Kwarya Tabi Kwarya Hausa Novles

Kwarya Ta bi Kwarya Chapter 1

This entry is part 1 of 6 in the series Kwarya Ta bi Kwarya by Sadnaf

*BISMILLAHI RAHMANIR RAHEEM*

*PAGE 1*

*Past*

Iska mai k’arfi da kwanun gidan dake ta Kara yasa Sulaiman dake kwance a Gefen Hanne mik’e wa da sallati a bakinsa.

 dan Karamin cocilan dake gefen gadon ya lalubo ya kunna dan sosai iska ke buga dan Karamin window nasu kafin ya kunna cocilan din Hanne dake kwance a gefensa ta tashi zaune itama bakinta d’auke da sallati tana “Abban Ameera Allah yasa ba ruwan sama za’ayi ba.”

Rufin kwanun dakin dake dagawa saboda iska yasa ta sake sakin sallati a daidai lokacin da sulaiman ya kunna cocilan din  ya haska su Ameera dake kwance a kasa ya Kalli Hanne Yana “Tashi ki mai dasu kan gado bari na fita waje na d’auko bokitan da zamu tari ruwan”

Yayi waje Yana Jin kamar yayi kuka dan tunda aka shiga damuna basu da wani kwanciyar hankali idan dai za’a yi ruwan dare dan rufin dakin ba Karamin yoyo yake ba dan idan har akayi ruwa da yawa  haka dakin zai cike da ruwa har sai ya kusa tadda gadon su dake jikewa jagab da ruwa.

Idan baya nan Hanne ke fama da kwashe ruwan tana zubar wa a waje.

Yanzu haka fadi tashin da yake na yadda zai samu kudi ne ya canza Kwanun gidan.

  burinsa kullum bai wuce Allah ya kawo masa hanyar da zai samu kudi da har gobe ya kasa samun kudin da zai ishe shi ya siyi kwanun da zai rufe dakin.

Ko da ya fita kamar iska zai d’auke shi dan saboda karfin iskar har bokitan dake ajiye a gefe sunyi nasu wajen ga kasa daya cike masa ido saboda karfin iskar kafin ya Kai hannu ya d’auko bokitin dake wajen k’ofar fita.

Iska ta d’auke kwanun rufin dakin nasu sallati yake da k’arfi kamar yadda Ya Jiyo Hanne na “Shikenan Abban Ameera asirin mu ya tonu”

Bokitin hannun sa ya saki  ya cigaba da sallati ya koma cikin dakin da sauri a daidai lokacin da ruwan Saman ya sauko da balain karfin sa.

Yana Isa bakin kofa yaji Ihun su Ameera dan ruwan kamar har da kankara hannu ya sa ya karbi Sadeeq daga hannun Hanne da su Ameera suka rike kafarta gam dan ruwan Saman ba Karamin jibgar su yake ba ta kuma tsaya cak bata motsa ba balle ta samu mafaka dan iya dakin nasu ke da rufin kwanu dan Karamin kitchen din nasu da bandaki ba wani rufi.

Gashi wajen karfe biyu ne na dare balle su nemi wajen da zasu fake.

 Hanne sai kuka take a cikin ruwa tana rungume da su Ameera dake ta tsalla ihu kamar yadda shi ma ya rungume Sadeeq ya b’oye shi a kirjinsa.

Ba gidan da zasu  iya zuwa a yanzu su fake dan ko sun buga gidan makotansu ba lailai suji su ba.

Yadda ruwa ya cike dakin  yasa ya cewa Hanne ta dora su Ameera kan gadon dan a cikin ruwan suke tsamo tsamo.

Tana dora su akan gadon ya bud’e wadrobe dinta mai k’ofa biyu ya jawo wani zanin gadon ta da yasan ko ya rufe su jikewa zasu yi amma haka ya d’auko zanin gadon mai kauri kamar towel ya rufe su Ameera,da Yana rufe su ruwa ya jike zanin gadon.

Hanne na kuka zaune a saman gadon kamar yadda shi ma ya zauna a gadon  rungume da Sadeeq da bai fi shekara uku ba ruwan yayi ta dukan su tsawon awa daya kafin ruwan ya fara tsagaitawa iska da sanyin ruwan yasa hakoran su haduwa suna rawar sanyi.

Ruwan na d’aukewa hannu na rawa ya bude wadrobe din ya hau lallubo kayan su Ameera da ya samu basu jike sosai ba ya mik’awa Hanne da idonta ya kumbure saboda kukan da ta sha,baya san ma yi mata magana dan gani yake shi ma zai iya fashewa da kukan dan a yanzu sai dai su tafi gidan gwaggo Mahaifiyar sa da yake b’oye mata halin da yake ciki a yanzu ita kadai ce zata iya taimaka musu.

Kukan Hanne ya katse masa tunanin da yake dan Sadeeq yake cirewa jikakken kayansa.

“Yanzu Abban Ameera ya zamu yi daga Ina zamu fara”?

Sai da ya hadiye yawu saboda shi kadai yasan tashin hankali da yake ciki duk tashin hankalin da Hanne zata shiga ba kamar shi da yake namiji da yake fadi tashin ganin asirinsa ya rufu ba.

“Idan gari ya waye zamu je gidan gwaggo ku fara zama a can kafin mu ga abinda Allah zai yi”

“Da muje gidan gwaggo mu daga mata hankali mai zai hana kaje wajen yayanka tunda Yana da halin da zai iya taimaka mana ko a cikin gidajen daya sa haya ne mu fara zama kafin Allah ya hore ma bansan mai yasa baka san zuwa wajensa neman taimako ba karka manta gwaggo yanzu ta tsufa bata bukatar abinda zai daga mata hankali wajen yayanka ya kamata muje mu nemi taimakon nan tunda shi mai rufa ma asiri ne”.

Murmurshin takaici yayi dan yasan Hanne bata san waye Habu da take cewa yaje ya nemi taimakon sa ba ya gwammaci yaje ko Ina neman taimako da yaje wajensa.

Cije lebbensa yayi Yana Jin wani irin daci a   bakinsa da ya tuna wulakancin da matarsa ta masa a lokacin da yaje satin da ya wuce akan ya ranta masa kudi ya siyi kwanun rufi, dan kwasar ruwa da wahalar da suke Sha Yana matukar damun sa.

idan ya fita buga buga na abinci kawai yake iya samu ya kai gida.

A lokacin da yaje ma sai da ya shafe awa daya Yana zaune a palon da kayan lebura a jikinsa,dan daga wajen aiki ya zarto gidan dan kudin aikin da aka biya shi da shi zasu ci abinci dare su karya,motar Habun da ya gani yasa ya san Yana gidan.

Akan ce kowa da irin zuciyar sa amma har gobe Yana mamakin yadda Habu yake masa rowa ba mai yarda ma dan uwan sa ne shi.

Mai nema baya fushi haka yayi ta zama Yana zabga hamma ga kamshin abinci da yake jiyowa daga kitchen daya sa ya ji yunwar na Kara taso masa.

Har ya fara k’ok’arin tashi dan ya tafi dan yasan Yanzu Hanne na can na zuba idon zuwansa.

Zinatu matar Habun ta fito tana yamutsa fuska kamar taga Kashi.

Kafin ma yayi magana ta fara magana tana “Alhaji fa bacci yake sai dai kaje ka dawo kila ya tashi idan kuma kudi kake nema bana Jin zaka samu dan dazu nan ya gama wani hidimar kudi”

Tace cikin yatsine fuska tare da nufar wajen da ya dosa na duwawunsa tsananin b’acin rai da bakin ciki ya hana shi motsawa ta karaso wajen da yake zaune ta  hau kada gefen Kujerar tana “kujerun nan suna da daukar datti dazu nan na Sha wahala wajen gogewa gashi  jikinka duk kasa da siminti  ai da ka zauna a kasa.”

Sulaiman kasa magana yayi saboda yadda jikinsa ya d’auki rawa da b’acin rai,yasan irin wahalar da hidima da ya Sha a lokacin da Habu zai  aurota ya tuna yadda take mutunta shi kafin ya aurota wai yau shi take gayawa magana tana wulakanta shi.

Yau da Habu bai wulakanta  shi  ba baya Jin Zinatu ta isa ta masa irin wanan wulakancin.

Mik’ewa yayi Yana “Banga laifin ki ba Zinatu Yau da Yaya Habun bai wulakantani ba bana Jin kin Isa ki wulakantani   amma ba laifin ki bane banda na   taka kafata nazo gidan nan da kinyi kadan ki wulakantani”.

Daga haka ya juya ya fice Yana Shan alwashin ba  zai sake taka kafarsa yaje gidan ba Koda talauci zai kashe shi ko gama fita bai yi daga palon ba yaji muryar Habun na kwallawa Zinatun kira.

Da bakin ciki ya isa gida dan yasan habu yasan da zuwansa yasan Kuma mai yasa yaje gidan nasa wulakanta shi kawai yaso yi dan kawai Allah ya masa arziki.

Bai tab’a fadawa Hanne irin wulakancin da Habun ke masa ba ko gwaggo da take Mahaifiyar su bata tab’a sani ba.

Muryar Hanne ne ya sake dawo dashi hankalinsa

“Kayi shiru Abban Ameera kaga yaran nan ma da alama zazzabi  zasu yi na dukan da ruwa ya musu sai karkarwar sanyi suke”

Mik’ewa yayi dan an fara kiraye kirayen sallah asuba “idan gari ya waye gidan gwaggo zamu je zanyi k’ok’ari na nemi kudin kwanu a rufe dakin”

Hanne na k’ok’arin magana ya katse ta Yana “Na gama magana Hanne”

Daga haka ya fice daga gidan.

Wajen bakwai suka Isa gidan gwaggo dan madaidaicin gida da duk suka yi rayuwa a ciki kafin duk suyi Aure.

Habu ne ya gyara mata gidan ya dawo sabo tana zaune da wata Yar kanwarta bazawara, su hudu Mahaifiyar su ta haifa,akwai babban yayan su Ibrahim  Yana zaune a can katsina da matarsa da Yayansa  shi ma ba wani kudine dashi ba buga buga kawai yake daga shi sai Habu da shi Allah yayi wa arzikin sai shi sai kanin su da suke cewa dan bature Yana karatu a can lagos shekara goma da suka wuce mahaifin su ya rasu Mallam Audu.

Duk ba wani karatu suka yi mai zurfi ba daga Ibrahim har shi Habun duk kowa ya kama gabansa ya tafi neman kudi da mahaifin su ya rasu iya shi ke zaune da mahaifiyar su da suke cewa gwaggo ya ringa buga buga Yana ciyar da ita da dan bature har Ibrahim ya dawo gida akan ya samu matar Aure Yana kuma da dan shago da yake siyar da kayan kwalliya shi ma kamar Habun  yake wajen rowa dan kullum cikin Ihun Babu yake.

Habu kuwa a buga bugarsa ya dawo da kudi akan Allah ya hada shi da wani dan china ko da ya dawo dabiunsu sun balain canjawa ba kamar yadda ya tafi ba,dan a yanzu kunyar ma nuna su yake a matsayin Yan uwansa dan ko a neman auren Zinatu da kyar ya bari dangi suka je dan yafi so yaga Yana harka da masu kudi dan ita kanta Zinatun Yar masu kudi ce.

Sulaiman da suke cewa sule ya d’auka zai iya taimaka masa tunda Allah ya Buda masa sai gashi baya baya ma yake dashi idan zai shekara Yana tambayarsa kudi haka zai dage akan bashi da ita sai dai yaji labarin yadda yake facaka da kudi yafi san ya kyautata wa na waje akan na cikin gida gwaggo kawai ke cin kudinsa.

Hakan da sule ya gani yasa ya hakura da bin Habun ya fara neman na Kansa a haka har Allah ya hada shi da Hannatu da ake cewa Hanne duk da bashi da komai haka ta aure shi da dan abinda ya tara ya kama musu gida.

Aikin lebura da kafinta kawai yake dan bashi da wani kwakwaran sana’a, gwaggo na yawan yiwa Habun maganar samun aiki ko jari sai yace mata bashi da hanya shi kam ba wani damuwa yayi ba tunda har ya d’auke masa nauyin ciyarwar gwaggo da wani zubin ma idan ya rasa abinda zai Kai gidansa zai wayance yaje gidan ya dan dib’ar musu abinda zasu ci.

Baya nunawa gwaggo gazawarsa dan tana da sa abu a ransa daga lokacin da Hanne ta fara haihuwa sai abubuwa suka Kara cakude masa dan aikin nasa ba na kullum bane idan ya rasa haka zai je wajen habu a babu yadda zai yi kamar ba dan uwan sa ba sai ya ci Sa’a yake dan bashi kudin da ba abinda zai masa a karshe ma sai ya nemi Mai dashi dan aikinsa.

Kudin haya da ya gaji da biya yasa ya siyi Karamin fili ya gina daki daya dak’yar ko ceiling Babu haka suka tare yaransa uku Ameera itace babba tana da shekara shidda sai Fareeda da Sadiq.

Sule kuwa a Babu yadda zai yi ya fadawa gwaggo halin da yake ciki ya Kara da “gwaggo su Hanne zasu zauna anan kafin na samu kudin da zan rufe dakin”

“Sule mai yasa baka tab’a fada min kwanun gidan naka bashi da kwari ba har ace Ina rayye a rasa mai taimaka ma naga Habu Yana da kananan gidan da ya sa yan haya mai yasa baka masa magana akan zaka zauna a a gidansa ba har zuwa lokacin da Allah zai Buda Maka Ka samu kudi ka gina gidan naka”

“Gwaggo dan Allah ki barni zan nemi kudin nan idan har zaman su Hanne ba zai takura ki ba nafi san na nemi na kaina bana bukatar taimakon Habu gwaggo dan ba zan iya jure wulakancin sa ba Allah da ya bashi zai bani nima”

“Toh ban yarda ba sule dan ba wai zaman su Hanne ne bana so ba Habu nake so ya jawo Ka a jiki shi ya kamata ya Maka kyautar gida ai nasan Yana da halin da zai baka gida ka zauna

Sule girgiza Kansa yayi Yana kokarin magana gwaggo ta dakatar dashi tana ta gama magana ta sa baki ta kira saudatu tana zuwa tace taje ta kira mata Habu tace yazo tana nemansa yanzu nan.

Present

  Ameera

   Da sauri ta sake rufe idonta da taji muryar Anne da doso dakin su tana kwalla mata kira.

Tunda Abbansu yace ta shirya su je gidan yayansa Alhaji Abubakar da ake bikin Yar sa ta fara tunanin hanyar da zata bi wajen dakile zuwan nata dan idan akwai wayanda ta tsana a rayuwarta bai Wuce su ba.

Bugun da Anne ta kaiwa kafarta da “Tashi Maza ki shirya mu tafi”

Yasa ta dan Bud’e idonta ta tashi zaune ta dafe kanta tana “Anne kaina mugun ciwo yake min wallahi ki tafi da Fareeda kawai sai nayi girkin kafin ki dawo”

“Ki Sha magani ki sa kaya mu tafi dan nasan karya kike yi zuwa ne baki so kiyi”

“Anne ba zan iya manta wulakancin da suka mana ba bana san zuwa dan nasan sai mun dawo da b’acin rai abinda na dauka a baya ba zan d’auka ba a yanzu wallahi abinda na jure a baya ba zan tab’a jurewa ba a yanzu duk Wanda Yamin wallahi sai na rama”

“Ameera kenan a baya ma da suka wulakanta mu ai dan bamu da kudine,nema muke a Wajen su amma a  yanzu Allah ya rufa mana asiri idan munje sun san ba nema muka je yi ba”

Ameera ido ta zubawa Anne da ta saka sabuwar atamfar da ta dinka mata  duk da ba super bace ba atamfar ba mai a raha bace da zasu raina mata Anne har ga Allah da tana da hali da ta hana zuwan nasu dan rabonta da gidan tunda ta mallaki hankalinta.

Jiki a sanyaye ta mike ta shiga bandaki ta watsa ruwa ta fito ta shirya cikin wani atamfa da ta masa dinkin 3 qtr dinkin yayi mata kyau matuka murmushi ta sakarwa kanta tana furta hamdala a fili dan yau rufin asiri da suke ciki silar dinkin da ta ke yi ne da ita kanta bata san yadda aka yi ta wayi gari ta kware a dinki ba daga yanke yanke da dinkin Yar tsana ta zama kwarariyar tela da a yanzu dai zagayen unguwar su ba Wanda ya kaita iya dinkin.

Lip gloss kawai ta shafa a sirrin lebbenta mai dan duhu ta dan fesa turare ta fito Palo.

Anne na ganin ta ta mik’e tana “dafatan kin d’auko kudin da zamu bata”?

Ameera murmurshi ta saki tana “Anne kema da zolaya kike hajiya Zinatun zaa kaiwa kudi wai halan kin manta wulakancin su”

“Ba abinda ya shafeni da wulakancinsu Ameera ba zai yu muje hannu na dukan cinya ba dole mu bata kudi ta siyawa amarya tsintsiya idan ta ga dama ta watsar da kudin wanan matsalarta ce”

Ameera a ba yadda za tayi ta koma ciki ta Bude akwatin da take ajiyar kudi ta kirgo dubu biyar ta fito ta mik’awa Anne.

Anne ta karba ta Saka a Jakarta suna fita suka samu abun hawa suka d’auki hanyar unguwar su Alhaji Abubakar.

Ameera kuwa shiru kawai tayi tana hasaso rashin mutunci da za tayi wa duk Wanda ya nemi ya wulakanta su,sultana da ta tuna yasa ta girgizani kanta dan da alama a yau zata rama Marin da ta mata a shekarun baya.

Sam bata san sun iso ba sai da Anne ta zungureta ta dawo daga tunanin da ta tafi.

Tana saukowa ta hango Amjad a tsaye da wani abokinsa gabanta wani irin faduwa yayi ta d’auke kanta da sauri ta d’auka baya kasar ya canja sosai kamar ba shi ba.

“Ameera”!!!!

Taji ya kwalla mata kira…

Series NavigationKwaya Ta bi Kwarya Chapter 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *