Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 6

Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 4

This entry is part 4 of 6 in the series Zakaran Da Allah Yanufa da Chara by Nuceeyluv

4…..

“Zan amince ki zamo ‘yar aikina saidai bansan wanne kala Zaki iya ba sbd mu Already munada ma’aikata a gidan Nan Zan taimakeki ne kawai badan mun rasa ba”

Cikin zumudi Saratu tace,

“Wlh kowanne iri ne Hajia Zan iya, daga kan share2 wanke2 da goge2 duk Zan iya Wlh, irin abincin ku ne dai bazan iya ba idan ba irin namu na gargajiya ba”

kallon ta Hajia Aisha tayi tace,

“naji kamar kince kina dauke da karamin ciki?”

Saratu ta girgiza kanta tace,

“sosai kuwa”

Hajia Aisha tace,

“Toh Taya Zan baki aiki Bayan kina da juna biyu? Ki Bari idan kika haife Abinda ke cikin ki saiki dawo muyi mgn”

da sauri Saratu tace,

“Dan Allah Hajia kimin Rai ni Wlh a hakan ma Zan iya inada dauriya sosai ko Dan goge2 Nan ki bani zanyi idan yaso na haife Abinda ke cikina saiki bani aiki me kwari”

Ta karasa mgnr cikin hade hannayen ta Alamar magiya, Shiru Hajia Aisha tayi tana Dan nazari can tace,

“Toh shikenan kiyi shawara da mijinki Zaki dinga gyara min dakina shi kadai ne masu aiki basa zuwa da Kaina nakeyi na barki ne kiyi min sbd Nima Abinda ke tare Dani wahala yake bani ba’aso na dinga Abu me wahala ko yawan zirga-zirga sbd be Gama kwari ba”

baki washe Saratu tace,

“Kai Masha Allah Hajia kema ciki gareki?”

Dan murmushi Hajia Aisha tayi ta girgiza kanta kawai, Nan Saratu tahau murna tana sanyawa cikin Albarka hakan ya karawa Hajia Aisha jin Dadi harta Dan Kara sakewa da saratun.

  Can tace,

“mgn ta gaba Saratu Ina tare da uwar mijina muna kiranta da Hajjaju nata bangaren nacan gafe ki tashi muje na gabatar dake wajenta”

Da sauri Saratu ta Mike tace,

“Toh Hajia muje”

Nan Hajia Aisha tayi gaba saratun ta bita a baya.

Tun a hanya Saratu ke ganin ikon Allah ko Ina na gidan gwanin kyau da ban sha’awa haka dai suka karasa part din Hajjaju, Tana kishingide akan lallausan kafet dinta tana Jan carbi yyinda gefe guda wata ‘yar aiki ke Mata tausa, da Sallama suka shiga ciki ‘yar aikin ta gaishe d Hajia Aisha sannan ta fice a dakin, Hajjaju ta gyara zamanta sosai tana kallon Hajia Aisha da fara’a a fuskar ta tace,

“Shatu kece tafe”

“Eh Hajjaju”

Nan itama ta zauna a hankali, kallon Bayan Hajia Aisha Hajjaju tayi tace,

“Ikon Allah Wannan Kuma wacece a Bayan ki?”

Tayi mgnr tana nuna Saratu data saki baki tana kallon dukiyar da aka narka a falon tsohuwa, Jin Ana nunata tayi saurin dukawa kasa tana kwasar gaisuwa sama2 Hajjaju ta Amsa tana kallon Hajia Aisha Dan jin amsar tmbyr ta, Hajia Aisha tace,

“sunan ta Saratu dama nazo da ita nan ne Dan na shaida Miki komai game da ita”

Nan ta kawashe lbrn Saratu da yadda zasu taimaka Mata ta gayawa Hajjaju, Hajjaju data saki kunne tanajin bayani tadan lankwashe hannun ta tana me kafe Saratu da idonta kurii, Saratu tayi kasa da kanta, Hajjaju ta dawo da kallon ta kan Hajia Aisha tace,

“Ashsha, Ashsha, ta yaro kyau take Bata kargo yanzu Shatu daga Jin Wannan bayanin shikenan harkin yadda da mutum? Meyasa kullum kike da saurin yadda ne? Karki manta yanzu fa duniya ta lalace marasa Imani sun lalata masu neman bukata domin dayawa mugu sai ya shiga rigar mabukaci ya cuceka a banza da wofi dayawa wasu burinsu su rabeka, badan komai ba saidan Wannan ni’imar da Allah ya baka su ture ka daga inuwa su maida ka Rana su Kuma su mamaye gurbin ka”

A sanyaye Hajia Aisha tace,

“kiyi hakuri Hajjaju Naga baiwar Allah Nan tana bukatar a taimaka Mata ne”

Hajjaju tace,

“duka yaushe kuka dawo daga waje har ta manne Miki haka? Aisha Allah fa Abin tsoro ne haka ma mutum”

Saratu dake zaune ta share hawayen dake malala a fuskar ta tace,

“Dan Allah kuyi hakuri bansan haka abin yake b saina je na nema a wani wajen”

tayi mgnr tana kokarin mikewa, da sauri Hajia Aisha ta kalli Hajjaju, Hajjaju tace,

“baiwar Allah ni bazan Hana taimako ba Abinda na sani kawai na fada ki tmbyi kowa a gidan Nan Hajjaju batasan meye munafurci ba duk dacin gsky fada take Dan haka kuje kiyi aikin ki Allah yyi jagora”

Da murna Saratu ta juyo tana kwasar godiya gurin tsohuwa Hajjaju.

…..Kamar yadda Hajia Aisha ta umarci Saratu ta fadawa mlm hakan ne ya kasance badan mlm yaso ba ya amince sbd takurawar da Saratu tayi Masa, shi yasan halin Saratu wajen kwadayi zata iya yin komai sbd kudi, da naci da komai dai ya barta, Anan Saratu ta fara zuwa aiki sai Hajia Aisha ta bada driver guda Yana dauko ta da maida ta sbd tausayin Abinda ke cikin nata itama.

*********

Sannu a hankali Saratu ta fara aikinta a gidan *ALHAJI ABDULLAHI OMAR MAI FATA* Tanada kokari matuka sbd cikin jikinta be hanata yin aiki da Allah ya taimake ta bezo da matsala ba kamar na Hajia Aisha da kullum ake lallaba shi tamkar kwai.

Saratu a zaman da tayi a gidan Tabbas taga yadda ake zaman aure, taga yadda ake tarairaya mace, taga yadda ake nuna kauna dayiwa matar gida bauta, Kai yadda taga Alhaji Abdullahi yake tattalin matar sa har abin Yana daure Mata Kai uwa uba idan taga daular da Hajia Aisha ke ciki abin na Bata mmki, daga Nan ta fara sakar zuci tana ayyana dunbin dukiyar dake tattare da Ahalin Babu magaji ko guda daya sai Wannan cikin da ake ta lallaba shi kamar kwai, daga tunani sai ta fara Jin inama itace? (Karamar hasada ta fara bullowa) daga Wannan tunanin sai kuma ta fara hango kanta a Matsayin Hajia Aisha da itace ita da tayi kaza da kaza, Kai a hankali dai shaidan ya fara tasiri a cikin zuciyar Saratu Saiya kasance tana Jin haushin ni’imar da Allah ya bawa Hajia Aisha, domin ta faraji a ranta inama duk wani Jin Dadi yabar hajian ya dawo gareta? Saiya kasance yanzu duk wani Budi na Alkhairin Hajian bataso, ta tsani ririta cikin da suke musamman Wannan tsohuwar Hajjaju dukda tana mugun tsoron tshowar sbd Hajjaju Bata sake Mata ba Sam Dan kullum suka kebe da Hajia Aisha ce Mata take Shatu hankalina ya kasa kwanciya da Wannan ‘yar aikin Taki dandai kin matsa ne Kuma ba’aso a hanaki Abinda kikeso a Wannan yanayin da kike ciki sai Hajia Aisha Tayi murmushi kawai Dan tasan halin uwar mijin nata itama Sarai Bata cika yadda da mutum da wuri ba, toh Saratu idan taga hajjajun nayin Nan Nan da cikin Hajia Aisha sai taji kamar ta make ta kullum tazo bangaren Bata da Abinda take fara fada sai Ina megida na? toh dai mutanen gidan Basu San me take ba Dan fuska biyu ta nuna musu a fili nunawa take tafi kowa kaunar su, a badini kuwa ji take kamar ta harbe su.

Ana Nan haka wata Rana likitar dake zuwa har gida duba Hajia Aisha tazo Bata sameta a parlo ba sai Saratu dake mopping itace ma ta shaida Mata Hajia na sama tare da Alhaji,

“Mtwss..”

Nurse din taja tsaki hade da zama kan kujera kasa2 ta fara mgn,

“aikin banza ciki kamar kanta farau Ayita ririta shi sai kace kwai Wlh suka isheni Ina iya sanadin cikin Nan yabi rariya Mtwsss”

ta sake Jan tsaki tana kwanciya jikin kujerar,

“Kika ce me?”

Taji anyi mgn daga Bayan ta a tsorace Nurse ta juya tana kallon Saratu rike da qugu ga abin mopping a hannun ta, ita Nurse tsabar zancen zuci dake cinta ne yasa Sam ta manta da Saratu a falon, Cikin wayancewa bakinta na rawa tace,

“ah..uhum..bance komai ba ai”

Tayi mgnr tana meyin fuska, Saratu ta saki murmushi tana Kama bakinta tace,

“au Ashe?”

Nurse ta zaro ido tace,

“ke nace ba Abinda nace”

Takowa Saratu tayi a hankali ta matsa jikin kunnen Nurse Nan ta zayyane Mata dukkan Abinda tace sannan ta dago kanta tana me bin Nurse da kallo tace,

“ko banji daidai ba?”

Nurse data daskare tun dazu jikinta na Bari tace,

“Toh naji Dan Allah ki rufamin Asiri ba nufina ba kenan Wlh”

Saratu ta maka Mata Harara tace,

“Kuma kikeso ki Raina min hankali?”

Nurse tace,

“Toh kiyi hakuri kinji Dan Allah karki fada Mata Wlh za’a iya daure ni akan Wannan mgnr”

 Saratu ce ta bushe da dariya tana Kama cikinta daidai lkcin Hajia Aisha ta sakko Tare da Alhaji zuwa parlon kasa, a take dariyar Saratu da makale tana me sunkuyar da kanta kasa wani tukukin takaici na sukar ta a kirji, kusan hakan ne a bangaren Nurse itama kamar an caki kibiya a kirjinta haka taji Abu ya rike Mata makogwaro,

    Tana takaicin wannan Abu, Wai meyasa komai Aisha Usman saita fita da komai ne a rayuwa? Tun suna school Aisha Usman take finta da komai harta kokari ma da fagen kyau, kafin Aishan tazo school dinsu itace mekyau da kokari Amma zuwan Aisha ya dishashe nata tauraron Abinda ya kona zuciyar ta kenan takejin tsanar Aishan har cikin ranta, duk wata kulla2 da zatayi Dan Hana ci gaban Aisha Usman tayi Amma abin yaci tura, lkcn da taji wa Aisha zata Aura Saida Nurse(Habiba) taji kamar ta kurma ihu Dan takaici har kwallar bakin ciki Saida ta zubar sbd yadda taga Aisha zata shiga daula ba itan ba Dan tun a zamanin baya zuri’ar Alhaji Abdullahi masu kudin gaske ne, dukda Haka Bata zauna ba Saida Habiba tabi bokaye Dan Hana zaman lfiyr Aisha Usman, Haka tasa akayi Mata Asiri karta samu ciki, Shine Abinda ya Kara Jan lkcn Hajia Aisha kenan dake Alhaji Abdullahi Dan halak ne sam be damu ba ya fauwalawa Allah komai Kuma shi suke rokon ya Basu, toh dake Allah maji roko ne sai gashi ya Amsa Addu’ar su dawowar su Nigeria gaba1 yyi daidai da tahowar karamin cikin Hajia Aisha, Koda Hajia Aisha taje hsptl domin a duba ta Anan maternity ta hadu da Habiba Musa(Nurse) da murna Aishan take gaisawa da Habiba, yyinda ita habiban ke gaisawa da ita cikin mmki, harda subutar baki wajen fadin Wai dgske ciki gareki? Hajia Aisha taji abin wani iri sai kuma ta share tace ikon Allah kenan, habiba tayi yaken Dole tace bashakka haka abin yake, Nan dai sukayi musayar number toh daga karshe dai Hajia Aisha ita ta nemi Habiba tana zuwa gidanta dubata sbd wuyar da take Sha Kuma ‘yar aikinta Saratu cikin gareta itama sai Ana dubata idan yaso sai ta dinga biyanta, Haka Habiba ta amshi tayin Hajia Aishan Kuma kullum cikin takaicin cikin take musamman idan tayi duba da daular da Aisha ke ciki yanzu zata sake samun dunbin dukiya matukar aka haife Abinda ke cikin, kullum nazari da tunanin yadda zatayi da cikin Hajian take sbd security ne Kota Ina a gida Kuma karta barar ta hanyar magani ko wani abun a gano ta gashi boka yace Mata cikin Nan fa sai yazo duniya saidai tayi hakuri Wannan karon ko Kuma idan ta matsa ita zata halaka, Dan Dole ta zubawa sarautar Allah ido Amma fa badan zuciyar ta taso ba……

“Kinata jira Koh?”

Hajia Aisha ta katse musu shirun nasu, da Dan yake Habiba tace,

“laa sai kace wani Abu ban wani Dade bama barka da safiya Alhaji”

Tayi mgnr tana kallon side din da yake, Da fara’a shima ya Amsa hankalin sa na kan matar sa Yana me daidaita zaman Hajia Aisha kan kujera Nan yyi musu sallama ya tafi, Dan cije lips Habiba tayi kafin ta Dan saci kallon Saratu data dage Mata gira Alamar Bata manta zancen su na dazu ba, saurin kawar da kanta tayi ta jawo jakar hannun ta tace,

“Hajia ga mgnin da nace Zan kawo Miki sai kisha”

Hajia Aisha ta karba tace,

“Kai Nagode sosai dama na wajena ya kusa karewa”

Habiba ta danyi murmushin da be Kai zuciya ba tace,

“Allah dai ya raba lpy”

“Ameen”

Hajia Aisha ta furta tana murmushi kafin tace,

“saiki duba saratun”

Saratu ta matso kusa tace,

“Wlh lpy Lao nake Hajia saidai nayi Miki fatan Alheri Ina godiya sosai bisa dawainiyar da kike Mana”

Hajia Aisha tace,

“ba komai ai yiwa kaine”

“gsky ne Allah ya Kara budi”

Saratu ta fada tana mikewa, wajen mopping dinta tayi ta dauko ruwan mopping din tayi waje, ganin Haka yasa Habiba Nurse tayiwa Hajia Aisha sallama a gurguje tabar falon.

acan nesa ta hango Saratu da sauri ta cim Mata, Saratu ta dakata da tafiyar ta sbd yadda taga Tasha gaban ta murya kasa2 sbd kada masu Kai kawo suji su Habiba tace,

“Dan Allah Saratu kin hakura?”

Saratu tace,

“a nawa?”

Habiba ta zuge jakar ta d sauri ta zaro dubu biyu tace,

“gashi Dan Allah shikenan Koh?”

“Kutmar…,”

Saratu ta furta taba duban Habiba tace,

“dake ance Miki ni matsiyaciya ce Koh? Da Dane sai nace kin bani Abu me nauyi ba yanzu da idona ya bude nasan me ake nufi da daula ba Nas”

Habiba ta rufe bakin Saratu da sauri tace,

“ki daina daga murya Mana za’a jimu”

Saratu ta kwace bakinta tace,

“sbd Naga kina neman Raina min wayo ne Kuma a yanzu naso Tona Miki Asiri Zan samu dunbin dukiya taban mmki”

Habiba ta rude tace,

“Toh yanzu me kikeso na Miki?”

Shiru Saratu tayi tace,

“Ai kinsan gidana Koh?”

Habiba ta Bata Rai tace,

“banason wulakanci Dan kinga inama binki?”

Saratu ta matsa zata wuce tace,

“Toh ai shikenan ki saurari sammaci”

Da sauri Habiba ta riko rigar ta tace,

“Toh naji Dana sani sai akayi me?”

Saratu tace,

“Saiki sameni da safe kamar karfe takwas kafin nazo Nan lkcn nayi nazarin Abinda Zaki bani”

Sosai Habiba ta hade fuska tace,

“ke ko aikatawa nayi iyakaci kenan bazan zo ba”

Saratu tace,

“Wannan Kuma ruwanki”

Tayi mgnr tana wucewa abinta, Habiba dake tsaye taja tsaki me ciwo sannan ta juya a tunzure tabar gidan gaba1.

~~~~~

A Daren ranar Saratu Bata rintsa ba tana saka da warwara harta mlm sale Saida ya tanka sbd idan ya bude ido Saiya ganta a farke Amma tace Masa karya wani damu kansa ai yanayin cikin ne yazo da Haka Nan kuwa karya take masa tana tunanin babban hukuncin da zata yanke ne, Dake mlm sale yanayin Asuba baya dawowa gida sai dare shiyasa be iya tsaida ido ba sbd bcci da gajiya Haka yaci gaba da Shan minsharin sa ita Kuma tana nazari. Kafin wayewar gari kuwa harta Gama yanke Abinda zata fadawa Habiba Nurse.

Washegarin ranar kuwa karfe 8:15 Saiga Habiba Nas a gidan Saratu, Saratu da tun dazu take zaman jiranta ta tashi cikin zumudi tana fadin,

“lale marhaban da zuwan Nas gidan Saratu”

Nas sai yatsina fuska take tana kallon gidan a wulakance Saratu Bata damu da hakan ba saima murna da take sbd Abinda ta yanke ya Mata dadi. A wulakance dai Nas ta zauna a gefen taburma tana kallon Saratu, Saratu tace,

“haba Nas irin Wannan Bata Rai kamar ni nace kiyi subutar baki?”

Nas ta wurga Mata Harara tanajin takaicin yadda saratun ke Mata badan taji komai ba tasan Bata Isa tana maida Mata mgn Haka ba Amma kalli daga jiya zuwa yau ta maidata kamar kakarta lalle masu iya mgn sunyi gsky da sukace mutunci Madara ne idan ya zube baya iya kwasuwa.

“Inajinki”

Nas ta furta a takaice, Saratu ta saki wani murmushin mugunta kai tsaye tace,

“a jiya naji kina zancen da kinada dama Zaki watsar da cikin Hajia Aisha koh?”

Da mmki Nas ta zaro ido tace,

“hakane kin ji ai toh mezan baki ne Dan karki fada Mata ni kina batamin lkci”

Saratu tace,

“So nake na karasa Miki cikar burin ki”

yanzu Kam hankalin Nas ne ya koma kan Saratu gaba1 da matukar mmki tace,

“me kike nufi?”

Saratu ta saki dariya kafin tace,

“Nas kenan A takaice dai yadda kike Jin haushin cikin jikin Hajia Ina tunanin na fiki Jin Takaicin sa”

A Razane Nas take bin Saratu da kallo cikin dunbin mmkin kalmar da taji daga gareta karkada kunnen ta tayi tace,

“da Saratu nake mgn?”

Saratu tace,

“Kwarai kuwa Abinda kikaji har cikin Raina nake fada Miki”

Nas batasan lkcn data bushe da wata irin mahaukaciyar dariya ba har tana dukan cinyar ta tace,

“Kam bala’in Nan kayyasa lalle masu iya mgn sunyi gsky da sukace Mutum mugun icce, Hajian Taki yau itace abar farautar ki?”

Saratu tace,

“ahto nayi laifi? Ke itafa duniya kowa kansa ya sani sai anayi Ana rufe ido a manta da Abinda ya faru baya sannan aci gaba”

Nas tace,

“Gsky ne yau na hadu da shadaniyar data fini”

Saratu tace,

“kadan ma kenan idan kikaji Abinda na yanke”

Nas tace,

“Toh me Kika yanke game da cikin? Karki manta fa Babu batun yin amfani da mgni Dan fita kasar waje ba wahala bace a wajen su yanzu kuwa sai a gano musabbabin zubewar cikin, idan kuwa gun boka ne Nima na buga na gaji tun kafin cikin yyi nisa.”

Saratu ta kyalkyale da dariya kafin tace,

“ni duk wannan tunanin banyi su ba sbd nasan kafin nayi tunanin kin gwada Babu sa’a”

Nas tace,

“Toh ke me kike takama dashi ne Haka har kike Jin yakini a zuciyar ki?”

Saratu tayi juyi da idonta cikin tsantsar mugunta da hada tuggu tace,

“Kamar yadda akayi Mana scanning ni da Hajia Yara maza ne a cikin mu, Kuma lissafi ya Tabbatar da lissafin watannin cikin mu tare yake tafiya, Haka nakeso duk ranar da muka haihu ki Tabbatar kin faki idon mutane kafin a yanyame jariran *KIYI MANA MUSAYAR ‘YA’YA, MA’ANA KI DAUKO YARON HAJIA AISHA KI KAWO A MATSAYIN NAWA NE, SANNAN KI DAUKI NAWA KI KAIWA HAJIA AISHA A MATSAYIN NATA NE* Toh daga lokacin……..”✍ðŸ?

Series Navigation<< Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 3Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 5 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *