…
Typing📲
🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐
…….Ɗan motsi Samraah tayi fuskarta a yamutse baki a taɓe kamar mai shirin sakin kuka. Idanu kawai ya zuba mata yana kallon yanda take laɓe bakin, ƙoƙarin motsa hannunta da tai ya sashi sakin wanda ya riƙe ya riƙe mata wancan gudun karta goce ruwan, sake yamutse fuskar tayi da ƙara tura baki.
“Cry. Cry”.
Ya faɗa a hankali saman lips ɗinsa yana kai ɗayan hannunsa a karo na farko kan fuskarta ya ɗan shafa gefen kumatun kaɗan. Idanunta ta shiga motsawa a hankali, sai kuma ta buɗesu gaba ɗaya. Cikin yanayin wadda barci bai saka ba ta ɗan zuba masa su, shima kallon nata yake…
Tar tar fuskarsa ta fara bayyana cikin idanun nawa sosai. Wani irin harbawa zuciyata tayi babu shiri na zabura. Sai dai jin an riƙeni yasa na kallesa a marairaice, batare dana san hawaye sun ɓalle min ba na fara roƙonsa cikin magiya. “Na roƙeka dan ALLAH kayi haƙuri ya Awwab, wlhy zan iya mutuwa bazan iya ba”.
Ganin bashi da niyyar tanka min sai rikitattun idanunsa daya zuba min yasa na sake fashe masa kuka mai ɗan sauti. Kansa ya ɗan girgiza tare da sakin hannun nawa ya kuma janye wanda ke a fuskata sannan ya miƙe, kaɗan ya ranƙwafo ya kama bargon. Sake marairaice masa fuska nayi ganin yanda ya duƙo kaina sai yanayin ya sake min kama da na wancan lokacin, idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe cikin soft voice ya furata, “I will go now. calm your mind”. Ya ƙarasa lulluɓa min bargon har saman ƙirjina. Idanuna na lumshe sauran hawayen dake cikinsu na ƙarasa gangarowa. A bazata naji saukar lips ɗinsa saman goshina. Kafin na buɗe idanuna a firgice harya juya yabar wajen.
Ƙofar daya maida ya rufe na zubama idanu, a hankali bugun zuciyata na sauka. Shigowar Mama Balki ɗakin ya sani kauda kaina daga kallon ƙofar. Kaina tayo kanta tsaye tana faɗin, “Kin tashi Samraah?”.
Kaina na jinjina mata da ƙoƙarin kai hannu na share hawayena, zama tayi a gefena tana mai kamo hannuna cikin nata. Cike da lallashi da kulawa ta ce, “Kukan nan ya isa mana haka Samraah. Abinda ya faru dai ya riga ya faru ai. Sai fatan ALLAH ya baki lafiya. Ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, bana son ko a fuska ki nunama Alhaji ƙarami wani abu. Koba komai shi ɗin mijinki ne, kowace mace kuma da haka ta girma. Komai zai wuce kamar bai faruba. Naga ya fita kamar cikin damuwa, gaki ke kuma kina kuka. Dan ALLAH ki daure ya samu sassauci ko’a wajenki ne. Kinga yanzu daga police station ya fito tun safe amma ko gida baije ba sai da yazo nan domin dubaki. Alhaji ƙarami abin tausayine wlhy”.
Idanuna na buɗe a hankali ina kallonta, sai kuma na kai hannuna na sake share hawayen da suka gagara tsaya min. Cikin dasashjiyar muryata na ce, “Mama ni babu abinda nai masa fa. Kawai dai shi yasan mike damunsa. Mi yaje yi police station kuma?”.
“Nasan babu abinda kikayi masa Samraah. Amma nasan kukan nan da yaga kinayi ma ya isa ya sake ɗaga masa hankali. Ki daure ki daina kinji. Idan shima yaga kin kwantar da hankalinki zai fi samun nutsuwa wajen baki kulawar da duk kike buƙata. Sannan ya fuskanci abubuwan dake gabansa. Dan nasan akan batun nan naku wata sabuwar cakwakiyace kuma. Su suna kallo al’amarin da wata suffa daban, idan kuma baya gadama ba duk abinda zasu yi bazai sanar musu alaƙarku ba dan da kike ganinsa nan akwai taurin kai da kafiya. Bamu san abinda ya faru ba da safe folisawa suka cika mana gida wai sunzo kamashi” daga haka ta cigaba da lallashina har na sake komawa barci raina fal mamakin zancen kamashi da tace anyi, a yanda yake da kuɗi da power ɗin nan har jami’an tsaro zasu iya kamashi ashe?…
💦💢💦💢💦
“Ni nai sa’a da masoyi mai fara’a, shi ya fara sa shadda duk garinmu an shaida bai ɗaya. Ni na shirya, zana baka soyayya, koda ƴan baƙin ciki zasu haɗiyi zuciya. Ni na dace, na faɗa ko na dace, da sahibi imamullah mijin ƙwarai”.
Halime kenan, ke raira waƙarta cike da nishaɗi tana wanke-wanke a babban kitchen dake mallakin kowa da kowa. Wanke-wanke take na kwanikan da akaci abincin rana da tayi, yau kuma ne zata fita a aiki Mom ta amsa. Da farko aikinta take hankalin kwance sai dai shigowar Mom kitchen ɗin da abinda tai mata ya ƙona mata rai. Maimakon ta biyema Mom ɗin sai kawai ta shiga raira waƙa. Idan tayi wannan sai ta saki ta kama waccan harta kammala wanke-wanken. Kasa haƙuri Mom dake tare da mai-aikinta tana bata umarnin abincin dare da zata ɗora musu tayi. Cikin fusata ta shaƙo wuyan rigar Halime ta baya ta fusgota.
“K ƙaramar ƴar iska waƙe-waƙe ai bazai kai miki ba. Rama abinda nai miki ya kamata kiyi sai na san kin cika matsiyaciya”.
Idanu kawai Halime ta zuba mata, sai kuma tayi murmushi da kai hannu ta janye hannun Mom ɗin a jikinta. Ƙoƙarin juyawa take ta ƙarasa aikinta Mom ta sake ƙoƙarin damƙota cikin masifa da haushin shirun da tai matan, dan so take ta tanka mata akwai abinda zata saka mata a gashi. Wani shegen tsalle Halimen tayi gefe kai kace tayi gamo da wani bala’i ne. Hakan yasa mai aikin Mom da ita kanta Mom ɗin sai da suka zabura. Sai kawai tsabar wulaƙanci Halime ta fashe da dariya. Galala Mom da mai aikinta sukai suna mata kallon mamaki. Itako sai ta kallesu sai ta fashe da dariya, da tayi kamar zata tsagaita sai ta kallesu ta sake fashewa da dariyar. Wani irin tuƙuƙi zuciyar Mom ta shiga yi, tana yunƙurowa a fusace zata sake shaƙo Halimen sai kawai ta kauce mata tare da ɗaukar kayanta data tara a kwandon kife kaya tai ficewarta. Sai dai taje bakin ƙofa sannan ta ɗan dakata. Juyowa tai ta kalla Mom har lokacin fuskarta da sauran dariyar ta ce, “Ƴar baƙin ciki, so kike na biye miki muyi dambe dalin Imamu ya talauce saboda ke kin gama shan daɗin romin zabbi. To wallahi bashi yiwuwa nima sai na dandali arziƙin nan. Ɗan romon kifin nan dana kaji da ban samu naci a gidanmu ba sai na sha farina ya sake fitowa nayi ɓul yanda zanje ƴan tumaki ana ku matsa ga matar Alhaji Imamu nan ta iso haaaah”. Ta ƙare maganar da gatsine mata baki tana yin gaba abinta.
Kasa ko motsi Mom tayi, sai zuciyarta dake wani bala’in yunƙurowa. Wai itako yaya zatayi da mahaukaciyar yarinyar nan a gidan nan. Tayi bala’in, tayi fitinar, tayi boren, tana kan asirin amma duk a banza. Babu irin maganin da batai amfani da shi ba a kofar shiga ɗakinta da cikin abincin da Abba da Halime zasu ci amma ko gezau. Jiya har layun da teacher ya bata ta shiga har ɗakinta ta sanya a ƙarƙashin gado amma ko gezau, bayan kuma Umma ta tabbatar mata idan har ta saka layun yarinyar nan ta kwanta a gadon bazata kwana a gidan ba sai dai gidan Ubanta. Kuma komai dare sai ta koma garinsu a ƙafa. Haka ta kwana zaman saurare amma har gari ya waye babu ko dogon motsi daya faru a gidan. Sai ma da farar safiya Halimen ta tashi ta damesu da aiki da waƙe-waƙenta na iskanci kai kace ita ɗin jikar barmani choge ce ko shata.
A fusace itama ta bar kitchen ɗin tana dakama mai aikinta tsawa….
💢🌟💢🌟💢
Suna akan hanya nufar gida Hayatu ke bashi labarin rikicin da Ummie tayi yau a gida na neman Samraah. Har falon ƙasa ta sakko yau tana riƙe duk wanda ta gani ta bisa da kallo, sai kuma ta girgiza kai ta saki wanda ta kama ɗin ta tafi na gaba. Bayan ta gama bin kowa bata ga wadda take neman ba sai kuma ta zauna ta sanya kuka. Abin yayi matuƙar bama kowa mamaki. Nima na koma amso kayan da zasuyi amfani da shi ne na tadda wannan drama. Da ƙyar na lallaɓata bayan na ambata mata sunan Aunt sai ta shiga gyaɗa kanta alamar dai tabbacin ita ɗin take nema. Lallashinta nayi tare da tabbatar mata zanje na kirawo mata ita sannan ta yarda ta koma saman. Shine dana kai musu kayan na samu abinci na kai mata taci na bata magungunanta. Tana kammala ci sai barci. Koda na koma bayan magrib ɗin nan na samu har lokacin tana barcin. Yaya abin nan yamun daɗi, da’alama Ummie ta fara samun lafiya, tunda har take iya banbance mai ƙyautata mata. Lallai Aunty Samraah alkairi ce a rayuwarmu. Lallai akwai hikima a cikin sanadin shigowarta rayuwarmu”.
Kamar yanda Hayatu yayi tsammani baice komai ba. Sai dai a bazata badan kar ace yayi ƙarya ba sai yaga kamar yayi murmushi. Amma dai baya ce ba, tunda ba gani yay ƙuru-ƙuru ba kasancewar fuskarsa na gefe.
Shiru ya samu gidan da alama kowa ya kwanta, maimakon wucewa nasa sashen duk da yunwa da gajiyar dake addabarsa sai ya nufi sashen Ummie. Daki-daki yake bin ko’ina da kallon tsaff, gaba ɗaya sashen ya canja yanzu akoda yaushe cikin ƙamshi da tsafta yake. Duk da a yanzu falon farko ne kawai mai kujeru, amma sauran duk an kwashe komai tunda Samraah tayi magana. Duk da a ɗari-ɗari yake bai dakata ba sai da ya dangane da bedroom ɗin da a yanzu yafi samunta. Sassanyar ajiyar zuciya ga sauke yana mai jingina da bango da lunshe idanunsa sannan ya buɗe a kanta. Barci take har yanzu, sai kuloli masu ƙyau ata gefenta alamar abincine a ciki, yasan wanda Hayatun ne ya kawo, dan haka ya ƙarasa a hankali cikin takun sanyin jiki ya bubbuɗe kulolin. Lafiyayyen abincine da ko ba’a faɗa ba yasan Falak ce ta yisa duk da tana fama da kanta itama. Ajiyar zuciya ya sauke tare da furzar da iska mai nauyi daga bakinsa. Sai kuma ya maida komai ya rufe ya koma bakin katifar ya zauna. Blanket ɗin data ɗan zazzame ya gyara mata, a hankali ya kai hannu ya gyara mata hularta da ita ta zame. Sosai ya zuba mata idanunsa da suka kaɗa sosai. Daka gani kasan kukan zuci yake yi. Ya jima zaune a ɗakin duk da uban barcin da yake ji har kusan gabannin asuba ciwon kai ya takura masa sosai sannan ya miƙe……..✍️