Rikon Kaka Chapter 6

Riqqon Kaka Chapter 5

This entry is part 5 of 6 in the series Rikkon Kaka by Sadnaf

RIKON KAKA

CHAPTER5

zaka siyar mawa, to ban siye, ka bani kudina

kawai”. ‘

Sunan qanwarsa da ya ambata shiya bugewa

Abubakar ‘dukkanin gaBoBin jiki, jikinsa a sanyaye

ya sa hannu ya Ciro kudin a gaban aljihunsa ya

mika masa.

Ya amsa yana fadar, “Mutanen banza kawai gaku

Musulmai amma kuna aikata aikin kafurai,

marasa tsoron Allah kawai”.

Abubakar dai bai tanka, masa ba. har ya fice

banda zafi da:. Kuna babu abinda zUciyarsa keyi,

yaji ya tsani ragon, bai son ma gaminsa

Yajasa ya fita waje ya sa

yaro yai masa sallama da makwabcin su malam

Bala talaka ne . Yana fitowa suka gaisa da

Abubakar sannan ya ce

‘ “Baba, dama ragona ne zai gaza, nasan kana

jinmu ma wata kila jiya. To shine na yanka, yau

na kira mahauci ya taya min shi yanda nake jin

ba zan iya siyarWa ba, gara ma na ba da shi

sadaka na San ladan tawa tana

wurin Ubangiji tunda mu ma za muyi layya shi

yasa na ce bari inzo in maka magana ka aika a

dauko maka”.

Malam bala ya shiga godiya yana zabgawa

Abubakar addu’a, shi dai bai ce komai ba ya

wucc ya koma gida, Malam Lado ya turo yara

suka daukar masa ragon.

Abubakar ya dauki buhun ya maidawa

Kaka, ya ce ”Ga buhun ki”. Kaka ta ce ,”Yo ya

fasa fedewar ne?” Abubakar ya ce, “Hmm! Idan

kun bari ba Kaka ta ce, “Kamar yaya kuma in

mun bari?” Ya ce, “Kamar yanda kika kitsa mata

taje ta sanar da mahaucin mushe ne na yanka”.

Kaka ta dauki Salati da sallallami, kafin

Ta hau rantse-rantsen ba ita tasa ta ba”. Ta ce

“Ke Jika, wannan kuma wacce dabi’a ce za ki

tsiro mana da ita ne?”

Abubakar ya ce, “Wadda ki ka’ koya mata, duk

abinda fitinanniyar yarinyar nan ke

Keyi kaka daurin gindinki ne take samu. Amma ba

komai, ni nasan maganinta, ba zai yiwu yarinyar

nan ta sangarce ta lalace ba, tunda har ta iya

wannan gaba ban san abinda zata yi ba, idan ta

Kara girma a haka to abin kuma sai yafi haka.

Don haka makarantar boko zan saka ta, taje can

ta koyi tarbiyya”.

Kaka da dauki Sallallami, “Wa za ka kai

makarantar Abubakar? Jikar? Baka isa ba,

wallahi babu inda za ka kaita a lalata marainiyar

Allah. Ka kai ta makaranlar boko ta koyi tarbiyya

k0 ta koyo iskanci?” Abubakar ya ce,”‘Oho dai, ni

dai na fada miki, k0 kina so k0 ba kya so sai na

kaita”. .

‘ Ya juya ranshi na suya ya ’bar‘ dakin, . yana jin

Kaka na rantse-rantsen babu me kai mata jika

makaranta.

Anci sallah lafiya, Kaka tayi layya ta

yanka dan marakinta, Abubakar bai yi ba don

gaba daya ya sai da ragunan sa,. ya ce kuma ya

gama kiwon.

Jika kuwa kayan Naira biyar bai siya mata ba,

haka tai sallar da tsofafin kayan ta, shi ya saka

ma ko kofar gida bata leqa ba _ Ana gama hutun

sallah Abubakar ya je yai wa Rukayya takardar;

haihuwa, washegari ranar Monday tun da sanyin

saflya ya sa tai wanka ta sauya kayan jikinta,

sannan ya tisa ta gaba suka tafi.

Kaka tace, “Wai gidan uban wa zaka kaita ne

Habu? Na fada maka kar ka sake ka kaita

makarantar bokon nan, ban son ta”. Abubakar ya

ce, ”Ai ko sai dai kar ki so . ta, amma makaranta

na kaita na gama”.

Ta sa kuka, yana jinta ya tisa‘ Rukayya gaba

suka ficce, can tsakiyar garin makarantar take

Sha ruwa Primary School, suka dauke-ta aka

kaita a‘ji uku, saboda ta wuce dauka.

Suna dawowa yaje ya yanko mata (uniform) ya

sai mata jakar makaranla da takalmi, sannan ya

sai mata littattafai.

. washe gari da kanshi ya tayar da ita ta: shirya

ya tisa ta gaba har kofar

makarantar, ya bata Naira ishirin kudin tara;

sannan ya wuce wurin aikinsa.

Rukayya ‘yan makaranta, karfe sha biyu aka taso

su daga makarantar, amma idan ka ganta ba

zaka ce ita ce tajc makarantar da sabbin kaya ba,

tai musu budu-budu, farar abayar har ta fita

daga kamannin ta.

‘Tana dawowa gida ta fada jikin kaka tana

murna, Kaka ta ce

“Oh Jika da tsiya dai Habu sai daya kai ki

makarantar nan don yasan ba yanda zan yiko?”

Rukayya ta ce “Kuma Kaka sai da aka buge

ni, dubi baya na”.

Ta cire abayar ta nuna mata, wurin yayi

,rudu-rudu da zanen bulala.

‘ Kaka ta ce, ”Wane dan iskan marar imanin ne

yai miki wannan dukan? Shi yasa na ga fuskar ki

‘ da zanen hawaye”. Rukayya ta ce “Wani malami

ne, wai daga muna fada ya ka mani yai ta bugu

ni kadai”.

‘ Kaka ta ce, ”Matsiyaci, ya kama ki yai ta duka,

to Allah Ya isa, tsinanne lnsha Allah bai gamawa

lafiya, kawai ka kama ‘yar marainiyar

Allah kai ta bugu kumar ka sami mandiri. Bari

Habu din ya dawo Jika, wallahi ba ki komawa

makarantar, sai dai yai duk abinda zaiyi, dauko

furar ki gata can ki sha”.

Rukayya ta mike ta dauko kwanon furar tana sha,

ta ce. _

“Kuma Kaka har Turanci aka koya mana da waka,

amma wai (This is a boll, These is our Apple,

That is your watch)”.

Kaka ta tintsire da dariya har saida sashinta ya

fito saboda bakin ba haqora, ta ce. ‘

“Kai amma abun da dadi, duk can aka koya

maku?“ ‘ Rukayya ta ce, “Eh Kaka”.

Ta cc, “Ai don dai azzalumin mutumin nan da kin

Kara zuwa”.

. . Rukayya tace. “Ai ban Kara zuwa nima tunda

buguna ake”. . Da yamma likis Abubakar ya dawo

gidan .ya iske Rukayya da kayan makarantar duk

ta: musu duwan-duwan, takaici ya cika Shi

Duk inda wata qazamar yarinya ta kai rukayyah

Tafita: Kazanta , daga cikin abubuwan da sukesa

yake qara tsanarta.

Ya watsa mata idanu babu sauqi a fuskarshi,yace

‘Wuce kije ki cire kayan ki kawo su wurin maguji’.

Ta mike a tsorace

ta nufi dakin nasu’.

Ya tsai da ita, ‘Tsaya ki tattaro dukkanin kayan

daudarki kawomani’.

Rukayya ta daga kai

Ta shige dakin, shi kuma ya wuce Washegari

yana tashi ya nufi dakin Kaka ya tashi rukayyah

tai shirin makaranta

Kaka tace kai babu inda zataje donka jini nan jiya

suka kamata sukaita bugu kamar jaka don haka

bata komawa

Abubakar yace,’ldanta zauna nan me zatai miki?

Nan makarantar allo ce kikai kane kane kika

hanata zuwa wao bugunta ake , sannan kuma

itama makarantar bokon sai ki

hana? To wallahi .ko kasheta za a rinka yi tana

dawowa sai taje har makarantar allon sai ta

koma“.

Kaka ta ce “Tunda dama ba qaunar ta kake ba ai

dole ka kaita inda za a kashe ta saboda

mugunta, haka kawai ka dauki karan tsana ka

dorawa yarinya, ka kaita a kashe ta don Allah,

idan an tashi a aiko mani da kai da qafarta gida”.

Abubakar ya finciko Rukayyar dake kan gado ya

jata suka nufi kofa YANA FADAR. ’

”Ba za, a kashe taba amma fa za ta daku kamar

ikon Allah”.

Bai ji abinda take fada ba don har ya kai bakin

kewaye, ya zuba mata ruwa a bokiti ya bata ta

shiga wanka.

Tana fitowa ya mika mata kayan makarantar ta

saka, ya ba ta mai ta murza ya zaro Naira

hamsin ya bata, ya ce.

Maza ki wuce ki tafi, kuma zan biyo bayanki

yanzu, ki tsaya wasa k0 da labe ne kiga ‘ yanda

zanyi da ke. Kina dawowa daga

makaranta ki ka ci abinci ki ka hula, ana kiran

sallar azahar kiyi sallah ki wucc makarantar allo

idan ba haka ba wallahi kika bari na samu labarin

baki zuwa na lahira sai ya fiki jin dadi wuce ki

tafi. ‘ Simi-simi ta wuce, daga daki Kaka tace.

”Yanzu baka barin tai kalaci haka za~ ta wuce ta

tafi?” , Ya‘ce, “Bata yi, ga Naira hamsin nan na .

bata ta siyi abinci ta ci”. ‘ -Kaka tace, “Indai

mugunta ce irin taka ai ta wucc da haka Habu,

yanzu haka zaka kora , min ita bata ci komai ba

salon tai karo da mayya k0 maye su lashe mini

ita?” » ‘ Abubakar ya e, ”Su hadiye ta idan ta

tafi”. ‘ , “ ” Kaka ta cc, ”Ba bakin ka ba, me

mugun baki. Insha Allahu aniyar ka sai ta bika”. .

Bai tanka mata ba ya wucc dakinsa yai nasa

shirin ya fice ya tafi wurin aikin sa, amma ‘yana

can sai da aka kawo mashi kashcdi wai Rukayya

tayi fada da wani yaro har ta cije shi a hannu ya

fasa. Ya basu hawuri sannan yaje

“Tana dawowa daga makarantar tana hutawa

akai sallar azahar ta fito zata tafi makarantar

allo

Kaka tace, ‘Yanzu zuwa za: kiyi k0? Mugun yaron

nan ya hanaki zama lafiya, duk indayasan za a

zalunceki saiya turaki Allah Ya saka miki’. .

Jika

Haka ta wuce makaran allon,.a can sukai sallar

la‘asar, Sai biyar na yamma aka tasosu

Tana dawowa tasamu Abubakar na gyaran cefane

cefane ta giftashi zata wuce ya ce‘

.. ’Kezonan’. , ta dawo gabansa ta durkusa ya

dubeta sosai kafin yace ,‘Wato saboda bakeke

wankinba shi ,yasa idan kika dawo makarantar

baki canja kayan sune na zaman gida kuma sune

na

Yawo cikin gari ko?‘

Shiru ba amsa, ya ce “Tashi kije ki ciri kayan ki

kawo mani”.

Haka ta mike ta ciro ta dawo da su a hannu, ya

ce

“Dauki bokiti gaya can da ruwa kisa ki wanke”.

Gaban‘ta ya fadi don tundatake bata taba wanki

ba, shi ke yi mata da kanshi. Haka ‘ ta mike taje

ta soma wankin kayan, yana kallonta har ta

gama ya amsa ya shanya. . .. ’ Sannan ya ce “ki

wanke hannunki ki , xo ki yanka mani alayyahun

can da albasa”. ‘ Rukayya ta dubi hannun nata

babu abinda ya yi amma har sai ta wanke ya ce.

‘ “K0 baki ji ba?”

, Haka ta wucc ta dauki buta ta wanke hannun

nata sannan ta je ta zauna tana yankan

alayyahun ya dora sanwar taliyar sa,tana gama

yankan alaiyahun ya ce

Jeki ki zuba” Ta tafi zata zuba cikin tukunyar .yai

saurin daka mata tsawa.

‘ “Ke banza, haka za ki zuba shi? Barbada mashi

gishin’ ki sa ruwa ki wanke”. ’

‘ Ta dauki uban gishiri ta maka yana kallonta ya.

ja tsaki ta zuba ruwa ta wanke ta tsane shi

sannan ya ce ‘

“Je ki zuba”. ‘ “

Taje ta zuba ta rufe, ta dawo gabansa.

“Na gama”.

Ya ce, “Jeki shi kenan”.

take ta nufl daki don kar ya qara saka ta wani

aikin

*** ******* ***

Wata ranar Juma’a RuKayya tana . makaranta tai

fada da (monitor) din ajinsu wai ta rubuta

sunanta cikin ‘yan surutu, malamin ya buge

su.duka Shine fA yana fita ta ‘ kama monitar da

kokawa’ gata ba iya fada tai ‘ ba, tai mata, duka

sosai. Akaje aka fadawa ‘ (headmaster) yazo da

kansa da bulalar sa ya zane Rukayya: radau har

tai fitsari saboda .

.azaba.

Yana fita ta dauki jikkarta ta gudo gida tana

kuka, ta fadawa Kaka. Ta ce, “Ai k0 yau sai ya

san ya debowa

kansa masifa”.

Ta dauki mayafinta ta ce “Muje inga matsiyaci”. ‘

Ta ja gida ta rufe suka dauki hanyar

makarantar har office dinsa ta kaita, yana

zaune saman kujerar dake gaban teburinsa sai .

wani mutum dake daga can gefe suna

magana. ‘

Kaka ta sawo kai cikin office din ba k0 sallama,

ta dubi mutumin dske saman _kujerar gefe tace. ‘

“Malam wurinka nazo, zuwa nayi inji uban da

yasa ka sa bulala ka rinka laftar mani

jika kamar ka samu jakka, k0 k0 shi Habu din

‘ nc da ya kawo ta ya ce ka sa bulala kai ta

bugunta harta ‘fita hayyacinta tai fitsari? To kotu

zata rabani da kai, wallahi sai nayi shari’a da kai,

sai ka bani labarin dalilin bugar mani ‘ya babu

gaira babu dalili”.

Mutumin yace Yi hakuri baiwar Allah, bani ne

(headmaster) din ba, gashi nan, nima zuwa nayi“.

Ta ce, “Karka sake ka zage ni’da turanci wallahi

na gaya maka, nima ina da

jika kamar ka dan makaranta” ~ Saurayin ya ce,

“Ikon Allah, yi hakuri don Allah Hajiya” ‘ ‘

Ya mike ya bawa (headmaster) hannu sukai

musabiha, ya ce.

“Ni zan wuce Yallabai, zan kira ka a waya k0 mi

kenan”. _ Ya wuce abinsa ya bar (headmaster) da

rigima. ‘ . Da yake kwararren dan boko ne sai ya

mike daga kan kujerar da yake ya ce.

“Hajiya zauna, bisimillah sannu da

_ zuwa, bari akawo miki lemu”. Kaka ta zauna

tana fadar, “Karka kaWO mani komi, dan iskan da

ya bugi Jika kawai

nake nema, wallahi sai na rama mata ,kaji na

fada maka

Lol ran kakafa ya baci mai zai biyo baya mu tara

later

a zallah shared a profile .

Series Navigation<< Riqqon Kaka CChapter 4Riqqon Kaka Chapter 6 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *