Rayuwa da gibi hausa novels

Rayuwa da Gibi Chapter 3

This entry is part 3 of 3 in the series Rayuwa da gibi by Batul Mamman

RAYUWA DA GIƁI 3

Batul Mamman💖

Masu tambaya littafin ba na kuɗi bane.

*

Auren Habibu da Jinjin ba na son zuciya bane kamar yadda ƴaƴansu suke hasashe. Yar mahaifinsu da suka fi ɗorawa alhakin saboda sunanta da Zee tace wato Anti Zinatu ma ba laifinta bane. Abu ne na karamci da sanin darajar wanda ya kiyaye taka darajar.

Aure ne na zumunci domin kuwa kamar yadda Iyaa da Baba Maje suka fito daga zuri’a ɗaya su ma iyayensu mata shaƙiƙan juna ne. Mahaifiyar Habibu ita ce babba. Tayi aure a Kano da ƴaƴanta maza uku da mata biyu. Shi ne na biyu. Ita kuwa mahaifiyar Jinjin a garinsu Ɓatagarawa dake Katsina tayi aure. Bata sami haihuwar ba da wuri sai akanta. Ta haifota kyakkawa mai kama da dangin mahaifiyar. Idan ka ganta da ƴaƴan Inna Batulu za ka rantse ita ta haife su duka. Sunanta Khadija amma ake kirantan Jinjin (jinjinniya don ƙauna). Soyayya da gata gwargwadon hali ta taso tana gani wurin uwa da uba kafin Allah Ya jarabceta da cutar shan inna tana da shekara biyu da rabi. Lokacin da iyayen su ka farga ƙafar ta mutu ba ƙaramar damuwa su ka shiga ba. Idan tana tafiya kafaɗa da ɓangaren ƙirjinta na dama sai ya ballaƙo waje. Wannan abu ya tsayawa uban a rai. Har ta kai indai yana wajen da ta miƙe zai ce,

“Don ubanki koma ki zauna. Kina faman tafiya kamar wata tsuntsuwa babu kyan gani.”

Ko ya ce “wannan da ma ciwon tafiya ya yi dake kika huta. Meye haka don Allah?”

Da bata da wayo uwar ke kuka idan yana wannan rashin albarkar. Ƙarshe ma yayi aure shi da matar da lafiyayyun ƴaƴan da su ka haifa su ka taru su ka mayar da rayuwar Jinjin ƙuntatacciya. Yanzu ita ke kukan uwar na rarrashi. Watarana Inna Batulu ta kawo musu ziyara ta tarar da ƴaƴan kishiyar ƙanwarta suna dukan Jinjin. Abin takaici uwarsu da ƙanwar na kusa amma wai kawaici ya hana ta ƙwaci ƴarta. Garin cangala ƙafa ta kifar da garin masarar tuwon dare. Kuma gudu ma take saboda an biyota za a ci zali.

Inna Batulu na gani tayi kukan kura ta damƙo yaran nan su uku ta bi kowa ta feffela musu mari. Ta ƙare musu zagi irin nasu na Katsinawa.

“Banda raini ba yayarku bace?” Ta juya ga ƙanwarta “shiga ki haɗo min kayanta yanzu zan wuce da ita tunda ba kya so.”

“Ba haka bane Yaya.”

Da takaici takalleta “kunyar marasa kunya asara ce Luba. Gidan nan kaf har mijin naki ban ga wanda ya dace ki ragawa akan kyautar da Allah Ya yi miki ba.”

Jijjiga Jinjin tayi a gabanta ta ƙara da cewa “don bala’in gidan nan ƴar shekara goma sha uku ji ƙirjinta kamar anyi daɓen siminti.”

“Kai Yaya Talatu?”

“Allah kuwa. Zuwa yanzu ai yaci ace an fara ganin…”

Da ɗan gudunta Jinjin ta bar wajen don bata son ƙarasa jin hirar iyayen.

Kamar wasa maigidan na dawowa Inna Batulu ta sauke masa nashi kwandon masifar ta ce kuma jiransa take a bata ƴa.

“Gata nan har abada da gaban abada na bar miki.” Ya furta ko ajikinsa.

Luba sam bata ji daɗi ba amma haka ta shirya mata kaya su ka tafi. Bata da wani farinciki ko nishaɗi a gidan idan ba Jinjin take gani ba. Da ita take hira tunda miji ya juya mata baya. Sauƙinta ɗaya ta san cewa yanzu za ta sami ƴanci ta wataya kamar sauran yara.

A Kano tabbas taga gata da soyayyar da tasa har take manta da nakasar dake tare da ita. Inna Batulu da maigidanta harma da yaransu sun mayar da ita ƴar gata. Matsala guda ta kula akwai a gidan ita ce ta yayanta Habibu. Lokacin yarintarsu tana iya tuna shi da yawan wasa da dariya. Yanzu kuwa kullum iyayensa cikin kukan sabuwar ɗabi’arsa suke yi.

Shi ne tafiya yana rangwaɗa da karairaya jiki kamar mata. Ga uwa uba muryarsa da bata san ya aka yi ta motse ba. Idan ya yi magana sai ka rantse wata budurwar ce. Duk wasu take taken daudanci yake nunawa. Indai zai yi sallama a gidan daga su Inna Batulu har ƴan uwansa basu da nutsuwa.

A yau da take da kusan wata biyu a gidan sallamar wata matashi suka ji a gaggauce. Babu kowa a gidan sai Jinjin da ta dawo daga makarantar islamiyya. Fita tayi ko kaya bata cire ba ta sami wani mutum da bata sani ba. Da gani magidanci ne ya sha shadda wagambari da ɓakar ɗara a ka.

“Inna Batulu ko Baba nake nema” ya ce kafin ta gaishe shi.

“Duk basa nan.”

Kallonta ya sake yi ya tuna sun taba shiga gidansu wurin iyayensa da Inna Batulu tace ƴarta ce daga Ɓatagarawa. Shi yasa kawai ya faɗa mata abin da ya kawo shi.

“Ki ce musu Habibu na gani a gidan abincin wasu ƴan daudu yana girki a kasuwa.”

Rasa abin cewa tayi don fuskar mutumin tayi nuni da matsanancin ɓacin ran da ganin hakan ya janyo masa.

“Kin fahimci abin da nace kuwa?”

“Eh, zan faɗa musu in sha Allahu.”

Juyawa ya yi babu sallama zai tafi ta tambaye shi wa za ta ce musu.

“Hayatun gidan Alh. Sule.”

Sunan da taji bayan tafiyarsa ya dawo mata da hirar da ta taɓa tsinkaya daga mutan gidan. Akwai gidan wani mai kuɗi nan kusa dasu wanda aka ce ɗansu Hayatu ya ɗauki Habibu tamkar cikinsu ɗaya. Saboda ladabi da ƙoƙarinsa a shekarun baya ya kasance duk wata lalurar karatunsa Hayatu ya ɗaukarwa kansa. Irin abin nan na maikuɗi ya cicciɓi talaka domin inganta masa rayuwa. Ance da Habibun ya fara canja akalar rayuwa Hayatu ya shiga ɓacin rai sosai. A son sa yaron ya ginu ya zama mutum amma kullum ana yi masa faɗa yana daɗa kangarewa. Me za ayi da namiji mai girki a ƙasar hausa? Har dukansa taji ya taɓa yi watarana da ya ganshi da ɗaurin zani a ƙirji ya fita. A ƙarshe ya ce masa zai iya tsaya masa ya koyi girkin harma ya mayar dashi sana’a amma sai ya ajiye duk wani abu da yake kamanceceniya da mata. To Habibu dai ana faɗa ta kunnen dama zancen na ficewa ta hagu.

Da Inna Batulu ta dawo ta sanar da ita sai da tayi kuka. Shi yasa ba a son zama unguwa ɗaya da wanda ake ganin zai iya jan ra’ayin yaran unguwa. Daga yawan aikensa siyan abinci a wurin wasu ƴan daudu dake bakin titi ita dai bata san yadda aka yi ya dinga rikiɗewa ya koma wannan Habibun na gabansu ba.

Ranar anyi masa faɗa sosai. Baba ya zage ya yi masa dukan mutuwa. Garin Allah na wayewa aka neme shi aka rasa. Wurin wata uku ana nema kafin daga bisani su sami labarin ya tafi Saudiya da wani ubangidansa. Sana’ar abinci su ke yi a can ɗin.

Akwai abubuwa da kan sami bawa ya rasa silarsu. Ka haifi ɗa kayi masa duk iyakar ƙoƙari amma idan ƙaddara ta faɗa masa kana ji kana gani zai zaɓi hanyar ta bata ɓullewa. Irin haka ta sami Habibun Inna Batulu. Dangi su ka sanyo su a gaba da yawan magana da famin ciwo. Wasu in sun sami zuwa ƙasa mai tsarki a unguwar su yi ta kawo labaran yadda aka ganshi ya ɗashe saboda shafe shafe. Zantuka barkatai harda wanda ya ce wai an faɗa masa ya yi aure da wani ɗan daudu irinsa.

Zancen da ya tayar da hankalin Baba fiye da kowanne kenan. Ya sayar da gonarsa da wani gidan haya ya haɗa kuɗi a shekarar ya tafi Hajji. Bai wani sha wahala ba aka sada shi da gidan da Simagade yake haya da abokan sana’arsa. Lokacin shekararsa tara baya gida. Jinjin ta gama sakandire har ta fara sana’ar kitso a gida tunda aure ya gagara. Ta kai matakin da kowane iri tana son samu saboda yadda mahaifinta ke jifanta da maganganu idan taje gida.

Baba fashewa yayi da kuka da yaga ɗan nasa sanye da jallabiya ya ɗora zani da ɗankwali. Ga haƙoran Makka har biyu. Tamkar ba a Jidda ba suna ta ƙazaman zage zage shi da wani da suke faɗa. Ganin mahaifinsa ne ya sagar masa da gwiwa ya yi shiru. Sai hankalin kowa ya kai kan tsohon dake zubar da hawaye.

“Shiga ka sako kaya ka zo ka rakani masallaci.”

Ba Habibu ba hatta abokan zamansa duk jikkuna sun yi sanyi. Ya shiga ciki ya samo aron wasu pakistan na maza ya saka. Ya fito tafiyar nan babu dama ne. Masallaci mafi kusa Baba ya shiga dashi. Ya umarce shi da yin sallah raka’a biyu sannan ya fuskance shi bayan sun idar.

“Saboda ka taka dokar Allah Habibu yau alwala da sallarka ma in ni nake karɓa ba za su bar rufin masallacin nan ba zan jeho maka kayarka.”

Kai ya sunkuyar cike da kunyar kansa.

“Daga wannan rana ba zan sake yi maka faɗa ko nasiha ba. Zan kuma roƙi Batulu da kada mu sake zubar da hawaye a kanka. Na barka da duniyar da ka zaɓa wadda nan da kwanaki kaɗan za ta daina yayinka. Idan tayi maka rawar ƴan mata ina jin za ka yi hankali har ma kayi tunanin dawowa gida. In na mutu tun yanzu ka sani na yafe maka. In kana da rabon shiriya ka zo gida kafin baƙincikinka yayi ajalin mahaifiyarka.”

Yana gama faɗin haka ya tashi. Habibu zai bi shi ya ce baya so. Haka ya koma ya gama kwanakin da su ka rage ya dawo gida. Habibu kuwa komai ya daina yi masa daɗi. Nadama mai raɗaɗi ta shiga ɗawainiya dashi. Ana gama kwaso mahajjata ya tattara komatsansa ya dawo gida.

Bai fi wata biyu ba Baba ya kama cuta har ya cika. Yayi kuka kuwa kamar ba gobe. A gefe guda yana godiya ga Allah da Ys bashi damar dawowa. Tun daga lokacin ya soma neman gyara rayuwarsa. Sai dai kuma jama’a da dama suna gagarar yiwa mai laifi uzuri ko ya tuba. Da yake har yanzu in ba jallabiyar nan ya saka ba sai yaji kamar yayi tsirara, amma yana bakin ƙoƙarinsa wurin yin abin maza. Matsalar dai an bar kari tun ran tubani. Murya ta gama shaƙewa. Karairaya ta zame masa jiki duk da ya rage. Ya yi ta neman aikin yi ya rasa. In ya kasa kayan sayarwa irinsu kayan miya babu mai saye. Har wurin Hayatu yaje amma yaƙi taimaka masa ya zama yaron shago kamar yadda ya nema. Allah Ya ɗora masa ƙyamar ƴan daudu sosai.

Da ya rasa yadda zai yi ne ya roƙi Inna Batulu ta yarje masa tafiya Lagos sayar da abinci. Ya tabbata a can da babu wanda ya san shi kuma girki ba a ɗauke shi sana’ar mata kaɗai ba zai sami sauƙi.

“Idan ka tafi Habibu ina jin tsoron kada ka koma ruwa. Gashi nayi imanin babu mai baka mata ka aura a halin da kake ciki.” Ta goge hawaye.

“Ki yafe min Inna. Na san na cuci kaina amma nayi miki alƙawarin ba zan komawa waccan rayuwa ba.”

Duk zancensu a kunnen Jinjin. Kafin tafiyarsu ta sake jin maganar ana yi tsakaninsa da ƴan uwansu. Ta kula Inna tana cikin damuwa. Barinsa babu abin yi matsala ne. Sannan zuwansa shi kaɗai akwai haɗari. Bayan dogon nazari irin na yarinta ta nemi izinin zuwa gida ta shawarta da mahaifiyarta. Luba ƴar halak ko mijinta bata bi ta kansa ba ta sako ƴarta a gaba su ka taho Kano. A gaban ƴaƴan gidan da mahaifiyarsu ta ce ga amana ta sake damƙa musu.

“Jinjin miskiniya ce na sani. Ban sani ba ko bawa Habibu ita zai zama gwaninta ko abin ɓacin rai a gareku.”

“Allah Ya kiyaye Gwaggo Luba” cewar yayar Habibu tana taya Inna Batulu kuka don ta kasa magana.

Sun yiwa uwa da ƴar godiya kamar su ari baki. A wata guda aka yi komai aka gama su ka koma Lagos da zama. Rayuwar ta fara daɗi Allah Ya karɓi ran Innarsa. Shi ne dalilin dawowarsu kuma ya kasa komawa.

Habibu yana ƙaunar ƴaƴansa kamar rai. Yafi kowa sanin akwai lokutan da basa son nuna shi. Shiyasa ya kan kame daga zaƙe musu don kada ya ɓata rawarsa da tsalle. Matarsa Jinjin kuwa duk duniya baya haɗata da komai. Shi ya sani cewa tayi masa alfarmar da da ace ana auren ƙanwa ko ya nasa ba za su taɓa aurensa yana ɗan daudu ba.

**

Alh. Hayatu Sule Maitakalmi mashahurin ɗan kasuwa ne a Kantin Kwari. Takalma dai na mata da maza daga shagunansa an gama magana. Karansa ya kai tsaiko a kasuwanci. Sunansa ya zaga duk inda ya dace a dama da shi. Mutumin cikin ƙwaryar Kano ne daga unguwar Soron ɗinki. Yana da kirki da ƙoƙarin cicciɓa na ƙasa da shi sai dai akwai tsatstsauran ra’ayi kuma baya tanƙwaruwa. Duk wanda ya san shi ya san kaifi ɗaya ne kamar bakin wuƙa.

Matansa huɗu kuma duk a gida ɗaya suke. Ƙaton gini ne na masu kuɗin da wanda yake yawan shan gyara domin ya tadda zamani. Ainihin gidan akwai ƙaton falo wanda in an shiga da ƙofofi huɗu a jere a ɓangaren dama. Kowacce in ka shiga falo ne babba da banɗaki da kuma ɗakuna biyu. Nan me ɗakunan matansa. Bangon dake kallon ɗakunan kuwa kitchen ne makeke da store sai ɗakin masu aiki dake haɗe da banɗaki. A jikin bangon tsakiya ne da matattakalar bene inda ɗakin maigidan yake da falonsa. Sai kuma ɗakuna biyu na ƴan mata suma kowanne da banɗaki duk a saman. Sai an fita daga bayan ainihin ginin ne kuma za a tarar da ɓangaren samari. Ta gaba kuma aka jona ginin falo da banɗaki inda yake ganawa da baƙinsa. Duka gidan ƴaƴa ashirin da takwas ne kuma a ciki biyar ne kaɗai maza. Sai ƴaƴan ƴan uwa da yake riƙo da ƙannensa. Shi yasa kullum gidan yake a cike.

Uwargidansa ta lalle Haj. Gambo da ake kira Hajiya kaɗai tana da goma. Ta biyun Mama A’i tana da uku. Sai Umma Jamila mai takwas. Sannan amarya Inna Abu mai shida. Ya taɓa sakin mace ɗaya wadda ta kasance ta uku a jerin aurensa. Ɗa ɗaya ta haifa kuma shi ne babban namiji a gidan mai suna Ahmad. Da fitina ta zo shi kuma ba zai lamunta ba. Tun yana lallaɓawa da yaga za ta wargaza masa tsari ya sallameta ya bawa Mama ɗan. Tun daga lokacin babu wadda ta sake gigin tayar masa da hankali. Zaman lafiya ake da ƙullewar zumunci. Har ta kai idan mace ta haihu wani zubin ɗan cikinta ma sai ya yi mata ƙyuya saboda kulawar da yake samu a wajen yayyensa da sauran matan. Irin rayuwar nan ta daga ni sai ƴaƴana bata da muhalli kwatakwata a gidan Alh. Hayatu.

Bayan Ahmad an ɗauki lokaci kafin a sake samun ɗa namiji. Don a haihuwa ta tara Hajiya ta haifi Kamaluddin. Yana da wata biyar Inna ta haifi Tajuddin. Bayansa tayi mata biyu sannan ta ƙara da maza biyu Sulaiman (Abba) da Bishir sai ta rufe da mace kuma autar gidan. Wannan yasa mazan su ka tashi a ƙarƙashin yayunsu mata tunda sun zo a sahun ƙarshe ƙarshe.

Kamal da Taj sun tashi tamkar ƴan biyu sakamakon rashin tazarar haihuwarsu. Wasu har basa gane su don hatta pant duk mai sayawa ɗaya za ta sai wa ɗayan. Bambancinsu da aka fi ganewa shi ne doguwar fuskar Taj da gashin fulanin Kamal wanda su ka gado daga uwayensu. Da yake jinin Alhajin akwai ƙarfi duk inda ƴaƴansa su ke basa ɓoyuwa. Musamman da cikakkiyar girarsu da ta zama wani sirri na ƙarin kyawunsu. Mama uwar riƙon Ahmad ita ce maman mazan gidan. Duk abin da ya shafesu ita ce a kai tun ana goyonsu. Ita take yayesu shikenan yaro ya koma ɗakinta.

Za a iya cewa Taj da Kamal wasu manyan jigo ne na farincikin gidan Alhaji. Indai suna gida to in sha Allahu dariya da nishaɗi baya yankewa. Zolaya da wasa duk halinsu ne. Har suna su ka sanyawa juna. Kamal ya kira Taj Happy, shi kuma Taj ya kira shi Happiness. Irin faɗan nan na sakonni da wuya kaga sun yi. Sannan daga yayyensu har ƙanne ba za ka ji wanda ya kai ƙararsu akan sun masa ba daidai ba. Duk kuwa da kasancewar Taj mai tsokana lamba ɗaya. To amma yana da tsoron yin laifin da za a hukunta shi. Shi kuwa Kamal dama green snake ne. Sai ya yi abu ya koma gefe kamar ba shi ba.

Tun tasowarsu akwai wata irin shaƙuwa ta musamman tsakanin Alhaji da Taj. Shi dai da zarar mahaifinsu ya dawo to ya gama wasu wasanni. Yana daga cikin lokutan da akan gansu wuri daban daban shi da Kamal. A gefensa yake zama yana yi masa tambayoyi musamman akan kasuwanci. Nan da nan ya zama sunansa abokan harkokin Alhajin su ka fi sani. Kowa ya buɗe baki sai ya ce Taj. Har dai aka fara hannunka mai sanda a gidan ana cewa da alama shi zai gaji Alhajin. Yawan maganar yasa Inna ta fara jin abin yana damunta. Bata son rigima ta ɓullo daga ɓangarenta. Shi yasa wata rana su na zaune su biyu da Alhajin ta tayar masa da zancen.

“To ke banda abin ki mene ne a ciki? Duk uba ai yana son magaji a fannin da ya yi zarra musamman idan halattacce ne.”

Wasa taga ya mayar da zancen ta girgiza kai.

“Kaga yana da yayye. Idan ana cewa magajinka wani zai yi zaton irin abin nan ne na son ture wasu don wata manufa.”

Kallonta ya yi yaga sosai ta shiga damuwa.

“Ku mata sai a barku. Tunaninku kullum babu nisa. Musulunci dai ya riga ya gama mana komai. Yau ko dama na kwanta yadda shari’a ta tsara haka za a raba abin da na bari a bawa ƴaƴana. Babu wani fifiko.”

“Na sani”

“Amma duk da haka kina damuwa saboda kada a ce Hayatu ya fifita ɗanki akan na sauran. Ƙila ma kina ƙarawa da cewa za a zargi ko don mahaifiyarki ƙanwar mahaifina ce.”

“A’a wallahi” ta ce da sauri.

Ya sake yin murmushi sannan ya ɗan tuna mata baya. A gidansu cikin maza su goma sha uku shi kaɗai ne ɗan kasuwa kamar baban su. Sauran duk aikin gwamnati su ke yi. Shi kuwa ya ajiye kwalin tun daga degree na farko ya rungumi sana’ar gidan ba tare da an tauye ƴan uwansa da komai ba. Duk abin da ya tara yanzu arziƙinsa ne na guminsa. Ya ma zamana duka ƴan uwan nasa duk wanda ɗansa namiji ya gama sakandire sai ya tura masa shi kasuwa na shekara ɗaya. A haka yanzu akwai mutum bakwai cikin ƴaƴansu da su ke jikinsa.

“Zan yi maganin damuwar nan anjima idan an zo cin abincin dare.”

Bai manta ba kuwa. Dama al’adar gidan idan ba baƙi gare shi ba duka tare ake cin abinci a babban falo. Ƴan shekaru kusa da juna ake haɗawa a kwano guda. Matansa ma yawanci tare su ke ci. Ana gamawa yaran za su nufe shi da buƙatunsu. Ko fensir ne ya karye sun fi gane su sanar dashi. Yana daga zaune zai sa a bashi reza don yafi gane mata ya fiƙe. Wasu ya koya musu homework. Masu buƙatar kuɗi ko wani abu makamancin haka duk a wannan zaman ake yi. Ana gamawa zai ja su sallar Isha sannan ya tashi. Su kuma daga nan za su ɓalle da hira. Ƙananun da duk mai ra’ayi su tarkata su koma wurin Hajiya indai ba girkinta bane domin jin daɗaɗan tatsuniyoyi.

“Mal. Bishir wai me ka ke son zama ne idan ka girma?”

Bishir ya ɗago kai daga rubutun da yake yi na homework ya kalli baban nasu.

“Shoe shiner.”

Falon gabaɗaya aka bushe da dariya harda Alhajin. Shekarar Bishir bakwai a lokacin.

Kuka ya soma yi yana cewa “Alhaji kaga suna yi min dariya ko?”

“Rabu dasu. Tambayar ma ta saraya a kanka sai ka ƙara girma. Duk wanda ya sake dariya kuma bana bashi da takalmin sallah. Dama kai zan bawa ka raba.”

Da haka ya kawo ƙarshen kukan nasa. Ya mayar da tambayar ka ga Abba.

“Babana fa?”

Murmushi ya yi “Alhaji ni police zan zama.”

“Ni dai bana son khaki Abba. Don Allah ka zaɓi aikin da ba zai dinga hana ni bacci mai daɗi ba” cewar Mama.

Alh. Hayatu ya ce a ƙyale yara a bisu da addu’a.

“Taj kuma fa?”

Abin nema ya samu. Kowa ya zuba masa ido ana jiran a ji ya ce kasuwanci irin na baban nasa sai ya basu mugun mamaki.

“Chef! Mai girki.” Ya ce hankali kwance yana murmushi.

Da yake yafi kusa da Umma a inda yake zaune bata san ma lokacin da ta buge bakinsa ba saboda wani hargitsatsen kallo da Alhaji ya watsa masa.

“Bar dukansa Jamila. Barshi ya maimaita.”

Ko ɗar bai ji ba ya sake faɗin abin da ya ce da ƙwarin gwiwa.

“Chef. Mai dafa abinci a restau…”

“TAJUDDIN!!!”

Tsawar ta gigita kowa. Ƴar autarsu ma kuka ta saka harda zubar da abincin da aka ajiye a gabanta tana ci da kanta.

“Ku tashi ku bani wuri.” Ya faɗa a fusace.

Da yake a lokacin sun kai shekara sha huɗu shi da Kamal duk da hankalinsu. Shi yasa Taj ya gane abin da ya faɗa bai sami karɓuwa ba. Bin sahun ƴan uwansa ya yi ya tashi.

“Ina za ka? Zama zaka yi ka faɗa min me ya burge ka da daudanci har kake tunanin kawo min wannan shaiɗancin cikin gida.”

A tsorace ya zauna yana kallo kowa ya tashi har iyayensu mata. Alhaji ya ɗan sausauta murya don ji yake kamar ya fara duka akan ɗan da yake matuƙar danne soyayyarsa. Ya tambaye shi ko ya taɓa yin girki a rayuwarsa.

“Abincin da aka gama ci yanzu ma ni nayi miya. Wallahi Alhaji na iya girki sosai. Indai babu islamiyya ni nake na dare.”

Sai da ya cije leɓe don wani irin sarawa kansa ya yi sannan ya ce “kirawo min uwayenka ka ce su same ni a ɗaki.”

*

A ɗakin Hajiya su ka tare su huɗu ashe suna ta caccakar Mama. Musamman Umma wadda ta jima da hango ɓacin rana a dalilin wannan abu.

“Na sha faɗa miki ki hana yaron nan shiga kitchen ki ka ƙi. Tun ana ɓare maggi har ta kai yana ɗora sanwar gidan nan.”

Mama da karayar murya ta ce “saboda Allah yanzu a ce mutum yana da yaro amma ba zai koya masa ayyukan cikin gida ba? Girki ai ba lallai sai mace ba. Kuma ra’ayinsa ne tunda duk yadda su ke da Kamal shi ko magin baya ɓarewa.”

Hajiya ta ce “Amma tun farko kin san Alhaji yaƙi jinin ganin mazan gidan nan da tsintsiya ma balle girki. Yana gani yake cewa a daina saka su kada su zama ƴan daudu. Ko kin manta tashin hankalin da aka taɓa yi akan gugar kuɓewa?”

Wata rana ne kusan shekara uku da su ka wuce mai aikinsu ta fita bata dawo da wuri ba. Girkin Hajiya ne ita ma sun fita dubiya dukkansu. Suna dawowa taga ba’ayi tuwon dare ba. Shi ne ta rabawa Ahmad, Kamal da Taj gugar kuɓewa ita kuma da taimakon yan matan gidan ta ɗora tuwo. Alhaji da ya shigo yaga suna aikin nan a falo ya dinga faɗa ba ji ba gani. Sai da ya yi sati baya cin abincin gidan yana kuma gargadi da tuna musu aikin namiji da mace a gida ba ɗaya bane.

Mama ta ɗan kalli Inna da tayi shiru kawai tana kallonsu.
“Ki ce wani abu mana. Ko kema laifina kike gani?”

“Laifi kamar yaya? Neman mafita kawai zamu yi kafin ya tasa mu a gaba don na san…”

Laluben ɗakin da Taj ya ɗaga da sallama ya katse mata magana.

“Alhaji yana kiranku a samansa.”

Hajiya kiransa tayi ganin jikinsa duk ya yi sanyi.

“Girki ko a gidanka kana da damar yi Taj amma kada ka sake cewa za ka zama mai abinci ko daɗin ji babu. Duk wani namiji mai sana’ar abinci ɗan daudu ne. Su kuwa Allah baya son su tunda sun zaɓi jinsi kishiyar wanda ya basu.”

Kai ya gyaɗa kawai ya fice. Sanin cewa zai haɗu da Ahmad da Kamal kuma lallai ba za su goyi bayansa ba sai ya gudu ɗakin Inna. Wuri ya samu ya kwanta ya rufe idanunsa yana tunani.

Kasuwanci da yake nacin koyo a wurin Alhaji ba don komai bane sai don yana da muradin buɗe gidan abincin da yake son ya yi suna. A rayuwarsa babu inda yake shiga yaji kamar an sabunta masa duniya kamar kitchen. Kuma a iya saninsa maza da yawa su na girki. Suna da shekara goma Alhaji ke kai yara Umra. Idan mutum ya yi shabiyar a kai shi Hajji. A Saudiyya in ka cire Takaru babu inda ya ga mata suna sayar da wani abu na ci. Maza ke girkawa su sayar. Maza musulmai magidanta waɗanda basu da wata siffa da duk hangen mutum zai danganta su da mata. Idan sana’ar haramtacciya ce ga namiji da waɗannan basu kai labari ba. Shi kam yana son girki kuma in Allah Ya so ita ce sana’ar da zai yi.

A ɗakin Alhaji kuwa faɗansa har falon ƙasa. Don ma ƴaƴan kowa ya shige ɗaki. Manyan sun haɗe kawunansu da ƙananan a ɗakunan iyayensu a ƙasa.

Ya fusata sosai don ko da su ka shiga ɗakin maganinsa na hawan jini yake sha.

“Ni za ku ha’inta? Girkin nan ba yau ya fara ba tunda ya ce shi ya yi miyar dare. Ace ko sau ɗaya idanuna basu taɓa gani ba. Abin da mamaki.”

Mama ce ta fara bada haƙuri “na bari ne kawai saboda ganin yawanci gidajen da su ke da yara maza duk ana koya musu girki. Hakan bai sa sun yi koyi da ɗabi’un mata ba.”

Cikin faɗa ya ce mata gidansa babu maza da yawa. A cikin mata ashirin da uku a rasa me yin girki sai maza? Shi yasa yake sanya ido sosai saboda idan ya yi sake tabbas mazan za su iya jin cewa kwaikwayon yayyensu mata ba laifi bane. Ko ɗankwali ya gani a hannun ɗansa ya dinga faɗa kenan.

“Da irin wannan sakacin wani yaro a unguwarmu ana ji ana gani wallahi ya zama cikakken ɗan daudu. Gidansu akwai mazan ma amma daga sai ga Habibu ya koma Simagade a unguwa.”

Gashi dai faɗa yake yi amma faɗin wannan suna sai da ya sanya Hajiya da Mama yin ƴar dariya. Umma da Inna dai a murmushi su ka tsaya. Ai kuwa sun janyowa kawunansu sabon faɗa. Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Musamman Mama da a yau tayi nadamar amsa sunan uwar maza a gidan.

“Dole ki yi dariya mana tunda ba ɗanki bane. Da alamu da gangan ma ki ka nemi ɓata min rayuwar yaro saboda baki san daɗin haihuwar namiji ba.”

Ba ita da ya yiwa gori ba, dukkaninsu hankulansu tashi su ka yi. Mama ta saka kuka, Umma da Inna su na taya ta. Hajiya kuwa fiƙe idanu tayi ta ɗauki ragamar girmanta.

“A’a fa Alhaji. Akan ƴaƴanka ba za mu lamunci irin wannan ba. Kai ka koya mana zama da juna. Tunda mu ka kai yanzu kuwa wallahi ba za mu yarda ka haddasa mana rigimar da bamu yi da ƙuruciya ba.”

“Ba akan ƴaƴana za ki ce ba. Ki fito fili ki faɗa min cewa akan Taj ba za ku yi min biyayya ba.” Ya dubi Inna ya cigaba da sababi “wato sai da ki ka ga lamari ya lalace sannan ki ka ankarar dani riƙon sakainar kashin da ake yiwa ɗana don kawai ana ƙyashin kusanci na da shi.”

“Na shiga uku. Alhaji yaushe mu ka yi haka?” Ta faɗi a ɗimauce ganin ƴan uwanta sun zuba mata ido.

Shi a ganinsa babu dalilin da zai sa taji wani ɗar a zuciyarta. Ya riga ya santa da kawaici saboda haka don ana yabon ɗanta a tunaninsa bai isa dalilin maganarsu ta ɗazu ba. Tabbas ganin rayuwarsa ta ɗauko hanyar gurɓacewa a hannun uwar riƙonsa shi yasa tayi magana.

Su Hajiya ficewa su ka yi aka rasa mai tambayarta abin da ya faru ma. Tana kuka ta tashi za ta bisu domin kwance wannan ɗauri da maigidan ya yi mata ya hanata fita. Dama girkinta ne. Sai kawai ya ce idan ta fita daga ɗakin ba da yawunsa ba.

RAYUWA DA GIƁI 4

Batul Mamman💖

*

Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa baƙo ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare ɗaya ana gab da samun gagarumar ɓaraka.

Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da ɗora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai ɗakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo ɗakin tare. Kai a ƙasa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya.

“Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu ƴan uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake ɗaukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba.”

Umma ta kalleta babu wannan fara’ar ta kodayaushe
“To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?”

“Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran ƴaƴan musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi.”

“Maganar girkin fa?” Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai.

“Yadda ba ku ɗauke shi laifi ba nima ban ɗauka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?”

Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta.

“Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ƙara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daɗi. Saboda haka zance ya wuce.”

Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga ɗakin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya.

“Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan.”

Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi.

Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ƙasar India inda yake haɗa degree ɗinsa a fannin Computer Science. Zaɓi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaɓa cikin ƙasashen da su ke cibiyar kasuwanci.

“Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya.” Cewar Taj.

Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce “ni dai Dubai.”

Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaɓinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta ɓangaren karatun da zai rabasu na ƴan shekaru.

“Anya kuwa Happy da Happiness za su iya rabuwa na shekara huɗu? Ku dai sake shawara ku zaɓi waje ɗaya.”

Kamal ya kalli Taj da sanyin jiki. Ya ɗauka sun gama magana akan za su zaɓi Dubai. Burinsa ya koyo larabci banda karatun da za su yi. Sannan idan da faraga ya sami wani balaraben malamin ya danɗaƙi haddarsa da kyau ta ƙara zama. Kuma lafiya ƙalau Taj ɗin ya amince har da cewa shi ma zai yi. To me ya kawo wannan sauyi?

Alhaji bai ce musu komai ba amma ya fahimci akwai matsala tsakanin yaran. Sai bayan kwana biyu ya kira kowannensu gefe don jin me yake faruwa. A yadda ya fahimta zaɓinsu bai zo ɗaya ba. Kuma kowanne yana so ɗan uwansa ya bi ra’ayinsa. Kamal sai daɗa kwaɗaitawa Taj koyon larabci yake. Shi kuma duk da yana so amma haka kawai zuciyarsa tafi kwantawa da India. Sulhu ya yi musu da alƙawarin kowa zai sami inda yake so.

Harka ta kuɗi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci an gama yiwa kowa cuku-cukun samun gurbin karatu har ana shirin tafiya. Iyayensu mata su ka sha kuka kamar lokacin tafiyar Ahmad. Ƴan uwansu hatta na gidan miji don an fara aurarwa a gidan duka aka haɗu a filin jirgi wurin rakiya.

Alhaji da kansa zai kaisu makaranta. Dubai su ka fara zuwa saboda karatun Kamal saura kwanaki a fara. Ya biya komai ya tabbatar ya yi settling sannan su ka wuce India. Ahmad ya taho Mumbai ya tarbesu su ka rankaya Hyderabad tare. Gari daban za su zauna da Taj amma haka ya zauna da shi aka gama komai. Bayan sun raka Alhaji filin jirgi ya sake bin Taj har hostel ɗin makarantarsu, Osmania University ya tabbatar babu matsala sannan ya wuce makaranta.

*

Washegari Taj ya fita ganin gari. Karatunsu sai nan da kwana goma masu zuwa. Yana cikin yawo ya ci karo da wani katafaren ginin gidan abinci na alfarma. Mutanen dake shige da fice a wajen ba za su ƙirgu ba. Murmushin takaici ya yi. Ina ma iyayensa sun bashi goyon baya. Da watarana idan Allah Ya albarkaci nemansa zai iya mallakar wuri irin wannan.

Baya tare da yunwa amma yana son ganin wurin. Musamman kitchen da masu girki. Wurin shiga ya lura layi ake bi. Gashi ginin hawa biyar ne amma ko ina ka kalla tunda zagaye yake da gilas kana hango cikowar mutane. Da kansa ya haƙura da shigar ya kama zagayen ƙayataccen ginin yana mai son ganin iya faɗinsa. Ƙamshin girki mai tada kwantacciyar yunwa gami da muryoyi da ƙarar kayan kitchen yaji yana cikin tafiya. Da sauri kuwa ya manna goshinsa da gilas ɗin wajen yana ganin yadda ake kai kawo a wani makeken kitchen cikin tsari duk a ƙoƙarin ciyar da kwastomomi. Zuciyarsa a take ta soma harbawa. Yaji saukar nishaɗi da farinciki a ransa. Bai san minti nawa ya kwasa yana bawa idonsa abinci ba sai da yaji an taɓa kafaɗarsa an yi magana da yaren punjabi, guda cikin yarukan ƙasar.

Da sauri ya juya yaga wani ɗan dattijo sanye da t-shirt da wando ya ɗaure ƙugunsa da apron mai tambari da sunan gidan abincin. Kansa wata irin hula ce kamar ta wanka amma ita mai laushi ce. Ana amfani da ita domin hana zubar gashi cikin abinci. A shekaru a ƙiyasin idonsa zai yi sa’an Alhajinsa.

Daburcewa Taj ya yi ya matsa baya a tsorace yana cewa “I’m sorry. Sorry. Sorry.”

Hanyar komawa yake nema don tsoronsa ɗaya kada mutumin ya haɗa shi da security a ce me ya kawo shi nan.

Murmushi mutumin ya yi ya ce “hungry?” Don dama ita ce tambayar da ya yi masa da farko.

“Come inside” ya umarce shi da yaga yana neman guduwa.

“Am sorry Sir. Please. I won’t come again.” Ya ce zuciyarsa na faman lugude a ƙirjinsa.

Ko sauraronsa mutumin bai yi ba ya riƙe hannun ƙofar da ya biyo ya fito zai koma. Buɗewarsa ke da wuya wani jibgegen mutumi ya tare ƙofar ya yi magana da yarensu yana kallonsa.

Dattijon sai ya amsa da turanci yana yiwa Taj kallon in kuma ka musa babu ruwana. Nunawa ya yi ciki za su shigo da shi sannan ba laifi ya yi masa ba.

Ƙuttt ya haɗiyi yawu sannan kamar mai taka iska ya bi su ciki. Ƙofar na rufewa gabansa ya sake faɗuwa. Sai dai duk wannan tsoron ya kau lokaci guda da ya ƙarewa kitchen ɗin kallo na kurkusa. Aiki kowa yake yi da sauri-sauri ga magana ana yi wadda ya fahimci karanto odar masu jiran abince ce ko bada umarni. A gefe guda kana iya ganin wasu suna ta jere plates ɗin da aka gama haɗawa a wani abin turawa za a fita da shi. Ga masu girki sun duƙufa suna yi. Wuta da mai da cokula sai chuu…chauuu su ke. Ganinsa ya ƙare akan masu yanke yanke kamar inji. Wasu su na yanka albasa, caras, da ma nau’ikan kayan lambun da bai taɓa gani ba. Wani haɗaɗɗen murmushi ya saki sai ga ƙaton mutumin ya dawo da tray shaƙare da kwanukan abinci.

“Eat.”

Mutumin tsoro yake bashi amma duk da haka ya faɗa masa gaskiya “Am not hungry.”

“Taste our food and we talk, okay?”

Juyawa ya yi yaga dattijon farko ne ya yi magana. Musu ma wuri yake samu. Karɓar tray ɗin ya yi babu shiri ya zauna a inda aka nuna masa. Ƙamshin abincin ya tafi da tunaninsa. Shinkafa ce da kaza. Ga kuma wani haɗin albasa, cucumber da tumatir da wani ganye mai tsami tsami da daɗi kamar kunne zai fita. Wani ɗan kwano mai zurfi a gefe kuma miyar naman sa ne wanda ya dahu ya yi luguf. Sai wani abu kamar bread ko gurasa mai faɗi. Abu ɗaya ya kula shi ne babu cokali. Ya ɗaga kai ya tambaya dattijon nan shi kuwa ya ce masa.

“We eat with our hands here.”

Taj ya gyaɗa kai ya miƙe yace zai wanke hannu. Sink ya nuna masa ya wanko ya dawo. Yana zama ya yi Bismillah ya fara ci. Miyar ya ɗauka zai zuba a shinkafar da wani ɓangaren nata ya yi jaja-jaja, wani fari-fari, wani kuma yellow. Mutumin ya nuna masa ai gurasar nan ake ci da miyar. Shinkafar kuma ya zuba salad ya dinga haɗawa da nama. Ya tambayi sunan abincin aka ce masa chicken biryani ce da kuma chappati da beef curry (miyar).

Tunda ya saka hannu bai cire ba sai da abincin ya rage ɗan kaɗan. Yana ture plate kawai yaji mutanen kitchen ɗin suna ihu harda masu rungume juna. Ashe duk sun ankara da tsayuwarsa tun farko. Shi ne ogansu mai wurin ya shigo da shi. Farincikin fuskarsa a matsayinsa na wanda su ke da yaƙinin ranar ya fara cin abincinsu ne yasa su murna.

Sai da kowa ya nutsu aka cigaba da aiki sannan mutumin ya tambaye shi sunansa da dalilinsa na leƙensu.

“Kenan kana son girki” ya tambaye shi da turanci bayan ya yi masa bayani a taƙaice.

“Sosai.”

“Ka taɓa yin makarantar girki ko ka koya daga wani professional?”

“A’a.”

“Muna da makarantu a nan inda za ka iya yin degree.”

Taj ya yi murmushi da ya hango fuskar Alhaji idan ya je gida da kwalin degree a fannin girke girke. Sanar dashi ya yi cewa karatu zai fara kuma banu damar canjawa.

“Idan ka tabbata kana da ra’ayi ni zan iya koya maka a nan. Ka je ka duba tsarin karatunka. Ranakun da baka da aji ka zo nan kayi aiki.”

Baki ya buɗe da tsananin mamaki.

“Aiki?”

“Baka so ne?”

Da sauri ya ce yana so. Ya dai yi mamakin samu ne kafin ya nema.

Ƙaton mutumin nan ya sakar masa fuska ya ce.

“Dukkaninmu a haka yake ɗaukar mu aiki. Ra’ayin yi kawai zai gani daga gareka sai ya ɗauke ka yaronsa. Wurin nan nasa ne. Idan ka bada himma tabbas za ka ji daɗi. In kuma yaga baka da ƙwazo a wata ɗayan farko zai sallame ka.”

Kamar wasa daga wannan rana Taj ya fara karatu kuma yana zuwa koyon aiki a ROYAL CUISINE. Abin farinciki shi ne kasancewar dattijon da ake kira Paaji (ɗan uwa ko yaya) musulmi. Yawancin ma’aikansa musulmai sun fi yawa ma. Komai na wurin halal ne. Sai da ya yi wata guda cur babu abin da ake koya masa a kwana ukun da yake zuwa duk sati sai sanin sunaye da amfanin kayayyakin abinci da kayan ƙamshi (spices). Hancinsa ya aikatu don ko abu na kama da ɗan uwansa idan bai tantance ba maimaici za ayi ta yi. Wasu abubuwan kuma a ido su na kama amma a zahiri ɗaya nada amfani ɗayan kuma guba ne. Dole suma sai ya gane bambancinsu don kada a bashi a kasuwa ya cutar da masu sayen abinci.

Bayan nasararsa a wannin fanin kuma aka koma koyon ɓare tafarnuwa da yankanta ƙanana. Kan kace meye wannan hannunsa ya cika da plaster. Irin wannan yankan na mugun sauri ake so ya iya. Da ƙwararre a wurin aka haɗa shi. Daga nan aka koma albasa. A haka, a haka ya ƙware a yankan kayan lambu da kayan marmari. Yankan nama ma zaman kansa yake. Sai da ya koyi haɗa mince meat ko babu na’ura da wuƙa kawai da ƴar muciya. Shekara guda ko mai ba a taɓa bari ya soya ba sai da ya zama zakara a fannin ƙananan ayyukan da su ne ƙashin bayan kowane girki.

Bayan an dawo hutu wanda yaje gida ya yi da kyakkyawan sakamakon ƙarshen shekara ta farko aka kai shi gaban wuta. Zo ka ga farincikinsa da na abokan aikin. Mutane ne ƴan asalin garin Punjab masoyan duk wani abu na farincikin al’umma. Su dai ayi nishaɗi a zauna lafiya. Shi yasa Taj ya saje cikinsu. Happy Taj su ke kiransa tun ranar da ya yi skype da Kamal su ka ji yana kiransa Happy. Da yake anfi samun ƴan ƙabilarsu mabiya addinin musulunci a Pakistan, shi yasa Paaji duk inda ya sami ƴan uwansa musulmi yake basu aiki. Taj da wani Uygur Chinese (wata ƙabilar musulmai a China) Aynur kaɗai ne baƙi.

A cikin shekara ukun farko Taj ya ƙware a girke girke da dama na yankin Asia. Banda na Indiyawa an koya musu na Larabawa da duk wani yankin Asia da su ka yi fice ta fannin abinci. Duk kuma wannan badaƙala ko sau ɗaya Ahmad bai taɓa sani ba har ya gama ya koma gida. Taj ya ci karensa babu babbaka ya haɗa riba uku a zaman nasa. Bai manta da ƙudurinsu na bitar hadda ba shi da Kamal shi yasa ya shiga wata makarantar ƙarshen mako da ake yi a masallaci. Kamal ne kaɗai ya san me yake ciki kuma ya bashi goyon baya tare da nanata masa mahimmanci barin abin a matsayin sirri.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Taj da Kamal sun ƙarƙare karatunsu a cikin shekara uku da ƴan watanni. Kowanne akwai taron convocation da za ayi a makarantarsu. Kamar yadda aka fara kai Kamal, ranar nasu taron ta zo sati uku kafin na su Taj. Alhaji sai ya ɗauki Hajiya da Umma su ka tafi Dubai. Satinsu biyu a can su ka koma gida tare da Kamal ɗin. Bayan kwana huɗu ya juya da Ahmad, Mama da Inna zuwa India.

*

Gagarumar gasar girki ce Culinary Academy of India ta saka domin samun zakarun da za ta bawa tallafin yin karatun degree na tsahon shekara uku a fannin Catering Technology and Culinary Arts. Makarantar reshe ce ta Jami’ar da ya kammala wato Osmania University. Kuma ɗalibanta ta buɗewa gasar masu ra’ayin girki waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba. Paaji na samun labari ya saka shi a gaba a gaban kwamfutar restaurant ɗin nasu ya cike komai online. Abokan aikinsu su ka yi ta murna domin da fari har ya soma yi musu sallamar komawa gida da zarar an yi convocation.

A kwana biyar za ayi komai a gama. Taj bai san da tahowar su Alhaji ba kamar yadda Kamal bai san ya shiga gasa ba. So ya yi ya yi surprising ɗan uwan nasa. Wanda kuma da ya faɗa masa zai gargaɗe shi da tahowar tasu. Duk wayarsu da gida ana ta ɓoye masa don an san ba ƙaramin farinciki zai yi ba idan su ka zo. Tahowar Ahmad kawai ya sani saboda zai zo registration na masters tunda ya gama bautar ƙasa.

Sun iso ƙasar awa guda kafin a shiga gasar a rana ta huɗu wadda ta kasance alhamis. Zuwa yanzu team ɗin Taj da aka haɗa da wani banufe ɗan Nigeria mai suna Wakili su ne su ke jan ragamar muƙami na biyu. Wasu wa da ƙani ƴan Indonesia kuma a sahun farko. Wayarsa Ahmad ya kira ya faɗa masa sunan hotel ɗin da su ka sauka.

“Yaya ka daure ka ƙaraso Uma Nagar cikin Culinary Academy.” Ya ce da farincikin isowar ɗan uwansa.

Don dai yau ɗaya yana ganin ba komai bane idan an sani. A tunaninsa nasararsa ta karatun da Alhaji yake so za ta sa ya bashi damar cika nasa burin.

“Me ake yi?”

“Gasar girki na shiga.”

Gefe Ahmad ya matsa hankali a tashe.

“Ashe ba ka da hankali Taj? Tun yaushe Alhaji ya soke maganar nan?”

Da yanayi na ban tausayi Taj ya ce “Yaya ina so wallahi. Domin neman amincewarsa na dage sosai a makaranta. Kana ganin yanzu ba zai sauko ba tunda nayi karatun da yake so?”

“Baka da hankali.” Ahmad ya sake faɗi yana jin zufa na karyo masa.

Duk abin da yake yi hankalin Alhaji dake magana da su Inna yana gare shi. Sauke wayar daga kunnuwansa ke da wuya yaji ya ce masa,

“Me ku ke ɓoyewa da har za ka tashi ka dawo nan?”

“Babu komai Alhaji. Ya ce min baya hostel ne.”

Rashin gaskiya ya gani ƙarara a fuskar ɗan nasa shi yasa ya ce,
“Kai ni inda yake!”

RAYUWA DA GIƁI 5

Batul Mamman💖

“Alhaji…”

“Zan saɓa maka.”

Ba yadda ya iya. Cikin minti shabiyar ya sama musu tasi su huɗu suka kama hanya. Mama da Inna ba su san me ake ciki ba. Shi kuwa Alhaji tunda yaga sunan makarantar a bakin gate jikinsa ya soma tsuma. Ahmad dai jikinsa duk ya mutu. Ya yi kiran Taj ɗin da su ka shiga bai ɗauka ba. Da tambaya su ka ƙarasa wurin da ake gasar inda mutane su ka yi dafifi kamar ƙudaje. Basu wani sha wahala ba su ka hango tebura huɗu na ƙasashen da su ka rage a gasar. A yau za a fitar da wani team ɗin sai ya rage uku. Washegari idan an yi na ƙarshe a fitar da na ɗaya, na biyu da na uku.

Cikin wata irin nutsuwa da tsantsar ƙwarewa Taj yake aiki. Shi da Wakili girkinsu cikin tsari yake kamar sun manta da lokacinsu na tafiya. Wannan nutsuwar ita tafi burge alƙalan gasar. Masu sauri saurin cimma lokaci kuwa daga kwano ya faɗi ya fashe sai ka ji su na washhh, mai ko ruwa mai zafi ya fallatso mu su saboda garaje.

Tunda Alhaji ya yi tozali da ɗan nasa wani abu mai masifar ɗaci ya sami wurin zama a maƙogaronsa. Taj yake gani sanyi da dogon wando baƙi da riga yellow mai tambarin makarantar sai apron fari tas ɗaure a ƙugunsa. APRON!?

Inna kuwa tamkar wadda aka watsawa ruwan zafi. Tunda ta nunawa Mama shi bata sake iya cewa komai ba. Maman ce ma ta iya yin magana da ƙyar.

“Ahmad me idona yake gani?”

“Gasar girki ce” ya bata amsa a sanyaye.

“Ku zo mu koma.” Alhaji ya ce da matansa “Kai kuma ka jira ya gama ka taho min da shi.”

Ahmad ya so raka su amma ya nuna masa yawo a ƙasar da ba tasu ba, ba baƙon abu bane gare shi. Haka su ka tafi babu mai cewa komai. Da isarsu Alhaji ya ɗauko magungunansa na hawan jini ya watsa sannan ya ce kada wanda ya tashe shi sai Taj ya iso. Dama ɗaki uku ya kama musu. Sai su ka koma ɗayan.

Ido cike da ƙwalla Inna ta ce “Yaron nan so yake ya jaza mana tashin hankali ko me?”

Kallonta Mama tayi ta girgiza kai.

“Matsi da takura yaro bai fiye haifar da ɗa mai ido ba. Taj ya yi masa biyayya an sami abin da ake so. Mene ne aibu don ya ɗan waiwayi burinsa? Don fa mun haife su ba yana nufin dole su rayu kwatankwacin tamu rayuwar ko ra’ayi ba.”

“Kayya dai Mama. Rayuwar yara sai da nuna hanya daga iyaye.”

“Nima ban musa ba. Amma babu inda addini ya bawa iyaye damar tauye ƴaƴansu akan abin da bai saɓawa addinin ba. Baki ji malamai suna faɗin ko sakin aure indai ba bisa adalci ba, iyaye basu da hurumin tilasta shi ba? Girkin nan kuma maza nawa ke yi? Mene ne aibu a ciki tunda ba daudu yake ba?”

Inna dai duk a tsorace take ta ce “tunda mahaifinsa ba ya so sai ya haƙura ko don neman albarka.”

Mama gani tayi cigaba da nunawa Inna illar takura tayi yawa ga ɗa mai biyayya bata da amfani ba sai taga Innar ta kasa fahimta. Idan ta matsa kada abin ya yi kama da tana son sanya shi yin bore. Zaman jiran tsammani su ka yi har bayan Isha.

*
Sakamakon gasa yau dai da su Taj ya tashi. Cikin nasara da taimakon Allah su ne su ka yi na ɗaya. Yawan makinsu idan an haɗa da na kwanakin baya ya basu damar iya yin na ɗaya gobe in sun dage. Banda ihun murnar ƴan Nigeria da su ke makarantar ba ka jin komai. Yanzu ya rage teams uku. Gobe za a fitar da na ɗaya, biyu da uku. Da su ka fito za su tafi Wakili ya tare shi da godiya.

“Ban san a ina ka koyi girki wanda yasa talent ɗinka ya zarce na kowa a nan ba. Your are truly amazing.”

Taj ya yi murmushi “ai ban kai ka ba.”

“Magana ta gaskiya ake yi. Idan muka yi nasara na san albarkacinka na ci. Saboda haka ina roƙonka don Allah gobe ka dage fiye da kullum. Samun karatun ya fiye min akan kuɗin da za a bawa na biyu ko na uku.”

Murmushi Taj ya sake yi da alƙawarin in sha Allahu gobe zai yi bakin ƙoƙarinsa.

Da tallafin gwamnati Wakili ya sami tahowa karatu. Ya gama degree kamar Taj amma yana tsoron komawa gida yanzu. A ƙauye su ke. Gashi samun aiki yanzu ya koma wa ka sani, wa ya san ka. Tunda yana aiki a wani gidan abinci a nan yana samun abin turawa mamansa da ƙanne ba zai so ƙarewar visa yasa shi komawa gida a sake naɗe hannuwa ba.

*

Murnarsa ta koma ciki da Ahmad ya faɗa masa tare da su Alhaji su ka zo akan hanyarsu ta zuwa hotel ɗin.

“Yaya don Allah kada ka sanar dashi zancen competition ɗin nan.”

Cije leɓe Ahmad ya yi wanda yasa Taj tambayarsa ko ya faɗa hankali a tashe.

“Tare mu ka shiga inda ku ke girkin. Ya riga ya gan ka.”

Bayan karanto duk wata addu’a da ya sani ta neman sauƙi, bai sake cewa komai ba har su ka isa hotel ɗin. Kai tsaye ɗakin Alhaji su ka je su ka tarar da Inna da Mama a zaune jigum. Jikin Alhaji har ya soma tsananta saboda damuwar da ya sanya a ransa.

Wuri ya samu kusa da Mama ya zauna jikinsa a matuƙar sanyaye. Shiru yana jira a fara yi masa faɗa amma babu wanda ya yi magana. Cike da fargaba ya rarrafa gaban Alhaji kai a ƙasa.

“Don Allah…”

Tassss. Alhaji ya tsinke shi da marin da ya gigita shi. Inna tsam ta miƙe ta fice daga ɗakin don ba za ta juri gani ba. Ko da ta koma ɗaya ɗakin fashewa tayi da kukan da bata san na mene ne ba. Tana tausayin ɗanta. Tana kuma son ya sami damar cikar buri sannan kuma tana so ya yiwa mahaifinsa biyayya.

Sake ɗaga hannu Alhaji ya yi zai kuma marinsa cikin zafin nama Mama ta riƙe hannun da sauri.

“Ka dubi Girman Allah kayi haƙuri.”

“Ki sakar min hannu” ya miƙe tsaye da fushin da yafi na farko yana mai fincike hannunsa.

“Haba Alhaji. Mene ne aibun girki a wurin namiji da har za ka kasa bawa yaron nan damar cikar burinsa.”

“Buri? Buri fa ki ka ce A’i?” Ya nuna ƙirjinsa “ɗan cikina ki ke so na bari ya yi daudu?”

A hasale ta bashi amsa saboda har ga Allah tana ganin da gangan kawai yaƙi fahimta balle ya sassautawa ɗan.

“Mece ce alaƙar girki da daudanci? Maza nawa ka gani da wannan sana’ar kuma ba su lalace ba? Ka kyautata masa zato mana ka bi shi da addu’a.”

“Ni ki ke ɗagawa murya?”

Ko ɗar bata ji ba ta ce “Gorin haihuwar namijin za ka sake yi min?”

Ahmad ya fice kiran Inna. Taj kuma jin yadda rigima take son tasowa tuni ya dawo daga duniyar raɗaɗin marin da aka yi masa.

“Mama bashi haƙuri mu fita.” Ya durƙusa a ƙasa “in sha Allahu nima ba zan sake tada maganar nan ba.”

Hannun Mama ya ja su ka haɗu da Inna tana dawowa ɗakin da jan ido. Ganin sun fito ita ma ta bi bayansu ita da Ahmad.

Kamar wancan lokacin yanzu ma nasiha game da mahimmancin yiwa iyaye biyayya su ka yi masa. Ya kuma karɓa hannu bibbiyu da zuciya ɗaya.

Ƙarfe goma da rabi na dare saƙon Wakili ya shigo wayarsa. Tuni akan fitowa da wuri ya soma yi masa. A ƙarshe kuma ya yi rubutu kamar haka.

“…My mum said we should keep reciting this Du’a tonight being friday night and tomorrow when the competition begins. RABBI INNI LIMA ANZALTA ILAYYA MIN KHAIRIN FAQIR. I will continue to thank Allah for bringing you my way no matter the outcome. Working with a pro like you is truly an honour. Thank you Happy Taj.”

Duk iya sata ta bacci daidai da sakan guda Taj bai runtsa ba. Shaf ya manta ba shi kaɗai bane a gasar har ya yiwa su Inna alƙawarin haƙura. Gashi daga cikin dokokin gasar duk wanda abokin girkinsa bai zo ba har aka fara da minti goma sha biyar sun zama disqualified. Anya zai iya samun kwanciyar hankali idan ya zama sanadiyar rugujewar rayuwar wani?

Kafin asuba babu irin tunanin mafitar da bai yi ba. Yana idar da sallah ya fice daga hostel zuwa hotel ɗin su Alhaji. Bai tsaya neman abin hawa ba saboda ƙarancinsu a wannan lokacin. Sannan babu wata tazarar azo a gani ma. Da gudu gudu ya isa yana faman haki. Kai tsaye ɗakin Ahmad ya fara zuwa. Da ba a buɗe ba ya durƙusa a bakin ƙofar yana mayar da numfashi.

Zaman kimanin minti shabiyar ya yi sannan Ahmad ya dawo.

“Lafiya me ya fito da kai da asussuba haka?”

“Alhaji yana ɗakinsa? Ya tashi?” Taj ya tashi ya ma manta da gajiyar jikinsa.

Yanayinsa na rashin nutsuwa Ahmad ya fara dubawa kafin ya shige masa gaba zuwa ɗakin Alhajin. Shi kaɗai ne a ɗakin don matan nasa sun yi yaji saboda abin da ya faru jiya. Sanye yake da farar jallabiya yana fitar da daddaɗan ƙamshin turaren larabawa. Gemunsa mai sirkin fari-fari da baƙi ya ƙarawa fuskarsa kwarjini. Kamanninsa da samarin ƴaƴan nasa ta sake bayyana.

Gaishe shi Taj ya yi ya faɗi buƙatarsa kai tsaye. Ahmad na ji ya fita da sauri ya kira su Inna don su dakatar dashi kafin maganar ta lalace. Sun shigo daidai lokacin da Taj yake cewa,

“Ba don kaina nake son zuwa ba. Nayi maka alƙawarin ko na nawa mu ka yi ba zan karɓi komai daga gare su ba. Izini kawai nake nema kada rashin zuwana ya zama silar rushewar ….”

“Tajuddin!”

Durƙusawa ya yi duk da kiran sunan nasa ya kiɗima shi cikin ƙanƙan da kai ya shiga magiya kafin ma ya ji me Alhajin zai ce. Wannan ya ƙara tunzura mahaifin nasa sosai.

“Indai ni zan yi maka izini to ka sani har abada ba zan taɓa yarje maka ka sake tsayuwa gaban murhu ba. Allah Ya yi min rufin asirin da ko mata cikin tsatsona ba za su nemi kuɗi da girkawa wasu abinci ba balle kuma namiji.”

Ƙwalla mai zafi ta shiga saukowa Taj a yayinda yake jin kamar da gayya mahaifin nasa yake tauye shi. To amma ko zai hana saboda baya son a haɗa ɗan cikinsa da sana’ar girki me yasa ba zai duba cewa rashin zuwansa zai salwantar da mafarkin cigaban ɗan marayan da bashi da gata ba.

“Alhaji ka yiwa Allah…”

“Na gama magana” Ya furta da izza sannan ya fuskanci Ahmad “ka canja mana booking idan akwai jirgi mu tafi yau da ƙanin naka. Takardunsa kuma ka tsaya ka karɓar masa.”

Hankalin Taj tashi ya yi ya miƙe da sauri “Alhaji na rantse maka ba don ni zani ba. Idan ban je ba za ayi disqualifying ɗinsa.”

“Wannan nauyin sai ya zame maka darasin rayuwa a gaba ta yadda ba za ka sake marmarin saɓawa umarni na ba.”

Inna da Mama har ma da Ahmad saka baki su ka yi wajen lallashin Alhaji akan ya amince amma ya yi biris da su. Taj kuwa kuka yake tamkar yaron goye. A wannan yanayin wayar Wakili ta shigo masa. Alhaji da kansa ya ce ya ɗauka kuma ya faɗa masa ba zai je ba.

“Happy Taj yi haƙuri na kira ka da sassafe.” Ya yi magana da ɗan jin nauyi.

“Kada ka damu na riga na tashi.”

Wakili ya yi ƴar dariya “jiya wanda mu ka gaisa ka ce yayanka ne ko?”

“Eh.” Ya amsa da sanyin murya.

“Breakfast na haɗa masa nake neman address ɗin ka. Na rasa da me zan karramaka. Ko a wannan matsayin mu ka tsaya kai ne sila. Zan so yin aiki tare da kai nan gaba.” Ya sake dariya “kana burgeni ne. Ina son koyon girki kamar kai.”

Kasa cewa komai Taj ya yi sai ruwan hawayensa da ya ƙaru. Daurewa ya yi ya ce da Wakili zai tura masa address ɗin yanzu. Bayan ya ajiye wayar ya dubi Alhaji da ya gama jin komai.

“Ka gani ko Alhaji? Yana da kirki kuma maraya ne. Cutar shi zan yi idan ban je ba.”

Gajiya Alhaji ya yi da magiyar dukkaninsu ya ɗaga murya ya ce ce “Ku fitar min daga ɗaki gabaɗayanku.”

Iko da izzarsa ba tun yau su ke damun Mama ba. Amma wannan ya fi ɓata mata rai. Wace irin zuciya ce da shi da za a dinga roƙonsa akan tallafawa rayuwar wani ya turje a kai. Sannan da girmansu ya haɗa su da ƴaƴan cikinsu ya yi musu kora irin wannan ta ƙasƙanci. Ta dubi hawayen Inna wanda ko ba a faɗa ba ta san na son share damuwar ɗanta ne. Bata cewa kowa uffan ba ta fita ta koma ɗaki inda ta baro wayarta. Kimanin minti goma ta ɗauka wurin yiwa mijin yayarta wanda ya kasance babban wa ga Alhaji ta fayyace masa komai.

“Zan kira shi yanzu. Kashe wayar.” Kawai ya ce bayan ya gama jin bayaninta.

Da ta koma ɗakin yadda ta fita ta barshi haka ta same shi. Saboda halin da Alhaji ya sanya jama’ar ciki hatta iskar ɗakin bata daɗi. Shigarta ke da wuya Alh. Jafaru ya kira shi kamar yadda ya yi mata alƙawari.

“Hayatu.”

“Na’am” ya amsa da ladabi domin ya yarda da aka ce babban wa uba, musamman wanda ya riƙe matsayin da gaskiya da amana irin yayansu.

“Ni Jafaru na bawa Tajuddin izinin fita yaje ya ƙarasa abin da ya fara. Sannan ina mai umartarka da ka zauna har a sallame su daga makaranta ku taho tare.”

“Yaya Babba?”

“Idan ban isa ba kana iya take umarnina ka ɗora naka.”

Bai bashi damar sake cewa komai ba ya kashe wayarsa. Alhaji ya kalli Mama da wani irin ɓacin rai mara misali. Sanin bata da gaskiya sai ta sadda kanta ƙasa kawai.

“Tashi kaje wurin gasar.”

Iya abin da ya ce kenan ya fice daga ɗakin ya barsu. Taj bai ma gane dashi ake ba sai da Mama tayi masa magana. Ya kalli agogo yaga takwas saura mintuna ƙalilan. Gashi da ƴar tafiya zuwa makarantar. Tunanin wanka ko kusa bai zo masa ba ya fita da gudu-gudu ya sauka neman abin hawa. Ya isa tara saura minti bakwai. Har an gama shirya komai sauran teams biyun sun tsaya suna jiran lokaci. Wakili kuwa shi kaɗai ne a can gefe yana ta baza idanu cikin tashin hankali.

Taj na shiga wurin aka kaure da ihu da tafi. Ashe ba Wakili kaɗai ke jiransa ba. Masu mara musu baya da dama sun shiga fargabar makomarsu da aka ga bai zo ba. Tara daidai aka buga wata ƙatuwar ganga wadda ta bawa participants ɗin damar farawa.

RAYUWA DA GIƁI 6

Batul Mamman💖

*

Kyakkyawan envelop Yaya Babba ya miƙawa Alhaji ya kuma bishi da kallo a tsanake don son karantar yanayinsa. Kamar yadda ya yi tsammani duk wani annuri da walwalar da yake tare da ita a farkon zamansu tsaf ya kau. Duhun da yake zuciyarsa ya sami damar nuna kansa a fuskar. Disappointment ɗinsa akan Taj ya kashe masa jiki da zai yi magana.

“Kawo maka ya yi?” Da Yaya Babba ya gyaɗa kai sai ya ce “to me yake so?”

Kallon tausayi Yaya Babba ya yi masa. Mutum mai kafiya irin ƙaninsa yana da wuyar sha’ani. Wani zubin ya tabbatar yana sanin cewa ba a kan gaskiya yake ba amma don kada ya sauya baki sai ya cigaba da riƙo da hujjojinsa masu rauni. Sai dai a yau ya ƙudiri niyar amfani da girmansa karo na biyu ya tanƙwara ƙanin yadda yake so.

A nutse yadda zai fahimta ya labarta masa zuwan Taj gidansa kwanaki uku da su ka wuce. A lokacin sun kusa wata biyu da dawowa daga India. Sakamakon gasar girkin nan ne Wakili ya taho masa da certificate ɗinsa na ɗaukar na ɗaya. Sannan ga admission letter kamar yadda aka yi alƙawari. Shi ne ya kai masa ya gani amma ya roƙe akan kada ya sanar da kowa domin ko iyayensa mata bai nuna musu ba. Ya kawo ne saboda ya nuna masa godiya akan shige masa gaba da ya yi har ya sami damar ƙarasawa. Sai kuma Wakili da ya nuna son zuwa ya gaishe da iyayensa kafin ya wuce Minna. Shi ne ya kai masa shi inda aka yi masa tarba mai kyau. Da yaji daɗi har mahaifiyarsa sai da ya haɗa da Yaya Babba su ka gaisa.

Alhaji ya gama jin zancen da bai gamshe shi ba ko kusa ya ce “mece ce manufar nuna min tunda ya ce baya son na sani?”

Yaya Babba dakewa ya yi babu alamun wasa ya ce “ina son ka sanya masa albarka ne domin idan Allah Ya kaimu lokacin fara karatun ni zan mayar dashi da kaina.”

“Kada mu yi haka da kai Yaya.”

Alhaji ya furta da ƙaramar murya yana jin wani irin yammm a sassan jikinsa. Yana matuƙar ƙaunar Taj sannan burinsa a duniya yaron ya gaje shi. Idan hakan bai samu ba ya yi zarra a duk sana’a ko aikin da ya nema amma banda GIRKI. Yadda rayuwar Habibu ta sauya salo a kan idanunsa ba zai taɓa lamuncewa ɗansa ya faɗa wannan hanyar ba. Shi fa ko duk jikinsa kunnuwa ne ba zai yarda girki ba wani nau’i bane na daudanci.

“Idan Allah Ya bamu yara masu biyayya, amfani da ƙarfin iko wurin hanasu farinciki ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba Hayatu.”

“Haka ne.”

“Ka amince?” Yaya Babba ya tambaye shi yana murmushi.

“Ai ka ishe shi uba Yaya Babba. Ba za ka taɓa faɗin magana na musanta maka ba in sha Allahu.”

Da zuciya ɗaya Yaya Babba ya miƙa masa hannu su ka yi musabaha cike da farinciki. Bai san cewa magana ce mai harshen damu Alhaji ya yi masa ba.

“Allah Ya ja kwana baban Tajuddin. Nagode da karamcin nan da kayi min. Da yardar Allah sai mun yi alfahari da zaɓinsa.”

“Uhmm” kawai Alhaji ya iya cewa don bakinsa ya bushe kamar an shanya a rana. Samu ya yi ya bar gidan kamar babu abin da ya riƙe a ransa.

Bayan fitarsa Yaya Babba ya kira Mummy (Ɗaharatu) matarsa kuma yaya ga Mama ya sanar da ita anyi nasara. Ta kama murna tana cewa hakan shi ne daidai.

“A neman haram ake yin fito na fito da burin ƴaƴa. Yadda Taj ya rame ya sanya abu a ransa ko ya zauna ba daɗinsa za su ji ba. Allah Yasa matakin nasara da samuwar alkhairi mu ka ƙulla.”

“Amin” Yaya Babba ya faɗi yana gyara zaman gilashinsa.

Duk cikin zuri’arsu shi da wata ƙanwarsu Jamila ne ake yiwa laƙabi da ƴan boko. Matarsa ɗaya da yara biyar waɗanda huɗu sun yi aure saura namiji ɗaya. Mutum ne da ya yarda da displine ɗin yaron da ya kauce hanya amma sam bai yarda a tauye haƙƙinsu ba. Ita kuwa ƙanwar tasu da yara ke kira Amma likita ce. Sai da ta gama karatu tayi aure har ana ganin da gangan taƙi yi tun farko. Mijin mazaunin Amerika ne a can yake aiki. Bayan aurensu da ta bi shi ita ma ya sama mata take aikinta a wani asibiti. Yaransu biyu mata.

*

Ɗaki Alhaji ya kira Taj bayan ya koma gida. Ya yiwa ɗan nasa kallo na ka bani kunya sannan ya miƙa masa envelop ɗin. A take kuwa jikin Taj ya kama rawa.

“Ba da wata manufa na kai masa ba Alhaji.”

“Ka ji na ce wani abu ne?”

“A’a.”

“Madalla” ya gyara zama “Yaya Babba ya ce ka haɗa kayanka ka koma gidansa kafin lokacin fara karatun naku.”

“Wane karatun? Ba service zamu tafi ba?” Ya tambaya da faɗuwar gaba.

A ransa Alhaji gani yake rainin wayo ne kawai Taj yake son yi masa amma ya san komai. Ƙarshenta ma shi ya roƙi Yaya Babban da ya taimaka masa ya sami komawa makarantar.

“Idan ka dawo sai ka zo kayi service ɗin. Ina yi maka fatan samun nasara da alkhairi. Allah Ya yi maka albarka. Tashi ka tafi.”

Kansa sake ƙullewa ya yi amma babu halin tambaya. Sai ma ƙarin bayani da Alhajin ya yi masa cewa ya bari jibi zai kai shi da kansa don ya sami damar hađa kayansa.

“Ba na kuma son jin zancen nan a bakin kowa har matan gidan don na san za su so hanaka tafiya.”

“To Alhaji” ya amsa a ladabce.

Kamal kaɗai ya sanarwa abin da yake faruwa. Da taimakonsa ma ya gama haɗa kaya. Ranar da za su tafi Alhaji ya faɗa masa zai dawo daga kasuwa da azahar sai ya kai shi.

“Happy” Kamal ya kira Taj suna zaune a ɗaki “ba ka mamakin chanjin ra’ayinsa?”

“Ni fargaba ce ma tafi damuna. Naga ko kaɗan bai nuna fushi ba duk da Allah Ya sani ba da wannan manufar na kai wa Baba Yaya takardun ba.”

“In sha Allahu ma babu komai. Dama tsoron da naji da ka ce wai ya ce kada a faɗawa kowa.”

Bugun ƙofa gami da sallamar Bishir ce ta hana Taj sake yin magana. Saƙon Alhaji ne yana jiransa a mota.

A take yaji gabansa ya yanke ya faɗi. Ya tashi jiki a mace sai Kamal da Bishir ɗin ne su ka ɗauko masa kayansa. Kowa yaga ana loda kaya a booth ɗin Alhaji sai ya yi mamaki amma an rasa mai tambaya don babu fuska.

“Ka shiga ka yiwa uwayenka sallama.” Alhaji ya umarce shi da ya fito.

Inna bata gida. Sai su Hajiya. Su ka biyo shi waje kuwa su na tambayar Alhaji me ya faru Taj zai koma gidan Yaya Babba. Cewa ya yi su koma. Idan ya dawo zai yi musu bayani.

A mota haka su ka tafi ko numfashi mai sauti Taj baya iya ja. Kamar tare su ke don ana buɗe musu gate su ka ga Yaya Babba yana fitowa daga mota. Dawowarsa kenan daga office. Yayi mamakin ganin Alhaji kaɗai ko direba babu da Taj. Sai dai wannan ba komai bane a yayin da yaga ya buɗe booth Taj na sauke kaya.

“Hayatu me yake faruwa ne?” Ya matso kusa dasu don jiran su gama su shigo ciki ma ba zai iya ba.

Alhaji ya dubi ɗan uwansa yana mai baƙincikin yadda yayi masa katsalandan a cikin harkar gidansa. Shi kuwa Taj yana jin haka wani irin tsoro ya kama shi. Kenan Baba Yaya ba shi ya nemi ya dawo gidansa kamar yadda Alhaji ya faɗa masa ba.

“Ga Taj nan. Suna na ne kawai addini bai halatta min cire masa ba amma daga yau na bar maka shi.”

Yaya Babba ya girgiza da furucinsa matuƙa. Fuskar ƙanin nasa a haɗe take kamar baƙin hadari.

“Me ya yi zafi? Don na ce zan mayar dashi makarantar da yake so?”

“Ai ban hanaka ba tunda ka isa. Shi ma da na isa dashi ina mai umartarsa kada ya dawo min gida.”

“Hayatu bana son rashin hankali.” Yaya Babba ya fara faɗa.

“Ai kuwa bai kamata ka kira biyayyata gareka da rashin hankali ba.” Ya cigaba da magana kai tsaye babu tauna lafuzza don yau dole ya amayar da ɓacin ransa “saboda gudun shiga haƙƙi ban taɓa yiwa kowa iko da ɗansa ba. Amma sau biyu Yaya kana bawa yaron nan abin da nake son hanawa. Hakan ba komai zai janyo min ba illa baƙin jini daga gare shi. Koda yayi min biyayya zata zama bisa tursasawa ba don son rai ba. Maganin kar ayi, kar a soma. Tunda ka nuna masa za ka iya bashi abin da na hana sai ka riƙe shi na bar maka.”

“Ni kake faɗawa magana Hayatu? Ashe zumuncinmu bai kai nayi umarni ko hani ga tsatsonka ba tare da ka ɗaga kai ba?” Yaya Babba ya faɗi yana mai jin ciwon maganganun da kunnuwansa ke ji.

Musayar yawun da suke ba ƙaramin tadawa Taj hankali tayi ba. Ya durƙusa a ƙasa yana kuka yake roƙonsu da su yi haƙuri.

“Wallahi ba zan sake tada zancen nan ba har abada. Ku yafe min don Allah.”

“Baka isa ba! Karatu ko ba kyauta aka baka ba sai kayi shi. Tunda ka iya raina ƙoƙarina akanka ka haɗani da ɗan uwana dole ka cika burinka.”

Taj na kuka ya riƙe ƙafar mahaifinsa yana roƙon yafiyarsa. Yaya Babba ma idanunsa sun kaɗa sun yi ja. A haka ya ja girmansa don gudun rigima ya bashi haƙuri.

“Kayi haƙuri. Ban yi zurfin tunani ba, da ban shiga huruminka ba. Don Allah ka ɗauki ɗanka ku tafi.”

“Na gama magana. Wallahi daga yau Taj ya bar gidana…”

“Kada ka rantse.” Ya yi nufin dakatar dashi sai dai ya makara.

Suna ji suna gani Alhaji ya juya ya shige motarsa yayi gaba. Taj ya bi motar a rikice kafin ya sami wuri kusa da akwatinsa ya zauna cikin wani irin yanayi na rashin kuzari. Zuciyarsa wani irin ƙunci kawai ke yawo a cikinta. Bai san lokacin da aka kwashe kayansa ba. Sai hannuwa da yaji na ɗan uwansa, ƙaramin ɗan Yaya Babba wanda ya kasance sakonsa ya tayar dashi. Da ƙyar ya yarda ya shiga gidan. Mummy tana kuka tana bashi baki tare da alƙawarin gobe Yaya Babba zai mayar da shi.

*

A wannan rana ko gyangyaɗi Taj bai samu ba. Kuma haka ta kasance a ɓangaren Baba Yaya da Alhaji da Inna. Don bayan ta dawo gida da ya sanar dasu hukuncin da ya ɗauka har suma tayi. Gidan ya rikice da koke koke. Iyalin Alh. Hayatu su ka taru su ka juya masa baya daga matansa har ƴaƴansu. Hakan kuwa bai yi masa komai ba face ƙara tsanar turbar da Taj yake son bi. Da kuma abin da Yaya Babba yayi masa.

Washegari duka ƴaƴan Marigayi Alh. Sule su ka taru a gidansu dake Soron ɗinki inda mata guda ɗaya da ta rage musu a matsayin uwa take. Ita ce mata ta uku cikin matansa. Zama irin na da yasa ita da ƴaƴan sauran abokan zamanta su ka cigaba da zumunci tamkar lokacin da mahaifinsu yake da rai.

Ita Yaya Babba ya kaiwa ƙarar Alhaji tun a jiya. Tasa aka kira mata kowa dake kusa. Amma ma dake nesa dama ta iso kwana huɗu da su ka wuce hutun shekara. Tana Abuja da niyar tahowa bayan sati guda. Amma kiran Gwaggo yasa ta biyo jirgin ƙarfe tara na safe.

Bayan an zazzauna Yaya Babba ya mayar da iya abin da ya faru ta ɓangarensa. Tun daga wayar da Mama ta yiwa Mummy da suna India har zuwa yadda ta kasance jiya. Aka tambayi Alhaji sai kaɗa baki ya yi ya ce bashi da abin sake tofawa.

“Yanzu Hayatu har kayi girman da za ka nuna mana iko akan ƴaƴanka?” Yayarsa mace mai bin Yaya Babba wadda daga ita sai shi tayi maganar da ƙwalla a idonta “na zata za ka yi farinciki da zumuncin da muke dashi wanda mu ka ɗora ƴaƴanmu da jikoki. Kai ba abin alfaharinka bane ace ɗanka yaje neman sauƙi a wajen ɗan uwanka? Shi kuma bai bashi kunya ba ya share masa hawaye.”

Ransa sosuwa ya yi da har suke ganin laifinsa.
“A cikinku akwai wanda zai bar ɗansa namiji ya ɓata lokaci a jami’a yana koyon girki da yadda ake sarrafa kayan abinci?”

“Me zai hana tunda ba haramun bane” wani ƙaninsa ya amsa kai tsaye. Wasu duk su ka amsa da za su iya.

“Wallahi ƙarya kuke yi. Ni ban taɓa ganin namiji a arewa mai sana’ar abinci ba wanda baya abin mata.”

“Saboda al’adar bahaushe ta mayar dashi aikin mata kaɗai ba. Amma a kudu da sauran ƙasashen duniya maza nawa ne su ka yi fice da girki kuma in ba faɗa su ka yi ba sai ka rantse ma ƴan dambe ne.”

“Ni yanzu me kuke so daga gareni?”

Gwaggo ta dube shi. Haƙiƙa akwai ciwo wurin iyaye idan ƴaƴansu su ka ƙi bin umarninsu. Gashi mutum mai aƙida wanda baya son ko yaya aga gazawar nasa. Kuma dole yanzu yaga kamar an haɗe masa kai. Don ko ita idan zata yi rantsuwa ta san babu kaffara da matuƙar wahala in ka cire Yaya Babba da Amma a sami mai barin ɗansa namiji ya yi wannan karatun.

“Hayatu kaje gidan Jafaru ka ɗauko ɗanka maganar nan ta mutu daga yau.”

“Ai nayi rantsuwa Gwaggo. Akan Taj wallahi ba zan yi kaffara ba.”

Cikin fushi Yaya Babba yace “Nima kuma wallahi ba zan zama silar raba ɗa da iyayensa ba. Idan rashin albarka ya bishi a dalilinka duniya ni za ta zaga.”

Gwaggo dai gajiya tayi da basu baki ta kama hawaye tana cewa don babansu baya duniya shi yasa su ke yi mata haka.

Amma da bata ce uffan ba tun farkon zamansu ce ta katse musayar yawun da suke.

“Gwaggo ki zama shaida. A gaban kowa duk sun yi rantsuwa ba za su zauna da Taj ba. To ni ina so kuma dashi zan koma. Zan taƙaita hutuna mu baku wuri ku sha iska.”

Kallonta kowa ya kama yi kafin kuma mazan su nuna a gidansu zai zauna.

“Jamila zai bi domin babu amfanin ya zauna a nan kowa yana yi masa kallon wanda uba ya kora.” Gwaggo ta kashe maganar.

“Gwaggo ina so ki min shaidar ƙarshe. Yadda kowa baya son a shiga abin da ya shafe shi da đansa to nima kada wanda ya shigar min gonata. Zan yiwa Taj abin da zan yiwa ɗan cikina tsakani da Allah.”

Kafin kowa ya sake magana ta tashi ta fice daga gidan gabaɗaya.

Kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Da kaɗan da kaɗan zance ya zaga zuri’ar gidan kowa ya san me yake faruwa. Wasu na goyon bayan Taj wasu na ganin laifinsa. Inna da Mama sun fi kowa shiga tashin hankali. Sai Kamal da ya kwanta ciwo sosai. Alhaji kuwa tunda Amma tace za ta ɗauke shi ya san sai abin da Allah Yayi. Bai fasa ganin laifin Mama ba akan zama mutum ta farko wajen haɗa shi da ƴan uwansa da kuma raba shi da ɗansa. Irin abubuwan da ya dinga yi mata sai da ya kaita ga yin yaji. Tana ficewa kuwa Inna ma ta kama gabanta. Butulci ne zai sa ta cigaba da miƙe ƙafa a gidan da mai son ɗanta ta kasa zama. Hajiya da Umma da basu tafi ba ba daɗinsu Alhaji yake ji ba. Abu sai da ya kai anyi zama na musamman da dangin kowannensu. An sasanta dai amma tunda Taj ya bar gidan kaso mai yawa na walwalar gidan ya kau.

*

Tafiya Amerika yana buƙatar visa da dogon cike ciken takardu wanda Amma take ganin ɓacin lokaci ne. Saboda haka ta nemi visar India da passport ɗinta na ƴar ƙasa na Amerika. Nan da nan ta samu. Cikin sati biyu suka bar ƙasar. Dama Abuja ta koma dashi. Ita ta kai shi makaranta ta jira komai ya kammala bisa tsari. Zai cigaba da aikinsa a wurin Paaji a duk ranar da bashi da lecture kamar yadda ya yi lokacin degree ɗinsa na farko.

Da za ta tafi ta kawo kuɗi ta bashi.
“Kada ka kunyata ni. Kada kuma kayi abin da zai ƙara girmama rigimar Yaya Hayatu da Yaya Babba. Ka kiyayi duk wani abu da Allah baya so. Shi kuma ba zai bari ka taɓe ba.”

Rufe ido ya yi yana kuka. Ta dungure masa kai “meye haka? Da Yaya Hayatu zai ga wannan kukan ai cewa zai yi abin da yake gudu ya faru.”

Dariyar dole Taj ya yi. Ta rungume shi tana rarrashi. Duk da yaji bambarakwai amma sai hakan ya sanyaya masa zuciya.

“Bana son ragwanta. In shagwaɓa ce dai I will indulge you amma ragon namiji baya burgeni kaji ko?”

Murmushi yayi. A rayuwarsa zai iya ƙirga sau nawa ya haɗu da Amma. Ya san tana da kirki amma bai san halayenta irin waɗanda yake gani yanzu ba. Uwa da uba ya samu a dunkule a tare da ita. Ta ƙarfafa masa gwiwa sosai sannan ta faɗa masa zata yi ƙoƙari kafin lokacin hutu tayi duk abin da ya dace domin ya sami visa.

Wannan shi ne mafarin zaman Taj a Amerika. Ƴaƴan Amma sun yi aure. Su suna Minnesota babbar Anisa kuma tana aure a Florida. Iman kuma a Lagos take zaune da mijinta. Yayinda maigidan yake yawo tsakanin Nigeria wurin amaryar da ya yi bayan ya yi ritaya da Amerika.

Sai ya kasance bayan Taj ya gama karatu shi da ita ne a gidan kodayaushe. Sun shaƙu matuƙa. Tana aikinta shima yana yi awani restaurant da ya yi fice a abincin Asia da Afrika. A wurin ma’aikatan wurin ya koyo nau’ikan abincin gargajiya na Nigeria na ƙabilu daban daban. Cikin ɗan lokaci ya yi suna sosai. Takanas aka zo aka gayyace shi gasar da ta ciwo masa wasu maƙudan kuɗaɗe bayan ya sami nasarar yin na biyu. Da kuɗin da kuma tanadinsa tun na India yake son buɗe mall a Kano.

Rashin zuwansa gida bai hana shi mu’amala da ƴan uwansa da iyaye ba. Musamman yanzu da aka sami cigaban hanyoyin sadarwa. Suna yawan bidiyo call ana ganin juna musamman yayin aure da haihuwa. Alhaji ne kaɗai baya ɗaukar wayarsa har yanzu. Amma ta tilasta masa tura masa saƙon gaisuwa kullum rana ta Allah na kar ta kwana. Sai dai da yake zuciya bata da ƙashi, ya riƙe uban a zuciyarsa. Ya ɗora masa alhakin raba shi da ahalinsa. Da nesanta fuskarsa da ta mahaifiyarsa. Shi yasa ya ƙudurcewa ransa ba zai sake taka gidansu ba sai Alhaji ya neme shi da kansa.

*

Hutu ya ƙare lafiya. Ranar da ƴan makarantar kwana za su koma Hamdi bata samu ta runtsa ba. Tana fama da tararrabin yadda Ummi za ta kwance mata zani a kasuwa. Duk siyayyar da Abbanta ya yi mata babu abin da ya burgeta. Rashin fara’arta ya dami Yaya har sai da ta kai ga yi mata magana kafin Abba ya kaita tasha.

“Sai da aski ya zo gaban goshi nake ganin alamun rashin son komawa a tare dake Hamdi.”

Zee ma ta ce “Ya Hamdi ko kukan bodin za ki fara a term ɗin ƙarshe? In faɗawa Abba a dawo dake makarantarmu?”

Duka Hamdi ta kai mata da wasa a ƙoƙarinta na danne damuwarta. Bayan fitar Zee daga falon Yaya ta muskuta kusa da ita.

“Hamdiyya.”

“Na’am” ta amsa a raunane.

“Na san baki so zuwan iyalin Maje gidan nan ba tunda aka zo da Ummi.”

A zabure ta kalli Yayan da tsananin mamaki. Ita kuwa tayi murmushi.

“Kina mamakin yadda aka yi na sani?”

Ta gyaɗa kai.

“Kin guji gida saboda kada a san waye mahaifinki. Yanzu kuma gashi an zo an ganshi har gidan kina tsoron kada asirinki ya tonu.”

“Yaya…” ta soma faɗi cike da kunya.

“Ki koyi son abin da Allah Ya baki sai Ya ninka miki da wanda baki zata ba.”

Yawu ta haɗiya “to.”

Yaya ta cigaba da cewa “Ban taɓa nadamar auren mahaifinku ba saboda bai bani wannan dalilin ba. Irin kulawar da muke samu daga gare shi wasu masu kuɗin sai sun yi kishi da mu. Zaman lafiya yafi zama ɗan sarki. Hamdi sandar hannunka da ita kake duka kin ji. Hangen ta hannun wani ba naki bane don baki sani ba ko duk ƙaya ce ko bata ma da ƙwari.”

Numfashi ta sauke ta sadda kai ƙasa ta bawa Yaya haƙuri. Ita kuwa da yake ba mace bace mai riƙo ko son ayi ta nanata zance sai cewa tayi a bar maganar.

To a haka Abba ya dawo shabiyun rana ya sanar dasu Baba Maje na nan tafe zai kai su makaranta tare da Ummi. Ya ƙare da faɗin,

“Tare zamu tafi.”

Albarkacin Yaya dake zaune a wurin da nasihar da tayi mata ɗazu ne kawai ya hanata fasa ihu. Ta rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi. Addu’a kawai ta kama yi Allah Ya kawo sanadin da zai fasa binsu don gudun kada ya dinga sakin baki a gaban Ummi.

Addu’arta ta ƙarbu domin an fara zuba kayanta a motar Baba Maje sai ga wani dattijo yana sallama da Abba. Kana ganinsa baka buƙatar ƙarin bayani za ka gane ba mutumin kirki bane. Shadda ce yellow shar a jikinsa tana uban ƙyalli ga hula ya harbo gaban goshi irin na tsofaffin ƴan duniya. Taunar cingam yake cakakal-cakakal yana karkaɗa muƙullin mota. Ga wata uwar yatsina yana faman yi a yayinda idanunsa ke ƙarewa layin gidan kallo.

“Maje anya ba za ku tafi ba kuwa? Ban san me ya kawo shi ba amma ina jin ba abu bane da zamu ƙare da wuri.”

“Ba dai abokin sana’arka bane ko?” Baba Maje ya tambaya don yanayin mutumin babu sha’awar son kusanci da shi.

“Agent ɗin wanda nake hayar gidan abincina ne.”

“To ko dai mu jira?” Baba Maje ya sake cewa da ƴar damuwar yadda yaga abokin nasa kamar baya cikin nutsuwa.

“A’a, ku tafi kawai.”

Godiya ya yi masa akan biyowa ɗaukar Hamdi sannan ya juya wajen mutumin su kuma su ka shiga mota.

Akan hanyarsu Baba Maje yayi ta ƙoƙarin haɗa hira tsakanin Ummi da Hamdi. Da yake Ummi akwai wayo sai ta fishi jan Hamdin a jiki. Ya kuwa ji daɗin hakan sosai.

Abba da baƙonsa kuwa ba komai su ka tattauna ba illa ƙarin kuɗin haya da aka yiwa gidan abincin nasa. Kuɗin ya yi biyun abin da yake biya. Ya fara roƙon alfarma mutumin ya ce sai dai ya tashi. Dama kuma ya samo mai biyan wannan farashin ne. Ya kuma san babu yadda za ayi Abba ya biya. Shi ne ya zo masa da dabara.

“Idan na tashi yaya zan yi da iyalina? Don Allah ka rage min wani abu.”

“Sati biyu zan iya baka ka tattare komatsanka ka tashi. Idan kuma kuɗin sun samu kafin nan sai ka kawo a sabunta kwantiragi.”

Yana gama faɗin haka ya shige motarsa ya tada ƙura ya bar unguwar. Abba ya koma gida da sanyin jiki ya labartawa Yaya halin da ake ciki.

*

“Ki fara kai min nawa kayan ɗaki don akwai abin da nake buƙata yanzu a ciki.”

Ko minti biyar Baba Maje bai yi da barinsu da kayansu da za su kwashe su kai hostel ba Ummi ta rikiɗa ta koma annobar ƴan FGC.

Wani irin kallon mamaki Hamdi ta bita da shi “ban gane ba.”

“Au…kin daina jin hausa ne saboda mun shigo school? To jirani a nan. Zan aiko miki da yaren da za ki fahimta.” Da tafiyarta ta ƙasaita ta wuce ta bar Hamdi a tsaye.

Ita kuma ganin ta tafi ta fara ɗaukar kayanta ta nufi hostel ɗinsu. Tana ajiyewa ta koma da sauri domin ɗebo sauran sakamakon garin da hadari saboda damina da ta tsaya sosai. Da isarta ta iske wata yarinya da ta tabbatar cikin ƴan koran Ummi take. Wata tsadaddiyar waya ta fito da ita daga ƙasan hijab ta yafito Hamdi da hannu. Da taga bata matso ba kawai sai ta danna wayar. Nan da nan wurin ya karaɗe da muryar Abba inda yake cewa (Altine kece haka? Ikon Allah) da muryar nan tasa da ko ita ƴarsa bata so.

Hankalinta ya yi masifar tashi. A take ta jiƙe da wani irin gumi. Ta miƙa hannu a firgice za ta karɓe wayar sai yarinyar ta ja da baya.

“Ummi ta ce ki kwaso mata kayanta idan ba haka ba duk makarantar nan kowa sai ya gani”

“To” ta amsa da sauri tare da duƙawa ta fara ɗaukar kayan.

Yarinyar ta yatsina fuska “no, ta ce da ɗai-ɗai za ki ɗauka.”

“To” Hamdi ta sake amsawa da rawar jiki.

Banda akwatuna biyu akwai manyan ledoji uku. Haka tayi sawu biyar tana zuwa hostel ɗin su Ummi. Bata ganta ba sai da ta kai ledar ƙarshe ta sameta zaune akan gadonta.

“Ina za ki baki jera min ba?”

Cak ta tsaya ta dawo da sauri ta jera kayan a kwanar Ummin. Ƴan ɗakin su ka zuba musu ido suna ganin ikon Allah. Bayan ta gama a gadarance Ummi ta ce mata gobe ta zo da wuri ta ɗebo mata ruwa. Ta amsa kawai ta fita.

Da ta fita ko ganin hanya bata yi saboda hawayen da ya cika mata idanu. Da haɗa hanya ta isa inda sauran kayanta su ke ta kwaso. An soma yayyafi ga iska mai ƙarfi. Saboda haka akwatin da jakar sun yi buɗu-buɗu. Zuciyarta a ƙuntace ta tafi nasu hostel ɗin. Ajiye kayan kawai tayi ta hau gado ta dunƙule jikinta tana kuka. Nan da nan wurin ya cika da mutane ana tambayarta me yake faruwa amma ko ɗago kai bata yi ba. Sai wata ce da taga yadda ta dinga ɗiban kayan Ummi ta basu amsa.

“Wannan hutun da alama ita Ummi Maje za ta takurawa.”

Alhini da tausayi su ka dinga nunawa bayan ta faɗa musu me ta gani. Abin bai yi musu daɗi ba domin kuwa Hamdi bata rigima.

“Lallai Ummi bata da sauran rabo don ko mu masu baki da take zalinta bamu yafe ba balle mara baki irin Hamdiyya.”

Wadda tayi maganar tana rufe baki wata ma ta kama. Su ka taru su ka gama ɗebe mata albarka (mu guji irin waɗannan laifukan da bama ɗaukarsu a bakin komai. Babu wani haƙƙi abin rainawa) sannan su ka watse.

RAYUWA DA GIƁI 7

Batul Mamman💖

Sanarwa
In sha Allah post zai dinga zuwa ranakun Litinin zuwa Juma’a.

*

Ummi dai baje kolin rashin mutumcinta tayi akan Hamdi har ya kasance sauran ɗalibai suna samun sararawa. Kowanne aiki Hamdi, kowacce bola da shara ma ita ɗin dai take nema. Wanki harda na su pant ita take mata. Su ɗebo ruwa da kwafar note dama tuni ta daina saka wasu. Kuma ko da wasa Hamdi bata taɓa faɗin wata kalmar neman sauƙi ba. Komai Ummi ta ce ‘to’ ce amsar. Ita dai burinta ta bar makarantar ba tare da kowa ya san ko waye mahaifinta ba.

Da yake a cikin hutun da su ka aka yi jarabawar JAMB, yanzu ƴan kwanaki su ka rage kafin a fara WAEC. Kowa ya duƙufa da karatu ba ji ba gani. Waɗanda basu ɗauki karatun a bakin komai ba irinsu Ummi kuwa shagalinsu suke yi.

Ranar wata laraba da safe aka tashi makarantar babu ruwa. Abin ka da lokacin zafi. Tsakanin April da May a garin Kano dama ba a cewa komai. Rijiyar makarantar mai dama dama ba a samun komai sai wani ruwan dauɗa wanda zai iya sati bai kwanta ba. Kowa ya shiga damuwa don ko darussan aji ba a shiga ba. Ga ɗan karen zafi ana ta zufa. Principal tun safe ta fice sai wajajen shabiyu ta dawo da tankokin ruwa har bakwai a bayanta. Yara sai murna. Aka umarci malamai da su kula da ɗaliban wajen bin layi ta yadda kowa zai samu. Sannan an ja musu kunne babu mai ƙarɓar ruwa sau biyu. Kuma bokiti biyu kaɗai za a cika wa kowa saboda kada wasu su rasa.

Layi layi aka jera ɗaliban na ajujuwansu. A sammakon Hamdi ita ce ta talatin da huɗu a layinsu. Kafin a zo kanta rana ta gama dafa ta. Ana zuba mata taji wani sanyi ya ratsata. Ta ɗauki bokatan hagu da dama ta wuce ɗaki. Tun kafin ta isa bakin matattakalar hostel ɗin ta hango Ummi da ƙawayenta a zaune kan dandamalin wurin suna ta hayaniya ana dariya. Fuska a haɗe Ummin ta tarbeta da ta ƙarasa.

“Kin daɗe a layi gaskiya. Ke ko irin turereniyar nan baki iya bane?”

Take takenta Hamdi ta gane sai dai ta riga ta yiwa kanta alƙawarin ko me zai faru ba za ta bata ruwan da ta wahala wurin samu ba. Jikinta gabaɗaya ƙaiƙayi yake yi mata. Ga ƙishi ga yunwa.

“Ban iya ba.”

“Mtswww, wuce ki kai min ruwan in samu nayi wanka kafin a gama abinci.”

Wata zaƙaƙura ta ce “Ummi kin ce fa nima za ki sa ta ɗebo min.”

“Ki bari ta juye min mana.” Ta cewa wadda tayi maganar a wulaƙance.

Juyawa Ummi tayi taga Hamdi ta ajiye bokatan ta sarƙe hannu a ƙirji.

Rai a ɓace ta ce mata “Ɗauki mu tafi mana.”

“Ki je ki bi layi don babu wanda za a zubawa sau biyu. Har ticking suna ake yi.”

“To sai ki san yadda za ki yi. Ni ki wuce ki zuba min zafi nake ji.”

Hamdi ta rasa daga ina take jin wani ƙwarin gwiwa kawai ta ce “naga kamar baki gane ba. Wannan ruwana ne. Ki je ki ɗebo naki.”

Wata uwar shewa Ummi tayi tana dafa ƙirji “dani kike? Har kin manta abin da zan iya yi miki idan ki ka ɓata min rai?”

Tunawa da alamun mutumcin su Iyaa tayi sai take ganin kamar duk haukan Ummi ba za ta fitar da bidiyo ɗin ba.

“Kin daɗe baki nunawa duk makarantar nan waye ubana ba.”

“Kanbu, dani kike?” Ummi ta faɗi cike da mamaki. Sai kuma ta fasa faɗan ta ce ƙawayenta su ɗauko bokitin.

Suna kai hannu Hamdi ta tare kayanta ta hanyar durƙusawa a gaban bokatan ta tarosu da hannuwanta.

“Wallahi ba zan baki ruwan nan ba.”

Mamakin me Hamdi ta taka a yau ne ya kama Ummi. Taga gara ta nuna mata idan tace za ta yi abu lallai babu fashi. Waya ta ɗauko daga aljihun wandonta na kayan prep. Gaban Hamdi na faɗuwa amma idonta yau ya ƙeƙashe. Tana ji kamar kowa muryar Abbanta ta ƙarade wurin. Kan kace meye wannan ɗalibai sun taru suna jin bayanin Ummi na cewa wannan zuƙeƙiyar muryar fa ta mahaifin Hamdiyya Habib ne wanda ya kasance ɗan daudu. Aka dinga tururuwar leƙa bidiyon ana cewa ga kama nan.

Kallon Hamdi aka fara ana zunɗe tayi kamar bata jinsu duk yadda ranta ke suya ta duƙa za ta ɗauke ruwan sai taji Ummi tayi wata maganar da ranta ba zai iya ɗauka ba.

“Mamanta kuwa cangal ce mai ƙafa ɗaya da kwata” ta cilla ƙafa ɗaya ta banƙaro ƙirji ɓari ɗaya “idan tana tafiya sai ka rantse Awilo ne zai yi rawar waƙarsa.”

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Hamdi ta iya faɗi don dariyar da aka tuntsire da ita a yayinda Ummi ke kwatanta tafiyar Yaya ta mugun baƙanta mata rai. Sakin bokiti guda tayi ta ɗaga ɗayan da hannu biyu ta juye shi tas akan Ummi. Kowa kuma sai ya bar abin da yake yi aka tsaya kallo.

Ummi bata gama dawowa hayyacinta ba Hamdi ta cakumi wuyanta ta soma kai mata duka. Dambe sosai ya ɓarke a tsakaninsu inda Hamdi ta dinga tumurmusata da ƙasa. Tunda kayanta a jiƙe suke sai jikin ya yi futu-futu kamar an tonota daga rami. Ƙawayen Ummi da suka ji ta fara neman ceto ne su ka ƙwaceta sannan su ka yiwa Hamdi taron dangi. Mutum uku ne su ka danneta a ƙasa suna duka. Ƴan hostel ɗinsu na ganin haka su ma suka saka hannu wurin kai mata ɗauki. Wurin ya hargitse aka dinga ɓarin ruwa ana doke doke.

Prefects ma basu iya yin komai ba sai malamai da aka kira. Duk wadda take waje a lokacin da ƴan kallo da ƴan dambe aka tasa ƙeyarsu sai ofishin Principal.

Baiwar Allah ji tayi kamar ta fasa ihu da taga yadda yaran nan su ka ɓannatar da ruwan da ta wahala wurin nemowa. Ba’asi guda ta nema shi ne su waye su ka fara faɗan. Aka nuna Hamdi da Ummi. Ta karɓi bulala kuwa ta zane musu jiki ta zauna tana haki. Mataimakinta ne ya karɓi shari’ar saboda abin mamaki yau Hamdi yake gani kuma wai ita ta fara faɗan. Duk yadda aka yi a sanin da ya yiwa shaiɗanci na Ummi ya san laifin ba zai wuce nata ba.

Masu tarar aradu da ka ya haɗa da displine master sannan ya zauna sauraron abin da ya haɗa yan matan. Ummi ta kitsa ƙarya da gsskiyarta ita kuwa Hamdi ko tari bata yi ba. Mutumin nan ya kaɗa ya raya amma ƙememe taƙi magana. Sai ajiyar zuciya kawai take saukewa. Waje ya tura su ya tattauna da malamai. Kowa ya riga ya san halin Ummi da Hamdi. Duk da haka tunda Principal tayi rantsuwa ya ce a dubo lambobin iyayensu a sanar dasu ana nemansu washegari Juma’a. Duk wanda bai zo ba ƴarsa ba za ta yi jarabawar da za a fara ranar litinin ba.

Hamdi a yau ko a jikinta. Ta riga ta sanyawa zuciyarta ɓoyon uba bashi da wata fa’ida. Da tun farko ma an san shi Ummi bata isa tayi amfani da wannan damar akanta ba.

A ɓangaren Ummi ne dai hankalinta ya nemi gushewa. Ƙaryarta ce za ta ƙare nannda ƴan awanni. Kiran iyayenta ba baƙon abu bane ko kaɗan. Inda gizo ke saƙar dai shi ne wani Sugar Daddy ɗinta ne yake zuwa a matsayin kawunta. Wai ita marainiya ce. Baba Maje da ke kawota kuma yaron kawun nata ne. Har ila yau baban nata yana karɓar wayarta duk ranar komawa makaranta tun da aka bata wayar. Wadda take amfani da ita ba tare da sanin hukumar makarantar ba wata ƙawarta take bawa ajiya. Babbar waya ce da wani saurayin daban ya saya mata. Tun kafin a dawo taje gidansu yarinyar ta tura wannan bidiyo ɗin da ta yiwa Abban Hamdi. Idan ta kuskura ta bari aka kira wani ba mahaifinta ba Hamdi za ta sami damar da ta zarce wadda ta samu ta cusguna mata. Gumin da ya tsatstsafo mata ta yarfe kafin ta tashi da rawar jiki taje ta sanar da Vice Principal numbar da zai kira a madadin wadda su ke da ita.

*

Ɗokin da ya kama shi tunda aka yi sanarwar jirgi zai sauka nan da mintuna kaɗan ya bashi mamaki. Belt ɗin da aka ce fasinjoji su ɗaura ya gyara gami da leƙa tagar jirgin. Garin Kano yake gani da tsakar rana ƙarfe biyu da rabi. Tsirarun bishiyoyi da yalwar ciyayin damina sai gine gine marasa tsayi ba kamar inda ya baro ba. Tayoyin jirgin na dira ƙasa sabon yanayi ya baƙunce shi na farinciki da tarin fargaba. Uwayensa da ƴan uwa tun a waya su ke nuna farincikinsu. Alhaji ne damuwarsa. Zai karɓe shi ko kuwa yanzu ma zai cigaba da nuna masa ƙyama kamar wanda yake aikin saɓon Allah?

*

Kafin kowa ya kula wata matashiya dake tsaye tare da iyalan Alh. Hayatu Sule ta hango Taj ta cikin ƙofar gilas. Kyakkyawan saurayi ne wanda duk hangen mace indai ta same shi ta sake ɗaga ido neman wani dole a sanyata a sahun marasa wadatar zuci. Yana kama da ƴan uwansa amma akwai wani abu dake tattare dashi wanda ya bambanta shi dasu da take iya gani. Ba hasken fata bane domin wasu cikin ƴan uwan nasa sun fi shi haske. Haiba da cikar halittarsa su ne suka fi komai ɗaukar hankalinta. Tana can duniyar saƙe saƙe bata kula da yadda ƴan uwan nasa da ƴaƴansu su ka bar wurin ba domin tararsa sai daga baya.

Idanu kansu su ka dawo ganin yadda ake pasin-pasin wajen rungumar Taj. Gashi taron mata don Ahmad da Kamal ne kaɗai maza in ka cire jikokin gidan da ba wani sabo suka yi dashi sama da waya ba. Bishir da Abba su na makaranta.

“Aunty Salwa mu je mana.”

Wani yaro ne ya yi maganar yana jan hannun matashiyar budurwar da Taj ya sacewa zuciya farat ɗaya. Murmushin jin kunyar kanta tayi ta kama hannun yaron su ka matsa kusa dasu. Yaron ya saki hannunta ya koma wajen Ahmad yana cewa ya ɗaga shi zai ga Uncle Taj.

“Daddy ni bai ganni ba. Ɗaga ni sama.”

Kamal ne ya ɗaga yaron ya miƙawa Taj. Ya karɓe shi ya rungume yana sumbatar kumatunsa.

“Babana da kansa.”

Yaron ya girgiza kai “Uncle Taj sunana Hayat.”

“Ba Hayatu ba?” Taj ya ce da alamun mamakin da yasa yaron saurin cewa “Hayat yafi daɗi.”

Dariya kowa yayi sannan Ahmad ya ɗan turo budurwar nan gaba.

“Ga Salwa ku gaisa.”

Taj ya sakar mata murmushi domin kuwa ƙanwar yayansa Ahmad ce da su ka haɗa uwa. A yanzu haka sakamakon karatu da ya kawota Kano daga Bauchi garin da mahaifiyar tasa ta sake aure shi ne take zaune a gidansa. Shekararta ta biyu kenan a Kano kuma iyalin Alh. Hayatu har matansa basu nuna mata wani abu da zai sosa zuciyarta ba. Ƙanwar ɗansu ita ma ƴarsu ce.

Shi Ahmad matarsa ɗaya da yara biyu. Hayat da ake kira da sunansa bisa umarnin Alhaji sai jaririyar da ko arba’in ɗinta ba ayi ba mai sunan Mama wato Aisha.

Ɗunguma su ka yi a motoci huɗu su ka nufi gida. Mazan motarsu ɗaya su kaɗai. Kamal ya yiwa Taj bayanin cewa sun canja shawara zai zauna a gidan Ahmad har lokacin komawarsa.

Jikinsa a sanyaye ya tambaye su “Alhaji ya ce kada na zauna masa a gida ne?”

“A’a” Ahmad ya faɗi da sauri.

“Yaya ka faɗa masa gaskiya mana.” Cewar Kamal dake tuƙi “ɓoyewar bata da wani amfani.”

“Faɗa min me ya ce Happiness.”

Tiryan tiryan kuwa Kamal ya faɗa masa yadda Alhaji yaje ɓangarensu har ɗaki ya ce yaga saƙon Taj na tahowa buɗe gidan abinci. Ba zai hanasu mu’amala da ɗan uwansu ba amma indai da niyyar cigaba da saɓa masa ya dawo ya nemi wurin kwana.

“Amma ya amince ka shiga gidan ka gaishe da su Hajiya. Kawai dai kada ka bari ku haɗu.”

“Zan zauna a hotel.”

Dukkaninsu kallonsa su ka yi. Ba kuma don abin da ya ce ba, yadda muryarsa ta fito kai ka san ba ƙaramar dauriya ya yi ba. A shaƙe take da wani irin rauni daga zuciyarsa.

“A gidana za ka zauna. Tun jiya nasa Salwa ta gyara maka ɗaki.” Ahmad dake baya ya zura hannu gaban motar ya ɗan bubbuga masa kafaɗa.

“Ba zan zauna na takura iyalinka ba. Infact mutumcina ma zai zube. Kawai bamu taɓa haɗuwa ba sai da aka koreni daga gida for the second time.”

Dariya Kamal ya yi “zaman hotel ɗin ba matsala bane amma ba mutumcin aljihunka bane gaskiya a garin da kake da gidan ƴan uwa sama da hamsin da za su so zamanka tare dasu.”

Kamar shi ya kar zomon, Taj ya ɗaure fuska ya ce masa “kawai ka faɗi abin da yake ranka. Kana tsoron kada naje ace na fara bin mata ko?”

“Ba a ji mutuwar sarki a bakina ba, amma dai kai da kake kan tsini idan ka ƙara da kwanan hotel ban san yaya za ku kwashe da Alhaji ba.”

“Allah ni ba ɗan isk* bane. Saboda tsoron kada Alhaji ya yi min baki watarana na lalace ko girlfriend na kasa yi.” Taj ya amsa defensively.

“Daga budurwa sai lalacewa Taj?” Cewar Ahmad, shi da Kamal su na dariya.

Shi kuma Kamal ya ce “dama me za kayi da busassun turawan nan da ba su da gaba da baya?”

Haɓa Taj ya riƙe yana kallonsa kafin ya ce “Yaya kaji irin zancen banzan da Happiness yake yi ko? He is long overdue for marriage.”

“Da za ku yi auren maybe da ka samu daidaitawa da Alhaji.”

Hirar tasu sai ta koma ta dacewar Kamal da Taj su nemi mata su yi aure haka nan. Da haka su ka isa gida. Sai dai kafin maigadi ya buɗe musu gate motar Alhaji ta tsaya a bayan tasu.

“Alhaji ne” Ahmad ya faɗawa Taj.

Zuciyarsa ya ƙarfafa ya fita daga motar duk da tunin da yayunsa ke yi masa akan gargaɗin Alhajin na baya son ganinsa. Da sassarfa ya isa bakin motar da gilasanta duka baƙaƙe ne. Ba a sauke ko ɗaya ba a ciki amma ya tabbatar daga cikin ana ganinsa. Direba ke tuƙin motar amma da dishi-dishi yana iya hango Alhaji zaune a baya. Ya taka har bakin tagar ɓangaren nasa ya durƙusa cike da girmamawa.

“Sannu da zuwa Alhaji.”

Tun a hanya jikinsa dama ya bashi zai ga ɗan nasa. Tunaninsa ne ma ya hana shi gama uzurin da ya fitar dashi. Yanzu da yake ganinsa kewar Taj ɗin ta mamaye zuciyarsa. Idanunsa su ka tara ƙwallar da yake jin abin kunya ne a ganshi da ita. Saboda haka bai ɓata lokaci ba wurin umartar direbansa da ya yi ribas su bar wurin.

“Alhaji ka daure ka saurari yaron nan don Allah.”

“Koma na ce!”

Direba ya so yin musu Alhajin ya manta da dattijantakar mutumin ya daka masa tsawa. Wannan yasa shi danna accelerator bayan yasa giya a ribas da ƙarfi. Ƙura kuwa ta tashi ta baɗe Taj da yake durƙushe har lokacin bai motsa ba.

Ba shi ya tashi ba duk da magiyar su Kamal da wasu cikin matan da su ka riga su dawowa daga airport. Anyi a idonsu ne saboda an buɗe gate. Kuma dama Kamal na yin horn su ka firfito tare da iyayensu.

Ahmad ne ya ɗaga shi zai shiga dashi gidan ya cije ƙafarsa.

“Mu je gidan naka.”

“Kaga su Umma fa a tsaye. Mu ƙarasa ku gaisa sai mu tafi.”

Kai a sunkuye Taj ya girgiza kai.

“Wallahi ba zan shiga gidan nan ba sai ranar da mai shi ya kirani ciki da kansa.”

Motar ya kama zai buɗe Kamal yayi saurin danna lock da muƙullin hannunsa.

“Kada kayi taurin kai. Don Allah ka shiga ciki.”

Kai Taj ya ɗaga ya hango Salwa a tsaye tare da sauran. Bai yarda ya haɗa ido da kowa cikin matan gidan ba ya ƙwala mata kira.

“Salwa…”

Gabanta ya faɗi, zuciyarta tayi wani irin bugu. Sai kuma wani irin ɗumi mai daɗi ya lulluɓe mata jiki da ta tuna sunanta kaɗai Taj ya ambata a wannan yanayin da yake ciki. Ƙafafunta kusan da ikon kansu su ka ƙaraso da ita gabansa.

“Kai ni gidan Yaya a rickshaw (haka ake kiran adaidaita sahu a India).”

Alamun rashin fahimta ya gani a tare da ita ya nuno mata guda da ya shigo layin nasu.

Kai Ahmad ya girgiza domin hanata sannan ya umarci Kamal da buɗe motar. Da kansa ya tura Taj baya ganin ƙanin nasa ƙiris yake jira ya saki ƙwallar da ta rufe masa idanu.

“Kai shi gida zan taho.”

Haka kawai ya ce da Kamal ya buɗe gaba ya ce da Salwa ta ɗauki Hayat su bi shi. Suna tafiya shi da sauran suka koma ciki.

“Korarsa ya sake yi?” Umma ta tambaya da kukanta.

“A’a. Ku shirya mu je gidana ku gan shi.”

“Me ya faru Ahmad?”

Mama da Hajiya duka kuka su ke yi. Inna kuwa jingina tayi da ƙofar shiga gidan ta runtse idanunta. Da yake duk da mayafi su ka fito Ahmad buɗe motarsa da ya bari a gidan ya yi ya ce su shiga.

“Alhaji zai yi faɗa Ahmad.”

Da mamaki mai haɗe da ɗimbin takaici Mama ta kalli Inna da tayi maganar baki buɗe.

“Sau tari damuwar uwa da jajircewarta na taimakawa wurin ragewa ƴaƴa raɗaɗin hukuncin uba. Kina tsammanin akwai riba idan duka ku biyun kun juya masa baya? Ko kuwa kina ganin yin hakan wata gwaninta ce da Alhaji zai yaba?”

Umma dama tafi kowa zafi kuma maganarta indai akan gaskiya ne ba kasafai take taunata ba.

Jiki ba ƙwari Inna ta ce “ba haka bane.”

Umma ta ce “to yaya ne? Sama da shekara goma rabon da ɗanki ya sanya ki a ido zahiri. Banda ma Allah Yasa Takwara (da yake haka su ke kiran juna da Amma) jajirtacciya ce da tuni ɗannan ya bi duniya. Uwa da uba a raye amma kun bar masa wawakeken giɓi mai wuyar cikewa. Baku san ku yabi ƙoƙarinsa ko kuyi masa faɗan kuskure ba.”

“Kiyi haƙuri don Allah” Inna ta ce tana kuka sosai.

“Magana ce ta gaskiya. Kin goyi bayan miji kun mayar da yaro marayan ƙarfi da yaji. Yau ko ɗan kafin Fatiha ya kawo muku gida wannan hukuncin ya yi tsauri, balle girki. Mene ne aibun girkin nan ne? Har mamakin ki nake yi idan kina sha’anin gidan nan kamar babu abin da yake faruwa.”

“Jamila ya isa haka don Allah. Na tabbata tana da dalilinta na yin duk abin da tayi tunda ita tayi naƙudar Taj. Ta fi mu son sa.” Hajiya ma ta gwaɓa tata maganar.

Kukan Inna ya sake tsananta da wannan rashin fahimta da abokan zamanta su ka yi mata. Ita fa tun lokacin da taga auren Mama yana girgiɗi a dalilin Taj hankalinta ya yi mugun tashi. Balle da aka zo sulhun nan ta fahimci ashe su Hajiya ma dake gidan sun daina girki. Wannan dalilin yasa ta sauke dukkanin tijarar da ta tanadarwa Alhaji. Domin tana da tabbacin muddin ya sallameta akan Taj su ma za su gwada masa rashin goyon baya. Ƙarshenta cikin fushi aurensu ya sami matsala. Indai ba butulci ba kuwa irin zaman da su ke yi a gidan bata jin ya kamata ta yi musu sakayya irin wannan.

Zafin da taga sun ɗauka ne ya bats damar yi musu wancan bayani yadda za su fahimceta.

“Kuna ganin rayuwar Taj za ta yi albarka idan sanadinsa gidan nan ya wargaje? Fushi irin na Alhaji nayi imanin sallamarmu duka lokaci guda ba zai yi masa wahala ba. Sai dai ya yi nadama daga baya. Sannan gabaɗaya yaran gidan nan da wuya su sake yiwa ɗan uwansu kallon mutumci. Da farin gashinmu a ka ace muna zawarci.”

Allah Sarki. Tana rufe baki Umma ta rungumota.

“Ki yi haƙuri Abullen Alh. Hayatu. Shaiɗan yaso amfani da ɓacin raina ya haddasa mana fitina.”

“Sunan da ki ka kira ni dashi na mene ne kuma?”

“Na ƙaunar rigimammen tsohon nan mana.”

Dariya su ka ji an kwashe da ita. Shaf sun manta da ƴaƴansu dake wajen a tsaye. Kowa da jan ido an sha kuka suke dariyar daidaitawar iyayen nasu. Da wannan kuma babbar ƴar gidan Yaya Bintu ta sanar da ƴan uwanta cewa babu masifa da za su bari ta shiga gidan sama da rabuwar kawunansu. Don haka kowa ya shirya abin da zai iya domin taimakawa Taj. Haɗin kansu kaɗai zai iya sassautawa mahaifinsu haƙƙin ɗansa da yake ɗauka.

Zaman lafiya aka ce yafi zama ɗan sarki. Alhaji bai san cewa duk cikim alkhairansa na duniya yadda ya gina gidansa shi ne mafi girman arziƙinsa ba. Gashi yana neman ɓata abin sa da hannunsa.

Motar Ahmad su ka shiga ya kaisu gidansa. Sai ga Taj ya manta da dukkanin damuwarsa da ya ganshi tsakanin uwayensa.

*

Abba ya maimaita zancen da yaji daga Vice Principal yafi a ƙirga a zuciyarsa bayan sun gama waya. Abin ne bambarakwai wai namiji da suna Hajara. Ta yaya ma za a ce Hamdi tayi dambe har ta kai rashin zuwansa akan matsalar zai iya jawo mata kora? Hamdi ce fa. Yarinyar da ko a cikin ƴan uwanta lokacin ƙuruciya da wuya a kawo ƙararta.

Damuwar da su ke ciki shi da Yaya akan matsalar tashinsa da aka yi daga wurin sana’a sai ta zama ba komai ba. Fatan wayewar gari kawai yake domin yaje ya ji me yake faruwa. Sai dai kuma hantsi na soma leƙowa yaji wani irin tashin hankali. Da hankalinsa ya riga ya san yadda yaran ke kunyar nuna shi musamman ita Hamdi. Shin za ta yi maraba da amsa kiran nasa ko kuwa?

RAYUWA DA GIƁI 8

Batul Mamman💖

*

Zazzaɓin gaske ne ya kama Ummi tun bayan ta saurari wayar Vice principal da mahaifinta. Aikin gama ya riga ya gama. Bayan ya ajiye wayar wani irin kallo ya yi mata ya jinjina ƙarfin halinta. Sannan ya ƙara tabbatarwa mace abar tsoro ce komai ƙanƙantarta.

“Wannan mutumin shi ne mahaifinki Ummi?”

Kai a ƙasa ta ce “eh.”

“Wanda yake zuwa kuma ya kuke da shi? Kuma me yasa ki ka zaɓi faɗin gaskiya yanzu?”

Shiru tayi babu amsa tunda Hamdi ma taƙi magana me zai sa ta fara?

Rai a ɓace ya ce “To kuwa ki kwana da sanin cewa yau ce ranarki ta ƙarshe a makarantar nan. Don ban ga wani dalili da zai hana a kore ki gobe ba ko da kece mai gaskiya. Sannan dole zan kira shi domin a warware komai gaban mahaifin naki.”

Yanzu ma kasa cewa komai tayi sai faman saƙe-saƙen neman mafita. Sannan a gefe guda babu irin ashar ɗin da bata saukewa Hamdi ba. Da farko ta san kawai jindaɗin samun mai yi mata bauta a makaranta tayi da sanin sirrin Hamdi. Yanzu kuwa wata irin tsana ce da za ka ji komai ma za ka iya yiwa mutum take ji akanta. Har lokacin bata saduda ba don tana jin da Hamdi tayi mata biyayya ta bata ruwan nan da bata ga wannan lokacin ba. Haɗuwarta da Baba Maje gobe ba ƙaramar tarzoma zai tayar ba.

“Ki tashi ki fice min daga office nace.”

Tsawar VP ta dawo da tunaninta inda take. Ta miƙe za ta fita sai kawai wani tunani ya zo mata. Guntun murmushi ta saki wanda har ga Allah sai da ya VP ɗin tsoro da shakku akanta.

Wurin ƙawarta konace babbar ƴar korarta Widad taje da saurinta. Sun gama nasu punishment ɗin na yau sai kuma washegari da ake sa ran samun ruwa. Za su wanke banɗakunan makarantar kaf har na malamai. Ga kuma sharar harabar makaranta da cire ciyayi.

Widad na ganinta ta tashi zaune daga kwanciyar gajiyar da tayi. Ummi ko kallon arziƙi bata yiwa ciwon dake babban yatsan Widad na ƙafa wanda taji a wurin faɗan ɗazu ba. Kuma ta gan shi sarai amma ba shi ne a gabanta ba.

“Bani wayarki in kira Uncle B”

“Kuna can aka zo inspection ɗin bazata tun bayan an nuna wayarki a wajen principal. Yau wayar da aka fitar daga ɗakin nan tafi ashirin.”

Muguwar harara Ummi ta jefeta da ita sannan ta yatsina fuska ta ce mata “banza, me yasa ko a pant baki ɓoye ba?”

“Korarmu aka yi waje bamu san dalili ba. Sannan aka yi searching ɗinmu da ɗai-ɗai.” Widad ta amsa tana mai ɓoye zafin zagin da halin ko in kula da Ummin ta saba nuna mata.

Plan ɗinta na farko ya faɗi tun kafin ta aiwatar. Dama niyarta ta faɗawa sugar daddy ɗin nata da take kira Uncle B idan an nemi numbarsa kada ya yarda ya zo. Shawara ta biyu kawai za ta ɗauka. Idan an zauna gobe kawai ta tada aljanu kuma duk yadda za ayi da ita kar ta yadda ta dawo daidai sai an koma gida. In ya so ko kasheta za ayi gara ayi a can.

*

A hanyarsa ta zuwa tasha cikin adaidaita sahu Abba ya kira ƙaninsa a waya. Hankalinsa ne sam bai kwanta da zuwa makarantarsu Hamdi ba. Yana son kare martabar ƴaƴansa daga dukkan abin da zai iya janyo musu raini daga mutane. Ya tuna wani lokaci da Yaya Hayatu kamar yadda yake kiran Alhaji yayi masa wata magana a baya.

“Habibu gaba nake jiye maka. Lokacin da za ka ji kunyar nuna kanka a wasu wuraren saboda kana ganin kamar darajarka bata kai ba. A lokacin ilimi ko rashinsa, talauci ko arziƙi ba su ne za su zame maka shamaki ba. Wannan mazantakar da kake gudu da Allah Ya karramaka da ita ce za ka so a baka aro ko na awa guda ne.”

Bai manta yadda ya murguɗa baki bayan wucewar Alh. Hayatu ba. Ya doka cinya harda tofar da yawu.

“Aniyarka ta bika. Sa idawa, ana ruwa kuna ƙirgawa.” Ya nuna ƙafarsa “wannan sayyara da Allah Ya bani babu inda ba za ta shiga ba sha Allahu.”

Ga ire iren ranakun sun zo. Ina ma ana mayar da hannun agogo baya. Da ya juya lokaci ya canja komai banda auren Jinjin. Matar da ta rufa masa asiri ta kuma bashi ƴaƴa mafi soyuwa a gare shi.

Gaisawa su ka yi da ƙanin nasa da girmamawa sannan ya faɗa masa halin da yake ciki a kunyace.

“Wallahi Yaya Habibu ka ganni a asibiti wani maƙocina ne babu lafiya. Daga shi sai matarsa ga yara ƙananu ta taho dasu. Basu da kowa a nan sai mu maƙota. Yanzu haka yayansa dake Zaria yana hanya. Tun asuba nake nan.”

“Ahhh, yi zamanka Abdulƙadir. Bari kawai naje.”

“Ka daina ɓoye kanka daga rayuwar yaran nan. Yau in dukkaninmu babu sai kai kaɗai shikenan sai ace zuri’armu basu da uba saboda abin da ya wuce?”

Yayi maganar ne saboda ya saba ji daga yaransa cewa ƴaƴan yayan nasa suna kunyar alaƙarsu da shi. Bai ga laifinsu ba Fisabilillah. Amma kuma Allah da Ya haɗa alaƙar Shi Ya san yadda zai tafiyar da al’amura. Tayasu ɓoye kansa ba dabara bace tunda duk lalacewa da uba ake ado.

Abba bai sake neman kowa ba ya tafi makarantar. Anyi sa’a yau shadda ya sanya ruwan madara, riga da wando harda hula. Da ya shiga makarantar bayan tafiyar minti arba’in tafiyarsa ya fara ƙoƙarin gyarawa. Sannan da zai tambayi masu gadi ofishin principal ya daddage ya kumbura murya. Amma kunne da idanu masu lafiya babu yadda za ayi su kasa fahimtar me ake son ɓoye musu. Basu dai nuna a fuska ba guda ya nuna masa hanyar office ɗin. A can gefe inda ake ajiye motoci ya ga wata kamar ta Baba Maje. Amma da yake baya tare da nutsuwa bai tsaya ƙare mata kallo ba.

*

A rayuwa babu abin da yafi tashin hankali kamar a samu wani ya san sirri a kanka wanda baka so a sani. Kuma in anyi rashin sa’a ya dinga amfani da wannan damar wurin cusgunawa rayuwarka. A shekara shidan da Hamdi tayi a makarantar nan bata taɓa shiga matsanancin hali ba sai da Ummi ta fara blackmailing ɗinta. A jiya da abu ya fito fili waɗanda su ka sami ganin bidiyon nan su ka labartawa waɗanda basu gani ba, sai taji zuciyarta wasai. Abin ya matuƙar bata mamaki. Tayi zaton in an sani an tsokaneta za ta iya yin kuka. Sai gashi babu wanda ya tunkareta tunda aka ga abin da ta yiwa Ummi da kuma maganar da ta yaɓawa wata Metiron bayan ta dawo ɗaki.

Da yake wasu manyan hankalinsu a ƙwauri yake, matar a gaban mutane ta tambayeta.

“Hamdiyya da gaske ne babanki ɗan daudu ne?”

A fusace ta amsa da “Eh, amma yafi uban wasu da yake zaman prison.”

Matar tayi matuƙar mamaki domin kuwa ba kowa ne ma ya san cewa mijinta yana prison ba saboda sata. Laƙwas tayi don babu halin sake magana saboda ƴan kallo sun sami sabon abin tattaunawa.

Ƙarfe goma aka aiko kiransu. Tana zuwa ta sami Ummi tayi kneel down a gaban teburin Principal. Ga Baba Maje zaune akan kujera. Yana ganinta ya saki fuska sosai yana magana da Principal ɗin.

“Yauwa ita ce kuwa.”

Principal ta dube shi da ɗan sakin fuska don taga sam bai fahimci zancen ba ta ce “Nima ita nake nufi Alh. Maje. Wannan Hamdiyyan ce dai su ka yi faɗa da Ummi jiya su ka yi sanadin hargitsa makarantar nan.”

“Na gane bayanin naki Hajiya. Dama abin da nake son fahimtar dake shi ne ina ganin ɗaya daga cikinsu ce ta shigar wa ƴar uwarta. Ba wai a junansu su ka yi faɗan ba.” Ya yi mata bayani dalla dalla a ƙoƙarinsa na son ta gane.

Murmushi tayi masa don yanzu bata jin za su fahimci komai sai yaran sun yi magana.

“Ko me yasa ka yi wannan tunanin?”

Ƴar dariya ya yi gami da gyara hannun rigarsa “mahaifin Hamdiyya abokina ne tun kafin a haifesu kin gansu nan. Shi yasa nake tunanin ko karewa juna suka yi. Ba kuma wai goyon bayansu nake ba. In sun yiwa makaranta laifi zan bada goyon baya ɗari bisa ɗari a hukunta su.”

Abin da ya fađa ya bawa Principal ɗin mamaki sai dai bata ce komai ba sakamakon sallamar sakatarenta da mutane biyu. Ɗaya wani ƙosasshen Alhaji ne ya sha babbar riga yana fama da kayan tumbi. Ɗayan kuwa Abban Hamdi ne. Su na shigowa VP da wasu manya cikin malaman su ka shigo su ma.

Abba na ganin Baba Maje ya ce “da na san za ka zo ai da nayi zamana a gida.”

“Ko kuma da ni na zauna ba.”

Dariya su ka yi sannan aka yi musabaha tsakanin duka mazan wajen.

Murya da yanayin mahaifin Hamdi kaɗai yasa malaman kallon kallo a junansu. Principal ta buƙaci a buɗe zaman da addu’a sannan ta ɗauko wayar Ummi ta miƙa mata.

“Buɗe min wayar nan don na sami labarin ita ta fara janyo rigimar.”

Kai Alhaji mai ɗan tumbi wato Uncle B da baka gane Baba Maje ba tunda Ummin bata kama dashi sai ya kama faɗan bogi.

“Ban hanaki zuwa da waya makaranta ba? Ke kenan kullum rigima ta tashi sunanki ne a sahun gaba.”

Baba Maje buɗe baki yayi don maganar ba tsoro ta bashi ba illa ruɗa masa tunani. VP na ganin haka sai ya taso har inda yake ya ja shi waje.

“Duk abin da za ka ji ko ka gani kada kace komai don Allah har ka gama fahimtar inda zancen ya dosa.”

“To amma…”

“Mu koma ciki. Komai zai warware kansa.”

Haƙuri ya bawa Principal na katse su sannan su ka jira Ummi ta buɗe wayar da rawar hannu. Jikinta babu inda baya ɓari. So take tayi aljanun ƙaryan tun yanzu amma bata da ƙwarin gwiwar pretending. Hamdi da bata san badaƙalar dake kwance ba kuwa ko a jikinta. Jikin kujerar da Abba ke zaune ta raɓa tayi kneel down abinta.

“Kunna min abin da ki ka kunnawa ɗalibai a jiya.”

Nan fa ɗaya. Kasa kunnawa tayi. Displine master ya daka mata tsawa amma ko gezau.

“Kin cika umarnin da aka baki ko sai na tashi?”

Muryar Baba Maje ta fito da kaushi. Uncle B duk ya zata malami ne da ake tsoro shi yasa bai ji komai ba da yaga ta cika umarni da rawar jiki.

Ofishin karaɗewa yayi da muryar Abba. Kunya tayi masifar kama shi. Idanunsa su ka yi jawur lokaci guda. Hamdi taji wani irin tausayinsa wanda yasa ta kuka. Baba Maje ya rasa me yake yi masa daɗi.

Principal ta miƙawa kowa wayar ya gani da idonsa sannan ta umarci Hamdi da tayi magana. Ba tare da coge ba ta faɗi abin da ya faru tun ranar da su Baba Maje su ka zo gidansu har abin da ya faru jiyan. Irin cin zarafin da Ummi ke yi mata da takura kawai don ta mallaki sirrin mahaifinta. Kallon takaici kala kala ya dinga sauka akan Ummin bayan ra gama magana.

“Ummi haka aka yi? A ina ki ka sami bidiyon?” Uncle B ya tambayeta har yana kai hannu zai ɗaga haɓarta domin kanta a ƙasa yake tana zubar da zafafan ƙwallar tsanar Hamdi.

“Wai kai ɗin uban waye a makarantar nan da za ka taɓa baligar mace?” Baba Maje ya tambaye shi a harzuƙe bayan ya doke masa hannu.

“Kai zan yi wa wannan tambayar.” Ya kalli Principal ɗin “ya kamata malamanki su san aikinsu in ba haka ba zan cireta daga makarantar nan.”

Baba Maje ya ce “Kai a wa?”

“Ni a mariƙinta” Uncle B ya bada amsa kai tsaye.

VP gaban kujera ya dawo don yaga an zo inda yake jira. Cikin zafin rai kuwa Baba Maje ya ɗago Ummi tsaye ya dubeta.

“Kalli ƙwayar idona ki faɗa min waye wannan.”

Numfashi ta fara ja tana shirin yin suman ƙarya taji Baban nata ya yi mata wata irin wawiyar jijjiga. Muryarsa tana rawa har wajen office ɗin kuma ana ji ya ce,

“Idan ki ka ce za ki yi min ƙaryarku ta ɗalibai zan sabauta miki halitta a wajen nan. Ki faɗa min waye shi.”

“Saurayi na ne.”

Tasss, tass, tas ya ɗauketa da wasu gigitattun maruka. Abba ya yi saurin finciketa daga hannunsa ya tsaya a tsakani.

“Haba Maje…”

“Matsa min Habibu.” Ya furta yana huci.

Uncle B na ganin haka ya tashi zai sulale ya gudu sai dai babu dama. VP ya sanya securities ɗin makaranta a bakin ƙofa. Hasashen haka zai iya faruwa tun a jiya yasa ya ɗauki matakin da ya dace.

Da ƙyar da suɗin goshi aka samu Baba Maje ya zauna. Abba ya dubi Principal ɗin ya yi magana.

“Da farko zan fara da baku haƙuri akan ɓarnar da yaran nan su ka janyo muku. Ummi tayi kuskure sannan ita ma Hamdi tayi na ɗaukar doka a hannunta. Amma fa duka abin da ya faru laifina ne…” ya sunkuyar da kansa.

Principal ta kalle shi da tausayawa “bari na ɗan ce wani abu a nan.” Ta kalli Hamdi “mu iyayenku da ku ke gani muma haifarmu aka yi ba da wayo muka zo duniya ba. Shekarunmu na hawa ne muna daɗa hankali. Duk wani kuskure da kuke yi a yanzu muma mun yi ƙila ma fiye da haka a lokacin tamu ƙuruciyar. Yanzu mun girma mun san illar abin shi ne dalilin da yake sa muke muku faɗa ma idan kun yi. Abin nufi a nan shi ne ƙuruciya da raunin hankali a baya yasa mahaifinki yin kuskuren bin rayuwar da kowa yake ƙyama. Gashi ita aba ce da ko ka daina da wahala đabi’unta su barka ɗari bisa ɗari. Amma tunda Allah Ya baki shi a uba ki rungume kayanki da godiya. Da baki ji kunya kin ɓoye shi ba, babu wanda ya isa ya ɗaga miki hankali akan shi. Ki nuna godiyarki ga Allah ta hanyar appreciating ɗin duk abin da Ya baki.”

Gyaɗa kai tayi tana goge hawaye “Abba don Allah ka yafe min.”

Da ƴar muryarsa ya ce “Allah Ya yi miki albarka Hamdiyya. Ki bawa iyayenki na makaranta haƙuri su ma.”

Ta kuwa bi umarninsa ta bawa kowa haƙurin abin da su ka yi jiya. Cike da kunya da jin nauyi Baba Maje ya bawa Abba haƙuri.

Abba ya yi murmushi “Don Allah ka bar wannan zance.”

“Ta yaya zan bari? Bayan shekara sama da ashirin da rabuwarmu ace ƴar cikina ce tayi maka irin wannan tozarcin?”

“Magana ni dai ta wuce don Allah.” Abba ya sake maimaitawa.

VP ya ce “yallaɓai ina ganin sanin alaƙar Ummi da mutumin nan shi ne abu mafi mahimmanci yanzu tunda an kashe wancan case ɗin.”

A lokacin aka fito da file na fitinannun makaranta inda sunan Ummi ya bayyana a kowanne term tun zuwanta a JS3. Bata fara laifin da ta cancanci a kira iyaye ba sai a SS2 da ta zama cikakkiyar senior. Kuma a lokacin ne duk sanda aka buƙaci iyayenta sai wannan mutumi dake zazzare idanu ya zo a matsayin kawunta. Ita ma aka bata dama ta faɗi yadda suke biyan maigadi su haura katanga ita da wasu. Samarinsu su kai su gari a shaƙata a sha ice cream da su shawarma a dawo. A rantsuwarta dai ta ce babu abin da ya taɓa haɗasu na fasiƙanci. Baba Maje kasa jurar jin maganganun ya yi ya finciki bulalar hannun wani malami ya shiga lafta mata. Da taron dangi aka raba shi da bulalar

“Kanki ki ka cuta Ummi. Nan duka ɗaliban da ki ka zalinta in basu yafe ba sai kin gani a ƙwaryarki.”

Fuskarta yaɓe yaɓe da majina da hawaye ta ce “Baba ka yafe min.”

“Ba dole na ba? Idan nayi miki baki rayuwarki ai sai tafi haka lalacewa. Ki tashi ki haɗo kayanki don kin gama karatu kenan.”

“Alhaji ba ayi haka ba.” Principal ta sa baki “ka bari mu ɗauki matakin da ya dace.”

“Maje kada ka ɗauki hukunci cikin fushi.”

“Kun san Allah ɗaya ne ko? To wallahi yarinyar nan ta gama karatu a ƙarƙashin ikona.”

Ya kalli Uncle B ya yi wani irin murmushi mai ciwo sannan ya ɗaga waya ya kira ɗan yayarsa police. Makarantar ya kwatanta masa.

“Ku taho yanzu don Allah.”

“Yallaɓai da ka bari an kira masa ƴan sandan dake kusa da nan. Ka san kowanne laifi ana shigar dashi a unguwar da ya faru.”

“A kira su. Shi wannan ɗana ne saboda haka ina jiran zuwansa saboda ina son komai ya tafi da jagorancin wani nawa.”

Suna wannan zance Uncle B ya matsa gefe yana ta bige bigen waya da hargagin iska. Bayan ya gama ya cigaba da masifa yana doka teburin Principal.

“Baki san ko ni waye ba a garin nan wallahi. Ina da damar sanyawa a rufe makarantar nan baki ɗaya a yau idan na so.”

“Ka daɗe baka aiwatar ba. Mutumin banza. Girma da matsayinka basu ƙara maka komai ba sai sanya hannu wajen ɓata tarbiyar yaran mutane.”

A cikin minti talatin motar ƴan sandan da VP ya kira ta iso makarantar aka yi awon gaba da Uncle B. Baba Maje da Ummi da VP ɗin su ka tafi tare dasu. Principal ta sanar da malamanta wajibcin neman iyayen yara a kurkusa domin tattaunawa da gujewa maimaicin abin da ya faru.

Hamdi da Abbanta su ka fito tare fuskokinsu babu walwala sosai. Shi yana cikin damuwar halin da abokinsa ya sami iyalinsa, ita kuma tana cike da kunyar ya san irin matsayin da ta ajiye shi a matsayinsa na uba. Hannunsa ta riƙe ganin yana raɓewa gefe guda.

“Abba in kai ka ka ga ajujuwanmu?”

“A’a Hamdi.” Ya zame hannunsa.

“Ba ka yafe min ba ko?” Idanunta su ka kawo ruwa.

“Ban taɓa fushi dake ba. Ba dai na son sake bar miki abin faɗi a cikin abokan karatunki.” Ya ce a sanyaye.

Wannan furuci nasa ya sanyata kuka sosai. Ta roƙe shi da ya jirata a nan inda yake za ta dawo bayan ya hanata kukan. Tana tafiya ta samu ɗalibai na dinning hall ana cin abincin rana. Duk da yadda take wasiwasi amma da ta tuno da maganar da Principal tayi mata sai taji zuciyarta ta daina tsoron komai.

“SS3 A” ta ƙwala kira da ƙarfi.

Tashi su ka yi wasu kuma su ka amsa da baki.

“Ku zo ku gaisa da Abbana.”

Ai kusan rabin hall ɗin ne su ka fita a guje. Aka kasa controlling ɗin su. Tana gaba har inda ta barshi tsaye. Kawar da kai taga ya yi tayi murmushi ta zaga gabansa.

“Abba an zo gaishe ka.”

Tunda yake kullum yaransa su ka zo gida da ƙawa basa taɓa cewa a gaisa da shi. Ƙawayen ma bai san kowa ba sai na dangi ƴaƴan ƴan uwa.

Ya juya suna ta ina wuni shi kuwa ya kasa amsawa saboda kada jin muryarsa yasa a yiwa ƴarsa dariya.

“Abba ka amsa mana” Hamdi ta ce tana dariya kamar ba ita ba. Yarinyar da kullum take cikin ƙunci da damuwa.

Ya buɗe baki ya dinga amsa musu. Ƴan matan nan maimakon nuna ƙyama sai yake ganin kamar ya burgesu. Wasu basu taɓa ganin ɗan daudu a kusa haka ba. Kamar wani abin sha’awa su ka dinga girmama shi. Kan Hamdi ya kumbura suntum saboda daɗi. Ranar da taimakon malamai aka ƙora su duka har ita cikin makaranta sannan ya samu ya tafi wajen Baba Maje.

*

Ganin su Inna ya yi saurin ɗaukewa Taj damuwar da ya shiga. Sai gashi ya zage yana ta hira kamar ba shi ba. A cikin hirar ne ya tambaye su ko akwai wani abu a tattare dashi da zai sa ayi masa kallon namijin da bai cika ba.

Ya naɗe hannun rigarsa har saman kafaɗa irin yadda yara su ke yi.

“Saboda son burge Alhaji har gym nake zuwa ina motsa jiki. Yanzu wannan…” ya nuna dantsensa “bai isa a kirani namiji ba?”

Kamal kula ya yi da Salwa da ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci da yadda tayi saurin ɗauke ido daga kallon hannun Taj. Shi kuma gwanin ya kama ƙasan riga zai ɗaga wai ya nuna musu packs ɗin ƙirjinsa. Gudun kada ɗan uwansa ya kunyata shi ne ya kai masa duka a hannun.

“Dalla malam rufe wannan sandar raken.”

Taj da yaji zafi ya rama dukan “ɗan baƙinciki in ka isa ka buɗe naka mai kama da taliya.”

“Mama kina dai jin abin da yake faɗa min ko?” Kamal ya faɗi yana miƙewa tsaye.

“Laifinka ne fa Kamal. Kai ka fara dukansa” Mama ta goyi bayan Taj.

“Saboda ya dawo daga America za ki nuna min wariya? Ke fa ki ka hana raini tsakaninmu.”

Su Hajiya sai dariya su ke yi. Taj ya sami goyon baya ya cigaba da tsokanarsa.

“Ka ci sa’a ban auro baturiya ba da kaga asalin wariya. In taho da ƴan ƴaƴana farare su na Mom…Dad…who is this black man” ya nuna Kamal aka sake tuntsirewa da dariya. Ya cigaba da tsokanarsa “Duk ƴan uwa su taru a kansu ana son burgesu. Kai kuwa naka sai dai kaji ana cewa ‘Sule maza tafi wurin babarka ta goge maka majina’ “

“Banza ƙazami. Wai majina kamar tashin Soron ɗinki. Kuma don wulaƙanci ba ma Sulaiman ba Sule zan haifa?” Kamal ya faɗi yana shure shi da ƙafa.

Taj dariyar da ya san za ta ƙular dashi ya cigaba da yi.

“Sule Kamalu Hayatu Sule. Irin ƴan chubby yaran nan masu ɗan ƙaton ciki ba.”

Ba ka jin komai a falon sai dariyar iyalin ta farinciki. Salwa da take ganin duk motsin Taj wani salo ne daban mai tafiya da zuciyarta ce kaɗai ta ƙare da murmushi.

Kamal da Taj su ka gaji da wasansu na dambe da girma bai hanasu yi ba su ka koma cin abinci daga plate ɗaya su na hirar da babu mai ji.

RAYUWA DA GIƁI 10

Batul Mamman💖

*

Numfashi ta sake saukewa a hankali bayan ta karɓi loudspeaker ɗin sannan ta rufe ido ta buɗe da sunan Allah. Da ido ta lalubo Taj wanda har ga Allah tayi matuƙar mamaki da ta iya gano shi a cikin mutane. Bata sani ba ko hakan yana da alaƙa da sahun gaba da ya dawo ya tsaya a jikin ƙarfen canopy bayan kusan kowa a zaune yake. Ya yi mata murmushi gami da gyaɗa kai kamar mai bata damar yin magana.

Mantawa tayi da kowa da komai ta yi taƙaitaccen speech ɗinta mai ma’ana wanda kalmominsa su ka dinga zuwa kamar daga sama. Wuri kuwa ya kaure da tafi. Ɗalibai ƴan ajinsu su ka dinga kiran sunanta da ƙarfi suna tafi. Haka kawai tauraruwarta ta ƙara haske a idanunsu tun bayan da ta kare martabar iyayenta.

Idanunta lokaci lokaci su na kan Taj har ta gama. Tana addu’ar gamawa taga Taj ya kalli wayarsa sai ya kara a kunne ya bar wajen. Za ta sauka aka dakatar da ita. Mai Girma hakimin Gabasawa da kansa ne zai bata kyaututukan da aka tanada dominta. Wani ƙayataccen kwando ne aka saka komai aka lulluɓe da ledar ado aka ɗaure. Ya miƙa mata aka yi musu hoto tare sannan ya ce tasa kyautar ita ce kujerar Makka a Hajjin shekara mai zuwa in sha Allah.

“Allahu Akbar” Malamin da yake MC ya faɗi, sai ɗalibai da iyayen yara su ma su ka amsa.

Murna a wajen Hamdi kuwa ba a cewa komai. Ta sauko daga stage ɗin idanunta cike da ƙwallar zallan farinciki. Wurin da su Sajida su ke zaune ta nufa da sauri. Banda Sajida da Zee harda ƴaƴan ƴan uwan Abbansu mata tsararrakinsu. Halifa ma ya baro ɓangaren maza aka yi murnar tare da shi.

“Hamdi ina kayanki? Yaya ta ce kada mu yarda mu wuce ƙarfe biyu nan.”

Halifa ya ƙara da cewa “ana can ana haɗa miki …”

Kafin ya gama magana Zee ta dage ta doke masa ƙeya.

“To fesal uban zance.”

Hannu Hamdi tasa ta saƙalo kafaɗarsa tana dariya “rabu da ita Halifa. Idan ka faɗa min me ake yi zan bar maka duk ragowar provision ɗina.”

Da sauri Zee ta riga shi faɗa.
“Walimar ƴan gida za ayi miki”

“Kin dai ji kunya wallahi. Da kayan ƙwalama za a sayeki cikin sauƙi” cewar Sajida tana taɓe baki.

Kayan nata ta nuna musu su ka haɗu da cousins ɗin nasu aka kwaso cikin ƙanƙanin lokaci. Ta koma cikin ƴan uwanta ɗalibai aka yi hotuna harda malamai da musayar lambobin waya. Wasu harda kuka sosai. Ita dai bata yi ba don sabon da tayi da abokan karatun nata na iya lokacin jarabawa ne. Kewar rayuwar makaranta tafi damunta.

Duk abin da take yi hankalinta yana komawa ga tunanin ina mutumin nan na ɗazu. Ta gaji da juyawa ko za ta gan shi Allah bai yi ba. Ga Sajida ta damu su tafi don ita za a yiwa faɗa idan su ka ɓata lokaci. Haka ta tafi zuciyarta tana begen sake ganin sa.

*

Wayar Amma ce ta sake shigowa, ita ce dalilin da yasa ya bar wajen. Kuka take yi wanda ya matuƙar tayar masa da hankali. Ta sanar dashi surukarta Hajjo ta ce lallai ta zaɓi tsakanin aure da aiki amma ba za ta haɗa biyu ba. Mijinta shekarsa huɗu da ritaya ya koma gida gabađaya.

“Wai zaman me nake yi a nan. Taji an ce kai ma ka dawo.”

“Ba ki faɗa mata ba daɗewa zan yi ba?”

“Nayi mata bayani duk taƙi ji. Yanzu don Allah 7 months to my retirement sai nayi resigning? An yi min adalci kenan?”

Ta maza ya yi bai nuna mata damuwarsa ba ya dinga rarrashinta. Da ƙyar ta haƙura bayan ya yi mata alƙawarin zuwa Abuja ya sami Hajjo a gidan mijin Amma ɗin inda take zama da amaryarsa da yaransa.

Yana dawowa cikin ƴan uwansa Firdaus ta janye shi tana ta nunawa ƙawayenta Uncle Taj. Daga hoto ɗaya sai da aka yi yafi goma. Masu ƙyasawa da yawa su ka kasa ɓoyewa. Shi dai ya biye mata ne kawai saboda ko a cikin jikokin gidan ita ce ƴar gaban goshinsa. Indai ana hutu tana yawan kiransa. Ana hoton da hayaniyar amma idanunsa yarinyar nan Hamdiyya Habib su ke nema. Da bai ganta zuciyarsa bata kawo komai ba tunda yana da yaƙinin Firdaus ba za ta kasa saninta ba. Bai san Hamdi bata da ƙawa ba. In ka cire sunanta ko sunan unguwarsu babu wadda ta sani.

*

Washegari jirgin ƙarfe bakwai ya bi zuwa Abuja. Idan buƙata ta biya so yake ya dawo a ranar don yanzu ya matsu ya koma wurin Amma. Da yake tun dare ya sanar da Daddy mijin nata cewa yana tafe, yana isa direba ya zo ya ɗauke shi.

Iyalan gidan ba baƙinsa bane tunda su na yawan kai ziyara America har Hajjo. Ƴan mata uku ne ƴaƴan kishiyar Amma da ake kira Anti. Su ma duka sun saba da shi. Dama tun zuwansa yana son tahowa Abujan su gaisa amma aiki ya hana. Tarba mai kyau ya samu daga Antin da ƴaƴanta. Sai da ya ci abinci ya ƙoshi sannan aka yi masa ido ɗakin Hajjo.

A hakimce kan kujera ya sameta ta kashingiɗa tana danna remote.

“Wannan zuwan na san na Jamila ne ba don neman albarkar tsofaffi ba.”

Taj ta sosa ƙeya “tuba nake Hajjo tawa ni kaɗai.”

Ƴar tsohuwar ta yatsina fuska “bana son daɗin baki. Ai da uwarka Jamila ce a gidan nan ba za ka saka aiki a gaba ka kasa zuwa ba.”

Anisa babbar ƴar Anti ta nuna rashin jindaɗin wannan furuci “abin kuma harda zagi Hajjo?”

“Fita ko ban guri ai ba kiranki nayi ba.”

“Ya Taj na biyo.”

Hajjo ta haɗe fuska tana neman abin duka “Duk gidan nan babu wanda ya isa ya yi min iko da ɗaki saboda haka get out.”

Taj da Anisa su ka saka dariya. Ita tana cewa “yeeyyyy, Hajjo ta tuno zama cikin turawa.”

“Zan zagi babanki wallahi. Zo ki fice.”

Kafaɗa Anisa ta noƙe ai kuwa Hajjo ta bita da daƙuwa hannu bibbiyu.
“Na iyayenki su uku.”

Alamun rashin jindaɗi Anisa ta nuna wanda Taj ya lura. Da ka ya yi mata ishara ta fita daga ɗakin.

“Hajjo sai ki yi ta zagar mana iyaye saboda Allah? Kinga bata jidaɗi ba daga ɗan yin wasa da kakarta.”

Lura tayi shima kamar bai jidaɗin ba sai kuma ta saki fuska. Ita a dole Taj ne kaɗai jikanta namiji na wajen babban ɗanta. Tunda ya koma hannun Amma bata taɓa canja masa ba. Saboda tun asali dama kakarsa wadda ta haifi Alhaji da ita ƙawaye ne da su ka yi ƴan matanci tare.

Ita ta fara zayyano masa ƙorafinta akan zaman Amma ita kaɗai a gida ga mijinta a wata uwa duniyar.

“Saura bai fi sati uku ba na koma in sha Allahu. Kuma zan zauna har tayi ritayar. Ai na san zamana ne sharaɗin da yasa ki ka yarda ta cigaba da aikin.”

Hajjo ta ƙara sakin fuskarta saboda Taj akwai iya tsara zance.

“Ka san ita mace bata tsufa da buƙatar kulawa. Yau ko ƙwan fitila ne ya mutu wata idan babu namiji a gidan sai dai ta zauna a duhu.”

Haƙuri ya sake bata da yaga ya samo kanta kuma ya yi mata bayanin gininsa da ya yi nisa.

“Shi uban taurin kan har yanzu baku daidaita bane?”

Dariya Taj ya yi. Kamar ba ita ta nuna ta daina ƴan mintuna ƙadan baya ba.

“An dawo kansa kuma?”

Ko a jikinta ta ce “Ai Hayatun ne akwai wuyar sha’ani sai ka rantse ni na haife shi. Don ita babar tasu haka take ba cas ba as.”

“Ahhhh. Ni fa Hajjo zan tashi wallahi. Harda kakata kuma.”

Yadda ya ɓata fuska sai da tayi dariya. Daga nan aka kashe maganar dawowar Amma. Sai kuma ta sako zancen da yake cin ranta. Dama can ba dawowar Amman bace a gabanta. Tafi kowa sanin halinta tunda a gabansu ta tashi. Ita ce ma ta haɗa auren nata da ɗanta. Da gangan ta tayar mata da hankali yanzu kawai don Taj ɗin yazo. Don tayi imanin indai yaji ba zai ƙasa a gwiwa ba zai zo neman sulhu.

“Tajo.”

Babu yadda ya iya. Dole yake amsa sunan nan da baya son a faɗi indai daga bakinta ne.

“Nace wai me zai hana ka nemi ƙanwarka Anisa ku daidaita? Karatunta sai gudu yake har an shiga aji huɗu a jami’ar nan.”

Gabansa yaji ya faɗi. Duk kirkin Hajjo kowa ya san rigimammiya ce ta buga misali. Yanzun nan sai ta yiwa mutum dabaibayin da zai sarƙe wuyansa bai sani ba.

Ƙofa ya kalla tana gama maganar “Hajjo daina faɗa kada ta zata gaske ne ta soma jin haushina don na tabbatar ba za ta rasa masoyi ba.”

Shan kunu tayi harda yi masa daƙuwa.
“Ƙaniyarka Tajo.”

Ya sunkuyar da kai yana sauraron sababinta.

“Da akwai wanin ai ka san ni ba mai yiwa jikoki shisshigi bace. Sannan na tabbata da daga cikin Jamila ta fito ba ma za ka ce komai ba.”

Hankalinsa tashi ya yi ya miƙe tsaye yana ɗan tausar kafaɗarta.
“Allah Ya huci zuciyarki. Ba haka nake nufi ba.”

“Za ka yi mata maganar ko na kirata yanzu?”

Gani ya yi za ta rushe masa ginin da bai fara saka tubali ba akan yarinyar nan Hamdiyya. Shi yasa da saurinsa ya ce ta bari shi zai yi.

“Alƙawari fa za ka yi min.”

“In sha Allahu zan yi mata magana.”

Tana jin haka ta washe baki hankali kwance. A ranar da washegari da zai taho bata sake tada wata rigimar ba. Daddy kawai ta kira ta ce masa tayi mai wuyar. Ya fara shiri don ba za ta zuba ido ya bar ƴan mata a gabansa babu aure ba. Da yaji waye zaɓin da ta yiwa Anisa sai taga ya fita farinciki. Kuma da murnarsa ya kira Amma ya faɗa mata. Sai ta nuna masa ta fishi jindaɗi domin ita ba butulu bace. Duk wata gudunmawa da ta dace financially da morally ya bata wajen kulawa da cikar burin Taj.

*

Rayuwa ta fara tsanani ga iyalin Abba. Da yake mutum ne mai sakarwa iyali aji daɗi da abin da Allah Ya hore masa, yanzu da ajiyar ta soma ƙasa sai suke ƙuntata. Yawancin samunsa in ka cire buƙatun gida to anyi amfani dasu wajen tarin kayan ɗaki da yake yiwa ƴan matansa. Komai na mutum uku yake saya. Yaya bata san yiwa ƴaƴa komai ba ta wannan fannin don bata sana’ar komai. Tun da ƙuruciya babu irin nacin da bata yi ba amma sam yaƙi yarda tayi saboda a cewarsa ta gama aikinta da ta aure shi. Nan kuwa yana tausayin lafiyarta ne. A ganinsa rashin imani ne zai sa ya sanya rai da ta dinga neman kuɗi a yanayin da take ciki. Gashi dama bai tsira daga dariya da surutun mutane ba. Idan ya bari tana shiga jama’a da sunan sana’a babu mamaki a karyar mata zuciya da zancen lalurarta. Shi yasa ya yiwa tufkar hanci da wurwuri.

Sauƙinsu ɗaya yanzu a gidan shi ne kitson da Sajida take yi. Hamdi kuma satinta biyu da dawowa gida Anti Labiban Abuja da ta zo Kano ta roƙi alfarmar tafiya da ita idan za ta koma. Kowa ya san miskilancin Hamdi idan ta so. Suna ta zaton za ta ƙi. Sai gashi da kanta ta amince za ta bita. Weekend na zagayowa kuwa su ka tafi.

*

Abin haushi da takaici da Taj ya tambayi Firdaus game da yarinyar da ta kasance overall a makarantarsu wai bata san komai a kanta ba.

“Ba ƙawarki bace?”

“Hamdiyya ai bata da ƙawa ko ɗaya. Sai da case ɗin babanta ya tashi ne ma ta ɗan sake da mutane.”

Interest ya nuna na son jin me ya faru da baban nata. Firdaus kuwa ta zage ta kora masa jawabi tiryan tiryan. Har hukuncin da makaranta ta ɗauka akan ƙawayen Ummi tunda ita an cireta.

Tana gama jawabin ta tashi tayi gaba abinta. Ta bar shi da shiga ruɗani da mamaki. Ba kuma komai bane ya sanya haka illa tuna sunan mahaifin Hamdi da kuma sana’arsa da Firdaus ta faɗa.

Tunani barkatai ya shiga yi game da yadda aka haihu a ragaya. Indai shi ne Habibun da Alhaji yake ƙyamar ya yi koyi da halayyarsa to yaya aka yi ya yi aure? Me ya faru da rayuwarsa? Kuma wace irin rayuwa yake yi yanzu?

Tabbas zai so sani. Shi Tajuddin zai so ƙwarai ya shiga cikin rayuwarsa ba don ƴarsa kaɗai da ta tarwatsa masa zuciya ba. Wasu burika ne suka mamaye zuciyarsa wanda zai so ya cimma in har shi ne wanda Alhaji ya sani ɗin.

Kwana biyar kacal su ka ɗauka shi da Kamal wurin neman Habibu Simagade na Soron ɗinki. Sai gashi an kai su har ƙofar gidansa. Mutumin da ya rako su magidanci ne amma har su ka isa hirarsa akansa bata wuce alkhairinsa da kyakkyawar tarbiyar ahalinsa ba.

“Ai wato banda ance kowa da ƙaddararsa da in kaga wani aka ce maka zai sami sauyin rayuwa sai ka ƙaryata.”

“Me yasa ka ce haka?” Kamal da Taj bai ɓoyewa komai ba illa son Hamdi ya tambayi mutumin.

Shi kuwa ya daina tafiya tare da binsu da kallon rashin yarda. Sannan ya nuna Taj.

“Ka ce min kai sana’ar girki kake yi. Ɗan uwanka kuma kasuwanci.”

“Haka ne.”

Da faɗa-faɗa ya cigaba da magana “zamanin yanzu ai babu yarda a tsakanin mutane. Da naji aikin naka na zata taimakon Habibu ka zo yi. Shi yasa ma zan kai ku gidan.”

Taj ya yi murmushi “sana’ar girki yake kenan?”

“Watannin baya ba. Kafin ƴan hassada su sako shi a gaba su ka ƙwace wurin da yake haya. Banda haka ko garau garau Habibu ya dafa maka wallahi sai ka ji bambanci.”

Duk surutun mutumin nan bai ƙara yarda ya đara daga inda yake tsaye ba yana jiran su faɗa masa gaskiya ko su waye su sai ga Abba ya fito. Daga yanayin tafiyarsa da kamanni da ya gani da Hamdi Taj ya gane shi. Kafin ya iso wurin da su ke ya tsaya ya fi sau huɗu yana gaisawa da mutane. Wannan abu ya sake burge Taj sosai har bai san lokacin da haƙoransa su ka bayyana da farincikin da ya shiga ba.

RAYUWA DA GIƁI 9

Batul Mamman💖

*

Irin kukan da Iyaa tayi bayan jin tsiyar da Ummi take shukawa dole ya bawa mutum tausayi. Bayan an kai ruwa rana a station ɗin da su ka je Baba Maje ya gane duk inda yake tunanin Ummi ta wuce nan. Fitina da gagara ta ƴan matanci kam tana bugawa a bayan idonsa. Ya sake yarda ba a shaidar ɗan yau. Ba don da bakinta ta amsa laifukanta ba da ya yi rantsuwar sharri ake yi mata. Ummin da ya sani daban. Wadda ya dawo da ita gida daban.

Abin baƙinciki shaiɗanin tsohon najadun da yafi kowa hure mata kunne Uncle B ashe makanike ne. Matansa biyu da ƴaƴa goma sha uku. Sau ɗaya ake ɗora tukunya a gidansa. Irinsu Ummi ke cinye ɗan abin da yake samu. Ita da yake tunanin raba hanya da ita saboda rashin bashi haɗin kai tuntuni ashe silarta asirinsa zai tono. Sai da ya yi sati guda a ƙulle kafin a yarda a bada belinsa. Shi ma kuma an haɗa masa da muguwar tarar da zai ji jiki wajen biya.

Hantara da kyara su suka marabceta daga dawowarta gida. Ta zama mujiyar da bahaushe yake kira mai baƙin jini. Iyayenta ba su dake ta ba don ciwon abin da tayi ya kai maƙura. Yayanta Baballe ne dai ya kasa zama bayan yaji kukan Iyaa yayi yawa a waya da tana labarta masa. Ya niƙi gari ya taho Kano ya sakar mata ƙarfinsa. Zaneta ya yi ciki da bai babu wanda ya hana shi. Sai ma dare da jikinta ya yi mugun tsami ne Iyaa ta tada ta zaune.

“Sau nawa ki ka zubar da ciki Ummi?”

Duk soyewar zuciyarta da ya hanata kukan dukan da ta sha wannan tambaya sai da tayi sanadin zubar hawayenta. Hannu ta ɗora akan bakinta tana danne kukan.

“Iyaa? Ciki kuma?”

“To Ummi meye abin mamaki a ciki? Samarin da su ke kashe miki kuɗi ƙannen uwa ne ko na uba da za a ce zumunci suke yiwa?”

Hawaye take ita ma ga tsoron kada Ummin ta amsa zargin da su ke yi mata ita da Baba Maje.

“Wallahi Iyaa ban taɓa yarda na bada kaina ba.”

“To me ki ke basu ko me su ke samu a madadin kuɗinsu? Don dai bana jin shaiɗancin naki ya yi tsamarin da za ki asircesu su dinga bin umarninki.”

Shiru Ummi tayi. Hankalin Iyaa ya sake tashi ta dinga kai mata duka da hannu ta ko ina.

“Ki faɗa min gaskiya kafin zuciyata ta buga.”

“Iyakarsu tattaɓani amma bana yarda da…”

Da sauri Iyaa ta tashi don bata son kuma jin ƙarshen zancen.
“Ya isa. Kin yiwa kanki.”

Fita tayi ta bar Ummi tana kuka. Kuma duk wannan abu bai zama ishara ya tuna mata yadda ta dinga cin zarafin mutane dole rana irin ta yau ta zo ba. Sunan Hamdi kawai ke yawo a zuciyarta. Ko harararta aka yi laifinta take ƙara gani. Musguna mata da ta dinga yi a makaranta ai bai shafi komai na karatunta ko rayuwarta ba a tunaninta. She was just having fun. Ba ita kaɗai bace senior mai yi wa na ƙasa da ita hawan karkatacciyar kuka, saboda haka bata ga dalilin da zai sa ita kaɗai ce rayuwarta ta kife irin haka ba. Da me ake so ta ji? Sanin waye Uncle B ko fitowar sirrinta? Ko kuwa rabata da makaranta a matakin ƙarshe da iyayenta su ka yi don ta ɗauki bidiyon ɗan daudu?

“Wallahi sai na rama Hamdiyya. Babu wanda ya isa ya saka ni kuka ban saka shi ba.”

Da wannan kalaman ta goge hawayenta a fusace ta kwanta tana shure Siyama da ƙafa don ta ɗan matso ɓangarenta cikin bacci.

*

Kwanaki sun ja inda a farko farkon watan August ɗaliban sakandire su ka kammala jarabawar fita. An yi WAEC har ta fito kafin a gama NECO. Da taimakon Allah da kuma dagewar karatu Hamdi ta sami kyakkyawan sakamako.

Kwana biyu bayan kammala jarabawar makaranta ta shirya gagarumin taron sallamar ɗalibai. Iyaye da ɗaliban suna shiryawa wannan rana wasu tun farkon shiga SS3. Ɗinkin ankon wata shuɗiyar atampa su ka yi mai adon fari da yellow. Tun kafin hutu aka fitar amma lokacin Hamdi bata ƙarɓi ƙyallen ba. Saboda ko kusa bata sa ran zuwa. Sai bayan faruwar lamarin nan taji a jikinta ta daina ɗararewa. Allah Ya taimaketa kafin a gama jarabawar lokacin visiting da Sajida da Zee su ka zo mata ta basu.

“Abba fa ya bar sana’arsa Hamdi. Ki haƙura kawai a kawo miki ko cikin kayan sallarki ne.” Zee ta faɗi bayan ta gama kallon atampar.

Mangareta Sajida tayi “Yaya bata gargaɗeki akan faɗa mata ba?”

“Gaskiya fa na faɗa mata don kada ta sa rai.” Zee ta bata amsa tana ƙunƙuni.

“Ya Sajida me yake faruwa? Ba don saboda ni ya daina ba?” Hamdi ta tambaya hankalinta na tashi.

Bayanin abin da ya faru su ka yi mata. Sannan Sajida ta ce kada ta damu in sha Allahu za a saya a ɗinka kafin ranar.

“Na haƙura.” Hamdi ta ce a sanyaye tana tuhumar kanta a matsayin wadda ta kasa godewa mahaifinta a lokacin da yake yi musu.

“Anti Labiba ce ta bani kuɗi da zan taho. Allah zan iya saya miki.” Sajidan ta bata amsa tana dariya.

Daga nan su ka koma wata caftar mai daɗi. Sajida tayi saurayi a Abuja daga zuwa taya cousin ɗinsu zaman jego. Mutumin da gaske yake. Yana aiki da rufin asirinsa. Ƴan maza zar su ke da mijin Anti Labiban (ƴa a wurin babbar yayar Abbansu Anti Zinatu).

Ƴan matan uku su ka haɗa kai su na ta murna kamar ma anyi auren an gama.

Zee ce ta dakatar da shewar tasu “Kin dai yi masa bayanin Abba ko?”

Fari Sajida tayi da idanu tana faɗaɗa murmushinta “Kada ku damu. Ya ce sai da su ka yi magana da mijin Anti kafin ma ya yi min magana. Yanzu dai ku sa rai da zuwansa nan da wata guda. Lokacin ma kin dawo gida ko?”

“Su Ya Sajida an fara kashe murya a waya kenan.” Hamdi ta tsokaneta.

“Zan ɗauko rahoto kafin ki dawo. Dama bata yi na gani ba don kada na fesawa Yaya.”

“Kin fa raina ni Zee. Ni da na raineki.”

Dariya Zee da Hamdi su ka yi. Ita Zee SS2 take don tsiransu da Hamdi babu yawa.

*

Aikin gini ya soma kankama son Taj ba ɓata lokaci ya zo yi ba. Shawarar Amma ya karɓa ya yi ginin a iya restaurant da shaguna ƙalilan. Wani Architect ya kwatantawa abin da yake so. Nan da nan aka zana masa plans kala uku. A ciki ya zaɓi ɗaya. Shi da Kamal kullum sai dare su ke komawa gida. Shi ya tafi gidan Ahmad, Kamal kuma ya koma don muddin ya kwana zai gamu da fushin Alhaji.

Tsarin da aka ɗauko ya bada ma’ana sosai. Gini ne da aka yi ɓangare uku manne da juna. Na tsakiyar yafi girma da faɗi kuma shi kaɗai ne aka ɗorawa bene. Na hagu anyi kitchen ƙato da komai domin aikin fulawa. Cake, doughnut, meatpie, samosa, pies da dangoginsu. A wadace yake sai dai babu wurin zama a ci a ciki. Idan mutum baya son fita akwai ƙofa da za ta sada shi da tsakiyar wato ainihin restaurant ɗin. Ɓangaren dama wanda shi dama za a fara tararwa shi kuma kana gani za ka san na masu gashin nama da kifi ne. Ko yanzu da ake matakin gini kaɗai kana gani zai burge ka. A tsakiyar sama gabaɗayansa kujeru da teburan zama ne. Sai wasu ɗakuna biyu domin masu gudanar da taron da zai iya cin mutane hamsin. Meeting, seminar, reunion da sauransu amma banda biki. Ɗakunan ɗaya normal ne ɗaya kuma VIP. A ƙasa ma da wurin cin abincin sai ɓangaren masu haɗa natural juice da za ayi bayan kayi order. Saii kuma makeken kitchen ɗin Taj da ma’aikatansa. Har ila yau a farfajiyar wajen an keɓe wani waje da aka soma tayar da garden. Za a ƙawata wajen da liluka da wajen guje guje da wasan yara. Sai kuma cikon alƙawarin da ya yiwa kansa. Zai gina madaidaicin boutique da gininsa zai kallon restaurant ɗin ya bawa Kamal amma bai faɗa masa ba.

Yau sun bar wurin duba aikin da wuri sakamakon zazzaɓi da ya rufarwa Taj gadan gadan. Kamar wasa ya ce kansa na ciwo, sai gashi kafin su isa gidan Ahmad yana rawar sanyi. Ɗauke hanya Kamal ya yi su na cikin tafiya. Taj ya ɗago kansa da ya yi nauyi da ƙyar ya dubi hanya.

“Sayar dani za ka yi don kaganni haka Happiness?”

Kamal ya yi murmushi “kwantar da hankalinka. Ai an taya kuma naji ba tsada za ka yi ba.”

“Ka ci bashi don sai na rama.”

“Allah Ya baka haƙuri. Yadda nake jin yunwa idan kayi fushi dani da alama Salwa ba za ta bani abinci ba yau.”

Wani irin kallo Taj ya yi masa na neman alaƙar fushinsa da cin abincin Kamal amma ya kasa ganewa.

“Wani abu ne ya haɗaka da ita?”

“No” Kamal ya bashi amsa mischieviously.

“Meaning?”

“A bar zancen sai ka warke.”

Taj bai matsa ba. Kansa kuɗa yake kamar zai cire. Asibiti Kamal ya kai shi duk turjiyarsa. Abu ya kai da ƙarin ruwa don likitan ya ce jikinsa babu kuzari. Gashi sakamakon gwaji ya nuna yana da malaria da thypoid duk shi kaɗai. Sun haɗe da rashin hutu sun kayar dashi lokaci guda.

“Amma ba kwana zan yi ba ko?”
Ya tambayi likitan bayan an gama saka masa canula a hannu.

“Ka godewa Allah da ka iya shigowa nan da ƙafafunka. Your temperature is abnormally high.”

Da Kamal ya barshi ya rufe ido don ya gaji sosai. Bayan fitar likitan da Alhaji yaji Kamal ɗin yana waya. Ya sanar dashi halin da yake ciki. Ƙaguwa ya yi yaji me Alhajin zai ce don kamar ya ƙwaci wayar a hannun Kamal. Ya dai daure har su ka gama. Shiru bai ji Kamal ya isar da saƙon Allah Ya ƙara sauƙi ba.

Sai da ya bari ya gama waya da su Inna da Ahmad sannan ya tambaye shi.
“Bai ce komai bane?”

“Yana hanya ne da alama ba ya ji na sosai” Ita ce kalmar da Kamal ya ƙirƙiro ya faɗa masa.

“Hmmm”

Kamal ya dawo kusa da shi “Happy kayi haƙuri sannan mu cigaba da addu’a.”

Abinka da ƴan dangi. Lokaci ƙanƙani asibitin ya fara cika da ƴan uwansu. Kowa ya zo faɗan rashin hutu yake yi masa.

*

Don son tabbatar da zarginsa, Kamal kiran Salwa ya yi ya faɗa mata bayan ya sanar da Ahmad. Tunda yaji ya ce baya gida shi ne ya kirata. Ai kuwa abin da ya yi tsammani yaji. Rikicewa tayi ba tare da ta sani ba.

“Ya Kamal yana iya magana?”

Ya yi murmushi “eh, ko in bashi ne?”

Da sauri ta ce “a’a” kunya na lulluɓeta da ta fahimci za ta bada kanta. Awa guda bayan sun yi wayar ta kasa sukuni. Jira take Zahra matar Ahmad tayi maganar zuwansu dubiya tunda tayi arba’in yanzu amma taji shiru. Bini-bini ta ɗaga waya ta duba lokaci. Da ta kai matakin da ba za ta iya haƙuri ba sai ta tambayi Zahran.

“Anti Zahra na ce ko sai Hayat ya taso in an kai shi islamiyya za mu wuce asibitin?”

Zahra ta zaro idanu tana laluben wayarta “ba ki da lafiya ne Salwa? Ina yake miki ciwo? Bari na faɗawa Daddy.”

“Ƙalau nake Anti. Dama maganar duba Yaya Taj ne.”

Zahra tayi murmushi “lahhh kada ki damu. Daddy ya ce zai biyo muje yanzu. Ke kuma ki zauna saboda Hayat.”

“In zauna?” Salwa ta ce ba shiri.

“Ina jin babu lallai ya kwana tumda yace min suna ta waya da Kamal. Meeting ne ya hana shi fita da wuri.”

Rasa bakin magana tayi ta fita kawai. Zahra ta bita da ido ba tare da kawo komai a ranta ba.

Da Ahmad ya dawo ko shiga gidan bai yi ba ya kira Zahra ya ce ta fito bayan la’asar. Kafin ta gama shirya Aisha Salwa tayi saurin fita wajensa.

“Ya Ahmad kana ganin daga gida ba za su fassara rashin zuwana duba shi ba ace don ba ɗan uwana bane?”

“Ke, gidanmu babu irin wannan kin ji. Bana son Hayat yayi missing islamiyya shi yasa nace ki zauna.”

“Naga kamar zamu iya dawowa kafin ya taso.”

Wani irin kallo mai tattare da tuhuma ya yi mata.

“To ko mu zauna ke ki je?”

Diriricewa tayi don bata tsammaci furucinsa ba. Ta ce “Haba Yaya ba haka nake nufi ba.”

Su na tafiya ta sake kiran Kamal ya ce mata jikin Taj da sauƙi. Don ya ƙara rura wutar da ya fahimci ta soma cinta ya ce
“Yanzu dai ya gama amai wallahi. Ya galabaita sosai don ko zama ya kasa. Amma dai da sauƙi za a ce.”

“Kace ina masa sannu don Allah” ta ce da muryar kuka.

“Ban gane ba. Ba za ki zo ba?”

Da sanyin murya ta ce “Ya Ahmad ya ce na zauna.”

Tausayi ta bashi ya daina ɗorata. Yana ajiye wayar ya yi murmushi “shege Happy. Daga zuwa ya yi ɓarna a zuciyar ƴar mutane.”

Wasa wasa sai da Taj ya yi kwana biyar aka sallamo shi. Kuma tun washegarin kwanciyar tasa kullum sai Salwa ta je. Duk wani motsinta Ahmad ya kafa ya tsare har ya tabbatar da zarginsa. Hankalinsa kuwa ya tashi don yana jiye mata abubuwa da dama.

*

Takarda ce cikin foolscap Hamdi take ta karantawa tun wajen kwana uku tana son haddacewa. Speech ne malamar English ta bata wanda za ta yi ra ranar taron. Cikinta har ƙullewa ya yi yau da aka kira assalatu saboda tana da tsoron yin magana a gaban mutane. Har aka gama yayin monitoci da mataimakansu da ma prefects bata taɓa karɓa ba. Komai na mutane gudu take. Sai gashi wannan karon Principal da kanta ta ce a bata. Wai jawabin godiya ne a matsayinta na overall student ta makaranta. Da shawarwari ga ƴan uwanta ɗalibai akan hanyoyin bi domin samun nasara.

Ga dai takarda ko daga bacci ta farka za ta iya kawota tas da ka, amma da zarar tayi tunanin mutanen da za ta fuskanta sai taji kan ya koma fanko. A haka ta janyo jiki ta zo wajen taron tamkar mara lafiya. Ana tsakar gabatar da shirye shirye ta tashi kafin a zo kanta. Bayan Admin block taje ta sami wuri ta zauna tana ta bita kamar mai zuwa musabaqa.

*

A cikin dandazon mutanen da su ka zo taron harda ƴaƴa da jikokin Alh. Hayatu Sule. Akwai jikarsa Firdaus ƴar wajen babbar ƴarsa Hajiyayye cikin masu fita. Yarinyar mutuniyar Taj ce sannan bata san ya zo gari ba. Rabonta da shi tun tana ƴar ƙarama. Shi yasa da Hajiyayyen ta gayyaci ƴan uwanta zuwa graduation shi ya fara amsawa zai je. A cikin hayaniyar programs ɗin da ake gabatarwa da hirar ƴan uwansa yaji wayarsa tana vibrating. Sunan Amma ya gani ba shiri ya tashi yana neman wurin da zai iya amsa wayar ba tare da hayaniyar ta hana shi jin me take cewa ba. Kamar ance ya kalli damansa ya hango wata yarinya tana tafiya da sauri sauri ta nufi bayan Admin block. Sanye take da ankon ƴan graduation ɗin da gown ɗinsu. Ta riƙe hular a hannu. Ɗaurinta na Maryam Babangida ya zauna đas a kanta. Sai ɗan mayafi da ta yafa a kansa ta rufe wuyanta da shi.

Numfashinsa kusan ɗaukewa ya yi da ganin yarinyar kamar yau ya fara ganin mace. A kallon farko ya iya tantance tsayinta da yake matsakaici. Fatarta da yake iya gani a fuska tayi daidai da wankan tawarɗa da ake kiran masu sirkin fari da baƙi. Fuskar ya sake kallo wadda ta fizgi duk wani rational tunanin dake yawo a kansa. A cike take da duk wani abu da yake muradi a wurin mace. Ga ƙarin kwarjini da nutsuwa da yake da yaƙinin tana da su daga yanayin tafiyarta. Wayar da yake son ɗauka tuni ya manta da ita har ta katse.

Kamar ana ingiza shi ya bi ta. Idanunta a rufe lokacin da ya hangota. Ta sanya hannu ta rufe kunne tana karanto abin da ta haddace.

Sannu a hankali ya dinga takowa gabanta har ya rage babu nisan kirki a tsakaninsu.

Ƙamshin da Hamdi taji yana ta kusanto ta ne ya hanata buɗe ido. A zuciyarta ta gama tsorata don an saba faɗin akwai ƙwanƙwamai a bayan Admin block. Wai ba a ganinsu sai dare. To me ya fito dasu da hantsin nan lokacin da ake ta kai kawo a makarantar?

Taj na jin yadda ta ja numfashi ta kasa saukewa da ya matso. Ya saki murmushi.

“Buɗe idonki.”

Hamdi ta tsuke baki don in ta sami wuri akwai tsiwa. To yau dai aljanu za ta nunawa bata tsoronsu don kada su maketa a banza. Ta sha jin labarin idan baka nuna tsoronsu ba, ba sa yiwa mutum komai.

“Anƙi ɗin. Tsakanina da aljani nan gani nan bari. Na riƙe Ayatul Kursiyyu.”

Dariya Taj ya yi a hankali ya a jin wani irin abu na bin jikinsa.

“Ni ba mai cutarwa bane so you can open your eyes.”

Ido ɗaya ta ɗan buɗe a hankali ta tabbatar mutum ne sannan ta buɗe ɗayan. A lokaci guda idanuwansu su ka sarƙe cikin na juna sai dai Hamdi bata iya zurfafa kallon ba ta kawar da kai. Babu abin da zai sa ta iya jurewa kallon idanun mutumin dake gabanta masu kaifi da su ka tsareta. A zuciyarta kuwa sai da ta kira sunan Allah saboda tunda take bata taɓa ganin wani namiji taji ina ma ace….ba sai a kan wanda yake gabanta.

A daidai lokacin su ka ji sanarwa ta sipika.

“Bayan wannan gajeriyar diramar da za ayi mana mai taken Ilimi a Karkara, za mu saurari speech daga bakin overall student ɗin makarantar nan Hamdiyya Habib.”

Wani haɗaɗɗen ruɗani Taj ya gani a idanun yarinyar gabansa. Da haka ya gane ita ce aka ambaci sunanta.

Takardar hannunta yaga ta kalla kamar za ta yi kuka.

“Kin taɓa ganina?”

“A’a.”

“Good. Ki yi imagining ni ne duka mutanen wurin can sai ki yi speech ɗin naki na ji.”

Kamar ta ce a’a sai dai ta gyara tsayuwarta. Ta rufe ido.

“Open your eyes and think of …” ya kalleta “Wa ki ka fi so a duniya?”

“Iyayena.”

“To ni ne su. Ki sa a ranki su kaɗai ne a wurin.”

Sallama tayi da rawar murya ta soma da gabatar da kanta amma ta kasa faɗin sunanta ma. Sai komawa baya take yi. Taj ya karɓi takardar ya dunƙuleta a cikin hannunsa bayan ya karanta a gurguje.

“Bayan godiya ga school da iyayenki za ki bawa students shawarar karatu. Do you realy need a paper to say all that?”

Hamdi ta ƙifta idanu “no.”

“Then say what you truly want to say from your heart. You will be fine in sha Allah.”

Haka kawai magana da shi ta sanya mata wata irin nutsuwa. Ta tattare doguwar rigarta sama kaɗan ta dube shi da murmushi a fuskarta.

“Thank you.”

Ya so sake cewa wani abu amma tunawa da ya yi tana buƙatar nutsuwa kafin ta iya yin abin da ke gabanta sai ya barta ta tafi. Ya raya a zuciyarsa idan an gama taron zai nemeta.

RAYUWA DA GIƁI 11

Batul Mamman💖

Yadda ya gaisa da kowa da zai wuce haka ya tsaya su ka yi musabaha da wanda ya rako su. Sannan ya ɗagawa Taj da Kamal hannu yana ɗan ranƙwafawa kamar yadda ya gaisa da sauran mutanen da su ka gani.

“Ƴan samari barkanku dai. Ya sanyi sanyi? Ya ayyuka? To Allah Ya yi jagora.” Ya dubi mutumin da da ya yi mu su rakiyar ya ce “na barku lafiya.”

“Dakata Mal. Habibu. Waɗannan fa kai su ke nema.”

Tsayuwa ya yi ya sake kallonsu sai dai bai tuna taɓa haɗuwa dasu ba.

“To Allah dai Yasa lafiya” ya ce muryarsa na raguwa saboda rashin sanin ko ba da alkhairi su ka zo ba.

Kamal ne ya amsa masa “lafiya ƙalau.” Sannan ya gabatar da kansa da Taj.

Jin cewa Taj chef ne kuma a yanzu haka ginin restaurant yake sai Abba ya sami kansa da daina saurin zuwa uzurin da ya fito dashi. Zancen bai wuce fita nema ba dama.

“Dama nayi tunanin maganar ba za ta wuce ta ɗaukarka aiki ba. Shi yasa na rako su. Bari na wuce.”

Abba ya yi masa godiya sosai sannan ya nunawa su Taj gidansa. “Ko mu ƙarasa daga soro mu zauna?”

A duk lokacin da ya yi magana sai Kamal yaji zuciyarsa ta karye. Allah Ya sani a yau ya daina ganin baƙin Alhajinsu. Tabbas da wannan rayuwar Taj ya faɗawa da shi ma sai ya yi kuka ba iyayensu ba. Ta yaya zuciya za ta jidaɗin ganin namijin da ya cika a halitta yana irin wannan muryar? Don ma bai san lanƙwasar jikin da sauƙi yanzu ba.

Gidan su ka bi shi. Daga soron ya ɗaga murya yana ta kiran sunan Zee amma sai da ya yi kamar sau biyar su ka ga ƴar budurwa ta fito a guje. Don shi Kamal ji ya yi kamar ya taya shi kiran saboda muryar ba ta tashi yadda ya dace.

“Abba yi haƙuri ban ji ba ne.”

Mutanen da ta gani tare dashi ne yasa ta saurin komawa da baya don bata fito da lulluɓi ba. Ta bayan ƙofa ta gaishe su. Su duka biyun yadda tayi ɗin ya burge su sosai.

“Tabarma za ki kawo da ruwa.”

Bata jima ba ta dawo da hijabi a jikinta ta shimfiɗa tabarmar. Abba ya sake gaisawa dasu sannan ya buƙaci jin neman da su ke yi masa.

“Kamar yadda ɗan uwana ya faɗa maka gidan abinci nake ginawa. To sai na sami labarinka a wajen mutane. Duk da ba haka ake so ba ance ka rasa wurin sana’arka.”

“Eh. Amma yanzu ma haka wani waje zan je dubawa. Idan mun daidaita sai na kama haya.”

Babu wani dogon tunani ko shawara Taj ya ce “hayar kafi so ko za ka iya aiki tare dani?”

“Kai da baka gama gini ba Happy? Zai yi ta jira ne har lokacin?” Kamal ya yi saurin katse shi.

“Me ya kawo ku wurina tsakani da Allah?” Abba ya tambaya da sakin fuska.

“Aiki nake so mu yi tare amma wurin nawa da saura kamar yadda ya faɗa maka. Ina so nayi recruiting ma’aikata da wuri kafin na gama ginin.”

Kamal da ya yi zaton ganinsa kawai su ka zo yi sai yaji hankalinsa bai kwanta ba. Me yasa Taj yake neman abin da zai ƙara nesanta shi da Alhaji? Ina shi ina aiki da wannan mutumin daga jin ance baya aiki?

Abba ya ƙare musu kallo sai ya yi murmushi. Da alama shawararsu bata zo ɗaya ba don yaga irin kallon da Kamal yake yiwa Taj.

“Samari nagode amma ina mai baku haƙuri. Ina da mata da ƴaƴa huɗu. Zama haka a yanzu ma yana damuna balle kuma na wasu watanni. Sannan ina da ma’aikata biyar da har yanzu dani su ka dogara.”

Kuɗi Taj ya ciro daga aljihunsa da sauri.
“Zan fara baka albashi tun yanzu kafin mu fara aikin.”

“Happy!”

Taj ya yi biris da Kamal. Shi kuwa bai barshi ba ya dubi Abba da kyau.

“Kayi haƙuri don Allah. Bari mu tafi.”

Taj ya ɓata fuska “Da gaske nake ina son aiki da shi Happiness.”

Abba sai ya nuna kamar bai ji haushi ba. Yana ƴar dariya ya yi musu godiya kawai ya tashi. Kamal kuma haƙuri ya yi ta bashi sannan ya janye Taj su ka tafi. A mota kuwa kafin su isa gidan Ahmad anyi faɗa kaca-kaca.

“So kake Alhaji ya mutu da baƙincikin ka ko me? Kai yanzu rayuwarka tana yi maka daɗi?”

“Kai baka ji komai ba da aka ce bashi da aiki yanzu?”

“Sai ka taimaka masa da kuɗi.” Kamal ya ce har zuciyarsa.

“Are you serious? Yanzu da aiki da kuɗi wanne ya fi?”

Da wannan cacar bakin su ka koma gidan. Don takaici Kamal ko shiga bai yi ba. A waje ya sauke shi ya tafi.

“Masifaffe.” Taj ya furta yana harar motar.

*

Ikon Allah Zahra ta gani yau tun dawowar Salwa gida. Kwananta shida a Bauchi da aka yi musu gajeren hutum mid-semester. Abin da aka bayar da kwana goma har weekend ya kama shabiyu, a daddafe tayi shida ta dawo. Ƙarya ma ta yiwa mamansu wai field work za su je. Da yake Agricultural Extention take karantawa. Nan kuwa kewar Taj ce ta isheta har tana neman zautar da tunaninta. Abin baƙinciki kuma shi ne tunda ta tafi ko sau ɗaya bai kirata ba. Ita ce ma da ta gaji tayi masa waya harda ɗan ƙorafi.

“Idan mutum yaje gida baya son damu Salwa. Tunda ba daɗewa za ki yi ba gara duka time ɗin ki ya zama na family.”

Ji tayi kamar ya faɗa mata magana. Ta daure ta ce “Ba ka cikin family ɗina kenan?”

“In ji wa? Idan kin dawo zan baki wayata ki gani a yanzu zan chanja yadda nayi saving sunanki.”

Zuciyarta ta harba da wani irin farinciki ta ce “me za ka saka?”

“Ƙanwata Salwa. Yadda nake saving sunan ƴan gidanmu. Manyan kuma ina saka musu Yayata” Kuma bai barta ta gama jin haushin hakan ba kamar shi ys kira ya ce “bari na barki ki huta haka. Sai da safe.”

Azahar a Kano tayi mata. Tana zuwa gidan ko hutawa bata yi ba ta karɓi girkin dare. Zahra tana ta faɗa mata ta jira ayi la’asar amma ta ce gara tayi da wuri tunda tuwo ne. Daga nan ta haɗa juice ɗin abarba, mangwaro da ɗanyar citta saboda ta kula Taj yafi son fresh fruit juice. Da su ta taho tun daga Bauchi.

Bayan tayi sallar la’asar ta shiga ɗakin Taj. Yana ƙullewa idan zai fita amma baya taɓa zare key ɗin. A cewarsa tunda masu gidan suna da kaya a ciki me yiwuwa za su buƙaci shiga idan baya nan.

“Salwa me ki ke nema a nan?” Zahra ta taho da sauri da taji alamun buɗe ƙofar.

Tsintsiya ta sameta tana gyarawa ɗauri. Tana ganinta tayi murmushi.
“Anti Zahra gyara ɗakin zan yi.”

Curiosity yasa Zahra ta ɗan leƙa. Baya buƙatar wani gyara na a zo a gani.

“Yana gyarawa. Ki fito don yayanki sai da ya yi min warning akan bari ke ko mai aiki ku shiga ɗakinsa.”

“Yau ɗaya dai Anti. Ai gara ayi masa gyara sosai. Tunda baya gida zan yi sauri.”

Tafiyarta tayi ta soma da wankin toilet. A sink inda ya tara boxers da singlets da socks ta haɗa komai ta wanke. Sai ta bar masa a bucket yadda zai shanya idan ya dawo. Wankin ma ana yi ana rurrufe ido saboda kunyar da ta dinga ji. Ɗaki ya fito fes dashi don har bedsheet sai da ta canja masa. Bayan ta gama komai ta rura gawayi akan gas cooker ta wuce da robar turaren wutan da ta siya online. Tun Zahra na bin ta da ido har tsananin mamaki yasa ta koma cewa ‘uhmmm’. Yau ko ɗakin miji ne aka yiwa haka ai dole ya yabawa matar balle wanda a iya saninta babu soyayya a tsakaninsu.

Ahmad ne ya fara dawowa gidan. Lokacin tuni Salwa ta gama har tayi wanka. Doguwar rigar atampa ta saka da ƙaramin mayafi ta zauna a falo tana ta ƙamshi. Wannan karambani duk aminiyarta ce ta kitsa mata. A cewarta da kyautatawa ake sayen soyayyar namiji. Jindaɗin yadda take kula da shi zai kwaɗaita masa mallakarta a matsayin matar aure.

Wuraren ƙarfe biyar da rabi Taj ɗin ya shigo da sauran fushin faɗansu da Kamal. Sama sama ya gaisa da Ahmad. Ya ɗauki baby Aisha bayan gaisawa da Zahra. Salwa kuwa sai da tayi masa magana ya kula da ita.

Ya dakata da tafiya “Har hutun ya ƙare? Ko dai kin dawo birnin da yafi ƙauyenku?” Ya ce da ita da zolaya.

Murmushi kawai tayi. Ahmad ya girgiza kai. Dama tunda ta dawo da wurwuri ya san ba zai wuce saboda taji cewa Taj ya kusa komawa bane.

Da Aisha ya shige ɗaki a kafaɗarsa ya kwantar da ita a kan gado. Ya yi mamakin yadda ya sami ɗakin. Waye ya gyara? Komai an killace shi gwanin sha’awa. Ya shiga toilet nan ma ƙamshi kawai yake tashi. Da sauri ya duba sink da ya tuna ya bar kaya da zai wanke sai yaga babu. Nan fa yaji wani abu ya taɓa masa rai. Yana duba bokiti kuwa sai gasu a wanke an matse. Ya fiddo gajeren wandonsa ɗaya ya tabbatar dai a wanke yake. Bai san lokacin da ya sake shi a bokitin ba. Ya ɗauki Aisha ya koma falo fuska babu annuri.

“Anti Zahra waye ya gyara min ɗaki ne?”

Ahmad ya yi saurin kallon Zahra ita kuma ta nuna Salwa dake faman doka murmushi tana sunkuyar da kai. Sauƙin hali irin na Taj bai hana shi nuna ɓacin rai ba kuwa.

“Ke ki ka wanke min underwear?”

Idanun Zahra waje su ka yo. Ahmad kuwa bai san lokacin da ya ce “underwear kuma?”

Da me tambayar da kuma yanayin maganar Ahmad sai Salwa taji tsoro.

Taj ya murtuke fuska.
“You shouldn’t have. Next time please kada ki taɓa min.” Ya duƙa ya miƙawa Zahra ɗiyarta sannan ya dubi Ahmad “Yaya zan ɗan kwanta kafin magrib. Da headache na dawo.”

Shigewa ya yi ya barsu. Da Zahra taga irin kallon da Ahmad yake yiwa Salwa sai ta tashi tsam ta shige ɗaki.

Ai kuwa kamar jira yake ya soma faɗa.
“Wannan wane irin rashin daraja kai ne haka Salwa? Are you crazy or what?”

Kai ta sunkuyar tana kuka. Ba kuma na faɗan yayanta ba. Fushin Taj da tsoron kada gwanintar ta tayi sanadin nesanta ta dashi kawai take gudu.

“Ba tun yau na kula kina son Taj ba…” sai a lokacin ta kalle shi hankalinta na tashi. Ya taɓe baki “wanda bai damu da lamarinki bane kawai ba zai gane ba.”

“Yaya…”

Tausayi ta bashi don ta soma kukan gaske. Amma hakan ba zai hana shi faɗa mata gaskiya ba.

“Kin san komai dake faruwa a gidanmu da dalilin zamansa a gidan nan. He is trying his best ya daidaita da Alhaji. Kina tunanin soyayyar Taj dake, ƴar matar da ya saka zai faranta masa rai?”

A tsorace ta kalle shi “Yaya ni meye laifina?”

“Salwa kin fini sanin rigimar Mama tunda a gabanta ki ka tashi. Ke shaida ce irin yadda ta fitini Abbanku. Abubuwan da take yi bana jin akwai wanda Alhaji bai sani ba. Tun da in naso zuwa wajenta hutu baya son bari saboda yana gudun kada na koyo abin da zai haɗa rigima a gidanmu.”

Hawaye ta goge da mayafinta. Da muryar da kuka ya gama dusashewa ta ce “To ni yaya zan yi? Ba ni na ɗorawa kaina ba”

“Kada ki yi komai sama da neman zaɓin Allah. Sai kuma tsare mutumci da darajarki ta mace. Ke kin sani da ina nan ko ɗakinsa ba za ki shiga ba. Ba kuma don ban yarda dashi ba. Amma wankin underwear…haba Salwa? It was totally wrong.”

Daga ƙarshe rarrashinta ya yi da jaddada mata lallai kada ta ƙwallafa rai akan Taj domin indai Alhaji bai amince ba da wuya ya aureta.

*

Hutu yana ta daɗi. Hamdi ta zaga gari sosai da Anti Labiba da yaranta. Basu da ƴan uwa sosai a garin sai abokan arziƙi. Shi yasa yawon nasu yafi ƙarfi a wuraren shaƙatawa da ciye ciye.

Wata rana sun dawo da yamma liƙis Anti Labiba ta ce da Hamdi ta ɗora abinci. Tayi tuƙi ta gaji ga bebinta na ta tsala ihu. Ɗaki ta shiga domin yiwa yarinyar tsarki amma har ta fito Hamdi bata ɗora komai ba. Gyaran kitchen ɗin take yi saboda ana gama cin abincin rana su ka fita.

“Hamdi baki ji na ce ki ɗora jallof ɗin macaroni ba?”

Murmushin ysƙe tayi “Anti Labiba don Allah ki ɗora. Duk wani yanke yanke zan miki.”

Ƙanƙance ido Anti Labiba tayi. Sai kuma ta tuna wata hirarsu da Sajida lokacin da ta zo mata zaman biƙi. Tabbas ta faɗa mata a duniya babu abin da Hamdi taƙi jini bayan namijin da ya iya girki kamar girkin kanshi. Ita duk abin da za ta ɗora akan wuta mai suna abinci zuciyarta bata son yi. Ba kuma komai ya janyo ba illa tsohuwar ƙiyayyar da take yiwa sana’ar Abbansu. Kuma fa da yake a wurinsa ta koya da wuya ka ci abincinta baka yi santi ba.

“Baki iya girkin bane ko me?”

“Idan na dafa ba lallai na iya ci. Don Allah ki ɗora kinji Anti…”

Sosai abin ya bawa Anti Labiba mamaki. Hamdi bata taɓa yi mata ƙiwar aiki ba. Ga iya sammako ta gyara gida tun zuwanta. Amma fa duk cikin aikin nata bata taɓa yin girki. Ita kuma Anti Labiba bata damu ba saboda mijinta baya son cin girkin mutane musamman a gida.

Abincinta tayi ta gama. Hamdi sai taji babu daɗi don sai da aka matsa mata taci abincin. Bayan sun gama ta bita ɗaki ta bata haƙuri.

“Ni ban yi fushi ba. Kawai ina mamakin yadda aka yi ki ka zafafa akan harkar girkin nan.”

“Idan ina yi sai Abba ya dinga faɗo min a rai. Wallahi Anti Labiba bana son ganin shi a kitchen kwata-kwata. Yanzu ma ina ta fatan Allah Yasa ya sami wata sana’ar tunda an karɓe gidan abincin.” Magana take yi muryarta tana rawa.

Anti Labiba ta saƙala hannunta a kafaɗarta.
“Nayi zaton kin daina abubuwan da ki ke yi da naga yanzu kullum sai kun yi waya dashi.”

“Ni me nake yi?” Ta tambaya da zumɓura bakin.

“Babu komai.” Ta shashantar da zancen “snacks da pastries fa? Su ma kamar girki ki ka ɗauke su?”

“Don ban iya bane amma ina so.”

“Saboda basa cikin girkin da Abba ya koya mu ku ko?”

Sunkuyar da kai Hamdi tayi a kunyace. Ita kuwa Anti Labiba sai wani tunani ya ɗarsu a zuciyarta. Ba dai za ta ce komai ba sai ta tuntuɓi ƙawarta Hauwa gobe. Idan Hamdi tayi sa’a za ta koyi small chops da youghurt from one of the best a garin Abuja.

*

Kwana biyu Taj ya yi baya zuwa site ɗin aiki. Idan Kamal ya zo sai ya ce kansa na ciwo. Abu ya taru ya dami Kamal sosai. Lokacin tafiyar Taj na gabatowa amma ya sanyawa ransa wani abu daban. Shi kuma yafi son ko zai tafi ya zamana aikin da ya rage ba mai yawa ba. Gara aci ƙarfin komai a gaban mai wurin.

Yau da ya bar gidan Ahmad wucewa ya yi gidan Abba Habibu. Bai wahala wurin gane gidan ba. Shaɗaya na safe ta ɗan wuce. Ya tura wani yaro ayi masa sallama da shi. Wata budurwa ba wadda ya gani a zuwansu na farko ba ce ta fito ta gaishe shi.

“Abba ya fita amma yanzun nan zai dawo. Ba nisa ya yi ba.”

“Ke ma ƴarsa ce?” Kamal ya kasa daurewa sai da ya tambaya. Ita da ta rannan da ya riƙe Zee aka kirata su na kama sosai. Kyawawan ƴan mata ne masu nutsuwa.

“Eh.”

“Yaya sunanki?”

“Sajida.” Ta amsa masa.

Kujerar roba ta kawo ta ajiye masa a soron ta koma ciki. Kimanin minti goma a tsakani sai ga Abba ya dawo.

Mamakin ganin Kamal ya yi sosai. Su ka gaisa sannan Kamal ya ɗan rissina kai.

“Na san za ka yi mamakin dawowata bayan yadda nayi a wancan zuwan namu.”

“Babu komai. Allah dai Yasa lafiya.”

“Alhamdulillah”

Shiru ya kuma biyo baya har sai da Abba ya sake tambayarsa sannan ya yi magana. Da farko ya fara da bashi labarin burin Taj tun ƙuruciya da duk wani abu da ya biyo baya.

“Wallahi ban hana shi don ƙyama a gareka ba. Amma indai Alhaji ya sami labarin kuna tare bana jin zai zai yafewa Taj.”

Kallonsa Abba ya yi sosai yana jinjina kai “to amma a ina mahaifin naku ya sanni.”

“Soron ɗinki. Shi ma mutumin cikin gari ne.”

A karo na uku Abba ya sake ƙurawa Kamal idanu na wasu ƴan daƙiƙu sannan ya yi murmushi.

“Yaya Hayatu ne mahaifinku?”

Da sauri Kamal ya kalle shi “ya akayi ka gane?”

“Da gaske ku ƴaƴansa ne?” Abba ya kuma tambaya yana miƙewa tsaye.

“Ƴaƴansa ne.” Ya faɗi yana gyaɗa kai.

Jiki a matuƙar sanyaye Abba ya ce. “Ka faɗawa ɗan uwanka kada ya sake zuwa gidan nan. Kai ma ka tashi ka tafi.”

Kamal bai jidaɗin yadda Abba ya koma ba. Da alama ba mutum bane mai son hayaniya. Amma jin waye mahaifinsu ya canja yanayinsa. Hannu ya sanya ys fiddo dubu ɗarin da ya tanada tun a gida.

“Ga wannan ka ƙara jari don…”

“Ɗauke kuɗinka yaro. Bana so ko da wasa Yaya Hayatu ya yi tunanin da gangan na kusanci rayuwarku.”

Ciki ya shige ya bar Kamal riƙe da kuɗin yana fargabar yadda za su kwashe da Taj idan ya sami labarin zuwan nan nasa.

RAYUWA DA GIƁI 12

Batul Mamman 💖

*

Da gaske ciwon kai ke damun Taj saboda bai iya sanya abu a rai ba. Ya so ƙwarai ya ja Abban Hamdi a jiki. Ba don neman soyayyarta ba, wannan da kansa zai yi ba ya buƙatar taimakon kowa sai Allah. Mahaifinsa yake son nunawa a rayuwa kowa da ƙaddararsa. Kuma a kowacce sana’a indai ba addini ne ya haramta ta ba, akwai mutumin banza da nagari. Don al’ada ta ƙyamaci wani abu ba shi yake nufin yinsa laifi bane. Sannan uwa uba akwai uzuri ga ƴan Adam domin ba kowa ke dawwama cikin saɓo ba.

A ganinsa rashin aikin Abban Hamdi wata hanya ce ya samu da zai iya sako shi cikin tasa sana’ar. Idan Allah Ya sanya musu albarka kasuwa ta buɗe Alhaji zai iya fahimtar kowanne bawa akwai hanyar arziƙinsa. Sannan ko iyaye ba sa so indai Allah bai haramta ba sannan ɗan bai kasance mai saɓawa kowa ba, albarka za ta iya binsa duk inda yake.

Ƙarar wayarsa ce ta tashe shi daga kwanciyar da ya jima yana yi. Sunan Salwa da ya gani ya sanya shi yin tsaki. Ita bata san gudunta yake yi ba? Har yau yana mamaki da bata yi tunanin kamar yadda mata ke killace kayansu na ciki haka kowanne namiji da ya san mutumcin kansa yake yiwa nasa ba. A iya saninsa ƙiwa da rashin son aikin namiji ba zai sa ya bawa ƙanwarsa shaƙiƙiya wankin ƙananan kaya ba. Ballantana kuma wadda babu wani abu da ya haɗasu.

Bari ya yi kiran ya katse sannan ya kirata.

“Don Allah ka buɗe min ƙofa na manta muƙullina a ciki.”

Falo ya fito sanye da dogon wando na sanyi ruwan toka da farar shirt. Ya buɗe mata jamlock ɗin ya juya zai koma ɗaki sai ta kira sunansa.

Tun ranar da ta gyara masa ɗaki da faɗan da Ahmad ya yi mata ta rage kuzari da karsashi a komai. Fargabarta ita ce ɓacin ran da ta gani tare da Taj da kuma shawarar da Ahmad ɗin ya bata akan ta cire shi daga ranta. Da za ta iya da tun kafin ta zubar da ajinta ta cire shi ta ƙarfin tsiya tunda ta fahimci bata gabansa ta fuskar da take so.

Sake kiransa tayi da bai juyo sosai ba.

“Ya Taj don Allah ka yi haƙuri akan abin da ya faru rannan. Na fahimci kuskurena.”

“Ya wuce, kada ki damu.”

Fasa tafiya ya yi da ya tuna ƙanwar Ahmad ai ƙanwarsa ce shi ma. A matsayi guda duk su biyun su ke zaune a gidan. Shi yasa yaga dacewar ya bata shawara.

“Ko don gaba ki kiyaye irin wannan. Ba ni ba, ko Yaya ki ka wankewa undies bana jin za ki burge shi.” Kai ta sunkuyar sai ya yi murmushi “ku mata ba kwa son a taɓa koda jakarku. So just imagine ace ni nayi miki wannan karambanin. Will you realy be happy that I helped?”

Kunya maganar tashi ta bata. Ta rufe ido ta shige ciki da sauri tana mayar da numfashi. Da tunanin yadda ya yi maganar a tausashe ta ƙarasa ɗaki. Sai da cire kaya za ta shiga wanka ta kuma tariyo zancen sai taji faɗuwar gaba. Shin magana ya yaɓa mata ko kuwa ya sauko ne?

Domin tabbatar da matsayin maganar da sai ta tura masa SMS da yamma da ya fito falo suna hira da Ahmad. Daga kitchen ta leƙo bayan ta tura tana kallonsa ya duba saƙon, ya kuma rubuta reply. Da wani irin sauri ta koma ciki ta buɗe. Nata ta fara bi inda ta rubuta masa saƙo kamar haka.

(Ya Taj nagode kuma ina mai sake baka haƙuri. If I am forgiven please give me a chance to be your friend.)

Shi kuma ya rubuta wannan amsar.

(Kada ki matsawa kan ki da son neman wani relationship dani bayan already akwai. Ƙanwar Yaya Ahmad ƙanwar Taj ce.)

Ranar da ƙyar ta gama girki. Saƙon dake cikin amsarsa ya fito ɓaro ɓaro. A matsayin ƙanwa kaɗai ya ɗauketa. Daga yau za ta gwada cire shi daga zuciyarta. Sai dai abin da wuya domin son bai yi shawara da ita ba ya yi mata kamun kazar kuku.

*

Faɗa Yaya take kamar ta ari baki a waya. Sajida da Zee su ka matsu ta gama ta basu labarin me ya faru. Sun dai fahimci Hamdi ce tayi wani laifin. Ita kuma Anti Labiba da su ke wayar banda dariya babu abin da take yi.

“Abin dariya ki ka ɗauki abinnan Labiba? Wace ƴar arziƙin ce za ta guji girki kamar ba mace ba?”

“Yaya ki barni da ita don Allah. Na faɗa miki ne fa kawai saboda kada ku ji shiru bata dawo ba. Zan ɗan riƙeta ne in sauke mata gammon da ta ɗauka.” Cewar Labiban tana murmushi.

Yaya ta gyara zama tana hararar masu matsowa jikinta don son jin me ake cewa “amma fa samun wuri ne. Bata taɓa gwada min wannan shegantakar a nan ba. Iyaka dai in tana gida girki ya faɗo kanta tayi ta cika tana batsewa kenan. Ita a dole bata son sana’ar uban da yake wahaltawa rayuwarta.”

Haƙuri Anti Labiba ta bata “ki barni da ita kawai Yaya. Girki kuma tunda ta iya ai magana ta ƙare.”

A haka su ka yi sallama bayan ta sake roƙon alfarmar kada Yaya ta yiwa Hamdi magana idan sun yi waya. Ƙarfe uku bayan yaranta biyu sun tafi islamiyya ya rage jaririyar da take goyo da yayarta mai shekara biyu da rabi. Ta fito abinta cikin shiri ta sami Hamdi a falo tana kallo.

“Hamdi zan fita amma ba jimawa zan yi sosai ba. Ga kaza can na fito da ita ki yi pepper chicken kafin na dawo. Sai ki haɗa coleslaw. Na riga na dafa jallof ɗin shinkafa.”

Jin abin da ta ce ba shiri ta kashe TV ɗin.
“Anti ni zan girka?”

“Kina nufin zancen da mu ka yi jiya da gaske ki ke?” Anti Labiba ta ƙanƙance idanu.

“Anti wallahi ni…”

“In fasa fitar kenan komai mahimmancinta in ƙarasa girki ko?”

“A’a Anti. Amma naga tattali ma yana da kyau. Tunda anci kifi da rana a bar kazar sai gobe.”

Ƙiris ya rage Anti Labiba ta fashe da dariya. Fuskar Hamdi na nuni da cewa da gaske take. Lallai idan ta biye mata ba za ta sami biyan buƙata ba.

“Abbansu ne ya aikeni. Gashi kuma yana hanya tare da abokinsa. Na zata ke me fitar dani kunya ce…” ta sauke mayafinta “nagode da ki ka nuna min ban isa ba.”

Jikin Hamdi rawa ya fara. Bata son ayi fushi da ita ko kaɗan. Musamman mai kyautata mata. Da sauri ta bar falon ko kallon Antin ta ta bata kuma yi ba ta shige kitchen. Anti Labiba ta ƙunshe dariyarta ta fice.

Bata zame ko ina ba sai bayan National Military Cemetary da an ɗan wuce National Stadium a nan cikin umguwarsu Karon majigi. Wurin aminiyarta Hauwa taje don nan ne take da tabbacin za ta juyawa jin kunya baya. Daga bakin ƙofa su ka rungume juna saboda sun ɗan kwana biyu basu haɗu ba.

“Sannu da zumunci Labiba. Ina ta waƙar sake zuwa ganin baby amma kwanakin nan orders suna neman fin ƙarfina.” Cewar Hauwa tana karɓar goyon Anti Labiba.

“Mu ai haka muke so. Ɗan kasuwa baya kiran yawa. Ki dai ce kasuwa tayi albarka ki kuma godewa Allah.”

“Alhamdulillah ala kulli hal.”

Hira su ka ɗan taɓa sannan Labiba ta faɗi abin da ya kawota.

“Ni kuwa kina ɗaukar ɗalibai ki koyar dasu?”

“Ban fara ba amma na gama duka shirye shiryen da ya dace. Nan da ƴan kwanaki za ki ji sanarwa.”

Anti Labiba ta saki jiki “Masha Allah. Nayi sara akan gaɓa. Dama ƙanwata nake son kawo miki. So nake ta goge sosai a harkar snacks ɗin nan ita ma.”

Hauwa ta ce “akan ƙanwarki ki ke tambayar class dama? Ai kin san ko bana yi dole na koya mata.”

“Allah Ya ƙaro kasuwa. Nagode sosai.”

“Babu komai. Ai yiwa kai ne.”

Hirarsu su ka cigaba da yi inda Labiba take ta koɗa daɗin kayan ciye ciyen da Hauwa ta ajiye mata. Da za ta tafi ta sayi frozen samosa.

*

Da yake babu wani abu da zai ɗauke mata hankali, bata wani jima ba ta gama ta gyare kitchen ɗin. Tana jin an taɓa ƙofa kuwa ta soma murmushin neman shiri. Ita kuma Anti Labiba sai da ta zo bakin ƙofa ta daina fara’a. Fuska a cinkishe ta shiga gida.

Hamdi ta shiga damuwa. A irin miskilancinta ɗaki za ta tafi amma ita shaida ce. Ganin ɓacin ran Anti Labiba na nufin anyi mata abin da ya ɓata mata rai sosai.

“Anti zo ki gani. Na gama.”

“To an gode.” Ta bata amsa ko kallonta bata yi ba.

Fuskarta canjawa tayi kamar tayi kuka ta ce “Allah na daina Anti. Ki yi haƙuri.”

Ledar pack ɗin samosan ta bata ta ce ta soya. Wannan karon ko kaɗan bata nuna komai na rashin jindaɗi a fuskarta ba. Da ta gama Anti Labiba ta ce ta ci ta faɗa mata ko da daɗi.

Tunda ta gutsira ta kama murmushi.

“Yayi miki?”

“Da daɗi sosai.”

Sai lokacin Anti Labiba ta saki fuska ita ma tayi murmushi.

“So nake ki koma gida da sana’ar hannu. In sha Allah nan da kwana huɗu za ki fara zuwa wurin Hauwa koyon waɗannan abubuwan.”

Farinciki sosai ta gani a tare da Hamdi. Ta dinga dariyar yadda ta canja lokaci guda.

A zahiri tana yiwa ƙannen nata uzuri idan su ka nuna ƙyamar wani abu na Abbansu. Maganar gaskiya duk kirkinsa akwai abin da fa dole ya tsayawa mutum a rai. Ƴaƴa yawanci babu ruwansu da talauci ko arziƙin iyayensu. Indai akwai jinƙai da kulawa a tsakaninsu za ka ga suna ƙaunar abinsu da zuciya ɗaya. Amma duk lokacin da kaga ƴaƴa na kunyar nuna iyayen a wasu wuraren, za ka samu nakasu ta wanni fannin. Inma dai daga ɓangaren ƴaƴan in aka samu marasa godiyar Allah, ko kuma daga iyayen idan sun shuka wani abin da zai kunyata yaransu.

Ga dai shekaru sun ja. Amma har yanzu kallo ɗaya ya ishi mai idanu gane waye Abba Habibu. Irin haka ne abin da ake gudu. Kayi abu ka barshi amma tasirinsa ya gagara barin rayuwarka komai tsahon lokaci.

*

Kwana biyu Kamal ya ɗauke ƙafa daga gidan Ahmad. Taj ya ƙule iya ƙulewa. Kuma ya naɗe ƙafa ba ya zuwa site ɗin aikinsu. Kamal ɗin kaɗai ke zuwa ya wuni yana monitoring komai. A rana ta uku ne ya gaji da gudun rigimar da za su yi da Taj akan zuwansa gidan Abba yaje gidan Ahmad ɗin. Bari ya yi sai gabanin azahar lokacin da ya tabbatar yayan nasu yana wajen aiki sannan yaje.

Babu kowa a gidan sai Taj da Zahra dake kitchen. Fitowa tayi su ka gaisa sannan yaje ƙofar ɗakin Taj. A rufe take, ya yi sallama sannan aka buɗe.

Taj bai jira shi ba ya koma ya zauna akan gado ya cigaba da aikin da yake a laptop ɗinsa.

“Wai nan gaba kake dani?” Kamal ya faɗi da sanyin jiki.

“Kai zan tambaya da ka daina zuwa gidan nan.” Taj ya mayar masa rai a ɓace.

Tausayinsa Kamal yake ji. Bayan abubuwan da yake rayuwa yana haƙuri da rashinsu, baya jin zai juri wani abu ko yaya yake ya haɗa su rigima ba. Zai fara bashi haƙuri sai aka kira Taj ɗin.

Abinka da sabonsu na rashin ɓoyewa juna komai. Gaisawa kawai su ka yi da Amma ta sako zancen Anisa. Ya kunna speaker ya yafito Kamal da hannu.

“Taj kana ji na kuwa?”

“Ina ji yanzu Amma. Me kike cewa?”

“Maganar Anisa. Kai baka ce min komai ba. Na share don ina zaton sai ka dawo za mu yi magana. To jiya Hajjo ta kira ta ce za ka wulaƙanta mata jika. Idan ba ka so ka faɗa ta samo mata wani.”

Hannu Kamal ya dinga juyawa yana son sanin me take nufi.

“Amma da kin bari na dawo dai.”

“Ai ka san halinta. Yanzu sai ta juya zancen. Ba ka son Anisan ne?”

Ƴar dariya ya yi daga ji bata kai zuci ba. Baya son karɓar abin da zai zame masa matsala don ko babu Hamdiyya shi bai taɓa kallonta a matsayin da ya wuce ƙanwa ba. Idan kuma ya ce baya so nan ma duk wanda ya san tarihinsa sai ya zage shi.

“Wa zai ƙi mace kamarta?”

“Wannan wace irin amsa ce?”

Sarai ya ji ɓacin rai a cikin muryarta. Ya kalli Kamal yana neman agaji. Shi kuma sai ya raɗa masa a kunne cewa ya faɗa mata zai je Abujan su fara fahimtar juna. Haka kuwa ya faɗa mata. Nan da nan sautin muryarta ya koma daidai. Ta dinga shi masa albarka. Bata ga laifin Hajjo ba da take so wa jininta Taj. Da tana da sauran ƴa ma kafin Hajjon tayi masa tayim Anisa za ta haɗa su. Abu guda ne dai ta ajiye a ranta. Idan yaje yace baya so to fa dole a haƙura. Don sun riƙe shi bata so ayi amfani da hakan a matsayin dalilin yi masa tilas. Zai zamana ba don Allah su ka taimaka masa ba.

Dariyar mugunta Kamal ya dinga yi bayan Taj ya gama faɗa masa yadda su ka yi da Hajjo.

“Salwa kuma fa? Ko har yanzu ba fahimci ta mato maka ba?”

“Hmmm, ai baka san me tayi min ba…” ya sake kwashe labari ya sanar dashi.

Kamal dariya harda faɗowa daga kan gado. Faɗan da su ka manta dashi kenan aka koma hirar masoyan Taj.

“Yanzu dai da gaske Abujan zamu je.”

“I’m not interested Happiness. Ina tsoron kada naje su zata na amince.”

“Sai mu yi mata bayani mu nemi haɗin kanta” ya ɗan kalli Taj ɗin “akwai wadda ka ke so ne?”

Kamar ya faɗa sai ya tuna reaction ɗin Kamal akan Abban Hamdi kawai ya fasa. Shiryawa su ka yi su ka tafi site tare. A hanya

“Na fa yi maka laifi Happy. Naje na sake lalata chance ɗin Mal. Habibu ya karɓi aiki da kai.”

Ana kukan targaɗe, ga karaya ta zo. Taj ya gama sauraron Kamal ya ma rasa abin da zai ce.

“Kayi shiru” Kamal ya furta yana satar kallonsa.

“Ka san bana ganganci da rayuwata. Ba don haka ba duka zan maka.”

“Sai da naje nake ganin kamar ban kyauta ba. Amma ni yadda ya ɗauki zafi da jin sunan Alhaji yafi damuna. Kana ganin ko shi ma yadda yayi maka haka yayi masa? Naji Yaya Hayatu ma yake kiransa.”

Da daddare Taj ya kira Hajiya ya tambayeta game da Abba Habibu. Don kada ta zargi komai sai ya ce,

“Hajiya don Allah mece ce alaƙar Alhaji da Habibu ɗinnan?”

“Me yasa kake son sani?”

“Don na kiyaye. Kada na taɓa bari girki yasa nayi koyi da irin tasa rayuwar”

Hajiya na jin haka kuwa tayi masa bayanin da yake nema. Alhaji ya so Habibu tamkar ƙaninsa na jini. A rayuwarsa kamar yadda ƴaƴansa su ke gani yana son kyautatawa duk mai mayar da hankali a harkar ilimi. To Habibu sai dai ace masa gifted. Kana faɗa yake kwashewa. Sai ka rasa wace irin ƙaddara ce ta karkata masa rayuwa ta mayar dashi ɗan daudu. Gashi a lokacin daudancin mafi akasari ba a raba shi da kawalci da sauran alfasha mai zubar da mutumci.

“Da ya dawo daga Saudiyya yayi ta bibiyar Alhaji yana neman ya taimaka masa da jari ko ya ɗauke shi yaron shago. Amma waccan ƙyama da yake masa tun farkon fara daudun tasa yayi masa kora ta wulaƙanci.”

Jikin Taj ya yi sanyi sosai. Idanunsa su ka kaɗa su ka yi ja.

“Bai taimake shi ba?”

“Inaaa. Ka san shi da kafiya. Tunda ya juya masa baya bai ƙara waiwayarsa ba. Ni dai ƙarshen labarinsa da naji ance ya buɗe shago yana abincin sayarwa.”

Shiru taji ya yi da tana magana. Ta rage murya,

“Taj ba za ka sauke naka ƙudurin kayi yadda yake so ba?”

“Hajiya ba haram bane. Ki cigaba da sani a addu’a. In sha Allah ba zan taɓa yin abin da za ku yi baƙincikin zaɓina ba.”

*

A cikin wata guda mamallakiyar Luciousbites.ng wato Hauwa ƙawar Anti Labiba ta san tana tare da haziƙar ɗaliba. Duk snack ɗin da su ka wuni koya to in sha Allah washegari idan Hamdi tayi kuskure ba zai yi yawa ba.

Ita babu ƙiwa ko ha’inci, ɗaliba kuma mai ƙoƙari. Aikin nasu yana tafiya yadda ake so. Wasu dama ta ɗan iya sai dai yanzu ta koyi hanyar da ta dace da zamani wurin inganta saninta. Sannu a hankali ta ƙware wajen yin doughnut, samosa, meatpie, springrolls, chinchin irin na ƴan gayu, gashin nama da kifi kala kala. Da kuma uwa uwa haɗaɗɗen plain youghurt, coconut infused youghurt da yogo fura.

A gida irin farincikin da Anti Labiba ke gani a tare da ita har mamaki take bata. Mijinta ma sai da ya ce wai gani yake kamar an canja ta da wata. Yaran gidan kuwa tunda an yarje mata gwada abin da ta koya, sun kwashi gara ba kaɗan ba. A ci a gida kuma aje makaranta.

*

Wannan wata gudan harda ƴan kwanaki a ɓangaren Taj cikin wahala su ka zo masa. Kacokan ya ajiye aikinsa bayan ya wayar nan da ya yi da Hajiya. Ya karkata akalarsa zuwa ga son lallai sai Abba yayi aiki tare da shi. Kamal da yaga ba zai iya hana shi ba sai ya bashi goyon baya.

Ranar farko tun safe ya shirya yaje ƙofar gidan Abba. Bai aika a sanar da zuwansa ba. Ya yi zamansa a cikin mota har Abban ya zo fita sannan ya tare shi. Ai kuwa yana ganin shi ya sauya fuska.

“Baka sami saƙona a wajen ɗan uwanka ba?”

Gaishe shi Taj ya yi. Bawan Allah yana faɗan ya tsahirta ya amsa sannan ya cigaba.

“Bana son rigima da mahaifinku. Ban san me ku ka ji game dani ba. Amma ko ma mene ne nufinku ni da Allah na dogara.”

“Don Allah ka saurareni. Da alkhairi na zo maka.”

Cikin gida Abba ya koma. Bai ƙara fitowa ba har la’asar. Taj ya tafi amma bai karaya ba. Washegari ma ya sake zuwa. Ranar Abba ko sauraronsa bai yi ba ya wuce ya yi tafiyarsa. A haka su ka cinye sati guda. Wasu kwanakin duk sammakonsa idan ya zo zai samu Abban ya fita kafin ya zo.

A kwana na tara Taj sai ya canja tsari. Tare su ka zo da Kamal wanda ya ce zai bada haƙurin abinda ya yi kwanaki. A zatonsa ko shi yasa Abban yaƙi sauraron Taj. Yaro ya tura ya ce a faɗawa Abba su Taj sun zo kuma wallahi yunwa suke ji.

Sajida ce kaɗai a gida da Yaya. Halifa da Zee suna makaranta. Sajida tana jin saƙon yaron ta figi mayafi ta fita. Yaya tana ta kiranta taƙi dawowa. Abba kuwa ƙwafa ya yi.

“Bawan Allah zamu haɗaka da ƴan sanda wallahi. Bar ganin kuna da kuɗi” ta harare su duka “wallahi muna da masu tsaya mana mu kara daku a hukumance.”

“Ki yi haƙuri ƙanwarmu. Aiki kawai ƙanina yake son yi tare dashi. Shi ma sana’ar girki yake.”

“To ya ce baya so. Ai.ya faɗa mana ko ku su waye.” Ta ce da tsiwa.

“Ɗan tsaya mu yi magana” Taj ya ce bayan ta gama magana. Tsayuwar tayi tana karkaɗa ƙafa ita a dole ranta ya ɓaci.

Tarihinsa ya bata a taƙaice.
“I believe yadda nake son in dawo da ƙimata a wurin Alhaji haka Abbanku zai so mutane su yi masa uzuri su karɓi sabuwar rayuwar da ya gina.”

Cikin mutuwar jiki ta ce “haka ne.”

“Ina son yin aiki da Abba amma a setting da ya bambanta da wanda ya saba. A inda maza masu yin komai na maza su ke girki. Burina idan an kwana biyu rayuwarsa tayi daidai ta yadda masu aibata shi a bayansa za su ji kunyar abin da su ka yi.”

Ƙwalla ta saukowa Sajida “zai yiwu? Kana ganin wannan abubuwan na mata za su barshi?”

Kamal ya sanya baki “Allah aka ce. Ba yadda za ayi ka bar kowa ka kama Shi sannan kasa rai da ganin ba daidai ba. Taj only wants to help.”

“Mece ce ribarsa idan ya taimaka masa?”

“Mutane su fahimci akwai sana’o’in da basu keɓanta ga mata ba kawai. Sannan ƙyama ba ita ta dace da irin wanda ya yi rayuwar Abba ba. In an bi hanyoyin da su ka dace shi ma zai karɓu a cikin mutane kamar kowa” Kamal ya sake bata amsa.

Abin nema ya samu Sajida ta koma gida da murnarta. Abba na ganin hawayenta ya tashi.

“Me su ka yi miki?”

Ta fashe da kuka “don Allah Abba ka sauraresu. In sha Allah wannan wahalar neman wurin hayar zai ƙare.”

Fita ya yi ya sallame su. Taj sai ya ƙi motsawa.

“Zan sa a nemo min mahaifinka ya zo ya tafi da kai.”

“Zan tafi amma don Allah ka bani abinci. Yunwa nake ji.”

Abba ya kallesu. Duk sun yi laushi.

“Ba ku karya bane?” Ya tausasa murya. Sai muryar tasa ta sake yin ƙasa.

“Ni dai na sha tea. Happy kuma bai ci komai ba.”

Abba ya kalli Taj da mamaki “Happy kuma?”

“Eh. Sunansa kenan” Kamal ya bashi amsa.

“Yana sallah kuma?” Abba ya tambaya harda matsawa baya.

Me kuwa za su yi banda dariya. Taj yana yi ya riƙe ciki. Abba ya sami kansa da yin murmushi bayan sun yi masa bayanin sunayen nasu.

“Innza ku ci ko indomie ce sai na karɓo a shago Sajida ta dafa muku.”

“Don Allah abinci muke so. Wanda ka girka.” Taj ya ce da sauri.

Girgiza kai Abba yayi yana ɗan murmushi.
“Ku jira nayi muku iso a ciki.”

Sajida ce ta leƙo ta kira su bayan ya shiga ciki. Aka yi musu shimfiɗa a tsakar gida. Yaya ta fito da lulluɓi su ka gaisa. Taj ya dinga kallon gidan yana ayyana wai fa a nan yarinyar nan da ya gani take rayuwa. Yana son tambayar ina take amma dole ya kama bakinsa.

Abba ya shiga kitchen suna iya hango duka motsinsa ta tagar dake tsakar gidan. Kai kawo kawai yake yi cike da ƙwarewa. Yaya da Sajida kuma suna jansu da hira jefi jefi. Kamal ne kaɗai yake amsawa. Hankalin Taj ya yi kitchen. So yake kawai yaga yadda Abba yake aiki.

Yaya ce ta lura da hakan ta yiwa Abba magana. Yaran sun burgeta saboda babu girman kai a tare dasu.

“Nace ko za ka bari ya shigo ciki ya taya ka?”

“A’a, nagode.”

Taj ya tashi “gani kawai zan yi. Ba zan saka hannu ba.”

Sai bayan fiye da minti ɗaya sannan Abba ya ce ya shigo amma iyakarsa ƙofa. Ai kuwa da saurinsa ya shiga. Aikin daɗewar shekaru wato experience yafi aikin iyawa. Taj yaga abin mamaki a tattare da kuzarin dattijon. Ga tsafta don ko ledar maggi babu a ƙasa. Ƙamshi mai rura wutar yunwa ya cigaba da matse masa hanji.

Fried spaghetti ce yayi musu babu nama a ciki sai busasshen kifi. Ya juye a tray. Sajida ta kawo musu. Sannan ita da Yaya su ka koma falo. Samarin Alh. Hayatu su ka zauna suna zuba santi har su ka cinye.

Da za su tafi ne Taj ya bashi nambar wayarsu rubuce a takarda.

“Don Allah Abba kayi shawara.”

“Naji. Ku tafi.”

Faɗan nasa bai hana shi raka su har mota ba. Kuma yaƙi tafiya har su ka bar layin. Yana komawa gida ya samu Sajida tana naɗe tabarmar da su ka zauna. A ƙarƙashinta sai ga farar takarda. Ta miƙa masa ya buɗe. Roƙo da magiya ne daga Taj. Sai kuma ƙarin bayani game da restaurant ɗinsa.

“…idan ka amince za ka yi aiki dani, zan kama mana wuri inda za mu yi developing recipe kafin a gama ginin. Bana son yin business ɗin da zai rushe kafin yaje ko ina. Ka taimaka min..
Happy Taj”

Da Yaya su ka zauna shawara. Sai dai washegari da kwanakin da su ka biyo baya kullum sai Taj yaje cin abinci. Har su ka yi masa kwano. Tun Abba yana basarwa har dai ya karɓi tayin da yayi masa. Ba kuma komai ya janyo haka ba sai rasa wurin da zai kafa sana’arsa. Duk inda yaje sai an biyo shi da ƙabali da ba’adi wanda shi ya san gaskiyar dai ita ce ɗan daudu ne. Ba sa ma damuwa da jin ko ya daina. A gida idan yace zai yi kuma akwai iyalinsa da ba zai so mutumcinsu ya zube ba.

Haka dai bayan kwanaki yana kai gauro da mari ya ce ya amince. Ya kuma duƙufa addu’ar neman taimakon Allah.

A lokacin kullum Hamdi tayi waya da gida sai anyi mata zancen Taj. Yaya da ƴan uwanta sunansa a bakinsu raɗau. Ita kuwa lamarin bai burgeta ba. Wanda zai zo ya mayar da Abbanta cikin sana’ar girki ba masoyi bane.

Su Taj da su ka tabbatar sun sami kan Abba sai aka fara shirin zuwa wajen Anisa. Lokacin bai fi kwana goma ya rage masa ya koma ba. A motar Kamal su ka tafi. Da yake ya san gari basu wahala ba da bin kwatance ta google map su ka isa gidan.

*

Aikin snacks da Anti ta ce a tanada saboda zuwan su Taj, Hauwa aka bawa. Hajjo tuni ta fesa musu dalilin zuwan nasa. Anisa sai murna. Sai dai anyi rashin sa’a ana gobe ranar tafiya ta kama ta. A waya ta basu haƙuri ta ce amma akwai ɗalibarta da duk abubuwan da su ka zayyano za ta iya ba tare da sun ji bambancin taste ba.

“Haɗani da ita” Anisa ta ce don in ba kayan Luciousbites ba, bata ganewa snacks ɗin.

A waya aka gama komai. Hamdi murna da godiya ta dinga yiwa Hauwa. Ita kuma ta dinga roƙonta kada ta kunyata musu brand.

Ƙoƙari kam bakin gwargwado tayi. Meatpie, doughnut da samosa su ke so. Sai coconut infused youghurt. Shi ne kaɗai Hauwan ta aiko mata da shi. Sauran kuwa babu komai a ƙasa dole sai anyi. Bayan ta gama ta kira numbar Anisan da aka bata ta sanar da ita an gama komai.

“To ki bawa mai delivery. Zan turo address.”

Nan fa ɗaya. Bata san kowa ba. Anti Labiba ma ta dinga kiran mutanenta amma kowa sai ya ce mai delivery baya kusa. Hamdi ta kuma kiran Anisa. Lokacin ita kuma bata jima da yin waya da Taj ba. Yana ƙara neman kwatance. A yadda ta ƙiyasta bai fi minti goma zai kawo su gidan ba. Gashi babu wanda za ta iya aika. Gari an tashi da rashin mai. Duk wata motar gidansu tana layi sai guda ɗaya ta Daddy.

“Hamdiyya ko za ki ɗauko bolt ki kawo min. Zan biyaki kuɗin tranport ɗin. Fitar ce babu halin yi yanzu.”

Hamdi ta faɗawa Anti Labiba. Su ka rasa yadda za su yi. Mijin Anti Labiba a wajen gari yake aiki. Ita kuma babu mota. Tayi shahada kawai ta samarwa Hamdi bolt ɗin.

RAYUWA DA GIƁI 14

Batul Mamman💖

*

Rashin wuta da ake fama dashi ya hana Hamdi sayen naman yin meatpie da ake sayarwa a shagon Abba kullum. Har ta haƙura da cinikin ranar saboda da ta saya a daren ko ta soya zafin da ake zai iya canja mata ɗanɗanonsa idan ta haɗa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa’a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin kwantai.

“Yaya zan kai masa da kaina.”

Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane. s
Sau ɗaya ta taɓa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huɗu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi taƙi jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler ɗin da ta sako meatpie ɗin mai hannu biyu ta kinkima ta ƙarasa.

Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ƙofa ta kuma tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta.

“Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi ɗiyarmu ce don ga kama nan. Ƴan mata shigo daga ciki. Aunty Simagade yau ana ta fama da baƙi.”

Gaban Hamdi ya yanke ya faɗi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caɓalɓala masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da ɗaurin ƙirji. Kansa kuma ya yi ɗaurin ture ka ga tsiya da ɗankwali irin zanin.

‘Me ya kawo ɗan daudu wajen nan?’ Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ƙuncin rai.

Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ƙafafunta wani irin baƙinciki ya turnuƙeta. Akwai kwastomomi da yawa a ciki. Amma fa a yau dandazon ƴan daudu sama da huɗu ne su ke ta karakaina wajen ɗaukar odarsu da kawo musu abinci. Muryoyinsu da taƙi jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna shaƙiyanci. Ita kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta.

*

Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. Ƴar Ficika ake kiransa saboda ƙanƙanta da ƙwarewa a iya shege. Duk wani mai ji da hayaƙinsa idan ya gamu da Ƴar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haɗawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ƙwarai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuɗi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haɗa abinci. Ƙaryar mutum ya ce ya taɓa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. Ƴar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum. Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo Ƴar Ficika ne ya biya masa rabin kuɗin jirgi.

Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haɗa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ƙarƙashinsa kaf babu ɗan daudu. Maza ne kawai masu ra’ayin girki a dalilin rashin wata sana’ar. To yau kwana uku kenan da Ƴar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ƙafa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haɗu da wanda ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa.

Abba bai ɓoye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. Ƴar Ficika yaji ya kwaɗaitu da samun darajar da ya rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ƙyama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa Abba ya ce kuma zai buɗe gidan abinci. Yana fata zai taimaka masa.

“Ɗan halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ƙoƙarina.”

“Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka sabon restoran ɗin sai na karɓi wurin nan.”

Abba bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kira Taj ya sanar dashi. Shi kuma jin taƙaitaccen tarihin Ƴar Ficika da tsoron da Abba yake na kada ya komawa rayuwarsa ta gidan jiya sai ya amince.

“Idan mai laifi ya so tuba yana da kyau a bashi dama. Rashin yin hakan na taimakawa wajen sake dulmiyar dasu cikin ayyuka marasa kyau.”

Taj ya ce “haka ne Abba. In ya rasa samun aikin da zai bashi halal zai koma ya nema daga haram ko yaya take.”

Da wannan shawarar Abba ya amince masa. Shi kuma saboda jindaɗi ya ce zasu dinga tayasu aiki duk lokacin da su ka sami lokaci tunda ba su da abin yi. Shi ne fa su ka zo yau. Girki harda wanda Abba ya manta. Yaji daɗi domin yau kasuwar ta buɗe fiye da kullum. Ya alaƙanta nasarar da kyakkyawar niyyarsa ta taimako. Don bai manta wulaƙancin da ya sha ba sanda ya dawo. Da wanda ya gani a dalilin neman wurin kafa sana’a da ya rasa wancan.

*

“Kai, kai, kai…Tabarakallah.”

Hamdi ta waiga baya ta haɗa ido da wani ƙarmasasshen mutum da ita kanta ta fi shi tsayi. Kanta ya yi yana murmushi kamar zai rungumeta. Kafin tayi baya Abbanta ya janyeta gefensa. Ƴar Ficika ya cigaba da murmushi yana kallonta.

“Wannan ma taka ce?”

Yaronsa da ta haɗu dashi a waje ne ya bada amsa.

“Aiwa, baka ga kama ba? Anti Simagade an dasa kyakkyawar shuka tayi fure mai ƙamshi.” Ya faɗi yana lanƙwaya hannu da juya idanu.

Wani irin ɗaci ya dinga kai komo a wuyan Hamdi. Da ƙyar ta yiwa Abba biyayya ta gaishe da mutanen da ya gabatar a matsayin abokan sana’arsa a Saudiyya.

“Cewa za ka yi mu iyayenta ne. An riga an zama ɗaya. Za ku yi ta ganinmu har sai mun saba.”

“To” ta ce da gatsali ta kuma juya ko coolar bata ajiye ba tayi waje.

Tana fita hawaye ya wanke mata fuska. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta ɗauka Abba girki da abubuwa na siffar mata kawai yake yi. Me zai sa ya mu’amalanci mutane irin waɗannan? Don sai da ta gansu ne ma ta gane me ake nufi da asalin ɗan daudu.

“Hamdi”

Sarai taji kiran da yake mata amma ta ƙara sauri. Kafin ta ƙarasa titi ta dire coolar a gabanta ta ɗagawa wani adaidaita sahu hannu. Kafin ya gama tsayawa ta faɗa ciki su ka yi gaba.

Abba ya kalleta ya juya ya kalli Ƴar Ficika da ya biyo shi.

“Ba dai ganinmu bane ya ɓata mata rai ba?”

Murmushi ya ƙaƙalo “ahh haba dai. Sauri take yi.”

Ƴar Ficika ya murmusa “ko kai a gabana ka ƙarasa girma fa Habibu. Ta yaya zan kasa gane abin da na saba gani?”

Cike da jin nauyi Abba ya faɗa masa yadda a baya bata ma son nuna shi a matsayin uba. Yana ganin babu mamaki yanzu wannan abin da tayi yana da nasaba da tunaninta na komawarsa ga ɗabi’ar baya.

“To ko mu daina zuwa? In ya so lokacin da ka bar nan ɗin sai mu dawo?”

Allah Ya sani kamar ya ce eh, to amma nauyi da tunanin me zai je ya dawo a rayuwar su Ƴar Ficika sai ya ce a’a. Yau kaɗai da ya haɗu dasu ya ga wani irin farinciki da annashuwa a tare dasu. Sun sake suna ta aikin abin da su ka fi ƙwarewa wato girki. Har sai da ya yi tunanin me yiwuwa tun dawowarsu babu wanda ya sami tarba mai kyau da mutuntawa sai yau.

*

Hamdi tayi kuka tun daga hanya har gida. Da ƙyar ta iya labartawa Yaya abin da ta gani. Abba na dawowa kuwa Yaya ta kawo zancen ita ma nata ran a ɓace.

“Yaya Habibu ka sani cewa bahaushe na cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne. Yanzu duk wanda ya ganka da mutanen nan zai yi maka kallon irinsu.”

Da laluma ya dubeta “Jinjin juya baya ba nawa bane ga wanda ya nemi taimakona. Duka duka yaushe muka sami wannan rayuwar bayan haɗuwa da yaron nan Taj? Ko har kin manta cin zarafin da aka dinga yi min akan neman shago? Duk unguwar da naje sai su ce kada yaransu su yi koyi dani basa so.”

“Naji kuma duk na fahimta. Amma hanyoyin samun lada ai suna da yawa. Shigowar mutanen nan rayuwarka a wannan lokacin da kake neman tada ƙimarka a cikin mutane gaskiya ba zai haifi ɗa mai ido ba.”

Ta sake faɗi cikin fushi. Duk yadda ya so ɓullo mata taƙi amincewa. Tsayuwa ya yi akan bakansa shi ma. Yau dai ɗaya zai yi abin da yake jin ya dace ko ba zai faranta ran iyalinsa ba.

“A bar maganar nan. Indai Ƴar Ficika ne, ba zan kore shi ba.”

“To ai shikenan. Allah Ya kyauta ɓacin rana.”

*

Yadda Salwa ta matsawa Taj da waya da messages a duk wata kafar da zai gani, haka Anisa ma take yi. Gashi dai basu san da zaman juna ba amma kowacce ta matsa lamba.

Ita Salwa banda ƙawa har Maminsu ta san irin soyayyar da take yiwa Taj. Da fari ta nuna rashin goyon baya saboda ɗan tsohon miji ne. Sai da taji ta kuma ga waye Taj a wani bidiyon girkinsa a youtube da Salwan ta nuna mata tayi mubaya’a. Matashi ne mafarkin duk wata budurwa. Burin duk wata uwa da take son ƴarta da arziƙi. Ko da wasa girkinsa bai zo ranta ba balle ya dameta. Yana da kuɗi kuma ta san asalinsa. To me ya rage?

“Kada ki yarda ya manta dake. In ya tafi ki dasa kanki a cikin rayuwarsa.”

“Ta yaya? Ko sau ɗaya bai taɓa nemana ba da kansa.”

Mami tayi dariyar manya “wannan ai duk ba wata matsala bace. Ke ki dinga bibiyarsa. Gaisuwa safe, rana da dare. Ƴan abubuwan nan namu na mata ku baku iya ba. Sai a zauna sakato ana jiran namiji ya yi komai.”

Salwa ta sunkuyar da kai “Mami idan mace tana bin namiji fa wulaƙanta ta yake yi.”

Taf…taji saukar duka a kafaɗa. Rai a ɓace Mami ta ce “banda shashanci dama ai ba da soyayya za ki bishi ba. Kulawa kawai. Ko kissar ma sai na koya miki?” Ta harari ƴarta.

“Na fahimta Mami.”

“Ko ke fa.”

Da haka Salwa ta kafa masa ƙahon zuƙa. Waya da saƙwanninta babu wani abu da zai bada ita har yasa Taj gudunta. Yayana sama Yayana ƙasa ne dai. Gaisuwa, bibiyar ayyukansa da yi masa fatan alkhairi. Tun yana sharewa har dai bisa shawarar Kamal ya soma amsa mata a mutumce.

“Ba’a san inda rana za ta faɗi ba. Ka daina wulaƙanta duk mai nuna damuwarsa a kanka.”

“Kada ta sa rai ne Happiness.”

Dariya Kamal ya yi “kai ma kamar wani ɗan yaro in kayi wani abin. Ai yadda ta zo maka a ƙanwa haka za ka je a matsayin yaya. Tunda baka so ta bijiro da zancen soyayya sai ka toshe ƙofar.”

“Kamar ya?”

“Ka dinga bata labarin wata a matsayin budurwarka. Wataran ka ce ma tana gaisheta.”

Girgiza kai Taj yayi kamar yana gaban Kamal ɗin “ba zai zama cin fuska ba kuwa?”

“A ƙanwa fa tazo maka. Kuma dai kayi mata hannunka mai sanda taƙi ɗaukar haske. Ba sai ka bita ba kawai a tafi a haka. Ya dai fi akan ka dinga shareta wanda za ta fassara a matsayin wulaƙanci.”

A haka suke ta tafiya. Ya Taj da ƙanwarsa Salwa.

A ɓangaren Anisa kuma bai san wane tudu wane kwarin aka bi ba sai ji ya yi Amma ta tado masa da zancen ko za su fara haɗa lefe kafin su koma gida.

“Lefe kuma? Na wa?” Ya tambayeta kai tsaye babu mamaki a tare dashi.

“Kada ka raina min wayo Taj. Ya ku ka yi da Anisa?”

“Anisa kuma?”

Amma ta ɗaure fuska “Allah idan na sake magana ka ce min ‘kaza kuma?’ Sai ranka ya ɓaci.”

“Yi haƙuri Ammana.” Ya yi mata murmushi.

Mayar masa tayi sai kuma ta sake shan kunu.

“Ka san sau nawa Daddy yana yi min maganarku? Sai dai nayi ta kame kame saboda ka ƙi cewa komai.”

Yadda su ka yi da Anisa da Hajjo ya faɗa mata.

“Ni na zata mun gama magana tunda ta fahimceni.”

Yanayin Amma duk babu wani kuzari ta ce “Maganar da aka fara daga sama ai a can ya dace a ƙare ta. Me yasa ba ka faɗa min ba?”

Ya yi shiru. Ba zai iya ce mata yaga kamar tana so ba shi yasa ya kasa sanar da ita ba.

Anti da kanta tayi mata waya tana cewa wai ta kira tayi mata murna ƴarta ta sami miji. Anisa da Taj sun daidaita.

Da murna Amma amsa mata da “cewa zaki yi na cigaba da tari. Allah Yasa damu za ayi.”

“Amin amin” Anti ta amsa da farinciki.

Da su ka yi waya da Daddy ma zancen kenan. Har yana cewa idan su ka dawo da kansa zai yiwa Alhaji magana. Ƙudurin Taj na aure bayan ya koma gida ba abin a kawo ido a zuba masa bane. Dole su za su yi nasu ƙoƙarin a yanzu da Taj ya zama successful su mayar dashi gaban mahaifinsa.

Ya gama tsare tsaren hanyoyin da zai bi domin bawa Alhaji haƙuri ya janye fushinsa. Wanda hakan ya yiwa Amma daɗi sosai. Shi ne ta tayar masa zancen shi kuma ya nuna ba haka aka yi ba.

“Ni yanzu ya kake so in yi Taj?”

Ta ma rasa ta inda za ta ɓullowa lamarin. Idan ta nuna bata so a yanzu da maganar ta fito daga bakin kishiyarta da mijinta kowa ita zai zarga. Za a ce ita ce bata so. Sannan ga dukkan alamu ma dai gadar zare Hajjo take neman ko ma a ce ta ƙulla mata. Kuskure guda zai sa a ce tana gudun ƴar kishiya. Ko kuma a gorantawa Taj rufin asirin da aka yi masa. Ta san Hajjo sarai. Idan abu bai tafi yadda take so ba to mutum ya shiga ɗari ba ma uku ba.

“Kasan me nake so da kai?”

Ya girgiza kai “ko mene ne zan yi miki Amma.”

Series Navigation<< Rayuwa da Gibi Chapter 2
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *