakan ya shige dakinsa da ledan hannunsa, Khalil yace “Karfe nawa xa kiyi tafiyar gobe?” Tace “Da safe in sha Allah” Yace “Ohk, ke kadai ce ai ko?” Ta ɗan yi shiru sai kuma tace “Aa yawanci tare da Nihad muke tafiya, idan sun ajiyeni sai su juya” Yace “Ohk” ajiye takalmin hannunta tayi tace “Idan Aminu ya fito ka basa inji ya Farooq” Yace “To” Tace “Sai da safe” Yace “Allah ya tashe mu lfya” Juyawa tayi ta nufi cikin gidan ya bi ta da ido letting out a Sigh. Washegari da safe Khalil ya fito ta dalilin aika Aminu da Abba yayi ya kirasa, A balcony ya tadda Abba ya gaishesa da ladabi Abba yace “Xaka ajiye Nihal a Zaria, tare xa su tafi da yar uwarta sai ku dawo tare” Khalil ya sunkuyar da kai yace “Na gane… Amma sai dai na tashi yau bana jin dadi ranka shi dade” Abba yace “Me ke damunka?” Khalil yace “Ina jin ko malaria” Abba yace “Ya salam, Allah ya sauwake, baka da net ne?” Khalil ya girgiza kai yace “Aa bani da” Abba yace “Toh anjima xan baka kudi kaje ka siya” Khalil yace “Toh nagode Abba” Abba yace “Madallah, Amma ko kai da Saminu ne ku je asibiti a duba ka yanxu” Khalil yace “Toh in sha Allah” Abba yace “Kafin ku tafi ka sanar da ni” Yace “Toh nagode” Abba yace “Ba damuwa tunda farooq na nan sai yaje ya ajiyeta, kaje kawai” Khalil ya sakema Abba godiya sannan ya bar wajen, da Nihal kadai ce xai kai ta, but kasancewa tare da Nihad ne shi yasa ya gwammace yace bashi da lafiya, dalilin da yasa ma ya tambayu Nihal jiya kenan ta sanar masa tare da Nihad ne, tun jiyan kuma yayi deciding he won’t be going shi yasa ya tashi da wannan plan din, he just can’t withstand driving that far with Nihad in the car… Abba na shiga parlor ya ga Nihal har ta fito da jakunkunan kayanta, yace “Nihal ki jira in yi magana da Farooq ya kai ki, driver yace baya jin dadi” Shiru Nihal tayi tana kallon Abba, sai kuma ta nemi kujera ta xauna, Abba kuma ya tafi dakin Farooq, sai ga Nihad ta fito rike da handbag dinta tana kallon Nihal tace “Ke wai wannan yaron ne xai kai mu har Zaria? Ni gaskiya i can’t withstand seating that long in the car with him, in har da shi ne gwara in fasa kawai, kar ma yaje da gangan ya kasheni a hanya idan muna dawowa” ko kallonta Nihal bata yi ba balle ta tanka ta, sai ga Abba ya fito yana kallonsu yace “Ku fita da kayan Farooq xai kai ku yanxu” Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Better” Trolly din Nihal daya ta dauka ta fita waje, tana ta tsaye a bakin motar har Nihal ta fito tare da Amina dake rike da wani Trolly din, Bayan farooq ya fito duk suka shiga motar, Mumy na tsaye balcony bayan tayi ma Nihal addu’ar Allah ya kai ta lafiya Allah ya tsare, Ummu ma na balcony din a tsaye, a duk sanda Nihal xata koma makaranta sai ta ji kamar xata yi xaxxabi, duk cikin yaranta babu wanda take ji har ranta kamar Nihal, a haka har farooq ya gama warming motar ya fita, Aminu ya daga masu hannu yana cewa “Allah ya bada sa’ar karatu, ku kuma Allah ya maido ku gida lafiya” Nihad da ke xaune back seat ita da Nihal ko kallonsa bata yi ba, Farooq da Nihal kadai suka amsa da Ameen…. Bayan sun dau hanya wayar Nihal dake jakarta ya fara ring, Nihad ta juya tana kallonta, bude jakar tayi ta fiddo wayar tana kallon screen din ta ga Khalil, Nihad ta kikkifta ido don ta kara tabbatar da sunan da ta gani a jiki, bata san sanda ta bude baki ba don mamaki, Nihal ta daga kiran ta kai kunne, Dubara Nihad tayi ta matsa dab da ita ko xata ji abinda xai ce, daga daya bangaren Khalil yace “Kin tashi lafiya Hajiya?” Nihal tace “Alhmdlh, ina kwana?” Yace “Lafiya, ban samu damar kai ki ba, kuma kin tafi ba mu yi sallama ba, Allah Ubangiji ya tsare hanya, ya kai ku lafiya, ya baki sa’ar abinda aka je nema” Ta sauke idonta kasa tace “Ameen nagode” Yace “Sai anjima” Tace “Nagode” Katse wayar yayi, Nihad ta matsa tana kallonta da kyau tace “Nihal ba driver din nan bane ya kira ki?” Nihal ta ki cewa komai, Nihad ta saki baki tana kallonta, Farooq dake jin su yace “Wani Driver?” Da sauri Nihad tace “Ji fa yaya, driver din gida fa, meye hadinta da shi har ma zai kirata yanxu??” Farooq dai sai kallon Nihal yake ta madubi, Nihal ta hade rai tace “You have problem Nihad, komai ke sai kin san yanda kika yi kika canxa masa ma’ana, what’s wrong with me having the drivers number, naga har number Saminu ina da shi me yasa be xama laifi ba? Ke lkcn da Habibu yake nan baki da numbersa? Waye yafi communicate da Habibu a gidan banda ke?” Nihad tace “Noo, ae Habibu daban wannan daban, kuma Habibu sai ta kama muke magana da shi a waya….” A fusace Nihal tace “Toh wannan din ma kamawa yayi muka yi maganar a waya” Farooq yace “Toh wai ke Nihad ina ruwanki??” Kallonsa Nihad tayi, lkci daya ta hade rai bata ce komai ba, yace “Ke ce ai kika dau girman kai kika daura ma kanki but there is nothing wrong to have people that are under you phone number” All through the journey Nihad bata sake cewa komai ba amma fuskarta a daure yake. Satan kallon Nihal take taga tana bacci, a hankali ta dauke wayarta dake kafarta ta bude don ita bata sa password, ta shiga call logs tayi blocking number Khalil sannan tayi deleting ta mayar mata da wayar ta ajiye. Har Nihad suka kai Nihal Zaria bata ce ma kowa komai a motar ba, Farooq ya kalleta yace “Sauka ki kama mata kaya ku shiga hostel” Ta ɗan daure fuska ta bude motar ta sauka, nan ta taya Nihal suka kwashe kayanta xuwa hostel din, bayan Nihad ta ajiye jakar karshe ta juya xata wuce Nihal tace “Are u still angry? Toh kiyi hakuri” Nihad ta kalleta tace “Baxan yi ba, ba dai driver ya fi ni ba” Nihal tayi Murmushi tace “Ya xa ayi driver ya fi ki, kema kinsan babu wanda ya fi ki a wajena, kiyi hakuri i didn’t mean to make u angry” Nihad ta harareta tace “Kamar da gaske” Rungumeta Nihal tayi tace “Wllh kema kinsan da gaske nake blood” Nihad tace “Toh shkkn na hkura” Nihal tace “Toh nagode” a tare suka koma gun mota inda Farooq ke jiran Nihad, Nihad ta bude jakarta jin wayarta na vibrate, ganin Aliyu ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa yace “Xan shigo kano in the evening, ki turo min address din gidanku” Nihad ta wara ido tace “Are u coming to our house” Yace “Ki turo ina jira” daga haka ya katse wayar, Farin ciki ne ya lullubeta, bai ta6a cewa xai je gidansu ba sai yau, a baya babu yanda bata yi da shi a kan ya xo gidan nasu ba amma sai ya ki, har ta kagu ta gansu a gida ta tambayi Umma abubuwan da xata dafa masa, nazari ta shiga yi… or is he coming because of that useless driver?? Ohh God that will be very great.

💖💖 *NIHAAD*💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

14…..

Karfe biyu saura Nihad suka iso gida tare da farooq, yana kashe motar ta bude ta sauka, kallon direction din Mai gadi dake kulle gate tayi bata ga khalil ba, ta juya ta wuce cikin gida, direct part din Umma ta tafi, Umma dake parlonta tace “Oyoyo, har kun dawo?” Nihad tace “Ehh Umma, yau dai in gaya maki bata yi kuka ba da xa ku tafi” Umma tace “Toh ai gwara haka, kukan ba shi da amfani” Nihad ta xauna gefen Umma tace “Umma guess what?” Umma tace “Aa… ni kinsan i am not a good guesser, gaya min abinda ya faru daughter” Nihad na Murmushi tace “Umma Aliyu xai xo gidan nan yau” Shiru Umma tayi tana kallonta babu ko kiftawa, can tace “Wani Aliyu?” Nihad ta wara ido tace “Aliyu dai Umma” Umma tace “Amma ba kince min ya daina daga kiranki ba?” Nihad tace “Ehh wllh, kawai sai na ga kiransa jiya Umma, he called me him self” Umma ta girgiza kai tace “Nihad…. Nihad, bakya ji Nihad, baki jin magana wllh, na gaya maki ki raba kanki da Aliyun nan kin ki ji, ban san yanda xan yi da ke ba kuma, Aliyu ba komai xai yi ba illa ya yaudareki ya kama gabansa, nace ki daina hada kanki da ya yan masu kasar nan, Aliyu ya fi karfinki, ki kula dai dai ke amma kin ki ji, yaudarar ki kawai yake idan kin bibiya ma an sa masa rana, su da junansu suke aure basa auren kasa da su” Nihad tayi narai narai da ido tace “Umma wllh ba yaudarata yake ba, Aliyu yana so na, kuma yace min ina shiga level 3 xai turo iyayensa wajensu Abba, wllh haka yace min ranan nan Umma” Umma ta bude baki tace “Ehh Lallai ke shashasha ce mahaukaciya, shi Aliyun ne xai turo iyayensa gun Abbanku? Nihad nace ki daina kai kanki inda Allah ba kai ki ba, shi uban Aliyun ne xai bari ya aureki ko uwarsa?” Nihad ta hade rai tace “Ni dai kawai Umma ki gaya min abinda xan girka masa…” Umma tace “Girki? Shi yace ki yi masa girki?” Nihad tace “Aa, amma daga Abuja fa xai biyo flight ya xo, kin ga ai ya kamata in ajiye masa abinci” Umma tace “Aa babu wani abinci, a xuwan farkon ne xaki yi masa wani girki? Ai ba a girki sai in mutum ya xo ya fi sau biyar, kawai ruwa xaki ajiye masa da lemo…” Nihad tace “To snacks fa?” Umma tace “Toh shkkn xan maki small chops ki ajiye masa” Nihad tace “Toh Umma nagode, sai in taya ki?” Umma tace “Aa ba sai kin taya ni ba, kawai ke dai kije ki shirya” Nihad tace “Toh Umma, amma parlon visitors din Abba xan shigo da shi ko?” Umma tace “A wani dalili mutumin da babu wanda ya san sa a gidan xaki shigo da shi parlon baƙin Abbanku? Ai daga waje xaki ajiye masa kujera fari ya xauna” Nihad tace “Umma fa har na gaya ma Ya farooq shi yace in ajiyesa parlon baƙin Abba” Umma tace “Toh shi wannan wawan me ya sani? A xuwa na biyu ko uku shine xa a shigo da shi cikin gida” Nihad dai tayi shiru, Umma tace “Yanxu dai tashi ki je ki shirya, nima xan tashi inje kitchen in yi abinda xan yi” Nihad tace “Toh” Daga haka ta mike ta fice daga parlon Umma ta bi ta da kallo, Nihad na komawa dakinta wanka tayi ta dauro alwala ta fito, tana xaune kan darduma bayan ta idar da sallah tana danna wayarta Mumy ta shigo dakin, Nihad ta ajiye wayar tana kallonta tace “Umma ina yini…” Sai kuma tayi saurin cewa “Au Mumy ina yini?” Mumy tace “Ban yini ba, dama jira kike in shigo in gaisheki da ku ka dawo?” Nihad ta xaro ido tace “Aa wllh Mumy, dama yanxu nake son idan na gama addu’a in je in gaisheki” Mumy tace “Toh yayi kyau, ai naha addu’ar kike yanxu” Nihad tayi Murmushi tace “Ya jikin su Sudais Mumy?” Mumy tace “Ban sani ba, kin shiga duba su ne da kike tambayata” Nihad ta marairaice tace “Umma wllh yanxu nake son in je” Mumy tace “Kika sake ce min Umma xan bata maki rai wllh Nihad” Rufe baki Nihad tayi, Mumy ta juya ta fita daga dakin, tashi Nihad tayi ta bi bayanta, suna komawa bangaren Mumy tace “Ina suke Mumy?” Mumy tace “Suna tsakar gida, hope Nihal bata yi kuka ba yau, na dai kirata daxu tace tun 11 ku ka ajiyeta” Nihad tace “Ehh Mumy bata yi kuka ba ta fara xama big girl, Mumy Kinsan me?” Mumy tace “Ina jin ki” Nihad tace “Mumy Aliyu xai zo yau” Mumy tace “Wani Aliyu?” Nihad tace “Lahh, Aliyu da nake baki labari mana” Mumy tace “Ohk, toh Allah ya kawosa lafiya” Nihad tace “Ameen” Mumy tace “Me xaki tanadar masa?” Nihad tace “Mun gama maganan wannan da Umma” Shiru Mumy tayi tana kallonta, Nihad tace “Bari in dubo su Fadil” Daga haka ta fita daga parlon, ganin basa main parlor din gidan kawai ta fita compound, nan ma ta bi compound din da kallo bata ga kowa ba sai Aminu a bakin gate, ta karasa tace “Kai Aminu ina su Fadil?” Aminu yace “Barka da dawowa Hajiya” Nihad tace “Su sudais nake tambayarka” Aminu yace “Ayyo suna can tare da khalil, da a nan ma suke” Ta wani yamutse fuska tace “Waye kuma haka?” Aminu dai yayi shiru yana sosa kansa, tace “Wai wannan driver din?” Aminu yace “Ehh Hajiya” Tace “Kan bala’i, me suka je yi wajensa” sai kuma ta juya da sauri ta bar wajen ta nufi chalet ai ko ta ga takalmansu a bakin kofa, nan da nan taji ranta ya baci, yanxu cikin kazantaccen wajen nan ya shiga da su salon su ki warkewa, k’in shiga parlon tayi ta xaga ta bayan windown dakin da tasan yake ciki, ai ko a bude ta tadda window din an dage labule, can ta hangosa xaune far end of the bed da waya karama kare a kunnensa, su kuma kannen nata suna kwance kan gadon ta jikin bango suna game, ƙafafuwan su kadai take hangowa, a fusace tace “Uban meye ku ke a nan Sudais?” Da sauri Khalil ya juya yayi stretching hannunsa ya amshi wayar hannun Fadil keeping the phone under the bedsheet, duk kannin nata suka taso suna kallonta, Sudais yace “Aunty Mumy ce tace muje mu yi ball a waje” Tace “In fasa maka kai a wajen, ball din kenan? Kun shigo nan salon wari ya kashe ku ko? To wllh idan baku taso ba ku ka bari na shigo duk sai na xane ku a wajen nan, meye hadinku da shi?” Duk suka nufi kofa, ita ko ta dinga hararan khalil da ko kallon inda take bai sake yi ba, ta ja wani dogon tsaki ta juya ta bar wajen. A bakin kofar chalet din ta tarar da su suna sa takalmansu, ta ce “Uban meye ma ku ke yi a ciki? Waye yace ku shiga ciki?” Fadil yace “Game mu ke yi da wayarsa ya ba mu” Ta tafe hannu tace “Shi game din nokia phone din ne ya burge ku? Toh daga yau na sake ganin ƙafafuwan ku a hanyar wajen nan sai na xane ku da dorina” Tana gama fadin haka ta fixgo hannunsu suka bar wajen, Sudais yace “Aunty irin phone dinki yake da shi” Nihad ta kallesa tace “Wa xai basa irin phone dina?? Ai har ya mutu” Fadil yace “Irin naki da na Aunty Nihal ne, exactly the type of ur own…” Nihad tayi dariya tana jinjina shashancin kannen nata tace “He can neva have the type of my phone till he die Fadil, my phone is over a million, kasan kuma meye million?” Sudais yace “Har da Diary Milk chocolate ya ba mu each, Kuma Aunty yana da su da yawa a jaka, ni dai i want him to be my frnd…” Muryar Umma ta ji tana kiranta ta sake kannin nata ta shiga parlor da sauri tace “Na’am Umma?” Umma tace “Yauwa nayi kokarin in ma Hafsah transfer taje kasuwa tayi min chefane babu network, ke idan kina da network ki mata ta je da sauri ta dawo yanxu” Nihad tace “Umma ba akwai abubuwan a freezer ba? Meye babu?” Umma tace “Aa ba komai bane akwai Nihad, ki mata transfer din in gaya mata abubuwan da xata siyo min” Nihad tace “Toh bari in dauko wayata” Daga haka ta wuce sama xuwa dakinta, tana dauko wayar ta tura ma Hafsah dubu sha biyar, tace “Umma na tura mata 15k” Umma tace “Toh shkkn, je ki ki shirya” Nihad ta koma sama. Tana fito da kayan da xata saka wayarta ya fara ring tana dubawa ta ga Aliyu ne, ta daga yace “Flight dinmu xai taso yanxu in sha Allah” Nihad ta wara ido tace “Toh sai ka iso, Allah ya tsare” Yace “Ameen” katse wayar yayi, nan ta hau shiryawa da sauri, kaya kawai ta saka bata shafa komai a fuskarta ba ta fito, tana sauka downstairs fridge ta fara dubawa taga wani drinks ne a ciki, duk yawancin drinks din Aliyu bai damu da su ba, his favourite drink is Can coke, sai kuma Hollandia milk, rufe fridge din tayi ta koma dakinta ta dauko Atm card dinta ta fito, ta gyara dankwalin dake kanta ta fita compound, gun Aminu ta nufa, yana xaune da Khalil a gefensa, ko kallon khalil bata yi ba tace “Aminu xan ɗan aikeka supermarket yanxu” Yace “Toh Hajiya” Ta mika masa Atm card dinta tace “Pack din coke na gwangwani xaka siyo min ka bude kunnenka da kyau na gwangwani na aikeka ba na gora ba, sannan ka siyo pack din Hollandia milk, amma farin ba jan ba….. farin ba jan ba, tamm don kana min shirme sai ka shanyesu tass ka biyani kudina” Ya amshi Atm card din yace “Toh Hajiya, in sha Allahu” Tace “Ka tuna password din?” Yace “Aa ya kwanta min wllh” ta saci kallon khalil da ko inda take bai kalla ba, ta yatsine fuska tace “Mu je kofar gida in gaya maka” Yace “Toh” Da sauri ya fita gate din, ta wuce ta gaban khalil xata fita kofar gida ba tare da ta damu da cewa babu gyale a jikinta ba, sai a sannan Khalil ya bi ta da kallo, tana fita waje ta kulle gate din ruf, tana kallon Aminu ta gaya masa pin din tace “Saura kuma kaje ka min wasa da Atm a titi, dama kana dawowa ko tsayawa kar kayi a bakin gate ka kawo min Atm card dina kada aje a min sata” Yace “Toh Hajiya” Daga haka ta bude gate ta shigo gidan, tana tafiya kamar baxata taka kasa ba tana yi tana yatsine fuska ta wuce khalil, juyawa tayi xata kallesa suka hada ido ta galla masa wani shegen harara ta rike kugu tace “Da bashi ne?” Yace “Ke xan tambayi wannan” Buda baki tayi tana kallonsa da mamaki, can ta dawo fuska daure tace “Kace me???” Shiru yayi yaki cewa komai yana kallon sky, tace “Aa in ka isa da ka maimaita ai tunda kai baka da kunya fitsararre kawai” Ya kalleta yace “Me kike son in maimaita wai” Tace “Ban sani ba” Yace “Ohk, amma tunda har kika ga ban saci abubuwan ki masu muhimmanci dake jakarki shekaranjiya ba, ba kuma wani satan da zan maki, ko duk cikin muhimman kayanki akwai abinda kika nema kika rasa, har kwalban nan ban ta6a ba ai” Tayi masa wani kallo tace “Wani kwalba??” Tashi yayi, yayi mika ya nufi gate ya fita ya bar ta nan a tsaye, ta bi sa da wani irin kallo, sai kuma ta juya ta bar wajen. Xama tayi parlor ta jira har Aminu ya kawo mata sakonta da Atm card sannan ta xuba su a fridge ta wuce sama. Har bayan kusan minti talatin Hafsah bata dawo ba, Nihad da har ta gama kwalliya ta kashe dauri ta fito parlor ganin Umma a xaune tana kallon wani film tace “Umma ya fa kirani 30 mins ago yace xa su taso” Umma ta kalleta daga sama har kasa don ba karamin kyau tayi ba, kamar wata balarabiya, atamfar yayi mugun amsar jikinta, ga make up din tayi sa very light, she look so beautiful, Umma ta tabe baki tace “Toh gantalaliyar bata dawo daga kasuwan ba har yanzu, ni ma har na gaji da jira abinda ya sa na xauna parlon kenan ina jiran dawowarta, don ma ai ba wahala cikin lkci kankani xa a gama…” Nihad ta kalli agogo tace “Toh Umma bata tafi da waya ba in kirata?” Umma ta nuna mata wayar a kan kujera tace “Kin ga inda nace ta ajiye wayar don ma kar taje wani yace mata su hadu a wani waje, kinsan gantalaliya ce, opportunity din fita kawai take jira” Nihad ta nemi waje ta xauna ranta a bace, sai kuma ta tashi ta tafi parlon baƙi ta kunna turaren wuta ta fito ta xauna, har bayan wani minti sha biyar din babu Hafsah babu alamarta, Nihad taji kamar ta fashe da kuka, Umma dai is so engrossed a kallon da take a parlon, wayar Nihad ya fara ring ta xaro ido ganin Aliyu ne, ta daga ta kai kunne, yace “Na kusa shigowa layin ku fa… In 2 mins time” Nihad ta mike tace “Ohk toh” Katse wayar yayi, Umma ta kalleta tace “Ya aka yi?” Nihad kamar ta fashe da kuka tace “Wllh Umma babu abinda xai hadani lakada ma Hafsah shegen duka yau, kin dai ga har gashi ya iso bata dawo ba ko, ni yanxu don Allah me xan basa??” Umma ta xaro ido ta mike tace “Haba dai har ya iso?” Nihad ta wuce sama a fusace, make up din fuskarta ne kawai yasa take danne hawayen da yake son ya taru a idonta, Umma ta rike ha6a tace “Amma Hafsar nan anyi yar iska yarinya, shegiya kawai, nan nan kasuwa taje ta dawo amma kamar an aiki bawa garinsu? To ai da na sani na bari ta tafi da wayar, kuma ni ma banyi dubara ba da naji shiru ko kaji ne sai in dafa ayi masa pepper chicken” Khalil na xaune kofar gida da Aminu tare da mai gadin gidan dake kusa da su, Kallon motar da ya shigo layin tun daga nisa yake with full interest, lkci daya ya gane motar from the other day, ya mike ya juya xai shiga cikin gidan, Aminu na tambayarsa inda xa shi yace “Ina xuwa” karo suka kusa ci da Nihad da xata fito gate din ita ma, ya koma baya da sauri, ta hade rai still inhaling his strong enchanted perfume, k’in basa hanya ya wuce tayi…..

💖💖 *NIHAAD*💖💖

15

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Khalil ya koma baya yana kallonta, still taki barin wajen sai ma wayarta da ta hau dannawa xata kira Aliyu taji ko ya karaso layin, kawai ya bangajeta ya wuce ciki, xaro ido tayi lkci daya ta riko rigarsa a fusace ta cakumo kwalarsa tace “Are you mad?? ni xaka bangaje ka wuce? baka da hankali ne ko ka fara shaye shaye?” Yana kallonta straight in the eyes yace “Irin wanda kike sha?” Bai bari ta gama digesting abinda ya fada ba ya fixge hannunta daga rigarsa ya juya ya bar wajen yana tafiya majestically, baki bude ta bi sa da kallo, irin wanda take sha?? Me yake nufi kenan?? Kallon wayarta da ya fara ring a hannunta tayi ganin Aliyu ne, ta daga a hankali tace “Ina ji” yace “Gani kofar gida….” Leka gate tayi taga yayi parking a kusa da gidan dake kallon nasu, ta fita gate din, duk yanda ta so ta sake fuskarta kasa yin hakan tayi don abinda khalil ya fada mata yayi mugun tsaya mata a rai, ta nufi motar, su Aminu suka bi ta da kallo, Aliyu ya sauke glass dinsa yana kallonta, ta kirkiri murmushi tace “Sannu da xuwa” Sai a sannan ta lura ba shi kadai bane a motar tare yake da abokinsa Mujahid, Mujahid yace “Madam ya gari” Tana murmushi tace “MB, ya kwana biyu?” Yace “Alhmdlh Nihad, ya karatu” Tace “Alhmdlh, sannun ku da xuwa” Ta kalli Aliyu dake kallonta tace “Bismillah mu shiga ciki” Yana kallon masu gadi yace “driver din ne can a xaune?” Ta girgiza kai tace “Ya shiga ciki” Bude motar Aliyu yayi ya sauko, Mujahid ma ya sauko, tayi leading dinsu xuwa cikin gidan, Aminu ya dinga kallonsu ta side eye, tun daga takalman kafarsu, kayan jikinsu, agogon wrist dinsu, da hula xaka san rich kids ne, su ne elite… tuni kamshin turarensu ya baxa tun daga bakin gate har cikin compound din, in dai kyau ne kam a wajen Aliyu ba a cewa komai sai dai kawai he is black! Fine black. Nihad dai na gaba suna baya, ta kai su har parlon baƙin Abbanta, the parlor was cool and smelling so nyc sbda AC da ta bari a kunne tun daxu, bayan sun xauna, ita ma ta xauna saman kujera ta gaishesu gaba daya, suka amsa tana Murmushi tace “Bari in kawo maku ruwa” Aliyu ya shafa kansa yace “With food, Kinsan ko lunch ba mu yi daga Abuja ba” Lkci daya jikinta yayi sanyi ta dai saki murmushi tace “Ohk, let me get the water first” Fita tayi daga parlon, she was so confused, bata san me xata yi ba, to ko order din abinci xata yi kawai ta juye masu a plate ta kai masu, but that might take a long time kafin ma abincin ya iso, tana shiga main parlor bata ga kowa ba, ta nufi kitchen jiki ba kwari, Umma ta gani tsaye a bakin kofa tana cewa “Ni dama idan da an bi ta nawa a gidan nan tuntuni da an sallameta, babu dama ka aiketa yanda kasan ta tafi da pillow da katifa, idan kayi magana ace ka fiye takura ka fiye tsanani, haka Farooq ke ce min, ko kema nasan haka kike gani, amma ba haka bane dole sai mutum yana yi yana jan ido, to ai gwara da ta guma ma kowa yau…” Umma ta juya ganin Nihad tace “Kin shigo da su Daughter?” Nihad kamar xata yi kuka tace “Umma abinci fa xa su ci wai, ni yanxu ya xan yi don girman Allah?” Umma tace “Atoh ai dama baxa mu bar su haka ba, dole xa a samu alternative….” Nihad ta leka kitchen din ta ga Mumy tsaye bakin gas tana hada ingredients din Chinese fried rice da yake akwai left over cooked rice a kitchen din, sannan ga kaza a gefe tana sarrafa shi, farin ciki ne ya rufe Nihad, Umma tace “Ai ban ta6a ganin tsinanniyar yarinya irin Hafsah ba, ko kare ya shafa mata lafiya a yawo, babu dama ka aiketa ko nan da nan ne sai ta bata maka rai” Mumy dai aikinta kawai take, Nihad ta karasa kitchen din ta dau abinda xata daura masu drinks, ta dau glass cups tana kallon Mumy, a hankali tace “Mumy nagode” Ko kallonta Mumy bata yi ba, sum sum ta juya ta bude fridge ta debi drinks din ta daura a tray ta fita kitchen din, tana ajiye masu a parlor Aliyu yace “Xa mu gaisa da su Mumy yanxu ko?” Tace “Toh bari in sanar masu” Mikewa tayi ta fita, suka dau lemo da cup, tana komawa kitchen ta kalli Umma tace “Umma wai xa ku gaisa” Umma tace “Toh su shigo nan parlon, ai a shirye muke” Juyawa Nihad tayi ta koma, Umma tace “Ai ba sai mun wani yafa mayafi kamar wasu tsofaffi Maryam, suna shigowa parlon sai mu fita kawai” Mumy dai tayi Murmushi tace “Gaskiya ne” Umma ta karasa bakin gas din tace “Ko da yake ke nasan sai kice baxa ki fita haka ba sai da Hijab, bari in dinga duba girkin ki dauko Hijab din naki a sama” Mumy tace “Xai iya yiwuwa sun shigo parlon yanxu ai ko” tana fadin haka ta tafi inda ta ajiye wayarta a kitchen din ta dauka tayi dialing number kanwarta Jamila, tana dagawa tace “Jamila sauko min da Hijab dina sai ki taho da snacks din” Tana fadin haka ta katse wayar, taje ta ci gaba da abinda take, sai ga Nihad ta dawo tace “Umma suna parlon” Umma tace “Toh bari mu je a gaisa” Umma na fita kitchen din jamila ta shigo da hijab din Mumy, Mumy ta amsa ta saka, Umma na shiga parlon ta samesu xaune su biyu saman lallausan Carpet dake tsakar parlon, Umma ta xauna saman kujera tana masu sannu da xuwa, suka gaisheta da ladabi ta amsa tace “Fatan kun xo lafiya ya tsofaffin?” Suka amsa mata da “Alhamdulillah” Umma tace “Toh madallah, sannunku da xuwa… Tana ta cewa xaka zo yau dai gashi Allah yayi” Mumy ta fito suka gaisa a tsattsaye ta juya ta koma kitchen din, Umma na Murmushi tace “Toh wanene surukin namu cikin ku” Mujahid ya nuna Aliyu yace “Shine Aliyu” Umma na kare masa kallo tace “Madallah, maa sha Allah, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi Aliyu, Allah yasa ayi da mu, ya nuna mana wannan lokaci lafiya” Suka amsa da “Ameen” Umma tace “Kai ne ɗan Janar na fari kenan ko?” Yayi Murmushi yace “Ehh haka ne” Umma tace “Allah sarki, Baabarka ce uwargida amma?” Jamila dake can bakin kofar kitchen tana juyo conversation din da Umma ke yi da su ta saki baki da mamaki tana saurara, Aliyu yace “Aa ba ita bace” Umma tace “Ikon Allah, ta biyu ce kenan, dama kam ance matansa biyu ashe da gaske ne, Allah sarki, amma kai ne dan sa namiji babba ko kana da yayyi maza?” Ya girgiza kai yace “Kanana ne kannena maza” Umma tace “Maa sha Allah, abu yayi kyau wllh, amma ai duk ku kan zo hutu kano” Yace “Ehh muna xuwa lokaci lokaci” Tace “Madallah, ita uwar gidan bata da namiji ko daya kenan?” Ya girgiza kai yace “Mata ne” Umma tace “Ikon Allah, matan har nawa?” Aliyu ya daga kai ya kalleta for the first time, haka Mujahid ma kallonta yake ta yi, Aliyu yace “Su uku” Umma tace “Wayyo, wato dai Ummarka ita ce me ‘ya ya da yawa a gidan, toh ai hakan da kyau” Farooq na tsaye can bakin stairs ya kasa karasowa jin interrogation din da Mum dinsa ke masu, Jamila ta shiga kitchen a fusace tana kallo Nihad dake hada inda xa a sa masu abinci tace “Ke, maza tafi kice masu ga abinci can xa a kai su tashi daga parlon nan haka” Nihad tace “Toh” Daga haka ta fita daga kitchen din xuwa main parlor, Umma tace “Amma ai kai ba kasar nan kayi karatu ba ko?” Yace “Eh” Umma tace “Yauwa ko da na ji, ka kama aiki dai” Ya sauke kansa yace “Eh” Tace “Aa abu yayi kyau, wani aikin kake yi?” A takaice Aliyu yace “Business” Umma yace “Toh Allah ya sa albarka, yaushe xa ka turo magabatan naka kenan, in ji dai ba yanxu ba ko?” Aliyu yace “Yanda Allah ya tsara” Umma tace “Gaskiya ne, batun aure a hankali ake bin sa ba abu bane na gaggawa, ku kara fahimtar kanku sosai kar ayi gaggawa a lamarin nan, Nihad dai ‘ya ta ce, bata da wata matsala wllh baxan cuceka ba, kuma ina fatan Mahaifiyarka tasan kana nemanta dai ko?” Yace “Eh” Nihad ce ta shigo parlon tana kallonsu tace “Xa a kai abinci can” Umma tace “Eh kwarai kuwa, ga abinci can ku je a kai maku, sannunku da xuwa, Allah yayi maku albarka” Mikewa Aliyu yayi Mujahid ma ya tashi suka koma can daya parlon, Umma na kallon Nihad tayi kasa da murya tace “Ke bandir din daloli ne a aljihunsa wllh na hango” Dariya Nihad tayi, Umma tace “Allah kuwa, kawai ki ce masa wayarki ta samu matsala, su ai kudi abar banxa ce a wajensu….” Aunty Jamila ta kwalo ma Nihad kira ta tafi da sauri, Farooq ya karaso parlon rai a bace yace “Haba Umma, Haba Umma yanxu duk wannan tambayoyin kina matsayin surkarsu kinga ya dace kiyi masu? Me ya kai ki wannan tambayoyin fisabilillah?” Umma ta buda baki da mamaki tace “Wani tambaya nayi da bai dace ba farooq?” Yace “Umma ina ruwanki da ko matan babansa nawa ne, meye na tambayar baabarsa ce ta farko ko ta biyu, meye fa’idar tambayarsa ko a kasar nan yayi karatu kuma wani aiki yake? Ina ruwanki da tambayar ‘ya yan kishiyar baabarsa nawa” Umma ta hade rai ta kunduma masa zagi tace “Ka fita idona in rufe a gidan nan farooq, haka lkcn Kamila komai nayi kace ban iya ba ko bai dace ba, wai shin kai ka haifeni ko ni na haifeka? Laifi ne don nayi bincike insan inda xa mu tura er mu? Meye aibun tambayoyina? Ba neman aure ya xo ba? To kuwa ai dole ayi masa tambayoyi, Ko dama ance maza ne kadai xa su yi bincike banda mata? To wllh ka shiga hankalinka, ba ruwanka da harkana ko lamarina a gidan nan ina sake ja maka kunne” Farooq dai sai kallonta yake, can ya juya a fusace ya bar wajen, Umma ta bi sa da harara, Hafsah ce ta shigo parlon da leda a hannunta, Umma tace “Makira sai yanxu kika ga dama kenan, to kin kyauta kin ji ko? Ki tafi can parlona a sama ki jirani in xo in sameki ki gaya min gidan uban da kika je” Hafsah tace “Zan kai ledar kitchen” Umma tace “Aa wuce da shi sama, xa mu hade da ke a can” Hafsah bata ce komai ba ta wuce sama xuwa bangaren Umma, Nihad ta kai masu abincin da Mumy ta gama hadawa, wani tray kuma ga meat pie, samosa, spring rolls da doughnuts da Aunty Jamila ta kawo bayan Mumy tayi mata waya ta gaya mata tayi ta kawo, da yake tana da ma’aikata cikin kankanin lokaci suka yi suka gama, wani bowl me dauke da apples kusan goma ta kai masu a karshe ta ajiye, sannan tayi serving dinsu abincin. Bayan sun gama cin abincin, Nihad ta shigo parlon tare da Ya farooq, bayan ya gaisa da su ya fita, Mujahid ya mike yana kallon Aliyu yace “Bani makulli in dauko wayata a mota, they might be plenty of calls i missed” Aliyu ya mika masa makullin ya amsa ya fita, Nihad dai kallonsa kawai take, wayarsa ya ciro a aljihu ya shiga gallery bayan few seconds ya mika mata, ta amsa tana kallon screen din wayar, sosai gabanta ya fadi, ta dai yi shiru bata ce komai ba, yace “You promised kin daina dukka ire iren outing din nan, so where did this come from?” Nihad ta marairaice tana kara kallon hoton, 4 weeks ago ne suka je wani babban restaurant da su Naf da Husnah da samarin su, shine aka yi hoton a can, wando ne a jikinta sai crop top me shegen kyau da tsadadden sneakers a kafarta, sannan ta daura baƙin dankwali a kai ta xubo dogon gashinta, su Husnah ma duk ire iren shigar suka yi a hoton… jin tayi shiru Aliyu yace “Why are u quiet?” Ta daga kai ta kallesa a hankali tace “Hoton nan ai ya dade” Yace “Karya kike, this is a recent pix, jiya da daddare Naf ta daura a status na gani nayi saving” Nihad tace “Am serious ba kwanan nan muka yi ba, kuma ai kafin in maka alkawarin daina fita tare da su ne muka yi hoton nan, ka tambayi Naf din ma” Yace “Nihad!!” Shiru tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, yace “Saboda ina sonki da aure ya sa ki ka ga har nake hanaki abubuwan nan da kike, banda haka i have no business with ur life style, quite alright kinsan i have other babes wa enda muke tare da su har yanxu, but ban ta6a daga kai na hana yarinya yin abinda tayi niyya ma rayuwarta ba, ban ta6a hanasu holewarsu yanda suke so ba, but ke saboda intention dina a kanki daban shi yasa nake hanaki duk wannan shiriritar da kike, Upon how wealthy my parents are, baxa su ta6a yarda in kawo masu mace mara kamun kai ince xan aura ba, baxa su ta6a amincewa, kuma ya kamata ki kara yarda yanxu tunda har na tako tun daga Abuja na xo gidanku to da gaske aurenki nake son yi, i will neva do that for any lady, sai sai idan dama ina da wata sabgar da xanyi a kano…. Nihad this should be ur last warning!!!” A hankali tace “Toh kayi hakuri, in sha Allah hakan baxai kara faruwa ba, i am promising u this” Yayi shiru yana kallonta, tace “Wllh da gaske nake baxan kara ba” Yace “Toh Allah ya sa…” A hankali tace “Ameen” Yace “Kince min driver din a nan yake zama” Nihad ta gyara xama tace “Ehh wllh, yanxu haka ma yana nan, ai yana kofar gida sanda ku ka shigo layin shi ne ya shiga cikin gidan” Aliyu dake ta kallonta yace “Da muka shigo layin ne ya shiga ciki?” Tace “Aa ai sannan baku karaso ba” Yace “Ohk where is he now?” Nihad tace “What will happen now, kawai mu fita sai ka xauna a compound ni kuma xan je in samesa a can boys quarters da yake zama, ince xan je karbo sako ya xo ya kai ni, daga nan idan ya fito compound xaka gan shi” Aliyu yace “Kamar wasan yara… But i urgently wants to see him” Nihad tace “Noo, ta haka kadai xai fito compound har ka gansa, so now let’s go outside” Tashi tayi ta dau bowl din apples tace “Bari in kai maka wannan ka dinga ci” Daga haka ta fita, ya mike ya bi bayanta suka fito compound din, can karkashin thatch dake dauke da kujeru ta kai masa apples din ta ajiye saman table, ya xauna yana kallonta yace “Kin yi kyau” Tayi wani blush tace “Thank you, bari in je in samesa yanxu” Yace “Ohk” Hanyar Chalet ta nufa ya bi ta da ido har ta bace, ya kalli agogon wrist dinsa dake nuna hudu saura, Nihad na isa chalet din ta hade rai tana lekan parlor, isiya ta hango yayi dai dai kan kujera yana ganinta ya mike da sauri ya fito yace “Kaya xa a amsa Hajiya?” Tace “Ina wannan yaron?” Yace “Wani yaro?” Tace “Halilu” Isiya ya ɗan gwale ido a ransa yana kara nanata yaro da tace, can yayi saurin cewa “Yana can daki” Tace “Toh kaje ka kirasa Mumy ta bada sako a basa” Juyawa yayi yace “Toh Hajiya” Ya fi minti daya yana kwankwasa kofar dakin da Khalil yake ciki amma bai bude ba, shi dai yasan baya baccin rana balle yace, to ko kila yana bandaki, bai yi gigin bude kofar ba tun ranan da Saminu yayi masa haka yayi cutting din masa warning me lafiya, Bude kofar aka yi khalil na kallonsa yace “Ya aka yi?” Isiya yace “Aa dama mamarsu Sudais ce ta bada sako wai xa a gaya maka a waje” Khalil yace “Ohk” Fita yayi tun daga cikin parlor ya hangota, yana fitowa ya tsaya bakin kofa yana kallonta, Tana yatsine yatsine tace “Yauwa xaka yi dropping dina in amso sako yanxu, kaje ka dauko makulli ina jira” Juyawa yayi ya koma ciki ba a dau lkci ba ya fito rike da makullin motar, yana kallonta ya mika mata, ta hade rai tace “Meye kake mika min makulli cewa nayi ajiye ni xaka je kayi in amso sako ko kai kurma ne” Ya ajiye makullin saman matakalan chalet din yace “Toh baxan je ba, wanda ya daukeni aikin ma ya daga min kafan aiki yau….” Ya juya xai koma cikin parlon yace “Shi saurayin naki ya kai ki ki amso sakon….” Kasa cewa komai Nihad tayi ta bi sa da kallo, ta fi minti daya tsaye a wajen kafin ta juya ta koma gun Aliyu rai a bace…. Murmushi Aliyu yayi bayan ta sanar masa yanda suka yi da Drivern yace “Ohk, there is next time, xan kuma sauke masa girman kan da ke yaudaransa” Nihad tace “Toh wai dama talaka na irin wannan girman kan? Wllh sai ka xata fa gidan Ubansa ne nan din yanda yake abubuwansa” Aliyu dai bai ce komai ba, but all his thought is with the driver, he seriously want them to meet. Sai kusan karfe biyar Aliyu ya bar gidan tare da Mujahid bayan sun shiga sun ma Mumy da Umma sallama, Dollar dari biyu ya ba Nihad, yana tafiya dakin Umma ta fara shiga ta nuna mata kudin, Umma ta ja tsaki tace “Meye haka, ko dubu dari da hamsin bai kai ba, amma ya bani kunya duk wannan girke girken da ya kwasa?” Nihad tace “Umma fa a ko da yaushe cikin yi min kyauta yake, wannan ma cewa yayi inje saloon inyi gyaran gashi da shi fa” Umma tace “Toh Allah na tuba ina laifin ya baki dubu dari biyu da hamsin ma, duk kudin ubansa sannan kuma shi ma yace min yana business nasan baxai wuce exportation and Importation yake ba” Nihad bata kuma cewa komai ba, ta bude karamin jakarta dake hannunta ta saka kudin. Bayan magrib Khalil da Aminu na xaune kofar gida Aminu sai basa labarin samarin Nihad yake da irin shigar da suka yi, Khalil dai yana ta sauraronsa amma ba kallonsa yake ba, Aminu yace “Ina gaya maka wllh turarensu har bakin titi, kai kaga wani rantsattsen takalman da suka saka kuwa, kana ganin yanda suke tafiya kasan ‘ya yan wasu shegu ne a kasar nan, wato barayin kasar nan” sai a nan Khalil ya daga kai da sauri yana kallonsa, Aminu ya kwashe da dariya yace “Allah kuwa, barayin gwamnati kenan” Motar da ke tahowa yasa Aminu yayi shiru suna kallon motar gaba daya don ta hasko su, Khalil ya mike kamar xai shiga gate, sai kuma aka yi kasa da fitilar motar….

Mu hadu after EID in sha Allah, sannan duk ku bi gidan yan uwa da abokan arziki aje yawon sallah a samo kudin littafin Nihad, don kuwa bayan EID sae dai in baku last free page inyi mursisi in koma gefe inyi shiru abu na, idan kuma an tattala kudin yawon sallah an xo an biya littafin Nihad ba wani xancen yin shiru daurawa kawai xa mu yi abun mu, idan Allah ya ta6a xuciyata ma har page biyu sae mu dinga yi…… 😁😜 Amma fa sai na ga kudi kaca kaca🙄

Allah Allah nake in gano wanda Abba ya aura ma Nihad da ja’irar ta suma amma abun ya ci tura jama’a, to ko dai Aminu ne don shi dama yace zai iya maneji da ita idan aka hadasa da kudi😯

💖💖 *NIHAAD* 💖💖

16

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Aminu ya kalli Khalil yace “Ni wallahi ca nake saurayin nata ne ya dawo da daddaren nan kuma, kasan fa sai ya iya xuwa ya dauketa su tafi babu wanda xai sani banda ni da nake bakin gate din nan” Khalil yace “Saurayin wa?” Aminu bai kai ga basa amsa ba aka bude Driver seat, Hamid ne ya sauko tare da abokinsa Mujahid, a tare suka nufo gate din, tuni Aminu ya dinga jera ma Hamid gaisuwa uwa maroki, Hamid ya amsa yana kallon Khalil, sai kuma ya mika masa hannu, Khalil ya kai nasa hannun suka gaisa, Mujahid dai sai kallon Khalil yake, kauda kai khalil yayi ya fara tafiya xuwa gun mai gadin daya gidan dake kusa da su, Bayan sun shiga gate Mujahid na kallon Hamid yace “Waye wannan gayen?” Hamid yace “I don’t know, ni ma yau na fara ganinsa, probably gidansu na nan layin” Mujahid yace “No, he looks a bit familiar, amma gaba daya na mance inda na san shi…” Hamid yace “Wait” Juyawa yayi ya koma bakin gate, Mujahid ya bi bayansa, Hamid na kallon Aminu yace “Aminu” Da sauri Aminu ya nufi gate din yace “Na’am ranka shi dade” Hamid yace “Wanene mutumin nan da ku ke tsaye da shi?” Aminu yace “Au.. ai sabon dreba ne, kasan Habibu ya bar gidan nan, Alhaji ya bude masa tafkeken shago ya koma can, shine ya kawo wannan, ai ya kwana biyu da fara aikin ma” Hamid dai sai kallon Aminu yake, Mujahid yace “Driver????” Aminu yace “Ehh dreban gidan ne” Mujahid ya kalli Hamid, Hamid ya juya ya koma cikin gidan, Mujahid ya bi bayansa yace “Seriously kamar na san shi a UK” Hamid yayi dariya yace “Kai dai kasan me kama da shi a UK” Mujahid yace “Toh amma kaman is very obvious, kawai dai i can’t recall…” Parlon gidan suka shiga, Nihad na kwance parlor tana danna wayarta, tana ganinsu ta mike tayi wucewarta sama, Hamid ya bi ta da wani irin kallo, Mujahid ya saki baki shi ma yana kallonta, can yace “Yarinyar nan fa na feeling kanta da yawa” Hamid yace “A very spoilt Brat, right from when she is little bata da manners dama, unlike her half-sister Nihal…” Hamid ya xauna ya dau wayarsa ya hau kiran Farooq don dama wajensa suka zo. Washegari Monday Nihad ta gama shiryawa misalin karfe tara da rabi ta fito parlor, gaida Farooq da ya bi ta da kallo tayi, yace “Amma ba da wannan ɗan iskan mayafin xa ki fita ba Nihad?” Ta juyo tana kallonsa ta marairaice tace “Yanxu yaya me ya samu wannan mayafin? Dubi fa ya sauka har bayana fa” Yace “Wuce ki canxa” Muryar Umma suka ji tace “Ta canxa a saboda kai ke siya mata mayafan? Ko kuma sabida a jikinka ta yafa?” Ya juya ya kalli Umma, Umma tace “Sharesa kije kiyi breakfast din ki, ki kama gabanki” Dinning area ta nufa, Umma ta shigo parlon ta zauna, Farooq bai sake cewa komai ba, Nihad ta gama shan shayin da ta hada sannan ta mike, ta gefen ido farooq ke hararanta taki yarda ta kallesa ta nufi bangaren Mumy, a handle din kofar parlonta ta rataye mayafin sannan ta shiga parlon, zaunawa tayi saman kujera tana kallon Mumy tace “Ina kwana Mumy” Mumy tace “Wato sai kin gama duk abinda kike sannan xaki shigo ki gaisheni ko Nihad? Nihal bata ta6a kai wa karfe bakwai bata shigo nan ta gaisheni ba, amma ke sai sanda kika ga dama” Nihad tace “Toh Mumy ai saboda Nihal a nan bangaren take kwana shi yasa, ni kuma ai ba nan nake ba” Mumy tace “Toh yayi kyau ki ci gaba, nan gaba ma ki daina shigowa gaisheni kawai xai fi maki alkhairi” Nihad tayi shiru sai kuma tace “Kiyi hakuri” Mumy na kallon kayan jikinta tace “Wannan ɗan iskan dinkin kika yi da tsadadden atamfar nan kenan?” Nihad tace “Mumy gown ne fa” Sai kuma ta mike tace “Mumy na makara, yau muna da test” Mumy tace “Ki tabbatar Hijab xa ki sa Nihad” Tace “Toh, sai na dawo” Daga haka ta fita daga parlon, zare mayafinta tayi ta bar wajen da sauri sai da ta tafi dakinta ta dau jakarta sannan ta dawo parlor, lekan parlon ta dinga yi ta ga har lokacin Farooq na xaune, Umma ma na parlon, tana kallon Umma tace “Umma sai na dawo” Umma na Murmushi tace “Toh Allah ya tsare daughter” Ta saci kallon farooq tace “Yaya sai na dawo” Banza yayi da ita, bata ko kallesa ba ta fita, tana isa gate ko kallon Mai gadi da Khalil dake wajen bata yi ba tayi ficewarta daga gate din tana tafiya cike da isa, ta riga ta dau vow daga yanxu, da dai Khalil ya sake jan ta a mota gwara taje ta hau adaidaita, tayi canceling ta hau mota yayi driving dinta. Mai gadi na mata Allah ya tsare ko kallonsa bata yi ba balle ta amsa masa, kamar yanda bata kalli Khalil ba shi ma haka ba kalli inda ta bi ba, Mai gadi yace “Ikon Allah, yau kuma da kafa xa a makarantar” Khalil yayi murmushi kawai bai ce komai ba. Nihad na isa makaranta har wajen karfe sha daya basu da niyyar shiga lectures da su Husnah suna xauna Cafeteria suna ta hira abunsu, kaf Clique din sun canxa xuwa latest iphone da ya fito ko wata daya ba ayi ba amma banda Nihad, kuma kaf dinsu babu warce iyayenta suka siya ma, sun dai yi kame kamensu sun samu waya, Naf tace “Amma nayi mamaki kice ke baki da just 250k da xaki cika ki canxa waya, to shi wannan saurayin naki Aliyu meye amfaninsa?” Nihad tace “Aa ni dai baxan tambayesa ba, kuma dama ni bana tambayarsa komai” Sai kuma ta dau wayarta tayi dialing number Abba ta saka handsfree tayi masu alama su yi shiru, yana fara ring Abba ya daga yace “Hello dear” Shessheka ta fara yi tace “Abbaa” Daga daya bangaren Abba yace “What happened?? Me ya sameki?” A hankali tace “Abba ina shigowa makaranta xan sauka daga mota wayata ta fadi screen din ya fashe gaba daya” Abba yace “Subhanallah” Nihad tace “Yanxu ga shi wayar ya dauke” Abba yace “Hasbunallah, baya yi yanxu wayar kenan?” Tace “Ehh baya yi” Abba yace “Toh abinda xai faru idan kin koma gida ki ba wannan driver din ya je inda ake gyaran waya a gyara ko nawa ne ma sai ya kirani ya sanar min” A hankali Nihad tace “Toh” Abba yace “Shikenan, Allah ya tsare gaba” Nihad tace “Ameen, Nagode Abba, sai anjima” Daga haka ta katse wayar tana kallonsu Naf dake sauraron Abba gaba dayansu, suka kyalkyale da dariya suka ce “Gaskiya ne er daddy” Nihad tace “Toh amma me yasa xai hadani da wannan fitsararren yaron, this plan isn’t going to work idan da shi fa” Husnah ta cije yatsa tace “Kashh, yau ga ranan Habibu, to wai shi wannan din dama har yanxu ba a koresa bane?” Nihad ta tabe baki tace “Toh mayen xai tafi ne? Wallahi duk abubuwan da nake masa ya ki tafiya sai ma gyara xama da yake yi a gidan yanda ku ka san gidan ubansa, yau ma fa wani gaye ne ya kawo ni schl don nace baxan sake shiga mota daya da drivern nan ba, ina tsaye busstop din anguwanmu sai ga benz din gayen, shine ya rage min hanya har cikin makarantar nan, amma da da adaidaita Sahu xa ku gan ni ae” Zully tace “Aa to baki yi masa yanda xai bar gidan bane, da nice tuni xan masa check out wllh, wannan ai karamin kwari ne” Nihad tace “Kai Zully wasu fa mayu ne, shi wannan a maitan ma yayi nisa, gaba daya na lura bai son barin gidan ne, tunda yana cin me kyau ya sha me kyau” Husnah tace “Kawai shiryawa xa mu yi mu je har gidan mu ci maki ubansa mu masa tijara” Nihad ta kyalkyale da dariya tace “Yauwa don Allah ku shirya ku zo dama 24/7 yana xaune bakin gate da mai gadi, amma fa you girls should dress decently kun san halin Mumy” Husnah tace “Wannan ba matsala bane duk xa mu sa Hijab a jaka, xuwa Thursday xa mu zo don ranan ne muke da time, gobe akwai club da xa mu je, Wednesday kuma xa mu je wani picnic, yauwa ki shirya mu je na ranan Wednesday din nan ba da daddare bane da yamma za ayi” Nihad tace “Ohk drop location” Throughout ranan babu wanda ya je kusa da dept balle ya shiga lectures, daga karshe ma fita suka yi xuwa wani babban eatry saurayin Zully xae siya masu abinci. Da yamma bayan la’asar Khalil na tsaye bakin gate yana sauraron Aminu dake basa labarin wani abokinsa da suka taso tare, lkci daya yayi mahaukacin kudi ya guji kowa daga karshe aka gano ashe kidnapping yake, Aminu dake ta kumfar baki yace “Har yau xancen da nake maka Inusa na dogon gida, yau kuma shekara uku kenan….” Bude gate aka yi duk suka juya, Inna ce ta shigo gidan da sallama tana rike da jakarta me kyau, Aminu ya mike da sauri yana washe hakora yace “Barka da zuwa Hajjaju” Inna ta ɗan kalli Khalil ta tsaya daga bakin gate din tace “Yauwa Aminu, yan gidan basa nan ne, naji ko ina shiru?” Khalil ya karasa ya gaisheta da ladabi ta kallesa tace “Auu, ni ai ban ganka ba Aminu kadai na hango, sannu ya kake” Khalil yace “Lafiya lau, Ya gida Hajiya?” Tace “Toh Alhamdulillah, yanxu Hamid ya ajiye ni a mota ko gama sauka ban yi ba ya juya yayi wucewarsa, gashi a can bakin titi in gaya maka naga wani apple me kyau ana siyarwa amma ya ki tsayawa in taya balle in siya, mun baro wajen can farkon shigowa anguwar nan wallahi” Khalil yace “Toh bari a dubo maki” Inna tace “Yauwa maza kaje kaji nawa nawa ne ka dawo ka gaya min” Fita gate din yayi, Inna ta bi sa da kallo, sai kuma tayi kasa da murya tace “Wai dama har yanzu basamuden nan na gidan nan Aminu?” Aminu na danne dariyarsa yace “Yana nan Hajiya” Inna tace “Toh saboda me? Shi Ibrahim din ne ya bar sa ya ci gaba da zama a gidan ko ko? Yau naga fitina” Aminu yace “Ae ba shi da matsala fa Hajiya, kowa a gidan ya shaida, kullum nan muke yini tare da shi” Inna tace “Aa rufe min baki Aminu, wllh in nice a gidan nan da ido daya zan dinga bacci” Tayi kasa da murya tace “Irinsu ne fa ke aikata mugayen abubuwa a duniya yanxu Aminu, ko kai baka ga siffarsa ba, wannan idan cacan baki ya hadaka da shi sai dai ya daga ka ya nana shege da kasa, to bai cuceka ba? Da nayi niyyar kwana amma gaskiya baxan iya ba da wannan mutumi a gidan nan, ina dalili” Dariya kawai Aminu yake, Inna tace “Bari in shiga mu gaisa da su kawai inyi fitowata in wuce” Daga haka ta wuce cikin gidan, tana zaune parlor da Mumy dake ta sauraronta Khalil yayi sallama bakin kofar, Inna tayi kasa da murya tace “Kaddai shi ne? Har nan ku ke bari ya xo maku??” Mikewa Mumy tayi ta nufi kofa, Khalil ya gaisheta da ladabi ta amsa tana tambayarsa ya aiki, yace “Alhamdulillah” ledan hannunsa ya mika mata yace “Sakon Hajiya ne” Mumy ta amsa ta juya ta koma cikin parlon, inna ta hangame baki ganin leda shake da manyan apples tace “Meye wanan din? a ina naga kudin biyan wannan apple cike a leda, amma dai wawa ne wannan yaron, maza ciro kwara biyu ga dari biyu ki basa, sauran kuma ya mayar yace ance baxa a siya ba” Mumy na kallon Inna tace “Wai da na nawa kika ce ya siyo inna?” Inna tace “Aa ni ban aikesa ya siyo ba, kawai cewa nayi yaje ya tambayo nawa nawa ne, ni ban aikesa ya kwaso min ba wallahi” Mumy tace “Atoh ina amfanin mayar da abinda aka riga aka karbo Inna” ko rufe baki Inna bata jira Mumy tayi ba ta mike ta fixge ledan tace “Ai ba sata nake yi ba da xan siye duk apple din nan, kuma ‘ya yana ba kudin banxa suke samu ba” Tana gama fadin haka ta fita waje da sauri, can bakin gate ta hango khalil a zaune tace “Yau naga gantalallen mutumi, wa ya bamu kudin siyan wannan uban apple din, ko don ya ga makeken gida ya zata sata ake yi” Tana isa kusa da su tayi kasa da murya tace “Ɗan nan cewa nayi ka tambayo nawa nawa ne, bar ganina haka, wllh rufin asirin Allah kawai nake takama da shi, bani da komai, maza ka maida masu kace biyu aka aiko ka kaji” Khalil yace “Aa Hajiya na siya maki ne kawai ki ci” Inna tace “Ka siya min? Ko dai lemo ka kwaso min?” Tana fadin haka ta kara bude ledan da sauri tana lekan ciki, ai ko taga apple ne ya fi goma, Inna ta gwalo ido tace “Albashin naka ka kwashe ka siyo min apple din?” Khalil yayi murmushi kawai, Inna ta rike ha6a tace “Kaii amma wallahi nagode, Allah yayi maka albarka, ko jikokina babu wanda ya ta6a min haka cikinsu, dari uku uku fa ake siyar da duk guda daya” Shi dai khalil murmushi kawai yake, Tace “Amshi ledan mu shiga Maryam ta maka godiya” Da sauri yace “Aa Hajiya” Inna tace “Amsa kawai mu tafi nace” Amsan ledan yayi tana gaba ya bi bayanta har main parlor, tana ganin ya tsaya bakin kofa tace “Aa shigo kanka tsaye” Still yaki shiga, Inna tace “Wai ba ni nace ka shigo ba, ni fa na haifi me gidan” Mumy dake kallonsu tace “Ka karaso” Shiga parlon yayi da sallama, Inna ta kulle kofa tana nuna ma Mumy ledan tace “Wllh Maryam ashe siya min yayi da albashin sa, kin dai ga bare ne fa amma yasan kyautata ma tsohuwa” Mumy tace “Toh Allah ya saka da Alkhairi, maa sha Allah” Inna tace “Allah sai naji ya fiye min Hamid da su Farooq sau dubu” Mumy dai bata ce komai ba, Inna ta rike ha6a tace “Allah yayi maka albarka ka ji” Yace “Ameen Nagode” Bude kofar parlon aka yi Nihad ta shigo, still tayi bakin kofar tana kallon Khalil da mamaki, sai kuma ta kalli Inna da Mumy tace “Me wannan kuma yake yi har cikin parlor?” Mumy tace “Uwarki yake yi” Nihad ta hade rai tace “Mumy parlon mu fa, privacy dinmu, this is uncalled for gaskiya, ko su Aminu da suka yi shekara da shekaru a gidan nan xa a bari su shigo nan balle wannan driver din…” Mikewa Mumy tayi tana ganin haka tayi hanyar stairs da sauri, Mumy bata fasa bin ta ba, Inna tayi kasa da murya tana kallon Khalil tace “Wallahi duk hakuri muke da ita, duk ta fi karfin kowa in gaya maka, shi yasa kwanaki da ta je ta kai karar ka gu na wai in sa a kore ka nace waa? Me ka min xan maka sanadin aikin ka, wllh naki biye mata shine ta kullace ni har yau, dama dai bansan mugun halinta bane shine xan biye mata amma ai kaga ban biye mata ba gashi har yanxu kana aikinka cikin rufin asiri har da siyo min apple, ni duk inda harkar rashin gaskiya take ba ni a ciki, Nihad kam bata da gaskiya wllh” Khalil dai kansa na kasa, Inna tace “In ji suna baka abinci isasshe dai?” Yana murmushi yace “Ehh ana bamu” Inna tace “Toh shkkn, can gidan Habubakar din ma ka iya dinga xuwa kullum, ai yanxu kam ka zama ɗan gida” Murmushi yayi yace “Nagode Hajiya” Tace “Yauwa je ka” Juyawa yayi ya fita daga parlon. Da daddare Nihad na kitchen tana pancake da xata ci kafin ta kwanta Sudais ya shigo kitchen din, cup din hannunsa ya ajiye a sink yana kallonta yace “Lahh Aunty Nihal ma tace mana tayi pancake ta ci yau a makaranta” Nihad na juya pancake dinta ba tare da ta kallesa ba tace “Did u spoke with her today?” Yace “Yess, Uncle driver ne ya kira mana ita, muna ta magana da ita for long” Juyawa Nihad tayi ta ajiye spatula din hannunta tace “Who is uncle driver?” Yace “Wannan da yake kai mu school” Ta bude baki, sai kuma tace “Yaushe ya kira maku ita?” Sudais yace “After magrib prayer” Sake baki Nihad tayi tana kallonsa, jin kaurin pancake dinta ta kashe gas din da sauri ta fita daga kitchen din, sama ta tafi bangaren Umma, har bedroom ta shiga ta sameta tace “Umma kinsan da wa Nihal ke waya yanxu?” Umma tace “Wa?” Nihad tace “Wai driver, yanxu su Sudais suke ce min ai ya kira masu ita, ranan da xa mu je shopping ne fa ya amshi numberta, toh a ranan da xa mu kai ta school ma ya kirata ya fi a kirga, sai ga yanxu su sudais suka xo suna gaya min ai driver ya kira masu ita” Da wani expression Umma tace “Driver? Wani drivern ni Sumayya?” Nihad tace “Driver dae da kika sani” Umma tace “Ko dai Nihal ta fara hauka ne?” Nihad ta kyabe baki ta zauna gefen gado, Umma ta dau wayarta ta hau kiran Nihal, yana fara ring Nihal ta daga, Umma tace “Nihal kiran me ku ke yi ke da drivern gidan nan?” Nihal tace “Driver kuma?” Umma tace “Ban sani ba” Nihal tace “Wallahi ba komai Umma kawai wani lkcn yana ba su Sudais ne mu yi magana da su” Umma ta kunduma mata zagi tace “Kanin uwarki ko na ubanki? Banda xubar da aji meye na wani waya da drivern gidanku? Sa’anninki na waya da mutanen arxiki ke kina waya da driver, ke wace irin yarinya ce? to wllh xan ci kaza kazanki idan baki kama kanki kin goge number tasa ba, kaji min gantalalliya dai” Nihal dai tayi shiru, Umma tace “Na dai gaya maki tun wuri ki goge number nan ko in ci maku ke da shi” Umma na kai wa nan ta katse wayar, sosai ranta ya baci, ita kam wace irin yarinya ce Allah ya bata, duk abun kaskantar da kai ta iya shi, banda haka meye ya kai ta dinga waya da driver, Nihad tace “Wllh Nihal is so annoying, how comfortable is she making call with that wretched man” Umma tace “Ki kyale mahaukaciya mana” Nihad ta mike ta tabe baki ta fita daga dakin, Zaga dakin Umma ta dinga yi. Nihad na gama pancake din ta shiga bangaren Abbanta, bayan ta gaishesa tayi shiru saboda Mumy dake zaune a parlon, Abba ya kalli Mumy, murmushi kawai tayi ta mike ta bar masu parlon, Abba na kallonta yace “Ya aka yi daughter?” A hankali tace “Abba na tambayi wata kawata gyaran screen din wai 150k ne” Abba yace “Har 150k?” Ta marairaice tace “Eh Abba” Shiru yayi, can yace “Ohk gobe zan tura maki, amma baxa ki wajen gyaran ke kadai ba, ko ku je da farooq?” Da sauri tace “Aa Abba ba kace driver ba?” Abba yace “Ohk, no problem sae ku je tare, kin gyara account din naki ne?” Tace “Aa sae next week, I’m busy with lectures throughout this week” Abba yace “Ohk xan sa kudin a account din Farooq sae ya baki” Ta hadiye abu da kyar sai kuma tace “Abba driver din bashi da account?” Abba yace “No I don’t know” Tace “Abba idan yana da shi kawai ka sa mashi tunda tare xa mu, ba sae ka tura ma ya Farooq ba” Yace “Ohk, Allah ya kai mu goben” tace “Ameen” mikewa tayi bayan ta ma Abba sae da safe ta fita tana Murmushi, tana da kusan  70k a account dinta, ga kuma dala dari biyu da Aliyu ya bata, now with additional 150k from her father, latest iphone is sure gobe. Washegari Nihad na ta kallo ta window har Khalil ya tafi ajiye su Amina a makaranta, Hijab ta saka har kasa ta sauko, gun Aminu ta nufa yace “Barka da Safiya Hajiya” Tace “Aminu ina son tambayarka ne don Allah” Aminu yace “Toh Allah ya sa na sani Hajiya” Tace “Yaron nan Driver yana da account number ne?” Aminu yace “Anyaa, gaskiya ban ta6a jin yace xai cire kudi ba” Ta ta6e baki tace “Okay” Juyawa tayi ta koma ciki, tun jiya take avoiding ya farooq wannan ne ma yasa ta ki zama a parlor, ta koma dakinta tana jin dawowar Khalil ta sauko kasa da sauri, hade rai tayi ganin Ya Farooq a parlor ta gaishesa tayi ficewarta ba tare da ta jira ya amsa ba, Direct wajen khalil ta nufa babu yabo babu fallasa tace “Ehm ya ma ake kiranka? Abbana yace ka bada account number” Khalil ya kalli Aminu kamar dai yana jiran Aminu ya bata amsa, a fusace tace “Malam ai ba Aminu xaka kalla ba, da kai nake ni xaka kalla” Ya kalleta yace “Ohk, bani da account” Ta masa wani kallo tace “I thought as much” sai kuma ta ja tsaki ta juya ta koma ciki, Aminu yayi kasa da murya yace “Alhaji fa ya tambayi account din naka kasan ko ihisani xai maka” Khalil ya girgiza kai yace “To ai bani da account din ne” Aminu yace “Kashh” Nihad ta daidaici lkcn fitan Abbanta ta fito parlor da sauri yana ganinta yace “Yauwa kin amso account din” Tace “Abba bashi da shi, kawai ka sa a na kawata Husnah ita ta ma san wajen gyaran don nata ma ya ta6a lalacewa kamar nawa, don haka ita xata raka mu” Yace “Okay, forward the account to me via Sms” Tace “Toh Abba nagode, Allah ya kara budi” Yace “Ameen” Daga haka ya fita parlon Mumy tayi masa Allah ya tsare, Umma na tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, Bayan fitan Abba Nihad ta juya da sauri xata bar wajen Mumy tace “Zo nan me xa a gyara?” Tace “Mumy laptop dina ne yake bani matsala shine xai tura min kudin gyara” Mumy tace “Toh amma lallai sai an sa kudi account din Husnah? Me yasa baxa ki je ki gyara account dinki ba, kuma nace maki bana son alakar ku da yarinyar nan kin ki ji, wai sai na fara nakada maki duka a gidan nan xaki nutsu Nihad?” Nihad ta marairaice tace “Mumy Coursemate dita ce fa, dole muna haduwa a class ko ban kulata ba ita tana kulani kuma ita kadai tasan inda ake gyara laptop din nan tunda nata ma ya ta6a lalacewa” Farooq yace “Dauko laptop din naki da ya lalace ki kawo min” Juyawa tayi ta kallesa, Umma ta karaso parlon tace “A saboda ka fara gyaran laptop??” Mumy tace “Ta dai je ta dauko masa laptop din da ya lalace” Umma tace “Toh naga ai ba shi ya bada kudin gyaran ba da xai hau tuhumarta” sum sum Nihad ta wuce sama, cikin lkci kankani ta shirya ta dau jakar laptop dinta ta fito, Umma kadae taje tayi ma sallama Umma tace “Toh Allah ya tsare daughter” Aminu ya kalli Khalil bayan ta fita yace “Kai fa yanxu huta roro, adaidaita take hawa xuwa duk inda xa ta.” Nihad bata dawo gida ranan ba sai da sabon Iphone dinta dal a kwali, babu wanda ta sanar ma ta canza waya banda Nihal da Umma, Umma na jujjuya wayar tace “Gaskiya ne er daddy, yanxu duk kawayen naki su ma irin wannan ke hannunsu kenan?” Nihad ta washe fararen hakoranta tace “Ehh wllh Umma, shi yasa nima na dage sai da na canza, ai abun kunya ce ace ni kadai ce ban canxa waya ba a cikinsu” Umma tace “Ai ko kina da gaskiya abun ki” Nihad tace “Umma kinsan me?” Umma tace “Aa sai kin fada” Nihad tace “Umma xa mu fara exams nan da kamar sati uku kuma wllh ina son in koma hostel don in dinga karatu sosai, nasan Mumy da Ya farooq xa su xuga Abba kuma baxai bari in koma ba, pls ko xaki taya ni convincing Abbana?” Umma tace “Gaskiya ya kamata ki koma hostel din don ki maida hankali kiyi karatu sosai, amma kinsan me xai faru?” Nihad tace “Aa” Umma tace “Zan ce ma Abbanku Mijin Kamila xai yi tafiya kasar waje kuma xai yi kusan wata biyu a can, tace ki je ki dinga tayata kwana idan ya so daga can sai ki dinga xuwa makaranta, ita ma Kamilan xan sa ta kira Abban naku” Nihad ta wara ido cike da farin ciki tace “Yauwa Ummana, wannan shawarar taki tayi wllh” Umma tace “Kinga kawai daga nan sai kiyi komawarki hostel har sanda xa ku gama jarabawan, babu wanda xai san baki gidan Kamila” Nihad tace “Ai kuwa Umma, don Allah gobe da safe kiyi ma Abba maganar da wuri, on Thursday ma nake son in koma ni dai” Umma tace “Toh shikenan, Allah ya kai mu goben, ai gobe Wednesday” Nihad ta fita dakin cike da farin ciki, shi yasa take son Umma, haba she will be free for a while, babu me takurata. Da safe babu wani bata lkci Umma tayi convincing Abba, yace “Toh Allah ya kai mu alhamis din” Umma tayi murmushi tace “Ameen Yallabai, sai kayi ma Maryam magana da kanka ko?” Yace “Aa kema xa ki iya yi mata ai, menene a ciki” Umma tace “Aa gwara dai kai kayi mata, kace mata Kamila ce ta roki alfarman Nihad ta koma wajenta na kwana biyu mijinta xai yi tafiya” Abba yace “Ohk, amma suna da driver ne a can da xai dinga dropping dinta school?” Umma tace “Anya, da yake kasan shi yake ajiye kamilan duk inda xata je” Abba yace “Toh duk safiya sai Ibrahim ya dinga xuwa can yana daukarta ya ajiye ta makaranta, when ever her lectures is terminating sai ta gaya masa yaje ya dauketa ya maida ta gida” Umma tace “Hakan ma yayi kam” kafin Abba ya fita aiki ya shiga bangaren Mumy, nan ya sanar mata abinda Umma tace masa, Mumy tayi shiru alamar ta ma rasa abinda xata ce, Abba yace “Sai ki gaya ma Nihad din ta fara shiri” Mumy ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace “Alhaji idan Nihad taje gidan Kamila babu me kwaba mata, kasan ta da rawan kai fa, tana nan gida ma ya aka karke balle bata gida” Abba yace “So what are u insinuating?” Mumy ta girgiza masa kai kawai, Abba yace “Kar taje ta taya er uwartata xama kenan?” Mumy tace “Ko daya ba haka nake nufi ba” Abba yace “Toh Maa sha Allah, gobe alhamis ta shirya ta koma can gidan” Daga haka ya fice daga parlon, har ran Mumy bata son xuwan Nihad gidan Kamila amma to ya xata yi? Hakan ya sa ta tunani iri iri.

Barka da sallah fams, Allah Ubangiji ya maimaita mana

💖💖 *NIHAAD*💖💖

17

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Har daki Umma ta tadda Nihad tace “Toh Abbanki ya amince sai ki fara hada kayanki” Cike da farin ciki Nihad ta mike ta rungumeta tace “Nagode sosai Umma” Umma tace “Sai dai fa Abbanki yace driver xai dinga xuwa duk safiya yana daukarki ya kai ki makarantar sannan idan kun gama lectures ya maida ki gida” Nihad ta zaro ido tace “Toh Umma ya xan yi?” Umma tace “To na dai amsa ma Abbanki, amma ke yanxu sai ki samu Drivern kice masa ba sai ya je ba, xaki dinga tafiya da motar Kamila, should Incase Abbanki xai masa magana….” Nihad tace “Toh shkkn Umma” Umma tace “Xaki makarantar yau?” Nihad tace “Ehh ina da lectures karfe sha biyu” Umma tace “Da sauran lokaci ai, sai ki fara harhada kayanki against tomorrow…” Daga haka Umma ta juya ta fita dakin, Murna a wajen Nihad ba a cewa komai, she is going to have enough freedom yanxu, wanka ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta shirya, bayan ta shirya ta fita xuwa bangaren Mumy, Mumy na gyaran bedroom dinta Nihad ta jingina da kofar dakin da damuwa tace “Mumy kin ji abinda Abba yace?” Mumy ta kalleta tace “Na me kenan?” Nihad ta marairaice tace “Mumy ni ba son zaman gidan Aunty Kamila nake ba, it’s so boring there, ni kuma ban san ya xan yi ba” Mumy tace “Then u speak for ur self Nihad, ni me kike son ince a nan?” Nihad tace “I don’t Know what to tell Abba” Mumy tace “Ki nemi abinda xaki ce masa ai baxai maki tilas sai kin ji ba” A hankali Nihad tace “Toh” Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakinta, hada kayanta ta shiga yi a akwatunan ta cike da farin ciki, bayan ta gama ta sauka downstairs tayi breakfast, sae wajen karfe sha daya da rabi ta fita gidan zuwa makaranta ranta fari sol, yau ma dai adaidaita Sahu ta tafi ta hau bata bi ta kan Khalil ba, su Husnah da Naf har sun fi ta murna da ta sanar masu xata dawo hostel ta kuma gaya masu irin plan din da Umma tayi ma Abbanta, Husnah tayi shewa tace “Kai amma Allah ya shi ma wannan Umman albarka, Allah tana sonki sosai, ta san kan komai…” Nihad tace “Ke dai bari, ba don ita ba i will keep on being miserable in that house ga Yaya Farooq ga Mumy, the house is already a living hell for me, yanxu gobe xan taho da kayana hostel, har na gama hadawa kafin in fito” Husnah tace “Kuma albishirin ki, kin san saurayina ya kama mana tsadadden hostel a off K, xuwa next week xa mu koma wllh…” Nihad tace “Haba dai” Husnah tace “Wallahi, dama ina ta son xan gaya maki sai in manta, yanxu kinga Da ni, ke, Naf, Zully, da Ummi xa mu xauna dakin, ita Ummi part time xata dinga xama kinsan tafi zama wajen saurayinta sai in baya gari ne take xuwa hostel” Nihad tace “But bamu yi yawa ba Husnah? Kinsan fa bana wani son takura a rayuwata” Naf dake danna wayarta tace “Kin ji ki, 2 bedroom ne fa sannan har da parlor with two toilet, ai baki kai ni rashin son takura ba” Nihad tace “Ohk that’s enough….” Kamar shekaranjiya da jiya yau ma dai haka suka shiririce a Cafeteria babu wanda ya shiga lectures cikinsu, daga karshe ma suka fita xuwa cin pizza a cikin gari, suna wajen cin pizza Nihad tace “Lah gashi har xan dawo hostel ba ku je gidan mu kun ga wawan yaron can ba” Husnah tace “Ai ko yau ya kamata kawai mu je” Nihad tace “Toh ae ke wannan gashin dake kanki ne matsalar kuma ya Farooq na gari wallahi” Husnah tace “A jakarki ba kina yawo da Hijab din sallah ba” Nihad tace “Eh” Husnah tace “To ara min kawai in sa don baxan iya wani komawa hostel ba” Nihad tace “Ohk” Zully tace “Kawai ku tashi mu tafi yanxu tunda biyu ya wuce” Naf tace “Amma yana gidan idan mun je yanxu?” Nihad tace “Nace maku 24/7 babu inda yake xuwa, da ma talla ya kasa a bakin gate din da ya dinga ciniki” duk suka kwashe da dariya, tashi suka yi gaba daya suka nufi motar Naf Husnah ta shige gaba, Nihad da Zully suka zauna baya, gaba dayansu tsadadden abaya suka saka, Nihad ce kadai ta sa atamfa da gyale. Karfe uku da yan mintuna Naf tayi parking dai dai gate din gidansu Nihad tace “Ashe dai xan iya gane gidan” Husnah tace “Ka ji ta bayan na gama baki direction kenan” Nihad ta sauka daga motar praying and hoping that khalil na bakin gate, sauran yan matan ma duk suka sauka daga motar, ta shiga gaba suna biye da ita har suka shiga gate din gidan, Aminu ya mike yana masu barka da xuwa, Nihad na kallonsa daga sama har kasa tace “Ina Drivern?” Aminu yace “Ai ko minti biyar bai yi da barin nan ba, yaje can ciki ya watsa ruwa yace min” Nihad tace shit a xuciyarta, why today of all days xai bar bakin gate din, kallon su Husnah tayi sai kuma da turanci tace masu su shiga ciki kawai kafin su fito xai dawo bakin gate din, a haka duk suka bi ta har xuwa main parlor din gidan, Aminu ya bi su da kallo, direct parlon Umma ta tafi da su, Umma ta fito daga dakinta jin sallama tana kallonsu tace “Sannunku da xuwa” Duk suka gaisheta suka xauna saman kujera, Nihad tace “Umma frnds dina ne da nake yawan baki labarinsu, Zully da Naf, Husnah kuma tana xuwa gidan nan ai kin ganeta ko?” Umma tace “Kwarai kuwa na gane Husnah, sauran ne dai sai yau na san su, Allah sarki, sannunku da zuwa yan mata, ya karatu?” Duk suka amsa da Alhamdulillah, Umma tace “Madallah, kun kwaso rana kuwa” Daga haka tace “Ina zuwa” fita tayi daga parlon, Naf tayi kasa da murya tana kallon Nihad tace “Is she ur step mom that u are talking about” Nihad tace “Yeah she is” Naf tace “Waow she is really nyc wllh, very nyc woman” Nihad tayi Murmushi tace “Sure she is” Ba a dau lkci ba sai ga Hafsah da tray din lemo da ruwa ta ajiye masu bayan ta gaishe su ta fita, sai gata ta dawo da warmer din abinci da plates da spoon, ta ajiye ta fita, duk suka sauko suka yi serving kansu, Nihad ma ta dau plate ta debi abincin. Aminu na ganin shigarsu Nihad gida dama ya tafi da sauri ya kai ma Khalil tsegumin Nihad ta xo da kawayenta su biyar suna ta tambayarsa da harshen turanci, ko minti daya bai kara a chalet din ba ya koma bakin gate da sauri ya zauna, sai bayan la’asar su Naf suka shirya xa su bar gidan bayan sun ci sun yi nak, har da coslow Umma ta hada masu, Umma tace “Toh kin kai su sun gaida Maryam kuwa Nihad?” Nihad tace “Tana nan ko?” Umma tace “Aa tana ciki, su je su gaisheta” Ta fita da kawayen nata xuwa ɓangaren Mumy, duk basu xauna ba suka gaida Mumy da bata wani sake masu fuska ba, kai kana ganinsu kaga yara marasu tarbiya marasu kamun kai, Nails Naf tayi fixing a farcenta, Zully kuwa kana iya hango tatoo dake bayan wuyanta duk da mayafin abaya dake jikinta, Husnah kuma boobs dinta da bayanta ba a cewa komai kuma farko da Mumy ta santa lkcn farawansu makaranta ba haka take ba, yar siririya ce ita ma, amma lkci daya ta dawo uwar mata, Duk gaba daya sun tsargu da kallon da Mumy ke masu, Nihad tace “Za su wuce ne Mumy shine suka shigo su gaisheki” Mumy tace “Toh maa sha Allah, Allah yayi albarka” suka amsa da Ameen suka fita daga parlon, Mumy ta kira Nihad ta dawo, Mumy na kallonta tace “Kar ki kuskura ki wuce bakin gate din gidan nan” A hankali Nihad tace “Toh” Daga haka ta juya ta fita tana turo baki. Downstairs ta tarda su, Zully tace “Ur mother is too serious oo” Nihad ta kyabe baki ta fita suka bi bayanta, Naf tace “The real African Mothers they are talking about” Duk suka kwashe da dariya, tsaye Nihad tayi balcony ganin har sannan Khalil bai fito ba banda Aminu kawai da take hangowa a bakin gate, Naf tace “Toh ina ɗan iskan drivern ne?” Nihad tayi shiru, sai kuma tace “Ina xuwa, ku jira ni” Gun Aminu ta tafi tana kallonsa tace “Kai Aminu har yanxu bai fito bane, zai ɗan rage ma kawayena biyu hanya ne” Aminu yace “Ni ma kin ga shi nake ta jira a nan Hajiya” Juyawa tayi ta koma balcony tace “Idan na tafi chalet da few minutes ku biyo ni can din” Tana fadin haka ta dau hanyar chalet din, bata ga takalmin kowa a bakin kofa ba, dama isiya da Saminu gantalallu ne wani lkcn idan suka gama duk abinda suke da safe sai su fita, su da dawowa kuma sai biyar xuwa shidda, a hankali ta bude kofar parlon duk da haka sai da yayi kara, ta shiga da takalminta tana yamutse fuska tana bin ko ina da kallo, ba laifi yau parlon bai yi kaca kaca ba, kuma babu wari, cikin sanda ta nufi corridor din dakuna, ta kai hannu handle din kofar dakin da Khalil yake ta murda a hankali ta tura kofar dakin, mikewa zaune yayi da sauri daga kwancen da yake saman gado, lkci daya ya hade rai kamar yanda ita ma ta hade rai, Tana masa wani kallo tace “Samun waje, kana bakin aikin ne xaka shanya baki da yamman nan kana bacci?” Khalil ya dau pillow ya daura kan wayarsa dake gefensa sannan ya saukar da kafarsa daga saman gadon, kallon fararen ƙafafuwan nasa take wa enda kamar bai ta6a taka kasa ba har ya mike tsaye calmly yace “Don ina aiki gidanku ba shi ne ya baki daman ki fado min daki kanki tsaye kamar ba musulma ba Hajiya” Wani dariyar rainin hankali tayi tace “Toh ai naga ba da dakin ka zo gidan ba, ko da shi ka zo?? kuma ashe kasan aiki kake gidanmu amma kake min rashin kunya iri iri saboda kai fitsararre ne, banda rainin hankali ma yanxu lokacin shigowa daki a kwanta ne? Shi kansa mai gidan naga yana wajen aiki yanxu haka, to idan ka ga dama ka fito Mumy tana kiranka, sako ne dama aka bani in isar maka kuma na isar, idan kuma baka ga dama ba sai ka shanya bakin ka ci gaba da baccin…” Jin motsi a parlor ta juya ta ga su Husnah bakin kofar duk sun shigo, alama tayi masu da su karaso, Khalil dake ta lura da ita ya karasa bakin kofar dakin bata ankara ba kawai gani tayi yayi banging kofar dakin almost on her face sannan ya sa makulli ya kulle, buda baki tayi da shock tana kallon kofar su Husnah suka karaso da sauri, tana zaro ido tace “Kun ga abinda yayi min yanxun nan” Naf ta kwankwasa kofar da karfi tace “Ashe dai kai karamin ɗan iska ne mahaukaci tunda har ka kulle kofar, da ka jira mu karaso kaga ikon Allah mana, wallahi da sai mun ji uban da ya tsaya maka yau kafin mu bar nan, kuma wallahi kaji kunya tunda har mata suka tsorata ka ka kulle kofa da sauri” Nan duk suka hau gaggayan bakaken maganganu marasu dadi a bakin kofar dakin, ita dai Nihad mamakin abinda yayi mata ya sa ta kasa cewa komai sai kallon kofar take, suka kare masa zagi na cin mutunci tass sannan Husnah na huci tace “Mu je, ai akwai wani lokacin, ni ban san shegen matsoraci bane ba ma ai….” Duk Khalil na jin su, and he was calming himself and controlling his mood at the same time, duk da it’s too much and too heavy for him, lokaci daya launin idonsa ya canza, daga karshe ya daina juyo muryarsu gaba daya, Mikewa yayi walking slowly ya tafi bakin window ya tsaya yana kallon waje ko kiftawa baya yi, tunda ya xo gidan sai ranan ya ji da gaske he truly hate the sight of Nihad, at first he was trying his best not to hate her sbda bai iya tsanar mutum, shi yasa yake kokarin ganin bai tsane mutum ba no matter what, but he now realized he hate everything about her, da ya san xai zo gidan nan har ya hadu da ita da ya hakura da zuwan nasa no matter what and he is going to loose nothing, juyawa yayi ya tafi jakarsa ya bincika har kasa ya fiddo wani abu me kamar diary da pen dinsa, ya bude plane page yayi rubutu da bai wuce layi uku ba ya ajiye pen din yana kallon takardan, rufewa yayi ya mayar karkashin jakar ya kulle sannan ya mike ya koma gun window din ya tsaya, he is so hurt, it’s been long he felt this way, but they can’t just come and insult him then go scot free, wayarsa dake vibrate saman gado ya karasa kamar bai son tafiyar ya daga pillown ya dau wayar, Nihal ce ke kiransa, ya ajiye wayar ya zauna gefen gado har ya katse, sake kira tayi hakan yasa ya dauka ya daga ya kai kunne cikin low voice yace “Barka da yamma Hajiya” Nihal ta gaishesa tace “Friend dita fatima tace min ka amsar min sakon nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi” Gently yace “Ameen, ya karatu?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Allah ya bada sa’a” Tace “Ameen nagode” Yace “Ki turo number Tailor din naki” Tace “Toh xan tura maka, nagode” Yace “Yauwa sai anjima” Daga haka ya katse wayar ya ajiye gefensa. Da daddare Nihad ta shiga bangaren Umma da sleeping dress dinta, zama tayi a bedroom dinta har ta fito daga bandaki tace “Ya aka yi Nihad?” Nihad tace “Umma dama wancan drivern xaki taya ni yi ma magana gobe da safe xai kai ni can gidan Aunty Kamila da kayana idan ya so daga can sai Naf ta zo da mota ta kwasar min kayan mu tafi hostel” Umma tace “Toh ke me yasa baxa kiyi masa maganar ba, tsoronsa kike ko me?” Nihad ta wani zaro ido tace “Cabdi, inji tsoron wa? Ko Abbana bana tsoronsa sai wani mere Drivern gidanmu, kawai bana son ko wani magana ya sake hadani da shi har abada a gidan nan, don naga ba shi da manner sannan ya gama rainani, tunda Mumy ta mareni a gabansa shkkn ya daina respecting dina yana ganin dai dai muke, duk Mumy ce ta janyo min komai, to wannan yasa na yi vow har motar ma baxan dinga shiga tare da shi ba, wannan ma kawai dole ne ya sa don babu yanda xa ayi kayana ya dau adaidaita sahu” Umma tace “Balle ma shiga adaidaita Sahu ba girmanki bane, ita kuma Maryam in taga disgaki gaban ma’aikatan gidan shine dai dai sai ta ci gaba, shi yasa a rayuwa kar ki kuskura ki raga ma talaka ina maki wannan hudubar, don da ya ga fuska shikenan raini sai wanda ya manta, barin yan kauyen nan shi yasa ko kallon arziki kar ki yarda ya hadaku ma” Nihad tace “Ai ni dama bana masu kallon arxiki Umma” Umma tace “Ya dai fi miki, ajin ki daban da nasu, shkkn ki je ki kwanta goben xan masa magana idan Allah ya kai mu” Nihad tace “Nagode Umma” Zata fita dakin Umma tace “Kuna dai waya da Aliyun ko?” Nihad ta juyo tace “Ehh muna yi, yanxu ma da shi muka gama magana na fito” Umma tace “To madallah, yaushe xai kara zuwa?” Nihad tace “Umma kinsan akwai wani business din Abbansu a can kasar waje shi ne manager so he is not always in Nigeria, though sauran business din Abban nasu na nan kasar ma duk shi ke running dinsu, haka ne ma yasa bayan watanni kadan yake shigowa Nigeria, amma yace min in a month time xai shigo in sha Allah” Umma tayi shiru, Nihad tace “His father owns a big company shi da wani White Man, so Aliyu is managing it for him in there” Umma ta ɗan yi murmushi tace “Ba shakka, Allah ya sanya Alkhairi, kice koman baban nasa a hannunsa yake” Nihad tace “Ehh, he is his dad favorite also” Umma tayi murmushi tace “Kamar ke kenan ko” dariya kawai Nihad tayi ta nufi kofa Umma ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin sai kuma ta sauke ajiyar xuciya. Washegari Umma ta samu Khalil bayan ya dawo daga kai su Amina makaranta, da ladabi ya gaisheta fuskarta kamar bata ta6a dariya ba tace “Kai nan da karfe tara xaka kai Nihad gidan yayarta” Khalil da kansa ke kasa yace “Toh Hajiya” Juyawa tayi ta bar sa wajen a tsaye, ya daga kai ya bi ta da kallo. Kamar yanda Umma tace karfe tara saura Nihad ta fara fitowa daga akwatunan ta nan balcony ta ajiyesu ta tafi bakin gate tana kallon Khalil dake zaune, Ta ɗan tabe baki tace “Ga akwatunan da xa a sa a booth a can balcony” Ko kallon direction din da take tsaye bai yi ba, sai ma kara hade rai da yayi, tace “Malam magana fa nake maka fa” Still khalil yaki kallon inda take balle ta sa ran yace wani abu, Aminu ya mike da sauri ya tafi balcony din Nihad ta bi sa da kallo, sai kuma ta kalli khalil cike da takaici amma ta kasa ce masa komai, har Aminu ya gama kwaso kayan ya ajiye a garage, ya taho gun khalil yace “Ɗan bude booth din a xuba su” Mikewa Khalil yayi ya tafi gun motar bayan ya bude booth ta makullin ya shiga driver seat, Nihad ta bi sa da wani shegen kallo, tana mamakin irin wannan feeling din da yake, sai kuma ta ji haushin kanta da bata sa Aminu ya kwaso akwatunan ba tayi ma wannan banzan magana ya kyaleta, bayan ya tada motar ta tuna bata ma Mumy sallama ba, komawa cikin gidan tayi ta tafi bangaren Mumy, khalil ya fi minti sha biyar a kofar gida yana jiranta cikin mota, tana sane tayi xamanta cikin gida don yayi ta jiranta a mota, sai da taga ta 6ata minti ashirin sannan ta mike ta fita tana rike da handbag dinta, back seat ta zauna ta kulle motar tana kallonsa, ya ɗan kwantar da driver seat ya rufe idonsa kamar mai bacci, da har xata masa magana ta tuna sabon vow din da ta dauka na cewar ba maganar da xai sake hadata da shi, yau ne last. Har bayan minti biyar bata ga ya bude ido ba balle ya tada motar su bar wajen, ta wani hade rai tana kallonsa, wasa wasa har sai da aka yi minti goma suna nan a haka, tana ta control din kanta kar tayi masa magana, Aminu dai sai lekosu yake yana dariya kasa kasa, wato sai ya rama shanyasa da tayi cikin mota, tana ta xaune motar ta cika tayi fam amma taki cewa komai kuma bata sauka ba har sai da aka yi minti ashirin da biyar sannan ya bude ido ya gyara zamansa ya kunna motar suka bar wajen, da yake ya ta6a kai Nihal gidan yayarsu kamar yanda ta ce masa, saboda shi ma baya son wata magana ta hadasa da Nihad direct gidan ya nufa ba tare da ya damu can din ne ko ba can ba, the ride was so silent, ko wannensu fuska a tamke, lkci lkci take satan kallonsa sai kuma ta kyabe baki ko ta ja tsaki can kasa kasa, har yayi parking dai dai gate din gidan kamila ya kashe motar, Nihad ta bude ta sauka ta tafi ta kira mai gadin gidan tace “Don Allah ka zo ka sauke min kayana a mota” Ya fito daga gate din ya bude booth don khalil ya riga ya bude, nan ya ciro mata akwatunan ya kai su bakin gate, kafin ya ciro na karshen tana kallonsa tace “Don Allah ka je kace ma wancan drivern nace ba sai ya wani zo yana kai ni makaranta ba don bana bukatarsa kwata kwata” Mai gadin ya tafi yana kallon Khalil bayan sun gaisa yace “Wai Hajiya tace ba sai ka zo kai ta makaranta ba” Khalil yace “Ok” Juyawa yayi ya tafi ya cire akwatin karshe ya kulle booth din, khalil ya ja motar yayi zoom off, Nihad ta bi sa da harara tace “Uwa motar ubansa, wllh ni ce sanadin aikinka a gidan nan mu dai je zuwa, sai kayi da ka sanin sanina a rayuwarka” Shi da mai gadin kallonta yake yana kokarin kai akwatunan cikin gidan, ko karamin bata dauka ba haka ta bar masa su dukka ta wuce ciki, Kamila dake parlor tace “Mutanen Maryam Abatcha American University” Murmushi Nihad tayi tace “Aunty ina kwana?” kamila tace “Lafiya lau, amma fa ki kira warce xata xo ta dau kayan naki xuwa hostel don karfe sha biyu xan fita nima” Nihad tace “Ehh tace min karfe sha daya xata zo” Kamila tace “Toh ya dai fi, daxu ma Mumy ta kirani wai in sa maki ido nace toh” Nihad tayi dariya tace “Aunty kamila mumy sai tayi ta treating dina kamar wata er yarinya” Kamila tace “Gaskiya kam, ga ki ke ba yarinya ba, makarantar ki ma ba ta yara ba” Dariya kawai Nihad take, Kamila tace “Atoh dai” Karfe sha daya Naf da Husnah suka iso kofar gidan Kamila na tsaye compound duk suka saka akwatunan a motar Naf, Bayan sun gama tace “Toh Allah ya tsare” Nihad tace “Ameen Aunty” su Naf suka mata sallama, tana kallonsu har suka bar compound din ta juya tayi komawarta ciki, murna a cikin Nihad ba a cewa komai, a haka ta koma rayuwarta a hostel babu me sa ta babu me hanata, duk sanda Mumy ta kirata sai ta shige bandaki ta kulle su yi waya don kar ma taji hayaniyar su Naf da Husnah, night party kuwa sai wanda suka mance ne baxa su ba, duk yanda suka so rinjayar Nihad ta dinga shan kwayoyin da suke sha bata ta6a sha ko da wasa ba, sau daya Husnah ta shammace ta ta xuba mata a lemo shi ma sai da ta kwana ta yini tana baccin wahala, hakan ya sa suka rabu da ita da batun drugs, sai kuma suka fara jan ra’ayinta zuwa kwanan hotels da suke da boyfriend dinsu, nan ma dai ta ki, ko min daren da suka yi a waje ita dai sai ta dawo hostel, duk sanda suka yi waya da Umma sai ta ja mata kunne kan cewar kar fa ta dinga bin duk wani wuri da xata iya haduwa da Abbanta ko Farooq, ita kanta Nihad is so careful about that, a haka har suka fara exams, duk cikinsu Nihad ce ke maida hankalin karatu, sauran ko bude takarda, duk sanda Mumy ta bukaci Nihad ta zo gida sai tayi karyan karatun exams yayi mata yawa, bayan an gama exams din ma don kar Mumy tace Nihad ta zo gida Umma ta sa kamila ta kirata tace xa su garin mijinta, haka nan aka kare hutu Nihad na hostel abun ta suna baza life, su ne har Kaduna da hutun, sau biyu ta je gidan Kamila shi ma ɗon Aliyu ya shigo kasar ne xa su hadu sai taje gidan kamila shi ma ta ce masa mijinta ne yayi tafiya take taya ta zama……

💖💖 *NIHAAD* 💖💖

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

17Har aka kare hutun wata biyu Nihad bata nufi hanyar gidan Kamila ba balle nasu gidan, kamar yanda Mumy ke kiranta kullum haka ma Abbanta, a ko da yaushe cikin demanding kudi take daga wajensa kuma ko sau daya bai ta6a hanata ba, da tayi magana xai tura mata fiye da yanda ta tambaya, Umma ma kusan kullum sai ta kirata, duk kuma wannan abun Abba da Mumy na xaton Nihad na Kebbi tare da Kamila, Umma ce kadai ta san Nihad na kano sai kamilar, gaba daya Kamila ta daina xuwa gida a zuwan tana can kebbi, idan da wani abu sai dai Umma ta shirya ita taje gidanta, A kullum Mumy bin Nihad take da addu’a, ta rasa dalilin da hankalinta ya ki kwanciya tun barin Nihad gidan, bata da rest of mind kwata kwata, gashi babu abinda xata iya yi game da hakan, ko me xata ce ma Abba baxai ta6a fahimtar ta ba sai dai ma ya juya xancen, a ko da yaushe ta kira Nihad sai ta mata nasiha a kan ta dai kula kuma banda rawan kai da yin kawaye, sai Nihad tace “Mumy ni da ba kowa na sani ba a garin sannan babu inda muke zuwa, kawai karatu nake ta yi against next semester” A haka dai kullum take gaya ma Mumy. Ranan wata juma’ah Nihad da kawayenta duk suka shirya xa su je duba wata kawar Zully da tayi rashin lafiya, Naf ke driving din, Husnah tace “Amma fa ku kirata ko an sallameta asibiti kar mu je mu yi wahalar banza” Zully tace “Ai ko dai” wayarta ta dauka ta kira kawartata Yusra ta sa handsfree, tana dagawa Zully tace “Ya kuna asibitin har yanzu?” Yusrah tace “Wani asibiti da aka sallame mu tun jiya, ni kin gan ni a Bristol ina shan Ac, Saurayina Alhaji Muktar ne ya biya kudin kwana hudu sai gashi tafiyar gaggawa ya kamasa yau da safe kuma yace min xai kwana uku a Abuja, sai jibi kudin xai kare shine nace gwara in yi zamana a nan” Zully ta kyalkyale da dariya tace “Me ya fi ranki, to bari mu taho can din kawai” Yusrah tace “Ai ko ku zo, ga abinci ga enough drinks, sannan ga Ac 24/7” Zully tace “To sai mun iso” Tana katse wayar, Naf ta dau hanyar Bristol, Husnah tace “Mu ma muje mu sha Ac kawai” Dariya duk suka yi, Nihad tace “Amma yaushe xa mu fito, kunsan ni bana son xuwa irin wajajen nan in broad daylight” Husnah tace “Mu da xa mu shiga daki mu yi xaman mu meye na wani damuwa” Nihad bata ce komai ba ta ci gaba da danna wayarta, suna isa makeken hotel din Naf ta samu wajen parking, Dai dai nan wayar Nihad ya fara ringing, ganin Abba ne ta ɗan wara ido, Husnah ta kalleta tace “Waye?” Nihad ta nuna mata screen din wayar, Husnah tace “Ohk, bari kawai mu sauka mu tafi ciki, sai ki tsaya motar ku yi waya, idan kun gama ki fito ki kulle sannan ki kirani mu gaya maki room number” Nihad tace “Ohk” Duk suka sauka daga motar, Naf ta mika mata makulli suka wuce ciki, tuni wayar Nihad ya katse sai ga Abba ya kara kiranta, dagawa tayi hade da sallama tace “Abba ina yini?” Yace “Lafiya lau dear, how are you?” Tace “Alhamdulillah Abba ya aiki?” Abba yace “Mun gode Allah, yaushe xa ku yi resuming ne?” Nihad tace “In two weeks time Abba” Abba yace “Ohk, yaushe kamilar tace maki xa ku dawo?” Nihad tace “Ana saura 2 days mu koma school, tare da mijin xa mu dawo gaba daya” Abba yace “Ohk that’s good, take care dear” Nihad tace “Alright Abba, bye” Katse wayar Abba yayi, ta bude motar ta sauka sannan ta kulle, tana rike da jakarta bayan ta kulle motar ta nufi entrance din hotel din tana kokarin dialing number Husnah, sunanta ta ji an kira, ta juya da sauri, wani tsohon saurayin Husnah ne, ya nufota da sauri yace “Hi Nihad” Ta ɗan yi murmushi tace “How are you Kabir” Yace “Alhamdulillah, ya kwana biyu?” Tace “Cool” Yayi er dariya yace “Kina da appointment yau a nan kenan?” Ta ɗan kallesa sai kuma tace “Tare da kawayena nake, suna ciki” Yace “Ohk maa sha Allah, ya school” tace “Fine” A tare suka jera xuwa cikin reception din hotel din yana jan ta da hira, zaune yake a haraban hotel din karkashin inuwa tare da wani da baxai wuce sa’ansa ba yana sauraron duk abinda yake ce masa, da ido ya bi ta da Kabir, at first he quickly imagined ba ita bace kamace kawai, but yanayin tafiyarta da kuma jakar hannunta wanda duk ya sani ya sa shi ajiye goran ruwan dake hannunsa ya bi ta da kallo babu ko kiftawa, Buga table din abokinsa yayi da mamaki yace “Heyy!!” Da sauri ya dauke idonsa daga kallonta ya kalli abokin nasa, abokin yace “Why are u staring at her that way, burge ka tayi ko me? Kaga yarinya da saurayinta sun zo holewarsu kayi ta kallonta?” Still bai ce komai ba sai kallon abokin nasa yake babu ko kiftawa, Abokin yace “Khalil” Sauke idonsa yayi daga kallonsa sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace “Yea mamaki abun ya bani shi yasa na bi su da kallo” Dariya Sultan yayi yace “Haba kai ma ai kasan wannan ba sabon abu bane, yan matan yanxu kam ai sun xama abinda suka zama sai addu’a, basa ma jin kunyan iskanci yanxu, ko wani hotels ka bi su ne, baka lura bane ko 10 mins ba ayi ba set of 3 girls suka wuce mu a nan, su ma kuma duk gun samarin suka zo na sani” Shi dai khalil bai ce komai ba, he was really shock, yarinyar da aka ce tana Kebbi ce ya gani a Bristol, Sultan yace “Kai dai tunda kana da Nadeeyah and upon her parents wealth she is decent sai ka gode ma Allah” Murmushi kawai khalil yayi, Sultan yace “Kuma kuna magana da ita all this while?” Khalil yace “Muna yi” Sultan yace “Tasan kana kano?” Girgiza masa kai kawai khalil yayi, Sultan yace “Ya batun turawa gidansu?” Khalil yace “Yana nan” Sultan yace “Toh Allah ya nuna mana, but ya kamata kayi nazarin duk abinda nace maka Khalil, pls do so Frnd” Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace “In sha Allah, and i appreciate u Sultan” Sultan yace “Nima nagode da ka bani lokacinka har ka saurareni” Murmushi kawai khalil yayi, Sultan ya mike yace “Toh ka koma can inda ka samar ma kanka aiki kar a fara nemanka ko” Khalil yace “Ina jiran wani ne still” Sultan yace “Wa kenan?” Khalil yayi kasa da murya yace “Another caring frnd like you” Sultan ya sauke ajiyar xuciya yace “All this shall come to pass in sha Allah Khalil” khalil ya ɗan yi murmushi ya mike tsaye ya mika masa hannu sannan yace “I truly appreciate ur care Sultan, nagode kwarai” Sultan yace “Mention not abokina” Har mota Khalil ya rakasa sannan ya dawo ya zauna inda yake zaune har sannan yana cike da mamaki, har karfe shidda na yamma yana xaune wajen bai ga fitowar Nihad ba balle shi mutumin da ta shiga ciki da, kiran Aminu ne ya shigo wayarsa ya ciro ya daga ya kai kunne, Aminu yace “Toh na ji ka shiru daga cewa xaka bakin titi ka dawo” Khalil yace “Ina nan dawowa yanxu” Aminu yace “Toh ga manyan mangwaro ma Hajiya Inna ta zo ta bada a ajiye maka” Khalil yayi murmushi yace “Toh nagode, sai na dawo” daga haka ya katse wayar. Har aka yi magrib Khalil bai ga fitowar Nihad ba, babu warce ta fado masa a rai sai Mahaifiyarta, ya ji tausayinta sosai, mata me kirki da mutunta ɗan Adam, and such a nyc woman didn’t deserve Nihad as a child… Wayarsa ya dauka yayi dialing number Nihal ya kai kunne, tana dagawa tayi masa sallama, ya amsa yace “Ya kike?” Tace “Alhmdlh, ina yini?” Yace “Lafiya lau, ya lectures?” Tace “Ya shirin jarabawa dai” Yace “Ohh haka ne, ya shirin jarabawa?” Tace “Alhmdlh” yace “Tare xa ku dawo da er uwarki kenan?” Nihal tace “Noo, ai ita tana kebbi” Yace “Ko?” Tace “Eh” Yace “Ita da wa suka tafi kebbi?” Nihal tace “Wannan yayar tawa da ka kai ni gidanta kwanaki” yace “Ohk, yaushe xa su dawo?” Tace “Jiya da na tambayi Umma tace min nan da sati biyu” Khalil ya ma rasa abinda xai ce, jin shiru tace “Hello” Yace “Eh ina jin ki, to shkkn, dama tambayarki xan yi ya jarabawa” Tace “Toh Nagode” Yace “Sai anjima” Daga haka ya katse wayar, kallon cikin hotel din yayi, yana ta xaune har kusan Isha’i ganin Nihad ba fitowa xata yi ba ya mike ya tafi can inda yayi parking motar gidansu Nihad ya shiga ya bar hotel din, direct gidan Kamila ya nufa, bayan sun gaisa da mai gadin yace “Matar gidan na nan?” Mai gadin yace “Ehh tana ciki” Khalil yayi shiru, sai kuma yace “Ohk an aiko ni wajenta ne” Mai gadin yace “Toh bari ayi mata magana” Yana shiga gate khalil ya juya ya shiga motar ya bar layin. Direct gida khalil ya nufa erasing everything off his mind kamar ba ayi ba, after all it’s none of his business and will neva be any of his business. Bayan sati biyun da Umma tace ma Abba su Nihad xa su dawo kano, sai ga Nihad tare da kamila a gidan da yamma, babu irin rokon da Umma bata yi ma Kamila akan su xo gida tare da kyar dai daga karshe ta yarda suka taho gidan da Nihad, akwatin kayanta daya kawai ta dawo gida da, tun da suka shigo gate Khalil ke kallon Nihad, ita kuwa shaff ta mance da wani batunsa a gidan sai yanxu da ta gansa, tana ganinsa kuwa mood dinta ya canxa, shkkn kuma ta dawo miserable house din nan da driver din nan a ciki, noo gaskiya ita dai baxata iya ba, xata roki Umma ta yi come up with another plan da xai sa ta sake barin gidan, Kamila ce kawai ta amsa gaisuwan mai gadi da khalil da ke gaisheta, Nihad kuwa tafiya take cike da isa ta nufi entrance din parlor, tayi wani kyau ta kara haske, kana ganinta kasan bata da damuwar komai, ba komai ya haddasa mata kara haske ba sai cream me shegen tsada irin nasu Husnah da take shafawa yanxu, ga sabulu ga shower gel, Khalil ya bi ta da kallo, suna shiga parlor Aminu yayi kasa da murya yace “Kaga yanda tayi wani haske tayi kyau uwa warce ta tafi duniyanci?” Khalil bai ce komai ba, but he really felt sorry for Abba and Mumy, ya jima bai hadu da mutane masu kirki da karamci irin tasu ba, a watanninsa kusan shidda a gidan Abba ya ja sa jiki kamar nasa, ya kai ya kawo yanxu hatta Atm card Abba na basa ya ciro masa kudi wanda ko Habibu baya ba Atm card dinsa, shi ko Abba ya ya6a da hankali nutsuwa da girmamawa irin ta Khalil, ya sha gwadasa ya aikesa ya siyo masa abu sai ya linka kudin sau uku ya basa yace haka ake siyarwa amma in sha Allah sai Khalil ya kawo masa canjinsa, ya gwadasa ta fanni daban daban wanda shi khalil bai ma san yana yi ba, duk gidan babu wanda yake da matsala da warce ta zama second Nihad sai Umma, gaba daya ta dau karan tsana ta daura masa tun da Nihad ta fesa mata yana waya da Nihal, to uban me Nihal dinta xata yi da shi, duk abinda take yi kuma baya damun khalil, Usman ma dai in ya zo basa wani gaisawa, amma Farooq idan yana gari mayar da bakin gate wajen zamansa yake yi sbda Khalil, xaka yi tunanin ya ta6a saninsa, kawai he enjoys gisting with him sbda yana magana kamar wanda yayi ilimi me zurfi, gashi he knows almost everything that’s happening in the world wato he is current, suna dadewa sosai suna hira…. Sai kuma Hajiya Inna da takanas sai ta aiki dreban gidansu Hamid ya zo ya kira mata khalil xata aikesa don hankalinta yafi kwanciya ta basa dukiyarta a kan yaran gidan, kuma aiken baya wuce na dari ko dari biyu. Tun da Nihad ta shiga bangaren Mumy bayan ta fito daga bangaren Umma Mumy ke kallonta, ita dai tana xaune tana ta danna waya, Mumy tace “Wani mai kike shafawa Nihad?” Nihad ta daga kai tace “Mumy cream din Aunty Kamila ne tace in dinga shafawa” Mumy bata ce komai ba, bayan few seconds tace “Ina sauran kayanki?” Nihad tace “Mumy Aunty Kamila tace in bar su a can gidanta” Mumy tace “To tashi driver ya kai ki ki kwaso yanxu” Nihad ta marairaice tace “Mumy ni fa ba abinda nake bukata a cikin kayan” Tsawa Mumy tayi mata tace “Baxa ki tashi ba” Tashi Nihad tayi kamar xata yi kuka, sai kuma tace “Toh Ai Aunty Kamilan na nan ki bari idan ta koma gida Mumy” Mumy tace “Ba dai gobe za ku fara lectures ba?” Nihad ta gyada mata kai a hankali, Mumy tace “Toh dama ki tabbatar baki dawo gidan nan ba tare da akwatunan ki ba” Mumy na fadin haka ta wuce dakinta, Nihad ta turo baki ta mike ta fice daga parlon, ita har ta mance yaushe rabon a harareta balle a mata fada sai yau… Washegari bayan ta shirya xuwa makaranta sai da Mumy ta kara jaddada mata kwaso akwatunan ta, har da guntun hawayenta, bayan ta fito compound ta ji ranta ya kara baci da ta tuna cewar shegen mutumin nan ne har yanxu Driver din gidan, kuma ita wllh baxata wani je ta hau adaidaita Sahu ba, tana isa gate suka hada ido da shi don kallon sama har kasa yake mata, wani matsiyacin kallo tayi masa tace “Da bashi ne kake kallona haka?” Aminu dai sai gwaggwale ido yake, Ta wani ja tsaki ta ma gwammace taje ta hau adaidaitan sbda ganinsa kadai na kona mata rai, ficewarta tayi daga gate Aminu yace “Ohh fitina ta dawo ni Aminu, wllh har na manta da ita a duniyar nan” Khalil dai bai ce komai ba. Bayan kwana biyu da komowar Nihad gida tana kwance bedroom din Umma tana bata labarin yanda suka yi da Aliyu jiya da daddare, Umma dake xaune gefen gadon ita ma ta mike da sauri tace “Kice wllh” Nihad na Murmushi tace “Wallahi Umma” Wani guda Umma ta saki tace “Alhamdulillah, Allah na gode maka… Yaushe yace xa su xo?” Nihad tace “Nan da sati biyu” Umma tace “Alhamdulillah, Alhamdulillah, amma in ji baki gaya ma kowa ba?” Nihad tace “Aa ke kadai da Husnah na fada ma” Umma tace “Kin ji ki, wacece kuma Husnah, meye na gaya mata xa a kawo kudin ki? Duniyar nan da ta lalace yanxu ai kowa boye kansa yake, kar ki sake gaya ma kowa” Nihad tace “Har Mumy?” Nihad tace “Aa ba dai kin gaya min ba ai shkkn, ni xan mata magana sannan inyi ma Abbanku magana, amma sai xuwa next week” Nihad tace “Toh Umma” Wani gudar Umma ta kuma saki tace “Allah nagode maka diyata xata xama surkar Janar jikamshi” Dariya kawai Nihad tayi, Umma tace “Toh sai ki kula ki kama kanki kar ki sake kula kowa tunda dai kina da tsayayye yanxu” Nihad tace “Toh, amma Umma yana wani ce min xai rabani da su Husnah” Umma tace “Ahhh!!! shi kuma ya haka??” Nihad tace “Wallahi, kuma ni banga abinda xai sa ya rabani da su ba” Umma tace “Toh ke dai kar ki musa masa ku samu matsala, kiyi ta bin sa duk abinda yace kice to, su kuma ko a hankali ai xa a rabu, ke da kasar waje xa ku xauna? Ko ba haka ba” Nihad tace “Haka yace min” Umma tace “Toh kinga, su Husnah da ba kasar wajen xa su bi ki ba” Nihad tace “Ai shine” Umma tace “Kai amma nayi farin ciki da wannan labarin Nihad, Allah Ubangiji ya nuna na yan baya haka” Nihad tace “Ameen, Umma bari in dauko wayana” Umma tace “Toh je ki dauko” Daga haka ta fita daga dakin. Ko da wasa Nihad bata sanar ma Mumy ba, tana ta sabgar gabanta throughout the week, kuma har tambayarta Aliyun yayi ko ta gaya ma Mumy tace masa eh. Duk da warning din da Umma tayi ma Nihad na kan cewa kar ta sake gaya ma kowa Aliyu xai turo sai da ta gaya ma Farooq, kamar yanda take favourite din Abbanta haka take favourite din Farooq a gidan, a WhatsApp suke chatting ta gaya masa sai ga shi ya sauka ya kirata, tana dagawa yace “Are you serious?” Tace “Ehh ya farooq” Yace “Tohh maa sha Allah, Amma Abba bai sanar min ba” Nihad ta zaro ido tace “Yaya Umma tace xata gaya masa” Farooq yace “Ohk, toh Allah ya kai mu next week din, though xan shigo kano jibi” Tace “Toh Allah ya kai mu” Sallama yayi mata ya katse wayar, Tana komawa saman chatting taga message din Nihal tana congratulating dinta, wato har Umma ta gaya mata, murmushi Nihad tayi tace “Thanks twinny” Washegari da Nihad ta fito xata school khalil ya bi ta da kallo disgustingly as usual, sarai jiya Nihal ta gaya masa xa a kawo kudinta next week ta kuma gaya masa daga familyn da xa a kawo kudin, and he really pity the well reputable family,  da shi kansa wanda xai aureta din, ganin irin kallon da yake mata ta tsaya tana kallonsa tace “Wai kai Allah ya tsine maka ne da xaka dinga min wani irin kallo idan kaga na fito? Ko da wani abu da muka hada ne ban sani ba? Toh wllh wllh wllh duk ranan da na sake fitowa ka min kallon walakanci Allah sai na gaura maka mari, kaji har na rantse” Khalil na kallonta yace “Ki mari wa?” Cike da rashin kunya tace “In mareka nace, ko uban waye kai da kake tunanin baxan iya marinka ba? Ni fa wallahi bayan na bar gidan nan na mance an halicce wani mutum me kama da kai a duniya? Toh akan me daga dawowa ta xaka dinga bi na da kallon raini?” Khalil bai ce mata komai ba cause the sight of her is making him feel feverish, ga wani tafarfasa da zuciyarsa yake, jin bai ce mata komai ba ta ja wani tsaki tace “Banza kawai” Daga haka ta fice daga gidan, Aminu dake lekosu ta dakinsa ya fito yace “kaii, Allah ya wadaran wannan yarinya”

Ana saura kwana hudu su Aliyu xa su kawo kudi, Nihad na bacci da rana Kasancewar ranan asabar ce babu lectures wayarta ya fara vibrate, bude ido tayi don Aliyu yace xai kirata tana jawo wayar taga wata Coursemate dinta Sajida da ba wani shiri suke ba ce ke kiranta, da kamar baxata daga ba sai kuma ta daga ta kai kunne, Sajidah tace “Nihad what is this i am seeing on social media?” Nihad ta bude ido tace “Kamar me?” Sajidah tace “Hau WhatsApp” Daga haka ta katse wayar, sai ga kiran wata secondary school mate dinta Hafsah, tana ta kallon kiran sai kuma ta daga, daga daya bangaren Hafsah tace “Nihad what’s happening?” Nihad ta mike xaune tace “Ban gane ba?” Hafsah tace “Ki hau WhatsApp” Nihad na kokarin shiga WhatsApp sai ga kiran wata warce suka yi islamiyya tare, kawai haka nan taji gabanta ya fadi, ta dai daga kiran, Badiyya tace “Nihad garin yaya haka don girman Allah??” Hankali tashe Nihad tace “Wai me ke faruwa?” Badiyya tace “Ki kunna data” Nan Nihad taji jikinta ya fara rawa, wani kiran ne ya shigo taki dagawa tayi rejecting ta bude data ta hau WhatsApp din da sauri, messages ta gani rututu na shigo mata, kawai ta bude wanda hannunta ya kai, Wata school mate dinta ce ta turo mata video tana tambayar “what is this Nihad??” Hannun Nihad na rawa ta bude video din, kanta ta gani with just skimpy undies a saman gado ba kuma bacci take ba, sai kuma taga ta mike tsaye turning all over jefar da wayar tayi jikinta na rawa tana zaro ido tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” sai kuma ta saki wani kara ta sauka daga kan gadon ta durkusa kasa, ringing kawai wayarta ke yi amma ta kasa motsawa daga inda take, bude kofar dakinta aka yi ta daga kai da sauri, Umma ta shigo tana zaro ido tace “Nihad me ke faruwa a social media yanxu Nihal ta kirani tana kuka, kuma wai ta kiraki bakya dagawa” Nihad ta kasa cewa komai, bata ta6a zama soo weak all her life ba kamar wannan moment din, ji take kamar komai na jikinta ma ya daina aiki, wayar Umma ne ya fara ring ta daga da sauri, Nihal na shessheka tace “Umma ki hau WhatsApp na tura maki” Umma tace “Tohh” Da sauri Umma ta hau WhatsApp ta shiga chat dinta da Nihal ta bude video din, salati ta saki bayan ta gama kallon video din har karshe ta jefar da wayarta kan gado tace “Nihaddd????” Dai dai da second daya wayar Nihad bai samu breathing space ba, kiran su Husnah ne, Naf, Zully, infact calls upon calls kawai amma ta kasa kwakkwaran motsi inda take a durkushe balle ta daga wani waya, sai rufe ido take tana budewa kamar dai warce ke mafarki tana son ta farka, Umma na tafe hannu ta fashe da kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, na shiga uku na lalace ni Sumayya, Nihad wa ya maki haka? Garin yaya haka Nihad?” Bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo da tashin hankali kwance fuskarta, Umma ta fashe da matsanancin kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah mun gode maka ni Sumayya, me xa mu gani haka Nihad” muryan Mumy na rawa tace “Nihad??” Kawai sai ga hawaye na xuba idonta tana girgiza kai, Wannan ne yasa Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku na lalace” Kwalban turare da Mumy ta gani gaban mirror din dakin ta figa tayi kanta amma tuni Nihad ta shige bandaki ta sa makulli, Umma kuma ta rirrike Mumy tana kuka tace “Aa Maryam ki kai zuciyarki nesa kiyi ta furta innalillahi wa inna ilaihi raji’un, nima shi nake yi” A haka ta ja mumy dake kukan bakin ciki da takaici suka fita daga dakin.

 kafin dare kai ka ce mutuwa aka yi a gidan, gaba daya iyalan gidan Alhaji Abubakar sun iso gidan Abba, makusantan Mumy duk sun xo gidan, Umma ma yan uwanta da kawayenta duk suna gidan, Aminu sai bin duk wanda ya shigo yake da kallo cike da mamaki don ba ace masu kowa ya mutu a cikin gidan ba gashi khalil da yake ma gulma baya nan tun rana ya fita, kowa kuma ya shigo babu walwala yake nufar entrance din parlor, all the way from Abuja haka Farooq ya biyo flight ya dawo, Usman ma daga kaduna haka ya taho… Tun faruwan abun nan Umma ke kuka non stop, handkici hudu duk sun yi jagab a hannunta, Mumy kuwa in ka ganta sai ka tausaya mata she is so heartbroken, banda kanninta mata biyu da Yaya farooq da suka jibgi Nihad son ransu babu wanda yayi attempting ta6a ta ko ce mata komai a gidan…… Tashin hankalin Nihad bai linku ba sai da taga alamar Aliyu yayi blocking dinta ta ko ina, WhatsApp, IG, Phone call, Twitter, infact all, kawai sai take fatan Allah ya dau ranta ta huta kawai, gashi har lkcn ta rasa a ina aka mata wannan video din idonta biyu ba bacci take ba…..

*Ci gaban labari*

A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take yashe da kallo, tsakiyar parlor ne kuma a kasan Carpet, gashi babu kowa parlon, everywhere looks strange to her, da sauri ta mike xaune as if trying to recall something, dai dai nan aka bude kofar wani daki ta juya suka yi ido hudu da shi, sai da numfashinta ya dauke na few seconds da kyar ta jawo numfashin, lkci daya komai ya dawo mata ta kurma wani uban ihu jikinta na rawa tana kallonsa, sai kuma ta mike a guje tayi hanyar kitchen kamar mahaukaciya….

18

At first tsayawa yayi kamar bazai bi ta ba amma ganin ta kulle kofar kitchen din yayi saurin bin bayanta, Tsaye ya ganta ta dau table knife tana kuka sosai facing the knife towards her stomach, ya kalleta daga sama har kasa, sae kuma ya shiga cikin kitchen din ya dau asalin wuka ya karasa har gabanta ya mika mata yace “In da gaske kike” runtse ido tayi tana kuka iya karfinta, ya kamo hannunta ya saka wukar a ciki sannan ya koma bakin kofa ya jingina da wall din wajen ya rungume hannunsa yana kallonta da wani scorned expression, ta bude ido a hankali ta jefar da wukar ta sulale kasa tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wayyo na shiga uku na lalace” sai kuma ta daura hannu a ka ta kurma uban ihu tana kallonsa, juyawa yayi ya bata waje, Ko sanda aka yi leaking Video dinta bata tunanin tashin hankalinta ya kai wanda take ciki yanxu, she is still yet to believe who she is seeing, wani ihun tashin hankali ta kuma kurmawa lkci daya kuma tayi shiru, to ko dai aiko sa aka yi gidan, tunanin hakan ya sa ta hau share idonta gabanta na bugawa da sauri, lkci daya tayi assuring kanta kawai aikosa aka yi gidan shine ya shigo masu har ciki, da kyar ta mike tsaye kamar me tsoron taka kasa ta karasa kofar kitchen din ta leko parlon a hankali with throbbing heart, zaune ta gansa saman kujera, suna hada ido ta wani hade rai har sannan gabanta na faduwa tayi karfin halin cewa “Malam idan aikoka aka yi sai ka shigo ma mutane har cikin nan? Wannan wani irin samun waje ne? Duk tsakar gida bai isheka ba sai ka shigo har nan” Kallonta kawai yake da wani stern look a fuskarsa, ta wani kara shan kunu tace “ko shi mai gidan ne ya baka damar shigo mana har cikin nan?” Ba abinda yace mata still, kuma babu alamar xai ce mata komai sai ma dauke idonsa da yayi, ta dake ta fito daga kitchen din gaba daya, tace “Wai baka jin ina maka magana ne ko nan din ma rashin kunyan xaka min?” Yace “Ok” Yana fadin haka ya mike ya juya yayi hanyar kofar fita daga parlon, wani irin kwanciya hankalinta yayi, taji ta samu relieve da nutsuwa, sulalewa kan kujera tayi ta jinginar da kanta da kujerar tare da sauke wani dogon ajiyar xuciya, haba ita dama ta san aikosa gidan aka yi shine xai shigo ma mutane har parlor saboda samun waje, shi kam yana fita ya kulle kofar parlon, Nihad ta share hawayen idonta a hankali tana tunanin to ina wanda aka aura mata din, har yanxu fa bata gansa ba, mikewa tayi ta nufi hanyar dakuna ta bude wani daki a hankali ta leka ciki taga babu komai dakin banda katifa, ta kulle ta sake bude wani taga shi ma katifar ce kawai, toh where is the so called husband, a hankali ta juya ta koma dakin da ta kwana ta xauna gefen gado, she is just imagining ace abinda tayi tunani daxu a kitchen gaskiya ne ai da kawai da gaske kashe kan nata xata yi kowa ma ya huta, but why will she even think that way at the first place, it is something that is neva and neva going to happen, agogon dake dakin ta kalla taga karfe goma sha daya saura, har lokacin bata ji tana jin yunwa ba, ita ta ma mance rabonta da cin abinci a cikinta, tana ta xaune dakin with different thought and imagination a ranta, can kuma ta mike duk jiki ba kwari tana tafiya a hankali ta koma parlor, windown dake kusa da kofar parlon ta tafi tana leka compound din, karamin compound ne da xai iya cin mota uku, ga mamakinta sai ta gansa xaune kan wani dakali a tsakar gidan ya rike kansa, wani faduwar gaba taji ya dirar mata, but seriously what is this man doing in this house for God sake, me yake har yanxu bai tafi ba, to ko dai mai gidan ne yace ya jirasa, this time around ta ma rasa wani takamaiman tunanin xata yi, duk sai ta birkice taji jikinta na rawa…. amma taki barin ƙwaƙwalwarta ya fassara mata abinda xuciyarta ke raya mata a lokacin, noooo it can’t and will never be, tasan aikosa gidan kawai aka yi wallahi……  _Har a lokacin da ya gama hada takalman idon Abba na kansa, ganin xai fita parlon Abba yace “Ibrahim” Juyowa yayi yana kallon Abba, Abba ya nuna masa waje alamar ya xauna, komawa yayi ya xauna a hankali yana kallon Abban, Abba ya nisa yace “Kana da mata ne Ibrahim?” Khalil ya ɗan yi jim, amma ganin yanda Abba ya kafe sa da ido yayi saurin girgiza kai yace “Aa” Abba yayi kasa da murya yace “Ohk! Kana da wani dalilin da yasa baka yi auren ba har ynxu ko kawai ra’ayinka ne?” Khalil ya sunkuyar da kai yace “Dama da kaka aka ce xan yi auren idan Allah ya yarda” Abba yace “Kana da yarinyar da xaka aura ne Ibrahim?” Khalil ya dago ya kalli Abba dake ta kallonsa, sai kuma ya sake sunkuyar da kai a hankali yace “Aa ban samu ba dai tukun” Abba yayi shiru yana kallonsa as if thinking of where to start from, kallonsa kawai Abba yake daga sama har kasa duk da a xaune yake, kamar jikinsa ya basa Abban na kallonsa, sai duk ya tsargu, upside down ya juya palm dinsa a hankali not wanting to disclose the ring he is putting on, muryar Abba yaji yace “Ina son xan maka aure, xan kuma yi maka komai na auren sannan in baka gida ku xauna don na ya6a da nutsuwa da hankalin ka, bana jin ina da fargaba a kanka Ibrahim…. amma baxan yi hakan ba tare da yardar ka ba, da kuma yardar iyayenka, ina rokan wannan alfarman a wajenka Ibrahim” Khalil ya ji komai ya tsaya masa na kusan 10 seconds, lkci daya ya ji he is feeling heat all over, ya dai yi karfin halin dago kai ya kalli Abba, ganin yanda Abba ke kallonsa wanda in dai ka san Abba to xaka fahimci yana cikin damuwa wanda baya iya boyuwa ko min pretence din mutum, Khalil ya kirkiri fara’a a fuskarsa yace “Amma nagode sosai Alhaji, Allah ya kara girma, Allah ya saka da alkhairi, Nagode Alhaji” Abba yaji dadin reaction dinsa sosai cause he neva expect that, ya xata xai ce Aa ko kuma ya kawo wani excuse din, Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace “Ameen Ibrahim, sai mu je can gun iyayenka yau mu yi magana da su ko? Su ma kuma ina fatan Allah xai sa su amince” Khalil ya hadiye abu da kyar yace “To ba damuwa Alhaji” Abba yace “Ka shirya nan da awa biyu mu tafi” Yace “Toh Alhaji” Abba yace “Nagode, amma sai dai baka tambayeni da warce xan hada ka ba” Khalil kallon Abba kawai yake, Abba yace “Yar cikina ce ba wata ba, saboda na yaba da komai naka ya sa nake son hada zuri’a da kai, ni kadai na yanke shawarar nan, kuma idan Allah ya yarda ban yi abun da xai cutar da kai a gaba ba Ibrahim, xaka yi farin ciki da hadin nan wataran, kawai tun yanxu ina neman alfarman ka koyi hakuri da ita don yarinya ce, kuma ita ma nasan watarana xata yi alfahari da xabin da nayi mata, fatana kawai Allah ya dora ni kan iyayenka” Khalil kam yayi nisa tunanin da yake don bai ma assimilating maganganun Abba, thousands of thought ne suka yi crossing mind dinsa a moment din nan, why him of all people, this means disappointing every of his relative, ko Abba bai fada masa wacece cikin yaran nasa ba ya san wacece, no!!! they are not and will neva be compatible, how will that even be? Muryar Abba ya tsinta a tsakiyar kansa ya a ce masa “Xaka iya tafiya, Allah yayi maka albarka” Ko Ameen din khalil bai iya ya amsa ba ya mike ya kwashi takalman Abba ya fita daga parlon, lkci daya yanayinsa ya sauya, wasu xufa suka hau keto masa, Yana fita compound ya nufi mai gadi ya dire masa takalman, Aminu ya mike da sauri yace “Lafiya na ganka a birkice haka? Me ya faru?” Khalil bai basa amsa ba ya nufi chalet, har idanuwansa sun kada …. Muryar Nihad ne ya dawo da Khalil duniyar tunanin da ya fada a tsakar gidan, ya daga kai fuskarsa daure yana kallonta, a fusace tace “Wai baka ji abinda nake ce maka bane? Ka gaya min uban me ya kawo ka gidan nan?” Mikewa yayi yace “Ki kira babanki ki tambayesa, don shi ya kamata ya baki wannan amsan” Kasake tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, har ya juya ya fara tafiya sai kuma ya juyo, severely yace “Sannan ina me baki shawaran kada ki sake daga min murya, ko kuma ki sake min wasu tambayoyi a gidan nan” Daga haka ya bar ta wajen tsaye ya koma cikin gidan walking fast, shikenan abinda take ta hana ƙwaƙwalwarta fassara mata ya tabbata, shikenan tsoronta da fargabanta ya tabbata, ta fashe da wani matsanancin kuka me ban tausayi ta sulale kasa ta daura hannu a ka ta kurma wani uban ihu tace “Na shiga uku na lalace, na banu na lalace, Me nayi ma Abbana xai min haka, me yasa Abbana xai min haka, me nayi ma yan gidanmu suka min haka, innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Kuka take sosai kamar ranta xai fita, ta fi minti ashirin xaune kasan interlock ta kasa tashi, she is more than shock, why her?? Ganin abun ma take kamar a mafarki, Nihad ta ci kuka ta gode Allah a zaune wajen, daga karshe ta kalli gate din gidan sai kuma ta mike da sauri ta nufi gate din amma tana kokarin budewa taji key aka sa, sulalewa wajen tayi tana ci gaba da kuka tana girgiza kanta, nan ma tafi min sha biyar, bata ta66atar da gaske an tsaneta a gidansu ba sai yanxu, sosai kanta ya fara mata ciwo, jin strength dinta ya fara karewa saboda kukan da take tayi karfin halin tashi tana layi ta koma cikin gidan, kitchen ta shiga tana kallon wukar da ya bata ta wurgar daxu, karasawa tayi ta dau wukar hawaye me xafi na sauka idonta, jingina tayi da cabinet tana kuka a hankali, to ai in tayi hakan wuta kawai xata, jefar da wukar tayi daga karshe ta fito parlon tana bin ko ina da kallo hawaye na bin idonta, karamar wayarsa ta gani saman kujera ta karasa da sauri saman kujeran ta dau wayar ta shige dakin da ta kwana, xaunawa tayi gefen gado hawaye wasu na bin wani a idonta tayi dialing number Nihal, tana sa wa sunan Nihal ya fito baro baro, ta kai kunne, yana fara ring ba a wani dau lkci ba Nihal ta daga, kasa cewa komai Nihad tayi tana kuka a hankali ta runtse idonta, jin shiru ba ace komai ba cikin sanyin murya Nihal tace “Hello” Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku Nihal, kinga abinda su Abba suka min ko, dama ashe har Abba baya so na, dama haka aka tsaneni a gidan nan ban sani ba? wayyo Nihal wllh da Allah baxai jefani wuta ba yau da na kashe kaina kowa ma ya huta, zuciyata kamar xata fashe nake ji yanxu, i can’t take this any longer, me yasa su Abba xa su min haka, sun san ma meye aure kuwa?” Kuka take kamar ranta xai fita, Nihal dai tayi shiru bata ce komai ba, Nihad na shessheka tace “Pls ki turo min number Husnah yanxu ta nan, nasan kina da shi send it now plss i need it….” Tana gama fadin haka ta katse wayar ta  fada kan gado tana rera sabon kuka, ko minti daya ba ayi ba Nihad taji shigowar message a wayar, ta mike xaune da sauri taga number Husnah ne Nihal ta turo mata, da sauri ta hau kiran number, yana fara ring Husnah ta daga tace “Hello” Nihad ta rushe mata da kuka tace “Husnah tawa ta kare, Abba na ya tsaneni baya so na, Husnah kila ma ba su suka haifeni ba wallahi” Da sauri Husnah ta rage volume din Mp da suka cika a daki tace “Calm down Nihad, kar ki je ki sa ma kanki wani ciwon mu shiga uku, wllh tsoron xuwa gidan nan naku nake saboda yayanki, babu ta inda kuma xan san halin da kike ciki tunda bani da number kowa a gidan, Nihal da nake da number ta tana school da na kirata tace min haka” Nihad tayi karfin halin cewa “Husnah kin san wa Abbana ya aura min?” Husnah ta gyara xama tana gwale ido tace “Aa waye?” Nihad ta kwanta gefen gado hawaye me xafi na sauka idonta tace “Husnah of all people wai drivern gidanmu Abba ya aura min” Husnah dake xaune sai da ta mike tsaye tace “Whattt???” Bude kofar dakin aka yi Nihad ta mike xaune da sauri lkci daya ta hade rai, yana mata wani kallo ya karasa cikin dakin fuska daure yace “Kar ki sake ta6a min waya a gidan nan” Wani matsiyacin kallo tayi masa ta wurgar da wayar tana ta6e baki tace “Wannan gwangwanin kake kira waya?” Kallonta kawai khalil yake babu ko kiftawa trying his possible best to calm himself, Nihad ta ja tsaki ta tashi ta koma can karshen gado ta xauna fuska daure tace “Wai waya, kai baka ma ji kunyan kiran wannan waya ba” Gyada kai yayi ya juya ya durkusa ya dau wayar da batur dinsa da yayi gefe daya ya mayar sannan ya mike ya nufi kofa ya fice daga dakin, wani sabon kukan ta saki tace “Wayyo Allah na.” Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad da har ta gaji da kukan da take ta ji ana kwankwasa gate din gidan, kamar tana expecting hakan ta mike da sauri tana share idonta ta fice daga dakin, dai dai fitowarsa shi ma daga dakin da yake, ta wani hade rai, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita, wani mugun tsanarsa da tafi ta ko yaushe take ji a ranta, even with joke baxata ta6a kiran wannan mutumin wai mijinta ba, mijinta ta ina? Shi har ya isa ya xama mijinta? This is even weird to imagine, bakin kofar parlon ta tafi ta tsaya fuska daure, yana bude gate din Umma ta shigo, har kasa ya durkusa yace “Barka da xuwa Hajiya, ina yini” Wani kallo Umma tayi masa sae kuma ta kyabe baki ta wuce ta bar sa durkushe a wajen, Nihad na ganin Umma ta taho da gudu ta Rungumeta ta sakar mata kuka da karfi tace “Umma na shiga uku, me yasa Abba xae min haka, me yasa Abba xae lalata min rayuwa, Umma ashe duk ba sona ake a gidanmu ba ban sani ba” Umma ta rungumeta cike da damuwa tace “Yi shiru mu shiga ciki Nihad, yi shiru” A haka Umma ta ja xuwa parlor, khalil da ya bi su da ido ya tafi kan dakalin da ya xauna daxu ya xauna, Umma na rungume da Nihad bayan ta zauna kan kujera tace “Wai ba nace kiyi shiru ba ko in tashe in tafi ne?” Nihad ta girgiza kai tana shessheka a hankali tana goge idonta, Umma tace “Ke yanxu kin yarda an aurar da ke kenan?” Nihad ta daga kai tana kallon Umma da kumburarran idonta, ba idonta ba har fuskarta ya koma ja, Umma tace “Ohh kin yarda kenan an daura maki aure da Driver?” Nihad ta girgiza kai disgustingly tace “Allah ya kiyaye wllh” Umma tace “Toh Alhamdulillah, yanda ko wace budurwa take rayuwarta haka xaki ci gaba babu batun auren kowa a kanki, kar ki kuskura ki amince wai kina da wani wai shi miji, a nan din ma bai wuce ɗan aiken ki ba kuma drivern ki, ki sa a ranki kema budurwa ce da xata iya shiga duk inda take so ta fito, ki ci gaba da rayuwarki yanda kika saba, sannan kar ki kuskura ki raga masa balle ya ga fuskar kawo maki raini, ba kowa bane shi facce drivern gidanku kuma har a yanxu dreban ne, kuma ɗan aike” Nihad tace “Toh Umma yanxu a gida daya xa mu xauna da shi kenan? Wallahi i just can’t imagine that, ta yaya xa ace muna gida daya da shi?” Umma tace “Ka ji ki, Toh ina ruwanki da shi? Meye hadin ki da shi? Rayuwarki kawai xaki dinga yi kamar kina gidan ubanki, kar ki yarda ko kallon kirki ya hada ku da shi, har yau shi din ma’aikacin gidanku ne don haka a karkashin ki yake” A hankali Nihad tace “Toh, amma Umma shikenan baxan ci gaba da karatuna ba kenan” Umma tace “A saboda me? Ai kwantar da hankalin ki, yanxu daga nan gidan Alhaji Abubakar xan nufa tunda dai sun aurar da ke sai su bari kuma ki ci gaba da karatun ki” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Nagode Umma” Umma tace “Kar ki yarda ki kara xubar da hawayenki a banza a hofi, ke da ma kika samu freedom din kanki yanxu, da kin tashi fita kawai fitar ki xa ki yi kanki tsaye babu neman izinin ko wani shege, sanda kika ga dama kuma xa ki dawo babu me tuhumarki” Nihad da ta ji hankalinta ya kwanta sosai tace “Haka ne Ummana” Umma tace “Toh ko ke fa, sannan duk kawayenki xa su iya xuwa nan su dinga kwana kuna yini tare, kuyi duk wani sabgarku a nan babu me cewa don me” Nihad tace “Gaskiya ne Umma, amma ni damuwata kawai ganinsa da xan dinga yi a gidan, baxai yiwu ya koma can gidan ba kawai gaba daya ni kadai in zauna a nan, wllh i hate the sight of him, na tsani ganinsa, na tsanesa” Umma tace “Aa ke kuma, ai xai ci gaba da aikinsa na tuki, kinga duk safiya xai dinga xuwa can gidan kilan kuma sai ya dawo da Abbanku daga office sannan ace xai dawo nan gidan” Nihad ta yatsina fuska, Umma tace “Ke ma abinda idan kika fita kilan sai daren xa ki dinga dawowa gida” Nihad tace “Dama mana, yanxu kawai xance su Husnah da Naf su kwaso kayansu su dawo nan mu zauna” Umma tace “Shikenan kuwa” Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve, Umma tace “Kin ci abinci kuwa?” Girgiza kai Nihad tayi, Umma tace “Me yasa? To tashi ki tafi kitchen ko indomie ne ki dafa” Nihad tace “Toh” Mikewa tayi cike da energy ta wuce kitchen, sosai ta samu nutsuwa bayan abubuwan da Umma ta gaya mata, ta dafa indomie sannan ta fito, Umma tace “Bari in xo in tafi don in samu Alhaji Abubakar a gida” Nihad tace “Umma bani da waya wllh” Umma tace “Akwai nokia din yayanku bari ko Amina xan ba ta kawo maki anjima” Nihad tayi Murmushi tace “To Umma Nagode” sai da ta gama cin indomie sannan Umma tace ta taso ta rakata, Nihad ta mike suka fito compound da Umma, har sannan khalil na xaune inda yake, Ya mike yana kallon Umma yace “Sai anjima Hajiya” Umma ta wani kallesa, sai kuma ta kyabe baki ta ci gaba da tafiyarta Nihad ta hade rai tana biye da ita a gefenta, Komawa yayi ya zauna ya bi su da kallo, suna isa gate Umma tace “Toh sai kin ji ni, idan Amina ta kawo maki wayar sai ki kirani don xan sa a siyo maki sim ayi register sai ta taho maki da shi” Nihad tace “Toh Umma” Umma tace “Maza tafi kiyi sallah ga azahar yayi, sai ki kwanta ki huta” daga haka tayi mata sallama ta wuce, Nihad ta kulle gate din, fuska daure ta nufi cikin gidan. Har bayan magrib Nihad na ta jiran Amina ta kawo mata waya amma shiru, gashi babu yanda xata yi ta kira Umma duk da tana da numberta a kai, wannan ne yasa ta kara shiga wani damuwa, karfe takwas da rabi ta mike a hankali ta fito daga dakinta, dai dai nan Khalil ma ya fito… sosai gabanta ya fadi ta ɗan koma baya, sai kuma ta daure fuska, ko kallonta bai yi ba ya shiga parlor, ta bi sa da kallo taga kamar fita zai yi, tuni turarensa ya gauraye duk parlon, ko burgeta kamshin nan nasa baya yi, ta kasa kunne taji ko fita gate xai yi, ai ko taji ya bude gate, da sauri ta shige dakinsa ta kulle kofar, banda kamshi babu abinda dakin ma yake, ta tafi gefen gado ta dau karamar wayarsa da ta gani ta hau dialing din number Umma sharp sharp, yana fara ringing Umma ta daga hade da sallama, Nihad ta marairaice tace “Umma ni ce” Umma tace “Aa Nihad, Number waye haka duk zero zalla” Nihad tace “Wayar yaron nan ne Umma, ya fita yanxu shine na dauka da sauri na kiraki kafin ya dawo” Umma tace “Kin ji shiru ko, wllh ba a samu anyi rijistan layin yau ba sai gobe wai, don haka gobe da kaina xanje ayi, ita kuma Amina tana dawowa islamiyya xan bata ta kawo maki kin ji” Nihad tace “Toh shkkn Umma, Allah ya kai mu goben” Umma tace “Toh Ameen, sai da safe daughter” Daga haka ta katse wayar, Nihad na duba call logs don ta kira Husnah tunda daxu ta saka numberta a wayar amma bata gani ba alamar ya goge number, instead sai number Nihal ta gani wanda ko awa daya ba ayi ba da suka yi wayan da ita, ta dinga kallon number babu kiftawa, bude kofar dakin aka yi, Nihad ta zaro ido hade da kurma ihu a tsorace ta saki wayar hannunta jikinta na rawa, tsaye yayi bakin kofa yana kallonta da wani Strict expression, lkci daya ta wani sha kunu ita ma, can dai ta tafi can jikin bango har sannan gabanta na faduwa amma bata nuna hakan a fuskarta ba, ya karaso cikin dakin ta hadiye wani abu da ya tokareta a makogwaro da kyar xuciyarta sai bugawa yake tana kara shigewa jikin bango, yana dukawa zai dau wayar ta yi hanyar kofa a mugun guje, da hannu daya yayi hanzarin fixgota ta fasa ihu tana kokarin kwace kanta tace “Wallahi xan cijeka idan baka sakeni ba, ni me xanyi da gwangwanin wayarka”

19

Hadeta Khalil yayi da bango fuskarsa a daure yana kallonta cikin kakkausar murya yace “Zan maki gargadi na karshe, kar ki sake ta6a min wayata a gidan nan, kar kuma ki sake shigo min nan, ina me baki wannan shawarar” Nihad dai gabanta sai faduwa yake ganin how huge he is a gabanta, ita bata ta6a sanin ma haka yake da tsayi ba, gashi ya murtuke fuska uwa ba drivern gidansu ba, amma duk hakan bai sa ta fasa daure masa nata fuskar ba ita ma, sai dai bata ce komai ba, komawa baya yayi yana kallonta, irin kallon kyama sannan ya nuna mata kofa calmly yace “Fita” Ba musu ta nufi kofa, tana isa dai dai kofar ta juyo ta kallesa tana wani yatsine fuska har da harararsa tace “Sai ka gaya min nawa ka siya shegen wayar taka in baka kudin wanda ya fi shi yanxun nan, ban ta6a ganin wanda ke takama da rakani kashi ba sai kai” Still yayi yana kallonta babu ko kiftawa, tana gama fadin abinda xata fada ta bar wajen da sauri tayi hanyar dakinta ta shige ciki ta kulle kofar tana sauke ajiyar xuciya, jingina tayi da kofar wani bakin ciki da takaici ya turnuketa wai yau ita da drivern gidansu ne kadai a gida daya har yana gaya mata maganar banza, ta ji xuciyarta na tafarfasa, she is still yet to believe this, ta kasa yarda wai da gaske wannan mutumin Abba ya sa su gida daya su dinga xama, how will that even be, fadawa tayi saman gado ta fashe da kuka tace “Wayyo Abba me yasa xaka min haka” Ita da dai drivern nan ai gwara ko almajiri ne Abba ya nemo mata su xauna gida daya, ta ci kukanta me isarta bacci ya dauketa a haka. Washegari har kusan karfe goma bata fito ba ga wani mugun yunwa da take ji, tashi tayi da kyar daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, daya daga akwatunanta dake dakin ta bude ta fiddo wata doguwar rigarta ta saka, xaunawa gefen gado tayi feeling so sad and dejected, daga karshe ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta fito parlor, babu kowa parlon sai take away din abinci da ta gani a tsakar parlon, ta saci kallon ko ina na parlon sannan ta karasa inda abincin yake tana ta6e baki ta bude take away din tana kallon abincin ciki, jollof rice ne sai sheki yake da katon kaza, ko rabi kuma bai ci ba, kazar ma bai wani ci ba ya bari, ta bude ledan dake wajen taga drinks ne sai chocolates me yawa, vibration din waya taji saman kujera ta kalla da sauri amma bata ga wayar ba, wanda hakan yasa ta gane wayar na karkashen throw pillow dake saman kujeran, har xata kai hannu ta daga pillow din ta ji an kulle kofar kitchen, sosai gabanta ya fadi ta juyo da sauri suka yi ido hudu da shi ya fito daga kitchen din rike da cup din shayi, sai a sannan ya ji vibration din wayarsa ya karaso da sauri, wanda tun kan ma ya karaso Nihad tayi hanyar dakinta tana harararsa, ya ajiye cup din hannunsa ya bi ta da kallo har ta shige dakin, xaunawa yayi saman kujera yana kallon throw pillow din kamar me son gano ko ta ta6a ko bata ta6a ba, da sauri ya dau wayar kafin ya katse ya daga ganin Abba ne, gaishesa yayi da ladabi Abba ya amsa yace “Anjima da yamma ka daukota ku zo gida ina son magana da ku” Khalil yace “Toh in sha Allah” Abba yace “Ai motar na can gidan ko?” Khalil yace “Ehh yana nan” Abba yace “Ina sauraronku xuwa nan da bayan la’asar” Khalil yace “In sha Allah” Daga haka Abba ya katse wayar, ajiye wayarsa yayi ya jinginar da kansa da kujera, this spoilt his mood the more, Allah ya sani he can’t endure staying under the same roof with this Brat, he wish this never happened, he detest the sight of her, da yasan this is how things will end babu abinda xai kawosa gidansu, da baxai fara ba, yanxu ta yanda ma xai ce ta shirya su je gida shine babban aiki a wajensa, ko magana baya son yana hadasa da ita, mikewa yayi ya dau wayarsa ya zura a aljihu ya fice daga parlon xuwa compound don ya fi zama comfortable xama a nan, abinda Nihad bata sani ba shine shi ya ma fita shiga damuwa kawai dakewa yake yi, kuma bata ki jininsa ba yanda shi ya ki jininta. Ganin yunwa na neman mata illa ta kara fitowa parlor, this time around hanyar kitchen ta nufa tana bin ko ina da kallo, ga kayan abinci amma babu kayan miya, gashi ita ba gwanar cin indomie ba ce, babu yanda ta iya haka ta dafa indomien ta fito ta wuce dakinta, tana ajiye indomien ta fashe da kuka sosai cike da tausayin rayuwarta, why did this happen to her, waye yayi mata haka yayi ruining happiness dinta all of a sudden, tasan duk rashin jin ta ko da singlet bata xama comfortable zama a inda ba gidansu bane, ko su Husnah da take bi she is very cautious of her self and her body, kuka take yi sosai wishing duk wannan abun bai faru da ita ba, indomien da bata ci ba kenan daga karshe, kawai ta tashi tayi alwala tayi sallahn azahar ta kwanta gefen gado hawaye na sauka idonta. Ana la’asar Khalil ya shigo parlor ya zauna yayi dialing number Abba, Abba na dagawa ya gaishesa sannan yayi kasa da murya yace “Abba tace ita baxata ba” Abba yace “Ohk, ba ta waya” Khalil yace “Toh” Mikewa yayi ya nufi hanyar dakin da take ciki, yanda kasan yana kallonta jikin kofar haka ya hade rai yana kallon kofar, sai kuma yayi Knocking kofar, Nihad da ke kwance har sannan ta mike zaune tana kallon kofar, sai da ya sake Kwankwasawa ta mike xaune ta wani hade rai, sai kuma ta tashi ta tafi gun kofar ta bude cike da tsiwa tana harararsa tace “Lafiya kake kwankwasa min kofa Malam? Ko da bashi ne?” Mika mata wayar hannunsa yayi ba tare da ya kalli fuskarta ba, ta kalli wayar da kamar baxata amsa ba sai kuma tayi tunanin kila Umma ce, fixge wayar tayi daga hannunsa tana kallon Number sai taga number Abbanta ne, sosai gabanta ya fadi, tayi karfin halin kai wayar kunne, cikin sanyin murya tayi sallama, Zaro ido tayi tana sauraron abinda Abba ke ce mata with strictness, can ta kalli Khalil da ya koma can gefe ya jingina da bango ya rungume hannunsa, Abba bai bar ma Nihad space din cewa komai ba ya katse wayarsa daga karshe, ta fashe da wani matsanancin kuka tana kallo Khalil tace “Allah ya isa, ban yafe maka ba wllh, yaushe kace min mu je can gida nace Aa?? Wallahi ni baxan ta6a yafe maka ba” Sai kuma ta durkushe wajen tana kuka sosai ta kalli wayarsa dake hannunta tayi wurgi da shi ta mike ta shige cikin daki ta fada kan gado tana rera kuka, ya dau wayar tasa ya bar wajen. Bayan Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta dau hijab din da tayi sallah ta saka sannan ta fito daga dakin, compound ta fito ta gansa xaune driver seat ya bar motar a bude alamar dai ita yake jira, fuskarta a murtuke ta bude back seat ta shiga ta xauna, ya sauka daga motar ya tafi ya bude gate….. Har suka kusa gida Nihad bata daina hawayen da take ba a motar, Horn khalil yayi mai gadi ya leko ganinsa ya daga masa hannu yana washe hakora ya bude gate din, Khalil na parking ya kashe motar ya sauka ya tafi gun Aminu, tuni Nihad ta shige cikin gida, Aminu yayi kasa da murya yana zazzare ido yace “Wani labari muke ji haka mutumina??” Khalil yace “Na me fa?” Kafin Aminu yace komai, Khalil yace “Bari in shiga in fito yanxu” Aminu yace “Toh ina nan ina jiranka” Juyawa khalil yayi ya nufi entrance din gidan, Khalil na tsaye balcony yayi dialing number Abba ya sanar masa sun iso, Abba ya masa izinin shigowa har parlonsa, babu kowa main parlor, Khalil yayi sallama bangaren Abba, Abba ya amsa sannan ya shiga ciki, kansa a kasa ya zauna nan saman Carpet ya kara gaida Abba, Abba ya amsa ganin Nihad bata shigo ba yace “Tana ina?” Khalil yace “Ta riga ni shigowa” Nihad kuwa tana shiga gidan dama direct bangaren Umma ta tafi, Abba ya mike ya fita, a side din Umma ya ga Amina yace “Ina Nihad?” Amina tace “Tana dakin Umma” Yace “Ki shiga ki kira min ita” Amina ta juya ta koma ciki, Abba ya koma parlonsa, bayan wasu yan mintuna sai ga Nihad ta shigo parlon Abbanta kanta a kasa, sallama tayi da muryarta da har ya fara dashewa saboda kuka, bata yarda ta daga kai ba balle ta kalli Abbanta, ta nemi waje daga opposite din inda khalil ya zauna ta zauna, Cikin rawar murya tace “Abba ina yini” Abba bai amsa ba, bai kuma kalleta ba, dai dai nan Umma ta shigo parlon da sallama, kallonta kawai Abba yake, Khalil ya gaisheta ta amsa ta zauna fuskarta dauke da damuwa tana kallon Abba, Abba dai ya kalli Khalil yace “Nagode da wannan alfarma da ka min na auren yarinyar nan Ibrahim, Allah Ubangiji ya baka aljanna” Khalil yayi kasa da kai a hankali yace “Ameen” Abba yace “Ina kuma fatan Allah Ubangiji ya baka hakuri da juriyar zama da ita…. In dai da akwai wani abu kar kayi kasa a gwiwan kirana ka sanar min koma menene shi” Nihad ta fashe da matsanancin kuka tana kallon Abba tace “Abba wallahi bana sonsa kuma baxan ta6a sonsa ba, na tsanesa na tsanesa, ni baxan ta6a xama da shi a gida daya ba, wallahi i hate him….” Mikewa Abba yayi lokaci daya ya sauke mata mari me lafiya a fuskarta, ihu ta fasa ta dafe kuncinta, Umma ta bude baki tana kallon Abba, sai kuma tace “Haba Alhaji, Haba Alhaji….” Dakatar da ita Abba yayi a fusace yace “Bana son jin komai daga gareki, ki tashi ma ki fita” Umma ta ja bakinta tayi shiru, cike da bacin rai Abba na kallon Nihad yace “U think i brought u here to ask for ur opinion? Is that what u think?” Abba ya girgiza kai cike da takaici yace “You are nothing but a disappointment to me Nihad, i regret having u as a child….” Kuka kawai Nihad take tana jin kamar a mafarki wai ita Abba ya mara kuma yake gaya mata wannan maganganun, wanda ko fada bai ta6a mata ba tunda aka haifeta, Strictly Abba ya ci gaba yace “Kuma in har ba so kike inyi disowning dinki ba baki da miji da ya wuce Ibrahim, kuma dolenki kiyi masa biyayya ki bisa, idan ko ba haka ba ki nemi wani uban ba ni ba, sannan idan ba shi ya dauko ki ya kawo ki gidan nan ba bana son in ga kafarki a nan ko da kuwa xa ayi shekara ne bai kawo ki ba, ki sa a ranki baki da wani a yanxu banda shi, shine gatanki, shine komai naki, samun kwanciyar hankalin ki a rayuwa ki bi sa, ko mu da muka haifeki yanxu bamu da iko da ke sama da shi” Kuka kawai Nihad take xuciyarta na mata xafi, ita fa she still can’t believe Abbanta ne ke gaya mata wa ennan maganganun, Abba na kallon Khalil da ya sunkuyar da kansa yace “Kai kuma Ibrahim ina me baka umarni in har Nihad xata kawo maka iskanci ko raini ka zaneta, ni na baka wannan umarnin ba wani ba” Khalil dai bai dago kansa ba, Abba yace “Shikenan kiran dama, xa ku iya tafiya” Da kyar khalil ya iya dago kai yace “Nagode Abba, Allah ya kara girma” Abba yace “Ameen” mikewa yayi yana kallon Umma yace “Sai anjima” Umma ta dinga harararsa, shi dai ya nufi kofa, ganin Nihad ta ki tashi sai kuka take kamar ranta xai fita Abba ya daka mata tsawa yace “Tashi ki bar min gidana, useless girl” Tashi tayi da sauri tana kuka sosai ta nufi kofar ita ma, sai kuma ta juyo cikin rawar murya tace “Abba makaranta na fa?” Abba yace “Sai abinda mijin ki yace, don shi ke da iko dake yanxu, don in xai dau shawarata ma babu ke babu makaranta har abada, maza bi sa ku bar min gidana” Khalil dake jin Abba ya fita daga parlon ta bi bayansa tana kuka sosai, shi dai ko kallonta bai yi ba ya fita xuwa gun mota, Aminu sai wage ido yake yana jiran fitowar Khalil, yana ganinsa ya fito kuma ya shige mota, Nihad ta bude bayan motar ta shiga ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tana jin kamar numfashinta zai dauke, Khalil na isa gate Aminu yace “Ina ta jiranka” Khalil yace “Xan zo da daddare” Aminu ya washe hakora yace “Toh toh sai ka zo” Da gefen ido ya dinga lekan Nihad dake bayan mota, khalil ya ja motar suka bar gidan. Sai kusan karfe shidda suka isa gida, Khalil na parking ya sauka ya tafi ya kulle gate sannan ya dawo ya kashe motar, har sannan Nihad bata dago kanta da ta kife a bayan motar tana kuka ba, tana jin ya kashe motar ta bude side dinta ta sauka, gaba daya ta jike hijab dinta da hawaye har a sannan kuma ba daina kukan tayi ba, ta fara tafiya towards the building of the house, ji tayi ko ina na juya mata a ido, Rufe motar khalil yayi da sauri ya nufeta ganin abinda take, amma kafin ya isa inda take tuni ta kai kasa, ba karamin faduwa tayi a wajen ba, ya zura makullin hannunsa cikin aljihu da sauri ya durkusa gabanta ya dagota amma tuni tayi pass out, daukarta yayi ya nufi cikin gidan da ita.

21

A hankali Nihad ta bude idonta tana bin inda take kwance da kallo, a daki take saman gado, ta mike xaune da kyar tana jin ko ina na jikinta na mata ciwo ga wani sanyi da ke shigarta duk da fankan dakin a kashe yake, ta kalli agogon dakin taga karfe biyu dai dai, window ta kalla ganin duhu yasa ta fahimci biyu na dare ne, hade kai tayi da gwiwa bayan tayi recalling duk abubuwan da suka faru, she couldn’t stop tears from rolling down her eyes, ta dinga shessheka a hankali, tunawa da tayi bata yi sallan magrib ba balle Isha’i ya sa ta dago kanta tana goge idonta da ya kumbura, tayi kokarin sauka daga saman gadon amma taji baxata iya ba, ko ina ciwo take ji yake mata a jikinta, hakan ya sa ta koma ta kwanta a hankali, Hijab dinta dake gefenta ta jawo ta lullube da shi ta takure waje daya sbda sanyin da take ji sosai, amma bai taimaka mata da komai ba sai rawan dari take, bayan kusan minti talatin ta ji an bude kofar dakin, ita dai tana takure inda take ta rufe har kanta da Hijab, tsaye yayi bakin kofar dakin yana kallonta, dama ya zo dubawa ne ya ga ko ta tashi or she is still unconscious cause he isn’t as bad as she is, he have human conscience in him unlike her, har xai juya ya fita sae kuma ya karasa cikin dakin ganin kamar she is shivering, ya isa kusa da gadon yana kallonta xai cire Hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta riko hijab din a fusace cike da tsiwa tace  “Baka da hankali ne?? Uban meye xaka shigo min daki cikin daren nan?” Sake Hijab din yayi ya juya ya fice daga dakin ta bi sa da harara sai kuma ta ja tsaki ta koma ta kwanta jikinta na rawan sanyi sosai. Har aka yi asuba Nihad ta kasa motsawa daga exact spot din da take a kan gadon tun cikin dare, she is so sick and weak, tayi yunkurin tashi ya fi a kirga amma kamar an danneta saman gadon take ji, duk da babu wani abun da ta ci tun jiya amma haka ta dinga jin amai yana damunta kamar xai taho mata, ga ciwon kai me tsanani da ya addabeta, wajen karfe takwas taji aman ya taho mata, bata san sanda wani strength ya xo mata ba ta sauka daga kan gadon tana layi ta bude kofar bandaki, nan ta durkusa ta dinga kakarin amai amma ba abinda ya fito, Khalil na kwance parlor yana jin ta amma ko motsawa bai yi ba daga saman kujeran da yake, a nan tsakar dakin Nihad ta kwanta tana maida numfashi hawaye me xafi na sauka idonta, tana nan a haka har kusan karfe sha daya na safe, zuwa lkcn kuma xaxxabin ya ci karfinta, Duk yanda ya so fita harkarta a gidan kasawa yayi, cause he wasn’t raised to be mean, ya kuma san bata ci abinci ba throughout jiya don shi ya fito da indomie da ta bari a daki bata ta6a ba, karfe sha biyu saura ya mike yayi hanyar dakin after soothing himself to do so, kwata kwata ba don ranshi ya so ba ko don tayi deserving ba yayi hakan kawai dai shi din me tausayi ne, yana bude kofar dakin ya ganta nan tsakiyar dakin a kwance, ya fi minti daya tsaye bakin kofar yana kallonta kafin ya karasa cikin bedroom din, ya duka a gabanta ya cire hijab din da ta rufe fuskarta da shi, ta bude idonta da yayi jajir amma babu strength din rashin kunya ko tsiwa, bai kai hannu jikinta ba but yana jin hucin zafi a jikinta, ya mike ya fita daga dakin ya dau wayarsa, bayan ya gama kiran da xai yi ya shiga kitchen, ruwan gora ya juye a kettle ya daura saman gas, bayan ruwan yayi xafi ya hada shayi a cup ya fito, dakin ya koma ya ajiye mata shayin, amma ya kasa ce mata ta tashi ta sha, har cikin ransa bai son ko magana ya hada shi da wannan yarinyar, kawai daga karshe ya fice daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, bayan kusan awa daya ya fita kofar gida ya shigo da wani likita, wani asibiti dake home service ya kira suka turo masa likitan, bayan sun gaisa ya kai sa har dakinta, likitan ya ajiye abubuwan da ya taho da su yana kallon Nihad, Khalil ya juya ya basu waje yayi zamansa a parlor, bayan likitan ya dubata ya tilastata ta dan sha shayi, sai da yayi yakin kusan minti sha biyar kafin ya samu da kyar yayi mata allurai, ya kuma bata magunguna ta sha, da tace masa sanyi take ji ya dauko wani zanin gado da ya gani a leda ya bude sannan ya bata ta rufa da shi, yace “Allah ya sauwake, Anjima da daddare xa a dawo yi maki allura” Ita dai bata ce komai ba don bacci taji yana hauro mata har ya fita daga dakin, yayi ma khalil sallama sannan ya bar gidan….. Tashi khalil yayi wajajen karfe uku ta dalilin gate da ake kwankwasawa ya fita zuwa gate din ya bude, Aunty Jamila ya gani bakin kofar, sosai take kama da Mummy, ya mata sannu da xuwa sannan ya bata hanya ta shigo gidan, sai da suka shiga parlor ya xauna kasa ya gaisheta ta amsa da fara’a tace “Ya sabon waje” Yace “Alhmdlh” Tace “Toh madallah, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya” Bayan few seconds ta sake kallonsa tace “Ina Nihad din?” Ya dan kalli hanyar daki yace “Tana ciki” Aunty Jamila tace “Toh sanar mata na zo” Mikewa yayi ya nufi hanyar dakin sai kuma ya dawo yace “Aunty bata jin dadi ne tun jiya daxu likita ya zo dubata, ki karasa cikin dakin” Aunty Jamila ta mike ta bi bayansa zuwa dakin, kofar kawai ya bude mata ya koma gefe, ta shiga dakin da sallama ya juya yayi komawarsa parlor, don tunda likitan ma ya bar gidan shi bai shiga dakin ba. A hankali Nihad ta mike xaune tana kallon Aunt dinta, Aunty Jamila ma kallonta kawai take don ba karamin rama tayi ba, Aunty Jamila ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace “Ya jikin” kamar jira Nihad take ta fashe mata da kuka tace “Aunty don Allah ku yafe min, wallahi ban san daga inda video din nan yake ba, ni ban ta6a video haka ba, kuma ban ta6a bari a min video haka ba, i don’t know how everything happened” Aunty Jamila ta ma rasa abinda xata ce mata, Kuka kawai Nihad take ta hade kanta da gado, Aunty Jamila ta dagota tace “Ya isa haka, ba kuka na zo ki min ba, abinda ya faru kuma ya riga ya faru babu me ja da Ubangiji” Nihad dai goge hawayen da ya ki tsaya mata kawai take, Aunty Jamila ta girgiza kai tace “Da kina jin maganar uwarki duk haka da bai faru dake ba Nihad, ke ce tara kawaye, ke ce gantali, ke ce shiga kamar ba yar musulmai ba, kina ganin yanda yar uwarki ke rayuwarta gwanin sha’awa ita da ma ba gaban iyayenku take karatu ba, kin bata wayonki Nihad, kin kuma yi ma kanki damage din da baxai ta6a goguwa ba a doron kasa ba, ina ne wannan Video din naki bai je ba a internet?” Nihad dai kuka take kamar ranta xai fita, Aunty Jamila tace “Da kika je can kebbi din kinyi kawaye ne?” Nihad ta girgiza mata kai kawai, Aunty Jamila tace “Ta yaya ma xa ki ce ke baki san daga inda video din nan ya fito ba? Ba fa daura fuskarki aka yi ba ko wani abu, ke din ce a video din, ko Inner wear din ma ai ni na siyo maki su a Lagos ba a dade ba” Nihad ta ma rasa abun cewa, Aunty Jamila tace “Idan kin je makarantar baki zama a hostel ne?” Nihad ta sunkuyar da kanta, Aunty Jamila tace “Buda baki xa kiyi ki min magana” Cikin rawar murya tace “Aa” Wani shegen kallo Aunty jamila ta mata tace “Ba kin ce min kawayenki a hostel su ke ba?” Nihad ta gyada kai tace “Ehh amma a aji muke haduwa da su” Aunty Jamila tace “Baxa ki daina min karya ba?” Nihad ta hadiye abu da kyar tace “Da gaske Aunty” Aunty Jamila tace “Toh ke kika sani, ki rike gaskiyarki a ciki, xan ga ta yanda xa ayi a gano ta ina video din ya fito idan kin ma mutane karya” Nihad dai tayi shiru gabanta sai faduwa yake, ta yaya ma xata fara ce ma Aunty Jamila babu wani kebbi da suka je da Aunty Kamila hostel ta koma da zama, cab ai rufeta kawai xata yi da duka a nan, sannan ko jiya da suka je gida sai da Umma ta bata shawaran ko da wasa kar ta ce ma wani ai bata je kebbi ba hostel ta koma, ko da xa a cika ta da tambayoyi, balle ita tasan Husnah da Naf da Zully, enemies dinsu ma basu ma video ba balle ita, idan ma Zully na video suna daki tunda ita mayyar video ce Husnah tayi ta masifa kenan tunda su dama sun saba xama daga su sai lingerie, Aunty Jamila ta katse mata tunaninta tace “Don uwarki wataran da kanki xaki bude baki ki fadi ta inda video ya fito, dena wani tunane tunane, yanxu dai ki gama nuku nukunki da karyarki aikin gama ya riga ya gama tunda ga ki a gidan mijin ki” Nihad ta fashe da matsanancin kuka tace “Wallahi ni ba mijina bane shi Aunty, kuma baxai ta6a xama mijina ba, shi drivern ne zai zama mijina? Wllh baxan ta6a yarda ba” Aunty Jamila tace “Gaskiya kam, tunda xa ki iya daukan takarda ki rubuta masa saki ki sake sa… Kinga karshen rashin yarda kenan” Nihad ta kara rushewa da kukan takaici, ita fa da taji ance khalil mijinta sai taji kamar an dau duniyar gaba daya an aza mata a kai, da dai a dinga furta mata wannan kalmar gwara a nuna mata bindiga kawai a harbeta, Aunty Jamila bata damu da kukanta ba ta bude cup din da ta gani a rufe ta ga shayi ne a ciki, tace “Me kika ci yau?” Ta girgiza mata kai hawaye caba caba a fuskarta tace “Ban ci komai ba” Aunty Jamila ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta fada kan gado tana rera kuka, Khalil na ganin Aunty Jamila ya mike yace “Za a dauko maki wani abun ne Aunty?” Aunty Jamila tace “Aa, so nake ko shinkafa da miya ne a samu a dafa, inji akwai kayan miya a gidan?” Yace “Aa xan fita in siyo yanxu” Aunty jamila tace “Toh shkkn” Daga haka ta shiga kitchen don daura ruwan shinkafa, Nihad ta hadiye kukan da take ta jawo jakar Aunty Jamila ta zuge zip din,  Wayarta ta ciro tayi dialing number din Nihal, sai ga number ya fito da suna, aika kiran tayi ta kai kunne, Nihal na dagawa tayi sallama hade da cewa “Ina yini Aunty?” Nihad ta wani kyabe baki tace “To ni ce nan ba ita ba” bata jira Nihal ta saurari Nihal ba tace “Kin ga Number Husnah xa ki turo min ta nan yanxun nan ba wani magana na kira ki min ba” Nihal tace “Ke me xa ki yi da number Husnar nan ne?” Nihad tace “Wannan bai shafe ki ba, kawai ki turo min abinda na tambaye ki” Magana Nihal take amma Nihad ta katse wayar kawai, ba a wani dau lkci ba sai ga number Husnah ya shigo wayar Aunty Jamila, Nihad ta mike da sauri ta tafi gun jakarta ta bude ta dauko biro da jotter, A hankali ta dawo ta zauna sbda har sannan bata gama dawowa dai dai ba tana dan jin jiri, bayan ta kwashe number ta tura takardan cikin pillow case dinta, sannan tayi dialing number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga, Nihad tace “Ni ce Husnah” Husnah dake cikin kasuwa ta nemi wani shago ta shiga da sauri ta zauna tace “Nihad ina ta kiran wancan layin da kika kirani da shi jiya naji kamar anyi blocking, line busy kawai yake sa min, har dare ina trying wllh, to ni kuma na rasa ta inda xan sameki” Nihad tace “Ai wayar wancan wawan yaron ne, wato blocking din ki yayi ko?” Husnah tace “Wallahi kuwa, wai yanxu kina nufin daga ke sai shi a gida daya?” Nihad ta fashe da kuka tace “Wallahi the thought of this na sa inji kamar in kashe kaina Husnah” Husnah tace “Ki kashe kanki a kan wa?? Aa wallahi turo min address din gidan yanxu” Nihad tace “Toh ai ban san ko ina ne nan din ba, amma bari in kira Umma in tambayeta” Husnah tace “Toh maza kirata ko ki turo min numberta ni in kira” Nihad tace “Toh” Katse wayar tayi ta hau kiran Umma, yana fara ring Umma ta daga, Nihad tace “Umma ni ce” Umma tace “Aa Jamilan na can kenan yau?” Nihad tace “Ehh” Umma tace “Toh anjima Amina na nan xuwa maki da wayar anyi rijistan layin” Nihad tace “Toh, Umma su Husnah ne ke son xuwa kuma ni ban san address din nan ba” Umma tace “Gaskiya baxa ki sani ba, kinsan me xai faru?” Nihad tace “Aa” Umma tace “Kice kawai su taho nan gida sai su biyo Amina tunda ita ta san gidan” Nihad tace “Toh Umma” daga haka Nihad tayi mata sallama ta katse wayar, ta kira Husnah ta sanar mata yanda suka yi da Umma, Husnah tace “Hakan ma yafi sauki wllh, turo min number Aminar” Nihad tace “Toh, amma kar ki kira layin nan na kanwar Mumy ce” Husnah tace “Toh shkkn, kawai sai mun zo anjiman” Nihad tace “Toh” Daga haka ta katse wayar, tayi deleting duk calls din da tayi ta goge message da tayi ma Husnah na number Amina, sannan ta mayar da wayar cikin jakar. Bayan la’asar Aunty Jamila ta gama girka shinkafa da miyan, A plate ta xubo ma Nihad ta fito parlor tana kallon khalil tace “Ga can abincin an gama” Yace “Toh sannu da aiki Aunty, Mun gode” Dakin Nihad ta wuce ta ajiye abincin a kasa, Nihad ta fito daga bandaki daure da towel, ta xauna gefen gado tana kallon Aunty Jamila tace “Sannu da aiki Aunty” Aunty Jamila tace “Yauwa sannu, kiyi maza ki ci abincin” Nihad tace “Toh nagode” nan ko ta rasa ta yanda xata tambayeta yaushe xata tafi don bata son su Husnah su zo tana gidan nan, ganin bata da niyyar tashi Aunty Jamila tace “Toh tashi ki fiddo kayan da xa ki sa mana” Nihad ta mike ta bude jakar ta dauko riga da skirt, bayan ta shafa mai ta sa turare sannan ta sa kayan, Aunty Jamila ta dauko abincin ta mika mata, amsa tayi ta fara ci, gaba daya taji bakinta babu dadi tura abincin kawai take, Aunty Jamila ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito tayi sallah, tana idar da sallah tace “Aunty ke baxa ki ci abincin ba?” Aunty Jamila tace “Aa na ci abinci kan in fito gida” Nihad bata kuma cewa komai ba, Aunty Jamila tace “Toh ni xan tafi Nihad” Nihad ta sauke ajiyar xuciyar relieve don abinda take ta jiran ji kenan ganin hudu da rabi yayi tasan kilan ma su Husnah na hanya yanxu, Aunty jamila tace “Ki bude kunnenki ki saurare abubuwan da xan gaya maki da kyau” Nihad ta sauke idonta a hankali tace “Ina ji Aunty” Aunty Jamila tace “Ki nutsu ki dawo hankalinki, kinga wancan mutumin dake parlor??” Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya har hawaye ya cika idonta tun bata ji abinda xata ce ba, Aunty Jamila tace “Toh mijinki ne shi yanzu….” Nihad ta rushe da kuka tace “Don Allah Aunty ki daina cewa haka, wayyo ni a daina ce min haka gaskiya” Aunty jamila tace “Ba shakka, to rufeni da duka sai in daina ce maki haka, ke ba taimakonki yayi ba da ya rufa maki asiri ya aureki?” Kuka kawai Nihad take, Aunty Jamila tace “Toh wllh idan ba fushin Ubangiji kike son ja ma kanki ba ki bi mijinki kiyi masa biyayya ki zauna lafiya a duniya, naga kamar baki saduda ba har yanzu baki dau darasi daga abinda ya sameki ba, ni iyakar abinda xan gaya maki kenan idan kin ji yayi maki amfani idan kika yi watsi da shi kuwa kuka bai kare maki ba a duniya” Daga haka Aunty Jamila ta mike ta dau mayafinta ta yafa, ta dau handbag dinta, kuka kawai Nihad take ganin ta nufi kofa sai kuma ta mike ta bi bayanta cikin rawar murya tace “Toh Aunty karatuna fa?” Aunty Jamila ta juyo ta kalleta tace “Wannan kuma sai ki tuntubi mijinki ki ji, mu kam ai bamu da iko da wannan, in ya amince sai ki ci gaba” Nihad na girgiza kai tace “Aunty don Allah kice masa ran monda xan tafi makaranta ni dai” Aunty Jamila tace “Ohk ni ce ma xan gaya masa, ashe shkkn iyakar karatunki kenan a duniya in har ni xan gaya masa” Fita Aunty Jamila tayi daga dakin tayi ma Khalil sallama a parlor, ya mike yace “Aunty har za ki koma” Tace “Ehh wllh na bar yara a gida” Yace “Toh bari in ajiye ki” Tace “Aa da kayi zamanka kawai Nagode, ina fita xan samu adaidaita sahu” Yace “Aa bakomai, xan ajiye ki yanxu” daga haka ya dau makullin mota ya fita, sai taji dadin yanda ya karramata sosai, kuma ko ba komai xata samu enough chance tayi masa magana a mota a kan Nihad, Nihad ta bi sa da wani harara, Aunty Jamila ta kalleta bayan ya fita tace “Wa kike harara Nihad?” Kin cewa komai Nihad tayi, Aunty jamila tace “To ki sani yau shine ganina na karshe da xaki yi a gidanki, indai baxa ki kwantar da kai ki zauna lafiya da mijinki ba” Nihad ta fashe da kuka har da bubbuga kafa tace “Ni Aunty ki daina ce masa mijina don Allah, wayyo Allahna na shiga uku” Kofa Aunty jamila ta nufa ta fice daga parlon, sai da suka fita daga gidan Nihad ta koma dakinta tana share idonta, Allah ya kiyaye wannan ya zama personal driver dinta balle kuma wai miji, suna fita ko minti goma ba ayi ba taji ana kwankwasa gate, da sauri ta mike ta fice daga dakin ta tafi compound don ta san su Husnah ne suka iso, tana isa gate din taji muryarsu kuwa, sosai wani farin ciki ya lullubeta amma kuma lkci daya fara’ar fuskarta ya bace da ta ji ta kasa bude gate din, kuma kamar ta waje aka kulle, Naf tace “Gate din ya ki buduwa ne kin bar mu tsaye cikin rana?” Nihad tayi narai narai da ido tace “Wllh kamar ta waje ya kulle” Husnah ta bude baki haka Zully, Naf tace “Amma dai wannan a yan iskan ma A ne shi, ta waje ya kulle gate? To a saboda me? Akuyarsa ya ajiye a gidan yake tsoron kar ta gudu da xai kulle ki cikin gida?” Nihad bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba shkkn da gaske kulleta yayi, Husnah tace “Ke kuma matsalarki kenan, to meye na wani kuka” Amina dai na tsaye rike da ledan waya a hannu, Naf tace “Toh wai ina yaje?” Nihad tace “Wai fa Auntyna ya kai gida shine sabida bashi da hankali ya kulle min gate ta waje kamar gidan ubansa” Husnah tace “Kuma wllh makulli ya sa, ni ko har na kagu in ga wannan me ido da kwallin” Nihad ta goge idonta tace “Kawai ku ɗan jira a nan yanxu xa ku ga ya dawo” Haka suka yi ta jira a bakin gate din, ita kuma ta zauna kan dakalin dakin da aka tanadar don mai gadi a compound din, tun daga nesa khalil ke kallonsu a bakin gate din, yayi parking ɗan nesa da gidan, Amina tace “Yauwa gashi can, motar gidanmu ce wannan” Su Naf duk suka kafe motar da ido ana jiran aga fitowarsa amma bai fito ba, Husnah tace “Ji gantalalle ya ki saukowa a motar” Zully tace “Shi ne ai nake kallon ikon Allah” Naf ta kalli Amina tace “Ke tafi ki karbo mana makulli wajensa tunda ba shi da hankali, uban wa zai bari tsaye cikin rana” Amina ta tafi a gun motar yana ganinta ya sauke glass din can side din don duk sun gwala ido su ga ya sauke glass din side dinsa ko xa su samu a little glimpse of him, Amina na ganin haka ta zaga tana kallonsa ta cikin motar tace “Ka bamu makullin gidan” Yace “Su waye bakin gate din?” Amina tace “Kawayen Aunty Nihad” Yace “Ohk, ke kika kawo su kenan?” Tace “Ehh Umma ta bani sako in kawo mata ne shine muka taho tare da su don basu san gidan ba” Ya mika hannu yace “Toh kawo a ajiye mata sakon, yanxu kasuwa xanje in yanko wani makullin wancan ya fadi” Amina tayi kasake tana kallonsa, mika hannu yayi ya amshe ledan hannunta yace “Ko xaki shigo in ajiye ki gida daga nan in wuce kasuwar?” Amina ta daure fuska tace “Ni ai a motarsu muka zo” Yace “Toh koma motar tasu” Daga haka ya ja glass ya tada motar yayi reverse ya bar layin…..

22

Husnah suka kalli junansu da sauri ganin Khalil ya juya motar xai bar layin, Amina ta dawo fuska a daure tace “Wai wani zai je ya yanko wani makullin” Husnah ta rike kugu tace “Tashin hankali, lallai wannan mutumin dan iska ne, karya fa yake yi wllh, mu din dai ne baxai bude ma gidan mu shiga ba” Nihad ta taso da sauri ta tsaya jikin gate din tace “Me ya faru?” Naf dai ta kasa cewa komai tun da ta bi motar da ido baki bude, Zully tayi wani dariya ta rike ha6a tace “Kan uban can… Amma gayen nan daga ɗan iska sai shi, but don Allah ku baku ji kun kagu kuna son ganinsa ba? It’s the gut for me” Nihad dake ta zaro ido ta kasa fahimtar abinda suke cewa tace “Don Allah ku min magana mana, ya dawo ne?” Husnah ta sauke wani uban ajiyar zuciya ta koma bakin flower ta zauna tana girgiza kafa, Naf da wani bakin ciki ya isheta tace “Amma idan ban tara yan sara suka da yan da6a sun ma drivern nan mugun bugu ba ku ce bani bace, don kaza kazansa da uwar me yake takama xae walakanta mu haka da girman mu, wa ye shi xai dinga feeling kansa haka yana fama da talauci…” Tuni Nihad ta fara fahimtar abinda ya faru hawaye ya cika idonta, ita dai ta shiga uku da abinda wannan yaron ke yi mata, Husnah ta kara sauke wani axababben ajiyar xuciya ta mike tace “Nihad mu xa mu tafi, ashe da gasken gaske tsinanne ne mutumin nan sai yau na sake tabbatarwa, wato tantirin ɗan iska ne na bugawa a jarida, har mu zai walakanta ya juya kan mota ya bar mu uwa yan iska a tsaye bakin gate? Who the hell did he think he is” Nihad ta sakar masu kuka tace “Ba ina gaya maku ba kun zata exaggerating nake, ai wallahi zai iya yin abinda ya fi haka, ina Amina?” Amina tace “Ga ni” Nihad tace “Ki kira Umma da wayarki ki gaya mata abinda dan iskan yayi maku” Amina ta fiddo wayarta a jaka ta hau kiran Umma, Umma na dagawa ta larabta mata abinda khalil yayi masu a bakin gate, Umma ta rike ha6a bayan ta gama sauraron Amina tace “Yau ga shegen mutumi, kuna nan har yanzu bakin gate din kenan a tsaye?” Amina tace “Wallahi” Umma tace “Ina wayar Nihad din?” Amina tace “Ya karɓe wai xai ajiye mata” Umma ta wani mulmulo zagi ta lafta mata tace “Uban wa yace ki basa? Wajensa na aiko ki xaki basa waya? To wallahi duk inda xaki nemosa ki nemosa ki amsar min wayata, kaji min doluwar yarinya kawai” Amina ta turo baki tace “To wai ba karbewa yayi a hannu na ba, ni me xan ce masa” Umma ta kara kunduma mata zagi tace “Ubanki ne ya siya min wayar da xa ki ba wani ɗan iska can? Na dai gaya maki kar ki kuskura ki dawo min gida babu wannan ledar wayar, shashashar banza kawai doluwa” Daga haka umma ta katse wayar tana huci, Nihad tace “Ban gane ba, wayar kika basa Amina?” Amina tace “Toh wai ba amshewa yayi a hannuna ba yace xai ajiye maki” Nihad ta kunduma mata zagi ita ma tace “Wallahi maza ki bi sa ki amso min wayata, meye hadina da shi da har xai amsar min waya yace xai ajiye? Munafuki kawai” Amina tace “Ni dai wallahi ku daina min masifa tunda ba ni na mika masa ba” Husnah tace “Toh wannan takadirin ai ko bata basa ba xai iya fizgewa a hannunta, don naga kamar ya ta6a dabanci, ni dai wllh bai walakanta banza yau din nan ba, xai san ya ta6a Clique dinmu…” Naf duk ta fi su shiga takaici a wajen, she really wants to meet with Khalil ya ga karshen rashin mutunci da tijara, Zully tace “Ni anya ma ba shi yaje ya samu Abban yace a basa auren Nihad din ba kawai don ya samu hanyar dinga walakantata?” Nihad na tafe hannu tace “Ai ko da kansa xai tafi ya samu Abban yace masa yayi hakuri ya fasa auren, i am going to make life miserable for him, xai san cewar ni ba sa’ar zama waje daya da shi bace balle uwa uba aure, shi har ya isa ya aureni? Wallahi da wuri wuri zai koma gun Abba yace ya fasa” Husnah tace “Atoh, duk wannan koke koken da kike yau kwana da kwanaki babu abinda xai tsinana maki sai ma 6ata lokacin ki da kike ki ji in gaya maki, yanzu kamata yayi ace kin zauna kin nutsu kin fara nazarin ta yanda zaki fara musguna ma shege, kar ki kuskura ki raga masa daga cikin tijara da iskanci da muka iya a Clique dinmu, In his next life ko million daya xa a dinga basa ya zo gidan masu kudi yayi driving wallahi baxai zo ba, shi din banza shi din hofi” Sosai hudubar Husnah ke shigar Nihad da taji daga wannan moment din ta daina kuka, baxata kara asaran hawayenta ba akan Halilu, sai dai ta fara daukan action a kansa, kuma da ƙafafuwansa xai gudu ya bar mata gidan ya koma kauyensu na har abada, Husnah tace “Kuma gidan nan ko da uban wa yake yawo sai mun shiga gobe, balle daga shi sai talauci yake yawon ma, wallahi kamar mun shiga gobe, Allah ya kai mu goben, kuma ina fatan Allah Ubangiji ya hada mu da shi face to face goben” Nihad ta sauke ajiyar xuciya saboda sosai ta samu kwarin gwiwa, tace “Amina ki ɗan ara min wayarki mana zuwa gobe” Amina tace “Toh ni sai in yi amfani da wanne?” A fusace Nihad tace “In za ki ara min ki ara min malama, banza kawai ba ke kika je kika mika ma wawan can wanda Umma ta baki ki kawo min ba? Dallah bani wayarki ai ba cinyewa xan yi ba” Amina tace “Ban ga xan iya ba, ni islamiyya ma xan yi tafiyata daga nan, duk an bata ma mutum lokaci ansa na makara kawai a banxa, sai da nace ma Umma ni islamiyya xan tafi amma ta ki” daga haka ta juya fuuu ta bar su wajen a tsaye, Husnah tace “Ke rabu da wani aran waya, gobe ni da kaina xan kawo maki waya, screen touch kuwa” Nihad tace “Toh ta yaya, bayan kina ganin abinda yake yi da gidan kamar na ubansa” Husnah tace “Baki yi trusting dinmu ba kenan?” Naf tayi wani Murmushi tace “Ai kamar mun shiga gidan nan gobe idan Allah ya kai mu, ki saurare mu idan mun tashi test” A hankali Nihad tace “Toh shikenan, Allah ya kai mu” Zully tace “Toh wai ya sunan wannan tatattcen mutumin ne?” Nihad tace “Halilu naji ana kiransa” Duk suka kwashe da dariya Husnah tace “Za mu haliro masa gobe kuwa” Daga haka suka yi mata sallama, tana jin suka shiga motarsu suka bar layin, ta sauke wani ajiyar xuciya ta juya ta koma cikin gidan. Sai bayan magrib Nihad ta ji shigowar Khalil gidan, nan da nan taji bacin ranta ya ninku a kan na da, tana jin sa ya shigo parlor ta mike ta fito parlon, bai ko kalleta ba ya ajiye ledan hannunsa ya zauna saman kujera ya dau remote yayi powering tv, a fusace ta karaso cikin parlon ta fixgo ledan da ya ajiye don a tunaninta wayarta ce, da ido ya bi ta har ta gama bincika ledan ganin fruits ne ta cillar a gefe, tana tafe hannu cike da tsiwa tace “Ka buda kunnenka da kyau ka saurareni, yau ya zama first and last day da xaka sake kulleni a gida idan xaka fita don ni ba akuyarka ko tinkiyarka bace, kuma ka bani wayar da Ummata ta aiko min” Kallon Tv kawai khalil yake, tayi masa wani tsawa tace “Baka ji na ne ina maka magana?” Still bai kalleta ba balle ta sa ran xai amsa, a mugun fusace ta tafi ta kashe socket din gun Tv din gaba daya tana kallonsa tana huci, Khalil ya kalli karamar wayarsa dake ring, dagawa yayi ya kai kunne yace “Idan na gama abinda nake xan kira ki Hajiya” Huci kawai Nihad take tana kallonsa, yana katse wayar ya mike ya nufi bedroom, wani bakin ciki ya kara rufeta ta bi sa da sauri ta shige gabansa tana cewa “Ni ce ma zan dinga maka magana zaka tashi ka bar wajen, to wallahi baka isa ba….” zata cakumosa kamar yanda ta saba ganin kallon da yake mata sai ta fasa kai hannun nata kwalarsa, Cikin kakkausar murya yace “Matsa ki bani waje” Duk da yanda gabanta ke faduwa tace “Baxan matsa ba, ka bani wayata tunda ba kai ka siya ba….” Irin kallon da taga yake mata yasa ta fashe da matsanancin kuka ta durkushe wajen don can kasan xuciyarta a tsorace take da shi, ya bi gefenta ya shige daki abunsa ya kulle kofar. Mikewa tayi tana kuka tana bubbuga masa kofa tace “Ni wallahi ka bani wayata tunda ba da kudinka aka siya ba, ina ruwanka da sakon da aka kawo min da xaka sa hannunka ka amsa” Banza yayi mata, ita kuma bata fasa bubbuga kofar ba, bayan kusan minti biyar taji ya bude kofar sosai gabanta ya fadi ta koma gefe da sauri amma kuma bata fasa fadan abinda take fada ba, taga ya sa ma dakin makulli ya cire sannan yayi hanyar kitchen ya shiga, bin sa tayi har bakin kofar kitchen din ta tsaya tana kuka tace “Wallahi idan na maka Allah ya isa sai ya bi ka har generation dinka, ka bani wayana nace” Gas ya kunna ya dau karamin tukunya sabo ya dauraye ya sa ruwa a ciki ya daura saman gas din, bata fasa masa fitsaran da take ba a bakin kofa, ya juya ya ɗan kalleta, ta wani maka masa harara tace “In kuma siyarwa kaje kayi sai ka gaya min in cire rai” Shi dai bai ce mata komai ba ya rungume hannunsa yana jiran ruwan ya tafasa, ta rushe da kuka ta hade kanta da kofa tace “Wayyo Allahna na shiga uku” Ya daga kai ya ɗan kalleta, juyawa yayi yana kallon ruwansa dake saman gas, ta dago kai cikin kuka tace “Koma me kayi da wayar ban yafe ba….” Ko rufe baki bata yi ba taga ya cire hannunsa da sauri daga handle din tukunyar alamar ya kona sa, ya koma baya yana kallon tukunyar, wani shegen dariya ta saki har da kyakyatawa ta durkusa a wajen, yanda take dariyar kai kace bata da sauran damuwa a duniya, ya ɗan kalleta sai kuma ya shafa kansa ya juya yana murmushi ya kalli inda ya tukunyar ta kona sa, ruwan da bai juye ba kenan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ya bar ta a ciki, bayan ta ci dariyarta ya isheta sai kuma ta mike ta hade rai, a hankali ta dauke tukunyar shinkafar da Aunty Jamila ta girka, ta dau na miyan ma duk ta kai dakinta da plate da spoon sannan ta koma ta jawo kofar kitchen din ta saka makulli ta zare, sai ta ga ta yanda xai sha shayin yau, infact forever and ever, don ta kulle kitchen din kenan har abada, Dakinta ta wuce ta bude akwatunta ta binciko duk kayan ta ajiye makullin karkashin akwatin sannan ta mayar da kayan ta kulle akwatin ta koma gefen gado ta zauna. Tun kafin tayi sallan magrib tayi wanka, don haka ta zuba abinci ta ci, ta tashi ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta dauro alwala, tana yin sallan isha’i ta sa ma dakinta makulli ta ta dawo ta kwanta. Washegari bayan Nihad tayi wanka ta wanke bandakinta, she can be lazy in all aspects but not  when it comes to her bathroom and Bedroom, bayan ta fito sai da ta fara gyara dakinta sannan ta saka kaya, sbda mugunta haka ta zuba sauran shinkafar da sanyi ta ci, ta koma bandaki ta kuskure bakinta da mouth wash ta fito, Hijab har kasa ta daura saman kayanta, sannan ta dau jakar da take xuwa makaranta da shi ta bude kofa a hankali ta fito parlor, yana kwance saman doguwar kujera, ta galla masa wani harara ta karasa cikin parlon, ta tsaya bayan 2 seater, ta dake tace “Makaranta xaka ajiyeni malam” Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma ya mike zaune yace “Ohk, wace makarantar?” Babu yabo babu fallasa tana juya ido tace “Wanda ka saba kai ni” ya gyada kai yace “Ohk” Sai kuma ya koma ya kwanta, a mugun fusace tace “Kana bata min lokaci lectures din safe gareni, ko kuma ka bani makullin motarmu inyi tafiyata” Khalil yace “Ki jira duk sanda Allah ya nufa kin koma can gidan naku da xama sai ki ci gaba da xuwa makarantar, amma a nan gidan kam ke da fita ko nan da gate sai wani ikon Allah, na soke xuwa wannan makarantar har abada” Da mamaki take kallonsa baki bude, sai kuma ta hadiye abu da kyar tace “Kai kuma a uban wa xaka gaya min haka? Kai a wa xaka soke min xuwa makarantata?” Ya kalleta yace “Kira Abbanki ki tambayesa” Bata san sanda ta fashe da kukan takaici ba tana kallonsa, yace “Allah ya amfana ɗan wanda kika samu” Yana kai wa nan ya mike ya shige daki ya bar ta wajen, sulalewa kasa tayi tana kuka sosai, wai yau common driver ne yake ce mata baxata je makaranta ba wai ya soke, whatttt??? Nihad ta ci kuka ta gode Allah a wajen kafin ta shiga daki, komai na duniyar ta ji ya isheta…. Throughout ranan haka ta yini a kwance tana hawaye, tana mugun son tayi magana da Umma amma babu dama, don babu wayar da xata yi kiran, she needs to tell Umma this, bayan Umma bata da wani wanda xata gaya ma, tana jin an kira la’asar ta mike zaune, sosai kanta yayi mata nauyi, ga magungunanta rabon da ta sha tun jiya, kuma bata jin xata sha, shiru shiru bata ji alamar ya fita gate ba gashi har an tada sallah, mikewa tayi a hankali ta fita parlor, ta dinga bin parlon da kallo ta kalli bakin kofa taga ba takalminsa, to har ya fita kenan bata ji ba, komawa corridor din dakunan tayi ta kai hannunta handle din kofar dakinsa ta murda a hankali kofar ya bude, ta leka cikin dakin ta ga ba kowa, kallon karamar wayarsa dake saman gado ta dinga yi, dai dai nan ya bude kofar bandaki ya fito, tayi masa wani tsinannen harara ta juya ta koma dakinta. Bayan ya dawo masallaci yana zaune compound bai shigo parlon ba yaji an kwankwasa gate, ya dinga kallon gate din kafin ya mike ya tafi bakin gate din, har sannan ba a fasa kwankwasawa ba, yace “Waye?” a fusace Umma tace “Malam xaka bude min kofa ko kuwa? Ji wani tambayar walakanci wai waye, shi dama talaka ai bai iya samun waje ba, ka tashi ka garkame gida kamar na ubanka, da an kwankwasa kuma kace waye, to masu shi ne sai ka bude ko?” Khalil na tsaye yana sauraronta, sai da ya dau kusan 40 seconds kafin ya bude gate din, Umma ce tsaye da su Husnah a bakin gate din, Yayi kasa da kansa yace “Ina yini”  Umma tayi mitsi mitsi da ido tace “Ban yini ba, nace ban yini ba, ɗan marasu mutunci” Ya so juyawa ya bar wajen amma ya kasa sbda girma da mutuncin da Abba ke da shi a idonsa, Husnah, Naf da Zully suka dinga kallonsa babu kwakkwaran kiftawa, duk tambaya daya ce ke yawo a xuciyarsu, wannan shi ne dreban, is he the driver? Husnah tace “Umma wai shine driver din??” Umma tace “Gashi kuwa kin gansa” Duk suka kalli junansu, Husnah ta tafe hannu tana kallon khalil tace “Wato kai ne ɗan rainin wayon da ya barmu bakin gate jiya? Kai ga ka shafaffe da mai ko?” Naf na nuna sa da yatsa tace “Kai kana buzu har xaka zo kasar mutane kana bubbusa hanci kamar algaita? Waye kai? Kuma uban me kake takama da shi? Kasan mu su waye da kake tunanin zaka mana walakanci ka kwana lafiya?” Zully tace “Ai ni na ma rasa ta cewa, wato wannan dai shine driver me ba kawar mu though time, toh hasken naka kake takama da shi kake tijara ko me?” Nihad ce ta taho da gudu ganin Umma ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Sai kuma ta sake Umma ta rungume su Husnah gaba daya har da hawayenta sbda tsabar farin ciki, juyawa khalil yayi ya bar wajen kamar zai tashi sama, Husnah tace “Sai ga mu ga ɗan rainin wayon nan yau” Nihad ta sauke wani ajiyar xuciyar takaici, Umma tace “Wato bai baki wayar ba dai” Nihad tace “Wallahi kuwa, ya ki bani” Umma tace “Mu je ciki, sai na ci kaxa kazansa, wato yanxu baya ganin kowa da gashi sbda Alhaji ya gama bada mu gabansa yayi mugun raina mu, yo ya bada mu mana tunda har xai dau yar sa ya basa, idan ma hadin yake son yi ina ‘ya yan abokanansa?” Duk suka dukufa xuwa cikin parlon Umma na ƙare ma Khalil zagi su Husnah na tayata, shi kam tuni ya shige daki ya sa makulli, sabuwar waya dal Husnah ta siya ma Nihad har da sim card a ciki, murna wajen Nihad ba a cewa komai, gaba daya ta mance damuwar da take ciki, Umma tace “Kinga shikenan sai ki kwantar da hankalinki yanxu, tunda sun ga gida kullum kya gansu, kafin dai su dawo nan din gaba daya” Nihad ta marairaice tace “Umma fa kulle gate din yake yi kuma makullin na jikinsa” Naf tace “Amma fa kamar a jikin gate din ya bar makullin yanxu da ya bude mana fa” Husnah tace “Idan ko haka ne kawai cirewa xa mu yi mu je a yanko mana spare” Zully tace “Bari in duba” Mikewa tayi ta fita, sai ga ta ta dawo rike da makullin tace “Ai ko dai gashi” Umma tace “Toh Alhamdulillah, tunda dare bai yi ba yanzu me xai hana ku je inda ake yankan spare din a yanka maku?” Naf ta mike tace “Yanzu kuwa, kawai kudi za mu cika masu yau yau din nan xa a yanka a bamu” Naf da Zully ne suka tafi da makullin wajen yankar makulli, Nihad ta dauko ma Husnah makullin kitchen xata dafa masu taliya wai, Nihad na kallon Umma ta marairaice tace “Umma yau na shirya xan je makaranta ya hanani wai ya soke” Buda baki Umma tayi tana kallon Nihad, sai kuma tace “Toh ba a haifi ubansa ba balle shi, shi har ya isa ya soke maki karatu? Bari dai su yanko makullin kawai, ki kwantar da hankalin ki, ai indai da raina babu me cutarki a duniya Nihad, sannan nace maki ki wani manta da batun dreba kiyi rayuwarki yanda kike so, ga makulli nan xa a kawo ai, rayuwarki kawai za ki dinga yi yanda kike so kanki tsaye” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh Umma” Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Yanxu shkkn har yau Aliyu ba neme ki ba ko?” Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad ta girgiza kai hawayen na sauka fuskarta tace “Ai blocking dina yayi Umma, kuma sim din ma na karya ai… Umma ban san waye yayi min haka ba kilan don a rabani da Aliyu ne.” Kuka take yi sosai kamar ranta xai fita, cikin rawar murya tace “Wallahi ina sonsa Umma, gashi yanxu an rabani da shi” Umma tace “Aa ki daina cewa an raba ku, kina fara xuwa makaranta duk yanda xa ayi ki nemi numbersa ki nema, ba kince min a kawayenki akwai me numbersa ba?” Nihad ta gyada kai hawaye na gangarowa fuskarta tace “Naf tana da numbersa, dama can sun san juna a Uk” Umma tace “Toh ko wajenta ki amsa, kar ma ko da wasa ki wani ce ai Abbanki ya maki aure ko da xa ku fara magana da shi” Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, har kusan magrib Umma na parlor da Nihad, Husnah ta kawo taliyar duk suka ci, all this while kuma khalil na kwance daki ko masallaci bai fita ba, Karfe bakwai su Naf suka dawo da makulli, Umma tace “Yauwa yan albarka, gasu nan kuwa har uku, toh sannunku, Allah ya maku albarka” ta mika ma Nihad daya, ta saka daya a jakarta sannan ta basu su ma daya, tace “Toh kun ga dare yayi ni xan koma gida, ku sai anjima ko? Ko dai a nan xa ku kwana kawai?”

23

Husnah ta kalli su Naf jin abinda Umma tace, Naf tace “Aa Umma bamu zo da kaya ba, mu ma kawai yanzu xa mu wuce, idan ya so ko gobe ne ma dawo” Umma tace “Toh shkkn, hakan ma yayi, Allah yayi maku albarka, tunda ba da mota na zo ba mu je kawai ku ajiye ni” Duk jikin Nihad yayi sanyi ganin xa su tafi su bar ta, babu yanda ta iya haka ta rakasu har bakin gate suka wuce sannan ta dawo cikin gidan tana ta kumbure kumbure. Sai da su Naf suka kai Umma har kofar gida tayi masu godiya tana sa masu albarka, sannan suka juya ita kuma ta shiga gate, Aminu na gaisheta ko bin ta kansa bata yi ba ganin Abba a tsaye balcony, karasawa balcony din tayi da sauri tace “Har ka dawo daga gidan Baffan?” Abba na kallonta daga sama har kasa yace “Daga ina kike?” Ta sauke ajiyar xuciya tace “Kayi hakuri ban ce maka xan fita ba, na fita babu izinu, wallahi Yallabai Nihad ce kira ba dare ba rana ko da yaushe cikin kuka, to shine yau da abun ya isheni nace bari dai in je in ga wani hali take ciki a gidan, kasan tun da muka kai ta ai ban koma ba” Abba dake ta sauraronta har ta kai aya yace “Toh daga yau kada ki sake xuwa gidan….” Da mamaki Umma tace “Kamar yaya fa Alhaji? Shikenan saboda iftilai ya fada ma yarinya sai ka sallama ma duniya ita, mu ma kuma ka nemi mu sallama ma duniya ita? duka duka nawa Nihad din take fisabilillahi Yallabai? Yarinyar da ko shekara ashirin bata yi ba a duniya, me ta sani akan rayuwa at this her early stage? so kake wani cutar yaje ya kamata a banza mu shiga uku? Kai kanka kasan wannan yaron tun zuwansa gidan nan ba shiri suke ba, jininsu bai ta6a haduwa ba amma ka rasa wanda zaka hadata aure da sai shi? Me yasa ma idan hadin ne baxa ka hadata da wanda bata sani ba bai santa ba, sai Dreban gidansu? Haba wannan ai babu adalaci yallabai, baka kyauta mata, wannan fa kaddararta ce, sannan ace duk soyayyar da kake mata amma ka rufe ido ka saka rayuwarta a garari kawai don an samu wasu shegu sun hada mata makirci?” Abba yayi shiru yana kallonta, can yace “Yanzu shawara kike bani a warware auren kenan?” Umma ta kalli Abba, ganin how sincerely he spoke, tayi kasa da kai tace “Ni ba haka nake nufi ba, kuma ai kai ba karamin mutum bane aji an daura aure kuma an warware sa, mutuncin da kimarka ya wuce haka, kawai dai ina jimamin abun ne, amma don Allah kar ka hanani zuwa wajenta ko ba komai zan dinga kwantar mata da hankali har ta hakura da wannan auren” Abba yace “Sumayya” Ta yi shiru tana sauraronsa, on a serious note yace “In har kina son zaman lafiya da ni toh na haneki da kara taka kafarki zuwa gidan nan, idan da wani abu xai kawota gida ba sai kin je, ina kara ja maki kunne babu ke babu gidansu, sannan ko mutuwa take ke kina tunanin zan sa a warware auren? Ai sai dai ta mutu a dakinta” Umma tace “Tabdi, to yallabai kamar yanda baxan yi shiru ba idan Nihal ce aka ma haka to Nihad ma baxan yi shiru ba don duk daya suke a wajena babu banbanci, don haka hanani zuwa gidan ‘ya ta bai taso ba….” Abba yace “Good! Don Allah gobe ma ki shirya ki kara komawa gidan, ina me tabbatar maki a nan xaki ga the other side of me” Yana kai wa nan ya juya ya shige cikin gida, Umma ta bi sa da kallo sai kuma ta kyabe baki ta bi bayansa. Su Husnah na komawa hostel duk suka shantake a saman gado babu zancen sallah balle salati, Naf ta sauke wani ajiyar xuciya tayi kasa da murya tace “Amma don Allah ku ya ku ka ga wannan drivern? Isn’t this strange?” Zully ta riƙe ha6a tace “Not as i expected, anya kuwa da gaske shine drivern? Ni fa har muka dawo ina kokwanto a raina gaskiya” Husnah tace “Kun ji ku, idan fa an bibiya irin shuwan nan ne fa wanda ba shi da galihu, farin fatarsa ce tasa ku ke kokwanto ko driver ne shi ko ba driver ba?” Zully ta kalleta tace “Aa maganar gaskiya duk da Umma ta tabbatar mana da shi din ne har xuciyata na kasa yarda, ta yaya wannan cikakken mutumin xa ace driver ne? His skin… Ko ku baku lura da shi ba, no plss he is so fresh abeg” Naf tace “Ohhhhoo ashe dai bani kadai ma lura da skin dinsa ba, ni wallahi da ba don kar inyi karya ba ma sai nake ganin kamar na ta6a ganinsa, ko me kama da shine oho” Husnah ta kyabe baki tace “Kanku ake ji” Zully tace “Kai amma gayen nan Allah ya xuba masa kyau frankly speaking, kawai mu fadi gaskiya, duk inda me kyau xai shiga shi ma xai shiga, kuma ina tabbatar maku Nihad haukan ta bai taba barin ta nutsu ta kare masa kallo ba” Husnah tayi wani dariya tace “Kai kuma da da wani zance, Ina amfanin kyau ba nera? kina jin mutum na tukin mota for a living, kun ishe ni da wani yana da kyau? kawai Nihad din ma kadai ya raina dan ya ganta er karamar yarinya ne, mu kuwa da muka kusa talatin a duniya baki ga da muka masa wankin soso da sabulu bai iya yace mana komai ba sai sissine kai da yake, ni fa baxan yi mamaki ba idan aka ce shege ne mutumin nan, kilan uwarsa a titi ta haifesa ta yarda shi shine yake ta garari har ya samu driving gidansu Nihad” Zully ta kwashe da dariya ita dai Naf bata ce komai ba, Husnah ta kalleta tace “Ya dai… Kin yi shiru” Naf ta ɗan tabe baki tace “No kawai ni dai i am not comfortable cewar shi din mere driver ne, he might definitely have a mission, haba u girls should think deep mana, sai kace ba big babes ba, ko kayan jikinsa idan kuka lura ai ba na banza bane, ni fa har takalminsa sai da na kalla, wallahi da kyar idan mutumin nan ba wani mission garesa ba” Husnah da Zully suka kwashe da dariya har da kyakyatawa, Husnah tace “Wllh shi ba kowa bane don ma ki ji in gaya maki, a wannan zamanin babu wanda xai bata lkcnsa ya zo gidan mutane for almost a year now wai da sunan mission, sai kace wani film ko novel, mission for almost one year ace ba ayi accomplishing dinsa ba har yanxu? Ke dai ki yarda ɗan talakawa ne mukus me shegen girman kai, don yaga fatarsa ja ce sannan gashinsa irin na halfcast shine yake wani feeling, ba ga ire irensa ba a can Ibadan da Lagos suna bara bakin titi, kilan shi ma daga can ya gudo arewa bayan ya girma” Zully tace “Kuma haka ne wallahi, gasu can a karkashin gadan lagos har Ibadan” Zully ta kyabe baki ta mike tace “Ni dai bari in je in yi wanka in zo in kira babyna, ba ruwana da wani batun shegen dreba can” Naf tace “Yanxu yaushe za mu je mata can din, kun san fa mun sa mata rai” Husnah tace “Mu bari kawai jibi don gobe kinga xa mu je minjibir park” Naf tace “Ehh haka ne kuma, Allah ya kai mu” Washegari tuesday da safe Nihad ta shirya tsaf xata makaranta abunta tunda ga makulli a hannunta, mayafinta ta yafa ta dau jakarta bayan ta feshe turare kusan kala biyar a jikinta ta fito daga dakin, yana jin fitowarta yayi saurain mayar da wayarsa dake hannunsa xuwa bayan kujeran da yake zaune, bata ko kallesa ba ta nufi kofa ta fita abun ta, da ido ya bi ta imagining if tsallake gate din xata yi, rabonsa da ita tun jiya bayan ya bude ma Umma gate da suka zo, can dai ya mike ya fita parlon ya tsaya bakin kofa yana kallon ikon Allah, tana isa gate ta bude jakarta ta ciro makullin tana kokarin bude gate din taji yace “Keee” bata fasa bude gate din ba ta juya ta kallesa bayan ta bude tace “Saboda baka yi karatu ba baka san muhimmancin karatu ba kana tunanin ka isa ka hana ni zuwa makaranta ko, to baka isa ba, ba a kuma haifeka ba” Tana gama fadin haka ta fice daga gate din, mamaki ne ya cika sa yayi saurin ciro makullin aljihunsa yana kallo yaga it’s intact, then where did she get a space key?? bai yi attempting bin ta ba balle har tayi showcasing altitude dinta a bakin titi, ya juya ya koma parlor filled with surprise. Ba karamin mamaki su Husnah suka yi ba ganin Nihad a school, Nihad ta zauna aji jikinta duk a sanyaye don tun da ta shigo schl ake nunata, wai ga warce ke cikin video din nan, har ta iso ajin da suke lectures idon jama’a na kanta, bata kara jin damuwan video dinta da ya bazu duniya ba sai a yanzu, dama haka abun ya tafi viral, a ajin ma sai satan kallonta ake ana kuskus, kai har ma da masu shigowa duk da ba department dinsu ba don kawai a zo a ganta, sai a sannan tayi da ta sanin fitowa, kuma fitowar ma da ɗan karamin mayafi, daga karshe dole su Naf suka dauketa suka fita makarantar xuwa hostel dinsu, Nihad ta zauna gefen gado lkci daya hawaye ya kawo idonta, Husnah tace “Kin ji ki, meye abun damuwa, abinda ba kanki farau ba kuma ba kanki za a kare ba, duk dan iskan da ya isa ya tinkare mu yace ai kece a video yaga yanda xa mu ci ubansa, ni ai baki ce min xaki taho makaranta yau ba da na hanaki don su yanxu ma suke tashen labarin, kuma ana ta jira aga kin shigo makaranta sai ga ki yau, ni ban ta6a ganin munafukai yan sa ido marasa aikin yi kamar yan makarantar nan namu ba, abu kusan sati daya amma kullum maimaita zancen ake kamar yau ya faru” Nihad ta hade kanta da gwiwa tana shessheka tace “Da na sani ban fito ba” Naf tace “Surutun mutane zai sa ki fasa rayuwarki yanda kike so? Ai ba a biye ma mutane, gwara su yi ta ganinki din har su gaji su yi shiru zancen ya mutu, yanzu dai ina kika baro ɗan rainin wayon Drivern can?” Nihad na goge idonta cikin sanyin murya tace “Toh meye hadina da wannan kuma kike tambayata” Naf tace “Aa babu hadinki da shi kam, ni ai na ga kokarinki ma da kike iya kwana gida daya da shi, da ni ce kwasan kayana xan yi in bar gidan iyaka Abba yayi bambami a wuce wajen” Nihad ta kalleta tace “Abbanmu yace xai yi disowning dina if i try anything of such” sai kuma ta fashe da kuka sosai, Naf tace “Aa ba kuka xa kiyi ba, nema ma kanki mafita xa ki yi” Nihad tace “Don Allah ku dawo gidan mu zauna gaba daya a can” Naf tace “Dama gobe muka yi ai za mu je can din” Nihad tace “Tunda na fito yau don Allah ku dau kayanku kawai mu koma can gaba-daya, the house is nothing but a living hell for me” Naf ta kalli Husnah dake ta danna wayarta bata ce komai ba tace “Husnah ya kika ga” Husnah tace “Duk yanda ku ka yi” Naf tace “Toh kawai duk mu dau kaya ko kala biyar biyar ne mu tafi can din gaba daya” Nihad tayi murmushin jin dadi tace “Amma naji dadi Nagode wllh” Zully tace “What are friends for, ai amfaninmu kenan” Nihad tayi kasa da murya tana kallon Naf tace “How about Aliyu?” Naf tace “Hmm, kinsan he is off social media tun da abun nan ya faru, to in gaya maki 3 days ago mun yi chatting da wani frnd dinsa yake ce min ai ba shi da lafiya ma” Nihad tayi narai narai da ido tace “Da gaske?” Naf tace “Wllh kuwa bari ma in nuna maki chatting din” Jawo wayarta tayi ta bude ta shiga chatting dinta da wani abokin Aliyu ta mika ma Nihad wayar, Nihad ta amshi wayar jiki a sanyaye ta dinga bin chat din, abokin gaya ma Naf halin da Aliyun ya shiga bayan faruwan lamarin yake, ya kuma ce mata har su abokanansa yayi isolating din kansa daga cikinsu ba ma social media ba kadai, abokin ya dinga nuna yanda Nihad ta kwafsa ga shi Aliyu yayi trusting dinta sosai kuma ya sa ran zai aureta duk da tulin manya manyan babes dinsa, Nihad ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka tace “I don’t know who did this to me, i don’t know who is this that ruined my happiness” Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace “Na fi ki son mu gano wanda yayi maki haka Nihad, amma abun akwai rikitarwa ni wallahi kawai zuciyata ta kasa yarda cewar ke ce a video din, ke baki zama da undies haka kamar yanda mu muke yi, sannan duk party tare muke zuwa balle ace wani partyn kika je aka maki haka, abun dai akwai confusion sosai wallahi, wanda ya sanki sosai sosai ne yayi maki wannan abun, i wish Abba xai ajiye duk wani fushi ya tsananta binciken ta ina wannan video din ya fito” Zully ta sauke ajiyar xuciya tace “Ai na dau darasi ni kam, ko daga ni sai singlet da skin tide baxan sake xama a waje ba balle undies, na saka kaina a shoes din Nihad ya fi a kirga but luckily the shoe did not even size me, waiii ai ni kashe ni kawai xa ayi a gida wallahi” Naf ta tabe baki tace “Koma waye da kansa zai tona ma kansa asiri nan ba da dadewa ba” Nihad ta share hawayen da ya ki tsaya mata tace “Pls Naf try calling Aliyu ki ga ko zai daga” Naf tace “Toh Allah ya sa ya daga, ko kuma ma dai Allah ya sa ya shiga” Contacts dinta ta shiga tayi dialing number Aliyu, ai ko ya fara ringing, gaban Nihad ya dinga faduwa tana kallon wayar, su kansu gaba daya kallon wayar suke, sai gashi kuwa ya daga, sai da Nihad taji xuciyarta ya kusa shigewa cikinta, Naf tace “Hello Aliyu what’s up?” Daga daya bangaren cikin cool voice yace “Fine Nafisah, how are you doing” Tace “Cool, ya garin” Yayi shiru, tace “Are u there?” Yayi kasa da murya yace “U saw how ur frnd played with my heart right?” Nihad ta kauda kanta hawaye sai zarya yake a fuskarta, Naf tace “Calm down Aliyu, duk wannan abun set up ne ba wani abu ba, ka fi kowa sanin halin Nihad, sannan mu da muke tare da ita always xa mu shaideta, wllh wllh Nihad bata tsayawa a cikinmu daga ita singlet balle undies, wannan lamarin da rikitarwa yake, wa ya sani ko anyi hakan ne don a raba ku tunda anji xaka turo gidansu” Aliyu yace “But i have warned her severally Nafisah, na sha ja mata kunne duk yawace yawacen zuwa party ta daina, but unfortunately bata daina ba, and ga abinda ya faru daga karshe” Naf tace “Kai wai wa yace maka a wajen party aka yi mata haka? Ko a gida baxa ayi iya yi ma mutum haka ba sai wajen party kawai? Kai dai kawai ka kyale makiyi Ali” Aliyu yace “I am so heartbroken Nafisah” Naf tace “So is she also” Yace “Tana ina yanxu?” Naf ta kalli Nihad sai kuma ta ɗan yi murmushi tace “Mun zo gidansu ne daxu ganin halin da take ciki shine nace bari dai kawai in kiraka” Yayi shiru, tace “In kai mata wayar pls?” Nan ma dai shirun yayi, tace “Don Allah kar kace A’a, ko sai kaji ta mutu xaka fara da ka sani an kai mata wayar? Wallahi she is seriously sick” Yace “Kai mata” tace “Yauwa my guy” kallon Nihad tayi tana Murmushi, ita dai Nihad ta sunkuyar da kanta kawai, Naf ta kamo hannunta ta saka mata wayar a ciki, a hankali ta kai kunne tayi sallama. Aliyu yace “Now u get the reason why nake rabaki xuwa party?” Bata iya ta ce masa komai ba ta a goge idonta, yayi kasa da murya yace “Why Nihad, why?” Cikin rawan murya tace “I don’t know how everything happened, kayi hakuri don girman Allah” yace “In yi hakuri Nihad? Ta yaya iyayena xa su amince da aurenmu bayan duk sisters dina babu warce bata ga wannan video din naki ba, hatta mum dita ta gani, innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Nihad dai bata ce komai ba, Yace “How will we mend this damage?” Nihad tace “Abbana yace min wai ya min aure” Aliyu yace “Ban gane yayi maki aure ba, kina nufin aure Abba xai maki?” Cikin kuka tace “Ehh har ya min” Aliyu yace “Stop it Nihad, yaushe yace maki haka” A raunane Nihad ta sanar masa yanzu ita da khalil suke zama gida daya, kuma Abba ya sanar mata wai yayi mata aure da shi, lkci daya ya birkice mata yace “Baby yanxu kina nufin aure aka maki, aure da drivern nan na gidanku?” Nihad ta girgiza kai da sauri tace “Ni ba a min aure da shi ba, kawai Abba ne ke fadan hakan, ni ban yarda an min aure da shi ba” Aliyu yace “Nooo, it can never be, not when i am alive, hakan baxai ta6a yiwuwa ba, na yi isolating kaina from everything na kwana biyu ne but nasan baxan ta6a iya rabuwa dake ko da nayi attempting din yin hakan ba, i know i will come back to you, kuma ko iyayena bana jin xa su hanani in aureki don sun san ina son ki, ko da nude video dinki ne yayi yawo i stil love u Nihad, and i will still marry u” Nihad dai ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai yace “Ki kulan min da kanki Nihad, do not break my heart for the second time pls, sannan ta ina xan dinga samunki ko 2 days ago i tried ur number naji switch off” a hankali tace “Xan kiraka da sabon line dina idan na koma gida” Yace “I will be expecting pls” Sallama suka yi, Naf ta amshi Wayarta tace “Alhamdulillah” Nihad ta ɗan yi murmushi, Husnah tace “Gaskiya Aliyu ya san kaddara, yanxu ke kuma sai ki san duk yanda xa kiyi ku raba jaha da wancan driver din, koma yaya xa ayi kawai ya sake ki tunda Aliyu is still willing to marry u” Nihad ta kalleta tace “Ya sakeni?? To da aurena yayi da xai sakeni? Ai kawai xama muke gida daya bisa umarnin Abba, but i am for Aliyu alone” Zully tace “Atoh, kunsan akwai wani aure da xaka ji sa kamar wasan yara, to irin auren nan naku da drivern kenan, ko ni bana kallonsa a matsayin mijin Nihad wallahi, kilan kawai Abba is playing u, amma ta yaya ma xai ce ya maki aure da dreba” Nihad tace “Toh kun ga lkci na wucewa mu tafi pls” Naf tace “Bari in kara watsa ruwa” Zully ta mike tace “Ina zuwa in kwaso kayana” daga haka ta fita daga parlon, Husnah ta kalli Nihad tayi kasa da murya tace “In baki shawara? Toh wallahi kar ki yarda su wani bi ki, gwara kiyi tafiyarki ke kadai daga baya ni kadai sai in biyoki gidan, idan ba haka ba akwai matsala” Nihad tace “Matsalar me fa?” Husnah tace “Toh shkkn ki tsaya tambayar ta me, naga dai ni kika fara sani kafin su, kuma ta dalilina kika san su, don haka kawai yanxu kice masu gidanku xa ki daga can ne xaki wuce gida kina komawa gida kuma xaki kira kice mu taho gaba daya” Nihad tace “Toh shkkn” Mikewa Husnah tayi ta fita daga dakin. Khalil ya fito compound jin ana Knocking gate, yana bude gate din ya ga Farooq a tsaye, welcoming dinsa Khalil yayi with smile all over his face, Khalil ya rufe gidan suka koma can parlor tare, Farooq na cewa “Gobe xan koma aiki shine nace bari in shigo yau dai” khalil yace “Allah sarki” Suna shiga parlon Farooq na bin ko ina da kallo yace “Ina take?” Khalil bai basa amsa ba kawai ya tafi kitchen don ya dauko masa ruwa, Farooq ya dau throw pillow da ke kan kujeran da yake kokarin zama sai ya ga Iphone, duk tunaninsa na Nihad ne duk da a gabansa Abba ya kwace Iphone din nata, Farooq ya zauna yana jujjuya wayar amma sai ya ga ba na Nihad bane, dai dai nan khalil ya fito daga kitchen with bottle water and glass cup, still yayi yana kallon Farooq…..

24

Farooq ya daga kai ya kallesa har sannan kuma wayar na hannunsa yana jujjuyawa, karasowa parlon Khalil yayi ya ajiye ruwa da glass din hannunsa, ya ki yarda su hada ido da Farooq yace “Oh kamar fa na makotanmu ne da suka shigo daxu, babu tantama wayar daya daga cikinsu ne, ban ma kula ba sai yanxu….” Farooq dake ta kallonsa ko kiftawa babu kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Now tell me who you are Khalil!!!” Khalil ya ɗan yi jim, can yace “Ban fahimce ka ba” duk wannan abun ya ki yarda su hada ido da Farooq, mikewa Farooq yayi ya dafa sa yace “Tell me what ur mission is, what is ur intention of coming to stay with us?  ka gaya min kai wanene, menene manufar xuwanka gidanmu” Sai a sannan khalil ya daga kai ya kallesa amma bai ce komai ba, Farooq yace “From day one, i know u are not who u claim u are, u lied about ur personality to us, you have a mission definitely, be it revenge, spy, Dss…. And what have u!” Khalil ya girgiza kai a hankali yace “I have no mission Farooq, and my intentions of staying with u people is pure, aiki kawai ya kai ni gidanku, baya ga shi kuma babu wani abinda ya kai ni gidanku….” Farooq na kallonsa keenly yace “I will like to know u more” Khalil ya koma ya zauna, kamar baxai ce komai ba sai kuma ya sauke ajiyar xuciya yace “Duk abinda na gaya maka a kaina a baya hakan yake, i am a nobody like i said earlier, i was just opportune to go to school, i was opportune to be a literate, nayi diploma a fce nan kano wanda har yau ban samu aiki ba, bayan wannan komai game da ni na gaya maka a baya, u can even call Habib and confirm” Farooq yace “But meyasa kace iyakarka secondary?” Khalil yace “Ina tsoron kar a ki bani aiki a gidan ne” Farooq dai kallonsa kawai yake as if forcing himself to believe him, Can yace “Wani course din kayi?” Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace “Business Admin” Farooq ya koma ya zauna kamar me naxari, ta gefen ido Khalil ke kallonsa hoping he is fully convinced, Farooq na daga kai Khalil yayi saurin dauke idonsa daga kansa, Farooq ya sauke wani ajiyar xuciya yace “Ohk then, in sha Allah xa mu yi magana da Abba, nasan xai yi iya kokarin ganin ya samar maka aiki dai dai da qualifications dinka” Khalil yace “Toh nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi” Farooq yace “Ameen” Bayan few minutes Farooq yace “Ina Nihad din?” A hankali Khalil yace “Ban san inda ta tafi ba” Da wani expression Farooq yace “Ban gane baka san inda ta tafi ba, isn’t she under ur control now?” Khalil yace “Nayi kokarin hanata fita amma ta ki” Farooq yace “What? Sai kai kuma ka saka mata ido har ta fita?” Khalil dai yayi shiru. Nihad ce ta sauka bakin gate ita da Husnah da tayi ma kawayensu karyan xata je park ta amso sako, nan kuma ta gaya ma Nihad inda xata jira ta su hadu sannan su taho gidan gaba daya, Sosai gaban Nihad ya fadi ganin motar ya Farooq a waje, Husnah ta zaro ido tace “Toh yanxu ya xa mu yi kenan?” Nihad ta hade rai tace “Toh ba daga makaranta nake ba, shiga kawai za mu yi, ai ba yawo na tafi ba” Husnah tace “Aa, kinsan yayan nan naki ba saiti garesa ba haka kawai inje ya ritsa da ni” Nihad tace “To me xai min? Kawai mu shiga idan ya so sai ki zaga bayan gidan ki nemi waje ki zauna, idan ya tafi xan fito in gaya maki sai ki shigo” Husnah tace “Toh gwara haka dai” A tare suka shiga gidan Nihad ta kulle gate, duk da yanda gabanta ke faduwa hakan bai hanata dakewa ba ta nufi cikin gidan kamar wata boss, Husnah ma dai duk a tsorace take, tayi sauri ta zaga bayan gidan ta nemi waje ta zauna, a hankali Nihad ta murda kofar parlon ta shiga ciki da sallama, ta kara kicin kicin da fuska ta karasa cikin parlon tana kallon yaya Farooq da ya bi ta da ido, ta ɗan durkusa tace “Yaya ina yini” Mikewa yayi, yayi ball da ita cikin xafin nama, yace “Daga gidan uban wa kike?” Ta fashe da kuka ta mike xata gudu ya fincikota, jikinta na rawa tace “Yaya wallahi makaranta na tafi ba ko ina ba, ka kira makarantar ma ka tambaya” Duk a gigice take don a wajen duka xa a iya ba Farooq A1, Ya kai mata wani wawan mari yace “Uban wa ya baki izinin tafiya makaranta?” Ta rushe da kuka jiki na rawa tace “Wallahi na gaya ma Umma kafin in fita, ita tace in tafi, ka kirata ka tambayeta” Hauri ya kai mata yace “Ke da Umma ce a gidan nan? Ko Umma ke da iko dake yanxu?” hankali tashe tace “Don Allah kayi hakuri yaya baxan kara ba wallahi, kaji har na rantse maka” Shi dai khalil na xaune bai ce komai ba sai kallonsu yake, Har baya Husnah ke jiyo muryar Nihad tana ihun neman agaji, ba shiri ta mike ta nufi gate da gudu tun kan Nihad tace tare su ke, da hannu farooq ya dinga makan Nihad, mari kuwa yayi mata har sau uku, kuka take iya karfinta tana basa hakuri tana cewa baxata kara fita ba, daga karshe yayi ball da ita ta mike tsaye da gudu ta shige dakinta ta sa makulli tana rusa kuka, Farooq yace “Gobe ko nan da gate ki fita in samu labari ki ga yanda xan faffasa maki jiki da belt, munafuka kawai” Ko minti uku bai kara a gidan ba yayi ma Khalil sallama, khalil ya rakasa har mota, farooq na kallonsa da kyau yace “Kar ka kuskura ka raga mata ko na second daya idan tace xata dinga kawo maka raini” Khalil ya ɗan yi murmushi kawai, Farooq yayi masa sallama ya ja motarsa ya bar layin, juyawa khalil yayi ya koma cikin gidan, ya zauna saman kujera ya dau Iphone dinsa hade da sauke ajiyar zuciya, tashi yayi ya tafi daki ya ajiye wayar, Nihad na jin ya bude kofar dakinsa ta fito da sauri, parlor ta tafi ta tabbatar da gaske yaya farooq ya tafi, sai da ta kara duba takalmansa nan ma taga babu alamar dai ya tafi, share hawayenta tayi ta nufi dakin nasa ta bude hade da turawa da karfi, tana kallonsa cike da rashin mutunci da tsiwa tace “Toh da ka kirasa ka gaya masa sai aka yi yaya? Nace sai me da ka kirasa? Mutuwa ka ga nayi bayan muguntan da yayi min? Kuma ka zata xan fasa fita in tafi makarantana ne ko in tafi duk inda nake so? To wallahi karya kake yaro don ko gobe ma ba a haifi wanda xai hanani xuwa makaranta ba kaji in gaya maka, Kuma da kai da ka kirasa da shi da dokeni Allah ya isa ban yafe maku ba….” Wani tsaki ta ja tana hararansa cike da tsana, ya girgiza kai yace “Akwai lkcn da matsayin tsayawa bakin kofar dakina ma baxa ki samu ba balle ki gwada min halinki na rashin tarbiya… bari kiji ba bakin kofar dakina ba har bangarena ma sai ya haramta gare ki wataran wallahi….” Sai kuma ya mike ya nufeta, sosai gabanta ke faduwa ganin yanda ya daure fuska amma ta dake ta tsaya bakin kofar, ya tsaya dab da ita yace “Kinsan me yasa baxan ke kulaki ba idan kina nuna rashin tarbiyar ki? Saboda ke din ban dauke ki a bakin komai ba, ban dauke ki mace ba, ba kuma kallon mace nake maki ba, kallon yar titi kuma er bariki nake maki, na dai girmama mahaifinki na amshi tayinki da yayi min don shi din mutum ne me daraja da kima a idona, banda haka ko da duk arxikin duniya aka hadani da ke wallahi wallahi baxan aureki ba don ni ba ajinki bane ta ko ina na fi karfin ki….” Nihad ta zaro ido hade da bude baki tana kallonsa, sai kuma ta cakumo kwalarsa cike da tsiwa tace “Ni kake ce ma yar titi kuma er bariki??” Shaketa yayi ya hadeta da kofa ba shiri ta sakesa gabanta na mugun faduwa, ya dinga kallonta fiercely yace “ina me baki shawara da kakkausar murya, Kar ki sake gigin kai hannunki jikina, idan ko kika sake yin wannan kuskuren to xaki sha mamakin abinda xan maki a gidan nan” Yana gama fadin haka ya turata waje ya kulle kofarsa, kiris ya rage ta fadi, tana huci bayan tayi regaining balance dinta tace “Kai din banza zaka bani shawara da kakkausar murya, aa sai dai karyayyen murya, waye kai kuma me kake takama da shi, kuma wallahi ni ba er titi bace don ina da gatana kuma da arxikin iyayena, kai kuma fa? Naga sai kayi tuki kake samun na xubawa a aljihu?” Sai kawai ta fashe da kuka ta shige dakinta ta fada kan gado tana rera kuka, duk Abba ne ya ja mata yau wai driver din gidansu ke kiranta yar titi kuma yar bariki, kuka take kamar ranta xai fita, gaba daya ta mance da wata Husnah, sai da taji ana kiran magrib sannan ta tashi ta goge idonta ta xauna saman gadon, tana jinsa ya fita masallaci, banda muguwar tsanarsa babu abinda ya cika xuciyarta, wallahi ta tsanesa, she hate him with passion, tana jin ya fita masallaci ta mike ta dau mayafinta ta fita xuwa baya wajen Husnah, wayam ta ga wajen, ta juya ta koma ciki, wayarta ta fiddo can kasan jakarta ta hau dialing number Umma, Sai da ya kusa katsewa Umma ta daga, bayan sun gaisa ta fashe da kuka tace “Umma ya farooq ya zo har gida ya zane ni saboda na tafi makaranta wai” Umma ta bude baki tace “Shi farooq din?” Cikin kuka tace “Ehh Umma” Umma tace “Yi shiru xan yi maganinsa don ubansa” Nihad na shessheka tace “Toh Umma yace kada in sake fita makarantar kuma” Umma tace “Ai ba shi ya haifeki ba da xai hanaki xuwa makaranta, kanki tsaye gobe ma ki shirya kiyi tafiyarki duk inda xa ki ba ma makaranta kadai ba, ki kyaleni da shi kawai xan yi maganinsa” Nihad tace “Toh” Umma tace “Kar ki sake asaran hawayenki a banza, kinji abinda nace maki” A hankali Nihad tace “Na ji” Umma tace “To sai da safe” Daga haka ta katse wayar, mikewa tayi direct ta tafi dakin farooq, luckily ta samesa xai fita Masallaci, strictly tace “Farooq daga yau sai yau in har ba baki kake son in maka ba bana son in sake kara ganin ƙafafuwanka a hanyar gidan Nihad, kuma babu ruwanka da harkarta da abinda take yi, in dai ba so kake in ce maka je ka ka gani, kai ko a waya na haneka da kiranta” Da mamaki Farooq ke kallonta, tace “Ni dai na gaya maka, kana kiranta ko da a waya ne Allah ya isa, balle har ya kai ka taka har gidanta, daga yau bana son magana ya sake hadaka da ita ko a ina kuwa” Tana gama fadin haka ta juya fuuu ta fice ya bi ta da kallo, a parlor ta tadda Amina xata fita, tace “Ke kuma ina xa ki?” Amina tace “Umma kati xan amso” Umma tace “Ban hanaki fesa turare haka ba idan xa ki fita? Kuma ba nace maki wannan hijabin bana son kina sa shi ba? Meye amfanin hijabi da xai dinga nuna surarka? Maza koma ki dau wani hijabin” Amina ta juya tace “Dama kyautar da hijab din xan yi Umma, kawai bana son daukan gogagge ne shi sa na sa shi yanxu” Umma tace “Maxa ki bayar idan ba haka ba in kona, bana son sake ganin ɗan iskan hijabin nan a gidan nan” Amina ta juya ta koma daki, Umma ta wuce ɓangarenta. Karfe tara da wani abu Nihad ta gama shirinta xata kwanta, har sannan taki daina kukan maganganun da Khalil ya gaya mata, wai er titi, sannan har da cewa tayinta Abba ya basa, takaici kamar ta hadiye xuciya, can ta mike ta fita daga dakin nata, a parlor ta gansa xaune yana kallo, tana harararsa tana huci tace “Ba dole ka sa tv a gaba ba tunda babu a house” Shi dai bai ko kalleta ba, tace “Kuma da kake cewa Abbana tayina yayi maka, in ka cika ɗan halas ka sakeni yanxu yanxu mana…” Sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta maka masa wani harara tace “Idan kuma baka da takarda da biro ni ina da su” Bayan few seconds yace “Ohk ashe dai kinsan da aurena a kanki?” Ta wani kyabe baki tace “Oho dai” Ya gyada kai yace “Kar ki damu akwai lokaci, kawai mu jira lokacin, ina son sai sanda kika fahimci ni ba sa’an aurenki bane sannan xan sake ki….” Tace “Aikin banza kenan, yanxu ya kamata ai, don tun yanxu nasan ni ba class dinka bace, kuma baxan ta6a xama class dinka ba” Khalil bai sake tanka ta ba, ta juya fuuu ta koma ciki, wayarta ta dauka a karkashin pillow tayi dialing number Aliyu, amma ta kasa samunsa sbda ba shi da number, Naf ta kira tace “Naf don Allah ki kira Aliyu kiyi mashi sending wannan number nawa yayi saving i want to talk to him” Naf tace “Ohk” Daga haka ta katse wayar, bayan wani lkci Naf ta sake kiran Nihad tace “Nihad na tura masa number taki yace xai kiraki” Nihad tace “Toh nagode sosai” Nihad na kwance tayi lamo kan pillow tana ta jiran kiran Aliyu, sai ga kiran nasa, farin ciki ne ya cikata ta mike xaune da sauri ta daga kiran, a hankali tayi masa sallama, ya amsa yace “How are you?” cikin sanyin murya tace “Alhmdlh” Yace “Are okay?” Lokaci daya hawaye ya kawo idonta tace “No” Da damuwa yace “Me kuma ya faru?” Tana girgiza kai hawaye na sauka idonta tace “Baxan iya jure xama waje daya da wannan drivern din ba, Har xagina sai da yayi daxu fa” Aliyu yace “Ya zage ki?” Cikin kuka tace “Ehh, wai ni ya ce ma er titi, er tasha, har da cewa Abbana tayina ya basa” Aliyu yace “Shi Drivern?” Tace “Ehh” kasa cewa komai Aliyu yayi, can yace “Wait u mean driver ne ya gaya maki wa ennan maganganun?” Nihad tace “Wallahi” Rai bace yace “Har ya kira ki da er titi?” Cikin rawan murya tace “Haka yace” Aliyu ya fuzar da iska yace “Kar ki damu, ki kwantar da hankalin ki, xan dawo Nigeria soon, and everything will soon come to an end in sha Allah” Tana share idonta tace “Nagode” Yace “Kar ki sake xubar da hawayenki, sai yayi da ya sanin zagin nan da yayi maki wallahi” Nihad tace “Sannan nace ya sakeni ya ki” Aliyu yace “He just have to, cause u are not meant for him….” Ɗan murmushin jin dadi tayi, yace “Are u on WhatsApp?” Tace “Aa xan bude yanxu” Yace “Idan kin bude, ki kirani” Tace “Ohk” Daga haka ya katse wayar, sosai hankalinta ya kwanta da abubuwan da Aliyu ya gaya mata, bayan ta bude WhatsApp din Video call suka yi da Aliyu har kusan karfe dayan dare, tun bayan da Video dinta ya tafi viral sai ranan tayi bacci cikin dadin rai. Cikin dare taji kamar ana daga pillow din da ta daura kanta, ta bude ido da sauri, bata ga kowa ba banda duhu dake dakin, gabanta ya dinga faduwa don da gaske taji kamar ana daga pillow dinta, ta mike xaune tana bin ko ina da kallo duk da duhun dake dakin, hannunta ta kai xata yi switching wutan dakin taji ta daura a kan hannun mutum, wani ihu ta fasa a mugun tsorace xata sauko daga kan gadon taga an kunna wutan dakin haske ya gauraye ko ina, yana jingine jikin bango kusa da bed side drawer, tsaye tayi bakin kofa tana kallonsa a mugun tsorace kuma da mamaki, ya daga pillownta ya dau wayar dake ƙarƙashi, xaro ido tayi ta taho da sauri tace “Wallahi kar ka kuskura ka ta6a min….” Wani mugun kallo yake mata yace “Kar ki matso kusa da ni” Ta fashe da kuka sosai tace “Wallahi ka bani wayata, kaga ba kai ka siya min ba, ba kuma da sisin ka aka siya ba” Kofa ya nufa ta koma gefe tana kuka tana kallonsa har ya fice daga dakin, da sauri ta bi sa dakinsa tana cewa “Wallahi ka bani wayata” Bude kofar bandaki taga yayi tana kallo ya tara ruwa a bucket sannan ya cilla wayar a ciki ya fito ya sa ma bandakin makulli, saboda shock kasa ce masa komai tayi ta tsaya tana kallonsa ko kiftawa babu, bai ko kalleta ba ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa saman gado…. Har gari ya waye Nihad bata yi wani bacci ba, ta ci kuka har ta gode Allah, ta sake tabbatar da cewa bata ta6a tsanar mutum a duniya irin khalil ba, karfe takwas saura taji kamar ana welding a bakin gate, ta mike da kyar ta fito parlor ta tafi kofar fita parlorn, tsaye ta gansa a compound, ga kuma me welder da me canza lock din gate suna ta aiki a bakin gate, juyawa tayi da sauri hawaye cike idonta ta koma dakinta, ta xauna gefen gado tana shessheka, ta shi tayi ta tafi dakinsa ta bude kofar bandakin ta duba bucket din da ya jefa wayarta taga babu wayar a ciki, ta fito ta ga karamar wayarsa a gefen gado, da sauri ta dauka ta fito ta shige dakinta, Call logs ta shiga taga number anyi Saving da Nadeeyah with love Emoji, kallon Number ta dinga yi sai kuma tayi scrolling xuwa kasa taga number Nihal wanda ko jiya ma sun yi waya, shiga tayi taga maganar minti nawa suka yi taga kusan minti goma, dialing number tayi yana fara ring Nihal ta daga, Rai bace Nihad tace “Ban san ke munafuka bace kuma algunguma sai yanxu Nihal, kuma in sha Allahu ke abinda xai sameki sai ya fi wanda ya sameni ki rubuta ki ajiye, don naga kamar farin ciki kike da condition din da nake ciki, banda kina farin ciki da abinda ya sameni wayar me xaki dinga yi da enemy din nan nawa? Me yake gaya maki, me kike gaya masa?” Nihal tace “Haba Nihad, what is this u are saying? Da kinsan wayar da nakeyi da shi da baki kirani kina gaggaya min wa ennan maganganun ba, kema kinsan baxan ta6a farin ciki da bakin cikin ki ba…” A fusace Nihad tace “Babu abinda xa ki gaya min da xai gamshe ni, kuma xan ga ta inda xaki sake waya da shi” Nihal tace “Toh shikenan, amma ki sani ko na kirasa ke nake cewa ya ba waya sai baxai baki ba” Nihad tace “Oho wannan ke da shi ya shafa” Nihal tace “Jibi xa mu yi hutu, and we need to talk idan na dawo Nihad” Nihad bata kuma sauraronta ba tayi ending call din, Yanxu tasan xamanta da kowa a duniya, Abba ne oo, Mumy, Ya farooq, Nihal, duk ashe ba sonta suke ba, kuka sosai ta saki, sai kuma tayi blocking number Nihal a wayar sannan ta bi duk calls din ta goge, Kallon Number Nadeeyah ta dinga yi ganin how special the line is with multiple 2’s, can ta ja wani tsaki ta danna masa block sannan tayi deleting shi ma gaba daya a call logs, sai kuma ta tuna cewar she needs to tell Aliyu cewar ya amshe mata waya incase zai yi ta nemanta, dialing number Aliyu ta fara yi, ko digit hudu bata sa ba sai taga number ya fito barau barau amma ba tare da suna ba, still tayi tana ta kallon screen din karamar wayar baki bude da mugun mamaki, to ko dai jiya da ya dau wayarta ne ya kwashe number??? lkci daya ta juya da sauri jin taku, wani irin faduwa gabanta yayi ganinsa a bakin kofar dakin yana kallonta, cikin rikicewa ta ajiye wayar hannunta gefen gadon gabanta na faduwa, shigowa dakin taga zai yi, ta marairaice ta koma can karshen bangon dakin xuciyarta na bugawa tana kallonsa amma hakan bai hanata hade rai ba, ya kalli wayarsa sannan ya kalleta, daukar wayar taga xai yi ta nufi kofa a guje yayi saurin fixgota, kuka ta saki ta rirrike hannunsa tace “Ni wallahi ka sakeni, me kaga nayi kuma again, ba yar uwata na zo inyi magana da ba na dade ban ji muryarta ba….”

25

Khalil na ganin number dake saman screen dinsa ya kalleta da sauri, bai san lkcn da ya saketa ba ya shiga call logs dinsa hurriedly to check if tayi sending kiran, Nihad tayi using opportunity din saketan da yayi ta fice daga dakin a guje ta shige nata ta kulle, jingina tayi da kofar tana maida numfashi with surprise written all over her face, why did Aliyu’s number appeared on his phone daga fara dialing, how will that be? lokaci daya tayi assuring kanta cewa ai jiya ne ya kwashe number a wayarta bayan ya dauke mata wayar, karasawa tayi ta zauna gefen gado da tunani iri iri a ranta, does it mean bayan ya jefa wayar cikin ruwan cirowa yayi ya busar kenan ya shiga call logs dinta ya dau number Aliyun? Dama kuma da Aliyu da Umma sai su Husnah kadai tayi magana da a sabon wayar, numbobinsu kadai ne a wayar, tsaki ta ja ta mike ta tafi kusa da window ta tsaya, why will she even be stressing her self, takaicinta guda yanxu da bata tsoma wayar tasa cikin ruwa ta fito da sauri ba, yunwan da ya addabeta wajen karfe sha biyu ya sa ta bude kofar dakinta a hankali ta fito parlor, bata gansa a parlon ba ta saci kallon kofar dakinsa sai kuma ta shige kitchen da sauri, ta bayan windown kitchen din ta hangosa xaune saman farin kujera yana waya, kasa kunne tayi amma babu abinda take ji saboda window din kitchen din dake a kulle, idan kuma tace xata bude xata yi drawing attention dinsa, juyawa tayi ta fice daga kitchen din ta nufi kofar fita parlor, cikin sanda ta isa har ta wajen da yake ta tsaya inda baxai hangota ba don backing wajen yayi, kawai tana son tabbatar da cewa da Nihal yake waya kafin ta san irin rashin mutuncin da xata mata sannan kuma ta hadata da Umma, ji tayi yayi kasa da murya yana cewa “Amma Baby me yasa kike tunanin ina Nigeria?? Wani yace maki ya gan ni a Naija ne?” Gwalo ido Nihad tayi ta bude baki tana kallonsa, murmushi taga yayi yace “Ranan da na dawo ai bayan wajen Mamina wajen ki xan taho har sai kince min in tafi, kinga ko abinci ma kadan xan ci na Mami…. Naki ne xan ci in koshi” Nihad dai ta kasa rufe baki sai kallonsa take da mugun mamaki, cikin cool voice dinsa yace “Nasani Nadeeyah…. In sha Allah ina dawowa babu bata lokaci kuma kamar yanda na maki alƙawari xa mu yi aure….” Sai a sannan Nihad tayi wani dariya tana tafe hannu tace “Yau naga ikon Allah, babba da shirga karya” juyawa yayi da sauri yana kallonta, ta wani hade rai tace “Katon mutumi da kai baka ji kunyar irin wannan karyar da ka zauna kake laftawa ba? Wato ba a Nigeria kake ba, na shiga uku ku ji wai baya Nigeria, to a wani kasar kake? ko da yake ita ce babban mahaukaciyar da ta tsaya take sauraronka har kake fesa mata wannan mugun karya haka…” Tuni khalil ya katse wayar ya mike yana mata wani kallo yace “Kar ki sake kiranta da mahaukaciya” A fusace Nihad tace “Ance mata mahaukaciyar me xaka yi? idan waya xaka yi da ita ka fita titi kayi mana ai dai naga nan gidan Ubana ne ko? Ko Abbana ce maka yayi ka zo ka dinga masa waya da mata a gidansa?” Khalil yace “Zaki gane ke ce mahaukaciya ba ita ba” Cike da tsiwa tace “Sai dai ku ne mahaukata ba ni ba wallahi, kuma kar ka sake kiran wata banzan mace a gidan Abbana” Bai kuma ce mata komai ba ya gyada kai kawai ya bar wajen, ta bi sa da wani harara, sai kuma ta ja tsaki tace “Wai baya Nigeria, kai har kana da kudin fita nan nan Niger ma balle wata kasar?? Ai har ka mutu ko kamshin airport baxa ka ta6a ji ba don ma kaji in gaya maka” Shi dai tuni ya bar wajen don Nadeeyah na ta kiransa a waya, Bin bayansa Nihad tayi tace “Dama idan waya xaka yi ka fita can titi kaje kayi ba dai a gidan Abbana ba na gaya maka” kafin ma ta shigo parlorn har ya shiga dakinsa ya kulle da makulli, ta ja tsaki tace “Aikin banza” kitchen ta tafi ta dafa indomie, tana kitchen din taji ana kwankwasa gate, ta ɗan leka parlor sai gashi ya fito daga dakinsa ya fita compound, kashe gas din tayi da sauri ta fito daga kitchen din ta shige dakinsa, gun wayarsa dake saman gado ta nufa, sbda tsoro har wani rawa hannnunta yake ta dau wayar ta shiga call log don taga da warce yake waya har yake karyan ba a Nigeria yake ba, Nadeeyah ta gani, mamaki ne ya cika ta don ai tayi blocking number jiya, ai ko yau sai ta tona masa asiri ba dai baya Nigeria ba, xai ga aiki da cikawa yanxun nan, dialing number tayi har ya gama ring ba a daga ba, ta sake kira nan ma yana ta ringing no response… Khalil na isa gate din ya bude, Husnah ce tsaye bakin gate din tana sanye da Hijab har kasa, ta ɗan yi murmushi tana kallonsa tace “Ina yini?” Babu yabo babu fallasa yace “Daga ina kuma wa kike nema?” Tana Murmushi still tace “Ba lallai dama ka nuna ka gane ni ba duk da nasan ka gane ni, dama ba wani abu ya kawo ni nan ba illa in baka hakuri akan abinda muka maka shekaranjiya ni da kawayena, tun ranan wallahi ban samu nutsuwa ba sabda walakanta d’an Adam ba shi daga cikin halina, ba tarbiyar gidanmu bane, ni ban ta6a ba sai ranan, kuma mun yi hakan ne kawai don mu faranta ma kawar mu kamar yanda ta bukaci mu yi, daga baya na gane bamu kyauta ba biye mata da muka yi muka ci maka mutunci…. Nayi magana da sauran kawayena mu zo mu baka hakuri ko ba tare da sanin Nihad din ba amma sun nuna baxa su iya xuwa ba shine ni na taso da kaina in zo har nan in baka hakuri, don girman Allah kayi hakuri ka yafe mana gaba daya, ko a jiya ma da ta fito xuwa makaranta idan ka lura ai da wuri ta dawo, to mu muka sa ta gaba muna nuna mata illan kin yi ma miji biyayya ko da kuwa baka son shi, dalilin barin ta makaranta kenan da wuri ta dawo gida, yanxu haka bata san xan xo nan ba, kawai kaina tsaye na taho….” Khalil yace “A takaice dai me ya kawo ki nan Malama?” Ta sauke idonta a hankali tace “In baka hakurin abinda muka yi maka ni da kawayena, kuma mu nemi gafararka” Yace “Toh rike hakurin ki, su ma ki mayar masu da nasu, don ba ku kai ku min abinda xai bata min rai har ki xo bani hakuri ba” Ta daga kai ta kallesa tace “Baka dai hakuran ba kenan?” Da wani expression yace “Shine nace kun min wani abu ne da ya bata min rai har xa ki zo bani hakuri tukunna?” Ta langwabar da kai tace “By the way, sunana Asma’u, amma kawayena na kirana da Husnah….” Ko rufe baki bata yi ba ya kulle gate din almost on her face ya juya ya koma cikin gida. Yana shiga daki ya dau wayarsa dake ring ganin Nadeeyah ce ke kiransa ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren tace “I saw ur calls” Ya d’an yi shiru, da mamaki yace “My calls?” Tace “Yea, minutes ago” Yace “Ohh, sorry mistake ne” Tace “Ohk, sai anjima kenan?” Yace “Sure” Katse wayar tayi, ya hau duba call logs dinsa da sauri, Nadeeyah kawai ya ga ta kira, ya kalli kofar dakin ko kiftawa baya yi. Da yamma Khalil ya shirya xai tafi can gida saboda kiransa da Abba yayi, Nihad dai na daki abun duniya duk ya bi ya isheta, da ta gaji da wannan bangaren gadon ta koma daya bangaren, ko kuma ta sauka kasa ta zauna, ita bata saba xama waje daya kamar jaririya ba, all through the week ko bata da lectures sai ta shiga school, daga school kuma su tafi yawonsu da su Husnah, tun goma na safe idan ta fita gida dama sai magariba take dawowa, sai gashi yanxu wai ita ce daga daki sai bandaki, sannan babu waya ba komai, ita da 24/7 wayarta na hannunta, tunanin hakan yasa ta rushe da kuka tana jin kamar ta samu wanda xai harbe mata khalil ta huta, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a duniyar, why is this happening to her, kuka ta dinga rerawa tana bubbuga kafa. Khalil na isa gida a waje yayi parking Aminu na hangosa ya taso da sauri yana daddaga hannu sama yana washe hakora yace “Sai kayi oga….” Khalil ya kashe motar ya sauko, Aminu ya kyalkyale da dariya yace “Shekaranjiya Saminu ya jiyo mana wannan lamari me ban mamaki daga bakin Hafsah me aiki, yanzu haka aka yi dama?” Khalil yace “Wani lamari kenan?” Aminu ya washe baki yace “Ahh haba ni ne fa Aminu, meye kuma xaka boye min banda abun ka” murmushi khalil yayi yace “Ba abinda xa a boye maka” Aminu ya ja sa har xuwa kan bencinsa yace “Shi kansa bencin nan yasan ba ka a gidan nan mutumina” Khalil ya shafa kai yace “Toh ya ake ciki?” Aminu yace “Ana nan dai yanda ka tafi ka bari in gaya maka, har yanzu kasan Alhaji bai fara fita aiki ba, yanxu haka yana da baki yan zuwa jaje a parlonsa, Ita kuwa uwar Nihad din na can kwance ba lafiya har da karin ruwa don har gida likitan ke xuwa dubata, kanwarta me shegen kama da ita din nan ce ke wajenta yanxu haka, Umma kuma jiya da sassafe ta fita a mota bata dubi halin da abokiyar xamanta ke ciki ba sai ga ta ta dawo mota duk ya lotse wai tayi dan karamin hatsari a hanya amma babu abinda ya sameta, ko kwarzane bata yi ba, xancen da nake maka har yanxu Alhaji bai sani ba, ko mu tace kar mu yi magana, baka ga inda taje tayi parking motar ba don kar ya gani” Khalil dai bai ce komai ba, amma Mumy da aka ce bata da lafiya ce ta tsaya masa a rai, Aminu ya tuntsire da dariya yace “Yanxu don Allah yaya zaman naku da yarinyar nan, ni fa na dauka xa ace ta kashe kanta da taga Alhaji ya aura maka ita, kiyayya ce fa ta gaske take maka” Khalil yace “Ni ban kashe kaina ba sai ita xata kashe kanta?” Dariya sosai Aminu yake yace “Gaskiya kam kai aka cuta, anyi mugun kwararka mutumina, yanxu fa har yara da jikoki sai sun ga wannan videon nata da yayi yawo a yanar gizo, tabo ne da baxai ta6a goguwa ba har karshen rayuwarta, kai don ma dai iyayenka ba yan boko bane basa hawa yanar gizo, ai da wallahi baxa su amince ka auri yarinyar nan ba, ko kai baka kare ma videon kallo bane? Saminu fa har jawo mana shi yayi kusa kusa yanda xa mu gani da kyau, ita wannan ba ma wani amfani ta sake yawo da kaya a jikinta bayan duk duniya sun san surarta” Lkci daya mood din khalil ya sauya, Aminu ya girgiza kai yace “Tirr, amma a gaskiya hada zuri’a da wannan yarinyar ma bala’i ne, banda kana jin nauyin ubanta me xai kai ka? Kai da kake da mutunci haka, Sauran titi ce fa, duk ta yasar da darajan nata ta rarrabar a titi, nan nan nan ranan ni da kai muka ganta da asuba ta dawo daga sheka ayarta tana ta rabe rabe bakin gate, kuma ta sha yin hakan tun ma baka xo gidan nan ba ya fi a kirga, labarinta ma ai sai a bakin Habibu, nasan bai san da wannan hadin ba da ya zuga ka yace kar ka yarda komin me ubanta xai ce maka, shi ma dai Alhajin ya so kansa da yawa, bai kuma yi maka adalci ba, ya rasa warce xai aura mata sai Nihad bayan ga salihar er uwarta Nihal, lalatacciya ce fa babu wanda bai sani ba, ni wallahi da kudi ma baxan amince in aureta ba balle kyauta….” Mikewa Khalil yyi ya nufi cikin gidan, Aminu yace “Auu har mun gama hirar? Ko xaka shiga ka fito?” Khalil na isa balcony ya kira Abba ya sanar masa yana gidan, Abba yace ya basa few minutes yana da baki, Khalil ya amsa masa da to sannan ya xauna saman kujeran dake wajen, har wani sarawa yaji kansa ke yi da maganganun Aminu, yana ta xaune balcony din sai ga Aunty Jamila ta fito xata kwaso kayan shanya da tayi a baya, mikewa yayi , ganinsa tace “Aa kai ne a nan…” Gaisheta yayi, ta amsa tace “Ya gida?” Yace “Alhamdulillah” Tace “Toh ka shiga ciki mana” kawai murmushi yayi bai ce komai ba, tace “Ka karasa Sudais ya kai ka ka duba Mumy kasan bata ji dadi ba” yace “Subhanallah, amma da sauki ko?” Tace “Alhmdlh” yace “Toh Allah ya bata lafiya” Tace “Ameen” tana barin wajen ya shiga parlon kansa a kasa, Sudais na ganinsa ya taho da gudu ya rungumesa yace “Uncle mun daina ganinka” Ya shafa kansa yace “Gani na zo ai, ina fadil?” Yace “Yana wajen Mumynmu bata da lafiya” Khalil yace “Toh kai ni in gaisheta” Har part din Mumy Sudais ya kai sa, yayi sallama bakin kofar parlon, Wata frnd din Mumy ta amsa, shiga parlon yayi kansa a kasa ya nemi saman carpet ya xauna ya gaishesu, duk suka amsa, Mumy dake xaune parlon an cire mata last drip dai kallonsa kawai take, Bayan few seconds ya daga kai ya kalleta yace “Ya jikin Mumy?” Cikin sanyin murya tace “Alhamdulillah Ibrahim, ya gida?” Ya sauke kansa yace “Lafiya lau, Allah Ubangiji ya kara Lafiya” Tace “Ameen Nagode” Bai kuma cewa komai ba, Hajiya Zara ta mike ta fita daga parlon, bayan few minutes Mumy tace “Kayi hakuri Ibrahim, an cuceka an hadaka aure da warce bata cacanceka ba, nasan baka da yanda xaka yi ne kuma baxa ka iya k’in amsan tayinta da mahaifinta yayi maka ba….” Da sauri yace “Aa Mumy, Allah ne ya tsara haka, kuma muna fatan Allahn yasa hakan shine mafi alkhairi” Hawaye na sauka idon Mumy tace “Ni kam bani da abinda xan ce maka sai dai in baka hakuri akan abinda Alhaji ya maka, sannan ni baxan ce kayi hakuri da Nihad ba, idan kaga baxa ka iya ba ko xaka cutu ina me goya maka bayan ka saketa kawai ta dawo gida….” Cike da karfin hali Khalil yace “In sha Allah baxa ayi haka ba Mumy” Mumy ta share idonta bata kuma cewa komai ba, Wani duniyar tunani khalil ya fada gaba daya jikinsa yayi sanyi, he couldn’t even think straight, kiran sallahn magrib da ake ne yasa ya dago kai ya kalli Mumy ya ga kallonsa take, a hankali yace “Xan je masallaci Mumy, Allah ya kara lafiya” Tace “Ameen Ibrahim nagode” Tashi yayi a hankali ya fita daga parlon, Umma ya tarar a main parlor ta masa wani kallo sai kuma ta ja tsaki tayi hanyar kitchen, ya bi ta da ido kawai. Bayan an idar da sallan magrib tare suka shigo gidan da Abba har xuwa parlonsa, Khalil ya xauna ya gaida Abba da ladabi, Abba ya amsa yace “Ya gidan?” Yace “Alhamdulillah” Abba yace “Ya kamata xuwa gobe ku shirya ka tafi da ita can garinku ta gaida iyayenka, bayan kwana biyu sai ku dawo” Khalil ya ɗan yi jim, sai kuma ya dago ya kalli Abba yace “Toh in sha Allah Alhaji, Allah ya kai mu goben” Abba yace “Ameen, farooq ya zo min da wani batu jiya amma sai kun dawo dai” Khalil yace “Toh Alhaji, nagode” Abba ya ciro dubu dari ya mika masa yace “Ka yi full tank, sannan kayi ma iyayenka tsaraba da sauran” Khalil ya sa hannu biyu ya amsa yace “Toh Allah ya saka da alkhairi Alhaji” Abba yace “Ameen, Allah ya maka albarka” Khalil ya amsa da “Ameen” a tare suka fito main parlor da Abba, Umma ta fito daga kitchen kenan ganinsa da Abba tace “Aa Ibrahim har xa ka tafi, bari to ga abinci ka kai ma Nihad tunda an gama” Ya kalleta yace “Toh” Komawa kitchen tayi da sauri, Abba dai ya zauna parlon har sannan kana ganinsa xaka san yana cikin damuwa, dake xuciyarsa kawai yake yana ma Nihad wasu abubuwan as form of punishment amma shi yasan sonta a jininsa yake, but he can’t help it, tayi disappointing dinsa sannan ta xubar masa da mutunci a idon duniya, Umma ta cika warmer da abinci, sannan ga wani warmer din daban na kaza ta fito parlor, sai da ta bubbude warmer din tana kallon khalil cike da damuwa tace “Don Allah idan ka je ka lallabata ta ci abincin nan, duk ta rame ta lalace wallahi, Shekaranjiya da naje ma da ya na samu ta ci abincin, yanxu kam ban san halin da take ciki ba baiwar Allah, wa yasani ma ko bata cin komai” Shi dai Abba bai ce komai ba, khalil kuwa banda kallonta babu abinda yake, Abba ya mike yace “Ka jirani Ibrahim” Khalil yace “Toh Abba” Ba a dau lkci ba sai ga shi ya dawo da dubu talatin ya mika ma Khalil yace “Ka siya mata carton din maltina da na madaran gwangwani” Ta gefen ido Umma ke ta kallon Abba, Khalil ya amsa yace “Toh In sha Allah Abba” Abba yace “Sai da safe, Allah ya tsare” Juyawa Umma tayi ta shige kitchen ta tsaya jikin cabinet kamar me nazari. Khalil na isa gida sai da yayi isha a masallacin dake layin sannan ya shiga gida da motar yayi parking, bayan ya kulle gate din ya dawo ya fiddo abincin daga cikin mota ya kai parlor ya sake fitowa ya kai maltina da madara parlon ya ajiye sannan ya kulle gidan, xaunawa yayi saman kujera ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, da yasan haka abubuwa xa su kasance masa da bai yarda ya fara shigowa garin kano ba, where will he even start this amendment from?? Babu warce ta tsaya masa a rai sai Mahaifiyarsa, this seriously isn’t going to be easy, Mikewa yayi daga karshe  ya nufi dakinsa yana tafiya a hankali, har ya bude kofar sai kuma ya fasa shiga, ya dawo ya bude dakinta, zaune ya ganta a kasa idonta yayi bulu bulu alamar tayi kukan gaske yau, ya tabe baki ya kulle kofar ya koma parlor kawai yayi xamansa, tashi Nihad tayi ta bi bayansa, ta tsaya bayan kujera tana shesshekar kuka…, ya ɗan daga kai ya kalleta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace “Da bashi ne?” Wani bakin ciki ya rufeta a fusace tace “Ban sani ba, ka zata kai ka isa ka dinga punishing dina? Waya biyu aka kawo min gidan nan ka salwantar min da su, toh wallahi zaka sha mamakin abinda xai faru idan baka bani wayata ba” Mikewa yayi ya bar mata parlon ya shige dakinsa ya kulle, kuka kawai take kamar ranta xai fita, babban tashin hankalinta shine Aliyu da xai yi ta kiranta ya ji a kashe, yanxu babu ta inda xata yi ta iya kiransa, da ma baya kulle gate ne ko makota ita sai ta shiga don ta kira Aliyu, amma ko daxu da xai fita kulleta yayi ta ciki, ko bin ta kan warmers din abincin dake parlon bata yi ba ta koma daki ta dinga kuka kamar ranta zai fita, har kusan karfe biyun dare Nihad bata yi bacci ba, abun duniya ya taru yayi mata yawa, last week fa warhaka tana baccinta peacefully a saman gadonta, tashi tayi a hankali ta goge idonta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar dakin nata ta fito, taga ya kashe duk wutan gidan, ko ina yayi duhu, tana lalubawa ta tafi hanyar dakinsa ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude ta shiga dakin, nan ma dai ya kashe fitilar, sai da ta fara tattaba socket din dakin cikin duhun ko xata ga karamar wayarsa a jiki taga babu, cikin sanda ta nufi gadon dakin ta durkusa, hannu ta kai xata laluba kan gadon taji hannunta saman broad haired chest dinsa, zaro ido tayi a mugun tsorace xata mike ta gudu ya fixgota ta fado saman gadon daga gefensa, yayi kneeling dai dai inda take har tana jiyo respiration dinsa, yana kallonta cikin duhun kafin yace komai jikinta na rawa tace “Wayyo na shiga uku, wallahi torchlight nake nema xan je in sha ruwa a kitchen….”

26

Kunna wutan dakin Khalil yayi ya koma gefen gadon ya zauna fuskarsa daure yace “Ohk, dauki torchlight din ki fita” Har sannan gabanta bai daina faduwa ba, a hankali ta dawo edge din gadon tana satan kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace “Dauki ki fita nace” Ta sauke ƙafafuwanta kasa a hankali tana kallon karamar wayarsa da ta hango gefen pillow, Ya jefa mata wani mugun kallo yace “Ko bayan shi da wani abun da kike so ne?” Ta ɗan turo baki tace “Ga can torchlight din da xan ara” Ya kalli inda take nuna masa, sai kuma yace “Ohk” dauko wayar tasa yayi ya mika mata yana kallonta, a hankali ta kai hannu xata amsa, da karfi ya buge mata hannu da wayar, da sauri ta janye hannunta ta bude baki tana kallonsa tana yarfe hannun, ya mike ya dau shirt dinsa ya saka sannan ya nufi kofa ya bude mata da kyau, fuska daure yace “Zo ki fita” Ta fashe da kuka tace “Shine har sai ka kwala min waya a hannuna? Sai kace kai baka shigo min daki idan ina bacci” Cikin kakkausar murya yace “Zo ki fita nace” ganin babu alamar wasa tattare da shi ta mike ta nufi kofar hawaye cike idonta, tana fita ta juyo ta kallesa tace “Ban yafe buge min hannu da kayi da shegen wayarka ba, don ma ka samu xa a ari torchlight din shegen wayar” Yi yayi kamar xai bi ta, ta ruga ta shige dakinta ta kulle kofar da sauri tana maida numfashi. Washegari da yamma bayan Khalil ya gama shiryawa yanda xai je ya sanar ma Nihad ta shirya xa su yi tafiya ne babban aiki a wajensa, tun safe ya fice gidan don kawai ya daina ganinta, ko awa daya bai yi da dawowa ba kuma bai ji motsinta ba bai kuma duba dakin nata ba, daga karshe kawai yayi dialing number Nihal tana dagawa ta gaishesa ya amsa yace “Ya makaranta?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Kin dawo ne?” Tace “Aa ya farooq yace min yana hanya” Khalil yace “Toh Allah ya kawo ku lafiya” Tace “Ameen” Shafa kansa yayi yace “Dama so nake ki sanar ma er uwarki ta shirya kayanta kala uku xa mu je can gida, kawai haka xa ki ce mata” A hankali Nihal tace “Baxa ka iya gaya mata ba kai kenan?” A takaice yace “Ehh” Tace “Toh Shkkn, ka bata wayar” yace “Zan kai mata yanzu” Nihal tace “Ohk” mikewa yayi ya tafi dakin Nihad ya bude kofar dakin, tana tsaye jikin window abun duniya ya tarar mata, har ta gaji da kuka, tun da garin Allah ya waye ruwa kawai take ta sha don ta gaji da cin indomie gashi babu kayan miya a gidan, yunwa take ji sosai, jin ya bude mata kofa ta juya a fusace tace “Malam ka daina shigo min daki kanka tsaye kamar wata matarka, idan ma wani abun ne baxa ka kwankwasa ka jira in fito ba?? Balle ma ni bana son kana min magana a gidan nan har abada” Kallonta kawai yake, ta murguda baki ta ci gaba da kallon tsuntsayen da take kallo ta window, khalil ya sa handsfree a wayar hannunsa yana daga inda yake tsaye yace “Gashi ki gaya mata” Nihal tace “Hello Nihad” Nihad ta wani tamke fuska tace “Menene??” Nihal tace “Abba yace ki shirya kayanki xa ku je can gidan” Nihad ta buda ido sosai tace “Don Allah da gaske?” Nihal tace “Ehh” Wani farin ciki ne ya rufeta, cike da murna tace “Ai kayana a hade suke ban ciro su a akwatin ba” Khalil bai bari Nihal tace komai ba ya katse wayar ya juya ya fita, kan kace me Nihad ta gama rurrufe akwatunanta ta ja su ta kai parlor gaba daya, ji take kamar mafarki wai xata koma gida, she sooo happy, da ido Khalil ya dinga bin ta, haka ta ja akwatunan duk da nauyinsu har gun mota sannan ta koma ta dauko handbag dinta, xata fita khalil dake ta bin ta da kallo yace “Duk wa enan kayan ina xa ki kai su?” Tayi masa wani shegen kallo tace “Ohk da so kayi in bar maka wasu ka dauka kaje ka siyar ka samu na xubawa a aljihu? To baxa a bari ba” tana gama fadin haka ta fice ta tafi jikin mota tana jiransa, bayan few minutes sai ga shi ya fito, cike da gadara tace “Bude min booth Malam” Ba musu ya bude mata booth din, ta daddage ta shigar da akwatunanta booth da duk karfin da Allah ya bata, back seat ta bude ta shiga ta zauna farin ciki fal ranta, ta lumshe ido tare da sauke wani ajiyar xuciya, at last…. Ganin ya ki tada motar ta ki ce masa komai, don ita kam baxata biyesa ba tunda dai ta samu xata koma gida, bayan few minutes ya sauka motar yaje ya bude gate, lumshe ido Nihad tayi bayan ya ja motar sun bar compound din, ya sauka ya kulle gidan sannan ya dawo cikin motar, Ta madubi yake ta kallonta kai kana ganinta kasan she is over happy, tun Nihad na tunanin traffic yake kaucewa ganin hanyar da suke ta bi har dai taga sun dau hanyar da baxae ta6a kai ka gidansu ba, ta dake tace “Malam mance hanyar gidan namu kayi ne ko kuma Shaye shaye ka fara? Ba ga can hanyar da xaka bi ba” Banza yayi mata, a mugun fusace tace “Tunda kai ba kurma bane nasan kana ji na, ka gaya min ta ina hanyar nan da muke bi xai kai mu gida??” Nan ma yaki tanka ta, mamaki ne ya cika Nihad ta dinga bin hanyar da kallo, to ina xai kai ta, bata kuma ce masa komai ba tana ta kallon ikon Allah, bayan tafiyar kusan minti arba’in taga sun shigo wani karamin gari da xa a iya kiransa da kauye, she was more than shock, wanda hakan yasa ta kasa ce masa komai, sae kallonsa take baki bude, a wani gida da aka xagaye da katangar kasa yayi parking bayan sun lula can cikin garin, ya kashe motar, sannan ya bude ya sauka, duk motar tayi butu butu da jan kasa, ga yara da ke ta bin motar tun shigowarsu karamin garin, har Khalil yayi parking, yaran duk suka kewaye motar suna murnan ganin mota, Haka Nihad ta dinga kallon inda suke with shock, khalil ya bude side dinta yana mata kallon cikin ido yace “Sauko” Ta fashe da wani matsanancin kuka tace “In sauko in yi me?? Wallahi baxan sauko ba” Duk da dariyar da ta basa haka ya dake ya hade rai yace “Baxa ki sauko ba??” Cikin kuka tace “Ehh, ina ne nan din da ka kawo ni da kake cewa in sauko?” A takaice yace “Garin mu!!! don ki tabbatar mu ma muna da gida, dolenki kuma ki sauko ki gaida iyayena, sannan adadin kayan da kika kwaso adadin kwanakin da xa mu yi a garin nan kenan” Ta fashe da kuka hankali tashe tace “Na shiga uku na lalace….” Ko sauraronta bai kuma yi ba ya xaga bayan booth ya hau sauke akwatunanta, ta gwale ido ganin yayi hanyar shiga cikin gidan da shi, kuka take kamar ranta xai fita tana cewa ta shiga uku ta lalace, tun da aka haifeta ita kam sai dai taga irin wajajen nan a Tv, dama da gaske akwai irin garin nan a reality?? Ba a dau lokaci ba sai gashi ya fito da wata dattijuwa tana washe baki ta taho ba ko takalmi a kafarta tana cewa “Lale lale” Sake baki Nihad tayi tana kallonta a tsorace, matar ta karaso kusa da mota tace “Sannu da xuwa, lale lale” Nihad ta hadiye wani abu da kyar tace “Ina yini?” Khalil dake tsaye gefen matan yace “Sauko” Da kyar tayi karfin halin saukowa daga motar, kana ganinta kasan a tsorace take, matar tace “Bismillah mu shiga ciki, lale” Tana jan kafa ta bi matar xuwa cikin gidan, Khalil ya bi ta da kallo yana wani side smile, sai da Nihad ta duka kafin ta iya shiga cikin gidan, nan taga hut a jere kusan hudu a karamin tsakar gidan, lkci daya tsikar jikinta ya dinga tashi taji ta fara jin sanyi kamar xaxxabi xae rufeta, Matar ta shiga wani hut din tace “Bismillah shigo ciki….” Nan ma sai da Nihad ta duka sosai kafin ta iya shiga hut din, banda karnin nono babu abinda hut din yake, sae da ta kara gwalo ido don ta tabbatar kasa ne kwance a dakin kamar waje, sai gadon kara an shimfida wani yamutsatsen zanin gado a kai, daga can gefe kuma kwarya ne sun kusa goma an jera, Matar ta dinga nuna ma Nihad gefen gadon karan wai ta xauna, cike da karfin hali Nihad ta xauna tana kokarin ganin bata fashe da kukan dake cin ta ba, dattijuwar ta fita daga dakin tana cewa “Bari a kawo maki ruwa” Wani hawaye ya xubo idon Nihad a hankali tace “Na shiga uku na lalace” da sauri ta goge idonta ganin wasu mata sanye da kaya irin na fulani sun tsaya bakin kofa suna gaisheta da fara’a, Da kyar tayi karfin halin gyada tana kirkiran murmushi tace “Nagode” Ai kuwa da wannan set din matan sun tafi sai wasu set din sun taho duk ana zuwa yi mata lale, sai ga dattijuwar da kwanon sha dauke da ruwa ta ajiye ma Nihad a kasa, Nihad ta dinga kallon ruwan ganin particles na ta swimming a ruwan, tun da aka haifeta bata ta6a ganin irin kwanon shan da aka xubo mata ruwan ba a ciki gashi duk yayi tsatsa, wata mata ce ta shigo rike da kwarya da nono a ciki, ta ajiye mata da wani karamin kwaryar me dauke da fura, tace “Sai ki dama hurar iya yanda kike so, idan kuma kina son suga sai a amso maki” Nihad dai ba bakin magana sai gyada kai, suka fita suka barta ita kadai da kudaje dake ta zaryarsu a dakin, a hankali ta fashe da kuka tana bin bukkar da kallo, who have she offend to deserve this in her life? Why is all this happening to her?? Khalil ya shigo ciki yana kallonta kasa kasa, cikin kuka tace “Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ka maida ni gida, wallahi baxan sake maka duk abinda nake yi ba….” Ko rufe baki bata yi ba sai ga akwatunanta ana shigo mata da su dakin, da sauri ta share idonta tana bin yaran da suka shigo da akwatunan da kallo kamar idanuwanta xa su fito, Khalil ya jira har suka gama shigowa da su yace “Yauwa sannunku” Tana kallonsa ya tafi ya hau jera mata akwatunan step by step, ta rushe da matsanancin kuka tace “Na shiga uku na lalace, me nayi maka kake min haka don Allah???” Ko tanka ta bai yi ba, ya dawo yana kallon fura da nonon yace “Ba lallai kin iya damawa ba, bari a dama maki” wata karamar tabarma da ya gani a dakin ya shimfida kasa sannan ya xauna ya tankwashe fararen kafarsa ya hau dama mata furan hade da nono a kwarya, kallonsa kawai take hawaye na sauka idonta tace “Don girman Allah kayi hakuri ka maida ni gida” Ba tare da ya kalleta ba yace “Sai kin gama sanye duk kayan dake akwatinki… Sannan nan din gidanmu ne, gidan iyayena ne dolenki ki xauna, adadin kayan akwatunanki adadin kwanakin da xa mu yi…..” Hade kanta tayi da gadon karan da take zaune kai tana shessheka a hankali. Bayan ya gama dama furar ya dauka yana kallonta ya mika mata yace “Gashi” Dago kanta tayi tana kallonsa cikin rawan murya tace “Wallahi baxan iya xama a nan ba kaji na rantse maka” Yace “Xa ki iya idan kika kwana biyu, har ma xaki saba da kowa na garin” Ta fashe da sabon kuka tace “Na shiga uku wayyo Abbana” mikewa yayi ya ajiye mata furan a gefenta sannan ya fita daga bukkar, Nihad ta ci kukanta ta gode Allah, da ta ji alamar xa a shigo sae tayi maza ta goge idonta tayi feigning smile kamar ba komai, ga mutanen are so hospitable, sun ma rasa inda xa su sa ta, they are trying all they can to make her comfortable, hankalinta bai kara tashi ba sai da taga yamma yayi likis alamar dabb ake da magariba, gashi har sannan bata sake ganin Khalil ya shigo ba, Dattijuwar ta shigo tace “Fito kiyi alwala kin ji” Da kyar ta mike ta fito daga bukkar ta tafi inda aka nuna mata buta kusa da tulunaye uku, tana xuwa wajen Dattijuwar ta bi ta tace “Ko xa ki kama ruwa?” Ta girgixa kai da sauri, haka dai tayi alwala ta dawo bukkar matar ta nuna mata inda xata kalla tayi sallah, Nihad na ta xaune saman abinda tayi sallah, ita kam yau xata ga yanda ake kwana a wannan hut din, Wata budurwa ta shigo ta kunna mata wani fitila wanda da shi gwara babu, yarinyar na fita Nihad ta fara sabon kuka, wata mata ce ta shigo mata da tuwon dawa da wata shegiyar miyar kuka wanda warinsa kadai ma ya isa yasa mutum yayi throw up, Nihad ta jinginar da kanta jikin gadon karan wasu hawayen na taruwa idonta, ita kam yau taga ta kanta, miyar kuka da ake yi me dadi da yaji naman kaza ma ba ci take a gida ba balle wannan me offensive smell, ga wani mugun yunwa da take ji, ko furan bata sha ba balle tuwon dawa, khalil kam babu shi babu alamarsa, har kusan Isha’i bata gansa ba wanda wannan ne ya kara daga mata hankali, ko ba komai ta ma dinga ganinsa kawai kilan hankalinta xai kwanta, hakurinta na rashin ganinsa ya kare, tana ganin giftawar tsohuwar ta mike da sauri ta tsaya bakin bukkar cikin sanyin murya tace “Mama ya fita ne? Naga bai dawo ba” Ko rufe baki Nihad bata yi ba sai gashi ya shigo gidan, dattijuwar tace “Toh gashi ma ya dawo” Khalil yace “Sannu Gwaggwo” Gwaggo tace “Yanxu matarka ke Tambayarka” Ya ɗan kalli cikin dakin, Nihad ta hade rai ta koma ta zauna, ya karasa ya shiga ciki ya fito da karamar wayarsa ya haska tuwon dake gabanta yace “Har kin ci tuwon” Cikin rawan murya tace “Ta yaya xan iya cin wannan abun fisabilillah?” Yace “Ta yanda kike cin abinci a gidanku mana, kawai wanke hannu xa ki yi ki fara kai loma” Ta fashe da kuka tace “Wallahi baxan ta6a iya cin wannan abun ba” yace “Ohk, ashe ba yunwa kike ji ba” Ya haska furan nan ma yaga bata sha ba, gyada kai yayi ya juya xai fita, da sauri tace “Don girman Allah ka daina barina ni kadai” Hankalinta a tashe tayi maganar, yace “Me xan maki in na zauna? Yau kuma nine baki son in bar ki ke kadai?” Shiru tayi ta sunkuyar da kanta,  ficewarsa yayi daga dakin ta bi sa da kallo hawaye cike idonta, har kusan karfe goma Nihad na xaune inda take sauro duk ya gama yagalgala ta, wata mata ta shigo bukkar da gidan sauro da wani yakunannen zanin gado tace “Can cikin dare xa ku ji sanyi sosai, sai ki rufa da wannan, bari a daura maki gidan sauro don akwai sauro” a hankali Nihad tace “Toh” can gefe matar ta matsar da tuwo da miya da kwaryan fura dake a kulle, ta gama daura net din a saman gadon karan ta fita, Har Nihad ta fara bacci a zaunen da take ba tare da ta damu da sauro ba Khalil ya shigo bukkar, kulle karamin kofar bukkar da yayi ne ya farkar da ita, ya haska ta da torchlight sannan ya haska saman gadon karan yace “Baxa ki shiga ki kwanta ba malama” Cikin rawan murya tace “Wallahi yunwa nake ji” Ya karasa ya dauko kwaryan fura da nonon da ya dama daxu ya ajiye mata, bata da wani option don mugun yunwa take ji, haka ta dau ludayin tana deban furan a hankali tana kaiwa baki, da kyar take hadiyewa saboda kyankyami, tana yin ludayi uku ta matsar daga gabanta ta rufe tana yamutse fuska, shi dai kallonta kawai yake, yace “Shiga net Hajiya” Ta daga kai ta kallesa ta marairaice tace “Kai a ina xaka kwanta?” Ya hade rai yace “Ina ruwanki?” Bata kuma cewa komai ba ta mike ta shiga net din, abinda bata ta6a shiga ba tunda aka haifeta, ji tayi kamar a saman siminti ta kwanta, ta kai hannu ta tattaba wajen, danne dariyarsa kawai yake, can dai ta hakura ta koma ta kwanta a hankali amma sai taji kamar she is going to suffocate inside the mosquito net, xaunawa yayi saman tabarma yana jin babban wayarsa dake aljihunsa na vibrate amma bai ciro ba, wajajen karfe sha biyu ya mike yana haska fuskarta yaga tayi baccin wahala, ya fi minti biyu tsaye kamar me contemplating, can kawai ya dage net din ya shiga ya kwanta ya juya mata baya sannan ya sake net din. Yana jin ta wajajen karfe daya da rabi tana juye juye, don bai yi bacci ba, can ta mike xaune tana lalubasa, hade rai yayi sae dai bai ce mata komai ba, bayan ta tabbatar shi din ne, ta hau tashinsa tace “Don Allah ni ban san inda xan je in yi fitsari ba” A takaice yace “Sai ki fita ki duba ai” Ya dage net din ya sauka don ya bata waje ta fita, ta sauko kasa tana kallonsa cikin duhun tace “Wayyo wallahi ya matseni” Ya kunna fitilar karamar wayarsa ya mike ya bude kofar bukkar ya fita ta bi bayansa da sauri ta dau butar da tagani tsakar gida, yana nuna mata bandakin dake xagaye da kara ta gwalo ido tana lekan ciki tace “A nan din xan yi fitsari?” Banxa yayi mata ya koma gefe ya tsaya, babu yanda ta iya haka ta shige ciki tana toshe hanci, tana fitowa ya koma bukka ta bi bayansa da sauri, ta xauna kasan tabarman dakin hawaye har ya cika idonta tace “Wallahi yunwa nake ji baxan iya bacci hka ba” ledan da ya shigo da shi daxu ya dauka ya ciro bread ya mika mata, ta dinga kallon bread din sai kuma ta amsa ta bude ta jinginar da kanta jikin gadon karan ta fara cin bread din a hankali, bata wani ci da yawa ba haka ta dau ruwan da take kyankyami ta sha kadan, shi dai yana zaune bai ko kallon direction dinta, a sanyaye ta mike ta shiga cikin net din ta koma can karshe ta kwanta, bayan wasu mintuna da shigarta shi ma ya shiga ya saki net din, nan da nan bacci ya kara dauketa, sae kusan karfe biyu da rabi yayi bacci shi ma, kusa da asuba garin yayi sanyi sosai, kamshin da ya ishesa ya sa ya bude ido a hankali, dab da shi ya ganta ta takure waje daya alamar tana jin sanyi, ya kalli gashinta wanda shi ne ya damesa da kamshi, hade rai yayi a hankali ya juya mata baya, ganin tana matsowa ya ɗan juya ya kalleta, bayan few minutes ya daga net din a hankali fuska daure ya sauka kasa, zanin gadon da mata ta kawo mata ya shimfida saman tabarma ya kwanta, bai sake komawa bacci ba har asuba tayi. Zaro ido Nihad da ta farka da safe tayi ganin gari yayi shar, ta kalli gefenta taga baya nan, da sauri ta sauka ta fita tsakar gida, bayan ta dauro alwala ta shigo bukkar ta dau hijab dinta tayi sallah, bayan ta idar ta mike ta koma gefen gadon karan ta zauna abun duniya duk ya dameta, ta kalli uban kayanta bayan ta tuna abinda ya ce mata wai sai ta gama sa su sannan xa su bar kauyen nan, da daddaya da daddaya aka dinga shigowa gaisheta, mata ta farko da ta fara shigowa gaisheta haka ta bude akwati ta bata atamfa riga da skirt, a haka ta dinga rarrabar da kayan nata, ai ko har da makota a shigowa gaisheta, har kayan kwalliya da shafe shafenta bata bari ba, daga karshe ta ba dattijuwar akwati daya, mata biyun dake gidan su ma duk ta basu kyautar akwatuna daddaya, da atamfa kala daya da Hijab ta tsira sai turare shi ma daya da handbag dinta da takalmi sauran duk ta yi sadakansu, ai ko ta sha godiya sannan albarka ta sha shi kwando kwando, wani kunu me ruwa ruwa aka dire mata as breakfast da dumamen tuwon da bata ci jiya ba, Nihad tayi tagumi tana kokarin ganin bata bar hawayen idonta ya xubo ba, wajen karfe takwas aka kai mata ruwa tayi wanka bayan ta dawo bukkar ta shirya sai ga khalil ya shigo gidan tun daga bakin kofa Dattijuwar ke basa labarin alkhairin da Nihad tayi masu da makota, har da fito da akwatin da Nihad ta bata ta nuna masa, yana shiga bukkar da Nihad take yaga babu kaya ko daya ya kalleta, ita dai kanta na kasa, can yace “Ina kayanki suke?” A takaice tace “Na rabar, ko kai baka ga kayan da suke sa wa bane” Yace “Ohk, ashe xaki yi ta maimaita kaya kenan….” Ta fashe da matsanancin kuka tace “Toh meye don na masu sadakan kaya, idan haka ne mu koma gida in kwaso wasu kayan sannan mu dawo mana” Yace “Koh?” Tace “Ehh mana” yace “Okay, xamu koma ki debo duk kayan naki sai mu dawo” tana share idonta tace “Na yarda, daga nan ma sai mu taho da ruwan gora da biscuits” Yace “Toh” Daga haka ya fita daga bukkar. Har rana ya fara yi Nihad na ta baza ido bata ga Khalil ba balle su bar garin, da rana aka kawo mata ordinary wake da aka dafa aka xuba masa man gyada ita da bata cin wake, ga shi wani axababben yunwa take ji, haka ta bar masu tsiyarsu, wasa wasa har kusan la’asar ba khalil ba labarinsa, da taga yunwa xai mata illa haka ta daure ta dinga danna fura da nonon da aka dama mata, shiru shiru har magrib, bayan ta idar da sllh ta ci kukanta ta gode Allah, har aka yi isha bata ga Khalil ba har ta daina tambayar dattijuwar dake assuring dinta yanxu xai shigo, bayan tayi sallan isha kawai ta dage net ta shige tana shesshekar kuka ba tare da ta bi ta kan tuwon dawar su ba, can wajajen karfe goma sha daya saura ta dinga jin kamshin turarensa, sai kuma ta ji suna gaisawa da mutanen dake tsakar gida kafin ta shigo, xa a kawo masa abinci yace masu ya koshi, bayan like 10 mins ya dage net ya hau saman gadon ya haskata da karamar wayarsa, duk da tana jin sa bata yarda ta bude idonta ba, kashe fitilan yayi ya kwanta, ta bude ido ta dawo kusa da shi ta fashe da kuka tana shessheka tace “Kai fa kace idan na gama sanye kayan da na kawo za mu tafi gida, toh gashi yanxu ko kayan da xan canza gobe bani da shi” Yace “Sae ki maimaita na yau” kuka take sosai, ya juya mata baya, ta ci kukanta ta gode Allah sannan ta koma ta kwanta a hankali, bayan kusan awa daya ya kunna torch dinsa ya haska fuskarta ya ga bacci take. Can kusan asuba xafin jikinta ya farkar da shi, kamar jiya tana kusa da shi ta takure waje daya, ya kai hannu jikinta ya ji da xafi….

27

Yau ma kamar jiya hasken rana ne ya sa Nihad ta farka, da kyar ta mike xaune tana jin duk jikinta na mata ciwo barin kanta da yayi mata nauyi, sosai hankalinta ya tashi ganin khalil baya dakin, ta hade kai da gadon karan da take kai tana kuka a hankali, can dae tayi karfin halin mikewa ganin lokaci na tafiya bata yi sallah ba, ta nufi yar jakar da ta sa brush dinta da Toothpaste ta dauka ta fita daga bukkar. Bayan ta idar da sallah tana xaune saman abun da tayi sallan lkci lkci tana share hawayen dake gangaro mata, rashin ganinsa na kara saka mata damuwa a kan wanda take ciki, shadow da ta gani bakin kofa ya sa ta daga kai da sauri hoping shi ne ya dawo, amma sai ta ga ba shi bane, wata budurwa ce warce xa su yi sa’anni da Nihad din ta shigo dakin, fara ce kal kal don duk hasken Nihad yarinyar ta fi ta, ga ta kyakkyawa ajin karshe, dogon gashinta da aka kitsa gida biyu manya manya har ƙafadunta suke tabowa, ga uban wushiryarta a baki, Nihad ta ganeta don jiya kaya kala biyu ta bata da turare, budurwar na murmushi ta duka gaban Nihad ta ajiye mata kwanon sha dake hannunta tace “Hannu, yau kamar kin makara ko” Nihad ta kirkiri murmushin ita ma tace “An tashi lafiya” Yarinyar tace “Lafiya lau, ga farau farau nan na kawo maki, yanxu xa a dunduma tuwon sae a kawo maki” Sosai gaban Nihad ya fadi jin kalmar tuwo, ita fa bata ta6a sanin akwai wani kalan tuwo bayan fari ba, gwara gwara amala ta san baki ne, to da wannan abun da suke kira tuwo ba gwara a bata amalan ba, ta dai sakar mata wani murmushin karfin halin tace “Toh, nagode” Yarinyar na wasa da gashinta tace “Ni sunana Furera amma ana kirana Fure ke kuma fa?” Nihad ta sauke idonta tace “Sunana Nihad” Yarinyar ta zaro ido tace “Sunan yan birni, ae baxan ma iya kiran sunan ba” Nihad tace “Toh ki kirani Ummi” Fure tace “Yauwa gwara wannan, amma ae xa ku yi sati a nan ko?” Nihad ta kalleta da sauri ta girgiza kai tace “Aa yau xa mu tafi” Yarinyar tace “Gwaggo fa tace min xa ku yi sati” Nihad xata yi magana sai ga Khalil ya shigo bukkar da sallama, lkci daya kamshinsa ya cika Bukkar, Fure ta koma gefe tana d’an Murmushi, tace “Hamma wai ashe yau xa ku tafi?” Yanda take maganar kasan a kunyace take da Khalil, Khalil ya kalleta yace “In ji wa?” Fure ta nuna masa Nihad, yace “Aa xa mu yi sati” Gaban Nihad yayi mugun faduwa ta gwalo ido tana kallon khalil a ranta ta dinga nanata satin da yace, meye kuma sati, ba dai sati daya yake nufi ba, cike da murna fure tace “Yauwa dama haka Gwaggo ta sanar min, ai ko naji dadi sosai, duk xan bi in xaga da Ummi kauyen mu da wanda ke gaba da namu, a kawo maka farau farau din ne ko fura da nono xaka sha, nonon ma sabuwa ce jiya aka tatso” Yace “Toh kawo min fura da nonon” Tace “Toh” daga haka ta fita, Nihad ta marairaice tana kallonsa tace “Amma dai xaka maida ni gida sae kai ka dawo kayi satin a nan?” Ya dauko tabarma ya xauna kai ba tare da ya kalleta ba yace “Ko kuma ni in tafi bayan sati daya in xo in dauke ki ba” Bata san sanda ta fashe da wani matsanancin kuka ba tace “Don girman Allah kar ka min haka ka rufa min asiri…” sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta hade tafin hannunta tana kuka a hankali tace “Don Allah kayi hakuri, wallahi baxan iya ba, kaji har na rantse” Gyara xama yayi yace “Bukka guda Gwaggo xa ta bar maki kiyi rayuwarki ke kadai har bayan sati dayan babu me takura ki” Nihad ta mike da sauri ta nufesa ta durkusa gabansa tana kuka tace “Wallahi xan iya mutuwa idan ka tafi ka bar ni a nan, kar ka tafi ka bar ni” Kallonta kawai khalil yake, dai dai nan Fure ta turo kai cikin Bukkar rike da kwaryan nono da fura, Nihad ta koma gefensa da sauri ta zauna, Fure ta durkusa gabansa ta ajiye fura da nonon tana kallonsa tace “Kana son sukari?” Khalil yace “Kadan” Mikewa tayi ta nufi kofa xata fita, khalil ya bi ta da kallo, Nihad ta kallesa, sannan ta kalli yarinyar har ta fita, Khalil tankwashe kafarsa yana kallon fura da nonon dake cikin kwarya a gabansa, muryar Nihad ya ji kamar daga sama tace “Kanwarka ce?” Ya ɗan kalleta, sai kuma yace “Aa, er makotanmu ce, Baabarta ai ta shigo kun gaisa jiya” Sai ga fure ta shigo rike da sugar a hannunta, durkusawa tayi gaban Khalil tana murmushi ta juye sugar din a kwaryan nonon, ta ɗan kallesa tace “In dama maka?” Ya gyada mata kai yace “Ehh” Nihad dake kallonta ta mike tace “Bar shi xan yi” Fure ta kalleta sai kuma ta mike tace “Toh” Kallonta kawai khalil yake babu yabo babu fallasa ta dawo gabansa ta durkusa ta dau ludayi ta saka cikin kwaryan, Fure ta mike ta fita, Nihad na kiciniyar dama fura da nonon kwaryan ya kife duk suka malale a kasa, da mamaki Khalil da ya koma baya yake kallonta, kana ganinta kasan bata ta6a dama fura da nono ba, ta turo baki ta mike ta bar wajen ta koma can karshen gadon kara ta zauna tana kallon mess din da tayi a kasa, khalil yace “Na kara sati daya a kan satin da nace xa ki yi a nan” da sauri ta mike ta nufosa ta fashe da kuka tace “Wallahi ba da gangan nayi ba, kwa6ewa yayi a hannuna” Ya hade rai yace “Da baki iya ba me yasa baki bar warce ta iya ba tayi” Tana goge hawayen idonta tace “Toh meye xata wani zo tana ma mutane yauki kamar kubewa a nan?” Mikewa khalil yayi yace “Ni dai na gaya maki, ki shirya kwana sha biyu nan gaba a nan” Nihad na kuka ta riko rigarsa da sauri ganin xae fita cikin rawan murya tace “Don Allah kayi hakuri, idan na kara ko kwana daya a kauyen nan yunwa xae iya kashe ni” Ya janye rigarsa daga hannunsa ya fice daga bukkar, Nihad ta sulale kan inda ya tashi tana kuka a hankali. Goge idonta tayi da sauri jin ana sallama, ta kalli matan da suka fara tururuwan xuwa kofar Bukkar da take don gaisheta, da murmushi take amsa masu gaisuwar tasu cike da karfin hali don yunwa ba na wasa ba take ji, tunda take bata ta6a jin irin wannan kalan yunwan da take ji ba, wata mata ta shigo ta kwashe kasar dai dai inda fura da nono ya xuba ta fita da shi, Nihad ta bi ta da kallo, to ko kiwon dabba ake yi ai a tunaninta ba a kiwonsa a ordinary sand balle mutum, ko kaji ma ana shimfida masu kwali…. Nan ko ga kasa kiri kiri a daki kamar a kofar gida, Gwaggo ce ta shigo daga karshe rike da kwanon dumamen tuwo ta ajiye mata tace “Hannu Ummi, an tashi qlau dai ko?” Nihad na Murmushin karfin hali tace “Ina kwana Mama” Gwaggo tace “Lafiya lau, ga tuwo ki ci kafin kiyi wanka, ko dai kina son yajin daddawa a kawo maki da man shanu” Da sauri Nihad tace “Aa nagode xan ci haka” Gwaggo tace “Toh, Don naga jiya ma kamar baki wani ci tuwon ba, wannan na barbada maki me tauraro a kai, xaki ji dadinsa, kinsan ku yan birni baku amfani da manda a girki” Nihad dai sai ka rantse tallan close up take yanda take murmushin karfin hali tana kallon tsohuwar, Gwaggo tace “Ko a damo maki hurar ki hada da tuwon naga faro faron ma baki sha ba” Nihad ta girgiza kai tace “Aa wannan ya isa mama, nagode” Gwaggwo tace “Idan kin gama ci sai ki fito an kai maki ruwan wanka” Nihad tace “Toh” Bayan fitarta da kamar minti sha biyar Nihad ta mike ta fita tsakar gida, haka duk matan gidan dake shirin surfe suka bi ta da kallo, Gwaggwo ta taso tace “Har kin cinye” Nihad tace “Ina son xan yi wanka” Gwaggo ta rakata xuwa bandakin ta bude mata kofar karan tace “Ga ruwan a ciki” Nihad ta saka kai ta shiga ciki, bayan matar ta bar wajen kawai ta fashe da kuka, yau ita ke ganin rayuwa haka, yanzu a haka xata yi wankan?? A daddafe ta watsa ruwa tana rike numfashi sbda uban zarnin da wajen ke yi ta fito da sauri, har ta shiga bukka kallonta matan tsakar gidan suke, ko mai Nihad bata shafa ba ta saka kayanta ta xauna gefen gadon kara jiki a sanyaye tana bin kudajen dake ta shawagi a dakin da kallo, Sai kuma ta hade kai da gwiwa ta fara shesshekar kuka tana jin kamar Ulcer xai iya kamata at anytime. Har rana bata ga Khalil ba, aka kawo mata gwaza da mai da gishiri, da farko tayi xaton doya ce amma bayan warce ta kawo mata ta fita, ta dauka tana kare masa kallo kafin ta 6are ta kai baki a hankali, da sauri ta fito da shi tana yamutse fuska, a haka ta matsar da kwanon a inda kwanon tuwo da faro faro suke tayi tagumi, cike da tausayin kanta. Kusan karfe hudu saura Gwaggo ta leko bukkar tace “Ke baki fitowa shan iska Ummi, ai da xafi dakin…” Nihad ta girgiza kai a hankali tana mata murmushin karfin hali, alamar bata son ta fitowa, Gwaggo ta kyaleta ta tafi ta ci gaba da abinda take, duk motsin da xata ji sai ta leka ko Khalil ne amma sai taga ba shi bane, a haka har ta fita taje tayi alwala ta dawo tayi la’asar, xuwa lkcn jikinta rawa yake saboda yunwa, she is very very hungry, amma babu abinda xata iya ci cikin abubuwan da aka kawo mata, kukan ma ta gaji da yin sa yanxu ta daina, tana idar da sallah ta kwanta saman gadon karan tana juye juye, daga karshe ta mike ta sauko kasa jikinta na rawa ta bude farau faron dake kulle ta dauka, runtse ido tayi cike da karfin hali ta kai bakinta kan kwanon ta rike breathing dinta sannan ta hau kwankwada, ajiye kwanon tayi da sauri bayan ta kwankwadi kusan rabi, saboda wani amai da taji ya taho mata, ta mike da gudu ta fita daga dakin, gwaggo da matan tsakar gidan dake surfe suka taso da sauri suna tambayarta lafiya, nan ta dinga kwararar masu aman abinda ta sha kamar xata shide, Gwaggo da duk ta rude tace “Subhanallahi, me ya sameki, gashi baya nan” Wata mata ta kawo ruwa da sauri suka ba Nihad dake maida numfashi, amsan ruwan tayi da kyar ta wanke bakinta duk jikinta na rawa, Gwaggo da hankalinta yayi mugun tashi ta kawo mata kujerar tsugunno tace “Hannu, zauna nan, zauna” Nihad ta xauna a hankali kan kujeran tana maida numfashi, Gwaggwo tace “Me ya sameki kike hararwa haka?” Da kyar tace “Bani da lafiya ne dama” Matan gidan suka dinga yi mata sannu, ganin yanda jikinta ke rawa Gwaggo ta maida ta cikin Bukkar tana mata sannu ba adadi, wata yarinya da ta aika ta dubo mata Khalil a waje ta dawo ta shigo Bukkar tace “Gwaggo bamu gansa ba” Gwaggo tace “Toh bari a mata jike jike tasha ko xaxxabin xai sauka” Daga haka Gwaggo ta fita, kuka Nihad take a hankali tana juye juye tana jin kamar kanta xai fashe don ciwo, bayan wani lokaci sai ga gwaggwo da kwano ta ajiye kasa ta dago Nihad tace “Ga nan jike jiken sassaken itatuwa na maki, tashi ki sha, ba daci ba bauri, ba hamami” Nihad ta mike tana rawan sanyi Gwaggwo ta dauko kwanon ta kai mata baki tace “Ungo sha” Cike da karfin hali Nihad dake ta kallon cikin kwanon ta kurbi ruwan ciki, Gwaggo tace “Kara sha” Nihad ta runtse ido ta kara kurba ta hadiye tsikar jikinta na tashi, dacin ruwan kuwa ba a cewa komai, Gwaggo tace “Yauwa, to koma ki kwanta yanxun nan xaki fara xufa, su ararrabi ne da sabara da tazargade, ga su nan dai” Nihad ta koma ta kwanta Gwaggwo na kokarin lullubeta Khalil ya shigo Bukkar ya nufo Nihad yana kallonta, Gwaggwo tace “Wallahi mugun zazzaɓi ne ya rufeta yanxun nan sai hararwa take” Khalil ya duka yana kallonta ya kai hannu jikinta wanda yayi zafi kamar wuta, cike da damuwa Gwaggwo tace “Akwai wani karamin asibiti a gidan Darho, kauyen da xaka wuto kafin ka zo wannan, ko xaka kai ta a dubata a bata magani ɗan nan?” Khalil yace “Toh xa mu je can” juyawa tayi ta fita daga Bukkar, Hannu ya kai goshinta duk da idonta a kulle yake yace “Ina ke maki ciwo” Ta fashe da kuka ta tura hannunsa daga goshinta tace “Ni ka maida ni gidanmu, idan ba haka ba sai Allah ya kama ka” kallonta ya tsaya yi, can ya gyada kai ya koma gefe yace “Ohkk” tayi karfin halin mikewa cikin kuka ta kamo hannunsa tace “Don Allah kayi hakuri ba don halina ba ka maida ni gida” Yace “Toh ina ke maki ciwo?” Tana shessheka tace “Kai na, kuma ina jin yunwa” Ya mike yace “Sakko” Da sauri ta mike xaune amma ta kasa tashi daga saman gadon duk yana kallonta, ya mika mata hannunsa ta rike sannan ta mike tsaye a hankali, dukawa tayi yana rike da hannunta ta dau Hijab jikinta na rawa ta saka, sannan ta dau handbag dinta, ko bin ta kan atamfarta na karshe da kayan shafe shafenta bata yi ba, a haka suka fita daga Bukkar, Gwaggwo da matan gidan suka taso, ana mata sannu in chorus, Gwaggwo tace “Can asibitin ku ka nufa ko?” Yace “Ehh” Nan dai aka dinga mata Allah ya sauwake, Fure dake tsaye kusa da wani ɗan mariki da aka daure tace “Gwaggwo in rakasu asibitin” Da sauri Nihad ta kalleta, murya can kasa Nihad ke girgiza ma Khalil kai tana cewa “Aa baxa mu je da ita ba” Ya ɗan kalleta ta gefen ido, Gwaggwo tace “Toh ko kama maka ita ai sai fure ta dinga yi a asibitin ko” Da sauri Nihad na Murmushi tace “Aa mama xan iya ai” Gwaggwo tace “Toh shkkn, Allah ya baki lafiya sai kun dawo” Nihad dai bata ce komai ba a ranta kuwa tunani take ina din xa su dawo da take ce masu sai sun dawo? Dalilin ma da yasa bata son Fure ta bi su kenan don in sun tafi da ita ai dole su dawo da ita kauyen, ita kuwa bata fatan abinda xai sake dawowa da ita kauyen nan, suna isa inda Khalil ya ajiye mota ya saketa ya zaga daya side din, a hankali ta bude front seat din ta shiga, bayan yayi warming motar ya ja motar, matan gidan da suka taru bakin kofar shiga gidan har da masu daurin kirji, ga yaransu duk ba wando a tsattsaye su ma, sai daga masu hannu suke kana ganinsu dai kaga yan kauyen kayau, haka ma sauran makota da suka fiffito jin karar mota, Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya, at long last!!! har taji xaxxabin ya tafi sai kuma bakar yunwan da take ji, tafiyar minti talatin suka yi ta ga alamar sun fara shigowa gari, farin ciki gunta ba a cewa komai, bata ta6a tunanin xata fito daga kauyen can da ranta ba, ta zata sai buzunta, so truly akwai mutane irin haka a rayuwar nan, akwai mutane dake rayuwarsu cikin kauye haka? lkci daya jikinta yayi sanyi, and they are leaving happily abunsu babu wani damuwa, ko pole din wuta ita bata gani a garin ba balle a je ga an ja masu wuta, parking ta ga khalil yayi dai dai wani pharmacy, duk da bata san inda suke ba amma tasan sun shigo cikin gari gaba daya, ya kashe motar ya sauka yana kallonta yace “Sauko malama” A hankali ta bude motar ta sauko ta bi bayansa tana jan kafa saboda jiri da take gani, suka shiga pharmacy din, bayan sun gaisa da me Pharmacy din ya koma gefe ya tsaya yana kallon Nihad da ta jingina da kofar pharmacy din bata shigo ba, har ta rame tayi wani uban duhu kamar ba Nihad ba, Ya kalli me Pharmacy din yace “Ita ce bata da lafiya” Me Pharmacy din yace “Sannu Hajiya karaso” Tana jan kafa ta tafi gaban table dinsa ta xauna, Tunda aka haifeta ba a taba kawo su pharmacy idan basu da lafiya ba, sai dai asibiti, amma wai yau ita ce a pharmacy xa a mata treatment bata da lafiya instead of hospital, muryar Pharmacist din ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi, ta sauke idonta kasa a hankali tace “Zazzaɓi nake ji da ciwon kai” Yace “Kina amai ne?” Ta gyada masa kai tace “Ehh nayi daxu” Yace “Ohk” Kallon khalil yayi yace “Xa a maganunguna da allurai….” Khalil ya rungume hannunsa yace “Sai dai magungunan kadai, don kauyen da muke akwai nisa, baxai yiwu mu dinga xuwa muna komawa ba kullum” Da mugun shock Nihad ta kallesa, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka tace “Don girman Allah ka rufa min asiri kar ka maida ni garin nan” Khalil ya danne dariyarsa ya hade rai, Me Pharmacy ya tuntsire da dariya yana kallon Nihad da duk ta gama rikicewa, Khalil yace “Shi garin namu kike ce ma garin nan” Ta hade hannunta cikin kuka tace “Ka rufa min asiri mu wuce gida don Allah” Khalil ya kalli me pharmacy yace “Malam ba mu maganin kawai, hanyar kauyen ba shi da dadin tafiya da daddare, kaga magariba ya kusa” Kuka kawai Nihad take hankali tashe tana kallon khalil, me pharmacy dai ya basu magunguna ya sa a leda ya mika ma khalil yace “Duk prescriptions din na jiki” Khalil ya amsa yace “Nawa ne?” Me pharmacy din ya gaya masa ya zaro kudin a aljihu ya mika masa, Yana kallon Nihad ya daure fuska yace “Tashi mu je” Ta mike tana kuka tace “Kayi min rai kar ka sake maida ni garin nan wallahi baxan iya xama ba kilan ma in mutu” Khalil yace “Fita mu je” Fita tayi daga pharmacy din ya bi bayanta, tayi mugun ba me pharmacy din dariya don sai kallonta yake, ta tafi gun mota tana kuka kamar an aikota ba tare da ta damu da mutanen dake kallonta a wajen ba, bude mata back seat yayi yace “Shiga inda kika fi jin dadin zama ki xage mutane kiyi masu rashin kunya….” Ta shiga bayan motar tana kuka kamar ranta xai fita, ya ajiye mata ledan maganinta ya koma driver seat ya ja motar suka bar wajen….. Wani eatry Khalil yayi parking ya kashe motar bayan ya ɗan sauke glass ya sauka sannan yayi locking motar, ita dai kuka kawai take don har ta saka a ranta cewar in har taga sun nufi hanyar kauyen nan to suma kawai xata yi a cikin motar kuma duk abinda xa ayi mata baxata farfado ba, ba a dau lkci sosai ba ya dawo rike da ledan take away, ya ajiye a back seat sannan ya shiga mazaunin driver yana kallonta ta madubi yace “Bari a kai ki inda xa ki yi wanka kafin mu koma, don naga babu wajen wanka a garin” daga haka yayi reverse suka bar haraban eatry din, Rokonsa Nihad ta dinga yi hankali tashe tana cewa ya rufa mata asiri su koma gida amma bai tanka ta ba, a wani hotel taga ya shiga yayi parking, tsaf ta gane hotel din don sun ta6a xuwa da su Husnah, yanxu da gaske wankan xata yi su koma wannan kauyen?? yana parking ya sauka ya kulle motar ya bude side dinta fuska daure yace “Sauko malama” A hankali ta sauko daga motar, ya dau ledan maganinta da abinci, yana gaba tana biye da shi suka shiga reception din hotel din, ya gaisa da masu aiki a nan, makulli kawai ya amsa alamar dai ya kama dakin tuntuni, ganin yayi hanyar stairs ta bi bayansa tana ji kamar iska xai kadata ta fadi, ya bude dakin ya shiga ita ma ta shiga sannan ya kulle kofar, bin dakin take yi da kallo, taga tray me dauke da kayan shayi da cup din shayi alamar an sha shayi, ya kunna wutan dakin ya sauke curtains sannan ya shiga bandaki, tana jin alamar wanka yake yi ta zamo kasa a hankali ta zauna ta jawo ledan abincin da ya ajiye ta bude, fried rice da yaji liver hade da spicy jollof rice a gefe ta gani, sai peppered chicken, tayi unwrapping cokalin daga tissue dake jiki, har wani rawa jikinta yake ta fara cin abincin, Nihad da bata wani cin abinci sai gata ta cinye abincin nan tasss naman kawai ta ci kadan ta bari don ita cin nama aiki ne a wajenta, kai ta yage yage kana bata baki da maiko, ta bude chilled chivita dake leda shi ma kadan ta sha sannan ta ajiye, Sai a sannan ta fara gani dai dai ta daina jin jirin da take ji, fitowa khalil yayi daga bandaki ya dinga kallonta da mamaki, can yace “Amma wa yace maki naki ne da kika dauka kika ci?” Ko kallonsa bata yi ba balle ya sa ran amsa, sai kuma ta mike ta wuce ta gabansa ta tafi jikin window tana kallon waje da motocin dake ta tafiya saman titi, waii lallai ta jinjina ma yan kauye, Allah Ubangiji ya kawo masu mafita. Tana jin ya fita daga dakin ta juyo a hankali ta dawo gefen gado ta zauna tana tunanin irin rayuwar da tayi na kwana biyu kacal, ita kanta tasan ta rame kuma ta yi baki, tashi tayi daga karshe ta shiga bandaki tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tana sallan Magrib, banda Aliyu babu wanda ke ranta, ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ta murda taji a kulle, dawowa tayi ta fada saman gado ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa……

28

A hankali Nihad ta bude idonta ta dalilin sanyin da take ji, at first sai da tayi imagining cewar ai fa kauyen nan take, a firgice ta tashi xaune tana tattaba daya side din gadon don wutan dakin a kashe yake, amma taji ba kowa wajen, jin laushin duvet yasa ta tuna ashe a hotel suke, wani boyayyen ajiyar xuciya ta sauke, ta sauka daga kan gadon tunda hotel din ba bakonta bane ta san inda switch yake, tana tafiya a hankali ta xagoya xata kunna wutan taci tuntube da mutum ta fada kansa duk da a zaune yake, da farko tayi mugun tsorata amma tana jin kamshin turarensa ta gane shi ne, tashi tayi ta dafa bango ta kunna wutan, zaune ta gansa saman darduma  alamar sallah yake, ta zaga daya side din ta kalli agogon dakin ta ga karfe biyu da minti goma,  komawa tayi gefen gado ta zauna tayi tagumi, sai kuma ta tuna bata yi isha’i ba ta tashi da sauri ta shiga bandaki. Har ta idar da isha’i sallah yake shima, ta ɗan yi jim kamar xata tashi ta koma ta kwanta can dai kuma kawai ta mike ta hau sallan nafila, har ta mance rabon da tayi qiyamul lail, sai dai in mistakenly ta kwana dakin Nihal shine Mumy ke tashinsu su yi sallan dare, don dare daddaye ne Mumy bata sallan dare, a wannan daren kuma tayi addu’a sosai a kan Allah ya toni asirin duk wanda yayi ruining happiness dinta cikin gaggawa, abinda bata ta6a yi ba tun da abun ya faru, daga karshe tayi addu’ar Allah ya sa khalil ya rabu da ita na har abada don ita ba class dinsa bace, sannan baxata ta6a zama da shi a matsayin mijinta ba, ta kuma yi addu’an bayan Khalil ya rabu da ita Allah ya mallaka mata Aliyu, wajajen karfe Uku da rabi ta fara jin bacci, ta ɗan saci kallon side dinsa, yana zaune saman darduma shi ma da alamar ya idar, amma kana kallonsa xaka san yayi nisa tunanin da yake, and he look so distressing, dauke idonta tayi daga kansa tayi kwanciyarta saman inda tayi sallan, har dai bacci ya dauke wajen karfe hudu bata ga alamar Khalil xai kwanta ba. Da asuba loudspeaker din masallacin dake hotel ne ya tasheta, bata gansa a dakin ba alamar ya tafi masallaci, bayan ta idar tana zaune saman darduma tana azkar ya shigo dakin, ba tare da ya kalleta ba ya shiga bandaki, tana ta zaune kan darduma taji ring din wayarsa kallon gaban madubin tayi da sauri don bata san wayar na nan ba, kuma bata ta6a jin wayarsa na ring ba sai da vibrate, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi gaban madubin, Mami ta gani gaban screen din karamar wayar, ta dauka kenan kawai ya bude bandakin ya fito da sauri ya nufota yace “Keee” Ba karamin rikicewa tayi ba ta juyo wayar na hannunta, zaro ido tayi ta saki wata er kara ganinsa daure da towel ta durkushe kasa ta rufe fuskarta da gwiwanta a tsorace, yana isa inda ta durkusa ya warce wayarsa a hannunta ya koma bandakin, duk da taji rufewar kofar bandakin taki dago kanta, bayan kusan minti daya ta dago a hankali tana kallon kumfan da ya sa mata a hannu wajen warce wayarsa, turo baki tayi ta mike jiki a sanyaye ta koma can daya side din gadon ta kwanta tare da juya ma kofar bandakin baya. Tana ji ya fito daga bandaki bayan kusan minti sha biyar sai kuma ta ji ya fita daga dakin gaba daya. Wajen karfe takwas ta gaji da kwanciya ta tashi ta zaga ta shiga bandakin, wanka tayi ta fito bayan ta goge jikinta ta maida kayan da ta cire, tana zaune gefen gado ta jinginar da kanta da gadon tana kallon Tv duk da hankalinta baya kan kallon ya bude kofa ya shigo dakin, tunda ta kallesa sau daya bata yarda ta sake kallonsa ba, ta dai ga ya canxa kaya, shi kam bai kalli inda take ba ya dau towel din da ta yasar saman gado ya shigar da shi bandaki ya fito, ya dauko magungunan da ya siyo mata jiya dake yashe kasan dakin ya jefa mata gefenta ya hade rai yace “Wato dama lafiyarki qlau kika sa naje chemist nayi asaran kudina ko?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Kudin babana dai” kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace “Gaskiya ne, kudin babanki ne, sai ki taso mu koma can garin kiyi kumallo a can gidanmu, kinga can ai kudin babana ne ba na baban wani ba” Kallonsa tayi da sauri, ganin hada abubuwansa dake dakin kawai yake, tayi karfin halin cewa “Wani garin xan je in yi kumallo?” Ba tare da ya kalleta ba ya nufi kofa yace “Ina jiranki a waje” Ta fashe da matsanancin kuka tace “Ni wallahi baxa ka maida ni wannan garin ba, wai kai baka tsoron Allah ne?” Juyowa yayi ya rungume hannu ya jingina da kofa yace “Sai ke” Cikin kuka tace “Allah baxan je ba, kaji har na rantse, dama ba kwana biyu kawai xa mu yi ba? To wllh baka isa ka maida ni ba” Yace “Ohk, xan nuna maki kuwa na isa, sannan in mun koma sai mun yi wata daya kafin mu bar garin, kinga baxa ki kara min gorin kudin babanki nake ci ba” Cikin tashin hankali tace “Kaga don girman Allah kayi hakuri ka daina ce min haka, wallahi in ka sake maida ni kauyen nan xan iya mutuwa kawai” Khalil yace “Toh mu je a ga adadin kwanakin da xaki iya a can din kafin ki mutu” Cikin kuka tace “Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri” Shiru yayi na few seconds, sai kuma yace “Ohk, baxan maida ki garin ba amma da sharadi” Tana goge idonta tace “Ina ji” Ya fi second talatin yana kallonta kafin yace “Nasan komin daren dadewa xa mu rabu… Don haka idan Allah ya kai mu lokacin ina son ko me xai faru baxa ki fasa nuna ma iyayenki cewar ke kika bukaci mu rabu ba ni ba…..” Nihad dake ta kallonsa da mamaki tace “Toh me yasa yanxun baxa mu rabu ba kawai, kuma wallahi babu wanda xan gaya ma, kaga babu wanda xai sani sae mu biyu” Yana kallonta yace “Ohk ta yaya kike tunanin xa mu rabun yanxu?” Ta gyara xama tace “Kawai kace ka sakeni, babu me sani sai ni da kai” Yace “Toh idan aka yi hakan sai me xai faru?” Ta daga kafada tace “Ba komai, kawai kayi rayuwarka inyi ta wa, ni xan ma iya bar maka gidan gaba daya kawai sai dai in dinga xuwa diban kayana, idan kana so ma sai ka saka yan haya ka dinga karban kudin kana xubawa a aljihu” Khalil ya ɗan yi murmushi ya gyara tsayuwarsa yace “Ohk, sai ki ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya kenan ko?” Tayi masa wani kallo tace “Me kake nufi? Ni nake yin iskanci? Kana nufin ni yar iska ce?” Yayi wani murmushin takaici yace “Toh baxan yi abinda kike so yanxu ba, kawai dai ki sa a ranki lokacin hakan na zuwa, nan ba da dadewa ba” Ta kyabe baki tace “Ni fa lokacin da kake nufi da yanxu duk daya ne ni a wajena” Ya daga kafada yace “Gwara dai a jira lokacin” Ita dai bata kuma cewa komai ba amma a ranta tunani take ashe ma ba wani babban sharadi bane, dama ita ai babban burinta su rabu na har abada, Ta kallesa tace “Ka dai yi alkawarin rabuwa da ni??” Yace “In sha Allah” Wani farin ciki taji ya rufeta tace “Toh nima in sha Allah ko ma me xai faru xan ce nice nace mu rabu babu ruwanka” Yace “Toh” Tace “Toh nima ina da deal dina in har kana son inyi abinda kace nima sae kayi abinda nake so” Yace “Ina sauraronki” tana gyara zama tace “Na farko ina son ka bar ni in ci gaba da xuwa makaranta na, na biyu baxa ka hana duk wanda xai zo wajena xuwa ba, like kawayena infact everybody, na uku xaka bani spare key na gida nima, sannan na karshe ina son ka bar ni da wayata…” Kallonta kawai khalil yake, ta langwabar da kai ta wara ido tace “Ehh, ni gwara nawa minor request ne, babu abinda xai ragu a jikinka idan kayi accepting, naka request din kuwa kilan har tsine min xa a iya yi a gida amma kuma ban damu da hakan ba na amince xanyi yanda kace” Khalil yace “Abu biyu kadai xan iya maki a abubuwan da kika ce, idan kuma kinga hakan bai maki ba kawai a bari, mu ci gaba da zaman mu yanda muke, kuma dole a titi ace maki matar drivern gidanku” Ta marairaice sai kuma tace “Toh ina ji, ka gaya min abu biyun” Yace “Babu xancen xuwa makaranta sannan baxa ki rike waya ba!!!” Shiru Nihad tayi tana nazari, wato kawayenta xa su iya xuwa gidan sannan xai bata makullin gida, daga kai tayi ta kallesa taga kallonta yake yana jiran jin me xata ce, tace “Toh ai shikenan, na amince” Yace “Sannan abu na karshe wanda muhimmancinsa kusan daya da sharadin farko….” Tace “Ina jin sa” Yace “Babu ke babu kallon inda wayata take balle ki ta6a, a takaice babu ruwanki da wayana har xuwa lokacin da xa mu rabu” Nihad ta kyabe baki tace “Toh dama ni meye ruwana da torchlight phone dinka bawan Allah??” Ya gyada kai yace “Toh” Juyawa yayi ya fita daga dakin, ta mike ta dau ledan magungunanta ta saka Hijab sannan ta bi bayansa. A reception ta tarar da shi ya bada makullin dakin ya fita compound din hotel din ta bi bayansa, wani ma’aikacin hotel din ne irin masu share share ya ganta yace “Ahh Hajiya kwana biyu kin buya, ya kawayenki” Nihad ta juya ta kallesa, murmushi tayi tace “Lafiya lau ya aiki?” Yace “Alhamdulillah, yau baku zo da kawayen naki ba kenan? Naga kullum tare ku ke” Sai kuma ya kalli Khalil dake tafiya yace “Au ashe da oga ku ke….” Katse sa Nihad tayi da sauri tace “Aa, drivern gidanmu ne, ya kawo ni in amshi sako wajen wani” Murmushi kawai Khalil dake tafiya xuwa inda ya ajiye mota yayi ba tare da ya juyo ya kallesu ba, Ma’aikacin ya fasa gaida Khalil da yayi niyyar gaidawa, sai kuma yace “Allah sarki ni na zata oga ne ae nagansa kalarki, to na gaisheki Hajiya” Bude jakarta tayi taga dari biyar ta zaro ta mika masa, ya amsa da ladabi yana mata godiya, tuni Khalil har ya kai gun mota ya bude driver seat ya shiga, Nihad ta karasa ta bude back seat ta shiga ta kulle, har suka isa gida bai ce mata ba bata ce masa ba, bayan yayi parking ya sauka ya tafi ya kulle gate, sannan ya nufi entrance din gidan ya bude kofar main parlor, Nihad dake ta tsaye tana jiran ya xo ya bude ta kyabe baki ta bi bayansa suka shiga parlon, wani ajiyar xuciya ta sauke direct ta nufi dakinta. Bacci sosai Nihad tayi bayan ta shiga dakinta, wajen karfe sha daya da rabi ta farka ta dalilin yunwan da take ji, a hankali ta mike ta shiga banɗaki tayi wanka ta wanke baki sannan ta fito, bata gansa a parlor ba har ta nufi dakinsa sai kuma ta fasa bude kofar ta dawo parlor ta zauna tana jiran ganin fitowarsa bude kofar parlor aka yi ta juya da sauri, taga ya shigo parlon rike da leda kallo daya yayi mata ya dauke kai ya karaso cikin parlon, a takaice tace “Makulli xaka bani xan fita in siyo kayan miya, sannan anjima xan je kasuwa siyo atamfofi don na kyautar da duk kayana a can garinku” Ya girgiza kai yace “Baya daga cikin sharadinmu, duk me kike bukata xa a siyo a ajiye maki” Ta kyabe baki tace “Toh a fita a siyo min kayan miya” Cike da isa tayi maganan, yace “Sai sanda nayi niyya” Yana gama fadin haka ya ajiye ledan hannunsa ya nufi kitchen don dauko plate, bin sa tayi da kallo yana shiga tayi saurin dauke ledan abincin nasa ta shige daki da sauri ta sa makulli, shinkafa ne da miyya da yaji uban nama sannan ga coslow a wani karamin takeaway din, ga ruwan roba me sanyi da drink, tayi er dariya ta gyara zamanta ta dau cokali ta fara cin abincin. Wajajen karfe uku Nihal ta kira Khalil, bayan sun gaisa yace “Kin dawo lafiya?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Maa sha daya, yaushe xa ki zo ganin er uwar taki?” Nihal tace “Shine dama nake son in ce mata xan zo yau, ka kai mata wayar pls” Yace “Xan gaya mata, Allah ya kawo ki lafiya” Tace “Ameen” daga haka ya katse wayar, tun da Nihad ta shige masa da abinci daki bata sake fitowa ba, don bayan ta ci ta koshi ma ramuwan baccin da bata yi a kauye ba ta ci gaba da yi. Wajen karfe biyar Nihal ta iso gidan, Khalil ne ya bude mata gate bayan ta kirasa a waya ta sanar masa tana bakin gate, ta sunkuyar da kai ta gaishesa ya amsa da murmushi yace “How are you Nihal?” Ta daga kai ta kallesa tace “Alhamdulillah” Yace “Maa sha Allah” Tana biye da shi suka shiga parlon gidan, ganin ta zauna a parlon ya daga kafada yace “Tana can daki, ki shiga” Nihal tace “Ko zaka dan mata magana ta fito” Yace “Aa, just go in” Mikewa tayi ta nufi kofar dakin da ya nuna mata, a hankali ta kwankwasa kofar, Nihad ta juya tana kallon kofar, to me xai ce mata yake mata Knocking, can dai ta mike ta nufi kofar ta bude a hankali, ido hudu suka yi da Nihal, wara ido tayi ta rungumeta tace “Yaushe kika dawo Nihal?” Nihal na Murmushi tace “3 days ago” Sai kuma Nihad ta hade rai ta koma cikin dakin, Nihal ta bi ta da kallo sai kuma ta bi ta cikin dakin ta kulle kofar, Nihad tace “Wato ke har xa a iya hada baki dake a cuceni ko Nihal? Ni nasan babu yanda xa ayi kice baki san komai a kan abin nan da Abba yayi min ba” Innocently Nihal tace “Wallahi ban san komai ba Nihad, kiji har na rantse” Nihad tace “Toh sai aka ce maki yarda xan yi da ke? Bayan nasan har tadi ku ke yi da drivern nan a waya amma kice baki sani ba?” A hankali Nihal tace “Allah ne shaida na, amma meye ribata idan nayi maki karya?” Nihad ta tabe baki tace “We have already sort out things da shi daxu da safe, and we are okay with our plan” Nihal tace “What plan?” Nihad tace “Ba sai kin ji ba, ina umma?” Nihal ta mika mata wayarta tace “Tace in na xo ki kirata” Murmushi Nihad tayi ta amshi wayar ta tafi can karshen gado ta hau kiran Umma, Umma na dagawa tace “Auta har kin je gidan ne?” Nihad tace “Umma ni ce” Umma tace “Aa Nihad, wato dai wannan matsiyacin duk wayar da aka baki sai ya karbe ga shi tatattce ko?” Nihad ta tabe baki tace “Wallahi Umma” Umma tace “Toh xa mu xuba da shi kuwa, xan kawo maki waya sannan in mika masa a gabana ya damka maki wayar da hannunsa” Nihad tace “Kin ma san abinda yayi min Umma?” Umma ta zaro ido tace “Me yayi maki?” Nan Nihad ta labarta ma Umma garinsu da ya kai ta ta kusa mutuwa, Umma tace “Ikon Allah, amma shine matsiyacin nan ya samu waje yake nuna ma mutane isa daga an aura maki shi? Asha ɗan kauyen kayau ne” Nihad tace “Wllh Umma ban gama rainasa ba sai da naje garinsu, yanxu 100% na rainasa wallah, Umma ko wuta fa babu a garin, sannan rafi suke xuwa debo ruwa, kai ni baxan ma iya baki labarin garin nan da baki ba, sai da nayi rashin lafiya kamar xan mutu sannan ya dawo da ni cikin gari” Umma da ke ta sauraronta tace “Ikon Allah, dama ance talaka da matsiyaci basu iya samun waje ba, ki ga yanda ya dawo birni ya kile yake daddaga ma mutane kai alhalin ko mage me gata baxata iya rayuwa a kauyen ba” Nihad ta sauke ajiyar xuciya tace “Na sha mamaki Umma, ɗan kauyen kayau ne wllh, kuma yanda kika gansa fari haka family dinsa suke da haske a kauyen” Umma tace “Toh Allah ya kyauta, in sha Allah gobe ko jibi ina nan shigowa daughter” Nihad tace “Toh Umma kar ki manta wayar, idan ya so kamar yanda kika ce sai ki basa ya bani a gabanki sannan ki ja masa kunne sosai kar yace xai amshe” Umma tace “Kar ki damu sai dai na zo” Daga haka suka yi sallama, Nihal na kallon Nihad tace “kinsan Mumy bata da lafiya kuwa Nihad?” Nihad ta kalleta tace “Haba? To ai ni ba a gaya min ba” Nihal tace “Ai kam bata da lafiya, in kirata ku gaisa?” Nihad ta ɗan yi shiru sai kuma tace “Ki bari anjima da daddare xan kirata” Nihal tace “Toh shkkn” Nihad tace “Idan xa ki ci abinci ga indomie can kitchen ki dafa fa” Nihal ta mike ta fita daga dakin, tana shiga kitchen taga kayan miya kawai tayi deciding ta dafa jollof rice, tana cikin grating kayan miyan taji muryar khalil yace “Sannu da aiki” Ta kalli kofar da sauri sai kuma tayi murmushi tace “Nagode” Yace “Yaushe xa ku kare hutun?” Tace “Nan da sati biyu” Yace “Ohk nan xaki gama hutun ko?” Tace “Aa ni da gobe xan tafi, i don’t want to over stay my welcome” Murmushi yayi yace “Aa kiyi hutunki kawai a nan” Ita dai bata ce komai ba tana ci gaba da aikinta, juyawa yayi daga karshe ya bar kitchen din. Bayan Magriba yana xaune a parlor Nihal ta fito daga daki xata je kitchen ta xuba ma ita da Nihad abinci, ganin khalil zaune parlon ta koma daki wajen Nihad tace “Ki fito ki zuba masa abinci, ban fa xuba masa ba tun daxu” Da mamaki Nihad ke kallonta, sai kuma tace “A saboda me xan xo in xuba masa abinci? Dama da shi kika dafa abincin ne?” Nihal dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita, Nihad ta rike ha6a tace “Ji wani iyayi wai in xuba masa abinci kamar wani mijina, ashe xai tsufa bai ci abincin ba” Tsaki ta ja ta jawo wayar Nihal for the 10th time ta sake kiran layin Aliyu amma a kashe, kwantar da kanta tayi saman pillow kamar xata yi kuka don har ta gaji da trying layin nasa, tun xuwan Nihal take abu daya, Nihal na komawa kitchen ta fara xuba masa abincin a plate sannan ta dauka ta fito parlor ta nufesa ta durkusa tace “Ga abinci” Yana kallonta yace “Thank you Nihal” Ta mike ta koma kitchen din ta xuba ma ita da Nihad a tare, kadan Nihad ta ci abinci duk hankalinta a tashe yake bata samu Aliyu ba, Nihal ta ci abinda xata ci ta bar mata ta koma saman gado ta dau wayarta tana dannawa, Daga karshe wajen karfe goma da taga Nihad ba ci xata yi ba ta dau plate din ta fita, Bayan ta kai kitchen ta fito khalil na kallonta yace “Wani level kike a makaranta?” Ta tsaya tace “Level daya muke da Nihad” Yace “But in tambayeki” Ta ɗan tsaya sai kuma ta dawo parlon ta xauna tana kallonsa yace “Ke kika ce ma Abba Ahmadu Bello University kike so?” Nihal tayi murmushi tace “Aa, kawai cewa yayi can xan je ni” Yace “Ita kuma er uwarki fa?” Ta sunkuyar da kanta tace “He gave her option” Khalil dake ta kallonta yace “Ohk ke daga baya baki ce masa makaranta daya kike son xuwa da er uwar taki ba?” Nihal tace “Ya Usman da Mumy sun masa magana a lkcn, Mumy tace masa tunda har Nihad ta zaba Maryam Abatcha nima ya biya mun Maryam Abatcha din mu tafi tare ko kuma duk mu tafi ABU, amma sai yace Nihad kawai xata je ni in tafi ABU, he can’t afford the fee of Maryam Abatcha for the two of us” Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace “Kuma Ummanku bata ce komai ba?” Nihal ta girgiza kai tace “Kawai ce min tayi inyi hakuri in tafi ABU din” Khalil ya gyada kai yace “Amma secondary daya ku ka yi ko?” Nihal ta girgiza kai tace “Shi ma ba daya muka yi ba, ita Nigerian Turkish tayi, ni kuma Yan dutse nayi” Khalil ya gyada kai yace “Ohk, yan dutsen kamar su Amina da Sudais nan  suke xuwa ko?” Nihal tace “Har Aunty Kamila da Ya Usman da ya farooq ma can suka yi, Nihad kadai ce tayi Nigerian turkish” Khalil yace “Amma kamar er uwartaki tafi sabawa da Ummanki akan mamanta ko” Nihal tace “To ai a bangaren Umma take, ni kuma ina side din Mum dinta, though I don’t know for her” Shiru Khalil yayi yana kallonta, can yace “Maa sha Allah, hakan yayi…. amma wani saurayinta da ya zo can gida ranan, sun dade tare ne?” Nihal tace “Wai Aliyu? Yea definitely shi, don ita bata kula wani saurayi idan ba shi ba, shekaran da ta shiga Maryam Abatcha suka hadu, shekara uku kenan” Yace “Ohk, kinsan saurayin sosai kenan?” Nihal ta bude ido tace “Nasan shi mana, he is the son of General Jikamshi…” Muryan Nihad dake labe jikin pillar din corridor tum daxu ya katse Nihal, cike da bacin rai Nihad tace “A gidan uwar wa kika san shi? Shi Aliyun kike tunani kinsani? Har da wani gaya masa sunan babansa salon yayi masa mugun abu irin nasu na kauye? To wallahi baki san shi ba kuma baxa ki ta6a saninsa ba, dama don ki zo ki hadu da wannan mutumin ku kafa munafurcina ya sa kika zo gidan nan ashe ban sani ba? To wallahi ni dai ki tashi ki tafi baxa ki kwanan min a gida ba, ai dai mun ga juna, har da wani ce masa ni kadai nayi Nigerian turkish, to wani yace kar kema kice ma Abba can kike so? Naga dai choice dina ne kuma Abba yayi accepting, sannan Maryam Abatcha ma wani yace kar ki sakar ma Abba kuka kice ke baxa ki je ABU ba sai dai Maryam Abatcha? Wallahi kin ban mamaki har xaki zauna da bare kuna cakalkalar namana ko tausayina baki ji ba, to Allah ya isa wannan gulman nawa da kika yi” Nihal dai bata ce mata komai ba, Banda kallon Nihad babu abinda khalil ke yi, tana huci tace “Shi kuma saboda gulma har da wani cewa nafi son Umma, dama ashe maza na gulma ban sani ba? Kuma ai Umma da Mumy duk daya suke a wajena babu wani bambanci, to tunda dai mun ga juna zo ki dau handbag dinki kiyi tafiyarki” Mikewa Nihal tayi ta nufi daki, Nihad ta bi ta da harara, sai ga ta ta fito sanye da hijab tana rike da handbag dinta ganin xata nufi kofa Nihad ta rikota tace “Ina xa ki tafi da daddaren nan” Nihal ta fizge Hijab dinta hawaye cike idonta ta nufi kofa, Nihad ta bi bayanta da sauri tace “Ke ni fa wasa nake maki ina zaki da daddaren nan” Tuni Nihal ta fice daga parlon, Nihad ta marairaice tana kallon Khalil tace “Don Allah kayi mata magana, ni wallahi ba haka nake nufi ba” Ko kallonta Khalil bai yi ba, hakan yasa ta fita da sauri, can ta tarar da Nihal zaune bakin gate dake kulle tana rera kuka, kukan ta ita ma ta fara ta durkusa gabanta tace “Don Allah kiyi hakuri wallahi i didn’t mean it, ni ba da ke nake ba, da shi nake”

29

Ganin Nihal taki tanka ta sai kuka take, Nihad ta mike da sauri ta koma cikin gidan zata kira Khalil, a bakin kofa ta kusa buge sa ya turata tayi baya xata fadi ganin hakan yayi saurin jawota ta fado chest dinsa, ta zaro ido ta daga kai tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba ya turata gefe ya sauka xuwa wajen Nihal, bin sa tayi da kallo, yana isa wajen ya durkusa gabanta a hankali yace “Ki yi hakuri Nihal, don’t take all what she said personal” tana goge hawayen da ya ki tsaya mata tace “Ka bude min gate in tafi gida” Yace “Ba amfani hakurin da nake baki kenan?” ta girgiza masa kai kawai, yace “Now, Behave like the good girl u always are, tashi mu koma ciki” Daga haka ya mike, ita ma ta tashi tana ci gaba da goge idonta, yana gaba tana bin sa har xuwa parlon, Nihad ta riga su shiga parlon kafin su karaso, bayan sun shigo tana kallon Nihal a hankali tace “Kiyi hakuri plss, i didn’t mean it” Nihal dai bata ce mata komai ba ta yi wucewarta daki, Nihad ta jefa ma Khalil wani kallo tace “Ai dai kaga abinda ka jawo, kawai ka sa yarinya a gaba kana koya mata gulma da munafurci alhalin ba halinta bane” Daga kai yayi ya kalleta, speaking calmly yace “Idan kina ci gaba da min rashin tarbiya, Billah xan tattara ki in mayar da ke kauyen can” Shiru tayi tana kallonsa, sai kuma ta 6ata fuska tace “Toh ni nace wani abu ne?” Bai sake kallonta ba, ta turo baki ta juya ta koma dakinta. Har Nihad ta gama shirin bacci Nihal bata ce mata komai ba, Nihad ta gama saka kayan baccinta wanda shi kadai ta tsira da shi a gidan ta dawo gefen Nihal da damuwa tace “Shine ina ta maki magana kin ki cewa komai ko?” Nihal ta daga ido ta kalleta tace “Me kike son in ce maki?” Nihad tace “Wallahi kema kinsan i didn’t mean it, you know i love u to the extent that i will never hurt you” Nihal ta ɗan yi murmushi tace “Amma duk kwanan nan jaraba kike min a waya ai” Nihad ta marairaice tace “Toh me yasa xaki dinga magana da worst enemy dina a waya? Yanxu da Amina ce ke waya da shi ko wasu can daban ai ni baxan damu ba, amma ke fa kinsan i Cherish u so much, why will u be communicating with my worst enemy?” Nihal tace “Toh shikenan, na maki alƙawarin baxan sake waya da shi ba, dama yawanci ina ce masa ya kai maki waya ne….” Nihad tace “No, just block him kawai” Nihal tace “If that will please u” Tana fadin haka ta dauko wayarta tayi blocking number Khalil sanan tayi deleting number daga wayar tana kallon Nihad tace “Done!!” Nihad tayi Murmushi tace “Kin hakura yanxu?” Nihal tace “On one condition” Nihad na kallonta tace “Ina jin ki” Nihal tace “Ki tashi ki tafi dakinsa” da mamaki Nihad ke kallonta, can tace “Amma  ina ga baki da hankali, inje dakinsa inyi masa me? So now u are keeping it in mind cewar mijina ne shi da har xa ki ce in je dakinsa? Why will u leave such thought a xuciyarki idan har ke masoyiyata ce?” Nihal bata ce mata komai ba ta ja bargo ta lumshe ido, Nihad ta ja tsaki ta mike ta koma can edge din gadon, ta fi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike fuskarta daure tana kallon Nihal tace “If that will please you shikenan” Daga haka ta dau Hijab dinta ta fice daga dakin kamar xata tashi sama, bayan ta saka hijab dinta ta kunna wutan corridor din tana kallon kofar dakinsa, can ta kyabe baki a ranta tace ba gwara taje parlor ta kwanta abunta kawai, kashe wutan tayi ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali sbda duhu, laluban dogon kujeran da xata kwanta ta shiga yi bayan ta shigo tsakiyar parlon, a tsorace ta koma baya rana zaro ido bayan lalubenta ya kai ta har jikinsa, ya mike zaune yana haskata da karamar wayarsa, kunya taji ya kamata ta juya tana sosa kai xata bar wajen, yace “Da wani abun da kike so ne???” Ta juyo duk da bata ganin fuskarsa sbda haskata da yayi ta daure fuska tace “Wani abu kamar me?” Yace “Kin fi ni sani ai tunda kika biyo ni nan kina tattaba ni” Tsayawa tayi tana kallonsa kamar me son fahimtar abinda yake nufi, can tace “Kai kasan abinda kake nufi ni ban sani ba” yace “Aa ki dai fada abinda kike so” a takaice tace “Abinda ke ranka shi nake so” daga haka ta xabga masa harara xata bar wajen ya fixgota ta fado gefensa, a tsorace tace “Don Allah kayi hakuri wallahi kwanciya na zo in yi, ni ba wajen ka na zo ba” Cikin husky voice dinsa yace “Duk dakinki babu wajen kwanciya sai kin fito parlor?” Ta boye fuskarta a huge muscles dinsa tace “Nihal ce tace idan ina son ta hakura sai na je dakinka, to ni kuma ina son ta hakura” kallonta kawai yake yana kara tabbatar da ainahin childishness dinta, Wani sanyayyen kamshi ke tashi a jikinta har gashin kanta, lkci daya kuma ya hade rai ya saketa, ta dago kai a hankali tana kallonsa, matsawa yayi daga kusa da ita ya koma daya side din kujeran, With full audacity tace “Xan shiga dakinka in kwanta kuma kar ka sake ka shigo har sai na fito” Bai tanka ta ba, ita ma bata jira yace komai ba ta mike ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi ta shiga tana bin ko ina da kallo, wani kamshi ke tashi a dakin, ta kalli jakarsa dake dakin ta juya ta kalli kofa, tana ta tsaye tana kallon kofar sai kuma ta nufi jakar ta tsugunna ta bude zip din, Chargern Iphone ta fara cin karo da, ta dinga kallon chargern tana jujjuyawa, wannan kuma na waye? Ko dai na Nihal ne? Tabe baki tayi ta ajiye, ta maida idonta kan Diary Milk chocolate masu uban yawa a jakar, kai….a ina ya samu kudin siyan wannan uban chocolate din, ko da yake kudin babanta ne, wato saboda samun waje har da su siyan chocolate, wani hoto ta gani ta dauka tana kallon matar da ke jikin hoton warce baxata wuce shekaru 54 ba, kana ganinta kaga halfcast, keenly Nihad ke kallon hoton tana ji a jikinta kamar ta ta6a ganin wannan matar, amma a ina?? Duk yanda ta so tunawa ta kasa, as in, she k6s sure ta ta6a ganin hotonta but where?? Bude kofar dakin aka yi ta mike a rikice, da sauri ya nufota ya warce hoton daga hannunta ya hadeta da bango yana mata wani mugun kallo lkci daya kamanninsa suka sauya, Sosai ta tsorata jikinta na rawa tace “A bude fa naga jakar xan….” Turata yayi har sai da ta fadi kasa rigijib, ya dau jakar gaba daya ya fice daga dakin. Da safe karfe tara saura khalil na zaune parlor Nihal ta fito, ta tsaya jikin kujera ta gaishesa ya amsa yace “How was ur night?” Tace “Alhamdulillah, Nihad bata tashi ba har yanxu?” Duk da tun jiya da daddare rabonsa da dakin bayan ya fita amma haka yace “Probably” Tace “Ohk, ni xan tafi” Yace “Ina za ki tafi?” Ta sunkuyar da kanta tace “Umma ta aikeni gidan wata frnd dinta in amsar mata sako, so karfe tara matar ke fita aiki, shine tace in je kafin tara” Khalil yace “But baki yi breakfast ba ai” Tace “Na tashi da azumi yau” Shiru yayi yana kallonta tace “Idan ta tashi kace mata naje amsar ma Umma sako” Yace “Toh mu je in ajiye ki” Da sauri tace “Aa ba fa nisa, kuma in sha Allah xan dawo anjima” Yace “Are you sure?” Tace “Sure” Yace “Toh Allah ya tsare” Tace “Ameen” Daga haka ta nufi kofa ta fita. Goma saura Khalil ya tashi ya shiga dakinsa don wanka yake son yi kuma yaga bata da niyyar fitowa, kwance ya sameta a kasa, ya tsaya bakin kofa yana kallonta, ta mike xaune cikin rawar tace “Ba shkkn ba hankalinka ya kwanta kafana na min ciwo yanzu” Kallon kafar yayi, kafin ya karasa kusa da ita ya durkusa ya daga kafar, ta sakar masa kuka ta janye, hade rai yayi yana kallonta sai kuma ya sake jawo kafar,  ihu ta kwala tace “Wallahi ciwo yake min” Targade ya ga tayi a kafar, ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, da kyar ta iya daurewa ta shiga bandaki da asuba ta wanke bakinta da mouth wash ta dauro alwala ta fito tayi sallah, kamar kar ta ɗan motsa xuwa bandakin shine kafar yayi mata tsami kafin gari ya waye, dawowa dakin yayi ta daga kai tana kallonsa, ya karaso gabanta ya durkusa ya bude man zafin hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, bayan ya debi man zafin ya kamo kafarta, zaro ido tayi tana kokarin janye hannunsa a kafarta ya daure fuska yace “Kar ki sake ta6a ni Malama” yana gama fadin haka ya fara ja mata kafar yana kokarin gyara mata targaden, ai bata san sanda ta yunkuro ta rirrikesa ba tana kukan azaba tace “Nashiga uku Abba” Bai sarara mata ba har sai da ya tabbatar kafar ta dawo dai dai, kuka kawai take ta kankamesa duk ta hada zufar wahala, bayan ya sakar mata kafa shi ma ta sakesa tana komawa baya, kallonta kawai yake, ta turo baki tana share idonta, yace “Sallan asuban ma yafe maki aka yi sbda kinyi targade ko” Ta hade rai tana kallonsa tace “Ai ni ba kafura bace” Bai ce mata komai ba ya mike ya nufi kofa, da sauri tace “Ka kira min Nihal plss” yace “Warce kika kora ko wacce?” daga haka ya fita dakin, a hankali ta lallaba ta mike ta hau saman gadon ta kwanta tayi lamo a saman pillow, wato tafiya Nihal tayi upon all her pleas. Kafin azahar Nihad taji tana iya taka kafar, a hankali take dingishin ta fito daga dakin, ta shiga nata dakin, kallon katon ledan dake saman gado ta dinga yi, kafin ta karasa ta bude ledan, abaya ta gani masu ɗan karan tsada sun kusa kala goma, da mamaki ta dinga kallonsu tana warwaresu, sannan ga undies da cream din shafawa da turarurruka duk a cikin katon ledan, da sauri ta fito parlor tana kallonsa tace “A ina ka samu kudi ka siya min abayan nan?” Ya kalleta a takaice yace “Kudin babanki mana” Nihad tace “To amma wa ya zabo abayan?” Yace “Ni ɗan aike ne, kasuwa kawai aka aike ni naje na amso” Ta kyabe baki tace “I thought as much” Daga haka ta juya ya bi ta da kallo har ta shiga daki, wani Murmushi yayi ya maida idonsa kan tv da yake kallo. Bayan ta yi wanka ta shirya cikin daya daga abayan, sosai yayi mata kyau ya amshi fatarta, ba laifi haskenta ya fara dawowa amma ramar na nan, ta fito parlor, kallo daya yayi mata ya dauke idonsa, ta wuce kitchen sauran abincin da Nihal ta dafa daren jiya ta kara dumamawa ta xuba ta koma daki ta ci, har kusan la’asar Nihad na ta xuba ido taga ko Umma xata zo yau din ko sai gobe, amma bata zo ba, wajen karfe biyar ya bude kofar dakinta yace “Ki sameni a mota” Da ido ta bi sa har ya bar wajen, sai kuma ta mike ta dau mayafinta ta bi bayansa, duk da yana cikin motar ta ki shiga, she can’t take that risk anymore, tana kallonsa da kyau tace “Ina za mu je?” Yace “Gidanku” Ta ɗan yi jim, sai kuma dai ta shiga bayan motar ta kulle, suna barin gida taga sun dau hanyar gida, ta ma rasa ko farin ciki xata yi ko akasin hka, the only good thing of going to that house is that xata ga Umma bayan nan ita bata marmarin ma zuwa gidan…. Sai da suka kusa yace “Ki bude kunnuwanki ki saurareni da kyau, zan kai ki gida ba don komai ba sai don ki gaida mahaifiyarki da bata da lafiya, idan Abba na nan shi ma ki gaishesa, bayan haka xa mu fito daga gidan…” Da mamaki Nihad tace “Kana nufin sai in shiga har gidanmu in fito ban je bangaren Umma na gaidata ba??” Dai dai nan suka shigo layin, yana kallonta da kyau ta madubi yace “Ba don ki je bangarenta ki gaidata na kawoki gidan ba, a duk inda kika hadu da ita a nan xaki gaisheta babu xancen xuwa ɓangarenta, idan kuwa kika ce baxa ki bi umarnina ba, Billah na maki alƙawarin muna fitowa daga gidan xan maida ke garinmu da zama na har abada” Shiru Nihad tayi bata ce komai ba, bayan yayi parking yace “Kin ji ko baki ji ba?” Ta hade rai tace “Na ji” Bude motar yayi ya sauka ita ma ta sauka fuska daure, har sannan dingishi take, Aminu kamar xai goya Khalil tsabar farin cikin ganinsa, Nihad ta kara tsuke fuska ko kallonsa bata yi ba ta shige cikin gidan, Aminu yayi kasa da murya yace “Ciwo ta ji a kafar take dingishi?” Khalil yace “Zan fito yanxun nan” Daga haka ya bi bayan Nihad, Umma ta fito daga bangarenta kenan ganin Nihad ta hau tafa hannu tana cewa “Oyoyo oyoyo” Nihad ta ɗan saci kallon Khalil dake bayanta yana kallonta, ta sunkuyar da kai a hankali tace “Umma ina yini” Umma tace “Karaso mu shiga ciki daughter” Nihad tayi karfin halin cewa “Xan shiga wajen Mumy ne tukunna” Umma ta saki baki tana kallonta, tuni khalil yayi part din Mumy, Nihad ta bi bayansa kamar xata yi kuka, haka Umma ta bi su da kallon mamaki, kai ko makaranta Nihad ta dawo ba wani lallai taje bangaren Mumy ta gaidata ba, Umma kuwa dama kafin ta fita sai ta shiga ta gaya mata ga inda xata, haka kuma idan ta dawo, abinda Nihad tayi yanxu sai yayi mugun daure ma Umma kai. Nihad ta kasa hada ido da Mahaifiyarta bayan sun shiga parlon, Mumy ta amsa gaisuwar khalil da fara’a, Yace “Ya karfin jikin?” Tace “Alhamdulillah jiki da sauki” Nihad na wasa da veil dinta tace “Mumy ya jikin?” Mumy dake kallonta tace “Alhmdlh” cousin din Mumy ce ta fito daga bedroom suka gaisa da khalil cikin mutuntawa, Nihad dai sae kallonta take, ganin ta juya ta koma daki ba tare da ta bi ta kanta ba,  Nihad ta mike a sanyaye ta bi bayanta, gaisheta tayi, maimakon ta amsa sai ta hau ta da fada, tace “Ban kara tabbatar da cewa ke mahaukaciya bace shashasha sai yanxu, ace uwarki ba lafiya tun da kika bar gidan nan amma kika rasa inda xaki samu wayar kiranta? nan kuwa a duk sanda matar nan Umma ta shigo sai tace ai kunyi waya, anya kina son gamawa da duniya lafiya kuwa Nihad? Kullum bawan Allahn nan sae ya shigo gidan nan gaida uwarki amma sbda ke ba yar halaq bace baki ta6a cewa xaki biyosa ki duba jikinta ba, to duniya ce dai wanda bai zo ba ma jiransa take, idan kuma Umma ce tayi nakudarki ta haifeki xa mu ji” Nihad ta zauna hawaye na sauka idonta tace “Aunty ni tsoro nake ji shi yasa ban kirata ba, kuma wallahi bai ta6a ce min xai zo nan ba ban biyosa ba” a fusace Aunty Zulai tace “Sai yace maki xai zo?? Shashasha kawai kin bi kin ja mana abun kunya a duniya wanda har yanzu kukan wannan mugun abun naki muke, wallahi sai nan gaba xaki yi kukan gaske da hawayenki a kan wannan video din Nihad, nan gaba xaki san illar da kika ma kanki a duniya a kan video din nan, kuma yau da ace wannan mijin naki iyayensa da danginsa yan boko ne ko a cikin gari suke wllh baxa su ta6a bari ya aureki ba ko da kuwa shi ya ganki yace yana so balle wannan manna masa ke kawai aka yi sbda babanki ya yaba da hankalinsa, amma da ace ɗan birni ne wllh gori wajen danginsa da yan uwa ma kawai ya isheki ki hadiye xuciya ki mutu wataran, kina ganin kamar abu ya lafa ai shkkn an manta, yarinya sai nan gaba xaki gane abinda nake gaya maki ba yanzu ba, don haka in zaki rungumi mijinki ki bisa ki masa biyayya ki lallaba aurenki, to gatanki, idan kuwa kin ce ba haka ba kika kuskura kika bari aurenki da bawan Allahn nan ya samu matsala to idan ba kauyen ubanki xai sake komawa ya samo maki wani mijin ba ina me tabbatar maki babu wanda xai aureki don ma in gaya maki ki ji da kyau” kuka kawai Nihad take tana kallonta, Aunty Zulai tace “Shikenan ni abinda xan gaya maki kenan, tashi ki bani waje” Nihad ta mike tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta fito parlor kanta a kasa, zaunawa tayi saman Carpet ta dago kai a hankali ta kalli Mumy taga kallonta take, cikin sanyin murya tace “Mumy ina su Sudais” Mumy tace “Sun tafi makaranta” Nihad bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes Mumy tace “Kin ga wancan bawan Allahn dake zaune?” Nihad ta daga kai ta kalli Khalil da Mumy ke nuna mata bata dai ce komai ba, Mumy tace “In har kina son gamawa da ni lafiya to ki zauna lafiya tare da shi, idan kuwa kince ba haka ba, ba baki na maki ba amma baxa ki ta6a ganin daidaituwar lamarinka ba, don haka kika kuskura kika kashe auren nan naki sae dai ki nemi warce ta haifeki ba ni ba” Nihad ta fashe da kuka sosai tana kallon Mumy, shi dai Khalil bai iya ya daga kai ya kallesu ba, Mumy ta kallesa tace “Ku gaida gida Ibrahim….  nagode sosai, xan shiga ciki” Yana kallonta cikin sanyin murya yace “Allah ya kara lafiya” Ta amsa da Ameen ta mike ta shiga dakinta, kuka kawai Nihad take kamar ranta xai fita a parlon, bayan few seconds Khalil ya mike ya fita daga parlon, mikewa ita ma tayi tana kuka ta bi bayansa.

30

Suna fitowa parlor Nihad na kallon khalil cikin kuka tace “Don Allah ni ka barni in je in gaida Umma” Juyowa yayi yana kallonta yace “Akwai wata Umma bayan warce kike gaida da muka shigo daxu?” Muryarta na rawa tace “Toh kawai a parlor xan gaisheta?” Yace “Eh” Kuka kawai take tana kallonsa ta wuce sa kamar xata tashi sama ta nufi kofar fita parlon, bin bayanta yayi ya sameta jikin mota tana kuka kamar ranta xai fita, ya zaga driver seat ya bude ya shiga, bude bayan motar tayi ta shiga don ita har yanzu Drivern gidansu ne shi, Aminu ya marairaice bayan Khalil ya fito da mota waje yace “Ina ta rokon Saminu ya jira min gate in kawo maka ziyara amma ya ki…” Khalil na kallonsa yace “Wataran ma baxa kayi gadin ba gaba daya, sannan matsayinka xai dawo dai dai da na kowa a duniya” Aminu ya daga hannu biyu sama yace “Allah Ubangiji ya amsa bakinka, Allah ya dubemu yanda ya dubeka lkci daya, wannan gagarumin ci gaban da ka samu Allah ya sa mu a danshinka, wayyo wa yaga Aminu ya daina gadi, duk basur ya cinye ni sbda zama kan benchi daga safe har dare, na ma ji Alhaji yace xa a dubo sabon driver tunda kai yanxu ai ba batun tuki kuma” Murmushi kawai khalil yayi ya sa hannu a aljihu ya ciro dubu daya ya mika masa yace “Ga wannan ka sha kankana” Aminu ya karba hannu bibbiyu yana cewa “Allah ya taimakeka oga” Wani shegen kallo Nihad ke ma daga Khalil din har Aminu tana jin kamar ta hadiye zuciya don takaici, nan ta kara jin wani sabon tsanar Khalil ya dirar mata, wato fafa yake yi sbda Abba ya aura masa ita, ji yake babu ya shi a duniya, Bayan sun bar layin tana kallonsa ta madubi tace “Kai yanzu kawai jin kanka kake saboda Abbana ya daukeni ya aura maka ko? Gani kake ka fi kowa sa’a a duniya tunda yanxu kudin da Abbana ke baka ya ninku linkin ba linkin har da su kyautar dubu daya, shkkn xaka dinga amfani da ni kana cin kudin Abbana” Khalil yayi wani murmushi bai tanka ta ba, ta murguda baki tace “Ai shi dama talaka bai iya samun waje ba, nasan yanxu alfahari kake yau gani matarka ko?” Yace “Ohk” Ta kara murguda baki bata kuma ce masa komai ba har suka isa gida, sauka tayi daga motar bayan ya bude gate tayi shigewarta ciki kamar xata tashi ciki, yayi wani murmushi kawai ya motar ya shigar da shi compound din. Bayan Nihad ta idar da magrib ta fito parlor ta samesa kwance saman dogon kujera yana waya, ganin bai lura da fitowarta ba duka a hankali ta rarrafa har bayan kujeran ta kasa kunne tana sauraron wayar da yake yi, A hankali taji yace “Nan da wata daya in sha Allah xan dawo, idan kuma na dawo baxan sake fita ba sai bayan aurenmu” Yana fadin haka babu sunan da ya fado ran Nihad sai Nadeeyah don har ta haddace sunan nata a xuciyarta, ta ɗan kyabe baki tana tsugunne bayan kujeran tana kara kasa kunne, Taji yace “Aa, akwai dalilin da ya sa na dade wannan karan Nadeeyah, ba wai da son raina bane, amma in sha Allah na kusa gama abinda nake yi, ni kaina na gaji da USA haka” Buda baki Nihad tayi hangangan jin sunan kasar da ya kira, Tunda aka haifeta bata ta6a ganin me lafta karya kamar wannan mutumin ba, wato USA?? Mutumin da ko ruwa ta kasa sha a garinsu balle ta ci abinci shine yake karyan yana USA, ya ma san full meaning din USA din kuwa?? Taji yayi dariya ya mike zaune yace “Wai da gaske??” Magana yake amma bin parlon kawai yake da idanuwansa don banda kamshin Nihad babu abinda yake ji a parlon, amma kuma bai ga alamarta ba, don haka ya koma ya kwanta a hankali yace “Ke ce farko kece karshe Nadeeyah, in sha Allah baxan hada ki da kowace mace ba, don kin min hallacin da baxan manta ba, in dai kuma ba baturiya kike son in auro mu dawo Naija tare in hada ku gida daya ku zauna ba, kinga ai nasan baxa kiyi kishiya da ita ba” bayan few seconds yayi murmushi yace “Ya na ji kin yi shiru?” Mikewa Nihad tayi tana tafe hannu tace “Ni wallahi ban ta6a ganin inda babba yake karya ba sai kai…” tuni Khalil ya katse wayar, ya mike tsaye yana kallonta, da mamaki Nihad tace “Kasan ma’anar USA kuwa? Kasan ina ne Usa? Me yasa baka tsoron yin karya a rayuwarka?” Yace “Kin karya daya daga sharadinmu don haka nima dole xan karya daya….” Yana gama fadin haka ya bar parlon ta marairaice ta bi sa da kallo har ya shige dakinsa, ta fi minti biyar tsaye parlon can dai ta bi bayansa, a hankali ta murda kofar dakinsa, tsaye ta gansa yana unbuttoning shirt dinsa, ta turo baki tace “Toh kayi hakuri” Ya juyo ya jefa mata wani kallo yace “Baxan yi” Ta marairaice tace “Don Allah mana” Bai sake kulata ba ya shige bandaki, ta ɗan kyabe baki, sai kuma ta dinga kallon wayar tasa dake gefen gado, tana tafiya a hankali kamar munafuka ta karasa gadon ta dau wayar, number Nadeeyah ta shiga tana kallon number tana ta6e baki, wai ba ma tayi blocking din number nan ba, wato unblocking yayi, tana dai ta kallon number, can ta ja tsaki kasa kasa ta kara blocking number tayi deleting ta ajiye wayar ta fita da sauri. Fitowa Nihad tayi dai dai sanda Khalil ma ya fito daga dakinsa, ta 6ata fuska tace “To ai cikin deal dinmu baka ce idan ana kwankwasa gate kai kadai ne xaka dinga xuwa budewa ba, nima xan iya fita in bude tunda ba kai kadai bane cikin gidan” Ba abinda yace mata ya nufi kofar parlor xai je bude gate din da ake ta bubbugawa kamar xa a cire, Nihad ta tafi jikin window dake parlon tana kallonsa har ya isa gate din, Yana tsaye bakin gate din yace “Waye?” A mugun fusace Umma tace “Uban me tambaya, nace uban me tambaya, halan gidan na ubanka ne idan ka ji an kwankwasa gate sai ka tambayi waye sannan ka bude?” Kawar Umma dake gefenta tace “Wai kaddai Dreban ne ke maki wannan tambayar?” Umma tace “Atoh ba matsiyaci bane? Kuma kin mance matsiyata basu iya samun waje ba?” Hajiya Turai tace “Aa ga alama” Umma tace “Ai kinsan gidan Ardo ko Nenne dake kauye ne shi yasa yake tambayar waye” Hajiya Turai ta kwashe da dariya tace “Sai dai haka kam” A mugun fusace Umma tace “Au, baxa ka bude min gate din ba??” Khalil yace “Me gyara yana hanya don tun jiya gate din ya samu matsala, mu ma bamu samu fita ba duk yau, don haka sai ku jira” Buda baki Umma da kawarta suka yi jin abinda yace, shi kam yana gama fadin haka ya juya ya bar bakin gate din ya koma ciki, Nihad na masa wani kallo tace “Waye a gate din da kaki budewa?” Yana kallonta da kyau yace “Warce kika yaudari kanki kika bai ma matsayin mahaifiyarki” Nihad ta zaro ido tace “Umma?? Shine kaki bude mata gate din?” Bata tsaya jin abinda xai ce ba a fusace ta taho xata fita daga parlon ta je ta bude ya fixgota, tana tsaye dab da shi yana kallonta da kyau yace “In har kina son mu rabu cikin salama ba tare da iyayenki sun yi fushi da ke ba ko an ga laifinki to kar ki tsallake umarnina ko daya, datse alqarki da warce kike kira da Umma yana daga cikin umarnina gare ki, bayan mun rabu xaki iya ci gaba da mu’amala da ita wannan ba matsalata bace, amma muddin muna tare babu ke babu ita” Nihad was shocked and lost of words at first, can dai tana girgiza tace “Amma kasan abinda kake cewa kuwa? Kasan warce kake cewa xaka datse alaqata da ita?? Kasan wacece Umma kuwa ko dai duk zamanka gidanmu baka san matsayinta ba? Matar Abbana ce fa? First wife din Abbana ce, She is my step mother, kuma duk duniya babu wanda ke sona baya ga ita, ban san dai ko Mumy da ta haifeni ba ba tunda ita bata ta6a nuna min son da take min a fili ba na Umma kawai na sani, Umma tun tasowata ban ta6a cewa ga abinda nake so a duniya an hanani a gidanmu ba, kome nake so shi nake samu, yanda Umma taga Abbana ke ji da ni haka ita ma tafi sa ji da ni, kuma bata ta6a hanani yin duk abinda nake so in yi ba tunda a ɓangarenta ma na taso, she is 100% in support of me always, ta daukeni kamar er da ta haifa a cikinta, dai dai da second daya bata ta6a banbanta ni da Nihal ba, don sai taki goyon bayan Nihal amma ni ta goyi bayana, ba kuma ta son bacin rai na ko na second daya, yanda na shaku da Umma ko Mahaifiyata ban shaku da ita haka ba wllh, don dama tun ina karama ta maidoni dakinta, ita ce komai na, amma shine yau xaka bude baki kace min xaka datse alakata da Umma?? Kana da hankali ma kuwa?” Kallon cikin ido kawai khalil ke mata, bai kuma ta6a jin tausayin rayuwarta ba sai a wannan lokacin, Ta fashe da kuka tace “In har a sharadin rabuwar mu har da datse alakata da Umma to kar mu rabu din, kai xaka wahala ba ni ba” Tana gama fadin haka ta kwace hannunta daga rikon da yayi mata ta shige dakinta, zaunawa khalil yayi saman kujera deep in his thought yana sake digesting duk abubuwan da Nihad ta gama fada masa….. Ana magrib Nihad taji fitar Khalil, tun da rana take kuka duk idanuwanta sun kumbura saboda ya hana Umma shigowa gidan, tana jin fitarsa ta fito bakin gate din sai taji ya sa makulli, ji tayi kamar ta kwanta wajen tayi ta birgima, ta dinga rera kuka kamar ranta xai fita a wajen. Khalil na zaune parlon Abba, ya gaishesa kansa a kasa, kallonsa kawai Abba yake yana son jin me ke tafe da shi, hoping ba wani abun Nihad tayi masa ba, Khalil yayi kasa da murya yace “Alhaji dama na zo neman alfarma ne gun ka” Abba na kallonsa yace “Ina jin ka Ibrahim, fadi koma meye kanka tsaye” Khalil yace “Ina son xan koma garin mahaifiyata can Zaria tare da ita… Saboda xan ɗan yi noma a can tunda damuna ya fadi” Abba yace “Yanzu ai karkashin ikon ka take Ibrahim, ba sai ka tambayeni izini ba don xaka canza wajen zama da ita, iyaka ka sanar min don in maku fatan alkhairi sannan idan da tallafawan da xan maku sai a maku” Khalil dai ya sunkuyar da kansa, Abba yace “Maa sha Allah naji dadin noma da kace zaka yi, don noma ai shine tushen arziki dama, Allah Ubangiji ya baka nasara Ibrahim” Khalil yace “Ameen Alhaji, nagode” Abba yace “Yanzu dai ka sa a bincika maka nawa ake bada hayan gida a garin” Khalil yace “Ina da wani aboki a can na tambayesa jiya” Abba yace “Nawa yace maka?” Khalil yace “Dubu dari yace min” Kallonsa Abba yake ba ko kiftawa, can yace “Aa da dai a samo na sama da hakan Ibrahim, ni ko nawa ne ba matsala bane xan bada” Khalil na kallon Abba yace “Gidan a kusa da kauyen da xan yi noman yake, shi sa nace xan amsa” Abba yace “Dubu dari nawa kace?” Khalil yace “Dubu dari daya” Abba ya kasa cewa komai yana kallonsa, Gaba daya tunaninsa na kan Nihad duk da haushinta da yake kwana yake tashi da shi a ransa yasan baxai ta6a son ta zama uncomfortable a rayuwarta ba, deep down him yasan he still love his daughter” Abba ya sauke boyayyen ajiyar xuciya yace “Shikenan zan sa maka kudin” Khalil yayi noticing change a muryar Abba hakan ya sa bai dago kansa ba, Abba yayi breaking few second silence da ya biyo baya yace “Yaushe xa ku tafi?” Khalil yace “Ko zuwa satin da xa mu shiga in sha Allah” Abba yace “Ohk to amma ka sa abokin naka ya ɗan bincika min ko za a samu filaye a nan arean” Khalil ya daga kai ya kalli Abba yace “Toh Alhaji” Abba yace “Ina sauraronka zuwa gobe da safe” Khalil yace “Toh in sha Allah” Daga haka yayi ma Abba sallama ya mike ya fita, ɗan murmushi yayi kawai ya fice daga main parlor. Yana fita parlon Umma ta shigo da sallama, bayan ta zauna tace “Bako kayi ne halan” Abba ya girgiza kai yace “Ibrahim ne” Umma tace “Allah sarki, haka dai kawai ka hanani zuwa gun ‘ya ta in dinga duba halin da take ciki, yau kusan sati biyu kenan rabona da ita, wallahi kullum da ita nake kwana nake tashi a raina, in ji dai suna lafiya?” Abba yace “Lafiya lau, zuwa yayi min da wani batu” Umma ta gyara zama tace “Wani batu kuma, to Allah ya sa dai lafiya” Abba yace “Lafiya lau, wai zai je noma garinsu xai tafi da ita” Umma ta zaro ido tace “Ya tafi da ita ina?? Yaushe Nihad xata wani iya zama a garinsu? To sai kace masa me Alhaji?” Abba yace “Toh ai a yanzu dai ya fi mu iko da ita, babu ta yanda xan iya hanasa tafiya da matarsa Sumayya” Umma na girgiza kai tace “Aa Yallabai wannan ba magana bace, to ko dai ka sallama ma duniya er nan ne bamu da masaniya? Duk wannan punishment din da kayi mata na aura mata dreba  bai isheka ba sai ka ba dreba goyon bayan tafiya da ita kauyensu da sunan noma? Haba Alhaji ko ba kai ka haifi er nan ba kaddarar nan ya fada mata ai ka ji tausayinta ka raga mata balle er cikinka ce kuma masoyiyarka, ina laifin kace ya kawota nan gida ta zauna har sanda xai gama nomar tasa ya dawo daga kauyen nasu?” Abba yace “Aa, ai mu ba kananun mutane bane da zance ya bar ta gida Sumayya, tunda har ya girmama ni ya zo neman izinin tafiya da ita ni kuma baxan yi karanta ba a matsayina na mutum me kamala a gunsa, yanxu dai nace ya sa a bincika min fili a inda xa su zauna din, ko nawa ne xan siya, idan ya so ko 3 bedroom flat ne in sa a gina babu bata lkci, don yana min maganan sun samu gidan dubu dari, dama akwai gidan dubu dari a zamanin nan?” Shiru Umma tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, Abba ya daga kai ya kalleta jin tayi shiru, tayi murmushi tace “Maa sha Allah, gida xaka gina ma Nihad din a can kenan?” Abba yace “Hakan xai fi gaskiya, idan ma babu wuta garin a saka masu solar 24/7, sannan ayi borehole a gidan, ayi furnishing yanda ya kamata” Umma ta gyara zama tana Murmushi tace “Hakan yayi kyau kam gaskiya, Allah ya saka maka da alkhairi ya kara budi, kaga zata zauna comfortably baxata takura ba, har ma ta sake a gidan ta ji kamar a cikin gari take” Abba yace “Yeah!! So i think duka duka da filin da ginin ai baxai ci miliyan goma ko sha biyu ba ko?” Umma tace “Ehh to, xai iya zama hakan tunda ai ba cikin gari bane kila, balle ace filin xai yi tsada sosai” Abba yace “In sha Allah, ko zuwa gobe aka samu filin xa a daura gini kawai” Umma na Murmushi tace “Madallah, Allah ya kai mu goben, bari in je in gama abinda nake a sama” Abba yace “Alright” mikewa tayi ta fita daga parlon. Yau ma kamar jiya ana kwankwasa gate Nihad da Khalil suka fito a tare, bai ko kalleta ba har ya fita, ta bi bayansa don wannan karan sai dai duk abinda xa ayi ayi a bakin gate din in dai Umma ce sai ta bude mata, Ya hade rai ya juya yana kallonta yace “Meye kike bi na?” Ita ma ta hade rai tace “Kayi tafiyarka inyi tawa mana” ya ci gaba da tafiya tana bin sa har suka iso gate din, yace “Wanene?” Husnah tace “Assalamu alaikum” Ya wani hade rai yace “Nace waye?” A hankali tace “Husnah ce” Nihad ta hade tafin hannunta kamar xata yi kuka tace “Don girman Allah kayi hakuri ka bude mata, ni kenan sai inyi ta zama babu wanda ke xuwa wajena kamar mayya,x kuma ai a sharadinmu nace baxa ka ki barin kawayena su zo wajena ba kuma ka yarda” Kallonta kawai yake, nan da nan hawaye ya cika idonta tace “Don Allah fa nace maka” Duk Husnah na jin su ita kanta addu’a take Allah ya ta6a zuciyar Khalil ya bude mata gate din, Juyawa khalil yayi ya bar wajen, Nihad ta wara ido cike da farin ciki ta bude gate din, tayi tsalle ta rungume Husnah tace “Wallahi nayi missing dinki kawata, ina su Naf da zully?” Husnah tace “Ba su ma san xan zo nan ba wallahi, tun shekaranjiya kike raina in gaya maki, shine kawai nayi tahowata ban gaya masu ba” Nihad ta kulle gate din tana Murmushin jin dadi ta kama hannun Husnah da ta bi khalil da kallo har ya shige parlor, suna isa balcony Husnah tayi kasa da murya tace “Amma dai kawai in gaida mutumin nan don gobe ma ya barni in shigo, kinsan abun sai da siyasa kawata, barin ma shi da yake ɗan kauye gaishesan da xanyi yanxu xa ki ga farin cikin da zai yi kansa yayi kato, kinsan bakauye akwai son girma” Nihad ta kyabe baki tace “Kar ki wani gaishesa, meye hadinki da shi ko ina ruwanki da shi bayan ba wajensa kika zo ba, ni kaina da nake gidan ban ta6a gaishesa ba saboda bai isa ba balle ke” Nihad na gama fadin haka ta ja hannun Husnah suka shiga parlon, Husnah na hada ido da shi ta janye hannunta daga na Nihad dake jan ta zuwa daki, ta dan yi murmushin yake tace “Ina wuninmu?” A fusace Nihad ta ja Husnah fuuu suka wuce daki ta kulle kofar tace “Amma ba nace kar ki gaishesa ba? Meye amfanin gaishesa yanzu?” Husnah ta yatsine fuska tace “Ni kaina wllh sai bayan da na gaishesa naga rashin dacewan hakan, baki ga ma wani shan kamshi da yake shi a dole ya aureki ba, yanzu fa ji yake shi wani shege ne ya auri er mai kudi” Nihad tace “Ke mu fa mun riga mun ajiye deal kan cewa xai sakeni, na amince shi ma kuma ya amince ya kuma yarda ni ba class dinsa bace” Husnah ta zaro ido tace “Haba??” Nihad tace “Wallahi in gaya maki, ai yaga tsanar da nake masa tayi yawa baxan kuma ta6a raga masa ba shi yasa yaga gwara mu rabu…” Husnah tace “Yanzu yaushe yace xai sake kin?” Nihad tace “Ku dai kawai ku zuba ido ku ga ikon Allah” Husnah tace “Kai amma na tayaki murna wallahi, ashe shegen ya san abinda yake yasan ke ba class dinsa bace cikin ruwan sanyi xai rabu da ke” Nihad ta tuntsire da dariya tace “Wallahi fa in gaya maki” Husnah ta cire Hijab din jikinta ta jefar kan gado, Nihad tace “Yaushe kika dinka hijab ke da baki da ko guda daya” Husnah tace “Wannan ma a hostel na aro shi, ke akwai abinci yunwa nake ji” Nihad tace “Ehh daxu nayi stew, kawai spaghetti xan yi boiling” Husnah tace “Toh bari in yi boiling dinsa, akwai a kitchen ai?” Nihad tace “Ehh akwai” Mikewa Husnah tayi ta bude handbag dinta ta fiddo after dress ta daura a kan riga da wandon jikinta ta fita, Nihad ta jawo jakarta bayan ta fita ta bude, as usual kayan maye iri iri ta ga a jakar da Prophylactics dinta, Nihad ta mayar mata da kayanta ta dau wayarta da ta gani ta bude password don tasan password din nata, har tayi dialing number Aliyu sai ta tuna ba shi da number Husnah don haka baxata samesa ba, lkci daya jikinta yayi sanyi, sai dai kawai tayi dialing number Umma, Umma na jin muryata tace “Daughter, ina ta tunanin ta yanda xanyi waya dake tun jiya wllh, har cewa Nihal ta kai maki waya gida nayi amma er nan taki, Amina kuma kinga tunda ana hutu islamiyya take safe da yamma ita ma baxata yarda tayi fashi ba don in aikota wajenki” Nihad ta marairaice tace “Nima babu ta inda xan kira ki Umma” Umma tace “Kina ji na?” Nihad tace “Ina ji Umma” Umma tace “Kullum nayi sallah ina saka wannan tsinannen dreban a addu’a kan cewa Allah Ubangiji ya rabaki da shi cikin aminci, to sunansa kawai na sani ban san sunan mahaifinsa ba ko uwarsa” Nihad tayi shiru, sai kuma tace “Nima wallahi ban sani ba Umma” Umma tace “Yo ai nasan baki sani ba, ke baxa ki iya dubara irin na mace ba ki tambayesa sunan ya gaya maki, sai kace ba wayayyar Nihad dita ba, ai cikin salo irin na wayayyun mata zaki bi masa har ya gaya maki” Nihad tayi Murmushi tace “Toh shikenan Umma” Umma tace “Yauwa zuwa yaushe xan saurareki?” Nihad tace “Gobe” Umma tace “Amma number waye wannan?” Nihad tace “Na Husnah ne” Umma tace “Au tana can shegen ya bar ta ta shiga kenan” Nihad tace “Wallahi kuwa Umma” Umma tace “To yaushe xata tafi?” Nihad tace “Kamar fa kwana xata yi naga kaya kala biyu a jakarta” Umma tace “Madallah dai dai kenan, kinga gobe sai ki kirani kawai ta wayar nata” Nihad tace “Toh Umma” Daga haka Umma tayi mata sallama Nihad ta katse wayar, dai dai nan taji Husnah tayi wani kara, ta mike da sauri ta fice daga dakinta, Tana fita parlor Khalil na shiga kitchen din, ita ma ta nufi kitchen din da sauri.

31

Husnah ce tayi zaman dirshan a kitchen din dake malale da ruwa, gaba daya ta jike jagab daga saman cikinta har xuwa ƙafafuwanta, ta wawwara hannu ta runtse ido cikin daga murya tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Wayyoo na shiga uku na lalace, gaba daya na kone a jiki… Don Allah a kawo min agajin gaggawa” daga gefenta tukunya ce dauke da ruwan zafi a ajiye, Khalil ya shiga kitchen din da sauri yace “Me ya faru haka?” Ta bude ido ta fashe da matsanancin kuka tana kallonsa tace “Don Allah ka taimakeni wallahi, ruwa me uban zafi ne ya kwaro min gaba daya tun daga cikina har kafa, taliya naje zan zuba ruwan ya kifo min, don Allah ka kawo min agaji kar jikina ya toye” Da mamaki Khalil ke kallonta, kuka kawai take tana jijjige kafarta da hannu tana cewa “Wayyo Allah na, wllh ruwan ya tafasa sosai, don Allah a taimakeni duk radadi jikina yake min” Khalil yayi ma kofar kitchen din kallon kasa kasa jin kamshin Nihad, ya ganta tsaye bakin kofar, bai yarda ya kalli fuskarta ba, ya kashe gas din ya karasa kusa da Husnah ya mika mata hannu yace “Taso” Karaf ta cafke hannunsa ya dagota ta mike tana kara sautin ihunta tana cewa “Wayyoo mamata, Wayyoo zafi, na shiga uku me za a shafa min ya daina min wannan radadin da nake ji..m” Hanyar kofar kitchen din ya nufa da ita still ya ki kallon Nihad, ita kanta Husnah bata kalli Nihad ba sai gunjin kuka take tana jijjiga kai tana yi tana runtse ido, ganin Nihad ta ki matsawa daga kofar kitchen din Khalil ya daga kai a karo na farko ya kalleta, rungume hannu tayi tana kallon su, yace “Matsa a hanya” Ta zabga masa wani ta juya da sauri ta bar wajen ta wuce dakinta, Husnah ta bi Nihad da kallon gefen ido tana cewa “Don Allah a taimakeni kar jikina ya kwaile in ma asibiti ne mu je” sai kuma ta zame hannunta daga nasa tayi dai dai a kasa ta kwanta tana birgima tana kuka, dakinsa ya nufa ta bi sa da kallo, sai ga shi ya fito da makullin mota yana kallonta yace “Mu tafi asibitin” tana girgiza kai cikin kuka tace “Wallahi baxan iya tashi ba” Yace “Toh kira kawarki” Daga haka ya fita ya je parking space ya tada mota, Mikewa Husnah tayi tana gunjin kuka ta tattale hannu ta bi bayansa, tuni ta isa gun motar tana cewa “Don girman Allah mu yi mu tafi asibitin kar na mutu, ko ina zugi yake min” Ya bude mata back seat ta shige ciki, Tun da ya tada motar Nihad ta fito parlor ta tsaya jikin window tana kallon su, sai da ya bude gate ta ga ya dawo zai shiga motar kawai ta fito ta nufi front seat ta shiga ta kulle, ya bude gefen mazaunin driver yana kallonta da kyau yace “Ina za ki?” Ba tare da ta kallesa ba tace “Asibitin da za ku” Ya kalleta daga sama har kasa yace “Ohk, haka za ki je asibitin kenan” Fuska daure tace “Sai ka jira ni in dauko mayafina” Daga haka ta fice daga motar da Husnah ta cika da ihu kamar warce ake gunduwa gunduwa da namanta, tana ganin Nihad ta sauka tace “Don ya Rasulullahi ka ja motar mu tafi kar a rasa fatar jikina, wllh jin jikin nake kamar ba nawa ba, kar fatana ya karasa zagwanyewa” Bai ce mata komai ba ya shiga motar, amma bai ja motar ba, sai ga Nihad sanye da Hijab ta shige gaban motar, ya ja motar suka fita gidan ya sauka ya kulle gate. Wani asibiti da babu nisa daga anguwansu ya kai ta, duk nurses suka tattaso da sauri saboda tun daga Gate ihun Husnah ya cika asibitin, Nurse daya na kallon Khalil tace “Me ya sameta?” Khalil da ya koma gefe ya tsaya yace “Wai konewa tayi” Nan aka shiga da ita emergency aka dau scissors za a fara barke riga da wandon jikinta, Nihad dai na reception din hospital din ta zauna, babu wanda zai ce tare suke, Khalil kuma na kofar shiga reception din ya jingina da bango ya rungume hannunsa, wani ihu Husnah ta sakar ma nurses da Dr din tace “Don Allah a kira min yayana ya zo kila mutuwa zan yi, a kirasa ya zo kusa da ni” Wata Nurse ta fita ta kira Khalil, yana kallonta yace “Me xan yi a can din?” Rai bace Nurse din tace “Haba bawan Allah ko da baka santa ba ta bukaci ka je ai ko don saboda condition da take ciki zaka je, wai ko ba matarka bace?” Daga haka ta juya ta koma emergency ward din, Khalil ya bi ta da kallo kafin ya shiga asibitin ya bi bayanta, Nihad ta bi sa da wani kallo, bai ma san tana yi ba, yana tsaye bakin kofar ward din Husnah ta hangosa ta dinga miko masa hannu wai ya zo ya ceceta kar ta mutu, likitan da Nurse dai sun gama 6arke kayanta da scissors suna neman inda ta kone, Can likitan ya kalli Khalil da ya ki karasawa ciki yace “Wani irin ruwa ne ya zubar mata?” Khalil ya buda ido yace “Ban sani ba fa, ko kafin na fito ruwan ya gama kwararewa a jikinta” Nurse din na kallonta tace “Ruwan zafi ne ko dai ruwan dumi” Husnah ta hade rai tace “Ban gane ruwan dumi ba, sharrin zan ma kaina ince ruwa zafi ya zubar min a jiki bai zuba ba, kawai dai dama fata iri iri ce, amma Allah kadai yasan zugi da radadi da nake ji yanxu haka, har cikin raina nake jin wannan axaban wallahi” Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, likitan ya cire safan hannunsa yace “Nurse ki basu magunguna” Yana kai wa nan ya fice daga ward din, nan nurse ta fito reception ta harhada magungunan ta dawo ta mika ma Khalil Bill din dubu sha biyar, amsa yayi ya fiddo Atm card dinsa ya mika ma nurse din, daga baya ta sake dawowa ta bukaci pin dinsa sannan ta juya, Husnah dai sai gunjin kuka take tana kallon wata nurse dake mayar da kayan aikinsu mazaunin su tace “Aunty Nurses babu wani abu da za a shafa min?” Nurse din tace “An rubuta maki magani da za ki sha, Allah ya sauwake” Daga haka ta fita, Nurse din ta kawo ma Khalil magungunan tana kallon Husnah tace “Allah ya kiyaye gaba, za ku iya tafiya yanxu ga magunguna da prescriptions a jiki” Daga haka ta juya ta bar wajen, Khalil ya daga kai ya kalli Husnah, share hawayenta tayi ta sauko daga kan gadon da take a hankali kamar me gudun kar ta fama wani ciwo a jikinta, duk sun yayyaga mata kayanta wandon ne kawai basu karasa ba, amma daga saman cikinta duk a bude yake, Khalil zai juya ya bar wajen cikin kuka tace “Wallahi baxan iya tafiya ba ko Nihad ce ka turo ta kama min hannu” Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo, da sauri ta karaso kusa da shi ta kama hannunsa, ya dake ya fara tafiya tana dingishi tana bin sa har suka fito reception din, har suka isa mota Husnah ta shiga baya ta zauna Nihad bata fito ba, Khalil na tsaye jikin motar for almost 5 mins ganin bata fito ba still ya koma reception din, hade rai yayi yace “Malama ke muke jira” Ko Kallonsa bata yi ba ta tsura ma Tvn dake aiki a reception din ido, yace “Ohk ga kudin mota duk sanda kika zaman sai ki dawo gida” Ya ciro dari biyar ya mika mata, zuwa lkcn nurses din sun fara kuskus ko kishiya da kishiya ne, can ta mike ta fice daga reception din fuskarta a daure, juyawa yayi ya bi bayanta sai yaga ta bude front seat ta shiga, ya shiga motar shi ma suka bar asibitin, suna hawa saman titi Nihad tace “Hostel za a kai ki ko ina?” Husnah tace “Wallahi kin bani mamaki Nihad har in kone a gidanki amma ki kasa budan baki ki min sannu? Sai yanxu ki wani bude baki kice hostel xa a kai ni ko ina?” Nihad tace “Saboda ai sai da nace ki bari in dafa kika ki, Yanzu idan wani abu da yafi wannan ya sameki su Mumy da Abba suka ji bayan sun hana in kawo kowa gidan fa? What did u want me to tell my parent? Ni yanzu dai hostel za a kai ki ko ina, kin dai ga dare yayi” Khalil yace “Kinsan dare yayi kike kira mata hostel yanzu? Ba kwana ta zo maki ba dama?” Nihad ta wani jefa masa kallo tace “Ni bata ce min zata kwana ba, salon mu koma gida wani abu da yafi wannan ya sameta in shiga uku? Kawai ta koma hostel ko gobe sai in kai mata jakarta can din” Kallon Nihad kawai Khalil ke yi, Husnah tace “To baxan wani je hostel ba jakana na gidanki kuma ID card dina na ciki, kuma ai soyayya ce tasa na zo gidanki ba wani abu ba, me yasa su Naf da Zully basu zo ba, amma ba komai Nagode da walakancin da kika min Nihad” Khalil dai ya nufi hanyar gida, bayan ya shiga ciki yayi parking Nihad ta bude motar ta sauka ta wuce ciki, Husnah ta sauka ita ma ta shiga gidan Khalil ya bi su da kallo, jingina yayi da motar ta ta6e baki. Husnah na shiga dakin Nihad ta fashe da kuka sosai tace “I never expect this from you, in wani yace min zaki min haka wallahi baxan yarda ba, saboda wannan mere Drivern ya taimakeni ya kai ni hospital kike jin haushi Nihad?” Nihad tace “Ya baxan ji haushi ba mutumin da ko magana bana yi masa za ki ja min raini a wajensa ya zata ya mana alfarma, ko kadan i am not happy with what happened da kawai kirawoni kika yi na fita waje na nemo mana taimako akan wannan yaron da kika kula, yaron da ya tsaneni nima na tsanesa shine har zaki yarda ya wani kai ki asibiti?” Husnah tace “Tohh idan mutum na cikin azaba ai baya ma tunanin komai, kawai burinsa a fitar da shi daga axaban da yake ciki, to situation din da na tsinci kaina kenan, amma ni kaina ina ni ina wani driver can” Nihad bata sake cewa komai ba, Husnah tace “Shikenan, tunda har kika koreni bari in yi tafiyata ko hotel ne in kwana don a hostel na riga nace masu baxan dawo yau ba” Nihad tace “Ni fa bance kar ki kwana ba, kawai haushin yaron can ne yasa nace mu kai ki hostel” Tana kai wa nan ta mike ta cire Hijab din jikinta tace “Bari in mana boiling din spaghetti din yanzu, daga can xan gyara kitchen din” Tana fadin haka ta fita parlor ta wuce kitchen tsaye taga Khalil yana kokarin mopping din kitchen din, ta wani hade rai, yana ganinta ya ajiye mop din ya fice daga kitchen din ya shiga dakinsa, bayan few minutes da fitar Nihad Husnah ta leko daga dakin tana lekan parlor amma bata ga Khalil a ciki ba, komawa dakin tayi ta cire yagaggen wandon jikinta da riga ya rage daga ita sai bra da skin tide ta dau after dress dinta ta saka tayi buttoning dinsa sannan ta fito, ta fi second goma tana kallon kofar da take tunanin dakinsa ne sai kuma ta murda, dago kai yayi suna hada ido ta sunkuyar da kai ta shiga dakin ta tura kofar tana tsaye bakin kofar tace “Dama nace bari in maka godiyan dawainiyar da kayi da ni, Allah ya saka da Alkhairi…. kuma don Allah abinda ya faru kwanaki ina sake neman yafiyarka don wancan ranan baka ce min komai ba da na baka hakuri” Kallonta kawai Khalil yake, can ya ajiye lemon kwalin dake hannunsa yace “Ohk, kawarki ki ce ta aikoki ki bani hakuri kenan?” Husnah ta zaro ido tace “Waaa?? Ai inda muka bambanta da ita kenan, da ita ce baxa ta ta6a baka hakuri ba, kasanta da taurin kai da kafiya, yanzun ma bata san na shigo nan ba da baxata bari ba, amma ka sani wllh tunda muka maka wannan rashin kirkin bana samun nutsuwa saboda ba halina bane” Yace “Ohk ai na zata duk ku ke sa ta a hanyar walakanta mu talakawa” Husnah ta dafe kirji ta karasa cikin dakin tace “Waa?? Halin kishiyar mamarta ne ta dauko, kasan duk abinda ta sata tayi shi take yi, amma basu san da talaka da mai kudi duk Allah ne yayi su ba, ka gan ni nan babana yalo yake siyarwa a kawo kaduna, ni ba er kowa bace shi yasa nasan mutuncin ɗan adam” Khalil yace “Ohk, ai ina ce er kano ce” Husnah tayi wani dariya tana jujjuya ido tace “Wallah er kaduna ce ni gaba da baya, Zully da Naf ne yan kano” Yace “Toh naga makarantar taki ta masu kudi ce” Husnah tace “Ehh wallahi wani saurayina ne ya biyamin tun daga level one har karshe, wata kawar mu zully ma saurayinta ke biya mata, Naf ce dai iyayenta ke biya mata don su ma masu kudi ne” Khalil ya gyada kai yace “Allah sarki” Husnah ta zauna gefen gadon tace “Amma ina jiye maka zama gida daya da Nihad, yanda bata kaunarka ta tsaneka kullum a makaranta cikin tsine maka take wai kana matsayin driver kana nuna mata isa, bayan anyi auren nan har ikirari tayi wai zata kasheka, nan kuwa kai jahadi kayi, halan baka hawa social media? Ina nufin baka da babban waya?” Ya girgiza kai yace “Bani da” Husnah ta gyada kai tace “Allah sarki, kawai dai ka saka ido sosai kada kiyayya yaje ya kaita ga aikata abinda ba shi kenan ba, in sha Allah in xan sake dawowa nayi maka alkawarin babban waya” Khalil yace “Toh Nagode, amma kawar taki bata da saurayi ne?” Husnah ta rike ha6a tace “Ita kuwa take da saurayi wanda ita ta makale masa ba shi ba, kana jin janaral jikamshi?” Khalil yace “Eh nasan shi, ko ba wani babban soja ba?” Husnah ta dafa kafarsa cike da kissa tace “Yauwaaa, Toh shi fa…. ɗan sa kwaya daya take so kamar ta kashe kanta, tun yana basar da ita har dai ban san sanda suka dinke ba, mu dai mun fi zargin bashi kanta tayi, don kawai lkci daya muka ga ya fara kiranta ba kakkautawa a maimakon ita da ke yawan kiransa” Khalil ya sauke idonsa kasa daga kallon da yake ma Husnah, Husnah tace “Kuma fa duk wannan abun sau daya ya zo wajenta a nan kano suka hadu a wani waje, kamar dai kar su hadu shkkn ya makale mata, kasan mu mata idan muna son abu babu abinda baxa mu yi kan abun ba, to tun dai daga sannan ya fara kulata sosai, kuma kar kace fa yana zuwa gidansu, aa sam… duk xuwan da yake yi wajenta nan kano sai dai su hadu a wani waje su yini sannan yayi tafiyarsa, toh kwanaki can ban san ya aka yi ba yaje gidansu wai xai tura iyayensa, mu dai ko gaya mana bata yi ba gaskiya sai daga baya, ai ko muna ta murna xa mu hade da ‘ya yan manya mu ma a dama damu tunda abokanansa duk ‘ya yan manyan kasar nan ne kawai wai sai ga videon tsaraicinta ya bazu a duniya, ni takaicina daya da ba a bari sai da muka hadu da abokansa ba, har yau mun rasa ta ina video din nan ya fita, muna dai tunanin garin yawace yawacenta ne aka mata video din nan” Khalil bai kuma cewa komai ba, lkci daya kuma duk mood dinsa ya canza, Husnah ta shafa kafarsa a hankali tana kallon kwayar idonsa tace “Sai kaji babu dadi ace videon tsaraicin warce aka aura maka na ta yawo a duniya ko? A ranka kana tunanin an cuceka ko?” Kallonta Khalil yayi, tana Murmushi ta janye hannunta a hankali tace “Toh Nagode bari in je inyi wanka” Daga haka ta mike tana juya manyan mazaunanta ta nufi kofa, tunda ya kalleta sau daya ya dauke kai har ta fita dakin, karo ta kusa ci da Nihad, Nihad ta tsaya tana kallonta daga sama har kasaasa, Husnah tace “Ke yace min maganin na wajenki kuma ni ban gansa a dakinki ba” can kasa kasa Nihad tace “Ba ya wajena” Daga haka ta shige dakinta, Husnah ta tafi parlor ta dau magungunan nata ta dawo dakin Nihad. Nihad dai na ta zaune gefen gado, Husnah tace “Wai taliyar bata yi bane Nihad?” Sai a sannan Nihad ta kalleta tace “Mu je mu duba” Husnah tace “Ohk” Daga haka ta mike ta fita Nihad ta tashi ta bi bayanta, tana tsaye parlor har Husnah ta shiga kitchen, a hankali ta bude kofar dakinsa ta leka taga baya ciki, ta kalli kofar bandaki sai kuma ta kulle kofar dakin, entrance din fita ta kalla bata ga takalminsa ba, ta karasa jikin window ta tsaya ta bude labulen a hankali tana lekan waje, yana tsaye balcony ya rungume hannunsa, can ta ga ya nufi dakalin da yake son zama ya zauna kana ganinsa kasan he is moody, Husnah ta fito daga kitchen tace “Me kike nema a waje” Nihad tace “Ba komai, kin zubo taliyar?” Husnah tace “Ehh na zuba, ashe har kin sauke” Nihad tace “Toh dauko mu je daki” Husnah ta koma ta dauko suka wuce dakin, bayan sun gama cin abincin Nihad ta fitar da kwanukan ta sake leka waje taga har sannan khalil na zaune inda yake staring into space, kafin Nihad ta dawo Husnah ta jawo jakarta ta fito da kayan mayenta ta sha sannan ta mayar da jakar ta ajiye ta kwanta, Nihad na dawowa dakin ta zauna gefen gado, tana son shiga bandaki tayi wanka amma ta kasa tashi, Wajen karfe sha daya da rabi Husnah ta mike Nihad na kallonta tace “Ina za ki?” Husnah tace “Ruwa zan dauko kitchen” Nihad ta dauko wani bottle water dake daya side din gadon ta mika mata, Husnah ta amsa ta koma ta zauna tana sauke numfashi a hankali, ita fa dama kwana biyu duk samarin nata basa Kano gaba daya a takure take dama, daga karshe dai Husnah ta kwanta ta kulle ido duk da ba bacci tayi ba, Wajen karfe sha biyu da rabi Nihad ta mike daga kwancen da take ta nufi kofa ta sa makulli sannan ta ciro, Da mamaki Husnah ta mike zaune tana kallonta tace “Me yasa zaki kulle mu har da cire makulli Nihad?” Nihad tace “Saboda duk dare haka nake yi dama” Husnah bata kuma cewa komai ba ta kyabe baki ta koma ta kwanta, Nihad ta saka makullin cikin pillow ta kwanta kai. Washegari da sassafe bayan sun yi sallan asuba sun koma bacci kiran Umma ya tashe su, Bayan Husnah ta daga jin muryar Umma tace “Auu Umma ce, ina kwana?” Umma tace “Lafiya lau Husnah baki yi saving number na har yanzu ba ko?” Husnah tace “Yanzu xan yi Umma, ya gida?” Umma tace “Alhamdulillah, ina Nihad din?” Husnah ta mika ma Nihad waya ta koma ta kwanta, Bayan Nihad ta gaidata, Umma tace “Ya, kin gano sunan iyayen nasa kuwa Nihad?” Nihad tace “Aa Umma, dama sai yau” Umma tace “Kin ji irin shiriritar taki ko? Ke da tun jiya nace kisan yanda kika yi ya gaya maki amma sbda shashanci baki yi ba? Ko dai kin fi son kiyi ta zama da dreban nan ne Nihad?” Da sauri Nihad tace “A’a Umma, in sha Allahu yau xan gaya maki” Umma tace “Toh kar ki bari Husnah ta bar gidan nan sai kin gano kin sanar min ta wayarta tukunna” Nihad tace “Toh Umma” Umma tace “A handsfree wayar yake ne naji maganata na dawo min?” Nihad tace “Aa” Umma tayi kasa da murya tace “To dai ki xama me rike sirrinki a ciki, ciki da kike gani ba don tuwo kadai aka yi sa ba, ko da mun gana waya kawarki ta tambayeki me muka ce kice mata ba komai kawai daddawa da kuka nace xan bada a kawo maki, don ba komai ake sanar ma k’awa ba, wa ya sani ko da hadin bakinsu aka saki video dinki a duniya” Nihad tace “Aa Umma ba haka bane gaskiya” Umma tace “Toh shikenan, ina sauraronki zuwa anjima” Nihad tace “Toh” Daga haka ta katse wayar, Husnah na kallonta tace “Wai me ya faru?” Nihad tace “Aa ba komai, abubuwan da zata kawo min ne take tambayata” Husnah tace “Ohk” Komawa tayi ta kwanta, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta ta daura kan kayan baccinta ta nufi kofa Husnah ta bi ta da kallo har ta fita, Nihad na murda kofar dakin Khalil taji an sa makulli, ta fi minti daya tsaye bakin kofar, can ta juya ta tafi parlor ta zauna, tana fitowa da minti biyar sai ga Husnah ma ta fito ta zauna parlon, jan Nihad ta dinga yi da hira, daga karshe wajen karfe tara Khalil ya fito daga dakinsa, babu warce ya kalla a cikinsu ya fita daga gidan, Husnah na ji ya fita da mota ta kalli Nihad tace “Lallai ke me hakuri ce da har kika kai warhaka da mutumin nan a gidan nan, Dubi fa yanda ya wani zo ya wuce mu ko gaisuwa babu, kai kana talaka da kai kayi ta yin abu isa isa?” Nihad ta kyabe baki tace “Ke ma kika lura da mutum ya zo ya wuce ta nan, ai ni ban ga kowa ba” Husnah ta kyalkyale da dariya tace “Ahh lallai kam” Nihad tace “Tashe mu je ko irish ne mu soya da kwai, ni dai na fara jin yunwa” Husnah ta mike suka wuce kitchen din, har kusan la’asar Khalil bai dawo gidan ba, kiran Umma uku duk sai Nihad tace mata ai bai dawo ba, kiran karshe da Umma tayi mata da ta kara sanar mata har sannan bai dawo ba, Umma tace “To kar ki yarda ki bari Husnah ta bar gidan, don tana tafiya babu ta inda xa mu yi communicate” Nihad ta kalli Husnah da ita dama bata ga alamar xata tafi ba tace “Toh Umma” Labari har da na kauyensu Khalil sai da Nihad ta ba Husnah dake ta kyalkyalewa da dariya har da faduwa kasa, tace “Kice ke kika ga asalin dreba ganin idonki?” Nihad tace “Hmm… I wish xaki ga kauyen nan Husnah, wllh with millons baxa ki yarda kiyi minti sha biyar a garin nan ba, it’s hell on earth” Husnah dai sai dariya take, sai ga Naf ta kira Husnah, Nihad da wayar ke kusa da ita tayi saurin dagawa ta kai kunne, Naf na jin muryar Nihad tace “Amma Husnah munafuka ce shine bata gaya mana ba tayi tafiyarta ita kadai” Nihad tace “Wallahi nima ban ji dadin da baku zo gaba daya ba, gashi throughout today I wasn’t lonely, muna ta hira da Husnah” Husnah ta fixge wayar tace “Toh ai naga xaku fita ne shi yasa bance maku mu taho ba Naf, amma meye a ciki next time idan xan zo ai sai mu taho gaba daya, ba wani tashin hankali bane” Naf tace “No but like seriously kinsan indai kince mana wajen Nihad xa ki babu abinda xai hanamu binki, kuma banji dadin abinda kika mana ba, yanzu ma kawai xa mu iya tahowa da zully tunda babu abinda muke” Husnah ta dinga cewa Hello hello, daga haka ta katse wayar tace “Ji shegen network din ya dauke” Hirar da take ma Nihad ta ci gaba da yi mata, Nihad tace “Kinga lokaci na wucewa me xa mu ci da daddare Husnah?” Husnah tace “Ni yanzu xan fita in amso wani sako na, ko indomie ce ma ci da daddaren, Hijabi kawai xan sa in je in dawo” Nihad na kallonta tace “Kar fa ki ki dawowa Husnah” Husnah ta zaro ido tace “Me xai hanani dawowa kuwa, cabb ai kamar na dawo kinsan yanda nayi kewar ki kuwa, to a nan ma xan bar wayata, amma kar ki cire min a flight mode har in dawo” Nihad tace “Toh” daga haka Husnah ta sa hijab ta dau handbag dinta ta bar gidan, ko da ta dawo bayan kusan awa daya Nihad ta dinga kallon hannunta ganin ba leda tace “Ina sakon?” Husnah ta ja tsaki tace “Wai ashe sai gobe, shine suka bari naje nayi asaran kudin motata na dawo” Daga haka ta shiga dakin Nihad. Sai after Magrib Khalil ya dawo gidan, Husnah da fitowarta daga wanka kenan ta dauki mai zata shafa ta rike ha6a tace “Dama haka yake yi ya fita tun safe sai dare kamar me siye da siyarwa a kasuwa” Nihad ta kyabe baki tace “Ohk ya dawo ne” Dariya kawai Husnah tayi bayan ta gama shafa cream dinta tace “Ke baxa ki yi wankan bane” Nihad ta mike tace “Zan yi” Daga haka ta shiga bandaki, mikewa Husnah tayi da sauri ta bude kofar dakin tana leka parlor, ba kowa parlon sai leda da ta gani a ajiye na eatry, ta dawo daki ta dau handbag dinta sannan ta fice tana waige waige kamar munafuka ta shiga kitchen ta bude handbag dinta ta dau allura me cike da wani liquid a ciki ta bude murfin syringe din, ta dawo parlor har tana tuntube ta tafi gun ledan ta bude ta ciro drink din kwali da ta gani ta tsira masa alluran ta sama ta juye duk content din ciki sannan ta mayar da shi ledan hannunta na rawa, sbda rudewa maimakon ta koma daki sai ta shige kitchen, ta fi second talatin a kitchen din kafin ta leko parlon a hankali still taga ba kowa da sauri ta wuce dakin Nihad ta kulle kofa ta zura doguwar rigarta ta dau wayarta ta kwanta saman gado tana danne danne tana ɗan murmushi….

32

Nihad ta fito daga wanka bayan ta gama shafe shafenta ta zauna tana tunanin abinda xata sa yau ta kwanta don dama kayan baccin biyu ne kawai ya rage mata kuma duk ta sa su bata wanke ba, ita tunda take ma ta ta6a wanki a rayuwarta banda pant da bra, Husnah tayi mika tana kallonta tace “Ke kuma tunanin me kike haka?” Nihad ta kalleta a sanyaye tace “Toh kayan baccin nawa duka duka biyu ya rage fa a gidan nan gashi nan kuma duk na sanyesu ba a wanke ba” Husnah ta mike zaune tace “Toh ke garin yaya kika zo da kayan bacci kala biyu kawai?” Nihad tace “Ko ba can kauyensu na rabar ba, da tsummokara fa mutanen kauyen ke yawo wallahi” Dariya Husnah tayi tace “Toh kawai ki saka undies dinki sai ki saka hijabi ki kwanta” Nihad tace “Kin ta6a ganin na kwanta haka?” Husnah tace “Yanzu ma dai ina kayan wanki naki yake?” Nihad ta nuna mata inda ta ajiye su har da hijab kala biyu, Husnah ta mike tace “Nasan ko tsutsa xa su yi a nan ba wanke su xa kiyi ba bari in wanke maki su in samu ladanki” Daga haka ta kwashi kayan ta shige bandaki, Nihad ta mike ta dau Hijab dinta kawai ta saka don dama akwai sanyi sanyi garin alamar hadari, tana ta zaune tana game da wayar Husnah, sai ga Husnah ta fito rike da bucket tace “Can waje zan je in shanyasu ko?” Nihad tace “Ehh ta baya xa ki ga wajen da xakiyi shanyan” Daga sama har kasa Nihad ke kallonta don wani skimpy night wear ne a jikinta, gashi ko bra bata saka ba, Mikewa Nihad tayi tace “Bari kawai in shanya” Husnah tace “Ka ji ki, Aa wllh gwara in cike ladana, da me ya hanaki wankewa balle ki shanya, kawai ni bari in je inyi shanyana” Daga haka ta nufi kofa, Nihad ta kwashe gwangwanin maltina da suka sha da bottle wata ta bi bayanta, Yana zaune parlor hannunsa rike da remote, ga ledan abincin nasa har sannan bai ta6a ba, Husnah sai satan kallon ledan take har sai da ta buge da kujera ta kusa faduwa, da ido ya bi ta, ta nufi kofa da sauri, Nihad dake kallonta har ta fita ita kuma tayi hanyar kitchen taje tayi disposing thrash din hannunta a dustbin sannan ta fito parlo, ta koma kamar xata shiga daki sai kuma ta tsaya bayan 2 seater dake side din tana kallonsa, shi dai idonsa na kan tv, ta yanda xata fara masa tambayar da Umma tace tayi masa kawai take tunani, Ganin bata da alamar barin wajen can dai ya daga kansa ya kalleta yace “Lafiya?” ta jefa masa wani kallo tace “To banda ina son inyi maka tambaya ance maka xan tsaya nan ne” Ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Wa za ki yi ma tambaya?” A takaice tace “Kai” Yace “Ohk, ni za ki yi ma tambaya kenan” Hararansa ta dinga yi wato har wani feeling kanshi yake zata masa tambaya, ya kafeta da ido yace “Yi tambayar ki” Babu yabo babu fallasa tace “Dama baka gaya min sunan gwaggwonka ba a can garin, har da babanka ma duk baka gaya min sunansa ba” Ita kanta tasan she sounds stupid, sai kuma ta fara sosa kai, kallonta kawai yake ba ko kiftawa, can yace “Tun a garin baki tambayeni ba sai yanxu da daddare?” A takaice tace “Ehh saboda sai yanxu na tuna” Yana gyada kai yace “Ohk!! To wa ya aikoki ki tambayeni sunan su?” Ta wara ido kamar munafuka tace “Aa fa, ba wanda ya aikoni yace in tambayeka nice kawai na tambayeka ina son sani” Yana kallon kwayar idonta yace “NIHAD” ta kara buda ido a ɗan rikice tace “Na’am” Yace “Sunanta kenan” Lokaci daya ta hade rai tace “Ban gane Nihad ba, sunanta ne sunana?” Yace “Ehh” Ta dinga masa wani mugun kallo, can tace “Toh don baka da kunya sai ka wani kira sunana gatsau wai Nihad, sunan nawa ka raina haka? waye ma ya gaya maka sunana? Aminu me gadi ko???” Khalil bai kuma ce mata komai ba ya bude ledan dake ajiye gabansa ya ciro drink din, dai dai nan Husnah ta shigo parlon ganin lemon a hannunsa wani farin ciki ya mamayeta tana kallon Nihad tace “Ke an fara yayyafi fa, kije ki rufe windows ko” Khalil ya ajiye kwalin lemun hannunsa ya mike ya shiga kitchen xai dauko glass cup, wajen lemon Nihad ta nufa da gudu, Husnah da ke kokarin shiga daki tana ta murmushi ita kadai kamar ance ta juya taga Nihad ta kinkimo lemun ta taho da gudu xata shige daki, cike da zafin nama Husnah ta fixge lemon daga hannunta tace “Meye haka sai kace mayunwaciya Nihad, bai siyo ya baki ba sbda rashin hankali kin wani dauko masa abinda kika fi karfi, me xa ki yi da abin hannunsa, bayan kudin ma kinsan na wanene ya ke ci, a’a wllh kin bani mamaki” Bata jira cewar Nihad ba ta koma da sauri sauri ta ajiye masa lemon ta bar wajen sai gashi ya fito kitchen, tuni Husnah ta figi hannun Nihad ta shige daki da ita ta kulle kofar tace “Wallahi kin bani kunya, me xa kiyi da lemonsa ke da ko ni kika ce in kawo maki carton din lemon can tsaf xan siyo in kawo maki, balle Umma ma kina gaya mata xata bayar a kawo maki har gida? Me ya kai ki? Ke fa har yanxu yarinta na damunki wllh, banda yarinta meye kike abu haka babu class, yanzu na gano dalilin da yasa yayi mugun raina ki” Nihad dai bata ce komai ba, Husnah ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, dai dai nan aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, Husnah ta zaro ido tace “Lahh ga ruwan ya sauko, ki kulle windows din dakunan ni kuma bari inje in kulle na parlor” Daga haka ta fice da sauri zuwa parlor, Nihad ta bi ta da kallo sai kuma ta bi bayanta, farin ciki bai kara lullube Husnah ba sai da tagansa rike da lemon a glass yana sha, ta kasa daina murmushi ta tafi ta kulle windown parlon ta shiga ma kitchen ma ta kulle sannan ta fito tana kallonsa tace “Sai da safe” Bata damu da ta ji ya amsa ba ta nufi daki tana jijjige inda ya kamata a jikinta, Tana kallon Nihad dake bakin kofa tace “Wai duk kika ga na fito sai ki biyoni” Nihad tace “Aa ni kitchen xan tafi ne” Husnah bata ce mata komai ba ta shige daki, Nihad ta shiga kitchen ita kanta tasan babu abinda xata yi a kitchen din bayan ta gama zagaye zagayenta ta fito ta nufi dakinta, da ido khalil ya bi ta har ta shiga dakin, makulli ta saka ta zare makullin, Husnah dake kwance tana danna waya tace “Kamar da wasa fa sai ga ruwa ko ba komai garin yayi sanyi naturally ayi bacci me dadi” Nihad dai bata ce komai n a ta hau saman gado daga daya side din ta jawo pillon ta jefa makulli a ciki Husnah dai na ta kallonta da gefen ido, Husnah ta mike zaune tana kallonta tace “I want to take malt but gaskiya baxan iya shanye daya ba, idan na rage maki xa ki sha ai ko?” Nihad ta girgiza kai tace “Aa na koshi” a hankali Husnah tace “Toh shikenan, bari in bari kawai kar ayi asaran sa” Nihad tace “Ki sha ki rage ki ajiye mana” Husnah tace “Aa ni kinsan bana son almubazzaranci ke kuma dama kin iya walakanta abinci, da dai kuna da fridge ne sai in je in ajiye sauran amma idan aka bar shi haka ai lalacewa xai yi, ba fa wai da yawa xan rage ba ni nasan gejin cika na, kadan zan rage wllh” Nihad tace “Wa yace maki malt na lalacewa??” Husnah tace “Ke dai tunda baxa ki sha sauran ba shikenan sai in hakura in kwanta da craving dina” Nihad tace “Ni wallahi ban ta6a jin inda malt ya lalace ba sai a bakin ki, ki sha kawai ki rage yayi ta lalacewan mana” Husnah bata kuma cewa komai ba ta kwanta, bayan kusan 10 mins ta mike zaune tana kallon agogo dake nuna karfe goma da rabi ta jawo malt daya kawai ta bude ta fara sha, kallon Nihad tayi ganin kamar ta fara bacci ta tasheta, Nihad ta bude ido a hankali Husnah tace “Wai kin daina alwala ne idan xaki kwanta?” Nihad na lullumshe ido tace “Zan yi” Husnah tace “Aa tashi kije kiyi gaskiya kafin bacci me nauyi ya dauke ki” Sai da ta tashi Nihad kusan sau uku sannan Nihad ta tashi da kyar duk da tunda ta xo gidan nan bata ta6a alwala idan xata kwanta ba amma dabi’arta ce yin hakan tun bayan da taje tayi wani hutu wajen Aunty Jamila na sati uku, Aunty Jamila bata ta6a barin ta kwanta bata yi alwala ba, kuma bayan ta dawo gida kawai training din ya zama jikinta, in dai xata kwanta sai tayi alwala wani lkcn Umma tayi ta mata fada idan taga tayi tace so take sanyi ya shiga jikinta, Nihad na shiga bandakin Husnah ta jawo jakarta da sauri ta bude wani abun maye ta zuba kusan quarter a cikin ɗan malt din ta rage sannan tayi saurin mayar da shi cikin jaka ta ajiye jakar, har ta dauko pillown Nihad xata cire makulli sai kuma ta fasa ta mayar da sauri, Nihad ta fito daga bandakin bayan tayi alwalan ta nufi inda xata kwanta Husnah tace “Don girman Allah ki shanye guntun malt din nan saura kadan, ta6a ki ji” Nihad ta girgiza kai tace “Aa baxan sha ba kawai ki ajiye” Husnah ta dinga kallonta sai kuma tace “Ohhh sai yanxu ma na gane, wai kyankyami yasa baki son ki sha kamar warce ta zuba na bakinta a ciki?” Nihad ta kalleta tace “Ni nace maki haka?” Husnah tace “Aa haka ne mana, banda haka meye don na sha malt na rage maki ki ki shi Nihad?” Nihad tace “Ke dai kin san yanda xa ki bi ki juya magana, ni na gaya maki haka? Ko daxu da kika dau ruwana kika sha gani kika yi na zubar?” Husnah ta mika mata gwangwanin tace “Ni dai gashi babu yawa ki sha don bana son Allah ya kamani da walakanci da abinci” Nihad tace “Wai ba daxu kika ga na dau malt na sha ba salon inyi ta tashi cikin dare fitsari” Tsaki Nihad ta ja ta amshi gwangwanin hannun Husnah ta kwankwade lokaci daya ta ajiye gwangwanin, Husnah sai kallonta take tayi wani Murmushi, Nihad ta kalleta, da sauri Husnah ta dauke kai ta lulluba da duvet tana cewa “Ki kashe mana wutan sai da safe” Nihad na yamutse fuska tace “It has a different taste” Husnah tace “Aa hajiya sai dai bakinki ne” Nihad na kallonta tace “Amma tsakaninki da Allah babu abinda kika zuba a malt din nan Husnah, ni na sha gaya maki bana son irin abubuwan nan kuna forcing dina sai na sha, dama shi yasa kika dage sai na sha?” Dariya kawai Husnah tayi tace “Oho dai, ko ba komai yau xaki yi bacci me dadi brain dinki yayi relax, habaa” Daga haka Husnah ta shige duvet, Nihad ta dinga mata wani irin kallo, can ta ja tsaki ta yi kwanciyarta, she wish ta gano abinda Husnah xata mata kenan da baxata sha malt din ba ko me xai faru, ko minti goma ba ayi ba Nihad ta bingire da wani nannauyan bacci, Husnah ta juya tana kallonta tana Murmushi, har sannan kuma ruwa ake kamar da bakin kwarya. Sha daya dai dai Husnah ta cire duvet din jikinta, ta sauka daga kan gadon, ta zaga ta inda Nihad take bacci kamar warce tayi tseren awa biyu, janye pillon kanta tayi ta ciro makullin ciki sannan ta ajiye pillown nan gefenta ta bude jakarta tayi shafe shafen da xata yi sannan ta nufi kofa, bude kofar tayi a hankali ta fita, taga duk an kashe wutan gidan, tana lalubawa ta nufi dakinsa, murda kofar dakin tayi slowly ta bude, she saw him kneeling a kusa da gadonsa ya daura kansa saman gadon wearing just his trousers, ta shigo dakin da sauri ta kulle kofar da makulli tace “Subhanallahi, me ya faru? Lafiyarka kuwa?” Lkci daya ya dago da fierce eyes yana kallonta, tayi kasa da murya ta karasa kusa da shi ta durkusa gabansa tana kallon broad chest dinsa tace “Ko dai baka da lafiya ne?” Bata jira me zai ce ba don she was more than Randy a moment din, ta kai hannu chest dinsa, lkci daya cikin dubara tayi loosening din igiyar  rigarta, rungumesa tayi gam murya can kasa tace “Ka gaya min me ya sameka….” rufe idonsa yayi sai kuma ya bude da sauri, da duk karfinsa yayi karfin halin hankadata gefe har sai da ta fadi, sai kuma ya mike cikin husky voice dinsa yace “Me ya kawo ki dakin nan?” Daga sama har kasa take kallonsa, dariya ma ya bata, a wannan yanayin da take kallonsa daga sama har kasa har yake da karfin halin tambayarta me ya kawota dakinsa, wani er dariyar bariki tayi, tasan yau TBD straight up, cike da kissa ta cire rigar jikinta ta jefar nan gefensa tana masa wani shu’umin kallo da lumsassun idanuwa, kauda kai yayi cikin zafin nama ya nufi belt dinsa dake saman jaka bata ankaraba sai jin saukan belt tayi a jikinta, gigicewa tayi saboda azaba, ya dinga zabga mata belt din iya karfinsa, ihu take tana jin kamar ranta ake zarewa sbda azaban belt, ta dinga neman yanda xata kubuta daga hannunsa ta ihu a gigice, duk inda ta yi haka ya dinga bin ta yana sauke mata belt din duk inda ya samu a jikinta, a wannan daren Husnah ta ga jalala, kawai ta sa ma ranta karshen rayuwarta ne ya zo, tun tana rokonsa da muryarta har muryar nata ya daina fitowa, dukanta yake iya karfinsa da belt kamar an aikosa, ga shi ta garkame kofar dakin balle ta fita, har bandaki ta shiga ya bi ta yana duka daga karshe ta fito da rarrafe, dukan da yake mata ya sa shi jin saukin axaban da yake ji a lkcn, sai da ya gaji don kansa bayan yaga yayi mata lilis sannan ya jefar da belt din after 30mins kenan, nan ya bude kofar dakin yana sauke numfashi, tsabar yanda ta jibgu ga kofa a bude amma ta kasa motsawa daga inda take balle ta fita, ya nufota ya kalla mata wani wawan mari har sau biyu a fuska ya dau shegiyar rigar baccinta ya hada da ita yana janta ya fito da ita parlor yayi wani hajijiya da ita sannan ya cillar da ita da rigar ya koma dakinsa, gudun kar ya sake dawowa ya sa ta karfin halim rarrafawa da kyar ta nufi kitchen, gaba daya jikinta shatin belt ne rudu rudu ga bakinta sai zuban jini yake, idonta daya kuwa ya kulle, tana shiga kitchen din hannunta na rawa da strength dinta na karshe ta saka makulli kafin ta fada kasa rigijib. Tun Khalil na daurewa yana cijewa, daga nan ya koma can, daga can ya mirgina ya koma nan kamar me labor har dai yaji he is going to harm himself, he couldn’t bear it anymore, Mikewa yayi kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin, tsaye yayi corridor ya hade kansa da bango corridon,  yana ta tsaye a haka for almost 5 mins sai kuma ya kalli kofar dakin Nihad, murda kofar yayi amma bai bude ba, can ya runtse ido ya sa kafa ya tura kofar staggering inside the room, ya manna hannunsa jikin switch din dakin yana sauke numfashi, standing there for another 2 mins kafin ya kunna wutan dakin a hankali, tana saman gado ta dukunkune can saman jikinta da hijab daga kasan waist dinta har ƙafafuwanta kuma babu wani obstacle sai na lingerie dinta and she is sleeping heavily, hade kai yayi da bango ya rufe ido yana sauke breathing dinsa a hankali, can ya bude idanuwansa da suka yi jajir, ya kashe wutan dakin ya nufi kan gadon, gefenta ya fada yayi rub da ciki, perceiving her scent all over, da yayi attempting kai hannunsa jikinta sai wasu abubuwa suka dinga fado masa a xuciya, and all of a sudden ya janye hannunsa ya zamo kasa a hankalii ya daura kansa gefen gadon, yana ta durkushe a hakan har kusan karfe biyun dare, zuwa sannan yayyafi kawai ake ruwan ya tsagaita… Da kyar Nihad ta bude idonta ta dalilin fitsari da take ji, ana ta kiraye kirayen sallahn asuba ta sauko daga saman gadon tana layi xata bandaki, gaba daya jikinta is so weak, tutunbe ta ji ta ci da mutum a kasa lkci daya kuma ta fada kansa, wani ihu ta fasa a mugun tsorace tana tattabasa amma lkci daya hankalinta ya ɗan kwanta jin kamshin turarensa, zamewa tayi ta sauka daga jikinsa ta zauna gefe tana kallonsa cikin duhun don jikinsa taji xafi kamar me, nan da nan mugun baccin da ke idonta ya washe gaba daya, da sauri ta mike ta tafi ta kunna switch din dakin, kwance ta gansa nan kasan tiles ko riga babu a jikinsa, ya bude jajayen idonsa, ta dawo ta duka gabansa tana kallonsa, bata san sanda tace “Baka da lafiya ne?” Bai ce mata komai ba yayi karfin halin mikewa zaune, ta koma baya bata kara ce masa komai ba, Mikewa tsaye yayi taga yana layi kamar wanda ya sha ya bugu, ta tashi tsaye da sauri kafin tace komai yayi baya zai fadi, xaro ido tayi ta jawosa ita a dole xata tarosa, amma ya rinjayeta sai ga su a kasa, ta zaro ido cike da azaba tace “Wayyo bayana” Cike da karfin hali ya dagata ya fada gefenta can underneath his breathe ba tare da yasan ya fada ba yace “Sorry” daga haka ya kulle idonsa, ta mike zaune tana kallonsa sosai jikinsa yayi zafi, bubbuga gado ta shiga yi da sauri tana cewa “Husnah, Husnah ki tashi” Amma jin shiru ta daga kai taga wayam babu Husnah a dakin, mikewa tayi da sauri ta fita parlor nan ma ta dudduba bata ga Husnah ba, kamar xata yi kuka tace “Toh ina ta tafi?” Sai kuma ta marairaice tace “Toh ni ya zan yi yanzu?” Juyowa tayi da sauri ta dawo dakin ta durkusa gabansa tana kallonsa, sai kuma tace “Toh Abba xan kira da wayarka?” Ya bude jajayen idonsa da sauri yace “Aa” Tashi tayi ta kara fita parlor dai dai nan taji kamar ana bude kofar kitchen, tsorata tayi tayi hanyar daki da sauri tana lekan kofar kitchen din, sai ga Husnah baki ya kumbura suntummm lebbenta ya koma kamar na rakumi, ga fuskarta yayi jajir kamar nama, jini kuma ya kwanta a idonta daya, dayan idon kuwa ya manne, kayan baccinta ne a jikinta, Nihad ta dafe kirji a tsorace tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Husnah what happened” Husnah na dingishi da kyar tace “Aljanun dare” Nihad ta jingina da bango a mugun tsorace tana zaro ido tace “Aljanun dare kuma?” Husnah ta gyada kai da kyar tace “Akwaisu a gidan nan wllh, Dauko min jakata da hijabi na” Nihad da hankalinta yayi mugun tashi tace “Ganinsu kika yi?” Husnah na sauke numfashi tace “Nace ki dauko min jakata da hijabi” Nihad taki motsawa daga inda take saboda tsoro, Husnah tayi zaman dirshan a kasa ta rasa inda xata sa ranta ta ji dadi, gaba daya shatin belt din jikinta yayi jajir gasu rudu rudu, Nihad dake ta kallonta a mugun tsorace tace “Husnah kalli jikinki fa” A fusace Husnah tace “Ki dauko min jakata da hijabi nace” Nihad ta juya ta koma daki da sauri bata ga Khalil kwance inda ta bar sa ba, cikin second biyar ta fixgo hijabi, jaka da wayar Husnah ta fito da gudu daga dakin, Husnah na ganinta ta mike ko ina na jikinta na rawa ta amshe jakarta da hijab da waya, bayan ta saka hijab din ta nufi kofa da sauri, Nihad ta fashe da kuka tace “Tafiya za kiyi ki barni Husnah?” Ko tsayawa Husnah bata yi ba balle ta juyo ta saurari Nihad tuni ta bude kofar parlon ta fice da sauri ta saka takalminta luckily taga lock kawai aka sa ma gate din babu key ta bude ta fice daga gidan. Nihad ta koma dakin Khalil da gudu ta kulle kofar, kan darduma ta gansa sallan ma ya kasa tashi tsaye, ta durkusa nan kusa da gado tana kallonsa kana ganin idonta kasan ta tsorata sosai, har ya idar taga ya fada kan darduman ya kwanta ya kulle ido, ita dai tana ta zaune maganar Husnah na mata yawo a kai, can ta mike a hankali ta nufi bandakinsa, a bude ta bar kofar, bayan ta kama ruwa ta dauro alwala ta fito da sauri… Tana idar da sallah ta juya tana kallonsa, tashi tayi ta koma inda yake ta duka hucin zafi take ji a jikinsa, ta dinga kallonsa, a hankali ya bude idanuwansa jin ta a gefensa, ta 6ata fuska tace “Toh kuma kace kar in kira Abba” Wayarsa da ta hango gefen gado ta kai hannu ta dauka, yayi karfin halin kwace wayar a hannunta ya lumshe ido, tagumi tayi tana kallonsa, a hankali tace “Toh ni ya zan yi?” Tana ta zaune gefensa har gari ya waye gaba daya, tun da ya amshe wayarsa a hannunta bai sake bude idonsa ba, duk da baccin da take ji amma bata yi ba tana gefensa a zaune, lkci daya taga ya yunkura ya mike zaune, ta zaro ido ta koma baya tace “Amai zaka yi” Ya sunkuyar da kansa bayan few minutes ya koma ya kwanta ya kulle ido, a hankali ta kai hannu forehead dinsa taji har sannan da xafi, ya bude ido yana kallonta, tace “Toh safiya yayi yanzu ka bani wayar in kira Abbana” murya can kasa taji yace “Dauko takarda da biro” Tace “Takarda da biro kuma??” Jin bai ce komai ba ta mike har ta nufi kofa sai ga ta ta dawo da gudu ta tsugunna kusa da shi kamar xata yi kuka tace “Wallahi Husnah tace min akwai Aljanun dare a gidan nan, duk sun mata duka bakinta ya canxa yayi wani iri”

33

Nihad tayi shiru tana kallonsa jin bai ce komai ba, bayan few seconds cike da karfin hali yace “Baxa ki dauko min ba?” Ta marairaice tace “To wai ba nace maka tsoro nake ji ba, ni baxan iya fita ni kadai ba wallahi, bayan Husnah tace min aljanun dare na gidan nan” Da kyar ya mike zaune ya nuna mata jakarsa murya can kasa yace “Bani shi” Mikewa tayi ta tafi ta dauko jakar ta ajiye masa tana kallonsa, ya jingina da gado, kana ganinsa kasan ba shi da strength, bayan few seconds a hankali ya bude side din jakar ya ciro jotter da biro ya ciri jotter daya ya daura kan main jotter din ya fara rubutu da biron, iya layi hudu yayi rubutun sai kuma ya rubuta digit hudu sannan ya ajiye biron ya kwanta breathing slowly, ta dau takardan tana ta kallon rubutun sai kuma ta kallesa tace “Wa ya koya ma rubutu haka?” Ya nuna mata makullin mota yace “Ki je pharmacy ki basu, akwai Atm card dina a nan, ga pin na rubuta, current account” Sake baki tayi ta kallesa ta sake kallon takardan hannunta, can tace “lallai, kai ne xaka wani rubuta ma kanka magani, a ina ka san magani da har zaka rubuta ma kanka? Ko mutuwa kake so kayi?” fizge takardan hannunta yayi a fusace yace “Bar shi ma” Ta wani hararesa ta kwace takardan tace “Toh a ina aka ce ka siya maganin nan ka sha tunda kai dai ba likita bane” Kamar baxai bata amsa ba don shi kadai yasan me yake ji a jikinsa, sai kuma yayi karfin halin cewa “Likita ya turo min jiya da daddare” Tace “Wannan da ya zo ya dubani ranan?” Mika mata hannu yayi yace “Idan baxa ki je ba bani takardan” Tabe baki tayi ta mike ta tafi inda makullin motar yake ta dauka tare da makullin gida da Atm card dinsa, sai kuma ta kallesa tace “Savings account?” Ba tare da ya buda idonsa da ya kulle ba yace “Current” Tsayawa tayi tana kallonsa, sai kuma tace “Kasan meye current account kuwa?” ya bude ido a hankali yace “Bani, ba sai kinje ba kuma” Ta turo baki tace “To ai ni dai ba ruwana idan naje aka sa current aka rufe maka account dinka” Daga haka ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta dawo ta marairaice tace “Ni fa tsoro nake ji” Lumshe ido kawai yayi, tayi shiru tana kallonsa, can ta bude kofar a hankali ta fita kafin kiftawar ido sai ga ta a compound tana maida numfashi, gun motar ta nufa ta bude ta shiga ta kunna tana warming, sauka tayi ta tafi gate amma ta kasa turawa har xata koma ta gaya masa sai kuma a hankali tace “Toh ai shi ma ba iyawa xai yi ba tunda ba shi da lafiya” bude gate din tayi ta fita kofar gida, ganin wani mutumi tace “Don Allah ka tayani bude gate din nan xan fita da mota” yana shigowa zai bude mata ta tafi ta shiga motar, bayan ya bude ta fita da motar waje, tana ganin ya kulle gate din ya fito tayi masa godiya sannan ta sauka ta kulle gidan da makulli ta hau motar xuwa pharmacy, bayan magunguna har da allurai taga an hada mata, ta basu Atm card dinsa da har xata ce masu Savings don bata yarda da current da yace mata ba, sai dai kuma tace “Current” Suka cire kudinsu suka mayar mata da atm card din ta amsa ta dinga jujjuyawa tana kallonsa, daga karshe ta amshi ledan maganin ta fito ta tafi zuwa inda tayi parking. Nihad na isa gida sai da ta kara neman wanda ya bude mata gate ta shiga da mota sannan ya kulle, godiya tayi masa ta nufi kofar shiga ciki ta bude ta tsaya tana bin ko ina na parlon da kallo, to ta ina Aljanun dare xa su shigo gidan bayan ko ina a kulle? sai kuma tayi karfin halin shiga tana tafiya a hankali ta karasa dakinsa ta bude ta shiga, kwance ta samesa yanda ta barsa ta ajiye ledan maganin hannunta ta durkusa tana kallonsa tace “Ga maganin na siyo” Ya bude ido a hankali yana kallonta, ajiye makulli da Atm card din hannunta tayi ta fita daga dakin zuwa kitchen, ba a dau lkci ba ta dawo dakin rike da cup din shayi ta ajiye masa tace “Gashi” Tashi yayi ya zauna ya bude ledan maganin da ta kawo ya fiddo su gaba daya, ta dau cup din shayin ta mika masa tace “Gashi” Ya kalli cup din ya kalleta sai kuma ya amsa, komawa gefe tayi ta zauna, lkci lkci take satan kallonsa kamar yanda shima yake satan kallonta, da sun hada ido kuma sai kowa ya dauke kai, har ya kusa shanye shayin sannan ya ajiye cup din taga ya fara hada allura, tana ta kallon ikon Allah, taga ya sauke trousers dinsa, zaro ido tayi ta kauda kai da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannunta, bayan few seconds ta juyo a hankali, empy syringe ta gani, ta mike da sauri tace “Me yasa zaka ma kanka allura?” Bai ko kalleta ba ya bude maganin ya sha da sauran shayin da ya rage sannan ya koma ya kwanta ya lumshe ido ta dinga kallonsa da mamaki, har bayan kusan minti goma bata ga ya bude idon ba sai ma taga kamar bacci yake, juyawa tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta zauna, ko minti sha biyar bata yi a parlon ba taji ana kwankwasa gate, ta tashi da sauri ta koma daki, bacci taga yana yi heavily, ta dau makullin gidan ta fita zuwa gate ta bude, Amina ta gani a tsaye sanye da uniform din islamiyya don ranan lahadi ce, Amina na mika mata waya tace “Ina kwana, wai gashi Umma xata maki magana” Nihad ta amshi wayar sai ga kiran Umma dagawa tayi ta kai kunne daga daya bangaren Umma tace “Kin isa gidan Amina?” A hankali Nihad tace “Umma ina kwana?” Umma tace “Ya haka Nihad, tun jiya ina ta jiranki shiru, Nayi ta kiran Husnah kuma bata daga wayar, ko ta bar gidan ne?” Nihad tace “Ehh ta tafi Umma” Umma tace “Amma ba sai da nace maki kar ki bari ta bar gidan ba sai mun gama magana da ke?” Nihad tace “Nima tashi nayi naga bata gidan” Umma tace “Toh Allah ya kyauta, kin tambayesan kuwa?” Nihad tace “Ehh Umma, yace min sunan Mamarsa Nihad” Umma tace “Amma dai ke shashasha ce wawuya, sai kika yi shiru kika kyalesa da yace maki haka?” Nihad tace “Wallahi haka yace min” Tsaki Umma tayi tace “Baki da wayo ko kadan wallahi, kuma banga alamar za kiyi wayon nan ba, ai shkkn sai kiyi ta zama da dreban, ni sai anjima, haba sai kace ba mace ba ki rasa yanda xa ki bi da shi har ya gaya maki sunan iyayensa, ni gata nake maki, gatan da uwarki ko mutuwa xaki yi baxata ta6a maki ba” Cikin sanyin murya Nihad tace “Toh xan kara tambayarsa Umma kiyi hakuri” Umma tace “Ni sai anjima da Allah” daga haka ta katse wayar cike da bacin rai, Amina ta karba tace “Kin gama?” Nihad bata ce mata komai ba, Amina tace “Sai anjima” Daga haka ta shiga adaidaita da xai kai ta islamiyya don kudin drop Umma ta bata, a hankali Nihad ta juya ta koma cikin gidan. Umma ce zaune gaban wani Rantamemen mutumi ita da Hajiya Turai, Umma na girgiza kai tace “Wallahi Malam ba a samo sunan iyayen nasa ba, kasan yarinyar shashasha ce ga ta kuma er fari, ba wayo” Mutumin dake kallonsu da jajayen tulla tullan idonsa yace “To ai tun farko nace maki xa a iya aiki da sunan nasa kadai kuma aiki zai ci kamar yankan wuka, kawai ku dai in ji dumuss” Umma ta gyara zama tace “Toh madallah malam, kuma ai kai ma kasan kudi ba matsala bace” Yana muxurai yace “Ya kika ce sunan nasa?” Umma tace “Ibrahim” Girgiza kafa ya dinga yi, bayan kusan minti daya ya kalleta da gefen ido yana murmushi yace “Yana nan wani me kyau, dogo sangameme sannan shi ba baki ba, yana kuma da faffadan kirji” Umma tace “Haka yake wallahi malam, duk yanda ka fada wllh haka ne” ya kyalkyale da wani dariya Yace “Toh ai jefaffe ne tun asali, Jifa kuwa ba na wasa ba aka yi masa, ga shi nan naga jifa iri iri a kansa, a jefe yake…” Su Umma dai suka yi shiru suna kallonsa, ya langwabar da kai kamar me nazari sae kuma ya gyada kai yace “Gashi nan an nuna min, ashe ma ruwa biyu ne, ko ta ɓangaren uwa ko na uba” Umma tace “Ba shakka, hakan take malam, ai buzu ne, uwarsa wai er Nijar ce” Yayi wani dariya yana jijjiga kai, Umma tace “Toh amma daga ina aka masa asirin Malam?” Mutumin yayi wani shu’umin murmushi yace “Ɗan wani kauye ne kika ce?” Umma ta girgiza kai tace “Aa, shi dai maigidana ne yasan sunan kauyen nasu tunda har can yaje aka daura auren amma ni ban sani ba gaskiya” Yace “Toh daga kauyen nasu aka jefesa, wato ana masa bakin ciki da ɗan abun da yake samu” Yana gyada kai yace “Shi din me kwazon nema ne tun da ya taso, yana kuma da farin jini, dalilin da yasa ake jifansa kenan…. Sihiri me karfi aka yi masa gashi nan na gani” Umma tace “Ikon Allah, kuma gashi an ga ya fito birni nema dole kuma ya dinga samu sosai” Mutumin yace “Kwarai kuwa, sannan kamar yanda nace maki Allah yayi sa da farin jini da cikar kamala, duk wanda ya ra6a sai ya so shi so na gaske, zai kuma iya damka masa amanar dukiyarsa sbda yarda” Umma ta wani hade rai tace “Toh ni sai6 yanzu so nake ayi masa yanda sisin me gidana baxai sake shiga hannunsa ba don Ubansa, kasa masa mugun tsanarsa wanda xai ji baya son ganinsa baya son mu’amala da shi har abada” Hajiya Turai dake kallonta tace “Idan aka yi haka ke kuma ai sai ya iya cewa sai ya sakar masa er sa” Shiru Umma tayi tana nazari, can wayar Umma ya fara ring ta bude jaka da sauri ta fiddo ganin me kiranta tace “Minti biyu Malam” Daga haka ta mike ta fita can tsakar gida ta daga wayar ta kai kunne tace “Malam barkanmu da safiya” Ta kara da cewa “Eh ba a dai samo sunan ba amma nan da awa daya za mu karaso in sha Allah, don Allah ka jira mu Malam kaga dai daga waje me nisa za mu zo” Hajiya Turai na kallon Mutumin dake gabanta tace “Kana ji malam? so muke shi Alhajin ya fita tsabgar daga shi dreban har yar tasa, sannan maganan gini da yace zai ma yar a Zaria a rushe zancen kwata kwata, malam gaba daya a sa yaji bai son su gaba daya, bai kuma son ganinsu, ita yar dama kawai ya sallama ma duniya ita, sannan abu na karshe ka saka ma shi dreban jin son zai koma inda ya fito wato kauyensu, ka sa zaman birnin ya gagaresa, idan ya so su koma can inda ya fito su ci gaba da zama shi da ita yarinyar” Umma ta shigo ta zauna, Hajiya Turai ta kalleta tace “Duk na gama gaya masa abinda zai yi” Umma ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh shikenan” Dariya mutumin yayi sosai yace “Kudi… Aikinku aiki ne babba, kuma aiki dole sai da kudi, kinga kafin mu daura aiki a kansa dole za mu warware kadan daga abubuwan da aka masa sannan aikin mu xai samu shiga, ba a hada aiki da aiki ai, sai wancan aikin nasu ya lalata min nawa, wato ya ki barin nawa yayi wani tasiri, ko kuma nawa ya rage tasirin nasu, haka abun yake, yanzu dai nine xan rage tasirin na kansa sannan in dora nawa” Umma tace “Tohh mu dai koma yaya za ayi kawai mu ga mun ci nasara malam, sannan ya dai ci ace an saba yanzu Malam, abu dai shekara da shekaru ana tare ana harka, wannan karan a dubemu karba tsula mana kudi” Hajiya Turai tace “Ai kuwa dai malam, ayi mana sassauci gaskiya” Yana ta6e baki na wasu yan sakwanni sai kuma yace “Kawai ki dire dubu dari da hamsin idan aikinki ya ci ki cika dubu hamsin” Umma ta bude jakarta ta ciro zoben gwal ta ajiye masa tace “Gashi nan wannan dubu dari da tamanin ce, ka rike ka fara min aiki” Ya amsa yace “An gama” tace “Toh malam zuwa nan da yaushe za a fara aikin sannan za a fara ganin tasirin aikin?” Yace “Yanzu zan afka jeji in fara aikinku babu bata lokaci, gaba daya a yau xan yi duk abinda xan yi, zuwa gobe kuma aiki zai fara ci kamar yankan wuka” Umma na Murmushi tace “Toh mun gode Malam, Allah ya saka maka da alkhairi, aikin ka ai mun san ba wasa, mu yanzu za mu tafi sai na kira ka” Daga haka suka masa sallama suka kama hanyar wani kauyen daban. Nihad na ta zaune parlor har kusan sha biyu, can ta mike ta nufi dakin da yake kwance, a hankali ta murda kofar dakin tana kallonsa saman gado ta gansa yana bacci, ta rufo dakin sannan ta shiga dayan dakin tayi wanka ta dauro alwala ta shirya ta fito, sai da ta fara zagayawa ta kwaso kayan da Husnah ta wanke mata ta kai su daki ta linke daga nan ta dawo parlor ta shiga kitchen, kallon kitchen din kawai take, akwai kayan miya da komai a gidan kawai nama ne babu tunda babu fridge, ta fito ta tafi dakinsa, ta bude kofar trying to make no sound, gun Atm card dinsa ta tafi ta dauka da makullin mota da na gida sannan ta fito, cikin mintin da bai wuce talatin ba ta fita taje ta siyo frozen chicken guda biyu da few spices sannan ta dawo gida, ta sake daura alwala tayi sallah bayan ta idar ta koma kitchen din, sai kusan karfe biyu ta fito daga kitchen bayan ta gama duk abinda take, gaba daya ta gaji likis uwa wace tayi girkin mutane goma, ta fada kan kujera, har ta mance rabon da tayi girki don ko da wasa Umma bata sa ta wai saboda hayaki da warin gas, duk sanda taje gidan Aunty Jamila ne take girki don dama Aunty Jamila chef ce, tana gwada mata abubuwa da yawa na girke girke, saving grace din Nihad kenan da har Allah ya taimaketa ta iya girkin, tana ta zaune parlon sai kuma ta mike ta tafi dakinsa ta bude tana kallonsa, bata ga alamar yayi sallah ba, ta karasa ciki ta tsaya side din gadon ta bubbuga pillown da yake a kai tace “Baka yi sallah ba” Ya bude ido da kyar ya kalleta yace “Ina ruwanki?” Kyabe baki tayi tace “Toh don ma ka samu ina tashin ka?” Ta wani juya ido ta juya xata fita ya bi ta da kallo, sai kuma yace “Ina son ruwan zafi” Ta jefa masa wani kallo tace “Toh meye zaka gaya min? Ko house help dinka ce ni?” Daga haka ta fice daga dakin, lumshe ido yayi yana son tashi amma ba shi da enough strength din yin hakan, bayan kusan minti ashirin har wani baccin ya kara daukesa ta shigo dakin rike da kettle din ruwan zafi, ya bude ido da sauri jin sound din bude kofar, bandaki ta shiga ta dauraye bucket ta juye masa ruwan zafin a ciki tana fitowa kuma ta fita daga dakin ba tare da ta kallesa ba, ya yunkura ya mike zaune sannan ya sauka daga saman gadon ya shiga bandakin. Ko da ya fito yaga abinci ajiye a dakin, ya gama shiryawa yayi sallahn zuhur, yana ta zaune saman darduma yana kallon warmers din abincin, can ya jawo karamin warmer din ya bude aroma din miyan ya doki hancinsa, ya bude dayan ya ga shinkafa ce, kawai zuciyarsa ya basa ai aiko mata da abincin aka yi ya kulle ya matsar daga kusa da shi. Har aka yi la’asar Nihad bata sake shigowa dakin ba, zuwa lkcn he is feeling much better, fitowa daga daki yayi ya ganta kwance kan 2 seater tana bacci, ya karasa cikin parlon, a hankali ya kai hannu ya buga kujeran, ta bude ido da sauri zata kwala ihu ta gansa, don duk tunaninta aljanin daren ne ita ma ya zo mata, Ya dauke idonsa daga kallonta yace “Sallah” Tace “Ina ruwanka?” Bai ce komai ba ya juya ya koma daki, karamar wayarsa ya dauka ya zauna gefen gado yaga miss calls din Nadeeyah har hudu sai kuma miss calls din Abba biyu, sannan message na debit din dubu ashirin da biyar bayan debit din drugs da ta siyo masa da safe, yana ta kallon debit din sai kuma ya mike ya fita daga dakin tana zaune kan kujera yana kallonta yace “Me kika min da dubu ashirin da biyar?” Ta kyabe baki tace “Toh kaza naje na siya na dubu goma nayi girki don ni baxan dinga cin abinci lami ba, bayan nasan Abbana na baka har da kuɗin nama, dubu biyar kuma na siyo spices, dubu goma kuma na zuba mai a mota, idan ma kudin account din ne suka kare ai sai ka kirasa kace sun kare” Kallonta ya dinga yi, ta ɗan kallesa ta gefen ido, sai kuma ta turo baki ta mike ta wuce dakinta ya bi ta da kallo, komawa cikin dakin yayi ya kara bude abincin da tace tayi yana kallo, har cikin ransa bai yarda ita tayi girkin ba duk da bai ci ba, can dai ya dau spoon yayi tasting stew din, nan ya kara tabbatar ma kansa ba ita tayi ba, duk da yunwan da yake ji bai ci abincin ba. Da magrib bayan ya fito daga masallaci ya ga almajirai biyu ya tsayar da su sannan ya shiga cikin gidan ya fito da abincin ya juye masu ya koma kitchen ya wanke warmers din ya fito, daki ya shiga ya dauko makullin mota da atm card dinsa ya bar gidan, tana jin ya fita ta fito balcony da sauri ko gama goge jikinta bata yi ba don wanka take taji ya kunna mota ta kwara ruwa kawai ta daura tawul ta fito da gudu, Hijab dinta da ta fizgo ta saka a kan tawul din, duk a tsorace take da gidan tun da taga gari ya fara duhu dama hankalinta ya tashi, can saman dakalin da yake zama ta tafi ta zauna hawaye cike idonta, ta fi awa daya wajen zaune ga uban sauro dake ta cizonta har da guntun gyangyadinta, sai bayan isha ya shigo gidan, bayan yayi parking ya tafi ya kulle gate ya dawo yana kallonta amma bai ce mata komai ba, juyawa yayi ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri cikin kuka tace “Ni wallahi kar ka sake fita ka barni ni kadai cikin gidan nan da daddare, don baka ga abinda ya faru da Husnah bane har ta bar gidan shi yasa zaka wani tafi ka bar ni kadai kuma ka tafi da makulli” Ya juya ya kalleta yace “Wacece Husnah?” Ta hade rai tace “Kawata da ta zo gidan nan ta kwana mana” Yace “Ohhh ta tafi ne?” Nihad tace “Aljanun dare ne fa suka zaneta fuskarta duk ya kumbura shine ta gudu” Yace “Au haba?” Ta wani daure fuska tana kallonsa, yace “Toh Allah ya sa kar su dawo kanki tunda ita ta gudu” Yana fadin haka yayi hanyar dakinsa ta bi sa da gudu ta fashe da kuka tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, me yasa zaka ce min haka? Me nayi masu ni za su dawo kaina?” Yana shiga dakinsa ita ma ta shige tana kallonsa tana maida numfashi hawaye cike idonta, duk a mugun tsorace take, yace “Malama kwanciya xan yi ki tafi dakinki sai da safe” Ta wani gwalo ido tana kallonsa, sai kuma kawai ta nufi can karshen gadon dakin ta zauna, ya tsaya yana kallonta sai kuma yace “Ohk, sai in bar maki dakin in koma wancan” Bata san sanda ta fashe da kuka ba tace “Don girman Allah kar ka barni ni kadai wallahi tsoro nake ji kuma baxan iya kwana a dakin ni kadai ba” Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana rera kuka, bai kuma ce mata komai ba ya kulle kofar ya karasa cikin dakin. A hankali ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito ta tada sallan isha, yana kwance daya side din gadon waya kare kunnensa, duk da can kasa kasa yake magana amma lkci daya ta gane da warce yake wayar, ta ja tsaki ta mike ta dauke darduman ta linke ta ajiye ta nufi saman gadon ta fizge duvet da ke kai ta dau pillow daya ta shimfida duvet din a kasa sannan ta ajiye pillon ta kwanta, tana ta juye juye kan duvet din can ta kara jan wani tsaki ta tashi ta tafi ta kashe wutan dakin ta dawo ta kwanta, shi dai bai daina wayar da yake ba kuma duk maitarta baxata ce ta ji abinda yake cewa a wayar ba, for almost one hour bai gama wayar ba, ya mike sabida iska da aka fara alamar hadari, kunna wutan dakin yayi Nihad da tayi lamo a kasa tana jin iskan ita ma ta mike zaune da sauri ta bi sa da kallo sai kuma ta tashi ta bisa parlon, ya juya ya kalleta, sai kuma yace “Zan kwanta yanzu kinsan nace maki bani da lafiya, za mu yi magana gobe” Daga haka ya katse wayar yace “Lafiya kike bi na?” Kin cewa komai tayi tana kallonsa, haka kawai tayi masa rashin kunya ya ki yarda ta kwana a dakinsa, shi sa ma taki ce masa komai juyawa yayi ya tafi ya kulle duk windows din gidan, duk inda ya nufa sai ta bi sa har dakinta sai da ya shiga ya kulle windows sannan ya fito tana biye da shi suka koma dakin nasa, kulle nasa windows din yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta daya side din, ba a wani dau lokaci ba aka fara yayyafi, Nihad dai duk a tsorace take a kasa da take kwance, can ta mike zaune a hankali tana kallon saman gadon, sai kuma ta turo baki ta mike ta dauke pillown da duvet ta koma saman gadon ta kwanta, yana jin ta bai ce komai ba sai ma juya mata baya da yayi ya rufe ido, Nihad na jin sauwkan ruwa ta mirgina a hankali ta koma bayansa tayi lamo, ta dade a hka ta kasa bacci, kamar yanda shi ma ya kasa baccin, da taji anyi tsawa sae ta kara matsawa gun sa, a haka har bacci ya dauketa daga karshe…. Can cikin bacci ta ji ana ta6a ta, ta bude ido a tsorace, xata bara ihu ya rufe bakinta da Palm dinsa.

34

Duk a zaton Nihad aljanin daren ne ke tattaba ta cikin Hijab, tunda dama da shi ta kwanta a rai, a rikice take tattaba jikinsa tana kokarin cire hannunsa daga bakinta ta kara kwala wani ihu kamar xata shide, bayan ta gano shine ta fada jikinsa da sauri ta rufe fuskarta a kirjinsa tana kuka sosai tace “Don Allah kace Abba ya canza mana gidan nan ni baxan iya zama ba wallahi, wayyo Allah na shiga uku” Ya rike ta very tight shi ma ya daura fuskarsa saman kanta, tana jin yanda yake sauke numfashi still holding her tightly, kamshin turarensa shi ma ya taimaka wajen kara kwantar mata da hankali, sun fi minti goma a haka, jin ya ki saketa ta dago a hankali har lkcn gabanta na faduwa tana kallonsa cikin duhun, a hankali taji ya saketa ya koma ya kwanta a bit relieved, tana ganin haka tayi saurin kwanciya bayansa tana kuka a hankali, ko minti biyar bai kara ba bacci me nauyi ya daukesa, Nihad kuwa bata sake komawa baccin ba, don duk tunaninta kilan shi ma ya ga aljanin daren ne shine ya ji tsoro ya riketa haka, toh shi ma ya ji tsoro ina ga ita, hakan ya kara daga mata hankali ta dinga shige masa tana shesshekan kuka ta takure cikin hijab dinta, raba daren Nihad tayi tana masu gadi, duk motsin da taji sai ta kara makale masa, sai kusan karfe hudu da rabi bacci barawo ya saceta. A hankali khalil ya bude ido ta dalilin tada sallah da aka yi, ya mike zaune da kyar ya kunna switch din dakin dake bangaren da yake ya juya yana kallonta, baccinta kawai take, ya kalli towel dinta dake can side din sai kuma ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, Har ya dawo masallaci Nihad bata farka ba, kallo daya yayi mata ya dauke kai da sauri, ya dau karamar wayarsa ya fita daga dakin. Sai karfe bakwai saura Nihad ta bude ido a hankali, bin dakin tayi da kallo sannan ta kalli gefenta towel dinta ta gani a yashe ta zaro ido ta kalli jikinta da sauri ta mike zaune tana gyara hijab dinta, kaddai ya ganta haka? Tunanin hakan yasa ta rufe fuskarta da pillow tana kara rufe jikinta da hijab dinta a kunyace, daga karshe dai ta mike ta shiga bandaki, bayan ta idar da sallah tana ta zaune saman darduma har gari ya waye gaba daya sannan ta mike ta fita ta koma dakinta, wanka tayi ta shirya ta fito parlor, bata gansa a parlon ba sai wayarsa dake saman kujera, ta kalli kofar kitchen din alamar yana kitchen, ringing wayar ya fara yi ta kalli kofar kitchen din da sauri, da ta ga kamar bai ji ba tunda bai fito ba tana tafiya a hankali ta karasa gun wayar ta dauka tana kallon me kiran, Father ta gani a screen din, dai dai nan ya fito daga kitchen din ta mayar masa da wayar ta ajiye, kamar yanda ta ki kallonsa shi ma haka bai yarda ya kalleta ba, ya tafi gun wayar ya dauka, kallon screeen din yake ko kiftawa babu, yana ta kallo har kiran ya katse, ta ga ya zauna without knowing he did so, still kuma idonsa na kan screen din, he looks a bit baffled, sake kiransa aka yi, ya daga kai ya kalleta suka hada ido, sai kuma ya dauke kansa ya mike ya nufi kofar ya fita compound, bayan ya fita still bai daina kallon wayar ba kuma ya ki dagawa, zaunawa yayi a saman dakalin da ya saba zama ya daga kiran tare da sallama, he wasn’t given the space to even greet or say anything, ya dai yi shiru yana sauraronsa har ya gama fadin abinda xai fada ya rufe ido a hankali yace “Gobe in sha Allah” yana fadin haka yaji an katse wayar ya kalli screen din, sai kuma ya jinginar da kansa da bango, and he sat there for more than an hour ya kasa shiga cikin gidan, Nihad dake ta zaune parlor ta mike ta shiga kitchen din taga shayin da ya hada a mug har ya huce. Har Nihad ta iso inda yake bai sani ba, shadow dinta da ya gani ya sa ya daga kai, ta jingina da bango tace “Me yasa ka bar shayin a kitchen a bude kuma?” Bai ce mata komai ba, ta tsaya for almost 2 mins, can ta juya ta koma ciki, dafe kansa yayi, a karo na farko yayi regretting barin wayarsa a kunne, yawanci sai xai yi waya yake kunna wayar yana gamawa kuma zai kashe but for almost 3 months now ya daina kashe wayar. Tashi yayi daga karshe ya shiga cikin gidan, tana zaune saman kujera ta bi sa da kallo kamar ya sani ya juyo ya kalleta, ta dan turo baki ta ci gaba da kallon tv da take, har bayan azahar khalil na daki, Nihad ta ji ana kwankwasa gate, ganin bata ga alamar zai fito ya bude ba ta mike ta tafi dakinsa, murda kofar tayi ta shiga ciki, a rufe taga idonsa, ta karasa inda ya ajiye makullin ta dauka ta fita, tana bude gate din gidan taga Naf da zully a tsaye, ta ɗan buda ido cike da fara’a tace “Lahhh, sannun ku da zuwa” Naf tace “Nihad, yaushe Husnah ta bar gidan ki?” Nihad da gabanta yayi mugun faduwa don suna cewa Husnah aljanun daren da ta manta ne suka fado mata, cike da karfin hali tace “Jiya da safe” Naf ta kalli Zully, sai kuma ta kalli Nihad tace “Toh lafiya qlau ta bar gidan ki?” Nihad ta marairaice tace “Ni dai da safe na ganta jikinta wani iri kamar an zaneta, fuskarta duk ya kumbura haka ma bakinta da idonta shine tace min wai aljanun dare ne suka mata haka” Naf da zully suka kwashe da wani dariya barin Naf da sai da ta kai kasa sbda dariya, Naf ta dago bayan tayi dariyarta me isarta tace “Halan ku biyu kadai ne a gidan?” Nihad ta girgiza kai tace “Aa shi ma yana nan ai” Zully tace “Ke kuma kina ina sanda aljanun daren yayi mata haka?” Nihad tace “Ni dai bacci nake, kuma ai kun san anyi ruwan sama, kawai na tashi da safe na ganta a kitchen duk an zaneta, tace in miko mata jakarta da wayarta” Dariya kawai su Zully suke har da kyakyatawa, Nihad dai sai kallonsu take with confusion, Naf tace “Toh sai ku daure ku zo dubata a asibiti don tana can rai a hannun Allah an bata gado, mu kuma ce mana tayi bata kwana a gidanki ba hatsari tayi xata tafi kaduna jiya da daddare an kirata mamarta ba lafiya” Nihad ta gwalo ido tana kallonsu, Naf tace “Ai kam dai tana asibitin da aka ta6a kwantar da kawar zully nasan kin gane asibitin” A hankali Nihad tace “Na gane” Naf tace “Sai ki gaya masa ya kawo ki ku dubata, don da aiki ma ake da niyyar mata a idonta daya daga baya kuma idon ya ɗan bude kadan” Nihad tace “Toh xan gaya masa” Naf tace “Mu yanzu akwai inda za mu, amma xa mu hade a asibitin anjima in ya kai ki kenan” Nihad tace “Toh” Daga haka suka koma motar Naf ta bi su da kallo, sai da suka bar layin sannan ta juya ta koma cikin gidan, tsaye ta gansa bakin kofar parlor, tana karasawa balcony ya hade rai yace “Wa ye ya Kwankwasa gate din?” Babu yabo babu fallasa Tace “kawayena ne, sun zo su ce min Husnah tana asibiti bata da lafiya wai har xa ayi mata aiki a idonta daya, ni dai wllh ka kai ni in dubata tunda a nan gidan aljanun daren suka mata haka” Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya dinga kallonta, can ya juya ya koma ciki. Bayan la’asar taga ya shirya yana rike da mukullin mota ta mike da sauri kafin tace komai yace “In kin shirya ina jiranki idan kuma baki shirya ba inyi tafiyata” Da sauri ta tafi daki ta dauko hijab din ta ta saka, bayan sun bar gidan taga sun hau saman titi tace “Asibitin xa mu je?” Yace “Ohk” Nan ta gaya masa asibitin, tana ganin sun kusa asibitin tace “Baxa mu siya mata wani abu ba?” Yace “Ohk za ki siya mata wani abu kenan?” Tace “Ehh” Yace “Me zaki siya mata?” Tace “Ga wasu masu fruits can kawai ka tsaya mu siya mata” Parking yayi dai dai wajen ta bude motar ta tafi tace su hada variety of fruits na 10k, suna hadawa ta shigo motar tana kallonsa tace “Dubu goma ne” Yace “Ohk, ki basu” Tace “Toh ina atm card din?” Yace “Atm din wa?” Ta wani kallesa tace “Naka mana?” Yace “Ni nace maki ina da kudin siyan fruits?” Ta marairaice tace “Toh amma ba sai da na tambayeka ba?” Yace “Bani da kudin biyan fruit din kawarki” Kamar zata yi kuka tace “Na shiga uku, bayan kasa nace su hada fruits din, ni yanzu ya zan ce masu?” yace “Ke ina atm card din ki?” Tayi narai narai da ido tace “Bama ni da shi ni, kuma wllh babu ko sisi account dina tunda Abba ya dai a bani kudi” Yace “Sauka kice masu su mayar da fruits dinsu kin fasa siya” Ta gefen ido take kallon alamar atm card din nasa dake aljihun rigarsa, can ta zura hannu da sauri ta cafki atm din, rike aljihun yayi yace “Keee” Ta hade rai tace “Idan baka sake ba zan karya wallahi” sai kuma ya cire hannunsa a hankali, ta turo baki ta zare atm card din ta sauka daga motar ya bi ta da kallo, ta basu suka cire kudinsu ta koma mota da fruits din ta saka atm card din a handbag dinta ta kulle, bayan few seconds kawai ya tada motar suka bar wajen. Suna isa asibitin Nihad bata taba tunanin zai shiga dakin ba, amma sai kawai ta ga ya shiga, Husnah na hada ido da shi sai da ta firgita, Su Naf da Zully da wasu frnds dinsu biyu dake dakin suka mike ganin irin firgitar da tayi, Nihad ta kasa karasawa cikin dakin ta makale jikin kofa ganin yanda kamannin Husnah ya canza, ita tsoronta ma take ji yanzu, shi kam ya karasa can cikin dakin har gun gadon ya kalli su Naf calmly yace “Sannunku” Siyama kawar Naf tana Murmushi ta tashi daga saman kujeran da take zaune ta ajiye masa tana kallonsa keenly, cikin taushin murya tace “Yauwa sannu da zuwa, have a seat pls” Ya dan kalleta yace “Nagode kiyi zamanki” Kallon siyamar kawai Nihad take babu yabo babu fallasa, ai tun da Husnah ta kalli khalil sau daya bata sake yarda ta kallesa ba sai mutsu mutsu take yi a inda take zaune kamar warce cinnaka ke cizo, Naf, Zully, da su siyama sai kallon khalil kawai suke, ya dafa gadon da Husnah ke kai yana kallonta da kyau yayi kasa da murya as if talking to him self yace “How are you feeling?” Naf ta kalli Zully da sauri, Husnah dai kai kawai ta gyada ba bakin magana, ko kadan Nihad bata ji abinda yace ba, Yana gyada kai yace “Quickest recovery dear!! And u are always welcome to our home you Slattern!!” Yana gama fadin haka ya juya ya bar wajen duk suka bi sa da kallo, Zully da Naf sai kallon juna suke da wani expression, Husnah dai bata dago kai ba, Yana isa bakin kofa ya amshi fruits din hannun Nihad ya ajiye masu nan bakin kofar a saman wani table, ya juya ya kullo masu ward din, har suka shiga mota Nihad bata iya ta ce komai ba kamar yanda shi ma babu abinda yace, she still can’t believe Husnah ce ta koma haka…. Tana ganin ya dau hanyar gidansu ta daga kai ta kallesa, a kofar gida yayi parking ta sauka ta shiga gidan ba tare da ta jira sa ba, tana shiga parlor ta kalli Nihal dake zaune parlor tana welcoming dinta da fara’a, Nihad bata wani saurareta ba tace “Umma fa?” Nihal tace “Bata nan” Nihal ta taso tana kallonta tace “Kin ga yanda kika yi wani fresh kika kara haske sis, amma kin rame, mu je ki gaida Mumy” Daga haka ta ja ta zuwa bangaren Mumy, Nihad dai gabanta sai faduwa yake don yau kuma bata san me Mumy xata ce mata ba, ga mamakinta da ta gaida Mumy sai taga ta amsa mata normal normal, cikin sanyin murya tace “Mumy ina su Sudais” Mumy tace “Sun tafi islamiyya ya gida?” Tace “Lafiya lau” Mumy tace “Ina Ibrahim din?” A hankali Nihad tace “Yana kofar gida” Mumy tace “Ohk” Nihad ta daga kai ta kalli Mumy dake kallonta, tace “Mumy su sudais basu ta6a zuwa wurina ba” Mumy tace “Za su je in sha Allah” Nihal dake zaune parlon ta mike ta fita, Mumy na kallon Nihad tace “Kin shiga kin gaida Abbanki ne, yana parlonsa” Nihad ta girgiza kai tace “Aa” Mumy tace “Toh in za ku fita ki shiga ki gaishesa” Nihad dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds a hankali Mumy tace “Ina sake tunatar maki ki rike mijin ki, ki bi sa, ki masa biyayya, ki zauna lafiya da shi, farin cikinsa ya zama naki, bakin cikinsa ma ya zama naki, a yanzu baki da wani gata a duniya sama da shi, shi ne gatanki Nihad, kar ki yarda ki bari baraka ya shiga tsakaninku har a ji kanku, Abbanki ba kallonki zai yi ba, tunda a haka kaddarar ki ta zo sai kiyi hakuri ki rungumi kaddararki sai Allah ya dubeki, in sha Allah ina da yakinin Ibrahim baxai cuceki ba, baxai bari kiyi kuka ba in har kika amshesa a matsayin mijin da Allah ya zaba maki a nan duniya” Nihad ta daga kanta hawaye na sauka idonta tana kallon mahaifiyarta, Mumy tace “Duk wani wanda zai zugaki kar ki zauna lafiya da shi ba sonki yake ba, makiyinki ne shi Nihad” Nihad ta gyada kai da kyar hawaye na bin kuncinta tace “Toh Mumy nagode” ita kanta Mumy daurewa kawai take, cike da karfin hali tace “Idan ma da wani abu zaki iya dinga amsar wayarsa ki kirani har zuwa lokacin da zai yarje maki rike waya, Allah ya maki albarka, Allah ya baku xaman lafiya me dorewa” Nan ma Nihad kai kawai ta gyada ma Mumy hawaye na sauka idonta, Sallama khalil yayi bakin kofar parlon, Mumy ta amsa ya shigo ciki, kallo daya yayi ma Nihad dake goge hawayen idonta ya zauna kasa ya gaida Mumy a hankali, ta amsa da fara’a tana tambayarsa gida, Mikewa Nihad tayi wasu hawayen na sauka idonta ta fita daga parlon ta koma main parlor, Nihal na ganinta ta mike tana kallonta har ta zauna kan kujera, Nihal ta karasa ta zauna kusa da ita a sanyaye ta jawota jikinta tace “Kiyi hakuri sis, nasan duk abinda Mumy ta gaya maki abu ne da zai taimakeki har karshen rayuwaki, i want to see u happy and lively once again as before plss sis” Nihad ta fashe da kuka sosai, Nihal ta rungumeta ita ma tana hawaye, Nihad tayi kukanta me isarta Nihal na rarrashinta, daga jajayen idonta tayi tana kallon Nihal da ita ma idonta yayi ja, cikin rawar murya tace “But kema ai kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba ko Nihal? U know baxan taba yin wannan video din in bar shi a wayana, ba halina bane yin video haka” Tana fadin haka ta kara fashewa da sabon kuka, Nihal ta rungumeta a sanyaye tace “I know sis, ba halinki bane hakan, but we are hoping one day one time gaskiya zata bayyana, in sha Allah xaki yi dariya wataran, in sha Allah” Kai kawai Nihad ta gyada mata tana share hawayen da yaki tsaya mata, A hankali Nihal tace “Mu je parlon Abba ku gaisa, he is inside” Nihad dai tayi shiru, Nihal ta mike ta kamo hannunta suka nufi parlon Abba, Nihal ce tayi sallama bakin kofar parlon, ya amsa ta shiga ciki tana rike da hannun Nihad, tun da yaga Nihad ya hade rai sosai, Nihad dai ta kasa dago kanta, Nihal ta sa suka zauna kasa daga gefen Abba tana kallon Abban a sanyaye tace “Sister dita ce ta zo za ku gaisa Abba” Sai a sannan Nihad ta daga idanuwanta ta kalli Abba cikin rawan murya tace “Abba ina yini?” Abba ya mike yace “Wa ya kawo ki gidan nan” Cikin kuka tace “Tare muka zo da shi” Abba yace “Ba nace bana son in sake ganin kafarki a gidan nan ba, wato u want to dare me shi yasa kika zo right?” Nihad na kuka tace “Don Allah Abba kayi hakuri” A fusace Abba yace “Toh bari kiji, yau ya zama first and last day da zan sake ganin kafarki a gidana, bana bukatarki, bana bukatar ki kwata kwata, kije can kiyi rayuwarki amma wllh kar in sake ganin kafarki a gidan nan, idan kuwa ba haka ba duk abinda na maki You caused it for ur self, sannan ita ma uwarki xan dau mummunan mataki a kanta in har kika sake shigo min gida” Nihal ta fashe da kuka sosai tace “To nima Abba ka samar min wani wajen daban don in na koma makaranta babu abinda xai sake dawowa da ni gidan nan, why will u be so harsh on her kamar ita ta rubuta ma kanta ƙaddara, why are you doing all this to her Abba, so kake wani abun ya sameta, kar ka manta she neva bargained for all what is happening to her, me yasa baxa mu taya ta rungumar kaddararta ba ko zata samu sassauci a ranta? Me yasa zaka dinga korarta Abba??” da mamaki Abba yace “Ohk rashin kunya za ki min? Ni kike gaya ma wannan maganan??” Nihal ta mike tana kuka sosai ta dago Nihad suka fice daga parlon, Tsaye khalil da ya fito daga part din Mumy yayi yana kallonsu, nan saman kujera suka zauna suna kuka a tare, sai ga Abba ya fito parlon, Yana ganin khalil yace “A kan wani dalili ka kawota gidana? Ba nace maka ko da wasa bana son ganinta a gidana ba, don me zaka karya min umarnina?” Shi dai khalil bai iya yace komai ba sai kallon Abban yake, Strictly Abba yace “Toh yau ya xama rana ta karshe da zaka kawota gidan nan, kai ma ba sai ka zo ba kuyi zamanku a can kawai, wai ma ba cewa kayi zaku koma zaria ba? Me ya zaunar da ku har warhaka? To Gobe ka tattarata ku bar garin nan, bana kuma bukatar duk abinda zai sake dawowa da ita kano, gidan da kace ka samar maku da farko nasan akwai sauran kudin da na tura maka last week a account dinka kayi amfani da shi ka biya hayan gidan, sannan ka ajiye min makullin motata….” Shiru khalil yayi yana kallon Abba babu ko kiftawa, duk wannan abun Umma da dawowarta daga anguwa kenan tayi still bakin kofa ta kasa karasowa, Mumy ma da ta jiyo muryar Abba ta fito tana tsaye kofar parlornta, Abba ya kalli Nihad yana nuna mata kofa cikin tsawa yace “Tashi ki fita” Tashi Nihad tayi da sauri Nihal ta rikota cikin kuka sosai tace “But she have all right to stay Abba, u can’t just send her away because of a mistake she never bargained for her self, ba ita ta rubuto ma kanta kaddarar nan ba ai naga” muryar Umma suka ji tana cewa “Kul Nihal, kul…. Karen hauka ya cije ki ne kike ja’in ja da mahaifinki? Ashe ke mahaukaciya ce dabba ban sani ba? Are you stupid? Kaji min mahaukaciya shashashar yarinya, ko duniyar ce baki son gamawa da lafiya?” Nihal ta sake Nihad tana kuka sosai ta mike da gudu ta wuce dakinta ta dau waya ta kira Yaya farooq, Umma ta nufi Abba tace “Alhaji ka yayyafa ma zuciyarka ruwan sanyi kada wani abu yaje ya sameka don Allah” Cikin tsawa Abba yace “Su fitar min a parlor kawai” Umma ta kalli Nihad da damuwa tace “Tashi ki fita Nihad….” Sai kuma ta kalli khalil tace “Ka ajiye masa makullin motar ibrahim, ku je kawai kun ji” Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta nufi kofa Khalil ya ajiye makullin motar dake hannunsa saman kujera ya bi bayanta har suka fita daga parlon, Juyawa Mumy tayi tana share hawayen dake ta zuba idonta ta koma bangarenta, Abba ya shige parlonsa a fusace Umma ta bi bayansa da damuwa. Har suka kai gate Nihad ta kasa daina kukan da take, tun da suka fito dama Aminu ke kallonsu, don duk wanda ke compound din nan ranan sai ya jiyo muryan Abba, Aminu dai ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, a karo na farko ya ji tausayin rayuwar Nihad, xuciyarsa ya karaya sosai, Khalil ya dafa sa a hankali yace “Xa mu yi waya” Daga haka ya fita gate din Aminu dai ya bi su da kallo ya kasa cewa komai, har suka isa titi Nihad bata daina kukan da take ba.

35

Bayan sun isa gida Khalil ya ba mai adaidaita sahun da ya kawosu kuɗinsa, Nihad dai ta jingina da gate ta rufe fuskarta da Hijab din jikinta tana kuka kamar ranta zai fita tana jin xuciyarta na mata zafi, har sannan she is finding it hard to believe Abbanta ne yace baya son sake ganinta har abada, wai yau ita Abba ke ce ma haka, where is all the love he showed her? she wish her life could end now let all this be over, Khalil ya bude gate din ta shiga ciki da sauri tana kara sautin kukanta, da ido ya bi ta bayan ya kulle gate din har ta shiga parlor, yana tafiya a hankali ya tafi inda yake zama ya zauna ya jinginar da kansa da bango, har aka yi magrib yana wajen a zaune yayi nisa tunanin da yake, at this point he knows he is confuse because things have taken another turn, he neva saw all this coming, daga karshe ya mike gwiwa a sanyaye yayi alwala a tap din dake compound din ya fita zuwa masallaci, bai kuma fito daga masallacin ba har sai da aka yi sallan isha… Yana dawowa ya shiga parlor, tana zaune a parlorn ta hade kanta da gwiwa har sannan bata daina kukan da take ba, ya karasa ciki yana kallonta, zaunawa yayi saman kujera still looking at her, he don’t even know what to say to her, beside he don’t even have anything to say to her, he felt exactly what she is feeling right now some years ago, and he knows the feeling, tuna hakan yasa zuciyarsa yayi rauni, tashi kawai yayi daga karshe ya shige dakinsa ya kulle kofar. Khalil bai sake fitowa ba sai kusan karfe sha biyun dare, kwance ya sameta inda ya bar ta bacci ya dauketa, ya karasa ya durkusa gabanta yana kallonta, gently yayi tapping dinta, ta bude ido da sauri, sai kuma ta mike xaune tana murza idanuwanta da suka kumbura, yace “Ki je ki ci abinci ki yi sallah” Daga haka ya mike ya koma dakinsa ya kulle kofar, ta jinginar da kanta da kujera wasu hawayen masu zafi na sauka idonta, gaba daya taji duniyar yayi mata zafi, me yasa Abbanta zai ce mata baya son ganin har abada, me yasa abbanta zai yi mata irin wannan koran kuma Umma na jinsa amma bata ce komai ba, she saw everything that happen amma tayi shiru, sosai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, bayan kusan minti talatim ta mike a hankali jiki ba kwari ta wuce dakinta tana jin jiri, alwala kawai tayi, tayi magrib da Isha ta kwanta kan darduman tana duk addu’an da ya zo bakinta hawaye na sintiri a gefen fuskarta, daren nan Nihad bata yi baccin kirki ba, da baccin ya dauketa zata farka a firgice, wajajen karfe tara na washegari Khalil ya bude kofar dakinta yana kallonta yace “Ki dau duk abinda za ki dauka ki fito parlor, ina jiranki yanzu” Yana fadin haka ya juya ya bar wajen, Nihad ta mike zaune just staring at the door, sosai kanta ke mata ciwo kamar zai fashe, bayan few minutes ta mike ta canza hijab kawai ta fito parlorn tana tafiya a hankali, yana zaune ya jinginar da kansa da kujera bayan ya kashe duk wani abun wuta na gidan, ya kalleta yace “Ina kayan?” Ta girgiza kai cikin karfin hali tace “Ba abinda xan dauka” Shiru yayi bai ce komai ba, can yace “Ki je ki karya…” Nan ma ta girgiza masa kai alamar baxata yi breakfast din ba, bai kuma cewa komai ba, ita dai tana ta tsaye parlon kanta a kasa, har zuwa lkcn tana ganin scene din abinda ya faru jiya ya kasa bacewa a idonta, daga karshe Khalil ya mike yace “Mu je” Bin bayansa tayi tana jin kamar zata fadi har suka fita daga parlorn, ya kulle gidan, suna fita gate taga motar haya irin warce ke zuwa kaduna, Abuja anyi parking a bakin gate din, tana dai tsaye har ya gama kulle gate din gidan ba tare da ya kalleta ba yace “Shiga motar za ki yi” A hankali ta kai hannu ta bude bayan motar ta shiga ta zauna ta kulle, ya zauna a gaba, tun da aka haifeta bata ta6a shiga ire iren wannan motar ba sai yanzu, ta goge hawayen dake makale idonta tana wasa da fingers dinta, sai da Khalil yasa suka fara zuwa can gida ya mika ma Aminu makullin gida yace ya ba Abba, Aminu har da kwallarsa yace “Toh yanxu sai yaushe kenan??” Khalil na kallonsa yayi murmushi cikin sanyi yace “Khairan in sha Allah Aminu” Daga haka yayi patting shoulder dinsa ya shiga motar, Aminu ya bi sa da kallo, dama tun da suka shigo layin Nihad ta hade kai da gwiwa hawaye na sauka idonta don bata ma son taga gidan nasu, balle ace kallon karshe ta ma gidan, har kuma suka bar layin bata dago ba sai shesshekar kuka take tana ganin duk abinda ke faruwa kamar a mafarki, sai da taji sun yi nisa sannan ta dago kanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata…. Ba su yi awa daya ba suna tafiya taji zuciyarta na tashi saboda warin fetur da take ji motar na yi, daga karshe ta toshe hancinta da hijab din jikinta, tun dai tana daurewa har dai suna dab da isa garin zaria ta tabo khalil dage gaba, ya juya da sauri, ganin yanda ta rufe bakinta da hannu biyu yasa shi ce ma Drivern ya nemi waje ya tsaya, dreban na bakin a gefen titi ta sauka da sauri ta dukurkusa gefen hanyan tana yunkurin amai, Khalil ya sauko daga motar ya jingina da motar yana kallonta, kasancewar ba abinda ta ci yasa bata yi aman ba, sai kokarin kakaro shi take amma babu abinda ya fito, shi dai yana tsaye yana kallonta, bayan few minutes ta mike da kyar ta koma motar tana maida numfashi, shi ma ya koma cikin motar, driver na mata sannu ta gyada masa kai kawai, a haka suka ci gaba da tafiya, kafin su isa kaduna tayi hakan yayi sau hudu amma duk bata iya tayi aman ba, Khalil ya sa drivern ya tsaya a wani restaurant cikin garin kaduna ya sauka ya siyo mata abinci, yana fitowa daga restaurant din ya ganta durkushe jikin motar ta sauko, duk tayi zuru zuru kamar ba ita na, tana ganinsa ta mike da kyar, hawaye cike idonta cikin sanyin murya tace “Ni baxan iya ci gaba da tafiya a motar nan ba, yana min warin fuel” Yace “Ohk, yanzu ya za ayi kenan?” Tayi shiru bata ce komai ba tana share hawayen idonta, yace “Ko kina da kudi ki biya mana jirgi” Ta daga kai da sauri ta kallesa, can kuma tace “Ina za mu je ne?” Yayi shiru yana kallonta, sai kuma ya dauke kai yace “in kina da kudin jirgi sai ki siya mana ticket kawai, babu ke babu jin warin fetur, in kuma baki da halin wannan za ki iya siya mana ticket din jirgin kasa mu tafi mu hau yanzu” A hankali tace “To ai ni bani da ko sisi a account dina” Yace “Shine kike korafin mota na maki warin fetur?” Ita dai bata ce komai ba, yace “Kina bata mana lokaci” Juyawa tayi ta bude motar ta shiga ya mika mata ledan hannunsa ta amsa ya kulle motar sannan ya shiga front seat yana kallon dreban yace “Muje” Driver ya tada motar suka ci gaba da tafiya, iya wahala Nihad ta wahala kafin su isa Abuja, abincin ma ta kasa ci, banda ruwa kawai da ta sha, shi ma duk sai da ta amayar da shi, sai bayan la’asar suka shigo Abuja, wani hotel kawai ya sa drivern ya sauke su, drivern ya sauko masa da kayansa daga motar, Khalil yayi masa godiya sosai, sannan drivern ya ja motarsa ya bar wajen, A reception din hotel din Nihad ta zauna ta kife kanta saman kujeran gefenta tana maida numfashi, har khalil ya biya masu kudin daki bata sani ba, sai da ya kai kayansa ciki sannan ya dawo yana kallonta, she looks sick and tired, yace “Nan din ya fi maki ne?” Ta dago da sauri tana kallonsa, ya juya ya bar wajen, sai kuma ta mike ta bi bayansa tana tafiya a hankali, bayan yayi leading dinta har zuwa dakin ya sake fitowa yayi masu ordering abinci a hotel din, daga nan ya fita pharmacy ya amso mata paracetamol sannan ya koma dakin, kwance ya sameta saman gadon tana baccin wahala, ya tafi kan kujera dake dakin ya zauna, bayan few minutes aka kwankwasa kofar dakin ya mike ya tafi ya bude ya amso abincin da yayi ordering sannan ya kulle kofar ya dawo ciki ya ajiye abincin, dama abinda yake jira kenan, ya shiga bandaki yayi wanka ya fito ya shirya sannan ya fita dakin don Bolt din da yayi ordering na location dinsa, da har zai kulle kofar dakin da makulli sai kuma ya fasa, yana fita hotel din ya shiga motar suka tafi. Tafiyar kusan minti talatin da biyar suka yi bayan sun shigo wani anguwa wanda kai kana gani kasan ba kowa ke shigowa area din ba, Drivern bolt din ya kalli khalil da turanci yake tambayarsa ana shiga ciki dai ko? Khalil yace masa ya shiga kawai, drivern ya ja motar yana driving din a hankali zuwa gate din dake gabansa, tasowa ma’aikatan dake wajen suka yi, drivern ya kalli Khalil da ya sauke glass din motar ya gaisa da su sannan drivern ya ci gaba da tafiya slowly, tafiyar minti sha biyar drivern yayi ya tsaya dai dai wani gida wanda nan ne location da Khalil ya saka, ma’aikatan dake wajen suka taso xuwa gun motar, Khalil ya bude motar ya sauka ya daga ma drivern bolt din hannu sannan ya nufi gate din gidan, bai amsa gaisuwan da securities din ke masa ba ya shiga ciki kawai, har ya isa main entrance din babban duplex din babu wanda ya kalla a compound din balle ya amsa gaisuwan da suke masa, direct part din Maminsa ya nufa ba tare da ya hadu da kowa a hanya ba, ya bude kofar parlonta na farko a hankali, babu kowa ciki sai sanyin Ac da kamshi me dadi dake tashi a parlon, ya karasa daya parlon ya shiga, nan ma ba kowa ciki….. Dai dai nan ta fito daga bedroom dinta da Mai aikinta, tsaye tayi with shock tana kallonsa baki bude, ko kwakkwaran motsi bata yi sbda shock, ya karasa a hankali ya rungumeta ya lumshe idonsa, cike da karfin hali tace “Khalil??” Mai aikinta ma haka ta koma gefe ta rufe baki da hannu tana kallonsa, kasa ce ma Maminsa komai yayi, ta dago kansa tana kallonsa hawaye cike idonta tana girgiza kanta, yayi mata murmushi cike da karfin hali yace “I have missed u soo much Mami” Ta kara rungumesa ta fashe da kuka sosai tace “How did you get here? Who allowed you in? Ta ina ka shigo?” Ya kasa ce mata komai lkci daya idanuwansa suka kada, Mai aikin ta nufi kofa ta fita ta kullo masa kofar a hankali, Mami ta ja sa zuwa bedroom dinta tana kallonsa hawaye na sauka idonta tace “How did you get here son?” Sauke idonsa kasa yayi ya tafi gefen makeken gadonta ya zauna, tafiya tayi da sauri ta zauna gefensa ta kamo hannunsa tana kare masa kallo, ba ainahin haskensa ba kenan, sannan ba haka ya bar gidan nan ba, ta fashe da kuka sosai ta dafe kanta ta kasa ce masa komai, yayi karfin halin cewa “Kiyi hakuri Mami, surely everything that has beginning will definitely have an end” Ta dago kai cikin kuka sosai tace “Amma ta yaya ka shigo gidan nan Khalil?” Kallonta kawai yake, Bayan few seconds a hankali yace “Abba ne ya kirani” Mami ta zaro ido tana kallonsa da kyau tace “You mean da kansa ya kiraka??” Khalil ya gyada mata kai yace “Yea Mami, i don’t know what he is seeing me for” Hankalin Maminsa ya kara tashi, ta hadiye abu da kyar tace “When did he call you?” Khalil ya sauke idonsa yace “Jiya….” Mami tayi tagumi with different thought running her mind, can ta tashi tace “Ohk, but u are not moving an inch from here today, ka bari sai nan da jibi, babu wanda xai san kana gidan nan, you just remain here for now, ok?” Kallonta Khalil ya dinga yi ya kasa cewa komai, ta mike ta dau wayarta da sauri tayi dialing number mai aikinta, tana dagawa tace “Bilkisu kada ki ce ma kowa khalil ya dawo yana gidan nan, make sure babu wanda xa ki gaya ma har su Mimi” Bilkisu tace “Dama babu wanda na gaya ma Mami” Mami tace “Good” Daga haka ta katse wayar, Khalil dake ta kallonta yace “But i have to go out before Magrib Mami” Mami ta zaro ido tana kallonsa tace “Out to where? u are going nowhere for now Khalil, ko nan da second parlor dina baxa ka fita ba i am telling you, u will remain here for now” Kasa ce mata komai yayi ya dinga kallonta, ta juya da sauri ta fita daga dakin, ba a dau lokaci ba sai ga Mami da tray me dauke da different fruits ta ajiye masa, Mai aikinta dake biye da ita ta ajiye nata tray din, before 5 minutes duk aka cika masa gabansa da abinci iri iri da natural drinks, bayan mai aikin ta fita Mami ta kasa daina kallon ɗan nata, tana yi tana share hawayen da ya ki tsaya mata, har sannan gani take kamar a mafarki ne, gani take xata farka taga babu shi, dawowa tayi kusa da shi cike da karfin hali tace “Tell me what u want to eat in zuba maka son, fried rice? Jollof rice, tuwo da miyar taushe, sinasir? Cous cous? Is it the pepper chicken u are taking first or the cow leg pepper soup?” Kallonta kawai yake ya kasa cewa komai, lkci daya jikinsa yayi sanyi, he knows he missed all this, ta fashe da kuka ta rungumesa tace “My prayers was always with you son, i know i have missed u a lot, i just had nothing to do about it” Kuka take sosai, ya runtse ido yace “Pls ki daina kukan nan Mami, i was fine and comfortable all through, kawai dai na kan yi kewanki da kannena sosai hakan ne kadai ke samin damuwa” Mami ta sake sa ta sauka ta fara zuba masa abincin iri iri a plate, shi dai kallonta kawai yake, bayan ta gama zuba masa tace “Ka ci duk abinda kake son ci sai kayi wanka son, let me get u what to change” Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, fadawa yayi saman gadon, gaba daya hankalinsa ya tafi kan Nihad da ya bari ita daya a dakin hotel, from where will he start convincing his mami har ta hakura ta bar sa ya fita?? Not even that, don kuwa wannan me sauki ne, now!! from where is he going to start explaining to Mami cewar ai an masa aure? Ta yaya zai fara mata wannan gagarumin bayanin and how will she even take it balle uwa uba Abbansa, tunanin hakan scent cold all over his body, ya mike zaune a hankali yana jin wani sanyi na shigarsa sosai, tun barinsu kano hankalinsa bai tashi haka ba sai yanzu, ta ina zai fara wannan bayanin yace ai an masa aure wanda shi ma ba da son ransa ya amshi auren ba, Yaya iyayensa da relatives dinsa da ma yan uwansa gaba daya za su dauki wannan babban lamarin, aure without his parents consent, this now is his biggest challenge so far, rike kansa yayi bayan yaji kansa ya wani tsara masa, After some minutes Mami ta dawo dakin da kayansa da ta saka a leda don ma kada wani ya gani, kannen Khalil kuwa duk ta hanasu zuwa ɓangarenta a sunan she is not okay and she needs privacy, da sauri khalil ya dago bayan Maminsa ta shigo dakin, ganin bai ta6a abincin ba da damuwa tace “C’mon pls ka sauko ka ci abinci Khalil kar ya huce, ko dai akwai wani abun dake damunka har yanzu…” Khalil ya dinga kallonta yana tunanin ta inda zai fara, can dai yayi karfin halin cewa “Mami na ji kince baxan fita ba, kuma fitan da xanyi yanxu is very urgent” Mami ta zauna kusa da shi cikin rawar murya tace “I am afraid baxan sake ganinka ba kuma Khalil, kilan idan ka fita baxa a sake barin ka shigo gidan nan ba, i can’t…” kawai sae ta fashe da kuka tana girgiza kai cikin tashin hankali tace “Haka jikina ke bani, i can’t endure loosing u for the second time son, ban san me zai faru da ni ba idan hakan ta kasance, me xaka fita kayi Plss?” Ya sauke idonsa da ya kada, bayan few seconds cikin sanyin murya yace “Mami gidan da nake zama a garin kano da nace masu zan taho Abuja yau sun hadani da er su muka taho tare da ita, zata karbi admission letter dinta a wani makaranta da tayi applying a nan, she knows nobody in here Mami, kuma har yanzu tana makarantar tana jirana” Mami tace “Oh my God, is that so?? Allah sarki, bari in kira driver sai ka bani numberta in tura masa yaje ya daukota yanzu” Khalil was shocked at what she just said, Mami ta mike da sauri xata dauko wayarta ya bi ta da kallo, can sai gata ta dawo kafin ta kira Drivern yayi saurin cewa “Mami she is just a young girl, bata da waya a hannu, dama sai xata fara karatun ne za su bata waya, kawai ce mata nayi zan zo in dauketa a makarantar later” Mami dake kallonsa tace “Toh ka fadi inda kace ta jira ka a makarantar mana in kira Drivern in sanar masa yaje ya daukota, why are you making this a big deal son??” Khalil ya kamo hannunta a hankali yace “Mami tsoronki kada in fita a hanani shigowa a bakin gate ko? but trust me ya sanar masu zan zo ya kuma masu izinin barina in shigo shi yasa har suka barni na shigo, idan da ba haka bane da baxan ta6a shigowa gidan nan ba” Mami ta fashe da kuka tace “Bana son kowa yasan ka dawo Khalil” Khalil ya girgiza kai a hankali yace “Mami, surely in dai yan gari xai tambayesu ko na zo kuma za su sanar masa na zo ina gidan, kiyi hakuri in je in daukota yanzu in dawo Mami, i promise you ko awa daya baxa ayi ba zan dawo” Mami dai tayi shiru tana goge hawayen dake ta sauka idonta, sosai zuciyarsa ya karaya ganin yanda Maminsa ke kuka, ya rungumeta ya runtse ido yace “Kiyi hakuri Mami, kowa a rayuwar nan da irin tasa kaddarar, and Alhamdulillah so far” Mami ta gyada kai tace “Haka ne son” Yayi kasa da murya yace “Ni kaina bana son ganin kowa na gidan nan a yanzu, don haka ki kwantar da hankalin ki, i will follow the back door idan xan fita…” Cikin sanyin murya tace “Toh mota fa?” Yace “I will order Bolt” Mami bata kuma cewa komai ba, yace “In sha Allah idan na dawo zan ci abincin Mami” Yana fadin haka ya lumshe ido yayi pecking dinta a forehead sannan ya mike, ta bi sa da kallo hawaye na zuba idonta har ya fita daga dakin.

36

Khalil na isa hotel din ya nufi dakin direct ya bude kofar, sosai ya ji gabansa ya fadi ganin babu kowa cikin dakin, da sauri ya karasa ciki yana kallon abincin da ya ajiye mata yaga ko ta6awa bata yi ba, lkci daya yaji zufa na keto masa, kallon kofar bandaki yayi nufi can da sauri ya bude kofar nan ma babu ita a ciki, nan yaji hankalinsa ya kara tashi ya fice daga dakin ya sauka kasa yana kallon receptionist din wajen yace “Don Allah yarinyar da muka shigo dazu…” Kafin ya karasa receptionist din tace “Ta fita ai” kasa daina kallonta yayi, yayi karfin halin cewa “Ta fita? When pls?” Matar tace “Some minutes ago” juyawa yayi da sauri ya nufi kofar fita daga cikin hotel din, receptionist din ta bi sa da kallo, Khalil na fita bakin titi yana waiga gefensa ya ganta can zaune daga jikin hotel din kamar marainiya, lokaci daya ya hade rai ya nufeta, ita bata ma lura da shi ba tayi nisa cikin tunanin da take, yana isa dai dai inda take yace “Baki da hankali ne zaki fito nan bayan kinsan jakata na dakin?” Ta daga kai ta kallesa, sae kuma a hankali tace “To ba kai nake nema ba” yace “Me yasa zaki nemeni? Saboda me?” Ita dai bata ce komai ba, sai a sannan ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, ya juya ya bar ta wajen, ordering wani bolt din ya mayar da wayarsa a aljihu ya juyo yana kallonta yace “Ki jira ni a nan” Daga haka ya koma dakin don dauko jakarsa, yana fitowa sai ga motar, bayan sun gaisa da drivern ya sa jakarsa a booth, ya juya ya kalli Nihad dake kallonsa, ai bata ma jira yace ta taso ba ta taso ta nufosa, ya zaga ta daya side din ya shiga motar, tana dai ta tsaye, jin bai ce mata komai ba ta bude bangaren da take tsaye ta shiga ta jawo kofar motar a hankali. Kamar me Bolt din dazu wannan ma sae da ya tambayi khalil ko zai iya shiga ciki ganin unguwan da suka zo, Khalil ya sauke glass din side dinsa ya daga ma securities din wajen hannu sannan suka wuce, Nihad dai tun da suka shigo anguwan nan take kalle kalle uwa idanuwanta za su fito, she is wondering where he is taking her to, duk inda suka wuce sai taga securities, very tight security, bata ta6a jin tsoron kasancewa da Khalil ba sai wannan moment din, she looked at him looking very afraid, to ko dai inda ake yankan kai ma zai kaita, sosai gabanta ya dinga faduwa hankalinta yayi mugun tashi, ta dinga kallon Mad houses din da suke ta wucewa na masu kudi da suka amsa sunan su kudi a kasar, hakurin Nihad ya soma karewa ta juya a hankali ta sake kallon Khalil for the 5th time, gabansa kawai yake kallo fuskarsa babu yabo babu fallasa, Ai bata san sanda ta marairaice masa ba cikin rawan tace “Don girman Allah ina zaka kai ni? Don Allah kayi hakuri ka rufa min asiri, ina ne nan ka kawo ni?” Sai ta sakar masa kuka a hankali jin ya ki ce mata komai, shi dai ko kallonta baya yi, ko ma wanene yanda Khalil yayi keeping serious and straight face sai ya tsorata balle Nihad da dama can matsoraciya ce, Shi kam drivern bolt din slowly yake tafiya sbda Securities that are everywhere don zuwa lkcn gari yayi duhu, amma sai kayi tunanin rana ce don ko ta ina haske ne tarr, har dai suka isa dai dai gidansu Khalil, sai dai ba ta inda ya shigo dazu bane, wannan second gate din gidan ne dake ta baya, drivern ya tsaya yana duban ma’aikatan da suka nufo motar gadan gadan, Khalil ya bude motar ya sauka, suna ganinsa suka gaishesa suna komawa baya, Ganin Nihad taki saukowa daga motar ya zaga ta inda take ya bude motar yana kallonta babu yabo babu fallasa yace “Malama kina bata masa lokaci” Ta marairaice tana kallonsa cikin rawan murya tace “Don girman Allah ina ne nan din ka kawoni, kayi hakuri ka gaya min” Gaba daya tayi zuru zuru da ita kamar ba Nihad ba, shi dai kallonta kawai yake, can yace “Neman taimako na zo yi nan din, tunda kin ga bamu da inda za mu je” Ta gwalo ido sosai tana kallonsa da mamaki, can tayi karfin halin cewa “Taimako kuma? Unguwar masu kudi ne sosai fa, ba kowa ne ke shigowa nan ba wallahi, kuma ko kallonmu baxa su yi ba sai ma su kore mu ko su sakar mana karnuka, wllh ka shigo idan ba haka ba securities din nan za su iya sa mu tsallan kwado yanzun nan” ya dafa motar yana kallonta da kyau yace “Sa’armu za mu gwada, kuma ni nasan ina da sa’a sai in ke ce baki da, Malama ki sakko kina bata ma me mota lokaci” Da sauri Nihad ta kalli me tukin motar dake jiranta ta sauka patiently, can ta kalli khalil pleadingly tace “Ni dai don Allah ka zo ka shiga mu koma, babu abinda za su mana a nan” Yace “Idan muka koma kina da kudin da za mu ci abinci gobe? Ko kina da kudin da zaki sake biya mana daki a hotel din?” Kallonsa ta dinga yi, lkci daya jikinta yayi sanyi, hawaye ya kawo idonta, sai kuma ta sa hannu ta share idon nata a hankali tace “Sai ka bani waya in kira ya Farooq nasan zai turo mana kudi” Yana kallonta yace “Aa, wannan gidan dai nake son shiga in gwada sa’a ta” Ta kallesa zata yi magana ya hade rai yace “Kina bata masa lokaci malama” a hankali ta sauko daga motar tana kallon Khalil hawaye na bin kuncinta, ya daga ma mai bolt din hannu ya ja motarsa ya bar wajen, cikin kuka tace “Toh ni dai da kace ya maida ni in jiraka a can hotel din, in ya so kai kadai sai ka shiga gidan” Wani kallo yayi mata ya nufi gate din gidan da tuni aka bude masa, Ta gefen ido take kallon securities din gabanta na faduwa don wasu dirka dirkan bayin Allah ne, can dai tana ganin Khalil ya shiga cikin gidan ta bi bayansa da sauri, ga mamakinta basu kulle ba suka jira har ta shiga sannan suka rufe gate din, Nihad ta dinga bin makeken compound din me dauke da wani ubansun mansion da kallo, kai kana ganin gidan nan kawai kasan ba karya malam, Compound din kuwa yayi ukun nasu ga parking lot kaca kaca, ko wanne da ride lafiyayye a parke, ita bata ma san ta bayan gidan suka shigo ba, don ta can ne zata ga ainahin kyan gidan, chalet da aka yi can gefe da ta hango kuwa ya kusa nasu main building din, tafiya kawai yake tana binsa zuciyarta na bugawa, but how comes yana ta tafiya kansa tsaye and nobody is even stopping him, taga sun zaga ta baya ya shiga wani stairs wanda aka shimfida ma carpet grass, shi kansa tsakar gidan wajen duk malale yake da Carpet grass din, bude wani kofa yayi bayan sun haura sama sun mike wani babban corridor, ya bude wata kofar duk tana biye da shi a baya a tsorace, ko nisa bata son yayi mata, gaba daya she is really confused at how he is just badging in babu shakka ba komai, ita tsoronta kada a kama su ayi masu dukan tsiya, da ido ta dinga bin parlon da ya shiga tana makale bakin kofa ta kasa shiga zuciyarta na bugawa, Can taga ya shiga wata kofar da sauri ta bi bayansa ko kulle kofa bata yi ba, nan taga kofar da ya shiga wani parlon ne wanda ya fi wanda suka baro haduwa, at this point, she is super confuse, bayan ya isa kofar dakin Maminsa ya juyo yana kallonta, ya fi second goma yana kallonta wanda hakan ne ya kara mugun tsoratata, can kuma babu yabo babu fallasa yace “Zauna nan” Ta kasa zama har taga ya shiga wani kofar, Mami na nan zaune yanda khaleel ya bar ta don ta kasa samun nutsuwa, gani kawai take shikenan kuma baxai sake dawowa ba, gaba daya jikinta a sanyaye yake har zuwa yanzu da ya shigo dakin nata, da sauri ta mike ganinsa with happiness written all over her face ta nufesa kace “U kept to ur promise son, baka wuce awa dayan ba, i was so worried ina ga kamar tafiya ka kara yi….” Yayi Murmushi ya kamo hannunta a hankali yace “Amma bana son ki saka rai da yawa ki sakankance a kan cewar na dawo in zauna Mami, kar ki manta ban san kiran me Abba ke min ba, he might still not be needing me in his house, kilan idan ya gama fada min abinda zai fada xai iya cewa in bar masa gidansa and i don’t have choice….” Hawaye ya shiga sakkowa idon Mami tana girgiza kai tace “Baxan yarda da hakan ba this time around son, sai dai duk abinda zai faru ya faru, shirun da nake masu ya zo karshe, baxan sake shiru ba in har yace ka bar masa gidansa for the second time” Shi dai khaleel bai ce komai ba sai kallon mahaifiyar tasa yake cike da tausayinta, kamar yanda take ganin ya rame, shi ma haka yaga ta rame saboda damuwa, Can Mami ta share idonta da sauri tace “Where is the young gal?” Ya kalli kofa yace “She is at the parlor” Mami tace “Ohk” Daga haka ta nufi kofar ta fita ya bi ta da kallo, zaunawa yayi gefen gado ya rike kansa, yasan ko me zai faru baxai samu courage din sanar masu ai Nihad yarinya ce da babanta ya aura masa ba, shi kuma ya amshi auren nata ba don ransa ya so ba sai don ganin girma da mutuncin mahaifinta sannan baxai iya turning down din offer din mahaifinta ba, yasan baxai ta6a fara masu wannan bayanin ba, fadawa saman gadon yayi ya kwanta ya lumshe ido yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Mami na fitowa parlor taga Nihad a tsaye bakin kofa tana shesshekan kuka, tun bayan da taga khaleel ya mata wannan kallon sannan ga shiga kofar ya kulle tayi saurin komawa bakin kofar fita parlon ta tsaya zuciyarta na raya mata shikenan babu wani tantama ya kawota ne kawai a gille mata kai ayi kudi da ita, dama masu kudin nan wasun su kowa yasan ai suna yankan kai, to kila mai gidan ya ba khaleel contract din samo masa kan da za a gille shi yasa har ya shigo gidan tare da ita babu wanda ya hanasa, sai ma bude masa kofa da securities din suka yi har da masu gaishesa, irin dai ya saba shigowa gidan kenan, sannan gashi taga kansa tsaye ya taho bangaren nan da ita, wato in da za a gille mata kan kenan, uwa uba tun da suka shigo gidan bata ga ko wani mutumin ba sai securities, Da mamaki Mami ke kallon Nihad ganin yanda take hawaye tace “Subhanallah, Baby are you okay? why are you crying?” Kallon matar kawai Nihad take hawaye na sauka idonta kuma taki ce mata komai, wannan ba ita ce ta gani a hoto ranan a dakinsa ba? Mami tace “C’mon, come in dear….” Nihad taki karasowa sai kallonta take, Mami na ganin haka ta juya ta koma dakinta ta shiga tana kallon Khalil dake kwance saman gadonta da mamaki tace “Khaleel na ganta tsaye bakin kofa tana kuka, is she okay? Nace ta shigo kuma ta ki” Mikewa Khalil yayi ya fita parlon Mami ta bi bayansa, yana kallon Nihad, ya dake yace “Shigo ciki” Mami ta karasa inda take tsaye ta kamo hannunta ta shigo da ita parlon tana kallon Khalil murya can kasa tace “Doesn’t she understands English?” Bai ce komai ba ya juya ya koma dakin, Mami ta zauna gefen Nihad da ta zaunar edge din kujera kamar me shirin fillawa da gudu, tace “Ya kike yan mata?” Nihad ta goge idonta tana kallonta a hankali tace “Ina yini” Mami na Murmushi tace “Alhamdulillah, ya su mamanki?” Nihad ta sauke idonta kasa cikin sanyi tace “Lafiya lau” Haka kawai Nihad taji hankalinta ya ɗan kwanta ganin Mami, Mami ta kwantar da murya tace “Ki saki jikinki kinji, nan ma duk gida ne” Nihad ta kasa ce mata komai, Mami tace “Kin yi sallan magariba?” Nihad ta girgiza mata kai, Mami tace “To ga banɗaki kije kiyi alwala, bari in kawo maki darduma a bedroom yanzu” Nihad ta mike ta tafi kofar da Mami ta nuna mata a parlon ta bude a hankali tana kallon ciki, bandakin ya kusa girman dakinta, ta karanto addu’ar shiga banɗaki a ranta sannan ta shiga, Mami ta mike ta tafi daki ta ga Khalil ya dauro alwala ya fito, area din da Mami tayi demarcating a dakin don yin sallah ya nufa, Mami ta dau ma Nihad darduma daya ta kai parlor ta shimfida mata, sannan ta koma dakin ta shiga bandaki ita ma ta dauro alwalan, Khalil na zaune saman darduma yana azkar bayan ya idar da sallah, Mami ta mike bayan ita ma ta idar tana kallon side din da yake tace “Yanzu abincin xan dauka in kai can parlon, ko ta shigo nan kawai ku ci?” Yace “Ki deba kawai ki kai mata can parlon Mami” Mami tace “Ai ban san abinda tafi son ci ba, kawai bari ta shigo ta yi serving kanta ko?” Mami na fadan haka ta fita zuwa parlor tana kallon Nihad dake saman darduma tayi kuri da ido tace “Baby shigo ki ci abinci” Nihad ta mike a hankali ta tafi kofar dakin ganin taki shigowa Mami tace “Shigo mana” Cikin sanyin murya tayi sallama ta shiga dakin, ta dinga bin abincin dake jibge a kasa da kallo kamar za ayi party, Mami tace “Ki duba duk abinda kike so ki diba” Mami na fadan haka ta fita daga dakin, Nihad ta durkusa tana kallon Khalil, murya can kasa tace “Don Allah ina ne nan ka kawo ni?” Sai a sannan Khalil ya kalleta tun da ta shigo dakin yace “Inda za a mana alfarma ba tare da an walakanta mu ko an ci zarafinmu ba, ba kuma tare da an damu da mu talaka ne ko masu arziki ba” Shiru tayi tana kallonsa, ya mike ya zauna gefen gadon yace “Debi abinda zaki deba ki fita” Ita dai ta kasa cewa komai kuma ta kasa bude ko warmer daya balle ta zuba abincin, Mami ta dawo dakin rike da teapot da cups dinsa biyu a tray, da mamaki ta ke kallon Nihad bayan ta ajiye tray din hannunta tace “Baki debi abincin ba” Sai kuma ta kalli khalil kafin tace komai ya kirkiri murmushi yace “Haka take Mami” Nihad ta daga kai ta kallesa, Mami tace “But why? pls tell her to feel free” Khalil ya maida idonsa kan tv dake aiki silently bai ce komai ba, Mami ta dau plate ta debar ma Nihad shinkafa da miya ta ajiye mata, ta debar mata duk wani abu da xata dibar mata sannan ta mike, Nihad dai bata ta6a jin she is confuse kamar yanda take ji yanzu ba, gaba daga kanta ya kulle ta kasa fahimtar komai, lkci lkci sai ta kalli khalil sannan ta kalli Mami, Mami na kallon Khalil a hankali bayan ta gama zuba ma Nihad abinci tace “When did you say he called you?” Khalil ya kalleta duk da ya gane wanda take nufi yace “Ke baxa ki ci abincin ba Mami? Ki zuba mana tare mu ci” Mami tace “Talk to me son, he is back now” Sai da gaban khalil ya fadi ya mike yace “Really? But hope you didn’t….” Sai kuma yayi shiru, ta gefen ido ya kalli Nihad da ta kafesa da ido babu ko kiftawa, sai kuma ya fice daga dakin, Mami na kallon Nihad da murmushi fuskarta tace “Ki ci abinci kin ji Baby” Daga haka ta juya ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo bata kwakkwaran numfashi, bayan kusan minti sha biyar Khalil ya dawo dakin shi kadai, har sannan Nihad na zaune position din da take kamar warce ruwa ya cinye, gaba daya jikinta yayi sanyi qlau kana mata kallo daya zaka gane hakan, Ta bi sa da kallo har ya dau teapot da cup zai fita, cikin sanyin murya tace “Ka gaya min, wanene kai?” Bai yarda ya kalleta ba yace “Driver!!” Daga haka ya fice daga dakin, ta bi sa da ido babu ko kiftawa, abinda ya fada dazu da turanci ne ke kai komo a ƙwaƙwalwarta, lokaci daya ta runtse ido ko zata samu saukin sara mata da kanta ke yi. Khalil na zaune parlor sai ga Mami ta shigo tana kallonsa, shi ma kallonta yake, a hankali tace “Kaje wajen Abbanka, yana kiranka parlonsa” Khalil ya kalleta looking so worried yace “Mami da baki ce masa na dawo yau ba” Mami ta girgiza kai tace “I never told him, tun daga gate ya tambaya securities, su suka sanar masa kana gidan nan…..” Yayi kasa da murya yace “But bana son kowa ya san am around Mami” Mami tace “Zaka iya zagawa ta baya ai, har yanzu babu wanda yasan kana gidan nan” Mikewa yayi ya nufi kofa yana tafiya a hankali ta bi sa da kallo har ya fita.

37

Khalil na shiga parlon Abbansa bai bari suka hada ido ba, yana tafiya a hankali ya zauna saman lallausan Carpet dake kasa, yayi gathering courage yace “Barka da dare Abba” Shirun da Abban nasa yayi yasa a hankali ya daga kai ya kallesa yaga jaridar hannunsa kawai yake dubawa, ya sunkuyar da kansa, bayan kusan minti biyu Abba ya ajiye jaridar hannunsa yana kallonsa a takaice yace “Wani international joint ventures na wata daya zaka min handling a Zanzibar, and the business isn’t new to you, you know everything about it, so u can chose to stay there in Zanzibar or come back to Nigeria weekly, bayan kayi min sorting komai zaka iya komawa duk inda ka fito ka ci gaba da rayuwarka since it’s the best for you and you are okay with it, i will neva beg you to come stay here!!” Yana gama fadin haka ya mike ya shiga dakinsa Khalil ya bi sa da kallo, sai gashi ya fito da files ya jefa masa nan kasa yace “Everything u will be needing is there, u can leave my sight now” Khalil ya dau files din a hankali yace “In sha Allah, Nagode Abba” Daga haka ya mike ya nufi kofa Abban nasa ya bi sa da kallo har ya fita, yana fita ya juya suna hada ido da Abba, Abba yayi saurin juyawa ya shiga bedroom dinsa. Har Khalil ya shigo parlon Mami na tsaye ta kasa zaune sai kai komo take a dakin, she is so disturbed and worried, Allah ya sa kiran alkhairi yake masa, tana ganin Khalil ya shigo ta nufesa da sauri tace “What did he say to you??” Khalil ya mika mata files din hannunsa ta amsa tana dubawa da sauri, can ta kallesa tace “What about this?” Yace “He wants me to be in charge” Mami ta dinga Kallonsa babu ko kiftawa can tace “He said so?” Khalil yace “Yea” Murmushi tayi ta rungumesa tana hamdala a zuciyarta amma ta kasa cewa komai hawaye ya cika idonta, ta sakesa tace “Yanzu yaushe zaka tafi?” Khalil yace “I need to prepare” Tayi kasa da murya da damuwa tace “Zan so ka shirya first thing in the morning ka bar gidan nan kafin wani yayi noticing dinka, har yanzu basu san u are around ba, nasan shi ma bai sanar masu ba” Khalil bai iya yace mata komai ba, ta goge idonta tace “Shigo ka ci abincin yanzu, i am so happy at this good news” Ta kama hannunsa suka wuce can bedroom dinta, tsaye tayi bakin kofa da mamaki tana kallon Nihad da ko motsi bata yi daga inda take ba balle ta ta6a abinda Mami ta zuba mata a gabanta, Mami ta kalli khalil tayi kasa da murya tace “Are you sure zata yarda ta kwana nan son? She hasn’t taken anything yet, are sure baxaka duba ko da akwai flight going to kano a yankar mata ticket ba?” Khalil dai sai kallon Nihad yake, Mami tace “Do so before it’s late plss, kasan wasu nature ne hakan basu sakewa a wani waje ba gida ba, so kar a takurata” Juyawa tayi ta fita daga dakin, khalil ya duka dab da ita yana kallonta, kin yarda su hada ido tayi, lkci daya yaga hawaye ya ciko idonta, still looking at her yayi kasa da murya yace “Where u offended in anyway?” Ta kallesa sai kawai ta fashe da kuka sosai, cikin karfin hali tana magana da kyar tace “Don Allah… Kayi hakuri ko a motor park ne ka kai ni ka sa ni a motar Jigawa in tafi wajen Aunty Jamila, don Allah kayi min wannan last alfarman” Tana kuka me ban tausayi ta fadi hakan, sai kuma ta hade kanta da gwiwa, yana ta kallonta kafin yace “An maki wani abu ne a nan din da za ki tafi jigawa?” Ta daga idanuwanta da hawaye ke zuba tana girgiza kai tace “Ni bance an min komai ba” ya dau duk abincin da Mami ta sa mata a plate ya kai parlor sannan ya dawo yace “Fito ki ci” Tace “Ni na koshi” Yace “Fito nace” Mikewa tayi trying hard not to burst into new cry ta fito daga dakin ta tafi ta zauna inda ya ajiye abincin, ta hadiye wani abu da ya tokare mata throat da kyar, Yana kallonta yace “Now eat” Bata san sanda kukan ya subuce mata ba tana girgiza masa kai, ya hade rai yace “Kee” ta daga ido da sauri ta kallesa, ya durkusa yana kallonta, sai kuma ya ciro handkerchief ya mika mata, Da sauri ta sunkuyar da kanta, ganin har sannan mika mata handkerchief din yake ta kai hannu a hankali ta amsa, ta goge hawayen da ke zuba idonta da shi shi dai kallonta kawai yake, bayan ta gama goge idon ta daga kai a hankali tana kallonsa, ya sauke idonsa ya matsar da plate din abincin gabanta, ta kalli cokalin dake cikin abincin ta dauka ta diba ta kai baki a hankali ta fara ci, mikewa yayi ta bi sa da kallo har ya fita zuwa next parlor din, gaba daya taji baxata iya cin abincin ba, she has clearly run out of appetite, this is the third shock of her life so far, but this particular one is so strong and it’s about giving her heart attack, of all the shock, this made her felt bata da sauran hope a duniya, this made her loose all hope, she now believe she is now all by her self a duniyan,  kwakkwaran wata daya ba ayi ba ta girgiza da lamari har kala uku, yanda take ji a ranta ta kara tabbatar da bata da wani sauran gata kuma a duniya, ganin komai take kamar mafarki amma ita dai tasan ba mafarki take ba, this is nothing but reality, bata ta6a jin ta tsani kanta duk abubuwan dake faruwa ba sae yau, she hate herself for everything so far, ta daure ta tashi da kyar ta mayar da duk abincin cikin warmer dinsu ta fito don tasan baxata ta6a iya ci ba, ta zauna kasa ta jingina da kujera, ko sanin hawaye na zuba idonta bata yi ba. Khalil na zaune first parlor da Maminsa dake waya da sister dinta, she is happily telling her that he is back, daga nan kuma ta kira aminiyarta warce kasar su daya and she is always there for her at all time, shi dai khalil kallonta kawai yake har ta katse wayar, Mami ta mike tace “An samu jirgin kuwa son?” Ya girgiza kai yace “Aa Mami” Tace “Toh gobe first thing sai kayi mata booking ticket kafin ka tafi koh?” Khalil bai ce komai ba, Mami ta koma can ciki, ba a dau lokaci ba sai gata da plate din abinci ta zubo masu, tare suka ci abincin, ya ci peppered chicken din kawai a maimakon pepper soup yace mata ya koshi, Mami ta kira Bilkisu ta kwashe duk abubuwan ta fita da su daga part dinta. Karfe tara da rabi Mami ta shigo parlon da Nihad take tana kallon Nihad tace “Toh ki tashi kiyi wanka don ki ji dadin jikinki ko?” Nihad ta mike tsaye ba tare da ta bari sun hada ido ba, Mami dai sai kallonta take, ganin ta nufi kofa tace “Ga bandaki nan a bedroom” Ta girgiza kai tace “Zanyi a na parlor” Daga haka ta fita daga parlon zuwa daya parlon wanda bandakin ke ciki, tayi hakan ne sbda  la’akari da tayi da Mumynta, bata sharing bathroom din dakinta da kowa, khalil dake danna waya ya daga kai ya kalleta, tun da ta kalli iphone din hannunsa bata sake kallon direction din nasa ba, yaga ta shiga bandaki, Mami ta shigo parlon ta kirasa ya mike ya bi bayanta, suna tsaye parlon farko tace “Toh yanzu a haka da taki sakin jiki zan kai ta bangarensu Mimi?” Yace “Aa Mami ki yi mata shimfida kawai a parlor nan ta kwanta” Mami tace “Aa haba dai, ya zata kwana a parlor, abinda yasa kaga bance zata kwanta nawa bedroom din ba i am leaving it for you kai ka kwanta, ni zan je in kwanta wani wajen” Yayi Murmushi yace “Aa Mami ba sai kin bar min gadonki ba, kawai ki kwanta ni zan kwanta parlor, kema kinsan i prefer sleeping on the couch” Tace “Toh shikenan sai mu kwanta da ita a daki, let me get her sleeping dress wajensu Mimi….” Daga haka ta fita sai gashi ta dawo da sabuwar rigar bacci na Noor ta kai dakinta ta ajiye ma Nihad a gefen gado da tsadaddun spray biyu sannan ta fito, Nihad na fitowa daga wankan taki shiga dakin, shi dai yana ta danna wayarsa, ta rakube jikin kujera, Mami ta fito parlon zata ma Khalil shimfida, ganin Nihad a rakube tace “Baby shiga ciki ki shirya, za ki ga sleeping dress da turare na ajiye maki saman gado” A hankali Nihad tace “Nagode” Daga haka ta shiga dakin, Shimfida me lafiya Mami tayi ma Khalil a parlor na biyu, shi dai bin ta kawai yake da kallo, yasan yayi kewar Maminsa fiye da zatonsa, he so missed all this, har bedroom dinsa Mami kan shiga ta gyara masa back then, tana gamawa ya mike ya nufeta yayi mata side Hug cikin sanyin murya yace “Thanks Mamina” Tace “Ai kai ma zaka yi wankan ko?” Yace “Sure” Tace “Let me get u ur pajamas” Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo, sai kuma yayi murmushi ya shiga dakinta don shiga banɗakinta yayi wankan, zaro ido Nihad tayi ta rufe jikinta da kayan baccin da take kokarin sakawa ta durkusa kasa da sauri ta rufe fuskarta, ya sauke idonsa ya juya ya fita daga dakin, bandakin da tayi wanka ya shiga kawai, Mami ta ajiye masa pajamas din saman inda tayi masa shimfida bayan ta dawo ta tafi dakinta, dariya Nihad ta bata ganin yanda ta rakube kasa jikin dressing mirror bayan ta saka kayan baccin, Mami tace “To tashi ki hau gado ki kwanta” Nihad ta kalleta da sauri cause she never expect it, can tace “Aa zan kwanta a kasa” Mami tace “Common hau gado kiyi kwanciyar ki Baby” Shiru Nihad tayi sai kuma ta mike a hankali ta tafi ta hau saman babban bed din wanda furnitures dinsa kadai ma abun kallo ne, Mami ta dago mata duvet ta mika mata ta amsa ta rufe jikinta ɗon dakin yayi sanyi ta dalilin Ac dake kunne. Har kusan karfe dayan dare Nihad bata ga bacci ba, tuni Mami tayi bacci, da ta tuna wasu abubuwan sai taji hawaye me zafi ta gefen idonta na zuba, she wish she could rewind everything from the scratch, she wish many things didn’t happen, daga karshe da taga she needs to cry out ko zata samu saukin abinda take ji a ranta, cike da karfin hali ta mike zaune tana kallon Mami cikin duhu, a hankali ta lallaba ta sauka daga kan gadon ta tafi bakin kofar, nan ma ta tsaya tana tsoron kada kofar yayi kara idan ta bude har ya farkar da Mami, can dai ta runtse ido ta kai hannu handle din kofar ta murda a hankali ta bude, bata ji yayi kara ko kadan ba, ta fita ta kullo mata kofar, yana kwance parlon nan ma wutan a kashe yake, a hankali tana tafiya making sure she isn’t making any sound ta tafi ta bude dayan kofar ta shiga daya parlon, can wani corner ta tafi ta zauna tana shesshekan kuka cike da tausayin rayuwarta, hawaye kawai take wani na bin wani, tun da ta fito daga dakin Khalil da shi ma bai yi baccin ba ya bi ta da ido cikin duhun har ta tafi daya parlon, he can’t say why he is still awake may be over excitement ne na cewar yau gashi a gida da Maminsa after some years, bayan kusan minti 7 ya mike a hankali, shi ma bai kunna wutan ba ya nufi kofar ya bude gently ya fita, ta direction da yake jin shesshekan kukanta ya nufa, kawai gani tayi wani abu da yayi mata kama da statue tsaye a kanta, er kara tayi a mugun tsorace ta mike xata gudu ya rikota, sai a sannan ta ji kamshin turarensa ta rufe fuskarta da sauri a jikinsa tana kuka a hankali, bayan few seconds yace “Saboda kiyi kuka kika fito nan?” Ita dai bata ce komai ba sai shesshekan kuka take tana Girgiza masa kai kawai, ya janyeta jikinsa yace “Zauna nan” ta tattaba bayanta taji kujera, hakan ya sa ta zauna a hankali, yana tsaye inda yake yace “Ki saurari duk abinda zan ce maki yanxu cause it’s for ur benefit” ita dae tayi shiru tana jin sa gabanta na faduwa, yayi kasa da murya yace “On no condition xa ki gaya ma wani a gidan nan relationship dinmu, that should be s secret between us har zuwa sanda xa mu cika ma juna alkawarin da muka dauka a baya” Nihad dai kanta na kasa, yace “Nace ma yan gidan admission letter kika zo amsa garin nan, so duk abinda zaki ji na gaya masu gobe ya zama hakan kema a wajenki” Nihad ta share idonta ta gyada masa kai kawai, ya kunna wutan parlon yana kallonta yace “Sai da safe” Bata yarda sun hada ido ba ta mike ta nufi kofar shiga second parlon Mami ya jira har ta shiga sannan ya bi bayanta. Washegari Nihad na tashi taga ita kadai ce dakin Mami, tana kokarin gyara gadon sai ga Bilkisu ta shigo, Bilkisu na murmushi tace “Ina kwana” Nihad ta sauke idonta tace “Mun tashi lafiya” Bilkisu tace “Ai da kin bar shi ma xan shigo in gyara, aikina ne” Nihad dai bata ce mata komai ba ta shigo ta fara abinda zata yi, Nihad ta fita parlor, tana bude kofar first parlor taga Mami da khalil a zaune parlon, Ta gaida Mami da ladabi Mami ta amsa mata da fara’a, ta kalli Khalil suka hada ido, ta kasa barin wajen bata gaishesa ba saboda Mami dake zaune, bata yarda ta kallesa ba tace “Ina kwana?” Yace “Lafiya, ga breakfast din ki” Mami tace “Bari a kai mata can parlon so that she will be comfortable” Yace “Aa za ta yi a nan” Nihad dai bata ce komai ba, can ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ya nuna mata breakfast din dake saman tray, ta dauka ya nuna mata inda xata zauna, Mami dai sai bin ta da kallo take because she is so cute and meek, Mami ta kallesa tace “Amma ‘yar mai gidan da kake ce min kana zama wani lokacin a gidansa ce ko?” Khalil zai yi magana aka bude kofar parlon, Mimi da Noor ne suka shigo, suka yi wani ihu a tare ganinsa, daga inda yake zaune duk suka tafi da gudu suka rungumesa so happy seeing him, sai ga wasu set din Yan matan biyu Hanan da Farhana, su ma duk suka rungumesa so so happy seeing him, he couldn’t help it but smile don shi ma yayi kewansu sosai, Mami dai sai murmushi take, Mimi ta kalli Mami ta fashe da kuka tace “Mami mene ya sa zaki boye mana yayanmu ya dawo, Abba yace he’s been around since yesternight” Sai kuma ta fashe da kuka, Khalil ya jawota gefensa yana kallonta yana murmushi yace “Is there any diff between now and the yesternight” Tace “Yes of course, wallahi da nasan kana nan nima a nan zan kwana jiya, i soo miss you yayanmu” Tana fadin haka ta kara rungumesa tana hawaye, Nihad dai sai bin su take da kallo kana ganinsu kasan su ne ainahin rich kids din, duk Mimi ta fi kama da shi, Noor ma fara ce Farhana da Hanan ne kadai haskensu bai kai nasu Mimi ba, Farhana sai kallon Nihad take keenly, can ta kalli Mami tace “Mami who is she?” Mami tace “Our visitor” Tambayarta ne ya ja hankalin sauran yan matan suka kallo inda Nihad ke zaune, Noor ta ɗan juya ido tace “Ohh She looks familiar” Hanan dai kallonta take babu ko kiftawa kamar me son gano wani abu, can ta ja Noor suka fita daga parlon tana zare ido tace “Kin tuna wata yarinya da video dinta ya tafi viral weeks ago?” Noor ta zaro ido bayan tayi recalling video din tace “Ohh yess!! exactly, wallahi suna kama sosai, i think baxan rasa video din a thrash bin dina ba” Tun da Khalil yaga sisters din nasa duk sun yi concentrating kan Nihad, yace “Ohk, ohk now, i need rest za mu hadu anjima a main parlor…” Mimi tace “Yayammu who is she, nima kamar na santa” Mami tayi dariya tace “A ina kika santa, banda karya Mimi” Mimi ta juya ta sake kallon Nihad da ta sunkuyar da kai gabanta na mugun faduwa don banda nude video dinta babu abinda ya fado ranta, mikewa Khalil yayi yace “Mimi za mu hadu anjima a main parlor, i said i need rest, ku fita” Sai ga Noor da Farhana sun shigo da gudu parlon, Hanan ta biyosu da sauri, Noor ta nufi Mami har tana tuntube tana mika mata wayarta tace “Mami u remember this???” Mami ta amshi wayar ganin video din da take nuna mata tace “Wai ba nace ki goge video din nan ba Noor? What is it still doing a wayarki?” Noor na zaro idanuwanta kamar za su fito tana nuna Nihad tace “Ba ita bace warcan” Mami ta kalli Nihad da sauri, sai kuma ta amshi wayar tana kallo, Kasa cewa komai Khalil yayi, Nihad da jikinta yayi sanyi kamar warce aka kwara ma ruwan sanyi ta kasa kwakkwaran motsi inda take zaune ta dinga bin su da kallo kamar warce tayi ma sarki karya, sai kuma ta sunkuyar da kanta with tears in her eyes, Mami ta kalli Khalil da sauri, sai kuma ta kara kallon Nihad, tuni Farhana ta tafi ta kirawo wasu set din yan mata biyu duk suka tsaya bakin kofa ko warce da wayarta a hannu, da ta kalli videon sai ta leko ta kalli Nihad baki bude, Mami da ita kanta jikinta yayi sanyi qlau ta kara kallon Khalil that is saying nothing, can ta hadiye wani abu tace “No, no may be resemblance ne kawai, ai akwai resemblance” Noor da Farhana suka wani gwalo ido har suna hada baki suka ce “Mami wallahi ita ce, the video is so clear fa ba wai yayi dishi dishi bane, ki duba mana ki ga, ita ce wllh” Da sauri Hanan ta tafi tana mika ma Mami waya wai don ta kara gani da kyau, Mami ta ki amsar wayar bata kuma sake cewa komai ba, Sajida tace “Ikon Allah, then who brought her to this house? Ance yar Maryam Abatcha American University ce fa” Mimi dake tsaye gefen Khalil ta kallesa a hankali tace “Yayanmu who is she?” Bai ce mata komai ba yana bin sisters din nasa da kallo ya nuna masu kofa yace “Ku fita” Farhana ta kyabe baki haka ma Hanan duk suka juya, Noor ma tayi ficewarta, Mimi ta dinga kallon Nihad dake ta hawaye, Ita ma ta fita daga parlon, Mami dai mutuwar zaune tayi a inda take. Daga karshe ta mike ta shiga dakinta ta zauna side din gado duk jikinta a sanyaye, a ina Khalil ya samo yarinyar nan har zai shigo da ita gidan nan? Bilkisu ta fito daga bandaki tana kallon Mami ganin yanayinta tace “Mami are you okay?” Mami tayi karfin halin cewa “Sure, ki tafi idan ina bukatarki zan kira ki Bilkisu” Tace “Toh Mami” Daga haka ta fita daga dakin, Har sannan Khalil na tsaye ya rasa abun yi, Nihad dai ta hade kai da gwiwa tana shesshekar kuka, Bayan Bilkisu ta fita ya juya ya tafi dakin Maminsa, yana shigowa dakin ya kulle Mami ta mike tana kallonsa cike da tuhuma tace “Khalil wacece warcan yarinyar ka kawo mana gidan nan? Who is she? Menene alaqarku?” Yayi gathering courage yace “Mami calm down pls, yarinyar mai gidan da nace maki nakan zauna wajensa a kano ce, kuma ai na gaya maki dalilin da ya sa muka taho tare, Banda wannan babu wani dalilin Mami” Mami tace “Toh zan tura maka kudin jirgi ka siya mata ticket ta koma, ai ta gama abinda take ko?” Ya rasa abinda xai ce, Mami ta hade rai tace “Ko baka ji abinda nace bane?” Yayi kasa da murya yace “Mami bata gama ba, bata samu amsan admission letter din ba ma” Mami tace “Toh me kake nufi? Ka gaya min me kake nufi Khalil?” Ya marairaice yace “Mami karki manta gidan babanta fa nake all this while, bai san ni ba ya yarda da ni, yayi accomodating dina na zauna cikinsu for almost 10 months now” Mami tace “Yanxu ya kake son ayi khalil? Me kake son in fada a wannan issue din? Sai kace baka san mutanen gidan nan ba ko mance halinsu ne? wait first…  Wai ma ita ce a video din nan ko ba ita bace?” Ya sauke idonsa kasa bai iya yace komai ba, Mami tayi masa tsawa tace “Baka ji na ne?” Cike da karfin hali yace “Ita ce” Mami tace “Nawa ne kudin jirgin, zan tura maka yanzu” Yana girgiza kai hankali tashe yace “Mami mun yi magana da mahaifinta kan cewa ta zauna nan gunki har ta karbi admission letter din tunda bai fito ba, Mami we can’t repay him this way, he is one of the nicest person i have met in life, kawai ka haifi yaro ne baka haifi halinsa ba, but her mother and father are down to earth, sun min abinda baxan mance su a rayuwa ba, sannan Mami duk yaran gidan mahaddatan qur’ani ne, kawai dai ita….” Sai kuma ya kasa ci gaba don ya rasa me xai ce, Mami ta fashe da kuka tace “Magana kake son ja min yanzu fisabilillah Khalil? A ina kake son in ajiyeta har ta zauna a gidan nan bayan kana gani duk yan matan sun shaida ita ce a videon nan kuma sun je su idar, sannan har shi Abbanku sae da ya tofa nasa a lokacin da ya ga video din nan kwanaki, he was so disappointed yayi ta addu’an Allah ya shirya mana zuri’a, sai kawai yau a ganta a gidan nan ba kuma kowa ya kawota ba kai?? Kai da kake da ta6o ta ko ina a gidan nan shine zaka kara shafa ma kanka kashin kaji? Check this out khalil, yaushe har Abban naka ya bukaci ka dawo da har zaka dawo tare da wannan issue din? Kayi min gata kayi ma kanka gata ka fitar da ita daga gidan nan kafin wani ya kara noticing dinta bayan kanninka, Plss take her out of this house Khalil”

38

Khalil bai kuma ce ma Mami komai ba sai kallonta kawai yake lokaci daya duk jikinsa yayi sanyi, juyawa Mami tayi ta fice daga dakin ta zauna second parlonta, a hankali Khalil ya zauna kan kujeran dake dakin yana jin kansa na mugun sara masa, gaba daya he is confuse, dafe kansa yayi thinking of where to start from, where will he begin now? Damuwar Mami ya ninka wanda shi ya ji ya shiga a lkcn, daga karshe taji ta kasa zaman ɓangaren nata, she just can’t imagine Khalil ya sake barin gida for the second time saboda wannan issue din, tafi kowa sanin halin mahaifinsa, this time around also he won’t take it likely with him,  tashi tayi tana jin wani sabon tashin hankali ta fita daga parlon, Nihad na nan zaune yanda take a first parlor din, Mami bata yarda ta kalleta ba amma jin yanda take kuka sai ta kasa fita daga parlon duk da ta bude kofa, kulle kofar tayi gently ta juya ta kalleta, sai kuma ta nufeta walking slowly tace “Kina ji na, ki daina wannan kukan ya isa haka, ga breakfast dinki ki tashi kiyi” Nihad bata iya ta ce mata komai sai kuka take kamar ranta zai fita, sai a yanzu maganganun Aunty Jamila ke dawo mata and it seems this is just the beginning of what she’s talking about…. Mami tayi karfin halin cewa “Taso muje can parlon ki karya, kuma nace ki daina wannan kukan haka nan” Daga haka Mami ta daukar mata abubuwan karin ta kai other parlor dinta ta ajiye, bayan ta dawo parlon tana kallon Nihad tace “Baxa ki bar kukan nan haka ba? Taso mu je can parlon” Sai a sannan Nihad ta mike da kyar, har sannan kuma ta kasa  daina kukan da take, Mami ta rike hannunta har zuwa daya parlon ta zaunar da ita tace “Eat now” Zaunawa kawai Nihad tayi, her heart is so heavy, and she is now beginning to feel useless, juyawa Mami tayi ta fita daga parlon, Visitor room dake bangaren nata ta shiga kawai ta zauna cike da damuwa. Khalil ya mike daga karshe jin kukan da Nihad take ya fito parlon don Mami a bude ta bar kofar bedroom din nata da ta fita, Zaunawa yayi kan kujeran dake kusa da inda take zaune, he is speechless at first, after few seconds ya kalleta, a hankali yace “It’s okay, and….” Sai kuma yayi shiru, Can yace “Kiyi hakuri” Ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, yace “Baki ji me nace ba” Sai a sannan ta daga kai ta kallesa da idanuwanta da suka yi jajir, ya kasa ci gaba da kallonta ya sauke idonsa yace “Kiyi hakuri, take ur breakfast now” A hankali ta dinga subsiding kukan da take amma tana jin xuciyarta na mata zafi, Ya sauka ya koma inda take without looking at her ya dau cup ya zuba mata ruwan shayi, ya haɗa mata shayin, ya ajiye side dinta, ita dai goge hawayen da yaki tsaya mata kawai take tana kallonsa, Bude kofa yaji anyi a other parlor din, ya dau shayin yace “Tashi mu je ciki kiyi breakfast din” Mikewa tayi da sauri ta bi bayansa zuwa bedroom din Mami, ya ajiye mata shayin sannan ya koma zai dauko sauran abincin, Mami ce ta shigo parlon, ganin Nihad bata parlon ta sauke ajiyar xuciya, juyawa khalil yayi bayan ya dau abincin ya nufi Bedroom da sauri saboda muryoyin wa enda yake ji, Mami ta zauna parlon har Hajiya Amina ta karaso ta zauna, Sai Hajiya Hassana ma ta shigo ta zauna, Hajiya Amina tace “Yanzu tun jiya dama Khalil ya dawo gidan nan aka ki sanar mana? Sai kace wani mugun abu, sannan kuma ya ki zuwa ya gaida mu?” Mami tace “Jiyan ai ba da wuri ya dawo ba” Hajiya Amina tace “Toh ai bai wuce duk mu yi barka ba, mu bama bakin ciki da abun alkhairi, daxu su Farhana ke ce min ya dawo nace to ai haka dama ake so” Hajiya Hassana dake girgiza kafa tace “Yana ina yanzu?” Mikewa Mami tayi ta wuce bedroom dinta, duk suka kalli juna suka ta6e baki a tare, Mami na shiga dakin ta kulle kofar, Khalil na zaune ya sa Nihad a gaba tana shan shayin hannunta da kyar, yana ganin Mami ya mike ɗan yana durkushe a gabanta ne, Mami tace “Ka fito ku gaisa” khalil ya kalleta ya ɗan hade rai yace “In gaisa da wa?” Mami tace “Ka rufa min asiri, minti nawa ne kun gaisa ka juyo” Ya girgiza kai yace “Aa kiyi hakuri Mami, wallahi baxan fita ba” kasa cewa komai Mami tayi tana kallonsa, ya koma saman kujera ya zauna yace “Saboda me xan gaisa da su, sanda xan tafi sallama muka yi da su balle mu gaisa yanzu da na dawo, i am sorry Mami i am not going out” Mami sai kallonsa take, can tace “Toh ko bakin kofa ai sai ka tsaya Khalil, kai baka gudun abun magana ko?” Yace “Aa gaskiya bana gudu Mami, i am not moving an inch from here, ita Aunty Hassana dama a shirye nake da ita na dawo gidan nan, she shouldn’t dare cross my part” Mami dai duk jikinta yayi sanyi ta kasa ce masa komai, daga karshe Khalil ya tashi ya bude bandaki ya shige, A hankali Mami ta juya ta fita ta koma parlon tana kirkiran murmushi tace “Shiryawa yake, idan ya gama duk xai je ya gaishe ku” Hajiya Hassana ta daga mata hannu ta dakatar da ita da sauri tace “Aa ba sai kin karesa ba Fatima, ai bamu isa ya fito ya gaida mu ba ne, mu a su wa?” Mikewa tayi tana kallon Hajiya Amina tace “Taso mu je Amina” Hajiya Amina ta mike suka nufi kofa Mami ta bi su da kallo har suka fita, Mami ta sauke ajiyar xuciya ta zauna. Daga karshe ta mike ta fita daga parlon nata, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da kayan Mimi, ta shiga dakinta ta ajiye gefen gado tana kallon Nihad tace “Shiga bandaki kiyi wanka yanzu” Khalil dai na zaune yana kallon Mami, Nihad ta tashi ta shiga bandakin, Mami ta fito parlor, biyota yayi ya zauna kujeran kusa da ita yayi kasa da murya yace “Don Allah ki saurareni Mami” Mami tace “Sauraran me xan maka Khalil” Yayi gathering courage xai yi magana aka bude kofa duk suka juya, Farhana ta shigo parlon tana kallon Khalil tace “Yayanmu wai kaje Abuu yana kiranka” Yayi shiru yana kallonta, Mami ta hadiye abu da kyar tana kallon Farhana tace “Ki je yana zuwa” Juyawa tayi ta bar wajen, Mami ta kallesa da damuwa tace “Ka je kaji kiran da yake maka” Khalil bai iya yace komai ba, can ya mike ya fita, slowly yake tafiya har ya isa bangaren Abba, yayi sallama sai da aka amsa masa sannan ya shiga, Abba na tsaye ya shirya alamar zai fita, Khalil yayi ma Aunty Hassana kallo daya ya zauna kasa, a hankali yace “I am here sir” Abba yana nuna masa Aunty Hassana yace “Who is she to me?” Khalil bai iya yace komai ba, Calmly Abba yace “Tambayarka nake” Khalil ya kallesa yace “Ur sister” Abba yace “Good, kasan da haka ka dawo gidan nan baka je ka gaida ita da Hajiya Amina ba” Khalil yayi shiru, Aunty Hassana tace “Aa yaya, uwar ce ta sa shi hakan ba kowa ba, ita ce xata hanasa ya shigo ya gaida mu saboda ba mu isa ba, sannan still mun tashi mun je har can bangaren nata don ganinsa amma kememe yaron nan ya ki fitowa ta wani fito tana karesa, ita Amina da abu kadan ke sa ta kuka muna fitowa ta kama kuka wai ai wannan cin mutunci ne, ni kuma kasan halina bana daukar nonsense shine yasa ma na zo na sameka yanzu, yaron da a haife na haifesa? Sau nawa nake saka ka a gaba ina cewa kayi hakuri ka bar sa ya dawo gidan nan, shine zai dawo ya saka min da haka?” Abba dai yayi shiru yana safa da marwa a babban parlon nasa, Khalil ya jefa mata wani kallo ta gefen ido, Can Abba ya juyo yana kallonsa da kyau yace “Bata hakuri, sannan duk ka bi su bangarensu ka gaishesu kace masu ka dawo” Khalil ya kalleta a takaice yace “Yi hakuri” Daga haka ya mike ya fice daga parlon, Da ido Abba ya bi sa, Anty Hassana ta saki baki ita ma ta bi sa da kallo, Can ta kalli yayan nata xata yi magana yace “Tashi ki je Hassana, xan nemesa anjima idan na dawo” Aunty Hassana ta dinga kallonsa da mamaki, sai ma taga ya nufi wajen takalmansa ya zauna yana kokarin sa wa, tashi tayi daga karshe ta fice daga parlon kamar xata tashi sama, Khalil na fita ya koma bangaren Maminsa, Mami na tsaye tana kallon Nihad dake sa mayafin Mimi da ta amso mata, Mami ta fesa mata turaren hannunta tana kallonta tace “Baki taho da dankunne ba?” Nihad ta girgiza mata kai kawai, Gaba daya in ka kalleta sai ta baka tausayi, duk ta fita hayyacinta, Khalil dake tsaye bakin kofa kallon Mami kawai yake ya ma rasa abinda xai ce mata, lokaci daya jikinsa yayi sanyi don bai san what she is up to ba, Mami ta dauko ma Nihad wani dankunnen gwal mara nauyi ta mika mata tace “Sa wannan” Nihad ta kai hannu a hankali ta amsa tace “Nagode” sannan ta saka dankunnen, Mami ta dau nata mayafin ta yafa a shoulder tana kallon Nihad tace “Mu je” Nihad ta nufi kofar ta bi gefen Khalil ta fita, Mami na isa bakin kofar ya matsa a hankali ya bata hanya, makullin motarta ta mika masa tace “Mu je” Yayi karfin halin cewa “Where Mami?” Mami tace “Amshi makullin a hannuna ko?” A hankali ya kai hannu ya amsa, Mami ta fita Nihad na biye da ita. Har suka fito compound din gidan babu wanda suka hadu da a hanya kamar dai babu kowa gidan, Nihad ta dinga bin compound din da kallo, it’s soo beautiful and big, Khalil ya nufi Ride din Maminsa yana tafiya a hankali, gaba daya ya rasa tunanin da xai yi, Mami ta dinga amsan gaisuwan da securities din cikin gidan ke mata, Nihad dai sai binta take tana satan kallonsu, back seat Mami ta bude tana kallon Nihad tace “Shiga” Nihad ta shiga motar a hankali, Mami ma ta shiga sannan ta kulle motar, bayan few minutes Khalil ya ja motar ya fita compound din bayan an bude masa wagegen gate din gidan, slowly khalil ke driving din har suka fita anguwan, sai a sannan yana kallon Maminsa ta madubi cikin sanyin murya yace “Where are we going Mami?” Mami tace “Take me to Maryam’s house” Ya d’an sauke boyayyen ajiyar zuciya sannan ya nufi gidan Aunt dinsa, Nihad sai kallon anguwanni masu kyau take, amma kana mata kallo daya zaka san she is worried, suna shiga estate din su Aunty Maryam basu dade suna tafiya ba suka isa gidan, Khalil yayi horn bayan an bude gate din ya shiga yayi parking, Mami ta sauka tana kallon Nihad tace “Sauko” Nihad ta sauko, ta bi bayan Mami zuwa gidan, Aunty Maryam ta rungume Khalil tana welcoming dinsa cike da farin ciki tace “Idon son dina kenan nake gani haka?? Alhamdulillah ya Allah, Alhamdulillah” Murmushi kawai yayi ya gaisheta, ta amsa tana kallonsa daga sama har kasa, Lokaci daya er fara’ar fuskarta ya bace tace “Welcome son, Allah Ubangiji ya saka maka abinda aka maka” Murmushi kawai shi dai yake, Aunty Maryam na rike da hannunsa ta nufi parlor tana gaida Mami da ladabi, murmushi dauke fuskarta tace “Har kinyi Kumari yar uwa, Allah Ubangiji ya raba mu da mugun ji da mugun ganin” Murmushi kawai Mami tayi, Nihad dai sai kallon Aunty Maryam take don ita ma kana kallonta kasan halfcast ce, fara ce kal kamar Mamin khalil, sannan ita ma ga gashinta da tayi packing har kusan gadon baya, Aunty Maryam ta kalli Nihad don sai sannan ta lura da ita tace “Sannu da zuwa yan mata, shigo ki zauna” Nihad ta sauke kanta ta zauna kasa a hankali ta gaisheta, Aunty Maryam ta amsa tana Zaunawa gefen yayarta, tuni mai aikin Aunty Maryam ta cika gabansu da ruwa da lemo da kayan maqulashe, Aunty Maryam ta kasa daina kallon Khalil tana murmushi, she is so happy seeing him, can dai ta kalli Mami tace “Ya gida Aunty?” Mami tace “Alhamdulillah, kira mai aikinki ta shiga da bakuwar nan ciki ta bata breakfast naga bata wani yi a can gida ba” Aunty Maryam ta kalli Nihad tace “Ayya, to bari in kirata ta zo” Aunty Maryam ta kira mai aikinta a waya sai gata ta taho tace “Gani Hajiya” Aunty Maryam tace “Ki shiga da bakuwar nan guess room ki hada mata breakfast yanzu” Yarinyar tace “Toh Hajiya” Aunty Maryam ta kalli Nihad tace “Tashi ku je yan mata” Nihad ta mike a hankali ta bi bayan mai aikin da tayi wani bangaren daban da ita. Mami na kallon Khalil tace “Ko da za ayi sati admission letter din bai fito ba xata zauna nan har ta karba sannan ta koma gidansu” Khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, Aunty Maryam tace “Who is she Aunty?” Mami tace “Tare ya zo da ita” Aunty Maryam ta kallesa tace “Wacece ita din” yayi kasa da murya yace “Yarinyar mai gidan da na zauna a kano” Aunty Maryam tace “Allah sarki, Admission take nema nan din?” Ya gyada kai kawai, Aunty Maryam tace “Lallai ya yarda da kai tunda har ya bar ka da yar sa har ku ka taho tare, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi” Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace “Ameen” Mami ta kalli Aunty Maryam tace “Yaushe tafiyar naku, naji shiru baki ce komai ba” Tace “Ohh wllh yace sai yayi settling a can kafin mu bi sa, may be nan da sati biyu in sha Allah” Mami tace “Toh Allah ya kai mu” Aunty Maryam tace “Ameen” Khalil yayi kasa da murya cike da karfin yace “Mami about that video…. yan dakinsu ne a makaranta suka mata bata sani ba, sannan suka saki a social media… the Case is silently in court now, mahaifin nata yayi sueing dinsu gaba daya, so that’s why zai canza mata makaranta yanzu, since the incident yake processing admission dinta a nan garin so coincidentally xan taho sai yace mu taho tare da ita” shiru yayi cause he him self knows he sounds so stupid, there is nothing making sense in what he is saying, Mami tace “Toh ni ka ji nace wani abu Khalil? Allah dai ya tsare mana zuri’a gaba daya, kawai ta zauna nan har sanda xa ta amshi abinda ta zo amsa sai ta koma gida, ae shikenan ko….” Aunty Maryam dake ta kallonsu tace “Wai me ke faruwa?” Mami ta sauke ajiyar zuciya briefly tayi mata bayanin abinda ya faru daxu da safe da yara suka shigo, Aunty Maryam ta saki baki da mamaki looking speechless, can ta kalli Khalil tayi kasa da murya tace “Wai kana nufin wancan ita ce yarinyar da video dinta yayi trending weeks ago?” Khalil bai iya yace komai ba, Aunty Maryam ta girgiza kai hankali tashe tace “Amma ta bata wayonta, tayi tarnishing image dinta a idon duniya, ta kuma yi ma kanta ta6on da goguwansa sae wani ikon Allah, duk yanda aka yi bata ji, banda bata ji meye zaki zauna daga ke sai skimpy inner wears a daki har maki video kina dariya, kai ai abun nan bai min dadi ba wallahi, Allah Ubangiji ya tsare mana zuri’a, amma wannan ta6on ai baxai gogu ba har tsawon rayuwarta sai ma ta tashi aure zata gane hakan barin idan tana da mahassada” Kallonta kawai Khalil yake baya cewa komai, Aunty Maryam ta rike ha6a cike da jimami tace “Kaii, sai kawai naji bata burgeni ba don bana son yaro mara kamun kai, don da tana da kamun kai da babu yanda xa ayi tayi abinda tayi, babu yanda xa ayi hakan ya faru da ita, wallahi ranan da naga videon ta sai da nayi tashin dare nayi addu’a Allah ya kare mana xuri’a da al’ummar Musulmi baki daya, abun sam babu dadi, gashi babu inda wannan videon bai je ba, kuma kun ga wllh ban ganeta ba ni banda kun yi magana, to ma banda abun uban nata ai aurar da ita kawai ya kamata yayi a yanzu ba wai ya sake biya mata makaranta a wani wajen ba, tana kanon ma a gabansu tana shakiyanci ina ga ta hadu da yan matan garin nan ai kuma sai abinda hali yayi, gata wata sumu sumu kamar bata magana… To kai garin yaya kasan mahaifin nata?” Khalil ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa take, Aunty Maryam tace “Kayi shiru” Ya dago ya kalleta a hankali yace “A sanda na sauka a kano bani da kowa bawan Allahn ya rike ni tamkar dan sa, yayi accomodating dina, yayi feeding dina without knowing who i am, mahaifiyarta mace ce mai kirki warce saboda ita nayi dadewar da nayi a tare da su, ina jin ta kamar ke da Mamina a gidan, yayyinta maza kuwa zaman mutunci da girmama juna muka yi da  su, basu ta6a nuna min ni ba dan gidan bane, haka sauran yan uwanta mata dake gidan, abinda nake so ku gane, ba wai na je masu da real identity dina bane, i went der as a nobody, babu wanda yasan wanene ni har yanzu da nake maku magana banda ita yarinyar yanzu, amma suka min karamci a irin wannan zamanin da muke ciki, i know i can never repay them their good deeds, kuma yace in taho tare da yarinyarsa ta amshi admission letter saboda wani mistake nata sai in ki?” Aunty Maryam ta sauke ajiyar xuciya tace “Baxa ka ki ba kam, amma surutun yan gidan nan naku ake gudu” Mami ta kalli Aunty Maryam tace “That is it dear, abinda na guda kenan na kawota nan gidan har ta gama abinda ya kawota ta koma, banda mu da muka san wannan labarin da ka fada a kan gidansu yarinyar waye ya sani? Nobody, kai ko sun ji cewa xa su yi karya kake, don haka duk abun magana gudunsa nake nan da ka gan ni, daxun ma da suka shigo ba saboda Allah bane, gulma ce ta kawosu, yarinyar kawai suka zo gani, ita kuma wannan yarinya ta bata wayonta don waje daddaya ne xata je aki ganeta, Allah dai ya kiyaye ya tsare mana zuri’a, ya bata mijin da xai aureta yayi overlooking mistakes dinta ya rufa mata asiri duniya da lahira, da da mijin ma da auren kawai yayi mata ta ci gaba da karatun nata a dakin mijinta don hakan zai fi mutunci, Allah dai ya takaita mata gori a duk inda xata kasance” Khalil dai kallonsu kawai yake, Aunty Maryam tace “Ameen, da ganin wannan lamari kasan influence na bad friends ne hade da rawan kai irin na yaran yau, saboda haka ne ya kamata mu kara sa ma yaranmu ido sosai” Wayar Mami ya fara ring ta daga ta kai kunne, bayan sun gaisa tace “Lahh ai gani a gidan Maryam, kin fito ne?” Mami tace “Yauwa to, kawai ki taho nan din idan kin fito, shima yana nan ai” Daga haka ta katse wayar, Aunty Maryam na kallonta tace “Wacece?” Mami tace “Hajiya Safeenah ce” Aunty Maryam tace “Allah sarki, taji sauki kenan” Mami tace “Aa da sauki sosai, 3 days ago ma ai taje can gida wajena” Aunty Maryam ta mike tace “Bari inje in sanar ma mai aikin can tayi mata wani abun kafin ta iso” Daga haka ta bar parlon, Mami na kallon Khalil tace “Wai fasa tafiyar kayi yau Khalil?” khalil na danna wayarsa yace “Sai na shirya Mami” Aunty Maryam ta ɗan tsaya kitchen din tayi assisting mai aikinta bayan da ta gama hada komai ta bar mata ta fito parlor, duk bata tarar da su a parlon ba, har zata wuce sama sai kuma tayi bangaren guess ta kara ganin Nihad, don kawai abun ya tsaya mata a rai tun daxu, bude kofar dakin tayi ta shiga ta ganta zaune kasa ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam na kallon abincin dake ajiye tace “Baki yi breakfast din ba?” A hankali Nihad tace “Na koshi” Aunty Maryam tace “Toh fito parlor kiyi kallo, yara sun jogane kayan kallon nan din sai an gyara” Nihad dai bata ce komai ba ganin Aunty Maryam ta juya ta mike a hankali ta bi bayanta, har suka fito parlor tare, nan din ma a kasa ta zauna, Aunty Maryam ta tafi ta kulle kofa sannan ta wuce sama wajen Mami, Khalil na kwance saman kujera Mami na basa labarin abubuwan da suka faru baya nan, Aunty Maryam ta zauna kenan aka kira Mami, Mami ta daga tace “Kin iso ne?” Sai kuma Mami tace “To bari a bude” Katse wayar tayi tace “Kin kulle kofar parlon ne Maryam?” Aunty Maryam ta kalli Khalil da sauri tace “Dr ka bude mata kofa, yanzu kuma na kulle kafin in hauro” Ya mike ya fita daga parlon ya sauka downstairs, Nihad na zaune ta k’ura ma Tv ido duk da ba fahimtar abinda ake yi a ciki take ba, kallo daya yayi mata ya nufi kofar parlon ya bude, Da ladabi ya gaisheta yayi mata sannu da zuwa, da fara’a tace “Maa sha Allah, ka dawo lafiya Khalil?” Yace “Alhmdlh mum” Tace “Toh Alhamdulillah, sannu, Allah Ubangiji yayi maka albarka” Yana murmushi yace “Ameen” Sannan ya koma gefe ta shigo parlon, ya juya ya nufi inda remote yake ya dauka don rage volume din Tvn, a hankali Nihad ta gaisheta ta amsa da fara’a, Khalil Yace “Suna sama Mumy” Upstairs ta nufa, Kamar ance ya juya ya ganta ta jingina da kofar parlon tana kallonsa tana murmushinta me kyau, wara ido yayi kafin yace komai ta taho da sauri ta rungumesa ta lumshe ido a hankali tace “I have missed you so much” Daga kai Nihad tayi ta kalleta, shi kam yayi stiff a wajen da yake duk ya daburce cause she took him unaware, Lokaci daya ta lura da Nihad dake wajen da sauri ta sakesa ta koma baya tana mata murmushi tace “Sannu, sorry i just badged in, Assalamu alaikum” Nihad dake kallonta daga sama har kasa ta dauke kai kawai, Khalil ya bude palm dinsa with surprise yace “But you didn’t say u are coming with Mum” Ta langwabar da kai smiling at him tace “Surprise” Kallonta kawai yake, a hankali hawaye na taruwa idonta tace “I missed u so much…” Ya mata wani kallo yace “Come off it dear” Lokaci daya Nihad ta mike ta fice daga parlon zuwa guess room da take ciki daxu, Nadeeyah ta bi ta da kallo, sai kuma ta kallesa tace “Dear Wacece ita? Ko dai taji haushin yanda na shigo ko? Wallahi i was just overwhelmed” Khalil ya daga kafada yace “No, kece dai kika ga haka….” Tace “Ohk, tayi hakuri in ma taji haushina ne, where is Mami?” Ya nuna mata sama tace “Let me go and greet her” yace “Ohk dear” Tana barin wajen ya bi ta da kallo har ta haura sama…

39

Bayan Azahar Aunty Maryam ta sakko downstairs tana kallon mai aikinta dake parlor tace “Kin kai ma bakuwar can abinci kuwa?” Mai aikin ta tashi da sauri tace “Wallahi na manta Hajiya” Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta tace “Amma ai baki mance naki cikin ba” Da sauri mai aikin tayi hanyar kitchen, Aunty Maryam ta nufi guess room, bude kofar dakin tayi taga Nihad zaune saman darduma, Aunty Maryam ta shiga dakin, Nihad ta daga kai tana kallonta, Aunty Maryam tace “Kiyi hakuri ashe wancan gantalalliyar bata kawo maki abinci ba ni ina can sama ban sani ba” Nihad dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Aunty Maryam tace “Me yasa kika ki zama parlon kiyi kallo?” A hankali Nihad tace “Ba komai” Aunty Maryam bata kuma cewa komai ba, Sai ga Murja ta shigo da abinci dakin ta ajiye ma Nihad, Aunty Maryam na kallonta tace “Ki karo lemun” Da sauri Nihad tace “Aa ya isa Aunty” Aunty Maryam tace “Toh zuba abincin ki ci” Daga haka ta juya ta fita daga dakin, All through Khalil na compound wajen shan iska tare da Nadeeyah, kana ganinsu kasan they really missed each other, abincin ma waje aka kai masu suka ci tare, bayan Nadeeyah ta zuba masa drink din kwalin gabansa yana kallonta yace “Thank you” Tayi murmushi tace “Continue… ina jin ka” Ya ɗan buda ido yace “Me xan ce kuma,?” Tace “Ba labarin stay dinka a kano kake bani ba, ai baka gama ba” Yayi murmushi yana shafa kansa yace “Shikenan, all the household are very nyc, i think that’s the most important of all” Tace “To ita wannan yarinyar da na ganku tare, yar gidan ce?” Yayi shiru, sai kuma yace “Nihal!! Of course yarinyar mai gidan ce…” Nadeeyah tace “Allah sarki, wani school take?” Yace “Ahmadu Bello” Nadeeyah tace “Ohk, but kasan har yau yan gidanku basu san inda kake ba all those while, a lot of time Farhana da Sajida suna yawan tambayata about u, irin dai suna son su san ko i know about your whereabout” Yayi murmushi bai ce komai ba, tayi sipping drink din gabanta tace “Kasan everything happens for a reason, may be don kaje ku hadu da yan gidan ku kulla zumunci shi sa Allah ya kaddara zaka je kano har kuma ka je gidansu, kaga ai baxa ka manta halaccinsu ba” Ya gyada kai yace “Haka ne” Tace “And you mean har yanzu basu san kai waye ba har bayan da ka dawo Abuja?” Ya girgiza kai yace “Basu sani ba” Tayi murmushi tace “Za su yi mamaki kuwa idan suka san kai wanene, but menene ya ja ra’ayinka har ka je gidan nasu ka zauna bayan baka ta6a saninsu ba sannan ba rasa wajen da zaka zauna a kano kayi ba, infact ko hayar nawa ne nasan xaka iya affording, u can even decide to stay in the hotel don duk da ba salary kake samu ba sannan babu wani source of income don duk Abba ya toshe hanyar but still nasan u neva ran out of cash all that period, Mami na tura maka, Aunty Maryam, Aunty Hamida even though bata kasar….” Murmushi yayi yana kallonta murya can kasa yace “And even you yourself” Ta hararesa tace “A’a ni ka cireni a lissafi don anything mine is urs” Ta tallabi chin dinta ta ci gaba tace “So how did u even know about them? And me yasa kayi deciding zaman gidan?” Yayi shiru yana kallonta kamar baxai ce komai, can kuma yace “I will tell u some other time Nadeeyah” Tace “Why?” Yace “I don’t want to talk about it now” Ta langwabar da kai a hankali tace “Amma ka ta6a saninsu ne?” Ya girgiza kai yace “Nace xan baki labarin some other time” Tace “Ohk, but ya kamata ko Mami ka hada da yan gidan su gaisa a waya, su ma za su san kayi appreciating dinsu” Yace “I will do that dear” a hankali tace “But why did u keep on telling me kana USA?” Yace “Saboda nasan xa ki iya cewa xaki zo kano saboda ni, shi yasa ma ranan da muka hadu nace maki in few hours time flight dina xai tashi, don kar ki saka ran za mu hadu” Murmushi kawai Nadeeyah tayi tana kallonsa… sai kusan la’asar suka shiga cikin gida, Nadeeyah ta haura sama shi kuma ya zauna parlor, ko minti biyar bai yi zaune parlon ba Nihad ta fito rike da warmers na abinci da mai aikin Aunty Maryam ta kai mata, tun da suka hada ido sau daya bata sake kallon direction dinsa ba, sai dai kuma bata san hanyar kitchen ba don tayi zaton zata hadu da mai aikin ne a parlor, juyawa tayi ta koma inda ta fito, sai ga Mami ta sauko downstairs tare da Mum din Nadeeyah da Aunty Maryam, Mami tace “Khalil xaka ajiyesu gida daga can mu tafi gida, xata kira driver nace ba sai ta kirasa ba mu ma yanzu za mu tafi gwara mu tafi gaba daya” Khalil ya mike yace “Ohk” Mami ta nufi Aunty Maryam dake answering call tayi kasa da murya tace “Kai ni mu yi sallama da ita, ina ga ai daga nan zata wuce in ta amshi abinda xata amsa” Aunty Maryam ta nufi bangaren da Nihad take Mami na biye da ita a baya, Aunty Maryam ta bude kofar, kwance suka ganta a kasa, Aunty Maryam ta katse wayar da take tace “Me yasa xaki kwanta a kasa ga gado?” Nihad ta mike zaune bata ce komai ba, Mami tace “Naga bata da sabo ne da wuri” Mami na Murmushi tace “Ya sunanki?” Nihad bata iya ta dago kanta ba a hankali tace “Fatima amma ana kirana Nihad”  Aunty Maryam ta kalli Mami, Mami tace “To maa sha Allah Nihad, yaushe xa a baki admission letter din?” Sai a sannan Nihad ta daga kai tana kallon Mami, Mami tace “Yaushe suka ce?” Cikin sanyin murya tace “Nima ban sani ba” Mami tace “Toh jiya me suka ce maki a makarantar” Ta sauke idonta kasa tace “Shi ne dai suka gaya ma ba ni ba” Mami ta kalli Aunty Maryam, Sai kuma tace “Toh, ya dai ce kafin sati za ki samu, idan na zo nan din kafin ki tafi to, idan kuma ban zo ba xan bada sako a kawo maki kin ji? Sannan ki gaida su mamanki da kyau” Nihad ta gyada mata kai kawai, Mami tace “Toh sai anjima” Cikin sanyin murya Nihad tace “Nagode” Tana fadin haka ta fara cire dankunnen dake kunnenta tace “Ga dankunnen” Mami tace “Aa, na baki ne ki dinga sa wa Nihad” Nihad ta mayar tace “Toh Nagode, Allah ya saka da Alkhairi” Mami na Murmushi tace “Ameen” Daga haka tace “Mun tafi” Ta juya ta fita dakin, Aunty Maryam ta bi bayanta ta kullo kofar dakin. Khalil kadai ke jiransu a parlon, Nadeeyah da Mum dinta kuwa sun fita compound, Mami na kallon Khalil tace “Ina suke?” Yace “They are outside” tace “Toh mu je” Ya kalli Aunty Maryam yace “Na sa wayata caji idan na ajiyesu xan dawo in dauka anjima Aunty” Mami tace “Ji wani wahalar da kai, ka dau wayar mana idan mun je gida ka sa a cajin” Aunty Maryam tayi dariya tace “Baki ga yanda na saki baki ina kallonsa ba” Ya ɗan yi murmushi yana sosa kai yace “Haka ne” Gun wayar ya nufa, Mami ta juya ta fita daga parlon, ya juya ya kalli Aunty Maryam yace “Kawai bari in bar shi Aunty, ai bamu gama hiran ba dama” Aunty Maryam tace “Toh je ka ajiyesu ka dawo, akwai abinda kake so ayi maka kafin ka dawo” Yace “Aa coffee kawai xan sha idan na dawo” Tace “Toh sai ka dawo son” Daga haka ya fita parlon da sauri zuwa parking space. Wajen karfe biyar da wani abu Nihad ta fito parlor, Aunty Maryam dake zaune parlon tana rungume da autanta Mus’ab ya dawo makaranta ta kalli Nihad tace “Kin fito” Nihad na wasa da fingers dinta tace “Eh, akwai aikin da xa ayi Aunty?” Aunty Maryam tayi murmushi tace “Aa Nihad, Murja ta ma kusa gama girkin ina ji yanzu, karaso ki zauna” Nihad ta karaso cikin parlon ta zauna a kasa, Aunty Maryam tace “Hau saman kujera mana” Nihad ta girgiza kai tace “Aa nan ya isa” Mus’ab dake kallonta yace “Ummi is she our visitor?” Aunty Maryam tace “Yes dear, sauka kasa ka gaisheta” Ya sauka daga jikin mamarsa yace “Good evening” Nihad na kallonsa tayi murmushi don mate din Fadil dinsu ne tace “How are you?” Ya koma jikin mamarsa yace “Fine” Har Bayan magrib Nihad na parlon tare da Aunty Maryam, aka bude kofa Khalil ya shigo da sallama, Aunty Maryam ta amsa masa tana kallonsa tace “Sai yanzu?” Ya karaso cikin parlon ya ajiye jakar hannunsa yace “Eh Aunty, good evening” Tace “Evening welcome, wannan jakar fa? Ko na ta ne?” Ya nufi wayarsa yace “Eh nata ne” Ya dauko wayar ya dawo ya zauna, Aunty Maryam na kallon Nihad tace “Dauka ki kai can dakin” Tashi Nihad tayi ba tare da ta kalli inda yake ba ta dau jakar ta wuce ciki, Aunty Maryam tana kallonsa tace “A kawo maka abincin ko coffeen dai” Yace “Na sha a gida Aunty” Tace “Ohk, Mami tace xaka yi tafiya, yaushe ne tafiyar?” Ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Nan dai da kwana biyu idan na gama shirye shirye” Tace “Toh Allah ya kai mu” Wayarsa yake dubawa ya ga missed calls din Farooq, ko jiya ya kirasa, Khalil yayi dialing numbersa ya kai kunne, Farooq na dagawa suka gaisa, Farooq yace “Har yanzu baka turo ba Khalil” Khalil ya shafa kansa yace “Nace kar ka damu Yallabai, da da bukatar hakan xan tura maka” Farooq yace “Ehh naji, amma kawai ka turo min” Murmushi Khalil yayi yace “Toh shkkn, Mun gode Allah ya saka da alkhairi” Farooq yace “Fatan dai kuna lafiya?” Khalil yace “Alhmdlh” Farooq yace “Zariyan a wani anguwa ku ke, ina ga in shigo ko jibi weekend” Khalil yace “Ohk zan tambaya” Khalil yace “Ohk, tana kusa?” Khalil yace “Bari in bata” Mikewa yayi yana kallon Aunty Maryam dake ta kallonsa ya mata alamar yana zuwa sannan ya tafi inda Nihad take, saman gado ya sameta kwance, ya karasa ya mika mata wayar, ta mike zaune tana kallon Iphone da yake mika mata, ta kai hannu ta amsa tana kallon screen din taga number ya farooq don a haddace yake a kanta, ta kai kunne cikin sanyin murya tace “Ya farooq” Daga daya bangaren yace “Na’am Lil sis ya kike” Lkci daya har hawaye ya kawo idonta tana goge idonta cikin rawar murya tace “Lafiya lau” Yayi shiru, sai kuma yayi kasa da murya yace “Yanzu kukan me kike? Ko akwai damuwa ne?” Ta kasa ce masa komai, yace “Nihad” Tana goge idonta tace “Na’am” Shi dai khalil na tsaye yana kallonta, Ya Farooq yace “Bana son wannan kukan naki Nihad, shi yasa ko na kirasa bana cewa ya baki, kukan nan yana damuna idan kina yi” A hankali tace “Toh na daina yaya” Yace “Good girl, kiyi hakuri in sha Allah komai xai wuce, komai yayi farko xai yi karshe in sha Allah, don haka ke dai ki zama me biyayya ku zauna lafiya da mijinki, sannan ki rike Ibada sosai, may Allah guide and protect you for us” Cikin sanyin murya Nihad tace “Ameen yaya” Yace “Har yanzu baki da atm card ko?” Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, yace “Hello” Tace “Ehh bani da shi” Yace “Toh shikenan, in sha Allah on Saturday xan zo, na gaya masa ma” Nihad tace “Ina zaka zo yaya?” Yace “Wajenku idan Allah ya kai mu, be a good girl always, Allah ya maki albarka” Tace “Ameen yaya” yace “Give him the phone” Mika masa wayar tayi ba tare da ta bari sun hada ido ba, shi dai kallonta kawai yake, bai kuma amshi wayar ba, ita kuma taki yarda ta kallesa, ganin still ya ki amsar wayar ta ajiye masa nan gefen gado ta koma tayi kwanciyarta ta juya masa baya, ya shafa beard dinsa, sai kuma ya dauki wayar ya juya ya fita ya kulle mata kofa. Wajen karfe tara da rabi Aunty Maryam ta bude kofar dakin da Nihad ke ciki, zaune ta sameta saman darduma ta jinginar da kanta da gado, Aunty Maryam tace “Sai yanzu kika yi isha’in? Nihad ta girgiza kai tace “Aa tun daxu nayi” Aunty Maryam tace “Toh baxa ki kara abinci ba ko?” Nihad ta gyada mata kai tace “Ehh Aunty nagode” Aunty Maryam tace “Toh shkkn, tunda ga kayanki ya kawo ki yi wanka sai ki kwanta, ga zani kiyi amfani da shi don towel din bandakin ba a wanke yake ba” Nihad ta nufeta ta amshi zanin da take mika mata tace “Nagode” Aunty Maryam tace “Ni xan tafi daki, Allah ya tashe mu lafiya” Nihad tace “Toh sai da safe” Juyawa Aunty Maryam tayi ta rufo mata kofar ta bar wajen, Nihad ta koma gefen gadon ta ajiye zanin, sannan ta cire Hijab din da tayi sallah ta linke ta ajiye don a dakin ta gani. Ta kalli jakar da ta shigo da shi daxu dakin, can ta nufi gun jakar ta durkusa ta bude zip din a hankali tana kallon ciki, Hijab da aka yi packaging a leda ta ciro har guda hudu, sai kuma Abaya kala biyar da undies masu yawa, sai kayan shafe shafe with perfumes kala biyar, da nighties su ma biyar, kulle jakar tayi ta mike ta bar wajen. Duk da Nihad felt secured a gidan Aunty Maryam amma wannan daren ma ta nemi bacci ta rasa, for almost 4 days now bata bacci da daddare ko tayi a firgice zata farka bayan wasu mintuna, or is she been traumatic, bata taɓa jin tana kewar Mahaifiyarta yanda take ji yanzu ba, maganganunta na karshe ya kasa fita daga ranta da zuciyarta, she could vividly remember every single word shi told her a rananta na karshe a gidansu, and she wish she could hear more of such from her, Magana da tayi da Ya farooq daxu shi ma yayi contributing a rest of mind dinta but she still couldn’t sleep, gaba daya idanuwanta sun kekyashe daga jin bacci, daga karshe ta tashi a hankali ta kumna switch din dakin ta ga karfe biyun dare, cike da karfin hali ta nufi bandaki tana jan kafa, har kusan karfe uku da rabi Nihad bata yi bacci ba tayi sallan har taji bata da sauran strength kawai ta jinginar da kanta da gado tana daga zaune kan darduman, sai a sannan taji hawaye na sauka idonta, cikin rawar murya tace “Ya Allah duk wanda yayi min wannan abun ka tona asirinsa cikin gaggawa, come to my aid ya Allah, Allah ka kawo min mafita alfarman ma’aiki” Kuka take sosai tana roƙon Allah, wanda tun faruwan abun yau ne ta kwantar da hankali take kai kukanta wajen Allah cikin nutsuwa, ko jin sanda aka bude kofar dakin bata yi, cause she is really hurt, sae yanxu take ganin she needs to know who is this that betrayed her, she needs to know who did this to her da ya tarwatse farin cikinta ya rabata da Abbanta ya bata mata suna yayi tarnishing image dinta a idon duniya, Aunty Maryam dai sai kallonta take tana tsaye bakin kofa, dama ka’idarta ce duk in Allah ya farkar da ita cikin dare ko dab da asuba ko da baxata yi sallah ba sai ta fito ta dudduba condition din yaranta idan suna gidan, har dakin mai aikinta takan bude ta dubata, in ma da wani bako gidan in dai ba babba bane xata bude dakin ta duba, sai in Allah bai farkar da ita ba wanda hakan ma ya zame mata jiki dole ko yaya sai ta tashi saboda ta maida shi daily routine dinta a gidan…. (Yana da kyau iyaye mata su sa ido su yi kokarin dinga yin hakan ko da ba kullum ba barin idan kana da yara yan mata teenagers, kai har ma da yara mazan, its very very important, i have this aunty that kullum da daddare sai ta leko ku taga halin da ku ke ciki a daki, ya ma riga ya zame mata jiki, da Mumyn Nihad na kokarin yi ma Nihad haka ko da ba a bangarenta take ba da abubuwa da yawa basu faru ba kamar zuwa night parties da take, wasu yan matan sai su kai har karfe daya ana video call da saurayi kasa kasa, ko chatting din banza, wasu kuma a wannan lokacin xa su samu daman shiga internet su yi kallace kallacen banxa, wasu masturbation da dai sauransu, duk kina can kin shanya baki hangangan kina bacci, Allah Ubangiji ya kare mana zuri’a ya raba mu da mugun ji da mugun gani) Duk abubuwan da Nihad ke fada Aunty Maryam na jin ta don daga karshe ma kulle kofar dakin tayi a hankali, wanda hakan ne yayi distracting Nihad ta juya da sauri, sai da gabanta ya fadi ganinta tsaye bakin kofar, ta hau goge idonta da sauri, Aunty Maryam ta karaso cikin dakin tana kallonta ta zauna gefen gado tayi kasa da murya tace “It’s okay dear, tunda ki ka kai kukanki wajen Allah kika hana kanki bacci a wannan lokacin, to in sha Allah addu’arki baxata tashi a banza ba, ta yanda baki yi zato ba Allah xai maki sakayya ya kuma tona asirin koma wanene yayi maki wannan abun” Hawaye ya dinga sauka idon Nihad ta kasa ce ma Aunty Maryam komai, Aunty Maryam da taji tausayinta ainun tace “Kiyi hakuri ki daina wannan kukan, tunda kika ambaci Allah ai an wuce wajen kuma, amma me yasa kika yarda da kawaye har zaki zauna cikinsu half naked?” Nihad ta girgiza kai cikin rawan murya tace “Wallahi Aunty ni ban taɓa zama ko a gidanmu haka ba, sannan ni ba a hostel nake ba kawai zuwa nake, lokacin da xa mu fara exams din first semester level 3 ne na koma hostel kuma ni ko da zani bana zama cikinsu wallahi” Aunty Maryam na kallonta da mamaki tace “Toh a ina aka dau video din?” Nihad ta buda hannu tace “Nima wallahi ban sani ba, yanda kowa ya gansa haka na gansa” Aunty Maryam ta dinga kallonta dumbfounded, can tace “Ban gane baki san a inda aka maki video din ba” Nihad ta fashe da kuka tace “Wallahi da gaske Aunty, ni ban san ta yaya aka yi hakan ba, kuma ban ma san ko wani waje ne ba” Aunty Maryam ta kasa cewa komai don mamaki, can dai tace “Toh kenan ba ke bace a video din” Nihad na goge idonta tace “Ni ce Aunty, amma ban san ta yaya ba, because under wears dina ne a jikina” Sosai wannan lamarin ya rikitar da Aunty Maryam, can dai ta sake cewa “Kuma ba a hostel din bane?” Nihad tace “Ba nan bane wllh” Aunty Maryam tace “Ba kuma gidanku bane?” Nihad ta girgiza kai tace “Ba gidanmu bane” Aunty Maryam tace “Ikon Allah, kin tabbata bayan gida baki zuwa wani wajen ko da kawaye haka?” Shiru Nihad tayi, Aunty Maryam tace “Kin yi shiru” Nihad ta hadiye abu da kyar amma tana tsoron ce ma Aunty Maryam ai sun kan je hotel da guess lodge da friends dinta, Aunty Maryam tace “Kina zuwa kenan?” Cikin sanyin murya tace “Ina bin kawayena duk inda xa su wani lokacin” Aunty Maryam tace “Toh su suka maki, ki gaya min tsakaninki da Allah baki shan komai?” Nihad ta dago da sauri tana kallon Aunty Maryam tace “Aunty kamar me” Aunty Maryam tace “Kayan maye, gaya min tsakaninki da Allah, kar ki min karya don kina min ma zan gwada ki kuma zan gane, don ni Nurse ce” Nihad na girgiza kai hawaye na sauka idonta tace “Wallahi Aunty bana shan komai kin ji har na rantse, idan ina shan wani abu Allah shine shaidata, ki gwada ki ga Aunty” Aunty Maryam tace “Toh kawayen naki fa?” Nan Nihad ta fara lissafo ma Aunty Maryam abubuwan da su Husnah suke sha Innocently, haka Aunty Maryam ta saki baki tana kallonta cause taga babu alamar karya a tare da ita, iya gaskiyarta kawai take fada, can Aunty Maryam tace “Ikon Allah, to kuma a gida an san kina bin wa ennan kawayen har ma ki bi su duk inda xa su?” Nihad ta girgiza kai tace “Stepmom dita ce kawai ta sani, ta ma san gaba dayansu” Buda baki Aunty Maryam tayi, sai kuma tace “Kuma bata hanaki alaqa da su ba?” Nihad tace “Aa, tace min in rikesu baxan samu kamarsu ba don suna sona sosai, kuma tana kare ni yanda yan sauran yan gidan baxa su gane ba, idan na dawo da daddare ita take bude min kofan parlon mu idan an kulle” Aunty Maryam was really shock jin abinda Nihad tace, taji zufa na keto mata, tace “Mamarki fa?” Nihad ta girgiza kai a hankali tace “Bata sani ba ai, dama a bangaren stepmom dina nake, so akwai distance tsakanin part din stepmom din tawa da na Mum dina….” Aunty Maryam tace “Wa ya ce ki koma part din stepmom din taki?” Nihad tace “Aa wai tun ina karama ta dawo da ni wajenta shi ne har na girma” Aunty Maryam tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, to ina jin ki, idan ta bude maki kofar da daddare sai tace maki me??” Nihad tace “Kawai cewa xata yi inyi sauri in wuce kar a gan ni” Aunty Maryam bata san sanda hawaye ya kawo idonta ba, nan ta kara tsorata da lamarin kishiya, bata san sanda ta dafe kanta da yayi mata nauyi ba, can ta dago da kyar tace “Bata da yara ne?” Nihad ta girgiza kai a hankali tace “Tana da yarinya mate dita, her name is Nihal, ita kuma tana side din Mumy na, sannan akwai Amina da Aunty Kamila that is married” Aunty Maryam tace “Kuma duk su ma yaran nata dake gidan suna fita su kai dare ta bude masu kofa?” Nihad ta girgiza kai da sauri tace “Aa babu inda suke zuwa su, ba ma su da friends” Aunty Maryam tace “Nihad” Nihad ta daga kai ta kalleta, Aunty Maryam tace “Ku nawa ne wajen mamanki?” Nihad tace “Mu uku ne, ni ce first born” Aunty Maryam was so heartbroken, tace “Ita kuma fa?” Nihad tace “Babban yayanmu ya Farooq sai ya Usman, sai Aunty Kamila, Nihal da Amina” Aunty Maryam na girgiza kai tace “Yanzu a tunaninki duk gidan wa yafi sonki? Yake maki duk abinda kike so?” Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace “Umma” Aunty Maryam tace “Wacece Umma?” Nihad tace “My Stepmom” cike da takaici Aunty Maryam na girgiza kai tace “Ta cuci rayuwarki, ta cuceki, ta cuci mahaifiyarki, ita kuma salon nata kishin kenan?? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, da wannan abun da ta maki da gwara ta fuskanci mahaifiyarki su xuba kishin yanda ya kamata, bata maki adalci ba, kuma ko tantama babu da sa hannun wannan matar a video din naki, Nihad wani masoyinka ne xai dinga supporting dinka kana bad things, kana abubuwan da basu dace ba? Wani masoyinka ne xai xuba maka ido ka fita ka kai har dare shi bai maka fada ba kuma ya kareka ta yanda wasu baxa su sani ba balle su maka fada? Wani masoyinka ne xai ce ka rike yan iska masu shaye shaye a matsayin kawaye har yana ikirarin baxa ka samu kamar su ba, sannan ya daure maka kugu ka dinga bin su duk inda xa su? Nihad me yasa ita nata yaran basu da kawaye sannan basa fitan dare?” Shiru Nihad tayi tana kallon Aunty Maryam ko kiftawa babu, Aunty Maryam tace “Ba shiru xa kiyi min ba bude baki ki bani amsa yanzun nan?” Tunda Nihad take bata ta6a zaunawa tayi wannan tunanin ba balle har ta gane komai tayi reasoning a kai, ita dai Aunty Jamila kawai rabata take da Umma ta karfi da yaji amma bata ta6a zaunawa ta zayyano mata abubuwan nan da Aunty Maryam ta zayyano mata ba yanzu, to ai bata ma san abinda take yi da sanin Umman ba balle har ta zayyano mata wannan abubuwan tunda komanta a boye take yi, Umma ce kawai ta sani… Aunty Maryam bata yi interrupting Nihad a duniyar tunanin da ta fada ba, kana kallon fuskarta zaka fahimci she is slowly trying to comprehend duk wani abinda Aunty Maryam ta fada ne, babu kuma abinda ya fado ran Nihad sai karyan da suka yi ma yan gida wai zata bi Aunty Kamila kebbi alhalin hostel xata koma da zama, Umma da Aunty Kamilar ne kadai suka san gaskiyar maganar, kuma har ta gama zamanta hostel din for more than 3 months Umma bata ta6a zuwa inda take ba, har ita Aunty Kamilan, alhalin idan mutum na hostel kuma iyayensa na garin ko bayan sati uku ne su kan kai masa ziyara.

40

Aunty Maryam ta kai hannunta saman shoulder din Nihad ta dafata a hankali tana kallonta don har sannan tunane tunane take with shock written all over her, da sauri Nihad ta daga kai ta kalleta, lkci daya hawaye ya cika idonta, ta hadiye abu da kyar, cike da karfin hali tana girgiza kai tace “Ni ba wanda ya taba gaya min abubuwan nan, ni ban sani ba, you are just telling me now” Aunty Maryam tace “And hope you’ve realized what i am saying?” Nihad ta gyada kai hawaye na sauka idonta, sai kuma ta fashe da kuka tana kallon Aunty Maryam tace “Ni ban san bata so na ba Aunty, Lokacin wani saurayina yace iyayensa xa su xo gidanmu shine na gaya mata sai tace min kar in gaya ma kowa har Mumyna, ita da kanta xata je ta gaya ma Abba, na gaya mata da few days aka saki Video dina a internet shine yayi blocking dina” Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonta and she was speechless, Nihad na kuka sosai don sai sannan abubuwan ke dawo mata, sai yanzu ƙwaƙwalwarta ya fahimci abubuwa da dama, Tana kuka sosai tace “Da Abbana ma ya koreni bata ce komai ba” Aunty Maryam ta dafata da sauri tana kallonta da mamaki tace “Ya koreki daga ina?” Cikin raunin murya Nihad tace “Gidanmu, yace baya son ya sake ganina har abada, she was standing at the door bata ce masa komai ba, and she saw me leaving the house” Sai ta kara fashe da kuka sosai, she is so pained, bata ta6a kallon Umma from this perspective ba, ga dai komai vividly a bayyane amma bata ta6a ganewa ba, Aunty Maryam tayi karfin halin cewa “Kina nufin he sent you away from his house?” Nihad ta gyada mata kai tana kuka, Aunty Maryam ta kasa rufe baki, can ta kalleta da kyau tace “Dalilin kawo ki garin nan da Khalil yayi kenan dama?” Sai a sannan Nihad tayi realizing she just said what she’s not suppose to say to her, ta dakatar da kukan da take da sauri ta hadiye abu da ya tokareta a throat, ta kalli Aunty Maryam, sai kuma ta fara kame kame “Aa Aunty kawai dama…. Dama, makaranta….” Aunty Maryam da tuni ta ganota tace “Kar ki min karya” Nihad ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali, Jikin Aunty Maryam yayi sanyi sosai, wato dalilin kawota Abuja da Khalil yayi kenan? But ai Mami tace mata Abba ne ya bukaci ya dawo kuma, she became so confuse at this point, Can ta kalli Nihad tace “Ya isa haka, ki daina wannan kukan, ki tafi bandaki ki wanke idonki ki kwanta kafin Asuba ya karasa” Nihad ta kasa ce mata komai, Aunty Maryam tace “Tashi” Tashi tayi da kyar tana jan kafa ta shiga bandakin ta wanke fuskarta ta fito, Aunty Maryam tace “Ki kwanta, kuma bana son ki sake wannan kukan kin ji me nace?” Nihad ta gyada mata kai ta kwanta saman gadon, Aunty Maryam ta mike ta fita daga dakin ta kullo mata kofar. Kwanciyar da Aunty Maryam bata sake yi ba kenan har gari ya waye, lamarin Nihad ya tsaya mata cak a zuciya, taji tausayinta da mahaifiyarta ainun, ta kuma ji mata takaicin wannan baƙin taɓon da aka mata da xai bibiyeta har karshen rayuwarta, this is soo painful, ta kuma tsine ma Umma ta la’anceta yafi a kirga, ta jima bata ji labarin irin wannan zaluncin da aka ma Nihad ba, ta kara tabbatar da cewa kishiya bala’i ce kuma masifa ce. ƙarfe takwas saura ta kira Khalil, yana bedroom dinsa kwance yayi nisa a tunanin da yake, he is so confused and looking for a way out a kan wannan lamarin, gaba daya kansa ya daure on what next to do, ko jiya da daddare sai da Mami ta sake masa magana yayi kokarin ganin Nihad ta amshi admission letter din nata ko gobe ne kar a shiga weekend, idan yaso idan ta amsa ko ranan sai ta bi jirgi ta koma gida, ita dai duk ta damu ace Nihad ta tafi gida, ga Abba a jiyan shi ma yayi masa maganan business din da zai yi a zanzibar, which he will be leaving Nigeria in 2 days time, that is on Sunday, kiran Aunty Maryam ya kara rikita masa lissafi ya mike zaune da sauri yana kallon wayar, Allah ya sa ba wani maganan Nihad tayi mata ba dai, sai da wayar ya kusa katsewa ya daga ya kai kunne, yayi composing kansa yace “Ina kwana Aunty?” Tace “Lafiya lau, idan baka komai ka taho yanzu ina jiranka” Nan yaji gabansa ya fadi sosai, Ya dake yace “Hope all is well Aunty?” Tace “Nace dai ina jiranka” Yayi gathering courage yace “Toh” Daga haka ta katse wayar, duk da sanyin Ac dake dakin ji yayi zufa na keto masa ta ko ina, he just can’t Imagine ace Nihad tace mata ai an daura mata aure da shi, yayi saurin kawar da tunanin don bai ma son yayi, ya sauka daga saman gadon da kyar ya shiga bandaki yayi wanka ya fito, cikin few minutes ya gama shiryawa ya dau perfumes dinsa ya fesa sannan ya dau makullin motar Mami dake wajensa ya fita, ko part dinta bai tafi ba ya fita zuwa compound, har Khalil ya isa gidan Small mum dinsa ba shi da nutsuwa babu tunanin da bai zo ransa ba, tunda ya san ba wani saiti gare Nihad ba nan da nan zaka bugi cikinta ta bude maka komai, yana parking compound din Aunty Maryam ya kashe motar ya sauka sannan ya nufi parlonta, xuciyarsa na bugawa ya kwankwasa kofar parlon, mai aikin ta bude, ta gaishesa ko amsawa bai yi ba ya karasa ciki ya zauna ya jinginar da kansa da kujera, sai ga kiran Aunty Maryam a wayarsa ya daga ya kai kunne tace masa ya hauro sama, ya mike yana kallon mai aikin yace “Ke ina bakuwar da take gidan nan?” Da ladabi mai aikin tace “Tana guess room” Direct can ya nufa da sauri maimakon sama da Aunty Maryam tace ya hau, ya bude kofar dakin ya shiga, tana zaune gefen gado daure da zanin da Aunty Maryam ta bata bayan ta fito wanka tana shafa mai, har sannan idanuwanta a kumbure suke don har gari ya waye bata rintsa ba, Umma tayi mugun tsaya mata a rai, bata ta6a viewing dinta from the this perspective ba sai yanxu with the help of Aunty Maryam, she wish ana iya maida hannun agogo baya, wani tsanar Umma kawai taji take ji a ranta idan ta tuna wasu abubuwan da ta sa ta dinga yi a boye, tunda Nihad ta juya da sauri bayan an bude kofa suka hada ido da Khalil ta dauke kai ta ci gaba da shafa man da take a hankali, ya nufota kirjinsa na heaving yace “Kee, me kika gaya ma Aunty Maryam?” Ta ɗan kallesa, sai kuma ta ci gaba da abinda take taki kulasa, jin bata ce komai ba ya hade rai yace “Magana nake maki” Tace “Toh ba ga ka a gidan ba kaje ka tambayeta mana” Sake baki yayi yana kallonta, ganin yanda ya tsaya mata a kai ta mike ta dau cream dinta xata bar wajen ya fixgota ta dawo dab da shi yana mata wani kallo, ta zaro ido tace “Ni wallahi ka kyaleni, ai ba ni kadai xaka tambaya ba ita ma sai ka je ka tambayeta” Khalil ya dinga kallonta sai kuma ya zaunar da ita gefen gadon strictly yace “Ina me tabbatar maki cewa in har kika gaya mata anything pertaining to relationship dina da ke, ko kuma dalilin da ya sa muka zo garin nan tare dake, i have no choice then to divorce you right in front of her, a nan take a gabanta xan sakeki” Nihad ta wani kyabe baki tace “Toh kayi ta saki na mana, dama ni ai ban san ina da wani aure a kaina ba, sannan Alhamdulillah tunda duk iskanci na ba a ta6a ganin ina rungume rungume ba, kawai dama in ka gama sakin nawa ka kai ni tasha ka saka ni a mota in tafi gun dangin mamata tunda ina da su kuma suna so na” Kallonta ya dinga yi babu ko kiftawa, kawai ji tayi magana da Aunty Maryam ya sa mata courage da tayi loosing few days ago, taji ta kara samun kwarin gwiwa sosai, because at least tayi magana da warce ta fahimceta ta yarda da ita, sannan warce ta ganar da ita abubuwan da duk bata sani ba bata kuma ta6a kawowa a kai ba a baya, Tashi tayi ta koma can daya bangaren gadon ta zauna tana shafa cream din a kafa, Wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya kalli screen din sai kuma ya nufi kofa ya fita daga dakin, direct sama ya haura yaga Aunty Maryam zaune parlornta, ta dinga kallonsa ya kasa barin su hada ido har ya karaso ya zauna, yace “Ina kwana Aunty?” Aunty Maryam na kallonsa a hankali tace “Lafiya lau” Sai a sannan yayi karfin halin daga kai ya kalleta, ta sauke wani boyayyen ajiyar xuciya tace “Ka gaya min gaskiya Khalil, dama saboda ka kawo Nihad garin nan ne ka dawo gida ko da gaske kiranka Abbanka yayi?” Khalil yayi karfin halin cewa “Aunty ai da Abba bai min izinin shiga gidansa ba kema kinsan babu ta yanda xan shiga, kawai coincidentally ne….” Sai kuma yayi shiru ya sauke kansa kasa don bai ma san me xai ce mata ba tunda bai san abubuwan da Nihad ta gaya mata ba, he don’t want to say something different, bayan few minutes yaji Aunty Maryam tace “Me ka fahimta game da kishiyar Mamarta tunda kace ka zauna a gidansu” Da sauri Khalil ya daga kai ya kalleta, sai kuma yayi kasa da murya yace “A wolf in sheep’s clothing, a green snake under the green grass….” Aunty Maryam ta girgiza kai cike da takaici tace “I was shock at Nihad’s story Khalil, nayi matuƙar girgiza da labarinta, kishiyar Mamarta bata mata adalci ba, ta cuceta ta gurbata mata rayuwa” Khalil ya lumshe ido ya bude bai dai ce komai ba, Aunty Maryam tace “Me yasa kace admission letter xata amsa a garin nan bayan ba haka bane?” Sai da khalil yayi stiff a inda yake zaune, Aunty Maryam tace “She told me her dad sent her away from his house” Sosai gaban khalil ya fadi jin abinda Aunty Maryam ta kara cewa, shikenan ya ma san ta riga tace an masa aure da ita tunda har ta iya buda baki tace an koreta a gida, jin tayi shiru Khalil yayi karfin halin cewa “Sai me kuma ta gaya maki Aunty?” Aunty Maryam tace “Iya abinda ta sanar min kenan, sai kuma wanda kai zaka kara min, sannan tace video dinta bata san garin yaya aka mata ba har ya fita…. Na kuma yarda da ita don babu alamar karya a duk zantuttukan ta” Khalil dai kallonta kawai yake, can ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya da ya fahimci iya abinda ta sanar ma Aunty Maryam kenan da gaske, yayi kasa da murya yace “Haka ne Aunty, but bansan ta ina xan fara gaya ma Mami all this ba, ni kuma mahaifinta yayi min halaccin da baxan iya kyaleta ta shiga duniya ba bayan ya koreta gidansa saboda offense din da ba yin kanta ba, her stepmom is behind all that happened to her amma bata sani ba ta kuma ki kwantar da hankalinta ta gano hakan, makira ce matar kuma azzaluma, ta lalata mata rayuwa ta dora ta a kan abubuwa da yawa da basu dace ba, wanda ita nata yaran bata basu wannan tarbiyar ba, duk nutsattsu ne babu na banza a yaranta, farkon faruwan incident din ai mahaifin nata bai koreta daga gidan ba amma matar nan ta san yanda tayi har ya koreta after almost one month da faruwar incident din, and i am telling you ba directly take abubuwanta ba, ni nasan mahaifinta baya cikin hayyacinsa ya koreta daga gidansa, coincidentally kuma nima na masu sallama xan bar gidan kenan in taho Abuja bayan Abba ya kirani, kawai naga baxan iya barin ta tafi wani wajen ba, And you know what Aunty…. bamu ta6a shiri da yarinyar ba duk tsawon xamana a gidan, amma sbda kirkin mahaifiyarta na tausaya mata muka taho nan Abuja tare” Aunty Maryam ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Dangin mahaifiyarta fa?” Ya girgiza kai yace “Babu su a nan” Aunty Maryam tayi shiru cike da tausayin Nihad, can tace “Kai yanzu menene next plan dinka Khalil?” Ya girgiza kai yace “I don’t know Aunt, i am confuse, ban san ta yanda xan yi convincing Mami har ta zauna nan zuwa sanda mahaifinta xai huce ba, gashi jiya da daddare ma sai da tace min ta amshi abinda xata amsa yau ta tafi sbda gobe weekend” Aunty Maryam tace “Kar ma kace mata komai don ba lallai ta fahimta ba, kawai dai ko da zata sake maganar admission letter din kace still fa ba a samu ba…. Nihad have to stay here kafin a samu wani solution din gaskiya, she is too young for this trauma at her age, kishiyar uwarta bata mata adalci ba, gashi ni kilan nan da sati biyu xamu yi tafiya” Khalil yayi shiru sai kuma a hankali yace “Aunty to me yasa baxan samar mata admission din ba kawai, sai ta zauna Abujan a zuwan dai karatu take” Aunty Maryam tace “Eh wannan ma shawara ce mai kyau kuwa, amma wani makarantar xaka samar mata?” A hankali yace “Nile or Baze University….” Buda baki Aunty Maryam tayi tana kallonsa da mamaki tace “Did you know the tuition fees of those Universities kuwa?” Ya ɗan yi dariya yace “Ohhh nawa ne ma?? shi su Mimi ke zuwa i think?” Tace “In ba dai ko Abbanku ya hada har ita ya dinga biya ba, tunda kowa ma biya ma kudin makaranta yake ai naga” Khalil yayi murmushi yace “I will process the admission for her as soon as possible in sha Allah” Aunty Maryam tace “Toh Allah ya rufa asiri, kaga dai dai kenan ma tunda sabon session xa su shiga” Bai ce komai ba, Aunty Maryam tayi shiru tana ta nazarin abubuwa iri iri, can ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Yanzu duk wani hanya da xa a bi a gano ta inda wannan video din nata ya fita babu shi kenan? Ai bai kamata ayi shiru babu bincike ba, kamata yayi anyi ta bincike har Allah ya sa a gano wanda yayi wannan ta’asar, duk da babu tantama ni nasan da sa hannun matar ubanta, sannan ina zargin kawayenta ma, don ta gaya min ko su waye” Khalil dai bai ce komai ba, Aunty Maryam tace “Amma tunda har ta iya tashi cikin dare ta kai ma Allah kukanta ni nasan komin daren dadewa wataran gaskiya zai bayyana, ta yanda komai ya faru duk Allah xai nuna ya tona asirin koma wanene, Allah Ubangiji ya kare mana zuri’a ya sa mu fi karfin zuciyarmu” Sai wajen karfe goma Khalil ya sauko downstairs daga parlon Aunty Maryam, Babu kowa parlon kasa ya nufi guess room da Nihad take, ya bude kofar dakin a hankali ya shiga ya ganta kwance tana bacci, for almost 4 days sai yau take bacci peacefully kuma me nauyi, ya karasa cikin dakin yana kallonta, juyawa yayi daga karshe ya fita ya kulle dakin. Ba laifi throughout ranan Nihad ta saki jikinta a gidan Aunty Maryam she really felt at home, Aunty Maryam bata barta ta zauna ita kadai ba, har fita suka yi tare da yamma ta rakata xata yi siyayya a shopping mall sae dai ta bata nikaf ta saka saboda yan kwakkwafi masu gane mutum farat daya, Aunty Maryam ta bata baki sosai a kan kar ta wani damu kanta in Allah ya yarda asirin wa enda suka mata haka zai tonu, kuma xata ga yanda Allah xai yi da stepmom dinta, hakan yasa damuwan Nihad ya ragu sosai ta samu relieve, bayan sun dawo daga shopping Mall din Aunty Maryam ta ware mata nata abubuwan da ta siyo mata ta bata, Nihad ta amsa a hankali tace “Nagode Aunty, Allah ya saka da alkhairi” Daki ta kai ta dawo ta zauna parlon, Aunty Maryam na ba Mus’ab dinta abinci Nihad tayi kasa da murya tace “Aunty don Allah xaki iya ara min wayarki in kira Mumyna?” Aunty Maryam ta dau wayar ta mika mata, Nihad tayi dialing number Mumy sannan ta kirata, lkci daya jikinta yayi sanyi jin wayar a kashe, ta mayar ma Aunty Maryam tace “Wayar a kashe yake” Aunty Maryam tace “Anjima sai ki sake trying” Nihad tace “Toh” Wayar Aunty Maryam ya fara ring ta dauko ganin Mami ce ke kiranta ta daga, bayan sun gaisa Mami tace “Ya ake ciki ta amsa kuwa Maryam?” Aunty Maryam tace “Kinsan sabon session ne Mami, so ina jin sai zuwa next week xa su fara badawa gaskiya, har yanxu bata samu ba kam” Mami tace “Wai wani makaranta ne?” Aunty Maryam tace “Toh ban dai sani ba gaskiya” Mami tace “Toh Allah ya kyauta, amma na so ace ko yau ko gobe ta koma gida” Aunty Maryam tace “Toh tunda Allah bai nufa ba sai mu saurari yanda ya tsara” Mami tace “Yana nan gidan naki ne Khalil din?” Aunty Maryam tace “Aa” Mami tace “Ohk tun safe ya fita naga kuma bai dawo gida ba” Aunty Maryam tace “Kilan yana can gidansu budurwarsa” Mami tace “To a gaida Mus’ab” Aunty Maryam tace “Xai ji” Daga haka suka yi sallama ta katse wayar, Aunty Maryam ta dinga tunanin ta yanda xa su bullo ma yayartata. Aunty Hassana ce xaune bangaren Hajiya Amina tana kallonta rai a dagule tace “Yanzu dai kin kara tabbatar da cewar bayan malaman da fatima ke bi na kasar nan har kasansu ma malamai yi mata aiki suke ko?” Da sauri Hajiya Amina tace “Aa na yarda wallahi….” Aunty Hassana tace “Wai ni yau yaya zai buda baki yace in bar masa parlonsa sbda na kawo masa shawarar kar ya tura Khalil Zanzibar, yaushe har ya dawo gidan balle a san ko ya sauya hali ko bai sauya ba, har zai kara yarda da shi ya daura sa kan miliyoyin kudinsa, kar ki dada kar ki raga shine yaya ya hayyako min har yana cewa in bar masa parlonsa cikin tsawa” Hajiya Amina tace “Toh wai yanzu me malamin yace maki da ku ka yi waya” Aunty Hassana tace “Ta lalata mana aiki, kuma da tsafi aka lalata aikin” Hajiya Amina ta rike ha6a tace “Aikin kusan miliyan daya fa?” Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciyar takaici tace “Wato an bata sa’ar dai dai sanda xata gaya masa ya shigo gidan babu wanda xai hanasa, shine ya shigo kansa tsaye asiri kuma yayi tasiri aka xuba masa ido babu wanda ya dakatar da shi, uban ma ya kasa cewa komai har yanzu shine ya billo da turasa Zanzibar yayi masa business” Hajiya Amina tace “Toh ni ance ba shi kadai ya dawo ba, kuma har yanzu ban ga yarinyar da aka ce ya dawo tare da ba, kinga ai ko yau naje bangaren, kuma har dakin Hajiya Fatiman na shiga kai tsaye ko yarinyar na ciki amma ban ganta ba” Aunty Hassana tace “Farhana tace fa bata gidan, tun da suka gane ita ce me wannan video din na kwanaki ya fitar da ita wai daga gidan, kinga tabbacin tsiyarsa kawai yaje ya tsula a duniya ya dawo, babu tantama kuma karuwarsa ce” Hajiya Amina tace “Wai daxu baki ga uwar yarinyar da ake son makala masa ta zo ba kuwa??” Aunty Hassana tayi wani dariya tace “Ai ko zata mutu baxai auri er ta ba sai dai in har ba Hassana sunana ba, Nadiya take ko wa? Toh wallahi baxai aureta ba, ba dai dukiyar yayana ake hari ba? to sai dai su gani su hanga daga nisa, ita fatima ta zaci ta fi kowa wayo shine take kokarin xata makala masa yar aminiyarta tunda kasarsu daya su hadu su wawushi dukiya ta ko ina su ci karensu ba babbaka, su yi wandaka son ransu su gayyato jajayen danginsu da abokai ayi biki a ci uban kudi, to kuwa xan ga ta yaya, don da dai in bari ya auri yarinyar nan gwara ya dauwama babu auren har ya mutu, yanzu in zai yi auren ai dukiya ne ba ta wasa ba yaya xai kashe, don har lefe shi xai yi masa, toh kiyi imagine nawa xai basu su yi lefen, ai miliyan 10 ma albarka” Hajiya Amina tace “To ke yanzu baxa ki yi ma Malam magana ayi duk yanda xa ayi ya auri ko Farhana ko Sajida ba? Ai gwara yan gida su mora da yan waje” Aunty Hassana tayi wani dariya kawai ta kyabe baki bata ce komai ba, Hajiya Amina tace “Allah kuwa da dai ya auri yarinyar nan gwara anyi haka kawai mu san har yanzu mu ne” Aunty Hassana na girgiza kafa tana wani Murmushi tace “Ke kin zata a banza ne har yanzu ba ayi auren nasa da Nadeeyah ba, sai yayi ta ce masu ba yanzu ba har ya bar gidan nan?” Hajiya Amina tace “Toh yanzu gashi ya dawo ga kuma uwar yarinya har ta fara mana sintirin gida” Aunty Hassana tace “Xata yi ta gama, baxai auri er ta ba, balle wata kuma can”

41

Umma ta shigo dakin da taga Nihal ta shiga for almost ten minutes bata fito ba, wato dakin Nihad, dube dube ta sameta take yi a dakin, tun da Nihal taga shigowar Umma ta dakatar da abinda take ta zauna gefen gado, da mamaki Umma tace “Me kike nemar mata a daki tun daxu?” Nihal dai bata ce komai ba, Umma ta kyabe baki tace “Ke idan fa kika ce xaki tafi makaranta a haka ba tare da kin saki ranki kin dawo yanda kike harkokinki da ba to ina me tabbatar maki zaki samu matsala a makaranta wannan time din, abinda baki ta6a ba, eh ansan er uwarki ce kuma ba dadi to amma so kike ki targada naki future din ne? Ko damuwar nan ne xai dawo maki da Nihad, to ma ta dawo ta maki me? yarinyar da ke can kauyen mijinta” Ita dai Nihal bata ce komai ba still kuma bata kalli Umma ba, Umma ta kara kyabe baki ta karaso ta zauna gefen gado tace “Ba kwanaki can kina da number shi dreban ba, ni da ma kin kirasa in ji ko kauyen nasu na nan garin suka tafi ko Zarian ya tafi kauyen uwarsa da yace” Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace “Ba da ke nake ba kika min shiru Nihal?” Nihal ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace “Bani da number sa” Umma tace “Toh amma ai farooq bazai rasa ba tunda shi ma Allah ya zuba masa shisshigi kira min shi ki tambayesa yanzu ina jira” Nihal ta dau wayarta tayi dialing number Ya Farooq ta sa handsfree, yana fara ringing ya daga bayan ta gaishesa tace “Yaya wai kana da number Khalil?” Farooq yace “Wa ke tambayar numbersa?” Duk da alamar da Umma ta dinga yi mata kan cewar kar tace ita ce ke tambaya amma Nihal bata kalleta ba tace “Umma ce” Farooq yace “Noo bani da shi, sai anjima” Tace “Toh sai anjima” Katse wayarsa yayi, Umma ta hade rai tace “Akan meyasa xaki ce masa ni ce ke nema?” Nihal tace “Nima na tambayesa Shekaranjiya yace bashi da, don ki tabbatar da hakan yasa na sake kiransa amma ni nasan bashi da number” Umma tace “Toh ai shikenan, dama wai da sai mu ji kauyen da suke, in ya kama mu je sai mu je kafin ki koma makaranta” Daga haka ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin, Nihal ta mike ta ci gaba da duba takardun da take. Ranan asabar da rana khalil na zaune parlon Mami sai ga kiran ya Farooq gaba daya ya mance sun yi waya few days ago yace masa xai shigo zaria, Ya ɗan kalli Mami dake parlon, bai daga wayar ba har ya katse, Ya farooq ya sake kira, mikewa yayi ya nufi kofa yace “Mami sai later” Daga haka ya fita daga part din gaba daya sannan ya kira Ya farooq, ya farooq na dagawa bayan sun gaisa ya sanar masa zai taho zaria from kaduna, Khalil yace “Ohk amma kaga muna gidan wata kanwar Baabata mun je gaisheta” Farooq yace “A ina kenan?” Khalil yace “A Abuja take” Farooq yace “Ohk, babu damuwa Usman na Abuja, so xai je inda ku ke in sha Allah” Khalil bai iya yace masa komai ba da farko, can kuma yayi saurin cewa “Toh Allah ya kai mu” Farooq yace “Zan tura maka numbersa yanzu ko da xai kiraka” Khalil yace “Ba damuwa” Daga haka suka yi sallama, kamar ance ya daga kansa ya ga Farhana a tsaye tana sauraron wayar da yake, ya hade rai yace “Ke ya kika tsaya min a kai?” Bata ce masa komai ba tana rungume da laptop dinta ta wuce tana ta6e baki, ya bi ta da wani mugun harara. Khalil na shirin xai fita da yamma sai ga kiran number da Farooq ya turo masa daxu, wato number Usman, yayi jim yana kallon wayar, can ya daga ya kai kunne, gaisawa suka yi, Usman yace “Yauwa wani anguwan ne a Abuja?” Khalil ya ɗan buda ido sai kuma yayi saurin cewa “Bari in tambaye Kanwar Baabar tawa” Usman yace “Ohk ina jira” Katse wayar yayi yana tunanin abinda xai yi next, bayan ya gama shiryawa ya fito zuwa bangaren Mami sannan ya kira Usman, yana dagawa yace “Tace Suleja ne” Usman yace “Ohk, akwai tazara sosai tsakaninmu, amma idan na shirya zuwa zan kiraka” Khalil ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace “Toh Allah ya kai mu” Usman yace “Ba Nihad din wayar mu gaisa” Khalil yace “Idan na shiga gida xan kiraka yanzu ina waje” Usman yace “Alright” Daga haka ya katse wayar, Mami da ta fito parlon tana kallonsa tace “Waye a Suleja?” Yace “Wasu ne” Tace “Ohk” Sannan ta zauna saman kujera a hankali tace “Ina son za mu yi wata magana da ke damuna Khalil” Ya kalleta yace “Toh ina ji Mami” Tayi kasa da murya tace “It’s High time kayi settling down son, tun baka bar gidan nan ba almost 2 years ago Abbanka ke maka magana har Allah ya kaddara tafiyarka, babban burina a rayuwa a yanzu shine in ga kayi aure….” Khalil ya sauke ajiyar xuciya yace “Mami kinsan fa she aure lokaci ne, idan time din yayi sai kika nayi Mami….” Tace “I am not talking about you settling down wai saboda ina son ka auri Nadeeyah, No son, idan da wata warce kake so daban fine, present her to us xa mu yi accepting as far as tana da tarbiyya, i can never force u on marriage son, kar kaga ko Nadeeyah yar aminiyata ce shi sa nake so ka aureta, a’a idan dai kasan da wata warce kake so da aure go ahead ka nemi aurenta just make sure yar gidan mutunci ce me tarbiyya ce like i said, sannan she should be from a reputable family, ka dai san halin Abbanka ai” Khalil yayi murmushi yace “Toh Mami ai ba ke kika hada mu da Nadeeyah ba, i met her abroad without knowing she is ur friends daughter, ba ta dalilin ke da Mumy muka san juna da ita ba, kawai Allah ne ya hadamu…” Mami tace “Haka ne, amma kaga ai yan sa ido gani suke mu muke cusa maka ita ka aura, don ta Hajiya Safeenah ma ta fi son Nadeeyah tayi aure a can Yemen tunda danginta suna can, kuma dama ita a can din ta tashi” Khalil yace “In sha Allah, as soon as i come back from this business trip xan kai ma Abba batun Mami…. Nima ina son settling down” Mami tace “Toh Allah ya nuna mana, amma kwana nawa xaka yi a can?” Yace “It depends, but nasan baxan wuce wata daya ba, but duk sati xan dinga shigowa Nigeria” Da mamaki Mami tace “Duk sati kuma? Me xaka dawo yi kai da ya kamata ka zauna can har ka gama abinda ya kai ka” Khalil yace “Bana son xama can har na wata daya, duk weekend xan dinga dawowa” Mami tace “Toh shkkn, amma ka sanar ma Abban naka?” Ya girgiza kai yace “He said i should do what suite me” Mami tace “Toh Allah ya tsare ya baka nasara” Yace “And one more thing Mami, ki amsar min Cv’s dina and my assets that he clutch” Mami tayi kasa da murya tace “No, kai ya kamata kayi masa maganan wannan idan ka dawo, kuma ina ga ko ka dawo din ma kar ka masa magana kawai ka zuba masa ido ka gani” Khalil yace “Aa i am asking him Mami” Shiru tayi bata ce komai ba, ganin ya mike tace “Toh shikenan son, Allah ya daura ka a kansa, Allah kuma ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya” Yace “Ameen” Daga haka yayi mata sallama ya fita daga parlon. Khalil na fita gidan Aunty Maryam ya nufa, can sama ya tafi ganin babu kowa a parlon kasa, ta fito daga bedroom dinta ta shigo parlor ta zauna ya gaisheta ta amsa tace “Ya su Mami?” Yace “Lafiya lau” Tace “Toh maa sha Allah, ya ake ciki?” Yace “Gobe ne zanyi tafiyar Aunty” Aunty Maryam tace “Toh Allah ya kai mu, sai ka dawo yaushe?” Yace “Nan da wata daya xan gama komai” Tace “Waii, ai ba lallai xaka dawo ka tarar da ni kilan a kasar nan ba, yanzu ya ake ciki maganar admission din?” Yace “In sha Allah an fara processing tun jiya” Sai kuma a hankali yace “But Aunty ya za mu yi da Mami yanzu? Kinsan halinta fa, and i don’t want her to be angry with me as a result of this issue” Aunty Maryam tace “I will think about that khalil, in sha Allah xan san yanda xa ayi, har yanzu nima tunanin ta inda xa a billo nake wallahi, da ina nan babu abinda xai hanani riketa a gidan nan” Bai kuma cewa komai ba, amma tunani yake, how will Mami be convinced, shi kuma he will neva let her stay in the hostel…. Bai wani jima ba yayi ma Aunty Maryam sallama kan zai je gidansu Nadeeyah, yana sauka parlor ya ga Nihad a parlon da mai aikin Aunty Maryam dake ta bata labari, ita dai tayi tagumi tana kallonta don ta gaji da surutunta gashi ko gane labarin bata yi, tun suna girki a kitchen take bata wannan boring  labarin, wannan yasa ta tuna nasu mai aikin a can gida, warce ko magana bata son ya hadasu da ita ba kuma ta zama inda take saboda tana ganin ta fi karfin hakan kamar yanda Umma ta ke yawan sanar mata, and for the first time Nihad felt bad at the way she treated Hafsah back then, yau dai ga ta ita ma a gidan mutane ba gidansu ba tana cin arziki…. Khalil ya sauko downstairs yana danna wayarsa, yayi dialing number Usman, yana fara ring Usman ya daga, ya nufeta ya mika mata wayar, tuni Murja ta gaishesa ta bar parlon da sauri, Nihad ta amshi wayar ba tare da ta kallesa ba tana kallon screen din amma bata gane number waye ba, ta kai kunne, jin muryarsa a hankali tace “Ya Usman” Yace “Ya kike Nihad?” Tace “Lafiya lau, ina yini” yace “Alhamdulillah, hope you are doing fine, babu matsala dai ko?” Ta sunkuyar da kai cikin sanyin murya tace “Eh” yace “Ohk are you still using ur account?” Tace “Bani da atm card ne” yace “Toh ya kaiki banki ki amsa wani” Tace “Toh” Yace “Xan maki transfer a ciki yanzu” a sanyaye tace “To yaya Nagode” Katse wayar yayi, hawaye ya cika idonta ta rufe fuskarta jikin kujera hawayen na zubo mata, bata son taji tana jin haushinsu a rai sbda Umma because she love all of them, basu ta6a nuna mata ubansu ne kawai daya ba, shi dai Khalil na tsaye don bata basa wayarsa ba, bayan few minutes ta dago tana goge idonta ta mika masa wayar ba tare da ta kallesa ba, kallonta yake, zata ajiye masa kan kujera ganin yaki amsa yace “Kee” Sai a sannan ta kallesa babu yabo babu fallasa, yace “Da xan baki wayar saman kujera na ajiye maki?” Ita dai bata ce masa komai ba, ya amshi wayar ta mike ta bar wajen, ya bi ta da kallo har ta bace sannan ya fita daga parlon, washegari kuma ya bar Nigeria for Zanzibar in the morning. Ranan Talata Mami ta kira Aunty Maryam, bayan sun gaisa Mami tace “Maryam bakuwar nan ta tafi kuwa?” Aunty Maryam tace “Ehh ta tafi jiya” Mami tace “Toh maa sha Allah, banda dai yace a gidansu ya zauna ai yarinyar nan bai kamata a gansu tare ba balle har ya kawota nan gidan” Aunty Maryam dake sauraronta tace “Saboda me Mami?” Mami tace “Kika ce saboda me?” Aunty Maryam tace “Au… Toh Allah dai ya kyauta, Allah ya tsare mana zuri’a” Mami tace “Ameen” Aunty Maryam tace “Ai ko yan gidansu suna ta godiya” Mami tace “Allah sarki, yanzu hostel din zasu kama mata ta zauna kenan?” Aunty Maryam tace “Toh ban dai sani ba” Mami tace “Toh idan ba nan din ba suna da yan uwa a Abuja ne? In basu da kowa ai sai dai hostel din dama” Aunty Maryam tace “Haka ne” sallama Mami tayi ma Aunty Maryam ta katse wayar, Aunty Maryam ta fara tunanin ta ina za a fara convincing Mami?? Tun bayan tafiyar Khalil Zanzibar duk sanda Mami taje gidan Aunty Maryam a daki Aunty Maryam ke sa Nihad ta zauna har sai Mami ta bar gidan, idan kuma ita ke son xuwa gidan yayartata ita kadai take xuwa da Mus’ab ta bar Nihad da mai aikinta a gida, unlike before da har da mai aikinta take zuwa gidan, a cikin wannan kwanakin kuma mijinta ya sanar mata nan da kwana biyar xa su taho kasar da yake, ta rasa ta inda xata billo ma yar uwarta a kan Nihad. Ranan friday ta shirya taje can gidan, bayan sun gaisa da Mami a bedroom dinta, it took her like five minutes kafin ta samu kwarin gwiwan yi ma yayartata magana, Mami tace “Wani magana kuma ke tafe da ke? To Allah ya sa lafiya, ina jin ki” Aunty Maryam tace “Mami dama iyayen yarinyar nan ne suka kira jiya, suna neman alfarman ta zauna wajenmu don basu son xamanta a hostel, and i think lectures will be commencing in 2 weeks time” Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take, Aunty Maryam tace “Toh ni kuma gashi nan da kwana biyar xa mu yi tafiya” Mami tace “Ikon Allah, to Maryam ke ko da ba tafiya xa kiyi ba ina ke ina rike yarinyar nan dama? Kuma ma da suka gaya maki haka ai sai kice barin kasar ma xa ki yi, sannan ni kuma da kika zo nan kika gaya min me kike son ince maki? Meye nawa a ciki?” Aunty Maryam tace “Amma Mami ke kam ba me mance alkhairi bace, bansan ki da manta alkhairi ba komin kankantarsa, ko albarkacin xama da suka yarda Khalil yayi a gidansu har na shekara daya ai bakya ce haka ba” Mami tace “Yanzu ya kike son ayi Maryam, ni dai kinsan baxai ta6a yiwuwa ince yarinyar nan ta zo gidan nan ta zauna ba, tsangwama da hantaran yan gidan ma kadai ya isheta balle aje ga shi matsalar da Khalil din xai shiga in har Abbansa ya samu labarin shi ya kawota gidan nan, a ina ya santa da har xai kawota gidansa, ku na lura yin abu ku ke kanku tsaye duk wani abun magana bakwa gudunsa, ke kinga da sararin zamanta nan gidan, kwana daya kadai da tayi kina ganin abinda ya faru” Aunty Maryam tace “Ni wallahi idan kina nuna shakkan matsiyatan gidan nan a fili abun kona min rai yake yaya, ita tsinanniyar Hasanar kike tsoro ko kuma Aminar? Haba Mami ko sau daya ke baxa ki kwatar ma kanki yanci ba, ke kenan baki son fitina ke kenan gudun abun magana, A haka rayuwar xai ci gaba? Yo Abun magana na nawa? Dubi tuggun da suka hada ma danki suka sa ya bar gidan nan kina ji kina gani baki iya buda baki kin tsaya kinyi defending dinsa ba shi da gidan ubansa, nima kika hanani magana a sannan, wannan wace irin rayuwace? Toh wallahi mu ba butulu bane, kuma ba mu mance alkhairi komin kankantarsa, in sha Allahu yarinyar nan bata da wajen zama tayi karatunta da ya wuce nan gidan, kuma wajenki tunda har iyayenta suka nuna mu ma sun yarda damu, sannan da iyayen nata basu rike shi khalil din ba Allah kadai yasan depression din da xai fada a lokacin, kana ji kana gani a kwace duk wani abu naka da ka mallaka, a amshe takardunka akan laifin da baka aikata ba, a toshe duk wani hanyar samun kudinka, sannan ace ka bar gidanku ba a son ganinka, infact garin ma gaba daya kada a samu information din kana ciki, ka tafi duk inda xaka tafi, me kike tunanin zai samu mutumin da aka ma hakan idan bai fada hannun na gari ba? Ni nasan zamansa gidansu really contributed wajen rage masa damuwarsa banda haka da baki gansa a yanda kika gansa ba yanzu, ai Allah ya tsine ma Hasana da Amina, ya walakanta su dai dai gwargwado, wato tunda ta kashe aurenta yau shekara kusan ashirin to bari naki ma ta kashe maki, ga agololinta ta cika gida da su suna ta baza mulki son ransu, wani abun ma sae ayi masu ba ayi ma naki yaran ba, to ai ni da xata burgeni ta auri Janar din kawai mana mu ga, for 20 good years kina daukan cin kashin matan nan kin kasa ta6uka komai, don dai kawai ni xamana ba steady bane a Nigeria amma wani abun da ba ayi ba wallahi, to gaskiya it’s high time kema ki kwaci kanki ki daina shirun nan Mami, yarinya kuma duk shegiyar da tace Khalil ne ya kawota gidan nan kice karya take, bai santa ba bai ma ta6a ganinta ba, babu sa hannunsa a zuwanta gidan, dama ai kowa ya sanki da taimako to wannan ma duk cikin taimakon da kika saba yi ne, amma babu ta inda khalil ya santa, kawai haka za ki ce masu, sannan hantara da tsangwama da kika ce baxa ma su ganta ba balle su yi mata, dakin baki na nan bangaren xata zauna, da safe ta tashi ta tafi makarantar ta, ta dawo da yamma to a ina za su ganta? Duk sanda na shigo Nigeria yin wani abu ta dawo wajena har sanda xan koma, ba shikenan ba?” Mami dai kallon Aunty Maryam kawai take ta kasa cewa komai, sallama aka yi a parlon duk suka daga kai.

42

Umma tace “Ayya inna ai suna can garinsu da ita” a tsorace Inna tace “Garinsu? Ina ne garin nasu? Buzu ne fa, ba shi da wani gari da ya wuce Nijar, Nijar din ya kinkimi jikata ya kai kuna gani baku hanasa ba? ta ina zata fara da zafin saharar su, ga shi ance mana ana ta juye juyen mulki a can yau kwana da kwanaki, ni da Abubakar muna ta jimami” Umma tace “Aa Inna, garin zaria ya tafi da ita” Inna ta saki baki, can tace “Kan uba, ku ka bar sa ya tafi da ita wannan garin, ai duk ɗan kano yafi karfin zama a can, Sannan da xai kai ta can din wani shegen ya bi su a cikinku??” Umma tace “Haba Inna, ai sun je sun dawo ya fi a kirga, Nihad fa ta sake fiye da yanda kike tunani Inna” Inna tace “Kai nima dai wallahi da na tsaya nake biye maki kamar wata er wiwi, maganina ma kenan, matsa ki ban waje wajen Ibrahim na zo ba wajenki ba, kai kuma Ibrahim wajenka na zo ba wajen Sumayya ba” Abba yace “Toh ya kike son ince Hajiya? Dama ana zuwa cigiyar wanda kulawarsa da komai nasa ya fita daga hannun iyayensa? Ai ni tuni na mikata garesa, alaqarsa da ita ya fi namu yanzu, don haka duk inda ma ya kai ta dai dai ne, ba ruwana, ba ruwanki, ba ruwan kowa” Inna da ta saki baki tana kallonsa tace “Yau ba lafiya, kace ba ruwanka Ibrahim?” Yace “Toh hanasa tafiya da ita xan yi?” Umma na murmushi tace “Banda abunki Inna mata da mijinta ki zo cigiyarta a gidansu, ita da gidan nan kuma ai sai dai ta kawo mana ziyara, idan aka ganta gidan nan yanzu ai ba lafiya kenan, kuma wallahi ko sati ba ayi ba sun zo gidan nan da shi sun mana sallama kafin su tafi Zarian wai garin mamarsa ce, kawai dai ba ku da rabon ganawa ne, amma yace ba jimawa xa su yi ba za su dawo, suna dawowa kuma da kaina xan je can gidan in dauke ki in kaiki gidan nasu” Inna tace “Toh wai ni shikenan nuna masa ku ka yi bani da matsayi ne da tun da aka aura masa ita daga shi har itan babu wanda ya taka yaje inda nake yace min ci kanki? duk da dai naje Bauchi kwanan nan na dawo” Umma tace “Au ashe dai kinyi tafiyar dai, to ki dai yi hakuri Inna, sun je ne baki nan, ki tambayi yan gidan kilan basu gaya maki bane da kika dawo” Inna tace “Kai Ibrahim fito za mu yi magana” Daga haka ta juya ta nufi kofa tace “Don ban ga xan iya magana gaban kwaɓeɓiyar nan ba” Abba ya mike ya bi bayanta suka fita, Umma ta bi ta da harara, can ta ja tsaki tace “A haka dai”

 Ranan alhamis Aunty Maryam suka fara shirye shiryen barin Nigeria tare da mai aikinta da yaranta mata biyu da ke wani boarding school a nan Abuja, duk sai jikin Nihad yayi sanyi, the present of Aunty Maryam use to make her feel strong, it’s making her move on with life, tana kara samun kwarin gwiwa har ta mance duk wata damuwar da take ciki and now she is leaving her, Aunty Maryam na lura da sanyin da Nihad tayi, and she felt really sorry for her, she wish she could do something about it, she wish xata iya tafiya da ita inda xa ta, daren Thursday Aunty Maryam ta idar da sallahn da take a sama ta sauko kasa ta karasa sauran kintse kintsen da bata yi ba a gidan don ranan Asabar za su tafi, har xata koma sama sai kuma ta tafi ta bude dakin Nihad duk da taga jiya bata yi tashin daren ba da ta leka ta, zaune ta ganta kan darduma ta hade kai da gwiwa, ta dago kai jin an bude kofar dakin, Aunty Maryam ta shigo dakin ganin idonta tace “Kukan me kuma kike Nihad?” Wasu sabbin hawayen suka ciko idonta ta kasa cewa komai, Aunty Maryam tace “Talk to me, why are you crying?” cikin rawar murya Nihad tace “Aunty you are leaving me… idan kika tafi kika bar ni i don’t have anybody here” tana fadin haka ta fashe da kuka, Lokaci daya jikin Aunty Maryam yayi sanyi ta dagota ta zaunar da ita gefen gado tana kallonta cikin sanyin murya tace “Ke da zaki fara makaranta Nihad, sannan wajen yayata fa za ki zauna, she is also nice, you will like her so much, and Khalil is also there for you always” kuka kawai Nihad take don tasan idan Aunty Maryam ta tafi shikenan she might go back to her former self, there will be no one to encourage her anymore, har ranta bata son gidansu Khalil, she don’t think she can cope staying there, ganin yanda take kuka Aunty Maryam ta jawota jikinta cike da tausayinta tace “Kiyi hakuri Nihad, bana son kina wannan kukan, ni ma ina son mu zauna dake kawai bani da yanda xan yi ne, but even with my absence baxa kiyi lacking komai ba” Kai kawai Nihad ta daga mata hawaye na sauka idonta, Aunty Maryam tace “Je ki wanke fuskarki ki zo ki kwanta” Tashi tayi a hankali ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito ta hau saman gadon amma wasu hawayen ne ke zuba idonta, mikewa Aunty Maryam tayi jikinta a sanyaye ta fita daga dakin, ita kanta tasan in dai ba khalil na gidan ba zaman gidan ba lallai yayi ma Nihad sauki ba, duk excuses da Mami ta kawo a kan dalilin da baxata riketa ba gaskiya ne, amma saboda babu wani option yasa Aunty Maryam duk tayi shunning excuses din. Washegari friday tana dakinta tayi dialing number Khalil, yana fara ring ya daga bayan sun gaisa tace “Baxa ka dawo weekend ba?” Yace “Ina airport yanzu haka, in sha Allah yau xan dawo” Aunty Maryam tace “Toh kana sauka ka daure ka fara biyowa ta nan gidana” Yace “Ohk, hope all is well?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Yaushe ne tafiyar Aunty?” Tace “Gobe in sha Allah” Yace “Ohk, sai na dawo in sha Allah” Sallama suka yi ta katse wayar, gaba daya ta kasa sauka gun Nihad don har ranta bata son ganin kukanta. Wajen karfe biyu zeenah ta shigo wajenta a daki tace “Ummi why is ur visitor crying since morning?” Aunty Maryam ta kalleta tace “Go and mind ur business please dear” Ta zaro ido tace “No i was only trying to show concern” Aunty Maryam tace “Je ki kira min ita” juyawa tayi ta fita daga dakin, Bayan wani lokaci sai ga Nihad ta shigo parlon Aunty Maryam tana tafiya a sanyaye, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kasan Carpet, Aunty Maryam ta dinga kallon idanuwanta da suka kumbura, can ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya tace “Wajen yayata ne baki son zama Nihad?” Girgiza mata kai kawai Nihad tayi bata ce komai ba, Aunty Maryam tace “Toh ki gaya min inda kike son zama” cikin sanyin murya Nihad na wasa da gefen gyalen jikinta tace “Bani da inda zan zauna” Aunty Maryam tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta, irin wannan yarinya karama haka ace wai an koreta daga gida, why? to yanxu da ba don Khalil din ya taho da ita ba da ya zata yi kenan, sai da ta shiga duniya kenan tunda gashi wai dangin mamarta basa nan, what a cruel world we are in, how comfortable is this her step mum now da tasa aka kori yar teenager haka daga gida saboda selfish interest dinta, lallai duniya abun tsoro, bayan few seconds Aunty Maryam tace “Je ki zuba abinci ki ci” Tashi Nihad tayi ta nufi kofa ta fita daga parlon. Karfe hudu saura Khalil ya shigo gidan ya tarar da Aunty Maryam dake parlonta a zaune, tayi welcoming dinsa ya zauna sannan ya gaisheta tace “Ya hanya?” Yace “Alhamdulillah” Kallonta kawai yake yana jiran ya ji kiran da take masa, Ta sauke ajiyar zuciya tace “Kjay, ina tunanin halin da Nihad xata shiga idan na tafi na bar ta a kasar nan, she’s been crying since 2 days ago, i feel really sorry for, she is too young to be passing through all this, tana bukatar tausayawa da soyayya irin ta uwa, ban san yanda xan yi ba….” Kallonta kawai khalil yake, can a hankali yace “Aunty ba wajen Mami za ki bar ta ba?” Aunty Maryam ta girgiza kai tace “Kai ma kasan mun banbanta da Mami ta ɓangarori daban-daban, yanda na jawota jiki har ta sake ta buda min cikinta Mami baxata yi haka ba, sanyinta baxai bari tayi hakan ba, ko me xa ayi mata a gidan kuma nasan iyaka Mami tace tayi hakuri, toh da wanda ya dameta zata ji ko da na yan gidanku KJay?” Khalil dake ta sauraronta yace “Toh meye shawararki Aunty?” Aunty Maryam tace “I am thinking of telling Abu Zeenah sai mu tafi tare da ita ƙasar da za mu” Khalil was speechless at first, can yayi karfin halin cewa “Aunty karatun nata fa?” Aunty Maryam tace “Sai a samar mata a can ta fara” Yayi kasa da murya yace “But i have paid all the fees, kuma kinga ai na kashe kudi da yawa, ni kuma baxan wani iya bin processes din refund ba” Aunty Maryam tayi shiru tana kallonsa, ya kwantar da murya yace “Kar ki damu Aunty in sha Allah she won’t be uncomfortable as you are thinking, beside Mimi na gidan, nasan baxata bari ana ci mata fuska ba, sannan nima next week zan gama abinda nake a can in dawo Nigeria gaba daya” Aunty Maryam still ta kasa cewa komai but deep down her tausayin Nihad kawai take ji kawai tana jin da kawai ya bari sun tafi da ita, shi dai kallonta kawai yake hoping she is convinced, daga karshe tace “Shikenan, Allah yayi mana me kyau, Allah ya bata ikon kwantar da hankalinta a gidan naku” a hankali Khalil yace “Ameen” Aunty Maryam tace “Ba komai, ka tafi gida kawai, gobe da safe za mu hadu a airport” Yace “Allah ya kai mu” har ya tashi tace “And one last thing xan bata waya, kar kuma kace zaka amshe, kawai dai ka sa mata ido wajen ganin da su wa da su wa take communicating” Yayi shiru yana kallonta, tace “Sannan na ba Ayman layin da na sa mata a wayar da xan bar mata” Shi dai Khalil kallonta kawai yake, tace “Ka ji abinda nace?” Yace “Na ji” tace “Sai anjima” juyawa yayi ya fita daga parlon nata. Khalil na sauka downstairs ganin Zeenah a parlor yace “Ina Moon?” Tace “She is sleeping upstairs” Yace “Ohk, ya preparation din tafiya?” Tace “Mun gama tun jiya” yace “Good” Ya fi minti biyar tsaye a parlon, daga karshe kawai ya fita compound, nan gidan ya bar motarsa don akwai wani abokinsa a layin da xa su je wani wajen tare yanzu. Washegari da safe Khalil ya nufi airport tare da Mami da Mimi with Noor, Aunty Maryam ta tafi da motarta da yaranta uku da mai aikinta da Nihad, don tun da taga motar khalil a gidanta ta sanar masa xata taho da motarta airport sai ya maido mata gida ya dau nasa, Noor kuma tayi driving dinsu Mami su koma gida, har suka isa Airport Nihad bata daina kukan da take ba, she felt everything is over for her, it’s just like they are sending her away from home for the second time, she felt insecure without Aunty Maryam, she won’t have anyone to confide in anymore, bayan Aunty Maryam ta isa airport din tayi parking, har ma ta daina ba Nihad baki ganin ba sauraronta take ba, ta dau waya ta kira khalil, ya sanar mata sun kusa isowa, tana ta jira har ya shigo airport din with escort, murmushi tayi don tasan babu abinda ya tsana kamar wannan escort din, kawai dai babu yanda xai yi don escort din na Mami ne sae in ita tace masu bata bukata, wannan kuma sai in ba waje me nisa xa ta ba, tuni aka masu providing wajen parking babu 6ata lokaci, bayan few minutes Mami da su Mimi suka sauko daga motar, Aunty Maryam ma ta sauka ta tafi ta gaida Mami, yaranta ma duk suka sauka xuwa wajen, Noor ta rungume Aunty Maryam tace “Ohh i feel like crying Aunty, xa mu yi missing dinki sosai” Mimi ma ta marairaice tace “Me too Aunty” Mami na murmushi tace “Toh ba sai ku tafi gaba daya ba” Noor tayi dariya tace “We wish” Nan mai aikin Aunty Maryam ta durkusa ta gaida Mami, Mami ta amsa tace “Murja sai Uk ko?” Murmushi tayi tace “Za mu yi kewanku Mami” Mami tace “Toh Allah ya tsare, Allah ya kai ku lafiya” Nihad bata yarda ta sauka daga motar ba ta hade kai da gwiwa tana shesshekan kuka, Aunty Maryam bata yi forcing dinta ta sauko ba cause she feel sad seeing her cry that way, Mami tace “Toh ina yarinyar?” Aunty Maryam ta ɗan yi murmushi tace “Kuka take a motar shi sa ma ban bari ta sauko ba” Mami tace “Kuka kuma? Kukan me?” Aunty Maryam tace “Sabo mana Mami” Mami tace “Allah sarki” Tuni aka sauke kayansu zuwa cikin airport din, Khalil dai na tsaye ya jingina da motarsa ya rungume hannu, lkci lkci yake kallon motar Aunty Maryam, Sai da xa su shiga cikin airport din bayan sun yi sallamar karshe da su Mami Aunty Maryam ta koma gun motarta ta bude back seat ta dafa shoulder din Nihad a hankali tace “Be a good girl dear, Allah ya tsare ki, Allah kuma yayi maki albarka, in sha Allah xa mu dinga waya sosai duk abinda ya dameki kar ki boye min ki dinga gaya min kin ji, kuma kar ki fasa addu’a da tashin daren da kike kamar yanda kika saba in sha Allah xaki ga sakayya cikin gaggawa, sannan ki dinga daukan kiran mutumin da na ba numberki banda walakanci my dear, he is a good guy, and u will enjoy communicating with him” Nihad ta kasa ce mata komai sai kuka take, Aunty Maryam ta juya cike da karfin hali ta bar wajen duk Khalil na kallonsu, Ta mika masa makullin motarta yace “Allah ya tsare Aunty” Ta gyada masa kai ta nufi cikin airport din su Mami na daga masu hannu, Khalil ya mika ma Noor makullin motar Mami dake wajensa, Ta amsa tace “Till we meet home yayanmu” Juyawa yayi ya nufi motar Aunty Maryam ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, ya riga su Noor fita daga airport din, har sannan Nihad bata daina kukan da take ba kamar ranta zai fita, shi ma kuma bai ce mata komai ba, har ya isa gidan Aunty Maryam, bayan an bude masa gate ya shiga yayi parking motar a parking space, Nihad ta kasa dago kanta, ya sauka daga motar ya jingina jiki, bayan few minutes ganin ba bude motar xata yi ta sauko ba ya bude mata, da kyar ta sauko daga motar xata bar wajen tana harde kafa tana kokarin danne kukan da ya taho mata taji ya jawota kusa da shi, lkci daya ta fashe da kukan ta rufe fuskarta a jikinsa, drawing her more closer to himself yayi kasa da murya yace “Da kin bi ta ai” Ya bar ta ta ci kukanta bai hanata ba, har ta gaji tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ta rufe ido tana shaƙar daddadan kamshin jikinsa, tana kuma jin yanda zuciyarsa ke bugawa. They stood in that way for almost 5 minutes, lokaci daya yaji ta sakar masa duk jikinta, yayi saurin rungumeta sosai kar ta zame kasa, he could feel her breathing calmly, kamar kuma warce aka tsikara ta bude ido da sauri ta janye jikinta shi ma yayi saurin saketa, ta koma gefe tana murza ido, shi kuma yayi keeping straight face…. she is so sleepy don jiya ba wani baccin kirki da tayi, ya ciro makullin motarsa ya bude tasa motar, ya shiga yana warming dinsa tana kallonsa tace “Kayana” Ya daga kai ya kalleta, ta koma gun motar Aunty Maryam ya bude booth din da makullin, ta ciro jakunkuna biyu, daya na wasu kaya da Aunty Maryam tayi mata, daya kuma wanda ya siya mata, ta zuba kayan a booth dinsa ta kulle sannan ta shiga back seat, bayan ya gama warming motar suka bar gidan, Nihad ta ɗan shinshina Hijab din jikinta jin kamshin dake tashi a jiki, a hankali ta kwanta jikin motar ta lumshe idonta, har suka isa gidansu bata sani ba tana bacci, bayan yayi parking ya kashe motar ya sauka still Nihad bata farka ba, ya bude back seat din yana kallonta, patting din kujeran motar yayi still bata bude ido ba, sai kuma ya kai hannu jikinta yana tashinta, sae a sannan ta bude ido da sauri tana bin inda suke da kallo, ganin compound din jikinta yayi sanyi, ya zaga ya bude booth ya fiddo jakunkunanta, ta sauko daga motar tana kallon securities din bakin gate din, ya kulle motar yana rike da jakunkunan nata biyu ya fara tafiya, ta bi bayansa tana jan kafa tayi kalan tausayi da fuskartar, ta inda ya shigo da ita gidan ranan farko da suka zo ya bi da ita yanzu ma, har suka isa bangaren Mami, ya kai mata kayanta guess room dake bangaren, tana tsaye bakin kofar har ya karaso ya shiga parlon Mami sannan ta bi bayansa, Mimi ce kadai zaune parlon, Mami kuma na bedroom dinta, ya zauna saman kujera Nihad dai ta koma gefe ta tsaya, kana ganinta kasan she isn’t happy being here, ya ɗan hade rai ya nuna mata kujera, ta sauke kanta kasa ta zauna saman kujeran, Mimi na kallonta tace “Hi” Nihad ta daga kai ta kalleta, Mimi na murmushi tace “I am Mardiyya, and you?” Nihad dai sai kallonta take jin yanda tayi pronouncing R din sunan alamar dae bata cikakken R 😜, Khalil ya juya ya kalli Nihad jin tayi shiru, Nihad ta kalli Mimi tana ɗan murmushi tace “I am Nihad” Mimi ta wara ido tace “Waow, You have a nice name, ina da wata fwend with ur name” Khalil na kallon Mimi yace “Hey take her to the guess room ta kwanta, she is sleepy” tashi Mimi tayi tace “Ohk mu je” Nihad ta tashi tana kallonsa, sai kuma ta bi bayan Mimi har zuwa dakin, babba ne dakin sosai sai kace ba guess room ba, furnitures din dakin ma kadai abun kallo ne, sannan ga bandaki shi ma babba a ciki, har da kayan kallo akwai a dakin, Yanda aka gyara dakin kuwa ga zanin gado sai sheki yake kai kace akwai mutum a ciki ne, Mimi tace “An wriga an gyara dakin yau, so za ki iya kwanciyarki” Nihad tayi murmushi cause her intonation and most especially how she pronounces her letter R is very funny to her, can dai tace “Thank you” daga haka ta kwanta saman gadon, Mimi ta juya ta fita, nan da nan bacci ya dauke Nihad… After sleeping for many hours ta bude ido a hankali, tsaye ta ga Khalil a dakin yana jera mata kayanta a press din dake dakin, Kallonsa take kawai don bai san ta tashi ba, duk Abayas din ya jera su waje daya, haka Hijab da atamfofi da Aunty Maryam tayi mata kusan kala takwas, tana ganin xai ta6a inner wears dinta ta sauko daga kan gadon da sauri ta turo baki tace “Ka bar min xan yi kayana da kaina” ya juya ya ɗan kalleta, sai kuma ya kwashi duk inners din ya mayar da su cikin jakar ya koma gefe ya tsaya yana kallonta, taki Kallonsa, a takaice tace “I need space” Daga sama har kasa ya kalleta sai kuma ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita daga dakin, duk sai da tayi seperating inners din nata, sannan ta koma ta kwanta tayi lamo saman gadon tana tunanin Mumy.

43

Mikewa Nihad tayi bayan ta tuna wayar da Aunty Maryam ta bata, ta sauko daga kan gadon ta tafi inda empty bags din suke ta duba wanda wayar ke ciki bata gani ba, mamaki ne ya cikata ta dinga kallon jakar, ta duba second bag din nan ma taga babu wayar babu alamarsa,  Knocking aka yi a kofar dakin ta mike tsaye da sauri tana kallon kofar, can ta karasa ta bude taga Mimi a tsaye, Mimi tace “Ki fito mu ci abinci” Nihad tace “Toh” Mimi tace “At Mami’s parlor” Nihad ta gyada mata kai, Mimi ta bar bakin kofar, komawa dakin Nihad tayi ta dau mayafinta tana kallon agogo, karfe sha biyu saura ake cin abincin rana kenan a gidan, ta dai nufi kofa ta fita zuwa parlon Mami tana tafiya a hankali, Mimi na zaune with 3 different foods a gabanta, Nihad ta karasa tana kallon abincin, Mimi ta nuna mata wajen da zata zauna, Nihad ta zauna, Sai ga mai aikin Mami ta shigo da ruwa me sanyi da drinks a hannunta ta ajiye masu tana kallon Mimi tace “Za a kawo fruit Salad din ne?” Mimi ta kalli Nihad tace “Will you take fruit Salad?” Nihad ta girgiza kai alamar a’a, Mimi ta kalli Bilkisu tace “No need” Bilkisu ta juya ta fita, Mimi ta zuba abinda xata ci a abincin gabansu, tayi ma Nihad alamar ta diba, Nihad ta dau plate ta debi shinkafa da miya, daga Nihad har Mimi cakalkala abincin kawai suke yi, ita Mimi sae danna wayarta take, daga karshe ta mike tana kallon Nihad dake mamakin wai har ta gama cin abincin kenan, Mimi tace “Let me go and brush My teeth” Nihad ta gyada mata kai kawai, Mimi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba Noor ta shigo parlon kallo daya tayi ma Nihad ta dauke kai ta nufi dakin Mami ganin Mami bata nan ta juya ta nufi kofa zata fita, Nihad ta bi ta da ido har ta fita, Mimi na dawowa parlon ta kira Bilkisu ta waya ta zo ta fitar da sauran abincin daga parlon…. Har yamma Nihad na parlon Mami, wayar da bata gani ba yayi mugun tsaya mata a rai, kuma ta ma san wa zai dau wayar, Lokaci lokaci Mimi ke shigowa wajenta a parlon, seems basa wani zama nan bangaren sae Mami ta kirasu ko kuma sun shigo gaisheta, shigowar Mimi na karshe tace “Pls mu je ki rakani saloon xan yi gyaran gashi” Nihad tace “Toh” Mimi ta jirata har ta dauko Hijab dinta sannan suka fito Main parlor din gidan, Nihad sai estimating uban tafiyar da suka yi kafin su shigo ainahin parlon gidan wanda girmansa ya wuce misali take, the house is really huge, Tun da suka shigo parlon Aunty Hassana dake waya ta bi su da ido, can ta katse wayar da take tace “Ke Mardiyya zo nan” Mimi ta dawo tana kallonta, ko kadan Nihad wasn’t comfortable at the way the woman was looking at her, Aunty Hassana tace “Wacece wannan?” Mimi ta kalli Nihad da tayi tsuru tsuru tace “Aunty bakuwa ce” Aunty Hassana tace “Bakuwar wa?” Mimi ta buda hannu tace “Bakuwar Mami” Nihad tayi karfin halin cewa “Ina yini” Aunty Hassana na kallonta daga sama har kasa tace “Lafiya” Mimi ta jawo hannun Nihad suka bar parlon, Sajida da shigowarta parlon kenan ta kalli Aunty Hassana tace “Wallahi Mama she is the one” Aunty Hassana tace “Anya kuwa? Naga wannan fara ce sosai fa” Sajida tace “I am telling you the fact, ita ce, bari in dauko wayata ki gani” Daga haka ta tashi da sauri ta tafi ta dauko wayarta ta shiga video tayi playing ta mika ma Mamarta wayar, Aunty Hassana tace “Toh ba cewa ku ka yi tare da wannan ɗan iskan suke ba? Kun ce shi ya kawota gidan” Sajida tace “We are not sure, kawai muna shiga parlon Mami muka ganta a zaune, kilan er uwarsu ce saboda yau da Aunty Maryam xata tafi ne ta sake dawowa gidan nan, all those while tana gidanta” Aunty Hassana tace “Kaiii, da yar uwarsu ce xan santa, da kyar dai in ba shi ya kawota gidan nan ba, idan kuwa ba shi bane ya aka yi sai da ya dawo ita ma muka ganta a gidan, amma ba komai xan samu yaya anjima idan ya dawo, ae dai baxa a kawo masa yarinya gidansa bai sani ba, xai min bayanin ko wacece” Nihad ta dinga kallon motar da wani mutumi sanye da camouflage yayi parking dai dai inda Mimi ke tsaye, ya sauka ya bude masu back seat, kana ganin shigar da Mimi tayi na English wear ga baƙin shade dinta a ido sannan ga wani jaka da ta rataye xaka san ba karya, she looks so cute and beautiful, Nihad bata ta6a jin da akwai wanda xata ji ya fita komai a rayuwa ba sai yanzu, ita da ganin kanta take babu ya ita, har University da take zuwa ma kallon kasa kasa take masu ba kowa take ma magana ba ko da kuwa an mata, don tana ganin ba class dinta bane su, sai gashi yanzu kawai taji ta raina kanta, Mimi na kallon Nihad ganin yanda ta ja gefe ta tsaya tace “Shigo” Nihad ta shiga motar ta kulle a hankali, mutumin ya ja motar aka bude gate suka fita daga gidan, Mimi ta ajiye wayarta da take dannawa tana kallon Nihad tace “Here is a question for you Nihad” Nihad ta dinga kallonta ba ko kiftawa, Mimi tace “How did u come to know my broda?” A hankali Nihad tace “Wanne?” Mimi ta ɗan yi jim tace “Yayana fa nake nufi, wanda ku ka dawo tare da shi dazu da safe” Nihad tace “Ohk, Yayanki ne?” Mimi ta buda ido tace “Yea he is my senior brother, we are having same father and same mother, Mami is our Mum, Noor is my senior sister, she is his immediate but ya girmeta sosai, ya bata 12 years, xan nuna maki ita idan mun koma gida kilan baku hadu ba har yanzu” Nihad sai kallonta take don truly Mimi na nugun kama da shi, both the nose and eyes, a hankali Nihad tace “Pls ki gaya min gaskiya gidansu ne wannan gidan da muka fito?” Mimi ta wara manyan Idonta tace “That’s funny, he is the first and only male child of our father, did he tell you ba gidansu bane?” kallonta kawai Nihad take tana jin ita fa yanzu da ta ga ainahin cikin gidan da irin girmansa da kyau ta kasa yarda gidansu Khalil ne, ita kawai yanxu gani take kamar rikonsa ake a gidan ko kuma gidan ɗan uwan babansa ne, abinda ta saka a ranta kenan don she is beginning to get confuse ta yaya ma xa ace wannan gidan nasu ne, mutumin da yaje gidansu yake driving ana biyansa for almost a year, sannan har kauyensu ya kai ta, to me yasa xai kawota irin wannan gidan yanzu ta yarda nasu ne, Mimi da ke ta kallonta ta katse mata tunaninta tace “What are u thinking about?” A takaice Nihad tace “I am finding it hard to believe, and I don’t think i will believe” Mimi tayi murmushi tace “Now i understand, he acted like he is a nobody right?” Nihad tayi shiru tana kallonta, Mimi ta shiga gallery dinta taje inda take ajiye hotunan yayan nata, wanda sun fi dari ta shiga ta mika ma Nihad tana kallonta, farkon hotonsa da Nihad ta gani ta dinga kallo babu ko kiftawa, sanye yake da farin labcoat with stethoscope round his neck, ta tafi next hoton, ta gansa cikin private jet an masa unaware picture, yayi crossing kafa yana danna waya with a serious face, ga tsadadden non-alcoholic wines a gabansa, designers ne kayan jikinsa, irin kyan da yayi kuwa a hoton ba ace wa komai, Nihad ta dinga kallon hoton don karya ne mutum ya kalli hoton bai sake kallo ba, bata san sanda tayi zooming ba still wanting to confirm and be sure shi din ne dai, taga wallahi shi ne, da zaka shiga zuciyarta kaga mamaki da shock da ya cika sa, a hankali ta tafi next picture din ta gansa a Newyork, then another in Los Angeles, Paris and another in United kingdom, infact duk yawanci hotunan a kasashen waje ne, wasu hotunan da turawa, wasu larabawa, she is really shock at all what she is seeing, sai kuma ta fara ganin hotunansa da Nadeeyah, a hotonsu na uku tare ta ki ci gaba da kallon, ta ɗan kalli Mimi dake danna second phone dinta giving it all her attention, tayi tapping dinta ta mika mata wayarta, Mimi tace “Are you done?” Nihad ta gyada mata kai, amsar wayar Mimi tayi ta mayar cikin jaka ta ci gaba da abinda take da dayar wayarta, har suka isa saloon din Nihad bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, Mimi ta kamo hannunta tace “Dear” Firgit Nihad ta dawo, Mimi tayi murmushi tace “Mun iso” Nihad ta kalli mutumin da ya bude masu motar yana jiran su sauko, ta sauka daga cikin motar, sannan Mimi ma ta sauka, kallon wajen Nihad ta dinga yi tana imagining duk nan saloon ne? How big and beautiful, ganin yanda ta tsaya Mimi tace “Mu je” Nihad ta bi bayanta ta kasa daina kallon saloon din har suka shiga ciki, nan taga fararen mata ne masu gashi har gadon baya ke zuwa gyaran gashi wajen, har turawa da larabawa, kana ganin cikin saloon din kasan ba karya, Mimi tace “Ke ma kiyi gyaran gashinki” Nihad dai bata ce komai ba, da Mimi ta sake mata magana tace “Ohk” sai da suka 6ata kusan awa daya da rabi a saloon din daga karshe suka fito, har sannan kuma wanda ya kawosu na jiransu a motar, har suka isa gida Nihad na duniyar tunanin da ta fada, mamakin Khalil kawai take…. why then did he disguise himself and come to their house as a driver? What might be his mission? And who were those villagers he took her to and claimed they are his parent? Tambayoyin da take ta ma kanta kenan amma babu amsa, ta kuma rasa amsan, kenan Nihal ta san wanene shi shiyasa take kulasa har da exchanging number? Nan abubuwa da yawa da suka faru tsakaninta da shi a gidansu suka hau dawowa mata vividly, lkci daya tayi saurin kawar da tunanin daga xuciyarta don ko tunawa bata son tana yi, a haka har suka isa gida… Basu tarda kowa a Main parlor ba Mimi ta raka Nihad har dakin da aka sauketa, Nihad na kallonta a hankali tace “Thank you” Murmushi kawai Mimi tayi mata ta juya zata fita, Nihad tace “Wait plss, ina son xan maki tambaya” Mimi ta juyo tana kallonta tace “Ohk” a hankali Nihad tace “I have this female friend, a guy came to stay in their house… he showed he was a nobody, i mean he disguised him self, he hide his identity, so all through his stay a gidansu yana mata abubuwa gadara gadara, sannan he don’t have an atom of respect for her as per somebody that came to stay and work under them, shikenan ita kuma sai bata raga masa, shi ma kuma bai fa sa walakanci da gadara da yake mata ba, to cut everything short har dai ya bar gidan, ita kuma it now happens tana nasu gidan da zama for just a while, and he wasn’t what she took him to be, she saw him a different person in his parents house, idan ke ce a shoes din kawar nan tawa tell me how u will handle everything….” Mimi ta fashe da dariya sosai, ta zauna gefen gado tana kallon Nihad still laughing tace “Really?” Nihad dai fuskarta babu yabo babu fallasa tace “Tell me how u will handle it” Mimi ta sauke ajiyar xuciya tana murmushi tana gyada kai tace “Ohk, if i should be in this shoe gaskiya xan ji kunyarsa sosai….” Nihad tace “Mind you, sanda yake gidansu baya respecting dinta sannan walakanci da gadara kawai yake mata da gaya mata bakar magana, ya sha hadata da parents dinta har ya kai ya kawo nobody is even supporting her again in their house, shi kuma ba a ganin nasa laifin, kullum shine me gaskiya ita kuma ayi ta mata fada” Mimi dai murmushi kawai take tana kallon Nihad tace “Amma ita bata masa walakanci ko cin mutunci ko cin zarafinsa ba, or even gori during his stay?” A takaice Nihad tace “Tayi mana, tunda ae shi ya ja komai” Mimi dai ta kasa daina murmushi, can tace “Ohk in ni ce, to make peace reign xan samesa a gidan nasu in basa hakuri ince let by gones be by gones plss, we just misunderstood ourselves amma yayi hakuri komai ya wuce” Nihad ta katse ta tace “Idan baxa ta iya basa hakurin ba fa?” Mimi tace “Then ko hanya baxan dinga barin yana hadani da shi a gidan nasu ba, i will try all possible best to be avoiding him sbda duk sanda na gansa a gidan xan dinga tuna abubuwan da suka faru a baya and i might be feeling guilty for everything…. So idan ni ce i will prefer in basa hakuri a wuce wajen, saboda with all that have happen baxan samu peace of mind din xama a gidan ba” Mimi na Murmushi ta kare maganar, Nihad tace “Ai shima duk abinda yake mata bai ta6a bata hakuri ba” Mimi tayi dariya tace “Toh shikenan, sai kawai tayi ta avoiding dinsa, that’s just it” Nihad tace “Thank you for ur advice to her” Mimi tace “Welcome dear” Daga haka ta juya ta fita, Nihad ta koma gefen gado ta zauna a hankali. Bayan Magriba Nihad ta tafi bangaren Mami ta dalilin kiran da Mimi ta shigo tayi mata wai Mami na kiranta, kwance ta ga khalil a parlon farko waya na kare kunnensa, ta kalli Mimi ganin ta shiga next parlor din, ta nufesa trying her possible best to be calm tace “Ka bani wayata da Aunty Maryam ta bani….” Ko kallonta bai yi ba, from the way yake magana har ta gane da warce yake wayar, ganin yayi banza da ita tace “Magana nake maka” Ya katse wayar da yake ya mike zaune yace “Why are interrupting my call?” Taki ce masa komai, mikewa yayi ya bar ta a wajen ya fice daga parlon ta bi sa da wani kallo, can ta shiga daya parlon. Mami na kallon Nihad bayan ta shigo ta gaisheta tace “Ba dai wani matsala ko? And i hope u are comfortable a dakin?” Nihad tace “Eh Mami nagode” Mami tace “Good, if there is anything u let me know” Juyawa Nihad tayi ta fita. Washegari da safe Nihad ta fito wanka kenan Mimi tayi Knocking, ta saka hijab dinta ta tafi ta bude mata kofar, Mimi ta sakar mata murmushi tace “Good morning Neehad” Nihad ta mayar mata da murmushin tace “How was ur night” Mimi tace “Alhamdulillah, Aunty Maryam wants to speak to you on phone” daga haka ta mika mata wayar tace “Idan kun gama ki sameni parlon Mami” Nihad ta gyada mata kai ta juya ta koma cikin dakin, wani farin ciki taji jin muryar Aunty Maryam, bayan sun gaisa Aunty Maryam tace “Ina wayar da na baki Nihad?” Nihad tace “Ban kara ganinsa ba Aunty” da mamaki Aunty Maryam tace “Baki gansa ba kuma? Ba a jakarki kika sa ba?” Nihad tace “Ehh na duba kuma ban gani ba” Aunty Maryam tayi shiru, can tace “Waye ya dau maki jakar?” A hankali Nihad tace “Shi….” Aunty Maryam tace “Khalil?” Nihad tace “Ehh” Aunty Maryam tace “Ohk, shikenan xa mu yi magana” daga haka tayi mata sallama ta katse wayar, Aunty Maryam na katsewa Khalil ta kira, bayan ya daga ko amsa gaisuwarsa bata yi ba tace “Bawan Allah akan wani dalili ka dauke wayar da na ba Nihad?” Khalil dake kwance ya mike zaune ya buda ido yace “Waya kuma… Ita tace maki haka? Beside Aunty ai ni ban ma san da wata waya ba” Ta dakatar da shi tace “Kar ka raina min hankali Malam, babu wanda zai dau wayar nan sai kai, yanzu dalilin da ka dauke wayar kawai nake son ji, period” Ya koma ya kwanta yace “Because kamata yayi tayi concentrating a kararunta yanzu ba ta rike waya ba….” Aunty Maryam ta saki baki tana sauraronsa, sai da ta bari yayi shiru sannan tace “Toh dauki wayar ka mayar mata, xan kirata da shi nan da minti goma….” Shiru yayi bai ce mata komai ba tace “Baka ji abinda nace bane?” Yace “Na ji” Tace “In kuma kana son mu samu matsala da kai ka kara dauke wayar nan daga wajenta ka ga, ai kana ji sai da nace maka na ba wani number layin shine xaka wani kama waya ka ɗauke, jaririya ce ita da baxata rike waya ba ko kuma waye ya ta6a xuwa jami’a ba waya?” Khalil dai bai ce mata komai ba, tace “kamar yanda nace nan da minti goma zan kira wayar bana son jin sa a kashe, sannan kuma ita nake son jin ta daga kiran” Daga haka ta katse wayarta ya taɓe baki, bayan few minutes ya sauka daga saman gadonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya dau shirt dinsa ya saka ya dau wayar sannan ya fita. Nihad ta gama shiryawa ta dau gyalenta ta fita zuwa parlon Mami, dai dai corridor that will lead to the parlor suka hadu da shi yana zuwa ta opposite dinta, taki yarda su hada ido har ta iso kofar xata bude taji ya fixgo hannunta ya bar bakin kofar, zaro ido tayi tana bin sa tace “Meye kake ja na haka?” Bai saurareta ba yana ta tafiya da ita, Balcony din part din ya shiga tare da ita, Ta dinga bin domain din wajen da kallo, kai baxaka ce ba a kasar waje bane, can ta kallesa tace “Why will you drag me this way??” Yace “Bana jin wannan yaren” Ta wani kyabe baki ta dauke kai tana kallon titi, a takaice yace “Zan baki waya kamar yanda aka ce in baki, amma ina son tunasar maki cewa shi aure ko ma wani iri ce daraja ne da shi sannan ba abar wasa bace, ba ruwan Allah da auren soyayya ko auren kiyayya ko auren hadi, so abu kadan zaki yi yanzu ki sa6a ma Allah, ki ja ma kanki fushinsa….” Da mamaki Nihad ke kallonsa har da bude baki, bai bata space din cewa komai ba ya ci gaba yace “Dama kawai ina mutunta iyayenki ne shi yasa har yanzu ban raba auren da ke tsakanina dake ba ina jiran appropriate time din yin hakan, sannan i have conscience baxan iya sakin ki a halin da kika shiga days back, don a sanda mahaifinki ya nuna baya bukatar ni dake a garin da yake, a sannan ya kamata ace na rabu dake na kama gabana don dama saboda shi nake zaune dake, amma ban yi hakan ba, tausaya maki da nake ne dalilin da yasa har yanzu aurenki ke kaina….  So a halin da ake ciki yanzu bazan so a rubuta maki zunubi ta dalilina ba, don haka idan na lura baxa ki daraja martaban aure ba kuma zaki janyo ma kanki fushin Allah to zan raba auren dake tsakaninmu don sama maki sauki, dama i was hoping to do that in the rightful time a lokacin da ya kamata, probably idan kinyi nisa karatunki kin kusa kammalawa, kinyi reconciling da mahaifinki, kinyi kokarin amending few damages that u did to ur self, kin kuma sake fahimtar rayuwa, kin fahimci duniya da mutanen dake cikinta da kyau, but i Sense duk wannan won’t be possible saboda hanyar da aka daukar maki na rike waya, and communicating with a guy….” Nihad dai kallonsa kawai take, yace “So how ever u chose it to be is left to u, ina maki abubuwa da yawa ne ba don kin cancanci in maki ba, sai ɗan darajan iyayenki…” Yana gama fadin haka ya ciro wayar aljihunsa ya mika mata yana kallonta yace “I will decide on what to do in few days time” ta sa hannu ta amshi wayar, ya juya ya bar wajen…. Nihad ta shiga parlon Mami ta tadda Mimi na jiranta su yi Breakfast, bayan ta zauna shayi kawai ta iya sha sai irish kadan, ta na dai zaune idonta na kan tv abubuwan da Khalil ya gaya mata na ta dawo mata, tabe baki kawai tayi, aka bude kofar duk suka daga kai, Aunty Hassana ce ta shigo parlon, bata amsa gaisuwar Nihad ba tana kallon Mimi tace “Ke ina uwarki?” Mimi ta mike ta shiga dakin Mami, Aunty Hassana ta dinga hararan Nihad, a hankali Nihad ta mike ta nufi kofa ta fita daga parlon don haka kawai ta ji tana tsoron matar, Aunty Hassana ta bi ta da harara, tana ta tsaye har Mami ta fito, Mami na kallonta tace “Mun tashi lafiya Aunty Hassana” Aunty Hassana ta dakatar da ita tace “Ba wannan ya kawo ni ba, ina ce ai ko ba komai Hajiya Fatima yanda xa ki mutunta uwar mijinki da tana raye haka nima ya kamata ki girmamani ki mutunta ni don ni din ba banza bace, Da mijin nan naki da kike takama ya sha nono ni ya sakar ma, amma naga baki da warce kika raina sama da ni, yanzu ace wannan yarinyar da ta zo gidan nan tun jiya har ta kwana zuwa yau ya dace ace baki turata ta gaidani ta gaida Amina a gidan nan ba? Idan ita Amina bata isa ba nima din ban isa ba kenan? Kawai yarinya ta shigo gidan mutane tsabar ba a nuna mata matsayin wa enda ta samu a gidan ba sai ta wuce ka wuce bata gaida ka ba, ko daga kai baxata yi ta kalleka ba, to akan wani dalili?” Mami ta kalli Mimi tace “Mimi je ki kai ta ta gaishesu” a fusace Aunty Hassana tace “Aa bama bukata, taje ta gaida wa? kawai dai ina kara baki shawaran ki daina abinda kike, in raini kike ji a gidan nan to karki matso da shi inda nake, don ni ba abokiyar yin ki bace Fatima” tana kai wa nan ta fice daga dakin kamar iska, Mimi ta kalli Mami tace “Why is she always creating issues out of nothing? From this to that, is she normal?” Mami tace “Jeki ki kaita nace ta gaishesu ban iya wahala da safen nan Mimi, da nasan abinda ya kawota kenan ma ni cewa xanyi kice mata ina bacci” Mami na kai wa nan ta juya ta koma dakinta. Khalil na zaune parlon Abbansa, ya jira har ya gama wayar da yake na kusan minti goma, Abba na kallonsa bayan ya gama a takaice yace “May i help you?” Khalil ya gyara zama yace “My Curriculum vitae, the key to my houses and their written document, my land title, my car…. Ina bukatarsu gaba daya, and I also want my business account unfrozen” Kallonsa kawai Abba yake, can ya mike yana kallonsa da kyau yace “Till u pay ur debt of 800m, idan ba haka ba duk assets din nan da ka lissafo ina me tabbatar maka siyar da su zan yi, kuma basu kai biyan bashin ba ma, shi kuma Cv din in kona, after all i sponsored you….” Khalil ya dinga kallon mahaifin nasa, Abba yace “So Now get out before i shoot ur leg” mikewa Khalil yayi ya nufi kofa kamar xai tashi sama ya bude, sai kuma ya juyo yace “But dad, I can’t pay for what I know nothing about….” Yana fadin haka ya fice daga parlon, direct bangaren Mami ya tafi, Mami na ganinsa ta mike tace “Lafiya” Yana huci yace “Mami me yasa har yanzu Abba ke danganta 800m dinsa da ni?? Ina zan kai har 800m” A hankali Mami tace “Saboda kai ya ba, a hannunka yasan kudinsa” A fusace Khalil yace “Toh ni ban san komai kan kudin nan ba, why is he not believing me?” Mami tace “Yanzu me ya kawo maganar kudin?” Yace “Naje na samesa xan amshi abubuwa na da ya amshe min” Mami tace “Amma ai na hanaka ko? What are you lacking now without them?” Khalil na girgiza kai yace “Baxan iya ci gaba da zama bana aiki ba Mami, ya sa anyi sacking dina a inda nake aiki, to ya bani Cv dina in nemi aikin a wani waje mana?” Mami tace “Idan da ka saurareni da baka je masa da maganar wani Cv ba Khalil, me kake bukata da baka samu a yanzu haka? Baka fi wani me aikin samu ba duk da haka? Every month ina tura maka 300k banda wanda kannena ke baka, so me xaka yi da Cv yanzu” a fusace Khalil yace “Ni neman auren Nadeeyar ma bana son yaje min, xan samu kawu kawai su je” yana fadin haka ya nufi kofa a fusace, Mami ta buda baki, sai kuma tace “Toh ai mun yi magana da shi jiya yace next week xai tura representative nasa su je neman auren, kar ka fara xuwa wajen kowa idan ba ɓacin ransa kake son gani ba” Tuni khalil ya fice daga parlon. Hajiya Amina ta shigo bangaren Aunty Hassana tace “Aunty Hassana kin ji abinda Oga yake ce min daxu kuwa?” Aunty Hassana tace “Me yace?” Hajiya Amina tace “Wai satin da xa a shiga xai tura a nema ma Khalil auren yarinyar nan dai, ita fatimar ta masa maganan hakan…” Aunty Hassana ta gwalo ido tace “Da gaske?” Hajiya Amina tace “Wallahi, kafin ya fita yake sanar min” Aunty Hassana tace “Ai ko bai gaya min ba kuma na shiga gaishesa daxu” Hajiya Amina tace “Toh dai shine nace bari in zo in sameki” Aunty Hassana tace “Toh bari inyi wanka zan fito yanzu” Hajiya Amina tace “Toh sai kin fito” Daga haka ta juya ta fita, Aunty Hassana ta mike da sauri ta dau wayarta ta shiga daki tayi dialing number aminiyarta, tana dagawa tace “Ke kuma haka ake Chamo daga cewa kina zuwa sai in ji shiru” Daga daya bangaren aminiyar tata ta kece da dariya tace “Ke dai bari na shiga rububi ne, ai da ma sai dai ki gan ni yau to kuma sai tafiya Kaduna ya kamani, ya gida ya su Sajida” Aunty Hassana tace “Lafiya lau, ni baki gaya min yanda ku yi da mutumin nan kan maganar da muka yi dake ranan ba har yanzu” Chamo tace “Wallahi yace daga dubu dari tara da hamsin ko biyar baxai sake ragewa ba, kuma ke ma dai kin shaida aikinsa, ba fa kowa yake ma aiki ba don shi aiki ma yawa yake masa” Aunty Hassana tace “Shikenan, don wallahi yanzu Amina ta shigo take gaya min satin da xa a shiga ma xa aje neman auren yarinyar” Chamo tayi wani dariya irin ta bosawa tace “Wuyarta ba a tura masa kudi an fara aiki ba, ke dai turo kudi kawai aminiya” Aunty Hassana tace “Toh Sadiya, yanzu kuwa zan saka maki, so nake da kansa zai birkice masu yace ya fasa bai sonta, kuma dab da xa a kai kudin” Chamo tace “An gama, sako kudi yanzu” Aunty Hassana ta katse wayar ta tura mata kudin.

44

Da daddare Mimi na parlon Mami tana ta danna wayarta bayan sun gama cin abinci da Nihad, kallo daya zaka ma Nihad ka gane she is moody, gaba daya she is uncomfortable da zaman gidan, Noor ta shigo parlon tana kallon Mimi tace “Hey Madam Dad yana kiranki…” Mimi tace “Ohk” Daga haka ta mike ta kalli Nihad tace “I am coming” Nihad ta gyada mata kai, ta nufi kofa Noor na biye da ita, Nihad ta bi su da kallo, a hankali ta kwantar da kanta jikin kujera tana jin kewar nata Abban, bayan sun fita Noor na kallon Mimi tace “I don’t like her” Mimi ta buda ido tace “Why?” Noor tace “Baki ga wani kallo da take ma mutane ba, beside bata iya gaisuwa ba sai bin mutum da ido, who does that” Mimi tayi murmushi tace “But she is nice, kawai bata son magana ne” Noor tace “Toh wa xata nuna ma rashin son magana, what’s even the reason of her staying here? Na zata kwana biyu xata yi ta wuce” Mimi ta buda hannu bata ce komai ba tana ci gaba da tafiya. Mikewa Nihad tayi daga karshe ta nufi kofa xata bar parlon, kafin ta bude kofar aka riga ta budewa, suna hada ido ta koma gefe without looking at him tana jiran ya wuce, ya shigo yana kallonta, tayi ficewarta ta bar wajen ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo… Nihad ta shiga dakin da take ta dau wayar da ya bata daxu, maganganunsa ne suka dinga dawo mata, ta tabe baki, kawai advice din Mimi ta dauka banda haka da tace masa to ya saketa din mana what is he even waiting for, though it’s better that she kept silent, miss call ta gani da foreign number, ta dinga kallon number, xata mayar da wayar ta ajiye sai ga wani kiran da same number, dagawa tayi ta kai kunne tayi shiru, sallama taji ya mata da accent dinsa na larabci, ta amsa yace “Is this Nihad pls?” Tace “Who am i speaking to?” Yace “I am Ayman Fadlullah, i got ur digit from Ukhti Maryam” Nihad tace “Ohk” Yace “So how are you?” Tace “I am fine” Yace “Can we chat on WhatsApp plss?” Tace “Ohk” Yace “Thank you, i appreciate” Daga haka ya katse wayar, ita bata ma san ko da WhatsApp a wayar ba, ta dai shiga ta duba taga an ma bude WhatsApp din da number, but ba a fara chatting ba, sai shi kadai da yayi mata sallama few hours ago, tayi replying sallaman, with pure English ya shiga yi mata introducing kansa as the first son to his parent, yana da kanni maza biyu, sai autansu mace, ya kara mata da cewa he is from Yemen but now resides in America inda yayi studying Accounting… Ita dai Nihad karanta chat din nasa kawai take bata cewa komai, har ta mance rabonta da chatting almost 5 weeks now, ganin she is not replying yace “Are you der Nihad?” Tace “Yeah… ” Yace “Ohk good, tell me more abou you” Kamar dai baxata ce komai ba sai kuma tayi masa introducing kanta a takaice a chatting din, yace “Waow, that’s nice… I will be flying to Nigeria soon to meet with you in sha Allah, i have already beginning to feel comfortable with you” duk hiran yawanci shi yake yi, sai dai tayi masa reply da ok ko kuma tayi shiru har sai ya tambayeta is she there, and she noticed he is jovial and very friendly sannan wayayye ne sosai, he chatted her for almost an hour, babu abinda ya boye mata game da kansa, ya tura mata hotansa da iyayensa with his siblings, ta gansu kyawawan larabawa kamar su suka yi kansu, da yayi requesting ta tura masa nata hoton bata ta6a fuskantar low self esteem a kanta ba sai yan kwanakin nan da suka gabata, da kuma yanzu da Ayman ya bukaci hotonta, jin bata ce komai ba yace “Nihad” ajiye wayar tayi ta koma a hankali ta kwanta, bayan kusan minti sha biyar sai ga wayar ya fara ring daukan wayar tayi tana kallon screen din, sai kuma ta daga ta kai kunne tayi shiru, yace “Did i hurt you in anyway pls?” Tace “Not at all” Yace “Ohk sorry about me asking of ur picture” Tace “Ohk” Ya ɗan yi shiru sai kuma yace “I won’t be asking u anymore” Tace “Good” Hiransa kawai ya ci gaba da yi mata, ta kalli agogo dake nuna sha daya da wani abu tace “I will be going to bed now” Nan yayi mata sallama ya kuma yi mata godiyan basa lokacinta da tayi, ta jira har ya katse wayar sannan ta kwanta ta lumshe ido, nan da nan bacci ya dauketa. Washegari da safe Mimi na dakinta ta fito wanka tana shiryawa gaban mirror aka yi Knocking kofar dakin tare da budewa, ta daga kai tana kallon kofar ya shigo tace “Yayanmu ina kwana?” Yace “Cool, are you having lectures today?” Tace “Yeah, yau muka yi resuming ai” Yace “Good, Nile ne makarantar naki ko Baze?” Tayi er dariya tace “Yanzu yaya har ka mance makarantar da nake, to su Noor ke zuwa Baze, but i and Farhana NUN ne” Yace “Ohk i now remember, did you have idea on when Jamb is commencing this year?” Mimi tace “Registration is still on progress, an kusa zana jamb din ma ai” Yace “Good, that girl… Ta samu admission a makarantar ku but she have to present her jamb result, don haka you take her with u zuwa center din da ku ka yi jamb registration tayi register” Mimi tace “Ohk, but that will be after my today’s lectures right? May be around 2” Yace “Ohk, ku tafi makarantar da ita kawai” Mimi tace “Ohk then” yace “But do not tell Mami about the jamb registration, xan baki admission letter dinta kiyi mata presenting kice zaku tafi makaranta da ita kawai shikenan” Mimi tace “Ohk” Juyawa yayi ya fita daga dakin, Bayan Mimi ta gama shiryawa ta tafi can dakin da Nihad take, ta tarar ita ma tayi wankan har ta shirya tana zaune gefen gado tayi shiru, yau din ma she is moody, gaba daya taji bata son zaman gidan nan, she isn’t comfortable, Mimi na kallonta tace “Good morning Neehad, yayanmu yace za mu je kiyi registering jamb yau, so xa mu fara zuwa school cause ina da lectures, after my lectures sai mu je wajen” Nihad na kallonta tace “Ohk”Juyawa Mimi tayi ta fita. A parlon Mami suka yi breakfast, daga nan Mimi ta sanar ma Mami tare za su tafi makaranta da Nihad, Mami tace “Wani makarantar ne nata?” Mimi tace “Makarantar mu daya” Mami tace “Really?” Mimi tace “Yeah, this is her admission letter” Mami tace “Toh Allah ya sanya alkhairi” Mimi ta fito tare da Nihad daga parlon Mami suka kusa cin karo da khaleel, daga sama har kasa yake kallon Nihad that’s putting on veil, though ba karami bane, don yawanci duk medium veils Aunty Maryam ta siya mata ba irin wanda ta saba sa wa a gida ba, Mimi tace “Za mu tafi yayanmu” Yace “Ohk” Nihad ta wucesa, Mimi na biye da ita ya bi su da kallo har sai da suka yi nisa yayi saurin cewa “Hey Mimi” Mimi ta juyo tana kallonsa, Nihad dai tsayawa kawai tayi bata juyo ba, shima abinda yasa ta tsaya bata son tafiya zuwa main parlor din ita kadai ne, ya nufesu har ya isa inda suke yana kallon Mimi yace “Erm sorry wayana zaki dauko min a dakina” Mimi tace “Ohk” Ta mika ma Nihad laptop dinta dake hannunta tace “Rike min pls” Nihad ta amsa, Mimi ta juya ta bar wajen, yana ta tsaye har ya daina hango Mimi, Nihad dai ta hade rai tayi backing dinsa taki juyowa, ya zaga ya tsaya a gabanta fuska daure yace “Baki da hankali ne zaki fita da gyale?” Bata san sanda tace “Saboda me baxan fita da gyale ba???” Yana kallonta da kyau yace “Saboda dama ke kina da baƙin taɓon da duk inda kika shiga dole xa a ganeki sai dai wanda bai san labarinki ba” Shiru Nihad tayi tana kallonsa babu ko kiftawa, lkci daya zaka iya ganin yanda jikinta yayi sanyi, ya buda hannu yace “So however u wish to dress is ur business not mine, kuma naga ai har nikab da hijabs Aunty Maryam ta sa maki a kayanki, but saboda ke kin saba tallan jikinki baxa ki iya sa su ba, to nan ba inda zaki yi abinda kika ga dama babu me sa maki ido bane” Ta sauke Idonta daga kallonsa tace “My dressing, my choice!!!” Tana fadin haka ta kara juya masa baya, Kallonta yake ko kiftawa babu, a haka Mimi ta dawo ya nufeta da sauri ya amshi wayarsa yace “Thank you” daga haka ya juya ya tafi parlon Mami, Mimi xata amshi laptop dinta Nihad ta ɗan kirkiro mata murmushi tace “I will hold it for u” Mimi tace “Oh thank you” a haka suka ci gaba da tafiya, luckily babu kowa parlon har suka fita compound, tuni wanda zai kai Mimi makaranta ya taso, ta fara shiga bayan motar sannan Nihad ma ta shiga, ya tada motar ganin Nihad bata kulle motar ba Mimi tace “The door Nihad” Nihad ta kalleta sai kuma a hankali tace “Plss baxan bata maki lokaci ba idan na koma ciki for just some minutes?” Mimi tace “Mantuwa kika yi?” Nihad ta sauke idonta daga kallonta tace “I am not comfortable with my dressing” Da mamaki Mimi ta dinga kallonta daga sama har kasa tace “What’s wrong with it? But you look smart dear, there is nothing wrong with you dressing, or is the veil too big?” Nihad ta ɗan yi murmushi tace “I will prefer i change” Mimi tace “Ohk then, xa mu jira ki” Sauka tayi daga motar ta koma cikin gidan. Da sauri ta wuce main parlor ta haura Upstairs har zuwa bangaren Mami sannan ta shiga dakin da take, she is just changing because kamar yanda ya fada xa a iya ganinta a ganeta amma ba don wai ya mata magana ba, hijab dinta ta dauka har kasa ta saka sannan ta dau nikab ta daura, baka ganin komai sai fararen hannunta da manyan idanuwanta with long lashes ta cikin nikab din, dama kuma Aunty Maryam tace mata ta dinga yawan saka Nikab in xata fita, tana fitowa ta sauko main parlor da sauri, Aunty Hassana da ke kokarin haurawa sama ta dayan stairs din ta bi ta da kallo, tadai san duk gidan babu me saka Nikab, sai kuma tace “Keee” Da sauri Nihad ta juya amma bata tsaya ba, Aunty Hassana ta sauko daga matakala biyun da ta hau ta nufota, hakan yasa Nihad ta tsaya gabanta na faduwa tana kallonta, Aunty Hassana ta isa har gabanta ta fizge Nikab din tace “Ke wa ya kawo ki gidan nan?” Nihad ta sunkuyar da kanta, a fusace Aunty Hassana tace “Baki jin ina maki magana ne” cike da karfin hali Nihad tace “Karatu nake yi” da mamaki Aunty Hassana tace “Karatu a ina? Wa ya kawoki kiyi karatu? Ke yar uwarsu Maman Mimi ce?” Nihad ta daga kai da kyar alamar eh, Aunty Hassana ta dinga kallonta daga sama har kasa, Mimi ce ta shigo parlon jin shiru shiru Nihad bata fito ba, Mimi na kallon Aunty Hassana tace “Good morning Aunt” Aunty Hassana tace “Wace makarantar take?” Mimi tace “Makarantar mu daya?” Aunty Hassana tayi shiru tana nazarin anya ba yayanta bane aka daura ma biyan kudin makarantar? Anya ba kawota gidan aka yi don yayanta ya dinga biya mata kudin makaranta ba, Aunty Hassana tayi mitsi mitsi da ido tace “Daga wani garin take?” Mimi ta buda hannu tace “Nima ban sani ba Aunty, Mami ce ta sani” Aunty Hassana tace “Ke baki ta6a saninta a er uwarku ba?” Mimi tace “Yan uwanmu suna da yawa wa enda ban sani ba, so she might be among them” Aunty Hassana ta gama nazare nazarenta  sannan ta kara kallon Nihad ta juya ta bar wajen, Mimi ta kama hannun Nihad suka fice daga parlon. The day was so hectic for Nihad don ta mance rabon da ta fita, NUN ya wuce yanda take tunaninsa, and it has always been one of her dream school don shi ta gaya ma Abba tana so amma yace Abuja yayi nisa sai yayi suggesting mata Maryam Abatcha and yayi assuring dinta she will like the school, though babu wanda ya san sunyi hakan, amma sai da taje ta gaya ma Umma which she is regretting right now, sai gashi yau she is going to be a student of her dream university amma kuma bata farin ciki da hakan, Ayman really whiled away her time a makarantar kafin Mimi ta gama lectures, sun dade suna magana da shi a waya tun bata son amsawa har dai ta fara amsa masa, shi ma saboda teasing dinta da yake ne sai tace sai ta rama, and she really enjoyed conversing with him caused he is so friendly and jovial, still tana makarantar Aunty Maryam ma ta kirata, sun kusa minti sha biyar suna waya, Aunty Maryam ta kara jaddada mata kada dai tace xata ma Ayman walakanci ta basa chance baxa kuma tayi da na sanin hakan ba, Nihad tace “Toh nagode Aunty” Daga haka Aunty Maryam tayi mata sallama, Nihad tace “A gaida min Mus’ab” Aunty Maryam tace “In sha Allah” Daga haka ta katse wayar. Sai bayan la’asar suka koma gida, tun da drivern motar yayi parking a parking space Khalil dake zaune karkashin wasu bishiyu da suka kawata makeken compound din yake kallon motar, Mimi ta sauka daga motar ta nufesa tana murmushi tace “Yayanmu good evening” Yace “How are you” tace “Alhmdlh, we are done with the registration, nan da sati biyu ne exam din ma ashe” Khalil yace “Ohk…” Juyawa tayi tace “Let me go in and take a shower” Daga haka ta juya taga har Nihad ta isa entrance din shiga cikin gidan, ta bi bayanta da sauri. Sai da suka fara shiga parlon Mami su gaisheta, kallo daya Nihad tayi ma Nadeeyah dake zaune parlon da Noor, ta dauke kai ta juya ta fita daga parlon, Nadeeyah ta kalli Noor da mamaki tace “Who is she?” Noor was speechless and astonished, ke baki yi sallama ba, kin shigo kin tadda mutane a parlor ba gaisuwa ba komai kin masu kallon tara saura quarter kin juya kin fita, Mimi ta sauke ajiyar xuciya tace “She is tired, yanzu muka dawo, it’s an hectic….” Noor ta daka mata wani tsawa ta dakatar da ita tace “Pls get lost, ke da kika shigo baki yi mana sallama ba? Ko baki gaishemu ba? How dare she? Who did she think she is?” Mimi dai bata sake cewa komai ba, Noor ta ci gaba da jaraba kamar xata ari baki, Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace “Calm down Noor, kilan kamar yanda Mimi ta fada ta gaji ne, so kiyi mata uzuri….” A fusace Noor tace “Baxan yi ba, kuma wallahi na sake ganin ta shigo inda nake tayi repeating nonsense din nan da tayi i won’t take it likely with her” Mimi dai ta karasa ta leka bedroom din Mami, ganin bata cikii ta juya ta bar masu parlon, Noor was still fuming with rage, Nadeeyah tace “Easy pls Noor, ya riga ya wuce ko? Stop the nagging pls” Noor tace “Nahhh bai wuce ba, i could slap her if she should repeat such kuma ba abinda xai faru” Nadeeyah tace “But who is she? Ranan na ganta gidan Aunty Maryam” Noor tace “How will i even know who she is, ni ban ma damu insan wacece ba tunda ba gabana take ba, i hate nonsense, na dai ji Aunty Maryam na ce ma Mami ai gidan iyayenta Yaya Khalil ya zauna when he was in kano, they were kind to him, they did that, they did this, bla bla bla, ita kuma tana so ta fara karatu ba a son ta zauna hostel, shine wai zata zauna nan gidanmu, cause at first Mami bata amince da zamanta a nan ba, but Aunty Maryam insisted, ta dinga kawo silly backups har sai da tayi forcing Mami yarinyar ta zauna gidan nan” Kallonta kawai Nadeeyah take babu ko kiftawa, can tayi karfin halin cewa “But who brought her here?” Noor ta karyar da kai tace “We saw her a day after yayanmu came back, which means tare kenan suka zo gidan, yes tare ma suka zo” Nadeeyah ta hadiye abu da kyar tace “Tare??” Noor tace “Yeah, and you know what?” Nadeeyah ta girgiza kai, Noor tace “You remember the video of a lady with undies that went viral last month?” Nadeeyah tayi shiru, Noor tace “Wani video that’s all over social media na wata yarinya babu kaya jikinta?” Nadeeyah tace “Yeah, i heard about the video amma i didn’t bother watching, so ban ta6a gani ba” Noor tace “Toh yarinyar ce” Nadeeyah ta zaro ido with surprise tace “Wace yarinya?” Noor tace “Yar rainin wayon da ta fita yanzu, ita ce a video din sure” Buda baki Nadeeyah tayi tace “Wai da gaske?” Noor tace “I mean it, bani da video din da na nuna maki, su Sajidah da Hanan ne ke da shi a waya” Nadeeyah was over shock, tayi karfin halin cewa “Kuma gidansu Kjay ya zauna a kano?” Noor tace “Yes, she was once a student of Maryam Abatcha” Nadeeyah ta sauke ajiyar xuciya tace “Toh Allah ya kiyaye” Noor tace “Waow its been long i hala this way, har kaina ya fara ciwo wallahi, shi sa bana son magana da yawa amma wannan yar kauyen ta sa ni magana, As i was saying….” Nan ta ci gaba da ba Nadeeyah labarin da take bata cikin nutsuwa irin na big babes, but gaba daya Nadeeyah was absentminded, Nihad ta tsaya mata a rai sosai, abinda ta mata ranan da suka hadu gidan Aunty Maryam ya fado mata, ita kuma a ranan bata dauka as komai ba, sai yanzu brain dinta ya tunatar da ita cewa warce suka hadu a mall a can kano ce fa da Kjay, mamaki da fargaba ya cikata, but why did he have to bring her all the way from kano to his parent house, sannan even for once bai ta6a ce mata tare suka dawo ba gashi yau satinsu uku, Noor dake ta magana ta lura gaba daya hankalin Nadeeyah baya wajen ta kai hannunta fuskarta tana waving, da sauri Nadeeyah tayi blinking idonta, Noor tace “What are you thinking of?” Nadeeyah bata ce komai ba amma kana ganinta kasan there is something bothering her, she looks so disturbed, Noor ta kamo hannunta tace “Tell me plss, me ya faru” Lkci daya Nadeeyah taji hawaye ya kawo idonta ɗon saurin kuka ke gareta, tana kokarin ganin bata fashe da kuka ba tace “He neva told me he came all the way from kano with her, even for once bai gaya min ba” Noor ta zaro ido tace “Ohh that? Meye abun damuwa a nan bayan dai kinsan aurenki zai yi? In 3 days time fa xa a kai kudin aurenku da shi, and baxa a sa ya wuce sati biyar ba, so why bother ur self about one filthy lady that’s all over social media half naked? ke sai kace baki san halin KJay ba? Ba abinda ya hada sa da yarinyar banda gidansu da ya zauna don ni tunda ta dawo gidan nan ma ko magana bana ganin yana hadasa da ita, you know he have class” Nadeeyah ta sauke ajiyar zuciya bata dai ce komai ba tana share idonta, Noor tace “C’mon chill plss, wannan bata kai ta sa ki shiga damuwa ba har ki zubda hawayenki a banza, me xai yi da ita? Da akwai wani abu tsakaninsu ma ai baxai fara kawota gidan nan ba, kuma saboda mugun abinda tayi shi yasa ma ba a son ta zauna hostel may be parent dinta suka yi requesting ta zauna a nan, shi sa ma kika ganta a nan” Nadeeyah ta gyada mata kai kawai, Noor ta ci gaba yi mata hiran da take mata a nutse….. Har karfe biyar khalil na zaune inda yake a cikin compound din yana danna waya, so yake ya maida Nadeeyah gida kafin ya je inda yake son zuwa, wayarsa dake hannunsa ya fara ring, ya dinga kallon number wanda ke kiransa, ya dai yi picking daga karshe yakai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace “Dama wani aiki ne ya shigo da ni Abuja yau, so gobe da safe in sha Allah xan koma kd, shine nake son inji wani wajen ku ke a Abujan?” Khalil ya sauke idonsa yace “Ohk, maa sha Allah, goben za ka zo kenan?” Farooq yace “No, na gama abinda nake yi yanzu, goben da sassafe nake son tafiya” at first khalil ya rasa abinda xai ce masa, Farooq yace “Hello” Khalil yace “Eh ina jin ka, xan tura maka address din yanzu” Farooq yace “Toh ina jira” Daga haka ya katse wayar, Daga nisa ya dinga kallon Nadeeyah har ta iso inda yake, ta dauke kai tace “Xan tafi gida” Ganin mood din ta yace “What happened Nady? Are you okay?” Ta ki ce masa komai, ya mike yana kallonta, lokaci daya hawaye ya cika idonta, da damuwa yace “Talk to me plss, me ya faru?” Cikin rawan murya tace “But you neva told me ba kai kadai ka dawo Abuja ba” Yace “Shit… Toh menene tsakanina da warce na dawo da? There is nothing Nady kawai karatu ta zo yi a garin nan, and she have no where to stay shine take zaune gidan nan, bayan nan babu wani abu kuma trust me” Ta goge Idonta tace “Naji, I want to go home” yace “Noo, not in this manner pls, but ta maki wani abu ne?” Nadeeyah tace “Kawai shigowa tayi ta hararemu ta fita babu sallama balle gaisuwa” Khalil yayi wani sigh yace “But you guys shouldn’t have taken it personal, she is a sociopath….” Nadeeyah ta tabe baki dai bata ce komai ba, khalil ya kalli wayarsa dake ring da sauri, ganin Farooq ne ya daga yace “Ina tura maka ne” Farooq yace “Ohk” Daga haka ya katse wayar, Khalil yace “Look Ki koma ciki yanzu, i will be having a visitor immediately, idan ya tafi sai muje ki sha ice cream sannan in maida ki gida” Murmushi kawai tayi ta juya ta fara tafiya, yea dama murmushin kawai yake son yaga ta yi which means komai ya wuce kenan, ya sauke ajiyar zuciya ya zauna ya shiga sending ma Farooq address…..

45

Farooq was perplexed bayan yayi parking dai dai inda Khalil yace ya tsaya ya jirasa, yana kallon sojojin dake opposite dinsa amma nesa da shi, ya dinga bin area din da kallo with mouth agape, ina ne nan din khalil yace ya zo? And why will he tell him to come and wait here? He could see 3 of the soldiers advancing toward his car with haste, and bai san me xai masu ya kawo shi nan ba idan sun karaso, can nesa ya hango khalil na tahowa ta inda sojojin suka yi creating barriers, sojoji ukun suka karaso har inda yake suna masa alamar ya sakko fuskarsu a murtuke babu rahama, Farooq ya kashe motarsa ya sauko with calmness ya gaishesu, Maimakon su amsa strictly suke tambayarsa where is he from kuma tsayuwar me yayi a nan? Farooq yayi karfin halin nuna masu khalil dake tahowa yace “I was waiting for him….” Da sauri khalil ya fito daga wajen barrier din ganin sojojin da suka tsare farooq, ya daga ma sauran soldiers din dake wajen a zaune hannu ya nufi gun farooq, sojojin dake gaban farooq na ganinsa suka juya suka koma position dinsu, Khalil na Murmushi yace “Yi hakuri na bar ka a tsaye, barka da isowa yallabai” farooq dai sai kallonsa yake still surprise, can dai yace “Ina ne nan din Khalil?” Khalil ya zaga daya side din motar not wanting to answer him yace “Mu karasa can ciki Yallabai, ba a tsayawa a nan….” Farooq ya shiga motarsa har sannan mamaki ne shimfide a fuskarsa  Khalil yace “Mu je can gaba” da wani expression Farooq ya masa wani kallo yace “Mu je ina??” Cause ta wajen barriers din da sojojin ke tsaye yaga Khalil na nuna masa wai su bi, Ba tare da Khalil ya kallesa ba yace “Gaba xa mu yi, kuma hanya ce ai” Farooq yace “Ta gaban sojojin can xa mu bi kake nufi?” Khalil yace “Ba komai, nace maka hanyar kowa da kowa ne” Bayan few seconds Farooq dai ya tada motar yana driving din a hankali yaga sojojin sun daga masa karfen da ya rufe layin, ya wuce ciki still driving careful, Bayan sun shiga Farooq na kallon Khalil yace “Wai ina ne nan din Khalil?” Khalil na nuna masa gaba yace “Can gaba xa mu karasa, ba nisa sosai” Farooq dai ya ci gaba da driving din amma carefully cause the security in there isn’t funny, very tight security, gasu fuskarsu babu rahama duk a murtuke, Farooq dai na driving yana kare ma anguwan kallo, bayan tafiyar few minutes, Khalil ya nuna masa gate yace “Baƙin gate din can xaka yi horn” Farooq ya juya yana kallon Khalil, Khalil bai yarda ya kallesa ba ya danna horn din da kansa, Sojojin wajen suka taso zuwa gun motar, tuni khalil ya sauke glass ganinsa suka koma, aka bude gate din, sai da Khalil yace “Mu shiga yallabai” sannan Farooq ya ja motar zuwa cikin compound din, Khalil ya nuna masa inda xai yi parking, kai kana ganin farooq kasan abun ya gama daure masa kai, he is more than confuse, Khalil ya sauka daga motar ya zaga yana kallon farooq, farooq ya sauko daga motar shi ma yana kallonsa amma ya kasa cewa komai, Khalil na dan murmushi yace “Ya kwana da yawa Yallabai? It’s a pleasure meeting with you after a while” A hankali Farooq yace “Now tell me, why did u chose to hide ur Identity? Why?” Khalil ya sauke idonsa kasa yace “I was left with no choice Farooq, but the beautiful part of all is that i meant no harm to your family, something’s are better left unsaid, and mind you this is my father’s house not my house, kuma shi namiji ai baya tutiya da gidan ubansa, all what u are seeing in here is for my dad, and i am not him in anyway” Khalil bai jira abinda Farooq xai ce ba yayi gripping hannunsa yace “Mu shiga ciki” Daga haka suka bar wajen, Farooq couldn’t stop looking at Khalil, babban tambayar da yaji yake bukatar amsarta shine me khalil yaje yi gidansu? meye manufarsa na zuwa gidansu yace zai yi driving? Driving fa?? Shi dai From day one yasan there is something about Khalil that is hidden, he knows that, and here is what was hidden today, Suna shiga Main parlor Khalil ya sake hannunsa, Farhana dake parlon ta bi su da kallo, Daga khalil har Farooq da yake tafiya with calmness babu wanda ya kalli inda take har suka haura sama, Farooq couldn’t hide how amazed he was with all what he is seeing, and he felt so happy for his Lil sis, har suka iso parlon Mami, Khalil na kallonsa yace “This is my mum’s part, za ku gaisa da ita” Farooq na murmushi yace “Sure” Suka shiga first parlor sannan second, Nadiya dake zaune ita kadai tana danna waya ta daga kai jin an bude kofa, Farooq yayi sallama ya shiga bayan Khalil yayi taking lead, Nadiyah ta kalli Khalil sannan farooq, Khalil yayi mata murmushi yace “Meet my frnd Farooq” Da fara’a Nadeeyah ta gaida Farooq ya amsa with calm smile written all over his face sannan ya zauna saman kujera, Tuni Khalil ya shiga dakin Maminsa, bayan few minutes sai ga shi ya fito tare da Mami, da fara’a Mami suka gaisa da Farooq dake ta kallonta saboda resemblance dinta da khalil is very obvious, khalil ya zauna gefen Farooq yana kallon Mami yace “Yayan Nihad kenan Mami, he is Farooq by name….” Mami tace “Maa sha Allah, you are welcome son” Khalil na Murmushi yana patting shoulder din Farooq gratefully yace “They are the most nicest family i have met so far in life, they really made my stay with dem a memorable one, they made me felt at home all through my stay with them, and i owe them for that…” Farooq dai kawai yayi murmushi, Mami tace “Allah sarki Allah Ubangiji ya karfafa zumunci, Allah ya saka da alkhairi…. This is so beautiful to hear” Farooq wish he could express how happy he is for his Lil sis at this moment, a ko da yaushe addu’arsa ga Nihad shine Allah ya dauwamar da ita cikin farin ciki bayan all What she’s gone through, yana mata addu’ar Allah yasa aurenta da Khalil ya zama sillar farin cikinta na har abada, he sees her as a strong young girl, don yau ace Nihal ce abubuwan nan suka faru da yasan she is definitely going to break, yasan she can never endure it for long, duk abubuwan da Khalil ke fada akan karamcin da suka masa a kano Farooq hankalinsa ba nan yake ba, ganin komai yake kamar a mafarki, tuni Mami ta kira Bilkisu ta kawo masa drinks and small chops, Mimi ta shigo parlon rike da laptop dinta zata dau charger da ta bari, Mimi na kallon Farooq tace “Good evening” With smile on his face yace “Evening dear” Ta dau charger xata fita Khalil na kallonta yace “Can you pls call ur new friend?” Mimi ta ɗan juya tace “You mean Neehad?” Yace “Yeah” Ta gyada kai tace “Sure” Daga haka ta juya ta fita daga dakin…. Kwance ta tadda Nihad kan gado, Nihad ta juya tana kallonta, ganin yanayinta Mimi tace “Are you okay?” Kai kawai Nihad ta gyada mata ta mike zaune, Mimi tace “But there is tears in ur eyes” Nihad ta girgiza mata kai trying not to break cike da karfin hali tace “I am fine, kawai ciwon kai nake….” With concern Mimi tace “Eyya Allah ya sauwake, i will get u drug, ki zo parlorn Mami ana kiranki” Nihad ta hadiye abinda ya tokare mata cikin karfin hali tace “Ohk” duk zaton ta Mamin ce ke kiranta, Ta sauka daga saman gadon ta bi bayan Mimi tana tafiya a hankali suka fita daga dakin…. A hanya suka hadu da Noor, ganin she is dressed up Mimi tace “Are you going out big sis?” Banza Noor tayi mata saboda tana tare da Nihad, ta wuce su kamar xata bangaje Nihad din, Nihad dai ta bi ta da kallo bata ce komai ba, Mimi tayi kasa da murya bayan Noor ta wuce su tace “Sorry…. she is angry at you may be because u just badged into the parlor when we came back from school, baki yi masu sallama ba kuma sannan baki yi recognizing dinsu ba, which isn’t right” Nihad ta dinga kallonta tace “Ta yaya zan shiga waje ban yi sallama ba, sai dai in basu ji ba, ko kuma nice ban yi yanda xa su ji ba, beside they were discussing ta ya za su ji?” Mimi tace “You just have to raise ur voice za su ji, and why didn’t you recognize them?” Nihad ta ɗan buda ido tace “Do i have to?” Mimi tace “Yeahh, as far as ke kika shiga kika samesu a wajen, sai kiyi acknowledge din haka” Nihad ta tabe baki tace “Sai dai in yi ma yayarki amma ita dayar i have no business with her don ban santa a gidan nan ba, why will i recognize her?” Mimi tayi letting sigh tace “But fiancee din yayanmu ce” Nihad ta buda ido sosai tace “Ohh ashe fiancee ce kawai!!” Mimi tace “Yeah, and she is going to be his wife soon” a takaice Nihad tace “Then i will wait till she becomes his wife if that’s possible, before i can recognize her….” Mimi tace “Now accept that u are wrong Neehad” Nihad tace “I accept, but by not recognizing only ur sister” Mimi ta daga kafada tace “Ohk then, and can i ask u one more thing” Ba tare da Nihad ta kalleta ba tace “Ohk” Mimi tace “I noticed u don’t greet my brother, why?” Nihad ta kalleta da mamaki, can tace “But u advised i should be avoiding him totally” Noor halted with mouth wide open tana kallon Nihad, bata san sanda ta fashe da wani dariya ba, she laughed for some seconds kafin tace “But u neva told me it’s you, u said ur friend” Nihad ta ɗan zaro ido tace “Oh, oh… I…. I mean to say….” Sai kuma ta rasa abinda xata ce lokaci daya taji kunya, Noor na dariya tace “You are so funny Nihad, ni bance kar ki gaishesa ba, i only said u should be avoiding him, but not ignore greeting him” Nihad dai ta ki cewa komai, Mimi ta langwabar da kai tace “Yayana na da kirki sosai fa, you only misperceived him, just try turning friends with him zaki gane hakan, he is a simple and sweet person…. Give what i said a trial pls” Nihad taki cewa komai ta ci gaba da tafiya Mimi na biye da ita har suka iso parlon Mami, khalil kadae Nihad ta gani zaune saman kujera, sai Nadeeyah dake parlon ita ma, bata ma lura da Noor dake tsaye daya side din ba, ta juya zata kalli Mimi ta tambayeta wa ke kiranta tayi ido hudu da ya farooq dake tsaye side din kofa ya rungume hannunsa yana kallonta with smile written all over his face, Kasa kwakkwaran motsi tayi a inda take, don kawai sai abun yayi mata kamar mafarki take, ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, ganin haka kawai ya nufeta yana murmushi ya rungumeta, he understands she is shock and neva expect seeing him at that time, Nihad ta kankamesa ta fashe da kuka, tana son magana amma ta kasa cewa komai, Khalil da Nadeeyah dai kallonsu kawai suke, haka Noor dake tsaye, lkci daya Mimi dake murmushi ta fahimci yayanta ne, haka Noor da ta kasa barin inda take a tsaye, ganin kukan da Nihad take farooq yayi kasa da murya yace “Ain’t you happy seeing me Lil sis?” A hankali cikin rawan murya tace “Don girman Allah kar ka tafi ka barni a nan yaya, wallahi baxan iya zama a nan ba, take me back home in roki Abba yayi hakuri ya yafe min” Farooq kadai ke jin abinda take cewa, yayi kasa da murya yace “You are a married woman now Nihad, you have to stay where ever ur husband is staying” Nihad ta kara rushe masa da kuka, ya kama hannunta ya tafi da ita suka zauna saman kujera yana kallonta, kuka kawai take tana share hawayen da yaki tsaya mata, shi dai khalil kallonta kawai yake, Farooq yace “Now stop that cry ko inyi tafiyata, and i am serious” Da sauri ta fara goge idonta tana kallonsa ta hadiye kukan da take ta jinginar da kanta kan shoulder dinsa.

Umma na kallon Kamila cikin fada tace “Magana nake maki kika kauda kai” Kamila dai danna wayarta kawai yake, Umma tace “Ke yanzu kina nufin ban isa in gaya maki kiji ba? Zaman gidan nan yafi maki ki koma dakinki kike nufi? To wai ma uwar me kike tsinana min a nan da kika zo kika jaɓe min?” A fusace Kamila tace “Umma ni wallahi baxan koma in zauna da manemin mata ba, baxan iya ba wallahi” Umma ta buda baki tace “Duk da baki san yana neman mata ba sai yanzu Kamila?” Kamila tace “Nace maki yanzu ya fara Umma, don wannan abun da nake gaya maki ko wata biyu ba ayi ba da ya fara… Sannan the worst part of all is that guilty conscience ya sa ya dau zargi ya daura min, kwata kwata na lura yanzu bai yarda da ni ba, ban isa in motsa ko nan da can ba, ba dama yaga wayana yayi ring, to a kan me?” Umma tace “Toh duk ba ruwana da wannan wallahi, tunda har ya kira ki tattara ki koma dakin ki, banda iskanci shekaranku biyu tare baki san yana neman mata ba sai yanzu? Dariya kike son a min a gari ko me? Kina zaune da mijinki lafiya ga arziki sai yanda kika yi da shi amma saboda shaidan na maki ganga a kai shine xaki billo da wannan iskancin? Ko duk matan duniyan yake bi ma ina ruwanki? Balle wannan sharri ne kawai kika masa” Kamila ta mike fuuu ta fice daga dakin a fusace, Umma tace “Wallahi baxaki kwanar min a gidan nan yau ba, maza dau jakarki ki koma dakinki, na gaji da boyeki haka kuma”

Nihad ta dade bata shiga farin cikin da ta shiga a yau ba, a haraban gidan take zaune ita da yayanta bayan sun fito parlon Mami, Farooq dai sai kallonta yake ganin yanda ta kara haske tayi kyau sai dai ta rame sosai, he just can’t wait to go back home and break this amazing news to His stepmom ko xata samu peace of mind, a hankali tace “Ya farooq yanzu Abba baxai yafe min ba? Wallahi i know nothing about all what that has happened to me” Farooq ya wara ido trying his best ya kwantar mata da hankali yace “Xai yafe maki mana Lil sis, amma sai kin zauna lafiya da mijinki, kin masa biyayya… I am assuring you wannan ne kadai zai sa Abba ya yafe maki, don ya gaya min haka” Nihad tayi shiru tana kallonsa, yace “Yea, when i begged him on ur behalf abinda yace min kenan, don haka kiyi kokari ku zauna lafiya, and accept him as ur husband” Hawaye ya cika idonta tace “But shi ma baya sona fa Ya farooq, we don’t like each other” Farooq ya girgiza kai yace “Da baya sonki baxai kawoki har nan gidan iyayensa ba, ke dai ce baki son zaman lafiya Nihad, ko da baya sonki ke ba mace bace, teach him how to love” Hawaye kawai Nihad take bata ce komai ba, Farooq yace “I know it’s hard dear, amma kiyi hakuri, komai xai daidaita wataran, za kuma kiyi farin cikin Kasancewarsa mijinki” Cikin rawan murya tace “Bayan sai yayi ta daga min shoulder saboda yaga suna da kudi” Dariya sosai farooq yayi yace “Ke sanda kika dinga daga masa naki shoulder din a gidanku fa?” Nihad ta hade rai tace “Aa ni ban daga masa shoulder ba, kuma shine sai yayi ta tsokanata” Farooq yace “Toh yanzu dai duk ba wannan ba, all i want from u is to love and accept him Nihad” Nihad dai ta ta6e baki bata ce komai, nasiha sosai Farooq ya dinga mata kuma yawanci duk sun shigeta kadan ne taji baxata iya abinda yace ba, bayan khalil ya basu at least 40min ya fito yayi joining dinsu tare da Mimi, at last dai Driver tare da Noor ne suka maida Nadeeyah gida, Nadeeyan kuma bata damu ba ganin yana da bako, Mimi sai mamakin Nihad take don bata ta6a tunanin tana magana har tayi dariya haka ba, shi dai Khalil sai dai ya kalleta ta gefen ido jefi jefi, sai da aka kira sallah sannan Khalil suka shiga ciki su yi alwala farooq before going to mosque, Nihad da Mimi suka koma parlon Mami, Bilkisu ta kawo abincin farooq nan parlon Mami ta ajiye ta fita, Mimi ta kalli Mami tace “Mami yayanmu yace in kai masa can dakinsa” Mami tace “Toh kai masu can din” Mimi ta mike tana kallon Nihad tace “I can’t take this all alone” Nihad da kamar jira take ta tashi da sauri, don dama tun da suka shigo ciki jikinta yayi sanyi duk da ya farooq din ya ce mata ba tafiya zai yi ba amma zuciyarta ya kasa yarda da hakan, Ta dau wani tray din ta bi bayan Mimi zuwa dakin Khalil, Khalil kadai suka tarar cikin dakin, Nihad bata yarda sun hada ido ba ta durkusa ta ajiye abincin hannunta a hankali tana bin dakin da kallo, Mimi tace “Yayanmu ga abincin visitor dinmu” Khalil yace “Wani visitor?” Mimi ta mike tana kallonsa, Nihad dai ta kasa tashi daga durkushen da tayi a kasa ita ma tana kallonsa babu ko kiftawa…. a takaice khalil yace “Ai ya tafi” Nihad bata san sanda ta zauna nan kasan tiles ta fashe da wani kuka kamar yar yarinya ba, Khalil na kallon Mimi yace “Go and make me coffee” Mimi ita ma jikinta yayi sanyi, but he should have at least say even a goodbye mana, juyawa tayi a hankali ta fita daga dakin ta kulle kofar….

46

Mikewa Khalil yayi ya tafi har bakin kofa ya tsaya ya rungume hannu yana kallon yanda take kuka, calmly yace “In da gaske kina son bin sa me yasa tun zuwansa baki ce masa xaki bi sa ba kika zo nan kina min kukan munafurci, tunda kinsan tafiya zai yi ba nan zai kwana ba” Nihad ta hadiye kukan da take ta daga kai tana kallonsa fuska daure, can ta mike tsaye tace “Ina ruwanka da ni? Kaga dai ba ruwana da kai a gidan nan, don yayana yace in daina kulaka duk abinda xaka min, kuma ni dai naji maganarsa, don haka kai ma ka fita harkata because bana son inyi disobeying yayana, idan baxa ka iya cewa inyi hakuri ba dole sai ka min maganan” ta karasa maganar kamar xata fashe da sabon kuka, kallon bakinta kawai yake, can yace “Ohk yace ki daina kulani kenan?” Tace “Ehh, kuma ko kana daga min shoulder dinka baxan san kana yi ba tunda ba ruwana da kai, I will pretend I don’t know” Tana kai wa nan ta nufosa fuska daure tace “Ka matsa min ni in fita” ita haushinta maimakon yace tayi hakuri shine yake neman tsokanarta kuma, Yace “Aa bari dai a baki kudin mota ki bi sa kawai, ai yana nan Abuja bai yi nisa ba” Wani kallo ta dinga masa, ya sa hannu cikin aljihun 3 quarter din jikinsa ya ciro 100 dollar ya mika mata yana kallonta, ta dinga kallon kudin sai kuma ta kwace ta cukuikuye ta jefar kasa, tana kallonsa da kyau tace “Kudin da ba naka ba” Kallonta ya tsaya yi baki bude, can yace “Kinsan hukunci warce ke ma namiji rashin kunya, namijin ma wanda aka aura mata daga gidansu?” Ta wani kallesa tace “Ohh dama kai mijina ne? Ai ban san ina da miji ba, kuma ai shi namiji baya neman tsokanar mace” Jin yayi shiru bai ce mata komai ba ta dauke kai ta turo baki, a hankali ya kai hannu ya kashe switch din dakin ta juya da sauri ganin duhu ya gauraye ko ina sai ɗan hasken screen din Iphone dinsa da ya ajiye saman gado, taji kuma yana sa makulli a kofa, komawa baya tayi a tsorace tana zaro ido tace “Meye haka kake yi?” Ba abinda ta ji yace mata, Ganin he is advancing toward her ta fara komawa baya da sauri cikin rikicewa tana cewa “Wayyo don girman Allah kayi hakuri, duk abinda na fada ba da kai nake ba don Allah kayi hakuri, dama yayana yace in daina maka rashin kunya kuma na daina tun….” Wani kara tayi a tsorace jin saura kadan ta fada saman gado don bata san har ta iso wajen gadon ba, zata tashi da sauri ya mayar da ita ta fada kan gadon, zaro ido tayi a mugun tsorace ganin he just lied directly on her, cikin rawan murya ko ina na jikinta na ɓari tace “Don girman Allah kayi hakuri, wallahi baxan sake maka rashin kunya ba har abada, kaji na rantse…” Gaba daya ta gigice tana kokarin turasa amma ta kasa, cause his weight is out of the world, nan kuma ba duk weight din nasa ya sakar mata ba, ta fashe masa da kuka tana sauke numfashi da kyar ga kamshinsa da ya cika ko wani breathing dinta, yayi kasa da murya still adjusting on her yace “Baki san kina da miji ba ko?” Cikin kuka tace “Wallahi na sani, kawai wasa nake maka, don Allah ka yafe min kayi hakuri baxan kara ba…. Wallahi numfashina zai iya daukewa” a hankali yace “Ya dauke mana” Bata san sanda tayi wrapping hannunta a bayansa tana kuka sosai tace “My chest is paining me plss” ai ko ya lumshe ido ya kara sakar mata weight hakan da tayi masa, as if he is going to sleep, sae kuma yayi placing forehead dinsa kan nata, joining his nose directly with hers, cike da karfin hali tace “I am sorry plsss” murda kofar dakin aka yi, yayi brushing lips dinsu ya mike da sauri ya sauka saman gadon, Nihad ta ja wani numfashin wahala ta mike da sauri, jikinta na rawa ta silalo kasa hawaye na sauka idonta, ya tafi gun switch din dakin ya kunna, ya fara dube duben Jallabiyarsa a dakin ya dauka ya daura kan kayan jikinsa sannan ya tafi ya bude kofar dakin, Mimi dai sai bin su take da ido ya amshi cup din hannunta da sauri yace “Thank you dear… Zata bi yayanta inda ya tafi shine na kulle kofar har ki zo, may be u can tell her not to” Nihad dai ta kasa dago kanta daga inda take durkushe a kasa har sannan bata ji kirjinta ya dawo dai dai ba, ga wani bugawa da zuciyarta yake alamar ba karamin tsorata tayi ba, Mimi ta karasa ciki ta durkusa gabanta soothingly tace “Kiyi hakuri, tunda yasan gidan definitely zai dinga zuwa wajenki ai, so ba sai kince zaki bi sa ba” Nihad taki yarda ta kalleta kamar munafuka, Khalil dake tsaye bakin kofa yace “Kawai ki tafi ki kyaleta idan ta gama kukan sai ta fita….” Zumbur Nihad ta mike har sai da ta ba Mimi tsoro, Mimi ta mike tana kallonta ganin she looks so afraid tace “Are you alright Neehad?” Nihad tayi karfin halin gyada mata kai, Mimi tace “Toh mu tafi” Tana makale bayan Mimi suka nufi kofa, taki yarda ta kalli inda yake tsaye, ya bi ta da ido har suka fita sannan yayi wani murmushi ya kulle kofarsa… Duk zaman da Nihad tayi part din Mami bayan sun koma da Mimi she is so silent duk da dama can ba wai tana magana bane amma na yanxu yayi worst, gaba daya ta kasa cire abinda yayi mata a zuciyarta, abincin ma kasa ci tayi wai ta koshi, Mimi duk tunaninta ai tafiyar farooq ne ya sa ta zama haka, shi yasa ma bata yi bothering dinta ba. Wajen karfe tara Khalil ya shigo parlon wearing on his pajamas, sai da gaban Nihad ya fadi ganinsa da tayi taki yarda kuma su hada ido, yana kallon Mimi yace “Mami na ciki?” Mimi tace “Aa tana downstairs tun dazu” Yace “Ohk, ni bani da abinci yau a gidan kenan?” Mimi ta ɗan zaro ido tace “Yayanmu wanda muka kai maka daki fa?” Yace “I called Noor ta fita da shi ban ci ba, ai wannan yayi yawa sosai” Mimi tace “Ohk sorry pls, should i get you another one now?” Yace “Yeahh, but ba nan zaki kawo min ba, and ki ɗan kara hada min irin wannan coffeen da kika yi min” Sosai gaban Nihad ya fadi da ta lura Mimi fita zata yi daga parlon, sai zazzare ido take uwa warce tayi ma sarki karya, Mimi ta dau after dress dinta ta daura kan sleeping dress din jikinta tace “I am coming Nihad” Nihad was shocked and confused on what to do, haba ai bata san sanda ta mike da sauri xata ce mata tana son bin ta amma tuni Mimi har ya fita, kamar munafuka ta fara tafiya zuwa kofa, Khalil dake kallonta yace “Kee” Ta tsaya a tsorace ta kallesa kamar zata yi kuka tace “Ni rakata zan yi” Bata jira me xai ce ba ta karasa kofar da gudu ta bude ta shige next parlor amma taga Mimi har ta fice daga nan ma ta kulle kofar, bin bayanta Khalil yayi tana ganin haka ta kwasa a guje ko kusa da kofar bata kai ba ta take dogon hijab din dake jikinta na Mimi, sai ga tim a kasa ta zaro ido tana yarfe hannu, dai dai nan aka bude kofar parlon, Mami ta koma baya tana kallonta tace “Subhanallah, garin yaya?” Nihad ta mike tsaye da sauri xuciyarta na bugawa tace “Zan tafi in kwanta ne, shine na fadu” tuni khalil ya koma daya parlon, Mami na kallonta tace “Toh ki dinga yi a hankali, Hope you are not injured?” Ta gyada mata kai da sauri, Mami tace “Toh sai da safe” Nihad tayi saurin fita daga parlon, Mami ta bi ta da kallo, sai kuma ta karasa next parlor din, zaune ta tadda khalil yana waya, the way he is talking on the phone xaka yi zata ya kai minti talatin yana wayar, Mami tayi wucewarta cikin bedroom dinta. Sai da Nihad ta shiga dakin da take taji knees dinta na mata zafi, ta zauna gefen gado tana dubawa taga ba ciwo amma zafi yake mata, da kyar ta samu ta shiga bandaki tayi wanka ta fito, ta saka kayan barci bayan ta shafa turare ta kwanta saman gado tayi lamo, incident din daxu ne ya dinga dawo mata, but what’s the meaning of that?? Lokaci daya ta kawar da tunanin ta jawo wayarta a hankali tana dubawa, taga miss calls din Ayman har biyu, zata ajiye wayar sai ga wani kiran nasa, dagawa tayi ta rufe har kanta da duvet, ko minti goma basu yi da fara wayan ba taji an kwankwasa kofar dakin, da sauri ta mike zaune ta katse wayar tana kallon kofar, aka sake Knocking sauka tayi a hankali ta tafi gun kofar tace “Waye?” Mimi tace “It’s me” Daga haka Mimi ta bude tana kallonta tace “Mami said i should ask if u are okay?” Nihad tace “Sure, thank you” Mimi tace “Ohk good night” Nihad ta dan mata murmushi ta gyada kai kawai, daga haka Mimi ta juya ta bar wajen Nihad ta kulle kofarta ta koma ta kwanta. Washegari Khalil na tare da Mami a parlonta Aunty Hassana ta shigo da sallama, Khalil na jin muryarta yayi saurin kara waya a kunne yana maganan da babu shi, Mami dai bata ce komai ba, har Aunty Hassana ta karaso, shi kuma ya mike ya fice daga parlon still making fake call, Mami tace “Mun tashi lafiya Hajiya Hassana” Aunty Hassana da ta bi sa da kallon gefen ido tayi saurin cewa “Lafiya lau, ya yaran?” Mami tace “Alhamdulillah, ya su Sajidah” Aunty Hassana tace “Toh ni naji kin min shiru, baki ce ga abinda ake ciki ba, don last week naji Abbansu yace xa a kai kudin auren yaron nan, to mu ba wani shirye shiryen da xa muyi a nan ne?” Mami tace “Ai gobe ne idan Allah ya kai mu” Aunty Hassana tayi shiru tana kallonta da mamaki, can tace “Gobe goben nan amma ba labari?” Mami tace “Ni ai na zata Amina ta gaya maki don muna tare da ita a parlon Yallabai ya saka lokacin, and that was last week” Aunty Hassana ta hade rai tace “Saboda Amina ce tafi kusanci da ni ko me?” Mami tace “Ba dai ta yanda xa ayi kice baki ji daga bakinta ba Hassana, ko ita bata gaya maki ba ai yaci yayan naki ya gaya maki, yaushe rabon mu hadu dake cikin gidan nan balle maganar ya hadu mu? Ai mun kwana biyu bamu hadu ba” Aunty Hassana tace “Gaskiya ne, kya yaɓa min magana son ranki ai, ba laifin ki bane” Bude baki Mami tayi tana kallonta tace “Meye abun ɓacin rai a zancena Hassana?” Tuni Daga Hassana ta mike fuuu ta fice, tana komawa bangarenta ta dau waya ta hau kiran kawarta Chamo, ta yaya za ace gobe xa akai kudi ita da ta zata Mami zata ce mata an daga lokacin kai kudin, Chamo na dagawa Aunty Hassana tace “Ke gobe fa naji ana cewa xa a kai kudin auren, yaya haka?” Chamo tace “Toh in kai kudin aure sai aka yi yaya? Baki ta6a ganin inda aka fasa aure ranan daurin auren bayan an tara jama’a ba?” Aunty Hassana tace “Haka ne, to amma idan kuma hakan bata kasance ba fa? Ai risk ne wannan Chamo, kamata yayi ko kudin ma kar a kai balle a saida rana” Chamo tace “Ke dadina dake gajen hakuri wallahi, sai kace yau aka saba maki aiki kiga aikin ya ci Hassana?” Aunty Hassana ta sauke ajiyar xuciya tace “Aa ba haka bane Chamo, ni dai kawai ina ga ba sai an wani je ga ranan daurin aure a fasa ba, kawai tun ba aje ko ina ba a fasa gaskiya hankali na zai fi kwanciya” Chamo tace “Toh ai abinda baki sani Malam yace min dole ne xa a kai kudin amma a banza tunda ba auren za ayi ba, daga sanda aka kai kudin matsaloli xa su dinga billowa daga both part har aure ya ruguje daga karshe” Aunty Hassana dai tayi shiru don ita fa bata gamsu ba, tasan karkari aka kai kudin nan a sa wata daya in dai yayanta ne, can tace “Toh daga ina ne xa su bukaci a fasa auren Chamo?” Chamo tace “Shi da kansa Khalil din xai ce ya fasa, ke ni bari kiji wllh malamin ma ce min yayi bai ga auren ba kwata kwata, xa dai ayi ta kashe kashen kudi, a siya wancan a siya wannan na biki amma fa ba auren” Aunty Hassana tace “Toh yanzu Sajidar ce ko farhana?” Aunty Hassana tace “Toh ai kya bari maganar auren ya ruguje tukunna ki kawo wannan ko?” Aunty Hassana tace “Toh shikenan, sannan abu na karshe kinsan ɗan iskan yaron nan ko gaisheni ya daina yi a gidan nan?? Wallahi tun da ya dawo ga maciji bai hadani da shi balle yarana, iyaka yayi da kanninsa ko Hanan” Chamo tace “Shi khalil din??” Aunty Hassana tace “Wallahi nake gaya maki” Chamo tace “Wannan ai abu ne me sauki, xan kira malamin in gaya masa xa a san yanda xa ayi….” Aunty Hassana tace “Toh Nagode, za mu yi magana zuwa anjima” Daga haka ta katse wayar tana ta tunane tunane, ita wallahi ko kudin auren ma bata son ya shiga hannunsu, don tasan ba amsa xa ayi ba idan aka fasa auren ai, ga kudi ba na wasa ba xa a kai ta sani. Throughout ranan Nihad taki fito dakinta don ko by mistake bata son haduwa da Khalil, wani sabon tsoronsa take ji har cikin zuciyarta, saboda yanda ta sa abinda yayi mata jiya da daddare a ranta sai da tayi mafarkinsa cikin dare, wajen karfe shidda na yamma Mami ta shigo dakin nata tana tsaye bakin kofa tace “Why are you inside throughout?” Nihad ta ɗan yi yake tace “Aa ina kallo a waya ne” Mami tace “Ohk, ga can takalmi Noor ta siya har da ke” Nihad ta dinga kallon Mami jin wai Noor, ko dai Mimi take son cewa, da sauri tace “Toh Mami, xan fito yanzu” Mami ta juya ta fita, a hankali Nihad ta mike ta dau mayafinta sannan ta fito daga dakin. Tana shiga parlon Mami taga Mimi zaune tana operating laptop dinta, Mimi tace “Kinyi scarce yau fa, hope you know you are having lectures tomorrow” Nihad ta ɗan yi murmushi kawai ta zauna ta gyada mata kai, Mimi ta dau takalmi ta mika ma Nihad tace “Noor got this for us all, same color same design” Nihad ta amsa tana kallon takalmin tace “I appreciate it” bude kofar parlon aka yi Khalil ya shigo, Mimi tace “Awnn Yayanmu you look good daga wajen Sis Nadeeyah kake ko?” Yace “Yeah, ina Mami?” Tace “She went in not too long” Ya ɗan kalli Nihad suka hada ido, ta ɗan daburce tace “erm… Good evening”  Yace “Evening” Daga haka ya nufi dakin Mami yana murmushi, Mimi ta wara ido tace “That’s sweet of u Nihad, kuma naji dadi da kika ji maganata” Nihad dai bata ce komai ba, can kuma dai ta dau takalminta tace “Zan je inyi sallah, it’s almost magrib” Mimi tace “Ohk” Daga haka Nihad ta mike ta fice daga parlon don bata ma son ya fito ya sameta. Tare Khalil da Mami suka tafi bangaren Abba ta dalilin kiranta da Abban ya aika khalil yayi, Mami ta gaishesa bayan sun samesa a parlor tare da Aunty Hassana, Mami tace “How was the trip?” Yace “Alhamdulillah” Mami tace “I was thinking ba sai ka dawo ba, representative dinka kawai zaka aika goben” Abban ya ajiye takardun hannunsa yace “Ni ba saboda shi na dawo ba ai, kuma i think gobe xan yi tafiya portharcourt…” Mami tace “Allah ya kai mu” Shi dai khalil na zaune nesa da su yana danna wayarsa, Abba na kallon Mami yace “Dama i want to confirm if ke ce ke aikosa ya zo nan yayi min rashin da’a” Aunty Hassana ta sauke wani ajiyar xuciya, Mami ta kalli khalil da sauri, Khalil ya ajiye wayarsa yace “But i see nothing wrong don na tambayi hakkina Abba, i am asking you for my property, i seriously need them” Abba ya mike yace “Toh daga yau ka sake shigo min nan da wannan maganar i am promising u i won’t take it likely with you….. Nace baxan bayar ba kuma i mean it” da mamaki Khalil yace “But why? I have all right to ask Abba” cike da damuwa Mami tace “Me yasa idan na maka magana baka ji Khalil? Me yasa kake daukan maganata for granted pls” Khalil ya mike yana jin ransa na ɓaci yace “Mami to saboda me za a rike min abubuwana akan laifin da ban aikata ba? Akan something i knew nothing about, why???” Aunty Hassana ta bude baki tace “Akan laifin da baka aikata ba? Ehh lallai ka cika mara kunya kuma fitsararre, Sannan da ka mike a zabure haka dukan uban naka za kayi ko yaya?” A fusace yace “Kee ni ban sa bakinki ba Hajiya, babu ruwanki da issue dina da mahaifina, stay in ur lane and stay out of family issues da bai shafe ki ba” Aunty Hassana ta fashe da kuka ta rufe fuskarta da gefen gyalenta tana girgiza kai, sake baki Abba yayi yana kallon Khalil, ya juya ya nufi kofa ya fice daga parlon fuuu, Mami dai ta ma rasa abun cewa, wato khalil baxai ta6a canzawa ba kenan, Abba ya hau kai komo a parlon fuskarsa a murtuke, cike da karfin hali Mami na kallon Aunty Hassana tace “Kiyi hakuri Hassana zan je in….” Wani tsawa ta daka ma Mami tace “Bana bukata, duk ba ke ke sa shi yake raina mu ba, kiri kiri yaron nan ya daina gaishe da ni da Amina a gidan nan, yaron da a haife na haifesa, yanzu kuma rashin kunyar tasa da fitsara har ya kai kan ubansa, kayi laifi amma kafi kowa bakin magana, miliyan dari takwas wasa ne yanzu? An daga maka kafa albarkacin tausasa yaya da muke tayi ka dawo gida amma kace mune makiyanka? Yanzu da nawa ɗan nan zai yarda da abinda khalil yayi min yanzu? Ba tashin hankali xa ayi ba kenan??” Abba yace “Ki bar zancen nan, i know how to handle it, ke Fatima yarinyar da kika kawo gidan nan without my knowledge wacece? Kuma daga ina take??” Mami ta kallesa da mamaki, sai kuma tace “Sauran yaran da ake kawowa gidan nan su karaci zamansu su wuce ka ta6a tambayar daga inda suke ko wa ya kawosu Yallabai? Yaran da har kudin makaranta kai ke biya masu sai wannan da ko biyar dinka babu a makarantar da aka biya mata?” Hassana ta mike a fusace tace “Kar ki kuskura kice zaki masa magana yanda kika ga dama a gabana Fatima, ke kiyi ɗan ki yayi, to baku isa ba, kuma wallahi baxan dauka ba don kiji in gaya maki” Mami ta daga kai tana kallonta, can ta kalli Abba tace “To er ɗan uwana ne, kuma karatu ya kawota gidan….” Mami na fadin haka ta mike ta fice daga parlon, Aunty Hassana tace “Toh wa yaki zamanta a gidan nan dama? Abinda Allah kadai yasan ladan ciyar da ɗan mutum, ai mu bamu ki tayi ta zama har abada ba ma, kawai damuwar mu kamar yanda na gaya maka Yaya, kwanaki can wani videon yarinya tsirara na ta yawo a kafofin sada zumunta, to ita ce yarinyar” Abba na kallonta da kyau yace “Ke kin tabbata Hassana?” Aunty Hassana tace “Zan maka karya ne yaya? Wallahi ita ce yara duk sun shaida mu ma kuma mun shaida, babu amfanin nuna video din ne yanzu da sai in nuna maka, sannan tun da yarinyar ta zo gidan nan bata gaida mu, sai dai mu wuce ta wuce saboda ta isa” Abba ya dinga zaga parlon yana nazari bai dai ce komai ba, ran Aunty Hassana yayi fari tass don duk hanyar da zata kuntata ma Mami nemansa take ido rufe…..

Mumy ce ta shigo bangaren Umma ta sameta a parlor tare da Kamila, Mumy tace “Dama kina gidan nan Kamila?” Da sauri Umma ta amshe tace “Daxu ta zo, yanzu ma mijin take jira wai” Mumy tace “Ohk, dama tambayarki zanyi kinji daga Nihal kuwa? Tun jiya bana samunta a waya wallahi” Da damuwa Umma tace “Yanzu ma abinda muke jajantawa kenan, har na gaji da kiran wayartata wallahi, na kira farooq yace min yana Abuja amma gobe zai shiga kaduna sai ya karasa Zaria yaga ko lafiya” Mumy tace “Toh duk yanda aka yi sace mata wayar aka yi” Kamila tace “Nima abinda nace kenan, amma Umma duk ta daga hankalinta, babu tantama an dauke wayar ne” Umma tace “Sai ta rasa wayar da xata kira mu da shi a kawayenta tace an dauke mata waya?” Mumy tace “In sha Allahu lafiya lau take” Umma tace “Toh Allah ya sa” Juyawa Mumy tayi ta fita daga parlon, Kamila tace “Ke abu indai ya shafi Nihal duk ki daga hankalinki ki daga na wasu, ni gashi na kawo maki damuwata ko bin ta kaina baki yi ba sai korata kike in bar gidan nan tun jiya” ko kulata Umma bata yi ba ta mike ta fita daga parlon.

47

Washegari wajen karfe tara na safe kiran Farooq ya shigo wayar khalil dake bacci, bude ido yayi a hankali ya jawo wayar yana kallon screen din, ganin Farooq ne ya daga ya kai kunne, bayan sun gaisa Farooq yace “Pls kwanakin baya kace min kuna gaisawa da Nihal, when last ku ka yi magana da ita on phone?” Khalil ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Not too long mun yi magana da ita, ta turo min waec result, birth certificate, i mean all those stuffs saboda makarantar da nake nema ma er uwarta….” Farooq yace “When was that pls?” Khalil yace “It was just last week, Though bana iya reaching dinta a line dina so i used my other line shine na kirata muka yi magana, hope all is well?” Farooq yace “For 2 days yanzu ba a samunta a waya, i just arrived zaria but bani da contact din any of her Coursemate as i am talking to you now….” Khalil ya mike zaune yace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, or did she lost the phone?” Farooq yace “Ko ma haka ne ai ya kamata tayi using ko wayar Coursemate dinta ta kira ta sanar, her problem is that she neva get close or mingle with frnds” Khalil yace “Haka ne…. I am hoping she is fine in sha Allah” Farooq yace “Shikenan, sae mun yi magana, thank you” Khalil yace “In sha Allah… Nima xan yi ta trying line dinta” daga haka suka yi sallama, khalil yayi amfani da daya wayarsa yayi dialing numberta don bata yi unblocking dinsa ba har sannan daga main line dinsa, shima yaji wayar a kashe, he felt a bit tensed, then what happened to her? Tambayar da yayi ma kansa kenan, after trying her line for like 3 times ya ajiye wayar a hankali ya sauka daga saman gadon ya shiga bandaki. Har kusan karfe sha biyu Khalil na trying line din Nihal also, he is just restless, and he prays she is okay… Yana zaune parlon Mami wajen karfe uku Mami ta fito daga dakinta ganinsa tace “Dama kana nan har yanzu?” yace “Eh” Mami tace “Wai har sun kai kudin, ai kunyi magana da ita ko?” Khalil ya daga kai da sauri yace “Ohh really, ni nama manta…” Mami tayi masa wani kallo da mamaki tace “Ka manta? I don’t understand ka manta” Yace “Wallahi i am disorganized ne gaba daya yau Mami” Mami tace “Me ya faru?” Da har zai gaya ma Mami what is happening sai kuma ya fasa cause bai san ta sigar da zata dau lamarin ba, bai san daga wani perspective zata yi viewing issue din ba, kar tayi tunanin gidan ba tarbiya or something like that, Mami tace “Kayi shiru” Ya sauke ajiyar zuciya yace “I am having a terrible headache tun dazu” Da damuwa Mami tace “Subhanallah, toh Allah ya sauwake, ka sha magani?” Yace “Yanzu xan je in sha” Tace “Do so immediately pls, ko da abinda kake so a girka maka?” Yace “No, i am okay” daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita other parlor din, dai dai nan Mimi da Nihad suka bude kofar parlon dawowarsu kenan daga makaranta, Hijab ne har kasa jikin Nihad with Nikab, she looks so cute in them, Mimi tace “Yayanmu ina yini” yace “Lafiya lau” Nihad ta sunkuyar da kai ba tare da ta kallesa ba slowly tace “Ina yini” ya ɗan kalleta yace “Lafiya lau” Daga haka ya nufi kofa ya fita daga parlon, suka karasa can parlon, Mimi ta zauna saman kujera looking very tired ta gaida Mami, Nihad ma ta gaisheta, Mami tace “Sannunku da zuwa” Mimi tace “Mami Noor bata dawo ba har yanzu?” Mami tace “Tana gidansu Nadeeyah, kinsan yau aka kai kudin” Mimi ta zaro ido tace “Seriously? Yaushe aka sa auren?” Mami tace “4 weeks in sha Allah” Mimi tace “Awwnn maa sha Allah, Allah Ubangiji ya nuna mana lafiya, nasan it won’t exceed that… I am so happy for the love birds” Mami dai ta juya zuwa dakinta ta dalilin wayarta dake ring, Nihad dake ta kallon Mimi ta mike daga saman Carpet da ta zauna, ta dawo gefenta ta cire Nikab din fuskarta tana kallonta tace “Who is getting married?” Mimi ta wara ido tace “I thought i told u yesterday, Yayanmu is getting hitched, yau aka kai kudin aurensa with sister Nadeeyah….” Tana murmushi ta kare maganar, Kallonta Nihad take babu ko kiftawa, Mimi tace “U remember me telling you?” Nihad ta sauke idonta tace “Sure” Tashi tayi tace “Xan je inyi wanka” Mimi ma ta mike tace “I too, i need warm shower” Tuni Nihad ta rigata ficewa daga parlon ta nufi dakin da take, ta fi minti 2 tsaye bakin kofar dakin bayan ta shiga ciki, can ta karasa inside of the room ta zauna gefen gado a hankali…. Khalil na komawa dakinsa yaga miss calls din Nadeeyah har hudu a babban wayarsa, ya zaune gefen gadon ya jingina bayansa da pillow yayi dialing numberta, yana fara ringing ta daga, a hankali yace “How are you Nadeeyah?” Kamar xata yi kuka tace “Why ain’t you picking ur calls, ina ta kiranka no response” Yace “Bana kusa ne” Tace “Ta yaya zaka ce min baka kusa, i called almost 2 hours ago” yayi kasa da murya yace “Kina da son korafi da yawa Nadeeyah, why?” shiru tayi, yace “Kinsan baxan ƙi daga kiranki just like that ba ai, so why not believe bana kusa and have rest of mind” Nan ma bata ce komai ba, yace “Hello, nasan kina ji na” a hankali tace “Shikenan, Allah ya baka hakuri, only called to say Hi, na ji ka shiru all through” yace “Ina parlon Mami tun daxu, i am sorry i missed your call, it wasn’t intentional…..” Ta gyada masa kai kawai bata ce komai ba, yayi murmushi sanin da kyar if she is not in tears already, yace “Karfe biyar xan zo in sha Allah, ki min wannan drink din da pancake me dadi da kika min the other day, immediately after Magrib kuma we will be going out for shopping” A hankali tace “Ohk” Calmly yace “I love you” Tana goge hawayen idonta tace “Love you too” Yayi murmushi kawai ya katse wayar. Khalil ya sake trying wayar Nihal for the countless time but a kashe, as at 2pm dazu ya kira farooq yaji if there is any positive news, farooq yace har yanzu ba labari, ya ma je har department dinsu wajen malaman, and an dubo few of her Coursemates sunce ai tun jiya bata yi attending lectures ba, wannan batu ya sa hankalin Khalil ya tashi. Biyar saura minti sha biyar Khalil ya shirya zai je wajen Nadeeyah kamar yanda yayi mata alkawari, yana fita ya nufi bangaren Mami xai je yayi mata sallama, a hanya ya hadu da Mimi tace “Yauwa yayanmu pls kana da paracetamol a dakinka?” Yace “Check my room, who is taking paracetamol?” Tace “Neehad ce tace min kanta na ciwo, so i want to give her to take” Yace “Where is she?” Tace “tana daki” Bai kuma ce mata komai ba ya karasa parlon Mami ya zauna, after like 15 minutes Mimi ta dawo parlon ya daga kai yana kallonta, tace “I have given her ta sha, yayanmu fita zaka yi kayi dropping dina gidansu frnd dita Aziza pls? Today is her birthday….” Yace “Aa, ki je driver ya kai ki” Tace “Ohk, tot u were going out” Ta figi jakarta don dama ta shirya tace “Bye” Yace “Wait kin gaya ma Mami?” Tace “Yeah i told her kafin su fita da Mom, i will be back in sha Allah after Magrib” Yace “Ohk, stay safe” murmushi tayi masa ta gyada kai sannan ta fita da sauri daga parlon, wayarsa dake hannunsa ya fara ring ya duba ganin farooq ne ya daga da sauri, farooq yace “I just reached her minutes ago, the stupid girl wai ta raka wata roommate dinta garinsu bata da lafiya a nan Zaria, i still don’t get dalilin da yasa bayan ta rakata bata dawo a ranan ba, wai kuma babu wuta and bata je da power bank ba….” Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace “Toh Alhamdulillah, but you have to take it easy pls, kasan ba halinta bane, baxata zauna haka kawai babu dalili a can ba” Farooq yace “That’s so stupid of her, tasan mutane nawa ta daga ma hankali a can gida, har yanzu maganar da nake maka bamu sanar ma Abba ba, we don’t even have the courage to do so, and God being so kind dama basu waya da shi kamar yanda yake da Nihad, sai in tana bukatar abu suke waya da shi” Khalil yace “Take it easy pls, it’s well in sha Allah” Farooq yayi masa sallama ya katse wayar, sauke ajiyar zuciya Khalil yayi don sai yanzu yaji hankalinsa ya kwanta, Nihal have a special place in his heart cause she’s one of the kindest soul he have ever met, ita ma baxai taɓa mance kindness dinta toward him ba, dialing numberta yayi ya fara ring, bayan some seconds ta daga, a hankali tace “Hello” Khalil yace “Me yasa kika yi abinda kika yi Nihal?” Ta fashe da kuka kamar jira take bata dai ce komai ba, yace “Are you okay?” Ta gyada masa kai kamar yana ganinta amma ta kasa cewa komai, yace “Nihal” tayi karfin halin cewa “Na’am” Yace “Don’t try that again pls, idan ma zaki je wani waje ki sanar before doing so, ur parents trusted you so well shi yasa har suka bari kika yi nesa da su kike karatu, ita er uwarki me gathering bad friends ai kinga they didn’t allow her move an inch from kano” Nihal dai kuka kawai take bata ce komai ba, a hankali yace “Kin ji abinda nace maki?” cikin rawan murya tace “In sha Allah” yace “Take care of ur self pls” a hankali tace “Ka gaishe min da Nihad” Yace “I will in sha Allah” Daga haka ya katse wayar ya mike ya fita daga parlon Mami, dakin da Nihad take ya nufa ya bude kofar dakin gently, kwance ya sameta ta rufe har kanta da duvet, ya karasa bakin gadon ya janye duvet din a hankali yana kallonta, she is just wearing a short gown, ta bude ido da sauri, suna hada ido ta hade rai ta juya, yace “Ni kika ma wannan kallon?” Ta fashe da kuka ta sake juyowa tace “Ni ba da kai nake ba” Yace “Tashi zaune” Ba musu ta mike zaune, zai cire duvet din daga jikinta ta rike da sauri tace “Ni ban sa kaya ba” ya daure fuska yace “Sake” A hankali ta sake ya cire ya mayar gefe, ta sunkuyar da kanta, yana kallonta yace “What’s wrong with you?” Taki ce masa komai, sai kuma hawaye ya hau zuba idonta, Kallonta kawai yake ba ko kiftawa, ta hade kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, bai san sanda ya zauna gefenta ba ya dagota da mamaki yace “Are you okay?” Kuka kawai take ta ki cewa komai, ta sauke kafanta daga saman gadon zata sauka ya jawota ta fado jikinsa, sai ta kara sautin kukanta, ya rungumeta yana kallonta amma bai sake ce mata komai ba, ta gaji don kanta tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya tana shaƙar kamshinsa, for almost 10 minutes suna nan a haka, jin ta sakar masa jikinta gaba daya tana sauke numfashi a hankali ya sunkuya yana kallon fuskarta, bacci yaga tana yi, ya dinga kallon lips dinta for almost a minute, sai kuma ya dago a hankali ya jinginar da kansa jikin gadon ya lumshe idonsa…. Da sauri khalil ya bude ido ta dalilin wayarsa da ke ring, he realized he just slept off also, shi da baya baccin rana balle na yamma, ya kalli Nihad dake kirjinsa tana ta bacci kamar warce ta samu lafiyayyen katifa, ya ciro wayarsa da sauri jin ana sake kiransa, yaga Nadeeyah ce, kallon agogon wayar yayi yaga har shidda da minti arba’in just few minutes to magrib, he was shocked and surprise at the same time, ya sake kallon Nihad sai bai daga wayar ba har ya katse, still Nadeeyah ta sake kira, Nihad ta bude idonta da sauri, dagowa tayi tana kallonsa, ya wani hade rai, ta fara kalle kalle kamar munafuka, sai kuma ta matsa daga kusa da shi, mikewa yayi yana rike da wayarsa ya fita daga dakin, sae a sannan ya daga kiran Nadeeyah, a hankali tace “But you said 5pm” Ya sauke wani ajiyar zuciya yace “I am sorry Nadeeyah, i slept off without knowing i did….” Tace “Which means bani da muhimmanci ko?” Ya ɗan hade rai yace “kin fara da korafinki again” a hankali tace “Shikenan, sae anjima” Daga haka ta katse wayar, dakinsa kawai ya wuce ya shiga bandaki…. Wajen karfe tara Khalil na zaune parlon Mami tare da Mimi da Noor, Mimi na basu labari, Nihad ta bude kofar parlon a hankali, duk suka daga kai suna kallonta, can ciki ciki tayi sallama that isn’t audible, gaisuwan ma can ciki tayi Noor dai sai kallonta take, Nihad ta nufi Mimi ta duka gabanta tana kallonta murya can kasa tace “Pls kina da Android charger? I can’t find mine” Mimi tace “Ohk let me check” Tashi tayi Nihad ma ta mike ta bi bayanta Khalil ya bi su da kallo har suka fita daga parlon, Ganin Nihad zata koma dakin da ta fito, Mimi tace “Mu je sai in baki na Bilkisu” Nihad ta bi ta har zuwa bedroom din Bilkisu, Mimi na kallon Bilkisu tace “Pls xaki ɗan mata lending charger dinki” Bilkisu tace “Ohk toh” daga haka ta tashi ta dauko chargern ta ta mika ma Nihad, Nihad ta amsa tace “Thank you” Bilkisu ta mata murmushi tace “My pleasure” Daga haka suka fito daga dakin, Nihad ta wuce dakin da take, Mimi kuma ta koma parlon Mami, tana kallon yayanta da Noor tace “Yauwa as i was saying” Nan ta ci gaba da basu labarin da take kafin ta fita, ganin yanda Khalil ya lumshe ido Mimi tace “Yayanmu you are not listening bacci kake” ya bude ido a hankali yace “I am sleepy” Mimi tace “Labari fa nake baka” Yayi kasa da murya yace “Bacci” Noor ta kallesa tace “When did u start sleeping early?” Mikewa yayi yace “Idan Mami ta shigo ku ce na tafi in kwanta sai da safe” daga haka ya fita daga parlon….

48

Nihad ta fito bandaki kenan taga mutum zaune edge din gado wayarta a hannunsa yana dube duben wayar with full concentration, lokaci daya mamaki da tsoro suka cikata, gashi bata san for how long yake dakin ba don tana dawowa daga amso charger wajen Mimi ta jona wayar sannan ta shiga wanka, tana tafiya a hankali taje inda Hijab dinta yake ta dauka ta saka don towel ne kadai jikinta, ta juya tana kallonsa, she don’t think ya san ta fito daga bandakin ma don gaba daya fa hankalinsa na kan wayarta, tana jan kafa ta tafi can karshen gado ta tsaya tana ɗan leka wayar trying to see what he is doing with it, a kan WhatsApp ta gansa yana duba duk chat dinta da Ayman tun daga farkon sa, sosai taji gabanta ya fadi, and she started thinking of what to do next, though ba wai dirty chat suke da Ayman din ba, but he use to chat romantically sometimes saboda wayayye ne gayen, ta kalli fuskarsa taga babu yabo babu fallasa yana ta scrolling chat din slowly, a hankali Nihad ta nufi kofar dakin gabanta na faduwa ta murda taji a kulle sannan ba makullin a jiki, ta juyo tana kallonsa kamar zata yi kuka, gaba daya hankalinta yayi mugun tashi, har at last ya gama karance kaf chat din ya ajiye wayar staring at the wall still fuskarsa babu yabo babu fallasa, hankalin Nihad ya kara tashi, she wish kofar a bude yake da tuni ta fice ta koma parlon Mami, shi kam for the next 2 minutes bai ko kalleta ba, ko tunanin me yake oho, sai kuma taga ya tashi ya dau wayar ya saka aljihu ya nufi kofa, ta bi sa da kallo har ya isa kofar yana kokarin budewa, da sauri tace “Ina zaka je da waya….” Bata kai karshe ba ya juya ya sauke mata wani lafiyayyen mari a fusace, ta dafe kuncinta da sauri with shock tana kallonsa baki bude, sai a sannan taga idonsa da ya koma kamar garwashi, ya fasa bude kofar ya fixgota ya hadata da bango cikin husky voice yana mata wani mugun kallo yace “I thought iskancin da kika yi a baya ya isheki ai? I thought it was enough for you ashe i was mistaken, ta waya kika ci gaba da iskancinki daga inda kika tsaya….” Nihad ta fashe da kuka sosai tace “Ni ban ta6a iskanci ba, ni ba er iska bace….” Ya daka mata tsawan da ya firgitata yace “Meye ban sani ba a kanki? Tell me, meye ban sani ba akan kazamin rayuwar da kika yi a baya? Idan zaki ma wani karyan baki bi maza ba don baki da kunya har ni za ki ma? Ke din da kika mayar da kanki taxi no garage, leaving home at night and returning back early dawn, kece warce naga kayan maye da Prophylactics a jakarki, what were you doing with them??? bayan haka har alcohol you do take…, bana tunanin akwai hotel ko club din da baki sani ba a garin kano, At times if i think of ur past life i regret my destiny of having to accept ur marriage for the sake of ur parents, i so regret that, ƙyamarki nake don ma ki ji ki sani babu yanda xan yi da aurenki ne, you are not worth being married to me, na fi karfinki ta ko ina, and i can never be comfortable to present you to anybody as someone i am marrying, kwanciyar hankalina kawai shine in dinga kawar da tunanin akwai aure tsakanina da ke, no responsible person will be proud to have u as the mother of his kids….. You have a dirty past, still not considering that shine kike chatting da wani katon banza har kina ce masa you have neva kissed all ur life, telling him no one have ever touched you before, ain’t you ashame of lying? Ke da kika gama rabar da mutuncinki a hotels? Ina ce garin haka ne har aka samu wanda ya maki video ya sakar ma duniya, nasan duk zaman da kike yanzu u are uncomfortable without a man tunda kin riga kin saba, shine kike biye wani namijin da aure a kanki ku ke chatting har da phone calls saboda ke baki san darajan aure ba” Nihad ta daga kai hawaye na sauka idonta tana kallonsa tace “Duk na ji, ka rubuta min takardata ka bani” Ya wani fizgota yana mata mugun kallo yana huci yace “Who are you to tell me what to do?? To baxan bayar ba, idan kin isa ki rubuta ma kanki takardan” Yana fadin haka ya turata har sai da ta kusa faduwa, ya nufi kofa kamar zai tashi sama ya bude kofar ya fice daga dakin. Hajiya Amina na parlonta tare da Aunty Hassana dake cin fruit salad, Hajiya Amina tace “Ke kin ta6a jin inda aka kai kudin aure har dubu dari bakwai, ba wai sadaki ba, sannan a hada da buhunhunan shinkafa? Wallahi abun yayi mugun daure min kai” Aunty Hassana ta ajiye bowl din hannunta tace “Toh ke kuwa ba mayunwata bane, ai ita fatiman ce xata ce a hada da shinkafar, ni fa ko a gyalena batun auren nan, don in dai wannan auren ne wallahi baxa ayi sa ba ina da assurance din hakan, don da dai Khalil yayi aure a waje gwara ya dauwama haka ba aure, in ma duniyanci xai yi shi yafi komai sauki wallahi” Hajiya Amina dai ta tabe baki bata ce komai ba, Aunty Hassana tace “Banda babana ya tsaya shiririta ai shi zai fara auren a gidan, kuma yanzun ma bai baci ba ya dawo shima yayi auren kawai shi ma ayi masa abinda xa ayi masa” Hajiya Amina tace “Ba gobe kika ce yana hanya ba?” Aunty Hassana tace “In sha Allahu kuwa” Hajiya Amina tace “Toh kuwa baxai juri ganin sabon walakancin khalil a gidan nan ba, dama can kinsan ba jituwa suke ba” Aunty Hassana tace “Ai dalilin da yasa na takurasa kenan ya dawo, Babana ne zai raga masa? Sai dai in bani na haifesa ba kuma” Hajiya Amina ta kyalkyale da dariya tace “Yana dawowa ki takura masa ya fiddo mata shi ma a masa auren tunda abun en aure aure ne” Aunty Hassana tace “Ke dai ki zuba ido mana, gwara shi auren zai yi, can kuwa kashe kudin xa ayi a banza babu zancen auren” Sallama aka yi bakin kofar duk suka yi shiru. Umma ce zaune dakinta tana magana da Nihal, Umma tace “Ke in zaki bude baki ki min magana ki bude, meye kuma ana maki magana kiyi ta amsawa mutane ciki ciki, ko baki da lafiya ne dai?” Nihal tace “Ce maki nayi ya turo min daxu” Umma tace “Nawa ya tura maki?” Nihal tace “Dubu hamsin” Umma ta tabe baki tace “Me dubu hamsin xai maki, ko dai baki ce masa kayan abinci xa ki siya ba?” A hankali Nihal tace “Na gaya masa” Shiru Umma tayi, don da Nihad ce ai dubu dari zai saka mata ko fiye da haka, shi sa fa ita bata jin ko dar akan abinda ta aikata, don akan Nihad sun ga abubuwa iri iri a wajen Abba a gidan nan ita da yaranta, haka ya kwashi kudi ya kai ta Maryam Abatcha dab da bikin Kamila bayan ga kayan gadon da kamila ta zaba ya ki siya mata wai yayi kudi, wanda a lokacin ko dubu dari takwas kayan gadon basu yi ba, tana ji tana gani kuma ya tura mata Nihal dinta Zaria, kuma ko nunawa a fuska Umman bata yi ba balle a gane taji haushi, Umma tace “Toh ai Shikenan, kawai ki kira farooq ko Usman su kara maki, ita er son ma ko biyar ta daina samu ai yanzu, wa ma yasan isilinta” Nihal dai bata ce komai ba, Umma tace “Ke in fa baki da lafiya ne nasanki da zurfin ciki ki dawo gida a maki treatment kar kije ki jaza min jaraba, lafiyarki kuwa?” Nihal tace “Lafiya ta kalau ni” Umma tace “Toh ai shikenan, Kina da labarin Nihad?” Nihal ta girgiza kai tace “Aa” Umma tace “Allah sarki, kamar ba ayi ta ba, ko ana wani kauyen yanzu kuma, yanzu kenan wayar dreban baya shiga?” Nihal tace “Ehh” Umma tace “Toh Allah ya kyauta, ya wannan saurayin naki ɗan senator, in ji dai kin ci gaba da kulasa banda walakanci ko?” Nihal tace “Eh” Umma tace “Yana zuwa wajen naki?” Nihal tace “Eh” Umma tace “To madallah, ki dai kula banda cewa xaki bi sa ko ina komin takuraki da zai yi, kuma ban amince da tadi a mota ba, sannan iyakan ku cikin makaranta, ko wajen makaranta ban yarda ki bi sa ba, banda dai mata sun zama abinda suka zama da sai ince ko hira xaki fita in ya zo ki dinga fita da roommate dinki wannan da kika raka garinsu, to yan matan ne sai su maka snatching” Ita dai Nihal bata ce komai ba, Umma tace “Ki dai kula don Allah kin ji Nihal?” Nihal tace “Toh” Umma tace “Naga kamar bacci kike ji sai da safe” a hankali Nihal tace “Allah ya tashe mu lafiya” Umma tace “Ameen auta” Daga haka ta katse wayarta, ta shiga neman number Husnah, ita kam tana son taji wani hali Nihad take a kauyen da dreba ya kai ta, yana fara ring Husnah ta daga, Bayan sun gaisa Umma tace “Kwana biyu ko leko mu kun daina” Husnah tace “Wallahi kuwa, nima ai banji dadi ba kwanaki, na ma kwana biyu a asibiti da kamar xa a min aiki a ido sai kuma Allah ya takaita, wallahi ban dade da fara fita ba yanzu haka, don idan na fita cikin rana idon kamar ya cire don azaba” Umma tace “Subhanallahi, to Allah ya tsare, Allah ya kara lafiya, gashi bamu da labari ai da ko dubaki ne sai in zo inyi” Husnah tace “Ameen Umma, ya mutanen gidan?” Umma tace “Lafiya lau wallahi, nace dai yau bari in kiraki in ji ko kina ji daga wajen kawarki, kamar anyi ruwa an dauke yau wata daya kenan ni Sumayya” Husnah tace “Wallahi jiya jiya su Naf suka gama wannan zancen, Umma kinsan wani abun mamaki kuwa??” Umma tace “Aa me ya faru?” Husnah tace “In gaya maki kafin su bar garin nan ina kwance asibiti sun je dubani, turanci a bakin dreban nan kamar bature” Umma tayi shiru, can tace “Turanci kuma?” Husnah tace “Wallahi” Umma tace “Aa to ai dama yace yayi sakandari, dama dole xai iya turanci ai in dai ba dakiki bane, amma tabbas iyakarsa dai sakandari” Husnah dai tayi shiru, can tace “Yanzu ko Abba baxa kice ya tuntubi….” Da sauri Umma tace “Aa ko xancen su bai so gaskiya, yanzun nan hawan jininsa sai kiga ya tashi, shi yasa na daina gaba daya, dama wai inji inda suke ne” Husnah tace “Shekaranjiya saurayin Nihad din ɗan janar jikamshi ya kira Naf asking for her whereabout, muka ce ai mu ma bamu sani ba gaskiya…” Umma tayi shiru, can tace “Shikenan dai, shi banda abunsa ko da ba a mata aure ba ta ina iyayensa xa su amince da auren wata Nihad, ai da ko Aminata ce sai ya nema tunda ita Nihal na da wani saurayi, ko ɗan minister ne ko sanata ni dai na manta yanda tace min, kuma yana sonta sosai sai kinga kudin da yake kashe mata, don da bata ma kulasa ni ke ta tursasata ta dinga kulasa bata san waye mijinta ba, kwanaki har mota yace xai bata taki, nima kuma ban goyi bayan hakan ba” Husnah tace “Gaskiya kam” Umma tace “Shikenan, sai dai yanda ta yiwu” Husnah tace “Muna nan dai muna binciken inda xa mu samota in sha Allah” Umma tace “Toh don Allah ku kokarta” Nan suka yi sallama Umma ta katse wayarta.  Da safe Mimi ta gama shiryawa zata tafi makaranta wajen karfe goma, bayan ta sallami Mami ta kalli Khalil dake parlon yana danna wayarsa tace “Yayanmu sai na dawo” ya kalleta yace “Isn’t ur frnd going to lectures?” Tace “I met her lying down tace baxata ba, i don’t think she is even okay” Bai ce komai ba har ta fita daga parlon, Bata jima da fita ba Noor ma ta shigo parlon ta je ta sallami Mami sannan ta fito, tana kallonsa tace “Yayanmu amma dai yau zaka je wajen Nadeeyah ko? You know u didn’t try yesterday, she made all u requested but u ended up not coming, you just spoilt her mind” Yace “Zan je” Tace “Better, cause she is so sad” Shi dai bai kara ce mata komai ba har ta fita daga parlon, wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Nihal ce, tun jiya da daddare ya kirata to check on her ya ji ta on another call kuma bata kirasa ba sai yanzu, Bayan sun gaisa jin she sounds dull yace “Are you okay Nihal? You sound stressed out” Nihal tace “I am fine, i just woke up, ya Nihad?” Yace “Alhamdulillah, yaushe za ku fara exam?” A hankali tace “There is still time, CA muka gama yanzu” Yace “Are you sure baxa ki je gida ko weekend ba so that u can get enough rest? Naga kamar wannan semester din da zafi” Nihal tace “Toh xan je” Yace “Or will you like to come over to ur sister?” Nihal ta ɗan yi shiru, sai kuma tace “I will love that” Yace “Ohk then, i will talk to farooq about it later, idan ya amince sai in zo Zarian gobe in daukeki” a hankali tace “Okay, i am grateful” Yace “Take care dear” Tace “Sure” Daga haka ya katse wayar, Mami ta fito, Khalil na kallonta yace “Mami are you going out?” Tace “Ehh xa mu fita da su Amina, xa mu je wani gaisuwa ne…” Yace “Ohk, are you staying long” Tace “Not at all, but i might branch Hajiya Safeenah’s place” Yace “Ohk Allah ya tsare” Tace “Ameen, ina da magana da kai idan na dawo” Yana kallonta yace “Maganar me Mami?” Tace “Sai dai na dawo” Ya bi ta da kallo har ta fita daga parlon, yana jin fitarsu daga gidan with escort bayan kusan minti sha biyar, mikewa yayi ya fita daga part din Mami. Dakinsa ya koma ya kwanta, deep in his thought, kiran Nadeeyah ne ya shigo wayarsa, ya dinga kallon wayar har ya katse, can ya dauka ya kirata, kamar me bacci yace “I will call u later Nadeeyah, i am still on bed…” Jin bata ce komai ba yace “Hello” Tace “Ohk” Katse wayar yayi ya mike zaune, bayan kusan minti biyar ya kalli agogon dakin dake nuna karfe goma da rabi, tashi yayi ya dau wayar Nihad dake gaban mirror dinsa ya fita, daren jiya Ayman ya kirata yayi sau biyar, yau da safe ma still sai da ya kira duk Khalil na kallon kiran, direct ya nufi dakin da Nihad take ya bude kofar ya shiga, kwance ya sameta ta rufe har kanta da duvet, ya karasa ya cire duvet din ya jefa mata wayar a gefenta, fuska daure yace “Kirasa yanzun nan kice kada ya sake kiranki, do that immediately….” Ko bude ido Nihad bata yi ba balle ta kulasa, ya wani hade rai yace “Ba dake nake ba?” Tashi tayi ta sauka daga kan gadon zata nufi bandaki ya fizgota, ta fashe da kuka tana turasa da dashashiyar muryarta tace “Ni ka kyaleni wallahi, kai me bakinka yake yi da baxa ka gaya masa da kanka ba sai ni??” Yana mata wani kallo yace “Ni kike gaya ma haka?” Cikin tsawa tace “Na fada maka din, tell him ur self and stop bothering me, ko kuma ka kira Aunty Maryam ka gaya mata ita ta gaya masa” Sai kuma ta fashe da kuka ta durkushe wajen, tayi me isanta duk yana kallonta sannan ta mike ta figi Hijab dinta zata fita ya fixgota, ta buge hannunsa cikin rawan murya tace “Ni ka kyaleni, baxan sake kwana a gidanku ba, gwara in tafi wajen grandma dita nasan she will accept me, it’s not as if I don’t have anywhere to go….” Yana mata wani kallo yace “Da izinin wa zaki je wajen nata??” Cikin kuka tace “Wallahi idan baka barni na tafi ba sai na gaya ma kowa a gidan an mana aure da kai, kaji har na rantse” Da mamaki yake kallonta baki bude, xata kwace kanta ya riketa gam yace “Ohk, kinsan an mana auren kike kula wani farin katon banza a waya har kike ce masa you love him too?” Ta hadiye kukan da take ta kallesa tace “Kai kuma da kake kula wata farar katuwar banza fa? Sai ni ce baxan kula wani ba….” Duk da dariyar da ta basa ya kara murtuke fuska yace “Ohh kika ce sai kin kulasa?” Tace “Kuma baka isa ka hanani ba, don bansan da auren kowa a kaina ba, i neva accepted ur marriage even for one second, nasan kuma da shi ne he is too gently and calm to raise his hand on my face, and dole ka sakeni in auresa because i am beginning to love him….” Kuka take sosai tana son kwace kanta amma yaki saketa yana kallonta babu ko kiftawa, ta fara kai masa duka a kirji ganin ya ki saketa, lokaci daya ya dauketa cak ya nufi saman gado da ita ya jefata kai, ta hadiye kukan da take tana kallonsa tana komawa baya ganin yanda ya daure fuska yace “I will show you ni mijinki ne yau, and you have nothing to do about it” Kawai taga ya juya ya yaje ya sama kofar dakin key, ta yi wani tsalle xata shiga bandaki, yayi hanzarin fizgota kafin ta shiga…..

49

Nihad ta fashe masa da kuka hankalinta a tashe ganin babu alamar rahama a tare da shi, ta hade hannunta pleadingly tace “Don girman Allah kayi hakuri, wallahi tallahi na maka alkawarin baxan sake ba, i am promising you this” Ko sauraronta bai yi ba ya sake mayar da ita saman gadon, tana ganin ya fara cire shirt dinsa ta hau zaga kan gadon tana cewa “Don girman Allah ka yi hakuri, wayyo na shiga uku” Bata kara tsorata da shi ba sai da taga ya cire both his singlet, bata san sanda ta kara sauka daga kan gadon ba da nufin sake attempting din shiga bandaki da gudu, ya kara fincikota ya mayar kan gadon, forcefully ya fara kokarin cire mata rigar baccin jikinta wanda dama iyakarsa knees dinta, ta zaro ido ta fasa wani ihu a tsorace tace “Wayyo na shiga uku, don Allah ka bari, wallahi ban saka komai ba…” bai ko saurareta ba har ya fixge rigar da karfi, ta kara gwalo ido cikin rikicewa ta jawo duvet tana kokarin rufe jikinta yana kallonta don bai yi zaton babu Bra a jikinta ba, cause the way they are firm and pointed babu wanda xai ce bata saka Brassiere ba, lokaci daya ya kwace duvet din yayi cilli da shi gefe daya yana ci gaba da kallonta, tunda take bata ta6a tsayawa haka gaban kowa ba, hakan yasa duk ta rikice taki barin ma ya kare mata kallo ta takure waje daya jikinta na rawa, tana ganin zai dagota and that will give him access to seeing her bare chest fully, kawai tayi saurin rungumesa ta fashe masa da kuka tace “Don Allah kayi hakuri ina rokonka, i am ashame plssss” Ba a tsaye yake ba but he just loose his stamina all of a sudden, ya tafi luuu ya fada kanta, bata damu da weight dinsa ba ta kara rungumesa sosai tana kukan tashin hankali, ita a dole kar ya tashi yaga jikinta, runtse ido yayi cause he is beginning to loose his mind, he is gasping heavily for breath, kawai taga ya fara canza salon rungumar da tayi masa to something else and at the same time trying to make her go completely naked before him, bata san sanda ta wani zaro ido ta fara turashi da duk strength dinta tana kokarin tashi amma yaki bata wannan daman, sai ta fara ganin abun da yake mata kamar a mafarki, tayi karfin halin wage muryarta ta fasa wani ihu tana girgiza masa kai a gigice tana cewa “Don girman Allah, don darajan iyayenka ka yafe min duk abinda na maka tun sanda ka fara sanina, wallahi sharrin shaidan ne, don Allah kar ka min haka, wallahi baxan sake rike wayar ba xan bar shi a wajenka….” Ko sanin abinda take cewa bai yi ba balle kalmomin nata su ceceta, idanuwansa suka yi matukar tsorata ta, bata taɓa ganinsa a haka ba, infact komai nasa ma ya tsoratata a lokacin nan, kamar ba Khalil da ta sani ba, he wasn’t even ready to waste anytime, he wasn’t wanting to be careful in anyway, ko kwakkwaran motsi yaki barinta tayi saboda yanda ya gwada mata ba karfinsu daya ba, shi dai kawai ya cika burinsa a lokacin, tayi karfin halin cewa “Wallahi ban ta6a ba, don Allah Khalil kar ka min haka xan iya mutuwa, wallahi ban ta6a ba” a karo na farko yayi magana cikin kaushin murya yace “Baki taɓa me ba?” Cikin tashin hankali tace “Abinda zaka min” Cikin muryar da bata san sa da shi ba “Karya kike” Kasa ce masa komai tayi kawai tayi give up, but she is so shock, lkci daya taji kamar numfashinta na neman dauke saboda yanda ta tsorata, kawai ta fasa masa ihu a wahale yaga tana kokarin jawo numfashi and she immediately passed out, duk yanda ya so ya hakura ya kyaleta bayan ya fahimci wani abu kasawa yayi, instead yaki yin abinda yayi niyya da farko, amma still bai kyaleta ba har sai da yaji hankalinsa ya dawo, ya koma gefenta yana kallonta babu ko kiftawa breathing heavily, he is a doctor but he is confuse at this moment ba wai suman da tayi bane confusion dinsa, he couldn’t stop looking at her for almost 30 seconds kafin ya tashi ya shiga bandaki ya fito da karamin towel, bayan ya gama abinda xai yi ya zauna yana kara kallonta, ya sake duba inside of her da kyau yaga ta kankame jikinta upon she is unconscious wanda hakan ke nuni da she is in severe pain hakan da yayi mata, and the smallest of his finger couldn’t gain access comfortable into her, balle kuma shi da kansa, jin siren tun daga nesa ya mike da sauri yana kallon agogo, ya dau singlet dinsa ya saka sannan ya sa shirt din, ya mayar mata da kayanta gaba daya, ya shiga bandaki ya debo ruwa ya fito, zaunawa yayi gefenta ya dagota yana kallonta yayi rubbing ruwan gently on her face, sai da yayi hakan sau biyu, ta fara kokarin bude idonta kamar warce tayi bacci me nauyi sai kuma ta kara kulle idon, jin an bude gate ya kwantar da ita kawai ya dau karamin towel din ya bude dakin da makulli ya fita ya kulle kofar…. Ya fito wanka kenan sai ga Mami ta shigo dakinsa, tana Kallonsa tace “Wanka kayi” ba tare da ya kalleta ba yace “Eh, sannu da dawowa” Tace “Yauwa, kayi breakfast din?” Still bai kalleta ba yace “Nayi, Mami baki je gidansu Nadeeyan ba?” Tace “Ehh xamu yi maganar da Hajiya Safeenah ta waya, idan ka shirya ka sameni parlor” Yace “Toh Mami” Daga haka ta juya ta nufi kofa ya bi ta da kallo. Khalil na gama shiryawa ya fito xai sauka downstairs ya sha ko tea ne don wani irin yunwa yake ji, karo suka kusa ci, ya koma baya yana kallonsa, kamar yanda shi ma yake kallonsa from head to toes, Khalil ya bi ta gefensa ya bar wajen fuskarsa daure yayi hanyar kitchen, a nan dinning table dake kitchen din ya zauna yana sha shayin da tunani iri iri a zuciyarsa, kawai yaji ya ma kasa shan shayin, daga karshe ko shanyewa bai yi ba ya bar cup din a wajen ya haura sama, direct bangaren Mami ya nufa, a hankali ya murda kofar dakin da Nihad take ya shiga, zaune ya ganta saman gadon ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, ta dago kai da hawaye shabe shabe a fuskarta tana ganin shine tayi saurin mayar da kanta bisa gwiwanta wani sabon kukan na taho mata, ya karasa ya zauna gefenta a hankali yana kallonta, amma ya rasa me xai ce, can ya mike ya shiga bandaki ya hada mata ruwan wanka sannan ya fito ya dawo gabanta yace “Go and take ur bath” Taki dago kai tana ci gaba da kukanta kamar ranta zae fita, ji tayi ya dauketa kamar wata er yarinya, ta bude ido da sauri cikin kuka tace “Don Allah ka bar ni” Bai saurareta ba har ya shiga bandakin da ita ya ajiyeta dai dai jacuzzi dake ciki, ta durkusa da sauri ta rintse ido tana kuka, yayi kasa da murya yace “Are you okay?” Ta kasa kallonsa don ita yanzu da gaske take tsoronsa, cire mata rigar jikinta ya fara kokarin yi tana son hanasa amma tana tsoron yin hakan, banda hawaye babu abinda take, tana ji tana gani ya cire mata kayan taki yarda su hada ido, ruwan dumi da ya tara a bathtub din ya dauketa ya sakata ciki, wayarsa ya fara ring ya ciro a aljihu ganin Mami ne ya mayar da sauri ya durkusa dai dai fuskarta ya rada mata magana sannan ya mike ya nuna mata clean water da ya tara a wani bowl daban, daga haka ya juya ya nufi kofar fita bandakin, sai a sannan ta bi sa da kallo hawaye na zuba idonta. Khalil na shiga parlon Mami ya sameta zaune, ya zauna, a hankali yace “Ga ni Mami” Mami tace “Hope kayi breakfast din?” Yace “Na yi” Tace “Ohk, ranan kana parlon Abbanka kanwarsa ta kawo maganar yarinyar nan dake karatu gidan nan ko?” Khalil dai yayi shiru yana kallonta, Mami tace “I am asking” a hankali yace “Ina jin na fita sannan” tace “Toh, I covered up everything that day, kuma nayi iya kokarin ganin i defend the girls stay in this house, na nuna masa lallai nan zata zauna tayi karatu tunda ae ana kawo wasu ma su zauna su yi karatun a nan babu wanda ya taɓa cewa don me, to ko sauraronsu ban yi ba ma na bar parlon, to ban san me er uwar ta kitsa masa ba bayan fita na, Allah kadai ya bar ma kansa sani, jiya da daddare kafin in kwanta ya kirani akan maganar dai still, and ya nuna lallai lallai baxata zaunar masa a gida tayi karatu ba, da na nuna hakan baxai yiwu ba naga xai xama mana ɓacin rai kawai na tashi na bar masa parlon, amma nasan Allah baya bacci, duk me nufina da sharri a gidan nan in sha Allahu zai kare masa, zai gani a kwaryarsa, tunda ni ban nufi kowa da sharri ba” Khalil dake ta sauraronta yace “Mami she is staying here, ni da kaina xan samu Abban, What if here is the rightful place for her to stay? What if she have every right to live in this house?” Mami ta hade rai tace “Ka samesa akan wani dalili bayan na nuna masu ni na kawota gidan nan ba wani ba, kai duk abun magana baka gudunsa a rayuwar ka ko Khalil? Duk sun sa kayi baƙi wajen ubanka amma duk da haka kai baka gani, baka tsaya ka gama saurarana ba xaka yanke hukunci just like that, quite alright iyayenta sun maka kirki to tunda abubuwa suka kasance a haka ba sai mu nemi wani solution din ba for the mean time” Khalil yace “Noo Mami, akan me zaki bari wannan matar ta maidaki so low a gidanki, meyasa zata dinga maki abubuwa haka and u are doing nothing about it” Mami tace “Ka saurareni pls khalil” Yace “Ina jin ki” Mami tace “I want to show them that ko da gidan nan ko babu zata yi karatunta lafiya a garin Abuja, kuma koma ina zata zauna she will be comfortable, wannan dalilin ne yasa na kira Hajiya Safeenah kuma ta amince zata zauna gidanta, ba wai xata yi ta zama gidan bne amma ina son in san ta inda xan billo ma lamarin ne, nima kaina hakuri na ya kare a gidan nan….” kallonta khalil ya dinga yi babu ko kiftawa, gashi ya kasa cewa komai, can yayi karfin halin cewa “Mami gidansu Nadeeyah kuma??” Mami tace “Ehh ko ina da sama da uwar Nadeeyan ne a garin nan tunda Maryam bata nan? Sannan i am not saying she will be staying there har ta gama karatun, kawai dai i want to sort out things yanda ya kamata, don naga mahaifinka is taking this issue so personal, he isn’t even giving me a listening ear” khalil was speechless, ya kasa daina kallon, Mami tace “Yanzu zan je in samu ita yarinyar ince mata zan yi tafiya, zata koma gidan kawata kafin in dawo…” Khalil dai ya kasa cewa komai, Mami ta mike zata fita, kamar wanda ya tuna abu yayi saurin tashi yace “Mami xan sameta ni, i know how to talk to her about it” Mami tace “No, kawai ka kira min ita ta zo nan” Bai ce komai ba ya nufi kofa ya fita, yana shiga dakin da Nihad take ya ganta ta dukunkune cikin duvet ta kulle idonta, ya zaune gefenta ya duka yana kallonta amma bata bude idon ba, ya dagota ta bude ido da sauri, tana ganinsa ta fara ja baya taki barin su hada ido, gaba daya jikinta a sanyaye yake and she looks so afraid, ya jawota jikinsa murya can kasa yace “Are you okay?” Taki cewa komai and he could feel the way her heart is beating so fast, ya kalli dogon gashinta dake a jike, ya jawo karamin towel din da yaga ta ajiye gefe ya shiga goge mata gashin, ita dai taki yarda ta kallesa balle su hada ido, bayan ya gama goge mata, a hankali yace “Kinyi breakfast?” Ta kasa ce masa komai hawaye na zuba idonta, ya kara rungumeta yana patting bayanta a hankali, ya kai bakinsa dai dai kunnenta murya can kasa yace “Why are you crying?” Still taki ce masa komai, bayan few minutes ya saketa ya mike ya nufi inda kayanta suke ya bude yana duba wanda xai daukar mata, dai dai nan aka bude kofar dakin, juyawa yayi da sauri yaga Mami ce, sai da heart dinsa is skipping, yace “Erm em Mami, bama ta jin dadi ashe tun jiya, i just came in and realize that” Mami ta kallesa ta kalleta, Nihad dai ta kara dunkune jikinta cikin duvet don towel kawai ta daura, Mami na kallonta tace “Me ya sameki?” Cikin karfin hali Nihad tace “Kai na ke min ciwo” Mami tace “Toh Allah ya sauwake” Khalil ya nufi kofa ya fita daga dakin da sauri, Mami na kallonta tace “Wanka kika yi ne?” Nihad ta gyada mata kai, Mami tace “Toh sauko ki saka kaya sai in baki magani” Nihad ta cire duvet din, ta jawo hijab dinta ta saka kam towel din jikinta ta sauko daga saman gadon tana tafiya a hankali ta nufi wajen kayanta, Mami na kallonta tace “Kinji ciwo ne a kafar?” Ta gyada kai da sauri tace “Bugewa nayi tun jiya” Ji take kamar ana mata azaba idan ta taka kafarta da kyau, she is feeling pain down there but not terrible pain, kawai tana jin haka ne sbda attempt da yayi, wanda ita in ance bai mata komai ba baxata ta6a yarda ba, duk tunaninta ya mata wani abu, Mami tace “Idan kin sa kayanki ina jiranki a parlor” a hankali Nihad tace “Toh” Bayan ta shirya ta fito tana tafiya a hankali zuwa parlon Mami, tun da ta shigo parlon yake kallonta, shi ya ma kasa daina mamaki seeing how she is walking, and he did nothing to her, ya kalli kofar dakin Mami ya mike da sauri ya isa kusa da ita don a kasa ta zauna ya durkusa gabanta yana kallonta

50

Nihad ta ki yarda su hada ido da shi, ya dinga kallonta don duk a tsorace take, ya kamo hannunta zai yi magana aka bude kofa Mami tayi ta fito daga dakinta, Khalil yayi saurin tashi daga kusa da ita ya nufi kujera, Mami ta kallesa ta kalleta, ita dai Nihad kanta na kasa, Mami tace “Ya ciwon kan? Kin sha magani?” Nihad still bata dago kanta ba tace “Na sha” Mami tace “Toh Allah ya sauwake, je kiyi kwanciyarki kawai….” Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita, Mami na kallon Khalil fuska daure tace “Ban gane ma’anar shisshige ma yarinyar nan da kake ba Khalil?” Ya zaro ido da sauri, sai kuma ya xauna yace “Mami shisshige mata kuma? I just saw she is sick and….” Mami ta katse sa rai bace tace “If she is sick ni baxan iya mata abinda ya kamata ba sai kai? Sannan who did she tell she is sick? i see no reason da xai sa kana shiga dakin da take at the first place ita ba muharramarka ba, meye ma’anar hakan? to gaskiya bana so, don’t ever try it again, idan wani abu ya dameta ta zo ta gaya min bana son wannan shige matan da kake we are not pagans” Khalil ya mike yace “Mami ai baki taɓa gani na….” Dakatar da shi tayi tace “Bana son jin komai, na dai gaya maka abinda xan gaya maka, khalil ya dinga kallonta ya kasa cewa komai, ta juya tayi komawarta cikin dakinta, a hankali ya koma ya zauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, kansa bai taɓa kullewa yanda ya kulle ba yanzu, ya ga alama it’s not going to be easy, it doesn’t look Mami will take things easy kafin aje ga Abbansa, sai a sannan ya fara tunanin he wished bai boye ma Aunty Maryam komai ba tun farkon dawowarsu, may be she will have understood him, yasan yanzu its too late ita kanta baxata fahimcesa ba yanxu, it’s just too late, bayan wani lokaci Mami ta fito daga dakinta ko kallonsa bata yi ba ta nufi kofa zata fita, ya jima bai ga ta hade masa rai haka ba, wannan yasa jikinsa yayi sanyi, he don’t think she will ever support him in any way, Mami xata bude kofar parlon aka bude before her, hakan yasa ta daga kai suka yi ido hudu da shi, da fara’a tace “Aa, Aliyu yaushe ka dawo?” Yace “Not too long Mami” Khalil ya wani murtuke fuska yana danna wayarsa, Mami ta koma ta zauna tana kallon Aliyu tace “Sannu da zuwa, ai ban san ka dawo ba wallahi” Ya zauna saman kujera yace “Ina yini Mami” Tace “Alhamdulillah, ka dawo lafiya?” yace “Lafiya lau Alhamdulillah” Mami tace “To maa sha Allah, gaskiya ka dade sosai wannan karan” ya ɗan yi murmushi da iyakarsa baki yace “Na shigo ne in gaisheki dama….” Tace “Toh Nagode Aliyu, i will be coming downstairs later, you are welcome dear” Yace “Alright” Mikewa yayi ya nufi kofa ya fita daga parlon, Mami ta kalli Khalil da damuwa tace “Why didn’t u speak to him Khalil?” Khalil kamar jira yake yace “Why will i speak to him Mami?” Mami ta girgiza kai tace “No…. gaskiya bana son haka, tunda ya shigo har nan ya gaisheni menene a ciki don ka gaisa da shi? Me yake yi som” Khalil yace “Am i his mate da xan fara gaishesa Mami? or da can ya saba shigowa gaisheki a nan idan ba hypocrisy ba, look Mami i am begging you to stop forcing me do what isn’t necessary, babu abinda ya hadani da su” Mami tace “No Khalil, me yasa kake daukan komai da zafi a rayuwarka ne? ko kaki ko ka so ɗan uwanka ne fa” Khalil ya mike yace “Ba ɗan uwana bane ban hada komai da shi ba…” Mami ta daure fuska tace “Kace min ba ɗan uwanka bane” Yace “I want to excuse my self plss” Kallonsa Mami ta dinga yi, yace “I said i want to excuse my self Mami” Mami ta sauke boyayyen ajiyar zuciya tace “Ohk” Juyawa yayi ya fice daga parlon a fusace, Mami ta girgiza kai irin zuciyar Khalil na damunta, he is the one always causing problem for himself, sai yace baya tsoron kowa, hatta mahaifinsa tasan yanda duk suke shakkarsa shi baya yi, shi yasa yana ce masa ya bar masa gida ko minti goma bai kara ba a gidan yayi gaba, bayan few minutes ta girgiza kai ta mike ta fita daga parlorn ta nufi dakin da Nihad take don ce mata ta hada kayanta, Khalil yayi stiff a bakin kofar dakin don zai fito kenan sai ga Mami, Kallonsa Mami take babu ko kiftawa ta ma kasa ce masa komai, confidently yace “I left my phone in here, so i came to pick it up” Daga haka ya bar ta tsaye bakin kofar without waiting for her reply, ta bi sa da kallo, Can ta shiga cikin dakin, Nihad na kwance ta rufe ido kamar me bacci, Mami ta dinga kallonta for some seconds, sai kuma ta karasa kusa da gadon, Nihad ta bude ido da sauri, ganin Mamin ta mike ta zauna tana murza idonta, Mami tace “Are you feeling better now?” Nihad tace “Alhamdulillah” Mami stood for almost a minute looking at her, Sai kuma ta juya ta fita daga dakin. Khalil na komawa bedroom dinsa yaga miss calls din Farooq, zaunawa yayi gefen gado yayi dialing number, yana fara ring Farooq ya daga, suka gaisa sannan farooq yace “I think Nihal will be going to kano for the weekend don dazu Umma ta kirani tace in tura mata Tp ta ce mata ta taho Kano, after exams ai xata iya zuwa Abujan ko?” Da sauri khalil yace “Sure ba damuwa, i think that will even be better” Farooq yace “Toh maa sha Allah” Daga haka suka yi sallama khalil ya katse wayar. Mimi na dawowa makaranta Mami ta shigo dakinta, Mimi dakw goge jikinta da towel tace “Mami good afternoon” Mami tace “Afternoon dear, kina ji na” Mimi ta kalli Mami tace “Ina ji Mami” Mami tace “Za ku je gidansu Nadeeyah ke da Nihad ku yi 2 days a can” Da mamaki Mimi tace “Why Mami? Me ake yi a gidan?” Mami tace “Ba komai, but you have to do as i say” Mimi tace “Ohk” Mami tace “Idan kin huta kin ci abinci anjima sai kice mata ta shirya kayanta, kema ki shirya naki” Mimi tace “Toh” Juyawa Mami tayi ta fita daga dakin. Nihad na kallon Mimi dake zaune gefenta a kan gado tace “Ina za mu je?” Mimi ta wara ido tace “Somewhere, gidan sister din Mami” Nihad felt a bit relieve jin haka, don dama har cikin ranta ta gaji da gidan nan, and har zuciyarta taji bata son tana ganin Khalil don wani tsoronsa take ji, da ta tuna abinda yayi mata sae taji hawaye ya zubo mata, ita duk tunaninta ae ya santa fa, a hankali Mimi tace “But pls tell me Neehad, why are u always unhappy, ur eyes are often swollen, u are always silent, ko baki son gidanmu ne?” Nihad ta sauke idonta bata ce mata komai ba, Mimi tace “Or are you not comfortable here? Am i not nice to you? Kinga ai bakya haduwa da cousins dina da step sister dita Hanan, basa shigowa part din nan so it’s rear ku hadu, and idan kika saki jiki da Noor xa ki ga she is also nice, u misunderstood her ne kawai from the beginning” Nihad dai ta kasa ce mata komai she wish she can tell her abinda khalil yyi mata ko zata samu saukin abinda ke damunta a zuciya, Ganin haka Mimi ta sauke ajiyar zuciya tace “So now kawai ki hada kayanki, nasan you won’t get boring gidan da za muje cause they are not strict, we will be having enough freedom there to go anywhere unlike here, and i will be taking u out to many places in Abuja” A hankali Nihad tace “Okay thank you” daga haka ta sauka daga saman gadon ta tafi wajen kayanta, Mimi ta bi ta da kallo, seeing how she is walking tace “Are you injured?” Da sauri Nihad ta kalleta tace “I am getting better now” Mimi tace “Ohk”

Umma na jera kayanta da Isiya me wanki da guga ya kawo mata dazu a Press aka bude kofar dakinta, daga kai tayi tana kallon kofar ganin Amina tace “Wai baki tafi islamiyyar ba?” Amina tace “Umma, Aunty Nihal ta dawo” Umma ta ajiye kayanta da sauri tace “Kai haba, oyoyo oyoyo” Daga haka ta fice daga dakin da sauri ta tafi can bangaren Mumy ta shiga dakin Nihal, Kwance ta ganta Mumy na zaune gefenta, cike da farin ciki Umma tace “Oyoyo autana, sannu da zuwa, sannu da zuwa” Sai kuma ta karasa bakin gadon tace “Aa baki da lafiya ne?” Nihal ta girgiza kai tace “Aa lafiyata qlau” Mumy tace “Nima tambayar da nayi mata kenan, ina jin gajiyar hanya ce kawai” Umma tace “To taso mu je, ga favourite dinki can na maki” Nihal tace “Umma bana jin yunwa sai anjima” Umma tace “Ni dallah taso, dubi yanda kika rame kamar baki cin abinci a makarantar, ni wallahi wannan jarabbaben makarantar ya isheni Allah ya so shekaran karshe kike ki huta mu ma mu huta” Mumy tace “Tashi kije Nihal” Nihal ta sauka daga kan gadon ta bi bayan Umma suka fita daga dakin, Mumy dai ta bi su da kallo, at times ganin Nihal na sa ta mance duk wani damuwarta, yana rage mata kewar Nihad da take, tana jin Nihal kamar Nihad a zuciyarta, sannan tun bayan da Farooq ya kirata ya sanar mata yaje har inda Nihad take a Abuja, Mumy ta samu rest of mind, duk da yace sauran bayanan sai ya shigo Kano zai mata amma ta kwantar da hankalinta Nihad is fine and comfortable where she is.  Umma ta cika ma Nihal abinci a gabanta, ita dai Nihal ta daura chin dinta a saman gwiwarta tana kallon abincin, Umma ta dawo ta zauna tace “Toh deba ki ci mana” A hankali Nihal ta jawo plate ta fara zuba abincin, Umma dai sai kallonta take don ta rame sosai ba kadan, sannan ba lively Nihal dinta take gani a nan ba, Umma tace “Nihal” Da sauri Nihal ta dago ta kalleta, da damuwa Umma tace “Did you have any problem?” Nihal ta girgiza kai da sauri tace “Aa Umma, i am okay” Umma tace “Na ganki a sanyaye kamar kina da damuwa daughter” Nihal ta girgiza mata kai kawai tace “Ba komai Umma” daga haka ta ci gaba da dibar abincin da take, Umma na ta kallonta tace “Ko dai Nihad kike tunani har yanzu Auta?” Lokaci daya taga hawaye ya kawo idon Nihal, nan da nan hankalin Umma ya tashi, ta mike don a duniya babban tashin hankalinta kukan Nihal ko kuma damuwar Nihal, Umma tace “Yanzu meye abun kuka? Wallahi in dai Nihad ce ni sai in sa duk inda take a samota in hakan ne xai sa ki daina damuwa, in ma kauyen xaki je ki masu kwana biyu sai kije in dai wannan ne damuwarki Nihal” Nihal dai ta kasa cewa komai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, nan Umma ta hau lallashinta tana jin kukan nata har cikin ranta. Da yamma Umma ta dau makullin mota ta fita sai gidan Hajiya Turai, bayan sun gaisa Umma tace “Anya turai baxa ki sake rakani gidan malamin nan ba a sassauta abin nan da yayi” da mamaki Hajiya Turai tace “Saboda me?” Da damuwa Umma tace “Toh Nihal ce har yanzu na rasa gane kanta wallahi, duk ta sukurkurce, kinsan sun shaku sosai da er uwar, wallahi daxu da naga test script dinta sai da hankalina yayi mugun tashi, Nihal da bata taɓa faduwa a makaranta ba, gashi shekaran karshe take, a’a gaskiya mu je a sassauta abin nan Turai” Hajiya Turai tace “A karya asirin kenan nufin ki?” Umma tace “Aa, a karya kuma?? Cewa nayi fa a sassauta yanda dai Uban zai bar Nihad din ta shigo gidan amma babu yabo babu fallasa sannan ko sisinsa baxai shiga hannunta ba balle na dreban, kin dai gane ai, ni dai in samu hankalin ‘ya ta ya kwanta, ta ci gaba da karatunta cikin aminci” Hajiya Turai tace “Amma abun da mamaki, tun da can bata daga hankali haka da abun ya faru yana zafi zafi ba sai yanxu?” Umma tace “Ke kuwa sabo, nima dai farko naga bata yi haka ba duk da ta damu gaskiya, amma wai daga zuwa makaranta shkkn abu ya lalace, Sai ma kiyi ta kiranta a waya bata son dagawa, gaba daya tayi sanyi yanda kika san an zare mata laka, wallahi abun na damuna, kuma nasan saboda er uwarta ne, gashi yanzu naga uban ma yana jan ta jiki tunda ba Nihad din, ko Shekaranjiya ce min yayi xai canxa mata laptop, to taki kwantar da hankali” Hajiya Turai tace “Toh sai mu koma gobe” Umma tace “Yauwa Hajiya turai, sannan ita ma Kamila ina son a kara aiki akan mijinta, don suna ta samun matsala kwanan nan, ita kuma Nihal wani da minister ya fito yana sonta shi ma sai ayi aiki a kai” Hajiya Turai tace “Duk Allah ya kai mu goben” Umma bata jima a gidan ba tayi mata sallama ta kama hanyar gida.

Dab da magrib Nihad ta gama shiryawa tana tsaye gaban mirror tana daura Nikab dinta sai ga Mimi ta shigo ita ma ta shirya, Mimi ta wani ɓata fuska tace “C’mon plss where r u going with this mask, ba fa school xa mu je ba” Bata jira me Nihad xata ce ba ta kwace Nikab din, Nihad ta juya tana kallonta don khalil ne yace ta sa Nikab din, da tayi niyyar baxata sa ba amma kuma kawai ta dauko daga karshe, Mimi na girgiza kai tace “Don Allah ki dau mayafi ki yafa mu fita, we are not going to school fa, beside this is evening” Nihad tace “I am more comfortable with the Nikab Mimi” Mimi tayi shiru tana kallonta, Nihad ta mata murmushi ta amshe Nikab din a hannunta ta shiga daurawa, Mimi ta daga kafada ta fita daga dakin xuwa parlon Mami, ganin Khalil zaune parlon tace “Yauwa yayanmu pls ka kai mu mana since u are around, i don’t want to be escorted” Ya kalleta sai kuma yayi kasa da murya yace “Tell Mami so” Da sauri ta shiga daki wajen Mami tace “Mami since yayanmu yana nan ya kai mu can gidan mana” Mami tace “Ohk” Mimi tayi murmushi ta juya ta fita ta kulle mata kofa, Tana kallon Khalil tace “She said ohk” Daga haka ta fice daga parlon. Mimi ta sauka downstairs tare da Nihad bayan Bilkisu ta kai masu kayansu waje, dai dai stairs din karshe Nihad ta makale jikin rail din staircase din tana kallon wanda ta gani zaune parlor ko kiftawa babu, yana tare da 3 of his frnds ga drinks da kaza with small chops a gabansu, they were all gisting suna dariya, Mimi ta kalleta ganin kamar she is shock tace “What happen Nihad?” Nihad tayi backing parlon da sauri kamar xata koma sama tana zaro ido ta cikin Nikab din fuskarta, Mimi ta kama hannun Nihad da mamaki tace “Are you alright?” Nihad ta kasa cewa komai xuciyarta na heaving, Mimi na rike da hannunta tace “Nihad” Da sauri Nihad ta kalleta, with confusion Mimi tace “What happen?” Nihad tayi karfin halin cewa “Nothing, nothing” Mimi ta kama hannunta suka sauka daga stairs din, kin kallon inda su Aliyu suke tayi tana makale da hannun Mimi tana shige mata kamar xata harde ta fadi, gaba daya mamaki ya cika Mimi, Can dai Mimi ta kalli su Aliyu da suka bi su da kallo tace “Yaya sai mun dawo” Yana kallonta yace “Ohk” Daga haka suka fita daga parlon tana rike da hannun Nihad, Mimi ta kulle kofa tana kallonta tace “Kin san wani a cikinsu ne?” Nihad ta hadiye wani abu da kyar ta girgiza mata kai, Mimi dai ta dinga kallonta, Nihad tayi karfin halin cewa “Who is the guy in white?” Mimi tace “He is my cousin brother, did u know him?” Nihad ta kasa ce mata komai tana kallonta babu ko kiftawa, lokaci daya taji komai ya tsaya mata ga wani jiri da ke dibanta, ta dinga nanata kalmar cousin da Mimi ta furta mata a zuciyarta, Can Nihad tayi karfin halin cewa “Can i know his name pls??” Mimi tace “Aliyu, his name is Aliyu Iliya, yayansu Sajida and Farhana” a hankali Nihad ta dinga gyada mata kai amma ta kasa cewa komai, Mimi tace “But don Allah ki gaya min, kin san sa ne? U reacted as if kin ta6a saninsa” Da sauri Nihad ta girgiza kai amma ta kasa cewa komai har sannan, bayan few seconds tayi karfin halin cewa “What is his relationship with ur brother?” Mimi tace “Of course they are cousins, my brother is Ibrahim Khalil Jikamshi, while he is Aliyu Iliya, mum dinsa ita ce Aunty Hassana ai kin santa….” Nihad was Baffled, taji zuciyarta na wani irin bugawa tace “Jikamshi?” Mimi tace “Yeah, that’s my father” Mimi ta wara ido tace “You mean all this while baki san gidan da kike ba?” sunkuyar da kai Nihad tayi a hankali tana jin jikinta kamar an zare mata laka, Mimi dai sai kallonta take, can dai Mimi tayi murmushi ta kama hannunta suka bar wajen, Har suka isa mota Nihad jan kafa take tana ganin komai kamar a mafarki, a ranta kuwa ta fadi Aliyu Iliya ya fi sau goma, for the first time she felt life had never been nice to her, she’s been deceived in so many ways by so many people, Umma, her frnds, and now Aliyu, nothing was in her favor during her pass, a yan kwanaki kadan taga abubuwan da bata ta6a zato ba a lkcn da bata ta6a tunani ba, a yan kwanakin nan ta fahimci not everything is as it seems, she felt so stupid of her self at this point, tayi da ta sanin abubuwa da yawa na rayuwarta a baya, she wish she can amend things, but how will that be possible, Mimi ta dinga kallonta bayan ta bude mata back seat amma taga bata shiga ba alamar tayi nisa tunanin da take, kamar ma bata san sun kai parking space din ba, a hankali Mimi ta dafata, firgit Nihad ta dawo duniyar tunanin da ta tafi, Mimi ta nuna mata motar, Nihad ta shiga da sauri trying all possible best kar ta bar hawaye ya taru idonta balle har ya kai ga zubowa, why she?? Why is all this happening to her?? Mimi ta zaga ta shiga gaban motar, sai a sannan Nihad ta daga kai suka hada ido da khalil dake kallonta ta madubi, sosai gabanta ya fadi, kuma bata taɓa jin kunyar duk abubuwan da tayi masa ba sai yau, she felt so ashame of her self, yau ne taji kunyarsa na gaske, a kwanakin baya tana jin guilt a xuciyarta na abubuwan da suka faru amma na yau ya wuce misali, and she remembered vividly ranan da ya kai ta Wellcare wajen Aliyu da abinda ya faru, yanda ta cakumesa a wuyar riga raining all sort of insult on him, bata san sanda ta hade kai da gwiwa ba wasu hawaye masu zafi suna sauka idonta, many things are not as they seem, truly not everything is as it’s seems, ta yaudari kanta sosai a baya, Khalil ya tada motar suka bar gidan, sai da suka yi nisa ya kalli Mimi yace “Ba ki bukatan komai?” Mimi ta ɗan buda ido tace “In dai expenses din na kanka” Ya ɗan yi murmushi yace “Ohk, where are we going now?” Ta kira masa wajen wani shopping, nan ya dau hanyar zuwa wajen, suna isa yayi parking ya ciro Atm card dinsa ya mika mata, ta amsa tace “I thought tare xa mu shiga” Yace “Nahh, ke kadai za ki shiga, i have done my part by giving u my card” tace “Can i shop for two?” Ya gyada mata kai, kulle motar tayi ta juya ta bar wajen yana ganin ta shiga ciki ya sauka ya shiga bayan motar, shi da yake bai biyo ta main parlor ba bai san su Aliyu na parlon ba ma, Nihad taji wani kukan ya taho mata jin ya shigo bayan motar, ya dago kanta a hankali yace “Now tell me what’s ur problem” ta kasa kallonsa tana shesshekan kuka sosai, she wish many things didn’t happen, she wish she was so kind to everyone back then, bata taɓa sanin Umma bata sonta ba sai da Aunty Maryam ta ganar da ita, she encouraged her to be mean to everyone, ya cire nikab din fuskarta yana kallonta, ta boye fuskarta da sauri wani kuka ya taho mata, kunyar hada ido da shi take, ya jawota jikinsa ya rungumeta a hankali yana kokarin kai hannunsa in between her legs yace “Does it hurts har yanzu?” Bata san sanda ta zaro ido ba ta rike hannunsa da sauri, closing her leg tightly tace “Aa” Yace “Then what?” Shiru tayi bata ce komai ba tana sauke ajiyar zuciya a jikinsa, she felt a bit relieved, tana jin breathing dinsa a fuskarta kamar me rada yace “You need the phone?” Shiru tayi Idonta a rufe bata ce komai ba tayi lamo a jikinsa, Shi ma bai kuma ce mata komai ba ya lumshe idonsa yana sauke numfashi a hankali, Nihad ta bude ido tayi karfin halin cewa “Me ya kawoka gidanmu?” Bai bude ido ba still yana taɓa kafarta yace “We should ask Habibu that” Da sauri ta daga kai ta kallesa, da sauri Khalil ya saketa ganin Mimi ta fito daga mall din rike da just er leda, ya bude motar ya sauka ya koma front seat, tana karasowa ta shiga gaban motar ta ajiye ledan hannunta tana Murmushi tace “just 2 perfumes” Yace “You are not serious” Dariya tayi, ya tada motar suka bar wajen. Har suka isa anguwansu Nadeeyah Nihad bata daina tunanin abinda yace mata ba wai they should ask Habibu, how did he know Habibu, gari yayi duhu suka iso gidansu Nadeeyah don har an idar da magrib, bayan yayi parking ya sauka motar, Mimi ta sauka ita ma tana rike da ledan turaren da ta siyan ma ita da Nihad, Nihad ta sauka daga cikin motar, Mimi tace “Bari in kira me aiki ta dau mana kaya” Daga haka ta wuce ciki, Nihad ta bi ta da kallo, sai kuma ta kalli Khalil taga kallonta yake da sauri ta sunkuyar da kai ta juya zata bar wajen ya fizgota ya hadeta da mota yana kallon lips dinta, gaba daya ta rikice don mai gadi na zaune kusa da gate, ta fara turasa zata bar wajen sai ga Mimi ta fito tare da Nadeeyah, da sauri ya saketa ya bude driver seat kamar zai dau wani abu.

51

Nihad ta dinga kallon Nadeeyah dake tahowa tare da Mimi ko kiftawa babu har suka karaso parking space din, Nadeeyah na kallonta murmushi dauke fuskarta cikin sanyayyen muryarta tace “Sannu da zuwa” Babu yabo babu fallasa Nihad tace “Yauwa” daga haka kuma ta dauke kai, Khalil ya kulle motar yana kallonsu ya ɗan yi murmushi yace “Hi Nadeey…” Nadeeyah taki yarda ta kallesa tace “Welcome” Mimi ta nuna ma mai aikinsu Nadeeyah da ta taho trolly dinsu dake cikin mota, yarinyar ta saukar da su daga booth din ta dauka ta wuce ciki, Nadeeyah ta dau wani karamin jaka ta bi bayan mai aikin, Mimi na kallon Khalil tace “Yayanmu xaka shigo ne?” Khalil yace “Yeahh, ki tafi ina zuwa xan yi waya tukun…” Mimi ta kalli Nihad tace “Let go in Neehad” Nihad ta ki ce mata komai, Mimi ta kalli Khalil da ya fiddo wayarsa yana danne danne kamar zai yi sending call, Ta sake kallon Nihad sai kuma kawai Mimi ta juya ta bi bayan Nadeeyah, bayan sun yi nisa Khalil ya mayar da wayarsa aljihu yana kallon Nihad ya dawo kusa da ita yace “Why are you not going in?” A takaice Nihad tace “I am not staying in this house” Ya dinga kallonta, sai kuma yace “Why??” Ba tare da ta kallesa ba tace “Ban ga zan iya ba” Shiru yayi yana kallonta, ta jingina da motar ta rungume hannunta ta hade rai alamar she isn’t moving an inch, Ya jingina gefenta yayi kasa da murya yace “Ohk, How about we spending the night at the hotel together” Ta kallesa da sauri, ya dage mata gira, ta dauke kai tana jin gabanta na faduwa, ya kamo hannunta a hankali yace “Kinsan Mami ce tace ku zo nan yau, so it won’t make sense in maida ke gida ince kince baxa ki zauna ba for now reason, so kawai mu tafi hotel” yana gama fadin haka ya bude mata back seat yana kallonta yace “Ur usual spot” Nihad dai ta kasa cewa komai kuma ta ki shiga motar, wayarsa ne ya fara ring ya duba yaga Mimi ce, dagawa yayi tace “Yayanmu Kai Mumy ke jira fa bata wuce sama ba, or ain’t you coming in again” Da sauri yace “Ohk, ohk I’m coming” Daga haka ya katse wayar, yana kallon Nihad yace “Bari in je mu gaisa da mutanen gidan, idan na fito sai mu tafi hotel din” yana fadin haka ya nufi cikin gidan, Nihad ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, lkci daya hawaye ya cika idonta, why will they bring her to this house, gidansu wannan er iskar yarinyar, tasan baxata bi sa hotel ba but she will surely not stay in this house… Khalil na shiga ya tadda Mum din Nadeeyah xaune a parlor, ya gaisheta da ladabi ta amsa da fara’a tace “Ina bakuwar?” Yace “Yayanta ne ya kira take magana da shi a waje” Nadeeyah dai sai kallonsa take, Mumy tace “Allah sarki” Khalil ya kalli Nadeeyah dake zaune saman kujera suna hada ido ta dauke kai, tunawa yayi bai yi sallah ba ya mike da sauri yace “Mumy xan yi sallah in dawo yanzu” Mum din Nadeeyah Tace “Toh je kayi… Ga abinci xa a zuba maka kafin ka dawo….” Kofa ya nufa ya fita yana kallon parking space, bai ga Nihad a wajen da ya bar ta ba, yayi still yana bin compound din da kallo amma babu alamarta, cikin few seconds ya karasa gun mai gadi dake bakin gate yana kallonsa da sauri yace “Wata ta fita gidan nan yanxu ne Malam?” Mai gadin yace “Ehh bata dade ma da fita ba” Khalil ya zaro ido with shock yana kallon mai gadin ya kasa ce masa komai, sai kuma ya fice da sauri daga gate din, at first ya ma rasa ina zai bi don hanyoyi ne daban daban a area din, kawai ya dau hanyar titi, cikin minti kadan ya iso main road din duk da nisan shi, amma bai ga alamar Nihad ba, ya dinga bin ko ina da kallo zuciyarsa na bugawa, lokaci daya yaji wani xufa na keto masa at the same time ƙafafuwansa suka masa nauyi…. Sai da Nihad ta tabbatar tayi nesa da anguwan sosai sannan ta tsaya, ta cikin layuka tayi ta tafiya har ta ganta a wani babban titi, wanda hakan yasa ta gane she is very far away from the area she just left, tana ta tsaye bakin titi tana bin lafiyayyun motocin dake wucewa da kallo ta rasa next step din da xata dauka, she stood there for more than 15min a bakin hanyar kafin wani mota yayi parking kusa da inda take tsaye, ta koma baya tana kallon motar, wani mutumi da baxai wuce shekara 55 ba ya sauke glass yana kallonta yace “Yan mata ina zuwa? Ki shigo in rage maki hanya mana kina ta tsayuwa a nan” Nihad dake ta kallonsa taki cewa komai, yace “Haba yan mata ya kika yi shiru, naga tun daxu kike ta tsaye a nan, har na shiga wancan supermarket din na yi siyayya na fito” Sai a sannan Nihad tace “Bani da kudin mota ne, na yar da jakata” Yace “Subhanallahi, to shigo in ajiye ki inda za ki ko, Allah ya tsare gaba” Nihad tace “Sai dai ka bani kudin motar” Dariya yayi yace “Toh nawa ne kudin motar” Ta ɗan yi shiru sai kuma tace “Ko nawa ne ka bani” Yace “Toh amma me yasa baxa ki shigo in ajiye ki ba, ba fa ɗan yankan kai bane ko ɗan Kidnapper, Kinga dare yayi bai kamata mace kamarki na tsaye bakin hanya a wannan lokacin ba” Tayi shiru ta ki cewa komai, yace “Toh bari a baki kudin motar tunda baki yarda da ni ba, amma wani anguwa kike?” Tace “Can gaba ne” Ya ciro kudi ya mika mata hade da wayarsa yace “To sa min number wayarki yan mata” Ta amshi kudin ta ajiye masa wayarsa kan kujera me zaman banza tace “Nagode, amma bani da waya wallahi” Tana gama fadin haka ta ci gaba da tafiyarta da sauri, ya bi ta da kallo baki bude. Tafiya kawai Nihad take amma bata ga alamar adaidaita sahu ko daya unguwar ba, gashi ta gaji sosai abun ka da bata saɓa da tafiyar kafa ba, har lokacin kuma bata duba nawa mutumin ya bata ba, daga karshe ta ganta a gaban wani babban supermarket, a nan taga wani me adaidaita ta nufesa da sauri tace “Tasha zan je” yace “Wani tasha?” Tace “Inda ake hawa motar kano” yace “Toh mu je” tace “Nawa ne?” Mutumin yace “Dubu biyu” Nihad ta kalli kudin hannunta ta fara kirgawa taga dubu biyar ne, ta shiga adaidaitan, ya tada suka bar wajen, Nihad na isa tashan bayan ta ba mai adaidaita sahu kudin ta shiga ciki, ai ko ta samu mota da xai kama hanyar kano a lokacin, nan ta tambayi nawa ne kudin mota aka ce mata dubu takwas, tayi kuri da ido ta kasa ce masu komai don dubu uku kadai ne a hannunta, can ta koma gefe ta tsaya kamar munafuka, dreban motar yace “Hajiya nawa xaki bada?” Tayi shiru sai kuma tace “Ni bani da kudi amma idan na baka wannan xaka karba?” Tana magana tana kokarin ciro dankunnen kunnenta, duk da akwai haske a wajen sai da mutumin ya kunna fitilar wayarsa yana haska ɗan kunnen da kyau, can ya kira wani abokin aikinsa shi ma ya duba, Mutumin na kallonta yace “Ai kawai ki fadi nawa zaki siyar ba cuta ba cutarwa sai a baki kudinki ki cire kudin mota” Nihad tace “Ai ban san nawa zaka siya ba” Yace “Kin siyar dubu talatin?” Nihad dai tayi shiru sai kuma tace “Toh” Mutumin yace “Toh ina zuwa” Can sai gashi da cash din dubu talatin ya mika mata, Nihad ta amsa ta kirga dubu takwas ta basa, sannan ta shiga motar wanda duk maza ne a ciki, suka bar mata jikin window ta zauna…. Mami ce tsaye parlor tare da Mum din Nadeeyah suna kallon Khalil dake zaune saman kujera ya ki ce masu komai, kana ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, Mimi sai hawaye take, Noor dai na zaune saman kujera don tare da Mami suka zo gidan, Nadeeyah kuma na tsaye can kusa da dinning area, Mami tace “Magana fa nake maka ka min shiru Khalil, ina kake tunanin yarinyar mutane zata tafi da daddaren nan? Lokaci fa na wucewa” Mikewa yayi without looking at them yace “Nima ban sani ba” Daga haka ya nufi kofa, Nadeeyah ta bi sa da kallo har ya fice daga parlon, Mumy ta saki salati tace “Wallahi duka duka ko minti goma fa basu yi da shigowa gidan ba, har nake tambayarsa tana ina da naga ita bata shigo parlon ba yace tana waje tana waya da yayanta, ina yar mutane ta shiga ni Safeenah” Mami dai ta kasa cewa komai don hankalinta ya tashi ita ma, where are they going to start from, kasa ci gaba da tsayuwa tayi ta nemi kujera ta zauna tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji’un a zuciyarta…. Ko barin Abuja Nihad basu yi ba bacci ya dauketa a motar, Khalil bai jin ya taɓa shiga tashin hankalin da ya shiga a wannan lokacin, ko abinda Abbansa yayi masa bai daga masa hankali irin wannan ba, ganin abun yake kamar a mafarki fa, ya ma rasa wani tunanin zai yi, sai da yaga karfe goma yayi tashin hankalinsa ya fara fitowa sarari, tun takwas su Mami suka koma gida don barinsu ma yayi a gidan yayi wucewarsa, amma saboda yanda hankalin Mum din Nadeeyah ya tashi haka ta sake bin su gidan tare da Nadeeyah, Duk suna zaune parlorn Mami wajen karfe goma da yan mintuna khalil ya shigo parlon ta dalilin kiran da Mami tayi masa, Mami tayi karfin halin cewa “Nace ka kira gidansu ka ki, nace ka kira yayanta ka ki, to wai ya zan yi da kai, in ma baxa ka kira ba ni ka bani numbersu mana, wannan wani irin tashin hankali ne” Khalil that was trying all possible means to be calm yace “In kirasu ince masu me Mami? I should call and tell them I can’t find their daughter cikin daren nan? In kirasu ince masu an kasa rike yar su a gidanmu saboda kanwar Abbana tace baxata zauna ba kuma Mamina bata da abinda xata iya yi game da hakan? Mami ni na zata akan yarinyar nan sai inda karfinki ya kare, i thought zaki yi repaying good deeds din da iyayenta suka min ta hanyar riketa just like su Mimi, ina ce you will always be there for her, if not for her family i would have been depressed by now, right in front of u Abbana sent me away from his house and u couldn’t do anything about it, kina gani na bar gidan nan baki iya yin komai a kai ba, naje inda suka rikeni ba tare da sun san ni ba har suka damka min amanar dukiyarsu amma ta haka za muyi repaying dinsu mu kasa rike masu tasu er?” Mami dai kallonsa kawai take ta rasa abinda xata ce amma duk jikinta yayi sanyi, juyawa yayi ya fice daga parlon Nadeeyah ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, Hajiya Safeenah ta nemi kujera ta zauna tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Wajen karfe biyu da rabi na dare Nihad suka shigo garin Kano, tayi bacci har ta gode Allah a hanya, mamaki ya cikata ganin adaidaita har sannan a tasha, tana kallon wanda ke tambayarta inda xata tayi shiru, tana tunanin ko dai kawai taje hotel ta kwana tunda tana da kudi kuma tasan prices din hotels na Kano, nan ta gaya masa hotel dai dai kudinta ya tafi da ita kuwa, tana sauka ta basa kudinsa ta shiga ciki, ta biya kudin daki aka bata makulli ta wuce zuwa dakin, wanka ta fara yi a bandaki sannan ta dauro alwala tayi magrib da isha ta kwanta, amma ta kasa bacci sai juye juye kawai take, babu wanda ke ranta kuma a lokacin sai Nadeeyah, she just hate her with passion, bata son ganinta kwata kwata, da tasan gidansu zasu je da tun daga gidansu Khalil ta gudu don ko haduwa da ita bata so har cikin ranta…. Karfe takwas saura na safe Nihad ta tashi daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, ta fita waje zuwa supermarket dake kusa da hotel din ta siyo brush da maclean ta koma ciki, kafin karfe tara har ta gama shiryawa ta fito ta tare adaidaita yana tambayarta inda xata tayi shiru, don sai a sannan gabanta ya fara faduwa don bata san me xata je ta tarar a gida ba, kilan ma Abba ya koreta idan taje, amma a haka ta dake ta gaya masa inda xata sannan ta shiga adaidaitan a sanyaye, ya kama hanyar gidansu, tunda suka dau hanya gabanta bai daina faduwa ba, bayan tafiyar kusan minti talatin suka iso gidan, at first kasa sauka tayi daga cikin adaidaitan ganin ya juya yana kallonta, tayi karfin halin sauka ta basa kudinsa ta nufi gate tana tafiya a hankali, she is so afraid, daurewa kawai take, bude gate din tayi taga Aminu zaune bakin gate da er radio a hannunsa, yana ganinta ya zare ido ya mike da sauri yace “Hajiya” Ta ɗan yi murmushi tace “Aminu” Bakin Aminu har kunne ya dinga mata sannu da zuwa, sai kuma ya nufi waje da gudu duk zatonsa tare take da Khalil, Nihad dai ta ci gaba da tafiya gabanta na faduwa ganin motar Abbanta a parking space, taga motar ya Usman ma alamar yana gidan, har ta isa balcony dinsu ta kasa daga kafarta da kyau, tsoro ne fal zuciyarta, ta kusa minti daya a tsaye kafin ta murda kofar a hankali ta shiga ciki tana kallon parlon, Umma ta fito kitchen kenan rike da breakfast din da ta hada ma Nihal tayi sororo bakin kofa tana zaro ido tace “Wa zan gani kamar ‘ya ta Nihad?” tun da Nihad ta mata kallo daya ta dauke kai ta nufi bangaren Mumy tana tafiya a hankali, Umma ta buda baki with shock ganin abinda tayi mata ta bi ta da kallon mamaki, tuni Nihad ta bude kofar Parlon Mumy a hankali ta shiga, Mumy ta fito dakinta kenan tayi ido hudu da Nihad, still tayi bakin kofar dakin tana kallonta with surprise, Nihad ta tafi da gudu ta rungumeta cike da farin cikin ganinta, Mumy dai ta kasa motsi, can tayi karfin halin dago kanta tace “Daga ina?” Nihad na Murmushi tace “Gida Mumy” Mumy tace “Ke da wa??” Nihad tace “Ajiyeni yayi yaje ya dawo” Bude kofar Parlon aka yi duk suka daga kai, Umma ta shigo, Nihad na ganinta ta shige dakin Mumy ta kulle kofar, Umma tayi kasake a inda take tsaye, Can tayi karfin halin cewa “Ko ba Nihad bace?” Mumy ta kirkiri murmushi tace “Ehh wallahi, yanzun nan ta shigo na ganta nima” Umma tace “Allah sarki, to sannunta da zuwa, ina jin ta gaji ne” Daga haka ta juya ta fita daga parlon, Mumy ta juya ta koma dakinta da sauri tana kallon Nihad tace “Me yasa kika yi mata haka ta zo ganinki Nihad? Why did u leave the parlor” Nihad dai tayi shiru bata ce komai ba, Mumy tace “Why didn’t u greet her?” A hankali Nihad tace “I need rest, and beside ke na zo gani” Mumy dai ta kasa cewa komai ta dinga kallonta, Nihad tace “Mumy ina jin yunwa” A hankali Mumy ta juya ta fita daga dakin don kawo mata breakfast, Mumy na fita ko minti uku ba ayi ba Nihal ta shigo dakin….

52

Nihal ta karasa har inda Nihad take tana kallonta ta zauna gefenta with smile all over her face, a hankali tace “Welcome sis” Nihad ta sauke idonta tace “Thank you Nihal” Nihal tace “Ina Khalil din?” Nihad ta kalleta tace “He is fine” Nihal tace “Ohk ba tare ku ke ba?” Nihad tace “Ajiyeni yayi kawai” Nihal tace “Ohk, kinyi kyau sosai sis” Ta karasa maganar tana murmushi, Nihad dai bata ce mata komai ba, Nihal ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace “And i miss you so much” Nihad tace “Same here” Nihal tace “I am happy u are home” Shiru Nihal tayi bata ce komai ba, can Nihal ta mike a hankali tace “Zan je inyi wanka” Nihad tace “Ohk” Daga haka ta nufi kofa Nihad ta bi ta da kallo har ta fita, Tana fita da few minutes Mumy ta shigo dakin rike da tray, Hafsah na biye da ita da flask, cike da murna Hafsah tace “Sannu da zuwa Aunty Nihad” Nihad ta kalleta tana ɗan murmushi tace “Ya kike Hafsah” Hafsat tace “Alhamdulillah Aunty” Nihad tace “Ya aiki?” Hafsah na washe baki tace “Lafiya lau, munyi kewarki sosai Aunty” Nihad dai tayi murmushi kawai, Mumy dai ta zauna sai kallon Nihad take cike da mamaki, yaushe har ta wani san da zaman Hafsah a gidan balle har ta mata fara’a haka har da tambayarta ya aiki, Hafsah ta juya ta fita daga dakin, Nihad ta sauko ta zauna saman Carpet ta dau cup ta debi ruwan zafi, bayan ta gama hada shayin ta daga kai ta kalli Mumy taga kallonta take, Nihad tace “Mumy Nihal tayi rashin lafiya ne?” Mumy tace “Me kika ga?” Nihad tace “Aa kawai naga ta rame” Mumy tace “Tun dai kwanaki a school but she’s better now, kawai stress din makaranta ne, you know she is in her final year” Nihad bata ce komai ba, bayan few seconds cikin sanyin murya tace “Su sudais sun tafi school?” Mumy tace “Ehh…” Shiru Nihad tayi tana juya shayin gabanta, Mumy tace “Ya yan uwan mijin naki gaba daya?” Nihad tace “Duk suna nan lafiya, suna gaishe ku” Mumy tace “Toh maa sha Allah, shi xai shigo nan ne a hada masa breakfast?” Nihad ta girgiza kai tace “Aa sai anjima” Mumy tace “Toh shkkn” Mikewa tayi ta fita ta bata waje don ta karya comfortably don taga kamar duk a ɗari ɗari take. Nihad na gama breakfast din ta dau tray din ta fita main parlor, har ta mance yaushe rabon tayi breakfast cikin dadin rai haka, Zaune ta ga Nihal da Mumy a parlor, Hafsah dake goge goge ta taso da sauri tace “Bari in kai maki kitchen Aunty” Nihad tace “Aa Nagode, ci gaba da aikinki xan kai” Daga haka ta wuce kitchen din Nihal ta bi ta da kallo haka ma Mumy, Dai dai nan Umma ta shigo parlon daga bangarenta kamar warce aka hankado rike da makullin mota, ko lura da Mumy bata yi ba tana kallon Nihal tace “Idan Abbanku ya fito kice masa jikar Hajiya Turai ta fada cikin ruwan zafi yanzu aka kirani na tafi gidan, bana son tashinsa yana bacci, sannan don Allah ki tafi dakina zaki ga kayana saman gado duk na birkito ki jera min, sauri nake shi sa ban maida su ba” Nihal tace “Toh Allah ya sauwake” Mumy dake ta kallonta tace “Subhanallahi, ayi masu sannu don Allah” Tuni Umma ta fice daga parlon cikin hanzari ba tare da ta ma san Mumy na wajen ba. Nihad ta fito kitchen kenan sai ga Abba ma ya fito daga parlonsa jin tashin motar Umma don ba bacci yake ba, hada ido suka yi da Nihad, Sosai gabanta ya fadi ta makale jikin kofar kitchen din ko ina na jikinta ma rawa, Ita kanta Nihal dake zaune sai da gabanta ya fadi, Mumy dai ta sunkuyar da kanta kawai, Abba dai kallon Nihad kawai yake babu ko kiftawa, Nihad ta sauke idonta kasa, lokaci daya taji hawaye ya cika idonta, Abba ya dauke idonsa daga kallonta yana kallon Nihal yace “Ina Baabarki ta tafi?” Nihal tace “Wai jikar Mama Turai ce ta fada cikin ruwan zafi shine ta tafi” Juyawa Abba yayi ya koma parlonsa, Nihad ta bi sa da kallo hawaye na sauka idonta, mikewa Mumy tayi ta bar parlon ta shiga nata duk jikinta a sanyaye, Nihal ta karasa kusa da Nihad ta kamo hannunta a hankali tace “Mu je ki gaishesa” Nihad dai bata ce komai ba hawaye sai bin fuskarta suke, haka Nihal ta nufi parlon Abba da ita tana rike da hannunta, Zaune suka gansa parlon ya jinginar da kansa jikin kujera, Nihad ta ki barin su hada ido ta durkusa daga nan bakin kofar tayi gathering courage muryarta na rawa tace “Abba ina kwana” Yana kallonta bayan few seconds yace “Me ya kawo ki gidana?” Ta girgiza kai hawaye me zafi na sauka idonta tace “Kayi hakuri Abba” Bai kuma ce mata komai ba sai dauke kansa da yayi daga kallonta, staring at the Ac in his parlor, Nihal ta juya ta fita daga parlon hawaye cike idonta, mikewa Nihad tayi da sauri ta bi bayanta tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, Abba ya bi ta da kallo lokaci daya yaji hawaye ya kawo idonsa, mikewa yayi ya shige bedroom dinsa, Nihad ta koma bangaren Mumy ta shiga bedroom dinta ta ga Mumy zaune gefen gado looking so worried, fadawa kan gadon Nihad tayi tana kuka a hankali, Mumy tayi karfin halin cewa “Me yace maki? Yace ki bar masa gidansa ko?” Nihad ta kasa cewa komai sai kuka take sosai, Mumy bata san sanda ita ma ta fashe da kukan ba, taji zuciyarta na mata zafi, Nihad na ganin haka ta mike da sauri ta rungumeta tana kuka sosai tace “I am sorry i never listened to you mum, kiyi hakuri ki yafe min plsss…” kasa ci gaba tayi saboda kuka da ya ci karfinta, Mumy tayi karfin halin cewa “Baki min komai ba Nihad, na yafe maki duniya da lahira, babu abinda kika min, haka Allah ya tsara maki rayuwarki babu kuma wanda ya isa ya canza hakan” Nihad na kuka bitterly tace “Amma Mumy baki taɓa ce min Umma ba so na take ba, u never told me she is misleading me, nobody was there to tell me all this, Umma caused me all what i am passing through now” Mumy ta dakatar da kukan da take tana sauraronta babu ko kiftawa, Cikin kuka sosai Nihad tace “Duk abinda nake yi a baya Umma ce take sa ni inyi, she neva gave me the chance to differentiate what’s good or bad, she is always supporting me in every aspect, i don’t know she was just ruining my life, ta cuci rayuwata, me yasa baki taɓa gaya min bata sona ba, me yasa baki gaya min ba masoyiyata bace? mumy me nayi mata?” Mumy ta girgiza kai kawai wasu hawayen na sauka idonta ta kasa ce mata komai, A hankali Nihad na girgiza kai sounding bitterly tace “Ita ta karfafa min gwiwa wajen yin kawance da su Husnah, she encourage me to follow them everywhere, ta nuna min duk wani dake aiki a gidanmu bashi da value i should treat them harshly idan ba haka ba za su raina ni….” Mumy tayi shiru sai sauraron Nihad take, Nihad tace “Mumy ba wani gidan Aunty Kamila da naje, duk watanni hudu da nayi bana gidan nan ina hostel tare da su Husnah, i never went to Auntt Kamila’s place Umma planned it for me….” Mumy bata san sanda ta mike tana kallon Nihad babu ko kiftawa ba, Nihad na share hawayen da yaki tsaya mata cike da karfin hali tace “Ita tace ma Kamila ta kira Abba tace za mu je kebbi amma babu wani kebbi da muka je, all those while i am staying in the hostel with my frnds, duk wani hotel da party da su Husnah za su Umma tasan ina bin su ita ke encouraging dina in bi su, duk sanda na fita da daddare zuwa party Umma ce ke bude min kofar parlor babu wanda xai sani, tun da na taso muke haka da Umma…..” Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka me ban tausayi, she is deeply regretting everything now, tayi da ta sanin abubuwa da yawa da tayi a baya, nobody was there to tell her Umma ba sonta take ba all that while, wasu abubuwan ma baxata iya gaya ma Mumy ba amma Umma ta cuceta ta cuceta iya cuta, sannan ta nuna mata da ma duniya gaba daya babu wanda take so sama da ita, Mumy dai ta kasa cewa komai sae kallonta take babu ko kiftawa, kana ganinta kasan she is shock, don duk bata san da abubuwan nan da Nihad ke fadi yanzu ba, ta dai san komin laifin da Nihad xata yi a gidan Umma bata barin a mata fada sai ta nuna ai yarinya ce babu abinda ta sani, sannan ko me take so wajen Abba Umma ke taimaka mata wajen amsa, ko kai maye ne baxaka ce Umma bata son Nihad da gaske ba, sai ta siya ma Nihad abu sau goma bata siya ma er ta Nihal ba, wannan ne ma ya sa Mumy ta kara jawo Nihal jikinta sosai…. Nihad ta zamo kasa muryarta na rawa tace “Don Allah ki yafe min Mumy, amma ban taso na gan ni a wajenki ba, i never knew u were my mother at first, Mumy me yasa kika bar ma Umma ni? Why did u hand me over to her?” Tana kai wa nan ta hade kai da gwiwa tana kuka sosai, Wani kuka ya taho ma Mumy bayan memory din yanda Umma ta rabata da Nihad ta karfi da yaji tun tana 5 years ya dawo mata vividly…. Mumy tayi duk iya kokarinta na ganin Abba bai dauke Nihad daga wajenta ya damka ma Umma ba har hakan sai da yayi sanadin igiyar aurenta daya a gidan, babu irin bakaken maganganun da Inna bata gaggaya mata ba a wancan lokacin wai bata da kara bata da kunya akan yar ta ta fari, ina ruwanta da er ta na fari da har zata zakalkake a kanta tana nuna tafi kowa iko da ita sae kace ba bafillatana ba, banda zamani ya lalace, su zamaninsu babu macen da ta isa tayi haka, har inna ke kara tunatar mata cewa Umma bata rike ɗan ta na fari da na biyu ba bata ma san ta yanda suka girma ba ta kauda kai a kansu kamar ba ita ta haifesu ba, Ya Farooq da ya Usman basu taso wajenta ba, tun daga yaye inna ta daukesu suka koma wajenta a Bauchi kuma Umma bata taɓa cewa don me ba, yawancin rayuwarsu duk a wajen Inna suka yi a lokacin ma kakansu na da rai, sae ya kasance Kamila ce kawai gaban Umma and she never complained for once, har dai ta zo ta haifi Nihal, washegari kuma Mumy ta haifi Nihad, wanda sai da Mumy tayi shekara goma a gidan kafin ta haihu, duk tana gidan aka haifi Usman da Kamila amma ita Allah bai bata haihuwa ba, dalilin da yasa da ta haifi Nihad Abba ya dau son duniya ya daura mata gashi fara ce kal kamar zaka latsa ta jini ya fito, ga masifar kyau kamar er larabawa, dama shi farin yaro da shegan shiga rai yake, ita kuma Nihal baƙa ce amma suna kama sosai da Nihad, sai ya dau Nihad sau goma bai dau Nihal sau daya ba don Nihal tana da kiwiya sosai shi sa ma bai bin ta kanta, ba ta yarda da kowa sai Umma, hakan yasa yafi shakuwa da Nihad da ko muryarsa taji ta dingi kuka kenan sai ta gansa ya dauketa, shakuwa me tsanani ya shiga tsakaninsu ya dau soyayya mara iyaka ya daura mata, har cikin ransa yake jin Nihad, wanda Mumy na lura da Umma kamar hakan baya mata dadi don bata iya boye hakan a fuska, ga kuma er ta Nihal shegen kiwiya da kuka, Mumy kan ce ma Abba ya daina bambanta su kar a samu matsala, nuna banbancin bashi da amfani don duk daya suke a wajensa, amma sai yace mata ai Nihal kiwiya gareta bata yarda da kowa, haka rayuwa ya ci gaba har aka yayesu, tun Nihad na shekara uku Umma ta fara nuna tafi damuwa da ita akan Nihal kamar yanda taga Abba ke yi, ta sha attempting mayar da Nihad dakinta gaba daya amma Mumy taki bada fuskar hakan, don babu Alkunya take shiga ta dauke er ta ko da kuwa bacci take a dakin Umma komin dare kuwa, ko hularta bata yarda ta bari a dakin Umma, Umma bata hakura ba har sai da ta san yanda ta hada makircin da ta hada tare da goyon bayan Inna Nihad ta dawo wajenta, Wanda har sai da Abba ya saki Mumy akan issue din wai tana son raba masa kan gida, ga inna ta saka ta gaba da gore gore wai ai ba da ita ta zo gidan ba sannan ina ruwanta da er ta ta fari idan ba rashin kunya ba, karfi da yaji dai aka raba Mumy da Nihad, babu yanda Mumy ta iya tana ji tana gani ta cire hannunta akan wasu lamarin Nihad ta bar ma Umma gaba daya, and that was the genesis of the whole problem…. Mumy ta kasa ci gaba da zama dakin ta fita kawai ta koma parlor tana jin xuciyarta na mata zafi, Umma ta cuceta ta cuceta, ita kuwa bata ma er ta irin rikon da tayi ma Nihad ba, Nihal da kanta ta koma bangaren Mumy a lokacin ma tayi shekara goma, tana ji tana gani sae Umma ta hana Nihad shigowa wajenta, babu kusanci kwata kwata tsakaninta da Nihad, to amma ya zata yi, tunda ga abinda mijinta da uwar mijinta suka ce, kawai sae ta rungume Nihal tana ganinta kamar yar cikinta. Nihad ta ci kukanta ta koshi ta mike ta koma saman gadon Mumy ta kwanta ta rufe idonta a hankali tana jin kanta na ciwo, a haka har bacci ya dauke ta. Wajen karfe goma da wani abu Nihad ta bude ido a hankali ta dalilin tashinta da aka yi, ta mike zaune tana kallon Nihal dake zaune gefenta, Nihal tace “Ana kiranki a parlor” Nihad na murza idonta tace “Waye?” Nihal ta mike tace “Ki fito” Daga haka ta mike ta fita daga dakin, Nihad ta mike da kyar ta nufi kofa ta fita Parlon Mumy, zaune ta gansa duk ya wani birkice yana kallon kofar dakin eagerly, suna hada ido ta sunkuyar da kai a hankali, Nihal ta juya ta fita ta rufe kofar parlon, sai a sannan ya mike da sauri, Nihad tayi saurin juyawa zata koma dakin yayi hanzarin bin ta har ciki ya fizgota, zaro ido tayi tace “Don Allah ka bari kar wani ya shigo” kin yarda su hada ido tayi taki dago kanta, da taga he is trying to raise her head up kawai ta kwanta saman kirjinsa tayi lamo, she could feel how fast his heart is beating, ta lumshe idonta a hankali, ya rungumeta sosai, Underneath his breathe taji yayi maganan da ita kanta bata ji ba, jin hawayenta a jikinsa ya dago kanta da sauri yana kallonta, kasa barin su hada ido tayi, cikin rawan murya tace “I am… Am sorry, i…” sai kuma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka, Lokaci daya ya saketa jin an bude kofar parlor, ta goge idonta da sauri ta fito parlon sai ta ga Nihal ce ta shigo rike da ruwa da lemo, Khalil ya fito parlon shi ma ya zauna, Nihal dai bata yarda ta hada ido da su ba. Tashin hankalin da Mami ta shiga ba a cewa komai da ta shiga dakin Khalil da sassafe taga baya ciki, kuma bata ga alamar ma a dakin ya kwana ba, tun sannan take kiran duk layinsa taji su a kashe, ta ma rasa takamaiman abinda zata yi, tun cikin dare take Allah Allah gari ya waye ta samesa tace masa ko za su je can kano ne gidan iyayenta ko Allah ya sa can ta tafi, sai gashi ta shigo babu shi a dakin, ta dawo bangarenta cike da damuwa, tana zaune tare da Mimi a parlon tace “Kuma ko number yayanta baki da shi ko?” Mimi ta girgiza kai a hankali tace “Bani da shi” Bude kofar parlon aka yi, duk suka daga kai, Mami ta dinga kallonsa da mamaki don in ba dai tana kwance ba lafiya ba baya shigowa bangarenta kai tsaye haka, sannan ko minti ashirun bai yi da dawowa gidan ba, kuma ba ita ce ma da girki ba, Mimi ta mike ita ma tana kallonsa tace “Good morning sir” Bai amsa mata ba ta nufi kofa ta fita, Mami na ganin yanayinsa ta san ba lafiya, to me kuma ya faru, ta dai mike cikin dakewa tace “Lafiya kuwa Yallabai? Is everything alright” Yana huci yace “Stop asking me that, Ina Ibrahim? Provide him now” Mami sai da gabanta ya fadi, tayi karfin halin cewa “Is everything alright” tsawa ya daka mata yace “Ina maki tambaya kina amsa min da tambaya?” Ta koma ta zauna bata sake ce masa komai ba, ya sake jefo mata tambayar ina Ibrahim, a fusace tace “Tunda dai ba goya Ibrahim nake ba ta ina xan san inda yake da sassafen nan? Ba dai ka san hanyar dakinsa ba” Yana muzurai yace “Ohh haka kika ce?” Tace “Ya kake son ince? Naga dai ba nan yake kwana ba da ka zo nemansa a nan, za ka wani zo ka isheni ina Ibrahim” Ya fi second ashirin yana kallonta yana gyada kai, kafin ya juya ya fice daga parlon almost ripping the door off, tagumi tayi tana tunanin to me kuma yaron nan yayi? Wannan wani irin fitina ne ita kam, Noor ce ta shigo parlon tana kallon Mami a sanyaye tace “Mami kin san me Yayanmu yayi?” Mami da taji gabanta na faduwa sosai tace “Me yayi Noor?” Noor ta zauna cikin sanyin murya tace “He broke into Abba’s room and collected all what Abba seized from him, lalata makullin dakin ma fa yayi” Buda baki Mami tayi ta kasa cewa komai zuciyarta na bugawa, Noor tace “Ina jin cikin dare kowa na bacci yayi haƙan, he scattered everywhere in the room” Mami ta saki salati ta rafka uban tagumi tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” sai ga Aunty Hassana ta shigo parlon babu ko sallama cike da rashin mutunci tace “Ke kam fatima kin haifar mana fitina a gidan nan, don Khalil fitina ne wallahi….” Mami ta dakatar da ita tace “Ban haifi fitina ba sai in ke kika haifi fitina wallahi”

53

Mami bata tsaya ta kara sauraran Aunty Hassana ba ta mike ta shige dakinta ta shirya ta fice ta bar masu gidan daga ita har yayan nata zuwa gidan Hajiya Safeenah. Tana zaune parlon Hajiya Safeenah abun duniya ya isheta, Hajiya Safeenah tace “Na fa ce ki kwantar da hankalinki Hajiya Fatima, yarinyar da har nude video dinta yayi yawo a gari ai kinsan dama can idonta a bude yake kome aka ce ta aikata to zata iya aikatawa, ke dai kawai Allah ya shirya mana zuri’a, kuma babu tantama kila gidan nasu ta koma, ke kuma kina nan duk kin bi kin daga hankali” Mami dake ta kallonta tace “You have a point, sai yanzu da kika yi maganan nan na tuna wacece yarinyar, duk yaron da idonsa yayi budewar da nata yayi koma meye zai iya aikatawa gaskiya kika fada, ni fa wallahi bani da yanda xanyi ne amma ni ba wai son zamanta nake a gidana ba, haka kawai taje ta kara aikata wani abun da ba shikenan ba, gashi baka gane gabanta balle bayanta, nukurcinta yayi yawa, sannan kwana biyun nan ina ta lura da yanda Khalil din ke shige mata, sam bana son haka….” Hajiya Safeenah ta rike haɓa tace “Au, ashe kema dai kin lura, jiya bayan mun dawo gida zancen da Nadeeyah ta kawo min kenan….” Mami tayi shiru da tunani iri iri a ranta, can ta sauke ajiyar zuciya tace “Wallahi abun ya dameni, to yace mana wajen iyayenta ya zauna a kano ya zanyi masa, ga Maryam me goyan bayansa, tukunna ma dai wasu irin iyaye ne xasu hada yar su da gandameme kamar Khalil wai su taho Abuja tare sannan ya bar ta a gidansu wai zata yi karatu? A ina aka taɓa haka kamar dai garin gaɓa gaɓa aka taso? Idan ma haka ne ai kamata yayi uwar ko uban wani ya biyota sai a damka mana ita a hannu ace gata nan don Allah zata yi karatu a sa mata ido, to wai sai aka hadata daga ita sai khalil ya kawo mana ita, ko marasu addini baxa su yi haka ba, ni wallahi na rasa yanda zanyi ne, i have a big question mark on this issue, ga Maryam tayi ɓake ɓake kan lamarin sai goyan bayansa take wai sai an riketa tunda iyayenta suka rike shi, to shi ba namiji bane ko da da kafafuwansa yaje gidan nasu shi kadai, ita kuwa ai sai cikin iyayen wani ya rakota saboda halin rayuwa, komai fa na son tsari a rayuwar nan, amma sam wannan lamarin ba tsari, a hada baligi da baliga wa enda ba muharraman juna ba” Hajiya Safeenah tace “Gaskiya abun dubawa ne wannan, kuma kika ce kwanaki yayanta yaje gidan ko?” Mami tace “Ehh yaje kam, amma ko da iyayen ma baxa su biyota ba ai sai su ba yayan nata ya kawota ba Khalil ba, it’s making no sense to me now, tun farko ya kamata inyi masa wannan tuhumar amma hankalina bai je ba, sannan ban taɓa jin an kirata daga can gidan nasu ba ko kuma ita ta kirasu” Hajiya Safeenah tace “Toh dai ki kara kiran layukan Khalil din ko xaki samu, aji in gidan ta koma kin ga hankalin kowa sai ya kwanta, sai kuma a koma next issue that’s on ground” Mami ta sake dialing number Khalil, luckily ya fara ring, gyara zama tayi ta sa handsfree tana jiran ya daga, sai da ya kusa katsewa sannan ya dauka, tace “Khalil me ya kai ka dakin Abbanka?” Khalil ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Ajiyata na dauka Mami” Mami ta bude baki tana kallon Hajiya Safeenah, can tace “Ajiyarka? Wato khalil duk yanda zaka daga min hankali shi kake nema a rayuwarka ko? Ba nace ka fita batun abubuwanka da ke hannun Abbanka ba? Me yasa baka jin magana ta ne fisabilillah” Khalil yayi kasa da murya yace “Mami i did nothing wrong, bayan takarduna babu wani abu da na taɓa masa a dakinsa, i seriously need them Mami, tunda ke baxa ki iya dauko min ba shine fa na dauka da kaina Mami….” Mami ta buda baki, ta ma rasa abinda xata ce masa, can tayi karfin hali tace “Duk inda kake ka dawo ina nemanka immediately, sannan kada kayi making mistake din zuwa gida ka zo nan gidan Hajiya Safeenah ka sameni” Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Toh” Mami zata katse wayar, Hajiya Safeenah tace “To baki tambayesa batun yarinyar ba” Mami da har ta manta tace “Ohh, Sannan ita kuma yarinyar can ina fatan gidansu ta tafi?” Khalil yayi shiru kamar baxai ce mata komai ba, sai kuma yace “Eh” Mami tace “Toh madallah, sai ka gaya ma iyayen nata taki zama Abujan, it’s better kawai su nema mata transfer ta koma Kanon da karatu ya fi” Khalil dai bai ce mata komai ba, tace “Baka ji na ne?” A hankali yace “Ina ji” Tace “Then do as i say, kai kuma immediately ka taho gidan Hajiya Safeenah ina jiranka” Yace “Ni bana Abuja yanzu” Buda baki Mami tayi tace “Kana ina?” Yace “Ina kano” Tace “Ohh kanon ka bi ta? Kana nufin kanon ka kama hanya ka tafi ko gaya min baka yi ba? To ka kyauta, maza maza ka nemi next flight ka taho Abuja yanzu” Yace “Ba jirgin da zai tashi yau saboda weather” rai bace Mami tace “To wannan kai ta shafa ka biyo mota kawai ka dawo na gaya maka” Daga haka ta katse wayarta, cike da fada tace “Banda ma lalacewa tunda yarinyar ta zo gidan daga uwar har uban babu wanda ya taɓa kira muka yi magana da su, don su ma ji ya yarinyar take, kawai ga ta nan dai kamar bata da iyaye, kana da ya mace har hankalinka zai kwanta idan bata gabanka, babu wanda fa ke bibiyar lamarinta nake gaya maki, duk ina lura da komai, kinga ai saboda tsabar yanda idonta ya bude ai Kano ta kama hanya tayi wucewarta daren jiya, wanda bai saba ba ai baxai yi haka ba, ko tsoron dare bata ji ba, dama can ta saɓa abunta ne, Allah ya shirya” Hajiya Safeenah ta sauke ajiyar zuciya, Mami tace “Tun farko da ya samu matsala da uban Yemen nace ya tafi ya ki, na dawo nace ko zai je Uk nan ma yaki, all that while ban san yana kano ba na dai san yana Nigeria, to gidan wasu irin mutane ne ya zauna wa enda basu da kula haka? Ka sakar ma duniya yar ka mace a wannan zamanin, sannan ga dai abinda yarinyar nan tayi ko wata uku ba ayi ba amma har ku sakankance baku bibiyar lamarinta, a’a ban taɓa ganin haka ba tun da nake” Hajiya Safeenah tace “Yanzu dai Hajiya Fatima kiyi hakuri, a bi komai a sannu ki kirasa ya bar zuwan nasa gobe tunda yace ba jirgi, biyo mota daga kano zuwa Abuja ai aiki ne babba yanzu, kawai ki masa hakuri ya bari har gobe, bari in kirasa” Daga haka Hajiya Safeenah ta kira Khalil, nan ta sanar masa kawai ya bari gobe sai ya biyo jirgin safe, bayan ta katse wayar Mami tace “Dama yana dawowa duk zan amshe takardun in mayar ma uban baxan iya fitina ba, idan jiƙawa zai yi ya shanye sai ya jika ya shanye, babu abinda zai raga Khalil da shi” Hajiya Safeenah tace “Aa kar kiyi haka, ki bar wannan issue din tsakaninsa da ubansa kawai kar kiyi involving kanki, gaskiya kar kiyi haka, kamar yanda ya fada ke baki amsar masa ba kuma ya amsa sai kice xaki mayar?” Mami tace “Wallahi mayar masa shine kadai mafi alkhairi gare mu gaba daya, sai kace baki san General ba, ni duk wani abun tashin hankali bana so wallahi, har fargaban zuwa asibiti nake yanzu yanda nake ji a jikina sai ya iya yiwuwa jini na ya hau” Hajiya Safeenah tace “Allah ma baxai sa hakan ba, kawai kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Hajiya, komai zae zo da sauki” Mami ta taɓa baki tace “Ya batun programs na bikin, kun gama shawaran da Hajiya Hauwa?”

Bayan Azahar ganin Khalil bai shigo ba Mumy na kallon Nihad tace “Ki je kiyi masa magana ya shigo ya ci abinci” Nihad da tunda tayi sallah take zaune saman darduma a bedroom din Mumy ta mike ta dauke darduman ta linke sannan ta fita, Hijab ne har kasa jikinta don ta shiga bedroom dinta ta kwaso sauran kayanta ta kawo bangaren Mumy ta ajiye, har zuwa sannan kuma Umma bata dawo gidan ba, babu kowa main parlor din ta fito compound ta gansa zaune tare da Aminu, ɗan zaman da Khalil yayi a wajen babu abinda Aminu bai sanar masa ba da ya faru a gidan bayan tafiyarsu sai wanda ya manta, dawowar Kamila gida, matsalar da Usman ya samu wajen aikinsa, rashin walwalan Abba a ko da yaushe tun tafiyarsu, yanda Umma ke fita ta dawo dab da magrib kafin Abba ya dawo motarta duk jan laka, zuwan karshen da Inna tayi gidan ta zauna nan compound tana ta tikar kuka wai an rabata da Nihad an daura mata aure da ɗan kauye tana can ita ma ta zama er kauye, sabon dreba da aka kawo me warin baki da warin hammata ga shegen gulma, murmushi kawai khalil ke yi yana kallon Aminu da ke basa labaran nan with passion babu abinda yake tsallakewa a labarin, in details yake badawa, he is so good in it, in wanda xai yi demonstrating ne sai ya tashi yayi demonstrating sannan ya koma ya zauna, yana cikin basa labarin yanda banki suka zo suka kulle gidan dake can karshen layi saboda bashinsu da ya ci na fitar hankali sai ga Nihad ta karaso, duk abinda Aminu ke cewa Khalil baya apprehending tun fitowar Nihad, don ainahin kamshin da ya santa da shi ne ya cika wajen still dai bai daga kai ya kalleta ba, Aminu ya mike yana washe baki yace “Sannu Hajiya, sannu da karasowa….” Nihad tace “Sannu Aminu” Daga haka ta kalli khalil tace “Mumy tace ka shigo ka ci abinci” Sai a sannan ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace “Kawo mana nan” Tayi shiru tana kallonsa, can ta juya ta bar wajen ya bi ya da ido har sannan kamshin na dukan hancinsa, sai da tayi nisa Aminu ya koma ya zauna yace “Kai mutumina, amma kayi jahadi wajen dawo da yarinyar nan hanya mai bullewa, wallahi duk jikina yayi sanyi kamar ba Nihad din da na sani ba a baya, dubi fa yanda ta zama ta gari, ko da dai dama wannan matar uban nata ce ke zugata duk mun sani, wani nutsuwa na musamman fa take da shi yanzu, shi yasa jiya da naganta ta dawo ita kadai na maza na kiraka inji ina kake don na zata guduwa tayi, ashe dai ta nutsu, sannan ga….” Khalil ya dakatar da shi ta hanyar cewa “Ina jinka, sai bankin suka kulle masa gidan” Aminu ya gyara zama yace “Wallahi kuwa in gaya maka, bawan Allahn ya fito yayi ta birgima a layin nan duk muka taru kansa, ga matansa da ya’yansa a gefe abun dai zar tausayi, an fa ce caca yake yi, kuma ɗan giya ne…..” Khalil ya dinga kallon Nihad da ta fito, hakan yasa Aminu yayi shiru yana ɗan murmushi ganin Khalil bai ma san me yake cewa ba, har ta iso inda suke da tray din abincin ta durkusa gabansa ta ajiye, shi dai kallonta kawai yake, ta mike tace “Me sanyi ruwan za a kawo?” Sae a sannan ya dauke idonsa yace “Duk wanda kika kawo” Juyawa tayi ta bar wajen still ya bi ta da ido, the perfume is just something else, Aminu dai sai wani murmushi yake irin na rubabbu, yau wai Nihad ce ke kawo ma Khalil abinci har ta durkusa ta ajiye masa a gabansa yarinyar da har hana a basa abinci tayi a gidan, Aminu ya rike haɓa uwa ɗan daudu yana nazari… Sai bayan la’asar Khalil ya shiga cikin gidan shi ma Sudais ne ya zo yace masa Mumy na kiransa, parlor ya samu Mumy, Mumy tace “Kana ta zama a waje Ibrahim” Ya ɗan yi murmushi yace “Muna tare da Aminu ne” Tace “Kuma ba rana” Yace “Aa babu” Tace “Toh ko bayan magrib ne sai ku tafi can gidan Inna ku gaisheta” Yace “Toh Allah ya kai mu” Bai wani jima a parlon ba tunda ba wai hira suke da Mumy ba ya fita ya koma gun Aminu, Mumy ta koma parlonta tana kallon Nihad tace “Me yasa baki je dakin er uwarki ba Nihad?” Nihad dake game da wayar Mumy tace “Naga kamar bata son magana ne, i don’t want to inconvenience her” Mumy ta zauna tana kallonta tace “Amma ai ta shigo nan har sau nawa saboda ke Nihad” Nihad tace “Ko ta shigo ba magana take ba, i don’t know why she is silent” Mumy bata kuma cewa komai ba, bayan few minutes tace “A ina kuke a Abujan?” Nihad tayi shiru, sai kuma ta daga kai ta kalli Mumy ganin kallonta take, ta sauke idonta a hankali tace “Maitama” Mumy ta ɗan bude ido tace “Maitama kuma? Akwai wani maitaman ne bayan wanda na sani?” Nihad ta girgiza mata kai tace shi wannan din ne, da mamaki Mumy tace “Wajen wa a Maitama?” Ita dai farooq yayi assuring dinta sosai yace ta kwantar da hankalinta Nihad is doing very fine, idan ya zo kano za su yi magana, iyakar abinda ya gaya mata kenan amma bai gaya mata anguwan ba ko inda take, Mumy tace “Kin yi shiru” Nihad ta ajiye wayar hannunta a hankali tace “Gidan iyayensa” Mumy look so confuse, tace “Wani iyayen nasa kuma?” Nihad ta sauke idonta tace “He is the son of General Jikamshi” Kallonta kawai Mumy take, can tace “Are you okay Nihad?” Nihad ta kalli Mumy, a hankali tace “He disguise himself, I don’t know his reasons, I don’t know…. but they are rich, he is the son of General Abubakar” Mumy da duk kanta ya daure tace “Ke ban gane ba, wani general din? Sannan ba Aliyu bane ɗan gidan General? Kanki daya kuwa Nihad, ko dai zaki je ki kwanta ne….” Nihad tayi wani murmushi kawai, can ta girgiza kai ta goge hawayen da ya taru idonta tace “Aliyu lied to me, ba shine yaron jikamshi ba, Jikamshi is just his uncle which is Khalil’s father” Sai kuma ta fashe da kuka cikin sanyin murya tace “Mumy naga abubuwan iri iri in just 3 months from every angle, Khalil isn’t who we thought him to be, i don’t know his intent of coming to our house, I don’t know his intent of coming here as a driver, they are super rich, his father is a General, his mum is from Yemen, i don’t just….” Sai kuma ta hade kai da gwiwa tana kuka a hankali bayan ta tuno abubuwa da yawa, Mumy was speechless, ta ma rasa me xata ce, sai kallon Nihad din take inna State of confusion, kuma har cikin ranta taji bata yarda da abinda Nihad ta fada ba, seems bata da lafiya, Mumy ta mike ta dagata tace “You need rest, go and have some rest” Har dakinta ta kai ta ta kwantar da ita saman gado, Mumy na ta kallonta har ta rufe ido sannan ta juya ta fita daga cikin dakin.

Bayan Magrib Nihad ta gama shiryawa ta sa Hijab dinta har kasa, tun labarin da ta ba Mumy da la’asar Mumy bata dawo dai dai ba kuma ba wai ta yarda da zancen Nihad bane, a’a kawai gani take kamar ƙwaƙwalwarta ya fara taɓuwa ne as a result of all what she passed through, gani take she isn’t in her right senses, gani take kawai sambatu take ba wai don tasan abinda take fada ba, Mumy ta nuna mata inda Makullin motarta yake, Nihad ta dauka, a hankali tace “Sai mun dawo Mumy” Mumy bata iya ta ce mata komai ba ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin, Mumy ta jingina da kujera rai ba dadi, ita dai tasan Nihad bata da lafiya don sanyin nata ma yayi yawa, Mumy bata san sanda ta fashe da kuka ba tana fatan kada ace ƙwaƙwalwarta ne ya samu matsala. Khalil na tsaye parking space bayan ya gaisa da Abba, sae dai Babu yabo babu fallasa Abban ya amsa masa har ya shiga ciki, yana ta jiran Nihad har ta karaso ta mika masa makullin motar ya amsa yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba duk da ta dai ga ya canza kayan jikinsa, ta zaga ta bude kofar gaba zata shiga yace “Aa koma normal spot din ki….” Ta ɗan yi jim sai kuma ta sauka ta koma back seat, ta madubin mota yake kallonta har ya tada motar yayi warming suka bar gidan, She doesn’t look like the normal Nihad anymore, seems abubuwa da yawa suna damunta a zuciya, this is a new Nihad he is seeing for 2 months now, har suka isa gidan Baffanta bata sani ba don tayi nisa a tunanin da take, yayi parking yana kallonta, ta dago kai ta kalli anguwan da suke da sauri, sai kuma ta bude motar ta sauka shi ma ya sauka. Tana gaba yana bin ta har suka shiga gidan, Hamid na zaune parlor Nihad bata kallesa ba ta shiga bangaren da Inna take, Khalil ya karasa har inda yake ya basa hannu sannan ya juya ya nufi bangaren Inna, Inna ta tsaya rike da darduman hannunta tana ta kallon Nihad, sai kuma ta fashe da kuka kamar yar yarinya ta ajiye darduman hannunta a gefen gado, ta zauna kasa tace “Allah ya isa tsakanina da duk wanda yayi sanadin rabani da ke, ko ma waye Allah ya saka min, Allah ya walakanta shi….” Sai kuma ta kalli Khalil da ya durkusa bakin kofa, ta wani tsuke fuska tace “Kai kuma haka ake yi kawai ka dau yar mutane ka tafi da ita kauyen Nijar saboda Allah ya ci da kai an aura maka ita babu ko sisinka, yau ga karfin hali ni patu, kai ba kowan kowa ba dillalin kashi a leda zaka dau min jika ka mayar kauyenku? Ashe haka buzaye suke basu da kamun kai basu da lissafi bamu sani ba, yau ko da kudinka aka aura maka ita zaka dauketa ka kaita kauyen ku balle babu kwandalarka, ina ma kaga kudin aurenta, wato ka samu xukekiyar yarinya a bagas shine ka tafi kana ta fafa da ita a kauyenku kai ga ɗan banza” Shi dai khalil kansa na kasa sai ɗan murmushi yake, Nihad kuwa banda hararanta babu abinda take tana turo baki, Inna ta rike haɓa tace “Tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin wannan azababben karfin halin ba, banda kaddara me Nihad zata yi da kai ɗan nan, ai kai ba ajinta bane tafi karfinka ta ko ina, iyaka kayi aikinka na dreba ka kama gabanka amma ina kai ina auran yar masu gida banda ƙaddara da ta riga fata, ɗan gidan Habubakar Jikamshi ne saurayinta fa wannan dai da kayi ma walakanci kwanakin baya, wanda da ba don mutuncina da na ubanta ba da ya daureka har karshen rayuwarka ka rube a gidan yari, wallahi mun sha gaisawa da shi yafi a kirga ta waya, abinda idan bashi da number mutum ma baya samunsa ba ko wani gaja yake waya da ba, sai in shi ya yi niyyar kiran mutum” Nihad tayi karfin halin cewa “Dama gaisheki muka zo yi” Inna tace “Toh ya tashi ya tafi sai kin huta haka kuma, wato ga ki ya sameki a banxa sai dai Ibrahim ya tura masa kudi kaca kaca, shi gashi ai sai kyau yake yana kara budewa uwa kirjin zai yage, ke kuma duk kin tsamure kin kanjale ke da kudin ubanki, da kyar idan kina samun abinci ma kina ci sau uku a rana” Khalil ya daga kai yana kallon Inna, a hankali yace “Toh bari muje ta debo kayanta Inna” Inna ta masa wani shegen kallo tace “A ina??” Yace “Gidan da muka ajiye kayan” Tace “Wani gidan ne?” Yace “Nan cikin gari” Tace “Toh wai da daga ina ku ke?” Yace “Kauyenmu” Ta buda baki tana kallonsa, can tace “Toh maza maza tafi ka debo mata kayanta, kauyen uban wa, kaga tayi kalar yar kauye banda dai baka tsoron Allah duk girmanka, kaiii Ibrahim ma dai sai Allah yayi masu hisabi da Nihad, don ya cuceta ya gurbata mata rayuwa, wallahi ya cuceta” Khalil ya mike yana kallon Nihad dake ta kallonsa, yace “Za muje ki debi kayan ne, don ban san wanda zaki bukata ba” Mikewa tayi, Inna tace “Ta debi me, Bawan Allah dukka zaka tafi ka kwaso mata ka kawo nan inyi jinyar jikata ko zata marmaro, shi kuma Ibrahim yaje hakkinta ma baxae bar sa ba duk da ni nace na yaɓa da hankalinka kawai a aura mata kai, bansan kai ma mugu bane, ashe kauyen da dadi ka gudo ka dawo birni ka nemi tukin mota, maza tafi ka kwaso mata kayanta” Nihad tace “Toh ai ni xan je in xaba kayan, ba dukka nake sa wa ba fa” Inna tace “Duk da haka kuje ki kwaso su gaba daya, baki ji yace wajen ajiya kayan suke ba, idan aka kwashe maki kaya ta ina za a fara….” Nihad tace “Toh” Khalil na kallon Inna yace “Sai anjima” da sauri tace “Toh” Juyawa yayi ya fita ta bi sa da harara, Nihad ta bi bayansa, Inna tace “Maza kiyi ki dawo” Har suka iso mota babu wanda yace komai cikinsu. Bayan sun bar layin ya juya ya kalleta yace “Kala nawa zaki debo kayan?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “Ko dukka za a debo?” Ta hade rai tace “Ni nace maka zan koma ne?” Yace “Ai ban sani ba” bata kuma ce masa komai ba bayan tafiyar kusan minti talatin ta gansu gaban wani hotel, ta kallesa, ya fiddo wayarsa dake ring ganin Mami ke kiransa ya jinginar da kansa jikin kujeran motar, can dai ya daga ya kai kunne a hankali yace “Ina yini?” Daga daya ɓangaren ba tare da ta amsa ba a takaice tace “Karfe nawa zaka taso goben?” Yace “Da safe” Tace “Ai dai ka ji inda nace kaje idan ka sauka ko?” Yace “Toh saboda me?” Mami tace “Ohh kace saboda me? To in baka da hankali ka shigar masa gida idan ka shigo Abuja, wai ma in tambayeka kana da wani kudurin na daban ne a ranka da yasa ka dage sai ka amshi takardunka dake wajensa bayan babu abinda ka rasa yanzu?” Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Ba komai, just in case of necessity” Mami tace “Toh kana sauka Abuja xaka bani in mayar masa kuwa” Khalil ya bude baki yace “Ki mayar masa kuma Mami?” Tace “Haka nace” Shiru yayi, yana jin ta kashe wayar ya ajiye, bayan few seconds ya kalli Nihad yace “Mu je ki dau wasu kayan naki da kika bari a Abuja na taho maki da su” Yana fadin haka ya bude motar ya sauka, ta bi sa da kallo sai kuma ta sauka, sai da ya kulle motar sannan ya nufi cikin hotel din ta bi bayansa, makullin dakin ya amsa tana biye da shi har zuwa dakin da ya sauka dazu da safe, a hankali take tafiyar har ta shiga cikin dakin ya kulle kofar, taga ya shiga bandaki ya dauro alwala ya fito, nan dakin ya shimfida darduma zai yi sallan don an idar a masallaci, Nihad dai ta dinga bin dakin da kallo don bata ga alamar jaka balle kaya ba, can dai ta nufi bandakin ita ma tayi alwala ta fito, ta dau wani darduman ta shimfida xata yi sallan…

Bayan ta idar da sallan ta kallesa don kwanciya yayi kan gadon ya rufe idonsa kamar me bacci nan ko ba bacci yake ba, kawai neman mafita yake na chakwakiyar nan da yake ciki, he don’t even know where to start from, it’s doesn’t look easy at all, definitely yasan ko harbesa Abba zai yi baxai mayar masa da takardunsa ba, to shi wannan ma ba damuwarsa bane, babban tashin hankalinsa daban yanzu, wanda da ya tuna sai gabansa ya fadi, throughout ranan kuma Nadeeyah bata kirasa ba, a hankali ya bude idonsa daga karshe yana kallon Nihad yaga ta kwantar da kanta saman gadon tana daga zaune kan darduma tana bacci, mikewa zaune yayi still yana kallonta, can ya sauka daga saman gadon, ya nufi switch din dakin ya kashe, sannan ya dawo gabanta yayi patting dinta, bude ido tayi da sauri amma taga ko ina duhu ta gyara zamanta da sauri tana gwalo ido, yayi kasa da murya yace “Tashi….” Gabanta na faduwa tace “Ni baxa ka kai ni gida bane?” Ji tayi ya dagata ta zaro ido kafin tace komai ya cire mata hijab din jikinta kamshinta sai da ya kusa Knocking dinsa down yaji ya kasa tsayuwa da kafafuwansa, gaba daya ta rikice zata duka ƙasa yaki barin ta, instead taji ya ja ta suka fada saman gadon, ta sauka kansa da sauri, cikin rawan murya tace “Don Allah kayi hakuri mu tafi gida kaga dare yayi” Kamar wanda ya sha wani abu yana lumshe ido yace “Saboda me?” Ta hadiye abu da kyar tace “Za a neme ni” Yace “Ke da wa ku ka fita?” Ta kasa cewa komai sai zaro ido take xuciyarta na bugawa, murya can kasa yace “I am asking you, ke da wa ku ka fita?” Still taki cewa komai tana neman sauka daga saman gadon, taji ya danneta, zaro ido tayi, kamar me rada yace “Answer me” jikinta na rawa tace “Mijina” Bata rufe baki ba ya daura lips dinsa kan nata giving her a deep snog…

54

It took Khalil a while kafin ya iya controlling urge dinsa a lokacin, it wasn’t easy for him, duk da dama babu abinda yayi niyyar mata, amma sai da ya kai zuciyarsa nesa kafin ya iya hakura ya kyaleta, ya koma can gefe ya kwanta breathing rapidly, jin yanda take kuka kamar warce aka ma duka ya mike zaune da kyar ya kunna switch din dake kusa da gadon yana kallonta, da sauri ta boye fuskarta da gadon tana ci gaba da kukanta, har sannan jikinta bai daina rawa ba, she is so afraid, he realized bakuwa ce gaba daya a lamarin, she is not use to it, ya koma kusa da ita ya dagota ya rungumeta ya lumshe ido yana jin yanda zuciyarta ke bugawa, ita dai taki yarda su hada ido jikinta sai rawa yake, ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace “Toh me aka maki?” Tayi shiru bata ce masa komai ba, suna nan a haka for almost 10mins har yaji she is completely calm, a hankali yace “Nihad” Da sauri ta daga kai ta kallesa saboda yanda ya kira sunan nata, yana kallon kwayar idonta yace “Me ke kai ki hotels a baya?” Sauke idonta tayi bata ce masa komai ba, lokaci daya hawaye ya cika idonta, still taki ce masa komai, shi ma bai sake ce mata komai ba, ya dauko rigarta ya mika mata sannan ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, kafin ya fito har ta shirya, ta jinginar da kanta jikin gadon tayi nisa tunanin da take, har ya karaso kusa da ita yana kallonta bata sani ba, wayarsa da ya fara ring ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta tafi, ya dau makullin mota yace “Tashi mu tafi” Mikewa tayi tana kallonsa, ya nufi kofa ta bi bayansa, har suka isa gida babu wanda yace komai a cikinsu, tunanin da yake a zuciyarsa daban, ita ma haka, yayi parking a compound sai a sannan ya juya ya kalleta yace “Kina da National ID card?” Ta ɗan kallesa, sai kuma ta gyada masa kai, yace “In kin shiga ki dauko min” Bata ce komai ba ta bude motar ta sauka, ya bi ta da kallo ta nufi entrance din gidan walking slowly, jinginar da kansa yayi da kujeran motar ya lumshe ido, he wish things won’t go as hard as he is seeing it now, he wish his parents will understand him, Nihad bata tadda kowa main parlor ba ta tafi bangaren Mumy, Mumy na kallonta bayan ta zauna tace “Ina Ibrahim din?” Tace “Yana waje” Mumy tace “Kun samu Innar?” Nihad tace “Ehh” Mumy tace “Bata dai yi fada ba ko?” Girgiza mata kai kawai Nihad tayi, Mumy tayi shiru, bayan wani lokaci ta kalli Nihad tace “Bayan kun fita zuwa gidan Inna daxu Umma ta shigo wai kina ganinta baki gaisheta ba shine hakan ya dameta shi yasa ma ta bar gidan, bana son ki nuna mata komai Daughter, pretend as if everything is okay, kar ki nuna mata komai har ku bar gidan nan kin ji?” Nihad dai sai kallon Mumy take, Mumy tace “Kwana nawa yace za ku yi?” Nihad ta sauke idonta a hankali tace “Nima ban sani ba” Mumy tace “Toh kiyi hakuri kar ki nuna mata komai, idan kun hadu ki gaisheta yanda kika saba” Nihad dai ta kasa cewa Mumy komai but deep down her tasan she will never greet her, don duk duniya babu wanda take jin tsanarsa a zuciyarta irin Umma. Khalil na zaune tare da Aminu wajajen karfe goma Amina ta iso wajen tana kallonsa tace “Abbanmu yana kiranka” ya ɗan kalleta wanting to make sure da shi take ko Aminu, Aminu yace “Tace Alhaji na kiranka mutumina” Khalil yace “Toh” Juyawa tayi ta bar wajen ya mike ya saka ID card din Nihad da Sudais ya kawo masa a aljihu sannan ya nufi cikin gidan, Umma na zaune parlor ta kafe ma TV ido duk da gaba daya hankalinta ba kan kallon yake ba, malamin nata da suke zuwa wajensa tare da Hajiya Turai sun ƙona man mota a banza sun je har kauyen da yake a kusa da Zaria amma wai bashi da lafiya an kawosa asibiti cikin kano, haka nan suka juyo a hanya kuma mota ta lalace masu, sai da ta kashe ya fi dubu saba’in wajen gyaran motar, suka ɓata awa kusan uku kafin aka gama gyaran ta kamo hanyar gida a wahale ga yunwa…. suna hada ido da khalil bayan ya shigo parlon ya dauke kai ya nufi kofar parlon Abba, ta bi sa da kallon mamaki don haduwarsu na farko kenan tun zuwansu gidan, Ya tsaya bakin kofar parlon yayi sallama, sai da yaji Abba ya amsa sannan ya shiga, Umma ta kalli Amina tace “Ko dai ya gaisheni ni ce ban ji ba Amina?” Amina tace “Ba wani gaisheki da yayi wallahi” Mikewa tayi ta nufi parlon Abban da sauri ita ma, Khalil na zaune kasa ya sunkuyar da kansa bayan ya kara gaida Abba, Abba yace “Wani garin ku ke?” Khalil zai yi magana Umma ta shigo, Ta nemi waje ta zauna parlon tana ɗan murmushi, Abba ya kalleta, can kuma yace “Is there any problem?” Da sauri tace “Aa babu komai, sannu Khalil, fatan kun zo lafiya?” Khalil ya kalleta yace “Alhamdulillah” Tace “To madallah” Abba ya ɗan yi shiru, sai kuma yace “Idan zaka kwanta ka tafi dakin Farooq, dakin nasa a bude yake…” Khalil da kansa ke kasa yace “Toh Nagode” Abba yace “Shikenan you can leave” Mikewa yayi ya fita daga parlon, Umma dai sai murmushin yake take tace “Allah sarki, sun dawo nan garin kenan?” Abba ya dau wayarsa dake ring ya daga ya kai kunne. Nihad na kwance saman gadon Mumy bayan tayi shirin bacci Mumy ta shigo dakin tace “Baxa kije ki ji ko yana bukatar wani abun ba Nihad?” Nihad ta daga kai tana kallon Mumy, Mumy tace “Duk da nasan akwai komai dakin farooq but ki je kiji if he is comfortable” Nihad ta mike zaune, Mumy ta juya ta fita daga dakin, Nihad ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta fita, bata gansa a dakin ba hakan yasa ta dawo tayi kwanciyarta kawai. Washegari bayan khalil ya shigo gaida Mumy ya sanar mata za su koma a ranan, Nihad dake zaune dai sa kallonsa take tana tunanin inda za su koma, Mumy tace “Toh ka samu Alhajin ka sanar masa?” Khalil yace “Na ɗan fita dazu, kafin in dawo kuma ya fita” Mumy tace “Toh ka kirasa a waya sai ka gaya masa” Khalil yace “Toh in sha Allah” mikewa yayi ya fita daga parlon, Mumy na kallon Nihad tace “Toh ki tashi ki fara shiri” lokaci daya jikin Nihad yayi sanyi, amma saboda bata son Mumy ta fahimci komai ta mike ta shiga bedroom dinta kawai kamar zata shirya, zaunawa tayi kan gado ta hade kanta da pillow hawaye na sauka idonta, Umma tayi sallama ta shigo parlon Mumy, Ta zauna saman kujera bayan sun gaisa da Mumy tace “Ina er tawa?” Mumy ta mike tace “Yanzu ta shiga ciki bari in duba” Daga haka ta shiga daki Umma ta bi ta da kallo, Nihad na jin muryar Umma dama ta shige bandakin Mumy ta sa makulli, Mumy ta ɗan yi jim a dakin, can ta juyo ta fito tana kirkiran murmushi tace “Kamar wanka take, tana bandaki….” Umma tace “Toh, ni sai naga kamar ta kullaceni, tana ganin na watsar da al’amarinta bata san Alhaji babu me iya masa ba sai Allah, kuma Allah shine shaida, nayi bakin kokarina kema shaida ce amma hakan ya so ya zame mana ɓacin rai da Alhaji, har yake ga kamar ina goyon bayanta ne, Nihad gani take kamar nayi shiru naki cewa komai akan abinda ya sameta nan kuma ba haka bane Allah ya ga zuciyata, babu yanda na iya ne abun ya fi karfi na” Tana magana tana matsar kwalla, Mumy dake ta kallonta babu ko kiftawa ta kasa ce mata komai, Umma tace “Toh idan ba kullatata tayi ba menene? Ni Nihad bata taɓa min haka ba wallahi, a jiyan nan da da tashigo da wajena zata fara shiga kafin ma ta zo nan, amma bata yi hakan ba, to kinga ai ta kullaceni kenan, duk sai jikina yayi sanyi na fita na bar gidan” Mumy ta sauke idonta kasa don bata da abinda xata ce ma Umma, banda zafi babu abinda zuciyarta yake, da Umma bata gurbata ma ‘er ta rayuwa haka ba, da zagewa tayi kawai su zuba kishi amma da bata ma er ta abinda tayi mata ba, daure kawai Mumy take a zaune a wajen, Umma ta sauke ajiyar zuciya jin Mumy ta ki cewa komai, tace “To amma zasu kwan biyu ai ko?” Mumy tayi karfin halin girgiza kai tace “Anjima za su koma” Umma ta buda ido sosai tace “Yau din nan? Ikon Allah, ni na zata sun zo su kwana biyu ne? Toh a wani kauyen suke ne halan?” Mumy tace “Ban sani ba gaskiya” Umma tace “Allah sarki, Allah me yanda ya so….”

 Nihad na shirya sauran kayanta dake gidan a cikin Trolly Mumy ta shigo dakin tana mata wani kallo tace “Ke kika kirata kika ce kin zo??” Nihad ta daga kai tana kallon Mumy tace “Wacece?” Mumy tace “Ban sani ba” Nihad tace “Mumy ni ban kira kowa ba ni da bani da waya, kuma ai kinga ban yi amfani da wayarki ba” Mumy tace “To wa yace mata kina nan?” Nihad tace “Ai ban san wacece ba” Mumy tace “Sai kije ki duba” Nihad ta mike tsaye ta nufi kofa ta bude ta fita parlon Mumy taga babu kowa, can main parlor ta fita, tsaye tayi parlon tana kallon Husnah dake zaune ta sha baƙin glass, Husnah ta mike da sauri ta rungumeta cike da murna tana kare mata kallo tace “Besty, meye rayuwa? yanzu da sai dai mu ji kin zo kin tafi babu daga hannu? Haba Nihad, amana bata ce haka ba ai, nafi karfin haka a wajenki” Nihad ta karasa ta zauna parlon tace “Wa yace maki na zo?” Husnah tace “Wallahi na zo wucewa ta anguwar nan ne nace bari dai in shigo mu gaisa da su Umma da Mumy, kawai sai na samu labarin wai kina nan, nace what?? abun ya daure min kai nace kina nan shine babu notice, yanzu ko ta waya kin daina neman mu Nihad, Duk kusancinmu ace kin ya da mu haka?” Nihad dai sai kallonta take, Husnah na gyara zama tace “Toh yanzu ya ake ciki? Naga kin yi haske amma kin rame, ina mijin naki?” Nihad tace “Lafiya lau” Husnah tace “To wai wani garin ku ke?” Nihad na kallonta tace “Ban san sunan wajen ba” Husnah tayi kasa da murya tace “Kar kice min kin hakura kin zauna da shi Nihad har abu ya shiga tsakaninku Nihad” Nihad tace “Do you have any problem with that?” Shiru Husnah tayi tana kallonta, Can tayi yake tace “Aa kawai tambaya nake kawalli, kinsan har yanzu Aliyu Jikamshi bai daina damun Naf a waya ba shi yasa ma nake maki wannan tambayar, wallahi Aliyu bai hakura ba har yanxu” Nihad dai bata ce mata komai ba, Husnah tace “To wai har yanzu baki da waya?” Nihad tace “Bani da shi har yanzu” Husnah tayi kasa da murya ta bude jakarta tana kokarin ciro waya tace “Toh ko in baki karamar wayata ki saka layi kawai, sai mu dinga magana….” Nihad tace “Aa yanzu bana bukatar waya” Shiru Husnah tayi tana kallonta da mamaki, Nihad tace “Toh naji dadi nagode da ziyara Husnah, ina son zan je in ci gaba da abinda nake yi a ciki” Husnah ta buda baki tana kallonta ta kasa cewa komai, Nihad ta mike tace “Toh sai anjima, nagode” Kai kawai Husnah ta iya gyada mata, Nihad ta juya ta bar ta a parlon ta koma parlon Mumy, Husnah ta mike da sauri ta shige bangaren Umma…

 Bayan Azahar Khalil na zaune balcony tare da Nihal, Hira suke amma gaba daya hankalinta baya jikinta, she is carried away with her thought, sannan tun dazu ake kiran wayarta amma bata dagawa daga karshe yana lura da ita ta sa wayar a silent, yace “Nihal” Firgit ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta kirkiri murmushi tace “Na’am” Yace “Pls tell me what ur problem is, Or don’t u trust me?” Nihal dai sai kallonsa take, can ta ɗan kirkiri murmushi tace “Sure i do… but i told u nothing, I don’t have any problem….” Khalil dai kallonta kawai yake, Da sauri tace “Yaushe xa ku koma?” Yace “Today” Ta wara ido tace “Yau din nan? Amma ai rana yayi” Ya girgiza kai yace “Bai yi ba” Tace “Ohk, nima next week zan koma makaranta in sha Allah” Yace “Allah ya kai mu, but if there is anything feel free to call and talk to me Nihal” a hankali tace “In sha Allah” Yace “Bani account number din ki” Ta ɗan buda ido tace “Ahh haba wallahi Nagode, ka bar shi” yace “I asked for it” shiru tayi bata ce komai ba, ya ciro wayarsa yace “Gaya min” Ta kallesa tace “Amma…” Ya dakatar da ita yace “Ki bani nace” Ta sunkuyar da kai ta karanto masa account din, cikin few seconds taji alert a wayarta ta duba taga dubu hamsin ya sa mata, ta daga kai tana kallonsa, ya mike yace “Ki duba min ko ta gama shiryawa, lokaci na wucewa” Tace “Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi” Shi dai bai ce mata komai ba, ta tashi ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba sai ga ta ta fito da trolly din Nihad, wanda duk hijabs dinta da wasu kayanta ne a ciki da turarrukanta, daurewa kawai Nihad take kar ta fashe da kukan da ke cin ta, Mumy ta gama mata nasihar da zata mata sannan tace “Ki je kar ki bata masa lokaci, Allah ya tsare, in kin samu waya ki dinga kirana kin ji?” Nihad ta gyada mata kai kawai tana goge hawayen idonta ta nufi kofa, Mumy ta bi ta da kallo ita ma hawayen har ya cika idonta, Aminu ya taho ya saka jakar Nihad a bayan motar yana kallon sabon drivern gidan cike da tsangwama yace “Kwata kwata baka san aikinka ba Iliya, kana ganin an fito da jakar ai da gudu zaka dauka ka saka a booth, haka ake yi ba wai ka tsaya kamar soja ba” Dreban yace “Wai kai ina ruwanka da ni a gidan nan ne bawan Allah” Aminu yace “Oho dai ka ji da warin bakinka” Daga haka ya koma gate, shi dai khalil na jingine jikin motar yana kallonsu, sai kuma kawai ya shiga ciki don yi ma Mumy sallama, Mumy tace “Toh Allah ya tsare Ibrahim, ayi ta hakuri da ita don Allah, idan tayi maka ba dai dai ba kar kayi kasa a gwiwa ka kirani kaji” Kansa na kasa yace “Nagode Allah ya kara girma” Tace “Ameen, Allah ya maku albarka” Ya amsa da “Ameen”  sannan ya bar parlon ya fita zuwa compound, ba a dau lokaci ba Nihad ta fito tare da Nihal, Nihal ta bude mata back seat tana kallonta tace “Allah ya tsare sister….” murmushi Nihad ta mata tace “Ameen” Daga haka ta kulle motar tana kallon Khalil tace “Safe trip” Khalil yace “Thank you Nihal” ya bude front seat ya shiga ya kulle, drivern ya ja motar suka bar parking space, Tun bayan barin Husnah gidan Umma ma ta fita shine har yanzu bata dawo ba, Aminu na tsaye gate tun kafin motar ya karaso yake daga ma Khalil hannu baki har kunne, suna isa gate khalil ya sauke glass din motar ya mika masa cash din dubu dari, Aminu yayi washarere da baki yana kallon tulin kudin da khalil ke mika masa ya kasa amsa, Shi kansa dreban sai gwale ido yake yana kallon kudin don dari biyar biyar ne sababbi, ita dai Nihad na bayan motar tana kallonsu, Khalil ya kamo hannunsa ya damka masa kudin sannan ya kulle glass din yana kallon drivern yace “Mu je” Drivern ya ja motar suka bar Aminu tsaye galala da kudi a hannu, Bayan sun hau saman titi drivern na kallon Khalil cike da ladabi yace “Ina muka nufa ranka shi dade?” Khalil yace “Airport” Nihad ta daga kai ta kallesa, drivern yace “Toh Yallabai yanzu kuwa” Daga haka ya nufi airport da su, suna isa Aminu kano bayan yayi parking Khalil ya sauka daga motar, da sauri Drivern ya zaga ya sauke kayan Nihad dake bayan motar, ta bude motar ta sauka ta tafi ta amshi trolly dinta a hannun drivern, Khalil ya ciro dubu biyar ya basa yace “Mun gode” Drivern har da risinawa ya dinga masa godiya, Khalil ya amshi trolly din hannunta ya nufi cikin airport din ta bi bayansa tana tafiya a hankali…. Suna shiga cikin airport din bayan ya amsar masu Boarding pass sai ga kiran Mami, sai da gabansa ya fadi, yau ta kirasa yafi a kirga, ya dai daga kiran yana sauraronta don bata basa space din magana ma, can yace “Calm down Mami, ina airport yanzu haka” Yana fada mata haka ta katse wayarta, sai da suka jira for almost 30mins kafin jirgin ya tashi zuwa Abuja.. kamar jira Nihad take jirgin ya tashi ta fara bacci, ya jawota kusa da shi a hankali ya kwantar da kanta saman shoulder dinsa, shi dai yasan banda Mami babu abinda zai kai sa Abuja, but he just have to go because of her, jirgi na sauka a Abuja bayan sun fito daga cikin jirgin hankalin Nihad ya tashi, yanzu gidansu zai sake mayar da ita kenan, tunanin hakan yasa taji kamar ta fashe da kuka, suka dau cab a airport din bayan khalil ya sanar masa inda zai kai su, tafiyar kusan minti arba’in suka yi, Nihad taga wani anguwan daban suka shigo, ta dinga bin ko ina da kallo har mai cab din yayi parking dai dai wani gida wanda ya haduwa iya haduwa, duk manyan gidaje ne a layin kamar wannan, Khalil ya sauka daga cab din don tun a hanya yayi masa transfer, mai cab din ya bude booth ya ciro trolly din Nihad, Khalil ya amsa yana kallonsa yace “Ka jirani zaka ajiye ni wani waje yanzu” Mai cab din yace “Ok sir” Daga haka ya nufi gate din gidan ya ciro makulli a aljihunsa ya bude sannan ya juya yana kallon Nihad dake tsaye, karasowa tayi a hankali kusa da shi ta tsaya, ganin jira yake ta shiga gidan kawai ta shiga shi ma ya shiga sannan ya kulle gate din, ta dinga bin compound din da kallo, it looks so beautiful, duk gidajen da taje a Abuja daga gidansu sai wannan a kyau, don ko na Aunty Maryam bai kai wannan kyau ba balle nasu Nadeeyah, kuma sabon gida ne kamar ba kowa ciki, yana gaba tana biye da shi har suka iso entrance din shiga cikin gidan, ya bude kofar da makulli ya shiga ta bi bayansa, waow the parlor is breathe taking, komai na ciki sabo ne dal, ya ajiye jakarta yace “Ki tafi sama kiyi sallah, i will be going out now” ta marairaice tace “Ni kadai a katon gidan nan?” Yace “Ke yarinya ce?” Ta dinga kallonsa gabanta na faduwa amma ta kasa ce masa komai, daukar jakar yayi ya wuce sama ta bi bayansa da sauri, ya bude wani daki ya ajiye jakar a ciki ya juya yana kallonta, ta shigo dakin tana bin ko ina da kallo yace “Ki shiga bandaki kiyi alwala” Daga haka ya juya ya fita sannan ya sauka downstairs, ya fita daga gidan ya kulle gate din da makulli ya shiga cab din dake jiransa don baya son Mami ta sake kiransa.

55

Khalil na isa gidan Hajiya Safeenah, ya ga motar Mami a compound din alamar tana ciki, ya karasa har kofar shiga parlon gidan yayi Knocking, ba a dau lokaci ba aka bude kofar suka yi ido hudu da Nadeeyah, juyawa tayi zata bar wajen ya bi parlon da ido ganin babu kowa ciki ya jawota da sauri yace “C’mon Babe, did i offend you in anyway?” Nadeeyah dai bata ce masa komai ba, ya karaso cikin parlon ya kulle kofar still yana rike da ita yayi kasa da murya yace “Haba Nadeey, nayi maki wani laifin ne? In ma nayi kiyi hakuri don’t punish me plss” Taki kallonsa, a takaice tace “Pls aiki muke yi a kitchen, let go of me” Ya sake bin parlon da kallo sannan ya rungumeta a hankali yace “I am sorry dear, I’m deeply sorry….” Kamar jira take ta fashe masa da kuka tace “Saboda ga budurwarka ta gudu shi yasa zaka daga hankalinka haka har ka dinga shareni ko?” Da sauri yace “Noo Nadeey, budurwata kuma? Haba… Kawai ya zama dole in daga hankalina saboda parents dinta trusted me har suka bari na taho da ita Abuja ta zauna a gidanmu, Kinga idan wani abu ya sameta i don’t know how to explain to her parents, bansan da wani idon zan kallesu ba, wannan shine dalilin da yasa kika ga hankalina ya tashi Nadeeyah, but Alhmdlh she is home now, ba shikenan ba” Hawaye na bin kuncinta tace “Ko farin cikin sa mana rana da aka yi baka yi ba, u are not even saying anything about the wedding, balle mu yi wani shirye shirye, You’ve been ignoring me for at least 2 weeks now….” Ya wara ido yace “Ko ba wata daya aka sa ba? ina fa lissafi Nadeey, i know yau saura 15 days in sha Allah, and kinsan ni bana son duk occasions din nan da ake yi ko events a biki, i told u that years back, so ba wani abu da xa ayi, just wedding fatiha sai walima a gida, but if su Mami za su yi wani program fine za su iya, kema in za kiyi da frnds dinki it’s okay the expenses will be on me, but count me out of any event…..” Nadeeyah dai bata ce komai ba, ya share mata hawayen idonta a hankali yace “You know i love you always dear, kuma baxan so ranki ya baci saboda ni ba…. Don Allah kiyi hakuri kin ji wife” Jin bude kofar kitchen yasa ya saketa da sauri ya koma baya, ya wara ido yace “Ina su Mami?” Bata kai ga basa amsa ba ya jiyo muryarsu, Ya kashe mata ido yace “Bari in karasa ciki Baby” Daga haka ya nufi kofar parlon Hajiya Safeenah, Nadeeyah ta bi sa da kallo, yana shiga parlon da sallama Mami ta dinga kallonsa, ya zauna ya gaida Hajiya Safeenah da ladabi ta amsa da fara’a tana tambayarsa ya hanya, yace “Alhamdulillah” Ya ɗan kalli Mami da ke kallonsa har sannan yace “Ina yini Mami” Mikewa Hajiya Safeenah tayi ta fita daga parlon ta basu waje, Mami na masa wani kallo tace “Ban ga komai a hannunka ba bawan Allah” a hankali yace “Kamar me fa Mami?” Ta jefa masa wani kallo tace “Kar ka raina min hankali mana, ina takardun da makullan da ka kwashe?” Khalil yayi shiru bai ce mata komai ba, Mami tace “Na lura baka son kwanciyar hankali na Khalil, duk wani abu da zai daga min hankali baka gudunsa a rayuwarka, banda haka what are you lacking in this life? Rasa motar hawa kayi ko rasa gidan zama kayi? Nawa ne salary din naka dukka? Sannan nawa kake samu currently a wata? Ka gaya min ko banbancin da wani tazara, ko kuma rashin godiyar Allah ne ke damunka?” Kallonta kawai Khalil yake ya kasa ce mata komai, A fusace Mami tace “Instead of you to sit and plan ur wedding cikin tsari sai ka ɓuge da dauko mana magana, Is this the rightful time da zaka amshi abubuwanka khalil in ba dai kana da wani kuduri na daban a zuciya wanda mu bamu sani ba, are u even okay? A kan bikinka that’s by the corner zaka yi concentrating yanxu ko takardunka?” Yayi kasa da murya yace “Kiyi hakuri Mami, ni ban yi hakan don ranki ya ɓaci ba, i am very sorry Mami….” Mami tace “Aa kayi ne don raina ya ɓaci don sarai kasan kaina komai zai dawo, you are lacking nothing, akan me zaka damu da takardu ko makullin gida? Yanzu maganar da ka jawo min dai dai ne?” Shi dai yayi shiru bai ce komai ba, tace “Toh duk inda ka kai su ma kaje ka kawo min su ina jira, duk da ba shiri ku ke da shi ba but he is planning on sending 6million da za a hada maka lefe shine kaje ka aikata wannan shirmen, sannan da ka kwantar da hankalinka nasan dole xai baka makullin gidanka idan anyi auren tunda nan din dai amarya zata tare…. Amma ban san meye manufarka nayi abinda kayi ba” Khalil ya daga kai ya kalleta, Mami ta girgiza kai tace “I am very disappointed Khalil” A hankali yace “Kiyi hakuri Mami, i am so sorry” Mami tayi shiru, can tace “Sannan ita Maryam akan wani dalili take kiranka for many days now baka daga kiranta?” Ya ɗan buda ido yace “No ban ga kiranta ba, or may be ban lura ba, but zan kirata” Mami tace “Ita kuma yarinyar can wato gidansu ta koma ko” Khalil ya sauke idonsa yace “Ehh” Mami tace “Ikon Allah, toh Allah ya kyauta, dama can ba wai ta saki jiki bane a wajen nawa, gwara ta koma gaban iyayen nata su kara sa mata ido don har ga Allah hankalina bai kwanta ta zauna wajen mu ba, kada taje ta ci gaba da abubuwan da take a makaranta mu muna nan gida bamu sani ba, so i am happy da ta koma gida” Shi dai Khalil bai ce mata komai ba, Mami tace “Don yarinyar na bukatar sa ido sosai, a shekarunta in zata iya aikata abinda ta aikata a social media to komai ma zata iya yi, dubi dai yanda babu tsoro ta bi dare ta kama hanyar kano, abun nan yayi mugun daure min kai wallahi” Still Khalil dai bai ce komai ba, Mami tace “Toh ya ku ka yi da iyayen nata da kaje can din?” Ya girgiza kai yace “Ba komai, the most important part is that gida ta koma ko da dai bamu iya mun rike masu ita ba” Mami tace “Aa baka masu bayanin yanda mu ka nemeta muka rasa bane? Ae ba wanda ya ki riketa, kin zama tayi instead” Yace “It’s not necessary Mami, kinga sanda take gidan Aunty Maryam ai bata taɓa attempting barin gidan ba, she was sad and cried all throughout bayan tafiyar Aunty Maryam” Mami dake ta kallonsa tace “Toh me kake nufi yanxu?” Yace “Aa ba komai” Nadeeyah ta shigo parlon da sallama ta ajiye masa tray me dauke da ruwa da lemo a kai, tana kallon Mami tace “Sannu Mami” Mami tace “Sannu Nadeeyah, kun gama girkin” ta girgiza kai tace “Aa da saura” Daga haka ta mike ta nufi kofa, khalil ya dau ruwan gora ya bude ya sha, Mami tace “Tashi zaka yi ka tafi ka dauko min takardun yanxun nan” Yace “Toh, amma ki bari sai gobe Mami, it’s almost magrib yanzu” Mami tace “Why not today?” Yace “Baya nan kusa sai naje na dauko” Mami tace “Toh Allah ya kai mu, da baka aikata wannan abun ba ko ni zan same Abban naku ince ya bada makullin gida za aje kai kaya ina da tabbacin baxai hana ba wllh, amma ka zo ka ɓata sha’anin” Khalil dai yayi shiru yana kallonta, don yanzu gaba daya hankalinsa yayi can gida bai son gari ya fara duhu bai koma ba, Mami tace “Ka ɗan samo min fruits masu kyau idan na koma gida xa a min fruit salad” Yace “Babu a gida ne?” Tace “No, i need fresh fruits” Yace “Ohk” Daga haka ya mike yace “But ba fa mota a gurina Mami” Tace “Ka amshi makulli wajen driver na yana waje, i will call him ya baka” Mikewa Khalil yayi ya nufi kofa ya fita, Nadeeyah na zaune parlor ya karasa kusa da ita yace “Zan je grocery in dawo yanzu Babe” Ta daga kai ta kallesa tace “Can we go together?” Yace “Sure” Ta mike tace “Bari in gaya ma Mumy” Daga haka ta tafi dakin Mumy, shi kuma ya fita ya samu sojan dake tsaye compound kusa da Motar Mami, yana isa ya mika masa hannu babu yabo babu fallasa yace “Bani makulli” Sojan ya mika masa don Mami ta riga ta kirasa kafin Khalil ya fito banda haka da baxai basa ba, in akwai wanda Khalil ya tsana a rayuwarsa bai wuce soja ba, ji yake kamar ya makuresu, he detest the sight of them, ga shi sun fi goma a gidansu, fuska daure ya bude motar ya shiga, yana ta zaune driver seat har Nadeeyah ta fito looking so cute, kallo daya yayi mata ya dauke kai, ta karaso ta bude gaban motar ta shiga sannan mai gadi ya bude masu gate suka bar gidan, Khalil na Driving din yace “So where did u suggest i should rent an apartment for us??” Tace “Amma wannan gudun na meye kake yi haka?” Yace “Abokina na jirana before magrib kinga ai it’s almost magrib now shi yasa nake sauri” tace “Toh amma ka rage speed din pls….” Yace “Ohk” Tace “Duk inda kaga ya dace nan za mu zauna ai ko?” Yayi Murmushi ya gyada mata kai kawai, bayan ya siya ma Mami fruits Nadeeyah tace “Pls ina son zan ɗan yi shopping amma ba me yawa ba” Yace “Ki bari gobe Nadeeyah kinga sauri nake yanzu” Ta ɗan yi shiru sai kuma tace “Toh Allah ya kai mu” Bai fasa gudun da tace ya daina ba har suka iso gida, bayan yayi parking ta bude motar ta sauka, ya ɗan zaro ido, don shaff ya mance bai mata tayin ice cream ko pizza ba tunda tana so sosai, kuma basu taɓa fita tare suka dawo bai siya mata komai ba sae yau, Yayi kasa da murya yace “Nadeeyah” Juyawa tayi ta kallesa, a hankali yace “I am sorry na mance i didnt get you anything, but let me order….” da sauri tace “Noo it’s fine, ai sauri kake shi yasa, gobe idan mun fita sai mu siya in sha Allah” Yayi mata murmushi yace “Thank you” a mota ya bar fruits din Mami ya sauka ya ba drivern makullin sannan ya bi bayanta suka shiga gidan, Yana tsaye parlon Mum din Nadeeyah ya sanar ma Mami fruits din suna mota, Mami tace “Baxa ka tsaya ka ci abinci ba? Saurin meye haka kake yi” Da sauri yace “Aa Mami, ni a koshe nake” Tace “Toh wai saurin me kake haka?” Ya ɗan buda ido yace “Aa ni ba sauri nake ba kawai bana son a kira magrib ina nan ne” Mami tace “Toh gidan naka ka bude ka shiga??” Sai da yaji gabansa ya fadi, lokaci daya ya girgiza mata kai da sauri yace “Not at all, ina gidan abokina ne fa” Mami tace “Gobe karfe nawa zaka kawo takardun?” Yace “Da safe” Tace “Toh Allah ya kai mu” Daga haka yayi mata sallama tace “Ka jira mu fita tare mana sai mu ajiyeka inda zaka, nima yanzu zan tafi gida” Yayi karfin halin cewa “Noo i am fine Mami, Bolt na jira na a waje tun dazu” a hankali Mami tace “Toh Allah ya tsare” Yace “Ameen” Daga haka ya fita daga parlon ta bi sa da kallo, Ko sallama bai yi ma Nadeeyah ba balle Mum dinta ya bar gidan. Ana idar da magrib Khalil ya isa gidansa don sai da ya tsaya eatry ya siyo abinci with drinks da bottle water, 3 houses away from his house yaga sojoji hudu a tsaye kofar gidan, nan ya fara imagining gidan waye wannan kuma har da sojoji masu gadinsa, ya tsani yaga an cika ma gida sojoji a bakin gate, ya ciro Makullin gidansa a aljihu ya bude ya shiga ciki, yana bude kofar main parlon Nihad ta mike tsaye da sauri, ya kulle kofar ya karasa ciki yana kallonta don kana ganinta zaka san ta ci kuka ba kadan ba, taki yarda su hada ido ta koma ta zauna saman Carpet ta dauke kai ta wani hade rai, ajiye ledan hannunsa yayi ya wuce sama ta bi sa da harara, har bayan minti goma bata ga ya sauko ba, ta jawo ledan da ya ajiye a hankali tana duba ciki, taga jollof rice ne da fried rice a takeaway daban daban sae kaza, jollof rice din ta dauka ta fara ci, har kuma ta gama cin abincin bai sauko ba, ta mayar da empty takeaway din sannan ta matsar da ledan daga kusa da ita, sae gashi ya sauko sanye da jallabiya bata taɓa ganinsa da jallabiya ba sai yau, ya karaso cikin parlon ya bude ledan ganin empty takeaway ya daga kai ya kalleta for like 20 seconds, sai kuma yace “Ke fa hana mutane abincin kike a gidanku, nan ba a hanaki ba an siyo baki jira a baki ba kin dauka, who does that?” Sai a sannan ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma tace “Toh me mutum yayi kafin aka hanasa abincin a gidan namu?” As if that was what he was waiting for ya zauna yace “Ba abinda yayi kawai baƙin hali yasa aka hanasa” Ta masa wani kallo tace “Aa ya dai tuna abinda yayi” Kallonta ya dinga yi, ta turo baki ta mike ta dau goran ruwan da ta rage, ta koma can jikin wani kujera ta zauna, sai kuma yayi murmushi, ya bude fried rice din da ta bar masa ya fara ci, lokaci lokaci yake daga kai sai su hada ido don kallonsa take, da sauri kuma take dauke idonta, sun yi hakan kusan sau uku, a na hudun ne ta mike da sauri, yace “Ina za ki?” Bata bari sun hada ido ba ya ga ta wuce sama ya bi ta da kallo, nan parlon yayi isha ya kai sauran abincin kitchen ya ajiye, babu abinda babu a katon kitchen din kamar da mace a gidan, komai kuma sabo ne, ko gas din gidan ba a taɓa kunnawa ba, ya kashe wutan kitchen din ya fito, ya haura sama, master Bedroom ya shiga ya yi wanka sannan ya saka pajamas dinsa yana zaune gefen gado ya dau wayarsa ganin kiran Nadeeyah ya kirata, tana dagawa yace “Hello dear” Tace “Shine ka tafi ba ko sallama Dr?” Yace “Ai nace maki sauri nake ana jirana” a hankali tace “Ohk, ya hanya?” Yace “Alhamdulillah, Mami ta tafi gida ai ko?” Tace “Yea tun daxu” Yace “Ohk, ya ake ciki?” Tace “Dama ina son zan maka maganar kayan da za muyi fitar biki ne….” Yace “Ohk, kawai kiyi shawara da frnds dinki sai ki gaya min” Tace “Alright?” Yace “Shikenan maganar?” Da mamaki tace “Are u eager to cut the call?” Da sauri yace “Noo, kawai dai i am tired ina son zan kwanta ne da wuri” tayi shiru, yace “Hello?” A hankali tace “Ohk, good night” Yace “Hope u ain’t taking it personal?” Har hawaye ya cika idonta tace “Yaushe rabon da mu yi magana a waya, kai idan ban kiraka ba baka kirana, kuma na kiraka yanzu kana ce min bacci zaka yi, shikenan kayi baccinka kawai ba damuwa” Ya sauke wani ajiyar zuciya yace “I am sorry Nadeeyah, to yanzu meye labari?” Tace “Noo, kawai kayi kwanciyarka sai da safe” Yace “I will sacrifice that because of you my love” Taki ce masa komai, sarai yasan kuka take…. A hankali yace “Nadeeyah” taki amsawa, yayi kasa da murya yace “Ke komai kuka, duk randa na maki kishiya shikenan haka zaki dinga mata kuka ita ma har ta raina min ke?” Diff yaji ta katse wayar, ya wara ido, nan ya dinga kiranta taki dagawa, ya kirata ya kusa sau hudu bata daga ba, ya ajiye wayar sai ga kiran Aunty Maryam, sai da gabansa ya fadi, for almost 3 days now yake ignoring kiranta don yasan dalilin kiran nata, yana ta kallon wayar har ya kusa katsewa can dai ya daga a hankali ya kai kunne, yayi gathering courage yace “Hello Aunty” Daga daya bangaren tace “Shaye shaye ka fara yi ne kana ganin kirana baka dagawa Khalil? Kiran na wa kake ignoring??” Da sauri yace “No ba haka bane Aunty, kawai i am not my self this days ne shi yasa, amma kiyi hakuri don Allah” Aunty Maryam tace “Yanzu dai ina Nihad? Mami tace min ta koma gidansu, garin yaya hakan ta faru Kjay? And did the parent accept her??” Yace “Gidansu Nadeeyah Mami tace ta koma saboda su Aunty Hassana, ita kuma a ranan ta bar garin which means bata son zaman gidan….” Aunty Maryam ta bude baki cike da mamaki tace “Ikon Allah, kaga kuma Mami bata gaya min haka ba wallahi, ce min kawai tayi an nemeta an rasa, daga baya aka gano ashe gidansu ta koma” Khalil dai yayi shiru, Aunty Maryam tace “Amma Mami bata kyauta ba, yanzu saboda su Aunty Hassana ta ki rike baiwar Allahn nan? Me yasa Mami tayi haka kai me baya? Gaskiya ban ji dadin jin haka ba, ka tabbatar kuma gidan nasu ta koma Khalil? Kar fa wani wajen daban ta tafi” Khalil yace “Can ta koma Aunty, naje har gidan nasu, i came back today” Aunty Maryam tace “Allah sarki, to me ya samu wayar da na bata ba a samunta, Ayman ma har ya gaji da kiranta” Khalil yace “I think charging point din ne ya lalace” Aunty Maryam tace “Toh ai kana da number Mamarta ka turo min yanzu” Khalil yace “Oh ohk, amma ba a wannan wayar nake da number ba, idan na kunna wancan wayar zan tura maki” Aunty Maryam tace “Toh yau nake son ka turo min Malam, don’t keep me waiting” A hankali yace “Ohk” tace “And lastly Mami tace min ka kwashe takardunka da Cv a dakin Abbanku, ta kuma ce zata amsa ta mayar masa, to shawaran da zan baka kada ka kuskura ka bata ko me zai faru kuwa, ban san me ke damun Mami ba kwata kwata wallahi, don’t make that mistake of giving her na gaya maka, idan ma ya kama ka bar masu garin ne ka bari gaba daya, ta yaya ita bata kwatar maka hakkin ka ba ka kwata da kanka kuma take neman amsa ta mayar masa, wannan wace irin rayuwa ce?” A hankali Khalil yace “Ban san yanda zan yi ba Aunty, and she is taking the issue so personal” Aunty Maryam tace “Kaga idan ya kama kawai ka taho inda nake kayi zamanka cikin kwanciyar hankali, with ur qualifications zaka samu aiki me kyau a nan, kada ka wani tsaya biyewa Mami….” Khalil yayi murmushi yace “Nagode Aunty” Tace “Toh ni dai na gaya maka, kuma ina jiran number Maman Nihad” Khalil yace “Toh Aunty” Daga haka ta katse wayar, ya sauka ajiyar zuciya ya ajiye wayar yana nazari, bayan few minutes ya mike ya fita daga dakin, dakin da Nihad ke ciki ya nufa ya bude a hankali, zaune ya ganta gefen gado ta daura sabon towel da ta gani cikin press din dakin tana shafa turarurrukan ta alamar wanka tayi, tana ganinsa ta jawo hijab dinta ta rufe duk jikinta, ya tsaya jikin mirror ya rungume hannunsa yana kallonta ga kamshinta da ya cika masa hanci, bayan few seconds ta daga kai ta kallesa tace “I need space” Ya ki ce mata komai kuma yaki barin dakin, ganin hakan ta mike ta dau doguwar rigar baccinta zata shiga banɗaki yayi saurin riketa, zaro ido tayi tace “Ni wallahi ka sakeni in je in sa kayana, meye haka mana” Ya janye hijab din ya jefar saman gado dama tana ganin haka ta rike towel dinta gam tana zazzare ido, hankalinta a tashe kamar zata yi kuka tace “Meye haka kake yi don Allah? It’s not proper plss” Ya kai bakinsa kunnenta ya rada mata magana a hankali, sannan ya kalli fuskarta to see her reaction, ta marairaice zuciyarta na bugawa amma ta kasa hada ido da shi, maganar nasa yayi mata nauyi sosai, mamakin yanda baya jin kunya ko kadan take, murya can kasa taji yace “Agreed?” Still taki kallonsa balle ya sa ran amsa, zai dago kanta taki barin yayi hakan gaba daya a tsorace take, ya kai hannu towel din ta rike hannunsa da sauri muryarta na rawa tace “Why are you doing this plss? Ni fa ba er iska bace” Ya kai bakinsa kunnenta a hankali yace “Toh ni ne ɗan iska?” Ta kasa ce masa komai banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, amma kuma a ranta taji gwara ta amince da abinda yace mata tunda iya hakan ne kawai, bata hanasa ci gaba da kwance towel din ba amma kafin ya cire ta rufe fuskarta jikinsa da sauri jikinta na rawa tace “Ni akwai haskeee” yanda tayi maganan just turned him on the more, ga kamshinta da ya gama rikitasa, Yana rike da ita ya nufi wajen switch din duk da yanda kafafuwansa suka masa nauyi, ya kashe wutan dakin, tun tana nonnoke masa har bata san sanda ta sakar masa jiki gaba daya ba kamar ba ita ba, he made sure she savour every bit of that moment, he let her forget the global she was in, lokaci daya hankalinta ya dawo jikinta bayan kusan minti sha biyar, tana zaro ido ta fara turasa tace “Kace min banda shi, wayyo na shiga uku, You excluded that…” cikin shaky voice yace “Plsss” ta fashe masa da kuka tace “Nooo, baxan iya ba wallahi” Bashi da option haka ya kyaleta cike da karfin hali ya koma gefe yayi kwanciyarsa upside down, har sannan jikinta rawa yake ta jawo hijab dinta da sauri ta saka, tashi taga yayi wanda hakan sai da ya tsoratata ta koma edge din gadon da sauri jikinta na rawa, sai taga ya sauka daga kan gadon, ta bi sa da kallo cikin duhun har ya shiga bandaki, sai da ya kusa minti ashirin kafin ya fito taga ya kwanta a kasan dakin, ita dai tana ta kallonsa cikin duhun, har dai ta gaji ta kwanta a hankali ta rufe idonta amma ta kasa bacci, tana ta kwance har kusan sha biyu, tana jin yanda yake juye juye a kasa da yake kwance, ta mike zaune tana kallonsa, can kuma dai ta sauka daga kan gadon ta koma inda yake ta durkusa dan nesa da shi duk da ba sosai take ganinsa ba saboda duhu tace “Are you okay?” A hankali taji yace “I am not” Bata san sanda ta isa dab da shi ba ta durkusa tace “Baka da lafiya ne?” You could tell from her voice that she is worried, taji ya jawota jikinsa with trembling voice yace “I promise i won’t hurt you, i promise, i promise” Sae da taji wani mugun faduwar gaba, ta fara kokarin tashi daga jikinsa ya ki saketa yana maida numfashi yace “Plsss, i promise it won’t hurt, trust me Nihad” Bai bata damar cewa komai ba ya cire hijab din jikinta ya jefar.

Mami ta kasa bacci tun da taji fitar motocin operation biyu na sojoji dake gidan wajen karfe biyun dare, kuma General na gidan, gaba daya ta kasa samun nutsuwa, ta kira Khalil yafi sau goma bai daga ba, kuma tasan bashi da nauyin bacci, ko karfe nawa ka kirasa na dare zai daga, sai ta fara tunanin to ko yana zaton maganar takardun zata masa yasa ya ki dagawa, ita kuma so take taji inda yake, daga karshe ta kira Aunty Maryam, Aunty Maryam na dagawa Mami tace “Maryam yanzu naji fitar motocin operation a gidan nan, to gaba daya hankalina yaki kwanciya, you know how cunning general can be, to na kira Khalil baya daga kirana, ki kirasa ki ji yana ina, though ni dai yace min ba gidan nasa yake ba, amma ki kirasa pls” Aunty Maryam tace “Toh bari in kirasa” Ba a dau lokaci ba Aunty Maryam ta kira Mami tace “Mami wallahi baya dagawa” Mami taji hankalinta ya kara tashi, a hankali tace “Toh shikenan Maryam” Aunty Maryam tace “In sha Allah babu abinda zai faru Mami ki kwantar da hankalin ki, balle ai General din ba sanin inda yake yayi ba” Mami tace “Toh shikenan, sai mun yi magana” Daga haka ta katse wayar ta ajiye tana ma ɗan nata addu’ar neman tsari daga Abbansa.

56

Khalil na zaune gefenta ya jinginar da kansa jikin gado yana kallonta ko kiftawan kirki bai yi, gaba daya a sanyaye yake kamar ba shi ba, bai taɓa jin haushin kansa irin yau ba, he know she will ever trust him again because he never fulfilled the promise he made to her, he can’t tell what came over him that way, he didn’t take it easy on her, and all this is making him feel so bad, duk motsin da Nihad zata yi idonsa na kanta, even in sleep she doesn’t look alright, baccin karfin hali kawai take, duk tayi laushi saboda wahala, wani mugun tausayinta yake ji har ransa, a karo na farko kuma yaji yana son sanin ta yanda video dinta ya fita, yaji yana son yasan who is behind the leakage of that video of her, da kuma a inda aka yi sa, this he is going to find out by all means…. Bacci take amma restlessly, kana ganinta kasan she is in severe pain, he wish he can help her more than the way he did, but babu wani abinda xai iya mata bayan wanda yayi mata don ko kwayar magani babu a gidan, ji yake dama zai iya mayar da pain din nata zuwa jikinsa, duk ya kagu gari ya waye ya bata full care din da take bukata, ya kamo hannunta a hankali ganin ta kasa kwanciya guri daya sai juye juye take, he is been sitting there for almost an hour now, and bai damu ya zauna a hakan har gari ya waye ba just to keep an eye on her, hannunsa ya kai goshinta yaji temperature dinta is gradually getting so high, hakan da yayi yasa ta bude idonta da suka kumbura a firgice tana kokarin tashi zaune ya kwantar da ita, cikin sanyin murya me cike da damuwa yace “I am only feeling ur temperature” Taki bari su hada ido ta juya kanta tana sauke numfashi a hankali ta kulle idonta, ya duka dai dai kunnenta cikin sanyin murya that is full of remorse yace “I am sorry Nihad, i never meant to hurt you this way…. Don Allah kiyi hakuri…. I was just…” Sai kuma ya kasa ci gaba, he felt so bad because he is making her pass through much pain, ya kife kansa saman gadon ya kasa cewa komai, Ita dai bata bude idonta ba duk da hawayen dake zuba ta gefen idon nata a hakan,  bayan few minutes ya dago kansa a hankali yana kallonta da idanuwansa da suka kada, ya ga alamar ta koma baccin, ya kalli agogo da yayi strucking karfe biyu da minti sha biyar, ya sake kallonta yaga baccin take yi, a hankali ya kai hannu ya goge hawayen dake fuskarta sannan ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa, karfin hali kawai yake don ji yake kamar zazzabi na neman rufesa, har ya fita ya dawo ya dau Hijab dinta ya ajiye saman bedsheet din sannan ya juya ya fita daga dakin ya kulle kofar a hankali, nasa dakin ya koma, ya shiga bandaki ya tara ruwan dumi yayi wanka sannan ya fito, a daddafe ya goge jikinsa ya saka Jallabiyarsa sannan ya kwanta ya rufa da duvet feeling feverish, ga wani sanyi da yake ji, yana son tashi ya koma dakin nata to check on her amma ya kasa tashi, lokaci daya zazzabi ya rufesa, yana ta kwance cikin duvet yaji kamar tsayuwar motoci a waje, ya bude fuskarsa wanting to be sure of what he heard, Bai san sanda ya yunkura ya mike ya nufi windown  dakin da sauri ya bude curtain din, sosai gabansa ya fadi jin ana taɓa gate din gidan, da hanzari ya shiga parlornsa ya bude kofar balcony dake wajen don ta nan ne kadai zai iya hango kofar gidan da kyau, still yayi yana kallon motocin wa enda yake hangowa a kofar gidan, lokaci daya hankalinsa yayi mugun tashi, ya juya da sauri ya fito ya koma bedroom dinsa ya dau wayarsa zuciyarsa na bugawa, nan ya ga missed calls din Mami ya kusa sha biyar, Ga kuma na Aunty Maryam duk few minutes ago, he was just confused at this stage, gaba daya ya rude, ya koma dakin da Nihad take da sauri, rasa yanda zai yi yayi, ya jingina da bango zuciyarsa na bugawa sosai, da shi kadai ne gidan sai dai su shigo su dau hotonsa da za su gani manne a parlor amma ba dai shi ba, definitely sai ya sami hanyar fita cikin lokaci kankani, he will surely find a way out for himself, but yanzu bazai yi hakan ba ga Nihad, yaji kafafuwansa sun kasa daukansa ya karasa da kyar ya zauna gefen gadon ya rike kansa da yayi masa nauyi sosai, duk wani tunaninsa ya kwance a lokacin, bai kuma sannua zai yi ba, his father really caught him unaware, yana jin suna ta kokarin bude gate din gidan babu kakkautawa, can yayi karfin halin tashi ya tafi dakinsa ya dauko duvet ya fito ya dawo dakin da Nihad take, lulluba mata duvet din yayi a jiki a hankali, don riga ce iya gwiwa da ya sa mata daxu a jikinta, ta bude jajayen idonta da sauri tana kallonsa, yayi kissing goshinta yaji jikinta yayi mugun zafi, ya lumshe idonsa yayi kissing lips dinta a hankali yace “I don’t want you to be cold…. I am sorry i made u sick Nihad” Ta rufe idonta don muryarta ma a dashe yake, bata taɓa sanin akwai irin wannan wahalan ba a duniya sai dazu, ya mike a hankali ya fita daga dakin, ya zura wayarsa a aljihu sannan ya sauka downstairs duk da yanda kansa ke juya masa, ya nufi kofar parlor ya bude ya fita, direct gate din ya nufa, ya ɗan tsaya for few seconds, can ya runtse ido lokaci daya ya bude gate din yana kallonsu, Sojoji ne sun kai su goma a bakin gate din, daya daga cikinsu yayi gripping din hannunsa yana kallonsa, Khalil ya hade rai yace “Easy Mr Man, kai ka kamani ko ni na kawo kaina??” Tuni wani ya miko handcuff, shi dai kallonsu kawai yake kirjinsa na sama da kasa, ganin yanda sojan ke kiciniyar saka masa handcuff din kamar wanda yayi sata, Khalil yaki bari ya saka, yana huci yace “Ce maku aka yi nayi sata ku zo ku daureni?” Duk cikinsu babu wanda ya kalli fuskarsa balle su ce masa komai a wajen, har sai da suka makala masa suka yi hanyar mota da shi, wani sojan ya tafi ya kulle gidan Khalil na kallonsa, anyi masa ire iren haka ya fi a kirga don haka ba sabon abu bane wannan a wajensa, kuma yanda Janar ya basu umarni su yi haka suke yi, shi sa duk bakaken maganar da Khalil zai gasa masu basa daga kai su kallesa balle su ce masa komai, don ko dungurinsa Najar bai basu umarni su yi ba, iyaka su saka masa handcuff su kawo masa shi har gida…. (au Janar xan ce wai Najar

😂)

 wajejen karfe hudu na asuba suka isa gida da shi, direct Guard room dake cikin compound din suka kai sa suka turasa ciki sannan suka rufe wajen da kwado, leaving him all alone, Khalil ya rike kansa dake sara masa, why didn’t he think twice kafin ya shiga gidan, he just forgot who his father is, babban damuwa da tashin hankalinsa yanzu bai wuce Nihad ba, she needs to be taking care of, she needs him by her side, yasan baxata iya yin komai ba, wannan tunanin yasa yaji zazzabinsa ya dawo da karfinsa, har aka yi kiran sallah na biyu ko gyangyadi khalil bai yi ba, ga sauro sai abinda suka manta ne basu masa ba a jikinsa, ko kwanciya mutum bashi da damar yi a guard room din, wajen ne ɗan tsut da shi, ana tada sallan asuba sojoji uku suka zo suka bude karfen Guard room din, fitowa yayi da kyar yana jin kansa na juya masa, ya dafa bango da sauri, ɗan cell ne wajen kafin ainahin guard room din, shi cell din ba laifi yana ɗan da sarari duk da shi din ma dai ba babba bane, a cell din kuma har da bandaki a ciki, yasan dalilin budesa da suka yi bai wuce ya fito yayi alwala a cikin bandakin dake cell din ba yayi sallah, yayi namijin kokari wajen shiga bandakin, ko kafin ya fito ya ga darduma an ajiye masa nan cell din, ya dauka ya shimfida, suna ta tsaye bakin kofa har sai da ya idar da sallah, suka sake maida sa cikin guard room din suka kulle sannan suka kulle cell din ma daga waje, Khalil ya hade kansa da karfen Guard room din, duk da yanayin da yake ciki Nihad ce kawai a ransa, he is so worried because of her, banda ita he don’t mind being in the guard room for weeks tunda dai ya saba zama ciki, kuma yanda Abba yasa aka ajiyesa a nan zai iya tafiyarsa ya mance da batunsa har sai randa Allah ya dawo da shi, iyaka a dinga kawo masa abinci da ruwa, for the sake of Nihad yaji zai iya mayar masa duk abinda yayi seizing, duk da zafin da guardroom din shi sanyi yake ji…. Yana nan a haka har wajen karfe takwas ya ji ana bude kofar cell din, ya daga kansa, sojan na gama bude cell din Mami ta shigo ciki tana kallon ɗan guardroom din, Sojan ya karaso ya bude karfen guardroom din… Khalil ya kasa fitowa saboda zazzabin da ya ci karfinsa, Mami ta karasa tana kallonsa, cike da karfin hali ya fito, Mami na ganin yanayinsa taji hankalinta ya tashi tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Yanzu meye amfanin haka khalil, kaga abinda nake ta gudar maka ka kasa ganewa….” Sai kawai ta fashe da kuka, Da sauri taga ya shiga bandakin cikin cell din wanting to throw up, ta bi bayansa hankalinta a mugun tashe, tana rike da hannunsa suka fito daga bandakin don ya kasa aman, ya zauna nan kasan cell din ya jinginar da kansa jikin bango ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, Mami dai sai hawaye take barin yanda taji jikinsa yayi zafi, it’s rare aga yana rashin lafiya shi yasa ma hankalinta ya tashi yanzu, to kiran Abban nasa zata yi tace bashi da lafiya yanzu kenan, tana yin hakan kuma zai ce ita ke supporting dinsa yayi duk abinda yake yi, gaba daya she is confused, ta durkusa gabansa tace “Abinda nake ta gudu kenan, kasan waye Abbanka Khalil, kasan abinda zai iya aikatawa, ban san me yasa zaka shiga gonarsa ba…” Sai kuma ta fashe da kuka, ya kamo hannunta cikin sanyin murya yace “I am sorry Mami….” Tace “Ka fada min wani maganin za aje a siyo maka idan kayi breakfast yanzu sai ka sha” Ya girgiza mata kai kawai, tace “You don’t look okay, so kake ciwon ya kwantar da kai a nan? Ka gaya min maganin da za a siyo maka in je yanzu a siyo” Yayi kasa da murya yace “I am not sick, i am just worried, i am disturbed, not because ina cikin guard room” Mami na kallonsa tace “What is making you worried then?” Ya kasa hada ido da ita, sai ma sunkuyar da kansa da yayi, da damuwa tace “Talk to me son, meye damuwarka? Ni mahaifiyarka ce kar ka boye min” Lokaci daya idanuwansa suka kada ya dago kai cike da karfin hali yace “Na maku laifi during my stay in kano” Mami ta dinga kallonsa tace “Laifi? Laifin me son?” Ya kamo hannunta gathering all sort of courage, muryarsa na rawa yace “I got married while in kano” da wani expression Mami ta dinga kallonsa kamar me son fahimtar abinda yace, can tace “Ban fahimta ba, menene married?” Ya kasa kallonta with shaky voice yace “I am sorry Mami, Allah ne ya kaddara min haka, but i never bargained for it” Mami ta janye hannunta daga rikon da yayi mata ta mike tana kallonsa with a weird expression tace “Zazzabin ne yasa kake wannan sumbatun Khalil? Kasan me kake cewa kuwa” Hawaye ta gani idonsa, cike da karfin hali yace “Mami i am in my right senses, i am telling u the fact, kuma tana can gidana yanzu haka” Mami na zare ido tace “Ita wa?” A hankali yace “Matar, kuma sojojin sun kulle gidan, she is inside the house” Mami ta fi minti daya tana kallonsa with shock, shi dai ya kasa hada ido da ita, burinsa kawai aje wajen Nihad a bata kulawar da ya kamata a bata, A hankali Mami ta juya ta nufi kofar cell din, kana ganinta kasan jikinta yayi mugun sanyi and she is speechless, ya bi ta da kallo zuciyarsa na bugawa har ta fita……

56

Mami ta koma bangarenta da sauri ta shiga dakinta, Noor dake parlor ta bi ta da kallo ganin yanayinta ta mike ta bi bayanta zuwa dakin, zaune ta ganta gefen gado kamar warce taji wani mugun abu, she look shock, Noor ta karasa kusa da ita da sauri tace “Mami are you alright?” Mami ta kasa ce mata komai sai kallonta take, cike da damuwa Noor tace “Pls Mami ki kwantar da hankalinki kar ki fara rashin lafiya, everything will be alright in sha Allah, don Allah kar ki sa damuwa a ranki” Still dai Mami babu bakin magana, furucin khalil na karshe ne kawai ke ta yawo a kanta, she is trying all possible best tayi apprehending din furucin nasa, Noor ta zauna gefenta ganin kamar ma bata san abinda take cewa ba, ko kadan bata son ganin Maminsu cikin tashin hankali, Noor ta kamo hannunta cikin sanyin murya tace “Plss Mami calm down, everything will be okay in sha Allah….” Sai a sannan Mami ta kalleta cike da karfin hali tace “Dauki wayata ki kira min Maryam….” Noor ta tashi ta dau wayar Mami dake gaban mirror tayi dialing number Aunty Maryam ta kai ma Mami bayan ya fara ring, Mami ta amsa tana kallonta tace “Ki je zan yi waya Noor” Noor ta juya ta fita daga dakin, Aunty Maryam na dagawa tace “Ya ake ciki Mami? Nayi ta kira baki daga ba, Is he alright?” Mami tayi karfin halin cewa “Maryam i wish kina kusa da ni….” Aunty Maryam da taji gabanta ya fadi tace “Lafiya Yaya? Hope all is well?” Mami ta kasa ce mata komai, she is just speechless, hankali tashe Aunty Maryam tace “Hello…. talk to me, me ya faru Mami?” Mami taji kanta ya sara mata, ta dafa kan tace “Zan kira ki Maryam” Bata jira me Aunty Maryam zata ce ba ta katse wayar kawai ta mike ta dau Hijab dinta ta saka ta fita…. Aunty Maryam ta gaji da kiran wayar Mami, daga karshe ta kira Noor, Noor na dagawa Aunty Maryam tace “Noor me ke faruwa?? Ina Mamin?” Noor tace “Wallahi ban sani ba, kawai tace min zata je wajen yayanmu a guardroom, kuma da ta dawo naga mood dinta gaba daya sae a hankali” Aunty Maryam tace “Ta samu ganinsa kuma?” Noor tace “Toh ban dai sani ba, kawai naga ta shigo wani iri, i asked what the problem is bata ce min komai ba” Aunty Maryam tace “Abban naku na gidan ne??” Noor tace “Baya nan tun jiya” Aunty Maryam duk hankalinta ya tashi, tace “Ina Mamin yanzu take?” Noor tace “Yanzun nan ta fita” Aunty Maryam tace “Kai mata wayar da sauri don Allah” Noor ta mike ta fita da sauri, har ta iso main parlor bata ga Mami ba sai Aunty Hassana dake zaune ta cika parlon da kas kas din cingam, Noor na fitowa compound ta gan Mami cikin mota za su fita with 3 soldiers, tsaye tayi tana kallon motar har suka fita daga compound din, Noor ta koma ciki ita ma duk jikinta yayi sanyi, ta kira Aunty Maryam tace “Aunty naga ta fita a mota kuma yanzu” Aunty Maryam taji hankalinta ya kara tashi sosai, ta ji kamar tayi tsuntsu ta ganta a Nigeria, Aunty Maryam tace “Kin tabbata kuma Khalil na guardroom din?” Noor tace “Da asuba fa suka shigo gidan nan, i am sure yana ciki, kuma na tambayi wani soja dazu yace min yana ciki” Aunty Maryam ta katse wayar kawai, babban damuwarta rashin maganar da basu yi da Mami ba har ta fita gidan, to ina zata? Ko gidan Hajiya Safeenah?

 Gaba daya hankalin Mami baya jikinta har suka iso gidan Khalil, ta bude motar ta sauka tana kallon gate din gidan dake a kulle, daya daga sojojin ya karasa ya bude mata gate din da makulli, har bakin kofar shiga main parlor suka rakata, cike da karfin hali tana kallonsu tace “Ku jira ni nan” Suka tsaya bakin kofar ta shiga ciki tana bin parlon da kallo, mutuwar tsaye tayi ganin takalmin mace dake kofar parlon, she became weak lokaci daya, taji kafanta sun mata nauyi, banda faduwa babu abinda gabanta yake, tana tafiya a hankali ta nufi staircase dake parlon ta haura sama kamar me counting stairs din, ta fi second ashirin tana bin kofofin dakunan dake sama da kallo, master Bedroom din Khalil ta fara shiga taga ba kowa ciki sai pajamas dinsa dake saman gado, ta fi minti daya tsaye a dakin kafin ta juyo a hankali ta fito daga dakin, ta tafi ta bude wani kofar very gently, gabanta ya yanke ya fadi, komai ya tsaya mata cak ganin mace kwance saman gado ta takure cikin duvet sae dai ba a ganin fuskarta sbda ta rufe da duvet sae gashin kanta dake baje, Mami ta ji ta k