Zafin kai Hausa Novels

Zafin Kai Chapter 1

This entry is part 1 of 6 in the series Zafin Kai by Mamugee

BismillahirRahmanirRaheem
Allah yabamu ikon gamawa lafiya

1
Gyara tsayuwarta tayi ahankali tana sauke idanuwanta daga kallon dattijuwa kuma tsohuwar matar dake a kansu tsaye tana musu fada cikin Iko da bayyanarda rashin ruwanta da abunda zai biyo bayan kuskuren da sukayi a lokacin tareda yi musu tini da ukubar dake tafe mai zafi.

Ita din dake tsaye a kan nasu tana fadan mahaifiyace ga Wanda ya haifesu ma’ana mahaifinsu babansu kaman yanda mutane ke Kiran Wanda ya haifesu da sunan baba kuma uba,
Su bazasu kirasa da kalman babansu ba sbd shi din Wanda ya haifesu ne kawai bawai babansu ba kaman yanda kowane uban yake,

Sun banbanta kalman mahaifi da baba ne sbd basu tantance me UBA Kuma baba yake nufi ba a zahirin haqiqanin gaskia dan basu taba gani ba ko samun kauna,kulawa,tausayi,jin qai ko wata fuskar dake tabbatar musu da su ‘din ‘yayane masu baba uba kaman kowane ‘yaya na halak da wainda bana halak din ba.
Amma a zahiri kusan sune suka fi tantance kalman mahaifi da ake nufi da wanda ya haifeka sbd zallar girmamamman ikonsa na haihuwarsu tareda juya rayuwarsu yanda yaga dama a mafi wulaqantacciyar hanya da karshen rashin daraja da rashin amfani shine mafi babban lamarin rayuwar dasuka tabbatar a duniya Gameda kalman mahaifi a gurinsu.

Matar data haifi mahaifinsu a zahiri itama bazasu kirata da kakarsu ba kai tsaye sbd babu wata sanyayawa ko kaunar Jini datake bayyanar musu da kalmar kaka da Ake kira a duniyar tasu,

Mahaifiyarsu,uwarsu,Annensu,Farin cikinsu kwalli daya a duniya dasike tsananin so da kauna sun kasance bayi a tare ita wadda itace asalin bautar acikinsu sbd shekarun data debo tun kafin haihuwarsu tana rayuwar bautar a tsakanin ‘da da uwar a wulaqance sbd takalmin daya saka kudi ya siya ya taka sunfita daraja a gurinsa bare mahaifiyarsa datake ganin tabbas Annen batada amfani a rayuwarsu kwata kwata saima wulaqantacciyar lalurar data zame musu da tarin ‘yayan matan data haife musu a gidan babu wata daraja ko daya dasuka qaru da ita,

Bayan shekarun data debo cikin azaba da ukubar uban nasu a yanzu gasu tareda ita cikin qangin bautar a tare,
Basuda yanci da ikon kansu sai yanda mahaifinsu yayi da raunanniyar rayuwarsu koda kuwa zaiyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsu basa iya dago kai ko fuskarsa su kalla bare idanuwansa dan kuwa sunfi maraba da masifa kowace irice akan dago kai su kalli idanuwan mahaifin nasu domin garesu kaman aikata wani babban mummunan sabo ne dazai iya kaisu ga shiga masifar datafi ka kona kanka da tafasashen ruwan zafi.

Sumayya da datafi kowanne a cikin su hudun rauni sosai a hankali ta sake yin qasa da kanta muryarta Mai rauni na Dan rawa tace,

“Zamu sake gyarawa kafin ya dawo Amma Dan Allah hande ki taimaka a bawa Anne abincin kafin ya dawo…”

Katseta hande tayi hankali kwance cikin Dan fada sbd batason batawa kanta karfi da rai ko lokaci akan lamarinsu sbd tasu rayuwar tagama lalacewa dan haka bazata bata karfinta a banza ba akan abinda yake tamkar matacciyar rayuwa mai numfashi tace,

“Babu ruwana da taka dokarsa,
Ita Annen taku zatace bata Saba da yunwa bane tsowon shekaru ashirin da Dori da aurenta dashi?

Kuda kuke yayanta kunzo daga baya Kuka Saba da yunwar bare ita,

Idan zata ara jarumta ta ara tayi rayuwar yanda ta Saba ni banason janye janye,
Kuje ku jira ya dawo yagama ku samu abinda zaku samu kuci din bansan sabon salon da bansaba dashiba.

Dukkaninsu babu wanda ya dago kansu na qasa suna sauraren fadan nata babu mai ikon dazai iya dagowa ya qara ko kalma daya acikinsu.
Ajiyar zuciya Annen dake tsaye jere tare dasu kaman bayi tsaye gaban sarauniyarsu ta sake tareda sake yin qasa da kanta cikin girmamawa mai tsananin gaske ta bawa Uwar uban gidan nasu hakuri sbd kwata kwata ba miji bane ko uba kaman na kowa uban gidansu ne a yanda suke rayuwar.,
Shi kansa bai daukesuba bare ya taba kallonsu a matsayin mata da ‘yaya kallonsu yake tamkar wasu dabbobi ko bayi daya saka kudi ya siyo suka zama garke.

Babu abunda Hande tasake ce musu bare ta sake kallon inda suke saima maida hankalinta datayi Kan sakon datake dubawa cikin qaramar wayar hannunta da batama gane komai da aka rubuto din.

Dagowa Anne tayi ta kalli ‘yayan nata ahankali cikin sanyin murya tace su tafi.

Babu Wanda jikinsa ba amace ba suka juya a jere kaman kashin awaki suki bi bayan mahaifiyar tasu kafafuwansu a sake ba qwari kaman taliyar hausa sbd yunwa da wahalar data Dade da ginuwa ta hade da Jini da gabban jikinsu.

****BENAZIR ce kawai me qwari da dauriya tareda karfin zuciya a cikinsu,
Sumayya da mahaifiyarsu nada rauni mai karfi da yawa Dan har gwara mahaifiyar tasu akan sumayya wadda ta kasance rauninta yayi yawan da kusan koyaushe ta tsaya gaban mahaifinsu numfashinta Neman fita kirjinta yakeyi sbd tsoronsa daya dasa musu tun suna qananunsu har zuwa yanzu,

Mahaifinsu tamkar wani dodon tsawa ne a rayuwarsu,
Bai taba barin tsoronsa da shakkarsa sun girgiza daga zuciyoyinsu Koda second dayaba sbd tsananin azabarsa da mummunan horonsa garesu,
A duk lokacinda amon muryarsa ya sauka kunnuwansu Gangar jikinsu da zuciyoyinsu shiga rawa da mafi girman firgici sukeyi tareda tsananin tsoro da tashin hankali mai girgiza hankali da nutsuwa,

Shi din kaman wata tsawa da walkiyar data gurbata rayuwarsu ne ta lalata musu,
Tamkar wulaqantaccin bayi da basuda daraja suke a karkashinsa,
Tufafinsa,talarmin sawarsa da dabbobinsa sunfisu daraja a gabansa sbd dabbobinsa yana musu kallon kadarar kudi ne dazai qaru dasu sabanin su dayake kallon wahala ce kawai da rashin amfani a gabansa,

Almajirai dake cikin bola suna yawo sunfisu yanci da gata sbd su din Sunada ikon daga kansu su kalli abunda sukeson kalla tareda ikon zuwa ko karban sadaka daga duk wanda suke so Amma su daga lokacinda mahaifin nasu ya wanzu a guri numfashi mai karfi basuda iko ko yancin yi batareda shine ya bada damar ba bare motsi Mai karfi saida izininsa,

Mahaifiyarsu ta share shekaru da aurensa cikin ukuba da azabar data cinye lafiyar kwakwalwar kanta da gangar jikinta harma da ganinta,

Ta haifesu su hudu duka mata cikin azaba da wahala,
Ra rena cikinsu su duka hudun a mafi wahalallan hali da kadaici da yunwa da ciwo rashin daraja,

Haihuwarsu ta ninka azabarta,quncinta,yunwarta da rashin darajarta,
Yawansu ya ninka azabarsu suma tun zuwansu duniya,
A duk lokacinda dayansu ya qaru a duniya sai sauran sunyi kukan qaruwar azabarsu,
Azabar datayi sanadin rasuwar daya daga cikinsu,

Duka wannan tsana da azabar akan suna ‘YAYA MATA ne,

Tsanar dayakewa Yaya mata ne kokuwa kaddararsa ce yasa Allah ya jarabcesa da haihuwarsu su hudu duka yaya matan?

Meye laifinsu?
Meye illarsu?
Meye illar samunsu dazai Rainesu tamkar dabbobin daya tsinto a daji.

Sun kasance tamkar mujiyoyi a cikin alumma sbd horon dasuka taso acikinsa hannun mahaifinsu da mahaifiyarsa yasa suke kallon kansu tamkar wasu halittun da kadan ne sukafi dabbobi daraja a cikin mutane.

Mahaifiyarsu ta rasa cikkakiyar lafiyar kwakwalwar kanta tun suna qananunsu,
Girmansu yasa tadawo kaman daidai sbd azabarta ta ragu anraba mata itada ‘yayanta,

Abincin dasukeci agidan suna samun cinsa ne bayan Mahaifinsu da mahaifiyarsa sunci sun rage Kuma Sunada iko da daman cinsa ne a gurinda zasu wanke kayan da aka Gama cin abincin dukkaninsu a kwano daya,.

Menene ci a koshi?
Wannan kalma ce da basu taba sanintaba Dan bata taba faruwa dasuba tsawon rayuwarsu,

Hutu, Shima wani Abu ne da basusan dashiba sbd babu shi a abunda suke samu.

Bauta,
Wahala,
Yunwa,
Azaba, sune abubuwan dasukafi sabo dasu,

Ribarsu biyu dasuke gani sun samu a rayuwarsu shine ibadarsu da kaunar junansu dasuke tsananin yi..

SUMAYYAH itace babba a haihuwa,sai SAMIRAHwadda tazarar shekara biyu ne rak a tsakaninsu,
sai BENAZIR wadda itama shekara daya da watanni ce tsakaninta da Safnah sai SAFNAH wadda itace qaramarsu itama shekarun dake tsakaninta da benazir biyu ne sbd yanda ako wane lokaci mahaifin nasu yake zuwarwa mahaifiyar tasu ba tsari ba kulawa ba komai,

Bai taba shaawar qarin aure ko neman wata matar banzar ba a waje sbd tsarinsa da tsananin so da kaunar abin duniya dake ransa,

Neman mata ko caca ko sunansu baa fada a gabansa sbd tsananin son kudinsa da bazai iya hakuri ko tinanin ma rasa ficika ba aciki yasa bai taba shaawa ko kallon inda ake caca ko zina ba.

Asalin tsanar Bena a ransa tafi ta kowa acikinsu ta musamman ce sbd cikinta ne ya cinye Rabin arzikinsa dayake ganin wata mummunar kaddara ce garesa zuwanta duniyama gabaki daya bayan haihuwarta sabanin duban da likita yayi masa akan namiji ne acikin,

Bai taba son wani Abu a duniyaba kaman yanda yaso cikinta,
Allah ya jarabcesa da son cikinta
So me tsananin dayasa ya kashe dukkanin tattalinsa akan cikin Wanda akan cikin yafara Kai matar tasa asibiti sbd ko uwarsa data haifesa duk ciwo Bai taba kaita asibiti ba sai akan wannan cikin
Daga karshe dukkanin burinsa da muradinsa ya lalace a kan idonsa da aka sake iso masa da sakon ‘ya mace aka haifa wadda tun a asibitin yaji tsanarta fiyeda uwar da sauran yayan da Ake haifar masa haka zalika tunda ta fado duniya bai taba daukanta a hannunsa ba haka bayajin zaiyi har abada kuma daga kanta bai sake ko kallon abinda matarsa tasa ta haifa.

Tsanar dayake wa Benazir ta bata qarfin zuciya fiyeda Yan uwanta dakejin radadi da raunin tsanar da Mahaifinsu ke musu sai dai dukkanin su basusan me kaddararsu ta tanadar musu ba a gaba dagasu har shi mahaifin nasu.

****Dakinsu suka shiga kowannensu ya nema guri ya zauna a hankali Banda safnah data tsaya daga bakin window Idanuwanta da sukai ciki sbd rashin kuzari tana kallon bayan gidansu a jikin windon jikinta na qarasa sanyi zuciyarta a ko yaushe babu abunda take tinani sai yanda rayuwa ba’a karkashin mahaifinsu ba zata kasance,

Shin sauran ‘yaya ya sukejin mahaifansu acikin ransu?
Da wani ahalin aka haifesu koda a matsayin ‘yayan shegu ne zasufi farin ciki da nutsuwa,
Meyesa basu zamto cikin yayan da ake haihuwarsu ana jefarwa ba sunfi kwanciyar hankali koda talaka ne ya tsincesu zaifi musu akan wanda suke karkashinsa a matsayin mahaifi yanzu,

A koyaushe burinta shin da gaske akwai wainda ke siyan mutane suyi bayi dasu kaman yanda mahaifin nasu keda tsananin buri da fatan Ina zai samu masu siyan bayi ya saida dukkaninsu Koda a farashi mara daraja ne a tafi dasu ya huta da ganinsu shima a rayuwarsa,

Idan da gaske akwai irinsu to tabbas itama tanason ta kasance a siyeta a tafi da ita tabar mahaifinsu da sunansa kawai aka kira dukkaninsu zuciyoyinsu tsalle sukeyi cikin tsoro Mai girma da firgici Wanda wani babban balain ne ma bayyanarda rawar jikin tsoronka a gabansa wannan ma wani nauyin horon azabar ne dasu kadai sukasan wutar tsoro da rawar dake gudana a jininsu gurin boye hakan.

Ahankali hawayenta suke gangaro
duk tsanani hawayensu ma basuda yancin gangarowa a gidan saidai idan sun shigo dakinsu su iya sakinsu,

Ahankali cikin muryarta datake bayyanarda rauni da qulafucinta akan rabuwa da rayuwar datake ciki tace,

“Allah yakawo kaddarar dazata rabamu da gidan nan Koda ta wahala ce.

Dukkaninsu sun ji abunda ta fada cikin raunin
Sun Saba jin hakan daga bakinta sbd a cikinsu itace tafi kowa raunin son tafiya tabar gidan Koda zata tadda rayuwar wahalar datafi ta gidan,

Duk tsanani sun San bazasu taba barinta kwatanta guduwa ba kaman yanda itama bazata taba kwatanta guduwarba sbd azabar kwatanta guduwar ne yayi sanadin rasuwar SAMIRAH wadda ta rasu rasuwa Mafi Karya zuciyoyinsu.

Series NavigationZafin Kai Chapter 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *