Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 6

Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 5

This entry is part 5 of 6 in the series Zakaran Da Allah Yanufa da Chara by Nuceeyluv

5….

“Toh daga lokacin ni Kuma zanyi kokarin nesa da jaririn yadda baza’a fuskanci matsala ba, toh idan har yaran suka girma Kinga kenan Dana ne a wajen Hajia Aisha ni Kuma nata a wajena sai sun Gama sakankancewa nasu ne, sannan sun mallaka Masa komai na duniya sai muyi kokarin kashe su sannan mu San irin mafitar da zamu samu Dan yaron ya yadda ni mamansa ne Koda karfin sihiri sai mu jawo ra’ayin sa a lkcn da muka Tabbatar da duka Ahalin gidan basa duniyar kenan.”

Tafi Nas tahau Yi tana guda can tace,

“Bashakka burina na tarwatsa farincikin Hajia Aisha Yana gab da cikawa, ni dama Babu Abinda nafi tsana sama da Naga tana farinciki ke tun a school dinmu na tsaneta, Dan haka shawarar da kika kawo tayi sosai na Kuma jinjina da basirar ki da Ina Miki kallon kamar tunkiya Ashe kinada wayo”

duka Saratu ta kawowa Nas tace,

“banson wulakanci abin harda bakar mgn?”

dariya Nas tayi sannan tace,

“babban farincikina shine na hango danki shine a gidan suke rike dashi a zaton nasu ne Alhalin ba hakan bane, gefe guda Dan nasu Yana karkashin bakar rayuwa a gidan”

Nan ta karasa mgnr tana kallon tsarin yanayin kodadden gidan da Saratu take ciki, Saratu tasa dariyar itama tace,

“Tabbas zanyi Masa riko na Allah ya tsine, domin Saiya gwammace bezo duniya ba Zan wulakanta shi a idon duniya, Zan kaskantar dashi, Zan zame Masa tamkar bakin kumurci Dan bazai taba samun farinciki daga gareni ba yyinda Dana Yana can cikin daula Ana Yi Masa rikon Gata rarrafen kafet.”

Nas ta Mika hannu suka tafa tace,

“kamar kin shiga Raina kenan sai gashi kin rigani furtawa Abinda zance Miki kenan karki ragawa Dan kokadan, Dan nafiso Naga jinin Aisha na wulakanta a ido na”

Saratu tace,

“Sha kurumin ki kawata”

Nas tace,

“Tabbas mun zama kawaye sbd Wannan babban sirrin dake tsakanin mu”

Ana sukaci gaba da tattauna mugun nufin su akan Hajia Aisha.

****

Allah sarki, kana naka Allah na nashi Hajia Aisha batasan wainar da ake toyawa ba harta kayan baby’s Saida ta siyawa jaririn Saratu ita kanta saratun Saida tayi Mata sutura ta fitar suna, Saratu dai murna ta isheta duk ta kosa ma ta haihu yaron cikinta ya samu Gata da daula Dan yadda taga Ana ririta cikin Hajian Nan ba karamin Gata zaisha ba, a kwana a tashi Babu wuya a wajen Allah, kamar hadin baki kuwa saiga Hajia Aisha na labour tare da Saratu, yyinda Habiba Nurse tayi ka’in da na’in akan su Duk Wanda ya ganta Kai kace har cikin zuciyar ta take tausayin Hajia Aisha yanda tabi ta kanainaye wajen, Sosai take ta zirga2 a tsakanin su biyun wasu nurses din na Taya ta wato na kasan ta,  cikin hukuncin ubangiji saiga Hajia Aisha ta haifo yaronta namiji tubarkallah da sauri Habiba ta karbi jaririn tasa sauran Nurses din su gyara Hajian, saiga Saratu itama ta sullubo nata yaron a gurguje Habiba ta sake karban jaririn ya zamana Yara biyu ne a hannun ta, wata Nurse tazo karba Habiba tace,

“barsu Zan wanke su”

nurse tace,

“kar aje a hade su ne a kasa gane na kowa a ciki”

Habiba ta wurga Mata Harara tace,

“Zaki koyamin aikina ne?”

Da sauri yarinyar ta Girgiza Kai kafin ta kauce a hanya, Babu Wanda ya kawo komai a ransa sbd kowa ya sani dama Habiba Nurse itace me kula da iyayen yaran, cikin sassarfa ta gyarasu tsaf tana wani irin mugun murmushi, lkcn data Gama an wuce da iyayen dakin hutu Dan haka itama din can ta wuce, a gurguje ta Isa bakin gadon yaran kowa ta aje Mata nata wato dai yaron Hajia Aisha an sashi a gefen Saratu shi Kuma na Saratu an sashi a gefen Hajia Aisha, Ajewar ta keda wuya Hajjaju ta shigo dakin da Sallama, adan tsorace Habiba ta Amsa sallamar tana matsawa gefe, Hajjaju tace,

“Yadai na ganki duk bakida da nutsuwa kodai da matsala ne?”

Hajjaju ta tmby sbd yadda taga habiban ta firgice, Dariyar dole Nas tahau Yi tace,

“Haba Hajjaju ba wani Abu”

tayi mgnr tana nufar gadon jaririn Hajia Aisha ta dauko shi da sauri tana me mikawa Hajjaju shi tace,

“Ina tayaku murna Hajjaju ga jikan ki ya iso cikin koshin lpy”

Fadar hakan yasa Hajjaju ta manta da tuhumar da take yiwa Nas din ta rungume jaririn cikin tsananin murna tana sumbatar sa hade da mikawa Allah godiya, Fadi take,

“Ashe Rai kanga Rai me gidana? Yiiiii….”

Ta saki kuka tana matse hawaye tace,

“Ashe da rabon Zan ganka kafin kasa ta rufe min ido”

ta Kara mgnr tana zuba Masa ido sosai, kirjin Habiba Nas ne ya bada dam a ranta tace karfa tsohuwar Nan ta gano wani Abu ga jaririn Nan? Batare da Bata lkci ba tayi azamar barin dakin da sauri Dan karma Hajjaju ta tsareta da tmby Kuma a yadda take da Kama mutum tsaf saita kamo ta musamman da yanzu Bata da nutsuwa SBD faduwar gaba, Tana fita kuwa Alhaji Abdullahi na shigowa dakin shima da murna ya karbi yaron sai sumbatu yake a takaice ma har sujjada yyi ta godiyar Allah daya bashi Da, Toh Ashe duk wainar da ake toyawa Saratu tanajin su kawai dai idonta a rufe yake farinciki ne sosai ya mamaye ranta tasan danta ake ta rububi haka, yanzu ma kenan bare an koma gida Nan Dadi ya sake Kama ta a kalla dai yaronta zai taso cikin daula.

Fadin irin bidirin da aka Sha ranar sunan abin ba’ace komai, Hajia Aisha taso a hada sunan yaronta Dana Saratu tace a’a gida zata tafi sbd makota da Wanda aka Saba za’a zo ganin jariri, Hajia Aisha tace toh shikenan Nan ta hadata da goma ta arziki tace gashi Nan asha bidirin suna Albarkacin Ni’imar da Allah yyi Mana, Saratu ta karba da murna suka wuce gida, A Wannan Rana ta suna Alhaji Abdullahi Omar Mai fata ya sawa dansa suna *SAGEER* yyinda a bangaren Saratu kuwa mlm Sale ya radawa dansa suna *OMAR* Aiko takaicin sunan ya Kama Saratu kamar ta hambare mlm sale sbd sanin da tayi yyi daidai da sunan kakan yaron na Asali kenan wato baban  Babansa Abdullahi, Gashi ba damar ta nuna Jin haushin ta mlm zai iya son yaji dalili to ita me zatace Masa? Shiyasa ma a takaice take kiransa da *MARU*

~~~~~~~

Bayan shekara 18, abubuwa da dama sun faru a Rayuwar gidan Saratu da gidan Hajia Aisha ciki harda sake haifar Yara Mata da sukayi saidai Wannan karon Hajia Aisha ta riga Saratu haihuwa da kusan 3mthns kafin itama saratun ta haihu, A bangaren Reno kuwa idan muka fada gidan Alhaji Abdullahi Omar zamu hango tsantsar so da kauna da ake nunawa Sageer, Sageer ya taso cikin Gata da soyayyar Ahalin sa hade da daula me dunbin yawa hakan shi yake Kara Masa girman Kai da jiji da Kai, tun Yana yaro ya taso da bakin hali da mugunta mutum ne da yake da son kansa kwarai da gske, dayawa Ansha kawo karar sa saidai a bawa mutanen hakuri su kansu iyayen basajin dadin halin na Sageer shiyasa dayawan lokuta Hajjaju kance Masa Sam Albasa batayi halin ruwa ba, shiyasa ko kadan basa shiri da shi tafi shiri da kanwar sa Safna, gashi tun Yana primary irin marasa ja dinnan ne Sam bayacin exam Kuma hakan baya damunsa sbd shi Yana Tara Yara ne irinsa tsageru suyita Wasa suna shashanci ba karatun bane a gaban sa shiyasa ake ta Masa repeating sbd Alhaji Abdullahi yace baza’a wuce dashi ba saidai yaci da kokarin sa Dan haka besa harkar kudi akai ba,

A Wannan repeating din nasa yasa Omar dake hannun Saratu yyi masa fintinkau a karatu Dan ya kasance ZAKARAN gwajin dafi a makarantar su dukda ta gwabnati ce Amma yanada kokari sosai Dan koyaushe shine ke zuwa na daya a class dinsu, sbd kokarin sa ya samu damar zuwa wata private skul dake cikin garin kanon da taimakon wani wakilin ilimi daya kaiwa primary dinsu ziyara ya fahimci kwanya da Allah ya bawa Omar din sai ya biya Masa prvt skul din gaba1 harya Gama sanadin daya hadu da abokin sa Sadeeq kenan.

Wannan kokarin da Allah ya bawa Omar Yana matukar konawa Saratu Rai, musamman idan ta kalli yadda danta baida kokari ko kadan dukda Yana makaranta me Tsadar gske dake Garin kano ba kowa ke shigar skul din ba sai Dan wane da wane, Ada tayi matukar farinciki sbd danta zaiyi karatu mekyau sai gashi taga sabanin haka, shiyasa duk lkcn da Omar ya nuna Mata jarabawar sa atake take kushe Masa, Omar a lkcn tun baya damuwa harya zo ya fara damuwa domin baya manta wata Rana ya zana placement dinsa yaci yazo da murnar sa da tsalle Yana kwalawa Saratu Kira ummah…, Saratu dake daki ta fito da sauri Sahabatu ‘yarta mace na binta a baya  tace,

“Kai lpy meya faru?”

Bakinsa a washe yace,

“Kinga takardar shaidar shigata secondary naci dama bana Gaya Miki wani mutum ya biyamin prvt skul ba matukar na samu takardar?”

Cikin kunar zuciya ta warce takardar tace,

“kana nufin makarantar masu kudi zakaje?”

Omar ya Amsa Mata da murna yace,

“eh Umma badan komai yasa nakeson zuwa can ba saidan principal dinmu yace matukar inason na zama Dr. Saina samu ingantaccen ilimi yace hakan bazai samu ba idan ba private din na shiga ba sbd can anfi samun isassun malamai”

Wani kululun bakin ciki ne ya Kama Saratu tace,

“toh bazakaje can din ba”

tayi mgnr tana keta takardar hannun ta, sandarewa Omar yyi a wajen Yana kallon yadda mahaifiyar tasa take yayyaga takardar hannun ta, a daidai lkcn mlm sale ya shigo gidan da Sallama da mmki ya karasa garesu yace,

“lpy kike yaga takarda?”

Saratu na huci tace,

“sbd yaron Nan ya Raina Mana Arziki shine yaje yyi roko a sashi a makarantar masu kudi? Duka nawa yake Yana Dan takala futuk?”

Mlm sale yace,

“sbd Allah meye lefin yaron Nan da kullum kike zuga Masa fada tamkar bake Kika haifesa ba? Na lura duk wani cigaban sa fa bakyaso bansan meyasa ba Sam”

a harzuqe Saratu ta taso dama duk takaici ya cika Mata ciki tace,

“eh naji tunda Kai ka  Haifa min shi ko? Kai kasan zafin haihuwa kuwa da kke cewa kamar bani na haifesa ba? Toh idan be aminta Dani mahaifiyar sa bace ga kofa Nan ya fita daga rayuwata fakat…”

da sauri Omar ya sunkuya Zuciyar sa na zafi abubuwa biyu sun dirar Masa na farko irin tsanar da mahaifiyar sa keyi Masa Yana damunsa kwarai, na biyu bayajin dadin sabanin da suke samu tsakanin su da Abban sa, gashi abin ya sake gaba har tana ikirarin yabar gidan, Cikin danne zuciyar sa yace,

“Dan Allah ummah kiyi hakuri abin bekai har haka ba ni Wlh yadda kike zato ba haka bane da taimakon Allah da kokarina yasa na samu gurbin karatu a Wannan makarantar”

wani kululun bakin ciki ne ya sake Kama Saratu ta warce kafarta da Omar ya Kama tana Jan mugun tsaki sbd ambato kokarin da yyi Abinda bataso shine Sam bataso taji Omar din yanada kokari batason Abinda zaisa Rayuwar sa farinciki, so take Rayuwar sa ta dishashe ya zama irin jahilan Nan marasa aikin Yi cikin zafin Rai tace,

“karka Kara tabamin kafa banza marar amfani da haihuwar ka gwara barin ka Mtwsss”

ta fada tana barin wajen da sauri, Barinta wajen  keda wuya mlm sale Yaja Omar dakinsa suka zauna Nan ya kwantar da Omar kan cinyar sa Yana shafa bayansa, yyinda Omar yake Jan zuciya da sauri da sauri idonsa duk yyi ja ransa na Masa suya kwarai, tunowa da yyi takardar daya Bata photocopy ce sai hankalin sa ya kwanta, anan mlm sale ya fara bashi hakuri da ban baki kamar kullum.

Toh dake duk Abinda Allah ya rubuta Saiya faru hakan ya kasance, Dan Omar ya samu gurbin karatu na secondary a wata prvt dake cikin garin kano Kuma babban farinikin sa ma boarding ce sai ransa yyi fari tas harma yaji zaman boarding din yafiye Masa Dadi fiye da gida Dan Yana sawa ya mance kunci da takaicin da yake kwasa a cikin gidansu, Ana haka cikin Rayuwar sa ta boarding ya hadu d Sadeeq, A farkon haduwar su basa shiri Sam kowa Dan Shan kamshi ne, Saida Sadeeq ya lura Omar ya fishi Shan kamshi nesa ba kusa ba sannan yadan risina sbd shima krtn yazo ba shashanci ba Kuma dama burinsa ya hadu dame ilimi sai gashi Allah ya hadashi da Omar, a zaton sa ya dauka Omar Dan wani babban me mukamin ne sai a hankali ya fahimci Ashe Shidin ba kowa bane saima ta hanyar Alfarma dayazo makaranta, abin ya bawa Sadeeq mmki sbd kafin Omar ya amince dashi Saida shi Sadeeq din ya yada makaman yakin sa kafin suka kasance abokai daga Nan abotar tasu ta daure har izuwa Yanzu da suke matakin karshe a university dinsu.

Mlm sale Yana Shiga damuwa sbd muguwar tsanar da Saratu takeyiwa Omar ya rasa meyasa hakan ke faruwa sai wanna lkcn Allah ya nufe shi dajin sirrin su tana waya ita da kawarta Habiba Nas da suka zama kawayen gaske. Dalilin kenan daya jawo kwanciyar Mlm sale a hospital kenan.

Taikaitaccen bayanin waye Omar kenan hade da sanin Asalin Sageer Hadi da sanayyar abotar Omar da Sadeeq.

*WACECE MEERA?*

Hafsat Ibrahim kenan ‘ya daya tilo wajen Alhaji Ibrahim Usman (Dad) kenan da matar sa Hajia Amina, yarinya hafsat wadda suke kiranta da Ameera sbd sunan maman Dad da taci yarinya ta taso cikin Gata da soyayyar iyayen ta, tana primary 4 mahaifiyar ta Hajia Amina ta rasu sanadin haihuwa yaron ma bezo da Rai ba, dad ya Shiga damuwa kwarai dgske gashi kullum Ameera kuka take itadai mamanta, haka Dad zaice zata zo, toh abin yaci tura sbd hafsat har Rashin lpy tayi sbd kukan Rashin mahaifiya, Ana haka abokin dad ya bashi shawara ya Kara aure kodan ita ameeran tunda mace ce sai a samu me kula da ita, sosai Dad ya gamsu da Wannan shawarar harya Shiga sahun zawarawa Dan neman aure,

Ana haka Allah ya hadashi da Sadiya(Mom) Sadiya bazawara ce Dan tayi aure harta haihu Yara Mata biyu Shafa’atu da Jamila, Karshe auren ya mutu ta dawo gida zawarci, Cikin ikon Allah dad ya nemi auren Sadiya batare da Bata lkci ba ta amince musamman data ganshi da maiko, kafin auren ya shaida Mata yanada yarinya me suna Ameera Sadiya tace ai kar yaji komai da na kowa ne zata rike Ameera da Amana, dad yaji Dadi kwarai da Wannan kalaman nata batare da Bata lkci ba aka daura aurensu cikin aminci, a kwana a tashi Sadiya tayi renon Ameera na marmari da ganin ido Bayan wata guda kuwa ta fara yunkurin fadar qudurin ta wajen Dad,

 Wata Rana suna tare ta nemi Alfarmar dad akan tanaso ta dawo yaranta gabanta sbd Yara Mata ne rikesu Dole sai uwa sbd tarbiya, Dad ya amince Mata sbd yaga yadda take nuna kulawa akan Ameeran sa, a takaice dai yaranta sun dawo sannu a hankali Ameera ta fara ganin banbanci a gidan, kafin wani lkci har an fara janye hankalin Dad akanta Saiya kasance Shafa’atu da Jamila sun fita nuna Isa da gidan ubanta akanta, Saiya kasance zuwa yanzu Ameera itace meyi musu duk wata wahala ta gida Dad Yana kallo bazaice komai ba saima hantarar ta da yake idan tayi lefi Ameera dai sai gani tayi kamar Wanda aka canja Mata Dad dinta me tsananin sonta zuwa wani can daban kamar besan wacece itadin agareshi ba. A kwana a tashi Babu wuya a wajen Allah sai gashi Ameera dakinta ya koma shine nasu Aunty Shafa haka wardrobe dinta shine nasu kayanta ya zama nasu sbd da kadan suka fita a shekara a surar jiki kuwa ta fisu shape saima ragewa da sukayi, ita Kuma me daki kayanta ya koma Ghana masgo me cike da kodaddun kaya, Kuma wajen kwanciyar ta shine dandanin kasa komai Sanyi kuwa.

 A haka Ameera ke rayuwa a gidan mahaifin nata tamkar Bora, inda Allah ya rufa Mata Asiri tana zuwa school har yanzu tare suka fita a secondary yanzu kuma zasu Shiga B.U.K.

*CIGABAN LABARI*

…..✍ðŸ?

8/15/20, 8:00 PM – Ummi Tandama: *ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA….🐓*

( _Ko Ana Muzuru Ana Shaho Sai yayi_)

Series Navigation<< Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 4Zakaran Da Allah ya nufa da chara chapter 6 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *