Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 6

Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 2

This entry is part 2 of 6 in the series Zakaran Da Allah Yanufa da Chara by Nuceeyluv

2…

Acan bangaren Saratu kuwa koda tabar unguwar direct wani lungu ta fada Bayan wata bishiya jikinta na kyarma ta zaro wayarta Tecno tana me latsa Kira, bugu daya aka dauka cikin sauri Saratu tace,

“mun shiga uku Nas(Nurse)”

daga dayan bangaren akace

“nifa dadina dake Sara kin cika rudu Wlh ni ki gayamin meye? Dama dazu muna waya naji kin kashe ba sallama na Kira wayarki daga baya a kashe”

“Hmmm…”

Saratu ta ja numfashi me nauyi hankalin ta a mugun tashe tace,

“Nas muna cikin tashin hankali Wlh Asirin mu da muka binne shekaru masu yawa Yana dab da tonuwa”

A Razane Nas ta Mike daga kishingiden da take tace,

“Me kike nufi Saratu?”

Wata wawiyar ajiyar zuciya Saratu ta sake saki tana me Dan waiwayawa Bayan ta Dan kar taje akwai me jinta a hankali tace,

“Wayar da mukayi dazu dake Ashe mlm sale Yana tsaye a bayana yaji dukkan Abinda muka tattauna musamman ma dake wayar a bolum(volume) take”

“Bantan uban nan kayyasa….”

Nas ta furta bakinta na Bari tace,

“Wlh duk inda kike kizo ki sameni Dan baki Isa ki ballo min ruwa Ina zaman zamana ba Wannan mgnr Sam Bata waya bace”

Saratu jikinta na rawa tace,

“yanzu haka ma gidanki na nufo”

“da yafi miki”

Nas ta furta tana datse wayar cikin tsantsan takaici. Gumi ne sharkaf ya jiqe Saratu dukda sanyi2 da akeyi a garin sbd Albarkar Ruwa da aka samu a ranar, Nan taci gaba da tafiya tana me kokarin tare Dan napep Bayan ta gama fitowa daga lungunan unguwar su kadan ya rage Bata afka Kwata ba sbd sauri, cikin sa’a kuwa ta samu Wanda ya tsaya cike da azama tahau direct ya wuce da ita inda tayi masa kwatance hade da kashe wayarta gaba1 sbd tsaro.

~~~~

A bangaren Dr. Omar kuwa batare da tunanin komai ba ya kinkimo Abban nasa Yana jijjiga shi hankalin sa a mugun tashe, ganin yadda jini ke malala yasa shi Dan janye Abba gefe guda, cikin azama ya fito daga dakin tunowa da yyi da ‘yar karamar First Aid box dinsa daya ajiye a daki, time to time Dama Yana siyan mgni ya ajiye sbd halin Babu kada rashin lpy ya Kama mutum azo a rasa kudin mgni Abinda befi a kashe 200 ba shiyasa daya samu kudi yake aje Abinda yafi zama emergency a gida,

Cikin sassarfa ya jawo box din sannan ya juyo zuwa dakin Abba, batare da Bata lkci ba ya shiga hada kayan aiki Dan tsaida jinin da yake zuba Dan idan yace zai Kai Abba a haka zaiyi asarar jini sosai kafin su Isa hsptl din musamman Matsalar goslow da ake fama dashi a garin, Kafin wani lkci harya gyara masa inda yake zubar jinin Nan Bayan keyar sa, jikinsa ne yahau tsuma dayaga mugun ciwon dake keyar Abba, kallon inda ya jawo shi yyi Yana nazarin wajen Tabbas Babu ko tantama Abba zamewa yyi a nasa tunanin kenan.

Da sauri ya fito kofar gida ko zaiga Makocin su mlm Shamsu ya taimaka masa su fito da Abba daga gidan, cikin sa’a kuwa Yana fitowa mlm Shamsu na kokarin Sanya mashin dinsa cikin gidansa da alama dawowar sa kenan, saurinsa ya Kara yacin masa Yana me Mika masa hannu, Mlm Shamsu da fara’a yace,

“Umara kaine Ina Abban naku?”

Omar ya shafa sumar kansa data zame masa tamkar Al’ada Kai tsaye yace,

“Dan Allah taimaka min zakayi na fito da Abba”

“Yah Subhanallahi!”

Mlm Shamsu ya furta Yana jirkice mashin din nasa gefe guda yace,

“meya samu mlm din?”

Yyi mgnr Yana bin Bayan Omar daya kusa shigewa gida, a haka suka karasa cikin dakin mlm Shamsu nata sallallami, Shidai Omar bece komai ba har suka fito anan wasu tsirarai dake unguwar suka fara taruwa da Al’ajabin Abinda ya samu mlm Sale, Shidai Omar bece komai ba tunda a takaice ya fadawa mlm Shamsu zamewa yyi ya bugi kansa da karfe shine sanadin suman sa, hakan yasa shi mlm shamsun shike Basu bayanin Abinda ya faru,

a gurguje yazo ya kulle kofar gidan nasu sannan ya shige motar cikin azama, wani irin juyi da yyi da kan motar Kai kace wasan tseran mota zaije, kafin wani lkci harya bacewa mutanen unguwar da suka taru yanzu fiye da dazu sai maida zance ake Ana jajantawa hade da Allah wadai da matar mlm Sale wacce neman kudinta shine tafi darajawa fiye da auren ta.

Yana hanya Sadeeq ya Kira shi, da sauri kuwa ya dauka Dan Yana bukatar hakan,

“yauwa pls a shirya gadon daukar marasa lpy kafin na iso pleaseeee..”

Ya katse hanzarin Sadeeq din tamkar shine yyi Kiran, hankali a matukar tashe Sadeeq yace,

“Waye baida lpy?”

“Abba ne.”

Omar ya fada a takaice kafin ya datse Kiran Yana me aje wayar gefe, Sadeeq dake daya bangaren be takura masa ba shima ya shiga matukar damuwa da sauri ya tashi Dan samun Wanda zasu riko gadon.

*

Cikin Rahamar ubangiji sai gasu a hsptl din, kamar yadda yace hakan ce ta faru Dan Already har an fito da gadon ma shi ake jira, cikin sassarfa aka fito da Abba daga motar zuwa kan gadon marasa lpy, a gurguje kuwa aka wuce dashi emergency room, tuni Dr. Sadeeq ya fito musu da labcoat da kayan aikin da xa’a bukata kafin wani lkci sun dukufa kan Abba Dama sauran wasu Doctors din Ana bashi taimakon gaggawa sbd dogon suman daya tafi.

***

Kadan ya rage tayi tuntube Allah ya kiyaye Nan ta afka dakin Nas da tun dazu take safa da marwa hankalin ta yaki kwanciya, ba xato kuwa taji fadowar mutum dakinta, A Razane ta juyo ganin Saratu ce yasa tadan saki ajiyar zuciya tana me zama kan kujerar ta, Cikin masifa tace,

“Saratu a wanne shirmen ne yasa kika sa Asirin mu ke dab da tonuwa?”

 Saratu tace,

“kinji na rantse miki da Allah Nas bansan Yana bayana ba sai juyowa nayi kawai Naga Yana shararar hawaye tamkar an balle famfo Fuskar sa babu Annuri kamar Wanda aka Aiko masa da sakon mutuwa, shiyasa na katse layin da sauri.”

“Toh Amma me yace miki?”

“Hmm..!”

Saratu tadan ja majina tace,

“budar bakinsa sai cewa yyi Allah ya Isa ban yafe miki ba Saratu, kin cutar damu, bazamu taba yafe miki ba, Ashe zaluncin naki yakai har haka? Ko a mafarki ban taba tunanin zakiyi makamancin Wannan ba, Kuma Wlh ki sani *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA KO ANA MUZURU ANA SHAHO SAI YAYI* bazanyi kasa a gwiwa ba dole na sanar dashi dukkan tuggun da kika kulla keda shadaniyar da kuke waya shekaru sama da talatin. Yana gama fadar haka ya juya cikin fushi ya nufi dakinsa Dan daukar wayar sa, ke na takaice Miki lbri Nas tunda ya fara mgnr hankali na yake a mugun tashe ji nake duniyar tana hautsina min, babban takaicina shine har yanzu ban fara cin moriyar Abinda na binne shekaru talatin baya ba, Kai ni yau Naga ta Kaina ni Saratu”

ta karasa mgnr tana dafa kanta, Nas tace,

“kina nufin haka kika fito batare dakin hanashi yin wayar ba?”

Tayi mgnr tana zaro ido cikin kidima, Girgiza Kai Saratu tayi tace,

“yaushe Naga ta zama? Binsa nayi Ina bashi hakuri kamar Wanda nake zuga shi, haka ya dauko wayar Ina labe Ina jinsa a lkcn duk wani dabarata ta kwance Tabbas da Allah yasa yyi mgn a lkcin Babu Abinda zai Hana Asirin mu tonuwa, toh haka na sake shiga dakin cikin bacin Rai nace yanzu bazaka hakura ba sai kace mutanen farko sbd taurin Kai? Kallo na ya tsaya Yi Yana girgiza Kai yace tsakanin ni da ke waya kamata a fadawa hakan? Wato kinga ban dauki mataki ba Koh? Jira nake sakon Nan ya Isa ga inda ya dace kafin na dauki mummunan mataki a kanki, jin hakan ya sake jefani cikin rudani da tashin hankali, kinsan Dama Yana Dan dogara sanda sbd kafarsa karshe zuciya ce ta debeni na warce sandar tare da rima Mai ita a tsakiyar ka, dake abin yazo masa a bazata tuni ya dafe kansa sbd tsananin xafin daya shige shi sannan kafar da tadan lankwashe sai gashi ya Fadi a daidai karfen gefen gado kafin nayi aune sai gani nayi jini ya fara malala ta kasan keyar sa, shiyasa banyi wata-wata na baro gidan da sauri sbd nasan yaron Nan Maru Yana hanya tunda yace yazo.”

“Kin kashe mu, kin kashe mu Saratu”

Nas ta furta tana dafe kanta,

“Tsautsayi, Tsautsayi ne Wlh.”

Saratu ta fada itama,

Wani mugun tsaki Nas taja me cike dajin haushi tace,

“Toh Wlh bazata Sabu ba Dole mijin Nan naki mu nakasar dashi”

Tayi mgnr cikin bacin Rai, Saratu tace,

“nakasar dashi shi zai Hana ya fada? Kinsan taurin Rai irin nasa kuwa?”

Nas tace,

“ke dallah bakya gane Abu Sam wani lkcin, zuwa zamuyi wajen bokan daya Saba Mana aiki boka na tsamiya domin ya rufe masa baki ya daina mgn kwata-kwata a Rayuwar sa haka zai dinga bin mutane da ido ba halin mgn”

Shiru Saratu tayi batace komai ba can Nas ta katse Mata tunanin da fadin,

“Ko bazaki iya bane?”

 Saratu ta girgiza Kai tace,

“nazari nake”

“kutt… Toh tsaya kallon ruwa kwado ya Miki kafa kin sani Sarai idan Asirin Nan ya tonu sai kinfi  kowa cutuwa Danni nawa kadan ne ehe”

Hankalin Saratu ne ya sake tashi ta Mike zumbur Fadi take,

“shirya, Maza shirya mu tafi Dan Allah Wlh bakiji yadda na sake fadawa tashin hankali ba matukar ya farka bazai fasa qudurin sa ba.”

Nas tace,

“haba ko ke fa”

tayi mgnr tana wucewa uwar dakin ta, kafin wani lkci itama harta shirya sannan ta sankamo Tata jakar kamar ta wanzamai suka fito a gidan da gaggawa.

~~~~

A bangaren Dr. Omar Kam cikin Ikon Allah suka samu nasarar Gyara ciwon mlm sale, komai sun gyara masa tsaf an  shirya shi tsaf gwanin ban tausayi, Saida aka gama Batare da shawarar Dr. Omar ba Dr. Sadeeq yasa aka maida mlm Sale special room sbd samun nutsuwa, Dr. Omar kamar zai masa mgn ya fasa Dan kar frnd din nasa yaga kamar Yana Raina masa taimakon sa musamman idan ya tuna da dazu akan shiga mota badan Allah yasa yaje da motar ba Tabbas da zasu wahala wajen neman abun Hawa hakan daya tuna sai yaji Dadi kwarai Dan ba karamin taimako ya masa ba.

Ba kowa a dakin daga shi sai mlm sale gashi suna Shirin komawa skul dama after zuhur prayer zasu koma, wayarsa ya Ciro cikin fargaba da Rashin sanin wacce irin Amsa za’a bashi ya lalumo number Ummansu, Dakyar dai ya iya danna Kiran sbd fargaba, rintse ido yyi kawai Yana sauraron Kiran ya shiga, Shiru number ta fara searching can yaji tace is switch off,

“Hmmm…!”

Wani marayan ajiyar zuciya ya saki Yana me maida wayar sa Aljihun sa hade da shafa sumar kansa Yana nazari, Shigowar Dr.  Sadeeq yasa ya dago Kai bece komai ba, Dr. Sadeeq yace,

“kasan muna d  lecture 2 to 4 ya kamata kazo muje Sallah sai mu fara Shirin tafiya kafin Nan ka Kira Umma saita tsaya a wajen”

Dr. Omar ya danyi shiru kamar bazai magantu ba can yace,

“Bata gida”

yyi mgnr a takaice, Dr. Sadeeq be zurfafa da tmby ba yace,

“Okay Bari nazo”

Nan yaje ya sako wata Nurse Rukayya matar tanada mutunci Dan tadan manyanta ma yazo da ita wajen, Dr. Omar sai ganin su yyi, kafin yace komai DR. Sadeeq yace,

“yauwa Aunty Ruky Zaki kula Mana da Abban mu kafin mu dawo munada wani uzurin ne me karfi”

Nurse Rukayya tace,

“Babu damuwa Sadeeq Zan kula da wajen sai kun dawo”

“yauwa mun gode”

Dr. Sadeeq ya fada Yana jawo hannun Dr. Omar subar dakin, Hade fuskar sa Dr. Omar yyi be jawu ba saima daskarewa da yyi a wajen, ganin haka yasa Nurse tace,

“Bari na jira ku a waje ku Gama saina shigo”

“Okay”

Dr. Sadeeq ya furta, Tana fita kuwa Dr. Omar yace,

“Ce maka akai bazan tsaya a wajen ba?”

Yyi mgnr a zuciye, Dan karamin tsaki Dr. Sadeeq Yaja yace,

“Da ace bamu da lecture me muhimmancin bazan ma fara neman wata ta taimaka Mana ba, ka sani Sarai ranar Nan mun Dade muna jiran tazo yanzu idan ta subuce Mana yaushe kke tunanin zamu sake samun wata damar? Kasan ba kamar sauran lectures bane da muka Saba Attending karka manta a kowanne lkci anaso mutum  ya dinga amfani da damar daya samu kafin ta kufce masa”

Dan lumshe ido Dr. Omar yyi Yana me shafa lallausan gashin kansa dayan hannun a qugun sa, yadan cije lips dinsa kadan a takaice yace,

“Alright!”

Girgiza Kai Dr. Sadeeq yyi Yana yowa gaba, haka shima Dr. Omar din ya biyo shi Nan suka bar dakin ita kuma Nurse Ruky ta shiga ciki Dan kula da Abba.

Suna cikin mota Babu Wanda yace wa wani kala sbd shima Dr. Sadeeq din wani lkcin akwai Shan kamshi saidai bekai Dr. Omar din bane especially daya kasance ya fito daga babban gida Wanda Nigeria kaf tasan da zaman mahaifin sa Alhaji Tukur Malami, Dr. Sadeeq Yana matukar ji da kansa Dan ba karya shima karshe ne gwanine wajen kyau da iya kwalisa, saidai daya hadu da Dr. Omar dukda shi ya fito daga karamin karfi sai yaga ya take shi nesa ba kusa ba ( oh ko ya akai suka kasance abokai aminai? Asalin lbrn nasu Yana gaba Insha Allah) a nutse suka fito daga motar Bayan Dr. Sadeeq yyi parking suna kokarin rufe mota suka ga wata irin kura ta taso daga can nesa da su, wani irin wawan tsaki suka ja a take duka su biyun wato Dr. Sadeeq da Dr. Omar, cikin jin haushi suke bin zugar motocin da sukayi convoy suna shigowa cikin University din Ta B.U.K,

Daga can barin wata arniyar mota ce wasu daga cikin bodyguard din me tafiyar suka zo suka bude wa me motar kofar, Cike da izza da takama na cikin motar aka fito da kafa daya waje Ana me karkada ta a hankali wayyo Allah kowa yaga Tsadar takalmin yasan Tabbas an narka Naira wajen siyan shi Dan ba karya takalmin ya hadu Naira tayi kuka a kansa. Dayawa dake harabar makarantar zuba musu ido akai kamar kullum yyinda wasu ke danyin kuskus kamar yadda aka Saba,

Dr. Sadeeq da Dr. Omar kuwa bakinsu ne ya sake haduwa wajen furta Fool.

*Tofah😱😱😱  Ana wata ga wata ko waye a motar? Fans karku damu nasan kun kosa kuji asalin lbrn, toh Yana Nan tafe sannu a hankali, kamar yadda nace Wannan lbrn yasha banban da sauran Wanda kuka Saba ji a hankali zaku fahimci inda na dosa musamman da muke taso muji me mlm sale yaji matar sa Saratu take kullawa ita da Nas? Kuci gaba da bin Nuceeyluv Dan ta warware muku Kullin zaren🏌️‍♂ï¸?*

 *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA…ð ( _ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Series Navigation<< Zakaran Da Allah Yanufa da Chara Chapter 1Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *