Zafafa Biyar Tsutsar nama Part 3

Tsutsar Nama Part 2

This entry is part 2 of 4 in the series Tsutsar Nama

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒐

…….Mal Saminu yazo da daddaɗan labari garemu cewar na samu scholarship na cigaba da karatuna. Misalta muku yanda na shiga ɗunbin farin ciki a wannan ranar ni da ƴan uwana guda biyu ɓata lokaci ne. Yayinda Abba da Mom da su Baby suka nuna baƙin ciki da hassadarsu a fili akan hakan. Dan da farko ma Mom catai ƙarya ne babu inda zanje, Abba kuma ya goya mata baya, sai da Malam Saminu ya tabbatar musu da in har aka hanani akwai matsala. Dan kuwa gwamnati zata iya bibiyar al’amarin ta kuma hukunta duk wanda yay uwa yay maɗaukiya akan hakan. Jin wannan bayani ya sakasu barina dole nima a wannan shekarar aka shiga damawa dani a harkar karatu a B.U.K. inda Baby da yayanta Abbas suke nasu karatun suma.

     
          MATAKON FARKO

   Uhm dole a kira wannan ajin da matakin farko. Domin kuwa akansa ne komai ya fara, farawar da kamar itace farkon buɗe shafin rayuwata ta hankali, domin kuwa ko babu komai shekarata goma sha bakwai a yanzu. Zan iya cewa na shiga jami’a a sa’a. Domin kuwa course ɗin da nafi so da buri shina samu. A shekarar farko dana fara karatuna na fahimci halin da Baby ke ciki a school ɗin. Dan kuwa tuni ta ajiye karatu gefe sune shegun makaranta. Iyaka su shiga ofisoshin malamai su ɓata lokaci wani lokacin ma harda gidajensu ko a ɗaukesu a mota a fita da su, batun karatu kuwa sam babu shi tare da su, sunada group kuma. Amma abin mamaki sunansu na gaba-gaba a allon kafe jarabawa matsayin wanda suka cinye komai sai ɗan abinda ba’a rasa ba. Ga Yaya Abbas ɗin ma bata sauya zani ba. Dan shima ɗin dai yafi maida hankali ga siyasar makaranta da bin abokai masu motoci fiye da karatun. Bayan Yaya Musaddiq ban taɓa sanarma kowa a gidanmu ba, shima kuma tunda ya kwaɓeni akan hakan ban sake kawo masa zancen ba na maida hankali ga karatu na. Ina a wata na biyar da zuwa mukai karan batta da Mansoor. Mansoor Khalil Musa matashin yaro ɗan ƙwalisa. Ƙyaƙyƙyawan gaske mai tarin ilimi. Yana shekararsa ta uku a cikin b.u.k. A yanda Mansoor ke shigar suturu na alfarma da mota zai tabbatar maka da shi ɗin ɗan masu hannu da shuni ne. Sai kuma ƙwazonsa da ƙyawunsa ya sake jan hankalin ƴammata na cikin makarantar da yawa a kansa. Sai dai sam bai ɗaga ido ya kalli kowaccensu balle ya yarda magana ta haɗasu. Hakan yasa ake masa laƙabi da mutum mai girman kai. Domin kuwa bayan abokansa biyu babu wanda yake kallo da gashin arziƙi a ɗaliban dake ƙasa da shi harma wanda ke sama da shi. Amma sai me rana ɗaya ALLAH ya haɗamu a cafeteria. Muna tsaka da cin abinci ni da ƙawata ɗaya tilo Joy muna hirarmu cikin nishaɗi ya shigo tare da abokansa. Duk da yanda naji cafeteria ɗin ta ɗauki gunaguni a kansa banko kalla sashin da suke ba. Sai kawai jin abokinsa mukai kammu cikin gadara yace wai mu tashi zasu zauna. Cikin tsoro Joy tai niyyar miƙewa, amma sai na balla mata harara batare da nace komai ba. Zungurina tayi cikin roƙo da magana ƙasa-ƙasa ta ce, “Please Sam Gee mu tashi, ni sam bana son fitina. Kin san kuma halin guys ɗin nan ba mutunci ne da su ba”.
       Kai tsaye na buge hannunta a fusace da faɗin, “Idan kinga na tashi a wajen nan na gama abinda nake yi ne Joy”. Daga haka na cigaba da cin abinci na. Zaram Joy ta miƙe, amma a mamakinmu dama duk mutanen dake wajen sai muka tsinkayi Mansoor na faɗin ta zauna abinta, cikin rashin damuwa yaja kujerar kusa dani ya zauna shima. Hakan da yay ya bama kowa mamaki, duk da dama bawai an taɓa ganinsa yana faɗa da wani bane ba, kawai dai an sanshi shi mutum ne mai girman kai da rashin shiga shirgin kowa, abokansa ne masu zuba rashin mutuncin ga kowa. Dan ko magana ma sai yaso yayita da mutum. Suma abokan nasa zama sukayi bayan sun musu order ɗin abinda zasu ci, ko gezau banji ba, ban kuma kalli kowannensu ba harna kammala cin abincina na miƙe bayan na saki niƙab ɗin fuskata. Dan kullum nakan shigo makarantar ne cikin hijjabi har ƙasa da niƙab, ko kuma nurse mask da eyeglasses, dan haka ba kowa ne zai iya shaida maka fuskata ba hatta ƴan department ɗinmu ma. Hasalima sunan Hijjab girl na neman bina, dan kowa idan zai kwatance da sunana yakan kwatantani da hakan ne. Idan ka cire Joy da ke kirana da Sam Gee. Mun bar wajen yayinda mutane keta ɗan ƙusƙus ɗin magana, kun san dai ɗalibai da rashin raina abin kace nace, yayinda Mansoor ya bini da kallo tamkar ya samu television. Tun daga wannan ranar al’amarin kamar wasa, sai ya zam a duk sanda mukaje cafeteria cin abinci Mansoor da abokansa zasu zo. Kuma koda tare muke da wasu a tebiri sai sun tashesu sun zauna. Ban taɓa tanka musu ba balle nuna nasan sunayi har muka shafe kusan sati biyu a haka, kafin shi Mansoor ɗin da kansa ya fara biyan kuɗin abincin da duk muka amsa a kullum. Anyi na farko anyi na biyu a ran ta uku na taka masa birki dayin hakan cikin masifa da kowa bai san na iya ba, amma maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai ya tashi ma ya bar cafeteria ɗin abinsa. Naji haushi amma sai na dake, na kumayi alƙawarin saboda shi bazan fasa zuwa cafeteria ɗin cin abinci ba, yayinda shi kuma bai fasa biya mana ba, kuma koda mun biya ba’a amsar kuɗinmu sai ace ai anbiya mana. Abin na ƙona min rai, na kuma rasa yanda zanyi, ina kuma akan bakana na bazan daina zuwa cafeteria ba. Tun ina jin zan sharesa har na fara magana, nan ma a banza, sai kawai na daina dan na fahimci maganar tawa ke tunzurashi kamar. A haka muka cinye wata guda. Abu dai kamar wasa sai ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai shaƙuwa ta fara shiga tsakaninmu da Mansoor da abokansa. Takai idan ma basu zo cafeteria ɗin ba nakanji babu daɗi, kamar yanda shima yakanji idan bai ganni ba. Abinda zai baki mamaki kuma har lokacin ba wata doguwar magana ke shiga tsakaninmu ba, gaisuwa ce kawai sai zaman cin abinci………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.


Join our WhatsApp group here

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆

……Tun dai muna shashshare juna har abinda ke cikin zuciya ya bayyana, domin kuwa Mansoor ya fito fili ya nuna min shifa sona yake. Tom kun san dai halin mutuniyar taku, ban gusa ba na balbalesa da masifar da zuwa yanzu wasu sun fara kallona da sumumu kasau macijin sari ka noƙe. Maimakon yaji haushi sai ya dinga sakar min murmushi, wannan shine karo na farko da nabar zuwa cafeteria da tunanin ai Mansoor zai ƙyaleni na huta, dan ni kam burina karatu ba soyayya ba. Sai dai kuma ba hakan bane ba, dan kuwa dai shima salo ya canja ta hanyar nuna ba soyayyar za’aiba yanzu karatu ne gaba, idan komai ya daidaita nan gaba sai soyayyar ta koma gaba. Tun ina shashsha masa ƙamshi harna miƙa wuya. Kafin wani dogon lokaci kowa yasan soyayyar mu da Mansoor kasancewar sa mutum popular a cikin makarantar, duk da dai kamar yanda ta faɗa karatune gaba ba soyayya muke ba, dan da wahala ma kaji ya saka min batun soyayya, sai yayta amfani da hakan shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tdakaninmu. Komai ya cigaba da tafiya yanda ya kamata, Mansoor na taimaka min matuƙa a ɓangaren karatu ni da ƙawata Joy. Hakan kuma ya sake fiddo ƙwazona. Sannan soyayyarsa na bani kariya sosai daga tsagerun ɗalibai harma da malamai ƴan bani gishiri na baka manda. Tun sauran ɗalibai na ɗaukar soyayyar yaudara ko wata manufa har suka yarda ɗari bisa ɗari da gaske muke, saboda komai muna gudanar da shi a tsaftace.
       Tafiya tai tafiya, shekaru sunja abubuwa sun canja. Su Mansoor sun kammala karatunsu, sai dai kuma muna nane da juna ta waya. Yana kuma zuwa gida duk da ban taɓa yarda kowa yasan da batunsa ba bayan Yaya Musaddiq. Koda yake su Baby sun sani, dan nasha jin ma wai ai Baby ta jima tana son shi, sai dai bansan minene ya faru koya katangeta da sanarwa a gida ina soyayya da wani ba, sannan ita bata taɓa tarata da batun Mansoor ba kai tsaye, sai dai tai habaici a wasu lokutan ko shaguɓe, ni kuma sai ban taɓa kulata ba ko nuna na fahimta. Ina zangon ƙarshe na kammala karatuna na fahimci ashe Yaya Musaddiq shike biyamin kuɗin makaranta babu wani scholarship dama. Ya haɗa baki da malamin namune kawai, dan a yanzu haka shima Hafizzullah yana a level 100 a jami’ar Umaru Musa ƴar-aduwa dake Katsina. Shima kuma dai da batun scholarship ɗin nan aka rufe bakunan su Uncle Imam duk da an kwashi tashin hankali sosai fiye da nawa lokacin kasancewar shi Nabil bai samu ya tafi ba har yanzu. Ranar da nasan wannan sirrin nasha kuka a gaban Yaya Musaddiq. Shiko ya dinga lallashina yana murmushi, a ranar ya sanar min da komai bai ɓoye min ba. Dan yace bazai taɓa iya zama bamuyi karatu ba, dan haka ya zaɓi bi ta wannan hanyar domin gina gobenmu. Shiko aikin kanikancinsa ya ishesa in sha ALLAHU. Na nuna masa ban yarda ba, shima dole ne musam yanda zamuyi ya koma karatu, dan kuwa zuwa yanzu yana samun kuɗi sosai, sai dai duk a hidimar gidanmu da karatunmu suke tafiya, dan har yanzu bai tsinanama kansa komai na rayuwa ba irin burin matasa na son gina gida da sauransu, hatta budurwa ma baida ita shi sam. Ya min alƙawarin idan lokacin komawar yayi zai koma in sha ALLAHU.
      Alhmdllh na kammala karatu cikin nasara, yayinda na riga Abbas da Baby da suka rigani farawa kammalawa saboda su sun saka wasa a karatun nasu. Bakuma su da niyyar gama school ɗin da alama, maybe sai an korosu su shiga hankalinsu oho, dan gasu nan koda yaushe cikin maimaita shekara suke. Bayan kammala karatuna da wasu watanni Mansoor yay uwa yay maɗaukiya ya sama min aiki a wani gidan tv da rediyo dake tashe a wannan lokacin. Hakan ya saka Yaya Musaddiq farin ciki, yayinda ran su Abba yay baƙi har suka kasa ɓoye hassadarsu a fili musamman ma Mom, dan da farko ma tuburewa tai akan tunda na gama karatu aure kawai ya kamata Abba yay min, wai akwai wani ɗan yayarta ya jima da cewa yana so na. Abba har ya ɗauki zancenta da muhimmanci niko na tibire nace wlhy idan aka aura min shi kashesa zanyi, dan ni ban shirya aure ba sai na fara aiki na. Ganin fa da gaske nake kuma sun san tsurin idona dan randa yaron yazo hira wajena zagin ƙare dangi na masa, hakan yasa Abba ya kashe maganar, sai dai ban san yaya sukai da matar tashi ba a ɓoye, a zahiri dai yace ya kashe wannan batu naje nai aiki na. Amma ya bani nan da ƙarshen shekarar nan na kawo miji. Oho ban wani damu dasu ba na fara aiki na, dan nasan dai inada Mansoor ɗina a hannu. Cikin nasara kafin kace mi na samu karɓuwa, albashina na farko dana biyu dana uku na haɗa da shi na sayama Yaya Musaddiq fili da taimakon Mansoor. Lokacin dana damƙa masa takardun sai kawai ya fashe da kuka. Nima kukan na fashe da shi tare riƙe hannunsa ina roƙonsa dan ALLAH ya daina, shifa uba ne a garemu yanzu, idan bamu masa hidima da abinda ALLAH ya azurtamu da shi ba wa zamuyimawa. Da ƙyar dai mukai shiru dan dama a wajen aikinsa na samesa, gudun kada na bashi a gida wani yaji a ƙwace. Tom Alhmdllh, yanzu dai a taƙaice watanni na shida kenan da fara aiki na, ina kuma matuƙar jin daɗin da nuna kwazo matuƙa. Dan bada ƙwaƙwalwa kawai nake aikin nan ba, harda zuciyata da ƙwanjina gaba ɗaya. Gashi ALLAH ya bani farin jinin mutane, dan tunda na fara gabatar da wani shiri akan matasa shikenan kamar nayi kiranyen masoya, dan da a iya rediyo ne kawai, amma wata guda kenan da fara gabatar da shi a television saboda yanda oganmu yaga shirin ya amsu yana sake jawo hankalin mutane ga channel ɗin tamu sai abin yay matuƙar birgesa. Dan haka aka sake ƙarfafa shirin ta hanyar fiddoshi a fanninmu na television ma, Alhmdllh kuma komai na tafiya fiye ma da yanda akai zato da tsammaninsa…….✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

Click here to join our group


….A gurguje nake faman shiryawa saboda makarar da naso nayi. Ba kuma komai ya jawo min hakan ba sai sharaɗin girka breakfast ga masu gidan a kullum kafin na fita bisa umarnin Mom bayan gyara ko ina. Ban isa nace bazanyi ba, dan na fahimci hanyar da zata tuzguɗe ɗan aikin nawa take nema. Dan haka na tsarama kaina time table ta yanda bazan cutu ba. Kullum ƙarfe huɗu na asuba na tashi, zan shiga kitchen na ɗaura breakfast. Inayi ina ɗan wasu aikin gyara gidan har na kammala, dana gama na maida hankali ga sauran ayyukan, ALLAH na taimakona kafin ai kiran sallar farko zaka samu na kammala komai, da Yaya Musaddiq ya fahimta ma sai ya zam shima yana tasowa muyi tare dandanan saina kammala nai shiri. To yau an samu akasi ne da alama Yaya ya makara, dan har na kammala bai shigoba, gashi ma har na gama shirina. Nayi ƙyau sosai cikin baƙar abayar dana saka, nai rolling veil ɗin ta da ya sake fiddoni tsamm kamar wata ɗiyar larabawa. A ɓangaren ƙyawun fuska dana jiki babu abinda zance sai Alhmdllh, sai dai ban taɓa jin alfahari ko son yin ɗagawa da wannan baiwar da ALLAH yay min ba. Nakan gode masa ta hanyar suturta kaina da ƙyaƙyƙyawar shiga, dan kullum cikin dogon hijjabi nake da nose mask. Dan ƙaryane kace ka ganni babu nose mask a fuska. A lokacin dazan fara gabatar da shirin nan a sashen tv ansha gumurzu dani a ranar farko dan har hawaye saida nayi saboda ciresa, dole dai na haƙura daga ƙarshe ma toshe idona da eyeglasses sannan na iya gabatar da shirin, a hakanma ina jin kaina kamar ba daidai ba.
    Kamar kullum mask ɗina na saka, sai dai yau baƙi ne, yay min ƙyau sosai dan ƙyawawan fararen idanuna masu girma da cikar gashi kawai ake iya gani. Cikin takun nutsuwata na fito, ga wani ƙamshi mai sanyi yana tashi a jikina, sai dai bamai ƙarfi bane, dan sai ka kasance a kusa dani sosai zaka iya jinsa yanda ya kamata. Sauri nake, dan haka bana fatan haɗuwa da kowa na gidan. Sai da na leƙo na tabbatar babu kowa a falon sannan na ƙarasa fitowa. Nan ma da sanɗa na fita, inayi ina waigen bayana. Ban sami nutsuwa ba saida na ganni a waje, na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina sakin murmushi, bag ɗita mai zubin school bag na rataya hannunta guda a bayana, ɗakin yaya na fara leƙawa, sai muka kusa cin karo dan shima yana niyyar fitowa ne.
       “Kandala ƴar jaridan Yayanta”.
   Ya faɗa cikin tsokana yana mun murmushi. Murmushin nima na mayar masa ina ɗan rufe fuskata da tafin hannuna. Sai kuma na janye ina ɗan ɓata fuska da faɗin, “Ai ni fushi ma nake da kai yaya. Na manta nai maka murmushi ma.”
     Cikin dariya ya ce, “Oh oh Tom ayi haƙuri Ƴar ficika, nasan laifin Yaya dai rashin shigowa taya aiki, wlhy jiya na matuƙar gajiya ne a gareji, shiyyasa tunda na samu na kwanta ko juyi banyi ba sai kawai naji ana sallame salla. Dan yau ma sai a ɗaki nayi tawa dan abin kunya”.
     Dariya na ƙyalƙyale da ita sosai saboda yanda yay da fuska kamar wani ɗan yaro. Sai kuma na kalla agogo da sake kallonsa. A zabure na ce, “Uhm Yaya zan makara. Ni dai taho muje ka saukeni, dan yau a mashin ɗinka zanje office, ina son na baka wani labari a hanya”.
         Babu musu yace min muje, saboda karna makara bai shiga gidan ya gaidasu kamar yanda ya saba ba. Ya kuma san sai yasha masifa akan haka ɗin, amma yafi buƙatar farin cikina. Cike da farin ciki muka bar ƙofar gidan tamkar bamu da wata damuwar rayuwa. Maganar da nace masa zamuyi na fara masa. Ba komai bane face batun fara gininsa, dan ina son a fara ya samu yay aure. Bai dai ce dani komai ba face murmushi kawai har muka isa, a ƙofar gate ya ajiyeni. Har lokacin fuskarsa da murmushi ya kalleni. Sai kuma ya ɗan ja fasali da harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallona.
      “Samraah!”.
   Ya kirayi sunana da tsantsar kulawa. Amsa masa nai nima da girmamawa. Numfashi ya sake furzarwa da ɗan duƙar da kansa ƙasa kamar mai nazari, sai kuma ya ɗago yana sake kallona. “Samraah inaga ba batun gini ya kamata muyi ba yanzu. Kamata yay ace mu tattali abinda muke samu domin kayan aurenki. Kin girma Samraah, kin kammala karatunki cikin aminci, ga aiki kin samu cikin sauƙi, kina da Mansoor a hannu, a ganina batun aure ya kamata ace kunyi da shi yanzu kafin ma lokacin da Abba ya baki ya cika. Kin san dai halin Mom basai na faɗa miki ba, wannan shirun da kikaga tayi wlhy bazai zama na alkairi ba. Gara mu fiskanci zahiri. Wannan ƙaramin jikin naki yabar kwasarki ba baya kike komawa ba shekaru ne ke ƙaruwa. mutanen wajene kawai suke miki kallon ƴar ƙarama ganinki ƴar ficit. Ni nawa batun mai sauƙi ne, namiji ne ni, konan da shakara goma bazan tsufa da aure ba ai. Ga Hafizzullah yanzu ya fara karatunsa, kamata yay har sai shima ya kammala koda zan yi batun wani aure, sai nake ganin kamar hakan zai fi, ni dama ba wata budurwa ba a ƙasa”. Ya ƙare maganar da zolaya.
     Baki na kumbura cikin ƴar shagwaɓa nace, “Yaya ni duk ban amshi wannan ƙorafin naka ba sam. Kadai bari mu samu lokaci mu zauna mu tattauna. Amma batun bazakai aure ba sai nayi ko Hafiz ya kammala makaranta duk baima taso ba. In dai Dan budurwar ce zan maka, amma bazan bari ka cigaba dama waɗan can mutanen bauta ba. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Wannan lokacin ya wuce muma yanzu munsan kammu”.
      Kansa kawai ya girgiza, nasan kuma ba komai ya sakashi yin hakan ba sai ganin yanda na ƙarasa maganar a hasale. A bayyane fushina da zafin mariƙanmu ya gama bayyana. Maimakon yace wani wani sai kawai yaymin nuni da gate alamar naje ciki. Banyi musu ba nai masa sallama na nufi shiga ciki ina kumbura baki da fiki-fiki da idanu najin haushi……..✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

Click here to join our group

Part 5

……..Ina zama office ɗinmu daya kasance mu biyar ne a ciki Asiya data kasance duk tare muke anan ta shigo da sallama. Ganin takardu a hannunta ya tabbatar min da ba yanzu ne ta shigo ba. Gaisawa mukai farko, kafin ta ɗora da faɗin, “Samraah MD na kiranki kuwa. Ya ce ki maza kuma dan zaiyi baƙi”.
       Kaina na jinjina mata batare da nayi magana ba na miƙe ina sake gyara zaman facemask ɗina daya ɗan zamo ta saman hanci. A cikin takuna na nutsuwa da yanga da mutane da yawa ke fassarawa na fito. Duk wanda na gamu da shi nakan ɗaga masa hannu da cewa good morning, wasu sukan ɗan tsokaneni. Sai dai iyakata murmushi kawai dan nifa idan ba kayi dogon zama dani ba bazaka taɓa tunanin inada surutu ba sam. Ban cika yawan magana a ko ina ba sai in nice naga damar hakan. Shiyyasa da yawan mutane ke ɗaukata mai shiru-shiru. Har wasu kan dangantani da hakan da iya yardarsu. Basu sani ba idan aka taɓoni banda ragi banda ragowa sam. Na isa office ɗin MD, bayan nayi knocking sai da nai tsaiwar kusan minti ɗaya kafin ya bani izinin shiga ciki. Kallo ɗaya na masa na ɗauke kaina, dan mutum ne shi mai shegen son kallon mutane kamar zai cinyesu. Cikin son kawar da idanunsa dake yawo a kaina ya ce, “Zauna”.
      Zaman nayi a ɗarare nace da shi, “Good morning sir”.
       A taƙaice ya amsani da, “How are you?”. Batare da ya jira amsawata ba ya cigaba da maganarsa yana turomin wata ƙyaƙyƙyawar mujalla da wani envelope mai kama da invetion card. Bana ganin fuskar mutumin daya mamaye bangon farko na mujallar gaba ɗaya. Sai jikinsa dake sanye cikin wasu shegun suit sky blue zuwa ƙafarsa dake cikin cover shoes dake wani shining duk da kuwa a hoto ne. Zaune yake a kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya, hakan ya bani ɗan damar ganin hannunsa mai ɗauke da dogayen fararen farata dake riƙe da glass cup da guntun drink ke ciki. Sai zobe guda ɗaya mai ƙyau sosai a yatsarsa…
         Duk da baifi a sakanni goma na ƙarema hoton irin wannan kallon ba a ɗan kamar fusace naji gyaran muryar MD a kaina. Saurin gyara yanayina nayi na maida hankalina gareshi, fuskarsa a ɗan ɗaure yana famar yamutsa fuska ya ce, “Ɗauka ki duba”. Ɗaukar nayi, sai dai ban kallaba yanzu na maida hankali garesa da nuna alamar shi nake saurare. Shima sai naga ya ɗan sassauta yanayinsa. Ya nuna ni da faɗin, “Samraah na zaɓoki ne saboda nasan zaki iya. Wannan mujalla ce ta TAURARINMU A YAU data fita jiya. A gaba ɗaya abinda ke cikinta ya ta’allaka ne akan matashin ɗan kasuwar nan da sunansa ke amsa kuwa a ƙasashenmu na Africa dama duniya a ɗan tsakanin nan. Wato AWWAB  EL-MU’AZZ. sai dai kowa yafi saninsa da MAASH ne. Maash ɗan arewa ne haifaffen garin Kano sai dai mazaunin jihar Lagos. Yana da tarin cibiyoyin kasuwanci a kudancin ƙasar nan dama wasu ƙasashen Africa. Hakama a ƙasashen turawan da larabawa yana da rassan kasuwanci. Amma abin mamaki bai taɓa kafa wani abunsa a arewacin nan namu ba. Hakan yasa mutanenmu sukai masa ca, suke kuma sukarsa akan hakan, har takai suna ƙalubalantar dukiyar tasa musamman idan akai dubi da ƙarancin shekarunsa. Duk da kuwa an san mahaifinsa nada kuɗi, hakama Kakansa sanannen mutum ne, sai dai ko kwatar abinda shi MAASH ɗin ke da a yanzu mahaifinsa bai mallaka ba. Kace nace ya sake yawaita a kansa ne a watanni uku da suka gabata, dalilin bayyanar Companyn sa na jirage dake jigilar mutane daga Nigeria zuwa ƙasashen ƙetare. Domin a farko jirage goma ne ciff suka fara aiki. Sosai manyan gidajen jaridu sun so tattaunawa da shi amma Maash yaƙi bada kowacce irin dama. A duk lokacin da hakan ta taso sai dai a tattauna da P.A ɗinsa. To nadai taƙaice miki zance a yanzu haka bayan ka-ce-na-ce da aka sha yimasa akan gudun arewa da ƙaruwa Mujallar nan ta fitar da bayanan buɗe ɓoyayyen katafaren company da kusan wata uku kenan ana aikinsa batare da mutane sun san na wanene ba a cikin Kanon nan. Company ne na ƙera motoci da babura da abubuwa masu yawa da suka shafi ababen hawa. Irinsa shine na farko a Africa, a duniya kuma na uku. Kuma Maash da kansa zai zo Kano bikin buɗesa. Hakan yasa tunda naga mujallar nan na shiga na fita sai da na samo mana invetion card ɗin shiga wajen, dan hatta ƴan jaridar da zasu halarci wajen a ƙa’ide suke. Dan haka na kwana nazari a daren jiya, na kuma hanga na hango a kaf gidan nan kece nake ganin zaki iya mana wannan aikin, fatanmu kiyi duk yanda zakiyi kisa Maash ya magantu a gaban ƴan jarida karo na farko dan ALLAH. Hakan zai zama ba ƙaramar nasara ba a garemu da ma wannan gidan namu baki ɗaya. Sannan ke a karan kamki ma wata sabuwar ɗaukakace da nike da tabbacin zata zamewa rayuwarki alkairi in ALLAH ya yarda.”
        Wani irin nauyi naji kaina yamun, dan haka da ƙyar na iya fisgo kalma ɗaya akan harshena na furta. “Amma Sir kaifa kace bai taɓa yarda yayi hira da ƴan jarida ba. Taya kake tunanin ni zan iya samo wannan nasarar? Yaushe ma na fara aiki, wane matsayi na taka a cikinsa? Ni wacece da zanyi abinda manyan ƴan jarida gogaggu suka gagara yi cikin sauƙi haka?”.
       “Ba cikin sauƙi bane Samraah. Sannan al’amarin ba iyawa bace ko kaiwa wani matsayi. Sa’a ce kawai kuma kowa da irin tasa a rayuwa. Nima ba ina ji bane wai lallai sai hakan ta kasance ba. Fata dai nake yi da jin yaƙinin zaki iya in sha ALLAHU”.
    Shiru kamar bazance komai ba, kafin kuma na sauke nannauyar ajiyar zuciya. Na ce, “Shike nan Sir zan gwada na gani, ai da gwaji jirgin sama ya tashi sama daga bisa ƙasa. Amma dai bani kaɗai ce zanje wajen ba?”.
      Ƴar dariya yayi a karo na farko, cikin tsokana ya ce, “Kada kice min ke ɗin matsoraciya ce mana. Bayan kuma kallon jaruma nake miki. Kallabi a tsakanin rawuna”.
    “Humm Sir bazaka gane ba. Irin waɗan nan mutanen da suke jin tamkar ma duniyar su suke mata alfarma ba itace ke musu na basu fili a cikinta ba suna kallon mutane ne tamkar wasu dodannin tsaffi a rayuwa. Dan a kullu yaumin zaka gansu ne zagaye da masu tsaro a kowacce kusurwa ta rayuwarsu. Ni gaskiya bana son ƙasƙanci koda a wajen wanda ya fini ne”.
         “Wannan itace ɗabi’a ta cikakken mutum ai Samraah. Duk wanda yasan darajar kansa haka ake so kuma ya kasance. Kada ki damu bake kaɗai zaki je ba. Hasalima ke aikin ki shine gabatar da shirin kawai. Akwai Davido da Mansoor da Khulsoom a tare dake. Yanzu sai kije ki tsara tambayoyin da zaki masa ki kawo min, ki nutsu sosai wajen tsarasun daga nan har zuwa Monday, kinga kinada kwanaki kusan huɗu kenan tunda yau muna alhamis. Kije da wannan mujallar domin duba abinda suka rubuta a kansa. Za kuma ki iya wani binciken a kansa ɗin dai koda ta hanyar yanar gizo ne ko wasu mutane. Hakan da zakiyi ne zai baki damar tsara abinda ya dace a kansa ɗin, dan ina fatan mu zama mune taurarin mako mai zuwa”. Ya ƙare maganar yana murmushi.
    Nima dai murmushin nayi, dan ya ba ni dariya. “In sha ALLAHU zanje nayi nazarin Sir. Maybe ma kafin Monday ɗin kaga na tura maka duk abinda na tsara ɗin koda ta WhatsApp ne”.
         “Masha ALLAH, ALLAH ya bada ikon hakan. Amma dai baki da matsala kibi komai a sannu tunda nunada kusan kwana goma kafin ranar”.
     “To nagode Sir”.
  Na faɗa ina miƙewa hannuna ɗauke da Mujallar. Harna fice a office ɗin ina jin idanunsa a kaina. A raina nace (Maye kawai sai dai kaci kanka kasha baƙin ruwa)…….✍️

Tofa masu karatu yaya kuke tunani akan wannan aiki da MD ya damƙama Samraah. Shin zata samu damar haɗuwa da wannan matashi mai wahalar sha’ani mai suna Maash ko kuwa?.

Idan ma ta haɗu da shi ɗin taya zata iya abinda wanda suka fita faɗa aji da gogewa akan irin aikinta suka kasa?.

Shin wai wanene ma Maash ɗin nan ne? Minene dalilinsa na gudun yarda ya bayyana asalinsa ga ƴan jarida. Miyyasa yake ɓoye kansa? Minene baya son a sani game da shi ɗin?

Duka wannan amsoshin suna a kundin littafin TSUTSAR NAMA… masu iya magana sunce wai ITAMA ƊIN NAMA ce. Kuzo ku mallaki naku domin jin abinda littafin zai zo muku da shi, domin kuwa ƙumshe yake da abubuwa masu ban mamaki, al’ajabi, makirci, soyayya, cakwakiya, zamba cikin aminci, tare da ɗan karan munafunci daga ɓangarori daban-daban.

In sha ALLAHU sayen nagari maida kuɗi gida😊😉😉😘😘🫡🫡.


Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne.

Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

Click here to join our group

Part 6

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙

…….Zaune na kai jagwaf a kujerar zamana ina dangwarar da mujallar da MD ya bani a desk ɗinmu. Mujallar Ruƙayya ta ɗauka tana faɗin, “Woow kaga wani handsome guy anan. Sam G daga ina haka? Waye shi?”.
     Baki na ɗan taɓe kaɗan batare dana amsa mata ba na shiga ƙoƙarin kunna computer ɗin gabana. Itama batabi takan jiran amsar tawa ba ta shiga karanta abinda ke jiki. Wata ƴar zaburowa tai da zazzaro idanunta waje tana faɗin, “Kutt Sam-G wannan ai Maash ne.”
   Duk ɗagowa sauran abokan aikinmu sukai suma suna kallonta. Sai kuma suka maido kallonsu gareni kamar yanda take kallona. Ganin na ɗauke kai tamkar bamma san mi sukeyi ba yasa suka sake maidawa kanta tare da miƙewa suka nufeta. Rufuwa sukai akan mujallar suna karantawa su duka huɗun, jin yanda duk suka nutsu yasa na ɗago na kallesu, batare da nace dasu komai ba na warce mujallar a hannun Ruƙayya. Ƴar harara na sakar musu ganin duk yanda suka ɗago suna kallona. “Malamai kowa ya koma kan aikinsa. Kun wani zauna karanta abinda bazai amfaneku ba.”
     Ƴar dariya Usman da Asiya da Khalid sukai, yayinda Ruƙayya ta balla min harara. Magiya Usman ya shiga min yana faɗin, “Sam-G Please ki bamu mu ƙarasa karantawa, anya kinsan kuwa wanene wannan na jikin hoton?”.
       “ALLAH bazan baku ba kuje kuyi aikinku, mi sanin nasa kuma zai amfaneni da shi da zan damu da so.”
   Magiya suka shiga mun nace bafa zan basu ba, dole suka haƙura suka barni badan sun so ba. Sai dan ayyukan dake gabansu. Nima nawa aikin na cigaba dayi batare dana sake bi takan mujallar ba. Haka muka cigaba da aikin gabanmu har lokacin tashi yayi. Tarkacena na shiga haɗawa domin wucewa gida aɗan gaggauce, dan nasan Mansoor na jirana. A karo na farko idanuna suka sauka akan fuskar mutumin dake jikin mujallar lokacin da nake ɗakkota zan saka a jakka. Duk yanda naso kauda idanuna hakan ya gagara, dole nai tsai ina kallon ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Sam a zahirance baya kamanni da ƴan Nigeria ma bare Kano, duk da kuwa muma munada ƙyawawan fiye ma da kamarsa, sai dai kuma yanda hasken fatarsa yake tsaka tsaki dan bai wani yi haske dau ba zaka iya kiransa ko haif caste. Abu mafi ɗaukar hankali a fuskar tashi siririn baƙin gashin daya zagaye kumatunsa har zuwa haɓarsa ya kuma zagayo ta bakinsa ɗan ƙarami kamar ba namiji ba. Sam babu fara’a akan fuskar, sai hasken idanunsa dake a wani irin salo kamar na mai jin bacci. Abin mamaki tsakkiyar ƙwayarsu blue-blue zaiba-zaiba bansan yazan kirashi ba, ataƙaice kamar dai na mage ko masu jajayen kunne oho duk yanda kuka fassara. Sai cikakkiyar girarsa mai faɗi. Sosai na sake waro idanu lokacin da nakai dubana ga sumar kansa. Kitso ne guda huɗu akan nasa a kusan tsakkiyar kan dan ta gefe-gefe an aske sai saisayayyen sabon gashin daya kwanta luf-luf baƙi siɗik. Daga ta bayan kunnensa kam a dai-dai dokin wuyarsa zanen tattoo ne anyi fuskar zaki. Kunensa ɗaya manne da ɗan kunnen stone daketa wani irin sheƙi da ɗaukar ido kalar sky blue mai garai-garai kamar diamond. Wani wawan tsaki da ban san dalilin yinsa ba naja ina mai tura mujallar a bag ɗin. Dan sam nikam abin bai mun ba. Ɗan musulmi haihuwar arewacin Najeriya cikin Kano ne haka tamkar wani jinin yahudawa. Toni wannan tunda ma ba wani kama yake damu ɗin ba sosai ai gara ma a dinga jinginashi da ƙasashen ƙetaran mu bar musu kawai yafi, dan gaskiya aka bincika kam a cikin iyayensa akwai wanda ba bahaushe ba ko nace ma ɗan Nigeria gaba ɗaya. Da wannan mitar na fita a office ɗin, dan kusan ma nice ƙarshe su Khalid duk sun fice.
      Horn da Mansoor yayi min ne ya ankarar dani in da yake, da alama dama ni yake jira, dan ina shiga yayma motar key muka fice. Har muka fita a layin da station ɗinmu yake muka hau titi sosai babu wanda yay magana a cikinmu. Sai zuwa can Mansoor ya katse shirun namu da faɗin, “Madam duk gajiyar ce haka?”.
    Cikin ɗan yatsine fuska na ce, “Kawai dai”.
Maimakon yaji haushi sai yay murmushi kawai, dan ya fahimci yau ɗin ƴan shiru-shirun ne a kaina. Dan ko ɗazu da muka haɗu dama bawani hira nayi sosai ba. Baiyi fushi ba ya cigaba da jana da hira, tun dai ina amsawa a sama-sama harna ware, dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi tsakanina da Mansoor. Muna a gab da isa anguwarmu na takalo masa maganar da Uncle yay min akan aure kamar yanda Yaya Musaddiq ya bani shawarar nayi. Kamar wanda ya ɗan razana ya kallan, sai kuma ya maida hankalinsa ga titi da sauri ganin nima shi nake kallo..
       “Lafiya kuwa? Naga kamar ka razana?”.
      Murmushi ya saki tare da ɗan dubana, sai kuma ya gangara gefen titi ganin yanda duk na wani tsaresa da kallo. Sai da ya kashe motar da ƙyau ya juyo yana fuskantata. Ɗauke nawa idanun nayi daga kansa. Murmushi naji ya saki mai ɗan sauti, sai kuma ya fara magana a hankali. “Dole ne na razana ai Baby, dan farin ciki ne da yazo min a matuƙar bazata. Kema kin san tsahon lokacin dana ɓata ina fatan jin wannan furucin daga bakin ki. Taya yau na jisa ba zanji kaɗuwar farin ciki ba. Ki godema ALLAH ma da ban saki kan motar mun daki fitila ba. ALLAH na gode maka da ganin wannan rana a gareni, ni Mansoor zan mallaki TAURARUWAR MATAN DUNIYA”.
      (🤥Ni dai banda ni eh🥱).
  Murmushi ne ya suɓuce min, na kauda kaina gefe inayi duk da kuwa akwai facemask a fuskata, harma da eyeglasses dakan ƙara fiddo tsarin ƙyawuna a duk sanda na saka shi. Ganin murnar tashi bazata ƙare ba ga shi lokaci na tafiya murya can ƙasa-ƙasa na ce, “Please ka tada motar nan magrib fa zai yi”.
         “A’a Madam, barni na gama murnata dan ALLAH. Mansoor ne fa zai mallaki Samraah Gwarzo. Wani shagalin ma ai sai naje gida hajjaju”.
    “To nidai kaini gidan, idan kaje sai ka cigaba dayi”.
    Da ƙyar na samu ya tada motar muka tafi, bakinsa baiyi shiru ba har muka ƙarasa. Nidai na sungumi bag ɗina na fice ina cemasa sai da safe.
  
       A falo na iske duk mutanen gidan. Amma babu Hafizzullah da Abbas, da Nabel, hakama Abba da alama bai dawo ba shi da Yaya Musaddiq. Koda yake shi dama Yaya Musaddiq sai kai ma wata baka gansa zaune a falon nan ba. Iyaka ya shigo ya gaida Abba da dare, daga haka ya koma ɗakinsa, abincin gidan ma yakan daɗe yanzu bai cisa ba duk da nauyin kawowa ta dawo kansa badan kuma Abban ya rasa ba sai dan haka Mum ta tsara ayi. Mum ta watso min wata muguwar harara da ta sakani tura baki ta cikin mask ɗina. Batare dana sake kallonta ba nace “Mum good evening”.
    “Ko kuma good uwarki ba”. Ta amsa a fusace. Dariya sosai Baby da Bibaa suka kwashe da shi. Sai autansu dake ta aikin homework ɗinsa kamar ma bai san abinda ake a falon ba. Tsawa ta daka min kan nazo.  A hankali na nufi gabanta na durƙusa, bamma gama kaiwa ƙasa ba naji saukar lafiyayyen mari daya nema gigitani, dan har eyeglasses ɗina sai da ya faɗi. Idanun kawai na rumtse da ƙarfi, sai dai naƙi yarda hawayen da suka ciko min ido su zubo. A fusace ta ce, “K dan uban uwarki har ni zan sakaki aiki ki tafi sabgar gabanki ki bar min?”.
     Karo na farko na ɗan kalleta. Cikin danne kukan dake neman kufce min na ce, “Mum wlhy duk abinda kikace nayi ban tafi ba sai da nayi sa”.
    “Oh ƙarya nake miki ke nan ko? Miyar da kika bari akan wuta uwarki ce tai fatalwa ta ƙarasa min?”.
    Wani irin rumtse ido na sake yi ina cije lips. Babu abinda kemin ciwo a duniya sama da zagin iyayenmu da Mum kanyi. Kuma in har tayi hakan bana iya daurewa sai na mayar mata da murtani. Yanzun ma hakance ta kasance. Dan cikin kaushin murya da tsiwa na ce, “Mum ai kunsha tubarraki kenan, dan nasan duk abinda zai fito daga Ummie na mai albarka ne, to balle kuma ace fatalwarta, ai nasan albarkar sai ta ninka ma. Bara naje nai salla na sake mata addu’a dan gobe idan zatazo a fatalwar ta dafa mana har abincin ba ƙarasa miya kawai ba”.
     Ba Mum ɗin ba hatta su Baby sagade sukai suna kallona. Nikam ko’a kwalar rigata na miƙe tsam. Batare dana yarda na kalla kowa a cikinsu ba na nufi hanyar ɗakinmu ni da su Bibaa, dan Baby tun muna yara tace bazata zauna dani a ɗaki ɗaya ba. Hakan yasa aka haɗani da Bibaa da auta. Nasha wahalar yaran sosai, dan dukkan nauyinsu kaina ya koma, ga fitsarin kwance. Dole nabar musu katifar na dawo kwana ƙasa saman tabarma. Bayan na fara zama budurwa nazata za’ace nabar cikin yaran na koma ɗakin Baby, amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Sai ma wani sabon salon iskanci da ita Bibaa kan min yanzu, wai ita tana takura gaskiya a ɗakin dan munyi yawa. Ban taɓa cemata komai a kan hakan ba dai, dan fatana ma a yanzu Mansoor ya fito kawai ayi auren mu a wuce wajen. Shima Yaya Musaddiq yay nasa Hafizzullah ya koma gidansa ba shike nan ba mun bar musu gidansu……..✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku.

Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

Click here to join our group

Part 7

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏

…….Ina shiga ɗaki kukan da banyi ba a gabansu ya kufce min. Ban yarda nai zaman yinsa ba, na zame kayan jikina kawai na nufi bathroom. Tsayawa kawai nai ina kallon bayin raina a matuƙar ɓace. An masa kaca-kaca tamkar banyi wahalar gyaransa ba kafin na wuce. Nasan Bibaa ce tai masa haka. Dan tsabar iskanci har pad data cire guda biyu ta yasar a bayin da pants ɗinta. Inada ƙyanƙyami sosai a rayuwata, dan abu kaɗan ke ɗagamin hankali, shiyyasa ma nake bugar jikina na tsaftace gidan yanda ta kamata batare da jin ƙyashi ba. Hawaye tab da idona na shiga gyaran bayin, sai da na maidashi ƙal na tattara trash ɗin data tarama mutane na fitar. Har lokacin suna a falon zaune suna kallo har Mum ɗin, kai kace basu ji sallar magrib da akeyi ba. Na jima da fahimtar Mum saita gadama take salla, shiyyasa ƴaƴan nata ma dai gasu nan sai a hankali babu wanda ya damu da ibadar. A da Hafizzullah har ya fara ɗaukar ɗabi’ar, sai da na miƙe kansa ni da Yaya Musaddiq tamkar bama ƙaunarsa sannan. Sake zuwa nai na wucesu na koma ciki. Sai da nayi wanka na saka doguwar riga mara nauyi nai salla. Bayan na idar zaman yin karatun Alkur’ani nayi, ban ɗaga a wajen ba sai da akai isha’i, har lokacin kuma ina jiyo hayaniyarsu a falon, sallar dai bazasu tashi suyi ba. Falon na fito na wuce dan ɗaukar abinci na, amma sai na samu wayam. Banyi ƙasa a gwiwa ba na dawo ina tambayar Bibaa. Wani kallon banza yarinyar ta watsa min duk da kuwa na bata kusan shekara bakwai zuwa takwas, dan kwata-kwata yanzu take a shekara ta goma sha uku, a gadarance ta ce, “Kin bani ajiya ne. Ka jimin rainin wayo dan ALLAH mtsowww!!” ta maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Bance komai ba na juya na koma ɗaki, dan hakan da tai na nufin yau banda abinci a gidan tunda na tafi aiki ban kammala miya ba, bayan kuma nayi komai har abinda ba’a sakani ba, miyar ma na barta ne kawai ta gama fidda mai dan karna makara tunda ta soyu. Wajen kwanciyata nakai zaune ina hawaye, dan haka kawai yau naji zafin abinda akai min ɗin duk da bawai yau ɗinne farko ba, amma kasancewar na dawo da yunwa sai abin ya zafeni. Tun muna yara idan Mum ta bushi iska takan hanamu abinci, haka Hafizzullah zaita kukan yunwa dan ni da Yaya Musaddiq mukan daure, ko zaiyi kukan mutuwa kuma bazata bashi ba sai dai Yaya Musaddiq ya fita ya samo masa a waje koda da bara ne, yanzu kam da muka girma idan aka hanamu zai sayo ya jamu ɗakinsa muci mu ƙoshi muna hirarmu. Sai kuma hakan ke ba Mum haushi take kai ƙararmu ga Abba wai muna haɗe kai muyita zaginta a ɗakin Yaya Musaddiq. Wani lokacin Abban kan mana faɗa, wataran kuma ya mata shiru, sai dai ta ƙaraci masifarta ita kaɗai. Ganin zaman bazai amfaneni da komai ba na miƙe ina share hawayena. Ƙaramin hijjab ɗina na zaman gida na ɗauka na saka, na ɗauki jakata dana fita aiki da ita na fito. Suna a falon har yanzu suna kallo, banko kalla kowa ba a cikinsu na fita zuwa ɗakin Yaya Musaddiq. Sai da na ƙwanƙwasa tare da yin sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. Tashi yay daga kwancen da yake a tabarmar barcinsa, dan koya sayi katifa amshewa Mum take ta bama su Bibaa su kasheta da fitsari ko a bama su Abbas. Kusan sau uku tana yin hakan shiyyasa ma ya bar saya shima. Murmushi yay min yana mai bina da kallo, na ɗan tura baki gaba ina zama a gefensa da ajiye jakar kamar a yanayin gajiye. Yaya Musaddiq mutum ne mai sauƙin kai sosai, da wahala ka iya ganin fushinsa a zahiri. Cike da kulawa ya ce, “Kandala miya faru kuma ake kumbura wannan cat face ɗin?”.
      Sake tura bakin nayi da faɗin, “Ni ba komai, yunwa nake ji”.
   Ɗan jimm yay yana kallona, sai kuma ya ɗauke kansa da sauke ajiyar zuciya ya miƙe. Rigarsa ya ɗauka ya saka a saman singlate ɗin jikinsa. “Ki jirani ina zuwa”.
      Kaina na jinjina masa ina kaiwa kwance a tabarmar tasa. Yana fita na ɗan lumshe idona. Kusan minti huɗu ina a haka sai kuma na miƙe zaune. Jakar tawa na jawo gabana, tare da zuge zip na ciro mujallar nan da MD ya bani ɗazun. Yanzu kam kai tsaye na zubama mujallar ido, sosai nama mutumin kallon ƙurilla a karo na biyu, badan baiyi haske dau irin na larabawa da indiyawa ba da tabbas zan iya cewa daga cikinsu ya fito. Dan daga suffar jiki har zuwa ta halitta fuska bai yi kama da ƴan Nigeria ba. Sai dai kuma abin mamaki fatarsa zamu iya cewa irin tamu ce. Duk da kuwa ba baƙi bane wulik, idan ma za’a kira farare za’a iya nunashi mu anan Africa, sai dai kuma farin nashi yasha banban, koda yake maybe camara ce ta maida shi hakan. Sake maida idanuna akan kitson kansa dake ɗaure a tsakkiyar kai kamar wani mace, sai kawai naja sirrin tsaki, banda ƙarshen duniya dai ace namiji da kitso da ɗan kunne. Kai ALLAH ya ƙyauta, inaga dai ɗan daudu ne gaskiya. Dangwarar da mujallar nayi gefe na sake komawa nai kwanciyata. A dai-dai nan Yaya Musaddiq ya shigo ɗakin da sallama. Amsa masa nai ina tashi zaune. Ya ajiye min ledar hannunsa yana faɗin, “Oya tashi kici”.
    Babu musu na tashi zaune, ina ƙoƙarin buɗe ledar shima yana kaiwa zaune ya ɗauki mujallar. “Tofa! Ke kuma ina kika samo Maash haka kandala?”.
       Baki na taɓe da fara kai lokar indomie ɗina. Kafin na ce, “MD ɗinmu ne ya bani yau wai zanyi aiki a kansa”.
     “Aiki kuma?”.
  “Eh Yaya, so suke wai nayi hira da shi a ranar bikin buɗe Companyn sa”.
  “Kai lallai sun haɗaki da aiki. Amma ALLAH ya bada nasara”.
      “Amin” na amsa masa ina sake jin karaya. Sai kuma na kallesa, batare da nasan ya akai bakina ya suɓuce ba na ce, “Yaya amma dai shi ba musulmi bane ba ko? Sannan ba ɗan Nigeria bane?”.
      Sosai ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! K waye ya gaya miki ba musulmi bane?”.
    “To Yaya wane musulmi ne zai zauna ai masa kitso a saman kai ya ɗaure haka kamar wani mace. Ga ɗan kunne kuma a kunne ga tattoo a wuyansa. Sannan kalli idonsa kamar na mage fa. Ni wlhy banji ya birgeni ba abu kamar ɗan daudu”.
      Dariya Yaya Musaddiq ya saki yana girgiza kansa. Ya ce, “Banda abinki Samraah dan mutum yayi duk wannan sai a fiddashi a musulunci ko a kirashi ɗan daudu. Wannan abun da kika gani yanzu shine samari suka ɗauka matsayin gayu da wayewa wai, baki ganin kuma shi ɗin mai lokaci ne da duniya ke ji da gani. Idan kuɗi na ɗibar mutum ai komai ma sai ya yi ba komai bane. Sannan shi ɗin kamar ance ruwa biyu ne. Tsakanin kakansa da kakarsa akwai wadda ba ɗan Nigeria ba, anan ma ya kwaso waɗan nan kamannin da kowa ke ganin ba ɗan 9ja ɗin bane ba. Amma asalin mahaifinsa ɗan kwanar Mashi ne ma, Kinga kuwa shi cikakken bakano ne, anan ma aka haifesa shi”.
     Baki na taɓe akan maganar yaya ta kusan ƙarshe, sai kuma na ce, “Humm, to ALLAH ya rabamu da irin wannan kuɗin masu mantar da bawa shi waye kuwa. Ni yanzu Yaya yaya zanyi to. Wlhy duk kaina ya gama kullewa fa?”.
“Karki damu in sha ALLAHU zamu samo mafita. Ke dai kawai ki saka a zuciyarki zaki iya. In dai shi ba aljani bane nasan duk taurin kan Maash bazai gagari Kandalata ba ai. Dan itama tauriƙiƙin kantace ga naci akan abinda tasa gaba”.
Dariya na ƙyalƙyale da shi da faɗin “Kai yaya?”
Ya ce, “ALLAH ai nasanki ne fiye da yunwar cikina kandala”.
Nanma dariyar nayi shima yana tayani, tuni Yaya ya mantar dani baƙin halin mutanen gidanmu. Ya kuma bani ƙwarin gwiwa sosai data bani karsashi akan tunkarar wannan aiki da MD ya bani, ban baro ɗakin ba sai da na fara hammar barci….

Washe gari ban ɗaga ko tsinke ba a gidan, dan banma tashi a barci ba sai ƙarfe bakwai. Salla nayi nai wanka nai shirin office nai tafiyata, dan har lokacin babu wanda ya tashi suna can suna barci ana jiran jaka ta gama girkawa a fito a ci. To ai na fisu iya tsiya, dan kamar yanda na saba in har aka gunziga min baƙin ciki a gidan sai na maida murtani. Yaya Musaddiq bai san tsiyar dana shuka ba ya ɗaukeni muka wuce a mashin ɗinsa. A hanya nake roƙonsa wannan weekend ɗin muje muga Hafizzullah a Katsina dan ALLAH idan baida aiki da yawa. Bai musa ba yace min in sha ALLAHU zamuje ranar asabar sai mu dawo lahadi. Sosai naji farin ciki, harma na manta da damuwata balle na sanar masa banyi breakfast ba na gudo yau. Yana sauke ni ya miƙamin 1500. Amsa nayi ina masa godiya da yima iyayenmu addu’ar samun rahama. Daga haka na shige shi kuma ya wuce.

         Kasancewar yau inada gabatar da program banfi zaman mintina talatin ba na tashi na fita tare Khalid. Kusan cin karo mukai da Mansoor dake ƙoƙarin fitowa. Baya naja da sauri, sai hakan ya sakani tuzguɗewa na tafi zan faɗi. Kusan tare suka kawo hannu shi da Khalid domin taimaka min, niko nai saurin sake maida jikina baya ta yanda kowannensu bai samu damar taɓanin ba, dan na gwammaci na faɗin kawai. Aiko faɗuwar nayi, na kuma ji zafi sosai, duk da kuwa na fuske Mansoor sai da ya fahimci hakan. Cike da damuwa yakai duƙe gabana tare da sake kai hannu zai riƙo nawa na ɗan hararesa. Murmushi kawai yay ya janye hannunsa yana kaisa saman kansa ya shafa cike da basarwa. Sai kuma ya sake maida idonsa gareni, a hankali ya ce, “Yanzu har kina da damar yin masifa babie. Naga dai hannun ai nawa ne”.
     Sake hararsa nayi tare da ɗauke kai ina ɗan murguɗa baki, na ce, “Sai ka bari sai ka biya ai”. Ina kai ƙarshen maganar na miƙe abina. Dariya ya saki mai sauti da faɗin, “Rigimammiya kawai ai saura ƙiris dai, mi kike ci na baka na zuba. Wata uku bazaki ƙaraba sai da igiya uku na ciff a kanki”.
         Murmushi kawai nayi ina ɗan murguɗa bakina dake cikin face mask ɗina na wuce na barsu a wajen Khalid na tayasa dariya. Sai da na gaishe da kowa kafin na wuce na ɗan ƙara gyara fuskata gaban mirror, suma su Mansoor sun shigo, dama mu zaije kira ashe. Hakama baƙonmu na yau ya iso tuni, dan haka babu ɓata lokaci aka fara gabatar da program ɗin……..✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Join our WhatsApp group here

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕

…….Yau ma kamar kullum Mansoor ne ya ɗaukeni zuwa gida bayan an tashi. Mun ɗan fara tafiya nake sanar masa aikin da MD ya saka ni. Da mamaki ya juyo yana kallona da faɗin, “What! Dama ke ya bama aikin nan? Taya zai haɗaki da wannan aikin mai wuya bayan yasan wanene wannan mutumin. A tarihinsa fa bai taɓa yarda yayi hira da ɗan jarida ba har yanzu. Kuma karki ɗauka wai ƴan jaridar nan gida Nigeria kawai. A’a har manya-manyan ma irinsu BBC, VOA, Aljazeera da ire-iren su. A duk sanda aka buƙaci hira da shi sai ya haɗa mutane da P.A ɗinsa…”
        “Hu’umm, to amma shi miyyasa yake yin haka? Kamar ba wayayye ba? Ko kuma bashi da gaskiya ne shiyyasa yake gudun hakan?”.
     “To ALLAH kaɗai masanin gaibu, sai kuma shi da ya barma kansa sanin dalilin. Amma dai wasu na ganin girman kai ne kawai da giyar kuɗi dake ɗibarsa. Dan a yanzu fa shine matashi ɗan kasuwa na biyu a duniya dake juya manyan kuɗaɗe, anama hasashen nanda shekara mai zuwa zai iya zama na farko. Wasu kuma na ganin akwai dai wani babban dalili nashi, dan in har da girman kai ne ai zaiso ƙara bayyanama duniya shi ɗin wanene ta hanyar ƴan media ɗin. Wasu ko na ganin ko dodon tsafinsa ne yace kar yay hakan, kin san dai mafi yawan ƴan kwasuwar nan dake shahara a ƙanƙanin lokaci sai a hankali, shiyyasa ake yawan ɗora musu zargi, ALLAH dai masanin gaibu. Amma gaskiya al’marin dai nasa akwai ɗaure kai”.
        “Ƙila to aljanu ne da shi da basa son hira da ƴan jaridar. Ko kuma dai da gasken dodon tsafinne da shi. Dan ni naga yanda kowa ke misalta dukiyar tasa akwai ban tsoro kam”. Na faɗa cikin halin ko in kula. Dariya sosai Mansoor ya sanya, tare da faɗin, “Kai Babie baƙya rabo da wauta ALLAH. Aljanu kuma? Namiji da aljanu? Adai tsaya a dodon tsafin”.
    “To inba aljanu ba shi kam ai abin nasa yayi yawa, dodon tsafin ma kuma ai aljanu ne. Yanda yake nuna kansa a matsayin wayayye irin haka ai ya kamata ace an wuce wannan ajin. Amma ni kam in sha ALLAHU sai na sakashi ya magantu, ni halin nasa ma sai ya ƙara min ƙwarin gwiwar tunkararsa.”
       Sosai Mansoor ya juyo ya kalleni cikin nuna mamakinsa a fili. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Anya yarinyar nan kin san wanene MASH!? kuwa? Babu sauƙi fa a ɗaukar wannan alwashin naki. Ni dai ina gargaɗarki da kar kiyi wani abu mara ƙyau dan ALLAH. Idan kin samu dama kamar yanda kowa ke fata fine, idan baki samu ba ba faɗuwa bace. Dan haka be careful sweetie. Kar ki biye ta MD kujerarsa kawai yake yunƙurin saitawa”.
        “Karka damu, ni ba wani abu mara ƙyau zanyiba ALLAH. Kuma duk ma tambayar da zan masa ai sai na kaima MD ɗin ya duba. Kaima kuma zan baka ka gani kafin ma na turama MD ɗin har ma Yaya Musaddiq. Kawai dai ina fatan karya masa wannan alfaharin nasa ne”.
       Kansa ya jin jina min, ya ce, “To ALLAH ya bamu sa’a, dan zanfi kowa kasancewa a farin ciki ace kece kika karya ɗin kam. Dan har ƙyauta sai na miki na musamman”.
    “Tami?”.
  “A’a ai ba sai na faɗa ba. Yanzu dai ajiye ma wannan batun. Su Alhajina fa zasu zo wannan weekend ɗin. Dan haka yau ina buƙatar ganawa da Abba yaya za’ayi kenan”.
       Da sauri na juyo na kallesa, ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. Kaina na ɗauke cikin jin kunya, sai dai wani irin farin ciki ne ke ratsa ƙashina da ɓargo har ina jin yanda jikin nawa ke rawa. Amma dai nayi juriyar dakewa. Sai dai ban sake cemasa komai ba har muka iso. Tunda ya tsayar da motar na kasa wani motsi, mun kai minti biyu a haka shi kuma yana kallona kamar ya samu tv kafin ya saki ɗan murmushi mai sauti. “Wai kunyar ce dai Babie?”. Sake kauda kaina nayi gefe batare dana bashi amsa ba. Ya saki ƴar siririyar dariya yana ɗan dukar sitiyari, sai kuma ya juyo gareni yana faɗin, “ALLAH ya kaini randa zan cire wannan kunya dai kowa ya huta, dan bazanyi sakaci ba a daren farko zata kama gabanta. Anya baki haɗa jini da fulani ba Samraah”.
       Hannu na kai ga handle ɗin ƙofar zan buɗe na gudu sai na jita gam alamar ya saka lock. Kasa sake wani yunƙuri nayi, na kuma kasa juyowa dan har lokacin ina jin kallon ƙurullar da yake min.
   “Kayi haƙuri ka buɗemin, zancen ganin Abba kuma ya kamata ka fara ganin Yaya Musaddiq dai first nake ga”.
        Sosai ya sauke numfashi mai nauyi, sai kuma ya amsa da, “Okay hakan ma yayi, zan bari to sai gobe in sha ALLAHU na samu Yaya a gareji”. Daga haka ya buɗe min. Wuff na fice abina kuwa. Batare da ko sallama nayi masa yau ba na shige gida, har lokacin kuma ina jin idanunsa a kaina. Ina rufe ƙofar gate ɗin na jingina a jiki ina sauke numfashi, sai kuma na kai hannuna saman ƙirjina da ke bugawa da sauri-sauri. Murmushi na saki kafin na buɗe idanuna a hankali na ɗan leƙa gate ɗin naga ko ya wuce. Sai lokacin naga yana ƙoƙarin yin reverse. Bazan ɓoye miki ba ina matuƙar ƙaunar Mansoor wlhy Bilyn Abdull, soyayya nake masa mai ƙarfin gaske da bama zan iya misaltata ba, dan Mansoor ya mun abubuwa na halacci da dama akan soyayya da bazasu iya ƙirgiguwa ba, na tabbata da aure kawai zan iya masa godiya a kansu amma bada fatar baki ko soyayyar saman titi ba.
    
        Cikin gidan na shiga kamar yanda na saba, sai dai acan ƙasan raina ina ɗan jin tsoro-tsoro. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ganin ban samu kowa a falo ba yau. Zuruf na shige ɗakinmu, in da na tarar da Bibaa kawai tana kallo a wayarta. Yanda bata amsa ko sallamata ba nima ban sake bi takanta ba. Wanka na farayi duk da kuwa cikin ƙyanƙyamin bayin nai haka, dan yanda ban wanke ba haka Bibaa itama bata wanke ba, sai ma datti da suka ƙara masa. Gudun kar lokacin sallah ya wuce min yasa ni saka doguwar riga kawai na saka hijjab na tada sallar. Na kai raka’a ta biyu ina sujidar ƙarshe kawai naji saukar duka kaina. Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un wata irin azabace ta ratsa ni, amma na daure sosai na cigaba da sallata. Abinda kuma zai baki mamaki ba’a daina dukan nawa ba har na idar. Karo na farko kenan dana ɗaga hannu sama ina kuka da neman sakayya wajen UBANGIJI na, ina ƙoƙarin shafa addu’ar dai dai nan Abba ya shigo kamar wanda aka jeho.
       “Haba Jalilah minene haka? Baki da hankali ne tana salla kina dukanta”. Ya faɗa a matuƙar hasale yana riƙe bulalar. Basu ba hatta ni sai da na shiga shock, dan nidai nasan ba yau ne karan farko da Mum take dukana ba a gidan nan. Hasalima ta dakeni a gabansa a lokuta barkatai amma bai taɓa cewa komai ba. Bama ni ba, hatta da Yaya Musaddiq yasha shan duka a wajen Mum, yanzu ne dai ta daina sai zaginsa da baƙar magana. Hakama Hafizzullah, sai dai duk ni na fisu shan wahala kasancewar akoda yaushe ni ina cikin gida a tare da su….
        Mum ce ta katse min tunani na, dan cikin hargagi ta hayayyaƙo ma Abba a gabanmu. Idan ni bazata ji nauyina ba ai ya kamata taji nauyin su Babie kasancewar sa na mahaifinsu. Amma ko’a kwalar kwagirinta. Dan sai da takai ya koma bata haƙuri da lallashinta. Ni al’amarin nasu ma sai ya nema fasan kaina dan al’ajabi. Haka dai ya jata da ƙyar suka fice a ɗakin. Harara Baby ta watsa min da faɗin, “Shegiya mayya. To kurwar iyayenmu kur wlhy. Kuma indai Mum ce kaɗan ma ta miki wlhy, bari dai Abban ya fita duk da ma ko yana nan zata iya cigaba da cin ubanki, yanzu ɗin ma ta ƙyaleki ne kawai kiji da wannan tsamin jikin mtsowww makwaɗaitan banza da wofi anzo an cika mana gida an hanamu rawar gaban hantsi”. Daga haka ta fice kamar iska zata ɗibeta. Dan sam Baby bata da wani jikin kirki, ta girman amma na fita cikar halittar jiki sosai, wanda ma bai sani ba sai ya ɗauka nice babbarta. Sai da suka gama zageni tsaf ita da Bibaa suka fita sannan na fashe da kuka, dan illahirin jikina raɗaɗi yake min sosai. Da ƙyar na iya tashi na zare hijjab ɗina, abinka da farar fata wasu wajen ma har sun fashe. Cikin ƙanƙanin lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufeni, haka na kwana ina makyarkyata ga ciwon jiki. Duk kiran da Yaya kemin a waya ban ɗaga ba, har ya gaji ya daina kiran, nasan dai ya zata ko barci nayi ne…
       Humm wato Bily inada taurin kai fiye da yanda kike tunani. Zaki sha mamaki idan nace miki washe gari ma duk da dukan da naci haka na sake tsallakewa nai tafiyata wajen aiki batare dana ɗaga ko tsinke a gidan ba. Nasan dai nabar ƙura sosai, amma ko’a jikina nai gaba batare da na jira ko Yaya Musaddiq ba yau. Sai wajen 12 sai gashi yazo lokacin ina kwance zazzaɓi ya addabamin. Ruƙayya ce data lura da haka ta matsa min nasha paracetamol da ƙyar. Da Yaya Musaddiq ma yazo itace tazo ta kirani dan ta ɗan fita taci karo da shi shine tazo ta kamani muka fita.
     Kallo ɗaya na masa na duƙar da kaina. Dan sosai naga ɓacin rai tattare da shi. Sai dai shima yanayin da ya ganni naga ya ɗan raunana fushin nasa, dan muna isowa inda yake sosai naji ya sauke ajiyar zuciya yana mai furzar da huci mai zafi………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

Join our WhatsApp group here

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆

……..Sai da Yaya yayma Ruƙayya dake shirin barin wajen godiya sannan ya juyo gareni. Kallo ya ƙare min daga sama har ƙasa sannan cikin yanayin fusata ya ce, “Miyasa kike da taurin kai ne wai Samraah?. Yanzu ga abinda kikayi jiyan wace riba kikaci tunda kinfi kowa sanin halin matar nan?. Amma ke da yake ba’a taɓa faɗa miki kiji shine yau ma kika kuma. To ai gashi nan ta sake ƙulla miki sharri kala-kala ita da yaranta. Tun ɗazu ina gidan basu barni na fito ba sunata min masifa akan wai ni nake sakaki. Har Abban na saka sharaɗin ko dai ki ajiye aiki ki dawo ki cigaba da aikin gidan ko kuma ya aurar da ke ga wa wanda ita Mum ɗin ta kawo. Idan yaga shi zai barki yin aiki ki cigaba, amma albashinki dolene kema ki dinga rabawa biyu daga yanzu kina basu rabi ana haɗawa ayi cefane. Nama kawo masa batun Mansoor yaƙi ya saurareni sam. Wai shi bai san da wani Mansoor ba kuma bazai aura masa ke ba, wanda Mum ta kawo kawai ya sani kuma shi zai bawa dan yaron nada tarbiyya sosai, kuma shi ya gamsu da hakayensa….”
      Kuka na sakar masa mai taɓa zuciya. Hakan ya sakashi yin shiru ya gagara cigaba da magana ya zubamin ido kawai. Kusan mintuna uku ina kukan sosai kafin ya kai zaune kusa dani. A jikinsa ta gefe ya sakani kawai shima hawayen na cika masa ido. “Amma kin san bana son kuka ko Samraah”. Ya faɗa muryarsa na rawa. Ɗagowa nai a karo na farko ina kallonsa. Sai kuma na sake fashewa da wani sabon kukan ganin yanda idanunsa suka kaɗa sukai jazur gasu cike da hawaye. “Yaya ya kake so nayi, shike nan haka zamu lalace a yima waɗanda basu taɓa jin tausayinmu ba biyayya. Kullum burin matar nan wulaƙanta mu, Yaya tun fa ban isa iya aiki ba nake bautar gidan nan, amma ko sau ɗaya ba’a taɓa min adalci ba idan nai kuskure a yafe min. Kullum kuma a banayi nake. Su Baby na kwance. Yaya na gaji wlhy, ji nake kamar na gudu na bar gidan nan kawai….”
        “Shiii!!! Karna sake jin irin wannan maganar a bakin ki. Samraah ai wuya bata kisa. Da ace tana yi wlhy da bamu kai haka a rayuwa ba. Duk can baya baki ƙosa ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi. Kwana nawa ma ya rage miki a gidan. Bama ke ba da kike mace zaki tafi gidan aure hatta ni da Hafizzullah in sha ALLAHU mun kusa bar musu gidansu. Gara kawai na tada gini na kamar yanda kike bada shawara mu koma can kawai. Amma dan ALLAH ina roƙonki kada ki sake maimaita abinda kika faɗa yanzu. idan kin gudu ina zaki? Ki daure ki cigaba da musu abinda suke so. Watarana sai labari ai. Maganarki kuma da Mansoor na yanke shawarar zuwa wajen dangin mahaifinmu, duk da sun watsar damu basu taɓa waiwayen mu ba tunda ɗan uwansu yabar duniya zanje na roƙesu su shiga wannan maganar a baki wanda kike so tunda dama sune ai da wannan alhakin ba Abba ɗin ba. Ki tashi kuma muje asibiti dan jikinki akwai zazzaɓi sosai.”
       Ɗagowa nai zanyi magana ya girgiza min kai alamar kar nace komai. Dole na haɗiye kuwa. Ruƙayya ya kira da wayata, yace ta tattare masa kayana dan ALLAH. Cikin mintuna kaɗan ko sai gata. Da taimakonta muka fita inda mashin ɗinsa yake. Ta taimaka min na hau muka wuce dan Mansoor yau baizo office ba sunje wani aiki Jigawa. Sai da muka fara tsayawa a camix aka dubani kafin mu ƙarasa gida dan nata roƙonsa kan bazanje asibiti ba, sanin da yay min na ƙin jinin asibitin shima yasa ya barnin mukaje camix ɗin kawai aka bani magani.

      Kamar yanda Mum ta shirya cin ubana shima Abba ya shirya hakan yau, sai dai a yanayin da Yaya ya shiga dani gidan ya saka jikinsa yin sanyi shi. Dan Mum ta fara min tujara da ƙoƙarin kai mari ya dakatar da ita.
   “Uhm Jalilah inaga ya kamata ayi hakuri ai, baki kula da halin da take a ciki bane? Kiyi haƙuri harta warke ni da kaina zan sauke mata taurin kan nan nata nayi miki alƙawari”.
     Wani shegen kallo ta watsa masa a fusace. Kamar zatayi magana sai kuma mita tuna oho tai shiru. Fuuu ta wuce bedroom ɗinta ta barmu tana faman huci. Wannan zazzaɓi dai shine ya ceceni a wannan rana. Washe gari kuwa duk da weekend ne asubar fari Mum tazo ta tadani. Bata damu da yanayina na har lokacin ban gama dawowa dai-dai ba. Nima sai bance mata komai ba na tashi na hau aikin da take buƙata, dan kwana biyun nan fa da banyi komai ba haka gidan yake zaune kaca-kaca. Kafin takwas na safe har brackfast na kammala haɗawa, na ɗauki na Yaya Musaddiq na kai masa. Na samu ya kammala shirin wucewa Gwarzo kamar yanda ya faɗa zaije. Ba haka naso ba, dan naso ace munje munga Hafizzullah kamar yanda muka tsara. Zama nai muka karya tare yana ƙara lallashina da mun nasiha, jinsa kawai nakeyi, dan gaskiya bazan iya haƙurin wani abun ba in har nayi wani. Amma dai zan rage taurin kan kodan shi. Ban bar ɗakin ba sai da ya ƙarasa shiryawa muka fito tare, yau zai dawo, amma ya musu tsaraba. Ciki na koma na samu mutanen gidan gaba ɗaya a falo zagaye da Abba. Sai dining dake kaca-kaca sun gama karyawa amma babu wanda ya iya kawar da ko cokali. Abban na gaisar, ya amsa min babu yabo babu fallasa, itako Mum bama ta amsani ba. Ban damu ba dan ba yau na fara ganin hakan ba ai daga garesu, na nufi ɗaki da nufin yin shirin islamiyya da nake zuwa duk weekend Mum ta dakamin tsawa.
       “K dan ubanki waye zai kwashe miki waɗan can kayan”.
    Ɗan jimm nayi a tsaye zuciyar na yunƙurowa, sai dai nasihar Yaya Musaddiq dana tuna ta sakani komawa cool. Batare da nace mata komai ba na nufi dining ɗin na shiga tattare kayan. Sauri-sauri na wankesu na fito, har yanzu suna a falon, ɗaki nai wucewata na shirya, na sake fitowa dai na samesu. Da harar Mum na fara cin karo, ɗauke kaina nayi kamar ban ganta ba, a ladabce naje gaban Abba na duƙa. “Abba zanje islamiyya saina dawo”.
        Kansa kawai ya jin jina min ya cigaba da kallonsa. Nima sai na miƙe. Mum dake watsamin hararace tai saurin faɗin, “Ya kake bata damar tafiya Abban Abbas, idan ta tafi ubanwa zai mana girkin rana? Islamiyya take zuwa ne ba yawon iskancinta ba”.
     Ƙoƙarin ficewa nake da sauri dan nasan zai iya dakatar dani. Amma a mamakina sai naji yana faɗin, “Baga su Baby nan a gidan ba suyi girkin su mana tunda sun ɓarar da tasu islamiyyar su….” daga haka ban ƙarasa jin abinda yake faɗaba nai wucewata ina murmushi. Wani lokacin idan Abban yay abu sai kaga kamar mai mutunci. Koda yake dama ba laifinsa bane ba, zama kawai ake ana shirya mana sharri a wajensa maybe ma harda asiri. Dan nikan ban taɓa ganin mijin dake tsoron ɓacin ran matarsa irin Abba ba. Oho koma dai minene su suka sani ina ruwana.. Tunda na isa islamiyya na samu ƙawayena biyu na manta da wata hidimar gidanmu. Sai ƙarfe huɗu muka tashi, anan nai sallar la’asar sannan na dawo gida. Abin dariya abin takaici, a galabaice na samesu wai babu wanda ya tashi yay girkin ana jirana, Abba dai ya fice sai su kawai. Sai Abbas dana samu a gidan shima ya shigo. Ko kallon inda yake banyi ba dan ni da shi bama magana. Haka na tuɓe uniform ɗina na shiga kitchen ɗaura musu girkin da suke jira ɗin. Abu mai sauƙi na musu nayi komawata ɗaki..
       Yaya Musaddiq bai dawo a ranar ba kamar yanda yace. Koda na kirashi a waya sai yace nai haƙuri bai samu kawu Musa bane a gida, su kawu Sa’adu kuma sunce dole ya jirashi. Mun ɗan yi hira mukai sallama saboda kiran da Mansoor keta faman yimin. Hira sosai mukasha da Mansoor, dan sai kusan ɗaya mukai sallama. A hakan ma ba kwanciyar nayi ba. Tambayoyin da zanma wancan mutumin nai zaman tsarawa, har biyu sannan na miƙe na gyarama su Bibaa rufa na ɗauro alwala. Nice ban kwanta ba dai sai kusan biyu da rabi, amma hakan bai hanani tashi da asuba ba yin ayyukana. 
 
         Washe gari da yamma Yaya Musaddiq ya dawo gidan. Na dawo daga aikan da Mum tamun rijiyar lemo wajen ƙawarta na samu ya dawo. Naji daɗi sosai, dan bamma shiga gidan kai aikar ba na zauna muka hau hira. Duk yanda sukai da su Kawu Musa ya sanar min. Sunyi faɗa sosai, da farko ma ca sukai su babu ruwansu. Shi Abban daya nuna musu shine dolenmu yaje ya aurar damu. Amma Yayan ya dinga basu haƙuru, da ƙyar dai suka haƙura, sun kuma tsaida shi kawu Sa’adu zai zo ya sami Abban.
Hakan kuwa akai, dan washe gari Litinin sai ga kawu Sa’adu. Lokacin mu duk mun fice wajen sabgoginmu. Shima Abban a office kawun ya samesa suka tattauna. Duk da dai a farko taso tayi tsami a tsakaninsu. Kasancewar kowanne yana son nuna ƙarfin ikonsa a kammu da kuskuren da ɗan uwansa yay masa. Bayan dai sunyi sama sun faɗo suka dai-daita kansu. In da da ƙyar Abba ya amince da batun Mansoor……..✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒆𝒏

…….Oho mu bama musan sunayi ba, dan lokacin da suke nasu bidiri ni inama can office ɗin MD na kai masa aikin daya saka ni. Kamar kullum yau ma a kwai mask a fuskata, sannan dogon hijjabi ne har yana jan ƙasa na saka. Dama dai shigar tawa kenan. Idan har ka ganni babu hijjab to abaya ce na saka kuwa. Amma gyale dai a jikina zan iya rantsuwar tunda ma mallaki hankalina na san kaina ban taɓa sakawa ba. To bamma da shi sam, sai ƴan madaidaita da nakanyi rolling idan zan saka abaya. Duk da yanda na suturta jikina bai hana MD zuramin idanu ba, dan shi indai kallone ya iya shi na masifa ma da UBANGIJI ya hanemu yi. Ni dai miƙa masa takardar nayi na maida hankalina akan wayata.
       “Wow! Kai Samraah sannu da ƙoƙari. Shiyyasa duk girman gidan nan ke na fara hangowa dan nasan bazanyi zaɓen tumin dare ba, saboda nai matuƙar yarda da basirar ki, kina da saurin ɗaukar abu wlhy. Sosai komai yayi, sai fatan ALLAH ya kaimu ranar kuma. Yanzu zuwa anjima sai kizo ki amsa kiyi printing nashi ko. Ki kuma je ki zama cikin shiri na musamman, dan wannan ranar muna fata ta zama ta musamman a garemu. Dan ALLAH kada ki saka dogon hijjabin nan tamkar matar limamin anguwa. Ki yi shiga ta ƴammatan zamani dan kin san irin manyan mutanen nan sunfi son komai na wayewa su balle shi matashi dake a ganiyar samartaka. Inda son samu ne ma ki saka sabbin kaya, ki samu makeup artist ta tsantsara miki irin kwalliyar nan taku ta zamani Please”.
       Yanda kuka san television haka nai galala ina kallonsa. To amma kun san tsiyar mutuniyar taku. Sai ban musa masa ba nayi murmushi kawai da faɗin, “In sha ALLAHU Sir”. Yako ji daɗi, dan tuni ya washe baki da jera min godiya. Niko sai nayi dariya kawai a raina. Kuga ɗan banza yana son iskantani kawai. Yo in ba son iskantawa ba taya zai ce nai irin wannan shiri dan kawai burge wani sakarai can da ban san ma a wace alƙibla yake ba, ta musulinci ko ta masu kaɗa ganguna. Humyim bai san halin ƴar Abdul-wahab ba ne ba, amma zan sanar da shi sannu a hankali. Office na koma na cigaba da harkokina. Bayan azhar kuma muka haɗu da Mansoor. Dan nifa da kuke gani na duk rintsi bazaka ganni office ɗinsa ba in ba a dalilin aiki ba. Dan tun farko daya fara nuna buƙatar hakan ta hanyar kirana wai nazo na samesa office na dakatar da hakan. Nama nuna masa anan fa aiki mukazo, ya kamata mu ajiye batun alaƙa gefe muyi abinda ke a gabanmu kamar yanda muka rayu a makaranta. Idan mun fita anan sai mu dawo da batun alaƙar. Mansoor mutum ne mai sauƙin kai da fahimtar abubuwa, sai in kana kallonsa daga nesa ne zaka fassarashi da girman kai. Ya fahimceni harma ya nuna jin daɗinsa da hakan. Bawai dan ina zarginsa da wani mugun haline nayi hakan ba. A’a nayine domin kare mutuncina da martabata ta ɗiya mace. Sannan kuma hakan da nayi zai ƙara bani kariya daga hare-haren irinsu MD da basu iya ɓoye maitarsu a fili ga ƴaƴan mitane.
       “Amarsu ta ango”. Daya faɗa ya sani ɗauke kai gefe ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yayi yana dawowa ta inda na maida kan nawa. Ƙaramar harara na sakar masa ina sake ɗauke kaina. Ya ce, “Tab irin wannan harara haka amarya ai sai kisa na zube ƙasa wlhy. Kinga adana min ita sai nan da ƴan watanni kawai,  kinga inma suma nayi dai ƙya farfaɗo dani da kanki babu wanda yaji ko ya gani ko?”.
    Dariya ya bani, amma kasancewar ba’a ganin bakin nawa sai nayi murmushi kawai na sake ɗauke kaina.
     
     ★ Alƙawarin ALLAH ya cika. Iyayen Mansoor dai sun kawo kuɗi gidanmu a ranar juma’a. Ranar ni naga baƙin halin Mum muraran. Dan zage-zage ta dinga yi da yima Abba masifa wai an munafunceta. Ashe bai gaya mata ba sai ganin su kawu Musa yasa ta fara tambayarsa abinda ya kawosu. Shine ya sanar mata iyayen wanda yake nemana ne sukace zasu zo yau. Takaici ya sakata zuba masa ido kawai, amma ta kasa cewa komai. Dai-dai isowar baƙi kuma sai ga abinci Yaya Musaddiq na shigo da shi da ruwa da lemo batare da tasan daga ina aka dafo shi ba. Shiko Yaya Musaddiq sanin halinta da yay ne ya sashi saka matar ogansa ta dafa abincin. To ranar dai munga tujara. Dan nima da ban san mike faruwa ba ina a wajen aiki ina dawowa na samu rabona. Baby kuwa banda kuka babu abinda take yi. Ni dai ko uffan bance musu ba, a wajen Yaya Musaddiq kuma naji komai yanda ya kasance. Iyayen Mansoor sun kawo 300k, amma su Kawu Musa sun barma Abba 200k su sun ɗauki 100k na ɓangaren uba. Hakan da sukai baimun ba. Dan kamata yay su su ɗauki 50k Abba 50k aba Yaya Musaddiq 200k dan nasan dai shine mai mun wahalar ba kowa ba. Ban dai ce masa komai ba muka ci gaba da hira. Dan banama sha’awar shiga gidan. Ko hijjabi na ma da zan saka a gobe idan ALLAH ya kaimu domin zuwa taron can anan ɗakin Yaya na gogesa. Sai kusan sha ɗaya na shiga. Baby kawai na samu a falon zaune. Bance da ita komai ba na kama hanyar shigewa ɗakinmu.
     Ji nai kawai an sakar min duka ta baya tare da damƙo hijjab ɗina. Da ƙyar naja numfashi saboda an shaƙe min wuya. Nai saurin riƙe hijjab ɗin ta gaba na yaga shi sannan na juyo ina sauke numfashi da ƙyar. Baby ce tsaye tana faman huci kamar mai shirin dambe. Na mata kallon sama da ƙasa kafin cikin mamaki na ce, “Lafiya kuwa baiwar ALLAH zaki shaƙeni kamar wadda ta ci miki bashi? Are you okay?”.
         “A haukace nake dan uwarki. Kuma kaɗan ma na miki, wataran idan na shaƙeki har sai kin daina numfashi zan ƙyaleki. Dan haka ina mai gargaɗinki in har kina son ranki ki fita a sabgar Mansoor wlhy. Ki kuma bar ganin ya kawo kuɗi da sunan na aurenki, wlhy sai dai in bana raye hakan zata kasance. Dan yanda ban samesa ba kema baki isa samunsa ba jaka kawai ƴan karoro a gidan mutane mai ƙwacewa yaran gida samari su mayya”.
       Murmushi kawai na saki mai faɗi dan wlhy ni dariya ma ta bani da tausayi. Bance mata komai ba nai shigewata ɗaki na barta tana ɗuran zagi kamar ba dare ba. Zuwa can kuma naji kamar maganar Abba sama-sama ita kuma tana kuka. Baki kawai na taɓe na gyara kwanciya dan so nake nai barci sosai kodan abinda zan tunkara a gobe in ALLAH ya kai mu. Sai dai duk da haka kamar kullum sai da na tashi nai ƙiyamullaili dan ya riga ya zame min jiki tashin a kullum, sai dai idan banda lafiya, amma ko prioud nake saina farka….

     DAMA ACE…..

            (Dama ace) kalmace mai harshen damo. Zaɓa mata gurbi a nawa labarin shine cigaba da nutsuwar saurarensa. Kamar kullum yau ma sai da nai duk ayyukan gidan kasancewar nasan yau ɗin Mum a cike take da haushina. Hatta shi Abban ban san a wane matsayi ya ɗauki auren nawa ba. Dan daya dawo da ga sallar asuba na gaishesa sama-sama ya amsa min ya shige ɗaki abinsa. Ga Baby a gefe da marasa kunyar ƙannenta su Bibaa da Nabil. Shiri na nayi kamar yanda na saba, dan baƙin dogon hijjabin jikina har jan ƙasa ma yake. Ban biye ta maganar MD ba, na kawo kuma face mask na saka kamar yanda na saba shima baƙi, na ɗaura sirrin farin eyeglasses ɗina da har ana iya ganin ƙwayar idona fes. Sai ƙamshi dake fita a jikina mai daɗin tsiya na humra da turare. Yaya shike sayamin turare da duk wani nau’in kayan kwalliya na mata. Hatta kayan ciki da suturu shine ke saya min. Hakan yasa banjin ƙyashin duk sanda salary na ya shigo account na tura masa su gaba ɗaya a account ɗinsa batare dana cire ko sisi ba a ciki. To idan na ajiye mizanyi da shi. Duk wani abinda nake buƙata baya gazawa wajen saya min. Idan abin yayi ya shigo zaka sameni a layin farko cikin masu sakashi. Da harda Baby yake saya, amma ta ce masa yama bar wahala bata so. Koda ta faɗa ɗin bai daina saya ba. Sai da yaga bata sakawa sannan ya daina. Hakan kuma baya hanashi bata kuɗi akan ta saya abinda take so. Wannan kam sukan amshe ita da uwarta kuma baza’a sayi abin kirki ba kuɗin zai gantale. Hatta da data sakara Yaya sakamin yake da credit, sai daga baya ne ma Mansoor ya amshesa wannan. Dan haka Yayanmu kallon uba nake masa ba yayaba wlhy, dan ya share mana kukan maraici tuni sai dai na kewar iyaye da bazai taɓa gushewa ba ga ƴaƴansu. Amma ta ɓangaren rayuwa komai Alhamdullah.
       Kamar yanda Yaya Musaddiq yay alƙawari shine ya ɗaukan a mashin ɗinsa da yasha wanki sai ɗaukar ido yake. Office ya kaini inda su Mansoor ke jirana dan da motar office zamu fita. Ba sauran abokan aikina ba hatta da Mansoor ƙuri yay kawai yana kallona cikin nuna mamakin ganin hijjab dana zuba har yana sharar ƙasa. Amma sai yay murmushi tare da kashe min ido ɗaya alamar yaji daɗin hakan da nayi. Nima murmushin nayi kawai na ɗauke kaina ina mai gaishesu. Duk suka amsa min da kulawa. Sai Davido ne ke magana akan shigar tawa. Ban tanka masa ba na shige mota abina na zauna batare da na yarda na kalla inda MD yake ba ko sau ɗaya, dan gaisuwa ma kaina a gefe nai masa. Naci sa’a dama sun gama loda komai dama ni suke jira. Kulsoom ma na ciki ita. Kusa da ita na zauna muka gaisa, sai gasu suma sun shigo. Da farko Mansoor na kula kusa dani yaso zama. Amma ganin yanda na koma jikin window muka saka bags ɗinmu a tsakkiya yasa shi haƙura ya zauna kujerar gabanmu, sai lokacin na ɗan saci kallon MD, yay kicin-kicin da fuska sai mazurai yake. Ƙasa nai da kai ina kwasar dariya, ɗan son banza an shirya ganin banza. To bata samu ba ai, sai a tafi wata tashar…….✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏

……..Tun kafin mu fice duk sun cika motar da hira, ni dai ban saka musu baki ba face ma bitar questions ɗin dake rubuce dan karna kwafsa. Dan a nawa shirin ina son masa tambayoyin ne batare da takarda ba. Duk da ma dai har cikin waya na kwashesu gudun samun matsala. Lokaci ɗaya naji motar ta ɗauki shiru, kamar zan basar sai kuma na gagara hakan, dole na ɗago domin ganin abinda ya sakasu nutsuwa haka. To nidai banga komai ba face uban cinkoso na ababen hawa da titin ya samu tamkar ba safiya ba kuma weekend. Da ƙyar drivern mu ya kutsa ya samu wajen parking ma. Haka muka firfito kowannemu na bin katafaran ginin da kallo. Dan sai yanzu na fahimci abinda ya saka su yin shiru ɗazun. Gini ne da akayisa da wani kalar zallar gilashi mai garai-garai ta gabansa. Ga wasu manya-manyan symbols da hoton motoci masu shegen ƙyau da mashina irin na masu kuɗin nan. Da manyan haruffan baƙi an rubuta MAASH.
       Tako ina jami’an tsaro ne, hakan yasa komai ke tafiya a nutse duk da alamu ma sun nuna duk wanda ka gani a inda motarmu ta samu damar shigowa to ba ƙaramin mutum bane, ko kuma dai yana da izinin zuwa wajen. Dan zuƙa-zuƙan motocine na nunama tsara. Yaku bayi kuwa na daga can tunkushe a titi an hanasu shigowa (🤥😞😏). Dan ƙa’idar sai ka nuna invition ɗin nan zasu bar motar ka ta wuce. A ƙafa muka cigaba da takawa saman lafiyayyen titin da aka ɗauka tun daga babban titi har zuwa cikin companyn. A dai-dai katafaren gate ɗin ma dai sai da muka nuna invition ɗin. Sannan akai searching namu aka tabbatar da bama tare da komai sannan muka shige bisa rakkiyar wani jam’i. Da alama wajen zaman ma a tsare yake kenan. Bazaka tabbatar da Companyn mugun ƙato na gaske bane sai ka shigo ciki. Ashe ta gaban duk wasan yara ne da ado kawai. Duk girman harabar an gyarata da uban decorations mai matuƙar ƙyau da ɗaukar hankali. Hakama an tsara kujerun zama cike da birgewa. Da ga can gefe abincine aka jera irin dai na taron ƴan gayun nan, dan ga masu zungura-zunguran hulinan nan irin nasu o,e a kitchen sun jeru kamar ƴan cocin yarabawa (😂lol). Mune ƴan jarida na farko da suka fara isowa, hakan ya mun daɗi, dan koba komai mun samu sits ɗin gaba a inda aka tsara domin ƴan jarida. Tuni su devido sun dasa camaras namu kuwa a inda komai bazai wucemu ba. Zuwan namu kamar ya buɗe ƙofa ne, dan sai ga mutane da ƴan uwanmu ƴan media nata shigowa a nutse babu wata hayaniya ko kace nace. Tun shigowarmu kuma tuni mun fara nuna komai live kamar yanda contract ɗin yake. Dan haka kusan komai daya fara da tushe kai tsaye ana fara ganinsa ne daga gidan tvn mu. Ni dai har lokacin ina a zaune dan ba’azo kan aikina ba. Kafin cikar awa guda waje ya gama cika taf da manyan mutane. Muryar mc kawai ake ji yana sanar da isowar manyan baƙi, sai mu kuma ƴan jarida dake namu bayanin domin gidajen tvn mu kai tsaye. Goma dai-dai dake tabbatar da duk wanda ake buƙata a wajen ya iso hatta da gwamna da sarki ma aka sanar da isowar mai gayya mai aiki. Wato Awwab El-Mu’azz Maashi. Tsitt wajen ya sake ɗaukar shiru kasancewar dai-dai nan zuƙeƙiyar baƙar mota da irinsu shugaban ƙasa kawai nake gani a ciki ta shigo. Ta gefe da gefenta da gabanta da bayanta kuwa wasu irin murɗa-murɗan basumadayen garada ne da gani kasan ba bugun Kano bane sai dai Lagos ɗin dan bamu da masu irin wannan suffar gaskiya😞. Su duka riƙe suke da bindigu kai kace zasu iya hana mutuwa ɗaukar wanda ke’a cikin motar ne😏. Har tsakkiyar filin motar ta shigo, inda mutanen dake a cikin motar bayansu suka fito a lokaci guda su huɗu. Mace ɗaya maza biyu. Wanda ke mazaunin driver ne ya buɗe booth da hanzarinsa ya ɗakko carpet maroon mai shegen ƙyau an rubuta Maash a jikinsa da golden mai ɗaukar ido. Yayinda macen baturiyar ta iso da sauri sauran mazan biyu a gefe da gefenta. Daka ganta kaga cikakkiyar baturiya. Duk tsaye sukai a ƙofar motar kowa cikin nutsuwarsa da kamewar girmamawa abin zam mamaki. (Humm jama’a MANDA fa duniya ce😜). Kusan minti ɗaya cif muna zuba idon ganin abinda ke faruwa kafin wanda ke gefen damar matar nan ya kai hannu jikin handle ɗin ƙofar ya buɗe tamkar mai gudun tashin yaro a barci. Wasu sakanni goma aka sake kwashewa kafin wani almurin baƙin takalmin haIf cover shoe mai adon golden ya sauka saman maroon carpet ɗin a hankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku sannan ɗayar ƙafar ma ta sauka baƙin wandon suit ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen har masu ji da mulkin da kuɗin babu wanda bai bi wanna halitta da kallo da ga ƙasa zuwa saman ƙyaƙyƙyawar fuskar mamallakin jikin ba. Tsaye yake gam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko ranƙwafawa. Suit ɗin jikinsa da basai an zauna ɓata lokacin lissafin kuɗin da suka lashe ba sun masifar zauna masa da tabbatar da shi a matsayin jaruminsa mai gara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da ALLAH ya bashi. Komai na jikin nasa baƙine, sai ɗan adon takalminsa da ta kasance golden da neck tie.. ɗinsa shima golden mai azabar ƙyau. Kamilalliyar fuskasa ma’abociyar kamewa da tsare gida ko nace baƙin hali a tsuke, sai kwantaccen gashin kumatunsa siriri daya zagaye bakinsa zuwa haɓarsa tamkar an zana ba biro. Yau ɗin ma dai akwai ɗan kunne ɗaya manne a kunensa, hakama zanen tattoo ɗinsa mai fuskar lion na nan zaune daram. Saɓanin hoto yau gashinsa ne a ɗaure kamar yanda mata ke parking sai dai shi nashi acan ta ƙasa ya ɗauresa har yana ɗan sauka jikin rigarsa dan babu kitso yau. Wanda bai sani ba tuni yake sakashi a jerin larabawa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar sakaye suke a cikin eyeglasses mai masifar ƙyau daya ƙara fidda taswurar halittar ƙyawun hancinsa daya zauna ɗaram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni ƙamshinsa ya baje wajen kai kace mu namu turaren baida tasiri ne ko Companyn da suka wallafo namu basu iya zaɓar ƙamshi ba. Kai jama’a akwaifa ƙyawawa a duniya. Idan kaga wani sai kaga kamar ka yanka kanka ka ɓoye wuƙar ƙawai. Bily karfa ki zata wannan bayanin da nake zayyano miki a kansa ya wani birgeni ne. Mtsowww ko kaɗan..
       Gaba ɗaya yaran nasa sake kame kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Karan farko na ɗan taɓe baki takaici kamar zai halakani. Shike nan a wannan rayuwar in har kana da dukiya ka zama saraki ko mai mulki?. Kai wani abun ma da ake maka ko kai mulkin ba lallai ya samu ba. Dibi dai wannan mutumin yanda yake wani busar isaka da shan ƙamshi fuska tamm kamar wanda aka aikama saƙon mutuwar tsoffinsa.
       Cikin isa da bajinta, a slowly tamkar wanda ake ɗauka a faifan video yay wani kalar haɗe hannayensa duk biyu a waje guda ya ɗagasu sama alamar gaisuwa wa duk jama’ar wajen. Kusan kowa dake wajen sai da sukai yanda yay ɗin idan ka cire gwamna da sarki. Sai ko ni ƴar balaja’un ku da saida Khulsoom ta zunguran amma na fuske naƙiyi, sai ma laɓe mata baki da nai na sake maida idanuna dake cikin glasses kansa ƙurr kai kace nice camara ɗin ma. Har inda aka tanada domin zamansa a tsakkiyar sarki da gwamna yaran nasa sukai masa rakkiya. Sai da ya zauna sannan suka koma ta bayansa suma duk suka zauna.
        Isowar tasa ta saka taron fara motsawa yanda ya kamata. An fara da gabatar da addu’oi kafin gwamna yay bayani mai birgewa a matsayin uban taro, dan ya nuna jin daɗinsa da farin cikinsa matuƙa game da wannan cigaba da aka kawo jiharsa, yana kuma fata da kira ga wannan shugaban kamfani akan idan har yaranmu sun cancanta yana roƙon ace sun zama mafi rinjaye da zasu samu aikinyi a ciki, yana kuma fatan ALLAH yasa kamfanin ya zamewa Kano dama arewacin ƙasar alkairi baki ɗaya.
     Kowa yaji daɗin bayanin gwamna. Dan zaka tabbatar da hakanne a fuskokin jama’ar dake a wajen ma. Sai sarki shima dai a matsayin uban taron. Sosai jawabansu suka ƙayatar suka kuma birge shima ɗin dai. Dan yayi kiranye sosai ga masu arziƙinmu da su shigo su kafa cibiyoyin kasuwancin a arewa domin matasanmu su samu aikinyi, hakan da zasu dingayi zai rage mana raɗaɗin rayuwa da ake ciki a wannan ƙarni. Zai kuma ƙarama matasan himma da nisantasu da ga shaye-shaye ko ɗaukar makamin da bai dace dasu ba a matsayin neman abincinsu ko zaman banza a bakin tituna mara amfani. Idan kuma har masu arziƙi suka cigaba da janye jikinsu da dukiyoyinsu da ga arewa to lallai watarana sai an wayi gari kowa ya zama abinda ba’a so. Idan kuma hakan da ba’a fata ta kasance ba arewan kaɗai ba, hatta su ma kudancin da wasu maƙwaftan ƙasashe zata shafesu, suma kuma ta nakasasu kamar yanda muma muke a nakashe yanzu. Bayan waɗan nan bayanan wasu masu muhimmanci ma sun sake biyo bayansu kafin shi ma ya miƙe……..✍️

          (🤭Ni dai nace faɗi gaskiya dai Samraah bama son kwana-kwana😜 idan Yaya Maash ya miki ne sai ai miki hanya🥱, dan kunsan bana ni gaskiya ƴar team Yaya Maash ce. Mu dama muna gidan kuɗi babu kwana-kwana🤣👌. Saura naji wani yace kwaɗayi🙄dan ɗan uwanmu ne Ya Maash ɗin na jini🤯, ai gwajin jini kuma a gani🤥😌).
     
         

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆

…….(Kutumelacy). Na faɗa a zuciya lokacin da yay sallama da wata jarumar muryarsa cikin yanayin mazantaka da nuna kamewa tamkar wanda akama dole, dan hatta lips ɗin ma da ƙyar yake motsasu. Bayan an amsa ya cigaba da miƙa saƙon gaisuwa da sannu da zuwa nan ɗin ma dai a fiffisge alamar maganar ta zame masa dolene ko kuma gayune ko kuwa girman kai irin na masu hannu da maiƙon kaza oho masa. Ga wata hausarsa da ta gama gurɓacewa da harshen ƴan kudanci ko nace harsuna da yawa dan tamkar ba cikakken bahaushen da akace an haifa a gari irin Kano ba. A wata gaɓar ma hausar ƙwace masa take sai dai ya kwakuso turanci ko faransanci ya maka a wajen ya kuma fuske ya cigaba da jawabinsa. Kuga wani ɗigimi, da dai a turancin ya tsaya da yafi, to waye ya wani iya faransanci anan?. Koda yake ban sani ba tunda naga taron duk nasu ne na masu jiki duk chocolates. Haka dai ya haɗa jawabin mintuna uku da ƙyar yana faman mana haɗin gambizar yaruka uku a lokaci guda da kai hannu saman kai ya murza tabbacin dai maganar ta dole ce a garesa. Hummm duniya makaranta, yo ALLAH na tuba su mu kuma indai zance ne ai ko akkun farkon ƙarni ta sama mana lafiya, duk da dai nima sai naso nake nawa surutun. Amma dai na ƙara ilimi, tunda naga yayin ƴar jan ajin nan ake da fidda zance ɗaɗɗaya billa sake kame kaina zan dingayi tunda ban sani ba ko nan gaba nima na kuɗance. Yo Bily abin ai na ALLAH ne, bafa zaune nake kurum ba daga aikin jarida sai na gida. Ina ƴar sana’ar sai da hijjabai da takalma duk da jarin bai wuci na dubu ashirin ba. To nadai fi su o’e ai masu cika gida da munsharin barci ko.
       Duk da fa jawabansa sun ƙayatar sun kuma tsaru tamkar daga takarda yake karantowa ni ƴar iyar taku sai da na taɓe baki. Yayinda wajen ya ɗauki tafi gaba ɗaya, a cikin ƴan jaridar mu harda masu yin fito. Hakama wasu gungun samari ƙyawawan da kallo ɗaya zaka musu kasan akwai ƴan canji dan kamar sun zaɓo kansu ne dan ƙyau da gayu, bana kuma raba ɗaya biyu abokansa ne sai salute nashi suke suma dai cike da isa da ƙasaitar. A haka taro ya cigaba da tafiya cikin nutsuwa, mudai ƴan jarida munata ɗaukar rahotanni babu mai damar cewa komai a yanzu sai nan gaba. Dan ya bada damar a masa tambayoyi a karo na biyu da zai fito, amma akan abinda ya shafi Companyn kawai. Nikam na taɓe baki, dan na shiryo nawa questions ɗinne akan komai kuma in sha ALLAHU sai na masa su duka, dan zan fara da manya-manyan cikine da dole sai ya magantu koda baya son hakan.
        Ana tsaka da sauraren jawaban sauran manyan mutanen wajen fitsari yay mugun matsata. Sosai hankalina ya tashi, na shiga dana sanin shan shayin da nayi kafin na fito. Tun ina daurewa har dai na shiga mutsu-mutsun da Khulsoom ta lura dani.
     “Samraah lafiya kuwa?”.
Ta faɗa tana tsareni da idanu. Fuskata dake cikin facemask a marairaice na ce, “Ina fa lafiya Khulsoom. Wlhy wani mugun fitsarine ya matseni kamar zai zubo. Dan ALLAH ki tashi ki rakani kada ayi abin kunya a bainar nasi. Maimakon mai buɗe Company ya zama topic of the day ni na zama.” dariya ta nema saki, amma ganin yanda na ɗaure fuska ya sata daurewa ta ƙunshe abarta. Cikin raɗa ta ce, “Kima Mansoor magana ya raka ki, dan wlhy tsoron waɗan nan jami’an tsaron da aka baza nake yi”.
     Wata hararar na sake watsa mata a karo na biyu, batare dana tanka mata ba na miƙe dan gab fitsarin yake da zubowa. Kasancewar wajen tsitt yake babu wani hayaniya kuma kowa a zaune yake a nutsensa sai tashina ya jawo hankalin mutane da yawa gareni. ALLAH ya soni komai nawa a rufe yake, idan ka cire tafukan hannuna da yatsunsu suka ƙawatu da jan lallale, na tabbata yau da ace ba hijjab na saka ba wannan idanun na jama’a sai ya sakani sakin fitsarin a wajen. Gudun karna taka doka ko yin abinda zai jawo min kunyata kai tsaye na nufi security dake kusa damu sosai. Gaishesa nayi cikin girmamawa bayan na sauke mask ɗina dan karma ya fassarani da abinda bashi nake nufi ba sannan nai masa bayani. Hakan da nai kuwa ya sakashi jin daɗi, dan har I’d card ɗina saida na nuna masa tunma kan ya buƙata. Wata mace a cikin jami’ansu ya yafito da hannu, ta iso wajen tana mai ƙamewa da salute nashi. Nuna mata ni yay yace ta rakani restroom. Da girmamawa ta amsa masa nan ma. Sannan muka wuce ta can bayan Companyn. Na zata anan bayin yake, amma sai naga ta shiga dani ta wata ƙofa alamar cikin dai Companyn zamu shiga amma ta baya. Dan ta gaba an gama zagayesa da zaren nan mai ribbon kuma ba’a kai ga yankawa ba. Lallai dukiya tayi aiki a wannan waje, duk da fa inda muka shiga bawani ciki-ciki bane ba. Amma tsayawa kwatanta miki Bily walla ɓata lokaci zamuyi. Har ciki muka shiga tare da ita, ta nunamin bayin farko, godiya nai mata munama juna murmushi. Ina shiga wayarta ta fara ƙara alamar shigowar kira, dole ta fita a wajen domin amsawa. Har kuma na gama abinda nake na fito babu ita. Mamaki ya kamani na shiga waige-waige. Ganin dai da gaske bata a wajen na nufi neman hanyar da muka shigo. Sai dai kuma na rikice dan hanyoyin da yawa ne ashe duk iri ɗaya. Canki in canka na shigayi a tsakani, ganin dai ba ganewar zanyi ba na shiga binsu ɗai-ɗai ina taɓawa. Sai dai me kowacce na taɓa sai na jita gam a kulle. Tun ina ɗaukar al’amarin wasa har hankalina ya fara tashi amma dai na dake ina ƙarama kaina ƙwarin gwiwa. Hope ɗina na gab da barina gaba ɗaya wata a cikin ƙofifin ta buɗe. Ji nai kamar na saki ihu dan daɗi, sai dai banyi hakan ba na saki ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna da buɗewa, cike da zumuɗi na sake kama handle ɗin ƙofar na murɗa, ina ƙoƙarin danna kai ciki naja wani wawan birki sakamakon abinda naci karo da shi mai ɗimauta zuciya da tunani.
       Sosai jikina ke rawa idanuna a matuƙar ware kansu. Ganin hankalinsu bai kawo kaina ba na sake jawo ƙofar sosai ta yanda bazasu iya ganina ba. Video recording na latso a wayata na fara ɗaukarsu. A dai-dai lokacin ya zare wuƙar da ga jikin mutumin, wani irin gurnanin ƙarasa fitar rai yayi ya ida zamewa da ga jikin bangon da yake yay ƙasa. Mutumin daya buɗe masa mota ɗazun ne a gefensa, gaban mutumin da suka kashe ɗin ya kai duƙe yana mai saka yatsunsa biyu a saitin hancinsa, a wani irin yanayi ya furta, “Ya mutu Sir”.
      Kansa ya ɗauke tamkar baiji miya faɗa ba. Hakan yasa wancan ɗin miƙewa batare daya sake cewa komai ba shima ya buɗe wani farin ƙyalle. Wuƙar ya saka masa a ciki tare da handkerchief ɗin daya riƙeta, sannan ya bar wajen cike da takun isa, bathroom dake cikin ɗakin ya nufa. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai gashi ya fito yana goge hannu da ƙaramin farin towel alamun wankewa yayi. Sai da ya gama goge hannun yana ƙoƙarin ajiye towel ɗin yake faɗin, “Lukman ya shigo da kayan can, ya fita da gawan zuwa can anguwan”.
     Kai yaron nasa ya jinjina masa cike da girmamawa. Ƙofa ya nufo, dan haka nai saurin tsayar da video ɗin na koma wani ɗan lungu na lafe. Wajen sauri face mask ɗina dake a hannuna ya faɗi ƙasa. Cikin takunsa da baya fidda sauti ya fito, cak ya tsaya tamkar wanda ake controlling da remote yana kallo mask ɗina dake yashe a ƙasa. Sosai na waro idanuna waje ƙirjina na wani irin mahaukacin bugawa da sauri-sauri. Lokacin da yake ranƙwafawa yana ƙoƙarin kai pen ɗinsa mai masifar ƙyau ya ɗauka facee mask ɗin dashi jinai kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Sake lafewa nai sosai tamkar ina shirin keta bangon na shige ciki. Yayi kusan sakan ashirin yana kallon mask ɗin, sai kuma ya zaro wani ƙyaƙyƙyawan handkerchief a aljihunsa ya warwaresa ciki ya saka. Da baya-baya ya koma yana ɗan waige-waige, ƙofar ɗakin daya fito ya ɗan buɗe kaɗan, sai kuma ya maida ya rufe ya sake juyowa. Kusan taku goma ya sake tsayawa cak. Da sauri na kai hannuna kan bakina na rufe kamar zan saki kuka dan tashin hankali. A hankali ya juyo da alama dai yana ji a jikinsa akwai mutum a wajen. Bakina na sake dumtsewa tare da hanci ina mai runtse idanuna da ƙarfin masifa. Nafi mintuna biyu a haka kafin na buɗe a hankali, wayam na gani alamar ya fice. Cikin sauri na zame nai ƙasa ina mai janye hannuna da sakin numfashi mai ƙarfin gaske. Inaga tunda nasan kaina nai hankali ban taɓa cin karo da matsanancin tashin hankali irin na yau ba. Kisan kai fa, na mutum ba wani ƙwaro ko dabba ba. Lallai mutum abin tsoro ne, taya zakai tunanin wannan mutumin zai iya aikata wannan ta’asar, jibesa kamar wani mutumin kirki. Koda yake wanda ke iya zana tattoo a jikinsa ga ɗan kunne ya kuma ɗaure gashi a kai kamar wani mace ko yay kitso komai ma ai zai iya aikatawa. Aiko bazan taɓa yin shiru ba, dolene nai gaggawar nunama duniya wanene shi, yanzu kuma ya kamata a cikin taron nan ba sai anjima ba. Zaram na miƙe kuwa ina tattaro wayata dake yashe a ƙasa da sauri……..✍️

        “🤯🤯Na rasa abin faɗa Samraah.  Yaya kin tona asirin nasa kenan?”.

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏

……Humm Bily nayi yunƙurin hakan kamar yadda na faɗa miki. Sai dai ina miƙewa aka buɗe wata ƙofa da sai yanzu hankalina ya kai na fahimci a itane muka shigo tare da jami’ar nan ɗazun. Wani ne ya shigo da kaya a hannu, da alama Lukman ɗin daya faɗa ne. Jikin bangon na koma na sake lafewa, har sai da ya shige. Maimakon na sake yunƙurin fita sai zuciyata ke bani shawarar tsayawa naga yanda zasu fita da gawar. Ga kiran Mansoor sai shigomin ya ke da alama jirana suke. Sauƙina ma wayar a silent take. A plane mood na sakata, na sake shiga video recording. Ko sakan goma ba’ai ba sai gasu sun fito da gawar kuwa, duk da an naɗeta cikin wani abu jini duk ya ɓata mayafin. Da ƙyar na iya tsaida karkarwar da jikina ke min. Suna ficewa nai saurin fitowa da hanzari nabi bayansu nima. Inayi ina waige-waige. Maƙalewa nai ta jikin ƙofa ina cigaba da ɗauka har suka sakata a cikin motar. Ina ganin sun kammala Lukman ɗin ya shiga motar ɗayan na shirin juyowa ciki na sake komawa wani lungun da gudu. Dan kar yaji sautin hakkina hijjab ɗina na kama na cusa a bakina har sai da ya koma ɗakin, babu jimawa sai gashi ya fito da mopper yana goge duk inda jinin ya ɓata. Ganin ya sake komawa ɗakin na fito da sanɗa, ta hanyar da muka shigo nabi na fita. Inda wani zai ƙuramin ido tuni zai gane a gigice nake, gashi babu mask ɗin a fuskata yanzun. Dawowata wajen taron dai-dai ana mimmiƙewa zuwa inda ribbon ɗin nan yake. Hakan ta bani damar isa inda su Khulsoom suke. Bag ɗina kawai na amsa a hannunta na jefa wayata na ciro wani face mask ɗin na shiga sawa. Ganin yanda suka tsareni da ido ya sakani ɗaga musu hannu cikin dakewa na ce, “Kuyi haƙuri ina a inda bai kamata na ɗaga waya bane ba. Badai har yay jawabi na biyun ba ne ko?”.
        Khulsoom ce ta amsa min da “A’a bai yiba sai an gama yanka abin can.” kai na jinjina mata alamar fahimta. Yayinda nake ɗan satar kallon Mansoor ta gefen ido, dan shi baice dani komai ba face zubamin idanu da yay kawai. Da alama bai gamsu da amsar dana bada ba. Dama nasan in kowa bai fahimci halin da nake a ciki ba shi sai ya fahimta. Dan akwai shaƙuwa ta musamman tsakanina da shi ta yanda ko motsi ɗaya daga cikinmu yayi sai ɗan uwansa ya fahimci mi yake nufi. Ban sake yarda na kalla inda yake ba muka nufi inda za’a yanka ribbon ɗin. Duk yanda naso kame kaina daga kallon mutumin nan na gagara haka. Mamaki abinda ya faru a cikin ƴan mintunan da basu wuce talatin ba kawai nake. Ban fahimci na tafi tunani mai zurfin da har bana fahimtar mi ake a gurin ba sai da Khulsoom ta zungureni. Numfashi mai nauyi na kawo tare da yin firgigit na ce mata, “Na’am mi kike ce?”.
       Da mamaki ta ce, “mike damunki ne wai haka Samraah. Duk kinyi wani iri kamar wadda ke a rikice. Kalla yanda kike zufa ga hankalinki sam baya kan abinda ma akeyi”.
    Cikin son basar da ita na ce, “Cikina ne ke ɗan juyamin. Inaga awaran da naci ne da kabeji ɗazun da safe.”
         “Ayya sannu, amma tunda kin san yana baki matsala haka ai da baki ci ba, ke da zaki shigo cikin taro babu daɗi kaita zaryar toilet ai”.
      “Haka ne, nima na shafa’a ne kawai. Amma in sha ALLAHU ina fatan ma bazan sake zuwa toilet ɗin ba. Akwai maganin da nake sha a bag ɗina bari na sha shi”.
    Kanta ta jinjina min tana sake min sannu. Inda muke zaune na koma na zauna dan hakan sai yafi min sauƙi. A dai-dai nan aka saki tafi alamar har an yanka. Na sake tafiya a tunani naji saukar muryar Mansoor a kaina. Firgigit na dawo hayyacina ina kallonsa. Sai kuma nai saurin ɗauke idanun a kansa ina ƙoƙarin dai-daita nutsuwata.
       “Samraah mike damunki?”.
   In har kaji sunana kai tsaye a bakin Mansoor babu wasa sam a ciki. Saurin girgiza masa kai nayi da faɗin, “Babu komai fa. Na dawo nan nasha magani ne kawai”.
     “Ƙarya kike”.
  Ya faɗa kansa tsaye kawai. Nasan za’ayi hakan. Dan Mansoor ya gama sanina matuƙa kasancewarsa mutum mafi shaƙuwa a rayuwata bayan ƴan gidanmu. Shekara biyar ai ba wasa ba. Ƙasa nai da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma na ɗauki wayata nai rubutu na tura masa. Ganin yanda ya cigaba da tsaiwa yana kallona ya sani ɗagowa ina masa nuni daya duba wayarsa. Baiyi musu ba ya zarota ya duba. Da sauri ya ɗago yana kallona. Sai kuma babu shiri shima ya kai zaune a kujerar kusa da ni. Sai da ya wawwaiga gefe da gefenmu sannan ƙasa-ƙasa ya ce, “Da gaske Baby”.
       Kaina na jinjina masa kawai ina ƙoƙarin riƙe hawayen da suka ciko min ido. Sai kuma na kallesa na ce, “Ina son nabar wajen nan yanzu. Dan na yarda face mask ɗina a ciki ya ɗauka. Na tabbatar zuciyarsu dole tana musu wasi-wasi akan dole wani ya shiga wajen. Dan na fahimci hankalin yaron nasa kamar tun ɗazun ma ya rabu biyu akan mutane.”
          “Ba tafiya bace mafita Samraah. Ki ƙara daurewa a kammala komai kawai. Sannan ki dawo da hankalinki jikinki, dan fitarki yanzu a wajen nan bazata zama mai sauƙi ba, sannan zasu ma iya ganewa ta hakan tunda baki da wani dalilin fita na zahiri. Kinga ma tashi mu shiga ciki kinga mutane sun kusa gama shiga za’a zagaya cikin companyn ne”.
      Badan naso ba dole na miƙe. A zuciyata kam sai addu’oi nakeyi. Kar kiga fa kamar na cika tsoro. Wlhy babu abinda ke tada min hankali sai ganin gawar mutum cikin jini. Dan abune da bai taɓa faruwa da ni ba. Kinga ko sanda Babanmu ya rasu banda wani cikakken hankalin daya kamata irin hakan yaban tsoro. Tunda shima har aka binne gawarsa yana a yanayin zubar jini saboda accident. Mamanmu kuma bamma san rasuwarta ba sam, tunda ban wuci 3years ba kwata-kwata. Haka dai da ƙyar na cigaba da riƙe kaina mukabi ayarin ƴan ganin cikin companyn. Ya haɗu matuƙa gaya. Ga wasu manyan machines a wani ƙaton hall da baida iyaka. Da alama daga nan za’a dinga ƙera motocin ko haɗa su ne ma oho musu. Bayan nan akwai wajaje daban-daban masu ɗauke da abubuwa kala-kala da bamusan na miye ba, duk da wani bature a cikin abokan nasa sunata ƙoƙarin yin bayani, ni dai ba wani fahimtarsu nake ba sam. Dan duk yanda wajen ya kai ga haɗuwa a yanzu ni sam baya birgeni. Sai ma ganinsa nake baƙiƙƙirin da duhu. An ɗauki kusan mintuna talatin a ciki kafin a fito. Ɗayan sashen da ya kasance shine ake fara gani daga titi, wanda an yisane da zallar gilashi aka sake nufa. Anan ne offices ɗin ma’aikatan yake ashe. Tun daga hawan farko har zuwa na biyar sai da muka shishshiga da taimakon lift… Duka offices ɗin sun haɗu, hatta na ƙananun ma’aikata dake a hawan farko ma duk da na haɗaka ne komai tsaf. Amma nasa na matsayin oga kwata-kwata yafi kowanne tsaruwa, dan tamkar ba’a Nigeria kake ba. Daga office ɗin kuma akan iya ganin cikin ƙwaryar Kano da ƙyau ta kowanne ɓangare. Sosai abin akwai ƙayatarwa. Sai dai ni bai ƙayatar dani ba. Dan yanzu baƙiƙƙirin ma nake kallon mai Companyn kamar baƙin maciji. Nan ma an kwashi wasu mintuna kafin a fito. ALLAH ALLAH nake kawai yayi jawabin ƙarshen nan na masa tambayar da zan masa na bar wajen. Amma sai akace abinci za’aci a yanzun, sannan aje salla a dawo a ƙarasa. Kamar zan fasa ihu haka naji, sai dai yaya zanyi. Dole yanda suka tsara haka kowa zai bi. An fara gabatar da abincin a nutse, za kuma azo har inda kake a baka zaɓin abinda kake son ci sannan aje a kawo maka. Koda aka yambayen nikam nace a’a. Dan na ɗau alwashin bazanci kuɗin jinin mutane ba. Wama ya sani ko tsafi yake yi ne. Ai dama al’amarin dukiyar tasa da mamaki, shiyyasama mutane suketa wasi-wasi a kansa. Haba mutumin nan ai yayi ƙarami da tara irin wannan dukiyar haka. Kwata-kwata fa bazai wuce talatin ba. Inma zai haura hakan kaɗanne kuwa. Yo ko iya wannan companyn akace ya mallaka a shekarun nan nasa ai abin ayi wasi-wasi ne balle kuma ace yana da ninkin baninkin hakan har dasu jirage. Jirgi ake magana fa dake tashi sama da ɗaruruwan mutane bawai kwale-kwale na katako da ake tsallaka ruwan ɓagwai ba. Sannan bama ɗaya ba, ba biyu ba fa….
         “Baby!!”.
    Mansoor ya sake katse min tunani, dan yanzu a gefena yake. Firgigit na dawo hankalina. “please be smart mana. Ko so kike abokan tafiyarmu su fahimci wani abu ne?.”
     Kaina na girgiza masa. Cikin dauriya na kalla abincin da ya saka a kawo min. Maimakon naji sha’awar cinsa kodan ƙyawun da yay a cikin ido ga kaza har rabi a ciki sai naji sam baya wani birgeni. A hankali na sauke a jiyar zuciya da ce masa, “Na ƙoshi da abincin nan wlhy. Kayi haƙuri dan ALLAH.”
       Kallona kawai ya tsaya yi, ni kuma na ɗauke idanuna daga sashensa gaba ɗaya. Da ga ƙarshe ma na ɗauka wayata na shiga buga game wai duk dan dai na dawo da hankalina jikina. Sai dai tuni na kasa cigaba da buga game ɗin, na koma kallon mutane a ƙasan ido musamman ma yaronsa da duk wani motsin sa……✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆

…….(Kutumelacy). Na faɗa a zuciya lokacin da yay sallama da wata jarumar muryarsa cikin yanayin mazantaka da nuna kamewa tamkar wanda akama dole, dan hatta lips ɗin ma da ƙyar yake motsasu. Bayan an amsa ya cigaba da miƙa saƙon gaisuwa da sannu da zuwa nan ɗin ma dai a fiffisge alamar maganar ta zame masa dolene ko kuma gayune ko kuwa girman kai irin na masu hannu da maiƙon kaza oho masa. Ga wata hausarsa da ta gama gurɓacewa da harshen ƴan kudanci ko nace harsuna da yawa dan tamkar ba cikakken bahaushen da akace an haifa a gari irin Kano ba. A wata gaɓar ma hausar ƙwace masa take sai dai ya kwakuso turanci ko faransanci ya maka a wajen ya kuma fuske ya cigaba da jawabinsa. Kuga wani ɗigimi, da dai a turancin ya tsaya da yafi, to waye ya wani iya faransanci anan?. Koda yake ban sani ba tunda naga taron duk nasu ne na masu jiki duk chocolates. Haka dai ya haɗa jawabin mintuna uku da ƙyar yana faman mana haɗin gambizar yaruka uku a lokaci guda da kai hannu saman kai ya murza tabbacin dai maganar ta dole ce a garesa. Hummm duniya makaranta, yo ALLAH na tuba su mu kuma indai zance ne ai ko akkun farkon ƙarni ta sama mana lafiya, duk da dai nima sai naso nake nawa surutun. Amma dai na ƙara ilimi, tunda naga yayin ƴar jan ajin nan ake da fidda zance ɗaɗɗaya billa sake kame kaina zan dingayi tunda ban sani ba ko nan gaba nima na kuɗance. Yo Bily abin ai na ALLAH ne, bafa zaune nake kurum ba daga aikin jarida sai na gida. Ina ƴar sana’ar sai da hijjabai da takalma duk da jarin bai wuci na dubu ashirin ba. To nadai fi su o’e ai masu cika gida da munsharin barci ko.
       Duk da fa jawabansa sun ƙayatar sun kuma tsaru tamkar daga takarda yake karantowa ni ƴar iyar taku sai da na taɓe baki. Yayinda wajen ya ɗauki tafi gaba ɗaya, a cikin ƴan jaridar mu harda masu yin fito. Hakama wasu gungun samari ƙyawawan da kallo ɗaya zaka musu kasan akwai ƴan canji dan kamar sun zaɓo kansu ne dan ƙyau da gayu, bana kuma raba ɗaya biyu abokansa ne sai salute nashi suke suma dai cike da isa da ƙasaitar. A haka taro ya cigaba da tafiya cikin nutsuwa, mudai ƴan jarida munata ɗaukar rahotanni babu mai damar cewa komai a yanzu sai nan gaba. Dan ya bada damar a masa tambayoyi a karo na biyu da zai fito, amma akan abinda ya shafi Companyn kawai. Nikam na taɓe baki, dan na shiryo nawa questions ɗinne akan komai kuma in sha ALLAHU sai na masa su duka, dan zan fara da manya-manyan cikine da dole sai ya magantu koda baya son hakan.
        Ana tsaka da sauraren jawaban sauran manyan mutanen wajen fitsari yay mugun matsata. Sosai hankalina ya tashi, na shiga dana sanin shan shayin da nayi kafin na fito. Tun ina daurewa har dai na shiga mutsu-mutsun da Khulsoom ta lura dani.
     “Samraah lafiya kuwa?”.
Ta faɗa tana tsareni da idanu. Fuskata dake cikin facemask a marairaice na ce, “Ina fa lafiya Khulsoom. Wlhy wani mugun fitsarine ya matseni kamar zai zubo. Dan ALLAH ki tashi ki rakani kada ayi abin kunya a bainar nasi. Maimakon mai buɗe Company ya zama topic of the day ni na zama.” dariya ta nema saki, amma ganin yanda na ɗaure fuska ya sata daurewa ta ƙunshe abarta. Cikin raɗa ta ce, “Kima Mansoor magana ya raka ki, dan wlhy tsoron waɗan nan jami’an tsaron da aka baza nake yi”.
     Wata hararar na sake watsa mata a karo na biyu, batare dana tanka mata ba na miƙe dan gab fitsarin yake da zubowa. Kasancewar wajen tsitt yake babu wani hayaniya kuma kowa a zaune yake a nutsensa sai tashina ya jawo hankalin mutane da yawa gareni. ALLAH ya soni komai nawa a rufe yake, idan ka cire tafukan hannuna da yatsunsu suka ƙawatu da jan lallale, na tabbata yau da ace ba hijjab na saka ba wannan idanun na jama’a sai ya sakani sakin fitsarin a wajen. Gudun karna taka doka ko yin abinda zai jawo min kunyata kai tsaye na nufi security dake kusa damu sosai. Gaishesa nayi cikin girmamawa bayan na sauke mask ɗina dan karma ya fassarani da abinda bashi nake nufi ba sannan nai masa bayani. Hakan da nai kuwa ya sakashi jin daɗi, dan har I’d card ɗina saida na nuna masa tunma kan ya buƙata. Wata mace a cikin jami’ansu ya yafito da hannu, ta iso wajen tana mai ƙamewa da salute nashi. Nuna mata ni yay yace ta rakani restroom. Da girmamawa ta amsa masa nan ma. Sannan muka wuce ta can bayan Companyn. Na zata anan bayin yake, amma sai naga ta shiga dani ta wata ƙofa alamar cikin dai Companyn zamu shiga amma ta baya. Dan ta gaba an gama zagayesa da zaren nan mai ribbon kuma ba’a kai ga yankawa ba. Lallai dukiya tayi aiki a wannan waje, duk da fa inda muka shiga bawani ciki-ciki bane ba. Amma tsayawa kwatanta miki Bily walla ɓata lokaci zamuyi. Har ciki muka shiga tare da ita, ta nunamin bayin farko, godiya nai mata munama juna murmushi. Ina shiga wayarta ta fara ƙara alamar shigowar kira, dole ta fita a wajen domin amsawa. Har kuma na gama abinda nake na fito babu ita. Mamaki ya kamani na shiga waige-waige. Ganin dai da gaske bata a wajen na nufi neman hanyar da muka shigo. Sai dai kuma na rikice dan hanyoyin da yawa ne ashe duk iri ɗaya. Canki in canka na shigayi a tsakani, ganin dai ba ganewar zanyi ba na shiga binsu ɗai-ɗai ina taɓawa. Sai dai me kowacce na taɓa sai na jita gam a kulle. Tun ina ɗaukar al’amarin wasa har hankalina ya fara tashi amma dai na dake ina ƙarama kaina ƙwarin gwiwa. Hope ɗina na gab da barina gaba ɗaya wata a cikin ƙofifin ta buɗe. Ji nai kamar na saki ihu dan daɗi, sai dai banyi hakan ba na saki ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna da buɗewa, cike da zumuɗi na sake kama handle ɗin ƙofar na murɗa, ina ƙoƙarin danna kai ciki naja wani wawan birki sakamakon abinda naci karo da shi mai ɗimauta zuciya da tunani.
       Sosai jikina ke rawa idanuna a matuƙar ware kansu. Ganin hankalinsu bai kawo kaina ba na sake jawo ƙofar sosai ta yanda bazasu iya ganina ba. Video recording na latso a wayata na fara ɗaukarsu. A dai-dai lokacin ya zare wuƙar da ga jikin mutumin, wani irin gurnanin ƙarasa fitar rai yayi ya ida zamewa da ga jikin bangon da yake yay ƙasa. Mutumin daya buɗe masa mota ɗazun ne a gefensa, gaban mutumin da suka kashe ɗin ya kai duƙe yana mai saka yatsunsa biyu a saitin hancinsa, a wani irin yanayi ya furta, “Ya mutu Sir”.
      Kansa ya ɗauke tamkar baiji miya faɗa ba. Hakan yasa wancan ɗin miƙewa batare daya sake cewa komai ba shima ya buɗe wani farin ƙyalle. Wuƙar ya saka masa a ciki tare da handkerchief ɗin daya riƙeta, sannan ya bar wajen cike da takun isa, bathroom dake cikin ɗakin ya nufa. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai gashi ya fito yana goge hannu da ƙaramin farin towel alamun wankewa yayi. Sai da ya gama goge hannun yana ƙoƙarin ajiye towel ɗin yake faɗin, “Lukman ya shigo da kayan can, ya fita da gawan zuwa can anguwan”.
     Kai yaron nasa ya jinjina masa cike da girmamawa. Ƙofa ya nufo, dan haka nai saurin tsayar da video ɗin na koma wani ɗan lungu na lafe. Wajen sauri face mask ɗina dake a hannuna ya faɗi ƙasa. Cikin takunsa da baya fidda sauti ya fito, cak ya tsaya tamkar wanda ake controlling da remote yana kallo mask ɗina dake yashe a ƙasa. Sosai na waro idanuna waje ƙirjina na wani irin mahaukacin bugawa da sauri-sauri. Lokacin da yake ranƙwafawa yana ƙoƙarin kai pen ɗinsa mai masifar ƙyau ya ɗauka facee mask ɗin dashi jinai kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Sake lafewa nai sosai tamkar ina shirin keta bangon na shige ciki. Yayi kusan sakan ashirin yana kallon mask ɗin, sai kuma ya zaro wani ƙyaƙyƙyawan handkerchief a aljihunsa ya warwaresa ciki ya saka. Da baya-baya ya koma yana ɗan waige-waige, ƙofar ɗakin daya fito ya ɗan buɗe kaɗan, sai kuma ya maida ya rufe ya sake juyowa. Kusan taku goma ya sake tsayawa cak. Da sauri na kai hannuna kan bakina na rufe kamar zan saki kuka dan tashin hankali. A hankali ya juyo da alama dai yana ji a jikinsa akwai mutum a wajen. Bakina na sake dumtsewa tare da hanci ina mai runtse idanuna da ƙarfin masifa. Nafi mintuna biyu a haka kafin na buɗe a hankali, wayam na gani alamar ya fice. Cikin sauri na zame nai ƙasa ina mai janye hannuna da sakin numfashi mai ƙarfin gaske. Inaga tunda nasan kaina nai hankali ban taɓa cin karo da matsanancin tashin hankali irin na yau ba. Kisan kai fa, na mutum ba wani ƙwaro ko dabba ba. Lallai mutum abin tsoro ne, taya zakai tunanin wannan mutumin zai iya aikata wannan ta’asar, jibesa kamar wani mutumin kirki. Koda yake wanda ke iya zana tattoo a jikinsa ga ɗan kunne ya kuma ɗaure gashi a kai kamar wani mace ko yay kitso komai ma ai zai iya aikatawa. Aiko bazan taɓa yin shiru ba, dolene nai gaggawar nunama duniya wanene shi, yanzu kuma ya kamata a cikin taron nan ba sai anjima ba. Zaram na miƙe kuwa ina tattaro wayata dake yashe a ƙasa da sauri……..✍️

        “🤯🤯Na rasa abin faɗa Samraah.  Yaya kin tona asirin nasa kenan?”.

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏

……Humm Bily nayi yunƙurin hakan kamar yadda na faɗa miki. Sai dai ina miƙewa aka buɗe wata ƙofa da sai yanzu hankalina ya kai na fahimci a itane muka shigo tare da jami’ar nan ɗazun. Wani ne ya shigo da kaya a hannu, da alama Lukman ɗin daya faɗa ne. Jikin bangon na koma na sake lafewa, har sai da ya shige. Maimakon na sake yunƙurin fita sai zuciyata ke bani shawarar tsayawa naga yanda zasu fita da gawar. Ga kiran Mansoor sai shigomin ya ke da alama jirana suke. Sauƙina ma wayar a silent take. A plane mood na sakata, na sake shiga video recording. Ko sakan goma ba’ai ba sai gasu sun fito da gawar kuwa, duk da an naɗeta cikin wani abu jini duk ya ɓata mayafin. Da ƙyar na iya tsaida karkarwar da jikina ke min. Suna ficewa nai saurin fitowa da hanzari nabi bayansu nima. Inayi ina waige-waige. Maƙalewa nai ta jikin ƙofa ina cigaba da ɗauka har suka sakata a cikin motar. Ina ganin sun kammala Lukman ɗin ya shiga motar ɗayan na shirin juyowa ciki na sake komawa wani lungun da gudu. Dan kar yaji sautin hakkina hijjab ɗina na kama na cusa a bakina har sai da ya koma ɗakin, babu jimawa sai gashi ya fito da mopper yana goge duk inda jinin ya ɓata. Ganin ya sake komawa ɗakin na fito da sanɗa, ta hanyar da muka shigo nabi na fita. Inda wani zai ƙuramin ido tuni zai gane a gigice nake, gashi babu mask ɗin a fuskata yanzun. Dawowata wajen taron dai-dai ana mimmiƙewa zuwa inda ribbon ɗin nan yake. Hakan ta bani damar isa inda su Khulsoom suke. Bag ɗina kawai na amsa a hannunta na jefa wayata na ciro wani face mask ɗin na shiga sawa. Ganin yanda suka tsareni da ido ya sakani ɗaga musu hannu cikin dakewa na ce, “Kuyi haƙuri ina a inda bai kamata na ɗaga waya bane ba. Badai har yay jawabi na biyun ba ne ko?”.
        Khulsoom ce ta amsa min da “A’a bai yiba sai an gama yanka abin can.” kai na jinjina mata alamar fahimta. Yayinda nake ɗan satar kallon Mansoor ta gefen ido, dan shi baice dani komai ba face zubamin idanu da yay kawai. Da alama bai gamsu da amsar dana bada ba. Dama nasan in kowa bai fahimci halin da nake a ciki ba shi sai ya fahimta. Dan akwai shaƙuwa ta musamman tsakanina da shi ta yanda ko motsi ɗaya daga cikinmu yayi sai ɗan uwansa ya fahimci mi yake nufi. Ban sake yarda na kalla inda yake ba muka nufi inda za’a yanka ribbon ɗin. Duk yanda naso kame kaina daga kallon mutumin nan na gagara haka. Mamaki abinda ya faru a cikin ƴan mintunan da basu wuce talatin ba kawai nake. Ban fahimci na tafi tunani mai zurfin da har bana fahimtar mi ake a gurin ba sai da Khulsoom ta zungureni. Numfashi mai nauyi na kawo tare da yin firgigit na ce mata, “Na’am mi kike ce?”.
       Da mamaki ta ce, “mike damunki ne wai haka Samraah. Duk kinyi wani iri kamar wadda ke a rikice. Kalla yanda kike zufa ga hankalinki sam baya kan abinda ma akeyi”.
    Cikin son basar da ita na ce, “Cikina ne ke ɗan juyamin. Inaga awaran da naci ne da kabeji ɗazun da safe.”
         “Ayya sannu, amma tunda kin san yana baki matsala haka ai da baki ci ba, ke da zaki shigo cikin taro babu daɗi kaita zaryar toilet ai”.
      “Haka ne, nima na shafa’a ne kawai. Amma in sha ALLAHU ina fatan ma bazan sake zuwa toilet ɗin ba. Akwai maganin da nake sha a bag ɗina bari na sha shi”.
    Kanta ta jinjina min tana sake min sannu. Inda muke zaune na koma na zauna dan hakan sai yafi min sauƙi. A dai-dai nan aka saki tafi alamar har an yanka. Na sake tafiya a tunani naji saukar muryar Mansoor a kaina. Firgigit na dawo hayyacina ina kallonsa. Sai kuma nai saurin ɗauke idanun a kansa ina ƙoƙarin dai-daita nutsuwata.
       “Samraah mike damunki?”.
   In har kaji sunana kai tsaye a bakin Mansoor babu wasa sam a ciki. Saurin girgiza masa kai nayi da faɗin, “Babu komai fa. Na dawo nan nasha magani ne kawai”.
     “Ƙarya kike”.
  Ya faɗa kansa tsaye kawai. Nasan za’ayi hakan. Dan Mansoor ya gama sanina matuƙa kasancewarsa mutum mafi shaƙuwa a rayuwata bayan ƴan gidanmu. Shekara biyar ai ba wasa ba. Ƙasa nai da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma na ɗauki wayata nai rubutu na tura masa. Ganin yanda ya cigaba da tsaiwa yana kallona ya sani ɗagowa ina masa nuni daya duba wayarsa. Baiyi musu ba ya zarota ya duba. Da sauri ya ɗago yana kallona. Sai kuma babu shiri shima ya kai zaune a kujerar kusa da ni. Sai da ya wawwaiga gefe da gefenmu sannan ƙasa-ƙasa ya ce, “Da gaske Baby”.
       Kaina na jinjina masa kawai ina ƙoƙarin riƙe hawayen da suka ciko min ido. Sai kuma na kallesa na ce, “Ina son nabar wajen nan yanzu. Dan na yarda face mask ɗina a ciki ya ɗauka. Na tabbatar zuciyarsu dole tana musu wasi-wasi akan dole wani ya shiga wajen. Dan na fahimci hankalin yaron nasa kamar tun ɗazun ma ya rabu biyu akan mutane.”
          “Ba tafiya bace mafita Samraah. Ki ƙara daurewa a kammala komai kawai. Sannan ki dawo da hankalinki jikinki, dan fitarki yanzu a wajen nan bazata zama mai sauƙi ba, sannan zasu ma iya ganewa ta hakan tunda baki da wani dalilin fita na zahiri. Kinga ma tashi mu shiga ciki kinga mutane sun kusa gama shiga za’a zagaya cikin companyn ne”.
      Badan naso ba dole na miƙe. A zuciyata kam sai addu’oi nakeyi. Kar kiga fa kamar na cika tsoro. Wlhy babu abinda ke tada min hankali sai ganin gawar mutum cikin jini. Dan abune da bai taɓa faruwa da ni ba. Kinga ko sanda Babanmu ya rasu banda wani cikakken hankalin daya kamata irin hakan yaban tsoro. Tunda shima har aka binne gawarsa yana a yanayin zubar jini saboda accident. Mamanmu kuma bamma san rasuwarta ba sam, tunda ban wuci 3years ba kwata-kwata. Haka dai da ƙyar na cigaba da riƙe kaina mukabi ayarin ƴan ganin cikin companyn. Ya haɗu matuƙa gaya. Ga wasu manyan machines a wani ƙaton hall da baida iyaka. Da alama daga nan za’a dinga ƙera motocin ko haɗa su ne ma oho musu. Bayan nan akwai wajaje daban-daban masu ɗauke da abubuwa kala-kala da bamusan na miye ba, duk da wani bature a cikin abokan nasa sunata ƙoƙarin yin bayani, ni dai ba wani fahimtarsu nake ba sam. Dan duk yanda wajen ya kai ga haɗuwa a yanzu ni sam baya birgeni. Sai ma ganinsa nake baƙiƙƙirin da duhu. An ɗauki kusan mintuna talatin a ciki kafin a fito. Ɗayan sashen da ya kasance shine ake fara gani daga titi, wanda an yisane da zallar gilashi aka sake nufa. Anan ne offices ɗin ma’aikatan yake ashe. Tun daga hawan farko har zuwa na biyar sai da muka shishshiga da taimakon lift… Duka offices ɗin sun haɗu, hatta na ƙananun ma’aikata dake a hawan farko ma duk da na haɗaka ne komai tsaf. Amma nasa na matsayin oga kwata-kwata yafi kowanne tsaruwa, dan tamkar ba’a Nigeria kake ba. Daga office ɗin kuma akan iya ganin cikin ƙwaryar Kano da ƙyau ta kowanne ɓangare. Sosai abin akwai ƙayatarwa. Sai dai ni bai ƙayatar dani ba. Dan yanzu baƙiƙƙirin ma nake kallon mai Companyn kamar baƙin maciji. Nan ma an kwashi wasu mintuna kafin a fito. ALLAH ALLAH nake kawai yayi jawabin ƙarshen nan na masa tambayar da zan masa na bar wajen. Amma sai akace abinci za’aci a yanzun, sannan aje salla a dawo a ƙarasa. Kamar zan fasa ihu haka naji, sai dai yaya zanyi. Dole yanda suka tsara haka kowa zai bi. An fara gabatar da abincin a nutse, za kuma azo har inda kake a baka zaɓin abinda kake son ci sannan aje a kawo maka. Koda aka yambayen nikam nace a’a. Dan na ɗau alwashin bazanci kuɗin jinin mutane ba. Wama ya sani ko tsafi yake yi ne. Ai dama al’amarin dukiyar tasa da mamaki, shiyyasama mutane suketa wasi-wasi a kansa. Haba mutumin nan ai yayi ƙarami da tara irin wannan dukiyar haka. Kwata-kwata fa bazai wuce talatin ba. Inma zai haura hakan kaɗanne kuwa. Yo ko iya wannan companyn akace ya mallaka a shekarun nan nasa ai abin ayi wasi-wasi ne balle kuma ace yana da ninkin baninkin hakan har dasu jirage. Jirgi ake magana fa dake tashi sama da ɗaruruwan mutane bawai kwale-kwale na katako da ake tsallaka ruwan ɓagwai ba. Sannan bama ɗaya ba, ba biyu ba fa….
         “Baby!!”.
    Mansoor ya sake katse min tunani, dan yanzu a gefena yake. Firgigit na dawo hankalina. “please be smart mana. Ko so kike abokan tafiyarmu su fahimci wani abu ne?.”
     Kaina na girgiza masa. Cikin dauriya na kalla abincin da ya saka a kawo min. Maimakon naji sha’awar cinsa kodan ƙyawun da yay a cikin ido ga kaza har rabi a ciki sai naji sam baya wani birgeni. A hankali na sauke a jiyar zuciya da ce masa, “Na ƙoshi da abincin nan wlhy. Kayi haƙuri dan ALLAH.”
       Kallona kawai ya tsaya yi, ni kuma na ɗauke idanuna daga sashensa gaba ɗaya. Da ga ƙarshe ma na ɗauka wayata na shiga buga game wai duk dan dai na dawo da hankalina jikina. Sai dai tuni na kasa cigaba da buga game ɗin, na koma kallon mutane a ƙasan ido musamman ma yaronsa da duk wani motsin sa……✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒐𝒖𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏

……..Kusan kowa da ke a wajen abincin yake ci. Amma banda sarki banda gwamna. A kansa idanuna suka sauka shima. Zaune yake ƙafa ɗaya kan ɗaya da takardu a saman cinyarsa yana dubawa. Gefensa baturiyar matar nan ce ke masa magana da nuna masa abinda ke a takardun. Babu komai a gabansa sai bottle ɗin ruwa alamar ba abincin zai ci ba shima. (Jibesa kamar na ƙwarai). Na ayyana a zuciyata cike da taicinsa, ji nake kamar naje na shaƙe mar wuya na kwarara ihu tare shelantama mutane wanene shi. Amma dai na dake. Mansoor ne ya farga da mugun kallon da nake masa, sunana ya kira a hankali. Hakan ya sakani dawowa hayyacina. Ina ɗauke idona daga inda yake kuwa yana ɗagowa shima. Da alama yaji a jikinsa ana kallonsa ne. Harararsa na ɗan yi ta gefen ido na ɗauke kaina gaba ɗaya da ga sashinsa.
        Bayan duk an kammala cin abincin aka fara shirin shiga salla. Akwai ƙaton massalaci a cikin companyn. Ƙasa na maza, upstairs na mata. Sarki ne da kansa yaja sallar. Bayan an idar aka fito domin cigaba da abinda ya tara mutane dan lokacin tashi ya kusa. Zaune nai a massalacin na kasa fita. Sai da Khulsoom tai kirana a waya. Mansoor na samu a ƙofar massalacin tsaye yay shiru alamar yayi zurfi a tunani. Tsayawa nai kawai ina kallonsa, kafin na ƙarasa gabansa naɗan jujjuya hannuna a saitin fuskarsa sannan ya kawo numfashi. Alamar (lafiya?) Na masa da kaina. Ya sake sauke numfashi da sakin murmushi. “Lafiya Lau Babie. Damuwarki ce ta daman. Gaba ɗaya bana jin daɗin yanayin nan da nake ganinki a ciki. Dan ALLAH ki saki jikinki har mubar wajen nan zamu san mafita, kinga lokacin da zakiyi aikin ki ya kusa cika”.
      Kaina na jinjina masa da faɗin, “In sha ALLAH zanyi ƙoƙarin hakan.”
    Cikin gamsuwa ya nunamin hanya alamar muje. Babu musu muka jera har wajen zaman mu. “Cikin ne har yanzu dai?”. Khulsoom ta faɗa dai-dai ina kaiwa zaune. Guntun murmushi na mata ina girgiza kaina. “A’a na tsaya ƙarasa addu’a ne kawai. Ga zaman nan na waje ɗaya baka ɗan motsawa kuma akwai gundira”.
      “Sosai ma kuwa. Bakiji yanda ƙafafuna sukai dayi ba. Amma ai an kusa tashi in sha ALLAH tunda naga ga shi ma yana shirin miƙewa yay jawabin ƙarshe. Sai ki shirya lokacin aikinki yayi”.
    Jinai ƙirjina yay wani kalar harbawa. Har sai da na ambaci hazbinallahu wa-ni’imar wakil sannan na ɗan ji sassauci. Cigaba da ambaton hazbinallah… ɗin nayi, yayinda shi kuma ya fara jawabinsa. Kamar dai ɗazun haka yake faman gwamutsa mana gurɓatacciyar hausarsa da turanci da faransanci. Dan in yay hausar yaji ya kakare sai kawai ya kwakuso turanci ya maka abinsa..   
Gaba ɗayanmu ƴan Jaridar da aka bari muka shigo wajen munzo da ga gidaje bai fi takwas ba ne. Dan haka tambayoyin da zamu masan ma daga inda muke zaune ne zamuyi su. Kuma za’ayi ɗaya bayan ɗaya ne. Bayan ya kammala jawabansa ya kawo dubansa garemu. Da yanayin gajiyawa dan hatta muryarsa ta nuna hakan ya furta, “Bismillah zaku iya yin tambayoyinku. Sai dai Please akan abinda ya shafi companyn nan kawai. Bana son wasu silly questions da basu shafi abinda ya taramu anan ɗin ba”.
    Cikin gamsuwa duk suka jinjina masa kai, dan ni dai bakina na taɓe ina mai jan tsuki ciki-ciki da ni kaɗai naji kayana, wannan ma ai rainin hankali ne, yanama mutane magana a gadarance. Wani dattijo ne ya fara miƙewa rigarsa da tambarinsu ya fara tambaya. Idanu ya zuba masa tamkar bazaice komai ba, harma kowa yay tunanin ko bazai amsa bane sai akaga ya ɗan murmusa kaɗan iya lips ɗinsa dake ƴan ficit. Gasu pink sosai dan sun ciza. Sai kuma ya nuna PA ɗinsa dake bayansa alamar shine zai amsa wannan tambayar. Hakan kuwa akai PA ɗin nasa ne ya bada amsar, hakama tambaya ta biyu da ga wasu. Duk yanda naso na motsa nayi tamu tambayar na kasa hakan. Gashi mune kuma ya kamata ace mun ma zama na farko. Ganinfa bani da niyyar tashi kamar ma hankalina baya tare da su dan har ya rage saura ƴam gida ɗaya Khulsoom ta zungureni. Firgigit na dawo hayyacina. Sai dai kafin na tashi ma waɗan can sun tashi. Dole na haƙura har sai da ya amsa tasu sannan na ɗaga hannu da taimakon Khulsoom. Dama ya bani kamar yanda yake bama kowa.
        A hankali na miƙe kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Yanda ya zuba min ido da ma kusan duk jama’ar dake wajen ya sani taune lips ɗina dake cikin face mask da ƙarfin tsiya ina mai karanto hazbinallah wa-ni’imar wakil a zuciyata. Da ƙyar na iya dai-daita numfashina ina mai janye idanuna da suma ke a cikin eyeglasses tare da sauke mask ɗin ƙasan haɓata sannan na furta.
“Sir a matsayinka na matashi da za’a iya shiga mamakin ganin yanda ka gina katafaren kamfani irin wannan da ya zama na farko a Africa, a duniya na uku kuma bama shi kawai ka mallaka ba, akwai wasu manyan cibiyoyi daka kafa a ciki da wajen Africa ma ba Nigeria kawai ba, ko nace duniya, shin ko zaka iya jan hankali matasa irinka dake tasowa dangane da neman na kai da asalin tarihinka dan su san kaima ba daga kwance ka kai wannan matsayin ba, sai da kai aiki tuƙuru, tare da tsallake ƙalubale masu yawan gaske kuma duk kai haƙuri ka jure har gashi a yanzu ka zama wani babban ginshiƙi tauraron duniya dake haska yankinsa da ƙasarsa, yarensa harma da addininsa?”.
           Bashi da naima tambayar ba, hatta sauran ƴan jarida ƴan uwana dama duk jama’ar dake wajen sai da suka zuba min ido, harma da masu hangame bakuna sama. Bama sai sun faɗi abinda ya basu mamaki ba, ni na sani. Yace kar a masa tambaya sai akan abinda ya shafi company, sannan tambaya ɗaya kacal zakayi. Amma ni dana tashi na haɗa kusan tambaya goma ne a cikin ɗaya, na kuma yi tambaya akan kamfani kawai da ya buƙata amma na saka abinda yake gudun a tambayesa ta yanda dolene sai ya amsa min ɗin. Yaja kusan mintuna biyu cif yana kallona kawai cikin wani irin yanayi, sai yatsun hannunsa daya dafe dogon tables ɗin da aka cika da mic.. yake ta motsawa, musamman biyun tsakkiya. PA ɗinsa ne ya ɗan yunƙuro amma sai ya ɗaga masa hannu alamar ya dakata. Tsayawar yayi, sai dai shima wani mugun kallo yake jefamin fiyema dana uban gidan nasa. Oho ko’a jikina, ni dai tunda nayi tambaya ta ai shikenan, amsa kawai nake buƙata. Motsawarsa da sakin wani shegen makirin murmushinsa ya saka kowa sake maida hankali kansa. Murmushin ya sake saki yana ɗan cizar lip ɗinsa na ƙasa. Yay wani ɗan diri-diri kamar wanda ya rasa abin faɗa sai kuma ya nuna ni yana sake sakin wani lalataccen murmushin. A hankali ya furta, “Hmmm you are very smart girl. A karo na farko na yarda zan bada wannan amsar, amma ba yau ba, ba kuma anan ba saboda munada ƙarancin lokacin hakan.”
       Wani ƙwarin gwiwa ne naji ya sake zomin. Kai na tsaye na ce, “Thanks you sir. Amma taya zan sake samun wannan damar kamar haka ku da ganinku ba wasan yara bane. Gashi kuma ina matuƙar son gamsar da ƴan uwana matasa da sake farkar da waɗanda suka shagala. Zan so ace na samu date da time tun anan tare da location kodan ni da ƴan uwana matasa mu kasance a cikin shirin ji da ga bakin gwarzon mutum irinka”.
         Ai da ƙarfi yanzu kam ya cije lips ɗinsa, yana wani kalar tsatstsareni da kaifafan idanunsa, dan duk da a cikin eyeglasses suke dolene ka fahimci hakan musamman yanda kai tsaye direction ɗinsa yake gareni. PA ɗinsa ne ya ɗan matso ya masa maganar da shi kaɗai ya ji abinsa. Yana gama faɗa masa ya ɗan ja baya kaɗan shi kuma ya juyo gareni. A bazata ga kowa ya furta, “Na baki dama, kisa date, kisa time ki faɗi location koda a office ɗin ku ne”.
       Kutumelacy, ai jina ƙafafuna na neman gagara ɗaukata. Yayinda gaba ɗaya wajen yay wani irin ɗaukar shiru duk aka zuba masa idanun mamaki. Dan abune da bai taɓa faruwa ba. Maash a gidan tv ko jarida ko rediyo ko mujalla ana masa tambaya akan tarihinsa ba harkar business ba yana bada amsa. Abin mamaki. In taƙaice muku har taron nan ya tashi ban dawo dai-dai ba. Dan duk da hakan shine burina a kwanakin nan, sai nake jin kamar bazai yiwu ba. Koda yake hatta a ƙiyamullaili ɗina na satin nan sai da naita saka addu’ar fatan ALLAH ya ɗorani a kansa banyi zaton zan samu damar ba sam, kuma a cikin sauƙi ma haka. Hummm al’amarin da ban mamaki kam….

            Kasancewar duk abinda ake a office ɗin mu suna kallo ne live dama mutane wata kalar gagarumar tarba muka samu. Musamman ma ni. Dan mata-matan staffs ɗin nan namu rungumeni suka dinga yi da kwarzanta ƙoƙarina. MD kam bakinsa tamkar zai yage ne. Wannan abin alfaharine a garesa ace mutum kamar Maash ya amsa gayyata da ga gidan tvn sa a gaɓar da kowa ke matuƙar buƙatar hakan. Oho su suke shirmensu ni nawa hankalin ma ba’a kansu yake ba. Maganar kisan can ne yay matuƙar tsaya mun a rai da zuciya. A dalilin sallar la’asar na samu damar zame musu. Dan bamu tsaya munyi acan ba kasancewar an tashi gab da za’a fara kiran salla. Ana idar da salla na MD yace muje gida mu huta. Haka dama nake buƙata. Dan burina kawai na keɓe da Mansoor na ji yaya za’ayi da batun video dake a cikin wayata. Muna barin office ɗin kam zancen dana fara masa kenan. Shima da alama abinda ke cimasa rai kenan. Dan haka muka shiga tattaunawa. Koda ya isa dani ƙofar gida ma ban fita a motar ba. Zancen muka cigaba da yi. Ni dai ina a matsayar mu kaima hukuma video ɗin. Tunda dai duk hanyar da zasu bibiyi batun gawar zai zama mai sauƙi kasancewar ya faɗi inda za’a kaita. Amma sai Mansoor ya ce nadai bashi dama yayi nazari tukunna. Na kuma tura masa video ɗin. Babu musu na tura masa, nima na adana wanda ke wayar tawa da ƙyau duk da babu wanda ke taɓamin waya ma. Daga haka mukai sallama ya wuce ni kuma na shiga gida. Dan Yaya Musaddiq na wajen aiki……..✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑭𝒊𝒇𝒕𝒆𝒆𝒏

……..Daga ajiye Samraah gida ya wuce shima. Sama-sama ya amsa gaisuwar maigadin su ya shige ciki. Shi da ɗan uwansa a duk sanda suka dawo gida idan sun fita sukan fara shiga sashen iyayensu ne, musamman ma shi da akance yanada ƙulafucin uwa. Amma yau sai hakan ya gagara garesa. Dan ko motar tasa yau a gab da sashensu ya ajiyeta. A falo ya samu yayansa kwance cikin kujera yana kallo, hannu kawai ya ɗaga masa nan ma yay shigewarsa ɗakin barcinsa. Da kallon mamaki Attahir ya bisa. Dan abune da bai saba gani ba. Amma sai ya ɗan girgiza kai da sake maida kansa ga tvn da yake kallo, zuciyarsa na ayyana masa maybe ya gaji ne. Ya cigaba da kallonsa da tunanin idan yay wanka ai zai fito ya nema abinci, amma shiru kake ji har magrib na neman yi. Tsam ya miƙe ya nufin ɗakin nasa, ya ɗanyi knocking, kafin ma a amsa masa ya tura ya shiga.
A tsaye ya samu Mansoor na faman kai kawo. Yay masa kallon tsaf sannan ya ce, “Kai wai lafiyarka ka kuwa? Ka dawo ma mutane kana ɗacin rai ka kuma shigo ka rufe kanka a ɗaki. Ko har ka fara tunanin auren ne? To bakai kace kana so ba, kama jirani kayi tsalle ka dire kai ba haka ba…..”
Ganin Mansoor bai maida masa murtanin tsokanar ba yasa Attahir yin shiru, gabansa ya ƙarasa tare da dafa kafaɗarsa. Cike da kulawa ya ce, “Baka da lafiya ne Kiddo?”.
Kai Mansoor ya girgiza masa.
“To mike damunka?”.
“Yaya babu komai fa. Kawai bana jin daɗine”.
Jimm Attahir ɗin yay yana kallonsa. Sai kuma ya jinjina kansa da faɗin, “Okay shike nan. Shiga bayi kai alwala mu wuce massalaci. Dan kar Dad yay zaman jiranmu”.
Kai kawai Mansoor ɗin ya jinjina masa yana nufar bayi. Attahir ya bisa da kallo har sai da ya shige. Shima kaɗa kansa yay ya fita yana ji a ransa ƙarya Mansoor ɗin ke masa. Duk da shi mutumin ne mara son hayaniya. Amma idan suna tare baka banbance wannan halin nasa na rashin yawan magana. Dan suna rayuwa ne tamkar abokai ba wa da ƙani ba. Sun tashi ne kamar ƴan biyu, komai nasu a tare yake. A halayyane kawai zaka iya banbance su. Dan tabbas sun banbanta tanan ɗin.

 Koda suka fito domin tafiya massalacin sun gamu da Dad ɗin su. Shima dai da mamaki yake kallon Mansoor ɗin. Harma ya gagara haƙuri ya ce, “Kai dama ka dawo gidan kabar Mamanku natama mutane shelarka?”.
    Kan Mansoor a rissine ya ce, “Dad amin afuwa na dawo ne kaina namun ciwo”.
“Dole kai ciwon kai ai wannan hidima da kuka sha. Ku muje massalaci za'a tada salla”.
Binsa sukai gwanin sha'awa suka fita har maigadi. Koda aka idar da sallar ma basu fito a massalacin ba har akai isha'i. A tare yanzu ma suka dawo gidan, kai tsaye ainahin sashen gidan suka nufa su duka. Sashene babba kuma mai ƙyau, dan komai yaji na ababen more rayuwa. Lallai gidan su Mansoor suna da kuɗi suma ba laifi. Dan idan wani ne ma zai iya cewa yafi ƙarfin aikin da yake yanzu, duk da kuwa yana a babbar kujera ne. Amma kuma aikin jarida hubby ɗinsa ne tun yana yaronsa. Sannan mahaifinsa nada babbar alaƙa ma da wajen aikin nasu, dan yanada hannun jari mai ƙarfi a cikin companyn. Shigowarsu dai-dai da fitowar ƴammata biyu masu kama da su Mansoor ɗin sosai daga wani ɗaki. Cike da murnarsu suka nufo Mansoor ɗin suna masa sannu, sai jera masa tambaya suke akan Maash. Amma a mamakin kowa ko a yaƙi ya furta, sai ma zagayesu yay ya wuce saman kujera ya zauna yana faɗin, “Malami kun isheni da surutu”.
 Babbar ce ta ɓata fuska tana kallon Dad ɗin su. Ya ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar sunfi kusa. Sake ɓata fuska tai sosai. Ta ce, “Dad kallafa yanda yake basar da mu. Shi dama Yaya Man idan baiso abu ba ya iyama mutane wulakanci”.
“To yayi fitinanniya.”

Wata mata dattijuwa ta faɗa tana fitowa a hanyar dake tabbatar da kitchen ne, itama dai kama take sosai da su Mansoor ɗin. Hararar yarinyar tai da nuna musu hanyar data fito. “Ku wuce kuzo ku fiddo abinci. An gaya muku kowama irinku ne da shegen surutu. Yaro yaje aiki ya gaji kun wani sashi gaba dolene sai ya baku labarin abinda ya farun? Idan son gani kuke miya hanaku zuwa”.
“To an taɓa ɗan lelen Mamy”.
Cewar Attahir na ƴar dariya. Murmushi Dad shima yayi, yayinda Mansoor ya miƙe ya nufeta yana harar Yayan nasa. Yana zuwa gab da ita ya bata side hug, tare da kamo hannunta ya sumbata. A marairaice ya ce, “Mamy barsu kada ma kanki yay ciwo”.
Kansa ta shafa fuskarta da murmushi. Kafin cikin kulawa ta ce, “Yaushe ka dawo?”.
“Tun ɗazun ya dawo yau baya yayinki ne kawai Mamy”.
Attahir ne ya faɗa yana kaiwa zaune a kujerar dining dan su Islam sun kammala jera abincin. Hararsa Mansoor yayi, tare da faɗin, “Mamy ƙyalesa so yake kawai ya haɗamu. Kaina fa ke ciwo amma nasha magani”. Yay saurin faɗar haka ne dan yasan yanzu zata iya ruɗewa. A hakanma tuni fuskarta ta nuna damuwa. Dan sai tattaɓa kan nasa take, daga ƙarshe dai ta ja hannunsa suka koma saman dining ɗin tana jera masa sannu, abincin ma a baki ta bashi dan kowa yasan ɗan gatan ta ne a gidan. Daurewa yay kawai ya ɗan ci abincin dan karta damu, amma gaba ɗaya hankalinsa na’a kan Samraah, babu abinda zuciyarsa ke hango masa sai yanda take a firgice har sanda ya ajiyeta a gida…..

 Bayan sun kammala cin abinci duk yanda Mamy taso suyi hira Mansoor bai cewa komai, zata nuna damuwa Dad ya dakatar da ita akan ta barsa yaje ya huta dole akwai gajiya. Mansoor yaji daɗin samun wannan damar, dan haka ya miƙe ya wuce sashensu. Yana shiga bedroom ɗinsa wayar Samraah yay ƙoƙarin kira. Cikin sa'a kuwa bugu uku ta ɗaga. Sai dai a yanda yaji muryarta na fita a shaƙe ya tabbatar har yanzu tana a cikin damuwa. Daɗaɗan kalamai ya shiga jera mata da lallashi akan ta kwantar da hankalinta. Ba shi yace mata zasuyi wani abu ba. Bafa itace ta aikata laifin nan ba da har zata takurama ranta haka suma dake tare da ita ta sakasu a damuwa. Sosai lallashin nasa yay mata tasiri, dan haka ya yanke kiran yana cewa bari yay shirin barci zai kirata video call. Yana yanke wayar Attahir na shigowa ɗakin, yanda ya kafesa da ido ya sashi duƙar da kansa, fatansa dai ALLAH yasa baiji wayar da sukai da Samraah ɗin ba.
  “Mike damunka Mansoor?”.

“Yaya nace maka babu komai”.
“Ƙarya kake yi. Idan kuma zakama kowa wannan ƙaryar ni kasan bazaka mun ba. Dan nasanka fiye da yunwar cikina. Koka sanar min, ko yanzun nan naje na kira maka Mamy da Dad maybe su ka sanar musu”. Ya ƙare maganar da juyawa kamar zai fita. Da sauri Mansoor ya riƙosa yana girgiza kansa. “Please basai ka kirasu ba. Ba wata damuwa bace mai yawa fa”.
“Kasan dai bama ɓoyema juna damuwarmu. Karka fara daga yau to”.
Numfashi mai nauyi Mansoor ya sauke tare da ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana harhaɗo ƙaryar dazai sanar masa dan bazai taɓa faɗa masa gaskiyar zancen ba tunda yayima Samraah alƙawarin haka…..

        ★💫★💫★💫★💫

          “Sir dan ALLAH kada ka saka kanka a damuwa. In dai batun yarinyar nan ne dai-dai yake da kaɗawar iska mai wucewa. Ita ta isa ta saka abinda bakayi niyya ba. Waye ubanta a ƙasar nan? Har micece ita a aikin jaridar ma. Yarinya ce fa ƙarama fitik”.
       Idanunsa dake lumshe ya buɗe a hankali. PA ɗin nasa dake magana ya zubama su kusan sakan arba’in. Sai kuma ya sake maidasu ya lumshe a kasalance. Dai-dai nan drivern sa yay sallama a ƙofar katafaren falon. PA ɗinsa ne ya amsa. Sai kuma ya bashi umarnin ya shigo dan yasan kayan boss ɗin nasu ne dake a mota ya kawo. Cike da tsantsar girmamawa yaje Centre table ɗin gabansa kuwa ya ajiye. Sai kuma yay ɗan jimm a duƙe kafin ya ɗago yana nuna wata jaka. “Sir wannan wani mutum ne yanzu nan ya kawo wai a baka. Naso ƙin yin hakan amma kausasan kalamansa suka daƙileni. Dan ya tabbatar min ƙin baka ɗin zai zama kuskuren da bazan yafema kaina ba kaima kuma bazaka yafe min ba. Dan saƙon nada amfanin da idan na wofamtar da shi dai-dai yake da gina harsashin tarwatsaka. Amin afuwa shine ya faɗi hakan”.
       A zabire PA ɗinsa ya furta,  “What! Wane ɗan iska ne haka. Su securitys ɗin gate kuma suna aikin mi ya shigo cikin gidan nan, kai kuma ka zauna sauraren wawancinsa, are you mad?”.
       Shiko gogan ko motsi baiyi ba. Sai idanunsa da ya ɗan buɗe kaɗan a ƙasa-ƙasa yake kallon drivern nashi da su. PA zai sake magana ya masa alamar ya barsa. Hakan yasa driver tashi da sauri ya fita ya bar saƙon da aka nannaɗe a cikin leda mai ƙyalli. Sake maida idanunsa yay ya lumshe kawai. PA da hankalinsa gaba ɗaya ke’a kan saƙon sam ya kasa nutsuwa, ganin ogan nasa baida alamar bashi umarnin ya buɗe suka miye a ciki ya furta, “Sir ya kamata musan minene a ciki. Dan bamu san mi mai saƙon ya taka ba har yake irin waɗan nan kalaman.” shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma ya kaɗa masa kai alamar ya buɗe ɗin. Jikin PA har rawa yake wajen ɗaukar saƙon. Kamar ƙyaftawar ido ya gama buɗesa ledar da aka nannaɗe sa. Sai dai kafin ya ciro abinda ke’a cikin kwalin da aka naɗe ɗin text message ya shigo wayarsa. Kasancewar wayar mai muhimmanci ce dan ta business ce ya ɗauka dan ya duba saboda akwai saƙon da dama suke tsammani. Rubutu ne da bai wuce words ɗari ba. Dan haka ya fara karantowa.
           Sosai jikin Hayatu PA ke rawa yana mai ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihiraji’un. Sir tabbas hasashenka ya zama gaskiya. A kwai wanda ya gammu, kuma tabbas shine mai face mask ɗin nan. Dan gashi anan ya turo saƙo?”.
Idanunsa ya ɗan buɗe batare daya tanka ba yay masa alamar miya faru?. Cikin rawar jiki Hayatu ya fara karanto saƙon a fili kamar haka………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒊𝒙𝒕𝒆𝒆𝒏

……..Barkan ka madubin wannan ƙarni. Ba sai na cikaka da gaisuwa ba, bari na tafi kai tsaye kawai. Ina buƙatar naira miliyan ɗari biyar daga gareka. Kuma cikin gaggawa. Idan ba hakaba, a daren yau zan rusa duk wani tanadinka da tunƙahonka da videon dake hannuna ta hanyar yaɗashi a social media. Kasan dai kisan kai ba abune mai sauƙi ba. Musamman ga mutum irinka sananne mai tarin magauta da masoya tako ina. Na baka awa arba’in da takwas. Idan kunne ya ji jiki ya tsira.

         Ya jima bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kwance jikin kujerar kansa a sama kaɗan. Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima ji ko fahimtar abinda PA ɗin nasa ya karanto masa bane ba sam. Yaja kusan minti uku PA nata kai kawo kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau, sai dai a nutsensa yake abin mamaki. Goran ruwa dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa. Sai da ya shanyesa tas sannan ya jefar da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na biyu yana sake nutsar da kansa, sai kuma kamar wanda ya tuna ya dubi PA ɗinsa. “Ina buƙatar duka cctv footage na company a daren nan?”.
      Cak Hayatu ya tsaya da ga kai-kawon da yake, sai kuma jiki a sanyaye ya ce, “Sir ka manta mun duba sanda muka shiga kafin faruwar abun amma basayi duk an kashesu”.
         “Hakane, amma kamar na kunna ukun farkon nan.”
      “Yes yes tabbas kuma hakane fa Sir. Wlhy sai yanzu na tuna. Aiko ko wanene wannan zaici ubansa.” baima jira umarnin ogan nasa ba ya fice da sassarfa tamkar zai kifa ƙasa duk kuwa da dare ne a lokacin. Dan kusan sha ɗaya ma ake nema, saboda bayan an tashi a taron company sun bu sarkine kamar yanda ya buƙa. Bayan sallar magrib suka bar gidan sarki, maimakon gida suka wuce wajen wani abokin harƙallarsa dan haɗuwar ta sirrice, sai goma saura suka nufo gida. Gashi yanzu ana harar sha ɗaya da wasu mintuna.

        Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga falon ya nufi bedroom ɗinsa. Tamkar mai hasashen ganin wani abu sai da ya gama kalle kowacce kusurwa da lungu da saƙon na ɗakin sannan ya kai zaune a bakin katafaren lafiyayyen gadon. Sabon gida ne fil dan yau ne ya fara shigarsa. Anyi aikin gininsa tare da Companyn nasa ne. Bai cika son zaman hotels ba a rayuwarsa sai in har ya zama tilas a garesa. Ta wani ɓangaren kuma gorin mutane akan kullum yana cika bakin shi ɗan Kano ne amma ko gida baida a arewa ma gaba ɗaya ya sashi ginin wannan gidan da ko makaho ya laluba yasan an kashe kuɗi. Dan yanda companyn ya haɗu shima gidan haka ya haɗu matuƙa.
         Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane. Abubuwane kawai suke masa kai-kawo a rai da suka faru a wannan yinin. Kallon komai yake tamkar wani film ba zahiri ba. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba. Amma na yau ɗin na musamman ne. Dan duk sunzo masa a bazata. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan. Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba?. Amma dai bari ya jira P.A ɗinsa da sakamakon da yake buƙatar gani kafin ya tsara komai akan mizaninsa. Da ga haka ya miƙe yana mai fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka…

        Yaja tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe ash color sabuwa dal. Dan yanda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan. Ƙaramin towel da a hannunsa ya kai kan jiƙaƙƙiyar sumar kansa mai tsaho data kwanto masa a fuska sosai, hakama ta bayansa kai kace bai haɗa jini da babaƙen fata ba balle ma har a kirashi da suna bahaushe. Tamkar ba shi kaɗaine a ɗakin ba. Fuskar nan a tsuke babu alamun rahama a cikinta. Duk da tun fitowarsa wayarsa ke tsuwwa alamar kira na shigowa, yay biris da ita tamkar bai ji ba. Sai ma ƙoƙarin nufar ƙaton mirrorn dake a ɗakin yayi abinsa. Tuni Hayatu ya shirya masa kayan shafe-shafensa a mirrorn, dan zaiyi kamar 1week ne a cikin Kanon kamar yanda yake fata. Hand dryer da aka ajiye a saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, sumar tasa ya fara busarwa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya kammala gyarata alamar ya riga ya saba da hakan. Kafin ya ɗan shafa mansa sama-sama tare da sprays masu shegen ƙamshi kala har biyu sannan ya nufi doguwar wadrobe data cinye bango guda. Ta farko kawai ya buɗe, anan ko yaga kaya kusan kala goma duk ƙananu, sai ƴar akwatin da yazo da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen ƙyau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da ƙamshinsu ba’a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko ƙaƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaɗaice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai ɗaga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai ɗaga ɗin ba to ka haƙura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka ɗauka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riƙewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya ƙarasa in da ya yasar da wayar, cikin ƙara ɗaure fuska ya ɗauka dan yana son ta barsa. A daƙile ya kai wayar kunensa sai dai yaƙi cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanks”. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barci”. Daga haka ya yanke kiran gaba ɗaya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai ƙarfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu’oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin…..

     ●´⌓●●´⌓●●´⌓`●

           Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa.
“Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haƙuri Yaya ne ya ɗauke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai haka”.
     Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawai”.
              “Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki ƙyau ba dan baki iya ƙaryarba tunda ga harshenki yana rawa”.
     Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faɗin, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?”.
        “Saboda mahaɗin zuciyata batayi ba”.
       “Humm”. Na faɗa kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun ɗan yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin ɗan uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?”.
      “A’a”.
   “Miyasa?”.
“Kawai dai”.
“Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya ɓoyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya ƙaremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yake”.
       “Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaƙi ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miƙawa ai”.
     “Baƙi naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a ƙasar nan. Yanzu koda mun miƙa video ɗin nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a ƙasar nan tamu KUƊI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da ƙasashen masu jajayen kunnuwan yanada ƙarfin faɗa aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a ƙasarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama ƙafar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuɗi. Kiyi haƙuri dai mu nema mafita mai ɓullewa. Mu kuma samu jajirtaccen ɗan sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuɗi sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu ƙyalesa ba sai an ƙwatoma mutumin nan hakkinsa”.
        “ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.”
     “Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haɗu acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za’ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Monday”.
      Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri……..✍️
      

Tofa masu karatu yanzunne fa ainahin wasan zai fara. Dan da alama mun gama sharar fage zamu tafi mataki na biyu a labarin. Wa kuke tunanin ya rubuta saƙon nan? Sannan karku manta a cctv footage fa Samraah za’a gani. Shin ko itace dai ta rubuta saƙon? Ko kuma wani yaji sanda take faɗama Mansoor yay amfani da damar? Ko kuwa ba ita kaɗaice ta gani ba? Shin minene dalilin Maash nayin kisan nan ma wai? Wanene aka kashe?….. Kai kai kai cakwakiya ce fa iya cakwakiya a labarin nan. Amma dai ina son jin amsoshinku a comment section. Yau har masu laɓe su fito inba haka ba gobe babu posting sai bayan salla🚴🚴🚴.

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑺𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏

…….WASHE GARI kamar yanda na saba na tashi nai ayyukana da sauri-sauri. Ana idar da sallar asuba nai wanka. Breakfast ɗin Yaya Musaddiq na ɗauka na nufi kai masa kusan bakwai da rabi. Nako samu har ya kammala shiryawa. Tunda na shigo yake bina da kallo, basai nace komai ba nasan ya gama fahimtar yanayina ne. Amma sai na dake. Sai dai ina gaishesa maimakon amsa min tambaya ya jeho min. Baki na buɗe zance babu komai yay saurin ɗaga min hannu da faɗin, “Karma kimun ƙarya. Faɗamin mike damunki?”.
      A hankali hawayen da nake riƙewa suka silalo. Nima babu shiri na silale ƙasa ina mai fashewa da kuka. Duk abinda ke a raina tun jiya ne ya samu damar fitowa. Kafin ma ya sake cewa da ni komai na shiga faɗin, “Yaya kisan kai yayi. Da idona na gansa yana zare wuƙa a jikin mutumin ga jini face-face. A kunnena naji yana faɗin akai gawar wani anguwa a ajiyeta…..”
          A cikin matuƙar tashin hankali ya katseni jikinsa na rawa. “Waye wai? Ki min magana a buɗe Samraah Please wa aka kashe waye kuma yay kisan?”.
    Maimakon bashi amsa sai na miƙa masa wayata kawai. Amsa yay da rawar jiki. Yana ko dannawa da video ɗin ya fara cin karo dan ni bana sakama waya password sam. A matuƙar birkice ya ɗago yana kallona tun a fara kallon video ɗin. Idanunsa a warwaje na shiga razana ya furta, “Samraah Maash fa?”.
      Kaina na jinjina masa da sauri ina faɗin, “Shi yaya! shi! Mutumin nan azzalumi ne bana kirki bane kamar yanda duniya ke kallonsa. Zata iya yiwuwa ma kuɗin nasa bana ALLAH bane na jinin mutane ne”.
     Tuni zufa ta wanke Yaya Musaddiq. Cikin tashin hankali ya ce, “Bayan ni wa kika faɗamawa?”.
          “Mansoor ne kawai Yaya. Tun jiya nace mu kai ma hukuma video ɗin amma ya hana. Shine ma yace na baka ka gani dan mu haɗu da shi a gareji mu tattauna”.
     “Gara daya hanaki Samraah. Dan dole wannan al’amarin na buƙatar nazari. Maash ba anyhow mutum bane da dokar hukuma zatayi tasiri akansa cikin sauri. Inaga yanzu ba zama zamuyi ba tashi mu wuce. Bara na kira Mansoor ɗin ya fito shima gara muyi abinda ya dace da wuri tun kafin ya bar garin nan. Dan bai zama lallai a sake samun irin wannan damar ba duk da naji ya amsa miki wai kiyi hira da shi. Ga gari nan duk ya ɗauki zance harda masu faɗin ba haka kawai kikaje masa ba akwai asiri saboda yanda ya amsa ɗin babu musu a gaban duniya. Amma ni zuwa yanzu na fara zargin akwai wata a ƙasa kam, bana raba ɗayan biyu ya ganki sanda kike ɗaukar video ɗin nan, ko kuma ta cctv, dan Company kamar nasa dole asamu camaras tako ina”.
        Idanu na waro sosai na matuƙar mamaki, Yaya Musaddiq ya jinjina min kai alamar tabbatarwa. “Samraah duk mai hankali dolene ya gane akwai dalilin Maash na amsa miki gayyatar da kikai masa cikin sauƙi. Dan bazai taɓa zama ya amsa miki bane kawai saboda kin jera masa tambayoyi. Kai ina dolene ma ya ganki fa, ya barki ne kawai bisa dalilinsa, sannan yazo a bainar jama’a ya amsa zaiyi hira dake, hakan na nufin akwai wani abu da yake ƙullawa”.
         Sosai na zubama Yaya Musaddiq ido, dan tabbas zancensa yasa na fara dawowa cikin hankalina yanda ya kamata. (Humm you are vary smart girl) kalmar daya fara ambata a kaina kenan. Tabbas wannan mutumin terror ne na gasken-gaske. Shin mi yake ƙullawa? Dan dolen dole akwai abinda ke ransa kamar yanda Yaya Musaddiq ya faɗa. Kai ina buƙatar ganin ma program ɗin jiya gaskiya…..
    “Kinga tashi muje, ba lokacin tunani bane yanzun”. Yaya Musaddiq ya faɗa cikin katse mun tunani. Miƙewa nai babu musu, dan basai na koma cikin gida ba dama….

       🤙❤️🤙❤️🤙❤️

   A ɓangaren Maash asubar fari ya farka, da ƙyar ya iya tashi saboda gaɓɓansa duk ciwo suke masa. Ruwa ya fara watsawa ya fito a gurguje ya kimtsa cikin wando da rigar polo. Koda ya fito su Hayatu suma har sun fito zasu wuce massalacin. A tare suka fita, bayan an idar da salla bai koma cikin gidan ba yace ma Tijjani ya fito da mota zasu je wani waje. Da sauri Tijjani ya shiga ciki, babu jimawa ya fito da mota, suma guards ɗinsa suka fito. Komai baice ba Hayatu ya buɗe masa baya ga shiga, shi kuma ya shiga gaba kusa da Tijjani. Jihar Jigawa suka nufa, a wani ƙauye dan akwai business ɗin da zai yi a wajen. Duk da dai da farko bai wani ɗauki abin da muhimmanci ba, sai da zasu je massalacin nan ne Hayatu ke sanar masa mutumin da zasuyi kasuwancin ya kira, kuma yana son suje da wuri ne.
       Yinin ranar guda a Jigawa suka cinyesa. Ko abinci bai sakama cikinsa ba garama su su Hayatun. Sai Black tea kawai yake faman sha kasancewar duk inda yake yana tare da flaks ɗin ruwan zafinsa a mota, sai kuma chocolate dan mayenta ne da haɗaɗɗun biscuits. Sai bayan la’asar suka dawo cikin Kano a matuƙar gajiye. Musamman ma shi duk da dai yaci chocolate sosai amma yana buƙatar dafaffen abinci, dan rabonsa da dafaffen abinci sosai tun shekaran jiya a Lagos. Ko zama a falon baiyi ba ya wuce bedroom, suma dai su Hayatun duk a gajiye suke, dan haka kowa ya nufi sashensa danya watsa ruwa. Bathtub ya cika ra ruwan ɗumi sosai sannan ya shiga ciki, sai da yaji ko inansa ya miƙe sannan ya ɗauraye jikinsa ya fita. Duk yau sau ɗaya kawai yay waya da Ummien sa. Ji yake duk kewarta ta damesa. Sai dai yanzu yasan koya kira bazai samu ba dan ba lokacin kira bane dan sallar magrib aketa kira. Shiri yay tsaf cikin kaya marasa nauyi. Ya baɗe jikinsa da turare sannan ya saka slippers da ke ajiye yay ficewarsa.
       Tun kafin ya ƙarasa fitowa cikin falon Hayatu dake zaune yana jiran fitowarsa ya miƙe da sauri. Dan tun ɗazun ya dawo daga wanka da yaje yayo shima a sashensa. Ya dawo ne da wuri akan batun cctv footage na jiya, dan yana ganin ya kamata su duba issue ɗin kar a samu matsala. Kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kansa, sai kuma ya nufi ƙofa a taƙaice ya ce, “Kayi alwala”.
       Cikin girmamawa Hayatu ya amsa da “Okay Sir”. Sai kuma ya saki murmushi yana mai binsa da kallo. A duniya boss ɗinsa da banne. Mutum ne mai abubuwan ban mamaki daban-daban. Ba kuma zaka tabbatar da hakan ba sai ka kasance a makusancinsa. ALLAH ya azurtashi da ni’imomi da yawa a rayuwa. Gadai ƙyawu kamar shine ya zana kansa. Ga dukiya, ga ilimin addini dana zamani. Yanada ƙyauta ga duk wanda ke tare da shi. Sai dai kuma hatsabibin kansa ne baifa mutunci a wasu fannin. Dan wani irin mutum ne a hagungunce da zaka iya ɗaukar lokaci baka fahimci alƙiblarsa ba. Ga taurin kam masifa da baƙar zuciya. Baya ragi ko ragowa ga duk ubanda yace masa kule. Yakan karya yatsar duk wanda ya nunashi dan baya ƙaunar raini. Shifa ko’akan business ana lallaɓa abokan harƙalla dan su dawo shi a garesa bai san wannan ba. Kana kawo masa hauka zai cireka a sabgarsa kawai. Sai dai baka isa tabbatar da waɗan nan halayyar tasa ba kai tsaye sai ka shigo gonarsa. Dan sumumu kasaune shi MACIJIN SARI KA NOƘE. A zahirinsa zaka ɗauka mutum ne mai sanyi da nuna halin ko’in kula, sai dai a kowanne motsi na cikin rayuwarsa a ankare yake. Domin indai brain ce ALLAH ya bashi. Irinsu ne ke juya akalar abubuwa a ƙanƙanin lokaci da kwanyarsu…..
        Firgigit ya dawo hayyacinsa jin kiran sallah. Da sauri ya shiga toilet ɗin falon ya ɗauro alwala ya wuce masallacin shima…

      Bayan idar da sallar isha’i suka shigo gidan. Sai dai Hayatu da Tijjani drivern sa sun rigashi shigowa. Dan su duka suna a gidan har baturiyar nan. Sai dai kowannensu yana a mabanbancin masauki da sai in shine ya buƙaci ganinsu zasu ganshin. Kusan mintuna goma suna a ƙaton compound ɗin gidan da ga jikin motoci suna hira sai gashi ya shigo shima. Ya ɗan dakata yay magana da masu gadi da suka kasance ƴan sanda har su uku sannan ya ƙaraso inda suke. Duk nutsuwa sukai kawunansu a ƙasa, baice da su komai ba ya wuce inda lafiyayyar ƙofar shiga sashensa take. Dan ta gilashi ce mai tsananin ƙyau da ɗaukar idon mai kallo. Gata golden daga waje sai walwali take kamar wani zinaren gaskiya. Da sauri Hayatu dake biye da shi ya buɗe masa ƙofar. Harararsa ya ɗan yi, Hayatu ɗin ya duƙar da kai ƙasa yana murmushi dan yasan laifinsa akan buɗe ƙofar ne tunda yana hanasu. Har ya shiga ya ɗan waiwayo. Driver dake ƙoƙarin komawa da baya ya dakatar ta hanyar faɗin, “Tijjani!”.
     Da sauri Tijjani ya amsa masa da “Na’am ranka ya daɗe”.
    Komai bai sake cewa ba ya cigaba da tafiyarsa ciki. Dan haka duk suka bisa. Duk da garin ba zafi ake ba, ba kuma sanyi ne mai tsanani ba dan ya fara bankwana falon a ƙanƙare yake da sanyin raɓar ac. Ga wani ƙamshi na musamman daya gaurayu da turarensa tamkar ba a jiya ne ya fara rayuwar cikin gidan ba. Zaune ya kai saman 3sitter. Kamar yanda ya saba zaman ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yanzun ma hakan yayi. Shiru kamar mai nazarin wani abu sai kuma ya ɗago yana ma Hayatu nuni da remote dake a Centre table. Remote ɗin Hayatu ya ɗauka da sauri, dan ko ogansa bai magana ba yana saurin gane karatun shirunsa saboda da hakan ya horesu tun farko. Dan shi bamai yawan magana bane sai idan shine yaso hakan da kansa. Sai kuma idan yana a gaban mahaifiyarsa ko mahaifinsa, shima a wasu lokutan ne yake hakan, sai ko Ammie. Volume ɗin tvn ya sassauta tare da canja tasha zuwa inda yasan yafi yawan kallo a irin wannan lokacin. Tasha ce ta addini, sai dai suna gabatar da duka programs ɗin su ne da turanci, hatta da wa’azi kuwa……..✍️
        

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏

…….Gyaran murya ya ɗan yi idonsa akan Tijjani. Cikin sauri Tijjani da idonsa ke akan tv ya maido hankalinsa garesa. Kafin ma yace wani abu cikin muryar nan tashi kamar ta rowa ya taresa da faɗin, “Ina za’a samu abinci mai tsafta?”.
       Cikin girmamawa Tijjani ya ce, “Ranka ya daɗe akwai gidajen abinci masu inganci dake tsaftace abincinsu sosai a garin Kano. Harma da masuyi a cikin gidaje sai dai kawai ai order suna da masu delivery da zasu iya kawo maka har inda kake, ko aje a amso”.
       “Good. Sai ka samo duka gidan. Ka tambayi kowa abinda yake buƙata”
     “In sha ALLAHU yanzu kuwa ranka ya daɗe”.
   Bai sake cewa komai ba ya maida idonsa a television dan an fara gabatar da program ɗin da yay zaman kalla. Hayatu ne ya miƙawa TJ kuɗi masu yawa. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Nidai jallop rice da ƙirjin kaza nake so.”
      Dariya TJ yayi ƙasa-ƙasa yana ƙumshe baki dan karta fito. Sai kuma yayma Hayatu nuni da ogan nasu da ido. Kai Hayatu ya jinjina masa yana sake gyara nutsuwarsa da maida hankalisa garesa ya ce, “Sir za’a karɓo maka kaima ko?”. Shiru kamar bazai tanka ba, dan yamayi biris tamkar baiji ba. Sai kuma batare da ya kallesu ba ya ɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai shegen ƙyau. Ya ɗan yamutsa fuska da jan siririn tsaki. “In dai bazai jima ba a samo min tuwon semo.. miyan kuka”. A tare suka amsa da girmamawa. TJ ya fita da hanzarinsa dan sun san baya cin abincin dare late, wani lokacin ma bai fiya ci ba. Yau ma suna ƙyautata zaton dan baici komai bane tun black tea ɗin safe. Haka yake abinci bai damesa ba, shiyyasa ga shi nan ko kaɗan baida wani tunbi, jikin ma badan yana haye-hayen waɗan nan tarkacen machines ɗin na motsa jikin zamani ba da zai kasance ne falen-felan.
TJ na ficewa Hayatu ya katse tunaninsa tare da matsowa inda yake. Da ga tsayen da yake kamar soja ya ɗan rissina yana fito da flash da ga aljihunsa da faɗin, “Sir ga cctv footage ɗin an samo”. Juyowa yay ya ɗan kalli Hayatu ɗin a yanayin jin daɗin hakan. Sai dai kuma ko kaɗan fuskarsa bata nuna komai ba tana nan a ɗaurenta tamau. Kujera ya nunama Hayatu. Zama yay yana ɗaukar laptop dake a Centre table ajiye ya saka flash ɗin jiki. Kafin ya miƙe yaje har gabansa batare da yayi playing video ɗin ba. Ajiye masa yay a stool ɗin daya jawo a hankali gabansa sosai. Sannan ya zauna a saman carpet kusa da ƙafafunsa yana shiga inda folders ɗin videon suke. Duk zubama screen ɗin laptop ɗin ido sukai. Cikin ƙwarewar aiki Hayatu ya zaluƙo video ɗin sashen da abin ya faru, tare da dai-daita lokacin da komai ya faru sai dai baiyi playing ba ya ɗan ɗago ya kallesa.
         A hankali ya furta, “Kunna”.
    Kunnawar yayi. Ko’ina ya fara nuna shiru babu kowa babu motsin komai. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai ga Samraah na bubbuɗe ƙofifi bayan ta fito da ga wani lungu da suka san restrooms na ma’aikatane a wajen. Yanda take taɓa ƙofofin tana ɓata fuska kamar zatai kuka zai baka tabbacin ta ɓata ne. Can cikin takaici ta fincike face mask ɗin fuskarta. Ƙyaƙyƙyawar fuskarta da babu zanen komai na kwalliya ta bayyana. Hayatu dai ya gagara haƙuri sai da ya furta “Masha ALLAH” a hankali. Dan ko makaho ya laluba fuskar Samraah yasan yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, duk dama eyeglasses ɗinta har lokacin yana a idanunta shi bata cire ba. Isowarta ƙofar da suke ciki ya sanya Hayatu waro idanu sosai, sai dai bai iya cewa komai ba. Ta buɗe ta ɗan leƙa. Sai kuma tai baya a rikice alamar akwai abinda ta gani. Wayarta data zaro tai danne-danne ta kanga tabbacin video take musu yasa Hayatu kasa haƙuri ya furta, “What! Sir itace kenan?”.
       Bai samu amsa ba, dan ogan nasa ko motsi baiyi ba har sai da ya kai ƙarshe. Fitowarsa, tsintar nurse mask. Har cigaba da video da Samraah tayi sanda suke fita da gawar mutumin. Cikin ƙanƙanin lokaci Hayatu ya gama haɗa uban gumi kamar wanda ke a filin kokawa. Shi kam duk da a birkice take video ɗin yaga matuƙar ƙarfin halin yarinyar nan. Motsin da ogansa yayi yasa hankalinsa dawowa jikinsa. Ya ɗan ɗago ya kallesa. Sai da gabansa ya faɗi ganin yanda cat eyes ɗinsa suka canja launi. Dan gaba ɗaya gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama ƴar siririya exactly yanda na mage suke komawa idan suna a cikin haske. Batare da ko kallon Umar ɗin ya sake yi ba ya miƙe ya fara tafiya. Sai da yaje gab da ƙofar bedroom ɗinsa sannan cikin dakiyar muryar dake tabbatar da ransa a ɓace yake ya furta, “A nemota duk inda take. A cigaba da bin duk wani motsinta daga nan zuwa sati biyu”.
        “An gama Sir. Amma in baka manta ba ka bata damar yin hira da kai ma”. Hayatu ya faɗa cikin tsumar jiki. Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shigewa da yake yi kamar mai nazari, sai kuma batare da ya juyo ba ya furta “Zanyi tunani akan hakan”.
Buɗe baki Hayatu yay zai sake magana cikin nuna gamsuwa, sai dai harma ya riga yay shigewarsa shi. Hayatu ya rabga tagumi tare da faɗin, “Tab ƙyaƙyƙyawa kin shiga uku wlhy, bama ke ba duk zuri’arki kin sakasu a masifa. Ke miya kaiki shiga gonar da bataki ba. Aikata wannan aikin da ba’a sakaki ba, karanbaninki ya ɗebeki shiga fadar sarkin aljanu. Dan oga ALJANI ne irin ifiritan nan.” yana cikin wannan sambatun nasa TJ ya shigo da ledoji masu ƙyau an musu tambarin gidan abinci. Firgigit Hayatu ya dawo hayyacinsa tare da gyara yanayinsa. TJ da ma bai wani lura da halin da yake a ciki ba ya ajiye masa tasa ledar sannan ya ajiye wata a Centre table yana faɗin, “Wannan tuwon oga ne. Shi na tsaya ma sai da akayisa yanzu-yanzu gashi nan da zafinsa yanda zai masa daɗin ci.”
        “Ai wannan tuwon mawuyacine ya samu shiga kuma yanzu”.
    Idanu TJ ya waro a rikice ya furta, “Na shigangaɗi Hayatu badai na makara ba? Wlhy babu tuwonne amma matar tace zatayi da sauri tana da miya. Ni kuma naga tunda yace yana buƙatarsa yana so ne shiyyasa nace tayi da sauri…”
      “Kai ka kwantar da hankalinka badan ka daɗe bane ba kawai dai wani abunne daban ya ɓata masa rai. Amma bari na gwada faɗa masa ka dawo mugani”.
     Ajiyar zuciya TJ ya saki, duk da kuwa yanayinsa bai warware ba. Dan in har ogan nasu na cikin ɓacin rai ko damuwa suma sukan shiga matuka saboda yanda suka ɗauki al’amarinsa da matuƙar muhimmanci a rayuwarsu. Tashi Hayatu yay ya nufi hanyar bedroom ɗin nasa, sai da yay jimm a tsaye bakin ƙofar kafin yay knocking a ɗarare. Ko motsi ba’aiba, bai gajiyaba ya sake yi tare da sallama. Nan ma anja kusan minti ɗaya kafin ya amsa masa a daƙile. Sake nutsuwa Hayatu yay kafin cikin dauriya ya ce, “Kayi haƙuri Sir, dama TJ ne ya dawo, a kawo maka abincin nan ne”.
        “No! I’m okay”.
    Shiru Hayatu yay cikin nuna damuwa ƙarara a fuskarsa. Sai kuma ya sake raunana murya ya ce, “Please Sir, duk yau fa bakaci komai ba. Ko nace ma rabonka da abinci tun shekaran jiya a Lagos. Abu mafi saka Ummie damuwa a rayuwa shine ka kwana da yunwa. Dan ALLAH ko kaɗanne ka daure kaci, saboda nasan duk da bata tare damu zata ji a jikinta kamar yanda ta saba”.
      Wani irin cizar lips yay da ga zaunen da yake a bakin gadon hannunsa dafe da kansa. Hayatu ya matuƙar sanin lagonsa a rayuwa. Dan shine kaɗai yake iya bi da shi fiye da kowa bayan mahaifiyarsa. Hakan kuma nada alaƙa da sanin da yay masa tun ƙuruciya. Duk da dai shi ya girmi Hayatun da kusan shekara biyar ma, amma kasancewar sun tashi ne shi da iyayensa a cikin gidan kakansa da ya haifi Ummien sa yasa yay masa farin sani na gaske. Ya jima a gurin kamar bazai motsa ba sai kuma a daƙile ya furta, “Kawo nan”. Cikin sauri Hayatu yabar jikin ƙofar cike da farin ciki bawan ALLAHn kamar cikinsa zai kai. Babu jimawa kuwa sai gashi da tuwon. A can ya shirya masa shi saman table ɗin gaban sofa dake bedroom ɗin, har lokacin kuma yana a zaune bakin gadonsa hannunsa dafe da kansa. Yanayi ne dake nuna yana cikin zafin rai, dan Hayatu ya sanshi a rayuwa fiye da tunanin mai tunani. Ganin Hayatu ɗin baida niyyar fita yaja siririn tsaki yana ɗagowa, harararsa yayi da faɗin, “Ka tsaya gadi na ne sai naci ka gani?”.
         Ƙasa Umar yayi da kai yana ɗan murmushi. Sai kuma ya rissina tare da faɗin, “Ayi haƙuri Sir”. Daga haka ya fice a ɗakin. Wani tsakin ya sake ja sannan ya miƙe zuwa gaban sofa ɗin ya zauna. Hatta ruwan wanke hannu Hayatu ya tanadar masa. A nutsensa cikin yanayinsa na rashin gaggawa akan komai ya fara cin tuwon dan yana son tuwo sosai saboda fevorite food ɗin Ummien sa ne, ada sanda yana yaro idan tayi tace sai yaci yakan zauna yayta kuka shi bazaici miyan daddawa mai wari ba. Amma bayan wani lokaci da rayuwa ta canja kanta zuwa abinda bai taɓa mafarkin riska ba a cikinta sai ya maida tuwon fovorite nashi shima. Yaci kusan rabin malmala ɗaya ya ajiye duk da kuwa tuwon ya masa matuƙar daɗi,  sai dai bai cika son cin abinci late haka ba. Shiru ya ɗan yi zaune a wajen kafin ya tashi zuwa toilet. Brush yayi da sake gyara jikinsa ya fito. Ya samu Hayatu har ya shigo ya tattare komai harda sakama ɗakin freshener ya ƙara dai-daita masa ac. Komai baice ba ya rage kayansa zuwa na barci, sai dai maimakon kwanciyar zama ya sake yi a sofar yana ƙoƙarin kunna laptop ɗinsa, dan yana son ƙarasa harƙallar wani business ɗinsa kafin ya kwanta. Dai dai kuma mi hakan kamar neman gagararsa yake. Dan tunda ya kunna ya gagara danna ko keyboard ɗaya tunaninsa ma neman tafiya yake wani sashe daban. Da ga ƙarshe dai ya ture laptop ɗin gefe ya ɗauki wayarsa. Wata number da aka saka Dude ya nemo tare da danna kira…….✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏

……Kusan lokaci ɗaya muka iso garejin da Mansoor. Dan haka babu ɓata lokaci muka nufi cikin motarsa, dan nan ɗin zaifi mana zama sirri fiye da ko’ina saboda abinda zamu tattauna ɗin. Gaba Yaya Musaddiq ya shiga ni kuma baya. Sun gaisa da Mansoor cikin mutunta juna kamar yanda suka saba nima na gaishesa. Amsawa yay idanunsa a kaina ta cikin mirror.
       “Ya kamata ki huta da kukan nan Samraah. Sai kace kece kika aikata laifin nan. Kinga kuwa yanda idanunki suka koɗe”. Mansoor ne yay maganar cikin nuna damuwa matuƙa. Yaya Musaddiq dake saurarensa ya ce, “Ai ita haka take bata bin al’amarin rayuwa a hankali ka ganta nan. So take sai ta jama kanta wani ciwon muma ta sake sakamu a wata damuwar sannan”.
     Idanuna na cikowa da hawaye na ce, “Kuyi haƙuri Yaya ba haka bane. Wlhy na kasa mantawane da ganin gawar kawai. Amma in sha ALLAHU bazan ƙara ba”.
    “ALLAH yasa hakan” Yaya Musaddiq ya faɗa. Yayinda Mansoor yaja numfashi ya fesar tare da amsawa da Amin. Idanuna na share tare da ƙoƙarin yin magana wayar Mansoor ta shiga ruri. Tamkar an saita sai tawama ta fara. Kusan a lokaci ɗaya duk muka kai hannu domin ɗauka. Sai kuma muka kalli juna tare da sake ɗagowa duk muka kalli Yaya dake tambayar mu “Lafiya kuwa?”.
        “Daga office ne”. Mansoor ya bashi amsa yana ƙoƙarin kai wayar kunnesa. Nima dai tuni nakai tawa tare da yin sallama. MD ne ya amsa daga can, batare daya bi takan gaisuwata ba ya ce, “I’am Sorry Samraah muna son ganinki a office yanzu Please”.
      “Yallaɓai lafiya kuwa?”. Na faɗa da sauri hankali a ɗan tashe.
     Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Kinga kwantar da hankalinki ba wata damuwa bace. Mun samu baƙuncin babban baƙone mai matuƙar muhimmanci da muka daɗe muna fata. Ya kuma ce da ke kaɗai yake son ayi hira da shi”.
         “Ni kuma oga? Duk mutanen dake a gidan sai yace sai ni. Wanene haka da ƙarfin halin nan? Sai kace wani abin cin rabo. Ya kamata Ku faɗa masa ba sashin da nake aiki ba kenan”.
      “Humm Samraah Please mana. Dan ALLAH ki shirya kawai ga driver na nan ma na aiko gidanku ya ɗaukeki a motata”.
    Sake tashi hankalina yayi, sai dai kafin nayi magana oga ya yanke kiran. Sagale nai kawai ina kallon wayar kamar wata gunki. Wane irin baƙone da zai tada hankalin oga har haka. Sannan kuma ma yace ni yake so nai hira da shi. “Kodai mutumin nan ne?”. Na faɗa a zahiri batare da nasan maganar ta suɓuce min ba. Atare Yaya Musaddiq da Mansoor da shima yay zororo alamar kiran da akai masa nada nasaba da nawan suka juyo suna kallona.
     Yaya Musaddiq ne yay ƙarfin halin cewa “Wane mutumi?”. Firgigit na dawo hayyacina. Dan na fahimci zancen zucini ne ya fito fili. Idanuna ne suka cicciko da ƙwalla. Cikin rawar murya na zayyane musu komai da MD yace min. Mansoor ne yay saurin faɗin “Tabbas akwai alamar tambaya. Dan nima akan abinda suka kirani kenan. Amma ina ganin ki kwantar da hankalinki bari muƙarasa office ɗin domin ganin wanene ɗin ko kuwa Yaya Musaddiq?”.
         “Tabbas shawararka yayi Mansoor. Tunda akan aikine bai kamata ayi sakaciba kam. Kuje idan kun dawo ma ƙarasa maganar in sha ALLAH. Nima zuwa lokacin na ɗan ƙara yin nazari.”
    Mansoor ne kawai ya iya amsa masa. Nikam sai binsu da kallo kawai nakeyi. Yaya Musaddiq ya fita yana buɗe baya yace na fito na dawo gaban. Ganin banda niyyar hakan ya buɗe ya kamo hannuna ya fiddoni ya maida gaban. Key kawai Mansoor yayma motar ya haura kan titi. Babu wanda ya iya sake yin magana a cikinmu. Kafin mu isa office ɗin kuma sai danno mana kira MD yake yana kuma sakawa amana. Da wasu kalar shegun zuƙa-zuƙan motoci na alfarma muka fara cin karo a harabar gidan. Sai mutane cikin baƙaƙen kaya tsatstsaye ƙiƙam kamar masu tsaron ƴan fashi. Mudai wucesu mukai muka shiga abinmu. Duk da lahadine mun samu ma’aikatanmu dake duty a wannan ranar dukansu. Harma da wadanda aka kira irinmu da ranar suna hutu suma kamar mu ɗin dai. Office ɗin MD muka wuce kamar yanda aka sanar damu yace muyi. Anan ɗin ma mun tadda mutane biyu irin waɗanda ke a haraba su biyu a jikin ƙofar. Matsa mana sukai muka shiga bayan Mansoor yayi knocking an bamu izinin shiga. Mun fara cin karo da ƙamshin turare mai armashi sosai. Sai sanyin ac a office ɗin kamar ba safiya ba. Wannan kuma ba halin MD bane zama cikin ac da ƙarfi haka.
        Akan MD idanunmu suka fara sauka. Kafin dattijon dake zaune a kujerar kusa da shi cikin shigar ɗanyar shadda mai tsananin ƙyau da ɗaukar hankali sai maiƙo take da walwali. Ƙyaƙyƙyawane sosai baƙi ga dogon hanci da shiryayyen farin gashinsa daya ƙawata taswurar fuskar tasa. Gaishesa muka farayi kawunanmu a ƙasa. Dan tun shigowarmu ya zuba mana idanunsa manya farare yana murmushin bajinta. Yanzun ma da fara’ar ya amsa mana. Sai kuma ya kalla MD ɗin yana faɗin, “Inaga idan kun shirya mu fara abinda ya kawomu kawai. Dan na faɗa maka zanbi jirgin ƙarfe biyu ne domin komawa Lagos, ina kuma da wasu uzirin bayan wannan. Gashi yanzu 10:30.”
       “Hakane ranka ya daɗe” MD ya faɗa cike da tsantsar girmamawa ga dattijon. A karo na farko muka kalla juna ni da Mansoor. Sai kuma muka maida kan MD da yay kiran sunanmu a tare. Idonsa akan Mansoor ya ce, “Mansoor ka duba tare da tabbatar komai yayi dai-dai a can ɗin. Muma gamu nan fitowa.”
       Amsa masa Mansoor yay cikin nuna ƙaulani, sai dai baice komai ba ya juya ya fita. MD ya maido da idanunsa kaina yana miƙamin takardun hannunsa. “Ke kuma Samraah ga wannan. Sune tambayoyin da zakiyi, ki ɗan dubasu ko. Sai kuma ya kamata kije ki gyara makeup naki kema gamu nan fitowa.”
        Ɗan jimm nayi kamar bazan amshi takardar ba, MD ya wani marairaice fuska tamkar zai fasa ihu cikin nuna alamar roƙona da idanu. Jinai kamar na balla masa harara. Amma dai na daure na amsa takardun kawai ina faɗin, “Okay Sir” a hankali. Ina daga tsayen na dudduba komai, batare da nace komai ba na ajiye masa a saman tebir ɗin. Sannan na juya na fita. Da ga shi har baƙon nasa ina jin idanunsu a kaina. Da ƙyar na iya ficewa zuciyata na ƙara nauyi ga mamaki da cushewar kai na rashin iya gane komai a wannan al’amari. Dan magana ta gaskiya duka tambayoyin da MD yace sune zan masam sun matuƙar bani mamaki. Na kuma sake tabbatar da lallai akwai wata a ƙasa. Watan da shi kansa MD idan yay wasa sai ya zurma ciki ƙwarai da gaske….

       “Tofa, mi kuke tunani masu karatu🤥? Nima fa kamar na shiga ƙaulanin ne🤔”.

✨・o・✨・o・✨・o・✨

           Sosai yasha barci mai lafiya a safiyar ta yau kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. Dan tunda ya dawo massalaci sallar asuba da Ummiensa kawai yayi waya ya sake komawa ya kwanta. Bai tashi ba sai yanzu babu jimawa. Wanka kawai yayi tare da gyara jikinsa cikin wando 3quater mai laushi kalar baƙi da rigarsa fara da adon baƙi kaɗan itama mai laushi. Dogon hannune da ita tare da hula. Sai dai ya saki hular a bayansa, sannan bai saka zip ɗin rigar ba. Hakan ya bama farar singlate ɗinsa damar fitowa sosai tare da ɗamammen cikinsa da har kana iya ganin kwanciyar gurayen kansa dake nuna shi matsayin mutum mai tsananin motsa jiki. Yau dai bai ɗaure gashin ba, sai dai yasha gyara sosai dan daga shi har siririn kwantaccen sagensa sai uban ƙyalli da ƙamshi sukeyi. Ga gashin ya ɗan sakko masa har kafaɗa kaɗan. Magana ta gaskiya babu wanda zai kalla bawan ALLAHn nan ya yarda wai ya haɗa jini da baƙaƙen fata. Dan sam baya kammani da su sai dai fatarsa da tai ɗan diff ba kamar na fararen dake kasancewa jazur ko fari fat ba. Amma shi yanayin da fatar tasa take ma sai ya ƙara masa wani ƙyawu na musamman. Kai tsaye ga coffee machine ɗin sa da ke a falon ya nufa. Cikin mintina kaɗan ya haɗa coffee. Ƙyaƙyƙyawan mug ɗinsa na zallar farin glass ya ɗauka ya tsiyaya fin rabi a ciki. Sannan ya tako a hankali yana kaiwa bakinsa zuwa cikin falon sosai. Furucin daya fito daga cikin television dake aiki a falon ya sashi karkata hankalinsa ga tvn. Dai-dai nan Hayatu ya shigo kamar wanda aka koro. Kaɗan ya juyo ya kallesa cikin yanayin nan nasa na rashin sakewa, sai kuma ya sake maida kansa ga tvn yana sake kai mug ɗin kan ɗan ƙaramin bakinsa ya zuƙi coffee ɗin duk da zafin da yake da shi.
        Hayatu da gaba ɗaya hankalinsa ke a tashe ya ce, “Sir kaga abinda ke faruwa kuw……” sauran maganar ta maƙale sakamakon saukar idonsa akan tvn shima. Da sauri ya ɗan yi baya kamar wanda ke shirin faɗuwa. Ya dai samu nasarar dafe hannun kujerar dake kusa da shi yana bin ogan nasa da ya ƙarasa ya zauna cikin kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da kallo. Yasan halinsa sarai akan dakiyar masifa dayin biris da abu kamar bai damar ba. Amma magana ta gaskiya wannan bai kamata ai biris ba. Zama yay ya samarwa kansa nutsuwa. Kafin ya furta, “Amma Sir mizai sa Baba prof.. zuwa Kano a yau har yayi hira da yarinyar nan ne? Kodai ya amince da batun buɗe companyn yanzu? Wlhy ni du kaina ya kulle ma”………✍️

Ni ma dai mai ɗaukar rahoton neman ruɗar fani ɗin kuke Hayatu PA.🤥🤔

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚

…….Kamar yanda Hayatu yasan bazaice komai ba baice ɗin ba kuwa. Sai ma aikin shan coffee ɗinsa da yake hankali kwance idanun nasa dai a tvn dan har an fara program ɗin. Gaba ɗaya hirar anyita ne akan abinda ya shafi harkar ilimi a Nigeria. Da rawar da su malamai ɗin suke takawa domin ganin matarbar ilimin ta dawo hayyacinta da ga mutuwar tsayen da tayi musamman daya kasance tun daga tushene. Dan yanzu secondary schools tafi kowace gaɓa lalacewa a harkar karatu, in ba makarantar kuɗi zaka kai yaranka ba sai a hankali. Gashi kuma Sakandire ɗin nan ne ake ganin tamkar mahaɗar dake riƙe da kowanne reshen ilimin dan anan ne ake karatu tuƙuru cikin halin ƙuruciya da babu wasu damuwoyin fara fuskantar ƙalubalen rayuwa irin na girma. Wannan hira ta matuƙar ɗaukar hankalin mutane, inda ta haifar da cecekuce sosai tare da yaba ma prof… ɗin. Dan tun kafin a kammalata saƙwanni sun cika kowane dandalin sada zumunta na wannan gidan tv da rediyo. Yayinda wasu ke tattaunawa a dandilansu na sada zumunta. A cikin awa ɗaya da akai da Prof.. K/Mashi an amsa harda wayoyin mutane, ya kuma bada cikakkun amsoshi masu jan hankali da suka sake birge mutane da ganin kimarsa da girmansa. Duk da a baya ana zaginsa akan yanda yake aiki tuƙuru ma kudancin Najeriya ɗin kasancewarsa mazaunin can shi da gaba ɗaya zuri’arsa. Dan wasu na ganin a komai nasa bama ya alaƙanta kansa da arewa sam, tamkar ma baida wani alaƙar dasu, musamman idan yana sukar ƴan siyasar arewan da ƙalubalantar shuwagabannin yankin.
         Koda aka kammala ma babu alamar Maash zaice wani abu. Zuwa yanzu dai kansa na jingine da kujerar idanunsa a lumshe. Ta ƙasan ido Hayatu ke kallonsa da nazartarsa. Sai kuma a hankali ya furta, “Sir miza’a kawo maka breakfast?”.
      Shiru babu alamar zaima motsa balle ya tanka masa. Sai kuma dai cikin motsa lips da ƙyar ya furta, “Waka ɗora akan aikin bincike akan yarinyar nan?”.
           Ƙasa Hayatu yay da kansa, cikin girmamawa sosai ya amsa da, “Da kaina nayi Sir. Dama abinda nazo kawo maka kenan. Sai kuma wanda zai ringa bibiyar tata ne kuma ina kan nazari. In sha ALLAHU daga nan zuwa yamma zan kawoshi shima.”
    Yana daga kwancen ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonsa. Hayatu ya ƙara rissinar da kansa yana ɗan murmushi, dan yasan abinda yay ɗin ya faranta ran ogan nasa koda bai fito ta faɗa ba. Ci gaba yay da faɗin, “Sunanta Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Wasu kan kirata Sam-G. Tana da yaya Musaddiq da ƙani Hafizzullah. Musaddiq ɗin makanike ne, shike riƙe da rayuwarsu, ƙanin nata kuma na jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina yana karatu. Iyayensu sun jima da rasuwa, a hannun Uncle ɗinsu suke tun suna ƙanana. Akwai wani yaro Mansoor da ko yaushe suna tare shine zata aura dan har maganar iyaye ta shiga. A zahiri Samraah bata da hayaniya ba kuma sabgar kowa take shigaba sai in itace taso hakan. Sai dai kuma tana da tsiwa a wasu lokutan musamman ga wanda ya shigar mata hanci. A shekarun baya kaɗan ta fara rubuce-rubuce kan abubuwa masu muhimmanci musamman da suka shafi ƙananun yara mata dake tallace-tallace a tituna. Sai dai tunda ta fara wannan aikin ta ɗan rage hakan. Bincikena kuma ya tabbatar min tanada fans sosai, dan a duka shafukanta akwai fallowers dake fallowing ɗinta sosai. Na tabbatar da yanda suke jin daɗin karatun rubuce-rubucen nata ne ta hanyar comments da suke mata. A office kuwa tana fannin ƙananun ma’aikata ne. A ɓangaren rediyo ta fara aiki kuma. Sai dai ƙwazonta da yanda program ɗin data bada shawarar samarwa akan matasa ya amsu, ya saka suka maidata itace mai gabatar da program ɗin. Da kuma a iya rediyo kawai akeyinsa, amma yanayin karɓuwarsa yasa suka koma gabatar da shi har da television, sannan shi MD ɗin su ne ya bata power sosai a al’amarin. Shiyyasa ma ake zargin yana sonta ne duk da yasan akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninta da shi wancan yaron Mansoor, amma har yanzu bai san iyayensa sunje gidansu ba ma har anyi maganar aure.” ɗan matsawa yay gabansa yana yunƙurin ajiye tab.. ɗin dake a hannunsa yana cigaba da faɗin, “Nayi fallowing duka shafukanta, gashi ko zaka duba”.
        Hayatun ya ɗan kalla sai kuma ya ɗauke idanun nasa. A daƙile ya ce, “Ba buƙata. Ka kammala komai dan zuwa jibi maybe zamu wuce. Ka tura ma MD nasu takardar amsa gayyatar da tai min, sai dai kar ya wuce gobe” daga haka ya miƙe. Har ya shige bedroom ɗin sa Hayatu da kansa ke ƙasa na binsa da kallo. Sai kuma yaja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana kaiwa zaune cikin lallausar kujerar dake a falon. Tagumi ya zuba da hannaye biyu, gefe ɗaya mamakin komai yake yi, wani gefe kuma na ayyana masa akwai abinda ogan nasa ke shiryawa. Kuma tabbas da wahala ace zai kasance mai daɗi, yana tausayin yarinyar nan, dan ta taroma kanta match. Bashi da zaɓin daya wuce cika umarni, dan haka ya ɗauka tab.. ɗinsa. A take yay kiran wani tare da buƙatar number ɗin MD na gidan tvn na AlHERI. Ko mintuna biyar ba’a cikaba kuwa sai ga saƙon Number ɗin ya shigo masa. A take ta shirya text message ya tura musu kamar yanda Maash ya umarcesan…..

    Yayanmu nima fa ka fara ban olo gaskiya😌🥺🥺.

      🌟(☉。☉)!(☉。☉)!(☉。☉)🌟

         
          Sam nutsuwa bata ɗan dawo jikina ba sai da aka kammala duka program ɗin. Bayan an ɗauke camara daga kanmu na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ina mai lumshe ido. Ɗan kallona prof.. yay a kaikaice sai kuma yay ɗan murmushin manya yana miƙewa. Yana fita a ɗakin shi da MD sauran ƴan uwana ma’aikata sukayo kaina. Ruwa aka fara bani nasha, na sake samun nutsuwa sannan nima na miƙe. Muna daga harabar gidan ni da Mansoor dake lallaɓani muje muci abinci aka aiko kiranmu. Dole cikin muka koma. Inda muka samu dukkan ma’aikatan da suka bada gudunmawa a program ɗin har ƴan bayan fage a office ɗin MD. Zama mukayi kamar kowa muma. Daga haka Prof.. ya fara mana bayanin godiya, tare da sanar mana dalilinsa na gabatar da wannan program ɗin cikin gaggawa haka. Sosai muka nuna gamsuwarmu. Musamman ma ni da kaina duk ke a ɗaure da farko. Ƙyauta dukanmu ya danƙa ma kowa a envelope ɗinsa. Daga haka yay mana godiya muma muna masa. Sai dai me ni sam hankalina ya gagara tsayawa waje guda akan hakan. Kallo na fara bin sauran ƴan uwana da shi, kafin na miƙe zaram kamar wadda akaima allura nabi bayansa da sauri. Mansoor na ƙoƙarin tsaidani da son jin ina zanje bamma sauraresa ba na fice da sassarfa. Isowata yayi dai-dai da buɗema prof.. mota zai shiga. Ga mutanensa zagaye da shi kamar zasu iya hana mutuwa ɗaukarsa. Amma ko’a jikina nai sallama kaina tsaye. Su duka juyowa sukai suna kallonna musamman MD da yay rakkiya tare da Prof….
        Fuska ɗauke da murmushi Prof.. ya ce, “A’a ɗiyata ko kinyi mantuwa ne?”.
    Ƙasa nai da kaina ina ɗan murmushin ƙarfin hali. Kafin cikin ladabi da dakiyata na ce, “A’a ranka ya daɗe. Dama uhm….” sai kuma nai shiru na kasa cigaba da faɗa ganin yanda suka tsatstsareni da idanu su duka. Murmushi mai sauti Prof… yayi yana sakin murfin motar ya juyi gareni da ƙyau. “Daughter yi maganarki ƙofa a buɗe take ai. Ko mu koma gefe ne?”.
     Da sauri na ce, “A’a Sir ba sai munje ko’ina ba. Mun gode sosai da karamcinka garemu, amma dan ALLAH kayi haƙuri zan dawo da wannan dan ana biyana albashi akan aikina, kuma yana wadatar dani”.
      Bashi ba hatta MD ina ganin yanda yay wani irin sororo yana kallona. Ni dai na ɗauke kaina ina miƙama yaronsa daya raba mana envelope ɗin. Ganin ya tsaya yana kallona bashi da niyyar amsa na ɗaura masa kan kayan hannunsa na juya a nutse na bar wajen. Ina jin yanda idanunsu sukai min riiiii aka. Amma ban waiwayo ba. Cin karo muka kusan yi da Mansoor da alamu suka nuna biyoni yayi. Na ɗan ja da baya ina faɗin, “Ya salam I’m sorry ban san ka taho bane”.
        “Babu damuwa” ya faɗa yana kallon hannuna. Fahimtar hakan yasa kai tsaye nace masa “Na mayar musu ne?”.
     “Mi ɗin?”.
   Ya faɗa cikin waro idanunsa sosai waje. Bakina da ke cikin face mask na tura gaba da faɗin, “Yo abinda suka bamu. Ni gaskiya bana ra’ayi dan zuciyata sam bata ma kwanta waje ɗaya ba. Ta yaya mutum zai taso rana tsaka ya ce muyi hira da shi babu wani goron gayyata babu notes sannan ya kuma kawo wani abu ya bamu wai matsayin ƙyauta. Dan ALLAH kai baka ji abin banbarakwai ba? Shine fa wanda kwanaki akaita kace-nace ɗin nan akansa game da abinda ya faɗa akan shugabannin arewa. Gashi kuma da bakinsa ya faɗa shi haifaffen jihar Kano ne. Amma bai ragi balle ragowa wajen sukar mana mutane kamar wani maƙiyinmu”.
       Idanu kawai Mansoor ya zuba min kamar mai nazari. Ya buɗe baki zaiyi magana sai ga MD ya iso kamar a fusace. Dan cikin yanayi kamar faɗa-faɗa ya ce, “Samraah sameni a office”.
        Sai da na taɓe bakina dake a cikin face mask sannan na amsa masa da to ciki-ciki. Yana juya baya kuma na bisa da harara. Ƙin tafiya nai har sai da Mansoor ya mun magana. Batare da shima na tanka masa ba na wuce fuu nabi bayansa……..✍️

“Amma Samraah miyyasa kika ƙi amsa bayan kuma kema kin gamsu da bayanin da yay muku na dalilin hirar? Sannan kin siffantashi da mutane kirki a halittar jiki da yanayinsa, kuma bayanansa sunja hankalin mutane da yawa a yau ɗin har hakan ya sake ɗaga darajar gidan tvn ku?”.

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝑶𝒏𝒆

…….Humm Bily a zahirance banda wani dalilin yin hakan kamar yanda kowa zai iya gani ko fahimta. Sai dai ni a ƙasan zuciyata ina jin dole-dolene bai kamata na amsa koma miye ɗin ba. Dan babu dalilin hakan bisa hujjoji da dama. Amma ban sani ba ko kema zaki iya fahimtar hujjar tawa a yanzu. Ko kuma sai anan gaba cikin abinda zai zo a labarin nan nawa. Dan a yanzu kam tabbas babu wani dalilin da nima zan tilasta miki gamsuwa dani. Amma dai muje zuwa ofishin MD dake kirana.
     (Babu musu na jinjina mata kai, amma magana ta gaskiya al’amarin wannan Sam-G ɗin taku yana ɗan rikitani. A ido zaka iya mata kallon like innocent people. Sai dai a ɗan zaman da nai da ita na fahimci taƙadarar kanta ce. Sannan akwai taurin kai yana jinjirin jaki. Kar dai na cikaku da zance ku muje zuwa dan jin yaya ta kaya a offishin MD)

       Tsaye na samesa yana faman kai kawo a tsakkiyar office ɗin nashi. Sai faman furzar da huci yake kamar wani bajimin rago. Ko ɗar banji ba a raina na rafka sallamata. Juyowa yay yana kallona da idanunsa da suka kaɗa sosai. Kamar wanda ke shirin dukana ya wani zaburo kaina har sai da na ɗan ja da baya ina waro manyan idanuna waje.
       “Samraah kin san mi kikayi kuwa? Kin san wanene wannan mutumin kuwa? Kin san ƙyautar mi ya baki kuwa? Amma kika watsa masa ƙasa a ido ta hanyar maida masa bayan ya fifitaki sama da kowa. Kuɗi duk ya bama sauran 50-50k, amma ke makullin mota ya baki batare da ko dubawa kinyi ba kika ɗauka kika maida masa…”
        “Mata fa dai?”.
Na tambaya da iya gaskiya ta. Shima cike da ƙwarin gwiwa ya amsa min da “Yes Mota Samraah. Shiyyasa a kullum nake faɗa miki ke ɗin mai sa’a ce dear”.
Kaina na ɗan girgiza da murmushin basarwa, na ce, “Humm to amma Sir mi zanyi da shi idan na riƙe? Sannan wace amsa zan bama iyayena idan sun tambayen a ina na samu mota? A shi karan kansa mi ma zaisa ya mana irin wannan ƙyautar haka dan kawai munyi hira da shi?”.
      “Tab ɗin, wlhy yarinyar nan baki da hankali…” ya faɗa cikin ƙunar rai, a take na sake tamke fuskata dan kalmar tasa ta mun matuƙar zafi a zuciya. Duk yanda naso na shanye na gagara hakan, kai tsaye nace masa, “Sir minene abin rashin hankali anan? Bayan kuma na faɗa maka hujjata. Wannan fa rayuwata ce”
         Wani irin tsayawa yay duka hannayensa riƙe da ƙugunsa kawai yana kallona tamkar ya samu television. Ni kam na sake fuskewa kamar ban san yanayi ba. Na fahimci takaicina ne ya maƙureshi ya hana shi cigaba da magana. Dan a fusace ya sa ƙafa ya tunkuɓar da flower base ɗin da akai ado da ita a office ɗin, sannan ya ce, “Samraah out. Get out of my office now..”
      Ko kallonsa banyi ba na juya nai ficewata. In ma ca yay na bar Company ɗin gaba ɗaya daga yau banda matsala da hakan. Ko takan Mansoor banbi ba nai ficewata gaba ɗaya daga gidan. Napep na tare zuwa garejin su Yaya Musaddiq. Na samu suna shirin shiga sallar azhar, sai dai shi Yaya bai kai ga tafiya ba yana ƙoƙarin ɗaura alwala ne. Tun kafin na ƙarasa inda yake na fahimci ya zuba min ido.
       “Lafiya kike?”.
   Ya faɗa dai-dai ina isowa gabansa shi kuma yana wanke ƙafarsa. Mai makon amsa sai na tura masa baki. Kansa ya girgiza kawai yana sake faɗin, “Je can ki zauna muyi salla to, idan na dawo sai kiyi taɓarar”. Daga haka ya wuce ya barni a wajen dan ya kammala alwalar…

  💫´⊙ω⊙💫⊙ω⊙💫⊙ω⊙`💫

            
        Zaune yake a falo tare da Hayatu da Juliet, tab.. ce a hannunsa, ƙafafunsa miƙe saman Centre table da aka turo gabansa sosai. Hankalinsa gaba ɗaya nakan screen ɗin tab ɗin, hannunsa ɗaya rike da haɗaɗɗiyar chocolate yana ci a hankali tamkar baya so. Yayinda Juliet ke bayani akan abinda ya zaunar da su ɗin, dan itama dai laptop ce a hannunta, sai Hayatu dake riƙe da takardu ta gefenta. Abinda juliet ɗin ta faɗa na ƙarshe ne ya sakashi ɗagowa cikin rashin sakewar nan tasa ya zuba mata ido. Da sauri ta risinar da nata dan Maash nada wani kwarjini dakan hana mai kallonsa iya masa kallon ido cikin ido na tsawon lokaci, koda kayi jarumtar yin hakan da zaran shi ya zuba nasa cikin naka zaka ji ka takura. A ɗan daƙile ya ce, “Ina son magana da Mustapha. Sannan ai cancel ɗin Thailand a cikin schedule namu a maida Finland”.
       Atare su duka biyun suka amsa masa dan zancensa ya shafi kowannensu. Babu ɓata lokaci kowanne ya shiga yin abinda aka saka shi. Juliet ce ta fara ɗagowa cikin harshen turanci tana tambayarsa, “Sir komai zai zama ne de same date?”.
            Kamar baima jita ba aikinsa yake, sai da ya mula dan kansa sannan ya bata amsa da “Uhm”. Cikin girmamawa ta jinjina kanta da amsa masa ta cigaba da aikinta. Dai-dai nan shima Hayatu ya taso daga inda yake da waya a hannunsa. Ta gefensa ya ɗan tsaya cikin risinawa ya miƙa masa. Batare daya ɗago ba a hankali ya furta, “Sa a hans free”. Da sauri Hayatu ya maidata hans free, sai ga muryar wancan da ya kira da Mustapha rangaɗam. Duk da a cikin waya yake cikin girmamawa ya gaishesa, zaka tabbatar da hakanne ta yanda yake magana cikin ƙanƙan da kai. Shikam kamar yanda ya saba ya amsa a taƙaice. Sannan suka tsunduma maganarsu, duk dai akan harkar business ne, mafi yawan maganar kuma Mustaphan keyinta.. ba wata doguwar magana sukai ba ya barsa suka cigaba da magana da Hayatu. Dai-dai Hayatun na ajiye wayar shima alamar sunyi sallama ɗaya daga cikin securitys ɗin gate yay sallama tare da yin knocking. Hayatu ne yaje garesa yana amsa masa sallamar. Jin abinda security ɗin yace ya sashi ɗan wara ido waje. Sai kuma ya juya cikin falon da sauri. Cikin ɗan yanayin rawar harshen wanda ya shiga ruɗani ya ce, “Sir Baba prof.. ne a gate”.
      Cak Maash ya dakata da abinda yake, sai kuma ya lumshe idanunsa tare da buɗesu luuu gaba ɗaya akan Hayatun. Bashi da alamar cewa wani abu, Hayatu kam duk ya ƙagu yace ɗin. Idanun nasa ya maida ga tab ɗin abinsa batare da yace komai ba. Sake birkicewa Hayatu yayi, sai dai baida tacewa.
        “A buɗe masa”.
     Zabura Hayatu yay yana sauke nannauyar ajiyar zuciyar da sai da ta saka Juliet danne dariya. Dan haka ya harareta ya nufi hanyar fita da sauri. Shiko Maash aikin gabansa ya cigaba dayi hankali kwance. Mintina huɗu ba’a cikaba sai gasu kuwa. Baba prof.. ne a gaba. Tun a taku biyu ya tsaya yana bin falon da kallo, kafin ya sauke ƙyawawan idanunsa na tsufa akan santalelen jikan nashi mai ji da lokacisa. Murmushi ya saki a hankali, sai kuma ya cigaba da shigowa cikin falon guards ɗinsa guda biyu biye da shi. Sai Hayatu a gefe. Juliet ma tuni ta miƙe tsaye. Cikin girmamawa ta shiga gaishesa, ya amsa mata da kulawa, har lokacin kuma Maash bai motsa ba balle ya kalla kakan nasa. Hayatu ne yayma guards ɗin Baba prof… da Juliet magana dan haka suka fice suka barsu su biyu.
         A karo na babu adadi Baba prof.. ya sake sakin murmushi. Idanunsa akan Maash ya ce, “Fushinne har yanzu? Common sweetheart ya kamata ka huce mana. Kaifa yanzu babban mutum ne ba little Awwab ɗin nan ba mai hawa saman wuyan grandpa ɗinsa yay doki saboda fitinarsa. Be a man mana my baby boy”.
      Fuska Maash ya sake tsukewa. Batare da yayi magana ba ya dangwarar da tab.. ɗin hannunsa yana miƙewa kamar a fusace zai wuce. Caraf Baba prof.. ya damƙo hannunsa, jawosa yay kawai ya faɗa jikinsa ya rungumesa tsam-tsam yana dariya. Sun jima a haka Maash nata faman sauke ajiyar zuciya, yayinda Baba prof.. keta murmushinsa shi dai. Sai da ya tabbatar ya gama haɗiyar zuciyar kafin ya ɗagosa. Hannu yasa saman kansa ya birkita gyararriyar sumarsa da yau bai ɗaure ba. Babu shiri Maash ya saki murmushi daya sake ƙawata ƙyawunsa. Baba prof.. kuma ya ƙyalƙyale da dariya tare da jamasa dogon hancinsa sannan ya sake maida hannunsa kan sumar tasa ya shiga kwantar da ita yanda take.
       “Dibeka so cute idan kana murmushi. Amma ka dinga ɗaurema mutane fuska har ni ɗin ma Kakanka ban tsira ba. Kai nidai naga takaina da kai balaraben Nigeria”.
      Murmushin Maash ya sake yi, batare da yace komai ba ya girgiza kansa kawai yana nufar kujera ya zauna kamar yanda Baba prof.. yayi. Cikin girmamawa ya gaida kakan nasa, shiko ya amsa masa cike da kulawa, sai kuma yabi falon da kallo yana cigaba da faɗin, “Mutumina alƙawarin ALLAH dai ya cika ka dawo mafari. Hakan nada ƙyau kuma naji daɗi kwarai da gaske. Ina fata kuma za’amin afuwa da rashin cika alkawarin dawowa da nai jiya. Gangar jikin nawane kawai acan, amma zuciyar na nan. Shiyyasa ma ina sauka a Lagos ko gida banje ba na sake biyo jirgi zuwa nan ɗin.”
         “Ba komai ya wuce ai, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya”. Maash ya faɗa cikin tausasa harshe duk da dai maganar da ƙyar take fita. Baba prof.. bai damu ba, dan yafi kowa sanin wanene jikan nasa. Wannan yanayin nashi kuwa halittarsa ce, tun yana ƙaraminsa baida sakewa da mutane. Sannan haka yake dai babu yawan magana. Wasu abubuwa da suka faffaru kuma suka sake maidashi dunɗun dukum ya zama miskilin gasken gaske. Gashi nan dai babu yabo babu fallasa a ɓangaren kirki. Dan babu wanda ke ɗaga masa yatsa bai karya ba. Ya iya rikici da rigima ƴar gaske. Dan tabbas Maash akwai rikici, tsagerane na bugawa a jarida, sai dai yanayinsa na shiru-shiru yasa sai ya zuba maka tsiya yay kamar bashine yayi ba, in kuma za’a tambayi mutum dubu su shedesa suma akan bashi ɗin ne yay ba. Sai dai su da sukai masa sanin ciki da bai na rayuwa, musamman ma shi kakansa da mahaifinsa da mahaifiyarsa sun san shine ya yin……✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆

……A tare Hayatu da saurayin sukai sallama. A saman lips ya amsa musu. Suna ƙarasowa saurayin ya zube a ƙasan lallausan carpet ɗin tsakkiyar kujerun, sai faman kalle-kalle yake kamar wanda ya buɗe ido da ga makanta. Sai da Hayatu ya ɗan zunguresa da ƙafa sannan ya dawo hayyacinsa ya ɗan nutsu. Ganin idon Maash a kansa ya sake nutsuwa tare da faɗin, “Ranka ya daɗe ina wuni”.
         A hankali Maash ya ce, “Lafiya, miye sunan ka?”.
     “Sani”. Ya bada amsa da sauri.
“Kayi karatu?”.
   “Eh ranka ya daɗe, har matakin N.C.E na kai. Sannan na sauke Alkur’ani tare da littatafan addini masu yawa”.
         Kai kawai Maash ya jinjina masa, dan shi hausan ma ba wai duka yake ganewa ba. Sai dai yaji dukkan bayanin saurayin. Hayatu ya kalla, dan haka yay saurin gyara tsaiwarsa da ɗan matsowa kusa da shi. Dan shi koda ido Maash ya kallesa yasan mi hakan ke nufi. Kai tsaye ya ce, “Na sanshi sosai Sir farin sani, dan ɗan uwana ne, da mahaifiyarsa da mahaifina uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sai dai su anan Kano suke. Yasan ciki dabai na garin Kano, sannan ita kanta yarinyar ma ya santa a dalilin shirin da take gabatarwa na matasa, har hira ta taɓa yi dasu wata biyu da suka shige lokacin bai kammala makarantarsa ba”.
           Nanma shirun yay ƙafarsa ɗaya akan ɗaya yana kallon saurayin kawai, sai da ya mula dan kansa sannan ya furta, “Ka tabbatar zai iya?”.
       “In sha ALLAHU zai iya Sir. Kuma zai riƙe sirrin dan in ma ya tona kamar kansa ya tonama asiri ne. Mu bamu sanshi ba bamu da alaƙa da shi idan aka samu kuskure”.
      “Fine.”
  Ya faɗa a taƙaice yana miƙewa abinsa. Ƙofar bedroom ɗinsa ya nufa, sai da yana gab da shiga corridor ɗin ya ce, “Ka bashi key ɗin mota da 500k na mai. Sallamarsa sai ya gama aiki”. Daga haka yay shigewarsa. Waro idanu sosai Sani yayi, jikinsa na rawa ya ce, “Yaya dubu ɗari biyar fa. For mai ɗin mota kawai? Na shiga uku ni Sani ɗan inna”.
        Dariya abin ya bama Hayatu, sai dai baiyi ba yay murmushi kawai da faɗin, “Kaga tashi muje waje sai kai murnar. Ka jirani bara na kai masa wannan”.
     Ai kafin ma Hayatu ya rufe baki Sani ya kai ƙofa da sassarfa…

       😂Sani a taimakan dana data mana🤣😝.

          💢💦💢💦💢💦💢

   A rikice Yaya Musaddiq ya iso gida sakamakon kiran da nai masa ina kuka. Sai dai kafin ma nakai ƙarshen abinda zan gaya masa Baby ta kaɗar da wayar tawa gefe ta daki tayis. A take tai ƙarar fashewa. Koda na ɗagota screen ɗin yay rugu-rugu ta koma fari gaba ɗaya alamar ta samu matsala. To anan ne fa na kasa haƙuri, bamma san sanda nai kukan kura a kanta ba sai ganina sukai na haye ruwan cikinta ina jibga tamkar ALLAH ya aiko ni. Aiko Bibaa da Abbas suka shigar mata suma suka hau dukana. Auta kuwa ya hau ihu da kururuwar kuka. Abba zai rabamu Mom ta riƙesa da makircinta. Sarkin yawa yafi sarƙin ƙarfi, duk da nima na more akan Baby suma sun dakeni sosai harda jimin ciwo. Wannan faɗa bai rabu ba sai da Yaya Musaddiq ya shigo. A haukace ya faɗo falon batare da neman izini ba ya hankaɗe Abbas gefe tare da Bibaa. Sannan nima ya ɗagani akan Baby. Sake yo kaina Abbas yay Yaya ya shiga tsakkiyar mu yana daka masa tsawa. “Abbas!! Kai miyasa baka da wayo ne? Maimakon ka rabasu matsayinka na babba amma rashin hankali da kai ma akeyi?”.

        Maimakon Abbas ya bada amsa sai Mom ce ta taso a fusace taba Yaya Musaddiq ɗin amsar. Daga ni har shi take haɗawa tana zagewa da kirani ɓarauniya, kai har iyayenmu ma haɗowa take. Yayinda ƴaƴanta ke faman huci kamar zasu daki Yayan shima. Duk da abinda ake Abba na falon ya gagara sake cewa komai.
    Karon farko dana ga ɓacin ran Yaya a fili game da abinda ake mana a gidan. Dan muryarsa har zuga take wajen faɗin, “Mom ki daina danganta Samraah da sata dan bata taɓa yima wani aka gani ba. Fitarta ta yau kuwa kowa yasan inda taje tunda abune a bayyane. Ya kamata dai ki binciki sarƙarki a tsakanin ku da kuke gidan zaune.” daga haka yaja hannuna dan mu fice. Amma sai Mom ɗin da Abbas suka sha gabanmu. Abbas ne ke faɗin, “Kai har ka isa ka fiddata anan bata ajiye sarƙa ko kuɗin sarƙa ba. An kuma kirata ɓarauniyar ko akwai abinda zakayi ne?”.
        Wani daƙilallen murmushi yaya Musaddiq ɗin ya saki a karo na farko. Sai dai baice komai ba ya sake jan hannuna zamu raɓasu mu wuce.
   “Mussadiq!”.
Abba ya ambata a karo na farko. Cak ya dakata, sai dai bai juyoba bai kuma yi magana ba har sai da Abban ya sake magana. Still dai hannun nawa na riƙe a nashi muka dawo gaban Abban. Da hannu yay masa nuni daya zauna. Nan ɗin ma kamar bazai zaunaba ɗin sai kuma dai ya zauna. Hakan yasa nima na zauna a kusa da shi. Mom ya kalla ita da su Abbas suma yace suzo su zauna…
Kusan mintina uku falon yay tsit sai ƙwafa da Mom keyi a jajjere tana harararmu ni da Yaya Musaddiq. Sai da Abba ya tabbatar kowa zuciyarsa ta nutsu kafin ya fara magana. “Bana jin daɗin wannan rayuwar da akeyi a gidan nan sam. Mu ace kullum sai maƙwafta sun jiyomu muna ihu da hayaniya kamar wasu marasa abinyi ko wanda basu je ajin makaranta ba. Bakwa ganin hakan zubarma da kammu mutunci ne?….”
      “Abban Abbas kaje ga maganarka kai tsaye nifa bana son wani kwana-kwana. Batun sarƙata ake anan ba wani mutunci ko yanda maƙwafta ke kallonmu ba. Su ya dama, sun kuma ga zasu iya ne. Dan haka ka musu magana su futomin da sarƙata in har ana son zaman lafiya a gidan nan. Inba haka ba wlhy police station zan kai su. Ai acan dole su fito da ita ya arziƙi ko tsiya.”
    Daga haka ta miƙe fuuu tabar falon. Shima Abbas miƙewarsa yay ya fice. Baby ta taɓe baki itama ta miƙe ta fita. Bibaa dai bata tashi ba, amma itama sai harare-harare take. Gaba ɗaya yanayin Abba ya sake sauyawa, sai dai mun san babu abinda zai iya. Ilai kuwa hankalinsa ya maido kammu. Babu kunya babu tsoron ALLAH ya shiga faɗin, “Ke Samraah ki fito musu da sarƙarsu ko ki faɗi ina kika saida aje a amso kinji, wlhy wannan fitinar ta isheni. Ku barni da abinda ya daman mana”.
          Kai Yaya Musaddiq ya girgiza kawai, yayinda ni kuma nakema Abban wani kallon takaici da baƙin ciki. Zanyi magana Yaya Musaddiq ya dakatar dani da faɗin, “Amma Abba bai kamata dan an nema wani abu an rasa ace Samraah ce ta ɗauka ba tunda ba ita kaɗai bace a gidan. Sannan ba kuma taɓa kamata akai da halin ba balle a kafa hujja da ita ɗin ce ba. Idan Samraah ta ɗauka sarƙa mizatai da shi. Karfa a manta tana aikinta, sannan ma kowa shaidane Mom bata taɓa barin tsakanin ni ko Samraah da Hafizzullah mu shigar mata ɗaki tun muna ƙanana. Amma tunda har kaima ka yarda da ita ɗince ta ɗauka ita Mom ɗin ta faɗin kuɗin sarƙar tata in sha ALLAHU za’a biyata. Amma kuma da ga yau zamu cigaba da gayama ALLAH kuma zamusa a tayamu kafin wani a cikinmu yabar duniya ALLAH ya tona asirin wanda ya ɗauki sarƙar”.
        “Amin ya rabbi, ba addu’a a Nigeria ba ku tafi gaban ka’aba kuyi mara mutunci. Ai dama na daɗe da sanin kaima ƙwallen shege ne nata ne kawai ya fita ita fitsararriyar. Sarƙata kuma naira dubu ɗari huɗu na sayeta sai a biyan kuma bana son ya wuce yau ɗin nan. In ba hakaba wlhy kaiwa police station babu fashi”.
     Murmushi kawai Yaya yayi, batare da yace komai ba ya miƙe. Kallona yay ya ce, “Tashi ki tattara kayanki ki maida ɗaki zanje na dawo”. Daga haka ya fice ni kuma na miƙe na shiga tattara kayan. Baka jin komai a gidan sai banbami da masifar Mom da zagin da take loda mana. Amma Abba kamar an ajiye gunki domin ado ko uhum bai sake cewa ba. Ni dai na tattare komai na nufi ɗaki, dan tuni na daina hawaye sai zuciyata dake wani irin suya da ƙuna tare da sake jin tsanar gidan da kowama na cikinsa. Yanda zuciyata ke mun zafi da raɗaɗi ji nake kamar nai kiran Mansoor nace masa gobe iyayensa suzo a tsaida bikinmu sati ɗaya kawai. Ni ko babu wani biki a ɗaura auren kawai na tare. Amma dai na dake dan bazan iya hakan ba, hasalima ni ban taɓa nunama Mansoor munada wata matsala a gidanmu ba, saboda hakan sirrinane bakuma zan iya tona sirrin cikina ga saurayi ba watarana yay min gori da hakan ko ya dinga kallon ƴan uwana a wulaƙance koda munyi aure. Koma dai mi suke mana su ɗin jininmu ne dai bamu da wanda ya fisu. Shiko wataran zai iya canjawa koma ya ɓata ɓat a rayuwata duk da bana fatan hakan kodan tsananin ƙauna da soyayyarsa da nake ji a cikin zuciya da ruhi na………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓

……Sallamar Yaya Musaddiq da naji a falo bayan sallar isha’i ta sani miƙewa daga kwancen da nake zazzaɓi ya rufe ni. Nasan kuma ba komai ya jamin hakan ba sai caskalen da mukayi dan da gaske naci duka a wajensu. Daga inda nake na zubama Yaya Musaddiq daya dire baƙar leda a gaban Abba idanu na dake cika da ƙwalla. Yayinda kunnena ke sauraren abinda yake faɗa.
       “Abba ga kuɗin sarƙar nan a bata. Naira dubu ɗari huɗu ne kamar yanda ta faɗa”. Daga haka ya miƙe ya nufi hanyar fita. Cikin sauri na take masa baya batare da nabi takan shewar da Mom keyi ba kuɗin daya ajiye ɗin a hannunta dan bata bar Abba ko taɓawa yayi ba. “Yaya!”. Na kirasa da sauri ganin bai san ina bin bayansa ba. Tsayawa yay tare da juyowa yana kallona. Ina isa garesa na kamo hannunsa na wani ƙankame ina mai fashewa da kuka mai ƙarfi. Shiru kawai yay yana kallona. Tsahon minti ɗaya batare daya ce komai ba ya kama hannuna kawai muka nufi ɗakinsa. A bakin tabarmarsa ya zaunar dani, sai kuma ya sake fita batare da yace dani komai ba nan ma. Tun ina kuka daga zaune har na zame na kwanta Yaya bai dawo ba. Sai da ya ci kusan mintuna goma sha biyar sai gashi da ledar magani da dafaffiyar indomie. Zuwa sannan nabar kukan sai jan ajiyar zuciya nake kawai.
     Abincin ya tasani gaba mukaci tare cikin lallashi, ya kuma bani magungunan nasha suma da ƙyar dan bana son magani, allura kam tsoron da nake mata ai ba’a magana. Ganin baida niyyar cemin komai har sannan akan kuɗin daya basun muryata na rawa nace, “Yaya ina ka samu kuɗi ka basu bayan kasan kuma ban aikata ba. sharrinsu ne kawai ya tashi ko kuma makircin Mom dan ta samu kuɗin dama”.
     Ɗan murmushi ya saki tare da ɗora hannunsa a kaina. “Ki kwantar da hankalinki kada kuma ki damu da abinda sukayin, tunda ALLAH yasan bake kika ɗaukar musu kaya ba ya rage nasu. Bana son naga kina wannan kukan sam. Kuɗi kuma wanda nake asusune dama akan hidimar aurenki tuni, ALLAH zai kawo mana mafita kafin lokacin dan shi mai rahama ne mai jin ƙai, dan ko a yanzu da suka amshi wannan nasan bazamu kunyata ba daga abinda ta rage mana. Kar kuma ki saka abinda sukayi ɗin a cikin ranki ko kice sai kin rama dan na sanki kuma bajin magana kike ba, ki bari UBANGIJI da kansa ne zai rama miki wannan faɗan, dan bazan gushe ba ina mai kai masa ƙarar su garesa, kasancewar sa Sarkin daya haramta zalunci a karan kansa balle ga bayinsa nasan bazai barsu ba Samraah. Ki cigaba da haƙuri kinji, watarana sai labari, komai zai shuɗe tamkar ba’a taɓayi ba. Kwana nawa ma ya rage miki a cikin gidan, ƙarƙari ki ƙara wata biyu fa, dan ko yau mun sake magana da Mansoor a weekend ɗin nan iyayensa zasu sake dawowa a tsaida rana, dan su sun ma so ayi komai a randa sukazo Abba ne bai basu haɗin kai ba. Ke dai kawai ki cigaba da haƙuri, dama in aski yazo gaban goshi yafi zafi”.
       Wasu hawayen ne masu zafi suka sake ɓalle min, Yaya Musaddiq yasa hannu yana sharemun da murmushinsa. Wanda ni nasan yana yinsa ne kawai amma shima ransa a ɓace yake matuƙa. Dan idanunsa jazur suke sosai…..

   
💦💦💦💦💦💦
  
     Da ƙyar Sani ya iya nutsuwa Hayatu ya masa bayani dan shigar 500k ɗin nan a account ɗinsa ta rikitashi matuƙa, daɗin daɗawa kuma Hayatu ya ƙara masa da 100k ƙyauta injisa kash a hannu. Ga kuma key ɗin mota da zai yi aikin da ita. Sai kawai Sani ya fashe da kuka. Dan abunne yazo masa ɓakatatan babu zato. Harga ALLAH zai iya rantsuwa bai taɓa ganin dubu ɗari biyar a dunƙule ba. Dan su talakawane sosai, ko karatun nan yayisane da ƙyar cikin buga-buga saboda yana matuƙar son yin karatu a rayuwarsa. A hakanma da ƙyar aka kammala, dan dai ALLAH ya bashi ilimine ma dan yanada basira sosai.. Kasancewar Hayatu har gida yaje yayma babansa bayani akan ogansa ya ɗauki Sanin aikin tuƙi koda yaje gida da mota babu wanda ya tambayesa, sai ma murna da suka taya shi. Kuɗi kuwa ko na wajen hayatu ma bank ya wuce aka saka masa su. Da dubu ashirin kawai ya shiga gidansu kamar yanda Hayatu ya bashi shawara, gaba ɗaya a yinin wannan ranar bakinsa yaƙi rufuwa. Motar ya kai aka duba kamar yanda Hayatu ya umarcesa, bayan an tabbatar komai zam ya koma da ita gida…

       
🌟💞🌟💞 🌟💞 🌟

      A ɓangaren su Hayatu da ogansu Maash kuwa babu wanda ya sake saka shi a ido sai da la’asar, dan shi baya sakaci da ibadarsa, duk wanda ya san Maash ya sanshi akan hakan. Mutum ne mai matuƙar riƙo da ibada, ko’a tsakkiyar taron turawa yake, komai muhimmancin kasuwancin da yake in har lokacin salla yayi sai yay excusing kansa ya fita yayita, koda kuwa zai iya rasa wannan kasuwancin ne hakan bai damesa ba. Koda ya dawo sallar ma ciki ya koma abinsa. Sai bayan sun dawo sallar isha’i ne Hayatu ke sanar masa saƙon da gidan tv’n ALHERI suka turo game da amsa gayyatarsu da yayi. Sun buƙaci ya bada lokacin da duk yake so daga takwas na safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu har zuwa tara na dare.
      Sai da yay ɗan jimma kamar bazai tanka ba kafin ya kalla agogonsa. Da wani salon lumshe idanu dai-dai yana ɗagowa ya furta, “Ƙarfe nawa Abubakar zai zo?”.
     “Eh Sir kamar yace zuwa four na pm ne. Dan zai baro Abuja kamar Three”.
    “Kafin lokacin akwai wani abu ne?”.
     “A’a gaskiya. Dama dai ganawa da Senetor Kibiya ne, kuma kace Juliet tai magana da shi.”
           “Okay ka sa musu ten to eleven kawai. Dan awa ɗaya zan iya basu”.
     “Ai hakama sun gode Sir”.
   Hayatu ya faɗa yana danne mamakinsa. Da ga haka Maash bai sake tankawa ba. Dan haka Hayatu ya fice ya barsa dan ya huta…..

(◕‿◕)➜(。◕‿◕。)➜(◕‿◕)

         Washe gari Monday da ƙyar na iya danne zuciyata nai aikin gidan kafin nai shirin fita. Nayi aikinne kawai dan nasihar Yaya Musaddiq. Ina kammalawa kuma ko karyawa ban ba nai ficewata. Na samu shima Yaya Musaddiq ya shirya, dama yace min yanada uziri akwai aikin wani mutumi da zai ƙarasa saboda yau da safe zai zo ya amsa motarsa. Tunda muka fara tafiya babu wanda ya tankama ɗan uwansa tun bayan gaishesa da nayi, a haka har muka iso. Yana ajiyeni ya bani 1500. Godiya na masa na shige shi kuma ya wuce.

        Sani da tun fitowarsu gida yake biye da su daga can nesa da wajen ya samu waje yay parking. Kujerar motar ya kwantar abinsa yay kwanciyarsa ya buɗe data da sabuwar wayarsa daya siya jiya. Tunda yanzu babu aikin wahala ai kuma abinyi ya samu kenan. (🤣)

      Ina shiga office ɗinmu na samu kira office ɗin MD. Takaici kamar nace bazanje ba amma dai na miƙe dan nasan hakan bai dace ba. Kamar yanda na saba sai da nai sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. A ciki na samu wata ma’aikaciyarmu mai suna Bashira, tunda na fara aiki a gidan nan nake ji ana faɗin son MD take kamar ta mutu. Amma shi yaƙi bata haɗin kai. Ina shiga da harararta na fara cin karo, ni saima taban dariya, amma dai banyi ba na ɗauke kaina kawai dan ba itace a gabana ba. Batare dana sauke face mask ɗin fuskana ba na ce, “Good morning Sir?”.
        A sake ya amsa min da “How are you?”. Kamar bashi ne jiya ya gama tijareni harda korana a office ɗinsa ba. A taƙaice na ce, “Alhamdullah Sir ance kana kirana”.
       “Eh zauna”.
    Ban musaba na zauna saboda ganin cika da batsewar da Badhira keyi. Sai da na zauna a daƙile nace mata, “Morning”. Duk da tana sama dani. Aiko harzuƙa naga ta sake yi. Sai dai kafin tace wani abu MD ya tari numfashinta da faɗin, “Uhhm inaga na gama da ke ko Bashira, zaki iya tafiya zuwa anjima zan shigo department ɗin naku dan ina son ganin yanda zakuyi aikin”.
       Kamar bazata muƙe ba sai kuma dai ta tashi a fusace tana cewa, “Okay”. Fuuu ta fita a office ɗin harda bugo ƙofa ji kake jifff. Daga ni har shi ƙofar muka kalla, ya girgiza kansa ni kuma na taɓe baki. Sai kuma ya kallan yana yin ƙaramar ƙwafa. “Sam bata da wayo. Ban cika son mace shasha mara aji irin haka ba”.
    Ban tanka masa ba ni dai, dan babu abinda ya shallan sunfi kusa. Nima ban wuce ya zagan da abinda yafi haka ba tunda dai namiji yake. Ganin ban tanka ba shima sai ya saki batunta ya kama wani. Cikin lallashi ya ce, “Samraah sam banji daɗin abinda kikayi jiya ba ga babban mutum irin professor K/Mashi ba. Mutum ne mai mutunci da dattako. Yanda kike zatonsa sam ba haka yake ba. Kuma bada wata manufa ya mana wannan ƙyautar ba face dalilin abinda kikayi a wajen taron jikansa. Yaji daɗin yanda kika sakashi ya maganantu har ya amsa zaiyi hira da wannan gidan tvn namu. Maganar yin tasa hirar kuma bawai a jiya ne aka shiryata ba. Dama mun jima da tura masa goron gayyatarmu har a karo uku tun sanda akai wannan dogon yajin aikin na wata biyu daya shuɗe har yaya wata magana akan gwamnonin arewa datai matuƙar tada hazo amma yana bamu haƙuri saboda baya ƙasar, yana india ganin likita ne. Yanzu haka a jiyan kuma daga can nan ya sauka saboda taya jikansa murnar buɗe company da kuma amsa gayyatarmu. Kuskuren da aka samu dai shine da yace ba zaiyi hira da kowa ba sai ke saboda abinda kika yi a jiyan ya matuƙar ƙayatar da shi”………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆

…….A karon farko na sauke ajiyar zuciya. Sai kuma a hankali na ce, “Kayi haƙuri Sir an samu kuskuren fahimta ne kawai saboda ni bakamin bayanin komai ba. Kuma nima banƙi amsar ƙyautar tasa da wata manufa bane, kawai dai albashin da ake bani ya wadatar dani”.
       “Humm kuma gashi ya dawo min da abinda ya bakin akan lallai na maida miki. Na kuma baki haƙuri tare da roƙonki kan ki amsa dan ALLAH.”
    “Gaskiya bazan amsa ba Sir kuyi hakuri. Dan Yayana zai ɓata min rai matuƙa. Nima kuma a karan kaina ma nayima kaina alƙawari a gafarce ni”.
       Shiru kawai yay yana kallona. Nasan mamakin taurin kaina yake yi. Dan har fuskarsa ta fara nuna jin haushi. Sai dai bai sake cewa komai ba akan batun face, “Okay ba damuwa. Sai batun mutuminki, a jiya PA ɗinsa ya turo mana takardar amsar gayyatar da kikai masa. Tare da bamu zaɓin lokaci amma kada mu wuce yau. Adai taƙaice yanzu haka ya tabbatar mana zai shigo kafin 11am, amma awa ɗaya kacal zai yi da mu. Dan haka yanzu zaki je ki kasance cikin shiri, nama su Tsanyawa magana akan su shirya kayan aiki da zauren da zaman zai kasance. A yanzu haka kuma sun fara in sha ALLAH”.
          Har cikin raina sai da naji zantukansa na dukana. Amma sai na dake na amsa masa da to kawai. Shima bai sake cewa komai ba ya miƙamin takardar gabansa. “Ki nazarci wannan, idan kina da wata idea sai ki ƙara, nan da awa ɗaya ki kawo min na gani. Zaki iya tafiya”.
       Zaram na miƙe kuwa na fice abina ko waiwayensa banyi ba. Zuciyata kuwa sai wani irin kai-kawo take. Ina fita kuma na dallama office ɗin harara. Ɗagowar da zanyi muka haɗa ido da Bashira, ashe tana tsaye a wajen bata tafi ba. Ko takanta banbi ba dan ba’itace a gabana ba nai wucewata a raina ina faɗin (Ballagaza kazar sakarai). Koda na koma office duk yanda naso samun damar tunani hakan bai yiwu ba. Dan su Ruƙayya tuni sun baibayeni da surutu akan ɗan ta’addan mutumin can mai kisan kai dako sunansa ban riƙe ba. Bana kuma fata ko ra’ayin riƙewar ma. Dan haka nafi maida hankali akan aikin gabana fiye da hirar tasu dan dama ba tofawa nake ba. A haka har lokacin da MD ya ban ya cika. Miƙewa nai na fita maida masa file ɗin. Yanda naga yana faman washe baki na tabbatar da abinda nai ɗin ya masa. Dan a take ya ɗaga waya yay kiran sauran wanda zamuyi aikin tare. Bayani ya sake mana ta yanda zamuyi komai ya ƙayatar ya kuma sake ɗaga kimar gidan namu. Ni sai ma naji kamar na makesa. Dan na fara saka MD a cikin jerin sunayen mutane mayun kuɗi. Jiba yanda yake rawar ƙafa tamkar zai ci da ka. Yana sallamar mu muka fice zuwa inda aka gyara domin gabatar da shirin. Makeup ɗin da akace na ɗanyi ƙi nai, sai ma shashsha musu ƙamshi nake famar yi. Sai da MD ya dinga lallashina sannan na ɗan sake saka fauda da ɗan lips gloss, daga haka ban sake bi takan komai ba na nema waje na zauna.

       10:42am dai-dai aka sanar da isowar sa. Gaba ɗaya wanda ke a ɗakin MD yace mu fita a tarosa. Ko motsi banyi ba. Bamma da alamar hakan. Ganin MD na ƙoƙarin maido hankalinsa kaina nai saurin miƙewa nace zanyi fitsari. Babu yanda suka iya dani dole suka barni na fita zuwa bayi, su kuma suka fita tarbosa. Sai da na kwashe mintuna biyar da nake jin tabbacin duk ƙasaitarsa ya riga ya shigo sannan na koma. Har yanzu face mask ɗina na a fuskata dan haka baka isa gane yanayina ba. Tun kafin na ƙaraso na fara cin karo da gardawansa. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina, dan ganinsu ma takaici yake sani. Yo banda rashin tawakkali miye na ajiyesu shi ba jami’in tsaro ba, shiba jinin sarauta ba, kawai dai giyar kuɗi da iyayi. Koda yake maybe al’adarsu ce hakan, tunda naga shima kakansa da nashi shekaran jiya. Baki na laɓe dai na ƙarasa shiga cikin takuna na nutsuwa da kowa kema kallon na yanga. Kaina tsaye na koma ɗakin da za’a gabatar da shirin, iya ma’aikatan mu kawai na samu a ciki suna ƙara gyagygyarawa. Ciki-ciki na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙarasawa ciki. Ban tambayi kowa ya iso ko bai iso ɗin ba. Sai Usman ne yay tsulum yana faɗin, “Sam-G ki kasance cikin shiri baƙonmu na office ɗin MD yanzu haka. Nan da ƴan mintuna zasu shigo nan”.
       Cikin taɓe baki na ce, “In dai ba mala’ikan mutuwa ne zai zo ba kuma dai Usman ai shirina yayi”.
     Dariya ya sanya ƙasa-ƙasa. Ni kuma na cigaba da duba takardar hannuna. Goma da mintuna hamsin da biyar dai-dai Tsanyawa ya shigo yana sanar mana gasu nan tafe shi da MD. Sake kimtsawa kowa ya shigayi, banda ni kam, dan ko motsi banba daga yanda nake zaune balle na cire idanuna daga takardar dake a hannuna. Duk da face mask dana saka bai hana turarensa dukan hancina ba. Wannan dai fitina da yawa take, nikam bana rabe muku ɗayan biyu shima turaren na jinin tsafi ne shiyyasa yake danne ƙarfin duk wani turare idan mai shi yana waje. To nidai gaskiya ba yafewa zan ba, dan nawa kamfanin turaren suna iya nasu ƙoƙari suma. Jin yanda ɗakin yay tsitt kamar babu mutane yasa takaici sake kume ni. Chewing gum PA ɗin nan nasa ne ya fara shigowa, dole ne a kirasa chewing gum saboda koda yaushe dai yana manne da shi. Kusan a tare suka shigo da MD, sai wani rawar jiki yake da ƙanƙan da kai abin takaici. Duk wanda ke a zaune miƙewa sukayi, banda ni da takaicin MD ya sani ɗauke idona da nake musu kallon ƙasa-ƙasa da ban san mike faruwa ba. Ashe su Usman da ke zaune a inda nake duk sun tashi wai domin girmamawa.
         “Samraah!”.
    MD ya kirani ƙasa-ƙasa, banji ba dan haka Usman dake tsaye ta gefena ya ɗan bubbuga kujerar. Da farko sharesa nayi, dan nazata surutunsa ne ya tashi, ganin ya cigaba na ɗago ina harararsa. Idanunsa ya ɗan rumtse cikin yanayin matse fuska tare da mun nuni da MD ƙasa-ƙasa. Sai lokacin na lura da kallon da MD ɗin ke mun. Kowa na ɗakin nabi da kallo, ganinsu duk a tsaye shi kaɗaine zaune a inda za’a gudanar da program ɗin PA ɗinsa tsaye a kusa da shi ya ɗan ranƙwafa yana nuna masa abinda ke cikin tab ɗin hannunsa ya sani miƙewa batare dana sake kallon MD ba na ce, “Sorry Sir”.
     Kansa kawai ya ɗan girgiza da mun nuni da can ɗin. Komai ban sake cewa ba na wuce inda zai kasance nawa mazaunin. Kujeru ne guda biyu kacal suna ɗan facing juna kaɗan, sai table a gabansu an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan kallesu dan koda na zauna ban tanka musu ba ban kuma cire face mask ɗin fuska na ba. Yau ma dai suit ɗinne jikinsa milk colour, rigar ciki, belt da takalmansa ne kawai suka kasance coffee. Sai wani almurin agogo dake hannunsa da duk da ban san kuɗin agogo ba a kallo guda zaka san ba’a sayesa da kuɗi kaɗan ba. Dan coffee fatarsa ma kawai ka kalla kasan ba’a magana. Yau ma babu kitso bai kuma ɗaure gashin ba. Ya sakesa ne kawai baya ya sakko masa har akan kafaɗa kaɗan, akwai kuma coffee ɗan kunne ɗaya a kunnensa na dama yau ma ya manna. Sannan babu neck tie, maɓallan ma rigar cikin ta sama a buɗe suke…. Umarnin cire face mask ɗin fuskata da aka bani ya maidoni hayyacina. Cikin taɓe baki na janye idanuna dake cikin eyeglasses daga kansa ina yin abinda akace ɗin, dan lokacin fara gabatar da shirin yayi. Shima PA ɗin nasa wajen ya bari, yayinda ɗaya daga cikin abokan aikina ya ƙaraso gabansa, cike da ladabi ya maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima miƙomin yay na maƙala a jikin hijjab ɗina. Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. MD ne cikin yanayin marairaicewa yay mun alamar na ɗan saki fusakata, jinai kamar na hararesa, amma na dake kawai cikin basarwa. Kamar bani ba, tuni yanayina ya koma zuwa sauƙaƙa fuska, sai da na kalla camara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan lokaci da musu albishirin shiryawa tsaf domin ganin babban kamun da wannan shiri yayo musu yau a bazata sannan na juya garesa a yanayin jan class ɗina na ce, “Assalamu alaikum ranka ya daɗe”.
       A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa’alaikissalam” cikin muryar nan tasa a daƙile. Bazaka taɓa fahimtar kallona yake ko ba hakaba, saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, “Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin ciki matuƙa na cika alkawarin amsa gayyata a cikinsa a lokacin da kowa baiyi zato ba. Na tabbata hatta masu kallo ma zasu kasance cikin farin ciki maybe ma harda mamaki. Amma dai barkan ka da zuwa”.
       Nan ma a takaice ya furta, “Barka. Tare da fatan alkairi ma kowa”.
    (Ɗan rainin hankali) na faɗa a zuciyata. A zahiri kam na ce, “Masha ALLAH. To masu kallo, zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu.” Sake juyowa nai garesa ina faɗin, “Ko zamu iya sanin cikakken sunanka ranka ya daɗe?”.
      Cike da wani salo da sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Awwab El-Mu’azz K/Mashi. Sai dai Maash akafi sani”.
    “Aiko nasan masu kallo zasu so sanin minene ma’anar Maash ɗin nan ranka ya daɗe?”.
       Sai da ya bushi iska na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya ce, “Kwanar Mashi ne ainahin sunan tushena kenan, abokai suka maida shi Maash tun ina secondary school, daga nan kawai ya zama ana kirana da shi”.
     “Uhhm Masha ALLAH. To ko zamu iya sanin wanene Maash a takaice. Dan wannan amsa ce da mutane suka jima suna son ji daga bakin ka amma basu samu damar hakan ba?”……..✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙

…….Ɗan jimm yay kamar bazai amsa ba, sai kuma ya kai hannu ya shafa ƙasunbarsa. Duk da glasses dake idonsa sosai nake jin kaifin idanun nasa yanzu kam a kaina. Amma sai na basar. Cikin yanayin rashin mafita da gurɓataccen harshensa ya bani amsa yana gwamutsa hausa da turanci sai na gyara masa ma wani lokacin.
      “Awwab El-Mu’azz shine Maash. Asalin ɗan jihar Kano girman Lagos. Karatu zuwa matakin masters, wasu courses sun biyo baya duka dai a fanin kasuwanci. Ɓangaren karatun addini ma Alhamdullah. A yanzu haka business man”.
       “Masha ALLAH. A yanda dai kake bayanin zabbirgewa, da daɗin saurare, sai dai a zahirance kafin aga Maash a haka nasan ansha gwagwarmaya bata wasa ba. Tare da ƙalubale kala-kala. Shin yaya ma akai ka fara kasuwanci?”.
      “Business tamkar logo ne na family ɗin Ummie na. Kusan zan iya cewa na gada ne daga wajenta. Dan tun ina mitsitsi na nake ganin yanda take tsaye akan ƙafafunta ita da mahaifinta, grand father ɗin a kenan, sai hakan ya zaburar dani tashi akan wannan burin, kuma Alhamdullah yanzu an cimma buri. Batun ƙalubale kam ga duk wani rai mai numfashi koda bai tashi da nufin motsawa ba sai an fuskanta, amma Alhamdullah komai ya zama tarihi, dan ko yanzu haka an cimma burika da yawa harma da waɗanda ba’a tsara za’a cimmawa ba”.
         “Gaskiya ne to Alhamdullah. Kafin yanzu Maash na kiran kansa ne kawai da suna bakano ɗan arewacin Nijeriya, sai dai mutane na ƙorafe-ƙorafe game da ko gidan kiwon tsuntsaye bai taɓa samarwa a arewacin ba duk da yanda ALLAH ya baka damar baza harkokin kasuwanci a duniya. Sannan ko cikakken Hausa ma bai iya ba. Shin ko Maash nada wani dalilin hakan?”.
    “So babu wani dalili gaskiya. Kawai lokacin yin hakan ne baiyi ba, amma yanzu yayi ai gashi mun fara. Za kuma mu cigaba da yi in sha ALLAHU. Batun yare kuwa kowane ɗa kan fara tashi ne da yaran mahaifiya. Kasancewar mahaifiyata ba yarenta bane yasa na samu rauni a kansa, amma nasan ko yanzu zan iya fafatawa da kowa a kansa”.
         Dariya maganarsa ta ƙarshe taban. Amma sai na dake na ce, “Kai ashe kace mu sake shiri bayan Companyn ƙera motoci akwai wasu ire-iren sa tafe ma kenan?”.
    “Haka muke fata a cikin tsare-tsaren mu.”
    “ALLAH ya cika buri”.
A saman lips ya amsa min da “Amin”.
    “Mi ya ja hankalin Maash buɗe katafaren Company irin haka a Kano da ba’a taɓa zato ba? Sannan ko Maash zai iya dawowa da rayuwarsa garin Kano gaba ɗaya?”..
   “ALLAH ya rubuta anan ɗin ne za’a samar da shi. Idan ALLAH ya ƙaddara hakan kuma game da dawowa ɗin mizai hana”.
       “Ko Maash nada aure?”.
  “A kasuwa yake”.
“A saka tallarsa kenan ko za’a samu wacce zata saya?”.
      Fuska ya ɗan tsuke. A ɗan daƙile ya furta, “Ba’a gaji dani a gidanmu ba ai”.
      (Wama zai so ka ɗan rainin wayo) na faɗa a zuciya. A fili kuwa sai na murmusa kawai na cigaba da faɗin, “Miyasa Maash baya son hira da ƴan jarida duk da suna ƙoƙarin ganin anyi hakan kodan tarin masoyansa da matasa irinsa da ake fatan su kallesa matsayin madubinsu?”.
        Shiru yay baice komai ba, kusan minti ɗaya sannan ya furta, “Nothing”. A daƙile.
   Nima a karan farko na ɗan kafesa da idanuna dake cikin glasses mai haske, dan sam ban gamsu ba. Amma sai MD dake bayan fage yay min nunin na barsa. Jinai kamar na dalla musu harara su duka. Amma na dake na cigaba da faɗin, “Wane kalar kaya Maash yafi so?”.
        “Kowanne”.
    “Abinci?”.
“tuwo”.
Wani kalar ɗan waro manyan idanuna nai waje a kansa. Shi kuma ya ɗan ɗauke kai cike da basarwa. Nima sai na ɗan basar ɗin kawai. Na cigaba da faɗin. “Wace shawara zaka bama matasa irinka dake tasowa?”.
        “Su zama masu jajircewa, juriya akan duk abinda suka sa gaba, dan kayi karatu ba dole sai kayi aiki ba. Dan ka fara business ba dole sai kayi kuɗi kamar ƙyaftawar ido ba. Ka kasance mai Gaskiya akan komanka, neman zaɓin ALLAH da haƙuri akan halak duk ƙanƙantarsa. Ka kuma zama mai tarin wadatar zuci, dan in babu wadatar zuci ko zaka cika duniya da dukiya zakaita jin baka gamsu ba ne. Shaye-shaye baida wani amfani face maida matashi bayan baya a cikin al’umma. Shi iskanci ba’a koyansa, kowa da kake gani zai iya yi, zama mutumin kirki shike da matuƙar wahala, sai mu faɗama kammu gaskiya kafin duniya ta faɗa mana”.
       “Masha ALLAH muna godiya da wannan shawara. Minene buri, ko nace shirin Maash na gaba?”.
    “Maash nada tarin burika da shirye-shirye masu yawa da shi kansa bai san adadi ba. Amma manya daga cikinsu a dai yanzu sune samar da companys da zasuna fitar da abinci kowane nau’i in sha ALLAH. Zamu fara tsara komai a yanzu haka, muna fatan kuma zuwa ƙarshen shekarar nan komai ya zama ready”.
      “Ko zamu iya sanin a ina wannan babban project ɗin zai kasance?”.
    “Duka anan arewa ne in sha ALLAHU. Amma sai lokacin yayi za’a sani”.
       “ALLAH ya cika buri”.
    “Amin” ya amsa a taƙaice.
“Mi Maash yafi so a rayuwarsa?”.
           “My Parents”.
      “Miye baya so?”.
“Cin amana”.
“ALLAH ya hanemu zama masu fuska biyu” na faɗa a yanayin kalma mai harshen damo ina ɗauke kaina daga kansa. Juyawa nai ga camara, fuskata ɗauke da ɗan murmushi na ce, “To masu kallonmu, gadai hira ta kwararo cike da daɗi, sai dai lokaci ya mana tsiyar tasa. Amma zance ku zama a cikin masu fatan wataran Maash ya sake zama a wannan kujerar domin amsa muku tarin tambayoyin dake a ranku da bamu kawo a wannan dandali ba yanzu saboda ƙarancin lokaci. Amma dai, ko a hakan ma mun gode, dan ALHERI TV ta kafa babban tarihi”. Sake juyawa nai garesa, na ce, “Ranka ya daɗe mun gode sosai da cika alkawari. Muna fatan ALLAH ya maidaka gida lafiya. Zaka iya yin sallama da masu kallo suma”.
        Hannu kawai ya ɗaga yana mai sakin murmushi kaɗan ya ce, “Fatan alkairi”.

     Ana ɗauke camara daga kammu ya wani sauke numfashi mai ƙarfi yana furzar da shi tare da jan siririn tsaki. Yinai kamar ma ban san da shi a wajen ba. Dan kafin ya tashi tuni na miƙe ni ina ɗaukar ruwan da aka ajiye mana da babu wanda yasha nabar wajen. Ban tsaya a ɗakin ba na fice gaba ɗaya. Office ɗinmu na koma. Bayan kamar mintuna sha biyar sai ga su Asiya sun shigo. Baibayeni sukai su duka har Usman da Khalid. Kowa na jinjina ƙoƙarin da nayi. Tare da nuna zumuɗinsu na fatan zuwan randa za’a saka shirin wa kowa dan su sake kallonsa a tsanake. Murmushi kawai nai musu nidai bance komai ba. Aikinmu muka cigaba dayi, har lokacin sallar Azhar yay muka fito gaba ɗaya. Bayan idar da salla kamar yanda muka saba na haɗu da Mansoor. Fita mukai restaurant ɗin kusa da ma’aikatar tamu cin abinci kamar kullum. Kusan a tare muka shiga da wani saurayi shima fuskarsa da fase mask. Bai mana magana ba bamu masa ba, kowa ya nema wajen zama ya zauna.
Munci abincinmu cike da nishaɗi muna ƴar hirarmu. Bayan mun kammala muka fita. Mun koma office kan ayyukanmu. Banfi zaman mintuna biyar ba sai ga MD har cikin office ɗinmu Harun biye da shi. Duk miƙewa mukai domin girmamawa a garesa. Fuskarsa ɗauke da murmushi yay mana alamar mu zauna. Shima ya zauna a kujerar dake facing ɗina.
“Sannu da ƙoƙari jarumarmu”.
Ya faɗa idonsa a kaina. Sosai na waro nawa idanun dan mamakinsa. Kasa haƙuri nayi sai da na furta, “Jaruma kuma Sir, sai kace wata ƴar Film?”.
“Ba’a Film kawai ake jarumta ba Samraah. A yau kinyi namijin ƙoƙari ƙwarai da gaske. Na tabbatar duk randa aka saki wannan hirar taku wa masu kallo ba ƙaramin tada hazo zatayi ba. Domin Maash yayi abinda bai taɓa kwatanta yi ba. Da ace kuma zan iya babu shakka sai na tambayesa ko miyyasa ya amince mana?. To amma ina, yana da wata irin kima da girma ga kwarjini mai saka shakkar koda kallonsa ne. Kin cancanci a kiraki kallabi tsakanin rawuna. Kuma in sha ALLAHU a dalilin wannan hirar zakiga babbar karramawa wa wannan gida dama duk wanda suka taimaka a ɗaukar shirin”.
Tafi su Khalid suka shiga yi cikin ihu. Yayinda MD ke faman washe baki shima cikin nuna a nishaɗi yake. Ni dai na tsaya kawai ina kallonsu ne galala. Su dai murnarsu kawai sukeyi basu bi takaina ba, Asiya ce ma dai na ɗan ga yanayinta ya canja, da alama abinda suke ɗin bai mata ba, ko kuma zantukan MD ne suka zafeta oho mata. Sallama MD yay mana ya fita. Ni dai na sauke ajiyar zuciya kawai. Yayinda Ruƙayya ta rungumoni. Duka na kai mata kaɗan, ta sakan tana dariya bayan ta ja min hanci. Babu shiri nayi murmushi nima. Ruƙayya nada kirki sosai. Sannan halayenta na matuƙar burgeni. Shiyyasa a wasu lokutan sai naji kamar nace ma Yaya ya nema auranta dan ALLAH su sasanta. Amma ina tsorom halin maza kada yace bata masa ba. Duk da dai nasan babu wani namiji da zai kalli Ruƙayya yace bata masan ba. Dan ƙyaƙyƙyawar yarinya ce sosai. Tana da haske gata ƴar duma-duma abinta. Itama ta taɓa gaya min mahaifiyarta ta rasu a wajen haihuwarta. Kuma ita kaɗai ta bari, hannun kishiyar uwa ta tashi. Duk da bata fito ta faɗa min duka matsalarta ba na fahimci bata jin daɗin zaman gidansu, sai dai haƙurinta yasa bazaka taɓa gane hakan ba kai tsaye sai in har itace ta faɗa maka…….✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏

……..Tunda suka fito Hayatu ya zuba masa ido ta cikin mirror ɗin gaban motar, dan shi yana zaune ne a kusa da Tijjani driver. A hankali kamar mai ɗan jin shakka ya ce, “Sir ko zamu koma gida ne ka huta?”.
Shiru kamar bazai tanka ba. Sai da ya mula dan kansa batare da ya buɗe idanunsa dake a rufe ba, ko gyara zaman ƙasaitar da yay ya motsa lips ɗinsa kaɗan. “Ba buƙata”. Ya faɗa a taƙaice. Kai kawai Hayatu ya jinjina yana mai haɗiye yawu. Kai tsaye Company suka nufa. Dan akwai zaman meeting da zasuyi sakamakon fara ɗaukar ma’aikata da za’ayi a gobe in sha ALLAHU. Sun samu duk wanda ake buƙatar gani a zaman meeting ɗin yazo. Tunda aka buɗe masa mota kuma ya fita kowa keta ƙoƙarin gaida shi cikin girmamawa. Hannu kawai yake ɗaga musu da bin yanayin wajen da kallo ƙasa-ƙasa. Hatta da turawa da Chaines ɗin da zasu jagoranci aiki a companyn girmamashi sukeyi. Kai tsaye hall ɗin da meeting ɗin zai gunada suka nufa.
Wajene da akai matuƙar tsarawa da ƙawatawa. Sai da ya zauna a babbar kujerar dake tsakiyar dogon tables ɗin sannan suma kowa ya zauna. Ya ƙare musu kallo ƙasa-ƙasa ta cikin gilashinsa ɗaya bayan ɗaya kafin suka fara gudanar da abinda ya tarasu..

 ★ A matuƙar gajiye liƙis suka bar Company bayan sallar la'asar. Koda suka isa gida sun samu baƙonsa Abubakar yazo. Saboda yanda yake jinsa a takure bai iya ganawa da shi ba ma ya shige bedroom. Wanka ya farayi sannan ya ɗan kwanta. Tabbacin ya gaji sosai cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba da shi kuwa. Bai fito ba sai lokacin sallar magrib, sai da kuma akai isha'i ya dawo gidan. A sannan ne yay ɗan zaman awa guda da Abubakar da Hayatu. Suna kammalawa ya bama Hayatu umarnin su shirya jirgin sha biyu na daren yau ɗin nan zasu bi zuwa Lagos. Hakan ba sabon abu bane a gare su. Dan shi duk sanda abu ya kaɗa masa yinsa kawai yake yi, ko dan jirgin nasa ne na kansa yake hakan oho masa . Tunda ma har aka tsaida time ɗin tafiyar yasan Juliet ita ta sani, amma duk da haka bayan ya sanar da guards da Tijjani su shirya sai ya nufi sashen da take. 
   Hayatu na gab da shiga falon wayarsa tai tsuwwa alamar shigowar saƙo. Baibi takanta ba ya ƙarasa. A falo ya samu Juliet ɗin tana waya. Ganinsa yasa ta katse sukai maganar da zasuyi ya fito. Shima nasa masaukin ya nufa domin kimtsawa. Duk da dai akwai ɗan sauran lokaci ma. Daga aljihu ya cire wayarsa da nufin ajiyewa sai kuma ya fasa saboda tuna shigowar saƙon ɗazun. 

       “What!” ya faɗa da ƙarfi, sai kuma ya miƙe da saurinsa cikin sassarfa ya fice. Kai tsaye sashen ogan nasu ya koma. Sallama ɗaya yay batare da jiran izini ba ya afka ciki. Dai-dai nan kuma Maash ke fitowa da ga bedroom ɗinsa kunnen sa manne da bluetooth alamar waya yake yi, yanda ya tsuke fuska matuƙa zai tabbatar maka koma da waye yake yinta bada daɗin rai bane. Kallo ɗaya yay ma Hayatu daya shigo kamar an korosa ya ɗauke idonsa. Cikin kujera ya kai yana wani kalar cije lips ɗinsa. Sai kuma kamar a fusace ya furta, “Nifa ba fushi nake ba Paa. Maganar yarinyar nan kuma nace a barta bana so. Ni ban taɓa cewa ai ina ra’ayin zama da ita ba, kuma ban taɓa cemata ina sonta ba”.
      Ɗan shiru yay alamar yana saurare, sai kuma ya sake ɓata fuska a yanayin shagwaɓa ya sake cewa, “Paa Please mana. Understand me.”
     Sai kuma ya sake yin shiru. Kusan minti ɗaya ya ce, “Okay naji, amma ni daga nan zan wuce Finland ne, bazan dawo ta Lagos ba. Kwana shida zanyi kawai in sha ALLAH”.
      Guntun murmushi ya saki kaɗan, sai kuma a hankali ya ce, “I love you too. Bye ka gaida Ummie da Mamma.” daga haka ya cire bluetooth ɗin yana maida hankalinsa kan Hayatu. Hayatu da dama kamar a ɗofane yake a saman wuta yay wata zabura zuwa gabansa. Cikin rawar hannu ya miƙa masa wayar yana faɗin, “Sir yarinyar nan ce fa ta sake turo saƙo ta number na. Ban san taya ta samu ba, ko yau da mukaje office ɗinsu ne?”.
      Komai baice ba ya amshi wayar. Kasancewar da turanci aka rubata text message ɗin yasa ya fahimci komai. Ya jima bai motsa ba ya ƙurama wayar kawai cat eyes ɗin shi, sai dai fuskarsa ta sake komawa wani bala’in kicin-kicin har blue ɗin cikin idanunsa na ƙoƙarin ɓacewa. Hayatu ne ya katse shirun da faɗin, “Wlhy Sir al’amarin yarinyar nan mamaki yake bani, na jima banga mace mai busashiyar zuciya irinta ba. Just small girl ɗin nan wai tasan yin irin wannan ta’addacin haka. Jiba yau yanda take wani basarwa da shan ƙamshi fa. Ni wlhy dan kawai kace a barta ne ai. Amma har ita wacece da bazamu sa a tattaro mana kaf zuri’ar gidansu ba taga ƙaryar tsagerancin nata. Haba ita wacece da zata zauna tana rainama mutane hankali. Kawai na kira Sani a daren nan ya kawo mana ita gidan nan a amshi wayar tata a gabanta mu goge video ɗin sannan mu danƙata hannun hukuma, muda muke da makami ma a kanta, dan biyowa ta bayan gida fa tai akan hira dakai har yanzu ba’a daina cecekuce a kansa ba a media, wani abun ma nasan sai randa aka saki hirar, tabbacin mutane da yawa na asiri tazo da shi wajen har ka yarda ka amsa matan zai sake gitowa”.
     Shi gaba ɗaya ma surutun Hayatun saka masa ciwon kai yake. Dan haka ya wurga masa wani kallon da ya sakashi nutsuwa, tare da jan bakinsa ya tsuke. Shiru falon ya sake ɗauka kowa na cuɗawa da kwancewa a cikinsu. Kafin shi ya miƙama Hayatu wayar yana faɗin, “Ba buƙatar mata komai a yanzu. Ina son ganin iya gudun ruwanta. Ka amsa mata da za’a bata 500m ɗin, amma a ina za’a haɗu da ita ta bada recording ɗin”.
          “Amma Sir…..”
     Hannu ya ɗaga masa, a daƙile ya ce, “Na gama magana”.
    Yawu mai ɗaci Hayatu ya haɗiye. Sai kuma ya jinjina kansa cikin girmamawa ya ce, “Okay Sir, in sha ALLAH za’ayi yanda kace. Na barka lafiya”. Daga haka ya juya ya fice. Ta gefen ido Marsh ya bisa da kallo. Sai kuma yay wani kalar furzar da iska yana maida kansa a kujera ya kwantare tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan mi yake ji a ransa game da yarinyar nan. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta ba. Amma zai bata lokaci ta gama nata kalar ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin saninsa a rayuwarta a kanta. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba neman kuɗi kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Ko abubuwan data dinga yi yau duk a rubuce suke a brain ɗin, ya fahimci tanada taurin kai da tsageranci. Duk zai sauke mata su kuwa nan bada jimawa ba.
      Ya jima a wajen zaune har Hayatu ya dawo ɗauke da abincin da Sani yayo order. Amma sai yace bazai ci ba. Ya haɗa masa coffee kawai. Umarninsa Hayatu yabi. Ya kawo masa coffee amma ya haɗo da biscuits mai daɗi. Dan yasan waɗan nan sune kalar ciye-ciyen da ogan nasu yafi so a rayuwarsa. Shiyyasa a duk inda yake baka rabashi da kalolin biscuits da chocolates kala-kala masu shegen daɗi. Sabone tun na ƙuruciya ya riga ya kamashi. Sake fita Hayatun yay ya barsa, shi kuma ya maida hankalinsa ga tv yana kallon film ɗin da sukeyi yana shan coffee ɗinsa da biscuit ɗin kamar baya so. Koda ya kammala zamansa ya cigaba dayi har sai da film ɗin ya ƙare sannan ya shige ciki. Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da yay minti talatin cur ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa’i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi uwa kamfanin haɗa turare kamar ba dare ba. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunne. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji. Baiyi mamakin ganin Hayatu a falon ba. Dan duk inda aka gansa dolene aga Hayatun. Duk da yana jin idonsa a kansa bai kallesa ba. Hakan yasa Hayatu ɗauke idonsa shima a ransa yana kirari wa UBANGIJI mahaliccin wannan ƙyaƙyƙyawar halitta, gaskiya dole ma aso mai ƙyau, dan ko shi dake a namiji, kuma ana yawan sanar masa shima ɗin ƙyaƙyƙyawane har ga ALLAH ogansa na birgesa. Dan mutum ne daya san hakkin tsara ado. Ya iya tsara saka sutura ta zauna ɗam ya haskata kuma tamkar dan shi kaɗai ake saƙa kaya irinsu. Ganin zai ɗago da sauri ya wuce sumu-sumu zuwa bedroom dan ya kashe komai ya gyara kuma abinda ya ɓata tunda basu san ranar dawowarsu Kano ɗin ba kuma. Suda suke kullum a tafiye-tafiye kamar ƴan sama jannati………✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕

…….Kamar ko yaushe yau ma Mansoor ne ya maida ni gida, koda na shiga na samu gidan tsitt. Banbi takan kowaba na shige ɗaki, auta na samu yana barci, ga books ɗinsa a gefensa barbaje alamar homework yake barcin ya kwashesa. Ɗagashi nai na maida kan katifa. Sannan na tattare books ɗin na ajiye masa gefe bayan na duba abinda yake. Yaron akwai brain, inba ni ba babu mai zama damuwar koya masa homework, sai idan Abba. Wani lokacin ma sai kika yayi da kansa kafin ma na dawo, sai dai na ɗan masa gyararraki kawai. Wanka nai ƙoƙarin shiga, sai dai bayin duk an ɓata shi, nasan Bibaa ce zatai wannan aikin ba wani ba. Na rasa mike damun kan yarinyar nan, amma zan koya mata hankali. Tanada ɗakinta ita kaɗai amma tsabar shaiɗanci tace tsoro take ji a can, shine Abba yace ta dawo nan mu zauna wai sai ta ƙara girma. Da farko na ɗauka haka ɗinne, sai daga baya na fahimci Mom ce ta sakata yin hakan dan ta dinga ɗaukar rahoton duk motsina tana kai musu. Tun wani lokaci da naji tana faɗama Mom wayar da mukai da Mansoor nagane hakan. Bayin na sake gyarawa sannan nai wankan. Harna fito na gyara jikina banji motsin kowa ba. Ba’a wani ɓata falonba yau sosai, dan haka na wuce kitchen. Shi kam yana nan jibge da kayan wanke-wanke tun daga kofunan kalacin safe har na rana da sukaci. Kaina na girgiza ina mai jin tausayin Bibaa da Baby a rayuwa. Dan ita Mom gani take gata take musu bata san kashe musu rayuwar take ba, haka kullum da rayuwar take a gidan, idan nai aikin safe na fita babu abinda suke kaudawa har sai na dawo na sake yi, badan nima na zama jan wuya ba abincin rana ma sai na musu na saka a kula. Sai da na nuna musu nima tsagerar kaina ce sannan, shiyyasa kullum basu da abincin rana a gidan sai taliya ko cus-cus ko macaroni, indomie. Sai idan akwai stew ne zakiga sun dafa farar shinkafa. Stew ɗin kuma zakiga dole nice zanyita, Mom taƙi yarda a ajiye mai aiki wai ita kishi, randa nayi aure to naga ubanda zai zo ya musu. Kwanikan na fara tattarewa na wanke, ƙafafuna duk sunyi tsami saboda tsaiwa. Haka dai na daure na kammala na maida komai muhalinsa sannan shima kitchen ɗin na shiga gyaransa. Ƙaramar indomie na dafa guda biyu, na raba biyu naci tawa anan na juyema auta tasa a plate. Har lokacin babu wanda ya dawo, mamaki ya sake kamani da tunanin ina sukaje haka ne?.
      Har akai sallar magrib sai mu kaɗai a gidan. Sai bayan an idar Abba ya shigo. Fita mukai ni da auta daya tashi muka gaishesa. Na wuce na kawo masa ruwa na koma ɗaki abina na barsu anan falo. Sun fita sallar isha’i nima zan kabbara tawa naji hayaniyar shigowar su Mom. Banbi takansu ba na tada sallata. Sai da nai har shafa’i da wutiri sannan na fito musu sannu da dawowa. Kaya na tarar barbaje a falon kashi-kashi. Na sakawa dana kwalliya harda na ciye-ciye alamar dai daga kasuwa suke. Ganin hankalinsu baya kaina dan ko gaisuwar ma da kai Mom ta amsa min na juya na koma abina ina mamaki, dan tabbas da kuɗin Yaya na jiya akai wannan sayayyar kenan. Jinai raina ya ɓaci matuƙa, dan haka na fito na wucesu. Yanzun ma hankalinsu babu alamar yana kaina. Ta ihun murnar kayansu suke kawai. Ɗakin Yaya Musaddiq na nufa, yana tsaye da alama yanzu ne yake dawowa massalaci. Ganina rai ɓace ya sashi faɗin, “Jikin ne?”. Kaina na girgiza masa ina kaiwa zaune. Cikin zafin rai na ce, “Wlhy Yaya zancen kuɗin sarƙar nan shirine kawai. Ko kasan matar can yau kasuwa suka shiga ita da ƴaƴan nata gasu can sun baje kaya a falo kamar za’a buɗe kanti. Kasan kuma babu yanda za’ai hakan ta faru Mom ta iya kashe kuɗin sarƙar nan a banza haka da gaskiya ne”.
       Murmushi mai sanyi Yaya Musaddiq yay hana kaiwa zaune kusa dani. Cikin sauƙaƙa murya tare da riƙo hannuna cikin nashi ya furta, “Cool down sweetheart. Sune a ƙasa ai. Bakiji shata na faɗin ku gargaɗi mai gina ramin mugunta ba. Ni nasan dama koda an ɗauki sarƙar ma bata kai ta kuɗin data faɗa ɗin ba. Amma ba komai ALLAH zai bamu wasu. Yanzu ma Abba ya bar ɗakin nan”.
       “Miya faru ya shigo?”.
Na faɗa cikin mamaki tunda nasan dole akwai dalili. Hannuna ya saki yana miƙewa da ɗan taɓe bakinsa. Ya zare jallabiyarsa ya ajiye sannan ya koma ya zauna dan jikinsa akwai dogon wando da t-shirt fara. “Yazo ya sameni akan wai tunda yaga inada kuɗi ni ne ya kamata na miki komai na aure. Dan shi gaskiya yana a cikin damuwar rashin kuɗi. Saboda hakane ma yaƙi yarda su tsaida rana a randa iyayen Mansoor suka zo. Amma da yasan har inada wannan kuɗin haka aida an kammala komai. Dan haka zai kirasu suzo weekend ɗin nan a tsaida ɗin. Na kuma bashi aron 200k zuwa ɗan wani lokaci zai bani..”
       “Kuttt! Amma mutumin nan ko! Wai mike damun Abban nan ne?. Dama ko bai faɗaba waye ke jiran wani abu da ga garesa mtsowww aikin banza. Sannan kuma bashin ka amsa zaka bashi Yaya?”.
    Murmushi Yaya Musaddiq ya saki mai haɗe da dariya, sai kuma ya girgiza kansa. “Kai wannan yarinya masifaffiya ce ke wlhy, wanda basu sanki bane kawai suke miki kallon mai haƙuri. Ni ALLAH har ma na fara tausayin Mansoor bawan ALLAH shi gashi da sauƙin halin tsiya”.
    Baki na tura ina faɗin, “Kai Yaya nice masifaffiyar?”.
      “Ta bugawa ma kuwa a jarida kandala. Wani lokacin da idan kina abu sai naga kamar ma kece Yayar tawa. Shiyyasa Hafizzullah ke cewa da kece Mamanmu da mun shiga uku”.
      Dariya na ƙyalƙyale da shi. Na ce, “Masherancine yaron nan ai. Dan ALLAH Yaya weekend ɗin nan muje mu gansa tunda wancan ya shuɗe. ALLAH ina kewarsa”.
        “Karki damu zamuje in sha ALLAHU. Dan na kammala masa ma siyayyarsa.”
     Cike da farin ciki nace “Yauwa Yayanmu, kuma Babanmu. Yanzu dai yaya mi kacema Abban?”.
       Sai da yay murmushi ya ce, “Mizan ce masa kuwa Samraah. Na gaya masa kuɗin dana bama Mom ɗin jiya ne kaɗai dama a wajena, sai abinda ya rage baifi saura dubu arba’in ba nama cire wani abu a ciki na haɗama Hafizzullah provision. Dama na tara wancan kuɗinne dan na basa shi da Mom ɗin su rage hidimar biki. Ga kuma abinda ya faru yanzu. Ina gaya miki sai kawai ya hauni da faɗa. Wai to wlhy sai nasan inda zan nemo wasu kuwa. Dan shi dai baida wani kuɗin yin hidimar nan bai kuma da hanyar samunsu. Inba hakaba kuwa sai dai a kaiki gidan mijin a haka.. inada yake shiga dai bata nan yake fita ba.”
       Wata shegiyar dariya na bushe da ita harda kwanciya ina hawaye. Yaya Musaddiq kuwa yay sagale yana kallona. Sai da yaga dariyar tawa ta tasamma ta hauka sannan ya ce, “Samraah kin samu motsuwar kai ne?”.
      “Babu wani motsuwar kai wlhy Yaya. Show ɗin ne yay matuƙar burgeni. Su Abba an lallaɓo aci banza. Banza bata samu ba, shine ya ƙare da borin kunya. To waye ya faɗa masa na damu a kaini da kayan ɗaki? Ko cokali ma kada su saya waye zaiji kunya”.
        “Shirme maganinka ALLAH kenan”. Yaya Musaddiq ya faɗa yana girgiza kansa. Da sauri na ce, “Yaya gaskiya fa na faɗa. Ni wlhy ban damu ba amin kayan ɗaki ko a kar ayin. Badai muna son junanmu ni da Mansoor ɗina ba”.
     “Baki da kunya, a gabana kike cewa kuna son juna”.
    Hannu nasa na rufe fuskata ina dariya. Shima sai ya shiga tayani…

        Washe gari koda na kammala aikina na shirya na fito na samu Abba a falo na gaishesa bai amsa min ba. Ko’a kwalar rigata nai ficewata. Yaya ga ɗaukan muka wuce ina bashi labari ina dariya. Shi kam murmushi kawai yayi yace “ALLAH ya ƙyauta”. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gidan Abba babu daɗi sai haƙurin UBANGIJI kawai. Yayinda a waje aiki ke caja kai kuma. Kamar yanda mukai shiri ranar asabar muka tafi Katsina ganin Hafizzullah. Ƙiri-ƙiri Mom ta nuna baƙin cikinta akan hakan. Ta shiga zuga Abba wai ya hanamu zuwa. Sai dai Yaya ya nuna musu babu abinda zai sakamu fasawar. Haka dai muka tafi Mom na banbaminta na rashin gaskiya. Hafizzullah yayi matuƙar farin ciki da ganinmu. Dan harda kukansa na murna. Ya rame saboda karatu, naita tsokanarsa nikuwa muna faɗanmu da muka saba. Tare da shi muka yini. Da zamu wuce masauki kuma ya bimu akan shi tare damu zai kwana. Nan ma raba dare mukai muna hira kafin su koma ɗakin Yaya Musaddiq su kwanta ni kuma nai kwanciyata ni kaɗai muka sha waya da Mansoor dake bani labarin an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za’a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a ƙasan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu ƴancin kaina. Na kuma samawa ƴan uwana. Dan insha ALLAHU Hafizzullah gidana zai koma, Yaya kuwa zan cigaba da dagewa akan yay aure……….✍️
         

Kandala ta malam Mansoor 😘

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆

……..Washe gari kamar yanda Mansoor ya faɗa muna a hanyar dawowa gida ya turamin saƙo na jerarrun kalaman godiya ga ALLAH. Tare da sanar min an tsaida wata ɗaya kacal, nanda kwana talatin in sha ALLAHU na zama mallakinsa. A gidansa zanyi azumin watan Ramadan. Duk da naji farin ciki ban maida masa reply ba, dan ina cikin mood mara daɗi na rabuwa da Hafizzullah. Shima mun barosa harda hawayensa. Munko samu gida cike da kayan sweet, biscuits da drinks a falo. Harda su goro sai akwatina guda biyu. Yanda babu wanda yay min magana akan kayan nima banma kowa ba. Sai auta ne ke faɗamin Uncle Mansoor ya gaya masa kayana ne. Sai kuma habaicin da Baby keta saki ranta a ɓace. A kallo ɗaya da nai mata kuma na fahimci tasha kuka. Ban kulata ba dan ba itace a gabana ba. Washe gari Monday na wuce aiki da wuri. Bayan mun dawo na tarar da Gwaggo Gudidi tazo daga Dawanau. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba da mamanmu kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Yanzun ma shine ya kirata ya gaya mata komai ganin Abba baida niyyar saka danginsa ko ɗaya a batun auren nawa. Ƴan Gwarzo kuwa sun kwashi nasu kason kayan da za’a rabama mutane sun wuce dasu tun jiyan, dan bamu samesu ma a gidan ba. Nayi murna ƙwarai da ganin Gwaggo Gudidi. A take na shiga hidima da ita dan naga babu alamar ko abincin kirki ma an bata. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha’i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da ƴaƴanta kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai Auta da uwar gulma Bibaa kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar Gwaggo Gudidi bata ji ba balle mu ƴaƴa. Shimfiɗata na barma Gwaggo, dan Yaya Musaddiq ya kawo mata babban bargonsa. Zan kwanta a ƙasa tace na hawo kan bargon. Badan naso hakan ba na hau dole. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima Gwaggo na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yaya Musaddiq ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara.
Gwaggo Gudidi itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Auta ya kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kano ta saka Yaya Musaddiq ya kaita ta kai ma kowa. Na Gwarzo ma tare sukaje takai duk na ɓangaren danginsu dai. Yaya Musaddiq ma da Hafizzullah ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama’ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Gwaggo ta wuce bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin Gwaggon yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa.
       A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Mansoor, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yanda muke komai cikin taku. MD kuwa ai kamar zai mutu. Dan masifa yayta zubama kowa a wannan yinin babu gaira babu sabar. Har dai ƴan uwana ma’aikata suka fahimci kishi yake yi. Ni dariyama ya bani wlhy. Mansoor kam yaji daɗin abinda nayi, dan bai ɓoye ba sai da ya sanar min. Murmushi kawai na masa nidai. Bayan an tashi aiki ya buƙaci kaini naga aikin gida da ake ƙarasawa. Amma sai nace masa ba yau ba ya bari weekend zai fi. Shima ya yarda da shawarar tawa. Dan haka ya maidani gida. A ranar ne kuma na fahimci wata farar mota na binmu a baya. Duk da naji tsoro sai banyi magana ba, nace bari dai na tabbatar. Ganin munzo titin shiga layinmu motar ta wuce yasa na sauke ajiyar zuciya har Mansoor na kallona.
     “Lafiya irin wannan ajiyar zuciya haka kamar wadda nai shirin sacewa. Ko tsoro kike kada na wuce dake ne?”.
        “Ai kaima bazaka fara hakan ba sai an baka”. Na faɗa cikin kauda kai ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yay da sake faɗin, “Hakane. Amma da zama a taimaka a banin yau zanfi kowa farin ciki. Maybe ma na ƙara samun ƙarfin aikin yanda ya kamata”.
      “Humm” kawai nace na buɗe motar na fice ina murmushi. Godiya na masa kamar kullum. Yanata son mu haɗa ido amma naƙi yarda da hakan. Sai ma na wuce da sauri na shige gida abina. Amma na maƙale jikin gate ina leƙansa. Yaja kusan minti ɗaya idonsa a gate ɗin fuskarsa da murmushi kafin ya tada motar ya wuce…

      ★★★

   Abubuwa kullum ƙara tsamari suke a gidanmu. Dan kullum al’amarin Mom da yaranta gaba yake yi. Ina sake samun tsangwama da hantara fiye da baya a yanzu sakamakon wannan batun auren. Yayinda Baby ta fito da maitarta akan Mansoor yanzu. Shi kansa ya fara nuna min tana matsa masa. Ashe tun da can ma da bata fiddo abubuwanta fili game da shi akwai abinda take shakka daga garesa, na kuma fahimci wani babban sirrinta ne ya sani duk da yaƙi fitowa fili ya faɗa min.
        Sam ba’a wani shiri irin na aurar da ƴa a gidan, musamman ma mace da bikinta ke da yawan hidima. Ko kaɗan hakan baya damuna. Dan nasan Yaya Musaddiq tsaye yake akan al’amurina ta bayan fage. Dan yanzu kusan duk sati zakiga Gwaggo Gudidi tazo mana. Da alama akwai abinda sukeyi ita da Yayan. Duk da madai ashe shi Mansoor ya samu Yaya akan shi baya buƙatar komai na gida duk zai zuba. Ni shaidace akan abinda ya faɗa ɗin domin ya kaini naga gida. A randa mukaje ɗin kuma na sake kama motar nan na binmu. Hankalina ya tashi fiye da ranar, amma nai jarumtar dannewa saboda kada na tada hankalin kowa. Nayi kuma alƙawarin saka ido sosai dan na tabbatar shin da gasken binmu ake kokuwa zargina ne kawai. Tun daga wannan lokacin na saka ido fiye da koda yaushe. Babbar magana kenan wai ɗan sanda yaga gawar soja, nako tabbatar bibiyata akeyi ɗin. Dan harna haddace Number motar duk da dai mai ita kan canja ne kusan da kala uku, sannan ita kanta motar wani lokacin bada ita ake bina ba da napep ne. Al’amarin ƙuruciya irin nawa da wauta, maimakon na sanarma ko Yaya ne sai nai tunanin kada na tada masa da hankali, gara na fara sanin wanda ke bibiyar tawa dai. Wannan ɗammara dana ɗauka tasa na fara ƙin daina bin yaya na koma shiga napep. Hakama Mansoor wataran sai na ƙi biyosa, ina amfani da yanayin da yake ciki na busy yanzu akan shirin biki. A ranar farko dana fara yin ƙundun balar tarar motar nan sai aka gudu. Karo na biyu ma haka. Ganin haka na sake himma dan a ganina tsorona ake ji. A karo na uku na haɗa kai da ƴan ƙato da goran anguwarmu a ɓoye akan idan ma fita su bini a baya. Na basu numbers na motar da ake amfani da su har kala uku. Abin zai baku mamaki, dan kamar mai motar nan ya fahimci abinda nake ƙullawa ranar sai bai bini ba. Tsahon kwana uku haka na ƙara yarda yaji tsorone na sallami ƴan ƙato da goran. Sai me a randa na sallamesu a ranar na cigaba da ganin motar kuma. Raina yakai ƙololuwar ɓaci. Na fara zargin MD ne kemin hakan ko kuma Abba ko Mom ko Baby. Kai har Mansoor sai da na zarga, to sai dai kuma shi danmi zai sa a bibiyan bayan kullum muna tare. (Bincike) zuciyata ta ayyana min. Ban gamsuba, dan in bincikene ai iyayensa ne zasusa ai musu. Sannan bata wannan hanyar ba, anguwarmu zasu je. Amma duk da haka sai nace bari na gwada kowannensu.
Da Baby da Mom na fara. Sai banga wata alamar hakan ba daga garesu. Shima Abba haka. Sai kawai na koma kan Mansoor. A randa na taresa da zancen ina magana cikin tsiwa kan basai fa yasa ana bibiyata ba zai san halina. Idan bincike yake son yi a kaina yazo ga ƴan anguwar dana tashi cikinsu tun ƙuruciya har girma mana. Amma sakawa ana bibiyata kamar son firgitar da ni ne. Tare da nuna rashin aminci a tsakanina da shi. Sagale yay yana kallona da mamaki, sai dai bai iya cewa komai ba harna fita a fusace. To ashe daga nan bai zame ko ina ba sai wajen Yaya Musaddiq suka tattauna akan hakan. Lokacin da Yaya Musaddiq ya dawo aiki yay kirana ɗakinsa…….✍️

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Series Navigation<< Tsutsar Nama Part 1Tsutsar Nama Part 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *