RIKON KAKA
CHAPTER3
Kaka tace”Ba kowa, zaluncine kawai da kuma ba
ya qaunar . ki” Rukayyah tace “Ai nima shi yasa
bana Raunar sa, dama ya mutu
~ Kaka tace”Idan ya mutu ai muma da mun
mutu, don da Allah muka dogara da shi muka
dogara, idan ya mum jika ai sai munyi bara“
‘Rukayya ta diro daga kan gadoh ta , dauko kofi
ta zuba furar da kaka ta gama damawa, sannan
ta koma bakin gado ta soma sha. *
_ Kaka ta mike ta kuskure bakinta saboda kiran
sallar la’asar da aka fara a masallaci.
Misalin karfe biyar dai-dai taiwa Abubakar a Kofar
gida, a gajiye liqis ya dawo gidan tamkar Wanda
aka bawa kashi. Ya cire kayan jikinsa ya fito ya
:nufi kewayrn gidan ya watsa ruwa ya dawo
ya‘saka ‘yan Kananan kaya mararsa nauyi,
sannan ya fito tsakar gidan ya
nufi dakin kaka.
Tana kwance tana hutawar ta sai jika ce keta
faman * ‘ wasan kyallaye, tana ganin Abubakar
gabanta ya fadi, ta shiga faman raba idanuwa.
Abubakar ya tsaya bakin kofar dakin ya watsa
mata harara, kafin yace
“Naga ranar da zakiyu hankali, qatuwa dake kin
tile kina wasan kyalle. Mtsw! Allah wadaran naka
ya lalace’. .
Kaka tai saurin tashi zaune, “Ah! Ka dawo kcnan
k0, sarkin mita uban ‘yan iyayi?”
Ya cc, ”Ni ba mita nazo ki min ba’“.
Ya wurgawa Rukayya Naira hamsin, yace
“Tashi maza kiyo min cefane wurin Haladu in
dora sanwa, kuma saura idan kin tafi kije ki ta
neme-nemen fitina”.
Ya juya ya barsu ya nufi wurin murhu ya hada
itatuwa ya dora sanwar wake, sannan ya koma
dakinsa ya kunna kallo a wayar sa
Rukayya ta tafi siycn cefanen tanata faman
dirc~dircn ta a hanya, tana shawo kwanar
Rukayya ta rinqa krta musu dariya har tana
dukawa ta zub da sauran duwatsun ta nufi gida
tana tsallen murna.
Ta kawo masa cefanen dakinsa, a lokacin ta
tsaya daga bakin kofa.
“Ga cefanen”.
Yai kamar bai ji ta ba, sai da ta mai maita wurin
sau uku sannan ya mike yazo ya amsa tamkar
wanda ya rike wani abin kyama, yana binta da
kallon kyama
Duk tai dagaje-dagaje da ita, kayan nan duk
sunyi dauda, ita kanta fatar jikinta taji jiki. Har
zata wuce yace.
“Ke, zo nan.
Ta dawo, “Gani“.
Kamar ba zai tanka ba. can kuma ya dame ya ce
”Yaushe rabon da kiyi wanka?” Shiru ba amsa, ya
daka mata tsawa koba dake nake bane
Tace; “Nima na manta
Abubakar ya girgixa kai wuce kije ki ciro kayan
jikin da sauran
daudar ki kawo min a bakin maguji, kije ki debi
ruwa kiyi wanka, sakarya, qazamar Wofi. Wuce ki
tafi
Da hanzarintata wuce, .ya rufa mata baya. Haka
kawaiyake jin tsanar yarinyar a. ransa saboda
qazantar ta da kuma‘ kin jinta kamar _ wadda
aka kadawa da ruwan sanyi. ., ’
Ya wanke cefanen ya zuba a turmi yana
jajjagawa, Rukayya ta debo kayan ta kai masa a
bakin maguji ta ajiye masa tuli guda, sannanta
debi ruwa a bokiti ta nufi kewaye tai wanka, ta
wuce daki. ‘
Kaka ta cc, “Da yake shi ne ai gashi nan kinyi
wankan,anfi sati ina matsa miki da kiyi wankan
amman kin kiya sbd kin rainani
Rukayya ta xumBuro baki, ta janyo jakar kayanta
ta fito da wata cukurkudaddiyar
doguwar riga ta saka, bata shafa mai ba balle
hoda, tai zamanta abinta.
‘ K0 kadan Rukayya bata son kwalliya,
Bata ma damu da tsaftar jikinta ba ballantana
wata kwalliya. .
Kaka tace, “Ki dauko k0 mai :neki murza Jika, kin
zauna da jiki haka furu-furu”.
Ta zumBuro baki tai kwanciyar ta hankalin ta a
kwance
Abubakar yai jalof din shinkafa da wake,
yana kammala sallar magariba ya filo ya ,dibi
nashi ‘abincin ya kwashe masu sauran ya kai
masu sannan ya wuce dakinsa. Washe gari .
tunda sanyin safiya Abubakar ya gama jidar ruwa
sannan ya ta da Rukayya ta nemo masa tsari, ta
zunguro baki‘ alamar bata so ba, ta dauki bokitin.
Abubakar na kallonta cike da takaici, ya. danne
zuciyar sa ya kyale ta. “
Gida biyu ta shiga ta samo tsarin ta nufo ~gida,
tana cikin tafiya ta hadu da Zulai da Rakiya, bata
kula su ba saboda tsarin da ta debo. Abokanen
fadanta ne sosai suma ‘yan neman rigima ne
Zulai ta bangaje ta har bukitin tsarin ya fado
daga kanta ya zube bokitin ya fashe.
Rukayya ta ce, “Kaikai! Ni ku ka fasawa bokiti?
Wallahi ba zan yarda ba
Sukace “An zubar, k0 akwai abinda za kiyi?“
Ba ta tsaya mai da masu magana ba ta cakumi
Zulai da kokawa, ta yarbar da ita a cikin tsarin
tana duka, ganin haka yasa Rakiya ta shiga
dukan Rukayya, suka tararmata su biyu, sai da
Allah Ya kawo wani mutum sannan ya raba su.
‘ Rukayya ta dauki fashasshen bokitin tsarin ta
nufi gida tana kuka, Abukabar na ‘shara a tsakar
gida yaji kukan ta, ya mike da tsinsiya a hannun
sa yana jiran shigowar ta.
Bai ,yi mamakin ganinta da fashasshen bokiti ba,
jikinta duk tsari da qasa. Wani irin bakin ciki ya
turnike mashi zuciya, yai tsaye yana kallonta. Ta
kasa motsawa daga inda take,
tai tsaye tana rera masa kuka. Kaka tai saurin
hankado labule
tana fadan ‘ ”Mugu, dukan nata din kake k0?
Indai ka
kashe ta Habu ka huta
Ganinta da tayi tsaye da tsari duk jikinta yasa tai
saurin nufarta tana fadar. ‘
Jika, wane la’anannen ne yai miki haka? Lahaula
wala quwata, kashe ki ake so ayi ne Jika? Wai
me ki kaiwa mutane ne yasa basa kaunar ki?”
Sai tasa kuka har da hawayen ta, cikin kuka tace
Waye yai miki haka Jika?” Rukayya ta ce, ”Su
Rakiya ne da Zulai’. * Kaka ta ce, ”Ai ko yau sai
na rama miki, don wallahi basu bugi banza ba”.
Abubakar ya qaraso yana fadar, ”Allah Yasa kije
su hada da ke ai ni zuciyata fari ta Allah Ya qara,
ai da ana miki haka da kin rage wani iskancin da
kike wa jama’a”. Kaka ta ce ”Tunda dama ba
tausayine dakaiba Ai idan sun kashcta baka da
asara, ai ni nasan ba qaunar mu kakc ba”dama.
Ta juya ta janyo zani ta yafa ta nufi hanyar fita,
Abubakar ya ce ‘ ‘ “Ina zaki kuma?”
“Zuwa zanyi in ramo mata tunda
Kai baka da amfani. Na lura ai na lura matsoracin
, banza nekai, baka da fushi sai cikin gida”,
Tayi waje tana mita ganin, bai ce mata Kala ba
har ta fice. Ya dubi Rukayya dake kokarin binta,
ya daka mata tsawa
“Karki kuskura , munafukar banza, duk wata
masifa ke ke haddasa ta, kinja ana ta zagar
mana kaka, kuma duk saboda ke. In bacin keda
kr debo mana rigima da wa ma yasan damu?
Masifaffiyar yarinya kawai.
Sai ki wuce kije ki cire kayan kiyi wanka ki canza
wasu, aike ne tunda baki so daga yau an gama
aikcn ki, sai ki zauna”, Ya watsa mata harara ya
wuce abinsa. .
Ta wuce simi-simi ta dauko zani ta debi ruwa ta
nufi krwaye tai wanka, ta dauro zanin ’ ta ajiye
mashi masu tsarin a bakin maguji, ta wuce daki
ta canza‘ wasu kayan. Sai dai babu mai ba
kwalli, haka aka sa kayan ta kama tai kwanciyar
ta saman gudo.