Sanyi da Zafi Hausa Novels

Sanyi Da Zafi Part 2

This entry is part 2 of 4 in the series Sanyi Da Zafi by M Shakur

💫 SANYI DA ZAFI 💫

EPISODE 2️⃣

✍🏻M SHAKUR

Kusan gudu gudu, sauri sauri yake tafiya acikin airport din bai damu da bala’in gajiyan dayayi ba sabida economy ticket yasamu bama business ko first class ba, tunda aka haifeshi yaune first time daya taba flying economy, kafafunshi sun sandare abunka da mai tsawo sunma kumbura.
Fitowa yayi daga arrival yafara tafiya dan zuwa wajen parking motoci wasu mutane biyu biye dashi abaya dake sanye da suit bakake da glasses akan idanunsu, lift yashiga harya danna 2nd floor kofan zai rufe mutane biyun suka sako hannunsu ciki kofan yakoma yabude dan dago kanshi yayi yaga wani black mutum ne yana sanye da suit baki ga wanima exactly irin kayanshi suka shigo elevator din suka danna boturin dazai rufe kofan, kofan yarufe yafara moving sama, dauke kanshi yayi daga kallonsu yadaga hannunshi dake daure da agogo na Rolex dan duba karfe nawa yanzu hakanan yaji bai natsuba amman yadake yana tsaye inda yake rikeda bag pack din dake rataye shoulder nashi that is very fine and unique dan babu kalan su ma a Nigeria, hannu daya daga cikinsu yakai ya danna lock elevator ya tsaya chak tareda juyowa yana zaro wani wuka daga bayanshi in seconds yakai zai chakamai aciki chak Matashin yarike hannunshi yana kallonsu cikeda fargaba da tsoro da komima, dayan mutumin shima yaciro tashi wukar yace “au gardama zakayi bazaka bari mu kasheka ba salin alin mu karbi ragowan payment dinmu” shima yaciro wata karaman wuka zai chakamai kwasheshi yayi da kafa yafadi akasa wukar tafadi zai dauka yatake hannunshi da boot din kafanshi, yawani lankwasa hannun wanda yarike tareda sa kafa yadakeshi a balls dinsa cikeda azaba gayen yayi ihu yayi baya yakama gaban wandonshi yanaji kaman zai mutu da sauri guy din yasa hannu yabude kofan elevator din baimasan wani floor bane suke kawai yafice dagudu gudu sauri sauri dayan dake kasa yatashi yace “call the rest bari nabishi” yafice yabar wanda ke rike da gaban wando yana kokarin kiran waya, yashiga gudu shima yana binshi abaya, sosai yake gudu ganin daya yabiyoshi yanakai hannunshi cikin wando dan ciro wayanshi yakasa kawai yahau staircase yashiga sauka yana kallon baya jin gudun sahu dayawa ana biyoshi dudda baya ganinsu dan basu riga sun hayo benen ba ganin wani kofan restroom na mata dan ansa ladies ajiki yasa kawai yabude kofan yafada jiki wani kalan mugun karo sukaci dan tana shirin fita ne tai tangal tangal zata fadi da bala’in sauri ta dafa bango shikuma yajuya ya tura kofan bayin dasauri tareda saka sakata na sama da kasa yana kara murza jam lock sannan yajuyo daidai tana dagowa tana shafa goshinta cikin tsananin fushi dan tadan buge kuma taji zafi zatai magana, cikin a very soft yet anxious voice guy din yace “please ki boyeni some guys naso su kasheni ne and call the police” dudda taji zafin bigewan datayi amman ware manya manyan dara daran idanunta tayi kaman fitila tana kallon mutumin dayashigo cikin bayin mata da ranan nan Allah yaso ba kowa ciki ma, farin guy ne bawai irin fari sosai dan zata fishi haske but yanada normal fair skin not black skin, dogo wanda akalla zaiyi 34-35 ko 36yrs hakanan, baida kiba at the same time baida rama, yana sanye da riga na latest collection na Dior fari yadaura wani leather brown jacket asaman sa da yabar boturan abude bai rufe ba hakan nasa kana ganin farin rigan ciki, saikuma yasa jean na Rick Owens, sai wani boot dake kafanshi brown na Tomford mai bala’in kyau da agogo daure a writs nashi na rolex, yanada very very dark hair dake nan kwance so wavy, dark eyebrows da eyelash nashi yamafi na wasu mata yawa, ga dan gemu dayake dashi da saje acike dudda gemun baida tsayi sosai looks like yana trimming gemun dan hair na wajen gabaki daya na dsame length, lips nashi are full irin asalin masculine lips that are a bit pinkish, idanunshi sunyi jaaa sosai, ganin yanda take kallonshi yasa yace “call security” hankalinshi atashe yadanna kofan da hannunshi yana kallon kofan jikinshi nadan rawa kana gani kasan da gaske he’s in trouble jin gudun mutane dayawa haka ga maganan su yana tashi kasa kasa “baku ganshi ba? We have to kill him ance kar mubari yakai gida araye wannan kofan fa kunduba ciki ko ya boye wajen”? Hankalinshi atashe yajuyo yana dan zaro idanu hakan yasa itama gabanta yafadi bayin tashiga kallo kafin idanunta su sauka kan cart din garbage can dake wajen wanda take juye dattin bayi aciki ta gungura tafito dashi takai bola, daga kafanta tayi without making sound taje ta tsaya kusada can din tasa hannunta ahankali tabude marfin sannan tadago kanta daidai sun fara knocking kofan zaro idanu yayi da sauri ta nunamai can din da hannu alamun yazo yashiga nan da sauri yazo ya tsaya kusada ita yakalli bolan cikin can din wani kalan yatsinewa cikinshi yayi yaji kawai amai yatasomai da sauri yadaura hannunshi kan bakinshi jin aman zai fito, tazaro idanu tana kallonshi yau da babuma wani bolan kazanta sosai ma shine zaiyi amai lallaima, daidai an kara knocking dasauri da murya kasa kasa tace “kaga idan bazaka shigaba nifa ba ruwana, kafita ni nacigaba da aiki na, I don’t have any security number I don’t work here yau kawai an kirani nai replacing wata ne just for today” juyo da kanshi yayi yakalleta itama kallonshi tayi da manyan idanunta kusan iya kirjinshi tsayinta ya tsaya daidai anyi mugun knocking kaman za’a balle kofan baisan lokacin dayay tsalle yafada cikin trash dinba yasa hannunshi yana kama hancinshi lekowa tayi takalli ciki yanda yakeyi yasa tai dariya dayasa fararen hakoranta suka bayyana more of dariyan mugunta tace “yi bacci toh” kallonta yayi yanda take dariya dimples nata na lotsawa bama ta tsoro yanda kasheshi akeso ayi, bama ta tsoro tana mace itama sujimata ko su illatata, he’s just staring at her da suprise, jakanta dake kan slap ta kalla saita wuce da sauri tabude taciro wani black gyalenta na abaya tazo wajen ta warware ahankali ta yafa kanfuskanshi, wani irin lumshe idanu yayi jin kamshi mai sanyi daya sauka kan fuskanshi mai ni’ima in this moment na wari dayake ciki sai kuma ya sauke gyalen da sauri ya kalleta yace “wat are you doing?” Tana kallon kwayan idanunshi itama ba kunya ko shakka tace “datti zan watsa akanka yanzu so brace up” takai hannun tadauki thrash can dake kasa wanda bata riga tajuye dattinshi ba kawai tajuye asaman kanshi tana murmushi ganin yanda yake kallonta kaman zai rufeta da duka tace “I am saving your life here it’s your choice” wani kalan ijiyan zuciya yake saukewa tsigan jikinshi natashi da kyar yaja gyalenta yarufe fuskanshi dashi yana rufe idanun duka dan yakasa standing dattin datake watsamai akai ta ijiye can din tasa hannunta dake sanye da working glove nata ta kwashi sattın ta rurrufeshi da kyau sannan ta rufe marfin tadan sauke ijiyan zuciya cike da karfin hali tawuce tai wajen kofan tabude cikeda masifa tace “wai waye ke knocking haka ina aiki”? Ganin maza kusan biyar yasa tadan koma baya kadan ta tsaya chak tana kallonsu dudda gabanta na faduwa bata nunaba dukansu kallonta suke ganin wata yarinya da akalla zatai 22yrs haka tana sanye da cleaners uniform riga da wando ash color tasa wani karamin farin hijabi daya tsayamata iya kirji hannunta sanye da glove kafafunta sanye da rain boot, cikin rashin tsoro tace “baku iya karatu bane duk girmanku ku gane ladies restroom ne nan”? Dukansu kallonta suke ganin yanda take musu magana gata wata kalan kyalkyawan yarinya fara sol saidai akwai uban baki ga rashin kunya ga muryanta shegen zaki kaman zai fasa dodon kunne, babban ne yahade rai yace “ke wani bai shigo nan ba”? Wani kalan matsiyacin kallo tamai tace “kai nan wajen yamaka kama da inda wani zai shigo”? Dukansu baki suka sake suna kallonta daya daga cikinsu yace “ke kinsan waye mu kike mai rashin kunya”? Tana kallonshi tace “kai kasan wayeni zakuzo ina tsakiyan aiki na bayan nayi stating agaban kofa working no entry kunzo kuna bubbugamin kofa kuna maza toh ubanme kukazoyi nan kuje men restroom mana, I will call security wlh” kallonta Oga yayi this loud girl can ruin work nasu ta tara musu jama’a yanda take this vocal ma killing her will never be easy still saita tara jama’a, they don’t want scene hakan yasa yace “please let her be she’s crazy, I don’t want problem, ku rarrabu kuje mu nemoshi ni nasan yana floor din nan” tsaki tayi tace “mahaukata kawai” dukansu su shiddan juyowa sukayi suka kalleta wlh ko dar batajiba tasa hannu ta maida kofan ta buga tarufe tadauki wayanta ta danna waka tamaida earpiece tacigaba da mopping kasan wajen wanda shiya rage mata dama tariga tagama wanke cikin bayukan yanda takebin wakan tana aikinta bata missing any verse wlh zaka dauka mawakiya ce kuma da karfi take wakan abinta..….

Dudda yanajin warin bolan dayake ciki kaman zai kasheshi ga tsoron dayakeji but hakanan muryanta da yanda take wakan hold on na calming nashi down sosai, muryanta yamafi na asalin wanda yayi wakan dadi, what a voice! Tass tagama aikinta ta jingine komi inda zata jingine sannan tadauki jakanta tarufe tagoya abaya tasa hannu tabude kofan bayin hada ido tayi da maza biyu daketa sintiri awajen ta ballamusu harara tacire board na close dake gaban kofan bayin takoma ciki ta ijiye sannan ta gunguro garbage can din da kyar sabida nauyi amman ta daure tafita tafito dashi ko kallonsu batayiba saima wakanta data cigaba dayi abinta tawuce tasauka har kasa tazaga baya inda suke ijiye dattin saida ta jujjuya ganin babu kowa yasa tabude marfin bolan batare data kalli cikiba tace “you are safe yanzu you can come out” kafinma ya yunkuro tajuya abinta tahau tafiya dan sauri take is already 3:30 by 4 zata shagon abinci gashi this whole drama yabata mata lokaci, da kyar ya iya ya lallaba yafito daga bolan sai amai duk wani abu dayaci saida ya amayar dashi sai kakkabe jikinshi yake yadago zai mika mata gyalenta daidai tanashan kwana harta tafi, he wanted to say thank u dudda she’s a crazy wicked girl tana zubamai dirt tana murmushi but she helped him, hannunshi yakai aljihunshi yataba but baiji wayanshi ba kuma baisan a ina ta fadi ba wlh kuma shi bazai duba bolan nan ba, daidai wani cleaner na gunguro nashi bolan dasauri yace “please bani aron wayanka nakira” binshi yayi da kallo ganin kaman ba lafiya yasa yabashi wayanshi Munir yakira kafin yayi magana yace “Munir kazo ka daukeni a airport pls karka fadama kowa kana zuwa katambayi wajen zuba bola ina wajen” kafin yayi magana ya katse wayan yabama yaron yazauna awajen kawai feeling terribly sick kusan 1hr yana wajen jikinshi yadau mugun zafi ga tsigan jikinshi na tashi kaman zai mutu yana zaune ahaka yaji ance. “Riyad” dasauri yadago kanshi da gudu gudu sauri sauri Munir yataho wajen yace “what happened to you like this? Wat are you doing here? Why are you so dirty”? Tashi yayi yana kokarin yima Riyad magana yace “someone tried to kill m…..” kawai ya sume da kyar Munir yasamu wani cleaner yazo kawo datti shima aka tayashi daukanshi suka tafi mota aka sashi sai gida bayan yakira Mom akira Dr.

Tawani special secret gate Munir yabiyo aka budemai already ga mutane tsaitsaye Gwaggo (Mai Babban daki) gawata black beauty mata dake sanye da hijab mai dan kiba (Mom), Wambai, Waziri, Kabeer da su Halilu, Ibrahim da Shuaibu, Baffa Mujitapa dukansu suna wajen da family Dr nasu, yayi parking agurguje Munir duk sukai wajen fashewa da kuka Mom tayi tace “what happen to yarona Munir? Wakeson kashemin shi daga shigowanshi garin nan? How did they even know ya shigo? Gwaggo jini a hannunshi look, Doctor do something” Mom tai maganan tana kama hannunshi ashe wukan ta yankeshi dazu, atare dukansu mazan suka ciccibeshi zuwa wani dabkareren flat na Mom Gwaggo tace “meya sameshi haka Munir? Jibi jikinshi? Meya faru Munir”? Dasauri Munir yace “Gwaggo nima bansani ba but kaman he was attacked ne, yana kokarin fadamin wai ana kokarin kasheshi ya sume ba wayanshi taredashi, shi babu akwati, akusa dashi, awajen bola naganshi da bag pack yana mota dawani dan kwali black, kafin yafadamin komi kuma yasuma” gam Mom tarike hannunshi har daki kan wani taskeken gado aka kwantar dashi Dr yashiga dubashi yanda skin nashi da fatanshi keyin wani bororo dahar wani motsi suke yasa yace “a chanzamai kayan jikin nan nashi maza, ku goggogemai jiki with clean towel, allergy ke damunshi, he’s allergic to dirt da kazanta right from small, kuyi sauri pls” fita kowa yayi daga dakin akabar Munir da Mom, Waziri da sauran duk suka zauna a falo yace “wazai attacking yaro daga durowan shi kasan nan?” Anatse Wambai yace “call the police I think sai anbincika airport din maybe ta CCTV za’a gani” faduwa gaban Kabeer yayi amman yadaure yaranshi always do a clean job he hope bazasu kwofasashi ba, fitowa Munir yayi yace “Dr an gama” dukansu komawa ciki sukayi Kabeer sai tsaki yake aranshi shida yakeso kowa yaji haushinshi amman jibi yanda kowa ke nan nan dashi, attention yakoma kanshi ma infact, skin nashi gabaki daya yakoma so red, drip akamai fixing da allurai ciki Dr yakalli Mom datafi kowa damuwa adakin yace “anjima kadan zai farfado don’t worry” dan murmushi tayi tareda gyadamai kai Waziri yace “ki zauna dashi” Gwaggo tace “nima ina nan kome za’a kawomai kowa zaizo yadubashi saina ganshi inga uban waye keso ya cutar mini da jika, bangama kukan mutuwan d’ana ba yanzu halakamin jika za’ayi wlh jinina yasha karfin kowa” kallon Munir Mom tayi ahankali tace “thank you Munir” gyadamata kai yayi yawuce yafita daga dakin hakan yarage daga Gwaggo sai ita, dafata Gwaggo tayi tace “ki tsare yaron nan ki dage da addu’a akanshi, tun ranan da aka haifi Riyad akace yanada taurari masu kyau kuma babban mutum ne shi, kiduba kigani yaran marigayi maza shidda amman shi kadai akeso ahalaka tun yanzu kenan bama asan waye zai gaji kujeran sarautan ba kenan amman so ake akasheshi balle kuma ace shine zai gaji sarautan ki tashi tsaye Maryama, saikin tashi tsaye, kinyi zaman gidan nan basai na fadamiki hadarorin dake cikinsa ba, inde kalubale ne yanzu Riyad yafara gani, idan kuma yazama Sarki yadinga ganin kalubale iri iri kenan har abada, ki tsare yaron nan, kizama idanunshi kunnuwanshi uwa uba kizama inuwarsa dakuma lullubinsa” gyadama Gwaggo kai Mom tayi takama hannun Riyad tarike gam tana kallonshi tace “Gwaggo meya musu Riyad dako zaman gidan nan baiso, na tabbata baimason ya gaji kujeran nan, dan bata gabanshi” Gwaggo tace “kwarai” Mom tace “shi kadai Allah yabani, shi kadai gareni, Riyad kadai Allah yabani yau ana kokarin rabani dashi” kankame hannunshi tayi tace “Gwaggo zan iya zuwa bangon duniya sabida Riyad! Kuma nayi alkawari duk Wanda yace zai cutar da yarona saidai yafara dani dan daga yanzu zan zama shamaki tsakanin Riyad da komi na duniyan nan, zan zama inuwa hazo zan lullubeshi nakuma kareshi daga duk wata hari” sosai Gwaggo take kallonsu sai kawai tai murmushi tadauki charbi ta tacigaba da ja itama bini bini tana tofama yaron addu’a aka.

Series Navigation<< Sanyi Da Zafi Part 1Sanyi Da Zafi Part 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *