Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒐𝒏𝒆
….Suna shiga cikin headquter ɗin Lawyers nashi na isowa shima. Sai dai kafin su ƙarasa gareshi an shige dashi wani ɗakin bincike. Table ne kawai da kujeru biyu masu facing juna. Sai da ya gama ƙarema ɗakin kallo fuskarsa a yamutse kafin yaja kujerar ya zauna. Yana zama cikin jami’an wani shigo, da girmamawa yake tambayarsa ko yana buƙatar wani abu kamar su tea haka. Ɗan jimm yay yana kallon ma’aikacin, sai kuma ya murmusa kaɗan alamar a’a. Fita Jam’i yayi, shi kuma ya jingina bayansa da kujerar sosai ya lumshe idanunsa kawai. Kusan mintuna fin ashirin sannan aka sake buɗe ƙofar. Bai motsa ba bai kuma buɗe idanunsa ba har jami’in ya kai zaune. Kaɗan ya ɗan buga table ɗin, sai dai a hakan ma Maash ɗin ƙin motsawa yayi. Sai da ya mula dan kansa sannan ya buɗe idanunsa ya zubama jami’in batare daya tashi ba. Ji Jami’in yay bazai iya jure kallon ba, sai ya kauda idanunsa cike da basarwa yana furta, “Sir bamu da isashen lokaci. Idan ba damuwa ka amsa mana wasu ƴan tambayoyi mana”.
“Jeka maganarka kai tsaye” Maash ya faɗa a daƙile.
Ran jami’in ne ya sosu, sai dai baice komai ba ya cigaba da faɗin, “Akwai containers ɗinka da suka tashi daga Lagos a shekaran jiya da dare zuwa ƙasar Ghana. An samu yara ƴammata a cikin ɗaya da muke da tabbacin safararsu aka shirya yi. Still dai a cikin container ɗin anyima yaran makwanci, a ƙasan shi mun samu kayan laifi”.
“Kamar……?”
Maash ya faɗa cike da rainin hankali. Yanzu kam a fusace jami’in ya kallesa. Sai dai kuma bai iya cewa komai ba ya cigaba da faɗin, “Drivers ɗin sun tabbatar mana da cewar sun fito daga companyn ka ne”. Ya ƙare maganar da tura masa hotuna gabansa. Batare da Maash ya ɗauki hotunan ba ya zuba musu ido kawai. Kansa ya ɗan girgiza cike da rashin damuwa ya furta, “A staff ɗina bana tunanin nasan waɗan nan fuskokin”.
“Ba zamu tabbatar da hakan ba, dan zaka iya hiding nasu. Sai dai kuma su containers ɗin ai bazai yiwu kace ba naka bane ba”.
Shiru babu alamar Maash ɗin zai tanka, sai da ya mula dan kansa sannan ya saki ɗan gajeren murmushi da kai hannu ya shafi kwantaccen gashin fuskarsa. Zamansa ya gyara da ƙyau gaba ɗaya hannayensa akan table ɗin ya zubama jami’in ido. “Mr Man kamar ya dace ka tuna kai jam’i ne ba alƙali ba. Damar samuwar amsar tambayoyinka kuwa zaka same su ne kaɗai a bakin lawyers ɗina”. Daga haka ya gyara zamansa ya sake lumshe idanunsa duka hannuwansa harɗe a ƙirjinsa.
Iya ɓacin rai Jam’in nan ya shiga. Dan haka ya miƙe a fusace ya fice abinsa. Murmushi Maash ya saki mai ɗan sauti batare da ya buɗe idanunsa ba.
Har yamma Lawyers na Maash na fafatawa a station ɗin, shi dai yana a inda aka kaisa har yanzu. Sai da lokacin Sallah yayi ya buƙaci yin alwala. Basu da damar hanashi. Abincin da Hayatu ya kawo masa kuwa ko kallonsa baiyi ba. Dan shi fa sam bawai cakwakiyar station ɗin ma bace damuwarsa. Hankalinsa ma gaba ɗaya baya a wajen.
Gab da magrib Baba prof… Ya iso, da ga airport kai tsaye shima station ɗin yayo, anan ya samu kusan duk ahalin gidan. Paah, Uncle Abdullahi, Hajiya Mammah, Maman Maleeka (Matar Uncle Abdullahi) sai Hayatu dake kai kawo tsakanin asibiti da aka kwantar da Samraah zuwa nan. Ko bayan isowar Baba prof.. ɗin shima ya kai awanni uku a station ɗin kafin su samu bell ɗin Maash ɗin bisa wasu sharuɗɗa masu tsauri.
Ƙarfe tara da wasu mintuna aka fiddo Maash da ga ɗakin nan. Kallo ɗaya yay ma ahalin nasa ya ɗan kauda idanunsa. Sai kuma ya cigaba da takowa a nutsensa har inda suke. Baba prof.. ne ya riƙosa ya rungume yana faman ambaton Alhamdullah. Shi dai Maash baice komai ba. Bayan ya sakesa kuma ya koma tattaɓashi da jera masa tambayoyi. “Kana jin yunwa? Akwai inda ke maka ciwo? Sun maka wani abu ne?…..”
“Grandpa! I’m not small boy now”.
Ya katse Baba prof.. ɗin cikin wata irin murya mai cike da rashin damuwa. Murmushi Baba prof.. yayi da kai hannu ya yamutsa masa sumar kansa kamar yanda yake masa a duk sanda suka haɗu. “Oh na manta Muhammad Awwab ɗina dutse na rimi ne baka fargaba sai ta ruwa.”
Dariya su Paah suka ɗan yi, kafin shima ya matso ya rungume Maash ɗin, hakama Uncle Abdullahi. Maman Malika ma tai masa barka. Ganin haka itama Hajiya Mammah ta bashi side hug. Shi dai komai bai cema kowa ba. Sai hankalinsa da ya ɗan maida ga lawyers ɗinsa da Hayatu dake fitowa. Cike da girmamawa suka shiga gaisheshi. Tare da jajanta abinda ya faru suma. Idanunsa ya lumshe kaɗan da sake buɗewa, suma ɗin dai batare da yace ma kowa komai ba ya motsa a hankali ya fara tafiya.
Suma duk ƙoƙarin ficewar sukayi, kowa da abinda ke a zuciyarsa. A motar da yazo da ita da safe ya shiga. Sai dai yanzu Hayatu ne a mazaunin driver. Har sun ɗauki hanyar gida a kasalance Maash da idanunsa ke rufe har a lokacin a hankali ya furta, “Hospital”.
Cikin girmamawa Hayatu ya amsa masa, tare da fita a cikin sauran motocin ya ɗauki hanyar asibiti. Sauran abokan tafiyar basu farga ba sai da akaje sauke Baba prof a gidansa. Da farko sun ɗauka ko gida su suka wuce saboda Maash ɗin ya huta, sai da drivern Baba prof ɗin ya sanar da inda yaga sunyi sannan ne a fusace Hajiya Mammah ta ce, “Eh lallai, al’amarin Awwab kullum sake gawurta yake wlhy. To amma kuma anya ba wani abun yaje aikatama yarinyar nan ko hana likitocin faɗa ba saboda ya rufe sirrinsa.”
Har cikin rai zancenta ya soki zuciyar Paah, sai dai baice komai ba. Baba Prof ne ya tambayi abinda ke faruwa? Har zagwaɗi Hajiya Mammah keyi wajen zayyane komai daya faru da safe har neman yarinyar da suka dinga yi da daddare. Wani yawu mai kauri Baba prof ya haɗiya idanunsa akan Paah da Uncle Abdullahi. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa. Wayarsa ya amsa a hannun drivern sa daya kwaso kaya zai kai ciki, dan duk abinda Hajiya Mammah ta faɗa ya laɓe yana jinta. Kai tsaye Baba prof ɗin wayar Hayatu yay kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga.
“Kuna ina?”.
Da ƴar in ina Hayatu ya ɗan kalla Maash dake ƙoƙarin fita a mota daya buɗe masa dan isowarsu ke nan. “Bab ba baba muna CLINIC”.
“Clinic! Yin me?”.
“Zamu duba mara lafiya ne”.
Ƙittt Baba prof ya yanke kiran batare daya sake cewa komai ba. Cikin damuwa Hayatu ya dubi Maash ɗinya ce, “Baba Prof”.
Komai baice masa ba, sai ma ƙoƙarin raɓasa da yake yi zai wuce abinsa. Dole shima ya haɗiye abinda ke bakin nasa ya bisa.
★★
Mama Balki na zaune a saman abin salla idar da shafa’i da wutirinta kenan akai knocking ɗin ƙofar. Miƙewa tai tana kallon agogo, azatonta ma Nurse ɗin data sakama Samraah ruwa ce ta dawo. Ruwan ta kalla taga ko rabi bai kai ba ma, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ƙofar ta nufa, sai dai kafin ta buɗe sai da ta tambaya waye?. Hayatu ne ya amsa mata da cewa, “Mama mune”.
Da sauri ta buɗe tana murmushi, tana ƙoƙarin bashi hanya ya shigo idonta ya sauka akan Maash. Wani irin washe baki tayi tana ambaton Alhamdullah. Da jerama UBANGIJI kirari. Ɗan lumshe idanunsa yayi tare da sakin gajeren murmushi ya shiga gaidata. Amsa masa tai tana ƙara godema ALLAH daya sa komai ya zama mai sauƙi.
Nan ma murmushin kawai ya saki baice komai ba, sai Hayatu ne ke tayata murnarta. Ƙarasa takawa yay a hankali zuwa gaban gadon idanunsa a kanta. Tana kwance samɓal idanunta a rufe alamar barci take. Fuskarta ta wani irin yin fayau da ita, sannan har yanzu idanunta a kumbure suke alamar taci kuka mai yawa. Lips ɗinta sun bushe tare da tsukewa waje guda sun ƙara pink sosai. Take wasu abubuwa suka shiga dawo masa game da ita. Cikin sauri ya kauda su tare da janye idanun nasa daga lips dinta, akan hannunta da aka saka ruwa ya sauke. Madaidaitan farcinanta dake da ɗan sauran jan lalle na biki kaɗan da bai gama fitaba yaja kusan mintuna biyu yana kallo, kafin ya maida ga ruwan da ake ƙara matan. Sai kuma ya janye gaba ɗaya ya matsa gaban side drawer dake a gefen gadon ya ɗauki file ɗin da aka ajiye ya fara dubawa. Juyowa yay da nufin yin magana sai ya ga ɗakin wayam, ashe Mama Balki da Hayatu sun fice. Kansa kawai ya girgiza yana ajiye file ɗin, sannan ya zagaya ta ɗayan side ɗin gadon inda hannunta ke free ya zauna kusa da ita jikinsa na gogar nata. Hannun nata ya kamo cikin nasa, ya zubama dan sauran lallen dake jikin faratan nata ido, abubuwa da yawa zuciyarsa ke tunano masa da suka shafi Ummie, mace ce mai tsananin son jan lalle, tunda ya santa kafin lalurarta lalle baya gama fita a hannunta take yin wani. Hakan ya sashi tashi da son lalle shima, lokacin yana ƙarami yakan saka mata rigima shima sai an masa. Takan ce masa maza basa lalli, amma ya tubure ya dinga bori ko yaje ya tsare Mama Balki ko mahaifiyar Hayatu akan dole su sai sun masan, dan a farkon ciwonta kafin komai ya damule har da kansa yake mata lallin a yatsun hannu saboda yasan tana so. Murmushi ne ya suɓuce masa da shi a karan kansa ya mance tsahon shekarun daya ɗauka baiyi irinsa ba. Sai kuma ya kai babban yatsarsa ya ɗauke guntun ƙwallar da suka taru masa a gefen ido kaɗan……..✍️
ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏
1 Comment
mun gode