Sanyi da Zafi Hausa Novels

Sanyi Da Zafi Part 3

This entry is part 3 of 4 in the series Sanyi Da Zafi by M Shakur

💫 SANYI DA ZAFI 💫

EPISODE 3️⃣



✍🏻M SHAKUR

4 daidai tashiga wani babban kanti na abinci irin local restaurant din nan, wata katuwar mata dake zaune a tsakiyan shagon kan kujera ga lalitan uban kudi a hannunta tana kirgawa ne ta kalleta tace “Allah yasoki baki latti ba” batace komiba kai tsaye tace “ina wuni Maman Miwa” batare data amsaba tace “nidai je ga wanke wanken ki chan na jiranki” bata damu da yanda tamata maganan ba dudda akwai mutane a shagon sunacin abinci tace “bari nai salla naje nayi” bata jira amsanta ba tawuce ciki chan bayan gidan shagon bayi taje tacire kayan jikinta tafito da dogon riga na abayan dake jakanta tana neman gyalen ta tuna tabawa mutumin nan tsayawa tayi chak sai kawai taja gajeren tsakiya saurin datake tazo nan yasa ta manta bata amsaba, karamin farin hijabin tasaka ta dauro alwala tafito tasami waje tai salla sannan ta cire hijabin tasa kan igiya fari ne batason ruwan wanke wanke ko mai ya bata mata taje gaban makwarara, ga wanke wanke zaka dauka na gidan biki ne ga manya manyan tukunyan abinci, omo ta dauka ta tara ruwa abaho dukta kawo sannan ta dauki wayanta kirar vivo duk taci screen tasaka earpiece ta danna waka ta soke wayan aljihun dogon rigan tashigayin wanke wanken da sauri sauri dan tanada kuzari sosai batada kasala ko son jiki.
Wata yar budurwa ce tazo wajen ganinta tana wanke wanke tana waka kasa kasa like zero worries dinnan yasa ta harareta tajuya tafito tadawo cikin shagon tazo gaban mahaifiyarta dahar lokacin take kirga kudi tace “wai Mama Yar gidan HIV dinchan kikesa take mana wanke wanke har yanzu banace ki sallameta ba gashi gashi abinda ake cewa ita da Mamanta sunada shi” batare da maman ta kalletaba tace “koyar gidan kanjamau ce ba HIV ba ina ruwana ko kinada wanda zaki samo dazatamin wanke wanken nan ta share ko’ina har zuwa katon shagon nan akan dubu biyu kullum aduk fadin garin kanon nan?” Baki yarinyar tabude zatai magana Maman Miwa tace “kinga ki kyaleni fa, nagadai nace kiyi aikin nan bayi zakiyi ba” dasauri yarinyar tace “Mama ni kyamanta nakeji wlh, sunada HIV tana mana wanke wanke” dasauri Maman Miwa tace “wai sau nawa zan gayamiki Maman ta kedashi ba itaba yarinyar datake karatun likita, to koma tanadashi me ruwana nagadai ciwon nan ajini yake kuma baya kwarara acikin ruwan wanke wanke ko? Miwa dan Allah ki barni na kirga kudin nan kinatasa ina mance abinda na kirga” tsaki yarinyar tayi tawuce tafita daga shagon cikeda bacin rai.
Kafin 1hr tagama wanke wanken nan tass, tukunyoyin har bayansu ta wanke kal sai kyalli suke ta share ko’ina tashigo shagoma ta share tsaf tai mopping lokacin biyarda rabi sannan takoma baya tasa hijabinta tadauko jakanta ta goya abaya tafito tazo gaban Maman Miwa tace “nagama” kallonta Maman Miwa tayi tace “ohh kudinki ko”? Gyadamata kai tayi, kudin hannunta Maman Miwa tashiga kirgawa taciro 10k tabata tace “gashi na litinin zuwa yau juma’a” murmushi tayi for the first time dan gaskiya she hardly smile kaganta tana murmushi ko dariya to sai in tana tareda Mamanta, takirga kudin tass dubu goma chip chip tace “nagode Allah yabiyaki” tajuya tawuce kallo Maman Miwa tabita dashi ance duk muguntan ka kaji an maka wani addu’an saikaji ranka ya sosu harta fita waje Maman Miwa tace “Rasheeda!” Dasauri yarinyar tajuyo jin an kirata, komawa cikin shagon tayi tace “na’am gani” kallon sales girl dinta Maman Miwa tayi tace “samata shinkafa da tuwo a takeaway takaima Mamanta” wani kalan murmushi tayi dayasa wani hot dimples suka lotsa a kumatunta Ya Allah! She looks damn beautiful dasauri tace “nagode sosai, nagode nagode” Maman Miwa sai kallonta take dan wlh today is the first time in almost 3months data fara musu aiki take ganinta tana murmushi, yarinyar kam badai kyauba, ta tabbata badan cutan su ba da tuni wani babban Alhaji ya aure ta, kawomata abincin akai a leda ta amsa wannan karan saida ta duka tace “nagode sosai Maman Miwa” murmushi Maman Miwa tamata tace “sai Allah yakaimu gobe” gyadamata kai tayi tafice Maman Miwa tabita da kallo wani zubin she wants to be wicked amman kuma indai kai ba shaidan bane u can’t be wicked to this girl cus zata maka aiki tsakani ga Allah dabazaka taba ganin abinda zakai complain akai ba, wanke wanke take maka tsaf, tai shara tai moping kaga ko ina na kyalli, banda haka daidai da tsinke bata taba sata a shagon ba wlh ko kwayar magi bai taba bataba dudda ko basudashi, kowa ya tsaneta kowa kyaranta yake sabida Mamanta but if u look at it ciwo nakan kowa, zata gudu tabar mahaifiyarta ne sabida tabada HIV? No, ba HIV ba ko HIVVV uwarta kedashi uwarta ce, dudda ma taji labari ance mai kudi mahaifiyarta ta aura but taje tai fasikanci tasamo HIV yakorota yace cikin ma ba nasa bane, hmmm tasauke ijiyan zuciya tace “Allah ya kyauta dai”.

Tafiyan datayi zaiyi nisan tafiyan inda zakaje kabiya 200 ko 300 kan adaidaita sahu amman akafa tai tafiyan nan tana shiga layinsu ta tsaya gaban wani chemist ta kirga 6500 tabashi tace “ga kudin maganin nagode” karba yayi yace “an dawo daga aikin Rashy” gyadamai kai tayi batace komiba ya karbi kudin yana kokarin kirgawa daidai ta juyo zata fito wasu maza guda biyu na zuwa wajen daya daga cikinsu yakalli mai shagon yace “kai Bala nagaya maka idan kana bari yarinyar nan na shigowa shagon ka bazaka taba yin ciniki ba ni nama fasa sayan abinda nazo saya mtswww yawa kake wlh gaye” yajuya harya fara tafiya Rasheeda tace “ko dabba yafi jahilin namiji mara ilimi daraja tirr, adaije makaranta akaro ilimi katon banza” chak saurayin ya tsaya saikuma ya juyo yanuna kanshi yana kallonta kur itama Rashida ke kallonshi yace “dani kike”? Dasauri Mai chemist din Bala yazagayo yana daga marfin kanta yafito yace “badakai takeba Rashida tafi gida kudin sun cika nagode” wani kalan kallo tama mai chemist din tace “akanme zakace badashi nakeba Bala? Inba dashi nakeba waye yamaka kama da jahili awajen nan”? Wani tahowa gayen yayi azuciye zai daketa yace “zan sumar dake wlh ke” dasauri Bala yatareshi yace “me haka kai Sani dukan mace zakayi”? Wani kalan dariyan daru Rasheeda tayi tasauke jakanta dake goye abayanta ta ijiye ledan abincin hannunta duka akasa tanuna kanta tace “nizaka daka?” Tasake dariyan keta tace “billahillazi yauka tabani saidai uwarka ta haifo wani zan gwada maka ni dakake gani kaman maza dari ce anan, try me I will make sure namaka abinda baxaka so ka karabin hanyan danake bi ba” tai maganan azuciye cike da fushi da masifa da rashin tsoro, dasauri Bala mai chemist yakalli abokin Sani yace “please rikeshi ku tafi dan Allah Kamal” kamashi abokin yayi yace “muje Bros shareta pls ba riba a fada da mace” Rasheeda tace “kasan Jahili baida ilimin sanin hakan wannan dahar yanzu ake raba shayin safe dashi agida” haba wani kalan fizge kanshi yayi yakawo mata duka da duka karfinshi kaucewa Rashida tayi da sauri yasami bango batai wata wataba ta daga kujeran dake wajen na zaman mutum plastic chair ne ta rapkamai a fuska kafan kujeran ya yakushi bakinshi haba bakinshi sai jini ganin jini abakinshi yayo kururuwa zaiyo kanta da sauri abokinshi da Bala mai chemist suka rikeshi, itama Rasheeda cikeda fitina ba tsoro azuciye tace “ku sakeshi yazo bakaga komiba duk bakin dazai kokarin bullying dina wlh saina fasa bakin, kai kayi kadan kahanani sakewa agarin nan sabida ka ganka namiji, akan wani dalili zaku hanani sakat bazan iya zuwa nasai abubu? Shaguna nawa nadena zuwa na layin nan? Wannan danake zuwa yanzu shima kuce ban isaba sabida wani dalilin ku na banza da wofi, cuta nakan kowa, babu wanda yasan karshen shi, yes Mamana nada HIV and so what? Kubi duniya a sannu kai kanka bakafi karfin kasami cutan ba dakiki kawai mahaukaci, katon banza wanda ake gutsurama buredi agidansu har yau akasa dashi da kannenshi sabida baida zuciyan nema, kar Allah yasa ka kara zuwa shagon siyan abu, jahili kawai” cika shagon akayi da mutane sabida yanda Rashida ke zubamai zagi shikuma yana kokawa dasu Bala asakeshi ya daketa ganin yanda ta fasamai baki, cikin taron mutanen wani dan tsoho ya leko ganinta sai kawai ya shigo cikin shagon yakai hannu ya karbe kujeran ya ijiye gaisheshi mutanen wajen sukahau yi. “Barka da yamma Baba Liman” cikeda hikima na manya ya dubi Sani yace “ayakuri Sani, kekuma wuce mutafi” hannunta yakama yace “wuce mutafi” batai musu ba akumbure cikeda taurin kai tace “ni jakata” sakinta yayi yana kallonta taduka tadauki jakanta ta goya abaya da ledan abincin tarike a hannu tana nishi kaman kirjinta zai fashe sabida fushi saikuma ta dago azuciye dan tanada naci wani zubin kaman mayya, takalli uban mazan dake wajen duk ana kallonta tace “Baba Liman kagayama yan anguwan nan su kiyayeni nida mahaifiyata, bamu shiga gidan kowaba munyi sata, Mama harni baya shiga gidajensu sabida yanda kowa ya kyamace mu, bamu rokesu kudi ba, banzo nacema kowa yabani kaza zankai mahaifiyata asibiti ba dan haka su fita daga rayuwata dana mahaifiyata Baba, sufita na gayamusu, I am enough for Mamana! ni kadai zan iya kula da ita, nayi girma kuma Alhamdulillah inada karfin yimata komi kowa yafita harkana, ban nemi fadan kowaba ban shiga hurumin kowaba dan haka duk wanda yashigo tawa koshi waye wlh sai inda karfina yakare kagaya musu Baba Liman” tayi maganan with a sound warning, ahankali tsohon yace “ya isa!” wucewa tayi fuuuuu tafice daga shagon kowa na wajen jikinshi yayi sanyi wani dakeda shago kusada na chemist yakalli yaron yace “kudaina abinda kukeyi mutanen nan ba akanku suke zaune ba, wlh Allah zai iya saka musu, shidai cuta nakan kowa, yau dauka fasikanci matan tayi tasamu Allah masani amman ina mai tabbatar muku, gulma, keta, rashin mutunci da sa’ido da menene menene kukema matan da yarta kadai ya kore zunubansu” anatse Baba Liman yace “muji tsoron Allah, mun kyamaci mutanen nan shi kadai ya isa wlh kudena takura musu kar Allah yakamaku, kar Allah yakamaku” yawuce shima yatafi, dasauri Bala yace “nima kada ka kara zuwan mini shagona kaje wani chemist din” tsaki Sani yayi yace “ka dinga shiganmata ko zaka mutu iyayyenka dai damuka sani bazasu taba barinka auren tijararriyan yarinyar me kanjamau dinchan ba” yayi maganan yana ficewa dağa shagon abokinsa na binsa.

Gidansu na wajajen karshen layin, wani dan karamin gidane sosai ciki da falo daya ne sai bayi ba kitchen a tsakar gidan suke girki, ko’ina kal kal agidan, maida kofan tayi tarufe tasa sakata tasauke ijiyan zuciya sannan tai murmushi dan bataso Mama tagane ranta yabaci daganan zaure tai shouting “Mamaaaaa, Mama nadawo” tai ciki da gudu labule ta daga Maman na zaune kan dadduma kaganta kamansu daya sak da Rasheeda itama tanada haske but ba kaman Rasheeda ba, batada kiba ko kadan ta rame ta bushe sosai, duka duka bazata wuce 40 ba but she looks kaman wacce ta tsufa, tana zaune kan dadduma tanajan charbi, ijiye kayan hannunta Rasheeda tayi saikuma tai tagumi tana leka fuskan Mama tace “Mama kiyi sauri kigama kimin sannu da zuwa niii” tafadi a shagwabe, hannu Ammi tasa ta shafe addu’an datakeyi sannan tajuyo kawai saita kama kunnenta ta saman hijabin jikinta tace “dan kaniyanki ba alwala yakamata kiyo ba kizo kiyi salla ba” dariya sosai tayi tana yarfe hannu tace “wayyooo kunnina Mama zai cire” sakin kunnin Mama tayi tana murmushi looking so happy tace “imaza to jekiyo alwala kafin lokacin magrib yafice baki salla ba” tashi tayi tafito tsakar gida alwala tayi tadawo tai salla kusada Mama sannan tadauki jakanta tabude taciro kudin tasa a hannun Mama tace “Maman Miwa tabiyani, hotel din nan gobe suma zasu biyani kuma manager tace nakawo zanen tagani idan na iya sosai zasu saya” karban kudin Mama tayi tana kallo tana murmushi Rashida tashiga fito da abincin tace “nabiya nabawa Abdul kudinshi Mama ga abinci Maman Miwa tace nakawo miki” bubbude komi tayi ta tashi tafita dasauri tadauko ruwa a bowl tadawo tazauna takama hannun Ammi tasa aruwan tace “wanke hannun muci” wanke hannunta Ammi tayi ta ijiye kudin agefe ta gutsuro tuwon instead takai bakinta bakin Rasheeda takai dasauri Rasheeda tace “Ammi ke kici” ahankali tace “ni naci abinci namana shinkafa, keko nasan tun safe bakici abinci ba banda karin dakikayi ko kinci wani abu”? Hadiye tuwon bakinta tayı tana fikifiki da ido most of the time idan tana aiki mantawa da abinci take, hararanta Ammi tayi tace “bude bakin, kidena wasa da abinci kinji Doctor” gyadama Ammi kai tayi tana murmushi Ammi nasa mata tuwo abaki tace “ko biscuit ne buy and eat kinji” sake gyadamata kai tayi, haka Ammi tadinga feeding nata kuma sosai taci ita bama tasan takusan cinye tuwon ba saida takalli takeaway dasauri tace “Ammi nacinye miki tuwon” murmushi tayi tace “haka nakeso dama Doctor” tass tacinye tuwon Ammi kuma taci shinkafan ba sosai ba dan batajin yunwa, sannan ta tashi taje tayo wanka da alwala tareda Mama sukai salla ta shiga tattara yan kwanukan zata wanke Mama tace “kibarshi jekiyi zanen ki zanyi wanke wanken” dasauri tace “Mama ni kidaina aiki, bayawa yanzun nan zanyi nagama zanyi zanen” kafin Mama tai magana tafice daga dakin biyota Mama tayi dudda haka tana wankewa Mama na dauraye wa suka gama suka dawo daki tayata Mama tayi ta kwaso board na zanen da colors nata da pen ta zuzzuba tafara zanen kome takeso Mama na mikamata suna cikinyi aka dauke wuta torch light Mama tadauka ta kunna Rasheeda tai murmushi tacigaba dayi sai wajajen 12 tagama tabarsu su bushe gobe zata sasu acikin frame, zama tayi anan danta huta kafin suje su kwanta sai bacci itakuma Mama na tattare brushes din tana dauraye mata su aruwa, munsharin ta da Mama taji yasa tajuyo takalleta ganin yanda take baccin azaune kanta na lilo

Series Navigation<< Sanyi Da Zafi Part 2Sanyi Da Zafi Part 4 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *