Rikon Kaka Chapter 6

Riqqon Kaka Chapter 6

This entry is part 6 of 6 in the series Rikkon Kaka by Sadnaf

RIKON KAKA

CHAPTER6

, Ya’ kwantar da ‘murya, “Ayi ‘haquri Hajiya,ai duk

abin bai kai na haka ba tunda ni da Jikar taki ai

duka jikokin ki ne,kua zaki’ iya‘ hukunta mu idan

munyi laifi, ‘ musamman idan ki ka same mu da

rashin gaskiya. Kiyi hauri kakata, ba a daki

qanwa -ta saboda zalunci ba, ‘sai don laifin da

tayi, ta

; kama shugabar ajinsu tai ta bugu Idan kika, ga

bugun da tai mats sai kin tausaya matA

. shi~yasa. Sanin da nai k0 ke ce kika ga haka

sai» kin daki jikar. nan shi yasa‘ na hukunta ta

saboda gaba amman kiyi haquri kaka Kalaman sa

sun Shiga Kaka don haka ta ~sassauta fadan

tace “Gaskiya kar a sake bugar min jika saboda

wasu yara can, marainiyar Allah ce uwarta da

ubanta duk sun mutu; ni kadai na rage mata. In

bacin yaya’nta ma da ba mai jin magana bané ai

daga yau bata Kara dawowa’ ‘ makarantar”. ‘

Ya ce, “A’a ayi hakuri, insha Allahu za a kiyaye”

ta mike, “To sai anjima, Allah Ya _ taimnka”. ‘

Ya ce “Amin Kaka”

Ta tasa Rukayya suka ficc daga (ofiicc) din,

(headmaster) ya koma ya zauna saman kujerar

sa yana murmushi, ya ce. _

“Ho! Allah Ya raba ni da ke lafiya” (Duk wanda ya

girmama tsohon wani shima ’za’a girmama nasa

a gaban idonsa k0 bayan idonsa

Da yamma bayan Abubakar ya dawo

~ daga wurin aikinsa yaji labarin zuwan kaka

makaranta, yai ta fada

‘ “Haba Kaka, .yanzu in bacin kin hadu da dan

mutunci ai da Allah kadai Yasan

yanda za ayi. Haba! ki ta abu sai kace kanki farai

jika? K0 ina sai kin fito da halin ki

To, “To ubaba, zoka dakan sai in san kaji haushi:

inba dukana kayi ba ai ban ssn kaji haushi ba

Abubakar ya ce, “Ai burinki inji haushi in fitar da

ita daga makarantar, kuma ba zan fitar da ita ba

wallahi ta zo ta dami al’umma, gara ta zauna can

duk wanda taimawa a zane ta”.

Kaka ta ce, “A daketa din ni kuma dukwanda ya

bugar min jika idan naji sai naje na rama mata

tabbas”.

_ ‘ Abubakar yace, “To shi kenan ki rama mata

din, hukumar makaranta ta sa a kama ki, wallahi

kuma k0 leke ba zan leka ba” Ta ce, “In ka tashi

ka manta dani k0 kasa a rufeni har dan makullin

ya bats” . ‘ Abubakar yai dariya ya ficce abinsa

don yasan halinta idan ya cika ta yanzu ta sa

masa kuka, ya tafi ya yo cefancn abinci ya_

dawo ya kira Rukayya, ya ce “Maza kisa tsintsiya

ki share gidan nan, idan kin gama ki min magana

ya wuce dakinsa ya barta tsaye”.

Ta sumBuro baki ta rasa dalili kwanan ‘ nan da

yake takura mata ba yanda ta .iya, dolenta ta

dauki tsintsiya.ta share gidan

sannan taje ta sanar masa ta gama. —

Ya fito yace, “Hada itatuwa ki hura wuta, ai dai

kinga yanda nake yi?”

. Idanuwanta suka ciko da hawaye haka ta je ta

hada itatuwan yana tsaye yana’ kallonta ya ce.‘

~ . .”To sa sabulu ki wanke hannunki ki . dauki

tukunya ki dauraye ki~aza saman ’

wutar”. Haka yai ta saka ta aiki daya bayan ‘

daya har sai da aka gama girka shinkafa’ da miya

k0 tsinke bai taBa da hannun‘ saba

Yasa ta dibar masa nasa; sannan ya ce. “Daga

yau aikin ki kenan a gidan nan kullum, don na gaji

komai ni sai kace dan daudu a gida.

_ Shekarar ki sha uku amma babu abinda kika iya

a aikace-aikacen mata, jikin ki ma ba ki damu da

gyaran sa ba balle na gida, , kullum kina, faMa da

qazanta ‘da shegen muni kamar don ke aka yi

shi, Mtsw!”.

‘ Ya wuce’dakinsa’ya barta tana ta faman

tukuki

“”””””. “””””””

. Lamarin Rukayya ya zama sai dai addu’a, don

ma Abubakar yana tsaye akanta

Wajen makarantar boko da ta all, idan kuma ta

dawo ya tisa ta gaba da aikin gida, yana zaune

yana bata umami haka zata yishi kotanaso ko

bataso

Kaka tai mitar tayi amma bai kulata, bai fasa

abinda yai niyya. Wani abin ma da gangan yake

saka ta don ya wahalar‘ da ita saboda ya lura

har yanzu bata yin hankali kullum abinta gaba-

gaba yake

Bakin ciki ya ishi Rukayya, Abubakar ya takuraWa

rayuwarta, bata da sukuni.

Yanda ya tsaneta itama haka take jin ta tsane

shi, musamman yanda yake nuna mata kyama.

‘kara’ra duk abinda za tai masa sai yasa ta

wanke hannu, idan k0 ta’na girki ta fyace ‘majina

sai yasa ta sa sabulu ta wanke hannu. Idan ta

shiga kewaye ta flto k0 tobai bari ta “qara taba

abinda za a zuba cikin abinci sai ta wankc

hannunta da sabulu k0me tai kuwa cikin

kewayen. .

‘ , Abun nan na ci mata tuwo a kwarya, haka

kuma take daurewa babu yanda zata yl,

duk duniya babu Wanda take jiwa tsoro irinsa; _

Ta ja wani gajeren tsaki yanda ba zai iya’juyo ta

ba, .ta ci gaba da tsane shinkafar cikin kwando

tana gamawa ta zubar da ruwar . tsane shinkafar,

sannan ta dauko mai ta zuba a tukunya, ta‘ zuba

jajjagen ta soya, yana soma soyuwa ta juya ta

dube shi.

‘ “Kamar yaya za a zuba ruwan?”

Abubakar ya dago kana daga karatun

jaridardayake, ya ce

“Wai ke wacc irin kwakwalwa gare ki ne? Komai

sai kin tamabayi yanda 2

Za a zuba‘? To ban sani ba, ki zuba yanda kike

ganin zai

isa Rukayya ta taBe baki ta wucc ta debi

ruwan ta tafi wurin tukunyar ta zuba, tana tsai da

ruwa .tashshin ya taso mata, sai atishawa wata

na bin wata. Abubakar ya mike da hanzarin sa ya

yo kanta cikc da takaici, ya cc. . . “Wai ke wacce

irin qazamar banza ce? Yanzu kina jin atishawar

ba za ki kauce ba k0ki tara rigar ki amma shi ne

za ki tofewa ; abincin da zamuci? To sai ki cinye

abincin” Ya ja tsaki ya balbalrta da harara ya

wuce abinsa, haushi ya kama Rukayya ta daure

ta ci gaba da. girkinta, ranar bai ci abincin gidan

ba. . Wa Shegari kuwa Rukayya cike take da

shi, sai ai ganin ‘nama me yawa za ayi falfcsu

yasa ta tsaki jiki taci gaba da aikin. ‘

_ Saida aka gama falfesun tas sannan Rukayya ta

bude da ‘niyyar’ ta motsa, da gangan ta zabga

atishawa a ciki har sau uku don taga iYakar shi.

Takaici da haushi ya cika Abubakar, yace”Kinyi

dai-dai, kin kyauta, daman burinki ki haramta min

cin naman kuma kinyi nasara”.

Ya karkace ya zaro dari biyar ya miqa mata. ‘

“Amshi, gashi kije ki siyo mani balangu na dari

biyu, tsire na dari, sai ki biya shagon dan Inna ki

siyo mani maltina guda”

Rukayya ta amshi kudin ta fice, tana jinsa yana

fadar.

Saura kuma ki tafi ki tsaya dambe k0 tsokanar

fada”.

Zuciyarta tai fes, saboda muguntar da ta shirya

mashi Tana siyo naman ta sami

zauren wani gida ta bude ta tattofawa naman

yawu sannan ta nannade yanda ba zai gane ba,

tai dariya ta wuce tai gida.

Yana zaune tsakar gida saman kujera ‘yar

.tsugunne, sai kaka wadda ke zaune saman~

tabarmar kaba, hira ake yi tana cin falfcsun

kamar duka kenan don da wuya a . gama hirar

abin bai zama fada ba.

Rukayya tai sallama ta kai mashi naman, ya

amsa ya ce ta dauko mashi flet ta nufi kicin ta

duko ta kawo masa.

* Ya ce, “Jeki daurayo min shi”.

. “ Dabi‘ar da ke konawa Rukayya rai,kenan sai

dai babu yanda zata yi wankakkrn filet din amma

sai an sake daurayo masa.

Ta daurayo ta kawo masa, ya ciro hankicif cikin

aljihu ya goge fllet’ din yana wani yatsina hanci,

ya zazZage naman cikin filet din ya Balle murfin

maltinar ya soma ci, yana ci yana Shan maltina

yana suburbudo . ” zance da alama naman na kai

masa karo

Rukayya ta zauna gefen Kaka suna cin falfcsun

naman, tana kallon yanda‘ Abubakar ke kwasar

naman har yana lumshe ido;

Dariya ta kwace mata sai kace wata zararra, ta

fashe da dariya har tana kyakyataWa. ‘

Abubakar ya tsaya da shan maltinar da yake

ya daddaure fuska.

, “Ke miye haka? Hauka k0 rashin hankali? K0 k0

mahaukata ne mu da zaki tisa mu a. gaba kina

kyalkyala mana dariya?” Rukayya ta guntse

dariyar saboda tsoron ‘ duka, ya ja tsaki ya ci

gaba‘ da cin naman sa.

Kaka ta ce “Ina ma laifinta harta iya yin dariya?

Haka kawai ka dauki karan tsana ka dorawa

yarinya, kai ta nuna mata tsana da Kyama haka

kawai, ai kaga naman yai mana auki, mu ci yau

har da safe a dunduma”.

‘ Abubakar ya ce, “Ba komai, da dai inci abinda

qazamar yarinyar nan tai Wa atishawa

to gwara in zauna da yunwa, saboda tunda nake

ban taba ganinta tana wanke baki ba balle

yankan akaifa, kullum hannunta na cikin baki tana

taunar akaifa, sai tai shekara kanta bai ga kitso

ba wai nan sunan tana mace sai fama ‘ take da

muni cike da fuska”

Kaka tace “Barakallahu masha Allah, duk wanda

ya raina tsayuwar wata to ya hau sama ya

gyara, kai nan har kyau ka fita?”

Yace, “Ai kyan namiji aljihunsa Kaka” ‘” . Tace,

“Gafara can, ai dai aljihun bai isa ya siyo maka

kyan ba”. , Abubakar ya ci gaba da cin namansa

yana fadar. “Maza dai ki kware saboda zafin

surutu, an kushc rabin ranki, masoyiyar ki. Kaka

tace “Fadi da‘ ihu ka qara da

‘ kururuwa” . Abubakar ya dukunkune takardar

Sannan ya wurga a Shara, ya shanye maltinar

yana faman gyatsa. Rukayya ta fashe da dariyar

da bata san

ta kwace mata ba. haushi ya kama Abubakar

ya zaro belt din wandonsa ya janyota daga gaban

Kaka ya soma dukanta, wai sai ta fada masa:

abinda takewa dariya.

Rukayya taji bugu ya ishe ta, tana kuka .. Tana

rokon sa yaKi ya kyale ta, Kaka sai zaginsa take

amma bai kulata ba. Da bugun ya isheta tace

“Tsaya don Allah in fada maka, wallahi naman na

tofawa miyau na kawo maka”.

Abubakar yai saurin sakinta.

What!”. ,

Ya fada hannunsa dafe da kirlji, ta ruga daki ta

rufe, Abubakar ya nufi wurin maguji yai ta kakare

kakaren amai, ya gaji aman yaqi zuwa,

idanuwanshi sukai jawur, ya nufi dakinshi.

~Kaka tai ta masa dariyar mugunta, tace

“Anqi cin biri anci dila ba Ai tai min dai dai, sai

muga ta kyankyami“. :

. Tsananin Bacin rai bai barshi ya kulata ba.

Hmmmm lol

a zallah shared a profile .

RIKON KAKA

CHAPTER7

Wata ranar Asabar abubakar ya zowa Kaka da

zancen yana so ya ajiye aikin kamfani ya ci gaba

da karatunsa.

Kaka ta ce “A’a Habu, yanzu sai ka

ajiye dan aikin da kake yi ka tafl wani karatun

boko?”

. Ya ce, “Kaka karatun boko yana da amfane

tunda aikin kamfani banda tabbacin dorewar sa,

gara in ajiye in samu in ida hada digiri dina, tunda

dai Allah bai hana

mu abinda za a ci ba. Ni dai ki min addu’a kawai

nake so”.

Kaka ta ce “To Allah Ya tsare, Ya ba

da sa’a, Ya shige maka gaba”.

Ya ce, “Amin Kaka, haka nake so”.

Lokacin da Abubakar ya jewa

Ogansa da zancen aje aiki ya ce

“Karkai gaggawar ajiye aikin ka Abubakar, yanda

aiki yake da wuyar samu a

Qasar nan, abinda ya Flye maka ka nemi alfarmar

kaje ka qarasa karatun ka

Akwai taimakon da muke bawa ma’aikatan mu

masu tafiya Karo ilimi, tunda wannan kamfanin

ba na gwamnati bane balle ace k0 ka tafl karo

karatu za a ci gaba da biyan ka albashi, ko ya ka

gani?”

Abubakar ya ce, “Hakan yayi YallaBai, ai ban san

da wannan tsarin ba, a gaskiya naji

dadi na gode Allah Ya tsare, Ya Kars budi”.

Ya ce, ”Amin Abubakar”.

Da wannan Abubakar ya baro kamfanin ya dawo

gida yaci gaba da buga-bugar. neman

(addmission) a Umaru Musa ‘Yar Adua University

amma abin ya gagara uban gidan ‘ nasa da

kansa ya sama masa (addmission) din.

A gaskiya Abubakar ya yi sa‘ar uban gida na gari,

mai tausayin na Kasa da shi.

Ba, a jima ba Abubakar ya soma zuwa (school)

suka kaishi aji biyu saboda yana da kwalin N.C.E

dinshi.

Abubakar ya soma karatu gadan-gadan, shigar

sa University ya haifar masa da ci gaba matuka,

daga Dandagoro yake hawa: mota zuwa Umaru

Musa Naira hamsin ya dawo hamsin.

Zuwansa makarantar yasa ya Kara wayewa, ya

Kara gogewa, ya fita daban da samarin kauyen.

Sai ma ya kasance kamar koyon kwalliya da sa

kaya yake zuwa, k0 k0 ganin samarin birni da

yake ne a wankc a goge yasa yake ta ruwan‘

dunkuna? Kullum cikin yin dinki da siyen kananan

kaya yake, gayun ya bi masa jiki k0 yaushe za ka

ganshi a cikin hadin (to match) yake

Da kansbi yake shiga cikin gari ya harhado kayan

kwalliya irin na samari masu jida kansu.

Abubakar ya samu ci gaba sosai a rayuwa, sai

kuma daukar kai da jan aji

wurin Rukayya kuwa abin sai , hamdala, ta dai

rage yawan tsokanar fada,

Amman qazanta da rashin san kwalliya sai inda

ya qaru k0 kadan bata son moriya. Ko Kaunar

abinda zaisa ta motsA jikinta

Harta shiga aji biyar a (primary) a lokacin

Abubahr ya kammala digiri dinsa, aka tura shi

(service) Kaduna

Rukayyu tai matuqar jin dadin; tafiyar shi

(service) din nan, ta sami sakewa. Ta ida hargitsa

tum, babu mai mata fadan tayi wanka ko wanki

Hatts gidan ya ida qazanccwa, Kaka k0 bata

sata: bata : hana ta, duk abinda ta ga dama take

yi

Duk lokacin da Abubakar ya dawo hutu ya

sameta haka zuciyarsa zataits: Baci, ya tirke. Ta.

sai ta gyra komi, hammr wankin sai ta yisu gaba

daya

A haka ya kammala (scrvice) dinshi ya dawnma

gida, wata ranar Juma‘a lokacin anyi ruwa: an

dauke ,

Ruwa yaima rukky mugun duka duk dauda ta

taso mata cikin jiki ta ishe ta da kaikayi

Kaka ta dube ta, “Don Allah Jika ki tashi k0 ruwa

ki watsa kiji dadin jikin ki”.

Rukayya ta ce, “Ni fa bazan yi wanka cikin sanyin

nan ba gaskiya Kaka”.

Kaka tace, “Ai shi kcnan, sai ki zauna jikin ki ne”.

Tana rufe baki Abubakar na yo sallama. tsakar

gidan, gaban Rukayya yai mummunar faduwa

saboda ta san sauran.

Abubakar ya sawo kai cikin dakin, sukai ido hudu

da Rukayya, yana sanye da suit baqa, ta matuqar

dacewa da jikinsa, idon sa na sanye da siririn

farin gilas, kamshin turarensa ya karade dakin.

Ya tsuguna ya gaishe da Kaka, baki washe take

amsawa.

“Lafiya lau Habu mutancn Turai , tubar kallah

masha‘Allah. Ni sai yanzu ma nake ‘ganin kamar

kana da dan kyau, ko k0 dai

idona‘ne?”

Abubakar yai dariya kafin yace ”Ke dai ki ka sani,

tsohuwar nan baki gajiya”

Ya mai da kallon sa kan Rukayya, ya bata fuska.

“Meke tsami ne a dakin nan?”

Ya kalli Kaka, “Hala waccar qazamar ce?”

Kaka ta ce “Ban sani ba, kafa dawo kenan zaka

soma k0?”

‘ Ya sake kallon ta, “ikon Allah, anya kina .da

hankali Rukayya? Kin k0 duba madubi kinga

yanda ki ke kuwa? Wallahi , wannan idan zan

ganki cikin dare sai in zaton Aljana ce take

kokarin firgita ni da mummunar kamar ta, tashi

kiyi: wanka ki sauya kayan jikin ki. Kazama kawai

dake, shi yasa gaki nan har yau babu bakon

takalmin da ya .taba takowa yana neman ki. Yo

wa ma

.zai kalleki yaji sha’awar kallon ki balle haryaji

sha’awar zuwa wajen ki?”

Kaka tace, “Kai ban son tsinannen surutun tsiya.

duka Rukayyar nawa take da harza a kafa mata

mugun bakin tsiya ‘

Abubakar yace, ”Amma k0 wancan zuwan da nayi

naji ance anyi bikin Zulai’ yar gidan malam Salisu

Mai tireda kuma ai duk

Sa o’inta ne.

Kaka ta ce ”Ka barts bawin jinin ya kashe ta kai

zaka aureta ne idan ta rasa nashinshinin balle

abin duniya ya ishe ka?”

Ya ce, “Allah Ya sauwaqe in auri wannan kucakar,

ai wlh k0 mata sun kare”

Kaka ta ce, itama Allah Ya tsare ta da auren

mugu kamar ka”.

Abubakar ya daka mata tsawa, “Za ki wuce ki tafi

kiyi wankan k0 sai jikin ki yayi tsami?” Aguje ta

wuce shi tai waje, ya Kara gyara zama

“Wallahi Kaka jikar ki kullum giRma take amma

tana cin qasa, wallahi ki mata

fada k0 ta gyara ta sami mashinsini”. Kaka ta ce,

“Kaga ka tashi ka fita idona

in rufe ka fada min inda ake da bolar mata?”

Abubakar ya mike yana fadar, “Allah YaSa kada a

bude ta a gidanki”. , .

‘ Ta ce, “Ba bakin ka ba mai mugun

bakin tsiYa, tunda fa ka dawo ai bakina ya

gama hutawa”.

Baice qala ba ya wuce dakinsa, Rukayya .ta

gama wankan ta fito ta sake wasu

Kayan ta fito ta shiga gyara kayan tsakar gida ta

dauki tsintsiya ta share gidan tai wanke-wanke,

don tasan sai ya saka ta tayi

Kaka ta ce “Sannu Jika, ai tunda wannan

jarababben ya dawo baki da sauran hutu sai dai

haquri”.

Bata dai ce komi ba saboda haquri ai ya zamar

mata dole

Kwanan Abubakar biyu da dawowa daga (service)

Rukayya ta gama karatun firamare dinta, har

(party) aka hada musu a makaranta.

Da dare Rukayya tana tsakar gida ita da Kaka

suna hira, ‘_Abubakar ya shigo da

« sallamar shi; ya ja kujera ya zauna yana fadar.

_ “Wasu samali na gani kofar gidan nan, na ma

dauka wurin jikar ki sukazo har zan kora su, ashe

makota suka zo zance

Kaka ta ccme,'”Ashe idan wurinta suka zo zancc

sai ka kora su’ saboda kai zaka aure ta ko?”

Ya. ce, “Ai ba ni din zan aurcta ba sai naga masu

aurcn nata sun zi

Kaka tace“Ai da yake idan zasu zo din sanar da

kai za muyi tunda muua jin tsoron ka”, ‘

Abubakar ya cc, “Wai da nayi magana saiki hau ni

da masifa, sai kace ni na hana mijin nan

yazo‘Tunda dai tayi nauyin jini Kaka ki haqura

kawai ta ci gaba da karatun ta har Allah Ya

k’awo mata mashinshini”.

Kaka ta cc, “Oho, sai yanzu na gane abinda .kake

ta yiwa ‘yan kewaye-kewayen nan, kace so kake

ka sa ta wata makarantar bokon, to baka isa ba,

wallahi kaci karya ka kwana da yunwa. Ai ba

tereren iskanci zanyi da ‘yar marainiyar Allah ba

kaji k0? Aure zan mata

Yanda ta taso mashi yasan ba karamin damben

tsiya za suyi ba kafin ta yarda ta amince masa

ya kaita (secondary school). Dinba yasa

Ya tausasa muryar shi kafin ya ce haba Kaka,

yanzu tunda babu mijin a hannu kiyi hakuri kawai

a kai yarinyar nan makaranta, tana ciki; kuma sai

kiga Allah

Ya kawo mata mijin ba har gida. amma yanxu

waye kike tunanin zai auri wannan gaibun?

Yarinya ba kyau, ba tsafta, ba natsuwa. ba

kwalliya, haba Ai abin yai yawa, don Allah ki bari

a kaita makarantar nan kawai sai kiga ma Allah

Ya taimaka ta ‘natsu ta zama‘ kamar kowacce

mace.

Kaka ta ce, “Kaga tun muna shaidar juna ka fita

idona in rufe

Yanda ta Bata rai yasa dole Abubakar

ya miqe ya fice ya bar gidan ma gaba daya.

Rakayya ta ‘sa kuka,”Wai ni Kaka kullum ya rinqa

cemin mummuna, wai ban da samari, wai ba farin

jini ne dani,ba wai haka ne Kaka?”

Kaka ta ce, “Ke kyale shi kinji, karyar banzar shi

ce, kina da kyan ki, kuma samari kisha kurumin ki

gobe da safe zan je gidan Malam mai almajirai in

karBo miki maganin farin jini, kiga yanda samari

za su rinwa tururuwar zuwa wajen ki. Sharc shi

kawai, dama .ai shi haka yake so ya samu ya

tura ki Hmmmm lol kakafa ta riqe wuta maizai

faru?????

allah shared a profile .

RIKON KAKA

CHAPTER8

wata makarantar boko, duk ki tsofr ki tsiyaye ‘ a

saman titi, ba dani ba sa lallrn kaza. Tashi mu

koma’daki ma kada ya sake dawowa ya ishe mu

da shegen dumi”. ,

Rukayya ta miqe suka wucc daki abinsu suna

labarin su har bacci ya’ kwashesu. _ ’ , ‘ ‘

Garih Allah na wayewa kaka‘ta dauki dan zaninta

kamar jira take gari ya waye ta tafl gidan Malam

mai ~almajirai; ta bashi sadaka ya bata rubutu

na sha da na wanke fuska, ya bata turare na

shafawa a jiki tarc da hayaki.

” Yanda ya rinka zuzzuta lamarin yasa Kaka ta

dawo gida da kwarin gwiwa, ta sami Abubakar ya

tisa Jika gaba tana cizgar wanki, a gefe kuma ga

sanwa ta saka, gidan yai wal, da alama shima

shire shi akai.

Kaka ta ce, “Kai jama’a Habu-baka da imani

wallahi yanZu duk rai. Daya ne kasa yai wannan

wahalar? ‘Daga wa‘yewar gari’ saboda rashin

tausayi?”

Abubakar ya ce, “ldan bata yi aikin gida yanzu da

sanyin saflya ba sai yaushe kike son tayi shi a

matsayin ki na mai rikon ta? Budurwa ce fa,

aurc’zata yi k0 yau k0 gobe, idan bata koyi aikin

gida ba sai yaushe kike son ta koya? K0 so kike

ta je gidan mijin tana Kazanta kwana biyu ya

koro ta?” Kaka ta ce, “Kai dai ka sani” ‘

Ta wuce daki ta barshi yana faman mita, ba

Rukayya ta samu ‘.ta samu kanta ba sai da ta

kammala aikin tas, tai wanka sannan ya kyaleta

ya wuce dakinshi.

Sai da ta ci abinci ta huta sannan Kaka ta dauko

mata kullin rubutun, ta ce

“Amshi kiyi bisimillah _ki shanye ki shafe fuskar

ki”.

Rukayya ta amsa ta sha ta shafe fuskar, sannan

Kaka ta bata turaren ta ce

‘ “Gashi wannan ki Boyeshi cikin kayan ki, duk

sanda za ki fita ki rinka murzawa a fuskar ki.

Jeki. ki. debo garwashi a marfin kwano ki kawo”.

Rukayya ta miqe ta fita taje wurin’ murhu ta debo

garwashin ta dawo daki, Kaka tace

“Dauko zani gashi can saman gado ki ‘ lulluBa”.

Ta mike ta dauko zanin ta zauna Kasai Kaka ta

lulluBa mata, sannan ta-zuba garin hayakin cikin

garwashin ta tura ‘ mata cikin‘ zanin. Hayaki ya

turnike Rukayya ta shiga tari, amma Kaka ta

hana ta fito da kanta .

‘ Abubakar ya hankadc labulen ya shigo. ’idon shi

ya sauka saman Rukayya wadda aka‘ rufe ruf da

zani, Abubakar ya zauna yana’ fadar ~ ‘

“Meye haka kuma?”

Kaka tace, “Hayaqi nake mata”. ‘

Abubakar ya,ce‘ “Subhanallahi! Don Allah bude ta,

ai sai ta sirqe, ke Ciro kanki ‘ kinji”.

RuKayya ta Ciro kan tana faman tari ,.

Abubakar ya cc, “Maganin mene wannan haka a

tura mutum cikin zani ai ta banka mashi hayaki?“

Kaka tace, “Maganin farin jini ne da kwarjini na

amso mata wurin Malam”.

Abubakar yasa dariya yana fadar, “Kai duniya,

idan har baka mutu ba baka gama kallo ba.

Yanzu samarin kuma har kiranyen su ake?

Kaka ta ce “Ashe baka da labari?”

Yace”Ban taba gani ba”. ‘ Ya mike ya dauke

zanin da Rukayya take lulluBe ya ce . ”Ke bude~

ki sha iska kinji, karku biyewa ‘ malaman‘ tsubbu

suyi ta cin kudin .ku saboda neman‘wasu sanari

haka kawai. Kema kin gaji da zaman gidan ko

kema samarin kike sone? ” Bata iya ce masa Kala

ba sai gwaggwale idanuwa take, Abubakar ya ce.

“To wa zai”so ki kina ‘yar banzar qazanta Ai k0

asiri yana bukatar

‘ mataimaka“.

Kaka ta ce, “Shin wai kai ina ruwanka

ne a cikin lamarin ,mu_ iye? .lna harkar ka daban

tamu daban, ka barmu muyi sha’anin . mu

kakoma kai naka tunda ciwon mace na mace ne. ‘

Abubakar ya ce, “Nima ba sa muku baki nai ba,

amma ba zan so samari su rinqa zo mana gida

ba haka kawai babu gaira babu dalili”. ,ba

Kaka ta tsare shi da idanuwan ta’ kafin ta ce,

‘Shin yarinyar nan idan sonta kake ka fito ka fada

kawai, ‘ ba wai kai ta ‘yan Zagaye zagaye ba”. ‘ ‘

‘ Abubakar ya mike yana dariya saboda zafin

yankar da Kaka tayi masa, bai ce uffan ba ya fice

abinsa

Kaka ta bishi da kallo har ya fice yana

murmushi, Rukayya ta zauna bakin gado tana

turo baki sai kacc shantu.

‘ Kaka ta ce “Jika anys sai inaga fa~kamar

Abubakar sonki yake don na_ lura duk

lokacin da za ayi maganar auren ki k0 saurayi

hankalin shi na tashi”.

Gaban RuKayya yai mummunan faduwa, ido waje

ta ce

“Kaka shi ya fada miki? Don Allah kada ki Kara

maimaita zancen nan har yaji”.

‘ Kaka tai murmushi kafin ta ce, “Jika Habu sonki

yake na riga na gama gano inda _. ya dosa”.

Rukayya ta ce “Kaka Yaya Abubakar din da ya

tsane ni, keda kanki kike fada mani ba ya sona,

yanzu shi nc za kice yana sona? To ni bana

sonshi, macuci, aZzalumi kawai”. Kaka ta girgiza

kai’Nima da farko

haka na dauke shi Jika, amma yanzu na ~ gama

amincewa Habu ne mijin daya dace dake’irinsa.

Dubi shekarun ki mana,‘yanzu shekarar ki sha

shidda, ya dace ‘ace .yanzu kina dakin mijin ki

amma kullum‘sai ya nuna mana ba haka ba.

Yanzu be na fahimci abinda , ke qarkashin ransa,

murmushin da yai kawai

‘ ya tabbatar min da komi”. ‘ ‘ ‘ ~

Rukayya ta kwanta bakin gadon ‘tace, “Ni dai‘

ban son maganar nan Kaka, k0 yana sona ni bana

son shi, ba zan auri wanda zai rinka zalunta ta

ba”.

Kaka tace “Ke denawa zai yi da anyi aurcn”. . ‘

Rukayya ta shareta tai kamar ma barci ‘ ya

dauke ‘ta, don bata ma son wannan ‘maganar,

dole Kaka tai shiru tunda babu , abokin magana.

********************

Da .yamma liqis Abubakar ya dawo wurin aikinsa

da ya koma yau tun dawowar sa daga sabis. Ya

rage kayan jikinsa ya leqa dakin Kaka yai mata

sannu da gida, a “lokacin Rukayya tana

‘makarantar allo.

’. Ya dawo ya nufi kewaye ya watso ruwa ya fito

sannan ya nufi dakinsa ya shirya cikin wani

lallausan farin yadi marar zane mai

gaShi-gashi ya saka (light blue) din hula ’marar

nauyi Ya sa farin gilas da takalmi kalar

hular, ya fcsa turare ‘mai sanyin kamshi sannan

ya fito tsakar gidan.

A lokacin Rukayya ta dawo makaranta tana zaune

tsakar gida ita da Kaka suna shan iska Abubakar

ya shigo, yana daga tsaycmr bakin Kofa yace.

‘ “Kaka, ni zan dan fita shagon hadi in dawo”.

Kaka ta ce, “Allah Ya kiyaye.

Ya juya‘ya fice abinsa ya bar su suna Shakar

kamshin turaren sa.

Kaka tace “Wallahi Jika ina maki kwadayin aurcn

yaronnan Habu, shi ne irin , mijin da idan ki ka

same shi za ki shiga cikin jerin sahun matan da

suka more miji a duniya”.

Rukayya ta kafewa Kaka idanuwa tsawon lokaci

tana mamskin yanda akai Kaka ta mance da

mugunta da zaluncin Abubakar cikin kankanin

lokaci.

Bata da abin cewa don haka ta mike ta nufi daki

tai kwanciyar ta don bata san

abinda zai dami zuciyar ta, in banda ma abun

Kaka ina ita ina yaya Abubakar? Dan birni,

wayayye, wanda boko ya ratsawa kai, yake ji da

kansa. ‘

“Mtswl”.

Ta ja wani gajeren tsaki tai juyi abinta, ta janye

tunanin ma kwata-kwata a zuciyarta.

Washegari tunda garin Allah Ya waye Rukayya ta

shirya ta tafi makaranta amsar (Testimonial) a

can wurin dawowa sukai fada ita da wata har ta

keta mata tata, aka taho gidan su Rukayya riyyy!

Abubakar yana tsakar gida yana wankin ‘

kananan kayan sa yara suka shigo, ya ce ‘ “Kai ‘

ya akayi ne?” Aka soma yi mashi bayani, “Ai

Rukayya Lawal ce ta yagawa Hamida Testimonial

dinta, daga suna fada Abubakar ya cire

hannunShi daga cikin bokitin wankin ya nufo su” .

” :tana ina?”

Sukace , “Tana baya”.‘.’

Ya amshi Testimonial din ‘yasa salatEf ya gyara

masu, sannan ya basu haquri. Kaka za ta hausu

da masifa wai jan Rukayyar .suka yi, Abubakar ya

basu hakuri suka tafi.

_ Suna fita tana shig0wa gidan°Abubakar ya bita

da kallo cike da takaici, har zata wuccme shi

yace.

“Ke, zonan”.

Ta dawo ta duka gabanshi, cikin takaici ya ce -‘

“Wai yaushc za kiyi hankali ne Rukayya? a,

Kullum kina girma kina~ qara cin kashi? Yanzu

baki ga yaran nan qannen ki bane duk kin

girmesu amma ki mai da kanki sakarya a. cikin

su sai kacc ba babba ba? Ke kenan kullum baki

gajiya da masifa, ta yau daban ta gobe daban tun

kina karamar ki har yau ba ki

barmu mun huta ba? _ . Yanxu dubi jikin ki, dubi

kayan dake ji kinki da yanda kike da qokarin fada

haka’ kike da qokarin tsafta ai da anji dadi. Tashi

. kije Allah Ya shirye ki”. ’

Rukayya ta mike ta wuce daki tana ..gun-guni

qasa-qasa. yanda ba zai jiyo ta ba. ~

Ta zauna gefen Kaka tana ta tukubiri,

Kaka ta ee. ‘ ‘ . . “Jika tunda kinga baya son

yawan fadace-fadacen nan ki barshi mana, ki

rage yawan Bata mashi rai tun kan ayi auren nan,

ba‘a son masoyi na yawan Batawa masoyin sa

rai, kidaina”. ‘ Cikin takaici Rukayya tace, “Ina

kika‘ taBa ganin yace yana -sona? Wai ‘tsanar da

yake mani ita ce soyayyar k0 mi? Ki daina fadin

yana_ so na wallahi bai taBa sona ba, qina’ kawai

yake”. Sai ta sa kuka.

‘ Kaka tai murmushi ta janyo ta jikinta, “Yi haquri

Jika, ki daina kukan nan, da za ki rage yawan

abubuwan da baya so da kin , .tabbatar da

abinda nake fada miki. Wallahi Habu yana sonki,

kuma za ki tabbatar da ‘ hakan, kiyi tunanin me

yasa yake yawan son kiyi kwalliya me yasa yake

son kiyi karatu.’ Me yasa yake son ki natsu‘ Ba

don kewa

yake yi ba Jika sai don kanshi yake yi. kiyi

tunanin hakan”. :

. Rukayya tai ‘shiru tsawon lukaci, a wannan

karon zuciyarta ta soma hararo mata abinda

Kaka ke son nusar da ila, to amma idan yana’

sonta me yasa ya tsaneta yake yawan dukan ta

yana hantarar ta? K0 k0 dai ~ shi kalar tashi

soyayyar kenan?

Tambayar da bata da mai amsa ‘mata, ta lumshe

idanuwanta tana hararo kamannin sa,

kyakkyawan saurayi ajin farko wanda ya kware a’

Bangaren iya sanya sutturar da ta dace da ‘shi

da hada kalar masu kudi.

Ta ji muryar. Kaka na fadar, “Ki budr-zuciyar ki ki

cusa sonsa Jika, saboda kada lokacin da zai

furta kisha wahala da zuciyar ‘ ki wajen amsa

tayinsa.

Yayanki namiji ne irin wanda matan

birni ke yayin sa kuma insha Allahu kafin ayi

auren zaku dai daita tsakanin ku, ku fahimci juna

ku watsar da duk ‘wasu makaman ,wiyayyar dake

tsakanin_’ku. Jiya har wajen

Rukayyah aurenku akwai alheri kuma akwai rabo

tattare dashi don haka Rukayyah ki nutsu sannan

iso habu sosai kii ragewa. kanki Kiyayyar nan don

Allah”.

Rukayyya tai shiru bata da abin ccmewa, ita ba

wai Rayuwar aurensu take jiba illa tsoron yanda

abin zai kasance, Ina fargabar yanda al’amurin

zai kasance don ita kanta ba wai sai ‘ an gaya

mAta ba, tasan Abubakar yafi karfinta ta kowace

fuska tasan ba sa’an aurcnta bane.

. Sai dai yanda Kaka take ta nanata

Kamarin ta sa ta soma ingiza zuciyarta a kogin

soyayyar sa ta soma yaudarar kanta, ta soma

sawa’zuciyarta kwadayin auren mutumin‘da yafi

karfin ajinta.

Abu kamar wasa Karamar magana ta soma zama

babba, saboda yanda soyayyar Abubakar ta soma

girma a cikin zuciyar ruky, .musamman yanda

‘_takcme ganin yana daukar Wanka’, dukkayan da

ya saka sai sun masa

kyau manyan kaya k0 qanana k0 shigar turawa

suit, har kayan lndiyawa yake sanyawa Pakistan,

suma suna masa kyau matuqa. ldan ka ganshi

sai ka rantse da Allah bai san hanyar kauyc ba,

saboda gogewa da haduwa amma ciki yake

kwana ya tashi.

Yanda zuciyar Rukayya take kwana ta tashi da

qaunar sa yasa har ta kai ta kawo bata iya barci

idan ba ta ji muryar sa ba k0 ta ganshi ko da

tsawa ce yai mata sannan take samun nutsuwa.

Abun har mamaki yake bata yanda ta tsinci kanta

a soyayya, abinda bata taBa yi ba.

Fatan ta dai Allah Yasa shima abinda kezuciyar

sa kenan.

‘ ****************

Suhaila ta kwaso a guje ta nufi falon

_ mommy dinta wadda ke zaune kan

lumtsimemiyar kujera 3 sitter

tana gyaran wasu tulin takardu, Suhaila ta fada

kanta gamida rungumeta cikin murna tana fadar

“Mommy albishirin ki?”

Hmmm lol

Allah

RIKON KAKA

CHAPTER9

Ta saketa ta zagayo ta zauna gefenta ta

ce “Mommy Mansir ya dawo daga Brazil, ya

kammala karatun sa” . ~. Mommy tai murmush1

kafin ta ce

“Hmmm! Ke wa ya fada miki?”Ta ce “Yanzun nan

Hanifa kanwar sa ta

kira ni take fada min jiya ya dawo cikin dare‘ ’ Ta

ce “Shi ya ce ta fada miki k0 k0.

gaban kanta . ne‘? ” Suhaila tace, “Kai mommy,

kema dai wanda ‘ya dawo cikin dare hadmr ya

isa yin wata hira?” Mommy ta tabe baki kafin ta

ce, “Iska na ‘wahalar da mai kayan kara, ni

wallahi in bacin ‘so‘_sone amma banga abin so

‘wurin wannan ‘yaron ba. ‘Yaro yana tafe yana

faman doro sai kace‘ ,shugaban zabbi‘, mutane

masu mutunci suna ‘sonki amma ki ka‘ zauna

jiran wani Mansir shekara uku kamar daga kansa

maza sun kare”. Suhaila ta mike tana fadar,”Kai

ni dai ‘kinga tashina, mommy ke kullum ba ki

gajiya

da mita. Ai dai . .tunda ya dawo zan iyasa direba

ya kaini in masa sannu da zuwa”. Ko

Mommy ta ce, “Da yake baki da magayi k0? Ai

duk saurin unguwar zoma ta bari a haife, tunda

bai fada miki ya dawo ba da bakinsaba sai ki

saurara ya kira ki ko yasa a taho miki da

Iefensa”.

Suhaila tace, “Kash! Mommy kina da (problem),

wa ya fada miki zamanin ku da namu iri daya

ne? Ai da mata ke Jawa maza aji,

amma banda yanzu”. ‘ Mommy ta ce “To aje a

yubar da ajin

tunda zamani ya canza”.

Suhaila ta fice tana gunguni, mommy ta bita da

kallo harta fice, ta girgiza kai ta ci gaba da aikin

gabanta. .

Suhailat tana shiga dakinta (toilet) ta fada ta

watso ruwa, ta jima tana wanke lungu ” da sako

na jikinta tamkar amaryar da sabon angonta zai

zo gareta. Ta fito daga (toilet) din tana tsane

jikinta da tawul. .

‘ Ta zauna bakin (mirrow) ta murzawa jikinta

(cream) mai kamshin gaske yabi fatar

jikinta yai (smooth) sannan ta shafa hoda ta kai

kala hudu. Ta qawata fuskarta da kayan kwalliya

irin na zamani, tai gwanin kyau. ‘ Ta mike ta nufi

kan gadonta ta dauki kayan dake sama, sabon

less né mai matukar kyau da tsada Wanda aka

amso mata dinkin shi jiya daga shago

‘ , Ta saka dinkin riga da siket ne sun bi jikinta

Sosai, ta dauki kalabin ta ta nufi gaban madubi

ta , raba gashin kanta gida biyu, ta jawo shi ya

hau ‘saman bayanta sannan ta nade ‘ shi a’baya

ta daure: Ta kafa daurin kallabinta mai“ kama

da_rawani, ya dauru sosai, gashin kama ya zame

mata tamkar acuci maza.

’ Dan kunne da sarwa duk na (gold) ne ta saka’

ta hau Wata ‘yar siririyar agogonta shima na gold

ne Ta dauki siririn mayafinta ta,yafa saman

kafadar ta ts saka takalminta’ mai tsinin gaske

saboda bata ‘da .tsaWo sosai ta dauki ‘yar

Karamar jikar ta’ :ta hannu ta dauki manyan

wayoyinta

Suhaila kyakkya’wa ce ajin farko, fara ce ‘ .

tas.har_ wani yalo-yalo take, gajeriya ce mai

matsakaicin jiki, Allah Ya wadala ta da dirin jiki

na daukar hankali. Tana da matsakaiciyar fuska

mai daukeda daradaran idanuwa da dogon hanci,

bakinta daidai misali.

Suhailat tana da kyau matuKa, matsalar ‘ta

kawai gajarta, itama gajartar ba a gane mata

saboda duktakalman da lake amfani da su masu

matukar tsini ne , . _ Suhailat ta wucc kai tSaye

zuwa harabar gidan ba tare da ta bi ta sashin

mommy dinta ba,tana fitowa harabar gidan direba

ya kwaso da dan gudu-gudun sa ya bude mata

gidan baya ta zauna, sannan ya tambaye ta.

“Ina muka yi Hajiya?” . . . Ta ce, “Gidan Alhaji

Maiwada zaka kaini, gidan su Hanifa” ‘

Dircba ya ce, “Oh,na gané”

Sannan ya rufe mata kofar, ya zagaya ya shiga

ya tashi motar suka fice daga harabar gidan,

maigadi ya hangame musu gate suka fice

Unguwar alkali suka nufa daidai saman

sabon titin unguwar alkali, qaton gida ne wanda

yake saman titi. Direban yai hon maigadi ya bude

ya sa hancin motar’cikin get din gidan. Sai da ya‘

fara gaisawa da maigadin Sannan ya nufi harabar

gidan kai tsaye ya faka motar Wurin da aka

tanada don ajiye motoci, sannan Suhailat ta bude

motar ta fito ta nufi gidan kai tsaye.

Katon gida ne kai da ganinsa kasan a .gidan an

zuba Naira, sai da Suhailat ta wuce faluka kusan

hudu Sannan .ta shiga Wani Emwaton falo, tana

yin sallama taji ihun qawarta Hanifa, ta kwaso

aguje suka rungume juna suna dariyar murna

suka shiga falon. .

Hajiya Sadiya tana hakimce cikin kujera . tana

lallatsa laptop, , ta dago tana kallon Suhailat har

ta shigo falon ta zauna tana fadar.

“Ina kwana Momcy“.

Sannan Hajiya sadiya tai murmushi, “Lafiya lau

Suhailat, ashé ana ganinki? Ai mu , tuni na riga

nayi fushi, mu baza kizo ki

Koxo“ ki ganmuba amma tunda hasken ranki ya

dawo ai gashi kinxo

Suhaila tai dariya ta dubi Hanifa cike da jin

kunya, tace

”Ba haka bane momcy’.

Hajiya Sadiya tace, ‘To yayane? K0 kina nufin

bakisan ya dawo bane

Murmushi kawai tayi don bata: data cewa kuma.

. Hajiya Sadiya ta miqe da laptop dinta a

hannuma tana fadar.

”Ni kinga nama haye sama tunda dai nasan

wannan :zuwan Mansir ne, idan kingama ganinsa

kin biya mu gaisa. Dariyn kawai tayi, Hajiya

Sadiya ta haye sama.

Tana barin falon Suhailat ta ce, “Ke qawar ina

Yaya Mansir din yake ne? Ni fa qagare nake naga

yanda ya koma‘

Hanifa tace, ‘Amma kya bari a kawo Maki

abubuwan motsa baki saunan k0?” , Suhaila

tace’A‘a, idan na ganshi na dawa naci. Hanifa ta

harare ta ce “Allah Sarki dadi

‘ ai nasanma k0 kinje yaxu bai farka

daga barci’ ba, ‘don Yaya Mansir sai ya kai

dayan rana yana barci”. Suhailat tace, “Eh naji,

dai yana ina .inje in tayar da shi?” ‘ Hanifa ta ce,

“Ai da yake kece nasan zai tashi, ba zai miki

masifa ba. Kije yana dakinsa da kika sani”

Suhailal ta mike da sauri tana dariyar murna ta

nufi hanyar dakin nasa, sai da ta fita ‘ falon ta

shiga wani sannan ta nufi bangaren sa,

ta, tura kyauren dakin. ‘ A bude ta Same shi, don

haka ta shiga da

sallamar ta. Duk da ba a amsa mata ba hakan‘

bai hana ta sa kai ba cikin falon, qaton falo ne

mai dauke da wasu kananan kujeru irin na‘

ma ‘aikata, sai wasu kujeru biyu da katon tebir a‘

‘tsakiya aka dira computer desktop a sama, a.

gefe kuma, jikin bango aka sa kayan kallo ‘ ‘

Suhailat ta nufi dayar kofar ta tura ta

; shi ga, karamin falo ne babu abinda ke cikin sa

.sai karamin gado da qatuWar wardrop da

“sauran tarkacen kayan maza.

Yana kwancc saman gadonsa a lullube da bargo

yana faman sharar barcinsa hankalin sa a kwance

Ta nufi kan gadon ta zauna. gefe idanuwanta na

kansa. Ya qara haske da qiba har wani tumbi-

tumbi ya ajiye, sai taga ‘ qibar tasa ta? rage

masa kyau kok0 saboda sumar da ya kara ne

oho.

“Yaya Mansir mutancn Brazil”

_ Suhailat ta furta tana murmushi tare da dan

bubbugar kafafuwan sa.

Ya motsa jikinsa kafin ya bude idanuwansa kadan

yana kallon ta, kallon qurillah. Suhailat ta sakar

masa murmushi _‘ wanda har ya bayyanar da

haqoranta.

Mansir ya yamutsa fuska ya tashi zaune suna

qarewa juna. kallo, babu riga a jikinsa, daga shi

sai dan gajeren wando na maza

Cikin nitsatssiyar murya ta ce, “Sannu da zuwa

Yaya Mansir ina‘ kwana?”

Cikin rashin kulawa ya ce, “Suhailat ashe ba kiyi

aure ba? Amma dai gaskiya kinyi jinkiri da

Aini na zata tuni kin tSUfa gidan miji qila ma har

da yara’‘ Kirjin Suhaila ya Shiga barazanar ‘

fashewa duk da A.c din dake dakin bai hana zufa

kwararowa jikin Suhaila ba ta rinqa jin tamkar

ana kada kalangun tashin hankali a ’kirjinta. Take

idanunta suka ciko da kwalla Fashewa da kuka

‘tayi, tace, “.Yaya Mansir ba dai kana nufin harka

mace da. alkawarin mu ba? Yaya Mansir kana

nufin har ka mance da Suhailar ka, Wadda kake

so take son ka, wadda ku kaiwa juna alkawarin

soyayya da amana? Haba Yaya Mansir, kada ka

cutar da ‘zuciyar da bata da tunanin cutar da kai

ba, kar ka guje ni don Allah‘ ‘wallahi zuciyata ba

za

ta iya jure rashinka ba, (please) Yaya Mansir don

Allah”

Hawaye suka ciko gaba da bin kumatun ta ‘

tamkar an kunna famfo

Mansir yai dariya kafin ya ce,”Suhailat

kenan, har yanzu kina nan da halinki

da na’ sanki da shi” .

Ya kara murmushi kafin ya ce, “Ke yanzu in

banda abinki Suhailat ai kin min tsufa; ina ke ina

ni me qananun shckaru? Yanxu haka fa shekarar

ki biyu da gama digiri, inajin ma har kin soma

aiki.

. Haba Suhailat,‘idan za kimin adalci _ai kema kin

san ba mu dace ba, yarinya nake ncma karama

mai kananun shekaru, wadda bata wuce (lebcl

‘200) ba a jami’a, (please) Suhailat ki taimaka

don Allah ki janye wannan xanccn tun wuri”. Cikin

firgici Suhailat ta ce, “Ban gane abinda» kake son

fada ba Mansir dukaduka a nawane shekarun

nawa‘? 25ycars nefa only, meye tsufan da nai wa

saurayi me shckara talatin da wani abu? Kai dai

kawai ka fadi. wani abin amma ba dai‘ wannan

ba,‘ kawai kaCe kai dai ka daina sona, ka sami

wadda ta fini kyau da komi amma ba kaita yimin

zagaye zagayeba, ka filo kafito kawai kacc ka

daina so na”

‘ Yanda take magana cikin daukar zafi yasa

Mansir ya lahimci ta soma shaqa don haka ya

kara kular da ita da cewa

“Suhailat, duk yanda kika dauka haka nake nufi

shiyasa: kike birge ni wani lokacin, saboda kinada

saurin ganewa. Ai dama na taba gaya miki Shi so

tamkar tsuntsu yake yakan tashi a duk lokacin

dayaso ya canja bishiya. Kiyi hakuri Suhailat in

har so cuta ne hakuri, ma magani””””’

‘ “Ya isa Mansir! Wadannan jahilan kalaman naka

sun ishe ni haka” .

Ta mike ta bar dakin gudu gudu sauri sauri ta

bar masa falon

Yana kallonta k0 a jikin sa don dama hakan yake

bukata. yai murmushi ya ‘ koma ya kwanta

abinsa yaCi gaba da barcinsa ‘ hankalin sa

kwance

Suhailat tana fitowa daga sashin sa kai ‘ tsaye ta

bar gidan, direba na tambayar ta lafiya‘! Amma

bata kula shi ba a dole yai shiru gida suka nufa

kai tsaye

: Kuka take sosai tamkar wadda ” aka . aikawa

uwarta da ubanta sun rasu ‘gaba daya har suka

isa gidan tana abu guda, jikin direban yai sanyi.

Yanda yaga ta bude murfin motar

Cikin tashin hankali

Lol soyayyah kenan

Mu kwana lfy

 zallah

RIKON KAKA

CHAPTER10

Fice tana shasshekar kuka ya bita da kallo, sai

dai bai da ikon da zai bata baki sai yaji duk

jikinsa yayi sanyi dole ya tsaya inda aka ajiye shi

Suhailat na shigowa falon gidan k0 gani bata yi

har karo take da tebir din dake tsakiyar falon,

mommy ta ce

“Ke meye haka da za ki shigowa mutane ~ . k0

sallama babu?” . Ba ta tankaba ta nufi –

bangarenta tana ‘ , faman kukanta, jikin’ mommy

din yai sanyi

ganin irin kukan da Suhailat din take tamkar ta ,

share ta, sai dai ba zata iya ba, a_ dole ta daure

‘ta mike ta nufi sashin nata.

Tana kwance saman gadonta tana faman ‘ ~ rera

kuka, k0 takalman ta bata cire ba. ~ ‘ ‘ ‘ Mommy

ta zauna gefenta ‘cikin tausassar‘ murya ta ce:

“Lafiya Suhailat? Me ya faru?” ‘ ‘

Ta gaza magaba sai dai kuka, mommy “tai juyin

duni’ya amma Suhailat taqi magana, sai dai kuka

har ta’gaji ta tashi ta barta‘ Ta nufi falo ta dauki

wayar ta, ta kira Hajiya Sadiya , taji k0 sun san

abinda akai mata?

Hajiya Sadiya ta ce’ai bata ma’san tafiyar taba,

tace bari ta kira Hanifa taji abinda ke faruwa. “

Mommy ta Ce, “To” ‘

_, Wasa-wasa har yamma Suhailat na abu -‘

daya, k0 abincin da aka kawo. mata taki. ci sai ;

. dai kuka kawai take, kuma taqi? magana. ,

‘ Ana idar da sallar isha’i Alhajin: su ya

dawo, tana falo Hajlyar ta tare shi, ta ce.., .

“Babu fa lafiya a gidan yau Aihaji,

Suha’ilat tun safe take kuka har yanzu, taqici.

taqi sha sai kuka”.

Alhaji ya ce “Dama nasan hakan zata‘

faru”. ‘ Ya‘ mika mata jakar hannunsa, yace

“Haumin da ita sama,‘ sai ki kirawo min ita

, Suhailat din”.ta‘ Dole mommy ta janye

tambayoyin da

‘ suka Cika’mata zuciya, ta wuce ta_hau benen

da ‘ ‘

zai kaita sashin Alhajin. ‘ Tana; fitowa ‘ta nufi ‘

Bangaren Suhailat din, a kwance ta ‘ same ta

tana kukan nata kamir’wata karamar yarinya;

Mommy ta tsaya daga bakin qofa, ta ce ,”Kije inji

Alhaji yana falo yana jiran ki”.

‘ Bata ji ma abinda za ta fada ba tajuya ta fice.‘ ‘

‘ Suhaiiat ta yunkura ta mike jikinta a mace ‘ ta

ja kallabinta ta daure gashin nata wanda duk ya

yamutse,sannan ta sauko daga .kan gadon ta

nufi falon. ‘

. Muryar ta a shake tamkar mai mura, tai ‘

sallama ta shiga falon, Alhaji ya kafa mata

idanuwa har ta zauna. Rana daya kacal harta

zabge, ta lalacc, sai kace wadda tai ciwon

’ shekara.

. Alhaji yace, “Suhailat, dazu Alhaji Maiwada ya

sameni kamfani yazo min da wani zance Wanda

ga dukkan alamu kema kin . sami labari , to

abinda nake so Suhailat ki sawa . ,zuciyar ki

haquri don Allah ki ‘mance da , Mansir da

labarinsa’, tunda bashi kadai bane namiji a “

duniya ‘

Suhailat ta Kara fashewa da kuka kafin tace ‘ “Ba

zan iya ba Alhaji, wallahi ba zan iya

‘ ”Zancen banza kenan Suhailat, ai ya zame miki

wajibi ki mance da shi tunda mahaifinsane ya

same ni ya sanar dani sun janye ‘ wannan

maganar tsakanin Suhailat da Mansir tuni dama

ai ba wata magana mai qarfi ta shiga tsakanin ku

ba, ke kika Kara karfafa abin har kika Bata

lokacin ki akan sa. ,

Mahaifinsa ya sanar dani dansu ya kawo masu

yariyar da yake so a yanzu, kuma babu yanda: za

suyi da shi tunda ba zasu yiwa dansu , auren

dole ba duk wadda ya kawo ya ce ita yake so ita

za su ba shi.

. Don haka kiyi hakuri Suhailat, nima a matsayina

na mahaifinki tun. a dazu da mahaifin Mansir ya

zomin da wannan zancen nima na Samar maki

nawa. Zan

hadaki da wani yaro dake aiki a kamfanina mai

suna Abubakar Dandagoro, shi da kakarsa suke

iyayen sa sun mutu, nai miki sha’awar auren‘ sa

tunda yaron kirkine, yana da mUtunci da

nutsuwa.

_-Mahaifinsa a lokacin yana rayé shi ya . kawo

min shi a kamfani na muka dauke shi aiki da

N.C.E dinsa; yana cikin aikin ya jona

yai digiri dinsa, na tabbatar yaron zai miki

saboda yaron bai da makusa. Nai mashi magana

kuna ya amince gobe zai zo ya ganki ki ganshi ku

gaisa kiga idan ya yi maki Suhailat ta ce, “Yanzu

Alhaji har nayi girman da za ace ana talla na?

Alhaji yanzu ban da kyan da zan iya samarwa

kaina mijin da ya cancanta dani? Wayyo Allah na”

Sai ta sa kuka ‘ Alhaji ya ce, “Kinji wani zancen

banza Hajiya, kinji wani sakarci. Ai’ maki miji ya

amince zai aure ki ai arziki ne, kuma shi kanshi

idan yazo ya ganki ai yasan ba rasa mijin aure

kikai ba, ban son sakarcin banza kinji, tashi ki

ban wuri, ki shirya kuma gobe zai zo”

‘ Suhailat ta mike ta Kara sa‘kuka ta nufi falonta,

jikin momy ya qara yin sanyi liqis, ‘tace .

“Amma Alhaji naji . kace yaron

.kamfaninka ne, anya ya dace da Suhailat

“kUWa?

Alhaji yace, “Ai idan dai har ya yi mata ” babu

abinda bazan iya yi masa ba, zan

bashi qaton gidan da k0 shi Mansir din iyakar shi

zai gina mata, zan bashi mota kuma in ‘samar

mashi aiki irin warida zai iya riKeta da Shi

Mommy ta ce, “To hakan ya yi, kuma’; Alhaji

Allah Ya taimaka Ya Kara budi”. ’ Ya ce, “Amin”

Ya mike ya nufi sama, Hajiya ta bishi a baya. ‘ ‘ .

A daki Suhailat kukanta yafi nada karuwa, saboda

a yanzu ta tabbatar da ta rasa; ‘Mansir, gashi

yanzu bata San ko waye Alhaji , ya zaba mata ba,

bata san ya yake ba. Yau dai ; ” tai kuka har ta

godewa Allah, batun barci kuwa babu shi a

wannan ranar. , Suhailat ta shiga tsananin

damuwa da tashin hankali, ta riga ta sadakar

data rasa Mansir, . , haka har‘ girin Allah “Ya

waye tana abu guda, sai da mommy dinta tai da

gaske sannan ta ” samu tai break, shima ba wani

da yawa ta ci ba. ‘

. Karfe hudu saura nayamma mommy ta tiSa

Suhailat gaba sai da tai wanka ta tsareta ta

shirya cikin wata doguwar riga baqa mai hawa –

hawa, rigar tai mata kyau, musamman

kasancewarta na farar fata.

Ta nada dan qaramin gyalensa saman kanta. Tai

kyau sai kace balarabiya, sannan mommy ta

kyaleta ta tafl,

ta sa masu aiki su gyara sashin da ake saukar

baqi. . ‘

*****************

Haka nan Abubakar-ya sami kanshi da damuwa

tun Iokacin da Alhaji Halliru ya kira shi ya sanar

da shi buqatar sa yake jin tsananin damuwa. Sai

dai babu yanda za ai ya watsa mashi qasa a ido,

ya ce baya son kyaular da yai masa, saboda irin

halaccin da yai masa a rayuwa. Kuma duk

jama’ar dake kamfanin bai, zabi kowa ba sai shi,

saboda yana ganin shi xai iya rufa masa wannan

asirin, bai kamala ace ya watsa masa qasa a

idanuwa’ ba, kuma tunda shi ba wata tsayayyar

budurwa ke gareshi’ ba. ’ yasan yana da ‘yan

mata amma, duk irin sha ka ‘. tafi dinnan ne.

Ya dade a gaban (mirrow) yana juya hular

hannun sa kafin yai ta maza ya dora ta a kansa,

ya dauki siririn farin gilas din ya dora a fuskar

shi. ” ‘

Ya tsaya yana karewa kanshi kallo shi dai yasan

ba wani kyakkyawa bane na azo a gani,ba to

amma yasan bai da muni. Yanada daidai nasa

kyan na misali.

Kuma inda yake kara birge kansa indai _ zaisa

kaya sai sun masa kyau a jiki tamkar don . ‘ shi

akayisu . don haka wata (light brown) din ’

shadda Ce. mai haske a jikinsa, an mata dinkin :

Hannu. {dark brown) din zare akasa mai cizziWa,‘

’ takalminsa sawu ciki da hular sa duk kalar

shaddar ne. . .

‘ yai kyau sosai, ya dauki turaren sa 24 hour ya

feshe bangarorin jikinsa sannan ya dauki makullin

dakinsa ya fito ya kulle, ya jefa ‘ key din a aljihun

wandon sa ya nufi dakin

Kaka . ,

A kwance ya sameta sai Rukayya dake zaune

tana kwance

Kitson daya gaji da_ dauda har ya

daddale dakyar take iya kwanceshi saboda kitson

ya harhade sai warin dauda kan yake

Abubakar ya tsaya daga bakin kofa ya tsugunna.

“Ni zan fita Kaka. xan shiga can cikin birni, gidan

ubangidana, ina tunanin wurin magaruba zan

dawo .

Kaka tace, “Me zaa kayi gidan nasa kuma? Ni

kasan ban son kana shisshigewa masu kudin nan

Habu, saboda yawancin su duk matsafane ajc a

sai da kai a banza,

. ‘ Abubakar ya cé, “Dadina da ke tsohuwar nan

tsoro, saboda’ ni kawai ake’jira’daga zuwa sai a

kama tsafe ni gasu sarakan tsafi Ai ni ‘naman

jikina ya haramta ga duk wani aljani ballantana

bil’Adama. ‘ ‘

Kaka tace, “Kai tashi can sai shegrn cika

_ bakin tsiya, ai sai wanda ya girka kanshi da

aYOyin Allah yake irin wannan ikirarin, wanda ya

sha kuma yai wanka”.

Abubakar ya ce “to ai abun sirri ne Kaka tunda ba

ki nemu mani ba ni da kaina nake nemowa

kaina”.

Kaka tace, “Hmm! Dama dai wata wata furar

amman bata gero ba”.

Abubakar ya mike yana fadar, “Kai bari in tashi

kinji, idan na biye maki sai mu kai magaribar

anan ban tafi inda zani ba abubakar ya dubi

rukky yace kai mai hali dai bai canja halinsa

amman wannan kan nasan ko tantama babu .ba

a rasa kwarkwata acikin sa ,

” Kaka tace,”inma da kwarkwatan ina ruwanka?

Kanka ne k0 nata‘? K0 dakin ka aka shiga , ana.

kwantar?” Abubakar yace, “Ko daya, sai na

daWo”.

Tace , “A dawo lafiya”. ‘

Yasa kai ya fice abinsa.

********* *************

Suhailat tana kwance a falo saman

duguwar kujera zuciyarta ta lula duniyar

tunani,kana kallonta kasan tana cikin damuwa

Sai admin yacemu tara donjin yaddah haduwar

abubakar da suhailat zata kasance

Naku har kullum A, I, S

ke cewa asha karatu lafiya

zallah shared a profile .

RIKON KAKA

CHAPTER11

end of book1

Mommy dinta ta shigo falon ta dan

bubbugata‘ “tashi kinji ga bakon can ya iso tun

Dazu na sa masu aiki sun kai masa abubuwan

motsa baki”Suhailat ta yunkura ta mike ta Sako ‘

qafafuwanta daga saman kujerar, ta saka

takalmantata mike; mommy tace . “A’a Suhaiial

ai kya dai Kara gyara fuskar mana, kin tafi haka

fuska duk a yamutse Suhailal ta Cinkuno baki, “Ni

dai ki barni ‘ mommy kaWai, ina ruwana “? .

‘ Mommy taja hannunta har gaban madubi ta

dauki hodar da kanta ta Kara shafa. . mata’, ta

dauki turaren bb ta fesa mata a , dukkann

gab0bin jikinta,dakin ya dauki , _ kamshi sannan

taja hannunta suka fice har bakin kofar dakin ta

kaita. Sai dataga Shigarta sannan ta juyo ta

koma tana roqon allah Yasa yai mata itama ita

tai masa ta samu ta aurar da yar tilon.’ yar tata

kwara daya

Sai Yayanta Wanda yanzu haka yana . qasar

Misra yana karatu

\

Suhailal ta Shiga falon da sallama idonta na

saman fuskar AbUbakar wadda take mannevda

siririn farin gilas ‘

Gaban Abubakar , yai mummunar faduwa,

tsantsar kyan da ya gani kWancc a ‘, fuskar

Suhaiiat ya rudar da shi. ~

“Anya wannan itace kuwa‘?” ‘ ‘ tambayar da

yaiwa kansa wadda bai da .mai amsa mashi ita. ‘

” kenan. , Suhaillat ta karaso cikin falon ta zauna

.saman kujerar dakr fuskar tasa, taci gaba da

.wasa da yatsun hannunta ba_ tare data furta

masa qala ha. ‘

Wani irin abu ne mai kamar iska wanda ke

tafiyarda dukkanin bakin .ciki da damuwa Suhailat

taji yana kewaye’ zuciyarta ha bata’san,“ lokacin

da bakinta ke bayyanarda Wani kyakkyawan

murmushi ba, abinda ya nutsar da ’

Zuciyar Abubakar kenan daga tsananin bugun’ ‘

da take harya samu

yai karfin halin fadin ‘ ” “Sannu da, zuwa Hajiya

,Suhailat, barka

Da isowa yake wannan kyakkyawar halittar

Shiru ta dan ratsa wurin xuciyar’

Abubakar taCi gaba da harbawa saboda tsananin

tsoron da ya cika ta, duk da yasan

Ba wannan bane lokaci na farko da ya saba zuwa

wurin budurwa tadi ba” Tsawon wasu daqiqu

sannan Suhailat ta

. iya danne tsananin farin cikin da ya dabaibaye”

Ta ta dube shi‘ “Sannu da zuwa YallaBai, -barka

da zuwa

‘, Abubakar yace’ “(Am sorry) Hajiya Suhailat,

sunana Abubakar Saddiq ai Yallabai yana Kofar

soro

Suhailat tai wani lakaitaccen murmushi “

kafin tace

“Na so ace ka karBi qarin ginnan da ka

samu daga wurin Hajiya Suhailat, amma tunda ka

noqe ba komi”.

Abubakar ya ce “K0 kusa ba haka nake nufiba,

naga dai kowane turmi da taBaryar data

Dace da shi ne shi yasa”. Suhailat ta cr, “Karka

damu Abbakar,

indai Suhailat ce zaka same ta a yanda kake ’“

Kake buKata, burina guda daya a rayuwa In auri

Wanda yakr so na nake son shi, ba wai wanda

yake sona ni kuma bana son shi ba”.

Abubakar ya dan yi jim, kafin ya ce, “Suhailat zan

fada miki wasu maganganu na gaskiya da

gaskiya, don Allah ki wa maganganun nawa

kyakkyawan kallo da kuma kyakkyawar fahimta.

Wallahi tunda na dora idona akan ki zuciyala ta

amince da cewar ke ce kadai wadda, . zuciyata ke

ncma, take yi min hasashen samu a matsayin

matar aurcna. .

Suhailat ki amince min na kasancc a tare dake

duk rintsi mu kasancc da juna. Soyayyar ki ta

garzayo a gare ni tunda na dora idona akanki

Zuciyata ta’darsu da qaunar ki, gangar jikina na

maki lale marhabin da zuwan sabuwar rayuwa

zan kasance cikin farin ciki da jin dadi idan har na

kalli kaina a matsayin mijin da aka kawo miki

Suhailat ki dauka ni na ganki ina so, son da idan

har muka kasance_ ma aurata zan’nuna miki shi

irin wanda babu macen data taba samun irinsa a

wurin masoyinta.

’ Ki amince min Suhailat mu gina wata

kyakkyawar alaka mai cike da soyayya irin wadda

k0 bayan ranmu za a dade ana tunawa da mu

Suhailat, please”.

Suhailat lai wani kyakkyawan murmushi, wani irin

shauki ya rinqa ratsa ‘zuciyarta, ta bishi da

kyawawan idanunta kafin ta ce . ‘

. “Abubakar idan soyayyar Suhailat kake nema to

ka’ riga ka samu, in baccin’ ma ina tsoron halin

ku na‘ maza~ ai dana ce kamar yanda na baka’

Soyayyata Abubakar haka na baka kaina gaba

daya, to ku din ne maza ‘ lamarin ku sai Allah”. ‘

Wani dadi ya kama Abubakar don tunda ‘ yakcmr

bai‘ taba tunanin zai samu soyayyar ‘

“kyakkyawar mace irin wannan ba, ya ce. “insha

“Allah Suhailat zaki same ni

mutum mai riqon amana da kuma alkawari”.

Suhailat ta ce, “Allah Yasa Abbakar”. . Hira sukc

a hankali a hankali har suka ‘ cinye lokaci, basu

ankara ba sai dai suka ji ana’ kiran sallar

magariba. Abubakar yai saurin

‘ ” kallon Suhailat da murmushi a fuskar sa, ya

ce.

“Wasa-wasa mun cinye loka¢i fa”.’~ Suhailat ta

dan hatare shi da wasa, kafin”ta ce’

“To da ba zaka yanxu ba kcnan?” _ Abubakar yai

dariya, “Tuba nake gimbiya Suhailat, ~aimin

afuwa, garin namu kauye ne dole zan wuce.

Gashi ba abin hawa nazo da shi ba Ran Suhailat

bai Soba,banda abinsa ma nan da garin

Dandagoro, amma don kar

tacika bayar da kanta ta sa ta ce ’ “To shi kenan,

muje ka gaishe da

mommy sai na sa direba ya mai da kai gida”.

Abubakar ya mike tai masa jagaba har

falon mommyn tata, suka gaisa ita kanta ta

‘ yaba da Abubakar har harabar gidan ‘ Suhailat

ta rako shi ta sa direba ya mai da shi, ‘ sannan

ta dawo

A falo momy na; tai mata tsiya, ‘tai ta Shiga

sashinta tana’ tsallen murna, ta. samu wayayyen

namiji irin wanda take, so.»

Ana sallar isha’i Abubakur ya iso gida zuciyar shi

fari tas don haka k0 dakinsa bai shiga ba ya

wucc dakin Kaka saboda alamun hira da yake Ji a

dakin Ya: xauna yai la zolayar. Kaka har sai data

gaji ta

Korashi

, sannan ya shafa masu lafiya ,. Washegai’i bayan

Abubakar ya Je wurin

aiki Alhaji Halliru ya kira shi office dinsa ‘ ya

Sanar da shi ya tura iyayensa da maganar aure

Abubakar ya nuna a dan jinkirta masa.

Alhaji Halliru yace Karka damu Abubakar babu

abinda ban tanada ba. na maganar auren nan kai

da Suhailat kaje kawai

ka ci gaba da shirye~ shiryenka kawai kuma

gobe idan zaka xo wurin aiki ka zomin da

lakardun ka Abubakar yace “Insha Allahu”.

Yai g0diya sosai

Rukayya ta dawo daga gidan kitso-Kaka ta lura

da, gashin ma Saida aka hada da ,

Da zare sannan ya ‘kamu, saboda duk ya

cUKurkude. ‘

Tana dawowa ta shigo tsakar gidan Kaka tace

“Haba har kin zama mace wallahi”. _Rukayya ta

zauna saman labarma kusa‘ da Kaka dake

Kunsawa kafa lalle, ta kwanta a gefe saboda

kanta dake faman zuqi

rashin sabo da kitson. Kaka tace “Dazu kina

makaranlar allo _

da safe lokacin da HabU-xai lafi wurin ‘aiki ya din

ga kiranki yana ncman ki, har sai dana fito da

kaina ina rokon Allah Yasa batun soyayyar ne xai

miki na tambaye shi mai zai miki. sai cewa yai

ba komai a barshi kawai .Don yanxu tun kafin ya

shigo ki tashi kiyi wanka ki canja wadannan

daudaddun kayan, don ‘Allah ya dan ganki da

haske tunda kema ba: sonki bane ace kina xaune

har yunzu~ babu mashin shini duk sa’o in ki duk

SUnyi aure

Rukayya tace ni Wallahi Kaka har’ ‘na fara shiga

damuwa ace yana sona amma har

yanzu yaki magana ni dai ko nagwna zaki

masa Kaka?” Kaka tace “Ki barshi muga iya

gudun

ruwansa tukun, kedai tashi. kije kiyi wankan” ‘ Ba

musu RuKayya ta tashi ta nufi bakin tanda, ta

dcbi ruwa a bokiti ta nufi kewaye ta watso

ruWan. ‘ ‘ta nufi dakin kaka ta bincika ta gano

wata atamfa mai saukin sakawa riga’da lani ta

daura ‘kallabin saman kanta ta ’ mike ta jawo

basilin, ta..murzawa fatar jikinta, ta shafawa

idonta farin’kwalli sannan ta fito tsakar gidan

Kaka ta ganta tace. “Haba k0 kefa jika, amma

kullum mutum .yai ta yawo kamar farar. kura?

Sai dai daurin “zanin ne har‘ yau ba ki iya ba

Jika, kullum ki ta sakin bakin zani yana jan qasa”

Rukayya ta ce, “Ni fa haka .na iya. Kaka“ Tace “

to ai sai ki tayi tunda keba a ba, a baki shawara

ace mace har yanzu bata iya daurin . zaniba

Rukayya’ta ‘warware zanin tana sake daurawa,

Abubakar yai sallama ya shigo yana kallon

Rukayya ya ce

“Ke kuma meye haka? Sai kacc wata aljana?

Kinga yanda kika kwabawa fuska mai sai sheki

take.’ Haka aka fada miki ana shafa man? Yo

ashe ma har gara da ba ki shafawar ma kibar

fuskar a bushenta sai kacc mai qazzuwa. ke

kokarcin jikin ki baki ji?”

Kaka tace”Shin wai kai in tambayc ka jikin ka ko

jikinta? Haba! ka takurawa yarinya da tsinannan

kicilin tsiya”.

Abubakar ya ce, “Amma saboda Allah duba fa

Kaka, dama abinka ga baqar fata ’ kuma ta qara

dabbaka uban Basilin, ta qara _ wani uban baqi

Kaka tace “To dai babu rUWan ka da ita kaji k0?

Ai jikinta ne ba naka ba”.

Rukayya ta gyara’daurin zanin ta koma ta zauna

gefen Kaka, Abubakar ya ja kujera. ‘yar tsugunnc

ya zauna, yace

‘ “Kaka da wata muhimmiyar magana na

Zo miki. Kaka ts washe baki ‘lna jinka nannan

. Sai da ya kara gyara zama kafin ya ce

“Dama maganar aurena ce Kaka ta taso don

wallahi na Janyo fadan da yafi karfina.‘ ‘Yar

gidan ubangidana ce muke soyayyah shi ne yau

mahaifinta ya kira ni ya ce naJe na turo iyayena

a cikin satin nan. ‘

Na fada mashi ‘yan matsalolin da ake ciki Shi ne

ya ce ai bai bukatar komi nawa indai

turob‘iyayena da abinda ya sauwaka shi xai Ji ‘,

da komi Shi ne na nace kije ki masu Malam

magana don su shirya tafiyar kamin -‘ inje inji

yanda ‘za ayi k0 ba haka ba?” ‘ ‘ Kaka Wadda a

farkon zancen sa bakinta ‘.yake a washe har” ta

gagara rufe gibinta, amma ‘tana Jin ya ce ‘yar

gidan uban gidansa 1mta hade fuska ta gabas da

yamma, har yaje karshen zancen sannan kaka

tace lallai‘ biri ya yi kama‘ da mutum haba! ashe

duk abin’da Uban gidan nan naka” yake maka ba

don Allah yakeyi ba sai don ya hada ku aure da’

yarSa, ti bai isa ba.Wallahi’yar.

Tasa tayi kwantai tayi Jibgaro an rasa mashin

sini ‘ shi ne za a lika maka ga sakarai, to bakaso

Ai muma nan gidan muna da wadda muka baka:

ga‘yar uwarku nan .jika, nima itace wadda na

zaba maka, kuma irmta ce zaka aura. Sai ka

koma ka bashi haquri ka fada mashi a gida an

maka mata kaji na fada maka baki

Sake Abubakar ke kallinta har ta kai aya. sai yace

tunda yake bai taba ganin. Bacin ran Kaka irin na

yau ba. ‘

Yace Haba Kaka yanxu ki dube ni ki dubi

yarinyarcan Kaka ai kin san bamu ma : dace ba

don Allah ki daina ma wannan

maganar”.

Kaka ta mike tsaye da qunshi a qafarta,‘ tace:

“Habu, wallahi lallahi na rantse da Allah

.’ in har kaga aure tsakanin ka da jika bai yiwu

ba to saidai in ko bana numfashi”.

Abubakar yace “Kiyi hakuri Kaka, abin ba na fada

bane, maganar aure tsakanina da Rukayya

babuma wannan labarin, gaskiya na

Fada ‘maki ma ~ba zan iya auren taba k0 da

kuwa kyauta za, aban ita

babu abinda zanyi da ita” Kaka‘ ta. fashe da kuka

“na shiga uku, yau nagata kaina, qaramin yaro zai

nuna min

iyakata. ‘zaka tozarta habu? Ni zaka wulaqanta a

bainar‘jama’a‘.’ to wallahi baka’isa ba, idan kaga

ka auri waccan to sai ka auri jika; Don ba ni na

haife ko eh ban haifr kaba habu amman riqon da

nai maka kawai ya isa idan nai maka baki ya

bika wallahi”. . Tashin hankalin da Abubakar ya

gani qarara a wurin Kaka yaSa ,ya miqe jikinsa a

mace ya bar tsakar gidan‘. ya nufi dandakinsa _

ya kwanta tsananin damuWa tamkar ya‘dora

hannunsa aka ya ce wayyo Allah ‘ Rukayya kuwa

yana tafiya itama ta miqe ‘ ta nufi dakin Kaka ta

fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai

sauti, Kaka ta cire kunshin kafarta dako kamawa

bai yi ba ta nufi dakin, ta janyo Rukayya a jikinta

tana lallashi tace

“Yi shiru Jika kinji‘. ’ Yi hakuri, ai wallahi

inhar ina raye sai ya aure ki don tada mashida

hankali zanyi dolema sai ya aurc ki”.

, Rukayya tace. “Kinji fa-wai bai sona yace

waiban da kyau, kazama ce ‘ni; Kaka saboda

Allah yanzu, ina qazanta take anan’? Ni

wallahi idan har yaqi yarda bazab taba auren

koWa ba, kuma ma mutuwa zanyi ‘Allah kinjima

na rantse .

Kaka tace”kiyi shiru, vaza ki mutu ba jika har sai

naga tattaba kunne na, da kaina gobe zan lafi

gobe da safe mu gama magana, ba zan dawo

gidan‘ nan ba sai an tsaida ranar auren ku”. Dadi

ya kama Rukayya ta ce “Ato Kaka, don Allah gari

na wayewa ki tafi

Kaka tace,”Karki damu Jika” “‘

‘ .WaShegari tun da sanyin safiya Kaka-ta’

shirya la lulluBa zani, Rukayya ta rako ta har

bakin hanya ta hau mota ta‘tafl, sai da Rukayya ’

taga Iafiyarsu sannan ta dawo gida.

Kaka na dira garin ta sauka gidan Malam Sale

kanin mijinta ne, qaton gida ne duk ”’yawanci

dangin mijin nata suna zaune a “,wannan gidan’ ,

Malam Sale yana makaranta tasa aka kirawo shi

yana shigowa ya ganta ya ce

. .ikon Allah, indo kcce a gidan namu yau‘? Allah

Yasa dai lafiya”

Kaka tacr “To zauna lafiya qalau”.

Malam ya ‘zauna yana fadar “Ai yanzu Habu

yazo mana da maganar aurensa data taso da

kika aiko kirana, shi yasa nai manaki

Kaka ta ce, “La’ ilaha illallahu! Kunga yaran

zamani yanxu har ya riga ni ‘zuwa kenan? To kar

ka saurare shi ‘

Malam yace, “Y0 don mi Hajiya yaron ya samu

yqrinyar da yakeson kuma ai yamin bayanin komi

don haka indo kiyi hakuri ki’ janye wannan

maganar tunda dai yaxu ga wacce yaro yakeso to

a barshi ya aura kawai”.

Kaka tace”Wallahi bai isa kaji na rantse tunda

itama jika bata da wani mashin shinshini koso

kake inbar yarinya a gabana shekara sha Shidda

babu aure?” . Malam yace, “Eh kuma da wannan

don wannan, amma abinda nake ganin mafita ‘

anan tundayace yana son waccan yarinyar .kuma

ubanta yace bai buqatar komi, to duk ya hada

da‘ila Rukayya din ya hada da dan abinda Allah

Ya hore masa “aci gaba da biki”.

Kaka ta ce, “To sai dai wannan, na yarda da

wannan din‘.‘

Malam yasa aka kira masa Abubakar yazo akai

masa bayani,da farko ya ki aminccwa, amma

daga baya da bakin su ya hadu sun jajirce sai ya

amince don ance sarkin yawa yafi sarkin ,yawa

yafi sarkin qarfi malam ya ba da kudin neman

aure a take Naira dubu biyar aka tsai da rana

daya da _wancan,idan an tsai da iokaci sannan

kaka ta baro kaunyen da yamma likis. ’

Washegari kakannin nasa suka tafi birni’ gidan su

Suhailat Abubakar ya ba da kudin neman aura

Naira‘ dubu ishirin” amma mahaifinta yasa aka

dawo da su bai amsa ba, ‘ aka tsai da ranar aure

Wata daya kacal. . Suna dawowa Kaka ta sa aka

sayo mata biskit ta fara rarrabawa makotan nesa

dana kusa bikin . Jika wata guda

Kowa ya yi mamaki, yarinyar da ba zance: take

ba amma har ta sami miji, kazamiyar-“yarinya

babu abin data iya sai masifa kOWa dai da abin

da yake fada.

Kaka kuwa dadi har ina an sawa Jika ranar aure

da Abubakar, daga tsai da ranar Kaka ta garzaya

gidan malam ta amso mata ganyayyaki. ‘

Kullum cikin yiwa Jika hade haden su na tsaffi

takewa jika jiqa wancan, dafa wancan, daka .

wancaHar Rukayya ta Soma gajiya da hade

haden da Kaka ke mata, dan haka k0 yauda ta.

dafa mata wata budurwar kaza ba maggi ba

gishiri sai baurin itatuwa take.

Rukayya tace, “Ni k0 Kaka na gaji da ciyeciyen

abubuwan nan da kike tura mini, dan Allah ki

kyaleni haka”.

-‘ Kaka tace, “Keda Allah gafara, wannan ‘hade

haden ai su ne za su kwato maki mutunci . da

daraja a gidan Abubakar din, baki san gidan

kishiya za ki ba? Ai nan ma ba a fara komi ba, ke

dai kawai ki sa mani ido, ta wannan hanyar ce

kadai za ki iya kwacc Habu ya zamo naki, duk

kyan kishiyar ki duk kuma kWalisar ta, ke dai

zuba ido.

Cikin‘ sanyin jiki RuKayya ta ce “Allah Yasa

Kaka”.

Ni kaina dai sai riqe wayata nai gam ina kallon.

’Rukayya, na kare mata kallo a zuciyata dai sai

cewa nai, “Amman da kamar wuya kwacewa’

“.Suhailat Abubakar kyakkyawan yarinya wadda

kanta ya faru da boko

” Ammadai..;, Muje zuwa wai mahaukaci ya hau

kura bari

llah

‘RIKON KAKA-2

CHAPTER12

RUkayya na zaune da safe daki aka gefen gado

tana dinkin . zaninta da allura, Kaka ta Shigo ,

dakin hanunta rike da kwanon sha, ta mikawa

Rukayya. ‘ ’

“Ungo, amshi shanye maza ki miko min kwanon”.

‘ . ‘ Rukayya ta ajiye dinkin, ta amasa tana kallon

.abinda ke cikin kwanon. Kindirmo ne wanda aka

dama da garin magani, Rukayya ta dago ta

dubeta. .. _.”Meye ne Kaka?” .Kaka tace “Ke in

zaki sha kisha kinji, ni

‘bana’ ,’ son yawan ‘ tambaya“. Rukayyah ta

bata fuska, “Ni fa na faragajiya kullum ki ta‘

banka min wasu jiqe-jike ‘sai kace jikar mai

ganye”. ‘ ‘ ‘_

.. Kaka ta ce, “Hum! Jika kenan,‘ai wannan jiqe-

jiken shi ne’zai janyo miki mutuncinki a wurin

Habu, ki kwacc shi a hannunki ,yarinyar‘nan”: ‘

Rukayya tai murmushin jin dadi sannan ta kafa

kai tana sha, bata damu da baurin maganin ba.

Sai da ta shanye tsaf sannan ta mikawa Kaka

kwanon, ta amsa ta miqo mata

wani kullin magani. “Ungo, ki dauka ki zuba a

babban baho, akwai ruwan zafl akan wuta ki zuba

a ciki, ki

dauka ki kai kewaye ki tube ki zauna a ciki har

sai ruwan ya huce”.

Rukayya ta amsa tana tsalle ta tice, Kaka ta

girgiza kai a zuciyarta tana raya irin tsantsar ‘

son da Jika kewa Habu. ‘ Rukayya na fitowa

tsakar gida ta hadu da .Abubakar yana shigowa,

yana sanye da , (suit) baqa, takalmin kafarsa

sawu ciki ne bar” a fusakarsa. Sumar kan ‘ nan

_tasha gyara, tai bakikkirin, kafadarsa na rataye

da jaka irin ra ma’aikata. ‘ Kallo daya tayi masa

gabanta ya fadi, irin kyan . da ‘ta gani kwance a

jikinsa. Tai ‘ Saurin jan kafafuwanta ta .wuce shi.

“Ke, Zo nan”,

M uryarsa ta daki dodon kunnen

Rukayya, gabanta ya fadi. Ta dawo ta tsuguna

gabansa a tsorace.

‘ Ya kara bata fuska, “Ke baki iya gaida mutane

bane? K0 ko’ raina’ ni ki kai?”

Tai shiru. _ . . _ gamida girgiza kai

, Abubakar yaja tsaki ya wuce ya barta nan a

tsugune, Rukayya ta daga kai tana satar.

kallonshi. . ‘

Ya daka yana cire takalmin qafarsa ya” ‘ hangota

tana kallon shi, ya dago a fusace.

‘ “Kallon uwar me kike min kuma iye?_ “Me kama

da tsohuwar mayya”.

. Yanda ya zaburo mata yasa ta zabura ta zura

aguje, yaja kwafa ya nuf dakin kaka . ‘ ‘ ,Yana

shiga ,dakin Kaka ya duka har qaga ‘yana gaishe

da ita, harara ta watsa mashi:

“Kai ko wannan anyi mai mugun hali, wallahi duk

abinka dai aure kai da Jika kamar anyi an gama”.

Abubakar ya cire gilas din idnnsa yana fadar.

‘ Ai kisa a zuciyar ki Kaka, kina son daurawa jikar

ki aure: da wahala, ne kawai kinji ma na fada

miki ban Boye miki ba”.

‘ Kaka ta ce muhammadu dan abdullahi habu to

“Kaje kayi duk abinda kaga dama wallahi ka sake

ka zalinci marainiyar ‘ Allah wallahi Allah ba Zai

barka ba kuma

Allah Ya isa ban yafe maka ba har‘ duniya ta

nade” .

Ya ce, “Ai in Allah Ya ,isanki ba bina zata yi ba

Malama. Na zone ki min addu’ a yau zan fara

zuwa (office) din da Alhaji ya samar min’ aiki,

don haka ga kaina ki dafa kimin addu’ a”_

Ya duka da kan nasa gabanta, Kaka ta dora

hannunta. ‘ .

“Allah Yasa alkhairi, Yasa wannan aikin

ya zamo abokin arziqinka. Ubangiji Ya dora ,

maka ciwon son Jika kamar ya kashe ka”. ‘

Yai saurin janye kansa yana daria yace.

Oh kaka harda wata mummunar

addu, a nara ‘karbuwa kuma?

Kaka tace“Hum! Habu kenan, ai insha Allahu

wannan addu’ar “karbabbiyace don koda raina ko

babu in Allah Ya yarda saika zo ka durqusa

gaban Jika kana kuka da idanuwanka saboda

soyayya’.

Abubakar ya mike, ya aje mata dari biyar

‘Yana fadin ni kinga tafiyata karki batamin lokaci

sannan karku tsaya jirana don karfe shiddah ake

tashi kinga kafin na dawo dare yayi’

Kaka tace“Allah Ya kiyaye, Ya bada sa’a”.

Yace amin

Sannan ya fice tana mashi addu‘a.

Bayan sati biyu hidima taima Abubakar yawa kai

ya dauki zafi. Sauqinsa guda ma uban Suhailat

ya dauki nauyin hidimar komi.

dai-dai da gidan da zasu zauna Mahaifin Suhailat

ya bashi qaton gida a cikin gari G. R. A mai kyan

gaske, ya bashi kyautar sabuwar mota’ yar

karama ta zamani.

‘ Abinda ya qara darsawa Abubakar tsoro

a zuciyarSa kenan har ya kasa sanar da su hadin

da iyayensa ke son yi mashi,kullum idan yazo zai

sanarwa Suhailat sai yaji ya kasa, don‘ haka ya

jaye komi a zuciyarsa ya cigaba da hidimo‘min

gabansa.

K0 kadan bai kula da hidimar bikin shi ” ‘da

RuKayya, ta Suhailat kawai yake

Kaka tana ta hidimominta, duk wasu yan tarin da

take yi ta fito dasu tanaiwa Jika hidimomi,” ‘ta

bigewa. kanta_ hadin ; kayan dakin Jika. Tasa

Abubakar a gaba , a dole ya harhada ‘yan

kUdadensa _a gidanshi na gado dakevcikin’

qauyen ya biya kudi aka gyara mashi shi sosai

akai fcnti, sannan ya biya kudi akai ‘mata kayan

faki daidai da zaman Rauye. ‘

‘ Ba laifi komai yayi kyau harta kayan aikace

aikace na mata sai da ya sissiya mata nadai

daidai da ita sannan ya dauko kaka ya nuna

mata

Komai yai mata yai sannan ya kama hanyar

katsina

ya Ci gaba da hidimar auren sa

Fatittika kala shida suka shirya fatittikak kuma

irin na gogaggun yan boko masu ji da kudi ‘

Kaka bata qarasa Abubakar a ido ba har

ranar daurin aure, inda jama’a suke ciko

dankam , a gidan , kowa yana ta hidimarsa ,d0n

haka hahkalin Kaka ya dauke batai mitar rashin

ganinsaba

Karfe sha daya na safe dangin su Abubakar suka

gama haduwa Sannan aka daura auren Rukayya,‘

sai suka wuce aka dauro na Suhailat.

“‘hiidima Sosai aka Shirya’wa ’dangin Abubakar

da ab0kansa da sukaxo daurin auren

An shirya maSu Sha tarata arziki Anyi anyi barin

naira abin harya soma bama yan uwan abubakar

tsoro

Abubakar bai samu dawowa kauye ba saboda

(dinner) da uwar amarya ta shirya masu bayan

faurin aure, don haka yaiwa abokansa waya aka

sami mota kwara biyu aka tura gidan Kaka aka

dauki amarya da masu mata rakiya a kai amarya

gidanta, daki biyu n sai dan .qaramin kicin da

kewaya Rukayya dai ita’ daya gidan ya isheta, ya

kuma sha gyara sosai. Rukayya bala shiga rudu

ba sai da taga kowa ya watse ya barta ita daya a

wuryar gado tana rarraba idanuwa tun tana

dakewa dare ya ‘soma tsalawa tsoro ya kamata,

ta fashe da kuka“ tana .rakube babu mai

lallashinta, dama Kaka ce gashi yanxu bata kusa

da ita tun RuKayya na kukan fili harta koma tana

na zuci batasan lokacin da har barci Barawo ya

dauketa ba Asuba farko Rukayya ta farka a rude

:kamar Wata zararriya, sai waige waige take

daqar ts iya daurewa ta mike ta fita tsakar gida

ta kama ruwa

Sannan ta dauro alwala ta dawo fakinta tai

sallah, duk

abinda take a. Tsorace take . ‘ , . ‘ ” Tai tSugunne

a kasa ta rafka tagumi,jira kawai take gari ya

kara haske ‘ tasan.abinyi; a haka, hasken” ‘

Fasuba ya keto, gari yai haske sosai. ‘

Rukayya‘ta mike ta janyo hijabinta,ta sa

takalminta ta fice« ta janyo “gidan tai hanyar

gida. .

~ ‘ Tunda ta sanya kafa cikin gidan ta take Jiyo

hayaniyar: jama, a’ da baSu da basu gama

watseWa ba tana sallama tsakar’ gidan jama, a

Suka yo kanta ‘ ca

Rukayya ta fashr da kuka,ta fada dakin-Kaka,

mutanen dake gdan Suka rufo mata

baya. Kaka na ganinta ta rude. ‘ ‘ “Jika maiya

fito dake daga gidanki K0 wani abin yai miki “‘

ne?” Rukayya tace kaka “Wallahi ni

‘ bazan koma ba, Allah Kaka bazan koma ba

. Kaka ta dauki Sallallami, “Ba zaki koma ba

Jika? Daga . kaiki gidan jiya‘?” Jika tace”Kaka ni

kadai fa na kwana

gidan jiya, har yau bai zoba, Bacin kice mani tare

zamu dinga kwana dashi, Allah. ‘ban komawa”. ‘ ‘

_ Kaka ta ce “Muhammad-dan’ Abdullahi! Yanxu

dan banzan yaron nan bai zo ‘ba can bifi yai

zamansa? Cafdijan! Yanzu, don iyayensa bai san

dake aka fara daura auren ba kuma kece babba

shi ne yaje yai mana haka? Wannan Yaro Allah

Yai maka’yanda kai ‘ mana“. ‘Mutancn dake.

tsaitsaye akansu ganin abin zai yi zafi suka soma

ba da’ hakuri’, Yaya rabi diyar qanwar Kaka.ta‘

ce’ . ‘

“Haba ai abin bai yi zafi haka ba, .

. .tunda dai can ya fara sai ku kyale shi, ai kwana

‘bakwaine dole zai dawo kuma k0?” ‘ ‘ .

Kaka tace “Kada ma ya dawo, nizai, dauka

mutuniyar banza? Wato ga ‘yar tsaron gida an

kawo masa, ai wallahi yanzu zan miqe Kafata

qafarki har birin yanzu~yanzun nan, ai ‘ ya kaini

naga gidan, na sani kuma zan iya kai ,kaina, sai

dai suci amarcin.nasu a lare” .

  zallah

RIKON KAKA

CHAPTER13

Yaya Rabi tace kar ki haka don Allah Inna, wallahi

abin magana ne zaki janyo mana kawai”. “Ta

kashe ku maganar Rabi batun zuwa kam babu

fushi, sai dai in bana numfashi”. Ta zabura ta

mike, “Tashi muje Jika,. ai banga ta zama ba wai

an sace dan barawo”. Murna ta kama Rukayya

wai za’a kaita birni, Kaka ta mike taja zanin

atamfarta ta yafa, ta dubi jika. “Yi maza harhada

kayanki muje”; Rukayya ta nufi wurin buhun

kayanta ta zazzagesu ta zazzaba ta kulle a zani

guda ta dauka, Kaka ta tasa ta gaba suka tafi,

mutane na bawa Kaka baki amma taki ta saurari

kowa. Suna lafiya kan hanya Kaka na fadar, “Har

ni za,a kawowa iskanci banza Ai wuyar ta kawai

ku hadu amma indai aka hadun. Jika kartyar duk

wani da namiji, don ma kedin ga_ki ga yadda

kike, amma dake wata ce Jika ki zage ki

kwatarwa kanki ‘yanci, duk wannan tsoron nasa

da kike ki ajiye shi gefe kija mijinki a jikinki, tunda

banga abinda wata mace ta fiki ba. Kuma ki bude

baki ki rinka magana, in ba haka ba. kishiya zata

raina ki ta maida ke sakarai. Da munje don Allah

Jika ki bude baki ki nuna mata kema fa ba

kanwar lasa bace”.

.jika ta duka ta Ciro takalminta guda dan maradi

da ya tsinke, ta dauki leda tana gyarawa, tace

“To Kaka ai da naje da ta sake tai min wata

magana sai dai taji naushi a baki kin san ni qarfi

gareni fa Kaka, kullum ni ke ba ‘yan makarantar

mu kashi”._ ‘

Kaka ta ce, “Haka nakeso Jika, ashe dai kina

ganewa”.

Rukayya ta tuntsire da dariya wadda tasa har

akuyoyin dake kiwo cikin bola suka kwasa -aguje,

a haka har suka qaraso bakin hanya, suka; tsaya,

suka tari mota suka hau tayo Katsina dasu.

**************

Abubakar anci amarci, an angwance sosai. Kallo

daya za kai masa ka tabbatar yana

cikin farin ciki don tunda gari yai haske‘ya mike

ya nufi kicin ya sanar da kuku abinda zai shirya

masu na (break fast), sannan ya dawo falon ya

gyaggyara, ya nufi (toilet) ya watso ruwa ya fito,

ya zauna gaban madubi ya shirya‘sosai, ya gyara

sumar kansa da mayuka, sai Kyalli take, sannan

ya mike ya nufi kan (wardrop) din dakin ya Ciro

qananan kaya na shan iska irin na Turawa ya

saka, ya mammatsa turare a jikinsa, sannan ya

nufi kan gadon da Suhailal ke kwance tana ta

sharar baccin da bata samu yi ba jiya.

Abubakar ya kwanto jikinta yana hura mata iskar

bakinsa, Suhailat ta Kara gyara kwanciyarta, ta

Kara kanannadewa a jikinsa ta ci gaba da

baccinta, Abubakar yai murmushi ya kira sunanta

a kasan makoshin sa, ta bude idanuwanta da

kyar ta kalle shi, sannan ta maida ta lumshe.

Abubakar ya kai bakinsa yai kamar zai sumbace

ta, ya dan cije ta a lebe kadan. Suhaillat tai

saurin bude idanuwanta tana kallon shi kamar

mai shirin yin kuka.

Yai murmushi, “Ki tashi rana tayi sosai fa, dubi

agogo sha biyu da mintina yanzu ki tashi ki

watsa ruwa za kiji dadin jikinki sosai (my l0ve)

Suhailat ta bata rai kamar mai shirin . kuka, tace

. “Amma don Allah yanzu sai ka tashe nik0 _

tausayina ‘ baka ji?

Abubakar yace “(Am sorry my lovelyM wife)”.

Kafin tai-magana har~ya sureta ya nufi’ toilet din

cikin dakin da ita.

**************

Me keke napep ya, faka babur din sa a. Kofar get

din gidan Abubakai’, Kaka ta fito’ tasa hunnu

cikin dan lalitarta ta ciro kudi ta bawa mai motar,

sannan suka ‘nufi (gate) din gidan. :Rukayyah ta

dora kullin tsummokaranta akai suka ,shiga

kwankwasar gidan, mai gadi ya miqe ya bude ya

gansu a tsaitsaye kamar mabarata Kaka tace “Ai

nan ne gidan Habu k0?”

Maigadi ya ce “Nan nc, sannu da zUWa”.

Ta amsa da, “Yauwa”.

‘Sannan ta ja hannun Rukayya suka. yi “cikin

gidan, mai gadin ya bisu da kallo. Bai. ‘ manta da

tsohuwar ba, ita ce wanda mai gidansa Abubakar

ya kawota taga gidan, ya ‘sanar dashi kakarsa ce

amma in ba haka ba ta yaya zai barsu su shigo

masu gida? Mutane

kamar sundawo daga aikin gona. Ya‘kada kai ya

nufi dan dakinsa da aka . ware masa.

Kaka ta tsaya ‘a bakin kofa .suna bubbugar kofar

kamar wadanda zasu Balle kyauren. suna (toilet)

suke jiyo bugun kofar, Abubakar har’ya fara

qulewa, a dolc ya sakar masu shawa suka

dauraye jiki suka nado tawul cikin hanzari suka

fito.

Suhailat k0 dan kwali bata tsaya dauka ‘ ba

ballantana ‘hijab, tai qofa da saurinta ta bude

don, ganin kowaye? Tana budewa suka shiga

kallon-kallo.

Cikin rashin fahimtar k0 su waye tace

“Lafiya. Baba‘? (my; dear) zo kaga wani ikon

Allah, almajirai har cikin falo”.

Abubakar .dake qokarin saka jallabiyya yai saurin

zirawa ya fito yana fadar. ‘

“Almajirai kuma. my love? mai gadin baya nan

ne?” , .

‘ Turus! Ya tsaya yana kallon Kaka da Rukayya,

gabanshi yai wata mummunar ‘ faduwa har

kanshi sai da ‘ ya sara, cikin

makyarkyatar murya ya ce

.”A’a kaka, kune? lkon allah

_ Ya dafa kai ya raSa ta cewa, yasan tabbas

asirinsa ne ya tonu Yasan tilas kaka sai ta_ fede

biri har wuziya. .

_ Suhailat dake tsaye ta dan sassauta murya

“(Am sorry)wallahi kaka ban san ku bane kuyi

haquri Muna (bathroom) ne shi yasa ku kai ta

bugun kofa Shiru

‘ Kaka datai mutuwar tsaye saboda_ takaici, tai

karfin halin fadar. . ‘ ‘ “Ki zagemu da kyau

yarinya dai wuri kika samu ai

dole kina tunawa da rama, wato kina baza ‘

rama, a’ a ba rama ba lafasa ma” “. ‘ Duk yanda

Suhailat ta kai ga dakewa sai da daria ya ta kusa

kufce mata, tace. ‘ “Wayyo! Ba baza rama naCe

ba Kaka,

‘ (bathroom) na ce, dakin wanka”. Kaka ta ce,

“Indai rainin wayo ne kinji

“dashi yarinya in kina nufin kin rainanine iyayenki

ma kauyen ne asalin su, kuma sai shege ke raina

mafarinsa ba dai dan halak ba, sannan kuma. .. .

Abubakar yai saurin tarar zancen, don ya tabbamr

yanzu ~Kaka ta Ballo masa ruwa,‘ ya ce.

”A’ a’ yi hakuri don Allah Kaka, mu shiga daga

ciki sannun ku da ‘zuwa”

kaka ta watsa masa harara.

” Kai rufemin baki, soko kawai. Ai dama nasan

hakan ce zata faru shi yasa tun farko na , hana

abin nan aka dage. “. TaJa tsaki. , , “Mu

ShigaJika kinji”.

‘ Kaka; ta fizgi hannun, Rukayya ta bita kamar

zariya tun shigowar su gidan jikinta yai sanyi ta

rinqa bin gidanda kallo da matar gidan wadda ke

tsaye jawur da ita da tawul a jikinta sai ka rantse

da allah baturi yace, ga fari ga ‘kyau, gashin nan

ya sha ruwa duk ya mammanne a kafadunta.

Kan kujera suka dire, Abubakar da‘ ‘ jikinsa ya

gama yin la’asar ya dubi Suhailat muryarsa a

raunane, ya ce

”Am sorry (my love) kar ki damu da ‘ rigimar

Kaka don Allah, kin san haka nake fama da ita,

rigimammiya ce sosai” ~

Suhailat ta ja wani gajeren murmushi, tace”Ba

komai (my dear) muje kada ranta ya Kara Baci

. ‘ Abubakar ya ce “A‘a, kije kawal daki ki ‘

shirya, kar ki damu zan iya da ita” ‘ Suhailat tace,

“Ahh. No my dear, muje

na soma rallashinta tukunna, don ba xanso

ta qara fusata dani ba”. Abubakar ya ce “A”a kar

ki damu kije

ni zan ji da ita” ‘

Ta ce. ”A’a, kai gaban ka barni Dear”. Cikin

tsananin rudani Abubakar yai ta

maza

ya bata”rai Wai ya zamu zauna muyi ta gardama,

‘ nace kije kawai k0?” _ Suhailat ta kafa mashi

idanuwa cikin

tuhuma, kafin tace. .

.’ ‘ _ “Anya Dear ‘ba akwai abinda kake

‘kakkarcwa da baka son in sani ba? Meye?” ‘Au

wai nan zaka girkemu kamar gumaka?”

‘ Suka ji muryar. Kaka ta daki dodan

kunnuwansu, bai iya bawa Suhailat amsa ba ya,

nufi wurin kakar a hanzarce ya duqa gabanta

cikin rudu yace. “ ”Don girman Allah Kaka kar ki

fada

:mata RuKayya mata tace wallahi mugun kishi ne

da ita”, ‘

Kaka tace “Ina ruwana yau sai dai ya kasheta,

kishin karuwar banza. Ai wannan daga gani kasan

ta zagaya .ina ganin idanuwannaN nasan

tantiriyar’ yar… _ Abubakar ya zabura ya dafe

mata baki._ yace don ‘Allah ki daina kaka, matata

cefa kuma,

kin san ko a Musulunci babu kyau Irin wannan

Daga shigowar ki kita aibata min mata,ba

kyau irin haka wallahi”. Kaka ta ture mashi

hannu. “Kai ni kyaleni kaji, ai dama idonka a

rufe yake, ba zaka gane abinda nake fada ba

tunda an riga an barbada maka kaci ka sha, kai

wanka shi yasa. aka dauro maka aure da

yarinya ka. .. . Abubakar yai saurin amshe zancen

da

‘ fadar. “A’a Kaka, kar muyi haka don Allah don

Annabi, ki rufa min wannan asirin” . Suhailat ta

nufo su da murmushin karfin hali a. fuskarta, ta

ce. ’ . “My Dear .kar ka damu, indai ta nice to

kuwa k0 kadan babu ruwana da duk kalaman da

Kaka zata fada akaina don inka lura ai tsohuwa

ce. _ _ , Kaka ta dauki sallallami, idan ta dauki

wannan kafin ta dire sai ta saki ta dauki wani. ‘ ‘

Cikin gigita ta soma fadar, “Yanzu

sana’ar da ka soma kenan Hubu? Dama aikin da

kake kenan a birnin siyar da giya? Me giya? giya

fa Habu? Yau na shiga uku ni Salamatu”; Sai ta

fashe da kuka. ‘ Abubakar ya dafe kai “Yau ni na

shiga uku, Kaka ki fahimta mana, my dcar ta cc

ba wai mai giya ba, kuma hakan yana .matsayin

maigidana, k0 mijina, k0 sahibina, k0 me sona, to

duk irin hakan ne shi ,ne ita kuma ta maida da

turanci, amma’Kaka k0 giya nake saidawa ai ba

zata rinka kirana da’ me giyar kai tsaye ba

k0?” .Kaka ta‘watsa mashi wani kallo, “Uhm! Kai

dai. ka sani, ni dai ga matar, ka nan na kawo

maka, idan ma kashe ka matar taka zata yi to.

sai dai ta kashe ka yau,tunda dai ka zama sauna

kira mana shashasha kar ta barka da rai”idan

taga dama Rukayya ta dibi tsummokaran

kayanta,

tana fadin

“Kaka tambaye’ hi inane dakina naje na

share? Suhailat tai saurin Waro ido waje tana

kallon su daya bayan daya, kafin kace me idonta

ya sauka tace ‘Abubakar, ; cikin »wata irin

rikitacciyar murya take fadar. ‘ ‘ ‘ ..

Hmmmmmmm asha karatu lafiya

naku har kullum A,I,S

kecewa gobema da labarizallah

RIKON KAKA

CHAPTER14

”Me kunnuwan suke jiyo min Abbakar? Da. gaska

ne abinda kunnuwana keji

Abubakar ya shiga dabur-dabur, ya rasa abin

fada

Suhailat ta dafe kai, ”Innalillahi wa inna ilaihi raji

‘un‘! Ka cuce ni, wallahi ka cuce ni, ka yaudareni

Abbakar, yanzu dama kasan kana da wannan

qazamar a qauye kace mani baka taBa auree ba?

Ashe dama kana da mata? Abbakar ka yaudare

ni, kasa‘ na mallaka maka zuciyata kaina

matsayina na mace ashe ban. sani ba kai

daudacce ne’. ba

T a fashe da wani irin kuka, “Ka cuce ni, ka cuce

ni Abbakar”. ‘ Ta kwasa da gudu ta nufi dakinta.

* ‘ Jikin Abubakar yai sanyi matuqa, hankalinsa

yai masifar tashi, yana matukar son Suhailat so

irin wanda baki ba zai iya furtawa ba. ya runtse

idanuwansa yana jin wani irin abu na tsirgawa a

kirjinshi. ‘ .

Kaka ta, mike ta dubi Rukayya, ”Taso muje in

zaar miki dakinki kinji Jika?“

Abubakar ’ya bude jajayen idanuwansa ya

dubeta.

”Kar muyi haka dake kaka don Allah, don Allah ki

rufa min asiri kada kisa na rasa matakin…

Cikin Bacin rai Kaka ta ce, ”Matsa daga nan Habu

.

Yandan yaga idanuwanta sun juye a dole ya

matsa ya bata wuri, dakuna ‘ne birjik a gidan,

kowanne an qawata shi da kayan more rayuwa

na zamani.

‘ . Kaka ta ZaBar mata wani qaton falo mai hade

da (bedroom) da (toilet) gaba daya an zuba

mashi Naira, da ganin tsaruwar dakin matsayin

dakin baki yake.

Dadi ya kama Rukayya, sai rawar jiki take. Kaka

ta ce. .’

. “Ki zamanki yarinya, babu uban da ya isa’ ya

takura miki a gidan nan. Ni zan tafi sai na dawo”

Rukayya tace”To Kaka, kisa aje gidana na kauye

a rufe, a bude na baro shi”.

kaka ta zabura a rufe kika barishi da gaske ?

Rukayya ta daga mata kai tace uhm kinga

tafiyata

, Rukayya k0 rakiya batai mata ba tana zaune

tana ta shafar tayil din dakin da’ katon kafet din

dake baje a tsakiyar dakin, ‘ cikin farin ciki ta

mike ta haye kan kujera tanata sukuwar murna ‘

*******

Tsananin tashin Hankalin da Abubakar’ yake ciki

baya misaltuwa, tunda ya fada kan kujera ya dafe

kai bai sake dagowa ba sai bayan minti talatin a

haka, kunnuwan shi sai rurin kukan Suhailat suke

jiyo’ mashi. Yai ta maza ya mike a kasale ya nufi

falon da yaga ta nufa, nufa kofar a bude take

don;haka ya tura da sallamar sa ya shiga ‘

Tana kwance saman makeken gadonta

‘dakin bakajin komai ciki, sai sautin kukanta.

ya

nufeta ya duqa gefen gadon gwiwoyinsa a qasa

yan fadin

“Suhailat don Allah ki dauro kima abinda zan fada

miki kyakkyawan kallo da kuma

kyakkyawar fahimta. Suhailat wallahi ba,,,

’Yi min shiru Munafiki, mayaudari, mai

mummunar manufa. Hum! Ai dama tsiyar talaka

kenan, duk yanda ka ganshi a rana yi kokarin

kara turashi cikin ranar, inba haka ba kuwa ya

sami dama: to kai zai jefa”.

Ta dan tsagaita tana share hawaye kafin

tacigaba. ‘

‘Wallahi nayi nadamar saninka da nayi a duniya,

ka tashi ka fice min daga daki, bana

son sake. hada ido da wannan. mummunar ..

fuskar tAka. tashi ka ficemin

Ta maimaita a harzuqe Ran Abubakar yai

mummunan vaci, kalamanta sun qona mashi”

zuciya, bai san

lokacin da ya mike yana kallonta ba ya girgiza

kai cike da bacin rai, ya ce

“Suhailat kenan, ban yi mamakin fadar wadannan

kalaman daga bakinki ba, saboda tun farko nima

nayi tunanin’hakan. Amma ina so ki sani,

Abubakar bai da matacciyar zuciya ‘ irin ta

sauran maza da kike tunani, kuma idan baki sani

ba yau ki sani, ba kudin mahaifinki sukasa na

soki har na aure ki ba, asali ma mahaifinki bai da

kudin da zai iya biyana. Na soki kuma na nuna

miki irin soyayyar da nake miki, kuma ki sani a

yanzu a shiryc nake zan iya ajiye duk wani

abinda mahaifinki ya mallaka min, sannan na

dauke ki na maida ke asalina cikin dangina da’

yan uwana.

Suhailat, duk da son na nake miki da irin halaccin

da ku ka nuna min ke da iyayenki, ba zai sa inyi

Karya ~ba don hangen wani abin hannunku.ba

Abinda‘na fada miki ada shi zan kuma maimaita

miki a yanzu, tunda nake ban taBa .aurc ba, ban

taBa sanin wata diya mace ba sai

akanki ‘

_ Rukayya Rmqanwata ce marainiya ce iyayenta

sun rasu kamar yanda nawa suka rasu Kaka ita

ta riqe ta tun tana jaririya cikin

tsumma a lokacin nima ina wurin Kaka sa,in da

mahaifina ya rasu Aurena da Rukayya Kaka ta

qulla shi ta

nace saidai in hada Rukayya dake in aura, ganin

abin zai zama rigima yasa na amince. Tunda

satin bikin nake tare dake ba tare dana leqa inda

sukeba kuma bawai don basa buqatar ganinaba

a’a sai don kawai naga na kasance da abinda

nake so

Suhailat idan kika ce don kudin mahaifinki nake

zaune dake kin qaskatar da: kanki kin ragewa

kanki (qualities)

Na rantse miki da Allah Suhailat kin kai ajin da ba

namijin da zai kalle ki bai yi sha awar ya

mallakekiba, babu shi. Sai ‘” dai ina Son ki sani

son da nake miki bazaisa in juri cin fuska daga

gareki ba, don a. qarkashina kike

‘ “ Suhailat idan har zuciyar ki bata amince

dani ba kada ki cutar da kanki, a shirye nake in

miki dukkanin abinda kikc so. Ina saurarenki

2page is missing

iya kula wata mace ne balle waccan qazamar?” ‘

Suhailat tace, “Ni dai zuciyar bata natsu bane

Dear, kawai ni dai ka saketa ka maida ita kauyen

in har kana so hankalina ya kwanta”.

Tana fadin sakin sai da gaban Abubakar ya fadi

har yana maimaita.

“Saki fa?” Suhailat ta daga kai, “Saki kuwa

Abubakar, don ba zan iya zama da wata mace a

matsayin kishiya ba” ’

‘ _ Abubakar yai murmushi kafin ya ce “Suhailat

kenan, wannan yarinyar ki dauketa a matsayin

‘yar aiki, wannan yarinyar ki dauke ta

‘ a matsayi ‘yar aikace-aikace, wannan yarinyar

ki dauketa tamkar baiwa ba mata‘ ba Saboda k0

da Abubakar bai da ke ba zai iya kallonta a

matsayin matar da zai yi rayuwar aure da ita ba”.

Suhailat ta rarrafa ta nufi jikin ‘Abubakar ta

kwanta, muryarta a sanyaye ta soma

magana.

“My Dear kai min alqawarin ba zaka taBa kulata

ba, ba zaka taBa kusantar ta ba

matsayin mace”ba. Abubakar yai murmushi, ya

lakacc mata

hanci yana fadar. “Nayi sarkin kishi”. Suhailat tai

murmushi cike da jin dadi,

Abubakar ya yunkura ya mike da ita a jikinsa.

Muje. mu karya kada yunwa ta kama mu”.

Suhailat dai batai magana ba sai dai murmushi.

Rukayya ta gama duk dokin da’ zata yi,

‘ tana zaune bacCi barawo ya sureta ba ita ta iya

farkawa ba sai ana kiraye-kirayen sallar la’asar.’

Ta mike tana faman murza idanuwa, tasha

,bacci matuka.

Wata irin yunwa ta bijiro mata saboda bata karya

ba, a dole tayo .falon gidan Suhailat ‘ da

Abubakar ‘suna baje a tsakiyar falon saman

kafet ‘Abubakar na kwancc ya tada kansa “da

da filon kujera suhailat na kwancee kanta a

saman qirjinsa suna kallon (laptop)

Gaban Rukayya ya yi wata mumnunar faduwa har

ta kusa faduwa saboda tsoro, ta datse bakinta

saboda ihun da ya nemi kufce

mata. Su duka suka zubo mata idanuwa sai

faman makyarkyata take.

Abubakar ya yunkura ya tashi zaune, ya daka

mata tsawa

“Ke Uwar me kika fito yi kika zo kika

tasa mu gaba kamar kin sami talabijin? Me kike

kallo?“ ~ Rukayya. ta hau rawar murya, “Um.“

Dama…dama… yunwa nake ji ne shi yasa abinci

zanci”. .

‘ Suhailat ta ce, “Abinci, ki ka bamu ajiya?

Tantiriyar mara’kunya, k0 dai kinzo kigag. abinda

muke tunda laben da kike bai miki ba?” Abubakar

ya ce, “To sai kizo ki wuce ga Sauran. abinci can

saman (table) kici, kuma idan kin gama ki

kwashe kayan ki kaisu kicin ki wanke

ai dai kina jina ko?”

Rukayya ta daga kai alamar ce, sannan ‘ta wuce

simi-simi ta gefensu, Suhailat ta watsa mata

harara har da jan tsaki, tace

Sakarya, bakauya kawai. Allah wannan

da ganinta za tai iyayi”. Abubakar dai bai ce

komai ba, ya koma ya kwanta ya ci gaba da

abinda yakeyi

Rukayya taje gaban (table) tana mazurai, shin

zata zauna ne koko zatA diba ne

ta wuce? Bata da amsa, don haka ta ‘dauki filet

da cokali ta dibu-iya yanda zata iya cinyewa ta

zauna a qasa tanaci sai kace wacce aka tsare sai

faman tutturawa take hannu baka hannu kwarya.

Abubakar dake kwance ya; hangota dirshan a

kasa kamar wata almajira ya tabe baki ya dauke

kansa.

Tana gama cin abincin.ta mike ta kama tattara

wurin, sai data gama sannan ta dauka ta nufi

hanyar fita.

Abubakar ya ‘ watso mata kira, “Ke

mahaukaciya! ‘Gidan wa zaki kai?”

Rukayya ta tsaya tana mazurai, sai da ya sake

maimaita mata tambayar sannan ta ce ‘

“Fita zanyi in wanke” . Ya ce,” Ke, zo ki wuce

dallah nazo nuna

miki”.

Rukayya ta dawo ta tsaya sai faman walqita

idanuwa take, sai da ya nutsa yasha iska tamkar

ba zai tashi ba, nauyi ya ishi ‘Rukayya

saboda‘kayan dake hannunta, sannan ya tashi ya

nufi hanyar kicin ba tare da ya tanka mata ba.

Sai da ya shiga kicins din yana tsaye yana jiranta

yaji shiru, sannan ya leqo.

“Ke uwar me kike anan tsaye?” ‘Rukayya tai

saurin binshi, bai ce ta sauke*’ kayan

hannuntaba, ita kuma tana tsoron ta. saukc tai

laifi “haka-ya shiga nunnuna mata yanda ake

amfani da kayayyakin na‘urorin dake kicin din

gaba daya, sannan ya ce

“Muje’kuma (toilet) in nuna miki”.

Da kayan ta bishi Abubakar ya watsa mata wani

irin kallo. _

“Ke wai me yasa har yau ba zaki hankali

ba, wai kullum’kina girma kina ‘cin qasa?

ajiye tiren kwanikan muje”. Rukayya ta ajiyc

sannan ta bishi, duk wani abin da yasan bata

sanshi ba sai daya nuna mata, sannan ya dawo

da ita kicin din tai wanke-wanke. .

Har ya nufi hanyar fita ya waiwayo, “Au . na

manta ban miki kashedi ba, nasan halinki da

tsinanniyar amsifa da fadan tsiya, to wallahi

tallahi duk randa ki ka sake gigi ya kaiki kika

takali mata ta k0 kikai mata rashin kunya, kin

san halina sarai yarinya, zan iya abinda yafi haka

ma.

Sannan batun aikin gida, ki tabbatar da garin

Allah yana wayewa duk abinda kike ki saki ki hau

gyaran gidan nan, da kuma kuku ya shiga kicin ki

bishi kina kakkama mashi ayyuka da safe, rana

da kuma dare, ina fatan kin gane”

Rukayya ta daga mashi kai, sannan yaja kwafa

ya wuce. Ta raka shi da kallo har ya bace,

‘sannan ta dawo da kallonta akan tilin kayan

‘wanke-wanken dake gabanta, taja wata .

nannau‘yar’ ajiyar zuciya ta duqa ta soma wanke

wankcn.

Tana cikin goge-goge a kicin din Kuku ya shigo

ya dora abincin . dare, saurayi ne dan kimanin

‘Shekaru talatin da fan wani abu, Bayerabe ne

amma Musulmi yaji Hausa sosai. ‘

Suna hada ido da Rukayya ya sakar mata

murmushi. .

‘ “Sannu ‘yan mata, ashe na samu abokiyar aiki,

yaushe aka kawo ki gidan nan ne?” Rukayya

tamkar ba zatai magaba ba, ta ce.

‘ “Dazu”.

Ya waro ido, “Daga zuwanki kuma ba za ki huta

ba har Zaki _ soma aiki?” Rukayya tai Shiru ba

tare da tayi magana ba, . don haka shima kukun

ya cigaba da abinda ke gabansa. ‘ . RuKayya ta

gama wanke-wanken, sannan

ta dauki doyar da kuku ya bata ta feraye masa,

ta cigaba da fira. Tana gama feran doyar ya miko

mata yanke-yanke, tana yi ba ita ta samu ‘tabar

kicin din ba sai da ya gama girkin tsaf. ‘ Abun

ya‘zama jiki, kullum in zai yi girki sai ya kira ta,

duk wani aiki mai wahala ita yake bawa tai masa,

sannan idan an gama duk

lol rukayyah dai ta zama yar aiki karfi da yaji

naku har kullum A,I,S KE cewa asha karatu lafiya

sannan a dinga comment

RIKON KAKA

CHAPTER15

abinda akai amfani dashi ita yake barwa ta

wanke ta goge kicin din, safe, ‘rana da daddare.

Tun Rukayya na jin wahala har ya kal‘ ga ta

saba. ‘

Tund da asuba Rukayya ta farka tai alwala tai

sallah, sannan ta koma baCCin asuba kamar

yanda ta saba a. kullum. Cikin barci taji an maka

mata wani uban duka a jiki tamkara mafarki, ta

zabura ta mike a gigice tamkar mai shirin fita

hayyacinta. ‘

.Suhailat ce tsaye a, bakin gadon tana” cikin

shiga ta alfarma, tai kyau har ta gaji, gashin kan

nan nata yasha gyara, yana zube > saman

kafadunta. Duguwar riga ce a: jikinta (miik

colour ) mai adon duwarwatsu bakake tun daga

sama har kasa sai daukar ido suke. Dan

‘qaramin bakin ya sha janbaki sai daukar ido

yake. ‘ .

Ta. nuna Rukayya da siririn farin danystsanta

wanda yasha bakin lallr ‘cikin tsawa tace

‘ ”Tashi ki fita munafuka kije ki gyara min

falulluka’na, wato ke har wani bacci koma saboda

samun Wuri. T0 idan ma kina _ tunanin barci kika

zo yi gidan nan to ki, gaggawar: sauya tunaninki,

don ko’ yan aikin .‘dake cikin gidan nan sai sun

fiki hutawa da Jin

‘ dadi kinji na fada miki Tashi muje ki gyara

.min dakuna kinji na fada miki

wani irin tsoro da fargaba suka kama

‘Rukayya ta zabura ta fice daga falon, ‘ ‘ .

Suhailat taja wani dogon tsaki tabi bayan‘ ‘

RUkayyar ta sameta tsaye a falon nata sai

makyarkyata take suhailat ta wur’ga mata

tsintSiya,ta daki fuskarta ta ce

‘ “Ki maza ki share ki kakkabe ki” ki goge,kiJe ki

gyara min komai kamin kuku ya iso ku shiga

kicin” ‘ .’

Rukayya bata iya cewa komi ba har ” Suhailat ta

wuce‘, sannan ta ja wata irin ajiyar zuciya wadda

ke bayyanar da tsananin tsoron daya kama ta

Rukayya kenan ko ina bakinta ya tafi da tsiwa da

fada? Wadda rigima k0 ba tata ‘bace ‘shiga take

ta siyi fadan tai ruwa tai tsaki; amma gashi yau

babban fada ya’ tunkarota tana‘ gocewa, k0 me

yasa‘? K0 da yake Hausawa na cewa k0 Baba da

Babansa ‘

Duk da rashin aiki irin na RuKayya da son‘jiki,

amma yanzu duK babu su, ta Saki jiki tana ta

faman aiki. Ta zama wata (Very silent), tai

(cooling) sosai tamkar ba ita ce mai shegen

surutu nan ba. Rayuwa kenan, duniya juyi~ juyi

wai kwarto ya da. ya fada ruwan zafi yace,

“Daminar bara ba irin ta bana bace”.

*

Y‘au wata daya da zuwan rukayyah gidan

Abubakar, kullum cikin wahala take, bata da zama

sai cikin dare, don haka idan ta kwanta kamar

matacciya, ana asuba kuma zata farka ta fara

daga inda aka tsaya. Saboda wahalar datake

gidan k0 Bangarenta bata iya gyarawa bata taba

wanka ba, tun kayan da aka kawota dasu

sune a jikinta har yanxu da take ‘duqe tama goge

gogen na’urorin duke qaton falon gidan.

Abubakar ya fito daga falonsa shi da Suhaiiat

tana manne a jikinsa, yana sanye da kayan

ma’aikata a jikinsa, Suhailat na rungume da

jakarsa ta ma’aikata. Rukayya ta saci kallon . su

tai sauri ta dauke kanta daga kansu. .

Suhailat ta dubi Abubakar, “Au Dear, na manta

don Allah ( just five minute)”.

Abubakar ya ce, “K0 minti daya ‘kika qara sai dai

ki dawo ki samu bana nan”.

Suhailat ta ce “Na yarda”

‘ Sannan ta kwasa da gudu gudunta ta nufi

falon da suka fito

Rukayya ta dauki bokitin da ta jiqa omo da mofa

ta gifta Abubakar,muryarta a raunane ta ce

“Ina kwana?”

Sai da ya matsa yana kakkare hanci kamar

wanda yaga wata Shara, fuskarshi a dagule ya ce

“Subhanallahi! Kina da hankaii kuwa? Dubi kayan

jikinki yanda sukai dakal-daqal, ke

ko warin jikinki bakya ji sai kace mai kuli kuli?

Mtsw!’ Allah Yai wadan wannan qazantar taki,

sakarya wadda’bata san ciwon kunta ba. Wallahi

kar ki sake na qara ganinki da wadannan kayan,

(stupid) kawai, wuce daga nan dallah”. . .

Rukayya ta, wuce simi~simi tana bin. jikinta da

kallo, ita bata ga wata shahararriyar dauda da tai

ba da har zai mata wannan cin fuska ba. ,

Hawaye suka ciko mata. a idanuwa, duk qazantar

da take ma ai ‘su suka ja mata, aikin ‘gidan

kawai da take ai ba qaramin ‘ tashin hankali

bane.

Ta sa‘hannu ta ‘share hawayen da suka ‘ zubo

mata, ta duqa tana zubar da ruwan

Kamar kullum, yau ma tamkar marar lafiya

Rukayya ta wuni, ana kiran sallar la’asar sannan

ta samu lokacin shiga (toilet) ta samu tai wanka

tana fitowa ta samu mai ta shafa sannan ta Ciro

daya daga cikin Kullin kayanta ta

saka, ta fito don tasan yanzu kuku yazo su dora .

. abincin dare. _ . , Suhailat tana zaune saman

daya daga

cikin kujerun dake zube a falon, tana sanye da , .

shigar shadda doguWar riga har kasa mai hade

da zanenta, ta sha ai’ki tun daga sama har kasa

sai daukar ido take, mai ruwan kasa-kasa da

ganin shaddar zata yi tsada. Tun daga kunnenta

har wuya har zuwa” ‘_ kafarta da yatsun

hannunta gwala-gwalai ne, ” . sai walkiya suke.

Babu abinda yafl daukar . ‘ ‘hankalin Rukayya sai

daurin kallabin dataima kanta, ta dora kafarta

daya kan daya da takalmi mai tsananin tsini a

qafar tana ta karkadawa. ’ ‘“ ‘ Ta watsawa

Rukayya wani irin kallo wanda ya .kusa ‘sata

makyarkyata, Suhailat tace. . ke zonan gaban

Rukayya yai wata mummunar

‘_ faduwa, ta nufi inda Suhailat take zaune ’ ..

Bata ankara ba sai dai taji ta flsgota ta fadi qasa,

ta sa hannu ta dauke la da Wani

‘ gigitaccen mari har sau biyu.. ‘ Rukayya tasa

kuka tana faman rawar

jiki, Suhailat cikin tsantsar masifa ta soma

magana.

“Uban waye ya koya miki yin wanka a cikin gidan

nan? Wallahi sai kin fada min wanda ya kitsa

miki wannan”.

’ Ta janyo Rukayya ta shiga duka tako’ ina, tun

Rukayya na ihu har ta soma qokarin kwatar.

kanta.

Suhailal ta tsaya tana tafa hannuwa,

“Lailaha illallahu, kokawa za kiyi dani iye? ‘

Kokawa za kiyi dani na ce? To bisimillah”.

_Cikin kuka Rukayya ta ce “Wallahi -ba

kokaWa xa muyi. ba, kiyi hakuri don Allah.

Suhailal tace”Ai Allah yau sai kin fada min wanda

ya koya miki yin wanka da sauya kaya a cikin

gidan nan”. ‘ Rukayya tace”Ai Yaya Abbakar ne ‘

Cikin kaduwa Suhailat= ta saketa tana maimaita.

“Abbakar, wane Abbakar din?”

“Yaya Abubakar, ai shi ne dazu zai fita ya….”tace

me? Dakin ki ya shiga? Ku kai ‘ me? ‘ Me ya ‘

shiga ku kayi‘?“ Cikin rudani da kaduwa Suhailat

ta jero mata tambayoyin da ita kanta bata san

ma ‘anarsu ba, sai ma tsoratar da Rukayyar da

tayi da ganin yanayinta, ta rinka ja da baya cike

da tsoro. ‘

‘ ,Suhailat tace, “Dakata daga nan inda kike’ ki

bani“ , amsar ‘tambaya ta“. Cikin ’rudani Rukaya

ta ce, “Dazu da zai fita a _ falo ina goge-goge ya

ganni yace in wuce inje in canja kaya, kar ya

dawo ya sameni dasu a jikina”.

Suhailat taja wata nannauyar ajiyar zuciya mai

karfi sannan tace ‘

‘ ’ “Wuce muje ki tattaro min duka kayan da kika

zo dasu gidan nan”.

Ta“ tisa Rukayya a gaba suka nufi sashinta jiki

na rawa ta tattaro mata duka‘ yan komatsan da

tazo dasu, Suhailat ta dauka ta zubesu a qasa ta

bincike kayan, ta zaro mata

1page is missing

taje ta kona kayan,” sannan .ta wuce sashinta,

kai. tsaye toilet ta fada ta sani

(scptol) da ruwan xai .ta Wanke hannayenta ,

sannan ta fito abinta. Bayan sallar magaruba

Rukayya na

kwance saman makeken gadon dake dakinta

tana. kallon t.v din dake manne jikin bangon .

.dakin, idonta ne kawai saman tv din, amma gaba

daya ilahirin hankalinta baya kai, xuciyarta

ta lula duniyar tunani

‘ ’ A .hankali ta dago kanta tana kallon kofar”da

taji an turo ,Suhailat ce ta shigo babu’

ko sallama, rukayyah ta zabura ta tashi zaune

sai rarraba idanuwa take . Suhailat taja ta tsaya

riqe da kugu kafin ta kallii rukayyah ta tabe baki.

““ “

tace lallai samun wuri wato anxo birni ansha jar

miya har kinsan kixo ki miqe saman gado kina

kallo ko , to daga yau kin gama shi, shegiya

wayar dake hannunta ta lallatsa sannan ta kara a

kunne

hello sagir don allah kazo ” zaka cire min

na’urorin kallon dake sashin bakine don Allah yau

k0 gobe

Ta danyi jim kafin ta ce”Okay, to Allah Ya kaimu”.

Ta kashe wayar, sannan ta ‘ dubi Rukayya. , ‘ .

‘ “To nayi maganin tsaffin idanuwa wanda duhun

gona ya riga ya kashe sai inga ta iyayi kuma.

Don na lura idan nai sake wata rana sai kin ce

dani zaki goga, don haka ke da gogewa sai dai a

lahira haka za ki qare cikin duhun’kai da‘ jahilci.

Ki tashi ki flto falo kuma dan uwan naki na kira”.

“Mtsw!”. ‘

Ta ja tsaki, ta balbadeta da harara

Jikin Rukayya ya kara sanyi tamkar mai

masassara, haka ta yunkura ta sauko daga kan.

gadon ta nufo falon kamar marar lafiya

. . Abubakar da Suihailat suna zaune saman

kUJera mal zaman mutum biyu, Rukayya ta

tsugunna a ..gabansu.

tace gani

Abubakar ya watsa mata, ‘ wani irin razanannen

kallon daya motsa mata hanjin cikinta

“Sannu, sannu marar kunya, wato kenan har jinki

kike wata tantiriyar marar kunya Hmm! Rukayya

kenan masu ilimi da wayewar kai ma sunyi sun

gama ballantana ke dake fama da ciwon jahilci

da duhun kai

K0 da yake ai ance dogo da hankali dama dacene

amma banyi tunanin ‘rashin hankalin naki har ya

kai kice zaki kokawa da iyalina ba. ‘ Ashe wautar

da sakarcin dake dankare cikin kanki sun‘wuce

iya sanina Wato duk nasihar’ danai miki ashe ta

bayan kunnen ki tabi ta wuce bata shiga ciki ba

kenan? ‘ Saboda kina ganin kamar ban iya

daukar mataki akanki wato don na daina taba

lafiyar jikinki ko to kisani ‘akan matata wallahi

zan iya jirkita miki kamanni in barki kwance

kinji na rantse miki wannan girman jikin naki da

kikai bazai hanani dinga jibgarki kaman allah ya

aikon ba

lol su abubakar manya

asha karatu lafiyaa zallah

RIKON KAKA

CHAPTER16

yace wannan ya zamo na farko kuma “na Karshe,

wallahi k0 kallon banza. kika sake kika Kara yi

mata na lahira saiya fiki jin dadi. Tashi ki bani

wuri!”. ?

Ya daka mata tsawar da batasan sandata zabura

ta rufta aguje tai hanyar sashintaba, yaja tsaki.

“Mtsw! Zokalar banza zokalar wofl“. -. Ya dan ja

numfashi kafin ya maida kallonsa akan Suhailat. ‘

“Kiyi hakuri’ don.Allah, ki qara daddaure mata,

saBoda‘ yarinyar bata da wayau ko kadan, k0 can

haka take da shegen fadan tsiya, ga shegen karfi

kamar namiji, sai ‘ kace -ba mace ba. kibita a

hankali, ‘ kinga ‘mahaukaciya ce, kar ta’zo ta

kayar min dake a” banza”. suhailat ta watsa

‘masa wani kallo mai kama da: harara, cikin sigar

zulaya tace ”Oh! Wato ni raguwa kakr dauka ta

kenan ko?,” ‘ Abubakar yai dariya kafin ya ce’

”zaki hada karfin mutumin kauye Wanda ya saba

da cin‘dawa da masara da na

mutumin birni, wanda bai da abinci sai biredi da –

indomie?” Suhailat ta ce, “Allah k0?“

Ya ce, ‘Da gaske idan kuma baki yarda

. ba na kirata tazo ku gwada naga wanda za’a

kayar”.

Suhailal tai murmushi kawai ta mike ta

janyo“wayarts dake ta faman ruri akantebir din

dake , gabansu.

Rukayya na shiga sashinta ta fada kan ‘ gado ta

soma rera kuka mai tsuma zuciya, kalaman

Abubakar sukai mata tsaye a makogoro’ _ tamkar

.mashi, ji. take tamkar zata hadiye zuciya saboda

tsabar bacin rai da bakin ciki. ‘ Ada bata damuwa

da duk wulaqancin da Abubakar ke , mata amman

to amman yanzu mai yasa abin ke damunta?

Tambayar .da taiwa kanta kenan’ wadda bata da

mai amsa mata ita. Tai saurin’ zabura ta mike

lokacin da maganganunsa ke dawo mata.

wallahi akan matata zan iya jirkita miki halitta in

barki a kwance kinji na rantse miki kuma

don wannan qatuwar da kikai bazai hanini dinga

jibgarki kamar allah ya aikoni ba

Rukayya ta maimaita, “Katuwa kuma‘!” A sanyaye

ta nufi gaban dogon madubin dake tsaye a gefen

gado ta soma bin kanta da ,idanuwa. Ita kanta

sai da gabanta ya fadi, ta sa hannu tana shafa

wuyanta wanda ya ciko duk wasu rami’ da gurbi

ya cike ldanuwanta suka dira saman kirjinta

wanda ya qara cika tamkar zai fasa rigar ya’ filo.

lol

Gabanta ya fadi, to tun yaushe ta zama haka?

Ta dan karkata yana kallon kugunta da cinyoyinta

wanda suka qara budewa, sai dai har yau bakin

nan na nan kamar baqin zunubi

Rukayya ta koma tanara sharar hawayenta,

tabbas samun cima mai ‘ kyau yana gyara jiki

fiye da shan wasu kwayoyin magani.

Ko ina Kaka take yanzu? Idan ba zata manta ba

yau satin su shida rabon da su hadu tun ran data

kawota gidan gashi jin dadin

da take mata kwadayinsa amma ba a sameshiba,

‘ kullum tana cikin zubar da hawaye amma gashi

har wata kiba take, kota mece ce Oho. Ta bawa

kanta amsa.

Ga dukkan alamu Rukayya ta shiga shekarar cikar

‘yan matancinta, saboda ga jikinta nan ya nuna,

sannan ga tunaninta ya soma canjawa daga na

quruciya zuwa na masu hankali.

Tasa hannu ta share hawayenta sannan ta laluba

ta kwanta tana maida ajiyar zuciya, a haka bacci

barawo ya lallaBo ya sureta.

A kwana as tashi ba wuya wurin Allah, yau watan

RuKayya biyu a’gidan Abubakar, babu wani

abinda ta samu na cigaba illa wata irin natsuwa

da tazo mata, da raahin son magana, ga wani irin

hakuri. In zaka sa yatsa a bakinta ba zata iya

cizawa ba.

gurin qazanta kuWa sai abinda yai gaba, ~

‘ ita kanta tsamin jikinta ya takura mata

ga

atamfar dake jikinta har ta soma yayyagewa

don dama can taji jiki shiyasa ko aiki

take ta shiga kare-kare kenan, kada wani yaga

tsiraicinta. –

Yanzu haka aikin take ita da kuku suna girki, shi

ne ta dauki tawul din da suke goge~ goge ta

daura a kugunta a saman zanin jikinta, tana

aikinta. ‘

Suhailat ta leko kicin din, “Da Allah ku

saki wannan aikin, ina da baqi maza a hada masu

abin motsa baki, (just 10 minute) na baku”. . , ‘

bata saurari abinda zasu cc ba ta juya ta. ‘ fice

Kuku ya dubi Rukayya cike da damuwa a

yanayinsa,kafin ya ce

“Gaskiya Hajiya tana da matsala, yanzu

maimakon ta bari mu qarasa abinda, muka dora,

a’a sai .dai mu sauke mu dora wani‘ Rukayya ta

tabe baki ba tare data tanka ba,taci gaba da

abinda‘ take. Shima ganin hakan yasa ya juya ya

soma abinda ke gabanshi, don yasan in ya biyeta

sai ya wuni yana maga’na bata bashi amsa guda

ba, don haja yaja bakinshi ya tsuke

Suka hadawa baqin kayan kwalama irin su

(snaks) kusan kala hudu, sai dambun naman kaji,

sannan farfesun da sukayi na naman zabi suka

hada masu dashi, Rukayya ta dauka ta fito musu

‘ dash

Kallo ,’daya taiwa bakin ta janye idanuwanta a

qasa ta ajiye kayan abincin ta yunkura ta mike ta

nufi (fridge) ta Ciro musu lemuka da robobin

swan water.

Muryar wata daga cikin qawayen ta daki dodon

kunnen Rukayya.

“Kai Suhailat, yanzu ki rasa wadda xaki dauka

aiki sai wannan. qazamar bakauyar? Haba! Ni

wallahi k0 cokalin data taba ba zan iya cin abinci

dashi ba Dubrta fa don Allah ‘ sai tsami take”.

*

Suhaiiat tace, “Haba Rahma, yar gayu kikeso in

dauka wadda zata kwace min mijin cikin qan

kanin Iokaci k0?”

Wata daga cikinsu ta ce, “Ah! Ai daga, baya

kenan , in banda sakarcin ki Suhailat ki rasa

wadda za ki dauka aiki sai mai

coca Cola sharp? Aike da gani wannan k0 bata

samu gyara ba sai ta dauki hankalin ‘yan maxa.

Ke baki ga yanda take ba a dire, ga tsawo ga

sharp? Ai wannan ita ce bature yaiwa laqabi da

Coca-cola , don haka tun wuri ki sake shawara,

don kada wata rana tazo ta tsokale maki ido har

yai ruwa, don kin san dan hakin daka raina…”.

Rukayya da ta ajiye musu lemuka saman tebir tai

sauri ta juya ta bar wurin, gabanta na faman

faduwa, saboda tsoron matakin da Suhailal din

zata iya dauka akanta yanzu kuma.

Yau sunyi daren girki, ba su suka kammala

abincin dare ba sai bayan sallar magariba,.

saboda Bata Iokacin da sukai wurin hadawa

baKin Suhai’lat abin motsa baki.

Suna kammala girkin kuku ya fice daga kicin din,

Rukayya ta dauki farfesun naman zabin ta zauna

ta ci da ruwan tca mai zafi tana gamawa ta mike

ta share kicin din ta gage, ana kiran sallar isha’i

ta filo daga kicin din a lokacin Abubakar ya fito

shima daga sashinshi yana daurA agogon hannu,

da alama alwalar sallar isha’i ya dauro.

Sukai ido hudu da Rukayya tana Rokarin gaida

shi, ya daga maya hannu.

“Rike gaisuwar ki”._

.Ya kare mata kallo cikevda kyama yace’

“Yanzu dama a haka kuke mana girkin da muke ci

da wannan tsinanniyar qazantar? Dubeki Rukayya

sai kace ba ‘yar mutum ba‘? Shin wai k0 dai

aljanu garc ki wadanda sukesa ki qazanta ne

iye?” Shiru ya dan ratsa wurin kadan, yaja yar

gajeren tsaki.

‘ .“Mtsw!”. _

Ya dubi Suhailat dake can zaune saman (

daya daga cicin kujerun dake baje a Cikin falon,

ya ce‘ .

“(My love) don Allah ki dan tsintsinto mata wasu

daga kicin kayan da kika gama dasu, wallahi ban

.qaunar qazantar nan k0 ’kadan”. ‘ Suhailat ta

mike tana fadar, “Wah! Ni zan bawa ‘yar aiki

kayana ta saka” Wallahi ba dai niba, a koma

qauye kenan aji dadin kullo mani wani ‘mugun

abin’? Ai ni bani ‘daga cikin

matan dake bawa yar aiki kayan da suka gama

ashema

Na kwashe kayana, a sami wurin jera nata kenan.

Abubakar ya ce. ‘a”a Yar uwar tawa?”

Suhailat ta ce. “Koma wacece inda har tana nan .

a matsayin ‘yar aiki to fa haka nake son ganinta”.

Abubakar ya ce “Ba zan iya ba, ai tsafta tana

daga cikon addinin Musulunci, kuma ke kanki za

ki iya rantsuwar kayan Rukayya ba za ‘ suyi

sallah ba. Dubi yanda take yawo da kaya a

yayyage”.

Suhailat ta ta tabe baki, “Matsalarta ce wannan

Dear, wa yace ta yayyaga in bata son yawo dasu

haka?”

Abubakar ya Juya ya dubi rukayya cike da bacin

rai, yai gaba yana fadar.

“Z0 muje Rukayya”. .

Ta bi bayasa a tsorace, kai tsaye gidan suka fita,

yana gaba tana baya. .

Gidan dake jikin nasu suka shiga, shima qatone

sosai,mai gadi yana sallah don haka kai

kai tsaye suka wuce ciki. haduwar gidan ya ninka

na Abubakar sosai, kai da gani ‘gidan wani

babban hamshaki ni

. Salda ya danna (bell) sannan aka bude suka

shiga matar gidan ce tsaye a bakin kofar da

murmushi a “fuskarta.

“A’a dan duniya, kaineka dawo? Ka gama yi min

tsiyar taka?” Matar gidan ta fada tana murmushi.

Abubakar ya ce, “Yanzun ma ba zama ‘nazo ba,

Kanwata na kawo miki don Allah ki bata’ kaya

kala guda ta canza wanda ke’jikinta kafin zuwa

gobe in san yanda za’ai”. ,Matar ta mai da

kallonta akan Rukayya tana fadan . “Wayyo Allah,

ina ka samo ta ,kuma Abbakar kai ko baka gajiya

da rakice-rakici Abbakar ya ce “Na’ce miki

qanwata ce, baki , yarda bane?” ’ Dariya tayi ta

janyo Rukayya jikinta tana “fadar.

matar tace”Ai qaryarka ba sallah take ba ”yan

mata ya sunanki‘!”

“Rukayya”.

Ta bata amsa a taqaice.

Matar ta kada kai uhm tace “Nice name“.

_ Abubakar ya ce, “Bari injr masallaci in

dawo.

Ta ce “Sai ka dawo”.

Ya juya ya fita sannan matar taja hannun

Rukayya suka nufi cikin gidan tana

murmushi

Saman bene suka hau kai tsaye suka shiga wani

qaton falo sannan ta jata suka shiga cikin dakin

dake gefe qaton (bedroom) ne wanda ya gaji da

haduwa

Rukayya tabi wani hoto da kallo wanda

aka girke a falon matar gidance da wani

magidanci suna mngume da juna sunsa wasu

yara a gabansu

To wai dama haka rayuwar birni take Mace tai ta

rungumar namiji ba kunya koko ya abin yake ne?

_

Duk zuciyar Rukayya ce ke raya mata hakan, bata

ankara ba, sai dai taji matar ta ambaci sunanta.

Tai saurin waigowa ta ga ta bude mata wata

qatuwar (wardrop) bango guda, babu abinda ke

danqare a cikinta sai suturu, tsoro ya kama

Rukayya, ta ce.

“A’a, ki bani k0 wanne Hajiya”.

Matar ta ce,‘ “A’a, kar muyi haka dake kizo kawai

kizaba idan kuma kina ganin sun miki girma bari

na kawo miki wasu dogayen riguna ki zaba

wadda kike so jiya maigidana ya dawo daga

Dubai yaxo min dasu guda hudu, ne naga duk

sunmin yawa, daya ce kawai tai mini Ina zuwa,

bari na dauko miki su”. .

RuKayya bata ce komai ba, matar ta fice daga

dakin, bataci minti biyar ba sai gata‘ ta .dawo

rungume da kaya a hannunta ta zubesu gaban

Rukayya

tace lol mu tara donjin ci gaba naku har kullum

A,I,S

KE cewa asha karatu lfysa zallah

RIKON KAKA

CHAPTER17

‘Gashi, ki dudduba’.

Rukayyya tasha jinin jikinta matuka, harta kasa

bincika kayan, sai saidai ta zari guda. ~ Mata

tace ‘To ga (toilet) can ki shiga ki wanka kisa

kayan ga kayan kwalliya a gaban (mirrow) sai ki

shirya’.

. Rukayya tace ‘To’.

Ta mike ta nufi (toilet) cike take da mamakin

yanda matar ke janta a jiki haka, ba tare da nuna

tsana ko kyama ba.

Wanka tayi sosai a(toilct) ta, fito sannan Matar

_bata nan don haka rigar kawai ta dauka ta saka,

ta rataya dan sirin gyalen rigar saman kanta ta

daure shi a wuya.

Tana cikin tattara kayanta matar ta shigo da

sallamana riKe da wasu takalma ruwan kalar

rigar ta nunawa rukayya.

“tace mahadin rigar, ne ai sun hau ko?‘

Rukayya bata iya magana ba amsa kawai ta bata

tace

“Nagode’.

Ta saka lakalmin mai mutuqar tsini ita ita kanta

tasan ta yaudari kanta idan tace zata iya

tafiya da takalmin, don haka ta dan dubi matar a

kunyace ta ce

“Anya zan iya tafiya dasu? Ba zan iya ba, sunyi

tsini”.

Matar tai murmushi, “Sister kenan, ai takalmi mai

tsini yana daya daga abinda ke fitowa mace

sharp dinta. Karki damu da ‘tsawon ki, ki daure

za ki iya tafiya da su, kije ki danyi (makeup) kafin

yazo k0?”

Shiru tai don k0 za’a dora mata bakin bindiga

bata san k0 meye haka ba. Ganin ta‘. danyi dam

yasa matar ta fahimta, don haka ta dafa kafadar

RuKayyar tana murmushi, tace.

“Ina nufin ki danyi kwalliya ko yaya”.

. Rukayya ta girgiza kai, alamar a’a, matar ta ce.

‘ ”A’a, kar muyi haka dake ‘yar uwa, tunda kika

ga Abubakar ya kawo ki nan to ki saki jikinki, mu

da shi tamkar ‘yan uwa muke, abokin aikin

maigidana ne, mijina shi ne babban su a (office)

din da suke aiki, don haka ki saki jikinki. Muje in

taya ki kwalliyar ma da kaina”.

Ta kama hannunta suka nufi gaban madubi, ta

zaunar da, ita saman kujera, ta mika mata mai ta

shafa a jikinta, sannan ta dauko (foundation) ta

shafa mata, ta dauki ta gari ta shafa mata,

sannan ta shafa mata wata kalar kuma. Sannan

ta zane mata girra da (brown air pencil) ta zana

mata a qasan ido tai‘ mata line a

, labba sannan ta shafa mata jambaki (24hours),

ta‘koma ta dora mata (pink) a sama. (Eye

shadow) shima (brown) ta shafa mata a saman

ido, sannan ta zana mata (cyc leaner) sannan ta

sharce mata girar ido da mascara ta shafa mata

bakin kwalli, sannan ta gyara mata mayafin, ta

nada mata shi irin yanda larabawa ke yi. Sannan

ta feffesa mata turare ta k0 ina a jikinta,‘ ta riqe

hannunta.

tace to dubi kanki a madubi yanxuu Rukayya,

har kin flto a macer ki sak”.

Rukayya ta bi kanta da kallo, ita kanta tasan tayi

kyau matuqa,” amma yanda ri gar tabi

jikinta shi yafi komi birgeta. Ashe haka take

dama? Ashe ba wani kyau ne aka fita ba kawai

an flta iya fito da kyan ne. ?

.Matar tace, ”T0 amma me yasa ba ki

gyarakanki? Baki ga yanda kitson kanki ya

dankareba Ga faratan ki sunyi zaqo-zako, . na

qafarkima tayi kina macen ki me yasa haka? ‘ ,

Haba Rukayya, ai ita, mace ‘yar gyara ce sai da

gyara. Na tabbatar Abubakar bai kai ki gidansa

kai, tsaye ba sai ‘don kar matarsa ta . ganki a

yamutse haka, kin san mata ’yan rainin wayo ne,

yanzu data ganki haka wani sabon (page) din

rainin wayo ne zai bude Don haka gobe “da kin

gama abinda kike ki dawo zan tsin-tsintar miki

kaya k0 kala goma ne aba tela ya gyara miki ki

rinka dan sauyawa kinji?”

Rukayya ta amsa da, ”To”.

. Matar tace “Yauwa, haka” nake so, kinga idan

kika gyara kanki matar bata isa ta raina miki ba

ballantana yayan naki Muje qasan don nasan

wata qila ya dawo

Sannu a hankali Rukayya ke taflya sai kace ‘yar

koyo, abin har ya bawa Hajiya

malar gitan), ta rinqa gwada_ mata yanda ake

taflyar har suka isa qasa. ‘

A zaune suka samu Abubakar da mutumin da

Rukayya ta gani a hoto suna cin abinci, Abubakar

ya kafe su da wani irin kallo tun daga nesa. Ba

wai kwalliyar da Rukayyar tai ya dauki hankalinsa

ba, saboda idan maganar kyau ne Suhailat ta

ninka ta, gaban rigar-shi yafl komi daukar

hankalinsa, ‘saboda duk tsawon rigar babu inda

akaiwa ado sai a’ Kirji, aka kuma qara ciko gaban

rigar da soso (breas cup) mai da tsohuwa yarinya

kenan, ko na ce a cuci maza. ’

To ila wannah dama yarinyar ce kuma . mai

kayan ya abin zai’ ba da kenan? Abuhakar ya

sauko da kallonshi har saman kugunta Wanda yai

wata Irin budewa tare da cinyoyinta, a take kuma

ya dauke kansa daga kallonsu saboda yanda yaji

kirjinsa ya buga da karfi Yai gaggawar kawar da

abinda ya zunguri zuciyarshi, don haka bai san

qarasowar su ba sai dai yaji maganar‘ Hajiya

Maimuna na ‘ fandar.

“Kai Yallabai, abin har ba’a ganin masu shigowa,

anya ba zamu ware maka kwano a gidan na ba?”

‘ Abubakar yai dariya kafin ya ce, “Magori wasa

kanka da kanka, idan maciyan abincin kike nema

ai kisha kurumin ki, don na fada miki, . Oga

Mahmud nan zai santalo maki tsala~tsalan ‘yan

mata har guda biyu, kinga sai kiji dadin

.girkin”.Dariya tayi sosai kafin ta ce “Ai k0 da kun

gwammace ku tari (transformer) da ruwa a jikinku

da kuce za kuyi wannan gangancin, don duk dan

da ya hana uwarsa barci wallahi shima ba zai

runtsa ba, kaji in fada maka”.’

-_Abubakar ya ce”Yo araduma tayi ta gama

kuma walqiya kawai akai aka dauke”.

‘Ta ja numfashi, “Hum! ‘to ai sai ku tanadi

manyan na’ urori don shirya sabon (film) din

Dakin Amarya (one to four).

Dukkan su suka kwashe da dariya banda Rukayya

da Hajiyar, Abubakar ya mike yana dariyarsa.

“Ke tashi muje kinji, idan muka biyewa wannan

sai mu kwana anan”.

Ya maida kallonsa wurin Hajiya Maimuna.

“To ranki shi dade, godiya marar adadi, sai na ce

Allah Ya sada mu da alkhairi,’d0n gobe zamu

wuce Atlantic insha Allahu ni da madam, saboda

Wani (course) da zanyi na shekara daya da rabi,

sai ai mana addu’ a”.

_ Ta ce, “Kai don Allah Abbakar da gaske?”

Ya ce “Gaskcn gaske”

. Ta ce”To ita wannan baiwar Allan fa ya . zakai

da ita? Ba zaka maida ita gida ba har zuwa

lokacin da zaku dawo?”

Abubakar ya ce “Nan zata zauna tunda akwai’

maigadi,kuma kema zaki rinka. shiga tana

shigowa itama, saboda zaman kadaici naiwa Oga

Mahmud magana“;

Haj. Maimuna ta ce, “To shi kenan,

Allah Ya kiyaye, Ya tsare Yasa a aje a sa’ a a

dawo a sa‘

Abubakar ya ce, “Amin, kuma don Allah duk

abinda ke nan Zan rinqa kiran waya sai ki fada

mana k0 da bukatata kudi k0 ta wani abu sai a

turo

Haj. Maimuna ta ce “Ba komi, Allah Ya kaiku

lafiya”. .

‘ Ya amsa da, “Amin”.

Har bakin kofa ta rako su tana zabga musu

addu’a, sannan ta koma su kuma suka fice. . .

A tare suke tafiyar, sai dai ba wanda ke tankawa

wani a tsakaninsu har suka shi’go cikin gidan.

Abubakar yabi ta baya ita kuma ta shiga ta falon

da sallamarta

‘ Kallon-kallo suka shiga yi tsakanin Rukayya da

Suhailat, Suhailat ta zabura ta mike a sukwane

tayo kan Rukayya tana fadar.

“Kaza-kazan uba! Uban wa za aiwa ‘ wannan

shigar a gida? Bala‘ il”.

Kafin Rukayya ta ankara har ta shiga kai mata

duka ta k0 ina, tsoro da fargabar abinda

zai iya faruwa shi ya hana Rukayya kwatar kanta

Dukanta take kamar mahaukaciya, ta rinqa keta

rigar, saida taga tabbalar ta yagalgala rigar . ta

yanda bata Kara sanyuwa sannan ta hankada ta

waje, tana. fadar.’

“Yau sai’ kin bar gidannan ‘yar iskar banza

inko ba hakaba wallahi sai na ‘tsugunar dake”.

ta hankadota tamaida kofar ta rufe, Rukayya tai

duke a gurin-tana .faman dibar kuka kamar ranta

zai fita gaba’daya Wata irin

iska mai qarfi ta taso mai hade da guguwa irin

mai Balle kwanikan Jama’ ar nan. _ Hankalin

Rukayy’a yai masifar tashi, tsoro da fargaba suka

Kara shigarta, ta rasa

mafita, To ina zata nufa? Kafin ‘ta gama

tunanin ruwan sama mai. Rarfi ya sauko tare da

faukewar wutar lantarki a tare.-Tsoron ne ya

dabaibaye ‘zuciyarta don saboda ko danyatsanta

bata iya gani saboda duhu.

Ta dunkule a gurin. ruwa‘ na sauka a jikinta da

karfi, kuka take sosai irin wanda bata taba yi ba

tudna Allah Ya halicceta. ‘

Abubakar dake nashi Bangarcn kwance saman

duguwar kujerar dake gefen gado yana

latselatse a laptop ya ga an dauke wuta, cikin

takaici yaja tsaki a zuciyarsa yana takaicin halin

wutar Nigeria.

Ya yunkura ya mike ya jawo rigar ruwa. ya saka,

ya dauki lema da (tourch light) sannan ya fito

daga falon don kunna (generator). Ya bude falon

yana faman haske-haske, tun kafin

ya fita kamar kar ya fitan saboda yanda yaga

ruwan na sauka da qartinsa, sai dai ya zama

wajibi ya fitan saboda sanin halin ‘yar mulkin

tasa, yasan ba zata iya kwana ba wuta ba.

‘ Ya runtse ido yai waje ya nufi inda injin yake, ya

sa makulli ya tayar sannan ya wuto . gabansa yai

wata mummunar faduwa, hatta (toureh light) din

hannunsa ta nemi suBucewa saboda razana. Ya

Kara ware ido, tabbas mutum ne a dunkule a

wajen.

Cikin dakiya irin ta mazan jiya ya daga ‘murya. ~

“Waye nan?” Rukayva ta dago a galabaice saboda

dukan da ruwan yai mata ba na wasa bane.

“Subhanallahi! Rukayya meye haka?” Ya nufeta da

sassarfa, ya kamo ta gaba daya ya dagata tsaye.

“Subhanallahi! Inna lillahi! Wa yai miki ‘ haka?”

Shiru ba amsa sai dai kyarmar haqoran da take.

‘ .

. Abubakar ya riqota sosai a jikinsa ya nufl falon

da ita, kai tsayr falonta ya nufa ya direta kan

kafet, ya mike da sauri ya fita bai jimaba ya

dawo da tawul da jallabiyya a hannunsa, ya

kamata ya tsane mata jikinta da tawul din,

sannan ya mika mata jallabiyyar.

“Amshi ki sanya, za ki iya?” Rukayya ta daga

mashi kai, ya-mika mata farar jallabiyyar sannan

ya juya ya fita.

Ta lallaBa ta mike ta cire rigar jikinta da ta

yayyage sannan ta saka jallabiyyar, sabuwa ce

qal irin ta mazan nan mai hade da hula, ta lallaba

ta koma kan kujera ta kwanta. .

Bata jima da kwanciya ba Abubakar ya

dawo riKe da (Cup) a hannunsa ya miKa mata

tare da Ballin magani, ta karba ta shanye sannan

ta miqa mashi kofin Abubakar ya amsa yana

kallonta, haka

kawai yake jin wani abu na masa yawo a

zuciyarsa game da yariyar, to meye? Shi dai

yasan ba so bane, sai dai wani abu mai kama da

sha’awa.

“Na gode.

Rukayya ta fada da sanyin muryar da bai san

tana da ita ba, abubakar ya dawo dashi ‘cikin

hankalinsa, don haka yai saurin (contoling)din

zuciyarsa.

“Okay, ba matSala”.

Ya fice da saurinsa sai kace wanda aka kora, ya

fice daga falon yaja mata Kofar. Rukayya ta raka

shi da idanuwanta wanda suka ciko da hawaye,

ita kanta ba zata iya ccwa ga k0 kukan meye

take ba

‘ Abubakar ya koma sashinsaya cire jallabiyyar

jikinsa, daga shi sai dan qaramin (short nickcr)

‘sai .dai ‘ ya ‘gaza’ kwanciya, ‘ qirjinshi yai mashi

nauyi matuka. Ya jingina

LOL akwai rikici fa

naku har kullum A,I,S ke cewa

asha karatu lafiya

CHAPTER18

bayansa jikin (wardrop) din dake like a‘ bango,

idanuwansa a rufe. Surarta ce kawai ke faman kai

komo a idanuwansa, shi kanshi bai san tsawon

loakcin‘ da ya dauka ba, sai

dai yaji muryar Suhailat na fadar. “Da kyau, dama

nasan wannan ranar

, tananan zuwa Abbakar, nasan k0 ba dadade k0

ba

jima sai kazo kana son yarinyar nan” Abubakar ya

bude idanuwansa ya kafe

su akanta yana maimaita.

“So… So fa kika ce Suhailat?”

Ta daga murya, “So na ce Abbakar! Ka ‘ soma

son Rukayya, karya na fada?” * Shiru ya danyi,

shin k0 abinda yake ji game da yarinyar nan shi

ne son? Kai gaskiya a’a ba‘ so bane; To meye?

Ya tambayi kansa kai ‘ tsaye tambayar dabata da

amsa.

D0n haka ya girgiza kansa yana fadar.

“Ki yarda dani Suhailat, abinda yakr cikin zuciyata

ba so bane. ‘

Cikin daga murya ta’ce, “Rufe min baki munafiki,

idan ba so bane mene ‘ne? Sha’ awa ?

ce ? tunda’ .ka kalleta a tsirara Allah dau yai

wadan irin wannan zuciyar taka Abubakar, wadda

ba

zata iya kare kanta daga fadawa sharrin shaidan

ba.

Kuma idan ma ka soma sonta Abubakar . ka sani

wallahi’tallahi ba zan taBa yarda wata mace a

matsayin kishiya ba ballantana

wannan sokuwar yarinyar, ballagaza, jaka, akuya,

‘yar matsiyata. Wallahi ba zan yi kishi

da ita ba, sai dai kwarya tabi kwarya, ‘don haka

ina gargadinka da kada ka ballo wutar da zai

kasheka Abubakar ya ce, “Ki dawo hayyacinki

Suhailat, kada ki yanke hukuncin da zuciyar ki ba

zata iya dauka ba, alhalin kin san zuciyata bata

tanadi dakarun da zasu kareta daga kamuwa da

son wata ba .. idan kuma kin aikata abinda kika ‘

so don ki salwantar da rayuwarta saboda kina

tunanin bata da gata to ki sani ni nine gatanta

daga yau kuma daga yanxu inason ki sani abinda

nakeji a zuciyata gameda ita baso bane

bane kuma ba Sha’awa bace, sai dai wani abu

mai kama da sha,awar”. Suhailat ta fasa wata

uwar Kara . “Wayyo na shiga uku! Inna lillahi

Wa’inna ilaihi raji un Ta zube Kasa ta fashe da

wani irin kuka

mai Kairfi.

Abubakar ya duKa gabanta, “Kiyi a hankali, kinga

dare ne, idan da kuma za ki dauki shawara da kin

adana haWayen tun yanzu, don wata qila akwai

ranar zubarsu”. Ya yunkura ya mike.

Suhailat tai saurin riqo hannunsa, “Kar kai min

haka Abbakar, don Allah don Annabi kada ka

zamo sanadiyyar rugujewar farin,cikin rayuwata,

,don Allah Abbakar don Allah, wallahi ba zan‘iya

kallon ka ‘da wata macc a duniya ba idan kace

kai. min kishiya

Abbakar mutUWa zanyi, wallahi mutuwa

zanyi. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Yau‘ ‘na

shiga uku”. ‘

ta hada kanta da hannunsa ta cigaba da rera

kukanta mai ban tausayi, Abubakar ya ja wata

nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce.

“Me yasa kike dauka cewa isarki da tinkahon ki

da zamantowar ki wata zai iya samar miki abinda

kike so da arziqi k0 da

tsiya? Me yasa kika dauka kudi zai iya samar

miki duk abinda kike so a duniya? Me yasa kike

zaton don ina qarkashin mahaifinki

zan iya kwantawa ki takani yanda ranki yakeso?

Kinyi kuskure Suhailat, zuciyar ‘ Abubakar tamkar

dutse take, dutscn ma na ‘ niqa wanda k0 nakiya

ba zata iya masa ba. ‘

‘Suhailat ina sonki son da ba zan iya misalta miki

irinshi ba, a duniya babu abinda ‘zaki‘nema a

wurina ki rasa, sai dai in in raina ne‘shima don

ban iya cire shi daga jikina in bayar.ne Amma ke

sai kike ganin kamar wata isarki ko da arziki yasa

nake miki abninda nake yi.~ Kinyi kuskure

Suhailat, dOn.

har yau ba ai dukiyar da zata sa in yima mace

bauta ba, kuma”

“Kayi haquri don Allah Dear, Wallahi ba zan Kara

ba. Ni dai don Allah kai min alkawarin ba zakai

min kishiya ba, wallahi zuciyata ba zata iya

daukar wannan tashin hahkalin ba”.Suhailat ta

katse shi. .

, , Abubakar ya danyi. jim yana jinjina girman

lamarin,” Suhailat ta‘mike ta kwanta a jikinsa’,

Cikin muryar kuka ta Ce. ‘

“Ba don halina ba, don Allah Abbakar, ni kuma nai

maka alKawarin zan zame maka . daya tamkar da

dudu. Nai maka alkawarin babu abinda zaka

nrma ka rasa na daga zamantakewar . aure da

kyautatawa da soyayyah Ta lalubo hannunsa ta

rike tana matsawa.

“Kai nake saurare my Dcar”. Abubakar ya ja Wata

ajiyar zuCiya mai

qarfi kain yace.”Nai miki alkawari Suhailat”

ta qara makalkale shi

tana sumbatarshi ta k0 ina. “Na gode my Dear,

Allah Ya saka da

alkhairi”. Murmushi kawui yayi saboda nauyin

jinjina girman alkawari da zuciyarshi tayi.

Misalin qarfe tara na safe Rukayya da kuku suka

kammala abin karyawa, sannan ita ’ ta dawo

falon tana gyarawa, bayan ta gama gyaran ‘kicin

din, Abubakar’ da Suhailat suka fito‘daga falo‘

suna ‘janye da akwatina, Rukayya ta sadda kanta

tare da gaishe su cikin girmamawa. Abubakar ne

. dai ya amsa banda

Suhailat da ta juye idonsa ta watsa mata harara

« Abubakar yaCe, ”Yauwa Rukayya, dama sallama

zamuyi za muyi tafiya sai idan mun dawo. na

sallami kuku saboda

gidan yanzu ke kadai ce akwai kayan abinci sai ki

rinqa dafa duk abinda kike so Sai har

Allah Yai mana dawowa”.

Ya zaro kudi masu yawa cikin aljihu ya ajiye

mata

“T0 sai Allah Yai mana dawowa”.

Muryar Rukayya na rawa tace “Allah Ya kiyaye

Ya amsa da, “amin”.

Sannan suka fice

. RuKayya ta raka Su da idanuwanta ‘wadanda

suka ciko da hawaye, haka kawai takejin tana

kewar su,‘ to me kenan?

Ta ajiye tsintsiyar hannunta ta zauna saman

hannun kujera tana kallon Rofar da suka fita

‘sharar da hata idar ba kenan ta lallaba ta miqeta

nufi sashinta ta kwanta.

‘ Da yamma liqis Rukayya ta fIto falon ta ida

shararta ta dazu, sannan Ia nufi kicin ta dora

Indomic saboda yunwar da ta soma ji

sama-sama ta rinka jiyo sallama. Ta dan

tadan

sauarara kadan, sallama ce kuma muryar mace.

Rukayya ta ajiye wukar da take yanka albasa ta

fito tana amsa sallamar. . “Lah Aunty. Maimuna,

sunnu da zuwa”. . ’ Ta nufeta da murmushi a

fuskarta, “Don Allah zauna ga kujera, bisimillah”. ‘

Haj. Maimuna ta zauna itama da fara’a ‘ a

fuskarta ta ce. ‘ “Rukayya kenan, ya zaman

kadaici‘. ’” Murmushi kawai tayi, Haj. Maimuna ta

ce. “A’a ban gane ba, ‘sai. dariya ba

magana?’Rukayya ta bar murmusawa kafin tace.

‘ “Alhamdulillahi”. _ Aunty Maimuna tace, “Haka

nake so

ki saki jikinki duk maganar da zanyi ki maido

mani amsa, “To, bari na kawo miki ruwa

’ ‘Tace “A’a sha zaman ki. na hutasshe ki ‘Yar

raihin wayo, kika’ce min kanwar Abubakar: ceke,

ashe Shara min ita ku kai jiya. Ogana (mijina)

yake-fada min cewa ke

matarsa ce.ke Nayi miki murna Rukayya sosai,

kin dace da miji kamar yanda shima nake masa

murnar samun qaruwar iyali, Sai dai ~ kiyi hakuri

mijinane yace nazo na danyi miki wasu ‘yan

nasihohi wadanda zasu amfane mu gaba daya.

Ina fata ba zaki damu ba shiga rayuwar ki da

zanyi” _ , Kai tsaye Rukayya ta ce, “A’a ba komi

Aunty”. Auty Mai‘muna ta ce “Okay, Rukayya

kinyi makaranta kuwa‘? ‘ Ta danyi Jim kafin ta

ce. “eh nayi (primary) a kauye

Haj. Maimuna ta ce “Daga nan baki Kara ba?” “ ‘

Tace Eh, Yaya Abbakar ya so kaini

makarantar gaba kakata ta hana

Tace-“Wayy0, Allah :sarki.. aidata sani da ta‘

barki kinci gaba don karatu yana da matukar

muhimmanci ga rayuwar ‘ya’ya mata ’ ‘

Yanzu Rukayya idan nace zan saki a makarantar

mata kina so?”

Tayi shiru tana wani dan nazari can anty

Maimuna ta datse mata tunanin ta hanyar ‘fadar.

. ‘ “Rukayya, shi ilmi; da kike ganinsa yana da

matuqar muhimmanci, yin ilimin nan zai

.taimakeki ya taimaki ‘ya’yan da zaki haifa.‘ Ta

hanyar ilimin zaki koyi hanyoyin da ya kamata ki’

tarbiyyantar dasu, ta hanyar ilimin ne Zaki koyi

yanda ya kamata ki kula da kanki da kuma

maigidanki

Makaranta ce wadda kungiyar kare haqqin‘ mata

ta _budé don horar da irinku da ‘ karatun shekara

guda, sai a baki kwalinki idan har kin maida

hankali sai mu tura; babbar makarantar sakandire

ta yan mata

ya kika gani?

Rukayya ta ce, “T0 dUk yanda yayan

ya ce” ‘ Haj Maimuna ta ce, “Ture batun yaya

mai sauki ne idan kekin amince, yanzu zan

cikc miki (form), ni na riga na gama magana da

shi, zai biya duk abinda aka kashe” Tace”To shi

kenan, ba matsala” .

’ » Aunty Maimuna tai dariyar jin dadi, sannan ta

bude jakarta ta Ciro (form) guda da biro ta cike

mata, ta‘dauketa hoto da wayarta sannan tamike

tana fadar.

“To ni zan tafi, insha Allahu zuwa gobe zan _ . ‘

-‘ dawo”. Rukayya ta ce, “To Allah Ya kaimu”.

‘ Har wajen harabar gidan ta rakata sannan ta

dawo, ta nufi kicin din ta Cigaba da girkinta, a

zuciyarta dadi ne fal zata koma

makaranta, k0 banza ta rage zaman kadaicin da

take a gidan. ‘

Washegari bayan sallar magarina Rukayya na

zaune a falo tana kallo

haji

Malmuna ta shigo da sallama dadi ya kama

Rukayya ta zabura cikin doki.

“Sannu da zuwa Aunty, wallahi yanzu nake

tunanin ki cikin raina”.

Aunty Maimuna tai dariya, “Kuma ba zaki lya

shiga ba?”

Tai dariya saboda yanda ta watsa mats harara,

ta ce

“Ba haka bane Aunty“. ‘

“To yaya ne?” Ta ce “Dama ina da niyyar shiga”.

Aunty Maimuna ta zauna tana fadar, “To ai gani

ni na‘shigo”. ‘

Rukayya ta zauna ‘tana gaisheta, “Ina wuni

Aunty” ‘

“Lafiya lau Rukayya kin wuni lafiya‘. ’”

Ta ce “Lafiya qalau”.

Aunty Maimuna tace“A’a ko dai’ k0

dai k0 dai?” Rukayya ta sa dariya tana fadar

ko dai me Aunty ?”

Ta ce KO dai tunanin mijin na nan na

dawainiya dake?” Rukayya ta ce “Kai haba, Allah

Ya sauwake

” “Da me?” . Aunty Maimuna ta fada cikin nuna

alamun firgici Rukayya ta ce, “Yo Aunty sai kawai

na

kama tunanin namiji don Allah kema ba zaki

min fada ba?” ‘ Aunty Maimuna ta ce “Ba zan

miki ba

Rukayya, .ai abu ne mai kyau ki nunawa mijinki

kin damu dashi, ‘ki nuna masa ke baki ’ ma da

lafiya tunda ya tafi ya barki kewarsa ta hana ki

sukuni”. ‘ . ’ Rukayva ta fasa qara, “La’ilaha

illallahu! Kai don Allah Aunty?” ‘ Haj. Maimuna ta

Bata fuska kafin ta ce.

“Ke dubcni nan Rukayya, kinga alamun wasa a

idanuwana?”

Ta girgiza kai alamar a’a.~Sannan Haj. Maimuna

ta ci gaba da fadar.

lol naku har kullum A,I,S ke cewa asha karatu lafiya

CHAPTER18

bayansa jikin (wardrop) din dake like a‘ bango, idanuwansa a rufe. Surarta ce kawai ke faman kai komo a idanuwansa, shi kanshi bai san tsawon loakcin‘ da ya dauka ba, sai

dai yaji muryar Suhailat na fadar. “Da kyau, dama nasan wannan ranar

, tananan zuwa Abbakar, nasan k0 ba dadade k0 ba

jima sai kazo kana son yarinyar nan” Abubakar ya bude idanuwansa ya kafe

su akanta yana maimaita.

“So… So fa kika ce Suhailat?”

Ta daga murya, “So na ce Abbakar! Ka ‘ soma son Rukayya, karya na fada?” * Shiru ya danyi, shin k0 abinda yake ji game da yarinyar nan shi ne son? Kai gaskiya a’a ba‘ so bane; To meye? Ya tambayi kansa kai ‘ tsaye tambayar dabata da amsa.

D0n haka ya girgiza kansa yana fadar.

“Ki yarda dani Suhailat, abinda yakr cikin zuciyata ba so bane. ‘

Cikin daga murya ta’ce, “Rufe min baki munafiki, idan ba so bane mene ‘ne? Sha’ awa ?

ce ? tunda’ .ka kalleta a tsirara Allah dau yai wadan irin wannan zuciyar taka Abubakar, wadda ba

zata iya kare kanta daga fadawa sharrin shaidan ba.

Kuma idan ma ka soma sonta Abubakar . ka sani wallahi’tallahi ba zan taBa yarda wata mace a matsayin kishiya ba ballantana

wannan sokuwar yarinyar, ballagaza, jaka, akuya, ‘yar matsiyata. Wallahi ba zan yi kishi

da ita ba, sai dai kwarya tabi kwarya, ‘don haka ina gargadinka da kada ka ballo wutar da zai kasheka Abubakar ya ce, “Ki dawo hayyacinki Suhailat, kada ki yanke hukuncin da zuciyar ki ba zata iya dauka ba, alhalin kin san zuciyata bata tanadi dakarun da zasu kareta daga kamuwa da son wata ba .. idan kuma kin aikata abinda kika ‘ so don ki salwantar da rayuwarta saboda kina tunanin bata da gata to ki sani ni nine gatanta

daga yau kuma daga yanxu inason ki sani abinda nakeji a zuciyata gameda ita baso bane

bane kuma ba Sha’awa bace, sai dai wani abu mai kama da sha,awar”. Suhailat ta fasa wata uwar Kara . “Wayyo na shiga uku! Inna lillahi Wa’inna ilaihi raji un Ta zube Kasa ta fashe da wani irin kuka

mai Kairfi.

Abubakar ya duKa gabanta, “Kiyi a hankali, kinga dare ne, idan da kuma za ki dauki shawara da kin adana haWayen tun yanzu, don wata qila akwai ranar zubarsu”. Ya yunkura ya mike.

Suhailat tai saurin riqo hannunsa, “Kar kai min haka Abbakar, don Allah don Annabi kada ka zamo sanadiyyar rugujewar farin,cikin rayuwata, ,don Allah Abbakar don Allah, wallahi ba zan‘iya kallon ka ‘da wata macc a duniya ba idan kace kai. min kishiya

Abbakar mutUWa zanyi, wallahi mutuwa

zanyi. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Yau‘ ‘na shiga uku”. ‘

ta hada kanta da hannunsa ta cigaba da rera kukanta mai ban tausayi, Abubakar ya ja wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce.

“Me yasa kike dauka cewa isarki da tinkahon ki da zamantowar ki wata zai iya samar miki abinda kike so da arziqi k0 da

tsiya? Me yasa kika dauka kudi zai iya samar miki duk abinda kike so a duniya? Me yasa kike zaton don ina qarkashin mahaifinki

zan iya kwantawa ki takani yanda ranki yakeso?

Kinyi kuskure Suhailat, zuciyar ‘ Abubakar tamkar dutse take, dutscn ma na ‘ niqa wanda k0 nakiya ba zata iya masa ba. ‘

‘Suhailat ina sonki son da ba zan iya misalta miki irinshi ba, a duniya babu abinda ‘zaki‘nema a wurina ki rasa, sai dai in in raina ne‘shima don ban iya cire shi daga jikina in bayar.ne Amma ke sai kike ganin kamar wata isarki ko da arziki yasa nake miki abninda nake yi.~ Kinyi kuskure Suhailat, dOn.

har yau ba ai dukiyar da zata sa in yima mace bauta ba, kuma”

“Kayi haquri don Allah Dear, Wallahi ba zan Kara ba. Ni dai don Allah kai min alkawarin ba zakai min kishiya ba, wallahi zuciyata ba zata iya daukar wannan tashin hahkalin ba”.Suhailat ta katse shi. .

, , Abubakar ya danyi. jim yana jinjina girman lamarin,” Suhailat ta‘mike ta kwanta a jikinsa’, Cikin muryar kuka ta Ce. ‘

“Ba don halina ba, don Allah Abbakar, ni kuma nai maka alKawarin zan zame maka . daya tamkar da dudu. Nai maka alkawarin babu abinda zaka nrma ka rasa na daga zamantakewar . aure da kyautatawa da soyayyah Ta lalubo hannunsa ta rike tana matsawa.

“Kai nake saurare my Dcar”. Abubakar ya ja Wata ajiyar zuCiya mai

qarfi kain yace.”Nai miki alkawari Suhailat”

ta qara makalkale shi

tana sumbatarshi ta k0 ina. “Na gode my Dear, Allah Ya saka da

alkhairi”. Murmushi kawui yayi saboda nauyin

jinjina girman alkawari da zuciyarshi tayi.

Misalin qarfe tara na safe Rukayya da kuku suka kammala abin karyawa, sannan ita ’ ta dawo falon tana gyarawa, bayan ta gama gyaran ‘kicin din, Abubakar’ da Suhailat suka fito‘daga falo‘ suna ‘janye da akwatina, Rukayya ta sadda kanta tare da gaishe su cikin girmamawa. Abubakar ne . dai ya amsa banda

Suhailat da ta juye idonsa ta watsa mata harara

« Abubakar yaCe, ”Yauwa Rukayya, dama sallama zamuyi za muyi tafiya sai idan mun dawo. na sallami kuku saboda

gidan yanzu ke kadai ce akwai kayan abinci sai ki rinqa dafa duk abinda kike so Sai har

Allah Yai mana dawowa”.

Ya zaro kudi masu yawa cikin aljihu ya ajiye mata

“T0 sai Allah Yai mana dawowa”.

Muryar Rukayya na rawa tace “Allah Ya kiyaye

Ya amsa da, “amin”.

Sannan suka fice

. RuKayya ta raka Su da idanuwanta ‘wadanda suka ciko da hawaye, haka kawai takejin tana kewar su,‘ to me kenan?

Ta ajiye tsintsiyar hannunta ta zauna saman hannun kujera tana kallon Rofar da suka fita ‘sharar da hata idar ba kenan ta lallaba ta miqeta nufi sashinta ta kwanta.

‘ Da yamma liqis Rukayya ta fIto falon ta ida shararta ta dazu, sannan Ia nufi kicin ta dora Indomic saboda yunwar da ta soma ji

sama-sama ta rinka jiyo sallama. Ta dan

tadan

sauarara kadan, sallama ce kuma muryar mace.

Rukayya ta ajiye wukar da take yanka albasa ta fito tana amsa sallamar. . “Lah Aunty. Maimuna, sunnu da zuwa”. . ’ Ta nufeta da murmushi a fuskarta, “Don Allah zauna ga kujera, bisimillah”. ‘ Haj. Maimuna ta zauna itama da fara’a ‘ a fuskarta ta ce. ‘ “Rukayya kenan, ya zaman kadaici‘. ’” Murmushi kawai tayi, Haj. Maimuna ta

ce. “A’a ban gane ba, ‘sai. dariya ba magana?’Rukayya ta bar murmusawa kafin tace. ‘ “Alhamdulillahi”. _ Aunty Maimuna tace, “Haka nake so

ki saki jikinki duk maganar da zanyi ki maido

mani amsa, “To, bari na kawo miki ruwa

’ ‘Tace “A’a sha zaman ki. na hutasshe ki ‘Yar raihin wayo, kika’ce min kanwar Abubakar: ceke, ashe Shara min ita ku kai jiya. Ogana (mijina) yake-fada min cewa ke

matarsa ce.ke Nayi miki murna Rukayya sosai,

kin dace da miji kamar yanda shima nake masa murnar samun qaruwar iyali, Sai dai ~ kiyi hakuri mijinane yace nazo na danyi miki wasu ‘yan nasihohi wadanda zasu amfane mu gaba daya. Ina fata ba zaki damu ba shiga rayuwar ki da zanyi” _ , Kai tsaye Rukayya ta ce, “A’a ba komi Aunty”. Auty Mai‘muna ta ce “Okay, Rukayya kinyi makaranta kuwa‘? ‘ Ta danyi Jim kafin ta ce. “eh nayi (primary) a kauye

Haj. Maimuna ta ce “Daga nan baki Kara ba?” “ ‘

Tace Eh, Yaya Abbakar ya so kaini

makarantar gaba kakata ta hana

Tace-“Wayy0, Allah :sarki.. aidata sani da ta‘ barki kinci gaba don karatu yana da matukar muhimmanci ga rayuwar ‘ya’ya mata ’ ‘

Yanzu Rukayya idan nace zan saki a makarantar mata kina so?”

Tayi shiru tana wani dan nazari can anty

Maimuna ta datse mata tunanin ta hanyar ‘fadar. . ‘ “Rukayya, shi ilmi; da kike ganinsa yana da matuqar muhimmanci, yin ilimin nan zai .taimakeki ya taimaki ‘ya’yan da zaki haifa.‘ Ta hanyar ilimin zaki koyi hanyoyin da ya kamata ki’ tarbiyyantar dasu, ta hanyar ilimin ne Zaki koyi yanda ya kamata ki kula da kanki da kuma maigidanki

Makaranta ce wadda kungiyar kare haqqin‘ mata ta _budé don horar da irinku da ‘ karatun shekara guda, sai a baki kwalinki idan har kin maida hankali sai mu tura; babbar makarantar sakandire ta yan mata

ya kika gani?

Rukayya ta ce, “T0 dUk yanda yayan

ya ce” ‘ Haj Maimuna ta ce, “Ture batun yaya

mai sauki ne idan kekin amince, yanzu zan

cikc miki (form), ni na riga na gama magana da shi, zai biya duk abinda aka kashe” Tace”To shi kenan, ba matsala” .

’ » Aunty Maimuna tai dariyar jin dadi, sannan ta bude jakarta ta Ciro (form) guda da biro ta cike mata, ta‘dauketa hoto da wayarta sannan tamike tana fadar.

“To ni zan tafi, insha Allahu zuwa gobe zan _ . ‘ -‘ dawo”. Rukayya ta ce, “To Allah Ya kaimu”.

‘ Har wajen harabar gidan ta rakata sannan ta dawo, ta nufi kicin din ta Cigaba da girkinta, a zuciyarta dadi ne fal zata koma

makaranta, k0 banza ta rage zaman kadaicin da take a gidan. ‘

Washegari bayan sallar magarina Rukayya na zaune a falo tana kallo

haji

Malmuna ta shigo da sallama dadi ya kama Rukayya ta zabura cikin doki.

“Sannu da zuwa Aunty, wallahi yanzu nake tunanin ki cikin raina”.

Aunty Maimuna tai dariya, “Kuma ba zaki lya shiga ba?”

Tai dariya saboda yanda ta watsa mats harara, ta ce

“Ba haka bane Aunty“. ‘

“To yaya ne?” Ta ce “Dama ina da niyyar shiga”.

Aunty Maimuna ta zauna tana fadar, “To ai gani ni na‘shigo”. ‘

Rukayya ta zauna ‘tana gaisheta, “Ina wuni Aunty” ‘

“Lafiya lau Rukayya kin wuni lafiya‘. ’”

Ta ce “Lafiya qalau”.

Aunty Maimuna tace“A’a ko dai’ k0

dai k0 dai?” Rukayya ta sa dariya tana fadar

ko dai me Aunty ?”

Ta ce KO dai tunanin mijin na nan na

dawainiya dake?” Rukayya ta ce “Kai haba, Allah Ya sauwake

” “Da me?” . Aunty Maimuna ta fada cikin nuna

alamun firgici Rukayya ta ce, “Yo Aunty sai kawai na

kama tunanin namiji don Allah kema ba zaki

min fada ba?” ‘ Aunty Maimuna ta ce “Ba zan miki ba

Rukayya, .ai abu ne mai kyau ki nunawa mijinki kin damu dashi, ‘ki nuna masa ke baki ’ ma da lafiya tunda ya tafi ya barki kewarsa ta hana ki sukuni”. ‘ . ’ Rukayva ta fasa qara, “La’ilaha illallahu! Kai don Allah Aunty?” ‘ Haj. Maimuna ta Bata fuska kafin ta ce.

“Ke dubcni nan Rukayya, kinga alamun wasa a idanuwana?”

Ta girgiza kai alamar a’a.~Sannan Haj. Maimuna ta ci gaba da fadar.

CHAPTER19

To ba wasa nake miki ba, ya kamata ki fidda kanki daga cikin duhun jahilci, ki sani tuni Annabi ya faku. ‘

Kin sani kin shigo cikin sahun manyan mata, wadanda suka dauki aure bautar Ubangiji, don haka yaki ne mai girma ya tunkaro ki ba wai dan Karami ba. D0n haka sai ki tanadi manyan makamai don tserar da

rayuwar ki”. ‘ ‘

Aunty Maimuna ta janyo jikanta ta zuge

‘ ta ciro mata wasu litattafai da abin rubutu tare

da qaton hijab mai ruwan toka har Kasa da _ nikaf ta miqa mata ‘ ’ “Amshi, ga wannan na gama miki’ k0mai gobe idan Allah Ya kaimu qarfe goma na Safe zaki shirya direba zai zo ya danke ki ya kaiki makaranta.idan da abinda ya shige miki. ‘_ duhu kizo ki tambayeni in kOya miki. . ‘ Kowacce ra‘na da abinda za’a koya muku ranar Litinin za’a koya muku Turanci, ” ran’ar Talata Hausa da Lissafi, ranar Laraba

‘ za a koya hausa da lissafi ranar, Alhamis,

za su koya muku yanda ake gyaran muhalli ranar Juma’a kuwa za’a koya muku yanda ake kwalliya, ranar Asabar kuma girki za su koya muku, Lahadi kuma su koya muku karatun lslamiyya da yanda ake kula da miji da yaran gida”.

Rukayya tace to Aunty Allah Ya kaimu”.

Aunty Maimuna ta dan tsareta da idanuwa kafin ‘ta ce

“Wai Rukayya ba zaki kwance Wannan dankararren kitson dake‘ kanki ba? Dubi akaifanki yanda sukai baqiqiRin a ciki da dauda, kin san fa na miki magana tun ‘

‘ rannan, kar ki bari gobe inzo in same ki da su kinji na fada miki”.

Yanda ta daure fuska ne tamkar ba ita bace sarkin zolaya da ban dariya ba yasa Rukayya amsawa a raunane

Aunty Maimuna ta ciro rcza daga

jakarta ta mika mata.

“Amshi, ga rcza nan. Ke yanzu wani namijin k0 me zaki dafa ki bashi ai ba zai cishi ba. Dubi akaifunki, dube su don Allah“.

Ta ja .tsaki ta mike ta suri jakarta tana fadar. ‘

“Idan na koma Zan turo miki mai aiki ta kawo miki kayan da na bawa teta ta gyara miki, ki huta da yawo da rigar maza k0 duk Kaunar ce?” . ‘

Ta fada sigar zolaya.

Rukayya tai _murmushi ta girgiza kai * alamar a’a, Anty! Maimuna tace

“A’a? Ba Kaunar bane Murmushi RuKayya tai bata ba ta amsa ‘

ba Haj. Maimuna ta ce ‘ “A’ a k0 da naji. ni dai nasan qaunar nan

, dai akwaita”. Dariya kawai tayi saboda’ ita halin

matar na bata mamaki, shin. ita kuma k0 wace irin mace cc? Rayuwarta na bata sha’awa.

w . w. . m.

Ganin ta sake yasa Aunty Maimuna ta tafi, don dama ta dan razanata ne don kar taqi yin abinda tasa ta

Ai k0 tana fita Rukayya ta bude rczar ta yanke akaifunanta tas, ta kankare su sukai Kalqal Sannan ta sa hannu ta kwance kai ta tafi (toilet) ta wanke shi da sabulu sosai, ta barshi ya bushe sannan ta shafe shi da mai, ta sharce sosai, sannan ta daure shi. Duk da gashin nata bai wani cika tsawo ba, to amma yana da sulBi sosai, gashi bakikkirin kamar wadda ta shafa masa baqin lalle. ‘

Tana idar da . sallar ish‘a‘i ‘mai aikin ‘Aunty Maimuna ta kawo mata kaya cikin wata qaramar jaka, Rukayya ta amsa tana godiya ta zauna tsakar daki ta bubbude

Kaya ne masu kyali, don kai da baka ‘sani ba sai ka, rantsc da Allah daga wurin dinki aka karBo su, sum kai kala ‘goma. Dadi ya gama Rukayya, itama ta samu kayan

canjawa, don haka cikin farin. ciki ta kwanta.

Washe gari ko garina wayewa ta watso ruwa ta zauna gaban madubi ta murza‘ mai da hoda, sannan ta dauko daya daga cikin kayan da anty maimuna ta kawo mata ta saka.wata Material mai fari da adon ja, ya hau jikinta ta dauki dankwalinsa , ta saka hijabinta, ta daura niqab din, ta sa takalmi sannan ta. dauki litattafanta.

‘ K0 karyawa bata tsaya yiba ta dauki hanya, ta fito. Maigadi ya rufe gidan, ta nufi gidan Aunty Maimuna. ,

‘ A can ta tsareta sai da tayi kalaci sannan dircba ya dauketa,_ har cikin makarantar ya. kaita kamar yanda Aunty Maimuna ta sanya shi, ya nemi Haj Rahma ya hadata da Rukayya sannan ya tafi da

niyyar dasun tashi zai dawo ya daukcta.

Wasa-wasa haka‘ Rukayya ta .soma

’ karatunta, sai ‘gashi har ta fara iya karatu da‘

rubutu, Turanci ma dan wanda bai‘taka kara ya karya,_ba tana dan damalmalawa.

Aunty Maimuna ma ta dage tana koya mata dan abinda bata gane ba.

Wata uku da tafiyar Abubakar amma Rukayya har ta soma canzawa sai kace ba itaba, duk wannan duhun kan da Rauyancin nata ta rage shi, an zama’ yan makaranta

Wata rana ta dawo daga makaranta da maraice ta sauka gidan Aunty Maimuna ta baje tana kallon kayan da aka kawo mata talla; lesissikane masu kyau da materials, sai _ lndian gaunt ‘ ‘kala-kala da jakunkuna da ‘ takalma na mata masu kudi. ~

. Aunty Maimuna ta dauki jaka da takalmi kala biyar, sannan ta dauki less biyu, materals biyu,sai indian gaunt guda da wasu riga da Siket

rukayya ta zauna tana yaba kyan kayan, Anty Maimuna tace “ke bazaki dauka bane? Bashi ne biya

uku nasan Abubakar ba zai qi biya miki ba” . . ‘

Rukayya ta cc, “Ah waceni da daura zani uwar miji na yawo xindir‘? Aunty bafa wani dasawa mukeda Yaya Abbakar din ba hasalima ya tsaneni don ko maganar kirki bamayi

. . ‘ Haj. Maimuna ta saki baki kafin ta ce”Yanzu dama zaman doya da’manja kuke kenan? K0 da yake nasan dama hakan zata faru, amma ki share kawai, kina’son irin nawa sun miki?” ‘ Rukayya ta ce, “Sun min mana”. ~ ‘Ta ce”T0 Kyale shi akwai wata’ mai kawo mana atamfofi zan mata magana ta kawo miki masu kyau k0 kala goma ne ai mishi bill dolensa zai biya” rukayyah tace wallahi baki san haiinsa bane .Aunty Maimuna ta’ce, “Kyaleni dashi, ‘ .da Oga zan hada shi, har kudin dinkin sai ya hiya, don shago za ‘a kai dinkin”. Dadi ya kama Rukayya ta miqe tana

murna.

Anty Maimuna tace “Sai daifa matsala “daya Rukayya, dole da sai anbi dare an k0rbo baqin aljani, don wannan baqin fuskar taki . yayi yawa”. ‘ “ Rukayya ta ce “Bakin aijani kuma Aunty?” ‘ tace Eh mana ai wannan baqin fuskar taki daketa sheqi ai shi ne baqin aljanin dake damun da yawan ‘yan matan zamanin nan da irin qananun kurajen nan na fuskar ki, idan kin shirya zan ‘ baki magani”. . Rukayya ta dawo ta zauna da zumudinta tana fadar. ‘

“Na shirya mana Aunty’, aikin me nake a gidan?”

Aunty Maimuna tace ‘ai ni ban. shirya ba, baki ji an soma kiran sallah ba? Ki bari dai gobo: ki shigo da wuri ni kuma zan karantar dake’darussan maza ‘ wanda k0 shaidan bai’san dasuba”. ‘ _ Cikin zumudi Ruqayya ta ce”to shi

kenan Aunty qarfe tara zanzo

Aubty Maimuna ta ce “A’a, inama laifin Sha daya sannan na sallami mijina?“ Rukayya tace, “To shi kenan, Allah Ya

kaimu”. _

Ta amsa da, “Amin Sistcr

Rukayya ta mike ta fice daga gidan ‘ tana kokarin shiga gidan nata taga mai keke napcp Shima ya’na Kokarin fakawa a kofar gidan nata, don haka ta dan tsaya taga waye?

kakace ta fito tana kokarin bawa mai keken kudinsa, Rukayya ta fasa qarar murna ta ruga ta rungume Kaka tana ihun murna

‘ “Muhammadu dan Abdullahi! Sakammrni ja‘irar nan kar ki karya ni’kinji”.

Rukayya ta saketa tana dariya, ta ce. “Wayyo Kaka ashe zakizo, baki manta dani ba?”‘

Kaka ta ce, “Jika kenan, ina ni ina mantawa dake? Ai kina cikin raina, dake nake kwana dake nake tashi”.

Rukayya. tace, ,”Wayyo, nima kina cikin raina Kaka”. ‘

Ta dubi mai keke napep din ‘Malam nawa ne kudin ka?”

“Dari . ne Rukayya ta zaro dari cikin jakar makarantarta ta mika mashi, sannan ta kama hannun Kaka

suka nufi cikin gidan ‘ A falonta ta sauketa cikin doki tace

“zauna nan kaka, me zan dafa miki?”

Kaka ta ce, “Karki ‘sakc ki wahalar da kanki Jika, a qoshe nake. Zuwa nai dama in ganki, kuma na ganki hankalina ya kwanta”. Rukayya ta ce “Ai k0 Kaka dole ne in dora , girki yanzun nan, dama muna da sauran. ,naman kaza da dankali, bari inyi sauri in hada -, miki (French soup) da tuwon semovita minti kadan”

‘ Kaka ta ce, “‘Yar nan yanZu nan birni har wani tuwon sama ake? Kai indai mutum yana duniya ‘ bai gama kallo ba”, Rukayya tasa dariya kafin tace, “Ba tuWon sama nace ba Kaka, tuwon scmonvita fa na

Ce.

Kaka tace, “To shi kuma wani abin ne

haka?” Rukayya tace, “Tuwo ne dai Kaka, amma da gari dan kanti ake yinsa, bari in miki kici kiji”. » Kaka ta ce, “A’a hanzana ki min ‘yar nan tunda naji kin ambaci nama”. Rukayya ta sa dariya ta mike ta nufi ‘kicin, mintina Kalilan ta gama .hada mata tuwon da miyar sannan ta gasa mata ‘yar Sauran hantar da ta rage, ta hada mata ita da kayan lambu, ta dauki komi ta kai mata, ta hado mata robar ruwa da fresh milk guda, da lermon . Duk Aunty Maimuna ce ta aiko mata dasu jiya. Kaka ta xauna suna Ci suna hirar yaushr gamo, kaka Sai zuba santi take suna zabgar .dariya. Sai da suka gama cin abincin sukai

sallah sannan suka dasa wata hirar, Kaka kira take. ‘ ‘

“Jika ashe dama za ki qiba? Ai ni ban taBa tunanin za ki qiba Ba. Na rantse da Allah .

kina jin dadinki, yanzu sai yaushe masu gidan zasu dawo? Don yaje min sallama, Ya maqare min kicin da uwayen kayan abinci sai kace ya ganni da yunwa”. * Rukayya ta ce “Kuma kina iya yin ‘ girkin Kaka?” , ta ce “Ni fa Lami ya dauko min ‘yar gidan Malam Hadi, ita ke min girkin, kin san ta dawo gida zawarci”.’ Rukayya ta ce “Allah Sarki baiwar Allah; har yanzu babansu yana nan kenan?” ‘ Kaka ta ce “Yana nan”. ‘ Kaka ta mike ta Belle zani cikin dan tOfintA lalita ta ciro wasu kulle-kulle ta miqawa Rukayya tana fadar. * “KarBi wannan Jika, da zan taho na ‘ biya ta wurin Malam Zakiru na karBo miki. ‘ Wannan hayaki ne na sammu, wannan kuma aniya makomiya ce da karya tambaya da ruwan bakin wuta ake shansa. Wannan kuma

maganin mu ne na tsaffi na biya na tsinko

hehehe su kaka manya

jama,a suwaye sukai missing din kaka to yau ga kaka har gida lol

CHAPTER20

A SHA KARATU lfy

miki, ki shanya ya bushe ki daka ya zama gari, ki tankade, ki dinga sha da madara ake sha”. RuKayya tayi murmushi, “Na gode ’Kwarai Kaka”. . i ‘

Tace, .”Ba komi Jika, yiwa kaine”.

Hira suka sha sosai, basu suka iya bacci ba sai da dare ya tsala sosai sannan bacci ya dauke su

‘ ‘ Kaka ta ga tattali wurin RuKayya, hatta ‘anty Maimuna da taji Kaka tazo kullum sai ta aiko’mata da abinci kala-kala. Sai da Kaka, ‘ta kwana uku sannan ta ce zata koma . ~RuKayya tai juyin duniyar nan ta Kara kwana taKi wai idan duniya ta samu labari sai a ‘ zageta. . ‘

RuKayya ta bata’kudin da Abubakar ya bata da zai tafi dubu goma ceta bawa’ Kaka, da Kyar ta samu ta‘karBi rabi, suma sai ‘da ta dage da gaske Aunty Maimuna ma tsaraba ta hadawa Kaka sosai a gaskiiya matar tana da mutunci ba wai dan kadan ba;

. Karfe hudu ‘na yamma Rukayya ta dawo daga rakiyar Kaka, kai tsaye gidan Aunty Maimuna ta Sauka, ta ,samu itama ta dawo daga unguwa.

Rukayya ta zauna tana fadar, “Wannan

kayan kuma fa aunty? Unguwa kika je?” Anty Maimuna tai dariya, kafin ta ce. “Yara najewa visiting (ziyara)”. RuKayya ta ce,”Wai yara kuma Aunty?” ‘ Sai da ta sake yin dariya kafin ta nuna mata qaton hoton dake falon, ta ce.

‘ “Gasu, Ammar da Saudiyya, Hassana da Husaina”. ‘

Rukayya tace, Ban gane ba Aunty wai dama wadannan manyan ‘ya’ yan naki ne?” Tai dariya, “Nawa ne Rukayya, Ammar ne babba ya gama (secondary school), yana qasar Saudi Arabia zai hada (degree) dinSa,

sai Saudiyya da Hassana da Husaina su kuma

suna «(secondary school). Saudiyya na aji ‘ hudu .Hassana da Husaina aji uku, su ne najewa visiting”. .

Rukayya ta ce “Ikon Allah, amma wallahi babu wanda zai kalle ki ya ce kin ajiyevkamar Hassana, ni na dauka ma: baki taBa haihuwa ba”

Haj. Maimuna ta sa dariya tana fadar, “Kai Rukayya, banda sharri”.

Ta ce, “Wallahi Aunty da gaske”. Ta ce “To na yarda. Yau dai ya kamata mu fara , darasinmu don nasan gobe za ki koma makaranta k0?” _ Rukayya ta ce “‘Wallahi kuwa Aunty, , abinda ke cikin zuciyata kenan”. Aunty Maimuna tai murmushi kafin ta cc. ‘ ‘ ‘ ‘Uhm,!‘ Mata, kenan, ku dai haka Allah Ya yiku, kuna nan kun kasa kunne, Kiris ku ‘ke jira ku dauke kudai ku gwara kawunan

mazaje‘ Allah Ya shirye ku mata”:

_ Rukayya ta sa dariya tana fadar, “Kai Allah Ya bar mana ke Aunty-“. Itama dariyar tayi, kafin ta ce

“Amin ‘yar nan. Duk abinda zan fada miki Rukayya ki daukc shi ki ajiye shi kusa da. zuciyar ki, ki aiki dashi don shi ne zai taimake ki tun daga. duniya‘ har lahira.

Rukayya, da farko ya. kamata’ na fara da ‘ abinda zai gyara miki fuskar taki ta. zama (very clear) tayi (smaoth)ne D0n haka da, farko ki nemi: ‘

lol frnds zamu tsallake nan don ba tallan magani mukeba so lets go A,I,S na tare daku

_ Rukayya idan na ce zan shiga ‘zayyano miki abubuwan nan saimu wuni ba a gama ba, ._d0n haka yanzu abu guda zan tunasar maki Rukayya, saboda nasan duk abinda zan fada miki makaranta sun fada muku, sai dai wanda suké jin nauyi da kunya, don haka ni ma nan zan sanar miki.

Rukayya a rayuwar auratayya ana son ki Zamo tantiriyar’ yar iska amma a wurin mijinki

kadai Sai kin Cire kunya idan har kina. son mallakar mijinki kin gane ai‘?” . .

Murmushi kawai tayi bata tanka Aunty Ma’imuna ta cigaba. tace

“Uhm! Ai dama nasan ba ganewa zakiyi ba Rukayya, sai nai miki practically

Ta mike tana gwada mallta yanda zata yi, daidai da kwanciyar auren sai da ta nuna mata yanda yakamata tayi,tun Rukayya na jin kunyar Wasu abubuwan idan ta fada har ta gaji ta‘daina, saboda babu alamar wasa a fuskar ‘Aunty Maimuna. Idan ma tai‘ abin dariya ita bata yi,-idan Rukayya na daria sai ta kara hade fuska tana fadar. ‘ Meye kuma na dari Meye abin dariya anan?” -Don haka dole Rukayya ta nutsu ta

rinqa gimtse duk wata daria’har aka gama,

sannan Aunty Maimuna ta ce. To aje ai sallah, gobe sai adasa”;

_ , Haka Rukayya ta tashi cike da nauyi a jikinta.

‘Wasa wasa kullum sai ,sun zauna abin ya zame . masu kamar wajibi data tashi makaranta gidan~ zata sauka. Kuma da alamun karatunna anty yana shigar Rukayyar don da , kanta‘ ta’ cewa Aunty ‘ ‘ Maimuna taiWa abubakar magana ya turo da. kudi a hada mata mayuka da sabulan gyaran jiki masu dan haskawa.

Aunty Maimuna tai dariya sosai kafin ta ce; ‘ . uhm”Ashe dalibar tawa tana gane karatun?” Dariya kawai Rukayya tayi don ita ba ma ‘don‘ ‘Abubakar din ba, saboda ‘yan makarantar su,‘

. don akwai wayayyune har’gasar kwalliya ake ‘

Cikin lokaci qankani Rukayya tacanza, ta zama ‘wata daban kamar ba ita ba, bakin nan ‘ nata ya disaShe ~ ta . zama wata’ (chocolate’ colour), baqinta ya’zama mai baske, irin wanda’ “ k0 farar. fata na sha‘awarsa. Gashin kannan nata sumul ya samu gyra, ya. ‘qara‘baqi da. sulBi, yana ta faman daukar ido Kurajen nan da sukai mata caba caba a fuska duk basu ‘ sun bace : babu k0 alamar tabbansu

fuskar tai gWanin kyau

Ni kaina ban san Rukayya kyakayawa . bace sai yanzu da gayu ya ratsa ta, ta. goge ta zama wata daban. Ashe k0 mummuna ya samu . gyara kyau yake? lol

-” Dama Hausawa sunce baqo yafi dan gari lalata . To ‘. kuwa na yarda,don Rukayya a yanxu kuwa‘cewa Aunty Maimuna zatai Kauce nan ban wuri don ‘kwalliya da tsafta har na banza yi take yi Don ‘haka Aunty Maimuna ta yanke shawarar bude

’ wurin (make up) da gyaran gashi {saloon}

Lokaci nata tafiya Rukayya ta kammala makarantar ta, amshi (result) dinta. ta kuma samu result mai kyau don haka Aunty Maimuna ta sama mata gurbin karatu a makarantar mata jeka dawo (Day) W,I,C

. Hankalin rukayyah a kwance karantunta kawai take kuma tana ganewa sosai don a yanxu saita rubuta letter da turanci

Bacin tafiyar Kaka ta sake dawowa, amma a wannan karon kwananta daya ta koma, shima da kyar ta yarda ta kwana.

Rukayya bata jima ,da fara zuwa W.I.C ba don k0 shekara bata hada“ ba suka zana jarabawar J.S.S.C.E. Jarrabawar‘ na filowa.ts shiga ss a lokacin Abubakar shckararsu daya da ‘ wata ‘ bakwai ‘ da ‘ tafiya. Rukayya ‘yan makaranta, qarfe biyu da mintuna mai adaidaita sahu ya sauketa a qofargidan, ta zaro Naira hamsin ta bashi,sannan ta ‘ nufi gidanta. ’

Tana shiga ta nufi (toilet) ta Watso ruwa’ ta fito ta zauna gaban madubi. Kwalliya tayi sosai, gashin kan nan tai masa ,wata kanannada sannan ta ciro wasu riga da siket ta saka, ta yafa mayafinsu ta nufi falo. Kai tsaye (dinning) ta nufa, ta zauna ta qarasa cinye sauran ‘(brcak) din safenta, sannan ta mike ta fice daga gidan

‘ gidan Aunty Maimuna ta nufa, falo ta {sameta rike da mayafi tana shirya wasu kaya

. cikin jaka, tana ganin Rukayya ta ce

“Yauwa. shi kenan dama gidanki zan

shiga“. . rukayya ta zauna tana fadar, “Allah

Yasa dai lafiya”. Aunty Maimuna tace “Babba ma ,don

-sai kin bani tukuici zan fada Rukayya tai dariya tana fadar, “Oho!

Aunty ki share kawai, idan naje (school) gobe Zan miki tsarabar katin waya”. *Ta ce, “Na nawa?” ‘

Tace ,”ina laifin na (four hundrcd) Aunty?”

Ta ce “A gaskiya ba zan iya fada ba in har katin (four hundrcd) ne

Rukayya tace ‘ “Kai Aunty, na (five humh fa?” Tace”Uhm (is okay) na yi maleji tunda .

tuxuruwa ceke ba kayan lol Uhm ‘Yarinya albishirinki?” .

Tace “Goro share kawai, gobe war haka zaki

amarce don ‘ angonki na kan hanya”. Rukayya ta yamutsa fuska,”Kai Aunty ni

wallahi. dana dauka wani abinne mai muhimmanci Allah bakici kati ba ” Anty Maimuna ta zaro id0 waje. “Wannan ba abin farin ciki bane Mijin naki zai dawo daga tafiyar daya share . , fiye da shekara. da rabi? To sai ki fada meye abin murna idan har wannan ba, abin murna bane?” Rukayya ta koma ta jingina, jikin kujera tana

fadar. ‘ “Aunty Maimuna kenan, ke kanki kinfi

kowa sanin zaman da nake da Abubakar, kinfi koWa sanin bafa ’kona yakeba. Ni tafiyar su . tafi komi yi min dadi wallahi. Aunty Maimuna ta Ce “Kina maganar” wancan lokacin ne, ai’ Iokacin da kike ’~ Rukayyar ki amma yanzu Rukayyar dana sani ada ba ita ce zai dawo ya iske a yanxu ba. rukayyar yanzu ta hada duk wata haduwa da wayewar da’ yan matan birni ke taqama da ita Ina mai tabbatar miki a yanzu Abuhakar ba zai iya juya miki baya ba don ba namijin ‘ zai iya wannan jarumtar. don haka idan har kin

’ idan har kikai amfani da shawarwarin dana baki wallahi

sai kin ja wa Abubakar aji har kin masa yanga Dama. nuna masa za ki baki ma san zai dawo ba goben”. Tajanyo jakar kusa da ita ta miqa mata. “Ga wannan kayayyakin dana harhada

‘ miki‘ne,‘ akwai hadin hade haden dana miki da ‘ruwan turare, ‘ idan zaki kwanya ki yayyafa a jikinki ki kwanta _

dashi,’idan gari ya waye ki, hada ruwan dumi kiyi wanka, sannan’, ki dauki wannan. ruwan turaren‘

ki wanke jikinki dashi sai kiyi kwalliyar ki.

Akwai less yana nan na amso’miki dinki

‘wurin tela, ‘shi zaki’saka, akwai takalmi ‘da

sarka da dan kunne da abin hannu duk na less . dinne, sai ki saka. Don haka yanzu zaki tashi muje a miki (saloon) dilka, sannan a zana miki lalle

Rukaya ta amsa da “To Aunty”. Haj Maimuna ta dauki mukullin mota

‘ Suka fice, basu suka dawo gidan ba sai bayan

sallar magaruba, kai tsaye kowa’ya’ wuce gidansa. ‘ ‘

Rukayya na’idar da sallar isha’i ta shiga’ gyaran gidan, saboda Aunty Maimuna‘ ta fada mata zuwan safe za suyi, don cikin dare za su taso. ‘ Karfe . goma na safe ta gama komi

sannan, ,ta cirekayan jikinta ta shafa hadin lalle mai ruwan turare sannan ta kwanta. , Da asuba tana farkawa ta nufi (toilet) tai wanka, ta Kara wanke jikinta da ruwan turare, sannan ta fito ta shafa (lotion) mai laushi a jikinta. Ita kanta tayi mamakin hasken da fatar jikinta tayi Kwalliya tayi sosai irin wadda akewa ‘amaren yanzu, hatta gashin kanta sai da ta. ‘gyara shi, ta daurc, ta matsa mashi acUci maza

saboda babu abin. lol

_ Tana gamawa ta mike ta CirO kayanta, less ne fari sosai, an masa adon ja mai haske,. sai digo-digon bakaqin‘ duwatsun dinkin riga da siket.din Sun bala’in zaunawa a jiki’nta, tamkar a jikintra ‘aka dinka su; Ta kafa daurin kallabi kamar an nada .rawani, sannan ta Saka sarka da

dankunne da abin hannu duk jajaye sun hau fatar jikinta wadda ta sha dilka da kurkur, ta zo tai lalle kuma.

Takalminta ja masu tsini ne ta saka, ita kanta ta jima tana kallon kanta a madubi.

“So beautiful” Ta fada tana murmushi. . Ta daga kai ta dubi agogo, qarfe bakwai

da mintina, don haka ta dauki turaren’wuta ta

fita tana‘turare falon har zuwa hanyar shigowa.

Das! Das’!! Gabanta ya fadi jin tsayawar

motar da tayi a harabar gidan. _ Tai saurin nufar taga ta bude labule, su din ne. Sun Kara wani haske da sheqi, har wata

‘ ‘yar qiba sukai. Shi yana sanye cikin shigar

(suit) baka, Suhailat tana sanye da baqar lifaya.

_. tai mata irin nadin nan da lndiyawa keyi. tayi

kyau kamar wata baturiya

A take wani tsoro ya dirarwa Rukayya “da faduWar gaba mai tsanani, anya kuwa zata iya takara da wannan mai kama da aljanar

saboda kyau? .

taja numfashi mai qarfi lokacin da taga suna nufo cikin gidan

shin in koma ko in tsaya ta tambayi kanta to amman idan na karaya tun yanxu bansan irin hukuncin da anty maimuna zata dauka a kaina ba

Ta bawa kanta amsa.

Kafin ta gama tunane tunanen da take taji an murda hannun kofa alamar za‘ a shigo gabanta ya hau wata irin rugurguza, tai mutuwar tsaye a gurin. , , Ni kaina dai tSayaWa nayi da typing ’ina jiran su shigo inga yanda zata’ al kaya. Shin wace ce ba wacece ba? .

-. Cikin su kuma wace ce zata zama

.Zakaran’ gwajin dafin zuciyar Abubakar? ‘

Shin Suhaiiat din ce ko Rukayya”

wace ce zata mallaki zuciyar‘ namijin maza Abubakar? ‘

Shin yana. dAsawa da canjin da rukayyah ta samu k0 gwaleta yake?

T0 idan ma ya dasa ina matsayin alkawarin da ya daukarwa Suhailat akan ba Zai taBa yi mata kishiya ba? Shin ita Suhailat din zata ma yarda ta zauna da Rukayya k0 , kuwa? . ‘ ‘ ’ ‘ Dukkah amsoshin ku na qunshe

a ciki

RIKON KAKA BOOK3

CHAPTER21

gabanta ya hau wata irin rugurguza tamkar ta‘ fasa kirjinta ya fito mutuwar tsaye tayi daidai sanda suke shigowa. . ‘ Suna sarke da hannun juna suka shigo falon, lokaci daya idanuwansu suka sauka a kan Rukayya wadda ta hau makyar-kyatar murya wurin furta. ‘ ”Sas…san..nunku da… da zuwa”Dukkansu suka qureta da idanuwa, babu wanda yai nasarar samun amsa mata abinda ya Kara tarwatsa mata zuciya, bata san lokacin da kyarma ta kamata ba, sai. dai taji kaskon da ‘ take turaren wutar yana qokarin kufce mata daga hannu. , Ta sadda idanuwanta tana kallon tiles cike da firgici, don haka bata san wuccwar su ba, sai dai tana jin qarar takun wucewar su. Don haka‘ ta dago kanta da niyyar ta koma sashinta. karaf sukai ido hudu da Abubakar Wanda ke tafiya yana:~ Wai-wayenta. Hasken idanuwansa suka‘ soki kwayar idanuwanta tamkar kibiya, tai sauri ta dauke idanuwanta

‘da wanna _tai cikin’ falonta har tana dubsa tuntube da qafa

‘ Tana shiga falon nata ta fada saman gadonta tai rub da ciki ta makalkale filo, wani irin ‘farin ciki ne da nishadi ke shigarta wanda bata taba jiba, wai Yaya Abubakar din neya koma haka? ‘tamkar wani bakin bature gaba daya ya ida cunjawa, lailai kuwa zai zame mata abin alfahari idan har Abubakar ya dauketa matsayin mata. . _

ta lumshe idanuwanta tana fasalta’ qirar

jikinshi bata san yanda akai ba ta tsinci xuciyarta da yaba lafiyayyen kirjinshi tare da . ayyanawa lokacin da zai rungumeta a cikinshi Dariya ta kufce mata tasa tafukan

hannuwanta ta rufe fuskarta tana murmushi Ni

‘ ‘kuwa nace “Lallai abin nayi ne hmm” ta rinka juyi akan gadi tsawon lokaci ‘kafin ta zaburata mike don Samawa matafiyan abinda zasu -_ci, ta fice. Babu kowa a falon dun haka ta wuce‘ kicin din kai tsaye, tai tsaye a. kicin din tana ‘tunanin abinda zata Shiryawa mijin nata don ta

burge shi. Tun gida can ta sanshi da son alala da qosan wake.

‘ Store ta nufa tasa roba ta debo wake ta dawo ta surfa shi da kanta ta wanke shi sosai. ta fitar da dusar, sannan ta zuba a‘ (blender) ta markada shi da sauri.

Tana gamawa ta raba qullunta gida biyu, kashi na farko na kosai ne, shi ne ta jajjagawa attarugu ta zuba, ta yayyanka albasa mitsimitsi, ta zuba ta fasa kwanta guda takwas ta zuba a ciki, ta sa magi, gishiri da curry. Ta buga kullun sosai sannan ta zuba ruwan mai a kaskon suya ta ‘soya wannan qosan ta zuba a kula. ‘ Sannan ta dauko daya Kullun ta jajjaga mashi attarugu mai yawa ta zuba, ta yanka albasa’tana. mai ‘yawa ta zuba. Sannan ta koma ta dauko danyen kifinta ta tafasa shi sannan ta zare qayar ta mashi sala-sala ta zuba a cikin kullun alalan, ta dauko dafaffen kwanta guda goma ta raba kwan gida

biyu tana sakawa a cikin kullun.

Ta dauko dafaffiyar hanta ta wadda ta dafa ta yayyanka qanana ta zuba a cikin qullun, ta dauko kabejinta da ‘karas ta yayyanka ta ‘zuba a ciki. “ta’ saka maggi, gishiri, curry da thyme ta juya’ sosai sannan ta zubamanja da man gyada ta Kara juyawa, sannan ta kukkulla a fararen ledoji ta.saka a tukunya ta zuba ruwa ta dora akan Wuta:

sannan ta koma ta dauko sauran dankalin turawanda ya rage mata ta wanke shi’ ta feraye . sannan ta rinka raba shi gida biyu.

‘. Tana gamawa ta ‘debo kayan miya ta jajjaga, ta dauko tukunya ta dauraye ta dora akan wuta, ta kawo man ‘gyada rabin ludayi ta zuba, ta dauko albasarta

lets go frnds ba koyon abinci mukaxo yiba am sorry

Ta kammala tsab, sannan ta soma shirya

su cikin qaton faranti, taji motsin fitowar’su a falon. gabanta ya dan fadi kadan ta dai dake ta dauko farantin ta fito. Bata dubi inda suke ba sai da ta jajjera .

kayan saman tebirin bin abincin, sannan ta dubi inda take jiyo dumin su, gabanta ya fadi ras’! ~rassl! Lokacin, da sukai ido hudu da shi a yanzu, ya canja kayan jikinshi zuwa kayan ‘shan iska

‘ fara tas irin na turawa. ita kuwa gimbiyar

dogon wandon jeans ne a jikinta baki, sai jar

shirt mai yankakken hannu. Rukayya ta sadda idanuwanta a qasa

muryarta a raunane tace

“ga abin karyawa nan na gama”.

“Sannunki, mun gode” .

Abinda taji ya fada kenan a sanyaye kafin sautin Suhailat ya karade falon.

“Waye zai ci ne Dcar‘? Ba dai Suhailat ba, sai dai k0 kai…

“To wa kika ji yace dama kici‘?”

Ya katseta.

Da mamakin Rukayya sai taji ta ja mashi tsaki, abinda yasa Rukayyar dago kai da sauri ‘ tana kallon su. kenan

Mikewa taga Suhailat din tayi daga gefenshi ta zira flat shoe dinta dake kan carpet tai wuce warta tare .da balbale Rukayya da

_ harara, tai gaba. Abinta Rukayya ta rakata da Idanuwa shi kuwa bai sake kallonta ba ya “mike Ya nufi wurin dinning din da ta shirya abincin akai yana fadar

“Bari naga me aka shirya mana”.

Rukayya dai ta kasa motsawa daga inda take har sai da ya zauna ya ja kayan abincin yana duddubawa, wani irin razanannen kamshi ya doki hancinshi, ya dago da sauri yana kallon inda take tare da fadar.

“Kinyi tsaye k0 kema ba zaki karya

bane?”

Da sauri ta kada mashi idanuwa alamar a’a, ba wai wani salo bane yasa ta yin hakanba illa ‘ nauyin da bakinta yai Shi kuWa zuba mata mayatattun idanuwansa ya yi kallonta yake yi tamkar ba Rukayyar da ya sani ba, ganinta yake tamkar wata ta daban Ce aka musanyo mashi ba wadda ya sani ba. Don a‘ ‘ farkon shigowar su k0 kadan bai ganeta ba, don ya yi zaton wata bakuwa ce, sai da tayi magana ya gane muryarta.

‘ K0 da wasa bai taba tunanin Rukayya zata zama haka ba,har a yanzu bai daina tantama akanta ba.

Wani abu yai mashi tsaye a zuciya ganin ta juya ta tafi yasa Shi saurin furta..

. “Ina kuma za kije? Ba zaki (saving) dina _ ba?” ‘ . ‘ ‘ Bata ce Kala ba ta juyo ta dawo ba tare da ta bari sun hada ido ba ta zuzzuba mashi komi idanuwanshi na kanta har ta gama, bata jira abinda zai ceba ta juya tai ‘gaba abinta.

‘ ‘, Ya bi Rugunta da kallo karo na farko da ya kalli sigar data data kusa kidimar daShi tare da sanya Shi suman_wucin gadi, ya dafe kanshi lokacin da’ ta Bacewa ganinshi.’Ya rasa abinda ke damunshi, idanunshi suka kada sukai . jajjawur. Da kyar ya samu ya lallashi zuciyarshi . ya ci abincin.

Ai kuWa ba kadan yaci ba, don shi da kanshi sai da yai mamakin irin abincin da yaci, to yauahe yarinyar nan ta iya wannan girkin haka? Lallai akwai wani Boyayyen al’amari dake shirin faruwa nan ba da Jimawa ba.

Ya rasa abinda ke damunshi, shi dai ya sani tunda ya tafi tausayin yarinyar ya tsaya mashi a zuciya har bai iya bacci ba tare da ya kira Hajiya Maimuna ba yaji yanda Rukayyar ta wuni,ba to amma yanzu da ya dawo

sai yakc jin abin yana neman ya rikide ya zama‘ wani muhimmin al,amari lallai dole ya kula, inba haka ba zata tono wuqar yankata

Rukayya ‘ _kuwa tunda . ta koma Bangarenta ta kunshe a daki ta kasa fitowa, .‘ duk rawar kan da take a wurin Aunty Maimuna ‘na wurin koyin lakanin mallakar maza amma kallon da Abubakar yake kafeta dashi shi kadai ya firgitar da ita, ya hanata sukuni. ‘ ‘Tana‘so ta fito amma tana gudun su bade, bata so suna haduwa kallon da yake mata yana firgitar da ita har taji tana ncman sukurkucewa, duk wata tsika ta jikinta sai ta tashi. Sabon yanayi ne takc ji a jikinta wanda bata jiba karo na farko kenan a rayuwarta da ta soma jin tana sha’awar su kasance a tare, to amma yaushc? Ta yaya‘? Dukkan wadannan tambayoyinne wadanda bata da amsar su ke addabarta har bacci Barawo ya lallabo ya sureta ba tare data saniba

ba ita ta farka ba sai qarfe biyu dan yan mintina

Ta zabura a hanzarce ta nufi (toilet) ta dauro alwala tayi sallar

akan sallayar tana addu‘a Abbakar ya dago labulen falon ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta har ta shafa addu’ar ta mike. Tana juyowa sukai ido hudu bata san lokacin da bakinta ya soma gayar da shi ba. Sai da ya fadada bakinshi da murmushi kafin ya amsa mata idonshi na akanta, ya ce. “Kin qosa da baqin naki kenan?” Muryarta a sanyaye tace, “Da nai me?” ‘ Ya ce, “To ba gashi kin hana su abincin ‘rana ba bayan ~ kin basu na safe”. Rukayya ta dayi wani takaitaccen murmushi ~kafin ta ce. . , “Bacci ne ya dauke ni, yanzu zan je inyi”, Tana maganar tana linke hijabin da tai sallar dashi Yana tsaye yana kallonta har ta nufo shi

a_ tunaninta zai kauce ya bata hanya ta wuce.

.amma sai taga bai da niyyar matsawa don haka taja‘ ta tsaya dan gab dashi tana fadin.

2pages is damages am sorry plz

jera akan dinning table ta nufi sashinta ta dauko hijabi ta saka ta fito tabar gidan

’ Kai tsaye gidan Hajiya Maimuna ta nufa . tai sa a kuwa bata je wurin aiki ba, tana zaune a. falo tana jera lemuka da ruwan roba a cikin firij, tana ganin Rukayya ta mike daga durkuson da tayi tana kallon Rukayya.

“Ke kuma me ya fito dake yau ke da miji ya dawo amarci yau sabo?” ‘

.Rukayya ta zauna saman hannun kujera jikinta a sanyaye tana kallon Aunty Maimuna tace

“Na gaji da gadin gidan haka nan Aunty, * Ya Abbakar ba zai taBa sona ba k0da kuwa Balarabiya zan koma don kyau’

Hajiya Maimuna tace”inji wa‘? Haba Rukayya, kada ki karaya tun yanzu mana duka yaushe daren ya yi balle garin ya waye?” ‘

Ta raBa ta zauna akan kujerar ta dafo

Rukayya tana fadar . Meya faru? Me yai miki kuma daga

dawowar “ sa?

Zuciyar Rukayya ta Kara karyewa, cikin raunanniyar murya ta soma fadar.

“Aunty tunda ya dawo bai shigo inda nake ba, da zai kirani inyi mashi girki ma daga baKin kofa ya tsaya, Aunty na gaji ba zan iya ba, kaUye kawai zan koma”.

Hajiya Maimuna ta ce “Saboda wauta? Ke yazu k0 wani ya baki shawarar yin hakan na zata ba zaki dauka ba”.

Taja numfashi kafin ta cigaba da fadar. “Dole sai .kinyi hakuri Rukayya, shi mai ‘ hakuri yana tare da nasara. ‘Abinda nake so yanzu shi ne da kinji motsin sun fito falo ki ,sauri ki gyara kanki, kema ki fito ki soma .share-share da goge-goge a falon. ‘Sannan ki cire tsoronsa, ki rinka yi mashi magana da’ yar xolayar sa cikin shagWaBa k0 da shi bai miki magana ba ke ki masa.

Sannan ki cire tsoron Suhailat ‘daga zuciyar ki,~ ki daina shakkarta, sannan ki rinka qokari ki cire shakka da tsoro k0 da sau biyu_a rana kiyi yanda zaki jikinku ya hadu”.

HMMM LOL

RIKON KAKA

CHAPTER22

Rukayya ta waro ido waje tare da toshe baki cikin

matuqar firgici Hajiya Maimuna ta ‘harareta. _‘

“Meye wani abin zaro ido anan? Da

Allah ba wai cewa nayi kije ki rungume shi ba, a‘a

k0 dai ki fadi masa da zummar baki sani ba, k0

kuma ‘dai ta wasu hanyoyin. Ki fara_ ‘gwada

wannan din tukunna; -duk_rintsi kuma . kada ki

yarda ki zauna, babu~ kamshi jiddin walahairan,

ki zamo cikin ; kamshi da…”. Rukayya ta katse ta

da niyyar yin magana, Aunty Maimuna ta tsayar

da’ ita ta hanyar fadar. ~. “Kada kice komi, ke

dai kiyi yanda nace Tashima ki koma kada ya

lura kin fito’.

Ba yanda Rukayya ta iya haka ta dawo gidan ba

don zuciyarta ta gamsu _da bayanin Hajiya

Maimuna ba sai don ba yanda ta iya, tai ‘ sa’a

kuwa: babu kowa a falon don haka tai .

wucewarta dakinta tai kwanciyarta zuciyarla ‘

cike da qunci bata fito ta dora girkin dareba sai

bayan’ sallar magaruba lokacin da taji .

shigowarsa ya dawo daga salla masallaci.

, Ta Zira takalminta mai madaidaicin tsini ta fito,

ai kuwa tai sa’a suna baje cikin falo shi da ‘yar

mulkin matarsa, dukkansu suka rakata da

idanuwa

‘ Sanye take da riga da :zani na sabuwar

atamfarta super exculisive wadda aka matse ‘

akaiwa lafiyayyen riga da siket wanda suka zauna

mata mata a jikinta,

“Me kake kallo‘?”

Muryar Suhaiiat ta katse Abubakar yai saurin

maido hankalinshi’ da tunaninshi a

wurinta, ya dan soshi Keya alamun rashin

’ gaskiya kafin ya ce.

“Me kika ‘gani?“ Suhailat ta watsa mashi harara ‘

“Ban gane wannan tambayar ba, ta mi na gani?” .

“To gani nayi ka tsareta da idanuwa, ban gane

wannan kallon ba to meye? meye ma ‘anarsa?”

Abubakar yai murmushi kafin Yace

“To yanzu mc zan kalla a can wanda ban taBa

kallonshi anan ba?” Yai wata shakakkiyar dariya

yana fadar. . “Yanzu duk ki rasa da wacca za kiyi

kishi sai da qanwata? Haba SUhaila, ai» k0 ana .

‘ Sara a tsallake icen kuka”. ‘ Suhailat ta Kara

Bata fuska tana facfar. . ,”A’a Wallahi, ai dan

hakin da ka raina shi . yake tsokane maka

idanuwa. Ni kuwa ban yarda ba, kai kace da mun

dawo zaka mayar da ita, kauyen su, ni dai kawai ‘

ka maida ita kamar yanda kace din”. Abubakar ya

shafi kansa yana fadar. “K0 baki ce ba insha

Allahu zan mayar “ da ita ta ma cigaba da

karatunta a can” ‘

Suhailat ta tabe baki tana fadar. “Da dai yafi”

Abubakar yai dariya yana girgiza kai cike da

mamakin halin kishi irin na Suhailat na

,babu gaira babu dalili, lallai ashe akwai

takaddama a gaba.

Rukayya dake tsaye a kicin tana jiyo-duk abinda

suke fada, ta lumshe idanuwanta _’

wasu hawaye masu zafi suka biyo kuncinta, ashe

dama ita ke haukanta a banza shi bai dauketa a

matSayin mata ba? Ashe dama tuni ya warware

auren nasa dake kanta.

“Innalillahi wa’inna ‘ilaihi raji’un!”.

Kalmar da bakinta ke iya maimaitawa kenan, inda

ruwan hawaye ke ta faman’ zarya a saman

kuncinta‘.

Yanzu ya zata yi kenan? Ya zata yi da dumbin

soyayyar sa da ta mamaye mata zuciya?

Ta rungume idanuwanta tana _ wani irin kuka

marar sauti. Tabbas Abubakar ya Cika babban

makiyinta, ya zalunccta, bai mata. adalci ‘ba.

Tabbas ya zame mata wajibi ta cire Sonshi a

zuciyarta ta cike gurbin da tsanarsa da kuma

kiyayyarsa ta sake rushewa da kuka mai sauti

dole zata bar “gidan ba ma sai ya maida ta da

kanshi, ba bata bukatar wani abu ya sake ,

hadata dashi, bata buqatar ganinsa har abada.

‘ Rukayya ,tai kuka har taji .kanta na .ciwo

sannan ta saurarawa raywuarta ta kalleshi kanta’

ta kunna gascookcr ta dora tukunya jellof din

taliya ce tayi express babu k0 kifi ballantana ’

suci arzilqin nama.

Ta juyeta a kula ta rufe k0 lemu bata hada ba sai

dai ta dauko na‘kwali ta hada da robar ruwa ta

jera akan tire ta dauka ta fito

Tana ajiyewa akan table tai gaba abinta ba tare

_da ta kalli inda suke ba, saboda hawayen dake

faman zubowa a cikin idanuwanta har a lokacin.

Tana shiga Bangarenta ta maida kofar ta ‘ .ruga

da gudu dakin baccinta ta fada akan gado ‘

‘tare da rushewa da wani sabon kukan mai ban

tausayi.

Tana cikin baqin ciki tare da Jin haushin kanta da

zuciyarta da har ta bari son Abubakar ya Shigeta,

sai yanzu ne ta soma takaicin yanda’ ta biyewa

Aunty Maimuna akan wai dole Abubakar zai sota

alhalin tafi kowa sanin irin

tsanar da yai mata.

. Tabbas itama zata kwatanta mashi kadan daga

cikin irin kiyayyar. da yai mata, dole zata

fatattaki soyayyarsa koda da qarfin tsiya ne

daga. zuciyarta. Ta qara makalkale filo tare da

rushewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

. Washegari tunda Rukayya ta kammala sallar

asuba bata sake komawa bacci ba, ta . shiga

tattaro komatsanta tana zubawa cikin Katuwar

jakar kayanta, sai data hada kan komi sannan ta

zube qatuwar jakar ta dauko atamfarta ta‘ jiya ta

saka, sannan ta saka hijabin _ sallarta, karfe

bakwai daidai ta dauko jakar ta tai hanyar barin

gidan.

. Tun kafin ta ida isa bakin get ta soma tunanin

irin qaryar da-zata shirgawa maigadi ta samu ta

bar gidan, sai dai cikin ikon Allah tana zuwa ta

samu qofar a bude da alama ya zagaya ne. Cikin

farin ciki Rukayya ta sa kafa ta bar ~gidan jikinta

na rawa, bakinta kuma na addu’ar Allah Yasa ta

samu ficewa daga layin -ba tare da wani ya

ganta ba, saboda unguwar tasu G,R,A CE ; k0 tsit

yake k0 da yaushe zaka samu babu kowa. Don

haka har ta samu ta iso bakin titi mutanen data

gani basu wuce uku ba, suma

amman babu wanda ta sani cikinsu. ta jima a

bakin titi kafin ta samu mai keke napep ya

dauketa daga nan zuwa Dandagoro naira dari

biyar. Rukayya bata samu nutsuwa ba sai da

taga sun fice daga‘unguwar gaba daya sannan ta

samu sukuni Karfe takwas saura mintina shidda

taiwa Rukayya a kofar gidan Kaka wanda rabonta

dashi tun randa Kaka ta kaita gidan abubakar, sai

yau data gudo da qafafuwanta

haka rayuwa take. Rukayya ta biya mai keke

napep sannan ,

ta dauki kayan nata duk da uban nauyi

ta nufi cikin gidan na Kaka.

tana Sallamar farko Kaka ta amsa tare da duban

qofa, sukai ido hudu da Rukayya. Kaka :ta dau

salati tana fardar

Rukayya yau a gidan nan ko ko dai gizo idona ke

mani?”

:Rukayya ta sauke jikarta a gaban Kaka taja

;kujera ‘yar tsuguno tana

kokarin zama

agaban tabarmar da kaka ke zaune, ‘Kaka ta

‘tsarrta da idanuwa tun kafin ta zauna ta soma

fadar.

“Ke ‘yar nan ya naga idanunki luhuluhu kamar

wadda ta sha kuka? Wannan uwar jakar ma wai ‘

daga ina?“ Rukayya ta zauna tare da sa gefen

hijjabinta tana share kwallar dake qokarin

zubomata ‘ Kaka ta sake daukar salati saida

takai aya ta ajiye sannan daga karshe ta furta. ‘,

“Kada kice min yaji kika yo Kada ” ki fada mani

wannan bakar kalmar” ‘

Rukayya ta tsaya da sharar kwallar tana

kallonta.

Haushi ya fara kama Kaka, tace.

‘ “Ke nak saurare Jika, me ya fito dake ciki

gidanki. Babu dai abinda kika nema kika rasa to

akan wacce hujjar? . A wane dalilin?” ‘ Rukayya

tacigaba da Sharar kwallarta, tabar ~. Kaka nata

sababinta har sai da Lami mai aikin kaka ta fito

daga cikin dan karamin dakinta

ta iso inda suke’ tana fadar. .

“Haba Kaka. kin tasa ‘ya a gaba da sababi

akan’abinda baki sani ba, sai‘ kace baki swn

halin mazan nan na yanzu ba lalatattu, na kirkin

cikinsu ragaggu ne”. ‘

”Kaka ta karkace kai tana fadar;

“Shi ne kuma za’a rinka lullubo zani a taho yaji?

Da kika ganni nan Lami shekarata arba’in da

mijina ban taBa zuwa gida –. kararsa ba balle in

rufa zani in tafi gida yaji ba kuma don baya saba

min ba”.

‘ Lami ta ce, “To k0 dai mene ne yanzu ai .kin

tsaya kiji ta bakinta lukun sai ki yanke hukunci

Kaka tace, “ai gata nan sai .ta gaya miki, ina

saurare

Lami ta juya kan Rukayya ta dafa kafadarta tana

fadar.

‘ “Yi shiru mana haka nan Rukayy’a, kiyi

hakuri ki fadi abinda ke faruwa sai a san ts inda

za’a taro al’amarin Ai ke kinyi sa’a ma

abin’duk na‘ gida. ne ba zai yi wahalar gyaruwa

ba Sai ‘da Lami ta bata lokaci wurin ‘lallashin

Rukayya kafin ta bude baki ta ~ Zayyano duk

_’abinda ya faru tsakaninta da

Abubakar har izuwa yanda Tun kaifin ta kai aya

Kaka ta soma

‘sallallami tana rusawa Habu zagi, tana

mmmmm. “Yanzu in wanke’ yar in bashi shi ne

zai

zuba mata ido yana kallo saboda rashin mutunci

da wulakanci? Ni habu zai nunawa iyakata?” . ‘ ‘

Rukayya na kaiwa qarshe Kaka ta rushe da kuka,

k0 kalonta Rukayya bata tsaya tayi ba ta mike tai

Cikin daki ta haye kan gadon Kaka taci gaba da

kukanta.

Tabbas abin ba qaramin bakin ciki yaiwa Kaka ba

don yau tai mashi zagin da bata taba kwatanta

yiwa wani irinshi ba don ma dai

lami na‘gefe tana tausarta da ban san irin abinda

za tai mashi ba

Duk yanda Kaka taso ta lallashi Rukayya taqi

saurarenta, ita ala dole fushi take da ita. ‘_ Kaka

kuwa duk tabi ta damu, har suka kwanta

~dadaddare. .

Kaka dai ta kasa daurewa don gaba daya baccin

ma ya gagari idanuwanta, ta tashi zaune tana

kiran Rukayya ya kai sau uku kafin ta amsa. ‘

Kaka ta ce “Tashi kiji abinda zan gaya miki”.

‘ Rukayya ta ce, “Ni fa bacci nakc ji, ki fada

kawai ina jinki”.

Kaka batai musu ba ta cigaba da fadar.

“In har’dai ba habu bane autan maza a duniya to

kin gama aurensa tunda har ya wulaqanta ki

haka, ki barni dashi. K0 gaisuwa ban yafe ba idan

ta hadaki da shi kinji abinda na fada’ ‘ . miki”.

Rukayya dai bata tanka ba, _amma a zuciyarta

gani take gaisuwar ma bazata qara hadasuba

Mutumin da ya wulakanta ta, ya nunawa duniya

’ita da dan uwansa namiji amfaninsu daya

wajensa, to gaisuwar mece ce zata hada su? Ai

ba ma zata yarda ya sake ganinta ba.

****** **********

. Bangaren Abubakar kuwa tunda gari ya waye

misalin qarfe bakwai ya gama shirinshi na tafia

(ofiice) a matsayin shi na’ sabon ma’aikacin da

aka tura (curse) .su goma su uku ne kawai sukai

nasarar fitowa da (result) mai kyau, don haka aka

dauke su aiki, yau kuma ita . ce rana ta farko da

zai fara zuwa (offlce) din.

Suhailat na kwance akan katafaren gadonsu, tana

ta sharbar barci, har ya kammala shiryawarsa.

Bai yi tunanin tayar da ita ba saboda .bai ga

amfanin hakan ba tunda babu . wani abu da zatai

mashi yasa kai ya fice yana daura tsadadden

agogonsa a hannu.

Ya so ya biya ta sashin Rukayya yaga yata

kwana? Sai daisaurin da yake ba zai barshi ba

don haka inda so‘ samu ne ya dan karya ‘da “

lafiyayyen girkin Rukayyar kafin ya tafi To hakan

ba zata samu ba, saboda qarfe bakwai dinma

harta dan gota

Hmmmmm kaka dai tace indai habu ba autan

maza bane a duniya ba to ba habu ba ruky

lol muje zuwa wai mahaukaci yahau kura admin

is back

RIKON KAKA

CHAPTER23

aka ce tai musu a can don haka bai tsaya Bata

lokaci ba ya dau motarsa a gaggauce ya tafi.

‘ Tunda suka isa wurin aiki shi da sabbin da aka

dauka irinShl basu samu sun shiga (office) ba sai

qarfe sha biyu tunda ya shiga (office) din nashi

sallar azahar da la’asar ce kadai ta fiddo dashi,

k0 abinci bai iya fitowa ya nema ba sai ruwan

(tea) kawai da yake ta faman kwarara ma cikinsa,

amma duk da haka har qarfeshidda bai samu ya

gama (clearing) din komi ba, a dole ya taho gida

saboda lokacin tashi ya riga yayi. ‘

‘ . Bai taho gidan ba sai da ya biya ta crepcy ya

kwaso tarkacen su (snacks) ice cream da lemuka

yayo leda biyu na Suhailal da kuma Rukayya

sannan ya nufo gida.

Tunda ya shigo falon bai nuti Bangaren kowacce

ba, kai taye wurin teburin cin abinci ya nufa

saboda wata irin yunwa da yake‘ji tana neman

kayar dashi.

Sai dai da mamakinsa ya iske tcburin wayam ji

yayi gabanshi yai wata irin faduwa wani irin

masifaffen Bacin rai ya shige shi, ya

‘juya a zafafe ya nufi Bangaren RuKayya tamkar

ita kadai ce a matsayin matar shi a gidan. Ya

tura kyauren falon, kai‘ tsaye yasa kai a cikin

falon nata yana kwala mata kira.

Jin da_ yayi babu alamar za’a amsa, yasa shi ‘sa

kai cikin‘ dakin baccin ‘ta sai dai mamakinsa, nan

ma wayam babu kowa a ciki. Ya maida kallonsa

akan qofar toilet din wadda ke a’bude.

Gaban Abubakar .yai wata mummunar bugawa,

ya juyo a firgice yayo waje. Dakin Suhailat ya

nufa, tana tsaye gaban (home theater recorder)

tana ta tikar rawa da wakar Adam Zango ta gayu

komai na mata ne.

Takaici ya kama Abubakar ganin bata ma san ya

shigo ba har sai da yaje ya kashe wakar sannan

ta waigo a tsorace sukai ido hudu dashi, ta

yamutSa fuska a gajiye tana fadar.

‘ “Am sorry, wallahi banji shigowar ka ba”. . _ ._ .

Abubakar yaja tsaki kafin ya ce.

“Ai dama ba‘zaki ji shigowata ba tunda kin qure

volume kina ta tikar rawa sai kace

“yar nanaye. lna Rukayya ta tafi ne?” Suhailat ta

bata tuaka tana kallonshi kafin tace. , “Rukayya

kuma? Akan wanc dalilin zaka lambayeni inda

take? Ka bani ajiyarta ne?” Abubakar ya hade

girar samadata qasa kafin yace

‘ “Ban gane na baki ajiyar taba? Ya zan lafi in

barki da yariya a gida in dawo kuma in tarar bata

nan in maki magana kuma kice na baki ajiyarta?

Jinan Suhailat, ban son rainin wayo kinji?”

itama ranta ya soma Baci, a ganinta ma in ba ya

rainata ba ya za’ai yai mata wannan tambayar? ’

Ta dauke kai tana fadar, “To na koreta ‘daga

gidan tunda ba gidan ubanta bane, ko nima zaka’

koreni ‘ ‘ ne‘?” Ran Abubakar ya yi wani masifar

baci, wai har ‘Suhailat tayi bakin da zata xagi

‘yar uwarsa‘? Lallai shi ya bata fuska, don haka

cikin

matukar Bacin rai ya shiga fadar

“Kin koreta kin kyauta, amma kamar

yanda kika ce ba gidan ubanta vane to nima ai ba

gidan uban babe hakaxalika tunda har gori ya

fara shigowa ciki nima zan bar gidan

yau kamar yanda itama ta barshi. Nine ke aurenki

Suhailat bake ke aurena

ba, don haka na baki zaBi k0 ki koma sabon

gidan da na gida da kudina kiyi zaman aure, k0

kuma ki zauna anan, .zaBi ya rage naki”.

Yana gama maganar ya fada dakin barcinsu.

Suhailat ta bishi da bala’i tana fadar.

“Yo aurenka din banza, Abubakar kai har kayi

kudin da zaka gina gidan da zaka sakani a Ciki‘.’

Ai dama tun kafin mu dawo qasar nan“ na gane

take-takenka, ka ajiye aikin kamfanin mahaifina

ne kanemi wani .aikin don kaji dadin’cin zarafina,

to baka isa ba, wallahi kayi tsururu. In banda ma

qaddara ai kasan nafi kariin ajin’. aurenka, ita

wadda kakewa rawar jikin dama can ita ce ajinka

ita ce dai dai kai ba __ ‘ ni ba”

wohoho mata kaiiii muje zuwa

Duk abin nan da take Abubakar na tsaye gaban

(wardrop) yana hada kayanshi a cikin akwati, bai

sake kallonta ba ballantana ya kulata. haka ya

hada duk ‘wani abu mai muhimmanci a cikin

akwatinshi ya gama zuge abarsa yaja hannun

akwatinsa ya fice daga gidan.

Har ya fice Suhailat ta raka shi da sababi, bai

sake kulata ba ya saka akwatinsa a bayan mota

ya fice ya zagaya gidan direba ya shiga yaiwa

motar; (key) yai gaba abinsa, ya barta nan. Da

Wauta kuma yana ficewa daga gidan sai. kuma ta

rushe da kuka cikin tashin hankali

‘ sai’ kace ba ita bace yanzu ke zazzaga masifa

‘ba har baki ’na kumfa. . ‘

Kai tsaye Abubakar gidan Haj. Maimuna ya fara

tsayawa, yai sa’a kuwa ya samu, oga mahmud a

gida, don haka suka baje a falo inda Hajiya

Maimuna ta qawata masu tebur da kayan abinci

da soye-soye kala-kala.

‘ Abubakar ya ‘ kasa taBa komi saboda tsananin

damuwa da yake ciki Mahmud ya

tsura mashi idanuwa yana fadar.

“Lafiyar ka dai Abubakar naga kamar baka .da

lafiya?” Abubakar ya jingina da makarin kujerar da

yake zaune yana kallon Mahmud da jajayen

idanuwansa cikin matukar damuwa ya soma

fadar

‘ “Lafiya qalau Oga, damuwa ce kawai”. ,Haj.

Maimuna dake tsiyaya masu lemu a glass cup ta

dago ta dan dube shi tana fadar

“Wallahi naga alama, don ni har na danji tsoro

don ban taBa ganika cikin irin wannan yanayin

ba” .

Abubakar ya shaki numfashi yana fadar.

“Ni ‘ kaina ina tausayin‘ _kaina Hajiya Maimuna

Suhailat ta. kOri yarinyar nan Rukayya –

ina’ (office) ban san ina ta ina zan fara

‘nemanta ba, na’ tabbatar matukar taje wurin

kaka ka’shina ya bushe”. ‘ . ’ .Haj. Maimuna

dake duke ta_ koma da baya ta zauna ‘akan

kujera tana fadar. “ta kori Rukayya yaushe?”

“‘Dazu”. Abuhakar ya bata amsa.

Haj Maimuna ta dafe kai cikin matuqar mamaki

tana fadar

“Ikon Allah, kuma har Rukayya ta baro gidan ba

tare data biyo tanan ba?”

Mahmud ya dubi Abubakar yana_ fadar.

“To kai tayaya ka sakarwa mace haka harta iya

korar wanda ka dauko ka kawo cikin gidanka

baka nan?” _ Kafin yai qokarin fadar wani abu

Haj. Maimuna ta karbe zancen da’ ‘. “Ai

Honarable duk abinda yake faruwa a cikin gidansa

ba laifin kowa bane laifin sa ne da sakacinsa.

Dama k0 da Suhailat bata kori Rukayya ba itama

Rukayyar ta soma tunanin guduwa ta bar maka

gidanka. _ . , Abubakar ka ajiye mata biyu a cikin

gida amma ka tauye faya akan daya saboda wani

son zuciya can ~ naka. Shin ita Rukayyar ba

matarka’ bace? Ko ita ba mace bacc? K0 kana

tunanin bata buqatarka? Amma ka’ biyema “mace

ka tauye yarinya, ka mayar da ita ‘yar aikin

gidanka ba’ wai matarka ba, ku ka dinka ‘

wahalar da.ita’don kawai an aura maka ita ba

. , . don kana so ba. Shin kana ganin Ubangiji zai

barka ne k0 kana ganin kana da wani makari da

zaka iya kare kanka a wurin Ubangiji?

Dama ni jiranka nake kawai ka dawo in hadaka

da Honarable yai maka nasiha tunda kuma an

koreta ai shi kenan, dama abinda kake

so kenan tatafi ta baku wuri ta yunkura ta mike a

zafafe tai falonta zuciya ta kawo mata wuya

kamar zata fashe saboda bakin ciki, ita a ganinta

Abubakar ya cancanta a kirashi azzalumi mai

bautar dana qasa da shi.

oga Mahmud ya dubi Abubakar yana fadar. “To

kai ta yaya duk wadannan abubuwan ~suka faru

haka Kana aikin me?”. ‘ ‘ ‘ Abubakar ya kasa

magana, ya rasa abinda ke mashi dadi daga

yanda yaga Hajiya Maimuna ta hau yasan zai

iske dubun haka a wurin Kaka. _ .

Oga Mahmud Yace”Kaifa nake saurare Abubakar

kayi shiru

Abubakar ya sauke numfashi kafin ya soma

magana.

“Wallahi Mahmud duk aikin zuciyane kasan

Rukayya ba sonta nake ba kakace tasa dole“: na

aureta, tasa dole na hada su da suhailat Gashi

gidan da nake zaune mahaifin Suhailat din ne ya

bamu aronshi kafin nayi nawa, gashi kuma ba son

Rukayyar nake ba, wannan ne ye ‘taimaka wurin

tauye mata haqqinta.

Amma da taflya tai tafiya ni da kaina

naji hakan bai kamata ba, hakan ne yasa na

harhada kudi masu yawan gaske nasai qaton fili

a Batagarawa low cost don a ganina idanna ce

zan bawa Rukayya matsayi na mata a ‘wurina a

cikin gidan uban Suhailat duk abinda akai mana

ni na ja.

‘ Ban fara ginin ba na samu tafiya qasar nan yin

wannan (course) din, na dauki Suhaila muka lafi

kudin alawus din da aka rinqa biyanmu daSu na

gina filina, daga can qasar na turo da zanen gida

da nake so muna dawowa

aikina na ajiye a ciki a kamfanin mahaifin

Suhailat tunda nayi nasara akan (course) din da

aka tura mu yai mana murna sosai

Tun kafinmu iso gidanmu na sanar da Suhailat a

gidana zamu_ sauka, amma ta qiya a dole muka

dawo gidan mahaifin nata.

Ni don da yanda naso in fara ajiyeta a gidan nawa

sannan in dawo in dauki Rukayya itama na kaita

gidan. Sashi uku ne iri daya nawa da na RuKayya

da kuma na Suhailat to sai ta Kiya a dole na

kyaleta, amma dai na sakawa raina zan dauki ita

Rukayyar da sunan na kaita’ qauye sai in kaita

can gidan nawa indai data matsayinsu na matana

sannan da na dawo in sanar da Suhailat gidana

na kaita na bata irin matsayin da itama na bata

nasan Suhailat tana matuqar sona zata haqura

idan ma bata yarda ‘ ba to sai ayi duk yanda

za’ayi tunda ni dai nasan inda .na dosa sai gashi

ta koreta ban sa yanda zanyi ba nasan da wuya’

idan kaka zata saurareni ballantana har ta

fahimce ni”. ‘

*Oga Mahmud yajinjina kai kafin yace.

“Ai duk da haka Abubakar kayi matuqar wauta,

amma ni a ganina shiryawa kawai zaka yi ka tafi

biko da sunan kai baka ma san yanda akai ta

taho ba, a can ne za’a fada maka kishiya . ce ta

korota, kaga daga nan sai kasan sauran “‘

bayanin da zaka yi ka samu a baka matarka ku

taho. ‘

Abubakar yayi murmushi cikin matukar jin dadi

yana fadar

”Aiko ka ba da shawara yanzun nan zan je don

banga abinda nake jira ba”.

Oga Mahmud ya ce, ‘Amma kafin ka tafi din ya

kamala ka fara biyawa ta gidansu Suhailat din ka

sanar da mahaifinta duk abinda ya faru

tsakaninka da Suhaila! din don kada ta rigaka

zuwataje tai maka ‘yan qulle-qulle’. Abubakar ya

ce, ‘Yanzu fa barima ka gani

Ya mike tare da miqawa Mahmud hannu suka

Kara yin musabiha sannan sukai sallama ya tafi

‘Abubakar ya isa gidan su Suhailat yai sa’a kuwa

mahaifinta yana nan’ don ‘haka a

falonsa akai mashi masauki, sai dai Abubakar bai

san yanda ake kai qara ba tunda bai tababa gashi

yana matukar Jin nauyin sirikin nasa hakan ne

yasa sai da yai tA ‘yan zagaye zagaye kafin ya

iya zayyanowa mahaifin Suhailat din abinda ke

faruwa tun daga aurensa da Rukayya har izuwa

yanzu.’

Alhaji ya jinjina kai yana fadar;

lkon Allah, yanzu wuyan .Suhailat har yayi

kwaridn da’zata dubi mijin aurenta tai .mashi

wannan rashin mutuncin? To ba‘komai, kada ka

damu, kayi haquri gida dai nawa ne don haka

tunda Allah Ya buda maka kayi naka to nima na

karbi nawa kuma bance ka dawo gidan nan

bikonta ba, yanda kace ta koma naku gidan tasa

Kafa ta shure to haka zata kwaso qafar dai nata

taje ta iske ka Ka’bani , dan lokacu

ln banda sukarcinta ai shi aure nufi ne na Allah,

idan Allah Ya nufi mutum da shi babu Wanda ya

isa ya hana Don haka Abubakar kaje ka maido da

matarka, kada ka bari mace tayi

rinjaye akanka“.

Hmmmm lol an kammala da iyayen suhailat

sauran mai ran qarfe hajia kaka koya zasu

kwasota da abubakar oho naku har kullum A,I,S

ke cewa mu tara donjin ci gaba da yaddah zataci

gaba da kasancewa

cont it

RIKON KAKA

CHAPTER 24

Abubakar ya amsa da, “Insha Allahu”. Sannan

sukai sallama da Alhaji ya tafi abinsa cike da

qarrfin gwiwa ya dauki mota ya nufi Dandagoro

zuciyarsa cike da addu’a tare da fatan samun kan

Kaka ta bashi matarsa k0 ya samu natsuwar

zuciyarshi.

Karfe tara na dare ya iso qofar gidan Kaka, ya

faka motarshi ya’fito ya kukkulle’ qofar motar,

sannan ya ‘nufi .cikin gidan ”zuciyarshi cike da

fargaba ya . soma jera sallama. Daga daki ya jiyo

muryar Kaka na

amsawa, don haka ya nufi dakin kai tsaye yana ta

faman addu‘a a zuciyarshi. Ya yaye labulen‘ dakin

ya shiga Kaka na daga kwance da hasken wutan

lantarki

Ya durqusa daga bakin qofa yana gaishe daKaka

cikin girmamawa-, tamkar babu abinda. ya faru,

ta amsa mashi cikin sakin fuska, abinda ya fara

bashi mamaki kenan wanda ya. sashi tantamar

anya kuWa Rukayya tana gidan‘.’

‘ Gabanshi ya yanke ya fadi,yaja daga

tsugun0n da yayi ya zauna yana kallon Kaka ya

ce

‘ “Harkun kwanta kenan?” Kaka ta ce, “To me

muke jira?” Ya danyi jim yana ta sakesake a

.zuciyarshi, so yake kawai Kaka ta tare shi da

maganar Rukayyar amma tai burus ta share shi,

abinda ya Kara sashi cikin rudani kenan, ya rinka

waige-waige cikin dakin, babu ta inda ya hangi

alamarta. ‘

Wata zufa ce ta soma keto mashi da yaga ya

share fiye da minti talatin a zaune, ita Kaka ma

tuni har ta soma barcinta. Ba yanda ya. iya

shima haka ya mike ya fice jikinsa a kasale bai

‘xo da Shirin kWana garin ba, amma kuma yanzu

baiga ta tafiya ba ina zai sa kanshi yanzu ’ idan

aka ce Rukayya ta Bace?

Sai da ya leka (toilet) yaga babu kowa a _ciki

sannan ya wuce‘ tsohon dakinsa ya budc ya

shigé ya kwanta akah katifarsa, babu alamar

barci a cikin idanuwansa haka yaita juyi shi kadai

a cikin daki daga qarshe kuma ya mike yaje‘ya

‘dauro alwala ya dawo dakinsa yaita . jero

nafilfili: yana addu’ar Allah Ya bayyana

mashi ruky

Bangaren Rukayya kuwa tunda ta jiyo muryar

Abubakar yana sallama ta wantsara ta. fada

bayan gado tai kwanciyarta, tana jinshi ya qaraci

zamansa har ya fice sannan ta mike ta haye kan

gadon tai kwanciyarta.

Washegari misalin qarfe. takwas Abubakar ya

gama shirin tafiya (office) ya shiga dakin ‘Kaka

da niyyar yai ma Kaka sallama,‘ akai sa’a

Rukayya tana kewaye tana watsa ruwa, saboda

wankan safen da ya riga ya kama mata jiki, don

haka har ya gama yiwa ‘ ,Kaka sallama ya filo ya

hau motatsa ya tafi

bata sani ba. ~

A moto Abubakar ya rasa abinda ke

mashi dadi, ya shiga cikin matukar damuwa da

tashin hankali Tabbas ya sani Rukayya bata

gidan Kaka, to ina ta tafi? To kuma idan har bata

‘zo gidan ba ya akai Kaka bata tambaye shi

.yaya Jika ba? Sannan bata tambaye shi yaushe

ya dawo daga tafiyar shekara daya da rabin daya

tafi ba, da kuma bata daure mashi ba ta ‘ :karbe

shifaran-faran anya kuwa babu wata

maqarqashiyar da Kaka ta :shirya masa‘? ldan

kuma akwai ta yaya zai iya ganewa tunda bata

bashi fuskar hakan ba? Da wannan tunae tunanen

har ya iso (office) dinsa zuciyarsa babu dadi duk

ya fita hayyacinsa. Shi ji ma yake tamkar bai da

lafiya, saboda da qyar yake iya jan qafafuwansa,

sai kace mai ciwon lakka kwatakwata bai da

kuzari a jikinsa.

Cikin kwana uku duk inda Abubakar yasan

Rukayya zata iya zuwa sai da yaje ya nemota,

amma bai sa meta ba gaba daya ya zabge ya fita

hayyacinsa, shi baima san zuciyarshi ta kamu da

son Rukayyar ba sai *yanzu data kufce mashi,

don haka washegardi safiyar.juma’a yana tashi.

daga (office). Karfe hudu ya nufo dandagoro

gidan Kaka, ya yanke :‘shawarar zai sanar da ita

kawai tunda barin kashi a ciki baya maganin

yunwa. . ‘ Da sallamarsa ya shiga cikin gidan

babu kowa a. tsakar gidan sai Lami mai aiki tana

“wanke a’laiyyahu a bakin famfo sai da ya gaisa

da ita sannan ya wuce dakin Kaka kai tsaye inda

yake jiyo sautin redio wanda ya karade gidan da

wakar mutanen Niger wadda aka sako a gidan

radio, Abubakar ya yaye Labule cike da mamakin

‘yau. Kuma Kaka kida ake sha

‘ kenan, ita da take fada idan wani ya kunna’ta .

ce xa’a cika mata kunne.

Ya yaye labulen dskin tare ‘ da sallamarsa, sai

dai wa zai gani? Rukayya ce kwance akan gadon

da radio a kusa‘da ita daga’ ita sai farin dogon

siket irin

‘budadden nan, sai ‘yar Bingilar bes dinta iya

cibiya mai siririn hannu, babu k0 kallabi akanta.

Ai Abubakar bai san lokacin da ya fado cikin

dakin ba yana kiran sunanta

“Rukayya, dama kina nan kika barni nai

.ta wahalar _ neman ki?”

RuKayya maganar tasa ta daki dodon kunnenta

tamkar saukar markade bata san lokacin‘ data

zabura ta mike ba ido waje

Abubakar ya bita da kallo tundaga sama har

qasa, kafin ya hadiye Wani abu mai kamar yawu

a abakinsa, ya langaBe kai cike da alamun

gajiya ya ce . “Kin tayar min da hankali Rukayya,

kin ‘wahalardani, kin wahalar da zuciyata.

Haba Rukayya, me yasa kika biyewa Kaka ku ka

~ dauki alhakina?”

Rukayya ta cigaba da kallOnShi cike da mamakin

kalaman ,dake ‘fitowa .daga bakinshi, shi kanshi

bai san lokacin da suke fitowa daga baccin nashi

ba, sai dai abinda ya sani kawai shi ne. gaskiyar

abinda ke zuciyarshi ne yake ‘ furtawa ganin tayi’

shiru tana kallonshi‘yasa ” shi matsawa da niyyar

damqo hannunta. ‘ , Tai saurin ja da baya tare da

bata fuska, cikin sanyin murya Abubakar ya ce . ‘

“‘Fushi kike. dani? Kiyi haquri, nasan nayi kuskure

kimin afuwa insha Allahu hakan ba zata sake

kasancewa b…”. . Tsakin da Rukayyar taja ne ya

‘katse shi daga cigabada zayyano jawabin naSa,

ya bita da‘kailo cike da mamaki. A dai ,dai nan

kuma

Kaka ta fado dakin riqe’da butar data fito daga

makewayi da ita sai faman haki take, ta dubi

Abubakar. ‘ “Kai malam, fice min daga daki kaji,

mutumin banza mutumin wofi”. Abubakar ya juya

inda take yana fadar. . “Haba_ Kaka, yanzu‘

dama Rukayya tana gidan nan shi ne ku ka

Kyaleni cikin tashin . hankali tsawon sati guda?

Duk da dai ni din

mai laifi ne amma ai..Kaka ta katse shi, “Habu ba

surutu na

nema ba da kai, cewa nai ka fitar min daga

‘ daki kawai”

_ Abubakar ya langobe kai, “To naji zan fita

amma tare da matala”.

’ Yana maganar ya nufi inda Rukayya take da

niyyar cafko hannunta, Kaka ta daga butan dake

hannunta ta maka mashi akai duk ruwan dake

ciki suka juye mashi a jiki, yai saurin rike butan

yana fadar ‘

“Allah Ya baki hakuri nasan nayi laifi koma dai

me: akai min ni dai hakuri ne nawa, kuma ‘

zan ta baki shi har sai ranar da kika huce kika _

bani matata”.

Yana gama maganar ya juya jikinshi a sanyaye

ya bar dakin Kaka ta raka shi da harara har ya

fice sannan ta maida kallonta wurin Rukayya ta

ce

“Ke kuma sakaran banza kinyi tsaye sokoko yana

ta tsaraki da wannan dadin bakin . nashi da yake

ba wayau ya isheki ba. Yo in nice har ya isa ya

matso inda nake ma ban rotsa mashinkai ba inga

ta karyar rashin kunya”. Rukayya dai bata ‘tanka

ba sai dai ta koma da baya ta zauna akan. gadon

bata da ta cewa ita ganin abin ma take tamkar a

shirin film in banda abin Kaka k0 giyar wake

tasha ta yarda ‘ta Kara komaWa gidan Abubakar

mutumin da bai sonta, bai qaunarta, haka kawai

ya cigaba dabautar da ita a banza. _ .

_ Bangaren Abubakar kuwa‘ ganin Rukayya ya

rage mashi tashin hankali a cikin zuciya saboda a

yanzu yasan inda take yaqi guda ya rage mashi

wato yanda zai yi ya shawo kan Kaka ta? bashi

matarshi ya sani ba abu bane

mai sauqi ba yin hakan. to amma ya ya iya da

samarin kakarsa? Haka dai zai ta haquri harya

samu ya tadda nasara. Duk da baizo da shirin

kwana garin ba amma a yanzu dole ya tare don

baiga ta tafiya ba har sai ya Shawo kan Kaka. ‘

Sai dai duk yanda yai zaton’ abun ya wuce nan,

don gaba daya Kaka ta ida birkice mashi. k0

kadan bata sauraren shi da ta gama ya samu

wuri ya tare a gidan saita tura Rukayyar ta

“tafi wurin .dangin mahaifinta wai ta gaishe su

tai masu kwana biyu.

Lokacin da Abubakar ya fahimci Rukayyar bata

gidan ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, ya

tisa Kaka gaba yana fadar.

“Don girman Allah Kaka ina kika tura mani

mata‘?” _ ‘ ‘

Sai data harare ‘shi kafin tace“habu tun wuri ka

fita idona in rufe na fada maka, na kuma

maimaita maka takardar sakin yarinyar nan nake

jira kaqiji to mu zuba‘ na rantse sai dai kaga

sammaci, don wallahi kotu zan maka ka”. ‘ -.

Abubakar ya dafe kai yana maimaita.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Wai Kaka sai

yaushe zaki ji tausayina ne? Kullum ina qokarin

in ’kwatanta maki ba zan iya sakin yarinyar nan

ba, amma kinki ki yarda na fahimci’ so kawai kike

ki kasheni da raina? Yarinya da aurena akanta

amma ki daukéta ki kaita wani ‘wurin da ban san

k0 ina bane don dai kawai kinga banda yanda

zanyi. ‘ ‘

’ Kaka ta ja filo ta haye saman gado tana fadar,

“In “ma da yanda zaka yi din ba sai kayi ba, aure

ne ance ba’a yi ka bawa yarinya takardar sakinta

tunda ba kai bane autan maza ba kaqiya. To ba

sai kai ta riKo ba duk ranar daka gaji‘ka’saki

amma Rukayya kam kai da gininta sai dai a gidan

wani. Tana can na kaita inda ‘zata samu mijin da

ya fika tayi aurenta, kai kuma saki ne kai ta riqo.

Gaban Abubakar ya yi wata mummunar faduwa

da bai taBa yin irinta ba, tabbas yasan Kaka

‘tana da sanin addini dai dai gwargwado, , amma

hakan bai hana shi gasgata zata iya aurar da

Rukayya da aurensa ba saboda yasan shekaru

sun ja akwai rudu da rikicin tsufa a

a

tattare da ‘ ita. Wasu irin hawaye masu zafi suka

tarar masa a cikin idanuwa, yanzu ya zai yi?

Wannan wane inn bala’i neya tunkaro shi’! Lallai

yana cikin jarrabawar rayuwa.

Ya bude bakida niyyar ya cigaba da yiwa Kaka

magiya sai gani ya yi tana kwasar munshari, lallai

ashe ya dade cikin duniyar tunani bai sani ba.

_Jiki a sanyaye ya. mike yai gaba. Washegari

tunda sanYin safiya ya shirya ‘ ya koma Katsina

bayan ya ajiye mata kudi

masu yawan da zata yi amfani daSu. ‘ ” Sai daya

kwashe tsawon sati biyu bai dawo garin ba har

saida ya turo mata su Oga Mahmud . tare da

matarsa Hajiya Maimuna’ suma sukai nasu

lallashin da ban baki amma Kaka taKi sakkowa

daga dokin naqin da ta hau, kira kawai take idan

bai kawo’ takardar sakin da tacc ba sai ta ishe

shi har gida da takardar tsammaci. Ba yan’da su

Hajiya Maimuna suka iya haka suka dawo bayan

sun juye mata sakon

tarkacen kayan abincin da Abubakar ya shake

masu but din mota, ya ce a kawo mata.

Duk rashin arzikin, da take mashi bai jin zai Iya

hana ta abu daya daga cikin abubuwan jin dadin

rayuwar da yake bata, duk da yana jin zafi da

kuma ciwon rashin tausayin da take nuna masa

qarara, bayan yanzu shi abin

shi yanzu shi abin a tausayawa ne mutumin da

yakr zaune da matarsa kamar Suhailat amma

yanzu ya zama gwauron qarfi da yaji, komai shi

yake yiwa kansa dai-dai da sharar falukansa da

gyaran daki daga girki kafin ya fita (office) sai ya

samu dan dama k0 da kunu ne k0 ruwan (tea) ya

ci da bircdi sannan ya tafl, haka idan ya

daw0_duk uwar gajiyar daya’ kwaso sai ya age

ya dafa abinda zai ci sannan yai wanka ya

zauna, tunani ya aure shi babu inda yake jin

dadin zuwa shi yasa yake zamansa a gida daga

shi sai maigadi ,sai kuma yaronsa Laminu mai

kula da fulawoyi shi ne kuma ke mashi wanki da

sauran ‘yan aikace aikacen da ba’a rasa ba. ‘

Hmmmmm su kaka manya gaskia na tausaya ma

habu

A,I,S

RIKON KAKA

CHAPTER 25

Abubakar ya zama bai da :abokin hirar da ~ya

wuce t.v sai’ kuma tunanin RuKayya wanda yake

kwana dashi ya kuma tashi da shi wannan ita ce

rayuwar Abubakar a sabon gidansa. Satin

Abubaka biyu ya kasa daurewa ‘ ya nufo

Dandagoro bayan ya sha jinyahar ta tsawon

kwana uku’, shi kadai babu wanda ya sani, duk

‘wanda ya. kalle shi a yanzu zai fahimci halin da

yake ciki saboda irin ramar da yayi ya zama

kuma wani (so silent) kamar ba

shi ba.

Lokacin da ya iso gidan Kaka bata nan ‘sai dai

Lami_ wadda ke ta darzar ’wanki, Abubakar yaja

kujera ‘yar tsugunne ya zauna a gajiye kamar

wanda yasha gasar tseren gudu ya gaji. Ya

gaishe da Lami cikin sakin fuska, La‘mi ta amsa

cike da, tausayin Abubakar din yanda yabi ya

zabge kamar bashi. ba, ita dai daukar alhakin

yaron ya isheta haka. Ta zauna akan kujerar da

take wankin akai tana kallon Abubakar dinda yake

tambayarta k0 Rukayyar

ta dawo?

Lami ta sassauta murya kamar mai tsoron wani

ya jiyota, tace. “bata dawo ba, sai dai k0 in fada

maka

inda take”. Abubakar ji yayi tamkar ta tsunduma

Shi

cikin gidan aljannah, don tun kafin ta fada mashi

ya soma jero mata ruwan godiya. Ai tana fadi

mashi tana Bakori gidan qanin“ mahaifinta tsam

ya mike yai mata kyauta mai tsoka ya fice ya

fada motarshi, kai tsaye ya dau hanyar‘ Bakori,

bayan ‘ya tsaya gidan man Dandhgoro ya shake

tankin motarshi taf da mai

,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,

Bakori gidan qanin mahaifin Rukayya ne marigayi,

uWarsu daya ubansu daya, yana zaune a

gidanSa_ shi da matansa guda ukuTasallah,

Lantana da kuma‘ amaryar su Larai. Yana da’

ya’ ya a qalla sun kai ishirin da wani abu, wasu

sunyi aure wasu kuma basu yi ba, suna nan mata

da maza.

zuwan Rukayya garin ba qaramin mamaki ya

bawa Kowa ba, saboda tun Rukayya tana yarinya

suke son Kaka ta rinka: turota tana ganin ‘yan

uwanta suna zumunci amma Kaka taqi, ita allan

kalafar bata yarda Jika tai nesa da ita ba, sai dai

ta dauketa suje su wuni tare su dawo. Wannan

ne: yasa ba wani zumunci mai qarfi ‘tsakanin

Rukayya da’yan uwanta.

Don haka yanzu da tayi aure tazo masu wannan

dogon zaman ba qaramin mamaki ya _ basu ba,

don haka sukai tunanin aurenta ne ya mutu.

Itama kuma ta tabatar musu da hakan.

‘ Kawu yaji haushi ba kadan ba, don ’ a ganinsa

irin hakan ceke sawa a guji auren zumunci don

gudun bata zumunci. ‘

Rukayya taji dadin zama a cikin kauyen

’saboda ‘yan uwanta da kowa na son ace ‘ ‘yar

gayun nan ‘yar uwarshi ce hakan ne yasa har

rububinta ake a cikin yara da matasan gidan. ‘

“ Jamilu .yana daya daga‘cikin matasan ” gidan‘

‘yan gayu masu ji da karatun N.C.E,

wanda yana ganin Rukayya zuciyarshi ta ayyana

mashi ya samu matar aure irin wadda yake burin

aure, don haka ya yi kane-kane ya hana kowane

saurayi na gidan raBarta don gudun‘ kada ma

wani’ yai masa shigar sauri..

Duk da bai furta son da baki ba amma aiyukanshi

sun nuna, don duk inda Ruqayya zata jeshi ne

mai kaita da sabon mashin dinshi Jincheng roba-

roba, a gidan har sun fara fahimtar inda ya dosa.

lnda ita kuma Rukayyar ‘ take daukar duk

zumunci ne kaWai;

A yanzu haka ta riga ta shirya komawa gida gobe

don haka yau shirye shiryen taflya _ kawai take,

tun safe suke yawo da Jamilu tana bankwana,

.zuwa yanzu haka gidan Mariya . zasu qanwar

.jamilu dake aurc cikin garin, amma basu samu

fita ba sai bayan sallar magariba. ‘

Tayi kyau sosoi cikin riga da siket na shadda

maroon colour, ta yane kanta da (milk) ’ din

mayafi mai Shara-Shara, sai dai yana da

dan girma ba Iaifi Ta Saka takalminta mai tsinin

dunduniya. ita kanta tasan tayi kyau balle Jamilu

da ya goyota saman mashin dinsa, sai yaba

kwalliyar yake tare da kwarzanta ta. ‘ ita k0 sai

dariya take mashi, don ta’san duk zolaya ce irin

tasa, don haka ta biye mashi suna ta kWasar

dariya. ‘

Suna qokarin hawa titi Abubakar na ‘ qokarin

shiga layin_ da suka baro, idanuwanshi sukai

tozali da su suna ta kwasar dariya, wani irin

gingimemen abu ya tokare mashi zuciya ~wanda

yasa saura kadan da motar ta kwace mashi. . ” _

Ya taka wani mahaukacin birki wanda « yasa

qura ta tashiya juya kan motar yai a sukwane ya

rufa masu baya, ya bar jama’ar wurin na faman

atishawa tare da Allah Ya isa ga wanda bai ma

san sunayiba saboda an shiga haqKinsu kuma

hakan haramun né a Musulunci.

’Abubakar bai samu shan gaban su ba har sai da

suka sauka daga kan babban titi suka hau .

Karamin titi sannan ya samu nasarar shan

gabansu da mota, ya haske su da farin hasken

fililun motarsa

Jamilu ya ja birki a haukace, sannan ya soma

aunawa mai motar zagi. itama Rukayya ranta yai

masifar Baci, sai da Abubakar .ya gama qare

masu kallo suna ta kare-karen idanuwa tare da

zage-zage sannan ya bude motar ya fito.

‘ Tun kafin ya qaraso Jamilu da Rukayya suka

sakko daga kan mashin din suka kaucewa

. dogon hasken da_Abubakar ya haske su dashi.

Abubakar na qarasowa Jamilu ya cire hannu da

zummar ya mare shi, Abubakar‘ yai caraf da

hannun ya rike gam,’ muryarsa a sanyaye ya ce.

“Ina zakaje mani da mata?” Jamilu ya fincike

hannunshi cikin zafin zuciya yana fadar. ‘ ‘ “Uwar

wacc ce-matar taka?” .

‘ Abubakar ya nuna Ruqayya ‘ da danyatsanshi

manuni ba tare da yayi magana ba.

. Takaic’i , ’ya_ .kama Jamilu, ya haske. ‘

Abubakar da kallon banza kafin’ ya ce.

“Lallai kai ka tabbata mahaukaci, qaramin ,dan

shaye-shaye. To k0 salansa kake sha qarewar

hayaqi ni na fika iskanci”.

Abubakar ya ce, “Ai na lura tunda har ka

iya daukar matar aure” Haushin maganar

Abubakar ta kama

Jamilu har ya daga, murya yana nuna Abubakar

yana auna’ mashi ashariya, abinda ma ya janyo

hankalin ‘yan tsirarun mutane masu wucewa

kenan sukayo kansu tare da buqatar jin ba’asin

maganar Jamilu ne ke ta faman kora masu

jawabi ‘

cikin bacin _rai, sai da’aka gama sauraronsa

‘sannan aka ,bukaci jin ta bakin Abubakar wanda

ya harde hannuwa a ‘Kirji yana kallon su’ daya

bayan daya. Ya maida kallonsa akan ‘

Rukayya,yace ita ya kamata ku tambaya, gata

nan”.

. Jamilu ya dubi Rukayya yana rawar haBa, ya

ce. ’ “Ai ni nasan wallahi bata sanshi ba, irin

yan iskan gari ne kawai, k0 kin sanshi Rukayya?”

Sai data tabe baki kafin ta ce

“Ni ban sanshi ba”. Ai kuwa jama’a kamar jira

suke aka

hayayyakowa abubakar, don Jamilu qarfin hali ma

har kwalar rigar Abubakar yake ciyowa wai a

duke shi. Ai kafin ma ya cire hannun nashi daga

kan kwalar abubakar ya dunkule yatsun

”hannunshi ya kai mashi ‘wani dan marayan

naushi a mahagurba, yai wani irin ihu ya dafe

wurin da tuni ya baci da jini.

Abubakar ya qara mika hannu ya cakumo shi

yana Kokarin sake narka mashi wani naushin

jama’a suka tattare masu zakalkalewar ciki suka

dawo neman sasanci naya saki wuyan rigar

Jamilun, amma babu alamar zai saki din duk da

idanuwan Jamilu da suka

yo warwaje yana ta kakarin wahalar Majiya masu

qarfin ciki ne suka fara qokarin bambare hannun

Abubakar din, amma k0

gezau bai yi ba, don haka aka soma rokonsa da

ya sake shi din ‘

Bai saurare su ba ya maida kallonshi akan

Rukayya dake tSaye tana ta rawar haBa tare da

rarraba na mujiya, ya daka mata tsawa.

“Yanzu kin sanni k0 sai na kashe: shi

tukunna za ki sanni?” ‘ Rukayya jiki ya dauki ciri,

muryarta na rawa ta ce ‘

“Idan na sanka sai me? Ina ruwana da kai?

Mugu, azzalumi kawai, wallahi Allah sai

. Yai mana sakayya”. Abubakar yayi wani

malalacin murmushi‘

sannan ya saki Jamilun .yana fadar.

’ “To kaji k0 ni wane ne a wurinta, mijinta

ne data gudo ta bari kuma kaine baka sanni ba

amma ni na sanka shi yasa ma tun farko ban yi

niyyar taBa lafiyar jikinka ba, kaine kaja da

taurin kai irin naka, amma kayi hakuri”. Jamilu ya

rasa abinda zaice sai faman

mazUrai yake Abubakar ya ”tura ‘hannu cikin

aljihu ya damtso kudi mai yawa ya soke mashi

cikin aljihu yana fadar.

ga wannan‘ ka rage zafi”.

Bai bari yace’wani abu ba ya damki hannun

Ruqayya tana turjewa tare da borin kwacewa

haka yaja ta da qarfi ya sakata a mota ya rufe ya

zagaya ya shiga mazaunin dirrba yaja suka tafi.

Kai tsaye gidan Kawu ya nufa ya kulle Rukayya a

motar shi kuma. ya nufi cikin gidan, saukinta ma

akwai AC a ciki daya kasheta.

da zafi

‘ A zaure ya samu kawu a kwance yana sauraren

rediyo, Abubakar ya durkusa a gabansa suka

gaisa. Bai gane Abubakar dinba sai da yai mashi

bayani sannan ya shaida shi. Nan fa Abubakar ya

sanar da shi duk abinda ke faruwa tun daga

dalilin barin Ruqayya gidanshi.

har zuwa yanzu. Mamaki ya kama Kawu ya rinqa

zuba

sallallami yana fada akan danyen hukuncin Kaka

da kuma wautar Jamilu, daga,qarshe yaiwa

Abubakar naisha da kuma fatan’ alkhairi. Yasa ya

kira Rukayyar itama yai mata nasiha sosai

Ya so su kwans sai gobe su juya, amma

Abubakar ya ce a‘a, saboda zai je office.goben.

Kawu yasa RuKayya ta kwaso kayanta,“ ya

zubaSU mota sannan sukai gaba bayan yaima

kawu kyautan kudi masu yawa sannan suka

kama. hanya babu wanda ya kula wani, Ruqayya

ta gaji da kukanta har tai shiru. Bai ce mata ci

kanki ba har burci barawo yai awon gaba da ita

Basu iso Katsina ba sai karfe goma .saura ‘da

yan mintina, maigadi ya bude_ mushi qofa ya

kutsa .motarshi a ciki kai tsaye gurin ajiye motoci

ya faka motar tashi sannan ya fito a gajiye yake

likis dan da kyar ma yake iya daga. kafa ya

budema Rukayya dake Zaune yana kokarin kaukar

ta ta farka a tsorace

gami da ture hannayen nasa Ya yi murmushi

sannan ya matsa yana fadar ., . ‘ “Ki fito mun.

iso” Ruqayya ta bata fuska tana fadar:

Ni wallahi bahu inda zan matsa ‘sai ’ka . maidani

gaban uwata

Abubakar yai dariya“ sosai kafin yace

”Wacece uwar taki kuma? Kidai ce kakarki me

sangartar dake, kuma yarinya ke da qara ganinta

qila sai kin koma wankan jego“ Rukayya ta

harare-shi tare da tabe mashi baki ta dauke

kanta ta turo mashi qeya.

Shi daria ta bashi don haka bata ga lokacin da ya

janyo hannunta ba sai dai ji tayi an sureta gaba

daya anyo waje da ita ; ‘

Rukayya ta soma shure~shure tana zillewa amma

bata kufce daga hannuwansa ba har$ai da ya

danganata da katafaren falon gidan wanda wurin

zilIe-zillenta tasa suka fadi akan‘tayils, amma duk

da haka nan bai saketa .ba, tana cikin

hannuwansa sai da ta gartsa mashi cizo a

hannuwan sannan ya sakcta ita kuma ta zabura

ta mike ta” kwasa aguje ‘ta barshi, falon,

amma‘sai ta kasa bude qofar a bude take ba kcy

aka Saka ba k0 sakata ba amma ta datse Haushi

ya kama Ruqayya, ta rinqa jijjiga qofar da ko

gezau bata yi.

Abubakar yana kallonla ya mike yana dariya yai

shigewarsa kicin hankalinsa a

kwance

Hmmmm lol jama,a wai ya za,a kwashe da

kakalle ne idan har taji labarin habu yaje ya

dauke matarsa?

naku har kullum A,I,S KE CEWA i luv y’ll

cont it

RIKON KAKA

CHAPTER 26

ya dora musu girki yau zuciyarsa fes take da

nishadi marar misali.

, Nama ne ya gasa sannan ya dafa

dankalin turawa da indomie ya gama komi tsaf ya

jera ‘a dan farantin ya dauko kwalin ‘Iemu guda

biyu tare da robobin ruwan Faro suma biyu ya

jera a saman (carpet) ya sameta ta hada kanta

da kujera kuka kawai take amma marar sauti sai

dai za’ a iya jiyu shasshekarta

Abubakar ya ajiye tiren kayan abincin a gabanta

sannan ya raba gefenta ya janyota jikinshi’ ya

rungume yana kokarin lallashinta bata ture shi ha

amma kuma bata daina kukan ba

Abubakar ya dora kanta a saman. qininshi ya

Kara rungumrta yana fadar.

‘ “Kiyi haquri‘ don Allah ki daina kukan nan haka

nan kada kanki yai miki’ ciwo”.

Yana maganar yana gyara mata gashin

kanta wanda ta turo kallabinta wurin kokawar

dazu.

Rukayya ta soma magana cikin kuka. “Na ce

baxan zauna ba ka maida ni gida, ka maida ni

amma kaki don dai ka kawoni in rinqa‘yi maka

girki da aikin gida. Na rantse da Allah ba zanyi

ba”. Abubakar ya yi murmushi yana fadar. “‘bama

sai kin rantse ba ‘yar gidan kaka, indai kin

amince zaki zauna dani magana ta qare, ni da

kaina zan rinqa yi mana girkin da aikin gidan, kin

amince?” ‘ Bata amsa mashi ba sa dai ta sa

bayan hannunta tana goge hawayenta. Bai ji

haushi ba ya dago ta daga jikin

nasa yana fadar.

“Daga yanzu ma za’a fara abincin ma abaki zan .

. rika baki”. .Ruqayya tai saurin zamrwa tana

fxmadar.

“Ka kyaleni inci da kaina matsa”.

Bai matsaba ya kyaleta sai dai hannunta na riqe

da nashi haka ta zuba abinci da hannu guda.

yana kallonta tana cin ,abincin kamar

tanacin kashi. Bai damu ba har ta gama, sannan

shima ya dauki sauran yana ci.

Tsabar gajiya da kukan da tasha kafin ya gama

cin abincin har ta fara gyangyadi, don haka yana

gamawa ya tasheta ya nuna mata hanyar dakin

bacci. Bata musa ba ta mike ta tafi abinta. Sai

dai duk da barcin da : take ji sai da ta jima a

tsaye tana qarewa tsararren dakin baccin kallo

wanda ya gaji da haduwa, a zuciyarta ta rinqa

tunanin k0 gidan waye Abubakar ya kawota kuma

oho.

Tunda bata da mai amsa mata don haka ta nufl

(toilct) ta dauro alwala tai sallah sannan ta dauki

kayan barcin da ta gani a ajiye akan gado ta

saka.

Doguwar riga ce fara sol har qasa mai .‘siririn

hannu, Rukayya ta saka hular rigar akanta

sannan ta kashe wutar dakin ta haye kan gadon ,

tai kwanciyarta. Haka kawai taji zuciyarta ta

samu nutsuwa tunda taji Abubakar yace ba aiki

zata cigaba

dayi masu ba a gidan, don haka hankalinta

kwance bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita. ‘

Abubakar ya gama shirinsa a Bangarenshi sannan

ya nufo Bangaren nata, ya samu sai kwasar bacci

take hankalinta kwance. Nan ‘ya hawo kan gadon

shima ya . kwanta, ya jawota jikinshi ya

tofesu’da addu’o’i sannan yaja bargo ya lullube

su. Washegari tunda asuba ya tayar da ita suka

yi sallah, ta Cika da mamakin ganinshi akan

gadonta, sai dai ganin Bai nuna wani (action) ba

akan hakan yasa itama tayi ta maza ta share

suka yi sallar asuba. Ya jata suka koma

‘suka sake kwantawa, sai dai har bacciya

’ kwashe shi amma ita ta gaza runtsawa,

mamaki take da kuma al’ajabi wai yau ita ce

yaya Abubakar kwance daki daya, gado daya

kuma manne’da juna. Wannan wacce rana ce mai

Sa’a haka a wurinta‘? tunanin da take. kenan har

barci Barawo ya lallaBo ya dauketa

Ba ita ta farka ba sai karfe goma saura, ta juya

ta ganta ita kadai kwance akan gadon. Ta llaBa

ta tashi zaune tai ido hudu da ‘ wasu riga da

siket sababbi dal akan gadon, hakan na nufin idan

tayi wanka ta shirya ta saka. ‘

Tsam ta mike ta fada (toilet) din ake

. manne’ cikin dakin ta watso ruwa ta fito ta

zauna bakin madubi ta shirya,kwalliya tayi amma

ba wata mai yawa ba, ta mike ta dauki kayan ta

saka ‘

English wears ne riga da siket Bakin siket ne ‘

T,Shirt body hock mai dogon hannu. Ta dauki ‘

dan karamin mayaifinta ta’ dora akanta, sannan

ta zira silifas na fata ta fito falon don tasamawa

kanta abinda zata ci.

A falon ta_ hange shi daga shi sai

,singilet da wando three quatcr ya zagc yana

ta gogegogen Show glass din dake shake da

kayan turaren wuta

Rukayya tabi. falon da kallo, ya gyara k0mai

tsabtsab sai kyalli yake yana fitar da ni ‘imtaccen

, kamshi

Rukayya ta tabe baki saman kujera ta zauna tana

kallonshi cike da al’ajabi, k0 da yake ba tun . yau

ta saba gani ba tun a kauye dama Abubakar

gwani ne wurin iya share-share wanke-wanke da

girki. ‘

Abubakar ya nufota tana kallonshi har ya Karaso

inda take, ya zauna kusa da ita yana‘ fadar,

‘”Sannu da tashi my dear,in kawo miki abincin

nan k0 zaki hau kan table ne?” Sai da ta yamutsa

fuska kafin tace

“Anan zan ci”.

Ya yi murmushi ya miqe yana fadar.

“An gama ranki ya. dace

»: Ya nufi dinning ya kwaso abin break din-daya

shirya ya nufo inda take. ya dora. tiren akan

center table sannan ya turi . tebirin zuwa gabanta

yana murmushi

“To bisimillah”

, Bai kuma jira abinda zata ce ba ya juya yai

gaba ya cigaba da aikin da yake

Rukayya ta jima tana kallon shi kafin ta mika

hannu ta bude kayan abincin, soyayyen dankali da

kifi ne mai hade da kayan lambu sai ‘ ‘ kuma

kunu. Rukayya ta soma ci tana mamakin shi

kuma a ina ya iya irin_ wadannan girKe-girken? ,

‘Anan inda ta gama karyawar anan ta zame

saman kujerar . ta kwanta tana kallon wani film

din~ India a qatuwar plasma din dake girkc ‘a

jikin bango ta kusa rabin bango.

Kafin ta gama kallon barci ya dauketa ba itata

farka ba sai ana kiran sallar azahar.

‘Ta mike taje tai sallah, k0 addu’a bata

shafa ba Abubakar ya shigo mata da abincin

rana. ,Mamaki fa ya qara kamata canjawar sa

lokaci daya na sakata cikin (compusing). ’Bayan

sallar isha’i Rukawa na kwance “a falonta babarci

take ba amma idanuwama a rufe suke, tunanin

Abubakar ne. yai mata

tsaye a zuciya, hidimar da yai mata yaudaya

kawai ta wanke mata zuciya, ta wanke dukkanin

bakin cikin da ya shafe shekaru

yana qunsa mata. Bata ji shigowarsa ba sai dai

taji an

riko hannayenta tareda sumbatar goshinta. Ta

bude idanuwanta a hankali tana

kallonsa, ya hasketa da murmushi kafin ya ce.

“Tunanin ya isa haka, ki tashi ki shirya

muje muyo (shopping) kiga gari”. Dadi ya kama

Rukayya ta zabura ta mike cike da doki tana

fadar.

“Don Allah yaya daga nan mu biya

gidan Aunty Maimuna”.

Ya noqe kafada’ “Naqi wayon, wato muje ta

cigaba da koya miki yanda zaki qara guduwa’

k0?” Rukayya ta zar0 ido tana fadar.

“tab! Yaya wa ya fada maka ita tasa ni na gudu‘?

Wallahi ni nai tafiyata da kaina”.

Ya ce, “To ai kin kyauta kinga yanzu nima ba zan

kaiki ba har sai kin fara sona kin daina guduna

. Ta langabe kai kafin tace to “To wai yanzu wa

yace bana sonka

Ya noqe kafada, “To idan kina sona ‘din ai sai ki’

fada” Rukayya ta zame hannunta tai gaba tana

faman turo baki, Abubakar ya rakata da kallo har

ta shige sannan ya sami bakin kujera ya zauna

yana wani dan murmushi’ wanda bai bayyana

hakoranshi. ba

Shiri sosai Rukayya tayi da wani rantsatstsen

lcshi (two c010ur) wato blue da brown tai kyau

sosai don hatta Abubakar sai ‘ da ya yaba..Ya

dauketa a‘mota.

‘ Sai da suka gama yawon su saman manyan

titina. yana gwada mata ‘manyan unguwannin

garin nan har sha daya sai data. gota sannan ya

kaita suka yo shopping din na kayan ciye-ciye da

lashe-lashe bayan sunci.

wasu can sannan Suka yo dakon wasu.

RIKON KAKA

CHAPTER 27

sai Sha ; biyu harda yan mintina sannan suka

shigo gidan. bacci ne kawai cikin idanuwan

Rukayya don haka ta bar Ahubakar yana sassaka

kayan firij ita kuma ta shige dakin baccinsu ta

watso ruwa tasa rigar baccinta cikin ta daure

gashin ta da ribon ya shigo. Ta madubi ta hango

.shi ya iso inda take bata san yanda akai ba sai

dai taji ya rungumeta ta buya ya miqa hannunshi

guda y; diuko kwalbar turaren cool water ya rinqa

fesa mata a jiki saidaya fesheta dashi sannan ya

ajiye turaren sannan ya jasu sukn fada saman

gadon dake bayan su, ya kashe wutar dakin

yaja bargo ya lullubc su. Washegari ita ita

takama Lahadi, ba aiki kamar jiya asabar, don

haka suna idar da sallar asuba suka koma suka

kwanta. Rukayya bata sake farkawa ba sai da Iaji

tamkar ana yamutsa ta ta bude idanuwanta da

kyar don ganin mai wannan aikin.

Abubakar yaja muta hanci yana fadar.

“A tashi haka nan ayi wanka a karya. ga ruwa

can: na hada miki”. ‘ .a toilet ta fara juye juye

yace kinga wasa sai dai kiji ki cikin ruwan

wankan’. Rukayya tai surin tashi zaune tana

. ‘ kallonsa da idanuwanta duk bacci, Abubakar

ya miqa hannu ya janyota ta sakko daga kan

gadon, ya tisata gaba har sai da ta shiga (tOilet)

din ta kullo sannan ya juya ya fice.

‘ Rukayya bata bata lokaci ba wurin .shiryaWa ta

fito yau a tare suka karya don ta ‘soma sakin jiki

dashi. Tarairaya da lallashi .tare da soyayyar da

yake nuna mata ita tasa ta soma jin wata irin

sabuWar qaunarsa na shiga zuciyarta. Yanda

yake nuna tausayinta a fili abin har mamaki yake

bata, wai yau yaya Abubakar ne ya abubakar ne

ya koma’ haka ya canza tamkar ba wannada

yatsaneta, ya hantareta ba. :

lallai Allah Ubangiji mai juya zuciya gashi yan’zu

ya juyo mata da zuciyar abubakar

gareta. Lallai a yanzu ta yarda’da maganar Aunty

Maimuna da take cewa, mai haquri yana tare da

‘nasara aiko ita dai taga nasarar. don ma zuciya

da taso ta rinjayeta daga farko lallai kuwa da tayi

‘asarar da ya kamata azo mata

jaje don rasa namiji kamar Abubakar ba

karamin asara bace Da wannan tunanin har bacci

ya

dauketa a daren yau inda ta kwana da zummar‘

garin Allah na wayewa litinin zata riga Abubakar

tashi, ita zata yi komai ba,hidimar gidan ta hutar

dashi don harta . soma tausaya mashi. ‘ ‘_ _ Don

haka tunda suka koma baccin

asuba ita taqi ta koma tana ganin bacci ya dauke

shitaja jikinta ta fice kai tsaye‘ ‘kicin ta Hula nufa

ta dora ruwan zafi ta Zuba masu garin chitta‘da’

na‘a-na‘a,. suna ‘ tafasa ta juye a flask din

ruwan . Ta koma ta dayko dankalin turawa ta

fere tasa a tukunya ta dafa shi sannan ta. ‘

tsame shi tamai bula bula ba koyon girki

mukaxoba am sorry

Dayan ta gama tsaf sannan ta dauki komi la

jajjera su gwanin sha‘awa, sannan ta koma kicin

din ta gyara shi ta hada ruwan omo ta wanke

dukkanin abubuwan da tai amfani dasu ta kife ta

share kicin din ta goge ko ina da tawul sannan ta

janyo kicin ta kulle ta dawo falon tasa tsinlsiyar

laushi ta share shi tun daga

qasan kujeru har zuwa qarkashin sai da tabi ta

share. Sannan ta dauki mopprr ta hada

ruwa a bukiti ta goge tayils din tsab, k0 ina ya

dauki sheki.

Ta koma ta sa wani tsumma mai Iaushi ta goge

duk wasu abubuwa masu daukar qura dake falon,

sai data gama tsab sannan ta dauko boner har

guda biyu daya ta zuba turaren wuta ta jona‘ a

socket daya kuma ta kunna tsinsiyoyin kamshi

masu kyan gaske ta tsilstsira a jiki ta koma ta

dauko room freshner ta ruwa ta feshe dakin.

Ai kafin kiftawa da bismillah dakin ya kaure da

wani ni’imtacccn kamshi ta saki

labulayen ta goge sannan ta qara qarfin A.C ta

nufl sauran falukan suma duk ta gyara su kamar

na farko, da turare su da kamshi.

Karfe takwas dai-dai ta shiga (facin baccinta

shima ta gyara shi, ya wanko toilet‘sannan ta

watsa ruwa tana gamawa shima ta hada mashi

sannan ta filo. _

Kwalliya tayi ba wata mai yawa ba, ta saka baqar

jallabiyya mai hade da gyalenta, sannan ta nufl

kan gadon da Abubakar ke kwance ta rasa ta

yanda zata tayar dashi. can

dabara ta fado mata ta dauki fIlo ta rinwa‘ buga

mashi a kafa amma babu alamar Zai tashi.

Rukayya ta rasa yanda zata yi dashi, can dai ta

saduda ta hayo kan gadon tana dan

bubbugar filon da yake kwance akai tare da kiran

sunanshi

Caraf ya yi da ita, sai dai taji ta cikin jikinshi ya

kanannadeta da hannayenshi yana dariyaya ce ‘ .

“Wato na ma zame miki tamkar wani. dodo. k0?”

Rukayya ta girgiza kai tana’ Roqarin zamewa. ‘

ya Kara riqeta yana fadar.

“Ki tsaya kada ki jiwa kanki ciwo. tambayar ki

zanyi”. ‘

Rukayya ta nuna mashi agogo tana Rukarin

zillewa, karfe takwas da rabi agogon ya nuna. Ya

yi saurin sakinta yana fadar,

“Kai-kai loakcin (office) ya kusa yi”..

Bai jirata ba ya Sauka‘da gudu-gudunsa ya fada

(toilet) yana faman yarfa hannuwa wai ya shiga

uku ya kusa makara.

Rukayya ta zauna bakin ‘gadon tana mashi dariya

har sai da ya shige sannan ta. mike ta yaye

zanin gadon ta canza wani mai ‘laushin gaske, ta

feshe Shi da (bed frcshncr) sannan ta bude

(wardrop) ta cirowa Abubakar kayan da zai saka.

Sannan ta flce abinta.

‘A gaggauce Abbakar ya shirya yai break dinshi

ya, bata wata sabuwar waya rantsatstsiya, a

cikin kwalinta mai matuwar tsada, tsabar doki

Rukayyabata san lokacin da ta Runkame shi ba

tana murna.

Abubakar ya lakace mata hanci yana mata dariya

ya fice ya ‘nufl wurin aiki‘abinshi. . Rukayya

kuwa wuri ta samu ta rashe‘a’ falo ta rinqa

cskule-cakule a wayar tata tunda take a ‘ duniya

bata taBa riqe waya ta kanta ba sai yanzu, lallai

.Abubakar ya gama mata komai tunda ya hadata

dawayar salula.

Shi kuwa Abubakar tunda ya isa (office) din aiki

kawai yake amma zuciyarsa na kanta, duk abinda

yake qarfin hali ne kawai da jarumta, amma a

yanzu yana ji a jikinsa qarfin halin nasa ya kusa

qarewa. Yana son Rukayya so ba na wasa ba,

haka kuma yana sha’awar komi nata.

Yasa hannu ya tallabe kansa cike da damuwa,

duk lokacin da ya kalli Rukayya yakan rasa

hankalinshi gaba daya, sigarta kawai takan nemi

ruguje‘ mashi lissafi. Lallai ya yi sa’a da

kasaitacciyar mace, sai a yanzu ne yake mamakin

kansa ta yanda har ya rinqa hantarar ta. Shin a

lokacin meke damun kwakwalwarSa da

idanuwansa da suka kasa ganin abinda ya dace

da shi? Wai har ya fifita Suhailat akan Rukayya,

yarinyar da in bacin kyan fuska babu mamora a

jikinta. Lallai shi ya gama wautar kanshi.

“Ya’ ja tsaki mtsw! Kafin ya mike yasa hannu ya

lalubo wayarshi dake kan tebirs ya lallatsa lambar

wayarta ya danna mata kira.

(Ringing) daya, biyu na uku aka dauka. Rukayya

ta: mike a saman doguwar kujera (three seater)

ta danno mashi siririyar sallama a cikin dodon

kunne, sai da Abubakar’ yayi murmushin jin dadi

don har

’ ‘tsakiyar kwanyar’ kanshi maganar ta ratsa.

Ya kwantar da kanshi a saman makarin kujerar

da yake zaune, ya cigaba da jujjuyawa da kujerar

yana fadar.

“Ruky Darling, kinyi kewata kuwa?” Rukayya tai

murmushitare da lumshe ido ta

_ bude, kafin ta ce.

-“Sosai ma Yaya Abbakar, duk gidan sai ya yi

shiru da baka nan

Abubakar jinshi yayi tamkar a saman

gajiimare tsabar shauki, ya bude baki da kyar

yana fadar.

“To me za ki shirya mana kafin na dawo?”

Murmushi tayi wanda har ya jiyo sautinshi a cikin

wayar, ta ce.

“Wani spccial girki ne Yaya Abbakar me ‘ motsa ‘

kunne” Dariya yayi sosaikafin ya ce”Sai kuma me

qanwata? K0 shi kenan?”

‘ sai da tai wani fari da idanuwa irin na mai

neman mafita kafin ta ce ‘

“To ai ban ‘san sauran abinda kake so ba

Abubakar ya ce “KeCe sauran, ke nake so

Rukayya, k0 ba zaki bani ba?” ‘

Ta ce “To ai kariga daka samu yaya Abbakar, me

kuma ya yi saura?”

Abbaakar ya ja numfashi kafin ya ce

‘ “Ai baki so na Rukayya, guduna kike shi yasa”.

Tai saurin rufe baki tana dariya, ta ce

“Kai Yaya, tun yaushe na daina?” ‘

‘ Shima dariyar ya yi kafin ya ce”Da gaske kike

mata ta.? Ta jinjina kai tare da fadar, “Da gaske

nake mana,

Ya ce “To shi kenan, kice yau inzo gida da kwarin

gwiwa kenan matata tana maraba . dani. To’

amma ai min irin kwalliyar jiya a shafa min

janbaki da jan ido ta yanda da na shigo zan yarda

da lallai abinda aka fada min yanzu da gaskene”.

RuKayya tana dariya ta ce, “Insha Allah Yaya, sai

ka dawo”. ‘ Ya ce”To qanwata, me kikc so inyo

miki . tsaraba?” ., Ta danyi jim kafin ta ce, “K0

dami ma ka taho ina so”. ‘ Ya ce “To Shi kenan,

sai na dawo“. Sukai sallama sannan kowa ya

ajiye ta kalli wayar _ Tsabar murna Rukayya ta

rasa irin . shirin da zatai na tarbar Abubakar,

tunda ‘ tayi la’ asa: bata sake samun zama ba,

ita ce

shiga kicin ta hau shirya abincin da tasan zai yi

farin ciki dashi.

Abubuwa ne ta hada mashi sun kai kala hudu, ‘

sannan daga qarshe ta hada mashi (juice) din

gwanda da karas. ‘

‘ Ana kiran sallar magaruba ta gama komi ta nufi

(toilet) ta sharto wanka ta tare da

alwala ta fito, sai da tai sallah tana zaune tana

lazimi Abubakar ya shigo gidan. A gajiye yake

don ya sha aiki a (office), ya turo qofar bedroom

din nata ya shigo da sallamarsa, Rukayya ta dago

kai tana kallonsa bakinta dauke da murmushi. ’

Abubakar ya durkusa a gabanta ya dora

hannayensa akan jikinta yana fadar.

“Na gaji da yawa Ruky na, don Allah k0 zaki .

taimaka mani da wanka?” .. Rukayya tai saurin

rufe fuskarta da tafukan hannayenta tana dariya.

Shima dariyar yayi ya mike yana fadar.

‘Shi kenan, bari intafi ‘sashina inyi tunda’ ‘ ba‘

zaki min anan din ba”. RuKayya dai na jinsa

amma bata dago din ba ‘ har ya fice, sannan’ ta

mike ta nufi

gaban madubi ta zauna ta soma kwalliyarta cikin

saurisauri ta samu ta gama, ta ciro kayan da

zata saka riga da wando ne blue din ’ jeans sai

sky blue din riga irin ta Pakistan mai’ adon pink

sama da kasa, ta kawo mata kusa’ da gaiwa,

tana da tSaga a gefe da gefenta. ‘ Rukayya ta

dauki siririn gyalen rigar kalar pink ta daura

akanta,’sannan ta saka dan kunne kalar rigar

Tayi kyau ba ma kadan ba, don haka ta dauki

hijabi ta saka tai sallar isha‘i, ,

sannan ta cire ta saka flat din takalminta ta;

fito falon . A kishingide ta same shi saman

kajera”

yana waya, don haka bata bi ta kanshi ba ta ,

wuce wurin (dinning table) ta rinka kwaso kayan

abincin .tana maido su akan carpet har ta

kammala’bai gama wa‘yar ba wadda*’ta fahimci

ba da kowa bane ba face Suhailat don daga

karshe taji yana fadar… ‘ ‘“ “Kinga Suhailat ina

da ababuWan yi masu yawa a gabana, sai

anjima” Ya kashe wayar. ‘ ‘

Ya sauko kusa da Rukayya ya zauna

tare da dafo kafadana, ya ce

“Ya dai madam? Kin san kuwa ina jin Yunwa?”

Rukayya tai murmushi kafin ta soma zuzzuba

musu abincin. ‘ ‘

Lallai kam Abubakar ya kawo yunwa, don narkar

abincin kawai yake kamar ba

gobe, sai faman zuba santi yake Rukayya na

Sheqa mashi dariya Aka murda qofar falon aka

turo tareda

sallama, su duka suka bi qofar da kallo don ganin

mai shigowar. :

Oga Mahmud ne ya shigo tare da Kaka, mamaki

ya kama Rukayya, ai bata san lokacin da ta tashi

ta nufi kaka zata

rungumetaba . Kaka ta tureta tana fadar

‘ “Ke ni kauce ki bani wuri, shashashar banza da

wofi, shi ne kika sa qafa kika biyo shi, wato ni

ban isa in yanke hukunci a kanki ba k0? . To na

gode.

Rukayya ta rike hannun Kakar ta Iangabe kai tana

fadar. ‘

“To ai kaka shi ya matsa sai da ya taho dani”. ,

Kaka ta fisge hannuwanta tana fadar.

“Ke gafara can sakarai, ya dai laye ki ‘ da dadin

bakinshi, amma k0 da ihu da cizo baki guduwa?

Meye amfanin zama da azzalumin mutum irin

shi? Sai ki juya yanzu

mu“ tafi” . . Ta kamo hannun kukayyar za ta jata,

tai sautin turjewa tana fadar.

A’a Kaka, bari in dauko mayafina mana”.

Ta ce, “To jeki maaza ki dauko, ina nan ina

jiranki” ,

Mahmud dake tsaye yana kallon su yai

murmushi kafin ya ce.

“Anyi haka kuwa Kaka? Ki shiga mana ‘ ki fara

zama tukun”.

kaka ta dalla mashi hararar da har saida yaji yan

hanjinshi sun motsa kafin tace

Wohoho su kaka manya

jama,a anya kaka zata bar wadannan ma,auratan

su huta kuwa Hmmm muje zuwa

RIKON KAKA

CHAPTER 28

Abubakar ya mike ya nufo inda

‘suke yana fadar; ‘ “D0n Allah Oga ta yaya ka

taho

mani da wadannan kayan rigimar?” ‘ ‘ Kaka ta ja

tsaki, “Ai k0 bai kawo ni ba ‘

wallahi ban barin garin nan k0 da zan mutu . .sai

na gano gidan nan, marar mutunci kawai”

Abubakar ya ce, “Ai k0 da na sanya’ maigadi ya

hadaki da kare ya raka ki har gida

Kaka ta ida rikice masu, “Eh, dama , iskancin ka

ai ya wuce haka Habu, ‘rashin imaninka da rashin

tausayinka ya zarce haka shi

yasa Kafata kafar jikata, bata yin zaman auren k0

dole ne?

Rukayya dake tsaye taiwaAbubakar

nuni da hannu alamar yai shiru, sannan ta kamo

hannun Kaka tana fadar.

“Zo mu shiga daga ciki Kaka kada ki biye mashi

ranki ‘ ya Baci” .

, Rukayya ta jata sukai dakin baccinta. -.

Abubakar .ya dubi Oga Mahmud yana fadar. . . ‘

“Ai fa yau na bani”. _ Oga Mahmud ya ce, “‘Haka

yau na wuni. ‘ ina rigima da ita ni da Madam

dana gaji da lallashin ta ne na ce ba zan kawota

ba, amma ta dasa mani kuka dole na kawo maka

,ita don haka sai ka samu ka lalabata da kalamai

ka “samu ku rabu lafiya”; , ‘

. Abubakar ya ce “An gama YallaBai”. . ’“ Sun

’dan jima suna hira‘ kafin ‘Oga’ , Mahmud ya tafi

bayan Abubakar‘ yai mashi rakiya ya dawo kai

tsaye dakin baccin . Rukayya yai tsinke. ‘ A

zaune ya .samesu Saman Carpet da .alama‘wata

rigimar ce suke yi da Ruqayya.

.Abubakar ‘ya‘ durqusa har qasa ya

gaishe da Kaka, Kaka ta dauke kai tana fadar:

kai”Ni ba gaisuwar kace ta kawo ni ba : kaji”

Abubakar ya saSsauta murya yana fadar.

“Allah Ya‘ huci zuciyar ki kuma sai kika yo tafiyar

dare haka maimakon ki kirani nazo da kaina na

daukoki?” .

Kaka ta» hayayyaqo mashi, “Motar banza gareka

‘motar wofi, da ka dauke ni da motarka ai gara

na taho‘ a qasa tunda kai ba mutumin kwarai

bane”.

‘ Ruqayyar tai saurin kallonta tare da Bata fuska

alamarbata jin dadin abinda take yi mashi, Kaka

ta banka mata harara

“Kike wani Bata fuska shegiya don ina kwatar

miki’ yanci shi ne kike Bata rai? To ba : zan fasa

ba”.

Ruqayya ta mike tana fadar, “To shi kenan, ki

cigaba‘ bari injr in hado maki abinci”. ‘

‘ Bata saurari abinda zata ce ba ta fice ta bar

Abubakar da rigimar ta. _ Kicin ta shiga ta jajjaga

kayan miya sannan ta kunna cookcr‘ gas ta dora

tukunya ‘ Farfesun ‘yan ciki ne tai mata wanda

yaji kayan yaji, sannan ta soya‘ mata indomie_

da kwai, ta koma ta tafasa mata ruwan zafi a ‘

‘flask ~ta dauka ta nufo . falonta Da mamakinta

sai ta iske Kaka ta Saki, Abubakar

na ta zuba’ mata uban“ dimi’ tana dariya.

Rukayya ta KaraSo‘ cikin falon ta ajiyeWa ‘ Kaka

abincin. Labarin “tafiyar Suhailat gidansu ne

Abubakar ke bawa Kaka. ” a’ Abin mamaki ta saki

lokaci daya har da

‘su dariya, Rukayya taja ta zauna tana fadar.

“Ga abinci nan kici kaka, kada ki biye

mashi yai sanyi”.

_ Kaka ta ja farantin ta soma ci ana hira, sai

aunawa Suhailat zagi take tana ‘roKon Abubakar

kada ya sake ya maida‘ ita. Shi‘

. kuwa ya samu yanda yake so, ya shawo ‘kan

‘kaka don. haka ya saki baki sai sheka uban

dimi yake, da wanda ma akai da Wanda ba ‘ai’ .

ba., . -‘ Ganin babu dama yasa Rukayya ta mike

tana fadar.

“Ni kam sai da safenka, bacci nakc ji”

Abubakar yace “Au ban gane ba, kina nufin don

Kaka tazo sai ki kyaleni na kwanta ni kadai

Rukayya ta dauke kanta tana fadar. “Sosai ma

kuwa”. Ya‘ kada kai yana fadar, “Ashe kuwa

zamu kwana a gado guda”. , Kaka ta dauki salati

cikin daga murya tana radar ‘ “Dawa zaka

kwanan tsohon marar kunya to Allah Ya tsare ni

yin kwai ban tanadi zakara ba. Kaji na gaya maka

ba dani ba Jika maza ki bishi ku tafi sashenku

sai da safenku”. ‘

Shi Abubakar ma dariya Kaka ta bashi,

‘yanda ta zage tana ta soko zance ta inda take ‘

‘.

shiga ba tanan take fita ba. Rukayya kuwa ,

haushi ne ya Rumeta don a yau burinta ta kwana

tarc da Kaka susha hirar su, don haka tun da

suka fito Abubakar ya tsaya jawa Kaka

kofa bata jirashi ba tai gaba abinta tana ta faman

gunguni

Bai shigo ba saids ta zira doguwar rigar baccinta

da ta gani ajiye a gefen gado sabuwa kar alamar

ya shiryawa, zuwan nata bangaren ‘ nashi a ya‘u.

taa haye kan gadon ta ja bargo ta luliuBejikinta. .

Abubakar bai shigo ba saida.yajé yai’, , sallama

da‘maigadi sannan ya nufo Bangaren nasa. Bai

‘yi mamakin ganinta da yai a * kwance duk da

yana da yakinin ba bacci take ba, don haka

hankalinshi kwance ya sauya kayan jikinshi zuwa

doguwar rigar bacci ya dauki turarensa ya fcsata

kowacce gaBa ta jikinsa sannan ya hayo kan

gadonYa kashe wutar dakin kafin ya kwanta

tsawon lokaci ya dauka yana faman saka da

warwara a . zuciyarsa kafin daga karshe ya kira‘

sunanta. ‘” “Rukayya”. Ta amsa a shaqe saboda

haushi da kuma kuma bacCin da ya fara kamata

Abubakar ya miqa hannu ya yaye lulluBin

da tayi yana fadar. ‘ “Barci fa kike koqarin yi, k0

kin manta ‘ da alkawarin. da kikai min?”

Rukayya ta bude idanuwanta wadanda suka

faraja, ta cr

‘ “Alkawari kuma na me?” Abubakar ya mirgina

daf da ita ya sa hannuwansa ya tallabo qeyarta

sukaiwa juna zuru na ‘yan daqiqu, kafin ya ce

“Yanzukina nufin har kin. manta da alqawarin da

kikai min za ki bani kanki? Haba Rukayya ‘na

soma tagayyara, plcasc ki ‘ taimakeni ki tausaya

min haka nan”. ‘

Gaban Rukayya ya yi wata mummunar faduwa, ta

fahimci abinda yake nufi don haka tai wani saurin

janye jikinta tare da juya mashi baya tana fadar. »

“Ni dai bahaka nake nufl ba, ka

kyaleni kawai inyi baccina”.

Abubakar yai sukuti yana kallonta, ta ja ,bargo ta

lulluBa‘bai da yanda zaiyi haka ya

kuma da ,baya ya kwanta. Bai da-burin ya’

takuraWa yarinyar k0 kadan, yana jin tausayinta

don haka ba zai iya yi mata komi ba sai da

yardarta.

Sai dai duk yanda’yake zaton al’amarin ya wuce

nan, don gaba daya bacci ya qauracewa‘idanu

wansa ya rinqa juye-juye har dare ya .raba

idanuwansa kyam, don haka’ ‘ ya mike ya fada

(toilet) ya dauro alwala ya fito ya soma jera

nafilfili na neman sauki a wurin Ubangiji.

Washegari tunda sukai sallar auba Abubakar ya

koma ya kwanta yana ta faman ramuwar bacci,

‘ita kuwa Rukayya tsam ta miqe ta dauri zaninta

saman rigar baccinta ta fito ta dawo Bangarenta

Bata shiga dakin baccinta ba kicin ta nufa ta

soma diminiyar hada abin karyawa

Doya Ce ta soya da kwai sai tai masu yam ball

sannan ta dama kunun tsamiya. Sai data gama

tsab sannan ta gyara falukan gidan

k0 ina da ina‘; hatta na sashen Abubakar din

wanda keta faman ramuwar bacci.

Karfe kawas da yan mintina Rukayya ta kammala

komai ta nufi dakin baccinta ta ~ ‘zaune ta samu

Kaka da ‘zurmemiyar casbaharta tana ta ja.

Rukayya ta waro ido tana tadar ., .

. . .-“Kai kaka, ba dai wai har kin tashi ba‘?” ,

Kaka ta ce”A’a ban tashi ba, sai yunwa ‘ta kashe

ni. Kuje ku kwashe wuri kuyi ta narkar bacci,

wato ni kuma da yinwa za’a horar ‘ dani ko?” .

Rukayya ta rike baki tana dariya, ta ce..“Wacc ni

da daura zani uwar miji-na yawo xindir? Wallahi

banyi tunanin kin farka ba, don tun dazu nagama

hada abincin karin

na tsaya na tsaya gyare gyare”. ‘ Kaka tace To

naji, kawo-mani nawa sarkin

. aiki”. “Rukayya ta ce”A’a bari dai na hada maki

ruwan wanka ki fara watsawa tukunna

., Kaka tace “Wanka’kuma tun uwar safiyar nan

‘sai kace wadda janaba ta hau. jika? To ban iya

wannan bidi’ar ba,kawo mani abincin idan naci na

koshi rana tayi nayi wankan”. ‘

Rukayya ta fice tana murmushi, rigimar ,kakakam

aisai ita. I . A kicin ta shirya kayan abincin gaba”

daya a .saman qaton faranti ta kawo mata, ‘ _

Kaka ta sauko saman carpet tana faman mita an

barta yunWa zata kasheta. ‘ ‘ ‘ Rukayya dai na.

jinta ta share ta

zuzzuba mata kOmai ta tura mata, Kaka ta

dubeta ‘

“To keba zaki karya bane Rukayya‘. ’” . Tai

munnu‘shi kafin ta ce “Sai goma ,_ tayi ke dai ki

fara karyawar ki”.

Kaka ta tabe baki ta soma karyawa tana fadar .

. “Ai ku .dai kuka sani indai kayan gulma ne ku

biyewa yahudu da nasara suyi ta . sauwwara

rayuwar ku Yanzu In ba haka ba

da kinyi kyan gani don wallahi duk macen dake

zama da kwarzabar miji indai bata Ci

_ tana koshi to yanzu ta lalace Rukayya ta ce “To

wai kewa ya ce

miki bana cin abinci.?_ Ta cE? “K3 tashi can, k0

baki zauna tarr

dani ba ina gani. Kin san Allah ki kula da kanki

kar ki sake kiyi wasa da cin abinci tunda dai

mijinki bai rageki da komai ba to karki sake

ki’bari ki .lalace, don irinsu Abubakar ne kesa

mace duk ta fita ‘ ‘hayyacinta, don haka ki dage.

Sai kuma kina yi kina gyara kanki, don dake wata

ce ki aika a siyo miki.

kaza da kaza da kaza da kaza

lol

« Rukayya nadai sauraron Kaka har ta gama

zayyano mata zancen sannan tai murmushi tana

fadar. “

“Lallai Kaka, kice abubuwan suna da yawa” _

Kaka ta ce, “Kadan ma kika Ji Jika, don akwai

saura ba ka_dan ba, irinsu sa maza kuwwa,

gumbar maza.. .ke da dai sauranSu”.

. Kaka ta datSe zancen saboda shigowar

Abubakar cikin dakiri

. Yana shirye cikin kayan tafiya (office)

‘ sai da ya durqusa ya gaishr da Kaka kafin ya

gefe ya zauna yana hararar Ru‘kayya wadda keta

faman gaishe shi.’ Rukayya ta zaro ido tana

fadar, “To ni kuma me nai maka yaya Abbakar

kake. hararata?”

. Ya~ce, “Au, baki ma san abinda kikai mani ba

kenan? kina jinta fa Kaka? Bayan bata tayar dani

ba ta barni ina’ta sharar barci har na , kusa

makara wurin aiki, sannan bata hada mani

. k0 ruwan wanka ba’ ballantana ta ciro mani

kayan da zan saka, amma wai batai min laifi ba”.

Kaka ta watsa mashi .kallo tana fadar. “Eh lallai

yai maka dadi, wato ka hanata barci da-daddare

kuma da safe kace duk ita ce zataimaka wannan

bautar? Lallai samun wurin :naka ma yayi yawa”:

.

‘. Abubakar yai dariya ‘yana kallon Rukayya

wadda ta dauke idanuwanta daga kansa, ya ce . ,

“Yanzu ita ce ta gaya miki na hanata ’ barcin k0

kuwa?” ‘

Kaka ta ce “Ban sani ba, marar kunya Ni idan ba

zaka karya ba tashi mujc ka maidani gida don na

gaji da zaman gidan nan naka da babu tsiyar

dake ciki sai rashin kunyar ka”. Abubakar ya kada

kai yana dariya kafin ya ‘ce. . “To ai ke kika

nema, haquri xaki yi ki bari sai anjima idan na

dawo daga (office) sai na maida ke”. , Kaka ta

mike tana fadar, “Wah! Ai dolen ka ma ka maida

ni yanzun nan, na gaji dai _ zaman gidan nan da

nake don na lura baka da ta ido”. ‘ Abubakar ya

saki hannun Rukayya da ya fakaici idon Kaka ya

rike ashe ta ankare, yaja tiren abinci gabansa ya

soma ci yana fadar. “To ai k0 abincin ai mun

haquri inci ‘tukunna ko~Kaka ta kyale shi ba tare

da ta sake tankawa ba ya cigaba da.cin abincin

amma gaba daya hankalinshi da Zuciyarshi suna ‘

wurin RUkayya sai a yanzu ya qare mata kallo

a cikin rigar baccin dake jikinta lallai Rukayya ba

qaramin kyakkyawa bace ‘

Tabbas ba ma kaka ba dake tsohuwa ba hatta

Karamin yaro idan zai kalli irin’ kallon da

‘Abubakar ke wurgawa Rukayya zai iya fassara .

shi da ma’anoni da dama.

Da kyar Abubakar ya gama karyaWar ya dauki

Kaka suka tafi yana‘faman mitar zata makarar

dashi. ‘

Suna tafiya rukayya ta fada (toilet) ta watso

ruwa ta fito ko .mai._;bata shafa ba ta zira milk

din doguwar riga marar nauyi komai bata shafa

ba ta dauki turarenta mai sanyin kamshi ta fesa

tabi lafiyar gado. ‘_

Misalin karfe shidda ‘ na yamma Abubakar yana

zaune a (office)_dinshi hadari ya soma har

haduwa da alama kuma idan har ruwan ya

kaucewa mutum akan hanya to zai gane kurensa

don da alama ruwan zai zuba bada wasa ba. . _

Abubakar ya qurawa sararin samaniya ido ta

tagar (office) dinshi yana kallon yanda hadarin ke

ta haduwa samaniyar tayi

baKiKqirin-sai iska ke tashi tare da buji mai karfl.

Abubakar daya tura kanshi a saman karfen tagar

yanajin’ wani irin abu na tagaya . mashi. zuciya,

son Rukayya ‘ne‘ k0 kuma sha’awar kasancewa

da ita ne oho.

Shi dai abu daya ya sani shi ne ‘idanuwanshi na

bukatar’ ganinta hancinshi na bukatar shakar

daddadan kamshin jikinta, burinshi kawai ya

rungumeta da hannayensa ya hadata da jikinshi,

shi k0 hakan kadai ya samu buKatarsa ta biya.

‘ Kamar Wanda aka tunzura yai baya da sauri ya

soma harhada takardunsa da duk wasu

komatsansa ya cusa a jaka ‘ya zuge ya rataya

ya . suri mukullin motarsa ya fice

Da gudu-gudu ya nufi motarsa, yasa makulli ya

bude‘ motar ya shige saboda ruwan da ya fara

saukowa. A gurguje ya iso gidan nasa, a lokacin

kuma ruwa ya kece kamar da bakin kwarya.

Don haka lokacin da ya ‘faka motarshi a harabar

gidan da gudunsa yashige falon gidan

hakan kuWa ya yi dai dai da‘ tahowar Rukayya ,

~ da zummar ta zuge labulayen ”kofar sukai .

karo da Abubakar wanda ya shigo da gudu,’ ‘

goshinta ya bugi kirjinshi. Tai saurin komawa

da baya dafe da goshi tana fadar ‘ “Wayyo Allah

na, kai Yaya”. ‘ Abubakar yai saurin janyota

jikinshi < yana fadar “Ayya, sorry baki‘ ji ciWo ba

k0?” Rukayya ta shafo goshin nata da hannunta

ta ‘ dubi Abubakar yai dariya yana fadar .

“Saboda sharri wato har kirjin nawa ya isa ya.

fasa miki goshi . . Murmuishi tayi tare da kokarin

zame

jikinta amma taji ya qara damqota a jikinshi yana

fadar Ina’ zaki Je kikr sauri haka?“.. .‘ Kofa ta

nuna mashi don ta ka’sa

magana saboda irin riqon da ya’ yi mata a’

jikinshi i

Abubakar ya juyatana jikinshi, ya rufe

kofar da key sannah ya nufi sashin shi da

Rukayyar yana fadar‘ ‘

“Muje ki tayani in canza kaya kada

masassara ta kamani “

Rukayya dai bata iya cewa komai ba ya jata har

bedroim dinshi’ yai mata masauki a saman

bedside chair din dake gefen gadon, sannan shi

kuma ya dauki jallabiyya ‘ya nufi (toilet), bai yi

minti goma’ ba ya filo sanye da jallabiyyar a

jikinshi, ya dubi Rukayya dake

takure a saman kujera yace. “My Ruky, kije ki

dauro alwala kizo

muyi sallar magaruba~ tarc da nafila ta nunawa

Ubangiji godiya”.

‘ Rukayya bata tanka mashi ba ta miqe taje ta

dauro alwalar ta filo ta iskeshi a tsaye yana

jiranta, ya miqa mata hijabi ta‘ saka sannan ‘yaja

su sukai sallar su tare da isha’i da . kuma

Shafa’i da wutiri.

‘ Suna‘ idsrwa Abubakar yasa Ruqayya taje ta

dauko masu abincin darrnsu suka ci sannan ‘ ‘

suka sake yin brush. Rukayya na fitowa daga

(toilet) din da tayi brush din ta nufi hanyar ficewa

daga dakin.

AbUbakar yai tsalam ya cafkota ta hadu jikinshi,

ya rungumeta yana fadar.

‘ “Ina kuma zakije cikin daren nan?”

‘ “bako ina

Ta bashi amsa muryarta na rawa saboda .

tsananin firgici. Abubakar ya dora

kanta a kirjinshi yana shafar gashin kan nata cikin

nutsuwa ya soma fadar. Kiyi hakuri Rukayya don

Allah daukar alhakin kada yai yawa nasan nayi

laifi amma na tuba ai min afuwa don Allah.

Wallahi ina sonki Rukayya ina buKatarki, please

feel free with me. Please ki taimaka mani,

please..; pléasé Rukayya’. ‘ Gabadaya ya gama

kashewa Rukayya ‘jiki, duk wata tsiga ta jikinta

sai da tatashi, bata da sauran burin da ya wuce

ta mikawa Abubakar kanta tana mai farin~ ciki

tare da . alfahari da hakan. ,_ ‘ ‘ ‘ ‘ Abubakai yai

amfani’ da duk wata ‘kwarewa da soyayyarsa ya

mallaki Ruqayya cikin salamaa ba tare da ya

Wahalar da baiwar

Allah ba, don haka hankalinta’a kwance take

sharar baccinta inda shi ya gagara runtsawa

Hawaye ke bin kuncinsa .na farin ciki

irin wanda bazai misaltu ba, ya godewa Allah

har bai san iya adadi ba. Shi da kanshi ya san

ya‘ zautu’, ya kuma zare Rukayya ta gama

gigitar dashi. Shin da me iya godewa Allah? Da

wane bakin zai nemi tuban butulcin da ya so yayi

akan baiwar da Ubangiji Ya yi‘ mashi? Lallai. da

bai samu Rukayya ba da‘ ya kasance a cikin

mazan da sukai rakiya a dunjya. ‘

HEHEHEHE SU HABU MANYA DAMAN DADIN

AURE NASA MUTUM yaji hawayen murna na zubo

masane ?

jama,a ku tauani duba

naku har kullum A,I,S KE CEWA BARKA DA

HUTUN QARSHEN MAKO

RIKON KAKA

CHAPTER 29

‘ Abubakar ya rinqa ririta Rukayya yana

shagwaBa ta hade da -lallashinta har garin Allah

ya Waye, bai Barta tayi komai da kanta-ba, dai _

dai da wanka shi yai mata da kanshi, haka A

abinci da hannunshi ya bata yana qara tattalinta

da lallashinta. Rukayya kuwa jinta take tamkar

zara a cikin taurari, ita da kanta ta tabbatar ita

wata ta dabance a cikin mata mai baiwar da ba .’

kowacce mace bace ke da‘irintaba; don haka

taiwa Allah godiya don ta san ba roqonshi

ba ya bata, :kuma wadanda basu sami irin nataba

suma ba laifi sukai mashi ba ya hana su.ba

Bayan wata guda duk wanda ~ya kalli Abubakar

yasan ya samu canjin rayuwa,’ yai wata kiba

kamar bashi ‘babya qara sauyawa ya zama wani

na daban a cikin ‘yan uwansa maza.

Duk wanda ya kalle shi yasan. yana samun‘

tallali da kular data dace ‘a wurin matarsa,‘ don

Shi kanshi bai san haka rayuwar aure take da

dadi .ba sai yanzu. Ashe da can ‘ haukan banza

yai‘ tayi ga inda dadin auren yake‘yaje yana ta

wahala a wani ‘wuri can.

‘ Shi da kanshi ya_maida ‘ta makaranta‘aji

shidda zafa Zana jarrabawar aji shidda Wadda

zata bata_ damar shiga babbar makaranta don

yin karatu mai zurfi.

***************

Bangaren Suhailat kuwa al’amura sun gama

dagule mata duk yanda ta motsa al’ amarin

ba haka suka kasane mata ba

don kuwa a ranar da abubakar yaje har gida ya

fadama mahaifin suhailat din abinda ke faruwA a

tsakaninsa da Suhailal din a ranar ya dauki

mataki yaje da kanshi ya ce ta koma gida

zai rufe gidan ya zuba’ yan haya . . Abin ya bata

mamaki, Sai dai bata da

damar yin magana don bata ga fuska a wurin

mahaifin nata ba, a’dolenta taja bakinta ta tsuke

ta dawo gida kwana daya, kwana biyu tana zaton

mahaifinta zai kirala yaji ba’asin ‘ abinda ya

hadata da Abubakar din daga bakinta, amma

bai’nemeta ba ta kuma sani duk abinda ya faru

Abubakar ne ya shirya matA makarkashiya.

Sati daya, sati biyu har. zuwa wata daya babu

wanda ya ce Suhuilat ci kanki. ‘ta soma ‘damuwa

ta shiga matukar tashin hankali kewar’mijinta ta

fara damunta tun tana boyewa har ta soma

gazawa ta fara yiwa momy dinta maganar amma

sai cewa tayi babu. ruwanta, taje taiwa

mahaitinta magana.

Suhailat ta kasa tarar mahaifinta da zancen har

saida takwashe sati guda, ganin

babu sarki <inba Allah ba Yasa Suhailat ta samu

mahaifinta tai mashi maganar.

‘ Amman sai ’da taji da ma bata jeba saboda

yanda ya rufeta da masifa ta. ta inda yake shiga

ba tanan yake fita ba daga karshe ma sai cewa

yai Abubakar yake jira idan ya gaji da qin

kumawarta gidansa ya aiko mata da lakardar

saki. ‘

Abinda ya dagawa Suhailat hankali kenan, ta sani

babu abinda ta rasa a gidanta sai tattalin miji da

soyayyar da bata faduwa. Lallai dole ta shiga

cikin matukar firgici, to amma yaya za’a ce babu

wanda’ zai kira Abubakar balle a sasanta su ta

koma gidanta? ldan ma hakan bata samu ba ‘ai

sai a tura manya su rakata, ya za ai aCe ita

kadai zata koma gidan Abubakar‘? Anya idan akai

mata haka an mata adalci kuwa? Anya ba‘a nemi

kwararar mata da aji ba a idanuwansa?

‘ Wannan ne k’esata tai ta kuka ba‘bu mai

lallashinta, shin wai waye ne zai fahimci halin da

take ciki‘.’

Bayan wata biyar Rukayya ta kammala zana

jarrabawarta ta fita sakandire ta zana jamb

Abubakar ya samar mata gurbi a’ Jami’ar Umaru

Musa ‘Yar Adua zata yi karatu a bangaren

likitanci (MediCine)._ ‘

Rukayya karatu ya kankama don ma laulayi da ya

matsa mata, sauqinta ma daya Abubakar na

taimaka mata da wasu aikace~ aikacen. ‘ ‘

Cikin wata goma cikin Rukayyay ya fara fitowa,

Abubakar ya bar mata motarshi shi kuma ya siyi

sabon mashin Motobi yana hawa kafin Allah Ya

qara buda mashi ya sake siyen ‘wata motar

shima ‘ Rukayya ta zama wata zara a cikin

taurari ta canza, ta sauya, ta xama wata daban a

cikin mata duk wanda ya kalleta saiya so ya sake

kallonta saboda yan’da ta zama wata ishasshiyar

mace ‘mai ta‘qama da namijin maza, da kuma

matakin ‘karatun .(dcgrce) ”wanda take akai.

‘ Cikinin rufayya ya shiga watan haihuwa don

haka ta dauki hutu a makaranta, don likita ‘

ya tabbatar mata nan da kwana biyar zata iya

haihuwa.

. A yanzu hak-a a zaune take saman’ carpet tayi

dai-dai .Abubakar yana zaune a gabanta yana

yanka’mata’tufa (apple)_ yana Saka mata ” a

baki aka kwankwaso kofar falon: Abubakar ne ya

bada izinin shigowa, sai dai wa zasu gani? » ~ .

Suhailat ce ta sha lullubi,kafadarta . _ rataye da

qatuwar. jaka, dayan hannun kumana

jaye da qaton akwati K0 dar Rukayya bata ji ba

lokcin da taga shigowar Suhailal din,Abubakar

kuwa zabura . ya yi ya mike, ya daga murya yana

fadar. “Lafiya? Me ya kawo ki gidana?” SUhailat

bata tanka mashi bahar ta Karaso sannan ta

soma fadar ’ ‘ “D0n Allah Abubakar kayi hakuri ka

mantada, abinda ya faru nasan nayi laifi kuma

nayi

nadama ka yafe min

Abubakar ya ce, “To amma neman gafarar ne har

sai kin biyoni cikin gidana?” Suhailat ta dago kai

da sauri tana kallonshi da idanuwanta da suke

zubar da hawaye Ciki” tsananin kaduwa ta soma

girgiza’ kai tana fadar.: “Abubakar, kar kai min

haka,’ka yafe min don Allah tunda na gane

kuskurena. Wallahi na gaza jurewa rashinka

Abubakar, ba zan iya rayuwa babu kai b_…”..

Kuka ne yaci. qarfinta, ta ja kafafuwanta wurin

Rukayya ta rungume kafafunta tana kuka da

hannu alamar ta taimaka mata.

Shi kuwa ‘Abubakar tsaki yaja don haushi ma ‘

take bashi. Ruqayya ta dafa Suhailat tana fadar. .

“Ya isahaka Suhailat, ki daina”. ,

Suhailat ta ‘ dago’ kai tana kallon Rukayyar cikin.

kuka ta soma fadar. .

“taya xan iya daina kuka Rukayya ‘ bacin son

zuciya ta da hudubar shaidan sun rinjayrni na

rasa mijina’na janyo haushin iyayena akaina?

Rukayya Ya Ya za ai in daina

na ‘zalunce ki saboda ‘ son zuciya kawai?”

Rukayya ta kyara mata kai tana fadar.

“A’a ki daina fadar, na yafe miki kuma Abubakar

ma ya yafe miki, kawai dai .yana cikin Bacin rai

ne nasan zai haqura”.

Rukayya ta takarkare ta mike da kyar tana kallon

AbUbaKar wanda_ ya bade mata fuska, ta matsa

daf dashi ta riqo hannunshi ta

‘ . riKe’ ta soma magana muryarta a sanyaye.

“Don Allah Yaya na ka zamo mai yafiya da kuma

karBar uzuri ga wanda yai maka ba dai dai ba. Ka

dubi Suhailat ta tuba tayi nadamar abinda ta –

aikata, ni na yafe mata kaima ka yafe mata ka

karBeta‘sai kaima Allah Ya yafe maka

kurakuranta wanda ka sani da ma wanda baka

sani ba

Abubakar ya. danyi shiru yana ‘wani nazari,

Rukayyata girgiza hannuwanshi tana fadar.

‘ “Please Yayana, plcasc”. Abubakar ya sauke

numfashi yana fadar.

“‘Shi kenan,’ na yafe mata saboda ke ‘Rukayya,

ina sonki kinfi qarfinkomi a wurina, babu abinda

bazan iya yi miki, ba a duniyar nan. Rukayya na

yafe mata”.

Wani irin farin ciki ne ya lulluBe Suhailat, ta

rungume’ Rukayy cikin matukar soyayya ‘da

qauna. Rukayya ta cika mace ta gari tunda har.

ta amince da sadata da farin cikinta, wato‘

Abubakar.

ltama Rukayya ta “saki rai da zuciyarta

‘ suka rungume juna ita da Suhailat suna masu

.yarda da aminci da Juna. ‘

. Abubakar na tsaye yana kallonsu bakinshi dauke

da murmushi, zuciyarshi na fatan su kasance a

haka har qarshen rayuwarsu ‘

MASHA ALLAHU.

ALHAMDULILLAHI.

MU HADU A WANI SABON LITTAFIN IN ALLAH YA

YARDA KUDAI KU KASANCE DAMU A KODA

YAUSHE

Series Navigation<< Riqqon Kaka Chapter 5
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *