Amatulmalik Chapter 5

Amatulmaleek Chapter 6

This entry is part 5 of 6 in the series Amatulmalik na Mamuhgee

6

A qasa kan tiles Maamah tayi kwanciyarta kan daddumar sallah tareda Abdulhameed Daya shige jikinta tin tana jiran farkowan AmatulMaleek har bacci ya Dan fixgeta itada Abdulhameed din.

So biyu ana Aiko khaltume dubasu ko sun tashi Amma Basu tashi ba Kuma Madame tace kada a tashesu Dan haka aka barsu sukai bacci sosai batareda Maamah din ta san ta dauki lokaci sosai haka tan baccin ba.

Sanyin tiles ya dayayi musu yawa ya farkar da ita dole lokacin karfe biyun Rana harda minti talatin da takwas Dan haka cikin sauri ta tashi tana janye Abdulhameed Daya cukuikuyeta sbd sanyi ta miqe tsaye tana kallan gadon Taga AmatulMaleek din itama tana motsawa alamar tashi zatayi Dan haka toilet kawai ta wuce Tayo alwala ta fito tayi sallah tana idarwa Amatu na farkawa Dan haka itace ta kamata da kanta takaita toilet tabarota.

Ita kanta Amatu ta Dan iya aiki da wasu abubuwan bandakin sbd zuwan da suka taba yi tafara Dan wayo lokacin.

Fitsari tayi Tayo alwala itama ta fito ta tsaya gefen Maamah tayi sallah tana idarwa Abdulhameed na na tashi daga baccin Shima.

Da sauri Maamah ta miqe ta rakasa toilet sbd fitsarin dayake cewa ya matsesa.

Bayan fitsari harda zawo yayi sbd abincin Daya Dan fara tabashi kasancewar ciki Bai Saba da wannan dadin ba,

Fitowa yayi bayan Maamah ta wanko masa hannuwansa da kyau da sabulu

Gefen AmatulMaleek ya zauna Yana kallan kayan abincin Dake gefen ajiye yafada mata nata ne sunci sun rage Mata tin dazu.

Kallansa Amatun tayi bayan ta Kalli kayan abincin Amma Bata motsaba sbd ba Maamah ce ta Bata ba.

Maamah kuwa toilet din tahau wankewa sosai sbd kada su lalata musu guri Dan tasan tsananin karfin tsaftan masu gidan sbd duk Wanda ko kalilan sani yayiwa ASH TALBA yasan inda qazanta take da inda yake akwai Nisa me yawa da zurfi.

Sosai ta Saka karfinta ta wanke toilet din tayi masa fes ta fito tana kallan Amatu Dake zuru tana kallan Abdulhameed Dake ta fada mata dadin abinda suka ci din tana bacci.

Wani sanyayyan murmushi maamah tasaki tana qarasowa fuskarta a sake ta kallesa tana cewa

“Gashi Kuma bazaka sake ci ba yanzu sbd yafara lalata Maka ciki.”

Dariya yayi Yana maqale kafadarsa Yana cewa

“Zan sake ci mana ai idan munkoma bazan sake ci ba shikenan.”

Daga Maamah har Amatu da batada karfin jikinta qaramar dariya suka saki sbd yanda yake matse da a dauko abincin.

Maamah ce ta janyo abincin bayan ta zauna itama a tareda su qasan.

Bude abincin tayi da kanta ta zubawa AmatulMaleek komai kaman yanda suka hade tana cewa

“Ki cinye tas sbd Kinga ba karfi jikinki ta yanda zaku samu kuzari sai muje akaimu ku gaida mommynku Abeeda harma da sauran mutanen gidan.”

Gyada Kai kawai AmatulMaleek tayi tana Saka hannu a abincin sbd itama ya shiga ranta sosai duk da batada kwadayi Amma shi abinci irin wannan basama ganinsa bare.

Abdulhameed ma dole tareda Amatun ya sake cin abincin itama Maamah hannu ta Saka sukaci abincin tare su uku Abdul naci Yana tambayar AmatulMaleek idan tanajin dadin dayake ji a abinda sukeci din.

Dariya Amatun ta Dan ringa yi masa tana cewa

“Maamah wlh ‘dan Nan naki duk ya haukace sbd cin abinda be taba ci ba.”

Itama Maamah din yar dariya tayi tana cewa

“Kyalesa yaci ai na kwana biyu ne muna komawa kaman yanda ya fada shikenan.”

Cikin kulawa da tsananin so da kaunar juna sukaci abincin su uku suna Dan magana Sam sama,Maamah kusan duk Rabin cin abincin nata su take gyarawa kidin tana ja ye musu qashinsa abubuwan data San bazasu iya ci ba tana musu fira cikin kulawa da kaunarsu.

Suna gamawa wannan Karan su ukun suka shiga toilet suka wanko hannuwansu Maamah na fitowa ta tattara gurin tareda kayan ta fito dasu  ta nufi hanyar kitchen tana isowa khaltume da Masu aikin abincin Dake girkin dare kallanta sukai tareda karban kayan hannunta.

Kallan khaltume tayi tana cewa Ina zata wanke kayan saita wankesu da kanta.

Karban kayan khaltume tayi tana cewa ta barshi kawai.

Kasa tafiya maamah din tayi sai data taimakawa khaltume gurin wanke kayan kafin ta koma.

Zama sukai a dakin shiru daga ita Se su Amatu suna Dan firarsu sama sama  sbd daga Amatun har Abdulhameed sun warware kamar ba’a nade aka shigo dasu ba ba lafiya sosai Daman yunwa ce da wahalar hanya Se iska da sanyin kwanan Tasha.

Har yamma Babu Wanda ya shigo inda suke aka nemesu Suma haka sukai zamansu.

Koda Akai sallan magrib Wani abincin aka sake kawo musu Basu ci ba sai da sukai sallah tukuna suka zauna sukaci a plate Daya su dukansu dayake wannan Karan farar Basmati rice ce da brown chicken stew wadda Babu Mai sosai acikinta sbd lafiyansu da suke kulawa da ita sosai a gidan.

Kazar Dake cikin miyan zata Kai guda harma da Rabi Kila Dan kuwa duk yanda sukaci ta Basu cinyeba hakanan suka tattara kayan Maamah dince ta sake fita dasu takai kitchen ta dawo.

Har Akai ishai baazo antafi dasu can gurin masu gidan ba sbd umarnin da Abeeda ta bayar na a barsu suyi kwana biyu suci su huta yanda ya kamata kafin su fara Dan zagayawa sbd sam Bata kaunar ganinsu a yanda suke din.

Da daddare maamah barwa Abdulhameed da Amatu gadon tayi sbd baida Wani girman da zai daukesu su uku Dan haka tayi kwanciyarta qasa tabarsu a saman sukai bacci.

Bacci sukai sosai Wanda suka jima Basu irinsa ba sbd samun gurin baccin me nutsuwa ba sauro ba komai Dan haka har Akai asuba Basu saniba Saida gari yayi haske Maamah ta Farka tana tashi zaune kafin ta miqe ta nufi toilet Tayo tsarki da alwala tana fitowa kafin ta tada sallah ta tana Amatu tana Kiran sunanta a nutse.

Cikin baccin dabe saki Amatun ba ta Bude idanuwanta masu Dan girma tana cewa

“Maamah baccin be sakeniba”

“Tashi kiyi sallah Se ki koma tinda Babu aikin da zamuyi anan din.”

Sake Dan juyawa tayi tana Bude idanuwanta tareda Kai hannuwanta duka biyu tana ture kafafun Abdul Dake kanta cikin Wani shegen mugun bacci Wanda ko a gida haka suke kafin safe ba qaramin shuri takesha a gurinsa ba sbd Mayen baccinsa.

Saukowa tayi gadon tana murza idanuwanta ta nufi bayin ta shige tana Bude idanuwanta dakyau sbd kada ta zame.

Koda ta fito Maamah tagama sallah tana zaune tana Dan kokarin tada Abdul Shima cikin kulawa da rarrashin ya tashi yayi sallan.

Sallah tayi tana idarwa itama ta zauna gefen maamah din wadda da kanta takai Abdul toilet yayo fitsari da alwala,

Inda ma Allah yayi mata babban rufin asirin dukkaninsu yayan nata Babu me fitsarin kwance da batasan ya zatai ba.

Bayan sun gama sallah Amatu ce ta kwanta qasa Maamah din Kuma da Abdul suka koma kan gadon suka kwanta dukkaninsu baccin ne ya sake daukansu hankali kwance.

Se qarfe Tara aka kawo musu abincin breakfast Wanda Tintini Daman sun tashi har sunyi wanka sbd kada Azo a taddasu da kowacce irin rashin tsafta.

Ayau ma lafiyayyan breakfast suka sake karyawa dashi Wanda kusan iri Daya Dana jiyan ne sedai yau tareda Wani Irin tea me shegen kauri Daya Saka Abdul ringa fadar akwai Madara sosai a cikin shayin.

Haka suka sake wuni guda Babu Wanda yazo ya tafi dasu sedai abincin da aketa kawo musu da lokacin cinsa yayi.

Bata damu da cewa Se sunje gurin Abeeda ba sbd tasan tana sane dasu Kila wata hidimance ta riqeta Batada lokacin ganinsu yanzu.

Abdul kuwa Jin yayi shikam yafara son gidan sbd dadin dasuke ci Kuma basa komai bayan kwanciya da Shan AC Wanda sanyinsa yafara taba Amatu ita Dan Sam Bata son sanyi duk da tana yarinya yanzu ne ze tabata.

****Kwanaki kusan hudu masu kyau aka Basu suka huta yanda ya kamata bayan ci me kyau da sha me kyau Babu abinda suke Samu,

Hatta yar suturar sakawa anbasu dukda ba masu yawa bane Amma sukam a gurinsa me yawan ce,

Abdul sosai a yanzu yaji bayason su koma gida Dan kuwa shi ko wannan ci a koshin da abinci mekyau aka barsa ganin yakeyi duniyarsu ta gyaru Dan haka tini shi Kam ya fara kumatun Kwana biyu,

Amatun ma ta Dan yi kumatun duk da batada jikin kiba ko kadan Amma dai ita cima me kyau da wuri take nunawa,

Maamah kuwa sosai ta dage da kulawa da inda aka ajiyesu din sbd karsu lalata inda aka ajiyesun kafin su tafi hakama duk takai kayan abincinsu kitchen seta Dan taimaka musu da Wani aikin sbd Bata Saba da zama Babu aikin komai ba Jin takeyi duk ba dadi sbd su Basu Saba da Hutu ba da wahala suka Saba.

Ranarda suka cika kwana biyar da zuwa aka Aiko khaltume ta tafi dasu cikin asalin gidan inda masu gidan suke,

Kai tsaye sashen Abeeda aka nufa dasu khaltume na gaba suna biye da ita.

Abdul na hannunsa na riqe cikin na maamah sbd kada yanda yake kalle kalle,

Amatu kuwa tana gefen maamah din itama tana Dan kallan koina.

Babban palon Abeeda ko yau aka nufo dasu suka zauna ‘yayanta na gefenta matse da ita suna Dan kallan makekiyar flat screen tv din Dake aiki a palon ba murya sosai.

Abdul sai taba Amatu yakeyi Yana nuna mata abubuwan da duk idanuwansa suka Gani na mamaki ita Kuma tana gyada masa Kai sbd batasan me zata ce masa ba.

Basu Wani jimaba Abeedan ta fito fuskarta dauke da murmushi me yalwa da kulawa tareda kauna a Fili tana kallansu ta qaraso sanye cikin Wani milk dry lace Daya gama bayyanar da kudinsa sbd yanda take a kwance kamar cotton.

Zaunawa tayi idanuwanta dasuka fada suna kan AmatulMaleek wadda gabaki daya Babu abinda ta baro na mahaifiyarta Asmaun sai haske data Fi Asmau Amma komai na maamah dinne.

Manyan idanuwanta farare ta kalla tana mamakin Irin kamannin Asamun da Amatu ta koma sak,

Numfashi ta sauke ahankali tareda sake fadada murmushinta da kulawanta tana miqa hannunta ta Kila Abdul Wanda yake kallanta Amma ya kasa zuwa sai maamah Daya kalla wadda cikin murmurshi ta gyada masa Kai tana cewa

“Jeka ka gaida mommyn UK da kaji Amatu na fada”

Amatu kuwa cikin nutsuwa da girmamawa itama ta Bude Baki ta gaidata cikin Dan sakewan fuska da ganin mommyn.

Amsawa tayi itama tana Jin kaunar yaran tace

“Asmau AmatulMaleek ta fara zama budurwa Ashe,

Allah yasa dai kada iyayen Nan nasu Maza suyi tinanin yimawa auren kauye da wuri sbd bazamu yarda ba Sam da wannan dabiar ta kauye”

Dariya mara sauti maamah tayi tana cewa

“Toh ai sedai ace Allah ya tsare Amma Kam Kila Hakan zaa samu”

Dan kame fuska Abeeda tayi tana sake qarewa Amatun kallo Tana cewa

“Sam wannan bazai yiyuba sbd zasu kashe rayuwarta ne,Ina Sam Sam,wannan ai rashin hankali ne da cutatar da rayuwar Yara qanana sbd wasu shekarun nasu da gaske Basu kaiba.”

*_AMATULMALEEK_*

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

7

Maamah kasa cewa komai tayi sbd batasan mema zata ce din ba idan Akan wannan maganar ne Dan kuwa ko ita bazata taba son ayiwa AmatulMaleek auren wuri na kauye ba Amma Babu yanda zatayi idan su kawu suka Yanke mata Hakan.

AmatulMaleek kuwa da Abdul dasuke gurin Basu Wani Maida hankali ga abinda su maaman ke magana akaiba Dan kallo sukeyi,

Ganin Hakan Abeeda takira khaltume ta tafi dasu palon Husnah da Haydar suyi kallon acan.

Bayan antafi dasu AmatulMaleek din zuwa can Abeeda kallan Asmau tayi a natse tana son jin da gaske idan auren kauye din zaawa AmatulMaleek.

Shiru Maamah tayi sbd batasan me zata fada ba Dan kuwa kota Bude Baki ta fada ko kada ta fada Abeeda tasan batada ta cewa akan Hakan,

San numfashi kawai ta sake tana cewa

“Tinda Bata karatu Kam ai auren dole ne da wuri Koda bamuso Hakan ba”

Cikin mamaki da Dan takaici Abeeda tace

“Ke Zaki yarda kenan ayi mata Hakan?

Kuma Asmau me zaisa ki bari ‘yarki taqi karatun Boko?

Yanada mahimmanci fa kema kinsan Hakan.

Fada Abeeda ta hau yi sosai Wanda ya Saka maamah yin shiru kanta a qasa batareda tasan me zata ce ba Dan kuwa fada ne Abeedan keyi kamar tanayi da ‘qanwarta ko ‘yar aikinta.

Abeeda ji tayi duk haushin Asmau ya rufeta Dan haka ma ko firar kirki basuyiba saita damuwa da takaici.

Su Amatu kuwa suna can zaune palon su Husnah duk da Husnah din Bata Nan tana can tareda mum Aisha tin da Akai rasuwar Basu dawoba tkuna Haydar ne kawai anan.

Kallo sukasha sosai hankali kwance sai kusan magrib maamah ta jasu suka koma inda suke wato bangaren masu aiki.

Kwana sukai Abdul na firar abinda suka ringa kalla a TV ita Kuma Maamah cikin damuwa ta kwana sbd Abeeda datai mata fada da maganganu dasuka Saka zuciyarta rauni akan rayuwar datake ciki da ‘yayanta.

Amatu kuwa data fahimci damuwa a tareda mahaifiyarta itama sanyi jikinta yayi Dan haka dukansu a sanyaye suka kwana.

Koda gari ya waye maamah data Dan fara sabawa da fitowa Taya masu aiki ayyukansu,fitowa tayi ta nufi dakin khaltume ta kwankwasa mata ta tambayeta idan akwai aikin da zaa Taya dashi.

Ba musu khaltume ta nufi kitchen da ita ta tayasu da aikin fere dankali da doya harma da wasu ayyukan Dan kuwa maamah din tanada nutsuwan aiki da tsaftan Daya sakasu Dan bari tana Saka hannu a aikin.

Dayake kowa ya samu Rana shanya garinsa yakeyi sai gashi cikin kwanaki kalilan masu aikin gidan Kokuma ace khaltume datake babba a cikin ma’aikatan gidan sun mayarda Maamah din kamar me aikinsu Suma kusan duk wasu ayyukan kitchen din Banda girki itace take yi musu,

Ita Kuma Bata taba Jin gazawa ba ko jin an Renata ko wulaqanci ne sbd dadi ma takeji ganin tana yiwa Abeeda da Ash hidima a gidansu da karfinta tinda batada abin biyansu da tarin alkhairansu gurinta Dan haka da zuciya Daya take aikinta.

Abeeda batasan tana aikinba sbd sam Bata zama sosai yanzu da asmaun iyakacinsu suzo su gaidata ta danyi fira sama sama da asmaun su koma.

AmatulMaleek ma data ga dai aikin na gaske ne itama sai tana biyo maamah din kitchen tana kama wasu ayyukan Dan kuwa zuciyarta Bata nutsuwa ganin mahaifiyarta na wahala duk da aikin gidan Sam bama zasu kirasa da aikin wahala ba tinda komai a tsare akeyinsa yanda yake a tsare.

Sunanan Babu cikakken sanin matsayin zamansu Wanda ake nufin jiran dawowar Me gidan sukeyi da mum Aisha maamah tayi musu gaisuwar rasuwar data sakota zuwa Amma ba alamar zasu dawo kusa hakama ita kanta Abeeda tafiya kamata tayi zuwa porthcrt ta kwana biyu Dan haka tana tafiya suka sake zama Wani iri a gidan.

Abdul dai tini ya koma Dan masu aikin gidan sbd maamah aka barwa Haydar Dan haka akace su koma can cikin gida suna kwana sbd Haydar din kafin maamah ta dawo duk da akwai masu aikin Dake kulawa da cikin gidan dama Haydar din Wanda kusan shekarunsa Daya da Abdul.

****Acikin kwana biyu da tafiyar Abeeda Haydar yaji dadin zama acikinsu maamah da Abdul da AmatulMaleek sbd su Kam tsananin son junansu da kulawa da juna sukeyi tareda wasa,

Duk da Amatu ta girmi Abdul sosai Hakan Bai hanata zaka qawarsa ba abokiyar wasansa Kuma abokiyar fadansa ba hakama itama Maamah sosai take sakewa da yayanta tana San biye musu wasu lokutan musamman idan ba kowa sbd idan akwai mutane tana bayyanarda kunyarta ta haihuwar fari ga AmatulMaleek sosai sosai shiyasa a duk lokacinda Abeeda tace mata “yarki AmatulMaleek” Jin Kalmar takeyi ta mata Wani irin nauyi.

Tsakanin Abdul da Haydar harma da Amatu cikin kwana biyu sunyi wasa da ‘yar sabuwa Dan haka Koda Abeeda ta dawo tayi mamakin yanda Haydar yake wasa sbd sam Baya wasa Baya Wani fara’a kamar ‘dan dayake cikin qunci,

Husnah ko tana Nan Sam Bata Wani sake masa sbd son girma da ganin batada lokacin wasan banza dashi ita datake zama ‘yan mata,

hakama masu aikin gidan Babu me Dan wasa dashi kulawa kawai suke basa Dan haka Sam shi rayuwarsa ta yarinta Bai ganewa komai na Jin dadi da sakewan qananun Yara ba,

Idan ya Dan samu wannan sakewan to Brother Naufal dinsa Yadawo hutun daga school Yana Nan Dan haka shi wata sabuwar rayuwar ya Gani a tattareda su Amatu da maamah.

Abeeda bataji komaiba saima dadi dataji Haydar din ya sake Yana wasa sosai Dan haka saisu Amatu da Abdul suka samu sake da Daman zuwa sashen aduk lokacinda sukaso ganin Abdul din haka Shima da Bai taba sanin tayaya ma ake zuwa sashen masu aikin gidanba sai gashi yana zuwa a duk lokacinda yaso.

Dawowar Abeeda ma ta fahimci maamah na aiki cikin masu aikin gidan ko datai mata magana maamah ta nuna mata ta gaji da zaman banzan ne shiyasa take taimaka musu.

Abeeda Bata hanata ba duk da dai tasan Hakan Bai kamataba sosai Amma tinda asmaun naso saita barta kawai.

Kullum da daddare suke zaunawa a palon na Asmau su tattauna maganganunsu da yar firarsu ta Aminai kafin Asmau ta dawo ta kwanta.

Ita kanta Abeeda a yanzu datake samun Wanda kullum take fira dashi sai take Jin dadin rayuwar tata da kullum Hutu ne da Bada umarnin sai wayoyi Dan aiki ma ta Dena zuwa kwata kwata.

*****Satinsu biyar harda kwanaki da zuwa Amma har lokacin ASH TALBA Bai dawo ba gashi Yara sunyi sabo sosai da Haydar Wanda a yanzu ko abinci yafison yaci gurinsu Abdul ko Amatu wadda yakejin yafisonta antinsa akan Husnah dasuke uwa Daya,

Hakama maamah Jin yakeyi yafison zama a gurinta sbd yanda ko abinci sukaci itace take wanke musu hannuwa da Baki hakama yanda Abdul tasaba duk da ya Dan girma itace take masa komai Dan haka Shima a yanzu din itace take masa komai tini ya Dena son wankan masu aiki Sena maamah hakama Amatu itace ke masa Shirin zuwa school yafison nata.

Duk wannan hidimar maamah bata Dena zuwa kama ayyukan gidanba Dan kada suyi zaman banza Dan haka a sane khaltume ta sallami masu aiki biyu daga cikinsu tabar biyi masu shara da tsafatace gidan kawai aikin kitchen kuwa daga me aikin girka abinci sai maamah Dake sauran duka ayyukan batareda Jin gajiyawaba ko damuwar komai.

Shakuwar Amatu da Haydar yasa Abeeda Jin batason su tafi sbd ‘danta ya samu sakewan da suketa son yayi ya more yarintarsa Dan haka ta ringa Jin batason tafiyar tasu ko dan Haydar.

Abdul kuwa yasamu abubuwa na karuwa sosai daga Haydar,

Kamarsu sutura masu kyau da takarma dasu kayan wasa haka masu girma da tsada Dan haka shima tini yaji bayason su koma musamman idan suna garden na gidan suna wasa dasu keke da lilonsu Haydar din su basuma San akwai irin wannan duniyarba a gidan Saida suka hade da Haydar.

Abeeda ba mace ce me yawan son fira ba shiyasa sai dare suke Dan zaunawa su zanta da Asmau wadda zuwa lokacin Asmau tafara Jin kanta a tsarge idan tana tareda Abeeda sbd matsayin ba Daya ba hakama ita datake cikin Yan aikinta Jin take kamar yanzu Abeeda tafi karfinta duk da so da kaunar junansu a jininsu yake Kuma Abeedan Bata taba nuna mata tafi karfin nata ba Dan kuwa bayan Maamah din Babu me zuwa ya zauna kujera Daya da ita suyi magana irin wadda Bata taba iyayi da kowa a duniya harma ASH TALBA Wanda yake mijinta da Bata hada komai da kowa dashi ba a zuciyarta da rayuwarta.

Lokacinda suka cika sati Shida cif a gidan su mum Aisha suka dawo tareda Husnah wadda take matiqar ji da ita sbd yanda Ash Shima yake matiqar ji da Husnah din kasancewarta suna mata kallan ‘dan uwansu da suka Rasa.

Daga isowarsu tun a harabar gidan mum Aisha ta hango garden din gidan da Haydar ke wasa tareda Abdul suna Jan gashin AmatulMaleek Da Maamah tagama kunce mata da wankewa tareda daure mata kafin da daddare ta mata kitsonsa Dan ta Saba itace ke Mata kitso tin tana yarinya Tin Bata iyaba kuma haryanxu bawai ta iya kitson bane sosai Amma de itace take mata ahakan.

Jan gashin sukeyi suna guduwa tana binsu fuskarta a Dan sake sbd ko taso tayi fushin dasu kasawa takeyi Dan batada zafin Rai ko zuciya ko kadan.

Abdul Daya Saba tsokanarta shike fadawa Haydar inda zasu ja gashin su gudu ai bazata iya kamasu ba.

Haydar ma da wasan ke masa dadi sake kamawa yakeyi Yana Dan ja ahankali.

Haydar din tafara kamawa tana cewa

“Wa na kama??

Zaku sake??

Hannunsa take kokarin dagawa sama ta kama kunnensa yafara dariya sosai me hade da ihun Kiran sunan Abdul Wanda yazo da sauri yaja janyesa suna dariya itama Amatun dariya takeyi duk da taso maganinsu.

Dakatawa mum Aisha tayi cikin Isa da Wani irin iKon Daya gama zama jikinta ta kallesu da kyau Taga Haydar ne ke wannan ihun da dariyar,abinda Bai tabayi ba,Babu Wanda a gidan ze ce ya taba ganinsa a cikin wannan Nishadin.

Husnah data fito motar a hankali itama riqe da qatuwar Apple iPad dinta sanyeda doguwar English straight gown black kallan gurin tayi fuskarta da Dan mamaki Kai tsaye tacewa khaltume

“Su waye wannan din??

Cikin girmamawa khaltume ta Dan dubi mum Aisha da ba ita tayi tambayarba tace

“Yar uwar Madame abeeda ce wadda take magana tazo tareda ‘yayanta biyu yau sati Shida da zuwan nasu.”

Mum Aisha da take ta fahimci Asmau ce tazo Bata tsaya sake Bata lokacinta a tsayuwarba ta wuce a natse qamshinta na cike iskar gurin, Husnah ma bayanta ta bi tana wucewa sashen mahaifiyarta Kai tsaye khaltume na bayanta da set din akwatinta biyu na lv suka shige

Ita Kuma mum Aisha saratu me aikinta ce ta ja nata kayan ta bita duk suka shige.

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

8

Koda su Husnah suka dawo gidan take masu aikin gidan suka sake shiga taitayinsu sbd mum Aisha da Sam Babu sauki a lamarinta Dan kuwa ko barin kaya baa da iKon yi zaka iya rasa aikinka a gidan Dan kuwa itace me fada aji,itace me iKon zartarwa akansu.

Husnah ma kusan halayenta tafi dauka Dan itace tamkar madubinta Kuma yar lelenta Dan haka kusan halayenta ne Husnan ke dauka duk da yanxu ne take zama Yan mata Amma dai halayenta a Fili suke Tin yanzu.

Koda maamah taga dawowan Husnah sosai ta shiga farin ciki sosai da ganinta ta rungumeta tana ambatar sunanta cikin tsananin kaunarta tana tambayarta ya gajiyan hanya.

Amsawa Husnah tayi tareda gaida maamah din Dan kuwa duk Wanda yake tareda mahaifiyarta Kona sati ne saiyasan maamah a bakinta da matsayinta a zuciyata Dan haka tasan wacece Maamah din a gurin mommynta.

Maamah datake farin cikin ganin Husnah itace da kanta ta gyare mata dakinta fes yanda takesonsa tareda komawa kitchen aikinta,

Ta sanar da AmatulMaleek da Abdul ‘yarta Daya ta dawo wato Husnah.

Dayake Abdul shi dinma dayake qanqani yasan sunan Husnah a bakin maamah hakama shi a farko ya dauka da gaske ita din ‘yar maamansu ce sbd yanda take fadarta har cikin zuciyarta da gaskiar kaunar datake mata.

Amatu da Abdul sunji farin cikin dawowar Husnah dan haka suka kwana da Shirin da safe zasuje su mata sannu da zuwa kamar yanda maamah tace.

Washe gari maamah din da kanta sukaje tare takaisu suka gaisa da Husnah wadda Babu laifi ta Dan sake musu din Su Daman ba saurin sabo ne dasu ba Suma Dan haka suna barowa dakinta gurin mommy Abeeda sukaje suka gaidata itama cikin kulawa da kauna ta amsa musu kafin suka fito suka tsaya gurin Haydar Amatu ta shiryasa bayan Maamah tai masa wanka Yana ihun bayason Amatu ta shiryasa sbd kada ta gansa ba kaya Amma hakanan suka dannesa itada Abdul harta shiryasa suna masa dariya ya fito yaci abinci Suma anan suka ci abincin dole sbd mommy Abeeda din da Husnah suna kan dining hakama Haydar Dan haka dole akace Suma suzo su zauna.

Dayake Amatu nada hankali sai Bata Wani sake taci sosai ba kamar yanda Abdul ya saki ciki yaci ya koshi Shida Haydar suna wasa da dariya Wanda Hakan ne ya Dan raya gurin daga tsit din Daya dauka.

Suna Hakan mum Aisha ta fito take suka nutsu Amatu tayi saurin gaisheta tana sauke kanta qasa daga kallan dataga mum Aisha din na mata Wanda ya Sakata Jin jikinta na sanyi.

Husnah ce ta gayar da ita tana sake fuska sosai.

Itama mum din murmurshi tayi tana sake fuska tafara amsa gaisuwar Husnah kafin ta amsa ta Amatu data cire tsammanin zata amsata.

Abdul kuwa Sam baima San da ita ba saida tayi musu magana cikin yar tsawar data Saka Abdul sauka daga kan dining din Yana dawowa gefen Amatu idanuwansa akan mum Aisha din wadda kyanta da fadan datakeyi suka sakashi yin shiru tsoronta na shigarsa.

Daga wannan lokacin suka nutsu sama sama suka qarasa suka koma inda suka fito.

Bayan tafiyarsu Babu Wanda yace komai sai Haydar Daya gama Shima ya sauko khaltume ce tazo ta tafi dashi zuwa inda driver ke jiran fitowansa ya shiga mota aka tafi dashi zuwa school.

Koda suka koma daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya fadawa maamah abinda ya faru saima zamansu da sukai daki suna abubuwansu.

Koda Rana tayi zaa tafi Kai Haydar Islamic school taredasu mommy Abeeda tace atafi su fara karatun kafin su tashi komawa.

Murna sukai sosai Dan kuwa Daman sunaso fita su Dan ga gari.

Su hudu aka tafi dasu harda Husnah wadda ta kwana biyu Bata zuwa sbd tafiyarsu.

A motar daga Abdul sai Haydar ne keta surutu suna farin cikin zuwan nasu makaranta tare,

Itama Amatun tana farin cikin zuwan makaranta duk da Babu Wani sakewa tsakaninta da Husnah Amma dai tinda gasu Haydar tasan batada kadaici.

Koda suka Isa makarantar tini akaiwa su Amatu komai Dan kafin zuwansu Akai wayar zaa kawosu.

Hatta uniforms da littafai da jaka a makarantar aka Basu sai gasu sun saje da sauran dalibai ‘yayan masu fada aji.

Dayake sunada karatun addininsu sai Basu Wani muzanta ba a cikin mutane aka Basu ajinda yakeda daidai da karatunsu

Abdul cikin saa aka basa ajinsu Haydar Dan haka murnarsu ta Qaru,

Amatu ma ajinsu Husnah aka kaita.

Wuni Amatu tayi a makarantar a kame sbd rashin sabo da shiga mutane sabanin Abdul da kamar Daman anan yake Dan kuwa Haydar tini ya jonesa da abokansa suka ringa murnan samun sake.

Koda yamma tayi sosai aka tadasu driver na gate Yana jiransu Dan haka suka shiga mota suka dawo gida.

Koda suka dawo maamah taga yayanta cikin uniform din makaranta Jin tayi jikinta yayi sanyi da farin cikin ganinsu a Hakan tana tausayinsu yanda suke farin ciki gashi dole zasu koma inda suka fito.

Da farin cikin da daddare suka ringa Bata labarin makarantar datake kamar a turai sbd kudinta da tsarinta.

Ita dai murmurshi kawai takeyi tana sauraronsu har dai aka gama dokin Abdul yaci abinci yayi bacci.

Amatu kuwa uniform din nasu ta nade musu ta tattara littafansa Daya barbaza ta mayar a jaka kafin itama taci abincin ta sukai sallar ishai da maamah ta kwanta

Maamah kuwa ficewa tayi ta tafi gurin ‘yar uwarta Dan sake nuna godiyarta akan abinda take mata.

********Ahankali su Amatu suka Dena dokin makarantar har suka fara sabawa yanzu Kam ba Doki karatu kawai Wanda kusan duk su biyun sunfi Husnah da Haydar kokari da Maida himma sbd ganin sukeyi sukam sun samu babbar sa’ar rayuwa ta zuwa makaranta bayan Basu tana Saka Rai da shiga kowace irin makarantar ba.

Husnah Sam babu Wani sabo sosai har lokacin a tsakaninta da Amatu Amma dai ta bangaren karatu hakanan take sakewa su koyawa juna ganin Amatu tafita saurin fahimtar karatun na islamiyya.

***ASH TALBA ya dawo kusan so biyu Yana sake tafiya Dan haka sudai su Amatu basuma San ya dawo gidanba harya komaiba sbd Basu taba ganinsaba Dan bayan ‘yayansa da matarsa sai mum Aisha Babu me shiga bangarensa Dan haka ko maamah dataje suka gaisa Saida yabada damar Akai mata iso tazo har palonsa suka gaisa Kuma sun Dan jima suna magana duk da rashin son Jan zancensa Yana tsayawa Dana gida su samu lokacinsa.

Karatun su Amatu yafara daukan harama sbd karfin maamah da Abeeda taci akan komawarsu ba yanzu ba.

Kowanne dare a palon su Husnah suke zuwa su Hadu su hudu suyi karatunsu na islamiyya harma da karatun Boko dasu Husnah din suke koyawa su Amatu Dan haka sukam su Amatun suka Bude Kai suna koya Dan daga Amatun har Abdul din suna shaawan na bokon.

Ahankali ahankali sabo sosai ya shiga tsakaninsu duk da halin Husnah din akwai wuyar shaani Amma dai sanyin halin Amatu da zurfin cikinta yasaka take shanyewa zaman nasu na tafiya,

A yanzu Husnah da batada qawaye Amatun ce kawarta har islamiyya har gida Dan haka sai duk abinda ta cire na kaya ko abun buqata da bataso sai tana bawa Amatun tareda nuna mata sai tagama da abu take Bata Dan nuna itace a qasanta Kuma take cin alfarmarta Wanda duk lokacinda takewa Amatun Hakan Bata taba Jin komai ba ita sbd maamah Dake nuna musu Husnah da Haydar Yan uwansu ne datakejinsu a ranta kaman yanda take jinsu.

Kaf a cikin gidan mum Aisha ce wadda Basa zuwa ko inda tabi tabar kamshinta sbd tsananin fadanta da zafinta akansu musamman mahaifiyarsu Dan haka kusan Yan aikin gidan biyu ta sake sallama Dan haka maamah karfi da yaji ta koma ‘yar Aiki a gidan Kuma aikinma Wanda ma’aikata uku zasuyi ita aka barwa tanayi.

Duk wannan wahalar da maamah din keyi haryanxu Bata taba Jin haushi ko bacin Rai ba,tsakaninta da Allah takeyi Kuma ko zatayi aikin dayafi wannan a gidan Abeeda batajin zataji Wani abu na dacin zuciya ko gajiyawa  sbd Abeeda ta inganta rayuwarta tin kuruciyarsu har yanzu dasuka manyanta gashi Kuma yanzu tana inganta mata ta yaranta.

Waya aka siyawa maamah tana waya da Yan can kauye tana Jin lafiyarsu da Kuma abubuwan Dake faruwa na zumunci da haihuwar da aketa sake yi a cikin Yan watannin da batanan

Ahakan ne katsam aka sanar da ita rasuwar uwar gidan kawu bello wadda take tamkar Yaya agareta Dan haka dole suka fara Shirin komawa gida.

Acikin gidan ASH TALBA Mansion Babu Wanda hankalinsa Bai tashiba da Jin maganar tafiyar maamah gida sbd baiwar data komawa kowa a gidan hatta masu aikin gidan aiki suke Sakata Kuma tayi,hakama tsaftar sashen Abeeda tini ya dawo hannunta hakama cimar Abeeda din,

Ta bangaren mum Aisha ma Amatu ce sabuwar me mata shara duk da Bata Wani iyaba Amma so take ta koya sbd a Qaru dasu Suma,

Su Husnah ma dasukai sabo da sakewa sosai ayanzu suyi wasa da guje guje harma da wasan ruwa a swimming pool dasu Amatun duk sai sukaji jikinsu yayi sanyi Dan haka suka roki mommynsu ta Hana maamah tafiya Amma dole saita tafi.

ASH Baya Nan zasu tafi Amma Kuma Saida ya Saka aka Basu kudin Daya bawa maamah tsoro sosai Dan haka aka Bude mata acct kafin tafiyarta aka Saka mata sauran suka riqe hakama Abeeda ta Basu kudi sosai itama bayan tarin kayan sawa da aka basu Wanda duk kayansu Husnah ne Dana Haydar aka bawa su Amatu itama an bata kayan sawa sosai Dan haka kaya Niki Niki sukai bankwana suka tafi ana kewarsu.

Bayan tafiyarsu har ciwo sosai Haydar ya kwanta kafin yaji sauki yakoma rayuwarsa ta Baya Babu abokin wasa Babu abokin fira bare karatu.

Itama Husnah bataji dadin tafiyar tasu ba duk da Babu abinda takewa Amatun a tarensu bayan Gori da nuna mata kamar komai na rayuwarta saita kashesa tagama dashi take bata.

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

9

Su maamah na isowa gida babban tashin hankalin farko data fara cin karo dashi shine rashin gurin zama Dan kuwa tini kawu bello yayi Amarya ya Sakata a cikin sashen Dan haka suka rakube dakin inna lami data rasu cikin ‘yayanta da jikokinta data bari a dakin gashi dakik a cunkushe yake Babu ko filin da zasu aje kayansu sbd kaya da hargitsin dakin.

Batada zabi bayan ajiye tulin kayansu waje a rumfar dakin inna lami din idan sunyo wanka anan suke shiryawa gashi yayanta sunyo Wani irin fresh da kyan Gani tini aka fara Saka musu Baki gashi ko bandaki Amatu zataje saita bita ta rakata Tayo abinda zatai sun fito tare sbd tsoro da fargaban abinda zai iya faruwa.

Amatun ma kanta samun kanta tayi da tsoron gidan da mutanen gidan sbd yanda kowa yake binta da Bakin jiki data Dan yi sbd batada jikin kiba ko kadan Amma ta Dan ciko tayi haske sosai duk duhun da fatarsu tayi ta rinewa ta wanke daga ita har Abdul maamah ce kawai ta Dan yi rama ta wahalar aikin datake sha Amma Kuma duk da Hakan itama fatarta tayi kyau sbd cima me kyau muhalli me kyau.

Kwanansu biyu da dawowa Akai addukar sati ta rasuwar Dan haka sai kowa ya koma sabgoginsa,

Mafarin Bude babin dawowan damuwar maamah shine sace kayansu da aka fara yi Daya bayan Daya Kuma batada iKon magana zaayita fada ana tashin hankali a gidan akan ta maqalawa yayan mutane satar kayan kunce da aka Bata tazo dasu Dan haka sai ta Dena magana ko sun duba sunga an sace musu abu shiru takeyi Bata magana hakama yayan nata Babu me magana.

Kudinta ma baa bari ba haka aka ringa sace mata su kadan kadan Dan haka ta tattara sauran canjin ta Siya abinci dashi ta aje Wanda zasu ringa dafawa da yayanta suna ci duk da tasan basuda ikom cin komai su kadai tinda tana dakin inna lami dole duk abinda zata nemowa yayanta suci Suma saita Basu.

Kawu bello Daya ga Hakan Saiya barta da lalurarsu ya zame Dan kuwa sauki ne ya zo masa.

Lalurar fara yiwa maamah din yawa tayi sbd ciyarda Yara da yawa bazata iyaba tinda ba Sanaa takeyiba gashi duk abinda tazo dashi din ya qare Dan Tama manta da anbude mata acct ansaka mata Koda Bata manta ba tayayama zata iya cire kudi tana cikin wannan kauyen dajin.

Tin tana boye gazawarta tana Fadi tashin ciyar da yaran duka har gazawanta ya bayyana Amma Kiri Kiri kawu bello yayi mata biris yabarta da ‘yayansa tana wahala dasu Dan bazata iya samowa ta bawa nata yayanba su ta Hana musu Dan haka tinda tana zaune dakin mahaifiyarsu a rakube dole ta taimaka musu itama.

*******Tafiya tafara Nisa sun wayi gari ko suturar sakawa Neman gagararta da yayanta takeyi sun koma inda suka fito ga yunwa da azabar aikin wahala Dan haka ciwo yafara kokarin kwantar da ita.

Amatu data fara iya aikin wahalar sai tana kamawa mahaifiyar tata dasu suna samu suna Dan rufawa Kai asiri.

Duk halinda take ciki Babu Wanda ya taba ko kallanta da daraja a gidan bare a tausayawa rayuwarta a dubi marayun yayanta Dan haka take Dan sake dauriya tana dagewa Dan inganta rayuwar ‘yayanta Amma jiki da jini dole Jikin ya fara kasawa sosai harta fara kwanciya ciwo kadan kadan saiga abu na Neman tsanani.

Amatu ce dole tafara fita da kanta Tana debo itace da zogalan da suke dafawa ana siyarwa.

Fara fitan Amatu shine yafi daga hankali da zuciyar maamah ba ciwontaba Dan kuwa tana tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo Bata kaunar abinda zai tana daraja da rayuwar ‘yarta,

Tinanin idan ta kwanta jinya me karfi Yaya rayuwar Amatu zata kasance acikin wannan gidan?

Yaya zata iya tsayawa ta taimaka gurin Bata kariya daga sharrin mazan gidan?

Komai zai iya faruwa da Amatu tana daga kwance Babu abinda zata iya yi…

Innalillahi wainna ilaihirrajiun,wannan tinanin kawai ke gigitata hankalinta yayi mummunan tashi harta Saka abin a ranta damuwa tayi mata yawa ciwonta sai qara gaba yakeyi.

Babu abinda yafara zuwa ranta da tinaninta sai komawa Abuja gidan Abeeda sbd Koda Allah yasa ciwonta bana tashi bane tasan tabar yayanta inda zasu tsira da mutunci su kuma su samu kariya da kulawa.

Wanna tinanin nata na sake komawa can din yake sake qarfafa a zuciyarta sbd Daman baaso dawowan nata ba ta dawo Amma Kuma babban abinda yake hanata zama acan din shine tayaya zataje tayi zaman dindindin gidan ‘aminiyarta duk da ta Dade da zama ‘yar uwarta tamkar jininta.

Wanna tinanin shine yake sake addabarta,takasa tafiya takasa Jin nutsuwar zama Dan haka abin ya taru ya sake mata yawa.

Su Amatu ma gaba Daya a tsorace suke da ciwon maamah din Dan kuwa a yanda suke ganin wainda iyayensu suka rasu a cikin wannan gidan almajirai suke komawa na karfi da yaji hakama lalacewansu yawa takeyi Dan haka tsoro ya kamasu Dan su tsoron ma irin wasu abubuwan Dake faruwa a gidan sukeyi sbd maamah datake Saka musu tsananin tsoron Hakan Tintini.

Rashin takamaimai shawara da madafa yasa suke cikin garari kullum Kuma suna waya sosai da Abeeda a yanzu sbd wayar data dawo da ita wadda aka Siya mata tin acan Amma bata iya fada mata halinda take ciki ba.

****Acikin wannan mummunan halin dasuke ciki kwatsam suka wayi gari da Kiran Husnah a wayar maamah din cewan Abeeda ba lafiya sosai.

Labarin shine Mafi tashin hankalin labarin Daya samu maamah sbd Abeeda Bata taba ciwon da harya kaita kwance ba Dan haka zuciyarta tayi nauyi da tsoron meya samu Abeedan,

 duk da ita ma a kwancen take Amma ciwon Abeeda ya sata danne nata azaban ciwon ta fara kokarin Shirin tafiya Dan kuwa ita kanta Abeedan zataso ta farfado Taga Asmau acikin wainda suke zagaye da ita.

Halinda ta shiga na tsananin damuwa da kokarin boye nata ciwon akan son zuwa inda Abeeda da kwana biyu batasan inda kanta yake ba yasa Amatu shiga mummunan damuwa itama da tausayin mahaifiyarta datasan tana cikin nata mawuyacin halin Amma kaunar datakewa Abeeda yasakata dannewa idan ba ganin kanta tayi sun Isa inda Abeedan takeba bazata taba nutsuwa ba.

Acikin kwanaki biyu sukai Shirin tafiya Abuja,

Dayake batada lafiya yanda ya kamata da Kuma kudi da Babu a hannunsu dole tareda kawu bello suka taho har cikin garin Yola suka banki ta basa komai aka ciro kudi daga bankinta ya cire kudin da aka basu aro daga can na tahowa tareda nasa kudin komawar harma Dana Shan ruwa a hanyar komawa tukuna ya rakasu suka hau motar Abuja shikuma ya hau ta komawa kauye.

Koda suka dauki hanyar Abuja a mota shiru Amatu tayi tareda zubawa hanya idanuwanta dasuka fada kwana biyu sosai sbd jinya da kulawa da maamah,

Wannan tafiyar tasu kaman yanda maamah ta fada ba lallai me dawowa bace sbd tanason Koda zata kwanta tabarsu a hannun ‘yar uwarta,

Meye makomarsu daga ita har Abdul idan maamah ta tafi kaman yanda take fada?

Daga dangin uwa harna Uba basuda takamaimai inane kaddararsu zata kaisu Dan haka take fata da adduar Allah yabarsu da mahaifiyarsu har girma da tsufa su rayu tare su mutu tare.

Kaman yanda sukasha wahalar hanya wancan Karan wannan ma sunsha sedai wannan da sauki sbd sunsan Daman tafiya ce me Nisa zasuyi ba kaman na farkon ba da basusan Nisan tafiyar ba.

Sai bayan ishai suka sauka Abuja Dan haka Kai tsaye driver ne yazo daukansu harda Husnah wadda itace tazo da driver din sbd ta matsu su maamah din su iso.

Tana ganinsu jikin Maamah ta fada tareda fashewa da kuka sbd tanata Neman Wanda zatai kuka a jikinsa Amma Babu Dan kuwa duk kauna da gatan da mum Aisha ke nuna mata ita Bata Jan Yara a jikinta ga mommynta akwance kwanaki batasan inda kanta yake ba.

Ita kanta maamah Jin tayi idanuwanta na cikowan da hawaye na tsinkewan zuciya Amma hakanan ta daure tana boye nata ciwon suka nufo gida.

Dayake dakinsu na Baya Yana Nan Babu kowa a cikinsa anan suka sauka bayan duk masu aikin gidan sun tarbeta tareda mata sannu da zuwa harma da gyara mata dakinta da wanke toilet da komai.

Basu zaunaba sai da sukaje har palon mum Aisha suka gaisheta tareda mata jajen jikin Abeeda din.

Sama sama ta amsasu tana kallan yanda duk suka sauya ba kamar yanda suka bar Nan din ba musamman Amatu data rame sosai.

Abdul ne ma dai take Dan sakewa Dan haka shi ta ringa tambayar Yaya kauye da karatu Yana amsawa har suka fito suka koma inda suke.

Wanka sukai dukkaninsu suka gasa jikinsu musamman maamah da jikinta yayi nauyi sosai na ciwo da gajiya.

Abinci aka kawo musu Saida sukai salloli suka ci take kowannensu bacci ya kwashesa a qasan tiles din sai maamah suka barwa gadon sbd rashin lafiyanta.

Washe gari Babu tinda Babu abinda sukeyi bayan cin abincinsu da mum Aisha zata asibiti ta tafi da Maamah gurin Abeeda din sbd yanda duk maamah tayi zuru zuru Babu baccin arziki sbd rashin sanin menene yake damu abeedan.

Koda suka Isa babban private asibitin me tsadan gaske suka Isa sama har dakin da Abeedan ke kwance baa Wani shiga sbd baa son motsi me yawa ko karfi.

Ahankali maamah ta iso har bakin gadon Abeedan tana kallanta da idanuwanta dasuka fara cikowa da wasu irin hawaye masu dumin kayewan zuciya na ganin mace kamar Abeeda a kwance gabaki daya kamar ba itaba a cikin qanqani lokaci Allah ya Maida ita Hakan,

Tayi Wani irin haske tayi fayau kamar wadda Babu jini ko kadan a jikinta hakama fatarta kamar wadda aka shafe da yar farar Hoda.

Kasa riqe hawayenta tayi suka fara gangarowa tana Sauke idanuwanta daga kan Abeedan tanajin kaman zuciyarta bazata dauka ba sai kawai ta fashe da Dan kuka mara sauti tana Jin halinda Abeedan ke ciki har cikin zuciyarta.

Ita kanta mum Aisha duk tazo Jin takeyi zuciyarta na karyewa sbd abu ne dayazo lokaci Daya hakama ASH TALBA yakasa fada musu abinda likitoci sukace akanta tin ranarda aka kawota asibiti zuciyarsa ke cikin Wani mummunan hali Amma qarfin halinda yaqi nunawa,

Abeeda wata tsoka ce a zuciyarsa dayakejinta musamman duk da baisan Menene so ba,

Idan Hakan shine so to tabbas Abeeda tagama zama sonsa qwal Daya da bayajin zai samu sassauci akan Hakan.

Kuka sosoi maamah Tasha a asibitin Wanda yasaka nata ciwon datake dannewa tashi sosai sbd Daman ita Kuma matsala ce ta zuciya datake kumbura tsaban kunci da damuwar datake ciki.

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

10

Badan mum Aisha taso ba dole ta Bada dama likita ya duba maamah a asibitin sai gata itama anbata gadon sbd sosai jikinta ya rikice.

Bayan likita ya gama komai akan mamah din ansamu tayi bacci yayiwa mum Aisha bayanin ciwonta da hutun datake buqata ya tafi.

Babu abinda mum Aisha take tinanin tsayawa tayiwa maamah din Dan haka ta dawo gida saima data huta tayi sallah taci abincin ta Tina da maamah din tasaka khaltume ta hada Amatu dame aiki Daya aka kaisu asibitin gurin maamah.

Amatu karan farko tana ganin halinda mahaifiyarta take ciki Jin tayi komai nata yayi sanyi sbd Koda sukazo tayi Amai Amma Babu kowa adakin bare ya taimaka mata harta koma bacci ahakan.

Share hawayenta dasuka gangaro tayi ta qaraso tafara kokarin tsafatace maamah din batareda wadda aka hadota da ita ta taimaka mata ba duk da qarancin shekarunta ita kadai ta tsafatace mamanta ta gyarata zuwa lokacin jikin maaman ya sake rikicewa Dan kuwa kaman Wanda beso aka zo asibitin ba.

Tsoro dukkaninsu suka shiga sbd Dena numfashin da maamah tayi hakama yanda take fizga tini suka kirawo likita Yana zuwa akace su fita.

Suna fitowa dole Fatima ta tausayawa Amatu itama jikinta yayi sanyi sbd itama marainiya ce tasan suna rasa mamansu a yawon aikatau Kila Suma zasu qare.

Zaman Jira suka dasa a wajen dakin har likita da sauran nurses suka gama duba maamah din suka fito suka wuce Babu Wanda yace musu komai sbd ganin basune sukeda iKon Jin komai ba sai mum Aisha tazo itada ta kawota.

Ciki suka koma suka zauna shiru Babu me magana sai kallan maamah da Amatu keyi a Kai Akai.

Anan Amatu ta kwana tareda Maamah ita kadai sbd ana kawo musu abincin dare aka koma da ita.

 Husnah ma taredasu Abdul da Haydar akazo dasu suka duba mommynsu da maamah din suka koma.

Acikin kwana biyu da wuni biyu maamah ta zabge itama Takoma kaman ba itaba ciwo ya sauyata,

Amatu ma sosai ta Dan sake figewa sbd Bata iya ko sabawa da dawainiyar asibitinba dukda Babu abinda sukasan ma Yaya ake biyansa komai Kai tsaye cikin bill na familyn ASH yake shiga.

Madame abeeda kuwa jikinta itama dai sai ahankali har lokacin Dan haka aka fara shirye shiryen fita da ita waje Amma saita farfado Dan haka ana Saka ran farkowanta kowane lokaci.

Maamah Saida tayi kwana bakwai tana jinya me wahala kafin sauki yafara zuwa lokacin Abeeda ta farfado itama jikin nata yafara sauki Kuma baa sanar mata maamah na asibitin tana jinya ba sbd kada a qara mata damuwa.

Koda Maamah tafara samun kanta dauriya da qarfin hali ta Saka sosai ta warware aka sallameta sai alokacin taje ta dubo Abeeda wadda ramarta ta bayyana sosai,

Ita kanta Abeedan dataga maamah sai data tambaya cikin sanyi da rashin qarfi cewan ko maamah din tayi rashin lafiya ne sbd yanda duk ya qanjame itama.

Murmurshin karfin hali maamah ta saki tana girgiza kawai tana qarasa zama a kujeran gaban gadon tareda Dan dafa bakin gadon tana kasa kallan fuskan Abeeda ta tambaya Yaya jikin nata.

Numfashi Abeeda ta sake ahankali tana Dan lumshe idanuwanta sbd gajiyan datake ji ta gyada Kai ahankali tana qure kallanta akan maamah din wadda take kasa kallanta.

Amatu ma da Bata samu zuwa duba mommyn ba sbd dawainiyar kulawa da maamah sai alokacin tayi mata sannu tana fatan samun lafiya.

Zuwansu Husnah tareda su Haydar ya Saka dakin Dan daukan hayaniya kadan sbd murnan ganin iyayensu sun samu sauki kowacce tana zaune da kanta sabanin yanda suke zuwa ganinsu a kwance Babu me sauki.

A Nan dakin suka wuni sai dare suka tattara suka koma gida gabaki daya sbd an sallami maamah,

Suna dawowa gida wanka maamah din tayi Amatu ta Sakata Shan maganinta kafin taci abinci ta kwanta hakama Haydar da Husnah na dakin nasu anan sukai dare kafin suka koma can cikin Mansion suka nufi dakunansu suka kwanta.

Washe gari wankin kayansu Amatu tayi nata Dana maamah Dana Abdul,

Bata gama ba sai Rana Dan haka tana gamawa sallah kawai tayi taci abinci itama ta kwanta ta samu baccin Hutu.

Sai yamma sosai ta tashi tayi sallan laasar lokacin maamah Dan karfin hali tabi masu zuwa asibiti zuwa dubo madame,

Amatu bataji dadin fitar maamah ba a halinda take ciki Amma Kuma batada abin cewa sai kawai tayi fatan samun lafiyansu su dukan.

Sai dare maamah ta dawo cikin ikon Allah tareda madame din suka dawo anyi sallama.

Madame din tareda daddynsu Husnah ta dawo Dan haka babu Wanda ya ganta sbd Kai tsaye bangarensa aka ajesu Kuma sun shige Dan haka Babu Wanda ya ganta sai washe gari Shima washe garin Se yamma ta fito sbd Babu abinda Babu acan da zata buqata,

Masu Kai abinci ne kawai ke shiga sashen Se masu gyara Suma suna gama abinda yakaisu suke fitowa.

Kowa yaje har palonta na kurya ya gaisheta ya mata sannu da jiki da fatan samun lafiya Mai dorewa kafin kowa ya fito aka barta dasu Husnah sai mum Aisha data shiga itama.

Maamah da Bata gama warwarewa ba haka ta ringa yawon kulawa da ita sbd Abeedan tafison maamah a kusa da ita akoda yaushe,

Tafi Jin sauki da qarfin jiki takeji idan maamah ce take kulawa da ita.

Ita Kuma maamah Sam bazata iya fadawa Abeeda batada lafiyanba tinda harta Nuna ita takeson ta kula da ita to tabbas zata danne tayi mata komaima.

Amatu a zuciyarta bataji dadin Hakan ba sbd maamah din kullum dare itama haka take kwana jikin Se ahankali.

******Da wannan kacokam lalurar kulawa da Abeeda ya dawo hannun maamah wadda har tsaftan bangaren Abeedan gaba Daya mum Aisha tasaka aka bar mata Dan haka sai maamah ta koma tamkar itace me aikin Madame abeeda a gidan.

Tafiyan da akaso yi da Abeedan ganin ta warware yasaka ta buqaci ASH din ya barta taci gaba da ganin likita anan,

Shawara yayi da likitoci qwararri suka ce zaa iya barinta Nan din duk ba matsala Suma sunada likitoci cancer masu kyau,,Hakan ya Saka ya barta din Badan hankalinsa ya kwanta sosai ba sbd bayyanar cancer a tareda Abeeda ya jijjiga duniyarsa da duk abinda yake cikinta sbd a ransa Abeeda wata haskensa ce da baya fatan rasawa a kusa Yana fatan su tsufa tare su mutu tare.

********

Amatu da Abdul sun sake komawa bakin karatunsu da suka bari a Nan din sedai wannan Karan harda Boko aka sakasu makaranta me kyau da tsada Amma ba wadda su Husnah keyiba.

Amatu Sam batajin kunyar girman data Dan Fi Yan ajinsu ba tace tafison tafara daga Js 1 din Daya kamata Dan haka anan aka Sakata akan idan anga kanta na budewa sosai sai idan zata shiga Js 2 a jefata Js 3 kawai.

Abdul ma nursery aka sakashi duk da yayi girma kamata yayi ace an sakasahi primary 2 ko 3 Amma dai sbd baida komai na karatun dole aka sakosa daga can.

Daga Amatu har Abdul Babu Wanda ya damu da girman da yayiwa Yan ajinsu su farin ciki ma sukai da Hakan Dan haka suka dage tareda Maida himma musamman Amatu datasan wahalar mahaifiyarsu ce suke mora da karatun Dan haka bazata bari uwarsu tayi wahalar banza ba Dan yanzu aiki bana madame Abeeda kawai takeyiba kusan aikin gidan Rabi yana rataye ne akan maamah din Dan haka tsufa na dole yafara rufarta ga ciwo shiyasa kowanne dare a wahalce take bacci gari ya waye Takoma aikin kamar engine.

*****Fara karatunsu ya Saka sosai Amatu ke sake wayo da Jin damuwan mahaifiyarta da Babu ranarda bata kwana da abin,

Ta bangare daya Kuma Husnah na taimaka mata sosai da karatunta hakama Haydar shima Yana taimakawa Abdul Dan haka abin yake zuwar musu da sauki suna ganewa.

Madame abeeda kuwa jikinta yayi sauki sosai Kuma har lokacin Babu Wanda yasan Menene ciwonta daga ita sai ASH Wanda Shima a qurarran lokaci ya sani Dan haka a yanzu koyaushe cikin ganawa da manyan likitoci yake ana masa recommending qwararrin likitocin Cancer na qasashe da ze Kai Abeeda ayi treating dinta.

Maamah dai a taqaice Takoma chief maid ta gidan Dan kuwa yanzu hatta abincin da masu gidan ke ci itace take girkawa Dan takanasa aka ringa koyar da ita bisa ga umarnin mum Aisha Dan haka tana qwarewa aka sallami chiefs din Dake girka abincin ASH TALBA maamah tayi replacing dinsu Dan haka ta sauya sosai ta sake manyanta ba kaman Abeedan Dasuke Aminai ba ita duk da tanada boyayyan ciwon da Basu saniba jikinta yananan me kyau da Hutu kamar yarinya take sake komawa.

**AmatulMaleek karatunsu yayi Nisa ta sake zama Yan mata Dan ma karatu na cinyeta sosai sbd yanda ta qwallafa masa Rai,

Kamar yanda aka fada idan anga tana ganewa zaa mata jumping to lokacin nayi Akai nata tsallake maimakon tayi Js 2 Kai tsaye Js 3 aka kaita wadda har sunyi jlc tayi SS 1 hakama yanzu tana Ss2 lokacin Husnah tagama harta shiga university.

***Ita rayuwa tana zuwarwa bawa ne a yanda ubagiji ya tsaro masa bawai Kaine kake tsarowa kanka ba,

AmatulMaleek matashiyar budurwar Dake tasowa a lokacin,

Wata irin rayuwa ce take gudanarwa ta kadaici da kamun Kai a cikin gidan dasuka Dade da zama ‘yan gida Kokuma tace gidan da suka Dade da zama ‘yayan me aikin gidan Dan kuwa ayanzu ba ‘yar uwa ko Aminiyar madame ake kallan maamah ba matsayin shugabar masu aikin gidan ake kallanta,matsayinta Daya da masu aikin,guri Daya da masu aikin gidan suke rayuwa,abinda ake bawa masu aikin gidan shi ake Bata,bambamcinta da masu aikin gidan shine Bata karban albashi hakama dauke ake da nauyin karatun yayanta Wanda zata iya qarasa rayuwarta a wannan wahalar sbd ‘yayan su samu gobensu me kyau duk da har Koda yaushe duk abinda takeyi na wahala da abinda ake mata a gidan bata taba Jin haushi ko damuwa ba sbd Dan Allah takeyi dakuma kaunar datakewa Abeeda wadda itama zata iya dawwama a wannan wahalar datake mata batareda taji komaiba.

AmatulMaleek zuciyarta ta taso ta Ginu da damuwa da Jin radadin irin rayuwarda mahaifiyarta ke ciki wadda a yanzu ko tausayi Babu bare kauna a yanda yake treating maamah a gidan,

Hatta dawainiyar Husnah data Haydar itace takeyi Wanda Hakan ke sake lullube zuciyarta da tausayin mahaifiyarta wadda har lokacin zuciyarta me tsafta ce Bata Jin qyashi ko gazawa.

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

11

Rayuwa a Mansion din ASH TALBA tamkar rayuwa ne a wata aljannar duniya Amma Kuma ga AmatulMaleek ba Hakan bane sbd halinda mahaifiyarta yake ciki ya danne duk Wani farin cikin datake samu a gidan,

A tsawon shekarun da suka share a gidan kowa yasamu ci gaba ya sauya daga sanin da Akai masa,sauyi kuma me girman gaske Amma Banda maamah wadda ta koma tsohuwar qarfi da yaji ga ciwon kirji Dana jiki Dana qafafu da Baya Wanda kowanne dare Bata iya bacci me dadi,

Ita kadaice tasan halinda mahaifiyarta ke shiga kowanne dare,

Maamah a Koda yaushe boye mata gajiyawarta da ciwonta takeyi sbd kada ta sani ta nuna damuwarta Dan haka maamah din ta zabi ta ringa hadiye damuwarta da ciwon dayake cinta sbd ganin AmatulMaleek na ajiye kowacce damuwarta a ranta kada Hakan ya taba rayuwarta da karatunta Amma Kuma abinda Bata saniba shine hakan ya Riga ya zaunu a zuciyar Amatun ta yanda take musu kallan Yan cin alfarma da jiran komai akashe abasu kaman yanda Husnah ke fada mata tin suna Yara.

Su ‘yayan me aikin gidan ASH TALBA ne Kuma bazasu taba tashi daga Hakan ba shine kalmomin da mum Aisha akoda yaushe take fadawa maamah a gabansu tin suna Yara haryanxu dasuka girma Hakan Bai taba canzawaba.

Ko mum Aisha da Husnah basa yawan tinatar dasu su din da matsayinsu Hakan a bayyane yake ba buqatan tini sbd haryanxu data zama budurwa Abdul yafara zama Dan saurayi a daki Daya suke su da mahaifiyarsu anan suke rayuwarsu.,

Jimawa sukeyii baa dinka musu sabuwar sutirar rayuwa ba kayanda su Husnah suka cire su ake Basu,

Basa shiga sashen madame Abeeda Sai Idan aikine ya kaisu Wanda tinda ta girma take kamawa mahaifiyar aikin gidan,

Har gobe abincin dasuke ci da Wanda mutanen gidan sukeci akwai bambamci,

Dan wannan matsayin dasuke Basai an tinanar dasu matsayinsu ba a cikin ASH TALBAs Mansion.

Abdul ma duk da kasancewarsa namiji har cikin ransa Yana tausayin mahaifiyarsu da wahalar datake sha Amma Shima kusan Amatun ne su dauko halin maamah na danne abu a zuciya tareda nuna ba komai bane Amma kusan Shima Yana taimaka mata da wasu ayyukan duk Yana gida kamarsu aikin kitchen Dan dole daga shi har Amatu sun iya aikin girki sbd taimakawa maamah.

Duk tsawon shekarun da sukai a gidan Babu abinda ya taba kaisu bangaren Mai gidan wato daddynsu Husnah sbd sam baa zuwa gurin hakama duk ganinda sukai masa daga nesa ne tinda ba mazauni bane sosai hakama Koda Hange Babu abinda ya hada bangaren masu aikin gidan da bangarensa bare su samu kusanci dashi.

Husnah anan Abuja take karatunta Dan haka wayewarta ta yayan masu kudin qasa suke bayyane gata batada hakuri ko saukin kai ‘yar Kai tsaye ce Bata iya boye zance ko maganar Dake ranta ba shiyasa da dama ake mata daukan me wuyar shaani,

Kusan Tako wanne bangare halayenta Dana AmatulMaleek sunyi hannun Riga Dan ita kanta Husnah duk yanda taso ganin bacin ran Amatu ko fushinta Bata taba iya Gani.

Shaquwan AmatulMaleek da Haydar wata irin kaunace a tsakaninsu me girma Dan kuwa jinta yakeyi a ransa fiyema da Husnah hakama itama Amatu a cikin familyn TALBAs gaba Daya Haydar shine Wanda tafi so fiyeda kowa da komai na gidan bayan Maamah da Abdul Dan ma kusan yanda take Jin Abdul haka take jinsa a ranta.

*******

Ayau gidan ASH TALBA sun tashi da sabon tashin hankalin dawowan ciwon Madame abeeda wadda haka kawai aka wayi gari ta sake shiga mummunan halin data taba shiga kwanaki.

Babbar rashin sa’ar da akaci shine ASH Baya Nan Dan haka su mum Aisha suka kira ambulance akazo aka dauketa hankalin gaba Daya jamaar gidan a tashe aka tafi da ita.

Bayan antafi da ita asibiti lokacin dukansu suna makaranta Dan haka maamah da mum Aisha ne dole a asibitin.

Wayar ASH da mum Aisha keta kokarin kira Bata samu ta sake Saka Kiran Amma dai still Bata samu Dan haka suka zauna jiran tsammani.

Har yamma suna asibiti Kuma har lokacin baa samun wayar ASH Dan haka likitocin basuda zabi bayan sanarwa mum Aisha Cancer ce da Madame abeeda Kuma takusa kaiwa last stage.

Shiru mum Aisha tayi idanuwanta akan likitan Daya gama bayanin cikin Hausa da turanci sbd bahaushe ne.

Maamah kuwa dafawa tayi Takoma zaunen data miqe sbd nauyin da qafafunta sukai mata suna Gaza daukanta.

Shiru sukai dukkaninsu Babu Wanda yake motsi sbd tinanin dasukai Nisa a cikinsa na ba zata da tashin hankali musamman maamah da hannuwanta duka dauki rawa ahankali

Ta damqesu sbd rawar da sukeyi zai iya haifar da matsala babba gareta musamman ciwonta datakeji zuciyarta na Neman Dena bugawa.

Cancer” mum Aisha ta furta ahankali tana Dan share guminta Dan duk abinta tana tsoron mutuwa haka Kuma duk lokacinda aka ambaci Cancer ga mutum Babu abinda suke fara hangowa akansa sai mutuwa a kusa kusa.

“Innalillahi wainna ilaihirrajiun” maamah ta fada ahankali tana rintse idanuwanta dasukai nauyi suna son hawaye Amma sunma kasa haduwan.

Mum Aisha a gurin ta ciro wayarta Babu Wanda ta fara kira sai ‘danta da kusan Babu abinda suke boyewa juna,kaf duniyarta shi kadaine Wanda takeso tsakaninda Allah da gaskia Dan haka ta tsaya akan karatunsa Dan yayi arzikin Daya kusa na ASH TALBA idanma har bazai fisa ba kenan.

Ringing wayar tasa takeyi harta katsae Bai daga ba Saida ta sake kira karo na biyu jikinta na rawa ta isar masa da zancen sbd damarsu tazo ta dawowansa gida ya baro turai sbd tabbas hankalim ASH TALBA zai tashi daga dukiyarsa da harkokinsa ya dawo Kan Abeeda sbd mahimmancinta da matsayinta yafi na komai daya mallaka so yanzu ne NAUFAL dinta zai samu matsayi da Daman shiga cikin huldodi da dukiyar ASH EMPIRE.

****

Madrid,SPAIN.

kwance yake akan lafiyayyan gadon dakinsa acikin gidansa da babu abinda ya rasa na Jin dadin rayuwa da  Hutu,

Dagashi sai Men’s tight Wanda baida bambamci da Babu komai a jikin nasa sbd kusan daga saman ya zame kadan hakama ya kamasa sosai ta yanda kana ganin shape na komai nasa.,

Fatar jikinsa Dake shining na qyallin Hutu da kyan fatar duk a Bude Dan bayan tight din baida komai a jikinsa,

Gefensa wata lafiyayyar blown skin mace ce da itama Babu komai a jikinta sai pant da bra wadda itama kusan a zame take,

Bacci sukeyi hankali kwance Wanda ke nuni da idanma da daddare idanma da safen to sungama mu’amalar mace da namiji ne kafin baccin.

Ringing wayarsa keyi duk da tana silent Amma vibration din na tashi sosai harya fara jinsa cikin baccinsa Dan haka ya Dan motsa Yana Bude idanuwansa ahankali daidai lokacinda Wani Kiran ya sake shigowa.

Akan fuskar sabuwar budurwarsa Dake kan jikinsa idanuwansa suka sauka ya Dan yamutsa fuska ahankali tareda janyeta daga jikin nasa Yana miqa hannu inda wayarsa take daidai kira na uku na sake shigowa.

Qaramin numfashi da tsoki ya Dan sake lokaci Daya kafin ya duba Mai Kiran yaga sunan Mum dinsa baro baro.

Ajiyar zuciya ya sauke me sanyi tareda tashi zaune Yana zamowa bakin gado ya sauko da qafafunsa qasa ya miqe daga gadon Yana daukan wayar Kai tsaye tareda dorawa kunnensa ya nufi hanyar fita dakin Yana cewa

“Yes mum,good morning”

Kallan time mum Aisha din tafara yi gana su anan din ba safiya bane Amma dai koma yayane bashine matsalarta ba cikin kulawa da ‘yar kamewa tace

“Morning,ka tashi lfy?

Ya karatun??

Ruwan dumi Daya zuba a cup ya jefa lemon aciki ya Kai bakinsa Saida yasha sosai kafin ya amsa da cewa

“All good mum,

Yaya Su Husnah and Aunt Abeeda?

“Husnah lfy kalau Aunt din taka ce dai take kwance asibiti batasan inda kanta yake ba.”

Shiru yayi Yana ajiye cup din hannunsa ya  nufi Daya daga tsadaddun kujerun palonsa ya zauna Yana cewa

“Meya sameta mum?

Wani abu ya faru ne?

Meyake faruwa?

Katsesa tayi da cewa

“Cancer ne da ita duk tsawon lokacin Nan Amma ba Wanda yasani sai yanzu..

Katsesa Naufal din yayi cikin mamaki da cewa

“Uncle ASH fa? Ya sani?

“Bansaniba ko ya sani Amma dai yanzu besan muna asibiti da ita ba bana samun wayoyinsa duka,

And duka bayan wannan ka saurare ni da kyau kaji……

“Heyy baby good morning” …shine abinda mum Aisha taji daga cikin wayar tayi shiru zuciyarta na yin nauyi sbd bata buqatan kowanne irin bayani ta sani mace ce a tareda Naufal din a cikin irin matan dayake kawowa gidansa suna kwana,

Babban baqin cikin mum Aisha a duniya biyu ne zuwa uku,

Na farko dukiyar ASH TALBA data tsone idanuwanta ta Hana zuciyarta sukunu tsawon shekarun datake zaune a gidansa cikin dukiyar tana yanda takeso da ita hakama ‘danta yake yanda yakeso da rayuwarsa tamkar shine magajin ASH TALBA din,

Na biyu shine Neman matan da Naufal yekeyi kamar bunsuru Sam Baya iya kwana a rayuwarsa batareda ya kusanci mace ba

Duk ranarda ya kwana biyu batareda mace a tareda shi ba to kamar zai zauce yake jinsa shiyasa gaba Daya Baya iya zama Nigeria sbd Jin Yana aikata irin wannan zinar haka kaman abinci zai iya Saka ASH TALBA nesantasa da ko inda zaibi ya wuce bare Kuma sakashi cikin dukiyarsa dasuke fata tin shekara da shekaru Shida mum dinsa.

Abu na uku kuwa shine Haka kawai takejin tsana da rashin Jin nutsuwar zaman maamah da ‘yayanta a cikinsu sbd maamah din tamkar kariya ce ga Abeeda data Dade tana Jin qyashinta da kishinta ga Dan uwanta dayaqi qara ko kallan wata macen bare Wani tinanin qarin aure da babusa a tinaninsa ko rayuwarsa ma gaba Daya.,

Zuwan maamah yasaka duk yanda Husnah take renanta Kuma tarbiyarta harma da yanda takeson ta zama sbd amfani da ita gurin ASH sosai ya ruguje sbd komai rashin saukin kan Husnah da zafin kanta tana kaunar maamah da gaskia Kuma kamar yanda maamah din ke tsananin sonta kaman AmatulMaleek da Abdul, Husnah Takoma kusancinta da maamah da shaquwarta da ita yafi na kowa Dan haka Sam yanzu sedai ayiwa maamah duk abinda zaa mata na cin zatafi ko aikin wahala Amma baa iya canza matsayinta gurin Husnah da zuciyarta.

Wanna dalilin ne yasaka taji tayiwa shigowarsu Maamah rayuwarsu tsana me karfi.

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

12

**********

Naufal dayaji mum dinsa Tayi shiru batace komaiba ya tabbatarda taji maganar Cynthia haka Kuma yasan yanda ta tsani mace ta rabesa sbd sam Bata masa shaawan aure batareda ya tsayu a cikin dukiyar data tsaya mata a zuci da ido Tim kafin ta haifesa ma.

Ajiyar zuciya ya Dan sauke a boye Yana basarda abinda mum din taji Yana cewa

“Mum ki bari zan kira anjima idan Aunt din ta farfado na mata ya jiki and I will call the grt ASH TALBA Shima na masa sannu da jikin nata”

Numfashi me zafi mum din ta hadiye randa duk ya gama Baci da daukan zafin halin Naufal din Dan haka Kai tsaye ta kashe wayar batareda ta amsa shi ba Dan kuwa zuciyarta zata iya kumbura a gurin.

Tana aje wayar ta koma dakin ta Tararda maamah data sha kuka Mai tsima zuciya da tausayin ‘yar uwarta datake Jin inama wannan kaddarar Bata sametaba Amma ko yanzu ciwo ba mutuwa ba.

 Cikin dacin zuciya mum Aisha ta nufi gurin zama ta zauna tareda jefa wayarta cikin lv handbag dinta Dake gefenta aje tana Jin zuciyarta na kasa hucewa Dan haryanxu Naufal ya kasa girman burin dataci akansa kwata kwata halin ubansa yayo bayan mace Babu abinda yake gabansu kamar Babu wata rayuwar bayan ta kusantar mata.

Tsoki data ringa saki Akai akai batareda tayi magana ba ya Saka maamah da idanuwanta sukai jajir dagowa ta kalleta itama batareda tace komai din ba.

Sai dare sosai suka dawo gida kuma har suka dawo Amatu batai bacci ba tana jiran dawowarsu cikin damuwa da tausayin Madame abeeda wadda ta San ciwon a jikinta yake Amma zuciyar maamah yake ci Dan kuwa maamah bazata sake walwala ba sai ‘yar uwar tata ta samu lafiya.

Wanka kawai AmatulMaleek ta iya hadawa Maamah din ruwan zafi tayi Amma ko abinci Bata ci ba ta kwanta,

Bata iya cewa maamah din komaiba sbd tasan Babu abinda zata iya cewa bayan adduar data yiwa madame Abeeda ta samun sauki a bayyane.

Shima Abdul dayayi bacci ya Farka daga baya ya tambaya jikin Madame din Amatu tace yayi shiru kawai.

Husnah kukan datasha Jin ciwon mahaifiyarta Saida ta Saka maamah kuka itama sbd kasa riqe kanta tai Dan ganin kawai sukeyi mutuwa zatayi ta barsu.

Amatu komawa tayi Husnah da maamah din take kulawa dasu sbd halinda suka shiga ahaka Kuma take zuwa makaranta ga aikin maamah da dole itace ta karba tanayi tinda maamah din Takoma asibiti itace take jinya.

*****Kwana biyu madame tafara Jin sauki Dan tana Dan iya komai da kanta hakama maamah komai itace take mata bautarta da sadaukarwa ya ninku Dan haka dole Amatu ta dauke idanuwanta da zuciyarta daga Hakan Dan kuwa ta yarda ta sadaqar kaunar maamah din da Madame din bazata iya Hana maamah bauta mata duk abinda zatai sbd maamah ta riga ta sadaukar da kanta ga Madame din da duk abinda ya shafeta.

Ayau asibitin suka taho tareda Husnah dasu Haydar da ita AmatulMaleek din wadda harta San fada sbd ayyukan maamah data maye gurbin kusan rabinsu ita keyi.

Koda sukazo madame din tana zaune kan kujera maamah na hada mata ruwan wanka a toilet na dakin.

Shigowarsu ya Saka Madame dago idanuwanta dasukai haske ta kallesu Daya bayan Daya tana Jin tausayin ‘yayanta da duk sukai sanyi tinda sukaji ciwonta.

AmatulMaleek ce ta nufi toilet din Mai tsaye cikin sanyi da nutsuwa bayan sun gama gaida Madame din da yi mata sannu Dan ta taimakawa maamah aikin datake ta yi a toilet din takasa fitowa.

Wanke toilet din takeyi Wanda baida komai fes yake sbd tsadan asibin tsaftansa na musamman ne bare su dasuke kaman vip room a can sama.

Kallan maamah din tayi tareda Dan lumshe idanuwanta ta qaraso ta Kai hannu ta kama hannun maamah din Dake goge ruwa da mopper sbd kada Abeeda ta taka ta zame.

Dagowa Maamah tayi ahankali ta kalleta da idanuwanta dasuka fada itama

Ganin AmatulMaleek ce ta saki Wani sanyayyan murmushi tana ambatar sunanta da cewa

“Yaushe kuka xo??

Numfashi mara sauti Amatun ta sake tareda karban mopper din tana sake kallan maamah da fararen idanuwanta masu maiqo aciki ta Bude Baki a natsenta tace

“Bari na qarasa kawai kije ki huta tareda su Husnah harma dasu Abdul mukazo.”

Murmurshi maamah ta sake zatai magana AmatulMaleek ta girgiza mata Kai a hankali tareda lumshe idanuwanta ahankali tace

“Maamah zan qarasa kije ki gaisa dasu”

Murmurshin kaunar ta sakarwa Amatun cikeda kulawa tace

“Shikenan ki kula kada ki zame yanada santsi sosai”

Gyada Kai ahankali Amatu tayi tana kallonta harta fice toilet din.

Hannun doguwar rigar jikinta ta Dan nade kadan sbd kada ya jiqe ta fara mopping toilet din da maamah tariga ta gama wankewa.

Cikin nutsuwa takeyi gogewan harta gama ta Dan dauraye mop din ta ajiye gefe ta wanke hannuwanta liquid soap din dayake toilet din tafara kokarin hadawa Madame din ruwan wanka.

Wani qamshi ne da Bata taba Jinsa ba a ruyuwarta sbd fitarsa daban da Kuma yanda qamshin yake daban a hanci harma da yanda yake sauka a zuci,

Qamshine me sanyi da Dan haka ta Kalli kayan wankan madame Dake Jere a gurin tana Dan sauke numfashi me sanyi mara sauti sbd sanin wani abu daga cikin kayan wankan ne yake wannan qamshin,

Ruwan wankan ta qarasa hadawa tareda sauke wanke hannunta kafin ta nufi kofa ta Bude ta fito ahankali tana Dan warware hannun rigarta data janye.

Qamshin Daya shiga hancinta a cikin sanyi na nutsuwane tareda Jin tsit din dakin ya Sakata dagowa ahankali idanuwanta Basu sauka a koina ba sai akan the grt ASH TALBA Dake zaune tareda Abeeda a kujera Daya fararen dogayen yatsun hannunsa na sarke da nata tayi shiru a gefen jikinsa kwance.

Firgita da mamakin da Bata shirya musu bane ya Sakata shiga faduwan gaba da shock lokaci Daya sbd ba kowa adakin kowa ya fice hakama tinda ta taso a gidansa suke rayuwa a cikin gidansa yaune ranar farko data fara ganinsa gashi ga ta,Dan kuwa idan ma ya Santa to a iya Baki ya Santa ‘yar Asmau takwarar matarsa Abeeda AmatulMaleek.

Rikicewa ta sake shiga sosai Dan Bata tsammanin fitowa Taga ba kowa ba Kuma Bata taba kawo tinanin zata fito ta ga the grt ASH TALBA a gabanta ba yau bayan ganin nesa Suka Saba masa hakama Wani irin zama ne sukai Shida Abeedan wadda tayi shiru a jikinsa da yanda shikuma nasa hannuwan suke sarqe da nata Dan haka duk ta sake rudewa cikin sauri ta nufi kofa tana furta Ina wuni batareda ta dago ta sake kallan inda suke ba.

Amsawa kawai Shima yayi da muryarsa me kauri da tarin nutsuwa da Kwanciyar acikinta batareda ya duba waye ba Dan kuwa gabaki daya tinaninsa da hankalinsa na kan Matarsa dayake Jin kaman ya bar qasar da ita a ranar.

Ita Kuma tana fitowa dakin Kai tsaye gurin da maamah ke zaune ta nufa ta zauna gefenta batareda ta furta komaiba,

Haydar Dayazo ya zauna gefenta Shima Yana kallanta cikin tsananin kulawa da kaunarta da Baya hadawa da komai sbd Allah ne ya Saka masa Hakan tin Yana yaronsa Amma yanzu daya fara zama saurayi Jin yakeyi kamar son dayakewa AmatulMaleek kullum qaruwa yakeyi batareda yasan wane so ne zuciyarsa ke kamuwa dashi ba tin Bai gama zama cikakken saurayi ba.

Jinsa a gefenta ya Saka Amatu juyowa ahankali ta kallesa da fararen idanuwanta Dake sakashi qure kallansa akanta koyaushe sbd kyanta dayake Gani fiyeda duk Yan mata tsaransa da wainda suka girmesa sosai kaman Amatun.

Ajiyan zuciya suka sauke atare tana dauke kallanta akansa sbd sai yau data taba ganin daddynsu a Fili ta fahimci daga Husnah harshi da ake cewa Yana yanayin mahaifinsa duk ba Hakan bane duk da kallo Daya tayi masa ta sauke Kai Amma a Hakan ma zata iya qararda Haydar ba Wani kama yakeyi dashi ba sosai sbd shikam ASH TALBA din batama San tayaya ake fassara kamanninsa ba.

Cikin kulawa Haydar ya sake kallanta yace

“Lafiya dai??

Sake juyowa tayi ta kallesa Dan itama har cikin ranta kaunar Haydar daban ce sbd jinsa takeyi kamar Abdul da uwa Daya Uba daya ya haifesu Kuma qarin girman kaunarsa a ranta shine yafi kowa Bata kulawa da tattali duk da Yana qasa da ita a shekaru Amma sosai yake nuna kulawansa akanta fiyema da Husnah Dan haka kaunarsu take da qarfi.

Bayan ta sake kallansa ahankali ta Sakar masa Dan murmushi tace

“Lfy kalau,Yaya Akai ne??

Ko mu tafi yanzu tinda dad dinku yazo babu me sake komawa ciki Seya tafi.”

Kofar dakin ya kalla kafin ya Maida kallansa kan Husnah Dake waya da Uncle Naufal dinsu tin dazu ya dawo da kallansa kan Amatun yace

“Mu bari Dad ya fito mu sake dubata saimu tafi din.”

Gyada Kai tayi tana cewa shikenan ba damuwa Allah yabawa mommy Abeedan lafiya.

Amin”kawai yace Yana kallan Abdul Daya dawo daga reception.

Zaman Jira suka fara suna Dan fira sama sama har kusan awa uku kafin ya Bude kofa zai fito.

Qamshinsa ne yafara gauraya gurin Wanda kowanne hancin dayake shaqan qamshin zai bambamta tsadan qamshin da wasu qamshin sbd Kai tsaye qamshin cikin sanyi me nutsuwa yake shiga ya wuce zuciya da itama qamshi me dadi ke isar mata.

Dayake Personal person dinsa Jameel na gurin Yanata waya Shima wanda kusan wayar duk ya harkar businesses na ASH dinne,

Shima ana Bude kofar ya kashe wayarsa ya qaraso kofar ya qarasa Bude masa Yana yiwa Madame sannu da jiki.

Fitowa ASH din yayi Haydar da Husnah suka bisa suka wuce Husnah na riqe da hannunsa Daya data kama Shima cikin kulawa yake Dan kallanta a da idanuwansa da idan ba iyalansa ba baayi kalla sbd tsananin kwarjininsu da haiba.

Maamah da ita ce kawai yayi magana da ita sosai kafin ta fito dakin su barsa ta miqe tafara komawa ciki kafin Amatu da Abdul suka bita.

Maamah Dake zaune har lokacin Amma da alama tayi wankan suka kalla suna sake mata sannun ta amsa tana kalla maamah da itama ita take kallan lura da jikin Abeedan din yayi sanyi idan Kuma ta canka abinda Abeedan take tsananin gudu da tsoro ne yake Shirin faruwa zaa dauketa daganan din zuwa Neman lafiyanta zata rabu da ‘yayanta.

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

13

*************

Ganin AmatulMaleek da Abdul na gurin yasaka Babu Wanda yayi magana a cikinsu kowa shiru yayi jiki a mace sbd tafiya ce da Kila batasan ranar dawowanta ba.

Amatu data lura da dukkaninsu jikinsu yayi sanyi Kuma Babu me magana acikinsu kowa yayi Nisa a tinanin,

Ajiyan zuciya ta saki a boye kafin ta miqe tsaye tana kallan Abdul Dake amfani da wayar Haydar tace masa su tafi waje su Jira su Haydar su dawo su wuce gida.

Miqewa yayi a tare sukaiwa mommy Abeedan adduar samun sauki suka kalli mahaifiyarsu sukai mata sai anjima suka fita maamah na bin bayansu da kallo cikeda tausayinsu sbd tasan zuciyarsu na cikin radadi da Jin ciwon wahala da bautan datakeyi Amma Kuma abinda Basu saniba shine duk wannan sadaukarwa ba iya Abeeda bane kawai sbd sune,sbd su samu ingantaccen ilimi da rayuwa me kyau ne Abisa ga sharadin mum Aisha data shimfida mata sharadin idan ‘yayanta zasu samu ilimi me kyau ita zata maye aikinta da iliminsu.

Numfashi Amatu data fita ta sauke kaman yanda Suma bayan fitarsu Amatun maamah ta Dan sauke numfashi me sanyi a boye.

Su Amatu suna saukowa qasa cikin saa lokacin ASH TALBA yabar asibitin Husnah tabisa Dan haka Haydar kawai suka samu zai hawo saman Dan haka suka Jira yaje yayi bankwana da mahaifiyarsa ya sauko suka tafi gida.

Tsawon lokaci da tafiyar kowa har dare yayi maamah tayi maga komai na Shirin bacci ta kwanta Amma bacci ya kasa zuwa idanuwanta Dake cikeda yanayi na ciwo na irin Wanda yake Jin jiki,

Tanason magana Amma Sam Bata iyawa Dan kuwa zuciyarta tariga tayi Wani irin sanyi da saddaqarwa akan rabuwarta da ‘yayanta tazo,

Wasu hawayene masu tsananin zafi suka gangaro daga cikin idanuwanta dasukai fari fes irin na ciwo.

Saukowar hawayenta akan idanuwan maamah suka sauko Dan haka tayi shiru batareda tace komai ba sbd duk abinda ya Saka Abeeda kuka yakai qololuwar raunana zuciyarta.

Tin hawayen na gangarowa cikin rashin sauti har kuka me sanyi da radadin zuciya ya kufce mata ta rintse idanuwanta tana yin sa sosai har lokacin Bata iya Bude bakinta ba.

Wani irin sanyi da mutuwa jikin Maamah yayi itama nata idanuwan suka ciko da hawaye sosai sbd Babu kalman da zata iya fadawa Abeeda yanxu ta sanyaya mata abinda take ji din.

Shiru dakin ya dauka bayan kukan madame Abeeda Babu abinda yake tashi cikin tsananin qunci da damuwar da tasan Allah ne kawai yasan Yaya rayuwa zatai da ita kodai ta dawo ga yayanta a Raye kokuwa a dawo musu da gawarta.

Duk yanda maamah taso daurewa kasawa tayi sbd maraicinsu dasuka taso aciki kowannensu batareda iyayensa ba dakuma yanda rayuwa tayi da kowannensu shine ya dawo musu zuciyarsu ta karye itama tafara gangaro da hawayen tana rufe fuskarta da mayafin Dake jikinta sbd yanda kukanta ya qara ingizowa da yanda ta rasa kowa nata daga iyayen har mijinta Abeeda kawai ta rage Mata itama gasu a Wani hali na fargaba da tsoron me zai iya faruwa sbd ciwonta.

Ita Abeeda kukanta me tsanani dayake sake karya zuciyar maamah na yanda zata bar yayanta duk da tasan suna cikin gata gaba da Baya Amma rabuwa da yayanta da mijinta ASH Wanda take Jin zuciyarta kawai Neman bugawa takeyi idan ta Tina tana tafiya shikenan zai iya shiga Wani hali na damuwar da zai iya nesanta kansa da kowa harma ‘yayansa Dan kuwa ayanzu ta tabbatarda soyayyarta data Dade tanason tabbatarwa a zuciyarsa.

Haka suka kwana Babu me dadin zuciya sai tinanin da kowa ya zurfafa aciki  qarshe Hakan ya tayarwa madame Abeeda Wani ciwon Amma ta daure sbd tanason kwanakin da zasuyi kafin tafiyar tayi su tareda yaranta cikin kauna da kulawa.

Ita kanta maamah daurewa tayi sbd damuwa na Neman tayar mata da nata ciwon zuciyar Amma batason kwantawa sai take dannewa da daurewa.

Washe gari qarfin halin da Abeeda ta nuna yasa aka sallamesu

Ko wannan Karan ASH da kansa ya dauketa ya tafi gida da ita.

Babu Wanda ya samu ganinta sai washe gari ta dawo bangarenta anan duk suka zo sukai mata sannu ‘yayanta kuwa suna tareda ita,

Ko baqin dataita yi mutanenta masu zuwa dubiya matan manya basa Wani jimawa suke tafiya sbd an Hana abarta ta gaji sosai.

Tinda ta dawo kulawan da akeyi da ita ta ninku sbd wannan Karan duk Wanda ya kalleta yasan ciwo ne a tareda ita sosai Dan gaba Daya Takoma fara tafara sauya kamanni hakama ko magana tayi sosai saita gaji Dan haka ko magana baa son ta cika yi.

Daga yayanta har masu aikin gidan a yanzu kowa jikinsa a sanyaye yake Babu me doguwar walwala a gidan kaf Dan kuwa me gidan kansa Baya cikin walwala da dadin zuciya ko kadan sbd halinda matarsa take ciki.

Husnah data tabbatarda ciwon mahaifiyarta akwai yiyuwar takewa akwai yiyuwar tafiyarta tabarsu yasa take depression yafara kamata sbd ko karatu ta dena ganewa,

Gashi kowacce safiya suka tashi jikin mum din nata ba sauki gaba abin yake sake yi,

A Koda yaushe mum din yanzu magarsu nasiha ce gareta,

Haydar ma dayake namiji depression din kamasa yayi.

Gidan ASH TALBA tini ya tashi daga gidan farin ciki sbd zuwa yanzu Madame abeeda tayi Nisa gashi tafiyar da zaayi da ita Bata kammaluba

Gashi ita kanta Abeedan ta shiga mummunan damuwa da Saka abin a ranta Dan haka sai hawan jini me tsananin gaske ya shigo ciki da ciwon zuciya Dan haka jikin ya kasa dauka.

Maamah datake Jin danginta daya data rage Mata zata barta kusan ASH da ‘yayan Abeedan ne kawai suka fita shiga damuwa Amma itama tini jikinta yake Neman rikicewa sbd damuwa Amma su Amatu nata kokarin kulawa da ita sbd ita idan ta kwanta basuda me kulawa dasu Dan haka suke lallabata duk da Suma suna cikin damuwa da kukan halinda madame Abeeda take ciki.

Madame abeeda takai matakin da ko magana Bata iyayi Amma ko acikin hali na tsananin ciwo maamah take sake bawa amanar ‘yayanta sbd kaf duniyarta tasan bayan dad dinsu Babu Wanda zai kaunacesu ya kula dasu fiyeda nasa yayan sai maamah Dan haka Babu abinda take iya daure ta furta sai amanar yayanta ga Asmau wadda itama cikin kuka sosai koyaushe take tabbatarwa da Abeeda zata kula dasu Husnah da Haydar kamar itace ta dauki cikinsu ta haifesu wannan alqawarine datai mata zata kula dasu har inda nata karfin da rayuwar ta qare.

Ciwon Madame Abeeda Wata babbar jarabawa da kaddarar familyn ASH TALBA ne Dan kuwa tini labari ya yadu sbd tayi Nisan da kusan duk sun fidda Rai,

Kuka da tashin hankali irin Wanda familyn suka shiga baa magana Dan kuwa shi kansa ASH din isolating kansa yayi sbd sai yanzu ne zuciyarsa take sake tabbatar masa da tsananin so da girman Abeeda a zuciyarsa hakama yanda yayansa abun ya tabasu musamman Husnah da tini kanta yake Neman tabuwa da lamarin da Basu tana sanin meye rashi na dukiya ba bare na Rai tinda Basu taba rasa Wanda yake shaqiqinsu da wayonsuba.

Husnah batasan cewa idan mum din tasu ta rasu ba ita shikenan batada uwa batada Uba da Kila abin saiyafi haukatar da ita,

Haydar Amatu sosai ta tsayu akansa tana kulawa dashi ta hanyar rage masa damuwa itada Abdul Wanda Shima harda Husnah Yana kulawa da ita hakama ta bangare daya maamah Kam ciwo ya kwantar da ita Amma ahakan take daurewa,

Mum Aisha tashiga damuwa Amma ta rashin dawowan Naufal a daidai lokacinda yakamata ace familyn gidan duk suna Nan tareda ASH wadda duniya ma ta tabbatarda yanda yake tsananin son matarsa Madame Abeeda Talba.

A lokacinda tafiya da Madame Abeeda yayi ta kwana biyu da fita hayyacinta Dan haka kamar gawa aka gama komai aka tafi da ita tareda mum Aisha da yayanta suka tafi.

Bayan tafiyarsu kusan gidan kwana biyu Akai ana zaman da zaa iya cewa kaman na makoki,

Maamah da abin ya Dan tabata dole su Amatu suka dage gurin kulawa da ita sai ya zamana kusan ragamar gidan ta dawo hannunta tinda a hannun maamah take khaltume yanzu ta dawo karkashin maamah Dan haka yanzu da maamah din batada lafiya sai komai ya dawo hannun Amatu.

*****Bayan kwanaki da tafiyar mutan gidan da addua da dagewa da kulawa suka samu maamah tafara samun sauki tana warwarewa yanda ya kamata.

Ganin karatun yaranta na Neman tabuwa yasa maamah din Saka qarfin hali tana warkewa Dan kada ta daqusar da yayanta.

Cikin wasu kwanakin ta warware gaba Daya ta koma ayyukan gidan da kulawa da Gidan Dan kusan kowa gidan a qarqashinta yake yanzu itace aka barwa amanar gidan da kulawa dashi sbd shi kansa ASH TALBA ita yabarwa kula da kowa na gidan.

AmatulMaleek kuwa tini Takoma bakin karatunta Daman tana zuwa ne tana skipping wasu kwanakin sbd jikin Maamah Dan haka yanzu da maamah ta warke saita dage tinda gamawa zasuyi watanni kadan masu zuwa.

****Sati hudu su Husnah sukai suka dawo gaba dayansu jiki a sanyaye batareda mahaifiyarsu ba wadda komai ya tsaya a duniyarta dama tasu duniyar Dan kuwa jiki dai ankai inda baason Akai,

Ana Saka ran paralyze ya shiga ciki Amma baa tabbatar ba sbd gaba Daya tayi slipping into coma Dan haka baa San ranarda zata Farka ba,hakama akwai yiyuwar daga coma din bazata tashiba shikenan ta tafiyarta Dan haka a cikin mummunan tashin hankali sukai kwanakin da sukai suka tattaro gaba dayansu suka dawo Dan qanwar mahaifinta Dake Greece din da zama zata kula da ita duk da asibitin Wani Baya zama sune suke kulawa da komai monthly ake zuwa duba patient sosai suke kulawa dasu tinda kudi masu yawan gaske ake zubewa gasu da qwararrin likitoci.

Bayan dawowansu ASH TALBA Babu Wanda ya sake ganinsa Sam Babu ma Wanda yasan yana qasar ya sanar da Personal person dinsa Jameel Baya buqatan ganin kowa da kowannen irin aiki sai bayan kwana biyu Dan haka Jameel ya sanar da securities na gidan kwata kwata ma baqi yanzu idan ba family ba kar Abar kowa yashiga mansion din.

Mum Aysha kuwa Basu fi sati biyu da dawowa ba ta bar qasar zuwa Spain sbd Naufal Dake Neman buga mata zuciya da baqin cikinsa da bacin Rai yaqi dawowa duk kira da massages din datake aika masa Dan haka a yanzu da ASH zaiyi rayuwa ba tareda matarsa ba abu biyu take buri da buqata a wannan bagiren Amma Naufal din da Allah yayi da jinin ubansa data Jin ranta na quna idan tana ganin halinsa yaqi dawowa sbd anan Yana ganin bazai samu mata yanda yakeso ba yana biyan buqatansa,Dan haka gwara taje ta taho dashi da kanta.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

14

**********

Husnah bayan dawowarsu komai tsayawa yayi a rayuwarta sbd duk yanda aka dauka zata iya riqe abin takasa sbd kanta da zuciyarta Sam basa iya daukan abinda Bata Saba gani ya faru a rayuwarsu ba Dan haka sai abin yafara yawa Yana bawa maamah tsoro da Haydar harma dasu Amatu Dan kuwa cikin kanta depression din yafara tabawa Dan kuwa a yanzu rayuwa ce sukeyi kamar mahaifiyarsu dai ta riga ta rasu Dan kuwa dukkaninsu sun saddaqar da ba tashin zatayi ba San haka take Jin ita mum din ma ta riga ta rasu.

Dad dinsu sosai ya Maida hankali akan kulawa da lafiyarta sbd kada abin ya taba kwakwalwanta sosai duk da yariga yafara tabawa Dan haka ya tashi tsaye Shida maamah ne suka tsayu a gun kulawa da ita da yawon ganin likitocin da aka ringa yi da ita harta Dan fara samun sassauci tukuna Dad din yakoma harkokin gabansa maamah ta ci gaba da kulawa da ita.

***Maamah ta zama uwa ta zama kusan Uba ga ‘yayan Abeeda da nata yayan Dan kuwa Dad dinsu Bai fiya zama ba kusan youshe Yana hanyar zuwa dubo Abeeda duk da Babu Wani alamar nasara ko zata Tashi din Amma Bai cire tsammani ba kamar yanda yake Jin idan Abeedan ta tafi tabarshi zuciyarsa zata samu raunin da Babu healing har abada.

Babu abinda Ba’a wadata maamah da ‘yayanta a yanzu da komai na ragamar gidan yake hannunta,

Babu duniyar da basa samu,

Lalurar Husnah itace Mafi wahalar da maamah Kesha a rayuwarta sbd tamkar me ciwon qwaqwalwan gaske Takoma mata Dan haka sai take Shan wahala da azabar kulawa da ita Dan kuwa itama abin sai yake Neman taba ta Dan ganin takeyi idan AmatulMaleek dinta ce Hakan ya sama duk abu Daya zata ji gashi kusan ayanzu marayu ake daukan su Husnah din.

Ahankali ahankali lokaci yaja sosai Husnah tafara samun lafiya sosai bayan lokaci me Dan tsayi data dauka a halin na wuya da tausayi,

Maamah nata yayan sun hakura sadaukarwa Husnah da ita Dan kuwa tin bayan shigar Husnah wannan halin maamah Takoma abin tausayi itama sbd kula da Husnah din,

Ta wahala iya wahala akan Husnah,

Wani tsufa da qanqancewa tayi sbd rayuwar data samu kanta aciki,

Daidai da rana Daya Bata taba Jin gazawa ko jin ba ‘yarta ce ta jini take dawainiyar da ita ba,

Husnah da ita maamah din sun samu Wani irin shaquwa da bond me karfi dayasa AmatulMaleek dole ta barwa kanta yarda da Babu abinda zai wanke ko rage kaunar da maamah kewa Abeeda da iyalinta,

A yanxu Husnah data saddaqar ta rungumi rayuwa a yanda tazo musu ba magaifiya sai maamah da a yanzu itace take wa kallan uwa ta gasken gaske harka tana Jin kamar ta Fi Amatu so da buqatan maamah a rayuwarta Dan kuwa kauna da so me tsananin gaske maamah ta nuna make a babu sirk,

Haydar kuwa Amatu ce ta cike masa gurbin uwa,Kuma ‘yar uwa harma da masoyiyar dayake fata a gaba Dan itama duk da karatun datake harta gama ta tsayu akan kulawa dashi da debe masa kewa da hanasa shiga kowacce irin damuwa itada Abdul Daya zama kamar twin brother dinsa Dan kuwa komai nasu a yanzu Daya ne Babu bambamci.

A bangaren ASH TALBA kuwa a zuciyarsa Wani matsayi me girman gaske maamah ta samu da Babu abinda zai iya biyanta dashi har abada,

Itace ta tsaya akan gidansa da ‘yayansa a lokacinda Babu Wanda zai tsaya masa,

Alokacin da ‘yayansa suke buqatan uwa,

Alokacin da Shima yake buqatan macen da zata tsaya masa gidansa,

Ta sadaukar da rayuwarta da karfinta da lafiyarta harma da ‘yayanta Bata bari gidansa ya shiga maraicin matar gidan ba,hakama yayansa Basu shiga maraicin da zai illata kuruciyarsuba, haka ma dashi kansa da itace ta tsaya tsayin dakan kulawa da duk wata lalaurarsa da komai nasa harya same qwarin gwiwa da zuciyar komawa kan qafafunsa ya tsayu a harkokinsa ya koma yanda yake a Baya,

Dan haka maamah itace jarumar rayuwarsu da bazasu taba iya biyan alkhairinta garesu ba daga shi har ‘yayansa Dan haka matsayinta yake me girma a garesa.

Ta sadaukar da sauran karfinta da kuruciyarta ta tsufa karfi da yaji sbd wahalar data rataya akanta Dan bazaka kalleta kace tsaran Abeeda bace wadda itama aduk lokacinda yake dubata karyewa zuciyarsa keyi Takoma kamar ba itaba ciwo ya sauya kamanninta gaba Daya,Dan idan tanada Rabon tashi ba lallai ta sake komawa yanda takeba a Baya.

Mum Aisha datai tafiyar zuwa dawo Saida ta share itama lokaci me Dan tsayi kafin suka fara Shirye shiryen dawowa Dan Bata yarda ta dawo batareda Naufal da baiso dawowan ko kadanba shiyasa ta jira ya qarasa kammala takardunsa suka hada komai tareda Shirin dawowa gidan da zasu bude sabuwar rayuwa.

******AmatulMaleek tinda ta gama secondary Babu inda ta qara a karatun sbd Babu Wanda ya Tina da Hakan tinda Daman Madame abeeda ce take kula da lamarinsu Se mum Aisha datake musu komai da manufa Dan haka a gida take zaune tareda daukewa maamah wasu ayyukan gidan duk da ankawo masu aiki sunayi Amma wasu abubuwan kaman kulawa da sashen madame dana Mai gidan kusan yanzu itace takeyi tinda ko islamiyya ma ta sauke Dan haka Babu komai datake a rayuwarta itama yanzu bayan bautawa gidan ASH TALBA da Madame abeeda wadda suka fara shafe tarihinta duk da bawai ta rasu bane Amma a gurinsu kaman hakanne Dan kuwa ko su Husnah yanzu karatu sukeyi sosai kowa ya dangana ya rungumi kaddara hakama so Daya Dad dinsu ya taba zuwa dasu suka dubota sai yaga abin na tabasu Sai Bai qara barinsu zuwa ba.

******Ayau gidan ya Dan rayu da hayaniyar dawowar mum Aisha da Babban matashin Gidan ASH TALBA wato Naufal Talba Wanda dawowarsa qasar ya gama zubar da duk Wani farin ciki da burin rayuwarsa Dan haka Koda aka daukosu airport fuskarsa Babu alamar wasa ko sakewa acikinta,

Sanye yakeda black sweatshirt da sweatpants sai fcap da sunglasses.

Husnah ce kawai tayi murnar ganinsa ita data sansa sosai Dan haka rungumeta yayi ahankali Yana sake mata kyakkyawar fuskarsa Yana cewa

“Oh my gorgeous”

Dariya ta Dan yi tana dagowa daga jikinsa tace

“Sannu da dawo N Talba”

Dariya yayi sbd tinowa da shine ya koya mata kiransa da N Talba Dan Uncle din Yana masa Wani iri kamar tsoho.

Mum Aisha ta rungume itama tai mata sannu da zuwa cikin farin cikin ganinsu.

Ciki suke kokarin qarasawa Haydar ya fito daga geam dayake ta hanyar cikin garden Yana ganinsu ya qaraso Shima cikin farin cikin ganinsu ya rungume Naufal din Yana cewa

“Happy to see you Uncle, welcome”

Dan rungumesa Shima Naufal din yayi Yana kallan yanda Haydar din duka duka shekarunsa Basu wuce 18 ba Yanaga amma sbd geamin da yaron keyi ya Bude sosai kamar Wanda yayi 25 koma fiye gashi

Yana budewa kamanninsa da ASH TALBA na sake bayyana.

Ciki sukayo dukkaninsu zuwa palon mum Aisha da tini Amatu ce ta gyaresa fes Dan tin can tafison aikin Amatu Dan yafi nutsuwa da tsari Dan haka ko yanzu Amatu ce ta gyare mata palonta da bedroom dinta da toilet.

Shi Kuma Naufal sabuwar me aikinsu ce ta gyare bangarensa dayayi shekaru bayanan Amma ana gyarewa komai ya dawo fes kamar ranar aka sauya komai.

Ko zama Naufal beyiba a palon mum Aisha ya jiya yanufi bangarensa da already ankai kayansa can.

Yana Isa Bai tsaya Palo ba Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ya jefar da wayarsa kan lafiyayyan gadonsa Yana sake numfashi a bayyane tareda zare duk kayan Dake jikinsa a tsakiyar dakin ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwa.

Mum Aisha ma wanka tayi ta fito tayi salloli Dake kanta dayake safiya ce ko abinci Bata ci ba ta kwanta bacci sbd ta huta.

Shi kansa Naufal Yana Gamo wankan ya shafa abinda zai shafa na Mai da tirare ya Saka Wani tight short ya fada gadonsa hutawa yake buqatan yi.

Su Amatu kuwa mum Aisha kawai suka samu damar yiwa sannu da zuwa bayan ta tashi bacci da kusan yamma.

Kallan Amatu mum Aisha tayi ganin yanda a yanzu ta zama cikakkiyar budurwar da Babu abinda Bata rasa ba a jikinta na kyau da kyan jiki harma da jiri me kyau,

Sannan nutsuwarta data Saka ake Gani kaman sanyine da ita duk komai na nan saima abinda ya qaru ga uwa Uba kamun Kai ko a cikin gida ba kowane zece AmatulMaleek ta sake dashiba sosai.

Cikin gatse mum Aisha tana kallanta tace

“Amatu yanzu da aka gama makaranta Se aure ko tinda ba Wani karatun gaba zakiyiba”

Shiru Amatun tayi tareda Dan sauke boyayyan numfashi a boye kafin ta Dan saki kyakkyawan murmushi tana qarasa nade kayan mum din datake nadewa tana jerawa a wardrobe daga cikin akwatin Data dawo dashi batareda ta iya cewa komaiba.

sake maimaita tambayar tayi itama fuskarta a sake Dan tabbas zata so Amatun tayi aure da wuri tabar gidan tinda Naufal ya dawo idan batai taka tsantsan da Yan matan gidan ba masu aiki komai zai iya faruwa da wuri halinsa da Bazata taba yarda ASH ya saniba to zai sani komai ya lalace musu Dan haka dole zata Bude wuta ayiwa Amatu aure tabar gidan Dan gwara Yan aiki idan ya lalatasu zata Basu kudi ta sallamesu asiri rufe Amma AmatulMaleek sbd matsayin maamah a gun ASH zaa iya samun matsala.

Duk yanda mum Aisha din ta bugi cikin Amatu Dan Jin ko tanada saurayi Sam Bata samu Jin komaiba sbd zurfin cikinta dakuma saurayinka da batadashi.

Harta gama gyara kayan mum din Janta mum takeyi da fira daban daban itama ta San amsawa da Wanda ta sani Wanda bazata iya fada Kuma sedai murmushi kawai.

Kayan da zaa Saka cikin kayan wanki ta fito dasu basuda yawa kala biyu ne ma Dan haka ta fito dasu ta miqawa me aikin da zata wanke su.

Tana kaiwa kofar ficewa mum ta kirata tareda cewa

“Ki kawomin salad Amatu bazan iya cin white rice dinnan ba yanzu zata dameni”

“Ok mum” ta fada a natse da muryarta me dadi tana juyawa zata wuce ba zato tai karo da mutum da sauran kadan kirjinta ya Hadu da nasa tayi saurin yin Baya tana dago idanuwanta da Dan mamaki.

Naufal da sauran kadan numfashinsa yabar jikinsa sakamakon kamshin jikinta Daya shiga hancinsa sosai harma da Dan haduwar da jikinsu yaso yi sauke mata mayun idanuwansa yayi Yana kallan mamakin inda ta fito da inda zata,

Wani numfashi ya hadiye tarewa yawu ta maqoshinsa da Saida Hakan ya nuna a wuyansa Yana kallanta da dukkanin idanuwansa Dake qarawa mata sonsa.

Amatu dauke idanuwanta tayi daga kansa fahimtar waye shi Din

Sai tasake yin gefe kadan tareda Bude Baki a hankali ta furta

“Yi hakuri ban luraba,sannu da dawowa.”

Har lokacin idanuwansa akanta suke sedai lokacinda ta Bude Baki tana magana idanuwansa a bakinta suka koma daqyar ya Bude Baki zai amsa mata mum Aisha ta katsesa da cewa

“Amatu wuce kije”

Batareda ta gama fadar ba Amatu ta rabasa ta wuce tana Dan sake gyara riqon kayan hannunta dasuka zame batareda ko waiwayosa ta sake yiba.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

15

**********

AmatulMaleek na barin bedroom din Naufal ya daure tareda basarwa yaqi bin bayanta da kallo sbd mum dinsa dayasan idanuwanta na kansa.

Qarasowa yayi kan kujera Dake dakin ya zauna ahankali tareda kallan kayan abincin Dake jere kan table Dake dakin.

Tukuna ya dago a lokacin ya Kalli mum din cikin share abinda take tinani a zuciyarta yace

“Mum bazan iya cin abincin me nauyiba zai dameni”

Kallansa mum Aisha tayi ta hadiye maganar dataso fada sbd kada ma ta ankarar dashi akwai Yan mata a gidan sai kawai ta share abinda ya faru ta Bude Baki tana ajiye wayarta Dake hannunta tana cewa

“Eh Nasa a kawo salad sbd nasan bazaka iya cin abincin Kai tsaye shi Daya ba.”

Numfashi ya sauke Yana gingina bayansa da kujera tareda Kai hannunsa ya lalaba jikinsa Dan dauko wayarsa Amma Babu Saiya Tina baida layin Nigeria shiyasa wayar nacan daki ajiye Saiya huta ya kira a kawo masa.

Shigowar Amatu ne ya katse yar maganar dasuka Shida mum dinsa

Bai dago ya kalletaba yaci gaba da maganarsa kamarma baisan da shigowa Wani Dan adam dinba.

Mum ma Bata Kalli Amatun ba harta qaraso ta ajiye bowl da salad din yake ciki ta juya tabar gurin.

Harta fice Babu Wanda yabi inda tabi da kallo itama Amatun abinda yake gabanta kawai takeyi Dan haka tana baro bangaren Kai tsaye kitchen ta nufa Dake palon Madame abeeda Wanda yanzu bangaren Husnah da Haydar ne kawai sai ita datake Dan kwana da Husnah Wani lokacin Amma dai tama Fi kwana a dakinsu na bangaren masu aikin tinda can suka taso Kuma acan maamah take haryanxu Dan haka batama Wani son zama cikin gidan tafison inda maamah take.

Abdul ma kusan yakoma dakin Haydar duk da kayansa suna dakin maamah har lokacin hakama Wani lokacin a dakin Shima yake zuwa yayi baccin ranarsa.

Girkin abincin dare data Dora ta duba Wanda na Dad din gidan ne Dan Yana gari Kuma maamah ce kawai ke dafa abincin dazaici Babu me Saka hannu Amma Kuma yanzu Amatu na kama mata duk da saidai ta kama mata Amma Bata bar mata girkinsa sbd kiyayewa da Kuma gudun ayi kuskure.

Tana dubawa tabar kitchen din ta nufi bangarensu sbd wanki takeson yi da yamman na undies nata da wasu kayan Maamah.

Tana shiga daki Bata Tararda maamah ba tana gurin mum Aisha Dan haka Bata damuba kayan da zata wanke ta shiga hadawa harta gama hadawa ta fito dasu zuwa Baya inda suke wanki maamh Bata dawoba.

Wankinta tayi ta gama sai guraren magrib ta shige taje tayi sallah tayi wanka ta fito sanyeda hijab dogo har qasa sbd jikinta ba Wani kaya doguwar rigar bacci ne a jikinta shiyasa ta Sako dogon hijab din.

Kai tsaye kitchen data San maamah na can ta nufa ta Tararda harta gama komai har an Kai dining room da Ash ke cin abinci da yaransa matiqar Yana gari to tareda ‘yayansa yake cin abinci yanzu Kuma dasu mum Aisha suka dawo to dining din ya cika kenan.

Itace ta kamawa maamah sauran ruwa da abubuwan da baa gama jerawa ba takai ta jera mata ta fito daidai shigowan Naufal palon su Husnah gaisawa kawai sukai ta wucewarta.

Qarasa tattara komai a kitchen din sukai suka gyaresa kaman baayi aikin komaiba a ciki suka tafi daki.

Suna shiga wanka maamah tafara yi da ruwan zafin da Amatu ta hada mata dayake Abdul Yana dakin Yana guga Dan haka maamah na gamawa Suma zama sukai cin abincinsu da kowanne dare tare suke ci.

Suna farawa Basu Wani yi Nisa ba Haydar ya shigo dakin sanyeda kananun kaya fatar jikinsa na daukan ido sbd kusan kayan Shan iska ne three quarter da shirt mara nauyi qamshinsa na Dan tashi na tirarensa me tsada Dan kuwa kusan komai dayake amfani dashi odar mahaifinsa ne.

Idanuwansa akan Amatu Data dago itama tana kallansa cikin Jin sanyin ganinsa

Shima numfashi ya sauke Yana Jin sanyin zuciyarsa da ganinta kawai da yau kusan ya wuni baiyiba ya qaraso ya zaune gefenta Yana gaida maamah Dake tambayarsa yau ina yaje Bai zauna gida ba sosai.

Amsawa yayi da daukan spoon da Amatu ta aje Bataci abincin dashi ba ya Saka cikin plate dinta yafara ci Yana bawa maamah amsa da cewa tareda Mr Jameel suka fita Dad ya sakasu zuwa Wani guri.

Kan Abdul Dake tambayarsa yanda ta kaya da abubuwan yace masa zai masa bayani daga baya,

Kan Amatu da ita shi ta kalla ya Maida idanuwansa Yana murmushi yace

“Amah ki qara mana abincin Nan bazai ishemuba zanci da Dan yawa”

Abincin Amatu take kokarin Kara musu maamah tace

“Kaida zakuci abinci da Dad dinku Karka cika cikinka anan”

Abincin yaci gaba da ci Yana cewa

 “maamah ko naje can naci idan banci tareda Amah ba bazan koshi ba Dan haka saina ci nata cikin yake cika”

Dariya maamah tayi Abdul kuwa harararsa yayi Amatu Kuma kallansa tayi tana cewa

“Zaka tashi daga Nan yanzu kuwa”

Wani Mayen murmushi ya Sakar mata Yana cewa

“Maamah Amah fa tawa ce da gaske nakeyi Babu Wanda zaa bawa”

Dariya kawai maamah ta sake yi sbd tasan kuruciya ce kawai ke damunsa Ina shi Ina Amatun datake yayarsa Kuma Amah ko yanzu ta samu Miji zaa iya mata aure shi kuwa yanzu yake ma a harkar karatu bare aure.

Ganin dariyar maamh yasa Haydar din sake kallan Amatu yace

“Ko bazaki aureni bane?

Rasa abin fada masa Amatu tayi ta juya tana Neman abin jifansa dashi da Bata samu ba ta juyo tace

“Tashi bazanci abincin dakaiba Kaci a gurin Abdul”

Abdulhameed Daya Fi kowa sanin yanda Amatu take a zuciyar Haydar da gasken gaske cewa yayi

“Karma yazo mun Nan bazanci tareda Shiba anjima kadan shiryawa zakuyi kece Zaki fara cemun munafuki Dan haka ku qarata can Yana zuwa Nan fasa masa hannu zanyi”

Hakan Daya fada yasa Amatu jifansa da mugun kallo itama tana cewa

“To koma gurin maamah Kaci Dan bazan ci da kaiba na fasa”

Maamah ma cewa tayi ta gama ita Kam Dan haka sedai ya dawo gurin Amah din tasa.

Marairaice fuska da idanuwa yayi Yana cewa

“Anty Amahn Haydar Talba”

Hakan Daya fada ya sata dariya Bata shirya ba Dan haka dole ta barsa sukaci abincin Yana sake bayyana musu yanda Amatu take a zuciyarsa da gaske Amma duk suna dariya kawai sbd sanin wasa yakeyi dakuma kaunar datake tsakaninsa da Amatun datafi ta kowa.

Harsuka gama kusan tayata cin abincin kawai yayi bawani abin kirki yaci ba suka fito ya rakata takai komai kitchen suka dawo ya rakata har kofan shigewa daki ta shige ya juya zuwa lokacin yasan kowa ya hallara a dining room, Kai tsaye can ya nufa Yana zuwa ya Tararda kowa a dakin shi kadaine Baya Nan Kuma Allah yasa Basu faraba zamansu kenan Dan haka cikin Nutsuwa ya qaraso Shima tareda kallan Naufal yace

“Yaya Naufal barka da fitowa,

Mum Aisha Ina wuni?ya gajiya?

Husnah kuwa kallanta kawai yayi tareda jefa mata kiss na kumata daga inda yake kafin ya zauna Kofar palon Dad dinsu ta Bude wadda take kawosa dining room din daga palonsa na farko Dan haka dukkaninsu kallan kofar suka juya sukai ahankali kafin qamshinsa ya huro musu cikin gurin Yana gauraya gun gaba Daya.

Sanye yake cikin Ash wandon Fendi fa farar rugby shirt sai black Lorenzo slippers marasa nauyi da tsadan gaske,

Idanuwa Naufal ya zubawa ASH TALBA Wanda ya kasance tamkar Wani madubi a idanuwansa da zuciyarsa,

ASH TALBA namiji ne Daya amsa sunan Maza ba muna Maza ba,

Namiji ne da kallo Daya zama masa kasan namiji ka kalla Tako wanne bangaren,

Babu Wanda ze kallesa yace shine ya haifi matashin saurayin Dake gabansa Haydar Talba,

Namiji ne da ko shi dayake amsa sunan matashi me lokacinsa zai rissina masa sbd ko karfinsu bazaa hada ba tinda daga karfin jiki harna zuci,harna Imani,harna komaiba ita dukiya da kwarjini tareda wata irin nutsuwa da aji bama zai hada kansa da the grt ASH TALBA ba da ake fada,

Tako Ina Ash namiji ne tsayayye da babu abinda yake masa shamaki.

Lafiyayyar fatarsa data ke daukan idanuwansu ya kalla ganin wato shi Hutu da jiqa cikin arziki da nutsuwa Wani abu ne na daban da idan Allah yayika cikinsu basa boyuwa,

Ya rasa Menene ya Saka akoda yaushe ASH TALBA da komai nasa daban ne,

Komai nasa unique ne,

Duk abubuwan tsadar rayuwar su Naufal yake Siya Amma haryanxu inda ASH yabi ya wuce ma yafi qarfin gwajinsa,

Duk shekarun Nan Babu abinda yake ran mahaifiyarsa bayan ya zama tamkar the grt ASH TALBA,shi kansa babban burinsa ne ya zama kamar Ash Talba Amma bayajin Hakan zai iya yiyuwa Dan kuwa izza da asalin kwarjini da haiban tareda kamewansa duk a jininsa suke hakama shi arziki irin wannan na Ash din Allah ne kawai zai baka irinsa ka samu zamowa.

Duk Izgilancinsa da nasa zafin Kai a gaban Ash Jin yake ya zube qasa warwas shiyasa Baya iya ko kallan cikin idanuwansa duk tsanani kuwa,

Ita kanta mum Aisha datake ‘yar uwarsa kwarjinsa durqusar da ita yake a gabansa Dan haka take gujewa tsayuwa a gabansa a duk lokacinda zata zartar da hukuncinta acan cikin gida Dan Bata iya kallansa a fuska ta aikata abinda take aikatawan.

Gaba dayansu dauke idanuwansu daga kansa sukai har ya iso a natse ya zauna tareda dagowa ya Kalli Naufal da shine ya fara gaidashi Yana masa barka da fitowa.

Fararen idanuwansa masu kwarjini ya saukar akan Naufal din da nutsuwa harma da kulawa yace

“Yaya gajiya?

Murya a natse Naufal ya amsa Yana sake gaidasa tareda sake jajanta masa jikin aunt Abeeda harma da mata adduar fatan samun lafiya.

Amsawa yayi a natse Yana kallan abincin da Husnah take serving nasa a taqaice yace

“Ya Isa”

Tambayan Naufal din yafara yi sama sama akan komai na karatunsa Daya kammalo Shima Yana basa amsa a natse cikin Kamala Dan dole idan zakayi magana da ASH din ka nutsu.

Abincin suka fara ci Babu me magana hakama kowa da kusan abinda yake ransa tsakanin mum Aisha da Naufal Wanda yakoma Wani irin kamilallen mutum,

Itama mum Aisha gaba Daya a jiqe take da zufa kada Naufal yayi abinda zai fara batasa a idanuwan ASH.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

16

***************

Ash dinne yafara gamawa ya dauki tissue ya goge bakinsa tareda miqewa yabar dining din kafin Haydar da Shima ba Wani yunwa yakeji ba tinda yaci a gurin Amah dinsa.

Bayan Dad dinsa yabi Wanda yaji Haydar din biye dashi har zuwa palonsa ya zauna ahankali akan 2 seater ta Turkish luxury sofas Dake palon sun gama daukan sanyin ac da qamshinsa da kusan komai na palon ya dauka.

Wayarsa Dake gefensa ajiye ya Kai dogon hannunsa fari tas ya dauka Yana cireta daga flight mode ya mayar ya ajiye tareda dagowa ya Kalli Haydar din Daya zauna kusa dashi Yana cewa

“Dad maganar AmatulMaleek din maamah Da karatunta Dana fada maka ne,

Ta gama school din tin kusan last year Amma haryanxu Bata qara gaba ba.”

Numfashi Dad din ya sauke tareda dauke kallansa kan Haydar daya marairaice sbd yasan Babu abinda suke tambaya gurin Dad dinsu Bai musu ba sbd sune kadai hasken idanuwansa a yanzu.

Idan Bada Haydar din ya tinatar dashi ba Sam mantawa yakeyi bayan Abdul da kusan koyaushe suke tareda Haydar cewan Asmau nada wata ‘yar sbd baitaba ganinta ba tin tana jaririya Daya taba ganinta haryanxu baitaba ganinta ba shiyasa ya manta da Yaya biyu ne da Asmau,

Amma a yanzu tinda Haydar ya tinatar dashi zaai mata komai na karatu a inda Husnah take inshallah.

Kallan Haydar daya gama Saka sakewa da jiran abinda Dad din nasa zai fada yake,burinsa da tsananin fatan buqatansa ta kasance yayi Yana tabbatarda mahimmancin maganar karatun yarinyar a gun Haydar din sbd Babu abinda ya taba buqatama da har sai yazo ya tambayesa sai ayanzu Dan haka ya sake kallansa cikeda kulawa da kauna me qarfin gaske yace

“Kaje Jameel zai mata komai inshallah zata ci gaba tareda Husnah”

Wani irin murmushin farin ciki da sanyin dayake zuciyarsa be ya bayyana kan fuskarsa ya qaraso ya rungume Dad din ahankali Yana cewa

“Thank you Dad”

Da mamakinsa ya Sakar masa tsadadden murmushinsa Yana dafa bayansa tareda nanata masa yafada mata tayi karatu sbd karatu ake makarantar sosai.

Gyada Kai Haydar yayi cikin farin cikin Yana cewa

“Dad zatayi,zatayi karatu sosai,kaima zakayi alfahari da karatunta inshallah”

Gyada kawai dad din yayi Yana duba wayarsa data kawo haske alaman shigowan kira.

Ficewa Haydar yayi cikeda farin ciki,

Surprising din Amah yakeso yayi Dan haka bazai fada mata yanzu ba.

Bayan ficewar Haydar daga palon wayarsa ya dauka ahankali cikin nutsuwa yakai kunnensa tareda amsa sallamar Wanda yayi Kiran Yana bin bayan Haydar da kallo harya fice.

Mum Aisha ma duk sunbar dining din kowa ya nufi bedroom dinsa Naufal kuwa Yana komawa fita yaso yi Amma rashin layin dazaiyi waya ya Sakasa fasawa dole ya shige da wuri.

Washe gari da safe kusan kowa fita yakeyi masu zuwa school da masu zuwa aiki Dan haka daga Amatu sai mamah da masu aikine a gidan yawanci da safe sai yanzu tinda mum Aisha sun dawo.

Amatu ce ta shiryawa mum Aisha da Naufal breakfast ta Jere musu a palon mum Aisha din sbd abincin dare ne kawai kusan Yan gidan sukeci gaba Daya atare sbd ASH da dare kawai yake zaunawa acikinsu cin abinci sai breakfast Wanda shikuma daga shi sai iya yayansa yake yinsa wannan shine qaidarsa sbd Yana son time dinsa na safe da yayansa kawai.

Bayan tagama shirya musu abincin Naufal ne ya shigo palon lokacin mum Aisha din Bata fitoba,

Sanye yake da designers qananun kaya blue Bai Wani Kalli Amatun ba Dan gargadi da iyakar da mum tai masa da duk wata macen Dake gidan Dan haka Koda ta gaidasa amsawa kawai yayi Yana zaunawa sama sama yayi breakfast din ya fice Yana ce mata idan mum ta fito ta sanar mata ya fita.

Ok” kawai ta furta masa batareda itama ta juyo ta kallesa ba daga gyaran palon datakeyi Hakan ya Sakasa dakatawa ya juyo Yana qure kallansa akanta sbd mamakin basarwanta da rashin basa mahimmanci.

Fararen yatsun hannuwanta masu tsayi da kyau ya zubawa hannu tana rufe zip din throw pillow data Dan Bude ta gyara na kujerun palon.

Gangarawa yayi da idanuwansa kan wuyanta da Shima fatarsa take fara tas kaman ‘yar Hutu,

Akan kirjinta ya dawo da idanuwansa Ya kalla yanajin zuciyarsa na harbawa da qarfi.

Motsin juyowarta ya sakashi Maida idanuwansa kan kyakkyawar fuskarta yana juyawa yabar palon zuciyarsa na shiga wasi wasi.

Batasan duk abinda ya tsaya yayi din ba Dan haka aiknta taci gaba da yi harta gama mum Bata fito ba dan haka ta tattara ta ficewarta.

Naufal driver yasa ya fita dashi a Daya daga cikin manyan motacin gidan Dake haraba,

Kai tsaye layuka ya Siya manya masu numbers me kyau kafin suka wuce Kai tsaye gidan dayake buqatan zuwa na Amininsa zayyan acan driver ya ajesa ya wuce.

Dayake suna tareda da zayyan din acan Spain kawai dai zayyan din ya rigasa dawowa Dan haka Yana shiga suka cafke Babu Bata lokaci yasa zayyan ya samo masa lafiyayyar mace anan gidan ya wuni Yana hutawarsa tareda sauke nauyin dayake Jin tin kwanaki Yana cikinsa Dan tinda mum dinsa ta tafi gidansa ya rage Neman mata sosai sbd fadanta da zamanta a gidansa shiyasama kafin su dawo yafi sati biyu rabonsa da mace Dan haka a tsananin matse yake.

Ba qaramin dadi yaji ba a wuninsa gidan zayyan Dan haka sai dare ya koma gida Kuma Yana komawa shigewa yayi kawai Dan Baya buqatan komai bayan bacci yanzu.

Washe gari Bai fita ba sai Rana ya dauki mota da kansa ya fita Kai tsaye Wani guri suka nufa da zayyan Wanda ya kusan kashesa da dadi sbd mata ne masu aji manyan mata ‘yayan masu kudi wasu Kuma manyan Yara Dan haka kusan budurwa hudu yayi lokaci Daya Kuma a ranar ya same yanda yakeso sosai ya huta qarshe a gidan zayyan suka kwana Wanda Shima ba anan yake zauneba gidan iyayensa yake zama wannan gidan hutawa ne kawai.

Washe gari tareda mum dinsa yayi breakfast batareda tasan baa gida ya kwana ba Dan kuwa sosai ya iya takunsa.

Ahankali ya goge sosai da Yan matan dayayi sabbi harya fara gajiya dasu yafara sauyawa Dan dama Babu Wanda maganar so take acikinsu kawai Jin dadine sai hutawa.

Ta bangare daya Kuma kwata kwata ya Dena kwana gidan Kuma Babu Wanda ya sani bayan securities da Babu abinda zasuce,

Acan Spain idan kanada budurwa baka iya kula wata macen sai ranarda kukai break up Amma anan yanzu mata kusan Shida ne dashi lokaci Daya Kuma Babu wacce Baya biyan buqatansa da ita duk da Basu saniba Amma dai sun San bazai iya zama a guri Daya ba.

Idan akace Naufal Neman mata yake kaman an ragewa lamarinsa girma ne Dan kuwa tamkar bunsuru haka yake da mata,

Sam baitaba gajiya da Neman mata ba,Baya iya kwana Bada mace ba,Baya iya wuni Bai Hadu da mace ba Sam Kwata kwata dai bazai iya rayuwa batareda yana samun mace ba.

Dawowansa Nigeria Babu abinda ta qara masa sai lalacewa da tabarbarewa sbd a yanzu Kam matan ma wasu sune suke nemansa sbd kwadayi da son abin duniya tinda kallan babban ‘dan the grt ASH TALBA ake masa Wanda a yanxu yake matsayin Dan takarar governor na jaharsu duk da ASH din Sam Baya shaawan siyasan shiyasa ma yaqi komawa state din yayi zamansa Abuja Dan Baya buqata manya ne suke son tsayar dashi.

Duk Nisa da lamarin Naufal yayi mum Aisha Bata ganeba sosai Dan haka taci gaba da cusashi agurin ASH musamman yanzu da lamura suka dauki zafi a harkar siyasar sosai gidansu ya koma Saida aka qara masa securities da jamian tsaro sbd komai yanata sake tabbata.

Suna sosai Naufal Talba yayi sbd rayuwar Dayake zubawa da Yan mata yayan manya da yanda yake sakewa Yan mata kudi kaman baisan zafinsu ba.

Abokansa biyu ne zayyan Mande da Fahad Sadam Kuma Suma dukansu yayan manyan ne da bayan su kashe kudi basusan wahalarsu ba sai mata da su kadai abinda suke buqata.

AmatulMaleek kuwa lokacinda labarin cigaba da karatunta ya sameta tayi farin ciki me tsananin gaske tareda Jin girman kaunar haydar a ranta ta Qaru Husnah ma ta tayata murna Dan haka suka maamah da kanta ta tafi da Amatu gurin ASH suyi masa godiya.

Da daddare bayan sun gama dinner kowa ya watse Haydar ne yaje ya sanar da Dad din Maamah na son ganinsa,

Baya yiwa maamah shamaki da kansa kamar yanda ko mum Aisha datake jininsa idan zata gansa saita kirasa a waya Amma maamah koyaushe tace tanason ganinsa Yana Bata wannan damar sbd matsayinta daban daban yake a gurinsa sbd yayansa da matarsa dayasan son datakewa Asmau hakama yayansa a yanzu basuda Wanda suke so a duniyarsu kamarta idan ya cire kansa.

Haydar dinne a gaba sai maamah sai Kuma AmatulMaleek din datake bayanta suka shigo a natse tareda sallama qamshinsa Daya shiga hancinsu tareda sanyi ya sakasu sake shiga nutsuwansu Dan kuwa akwai Wanda qamshinsa kawai zakaji kasan ya cancanci respect,to kamshin ASH TALBA kusan Hakan ne kanajinsa zakasan ba qaramin mutum zaka ganiba.

Idanuwansa masu haske akansu suka shigo batareda ya lura da AmatulMaleek Dake bayan Maamah ba Saida Haydar ya ambaci sunanta tukuna Dad din ya lura da akwai mutum bayan Asmau.

Kujera ya nunawa Maamah din yace ta zauna ta zauna sbd akwai sakewa ba laifi tsakaninta dashi, AmatulMaleek kuwa aqasa ta zauna gefen Maamah din tareda Dan dagowa cikin nutsuwa ta gaidashi muryarta a natse ba rawan jiki ko sanyin murya kawai dai asalin nutsuwanta.

Kallo daya yayi mata ya fahimci itace AmatulMaleek ‘din Asmau ya amsa da kulawa tareda mayar da hankalinsa kan maamah suna sake gaisawa tayi masa godiya sosai Akan karatun Amatu itama Amatun cikin nutsuwa ta miqa tata godiyar.

Tinda suka shigo Amatu Bata iya dagowa ta Kalli fuskarsa ba sbd Wani irin kwarjini da haiba ne yake cika duk inda ASH TALBA yake musamman ita da Bata Saba ganinsa a zahiri ba sedai a waya ko hoto uwa Uba yanzu da ake kirarinsa da sunan governor guda.

Haydar kuwa tinda suka shigo shidai nasa idanuwan akan Amatu suke har suka gama suka fice Ya bisu Yana tsokanarta akan zai fadawa Dad din ita zai aura idan ya tashi aure.

Harararsa Tayi tana murmushi Dan batasan ma me zata ce masa ba Dan takaici.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

17

**********

Fara karatun AmatulMaleek ya Sakata qara gogewa a cikin wayewa duk daman Bata cikin duhun Kai a wanke take Dan duk wahalar dasuke a cikin gidan to basa cikin wahalar rayuwar tinda me kyau suke ci Kuma su sha me kyau hakama su kwanta me kyau su Saka me kyau Dan itama kusan komai sabo take sakawa yanzu da Haydar ya Saka Dad dinsu yayi noticing dinta a suna Banda kamanni Dan haka kamar yanda a Baya ake siyawa Abdul duk abinda aka siyawa Haydar to kusan itama hakanne yanzu komai nata ya sauya tana samun komai yanda ya kamata.

Naufal kuwa tini yafara aiki a matsayin director na kamfanin kasuwancin ASH empire Dan haka rayuwa taqara yi masa yanda yakeso duk ba wannan matsayin sukaso ba daga shi har mum Aisha Amma Kuma Basu cire tsammanin kaiwa inda sukesoba dan haka mum Aisha ta dage sosai tana sake cusa Naufal a gun ASH.

Gaba dayansu yaran gidan baa barinsu Jan mota da kansu bisa ga umarnin ASH Dan haka dukkaninsu drivers ne suke kaisu makaranta tareda security Daya hakama duk Wanda ya gama cikinsu driver yake kira yazo ya daukesa har Amatu

Haydar da Abdul kuwa dayake dama yanzu ne suke Shirin rubutawa exam din gama secondary school tare ake kaisu a daukosu tare.

Barnar Naufal tayi yawan da tini mutane suka fara sanin halayyar tasa Dan haka sai Hakan nason taba mutuncin Ash ga wainda suka fara sani batareda shi yasaniba.

Tafiye tafiye sosai Naufal keyi sosai Dan yafi sakewa idan ya bar garin yaje can yayo sharholiyarsa y dawo.

Ana Hakan matan da suka zubar da cikinsa a jikinsu yafi nawa Dan haka sai zancen yafara bayyana ga mum Aisha wadda ta kamasa dumu dumu sakamakon cikin wata yarinyarsa da aka zubar ta rasa ranta sanadin Hakan Dan haka tini zancen ya fita aka fara sharia saiga zance a duniya yafara yawo ‘yan jarida Dake Jira tini aka yada labarin.

Tashin hankalin da baa Saka masa rana ba mum Aisha tashiga gashi Shima Ash Talba din dole sai ya fito yayi magana akan zancen da Yan jarida tinda a kotu ake.

Su Husnah kuwa mamaki sosai suka shiga Amatu Kuma Daman Bata shiga abinda Bai dametaba sosai kawai dai damuwarsu shigowar bacin sunan Ash da ake Neman yi Dan haka suka Dan shiga damuwa Maamah kuw sosai tashiga damuwa Dan Naufal din mutuminta ne Yana yinta ba laifi.

Cikin baqin cikin data samu kanta mata adadi mum Aisha ta samu case din ya mutu Wanda aka tabbatarda ba Naufal ne yake muamala da yarinyar ba Maza da yawa ne Kuma daga karshe ma dai ba wannan ne cikin farko data zubarba Kuma Babu Wanda ya tilastata zubarwa itace tayi Kuma Hakan yaxo da matsala har yayi ajalinta.

Mutuwar case din ya Saka familyn gidan samun nutsuwa da hamdala Amma ASH TALBA ya dakatar dashi daga fita aiki gaba Daya sbd hukuntasa.

Wannan hukuncin baiwa mum Aisha da dadi ba Dan haka ta daga hankalinta sosai,zagi da fada Babu ranar da Bata wuni sai a kwana Bata yiwa Naufal daga qarshe ma tayi rantsuwar bazai qara fita mansion din ba.

****Abu Daya da mum Aisha Bata sani ba shine hanasa fita shine ya bullo sabuwar matsalar cikin Mansion din,

Bai Dena fitaba sbd Yana ficewa yaje yayi abinda zaiyi ya dawo batareda ansan ya fita din ba Dan haka Neman matan nasa ya rage tinda Baya samun isashen time sosai a waje,

Ta bangare daya rashin samun yanda yakeso a aynzu yasa idanuwansa suka dawo Kan ‘yan matan gidan masu aiki yafara farautarsu Daya Baya Daya yana lalabewa duk da qyamarsu yakeyi Amma dai tinda Yana samun yanda yakeso sai yana manejinsu hakanan.

A qanqanin lokaci kusan Yan matan biyu masu aiki ya Maidasu kaman matansa Babu ranar da baya kusantarsu idan yayi yau da wannan gobe da dayar zeyi.

*****AmatulMaleek datafi duk matan dasuke gidan kyau Tim daga masu gidan har masu aiki itace maqale a zuciyarsa da idanuwansa,

Kyakkyawa ce hakama Mai aji da kamewa ce Sam saikayi sati nawa a cikin gidan batareda ka Sakata a idanuwanka ba Dan Babu abinda yake fiddota sai ayyukan da baa rasaba tinda karatu yanzu Baya barinta ma ayyuka tini maamah ta dauke mata iyakacinta karatu da hutawa sai ranakun datake gida take Saka hannu a wasu ayyukan gidan.

Ta bangare daya siyasan ASH TALBA ya dauko zafi gadan gadan sbd lokacin zabe Daya gabato sai gidan yakoma tsaronsa yanata qara ninkuwa Dan Babu abinda Ash ya hada da tsaro tareda kariyar familynsa.

Husnah Bata Nan tana porthcrt gurin Hutu tareda Haydar gun dangin mum dinsu wadda daga can kafin su dawo zasuje dubota.

Abdulhameed ma wannan Karan ya sake zuwa kauye Shima ya dubo dangin nasu mahaifin a karo na uku Dan haka daga AmatulMaleek sai maamah sai su mum Aisha.

Kwadayinsa Naufal ya fara bayyanarwa akan Amatu Dan haka maamah tafara shiga fargaba da shakku Amma dai Bata nuna komaiba ganin itama Amatun tafara shiga taka tsantsan dashi.

Mum dinsa ganin wadda yafara kaiwa hari baqin cikinta ya tsananta ta kallesa a lokacinda suke zaune palonta tace

“Wane irin Dabba kakeson zama ne Naufal akan mata?

Wace masifa da balai ne wannan ni Aishatu take bibiyata,

Nayi Dana sanin dawowarka ma Dana sani nabarka acan qasar Kayita abinda kaga dama idan yaso ranarda ASH yasan abinda kakeyi Saiya dakatar da duka kudinsa da aka Sakar Maka kana wannan ta’addancin alokacinne zaka gane me nake nufi daka nutsu mu samu gurin zama da gurbi a wannan dukiyar……

Magana ya Bude Baki zeyi ta katsesa cikin baqin ciki da takaici tana cewa

“Ka fitarda macen aure kawai kayi aure tinda bazaka iya kame kanka ba kayo mummunan gado harka zarta,

To wlh Bazan iyaba,idan ka lalatamun komai to tabbas saikaga yanda baka so Dan wlh Nima dubu Daya bazaka sake samu ta hanyataba tinda zuciyarka ta Dade da mutuwa a gurin mata.”

“AmatulMaleek kuwa da wuri da gaggawa kayi saurin dauke idanuwanka akanta Dan duk kaje ka lalata musu ita to ko ni wlh Kila qarshen zamana a karkashin ASH yazo bare Kai Dan akan Asmau zai iya aikamu inda mukaqi jinin zuwa wato inda muka fito Dan haka Maza Maza ka cire kwadayinka akanta tinda ka riga ka gama lalata Yan aikin gidan Nan tas,

Kai ko qyama bakaji ne?

Bazaka iya hakuri ba bayan kwana bibbiyu kaje ka samu na wajen ba ka biyasu ka sauke buqatarka Amma ace Yan aiki ma nema kake,mtswwee.

Zafi zuciyarta keyi kaman zata fashe Dan tana cikin baqin cikin wannan muguwar kaddarar ta hada jini da hamis Da Danta ya dauko halinsa.

Fadanta da zafinta koyaushe Sosa ran Naufal sukeyi Shima sbd idan ta fada kalamanta Sam Babu alkhairi a cikinsu koyaushe Dan haka Bai iya cewa komaiba Shima ya miqe yabar palon Dan kuwa ayanzu yake Jin AmatulMaleek din a ransa ko aurenta ze iya yi Dan biyan buqatansa idanma har be samu yanda yakeso ba kenan

Idan Kuma mum din ta matsa akan maganar auren Amatun zai aura kawai kowana ya huta.

AmatulMaleek data gaji da kadaici sai kawai ta fara fita wasu lokutan zuwa guraren Shan iska musamman tinda  Hutu sukeyi gashi ba kowa.

Ana cikin Hakan Barr Faisal turaki ya ganta a cikin gidan zuciyarsa ta kamu da kaunarta alokaci Daya duk da ya jima sosai da familyn TALBAs din Amma Bai taba ganinta sbd shine lawyer din Madame Abeeda Kuma shine babban ‘dan Wani yayanta Dake porthcrt da maman babansa da maman Abeeda uwa daya Uba Daya suke Dan haka dadynsa yayan madame Abeeda ne,

A UK sukai zama taredasu Abeeda har suka rigasa dawowa Nigeria Amma Shima ya jima da dawowa kawai dai Baya zuwa Nan dinne sbd madame Abeedan Bata Nan hakama da Husnah kawai yake communicating Shima sbd Husnah dinne tafi nemansa koda yaushe har shaquwansu yayi qarfi sosai da sosai,

A bangaren Husnah Faisal turaki ba iya Dan uwanta take kallansa ba,

So ne take masa me tsananin gasken da kusan ko familyn mum Abeedan sun sani,so ne me tsananin gaske gaba Daya ma she’s obsessed,

Bata iya boye sonsa duk da tsakaninsa da ita baitaba fada mata so hakama yasan yanda take tsananin sonsa sedai bayajin zai iya takura kansa ya aureta batareda yana sontaba,Hakan zai cutatar da ita yakuma cutatar dashi Amma Sam ta kasa gane Hakan shikuwa a matsayinsa na dan Boko sosai da sanin YANCI ya gama ratsashi bayajin zai iya auren damuwa da takura tareda cutatar da juna Dan kuwa Yanda yake Sonta na tsakani da Allah har zuciyarsa ta Yan uwanta bayason ya aureta su lalata rayuwarsu gaba Daya ya zabi tsayawa kan raayinsa duk maganar da iyayensu da Yan uwansa keyi ya tsaya akan Hakan.

Ayau Kuma Daya zo duk da Husnah batanan yazo ne sbd aiki Daya dawo dashi Abuja da zama Dan haka yashigo su gaisa dasu mum Aisha harma da Naufal dayake mutuminsa.

Sosai yayi mamakin ganin AmatulMaleek wadda yake Jin sunan a bakin Husnah tin shekaru…

AmatulMaleek dinne tayi serving nasa duk Wani abin motsa Baki tareda gaidasa cikin nutsuwa ta juya ta fice  daga babban palon gidan Takoma daki Dan dama fita zatayi zata wankin Kai.

Mum Aisha da lokaci Daya taso fahimtar Barr Faisal akan kallan Dayabi AmatulMaleek dashi take taji Babu ma abinda zata so a yanzu Daya wuce barr din ya aure AmatulMaleek din tabar gidan kafin Naufal ya janyo musu abinda zai riguzasu akan kwadayinsa da Amatun Dan tasan tinda ya qwallafa Rai akanta sai Allah idan zai hadiye wannan tsinannen kwanadayin nasa Dan haka zama ta gyara tafara yin bayanin waye AmatulMaleek din a gidan tareda yabon halayenta.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

18

************

Shiru kawai Faisal turaki yayi Dan kuwa shi a tsarinsa shine yake karantar abinda yakeda raayi akansa da kansa Baya daukan bayani ko yabawar Wani Dan haka duka bayananta Babu Wanda ya damesa hakama Babu Wanda zai qara masa Sonta ko Rage masa Dan haka shiru kawai yayi harya gama ya fita ya wuce tinani da yawa ne akansa.

AmatulMaleek da bama zatace Ta Kalli fuskarsaba bare riqe kamanninsa tini ta manta da Wani baqon da Akai ta kama alamuran gabanta.

Shikuwa kwana biyu ya sake zuwa gidan dayake Shima yasan maamah wannan Karan da ita yayi fira sosai har Amatun ma Saida suka gaisa ya Dan jata fira gameda karatunta sbd law take karanta itama.

Yanda ya ringa fahimtar da ita wasu abubuwan gameda course din ya sata Dan sakin jiki tana fahimtarsa Wanda har dare Yana gidan Saida yayi dinner tareda jamaar gidan kafin ya tafi.

Dayake me saukin Kaine shi da sanyin hali kaman Amatu tini suka fara fahimtar juna Yana Bude mata sani akan karatunta da Daman tana Neman me zaunawa da ita suyi karatun yanda ya kamata sbd a school Batada qawaye.

Karatuta dayazo Daya da nata shine ya Basu Daman fara kusanci da juna da yawan waya batareda tasan Menene abinda yake zuciyarsa akanta ba,

Maamah data fara fahimtar sosai son Amatun Faisal turakin keyi sai Hakan ya Bata nutsuwa sbd Bata taba sanin Husnah Faisal dinne a ranta ba sbdz Bata taba fada mata ba su mum Aisha ne kawai suka sani da sauran dangin Abeeda.

Dan haka ita idan har Amatun zata auri Faisal turaki hankalinta zai kwanta da yanzu yake a Dan tashe da lura da Naufal ma Amatu yakeso.

Hutunsa Amatu ya qare Dan haka su Husnah Basu dawoba a satin sai kusan bayan sati biyu sbd basa qasar suna Greece tareda Dad dinsu gurin Madame Abeeda.

Amatu tayi mamakin ganin Faisal turaki a university dinsu Ashe Nan ya dawo da aiki sosai tayi farin cikin Hakan Dan kuwa ba qaramin taimaka mata Hakan zeyiba.

Shi kansa yayi mamakin farin cikinta shiyasa ma Bai fada mata ba tin Farko,

Sabuwar shaquwa suka sake samu ta Hakan Dan wasu lokutan shine yake dawo da ita gida.

A satin dasu Husnah suka zasu dawo a satin ya sanar da AmatulMaleek son da yake mata tareda Neman damanta na Neman aurenta idan sun sake fahimtar juna.

Da farko mamakinsa tayi sbd Kai tsayensa daya sata Jin nauyinsa tinda baa taba furta mata ana Sonta ba bayan Haydar da kullum yake fada mata yana sonsa sosai takuma San shi nasa wasa da Kuma kaunar Dake tsakaninsu ne.

Kunya ta hanata amsa masa Amma Shima yaga alamar ya samu karbuwan Dan haka sai hankalinsa ya kwanta sosai ya tashi daga matsayin Dan uwa dayake ya koma na masoyi Kuma mijinta inshallah.

Bata fadawa maamah ba saida suka kwana biyu maamah taga yanayinsa ya sauya daga yanda yake gaidata da sauran abubuwan.

Itama mum Aisha data fahimci a sosai Faisal din ya mutu akan Amatu cikin qanqanin lokaci tini tafara Jin nutsuwa tareda fatan ASH na dawowa  zata fada masa ayi auren ba Bata lokaci Amatu tabar gidan.

Mum Aisha nata gaggawar kusan baifi na maamah ba data fita son Amatu tayi aure ta tafiyarta batareda matsalar komaiba itama ASH din take Jira ta sanar masa da kanta.

*****Su Husnah sun dawo sun tarar da wannan mummunan labarin Daya kusan tayarda ciwon Husnah na qwaqwalwa Dan kuwa shock Mai tsananin gaske ta shiga Jin Faisal da AmatulMaleek suna tare har ana maganar afadawa Dad dinta maganar aurensu.

Haydar ma kusan shock din ya shiga sbd baitaba kawo Amatu ma zatai saurayi a yanzu kafin shi ba hakama da Wanda ‘yar uwarsa ke tsakanin so tin Bata gama zama cikakkiyar budurwa bama.

Kai tsaye Haydar ya soke zancen akan Bai yarda ba tareda tada rigima wadda tasa maamah da kowa ma shiga mamaki me girman gaske Dan har lokacin dauka sukeyi wasa yakeyi kamar dai yanda suke dauka a bayan wasa yakeyi idan Yana cewa Yana son Amatun.

Ita kanta Amatun kasa yarda tayi har lokacin da gaske yake Dan haka ta sharesa sai dai Kuma ga mamakinsu da tashin hankalinsu da gaske yakeyi Sonta yakeyi Kuma wlh bazai yarda ta auri kowa ba.

Naufal ma da sai alokacin yake samun zancen tashi hankalinsa yayi Dan bazai yarda Shima ya gama hadiye mata yawu Wani yazo ya aureta yabarsu da raba ido Amma dai Shima hauka yake daukan zancen Haydar.

Mum Aisha dataga wannan sabuwar masifar gargadin Naufal tayi akan karya yarda ya fidda nasa zancen akan Amatu Koda wasa.

Faisal ma mamaki da kishi me tsananin gaske ne ya fara cinsa sbd dai anbuga an raya Haydar da gaske yake ya daga hankalin jamaar gidan akan Amatu bazatai aureba.

Tashin hankalin Daya Saka mutane ya Hana a fahimci halinda Husnah take ciki itama ga ASH Baya Nan Saida kusan komai ya lalace yayi girma ya sani cikeda mamaki me girman gaske ya dawo Dan yakasa fahimtar Haydar din duka duka nawa yake yanzu ne yake jamiaa shekarar farko zaice Babu Wanda zai auri Yarinyar sai shi.

AmatulMaleek hankalinta tashi yayi a lokaci Daya kuma tareda sanyin jiki sbd har cikin zuciyarta batason ganin Haydar a halinda ya shiga na wannan tashin hankalin Dan haka take Neman shiga Wani hali na matsanancin damuwa,

Hakama maamah damuwa ta shiga sbd su duk sun dauka acan Baya wasa yekeyi da tini a andakatar da abin yanzu gashi komai na Neman zama babba.

Ranar da ASH ya dawo qasar Babu Wanda yayi magana dashi sai washe gari Bai nema kowa ba sai maamah wadda suka jima suna magana ya Sakata tayi magana da AmatulMaleek idan tanason Faisal din.

Daga maamah har Amatu Babu Wanda yake farin ciki da halinda Haydar ya Saka kansa Dan haka kamar ta fasa auren haka Amatun ta ringa ji to Amma zuciyarta ba qaramin so takewa Faisal ba shikuma hakama Shima acan nasa familyn anata rikicin nasu aminta da aurensa da Amatun ba da Husnah sukeso sai alokacin ASH TALBA yasan wannan sabuwar damuwar.

Rasa abin yi yayi sbd Shima bazai iya aurawa Husnah namijin da Baya Sonta ba bazata taba Jin dadi ba Dan haka ya Yanke hukuncin bawa iyayen Faisal turaki din dama su Turo zai aikawa dangin mahaifin AmatulMaleek din ko mutum biyu suzo.

*****Wannan hukuncin ya gigita kowa Banda mum Aisha datake Jin hankalinta na sake tashi matiqar Amatu Bata bar gidan ba batasan waye Kuma zai sake cewa Yana sontaba tinda kowa ya mutu akanta ana Neman shiga yaqi duk akanta sbd ko acan familyn Faisal din anata samun tashin hankali da matsala wasu basason ya aureta wasu Kuma Husnah sukeso hakama wasu na son ya hakura yabarwa Haydar Amma duk yaqi Dan haka aketa tashin hankali da Neman rarrabewan Kai.

Anan gidan ASH ma matsalarce Tako Ina Dan kuwa Haydar ya sake haukace musu,

Husnah kuwa Saida ta tabbatarda ta cirewa maamah so da shaawan auren Faisal din da AmatulMaleek dan haka takejin hankalinta na rabuwa biyu tsakanin Amatun da Husnah gameda auren.

Babban tashin hankalin da suka wayi gari dashi shine rantsuwar mahaifiyar Faisal akan Bata yarda ya auri Amatu ba idan ba Husnah ba.

Wanna shine karshen tashin hankalin da kowa ya shiga Daman Kuma dad dinsa ya rasu ummansa ce kawai.

Fasa auren shine babban bacin Rai da ASH ya samu a Dan lokacin Dan haka Shima ya Hana musu auren tasa ‘yar yakuma kashe maganar yabar qasar.

Faisal, AmatulMaleek, Husnah, maamah, Mum Aysha harma da Haydar Babu Wanda wannan hukuncin ba yiwa mummunan girgiza ba.

Lamarin yazo ne ya tafi tareda Bata kusan komai da wasu alaqar gidan Dan kuwa kusan kowa a cikin damuwa yake yanzu musamman Amatu da Faisal

Hakama Husnah da datasan tinda Dad dinta yace aa to tabbas bazaiyiba hakama itama idan ba Faisal dinba wlh bazata aura kowa ba.

Haydar kuwa Dad dinsa ya Yanke hukuncin ze bar gidan ya fasa barinsa qasar yayi karatu waje zai turasa bazai taba dawowaba sai ya kammala.

Wannan hukuncin ya sake jefe kowa cikin sanyin jiki da damuwa ga Faisal ya kasa rabuwa da AmatulMaleek Dan kuwa Shima bayajin zai iya auren a yanzu idan ba Amatun ba.

Haydar fadan nasa tashin hankalin bama zai yiyuba sbd Bai taba tinanin tafiya wata qasar karatu ba Kuma babu ranar dawowa a kusa Dan haka ya rikice ya ringa rokon Dad dinsa Amma Sam Babu ko sassauci daga Dad din.

*****

AmatulMaleek gaba Daya tayi sanyi sosai Takoma rayuwarta ta Baya ta kadaicewa da kame Kai sosai Sam idan ba makaranta zata ba bata ma fitowa sai gashi sunyi Hutu ma Bata zuwa koina

Faisal dinma ganin yanda Husnah take tsananin son nasa da gaske saita danne nata son ta hakura sbd a kwanakin ma Husnah din jinya takeyi sosai Bata Jin dadi rashin mahaifiyarta ya dawo mata sabo Dan kuwa da mahaifiyarsu na Nan zasu samu sauki da mafitar wannan hukuncin na Dad ga Haydar shima acikin mummunan hali bayason tafiya koina musamman jin bazai taba dawowa ba yanzu.

Ita kanta maamah Jin tayi komai ya fita kanta kaman ta kwashe nata ‘yayan takeji su koma inda suka fito sbd wannan fitinar ba lallai a Denataba idan ba tafiyar sukaiba,

Ba lallai Amatu ta samu Wani mijin a qanqanin lokacin Nan ba Tayi aure hakama ga Naufal bangare daya dasuke tsoron abinda zaije ya dawo.

***Ana saura kwana biyu Haydar ya tafi a ranar jikin Husnah din ya tsananta sosai Dan haka maamah a gurinta ta wuni hakama dole zata kwana tareda ita shiyasa yau Amatu tana sallan ishai taje ta sake dubota ta  dawo a natse ta koma dakinsu.

Ko data shiga dakin sake gyarasa tayi kafin ta kashe wuta ta tube ta shiga toilet wanka.

Bata jima ba Dan Koda Rana tayi Wani wankan yanzu dinma tayi ne sbd batajin karfin jikinta itama zazzabi ne yake damunta.

Bayan fitowarta kofar dakin tafara zuwa ta Saka key ta rufe tareda shafa Mai sama sama ta Dan fesa spray kadan a armpit nata ta dauko duguwar Rigar bacci me Dan tsayi da kauri ta Saka tareda socks me laushi.

Wayarta Dake caji ta kalla batareda ta daukoba ta hau gado ahankali tareda rufe Rabin jikinta da abin rufa ta rife idanuwanta ahankali tareda karanto addua tana sake rufe ido Jin kanta dayake mata nauyi.

Babu jimawa bacci ya dauketa me nauyi sbd ciwon kan datake fama dashi.

Karfe 2 da mintina na dare taji Wani irin sanyi na ratsa wuyanta zuwa cikin rigarta,

Motsawa tayi ahankali tareda kokarin juyawa Amma Hakan Bai samuba sakamakon Jin mutum a bayanta kwance matse da ita sosai.

Wani irin mummunan faduwa gabanta yayi baccin idanuwanta na sakinta take ta yunkura da karfin gaske zata Tashi sedai Hakan Bai samuba sakamakon mirginowa da yayi ya danneta gabaki dayanta tareda Sakar mata nauyinsa.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

19

********

Mummunan tashin hankali da zaucewa taji tana Neman yi sbd gaba Daya rikicewa tayi ta Bude idanuwanta da qarfi tana kokarin Bude Baki zata kurma ihu dukkanin jikinta n wata irin mummunan rawa ya rufe mata Baki da hannunsa Wanda Hakan ya Bata Daman yunqurowa da karfi ta taso Amma ya sake turata da karfi ya danne Yana Kai fuskarsa kan tata Kai tsaye Dan samun hade bakinsa da nata ko yawunta yafara lasowa yaji sanyi sanyi Dan kuwa yau Ayanda yakejinta a zuciyarsa idan ba samunta yayiba zai iya rasa ransa.

Kai fuskarsa ya hade da nata yasata dagowa da karfi tana Neman numfashi da bakinta zatayi ihu jikinta na rawa sosai hakama tini Wani irin mummunan zufa ya fara jiqata sbd Bata taba shiga matsananci Kuma mummunan tashin hankali me tattareda masifaffiyar tsoro irin wanna lokacinba,

Jijjiga tafara yi tana jujjuya fuskarta dayakeson hade bakinsa da nata

Dan haka a zalame yakai bakinsa nata tareda janye hannunsa daga bakin nata zai Dora nasa ta saki Wani ihu me qarfin Daya sakashi Sakar mata Wani mahaukacin Mari me qarfin gaske na bayan hannu daya Saka bakinta fashewa take hakama ya sake rufe bakin nata yana fara kokarin yawa rigarta cikin takaici da zalama tareda matsuwa da tsananin buqata.

Hannu ya Saka cikin rigar nata yana kokarin tabo kirjinta da babu bra a jikinta ta yanka masa Wani mugun cizo da hannunsa Daya tashe mata Baki take hannun ya fashe da jini sbd cizo ne na tsananin tashin hankali da firgici

 azabar da Bai taba ji ba ce ta ratsa qwaqwalwan kansa tana Neman gigitasa sakamakon mugun cizon dayake Jin ma kila ta cire masa tsokar tafin hannu Dan haka ya ware hannu a zafafe cikin rudewa ya sake falla mata Marika guda biyu dasuke dauke jinta gaba Daya tareda ganinta duk da Bata ganin komai dama sbd duhu.

Yarfe hannunsa ya fara yi Yana Jin zuciyarsa tagama kaiwa maqura

Kafin ta dawo hayyacinta daga marikan Daya faffala mata ya Saka hannu biyu da qarfi ya yaga rigar jikinta Yana kokarin shafata da hannunsa duka Amma azabar hannunn na Neman kasa riquwa

 shimuma bayajin zai tsaya Dan kuwa kusan duk ya qara fita hayyacinsa kota Yaya yau dai idan be sameta ba to kowama tsautsayin ze iya Hawa kansa Dan a mugun matse yake.

Kanta juyawa yakeyi sbd azabar marikansa Amma hakanan ta Yunkura ta turesa da qarfi Bata iya Bude bakinta sbd naushin Daya Sakar mata data sake budesa zatai ihu.

Da qarfin gaske ta turesa ya fado kasan gadon ta yunkura Bata Gani Hakan kanta na juyawa itam ta fado daga gadon tana kokarin miqewa ya tashi zai dafeta ta lalibo iron da Abdul yagama guga yabari a gurin da qarfi ta kwada masa Akai take goshinsa ya fashe da kansa ya Bude Baki ya Saki ihun azaba sedai Bai yarda ya saketaba

Jin jini na gangarowa daga goshinsa zuwa hancinsa da bakinsa ya sanyashi tabbatarda wlh bazai bartaba Dan haka bakinta ya ringa nusa da karfi batareda tinanin zamowarta mace,

Hannunta Daya da iron din yake ya murde da karfin gaske ya targada ta ya Saka fuskarsa gan yagaggiyar rigarta Yana lasa fatarta jikinsa na rawa Dan kusan duk ya jiqa kansa.

Hawaye masu tsakanin zafi da baqin cikin rayuwar data samu kanta takeyi tana ci gaba da turesa da Dan karfin Daya rage mata Dan kuwa mummunan dukan da ko Wani qaton bazai dauka ba yayi mata ganin tanada sauran karfin motsawa ya sakashi sake Sakar mata qarfi ya daketa sosai takai Bata iya motsi kafin ya zame mata rigar Yana kokarin cire wandonsa jikin na rawa

Dan motsawa tayi cikin tsananin azaba ta rashin kuzari ko kadan Dan kuwa daqyar take nufashi sbd daga bakinta har hancinta jini sukeyi sosai haka hannunta a targade yake.

Iron din ta sake lalabowa lokacinda yake gab da samun nasarar wulaqanta mata rayuwa tanaji Yana  lasa fatan jikinta ta daga iron din da Wani irin karfin hali ta sake qwala masa wannan Karan a gefen fuska ta gurin kunne take yaji Wani irin qarar datafi masa kama da boom acikin kunne da qarfin gaske ya sake qara kunnensa na daukewa hakam jini na fitowa da gudu baisan ya akaiba ya miqe tsaye Yana sake ihu da kansa tareda binta Yana harbi da qafa Yana cewa ta kashe masa dodon kunne ta kurmantasa.

Dukan dayake mata Yana ihu yasaka masu aikin kusa da dakin suka jiyo hayaniya hankali tashe suka fito sedai sunajin abinda yake faruwa Kai tsaye sashen mum Aisha suka nufa cikin saa fitowarta daga toilet kenan fitsari taji ana knocking kofarta ahankali tana budewa tagansu.

Da mamaki da takaici take kallansu tace

“Lafiya?”

“Sir Naufal ne a dakinsu Amatu yanata ihu……

Basu qarasaba mum Aisha ta katsesu zuciyarta na shiga tsoro da son kasa gasgatawa tace

“Wane Naufal din? Kuma wace Amatun?

Sake maimaita mata sukai ai Bata tsaya qarasa ji ba ta nufi hanyar dakinsu Amatun zufa na fara tsatsafo mata Dan kuwa idan da gaske ne Naufal yazama masifarta,qaddararta,asararta Kuma.

Koda suka Isa Kai tsaye mum Aisha ta karbi Wani key na dakin tana budewa wutar dakin tafara kunnawa abinda idanuwanta suka Gabar mata yasata sakin ihu me qarfin gaske tana ambatar sunansa.

Dagashi har Amatun kowannensu jini yake fitarwa hakama Amatun tini ta mutu Kokuma sumewa sbd irin Harbin dayake mata da dukan Daya mata

Shikuma gaba Daya goshinsa da kunnensa Jini sukeyi.

Mum Aysha hannu ta Dora Akai dukkanin jikinta na jijjiga da tashin hankali da tsoro tareda azabtaccen baqin cikin haihuwar Naufal.

Fizgoshi tayi a zafafe tareda fitowa dakin dashi ta nufi dakinsa dashi suna shiga ta sakesa tareda tsayawa gabansa da kyau kafin yayi Wani motsi ta saukar masa da lafiyayyun Marika guda biyu tana cewa

“Ka tsaya anan zan dawo kanka idan Kuma ‘yar mutane ta mutu wlh bani Bakai har abada tinda bakada dangan”.

Juyawa tayi ta fice daga dakin.

Ihun mum Aisha tin isowarta dakin da farko shine ya isa har dakin Husnah Wanda maamah ke kwance a kujera Amma Sam bacci ya kasa daukanta zuciyarta kwata kwata ba dadi Dan haka a kunnenta ihun ya sauka sbd akwai window me girman gaske Kuma dare ne sauti kadan Saiya Isa nesa.

Tashi tayi zaune tana Jin gabanta na sake faduwa.

Bata tsaya komaiba ta Bude dakin ta fito

Tana isowa tsakiyar babban palon Suma Abdul da Haydar na fitowa daga nasu dakin Dan sunji ihun hakama Suma Babu Wanda yake baccin kirki a kwanakin.

Kallansu maamah tayi batateda tace komaiba tayi gaba Suma da sauri suka mara mata Baya kowannensu tinanin Amatu ne yake ransu Allah yasa lfy.

Suna doso dakunan nasu suka hango mum Aisha na shigowa itama kusan a tare suka iso dakin suka shigo.

“Innalillahi wainna ilaihirrajiun”

Shine Kalmar da maamah ta ambata idanuwanta na Neman disashewa.

Abdulhameed kuwa da Shima take jikinsa ya dauki mazari da Wani Irin gudu ya qarasa ya fizgo zanin gado ya rufeta sdb wasu bangaren na jikinta Dake bayyane.

Mum Aysha ma rawar jikinta yakeyi hakama Haydar jijjiga jikinsa keyi.

Murya na rawa maamah ta Bude Baki jikinta ma kakkarwa tanason magna Amma maganar ta maqale sai kawai ta Yanke jiki ta zube a gurin.

Da gdu Haydar ya tareda mum Aisha ma da sauri ta riqota tana cewa Farida me aikinsu ta kawo ruwa da sauri.

Abdulhameed gaba Daya ganinsa daukewa yake Neman yi jikinsa rawa yake sosai ya qanqame Amatun Yana son tambayar abinda ya faru Amma zuciyarsa na tsananin tsoron abinda zaa fada masa.

Ruwa mum Aisha ta antayawa maamah masu yawa Amma Sam Babu alamar zata Tashi Dan haka suka qarasa rikicewa Haydar kuwa kuka ya fashe dashi sosai Yana yi agaban Amatu Abdul kuwa kan mamah ya dawo wadda take Neman barinsu a duniya.

Rikicewa mum Aisha tayi sbd idan maamah ta mutu ga AmatulMaleek dinma Kila ta mutu hukuncin zaiwa Naufal yawa Dan haka hankali tashe tasa Nemo key din mota da kanta zata ja dole haka suka kwashi maamah da AmatulMaleek zuwa asibiti bayan securities biyu sun bisu sbd tsaro.

Sun Isa asibitin aka karbi maamah aka qi karban Amatu Saida police Dan haka hankalin mum dana Kowa ya tashi da kuwa police na shigowa zancen yagama fita hakama shikenan Siyasar ASH ta lalace.

Hankalinta Bai sake tashi ba Saida suka tabbatarda Bazasu karbetaba Saida police bayan uban maqudan kudin data bayar Amma Sam sunqi sbd asibitin ta kudin gaske ce likitocinsuma kusan duk turawa da Yan India ne harma da Chinese Dan haka basa buqatan cin hanci komai yawansa.

Basuda zabi bayan kiran Faisal turaki dayake lawyer acikin tsakiyar daren sbd yazo ko zasu amsheta da nasa matsayin na jami’in sharia.

Zuwansa ya Tararda wannan mummunan kaddarar ga Amatunsa take shima ya yanke jiki ya Fadi Saida akai emergency dashi.

Zuwansa yasa aka amsa Amatun duk da Shima ya shiga Wani mummunan halin Dan haka su biyu shi da maamah aka kwantar lokaci bayan Amatun.

Haydar kuwa irin kukan dayake yi yasa gaba Daya kamanninsa suka sauya Dan kukane sosai Mai tattareda baqin Mai tsananin gaske.

Abdulhameed jajir idanuwansa sukai zuciyarsa gaba Daya ta qame da girman baqin mara ranar warkewa idan har anyi nasarar wulaqanta rayuwar ‘yar uwarsa.

Mum Aysha kuwa itadai fatanta Amatun Bata mutu ba sbd kada hukuncin kisa ya hau kan Naufal din,

Hakama tana fatan Bai Kai ga raping din Amatun ba.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

20

************

Asibiti take sukai filing matsalan Amatu akan rape gashi ba qaramin duka da azabtawa Tasha a hannun Wanda yaso raping din nata ba da kuwa fuskarta da jikinta koina shatin hannuwansa ne na Mari da naushi ga tashin hankali matsananci da tsoro sosai me hade da firgici Daya daketa sosai shiya qara tsananta yanayinta ta fice hayyacinta gaba Daya batasan waye yake kantaba.

Haydar da idanuwansa sukai jajir qurawa kofar dakin datake idanuwa yayi Yana Jin zuciyarsa bayan ci da wuta Babu abinda takeyi,

Abdulhameed Daman tinda suka zo asibin Bai iya qara dogon motsi ba zaune yake shiru idanuwansa jajir suna jiran tsakanin maamah da Amatun waye zai fara farkawa Dan kuwa idan har ansamu nasarar lalata rayuwar Amatu to zamansu TALBAs ya qare har abada sbd zuciya zata iya Kaisa ga aikata abinda zai janyo babbar matsalar da zata iya fin wannan.

Faisal ma kusan tasa zuciyar me rauni kasa dauka yayi Saida yafara tsiyayar hawayen baqin ciki idan har abinda suke Gani ya tabbata din Wani ya lalata masa rayuwar Amatunsa.

Mum Aysha kaida kawo takeyi zuciyarta itama kusan tafi ta kowa shiga tsalle da tsinkewa,

Batasan tayaya zata rufe Naufal daga wannan maganar Dan kuwa ana sanin shine yayi wannan aikin yagama yawo a gurin ASH hakama ga maamah na Neman rasa nata ran sanadin Hakan.

Tamkar zaman makokinda baa samu gawar ba sukeyi a kofar dakin emergency din asibitin Babu Wanda hannuwansa basa rawa da zuciyarsa hakama Yan mazan uku kowannensu idanuwansa tamkar an zuba masa borkono sbd jajir din dasukai.

Har Akai Kiran sallan asuba Babu Wani zance Saida sukaje sukai sallah suka dawo likita ya fito ya sanar musu Amatu anyi dressing raunikan Dake jikinta da fuskarta sedai sakamakon anyi mata fyaden ko baayi ba sai anjima idan babban lokitansu ya fito zai sanar musu,

Maamah kuwa jininta ne yayi mummunan Hawa tareda bugawan zuciya Wanda suke fatan idan zata farfado ta farko lafiya batareda matsalar dasuke gudu ba ta shanyewan jiki ba.

Wanna bayanin na likita ya Saka dukkaninsu shiga sabon tashin hankali da radadin zuciya Mai tsananin gaske Dan kuwa a matse suke kowannensu da Jin ko kaddadar ta faru ne da Amatun ko kuwa?

Haydar ne yafara juyowa ya Kalli mum data yi nesa dasu tana waya a hankali tana fadawa Naufal yafara Shirin barin gari sai komai ya lafa.

Daga Haydar har Abdul da Faisal Babu Wanda ba Naufal dinne a zuciyarsa ba Dan haka kowa da abinda zuciyarsa ke Saka masa.

Faisal ne yafara juyawa ya fice daga gurin yana Isa motarsa ya fada Bai tsaya komaiba ya tada motar yabar asibitin cikin mugun speed ko Gani sosai bayayi Allah ne kadai ke taredashi.

Haydar ma juyawa yayi zai fice Abdul ya rigasa juyawa ya fice Dan haka kusan tare suka fito a karo na farko rayuwarsu da suka hau motar haya.

A tare suka furta ASH TALBAs..

Babu me magana a cikinsu hakama Babu Wanda hannuwansa da zuciyarsa Bata rawa har suka Isa gidan.

Securities ne suka biya me motar su kuwa Kai tsaye ciki sukai Babu me Rahama ko sauki a fuskarsa.

Kai tsaye sashen masu aiki suka nufa suna Isa Abdul ne yafara cin karo da Farida tana ganinsa tayi Baya da sauri Bai tsaya komaiba ya shaqota cikin rawar da jikinsa keyi yanason tambayarta waye ya shigarwa Amatu Amma zuciyarsa ta rufe sai hawaye kawai matsu tsananin zafi suka gangaro masa jikinsa ma sake daukan rawa,

Haydar ne ya jefa mata tambayar Shima nasa Idanuwan na sake hada hawaye masu tsananin zafi.

Yanda jikinsu ke rawa da tsananin baqin ciki mara misali yasa Farida data shiga tashin hankali da tsoro ambatar sunan Naufal Wanda ya fito daga sashensa janye da qaramar luggage da jakar laptop dinsa da wata jakar zai nufi harabar gidan.

Haydar ne ya juya da sauri yabi bayansa daidai ya Isa bakin motarsa zai Bude motar Faisal na shigowa harabar gidan da Wani irin gudu.

Saurin Kai hannunsa Naufal yayi kan motarsa zai Bude daga bayansa yaji tahowa Yana juyowa Bai gama tantance waye ba yaji daukan Wani mummunan naushin Daya Sakasa yin baya ya fada jikin motarsa,

Haydar ne Wanda yafara Kai masa wannan naushin idanuwansa na rufewa sbd gaba Daya baa Dan uwansa Kuma yayansa yake kallansa a lokacin ba se rapist Wanda ya illata masa rayuwar macen dayake tsananin so rayuwarsa.

Abdulhameed na isowa a tare dashi da Faisal suka Sakar musu nasu naushin dasuka Saka bakinsa da hancinsa fashewa da jini a tare.

Acikinsu Babu Wanda idanuwansa Basu rufe ba da zuciyarsa da tsananin tiririn bacin Rai da zafin zuciya.

Husnah data Dan ji sauki ta fito cikin tsoro Jin hayaniya da ihun masu aiki na tashi

Hakama securities tini suka yo harabar gidan ganin abinda yake faruwa Dan kuwa duka ne su ukun sukewa Naufal kaman zasu rabasa da ransa duk da basuyi girma da shekarunsa ba Amma Suma karfinsu na samartaka ya Riga yazo gasu suna geamin a dakin geamin na Mai gidan Wanda Babu kalar kayan geamin da Babu a makeken geamin room din.

Shi kuwa Faisal ma kusan yafi Naufal din karfi Dan Shima sosai yake exercise na Bude jiki sh kuwa Naufal Neman mata da Hutu kawai yasani baisan ya motsa jikina bare building jikin nasa.

Kowannensu zuciyarsa tafasa takeyi me tsananin gaske Dan haka kusan basaji basa Gani.

Shigowar motar mum Aisha gidan Taga abinda yake faruwa ko parking batai ba ta kashe motar ta fito tana qarasawa da wuri tana cewa securities su futar da Faisal da Abdul a gidan tinda ba gidan ubansu bane zasu kashe make a ‘da ana kallo.

Dole securities suka ja Faisal  da Abdul da sai alokacin yake fashewa da kukan baqin Daya danne zuciyarsa tin tsakar Daren.

Securities ne suka fito da motar Faisal daga mansion din ya shiga tareda Abdul Dake kuka sosai suka bar anguwar kowa zuciyarsa na fadawa da rage baqin cikin dasukai.

Haydar kuwa Husnah ce ta qanqamesa tana fashewa da kuka cikin tsoron ganin yanda jikinsa ke rawa dakuma ganin tashin hankalin da Bata taba Gani ba ga shiga mummunan tsoron Jin abinda akaiwa Amatu a cikin gidan.

Mum kwasar Danta tayi jiki na rawa itama Tayo asibiti dashi Dan kuwa ba qaramar sa’arsa suka samu ba sun dakesa sosai ga illar da Amatun tai masa cikin dare.

Haydar ciki Husnah tai dashi har lokacin kuka takeyi sosai tana sake qanqamesa sbd Bata taba ganin fushinsa haka ba,jikinsa koina rawa yakeyi.

Isarsu mum Aisha asibiti Shima kusan Naufal din qin amsarsa Akai dataga Yana Neman mutuwa a banza dole ta sanar musu shine Wanda yayiwa Amatu abinda Akai mata hakama su Barr Faisal ne sukai masa wannan dukan Da wannan suka amshesa tafara kaida kawo cikin masifa da balai biyu da biyu.

Bata taba ganin baqar Rana irin wannan ba Dan kuwa ASH kawai take tinowa da zancen kowane lokaci zai isar masa Menene zai biyo Baya shine babban tashin hankalinta da masifarta.

Abdulhameed Faisal turaki gidansa ya Kaisa yayi jarimta da karfin halin danne nasa damuwa da dacin ran ya rarrashesa tareda basa qwarin gwiwan inshallah Babu abinda ma yafaru har tsawon lokaci suka samu zuciyoyinsu suka sauka kafin suka koma asibiti.

Koda suka Isa Husnah ta iso asibitin tareda Haydar hankalinta tashe Jin halinda maamah take ciki harma da tausayin Amatun.

Kallon tsanan da takaici harma da damuwa mum Aisha tayiwa Faisal turaki da Abdul din dasuka iso kofar dakin emergency da kusan duka su uku dakunansu na ciki Kuma baa buqatan kowa ya shiga.

Suma babu Wanda yace komai sai Husnah data Kalli Faisal cikin sanyi da kulawa tana tambayarsa idan Yana lafiya bayan tashin hankalin.

Gyada mata Kai kawai yayi Yana Dan kallanta cikin nutsuwa.

Abdul ta Maida kallanta akansa Shima kasa magana tai da idanuwa kawai ta masa alaman komai zai daidaita inshallah.

Wuni guda suke Neman yi a asibitin Babu Wanda aka samu kansa a su ukun Dan haka hankalinsu yafara tashi musamman akan maamah da AmatulMaleek.,

Basu sake shiga tashin hankali ba Saida yan jarida suka zagaye asibitin take aka juya labarin cewan

“Anyiwa ‘yar me aikin gidan ASH TALBA Dan takarar governor fyade tareda attempting na kasheta sbd zancen kada ya fita,hakama ana zargin ‘dansa na cikinsa da ‘dan yar uwarsa hakama uwar yarinyar ma na kwance Rai a hannun Allah.”

Wannan mummunan labarin ne ya girgiza gaba Daya jamaar gidan da duk Wani masoyin ASH TALBA ta bangaren siyasa harma da dangi sbd take aka girmamam abin cikin mummunan sigar danganta lamarin harda kisa.

ASH Baya qasar wannan mummunan labarin Mai Muni da girgiza zuciya ya samesa Dan haka take ya shirya dawowa Dan kuwa babbar masifa ta sauka a familynsa kenan.

Su kansu ‘yayansa dake asibitin Dole jamian tsaro sukazo aka zagaye asibitin sbd komai zai iya faruwa Dan kuwa mutane sosai suke Neman tada fitinar datafi karfinsu.

Husnah tsoro da tashin hankali ta shiga kamar yanda mum Aisha ta shiga nata tashin hankalin Mai tsananin gaske Dan haka ta fara shirye shiryen hadawa Naufal tafiya ya gudu kafin ASH Yadawo Idan komai ya lafa ya dawo Dan kuwa tasan wannan guguwar zaiyi wuya Bata Bata siyasar ASH ba da Daman bawai sonta yakeyiba gashi akan Hakan maganganun masu zafi da cin zarafi ke fitowa Tako Ina.

Abdulhameed ma tashi hankalinsa yayi tareda baqin cikin fitar zancen sbd duniya taji fyade akaiwa Amatu bayan likitan ya tabbatar musu da Bai samu damar yi mata fyaden ba.

Gaba Daya jin yayi garin da rayuwa acikin TALBAs din ta fita ransa

Rayuwar mutunci kawai yake yiwa yar uwarsa fata Dan wannan mummunan tabo ne Daya Riga ya taba rayuwarta.

Naufal ne yafara farfadowa cikin dare Kuma dayake anyi dressing raunikansa tareda allurai da ruwa na rage radadin da tsamin jiki

Da Dan damarsa ya tashi.

Mum na ganin Hakan Batai sanyaba a cikin Daren ta tserar dashi daga asibitin zayyan Mande Dake jiransu ya daukesa da motarsa suka bar garin Dan Shima yasan koma Menene Naufal ya aikata ranar akwai sunansa aciki tinda shine ya basa qwayar Daya sha din me qarfi.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

21

************

Washe gari Koda aka duba dakin Naufal bayanan ya tafiyarsa ga mum Aisha a gida ta kwana Babu Wanda yake tinanin tanada Saka hannu a tafiyar tasa ko sani Dan kwata kwata baa asibitin ta kwana ba.

Suna cikin wannan mamakin da baqin cikin maamah da Amatu suka farfado Suma Dan haka suka mayarda duk hankalinsu kansu Amatun.

Amatu tinda ta farfado bayan kuka Babu abinda takeyi zuciyarta nauyi take mata sosai musamman mummunan labarin dasuka tadda ya gama zagaya koina.

Maamah ma kukan zuciya takeyi me tsananin ciwo da radadin zuci,

Wannan shine karo na farko dataji Babu inda take buqata da so bayan kebancewa daga wannan duniyar ta masu kudi,

Rayuwar Amatu ta samu tabo me wuyan warkewa duk da baayi mata fyaden ba Amma duniyar daukakan Wanda suke qarqashinsa ta qarasa lalata sauran mutuncin Daya ragewa Amatun tinda gashinan koina an gama watsawa mummunan fyade Akai mata.

Kuka da Hana kowa kusanto inda take yasaka yanayinta sake tsananta tanajin komai da kowa Bata son Gani ko kasancewa dashi.

Maamah ce kawai ke iya rabarta ta rarrasheta duk da itama tata zuciyar quna takeyi tana yanka da azabar qunci da baqin ciki.

Mum Aysha datazo tashin hankalin rashin ganin Danta kawai tayi ta gama masifarta ta juya Takoma gida tana jiran ta inda zasu fuskanci fushi da bacin ran ASH Wanda kusan koina yanzu abinda ya faru din aketa magana wasu na cewa bazasu zabesa ba tinda a gidansa ba Babu adalci ga masu aikinsa bare Al’umma.

Abdul da su Haydar na cikin damuwa da sanyin jiki Mai tsanani na ganin halinda Amatu take ciki da yanda maamah ta kasa cewa komai har lokacin.

Maamah aka fara sallama kafin aka sallami Amatu wadda ta batajin zata iya komawa gidan gaba Daya.

Ita kanta maamah ta Yanke hukuncin bazata iya komawa gidan ba sai Kuma ga Kiran kawu bello da Babu labaran Daya shafi ASH TALBA da basa bi Dan sanin sunada alaqa da gidansa tinda Asmau na can da ‘yayanta dasukaci buri da jiran su zama Wani abin a duniya su fito suce sune dangin mahaifinsu.

Samun wannan mummunan labarin ya girgiza su sosai Dan sun dauka iya irin gidajensu irin wannan yake faruwa sai gashi har gidan masu taka Naira ma Yana faruwa Dan haka kwadayin Asmau ya qare ta dawo gida kawai.

Irin zagi da cin mutuncin da kawu sukai mata a waya tareda gori masu tsananin nauyi ya Saka zuciyarta ta kasa dauka ciwon zuciya na Neman kasheta cikin sanyi Dan haka hankalin Abdul ya sake tashi ya ringa rokon Amatu data sassautawa kanta ko maamah din zata sassautawa tata zuciyar.

Daga asibitin maamah ta Yanke hukuncin tafiya su koma kauye gaba Daya,

Wannan hukuncin na maamah shine ya girgiza duniyar Husnah Dake cikin tsananin tsaka me wuya sbd a Daren Haydar jirginsa ze tashi hakama idan maamah ta tafi tabarta zata iya haukacewa a rashin maamah da Haydar din lokaci Daya Dan haka ta haukace cikin tsananin tashin hankali da kukan rokon kada maamah tabarta rayuwarta zata lalace.

Shi kansa Haydar yashiga damuwa sosai ta halinda Husnah ma zata shiga duk da zuciyarsa sai ta Wani bangaren take samun nutsuwar Amatu ta koma kauye Dan acan zatafi zama safe daga Maza ma gaba Daya har lokacin dawowansa to Amma Kuma Husnah tini ta rikice gwanin tausayi tana rokon kowa kada a tafi a barta ita Daya.

Zuciyar maamah tariga ta Yanke hukuncin tafiya duk da zuciyarta na yanka sosai da ganin halinda Husnah tashiga na fita hayyaci kaman zata zauce Amma batajin zata zauna gasu kawu sunyi rantsuwar saita dawo da AmatulMaleek kauye idan ita bazata dawo ba saisu Amatu sun dawo.,

To idan ta bar Amatu suka koma ita tana nan batasan mezai faruba acan Dan kusan duk abu Daya ne suke tsoro da can da Nan din.

Haydar da zai wuce tin yamma yake asibitin tareda Amatun wadda itama adaidai wannan Gabar kukan rabuwar dashi takeyi Dan kuwa tabbas da Haydar ya Isa auren shi zata aura zuciyarta tafi nutsuwa dashi a aynzu fiyeda kowanne namiji a duniya.

Kuka takeyi sosai Yana rarrashinta kamar zaiyi kukan Shima.

Husnah kuwa har airport ta rakasa tareda Faisal Wanda dole Saiya kula da ita Dan tana cikin wani mummunan hali na kadaici da gariri yanzu.

Qanqame Haydar tayi tana kuka sosai kaman shine yayanta itace kanwarsa,

Shi kansa hawayen yakeyi sosai yake tausayinta Dana kansa duk da tareda Jameel zasuyi tafiyan sbd yariga Dad dinsu isowa.

Husnah Jin takeyi kaman tabi ‘dan uwanta su tafi duk inda zasu tare Amma ba Daman Hakan tayi kuka sosai Wanda yasaka dole tausayinta cika zuciyan Faisal haka ya lallabota suka dawo gida kafin da safe tasake komawa asibiti ta Hana maamah tafiya Dan bazata iya rayuwa babu maamah dinba Babu Haydar Babu mahaifiyarta da tini ta barsu.

Faisal ma daga mansion din gidansa ya wuce sbd dare yayi Saida safe ya koma asibitin.

********karfe Biyar na asuba su mamah suka Isa Tasha daga asibitin bayan Abdul yaje da kansa ya tattaro kayansu da duk abubuwansu da zasu iya tafiya dasu.

Maamah Bata sanar da Husnah ba sbd kaucewa tashin hankalin da zata shiga ita Kuma mum Aisha Daman itace ma da kanta ta sake tsayawa akan tafiyar tasu duk da Basu ce mata komaiba kaman yanda Bata ce musu komaiba gameda abinda Naufal din yayi.

Cikin saa Basu Wani jima ba karfe 6 na safe motarsu ta tashi Babu me walwala a cikinsu hakama Babu me magana suka dauka hanyar tafita me Nisa.

Husnah kuwa lokacinda taje asibiti tinda safe karfe 7 ta Tararda sun wuce sakewa jikinta yayi ta zubewa Faisal da Shima isowansa kenan.

Tashin hankali me tsananin gaske ta shiga da Bata gane komai bayan kawai dawowan maamah gareta kota halin Yaya.

Babban tashin sa’ar da aka samu da sabani shine a ranar ASH ya sauka kasar,

Securities masu yawa suka tarbosa sbd yanda Yan media suka cika suna jefa tambayoyinsu akan abinda ya faru Baya qasar dakuma mataki da adalcin da zaa yiwa me aikinsa wadda akace ‘yar uwar matarsa ce da ‘yarta.

Ganinsa yanda ya kamata Yan media din basuyiba sbd tsananin tsaro da yawan securities dinsa harya shige mota Babu inda ya kalla bare Saka ran tankawarsa hakama kwarjinsa ya hanasu jefa wasu tambayoyin da sukaso.

Koda ya iso Mansion din Daman tini aka qara securities Dan haka Babu Yan jaridu ko a anguwar.

Bangarensa Kai tsaye ya nufa sai kusan bayan awa Daya ya fito cikin wasu kayan daban Dake nuni da yayi wanka.

Kofar palonsa da zata sadasa da Babban palon iyalinsa ya nufa ya fito palon dayake tsit Babu motsin kowa sai AC da qamshin gyaran da Akai Dake tashi.

Kai tsaye dakin Husnah ya nufa wadda ke kwance a dakin ita Daya Babu kowa shiru.

So Daya yayi knocking tareda Murda kofar ya Kalli cikin dakin yaganta kwance a qasan tiles sbd ba zuciyarta kadai ke Mata radadi da zafi ba hatta gangar jikinta da jininta Jin takeyi suna mata zafi sosai.

Lumshe idanuwansa masu haske sosai yayi ahankali tareda Jin zuciyarsa na yanka ya Tako a natse ya nufota cikeda tausayi da tsananin so da kauna irin na Uba da ‘yarsa.

Idanuwanta Dake rife ta Bude ahankali batareda ta motsa ba Jin motsin mutum.

A fafaren qafafuwan datasan Babu me  irinsu a gidan idan ba Dad dinta ba Idanuwanta suka fara sauka ta motsa ahankali tareda yunkurawa ta tashi zaune idanuwanta suka sauka akan fuskar Dad din da shi kansa idanuwansa sun Dan fada sbd damuwar yayansa da akaita wannan tashin hankalin bayanan Dan haka yayi alqawarin daga wannan Karan bazai qara tafiya yabarsu a irin wannan rayuwarba zai zauna ya kula da yaransa da kyau tareda inganta rayuwarsu da kansa dakuma taimakon Asmau da kokarinta da bata gajiyawa.

Husnah kasa cewa komai tayi ganinsa bayan hawaye masu tsananin gudu da suka balle mata Kai tsaye abinda tafara Bude Baki ta furta kuka na tsinke mata shine

“Dad muna buqatan Mum kowace iri ce koba mum dinmu ba”

“Dad I can’t live like this,

Dad ka dawo min da maamah,

Dad Ina tsoron kadaice,

Dad maamah ta tafiyarta ta barni,

Haydar ya tafi,

Banda kowa,

Mum Aysha Bata zama,

Banda kowa,

Ina son maamah ta dawo,

Dad Dan Allah kayi aure ko zan samu wadda zata zauna damu batareda tace zata tafiyarta ba kaman Maamah……kuka ne me karfin gaske yazo mata ta soka kanta cikin qafafunta tana Jin tsanani kewan mahaifiyarta ayau fiyeda kullum.

Shi kansa kasa cewa komai yayi ya qaraso a hankali kafin yayi magana ta fada jikinsa tana sake fashewa da Wani kukan sosai zuciyarta na Susa batareda kowa yasan irin radadin datake ji ba Dan kadaici tsananin tsoro da firgici yake Sakata.

Kasa magana Dad din yayi sai Jin dayayi tinaninsa Shima ya tsaya cak da Jin Maamah ta tafiyarta,

Tabarsa da yayansa itama kenan..

Jin yayi kansa ya Sara Dan kuwa komai Yama wuce yanda yake tinani kenan tinda maamah ta tafi to tabbas abin ya girmama.

Kukan da Husnah takeyi sosai Yana shafa bayanta cikin lallashi da kauna me karfi batareda yayi magana ba Dan idan ransa yayi mummunan Baci Baya iya furta ko Kalma Daya shiru yakeyi sedai aga hukuncinsa data Baya.

Ciwo ne me qarfin gaske na zazzabi ya rufe Husnah dole ya kira asibiti aka Aiko likita da nurse wadda zata kula da ita sosai sbd mum Aisha itama a ranar ta silale tayi tafiyar kwana buyi kafin ASH ya Dan huce Dan tasan akwai babbar masifa a kwance.

Kasa rintsewa ASH yayi a Daren Shima sbd kusan a qanqanin lokaci Naufal ya wargaza masa gidansa da rayuwar yarda harma da yar Asmau,

Kewan Abeeda ce Shima ta dawo masa sabuwa Dan kuwa ya tabbatarda harda rashin matarsa ya Sakasa cikin wannan halin Shida yayansa.

Husnah jikinta yaqi sauki gaba Daya ta daga hankalinta ta daga na Dad din akan dawowan maamah Dan tasan idan bata daga hankalinsa sosai ba bazaa dawo mata da maamah da wuri ba,

Shi kansa baida niyar Bata lokaci batareda yaje da kansa ya dawo da Asmau ba sbd Bata adalcin datake buqata itada AmatulMaleek din bisa ga abinda akaiwa Amatu hakama a ayanzu da babu kowa mansion din sai Yan aiki Husnah na tsananin buqatan maamah da mutane a tareda ita.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

22

***************

Shirin tafiya kauyensu maamah da kansa yayi a karo na farko rayuwarsa dazai tafi Dan dawowa da ita sbd zai iya rasa yarsa matiqar Asmau Bata dawo ba hakama Yana buqatan yin adalci a lamarin da Naufal ya aikata sbd bazai dawoba alqawari ne ya dauka Saiya daurowa Amatun aure da Naufal idan har Hakan zai rage ciwo da baqin cikin abinda Naufal din yayi.

Husnah dataji tafiyar ta Dad Jin tayi bazata iya daurewa baa tafi da itaba Dan haka ta daure ta samu karfi a tafi da ita zata roki maamah,zatayi mata kuka ta taimaki rayuwarta su dawo Dan zata iya shiga Wani halin daga ita har Dad dinta dashima yake cikin tsananin damuwa yabarwa zuciyarsa ne kawai Amma Shima Yana buqatan macen da zata kula dashi Amma tsananin son Mum dinsu ya hanasa iya kallan kowacce macen bare yayi tinanin qara Wani auren musamman mum dinsu nata kishi me girma a kansa tayaya zata karbi mijinta yayi aure duk ranarda ta tashi.

Faisal da baisan zasuyi tafiyarba Shima Shirin tafiyar yayi harma ya rigasu wucewa.

Dangin mahaifin Naufal ASH ya kira Kai tsaye ya sanar dasu hukuncinsa akan abinda ya faru din Suma Kai tsaye suka amince da maganar auren Dan haka su uku suka yanke shawarar biyo bayan ASH zuwa kauyen idan ankai karshe zaa dauro auren su dawo.

Mum Aisha a bakin kawun Naufal din takejin zancen auren batasan tafara hada kayanta ta dawo Abujan ba hankali a matsanancin tashe Dan kuwa idan aka daurawa Naufal aure da Amatu wlh angama cutatarda ita da duk burinta ita da ‘danta hakama a rasa wadda zaa daurawa Naufal din aure da ita sai Amatun bayan fyaden ma da aketa tashin hankalin anyi beyiba to Menene na daura masa aure da ita.

Shi kansa Naufal din ba kunya ya tattara yafara Shirin dawowa Dan Shima wlh baitaba shirin aureba yanzu Amma idan har andage akan daura masa aure da Amatun to zai amince Kodan ya mayarda yawunsa da ran Daya qwallafa akanta.

Mum Aisha najin abinda ya fada din na idan sun nace ta bari a dauka auren kawai tasan abinda yake nufi da Hakan

Wani mugun baqin cikinsa da takaicinsa ne ya Sakata jefa masa Wani mugun zagi tana cewa

“Kenan haryanxu baka dawo hankalinka ba,

Wai uban me ne Amatun take dashi da matan duniya basuda shi da haryanxu tsinannen abinda kake ji din Bai sauka ba?

Wlh tallahi bazaka aureta ba,

Ko an daura auren saika ana kawota saika mata saki uku,

Kwadayinka bazai taba bari kaga abinda yake gabanka ba,

Me zakayi da Amatun?

Yarinyar da uwarta take wankewa taka uwar toilet?

Yarinyar da sukewa gidanku bauta zaka nacewa sbd masifaffiyar jaraba.

Baqin cikin yawa yayi mata ta saki Wani mummunan tsoki tana kashe wayarta tareda kashewama gaba Daya sbd tayiwa ASH kira yafi ashirin Amma Baa dauki ko Daya ba karshe ma a kashe taji wayar Dan haka ta matsu ta iso Abuja kafin ASH din su wuce kauyen.

******Su maamah tinda suka iso kauyen a ranarda suka dawo

Da yamma suka dauka Dan haka Koda suka iso gida har anfara Kiran sallan magrib a masallatai.

Da kawu bello suka fara cin karo a kofar gida tareda kawu ashiru

Da kallo suka bisu kowa zuciyarsa a wuya da Asmaun,

Ta kwashi Yara sunje yawon kwadayi gidan masu abinda duniya gashinan Babu abinda suka tsinto sai mummunan tozarci Wanda aka gudu Dan kada ‘yayansu su da ake gujewa gashinan Wani a banza ya samu ya farke mata mutunci.

Dayake kawu ashiru yafi fushi da zafi ko gaisuwar asmaun Bai amsaba bare tasu Abdul Wanda yasan Daman ba qaramin tozarcin zasu tararba anan din.

Kawu bello ne kawai ya amsasu Shima Yana bin kayansu da mugun kallon takaici da baqin ciki.

Ciki sukai mutanen gidan kusan kowa nata fitowa ana musu sannu da dawowa wasu Kuma Amatun kawai suke kallo cikeda manufofi da tarin gulma a zuciyarsu,

Wasu kuwa Kai tsaye suke nuna sunsan abinda yasa suka dawo din.

Basuda gurin sauka ma kaman baya dole dakin inna lami suka nufa Wanda yagama mutuwa sbd rashin gyara da tarin kayan Dake cikinsa ga Kuma Yara da Yan mata kusan dai dakin ko sabulun wankanka baka ajiyewa minti Daya zuwa biyar yayi yawa an dauke.

Dayake zuciyoyinsu da hankalinsu acikin damuwa me girma suke Babu Wanda ya damu da yanda dakin yake haka suka Dan gyara suka samu inda suka ajiye nasu akwatinan da ko da ganinsu kasan masu tsadan gaske ne.

Sallah sukai suna sake amsa gaisuwar masu leqowa yi musu barka da dawowa harda abinci aka kawo musu daga sashen amaryar kawu bello Amatu dai Bataci ba hakama maamah daurewa tayi ta tura sbd kaucewa abin magana da zaa gara sakosu gaba dashi suna fama da kansu.

Abdulhameed a waje yaje yasha shayi a gurin me shayin kauyen ya dawo gida tareda shigowa ya dauki kayan bacci da abin rufa daga kayansu ya nufi dakin samarin gidan da warin qatti yagama kame iskar dakin da yanda Babu yanda za’a yi a iya fidda warin Se babban gyara.

Hakanan ya daure Yana dauke numfashinsa ya kwanta cikinsu daga bakin kofar dakin Dan idan yayi ciki da yawa zai iya rasa numfashinsa.

Su maamah acan cikin gida haka sukai kwanan hakuri da damuwa Amma Kuma dole su sabawa kansu tinda sun dawo rayuwar da itace tasu Daman.

Da asuba su kadai ne suka tashi sallah kusan Yan gidan kaf basa tashi sallan asuba sai gari yayi haske suke fitowa ba kunya ba tsoron Allah suke sallah.

Dan haka daga maamah Se Amatu da Abdul din sukai sallah da asuba

Bayan gamawarsu Babu Wanda ya koma bacci Dan Daman Basu Wani samu yin baccinba dole sai ahankali Kuma yanzu zasu Saba da Nan din.

Da safe still anbasu abincin Karin kumallo Hakan dukkaninsu suka daure suka ci sbd fada da kawu bello keyi akan ai bazasu iya cin abincin gidan ba tinda a gidan the grt ASH TALBA suke rayuwa komai na aljannar duniya akwai acan din.

Koda sukai Karin Babu Wanda ya sake bi ta kansu tinda angama musu sannu da zuwa hakama tini samari da matasan gidan suka sauke idanuwansu akan Amatu datake tamkar an kwana qwai da Madara tsaban kyan fata da kyau me sunan kyau da nutsuwa,

Masu aure da marasa auren tini suka fara fitarda maganar su zasu aminta su auretan duk da abinda akayo mata a birnin zasuyi jahadi.

Bayyanar wannan zancen ya daga hankalin maamah da Abdul

Ita Amatu gaba Daya a yanzu Jin takeyi ai rayuwarta tagama mutuwane daga lokacinda Naufal yayi yunqurin yi mata wannan fyaden Kuma har duniya ta sani Babu abinda y rage mata Dan tasan kowama cewa zeyi zai aureta Dan ya taimaka ya rufa mata asiri.

Kawu bello da kawu ashiru harma da sauran qannen mahaifinsu Amatun zauna sukai da maamah sukai mata tatas da maganganu masu tsananin ciwo da radadi a zuci Wanda ya Sakata kukan da Bata taba yi arayuwartaba tin bayan rasuwar Babah sai yau daga qarshe Kuma suka yanke hukuncin daura Amatun aure a satin da Daya daga cikin yaran gidan tinda Babu abinda zasu ajeta a gidan tayi hakama kowa na kallansu da abinda ya farun gwara su aurar da ita a huta.

Wannan shine Mafi girman tashin hankalin da maamah ta shiga a rayuwarta bayan fyaden da aka kusa yiwa Amatun,

Tayaya zasu aurar da Amatu ga yaran gidan da ko Yan uwansu dasuke daki Daya dasu suna iya bibiya tinda gidan taro ne kusan sunayen ma da ake sakawa Yaya sun kusa qarewa.

Kukan da maamah Bata taba yiba a rayuwa shine a cikin kwana biyun da dawowansu takeci kowannen dare ta kwanta,

Ita kanta Amatun batasan me zatai ba sbd zuciyarta tagama daskarewa da Wani irin girmamman tashin hankali da tsoro.

Abdulhameed ma a cikin tashin hankalin yake Yan Jin inama yanada karfin arzikin dauke uwartasu da yar uwarsa subar garin gaba Daya suje Wani gurin suyi rayuwa Amma Sam Shima Yana cikin tashin hankalin wannan auren da ake shirin daurawa Amatu.

A cikin gidan ta bangaren Wanda ma zaa bawa Amatun fada ne ya barke sosai Dan kuwa masu matan da samarin kowa yace yanaso hakama kowa yace bazai hakura ya barwa Wani ba dan haka aka kasa tsayar da mijin ga lokacin da kawu yayi rantsuwar ya Yanke Yanata cikewa.

Kwanansu biyar da dawowa saiga Faisal kamar a mafarki ya dira kauyen cikin tausayi Dan duk ya gama jigata da Nisan tafiyar.

Mamakin zuwansa dukkaninsu kamasu yayi musamman Amatu wadda ta yanke Rahama da sake ganin kowa daga Abujan.

Shi kansa Faisal yashiga mamakin ganin inda suka yanke shawarar dawowa suyi rayuwa ta dindindin.

Abdul ne dole yaje gidan uzaifa daya gama ginawa Tim kafin zuwansu na qasa Wanda aciki zai Saka Amatu idan shi aka bawa ya gyara tareda siyan sabuwar tabarma ya shimfama masa acan ya saukesa.

Ba wata wata zazzabi ya kwantar da Faisal din sbd shine ya janyo motarsa Tim daga Abuja din.

Abdul tareda Faisal ya kwana a gidan Yana kulawa dashi Dan zazzabi me karfin gaske ne ya kamasa sbd Shima Bai Saba da wahala ba.

Washe gari bayan Faisal din yaji sauki yadan warware ya sake zuwa suka gaisa da maamah dasu kawu da basusan waye Faisal din ba kafin a shiga zancen daya kawo Faisal din saiga isowar motacin ASH TALBA da securities dinsa duk da ba masu yawa bane tinda flight suka biyo

Sai motar iyayen Naufal Dake bayan nasa motocin.

Kaf jamaar Dake kauyen idan aka cire su maamah da Faisal Babu Wanda ya taba ganin motacin da suka kawo ASH din Dan kuwa motaci ne dasuke shiga dashi matsu tsadar gaske duk da babu hanyar mota a kauyen sai gasu har cikin kauyen da motacinsu har gaban gidan zuraiar Sanda Fulde.

Maamah batai mamakin zuwan ASH ba sbd tasan bazai taba barinta da yayanta su wulaqanta ba su tozarta Amma zuwansa da iyayen Naufal shine ya Sakata cikin Mafi girman tsoro da mamaki sbd tasan dole da niyar Wani abin sukazo Wanda take da tabbacin idan aure ne bazata taba iya barin AmatulMaleek ta auri Naufal ba Dan haka ta zabi zaman kauyen har tsufa da mutuwarta da Naufal ya auri Amatu.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

************

Cikin girmamawa da rawar jiki kaman zasuyi masa sujjada su kawu da manyan gidan gaba daya suka tarbi ASH TALBA ana masa barka da zuwa Dan haka tini Akai shimfidu na alfarma a babban kofar gidan Dan gidansu na cikin manyan gidajen kauyen.

Husnah cikin gida Abdul yayi da ita gurinsu maamah ta fada jikin Maamah ta qanqameta tana ko gaisawa basuyiba ta fara furta mata maamah Dan Allah ki bini mu koma bazan iya rayuwa ni kadaiba.

Numfashi me sanyi maamah ta sake ahankali tareda Dan sake rungume Husnah din tana Jin kewan Abeeda ita kanta sbd harda rashinta duk ya sakasu a wannan tsaka me wuyar tinanin abinda zasuyi.

AmatulMaleek dai na gefe tana yanka kayan miyan da za’a yiwa Faisal abinci dasu sbd bazai iya cin abincin gidanba sun sani ko tinawa da ita Husnah bayayi ba sbd Daman ita sbd maamah tazo Kuma komawan maamah dince burinta da nutsuwarta.

Ahankali Amatun ta Bude Baki tai mata barka da zuwa Wanda sai alokacin Husnah ta juyo ta amsa tareda kallan aikin da Amatun keyi sai alokacin tafara kallan gidan da inda suke cikin mamaki da rashin tauna zance da Bata iya ba tsoron gidan na Dan kamata Kai tsaye tace

“Maamah anan kika dawo kuyi rayuwa?

Tayaya kuka iya kwanaki anan?

Maamah bazan iya kwana anan ba tsoro nakeji Dan Allah mu koma yau.

Wani murmushin yaqe Maamah ta saki batareda ta iya cewa komaiba Dan kuwa Suma sunsan rayuwa anan din zata musu wuya kafin su Saba Amma Hakan yafi mata Dan matiqar suna can din AmatulMaleek na cikin hadarin Naufal.

AmatulMaleek dai na jinsu Bata iya cewa komaiba sbd tasan tata rayuwar Kwanciyar hankalin tazo karshe daga ranar da abinda ya faru din ya faru sbd batajin Koda maamah zata koma su kawu su bari ta tafi da ita,auren dasuka rufe ido sukai Niya shi zaayi mata Wanda ita kanta maamah tasan Hakan Dan haka take cikin matsanancin tashin hankalin Dan kuwa tasan qunci da damuwa me tsananin gaske tana daskare a zuciyar Amatu Amma Bata iya fadaba sbd zuciyar ta riga tayi nauyin da bama zata iya fadan ba.

Abdul zuwan ASH TALBA ba qaramin farin ciki ya Sakasa ba Dan zai iya Hana auren da akeson yiwa Amatu na rashin daraja da Kash rayuwa,tinda su kawun sun rantsuwa ga Faisal Nan Allah ya kawosa a daura dashi.

Ita kanta maamah abinda take fata kenan tinda sun rantse kodai ASH ya rokesu a fidda musu hatsin rantsuwar Kokuma ya amince a daura da Faisal duk da tashin hankalin Daya faru to Amma Kuma tanajin Husnah idan aka daura da Faisal zata iya shiga mummunan hali sbd mental health dinta Kuma tayi alqawarin bazata taba yin abinda zai cutatar da Daya daga cikin Amatun da Husnah ba sbd matsayinsu dayake Daya a gurinta shiyasa ma Tintini auren Faisal da Amatun ya fita ranta Amma ayau suna cikin tsaka me wuyar fita.

Acan kofar gida bayan angama gaisawa da barka barka maamah ASH  ya buqaci Gani sbd magana da ita kafin komai.

Jiki na rawa kawu ya nufi cikin gidan kaman zai kife sbd rawar jiki da gaggawa.

ASH Kuma gidan uzaifa Dake maqale da Gidan aka Isa dashi har kan sabuwar tabarmar dake shimfide ta Barr Faisal.

Maamah tsayawa Kawu yayi akanta Yana tayi sauri Maza Maza me girma ASH TALBA na son ganinta yanzu.

Mayafi ta sauya babba akan Riga da zanin jikinta fuskarta tayi mummunan fadawa sbd damuwa data gama cinye zuciyarta da Kwanciyar hankalinta.

Dayake akwai kofar dazata shigar Dake tsakar gidan uzaifan ta cikin gidan Dan kusan ma a hade gidan yake kawai dai shi yayi wata kofar ne ta waje Dan yanason kebe kansa da amaryarsa, ta Nan sukabi tana tafe Husnah na bayanta kaman qaramar yarinya Dan qasar gidan ma Jin takeyi tana tsoron takawa Dan koina gidan ba Wani kyan Gani.

Suna shigowa madaidacin tsakar gidan Yana zaune kan tabarma gabaki daya qamshinsa ya cike iskar gidan har can cikin gidansu iska ke Kai qamshinsa duk Yan gidan suka rude da son ganin me girma ASH TALBA da aketa fada a redion kawu bello tinda gwamnan jaharsu zaiyi.

Kallo daya maamah tayi masa ta kasa tareda sauke idanuwanta daga kansa kaman yanda ta Saba Bata iya kallansa ko a bayan sbd kwarjinsa da tsananin haiba.

A mutunce ta qaraso tayi gefe Daya inda aka shimfida wata tabarmar bayan wadda yake Kai shi Daya ta zauna cikin sanyi ta Bude Baki ta gaidasa tareda masa barka da zuwa.

Shiru yayi na mintina kafin ya Bude Baki Bai kawo mata zancen tahowar datayi batareda ta jira dawowansa ba yayi mata uzurin tashiga Wani hali ne Mai wuyar tsayawa kayi tinanin Daya kamata Dan haka bazai dawo da zancen ba Kai tsaye hakuri ya Bata akan abinda ya farun Dan shi kansa Baya kaunar dawo da zancen dayake kamar tabon baqin ciki ne ga kowa na abinda yakusan faruwan.

Yana gama Bata hakuri ya Dora mata da zancen auren Naufal da zasu daura da AmatulMaleek tareda komawarsu ayau din duk gaba Daya.

Ba maamah ba hatta Husnah shock ta shiga sbd tasan maganar aurawa Naufal Amatu zai lalata maganar komawan maamah taredasu.

Da sauri ta kalli maamah idanuwanta na cikowa da hawaye masu tsananin dumi da tashin hankali batareda ta Saka Baki a maganar ba Dad din dayake gurin Kuma shiga zancensa idan bashine ya baka dama ba.

Ita kanta maamah din wasu hawaye ne suka tsinke mata wanda ya Saka ASH dauke kansa sbd ganin Kai tsaye alama ce da Bata aminta da Hakan ba.

Zai sake magana a karon farko a rayuwarta data fasa kuka a gabansa mara sauti sosai sbd baqin cikin dayake ranta yayi mata yawa batasan Yaya zatai da rayuwartaba.

Husnah ma kukan ta fashe dashi tana rarrafawa gurin Dad din cikin tsananin kuka tana cewa

“Dad Dan Allah maamah batason yaya Naufal ya auri AmatulMaleek,

Dad Yaya Naufal bayada halin kirji ko Daya wlh,

Babu ranarda ya kwana a gida tinda ya dawo kwanakin dayake yi a gida a kirge suke……

Abdulhameed Daya shigo sbd tashin hankalin Daya barke acan waje ma akan maganar Neman auren Naufal da AmatulMaleek su kawu sun buga hannu a qasa sunce Basu amince ba bare da Faisal cikin tashin hankali ya zayyano halayen Naufal din Babu na arziki hakama su kawu na Jin shine yayiwa Amatun qaramar kisa da fyade Dan haka wlh sun gwammaci bawa yayansu ayita ta qare kowa ya huta.

Faisal na Jin Hakan ya bayyanar da kansa Shima tareda bayyanarda manufarsa ta zuwa Shima take acikin iyayen Wasu sukace Shima ai sun tozartasu akan aurensa da Amatun Baya.

Rikici da hayaniya ce suka kaure a waje kawu bello ne kawai ya tsaya akan idan ASH TALBA yace Naufal zaa daurawa to wlh shi zaa daurawa Dan haka sauran Yan uwa sukai kansa Shima.

Abdulhameed ne ya sanar da ASH abinda yake faruwa a wajen Wanda dole ya Bada umarnin aka shigo cikin gidan uzaifa sbd sirrinta abin.

Bayan shigowarsu ganin irin kukan da maamah keyi yasa zuciyoyin kowa harziqa kawu bello ya kalleta Yana cewa

“Kuka kikeyi Asmau sbd zaa rufa Miki asiri a aurar Miki da ‘ya bayan abinda  yafaru?

Kawu ashiru ransa yagama Baci har Wani zafin kunnuwa yake ji sbd takaici yace

“Kuka kikeyi zaa bawa ‘yayanmu aurenta ko kuwa Dan zaa daurawa Wanda ya lalatota din ita?

Asmau bansan me kikeso ki mayar damu ba, mutanen banza kika dauke mu ko me?

Bamu Isa da yayan naki bane?

To wlh rantsuwar aure ta Nan ba fashi a yau ma zamu daura mata aure wlh kowama ya huta da wannan tashe tashen hankalin.

Kawu ma maimaita rantsuwar yayi ta sai an daurawa Amatun aure yau kowa y huta musamman me girma ASH da yazo bazaiyi zuwan banza ba aure kaman anriga an daura da Naufal.

Faisal da Shima ya hankalinsa ya tashi matiqar gaske ganin Yana Neman rasa Amatun a gaban idonsa.

Shiru ASH yayi kowa yagama fadan nasa kafin ya sake buqatan a basa guri da maamah.

Maamah zuwa wannan lokacin kuka takeyi sosai ta dago cikin mawuyacin halin ta Kalli ASH bayan kowa ya fice daga ita sai shi dai husnah,

 dukkaninsu sai abinda yace zaayi cikin tsananin kuka ta rasa abin fada a karo na farko Daya jefa mata tambayar Kai tsaye da cewa

Kinada Wanda kikeso a aura mata din??

Numfashi me nauyi ta sauke Babu Wanda yake ranta bayan Faisal Wanda ita kanta tana kunyar ambatar sunan Faisal din a gabansa da husnah.

Hakama itama Husnah Dake cikin tsananin tashin hankalin ganin Faisal zai iya auren Amatu tasan shine a ran maamah Wanda tana fada Dad zai iya daura auren,idan Hakan ta faru zata iya zaucewa,Dan haka gwara a daura da kowa Amma Banda Faisal,

Idan Kuma baa daura da Faisal ba duk Wanda Amatun zata aura a kauyen maamah bazata taba barinta a kauyen ta tafi tabarta ta shikenan ita Kuma ta rasa maamah……

Wani kukan Husnah ta fasa itama tashin hankalinta na qaruwa da duk abinda zai faru ayau din bazata iya barin AmatulMaleek ta auri Faisal ba kaman yanda bazata iya tafiya tabar maamah ba rayuwarta zata lalacewa zata iya qarewa daga qarshe asibitin hauka Dan ciwonta bazai bari ta iya karban wannan rayuwarba.

 Maamah datasan kuka da tashin hankalin Husnah Menene a ranta itama abin a kirjinta ya tsaya tsananin quncinta na qaruwa

shiru sukai dukkaninsu bayan kukan husnah Mai cikeda damuwa da qunci Babu sautin dayake tashi,

Shi kansa ASH din shiru yayi sbd yasan a daidai wannan Gabar shi kansa baisan Menene mafitartaba,

A yanda yayiwa Husnah alaqawarin zai dawo da maamah gidansa

hakama itama yayi alqawarin bazai tilastata ba ko yin hukuncin da zai quntata mata sbd halaccinta dakuma cutatar da Akaiwa yarta.

Rarrafawa Husnah tayi zuwa gaban Dad din ta zube kusan kukanta ma ya Dena fita rawa jikinta keyi sosai tana son magana ta kasa sbd shaqewan datai na kukan maamah da Faisal.

Maamah ahankali ta dago idanuwanta jajir batareda ta iya ambatar sunan Faisal ba ta Bude Baki tace masa

duk hukuncin Daya Yanke zata bi Kuma duk Wanda ya aurawa Amatun ta amince Amma Banda auren Naufal wannan shine kadai adalcin da zai mata itada ‘yayanta sbd tayi imanin zai tsayawa Amatu yayi mata adalcin abinda Akai mata tareda wanketa daga baqin fentin da Akai mata da bazai goguba har abada ga duk namijinda zata aura zai ci gaba da tinawa da goranta mata antaba kwatanta illata rayuwarta da fyade.

Miqewa tayi a hankali ta juya ta koma cikin gida.

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

24

************

Bayan tafiyar maamah daga Husnah har Dad dinta suna shiga damuwa da rashin mafita ta Dan lokaci sbd magana ce a Bude,

Idan har ba Naufal Amatu ta aura ba maamah bazata bisu su koma ba,

Sai Idan Faisal zaa bawa shine zaita Takoma Wanda shikuma bazai iya daurawa Faisal aure da AmatulMaleek ba sbd tasa ‘yar da bazai iya rasawa ba,

Hakama idan maamah Bata komaba still yarsa da gidansa suna cikin hatsari da tsaka me wuya.

Husnah data rarrafo gabansa ya zubawa idanuwansa Yana zurfafa a tinani..

“Dad Dan Allah Kada kabari a daurawa Amatu aure da duka Yan kauyen Nan,

Dad zan shiga Wani hali idan Hakan tafaru,

Dad mum dina idan da zata Tashi ayau itama zatace Karka bari a lalatawa maamah rayuwar Amatu,

Dad kayimun alqawarin komawa da maamah..

Shiru tayi tanason furta abinda yake bakinta na son fadan a daurawa Amatun aure da Haydar sbd a wanna lokacin ita kowama zaa daurawa Amatun a daura Amma Banda Faisal ciki kuwa harda Dad dinma Koda zai aura Amatun yafi mata a maimakon Faisal ya aureta Dan haka ta zabi a daura da Haydar Dan kawai kada a daura da Faisal hakama sbd maamah ta koma dasu Dan haka ta sake rikicewa Dad din tareda shiga mawuyacin halinda ya sake Sakasa halin damuwa akan yanayinta da kalaman maamah harma da duba tashin hankalin da duk aketa yi a wajen har lokacin.

Abdulhameed yasa yaja Husnah yayi cikin gidan da ita aka barsa a gurin shi Daya Yana jiyo yanda su kawu ke rantsuwa kan rantsuwar Babu inda Asmau zataje da AmatulMaleek aure zasu daura mata tayi gidan mijinta ayau din idan yaso Asmaun ta koma rayuwarta ta daula dasuka sabo.

Faisal ma acikin mawuyacin halin rashin sanin mezai faru yake,

Ga Abdulhameed ma nasa hankalin a tashe yake idanuwansa sunyi jajir musamman gano yanda AmatulMaleek idanuwanta sukai jajir batareda hawaye sun gangaro mata ba Amma yasan a zuciyarta tafi kowa shiga mummunan hali akan duka wannan tashin hankalin zaune kawai take Amma hannuwanta rawa sukeyi Dan haka ta rufesu cikin doguwar hijabin jikinta kowane lokaci zuciyarta zata iya bugawa.

Husnah ma gaba Daya a tsinke take cikin tsoro da tashin hankalin hukuncin da Dad dinta zai Yanke,

Maamah ma zaune kawai take Amma hannuwanta Dake hade da juna rawa sukeyi kaman yanda zuciyarta ke rawa,

Tsakanin waje da ciki Abdul yayi zuwa yakai so goma yakasa zama Shima a tsinken yake kaman yanda Suma a wajen duk sai rarraba idanuwa sukeyi Kowa a matse yake suna jiran fitowan ASH da hukuncin Daya Yanke Dan yanzu sun yarda sai abinda yace din zaayi Amma dai Banda aurawa Naufal sbd tini hayaniya tayi tsanani tsakaninsu da iyayen Naufal din dasuka kasa danne irin diban albarka dasu kawu suka ringawa Naufal Daya rugusa rayuwar Amatun.

Faisal ma a tsinken yake yakoma abin tausayi a cikin qanqanin lokaci sbd shi baida Wanda zai tsaya masa,

Su kawu sun tsayawa yayansu,

Iyayen Naufal sun tsaya masa hakama Amatu ga ASH TALBA zai tsaya mata itada mahaifiyarta

Shi kuwa Abdulhameed kawai yake tareda shi sedai Abdulhameed din baida iKon basa auren yayar tasa ko Hana masa.

Su Auwalu da uzaifa kusan su hudu kowannensu yaje yayo wanka ya shiryo cikin shaddodinsu na Roba sun hallaro sbd jiran Wanda Rabon tsaleliyar mace zai fado kansa yau ba sai gobe ba su ragargaji amarci.

Lokaci me tsayi ASH TALBA Bai fitoba Saida su kawu suka ringa zuwa dubawa Amma Babu me iya magana sbd Babu abinda yake da sauke a tareda shi,

Qarshe ma securities dinsa ne suka zagaye kofar gidan dole kowa ya zauna ya nutsu Jiransa su kawu ma ganin sukeyi tinda yazo gwara a daura yananan tinda tamkar Uba yake ga ‘yayan Asmau.

Samarin hudu harda Faisal Babu Wanda kudinsa na sadaki basa jikinsa hakama cikin iyayen Naufal Uncle dinsa Daya yanke a ransa idan fitinar bata samu mafita ba zai biya sadakin Amatun ya aureta kawai Dan kuwa yasan duk macen da Naufal zai kutsa yaso yiwa fyade ta cika mace hakama duba da Barr Faisal Daya mace akanta duk kyau da kudinsa da gatansa to tabbasa takai,

Hakama ya Kalli Abdulhameed da kyau dayake uwa daya Uba Daya da ita dole acikin kyanta ita datake mace Abdul Bai kamota ba.

Kiran sallan Azahar na karfe biyu akai sai alokacin ASH yafito kowannensu idanuwansa akansa kaman zasu fado qasa suna jiran abinda zai fada.

Cikin nutsuwa da kamewansa Kai tsaye ya sanar dasu suyi sallah tukuna.

Ba musu kowa ya nufi Neman butar alwala sbd Allah yagani kowa dai a matse yake da ayi me yiyuwa a gama.

Shi kawu abinda zaayi a gama yakeso ASH din idan zai tafi ya basa abinda zai basa,

Suma sauran kowa da abinda ya matsu yakai garesa a lamarin.

A cikin gida ma kusan kowa jiran yanda zata kasance akeyi,

Iyayensu uzaifa murna sukeyi yayinda matansu Auwalu suke cikin baqin ciki da takaici tareda adduar Allah yasa a aurawa Wanda zai kwashi Amatun su koma inda ma suka fito Dan su zamanta a kauyenma barazana ce garesu fa mazansu da Allah ya jarabta da Sonta Dan kyanta da rayuwarta ta daban.

Daga mota Babban security dinsa ya kawo masa babbar roban bottle water sbd Jameel Baya Nan da shine me kulawa da komai na ASH din.

Karban ruwan yayi yai alwala securities dinsa duk suna zagaye da gurin wasu a bayansa harya gama.

Wata sabuwar tabarmar aka dauka aka Kai masallacin kauyen da Babu shimfidar kirki a cikinsa aka shimfida ta aciki

Daddaiku mutanen Dake masallacin sunata kallan ASH TALBA Wanda yake Dan bawa wasu daga cikinsu hannu suka gaisa,

Liman da me gari tini suka baro inda suke sukazo suna Dan ranqwafawa gurin gaishesa cikeda girmamawa ya miqa musu hannuwansa da kaman saika wanke hannu da sabulu zaka taba sbd tsaftarsa da hasken fatarsa me kyau.

Sallah aka tayar wadda kusan kowa yau adduarsa ta musamman ce ga Allah Dan kowa da abinda yakeso ga ASH TALBA da duk gurin acike yake da kwarjinsa da qamshinsa da Babu Inda Bai cike ba acikin masallacin kowa sai Bude hanci yakeyi Yana Jan qamshin.

Koda aka gama sallar Babu Wanda ya tashi Dan Babu me niyar fita sai sai sungama kallan ASH TALBA

Su kuwa ahalin Sanda Fulde babu me niyar fita yabarwa Wani ya samu damar cusa kansa a gun ASH din Dan abasa auren Dan haka kowa ya kasa ya tsare.

Kawu bello da kawu ashiru Dake gefen Daman ASH ya juyo ahankali ya kalla cikin nutsuwa da kamewansa data gama cika musu idanuwa ya Bude Baki da kalamansa masu nutsuwa da girma yace

“Auren AmatulMaleek zaa daura yanzu kamar yanda kukai rantsuwar daurawa ayau amatsayinku na iyayenta idan Kun Bada dama da duk Wanda na zaba….

Bakin kawu bello na rawa yayi saurin cewa

“Tabbas mun amince mun bawa duk Wanda kazaba aurenta a daura a yanzu.

Kawu ashiru ma Dayake Jin qamshin kudi aduk lokacinda ASH ya motsa shi kudi kawai yake hangowa da Jin qamshi yace

“Tabbas mun amince har Naufal dinma idan kace shi kakeso mun basa Allah ya Bada zaman lfy da hakuri,zasu daidaita ne daga baya idan sungama rigingimunsu.”

Su Auwalu kowa kasa kunne yayi zuciyoyinsu na tsalle,

Faisal kuwa rawa hannuwansa keyi zuciyarsa na bugawa hakama iyayen Naufal.

Boyayyan numfashi me dumi ya sauke batareda yace komaiba ya Ciro wayarsa yayi rubuto ya ajiye.

Minti Daya Bata gama cikewaba saiga AK babban security dinsa Ya shigo da sauri ya wuto har inda ASH din yake ya ajiye masa daurin kudin dasuka Saka kowa hadiye yawu a gurin suna kallan kudin.

Auwalu take yaji shi in kudin zaa bawa Wanda zai hakura to ya hakura ya janye yabarwa ‘yan wahala.

Sadi ma Jin yayi yafison kudin akan Amatun,

Uzaifa ne yafara wasi wasin daurin kudin ko Amatu.

Kallansu ASH yayi Dayan bayan da idanuwansa masu kyau da tsari Yana karantar kowannensu da a Fili son kudin ya take Wani maganar auren Amatun batareda sun fada ba.

Wani numfashin ya sake saukewa me zafi a boye tareda rintse idanuwansa a karo na farko dataji krjinsa yayi nauyi da abinda yake Shirin faruwa dashi din ayau Wanda baitaba tinani ko kawo Hakan akansa ba Amma baida zabi ko mafita bayan wannan din sbd kashe matsaloli da fitintinu harna da bawa maamah Mafi girman adalci da halaccin data buqata na tsawon shekarun datai tana kulawa da iyalinsa da Gidansa bisa Amanar da Babu Wanda zai iya masa Hakan.

Kudin ya Kai hannunsa Akai ya dauka ya miqawa kawu bello cikin nutsuwa da Hana kowa fahimtar abinda yake ransa ya Bude Baki Kai tsaye yace

“Ga sadakin AmatulMaleek dinnan a daura mata aure a yanzu”

Hannu biyu kawu yasaka ya karba hannuwan na rawa sosai harsai da kawu ashiru ya Saka hannu ya kama masa sbd kada kudin su zube qasa yanda hannuwansa ke rawa.

Tsit masallacin ya dauka aka rasa Wanda zai motsa bare magana

Su kawu kuwa Babu abinda suka tsaya jiki na rawa suka kalli su me gari da liman suna cewa

Bismillah ranka ya Dade megari da liman ayi haramar daura auren,batareda sun tambaya waye mijin ba.

Sauran jamaar masallacin tini suka fita suka farfadowa mutane aure zaa daura ba Bata lokaci jamaa suka ringa  dirarowa masallacin take ya cika anata rarraba idon daurin auren wasu Kuwa ASH TALBA kawai suka ringa zuwa Gani Wanda duk Taron Jamaar gurin har lokacin tirarensa ya doke duka qarfin warin zafin dayake tashi duk da securities sunso Hana kowa shiga masallacin Amma ASH ya Bada damar duk Wanda yazo abarsa ya shiga.

Sbd son zuciya Dana Rai take aka fara kokarin daura auren da Basu San waye mijin ba Saida akazo ambatar sunan mijin Kawu bello ya Fadi sunan da ya Saka duka masallacin daukan shiru tareda shiga mamaki da firgici lokaci daya.

Shi kansa madaurin auren rudewa yaso yi dole aka nutsu aka daura auren da sai bayan da aka daura me sanarwa cikin babban sauti da farin ciki ya sanar da  “AN DAURA AUREN MAI GIRMA ASHRAF MUH’D TALBA da ABEEDA AMATULMALEEK SANDA FULDE AKAN SADAKI NAIRA DUBU DARI BIYAR”

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

25

***************

kawu tsabar farin cikin auren da rawar jiki shi da kawu ashiru rungume juna suka ringa yi sunawa juna barka barka da Arziki.

‘Yayansu ma da a take sukasan tinda ASH ya aureta sallamarsu zeyi tini suka hau washe Baki ba baqin cikin komai suna juyewa zuwa yayun amarya Kuma wainda suka hada dangataka yanzu da ASH TALBA suka hau amsa gaisuwar masu Allah ya Sanya alkhairi.

Jamaar masallacin sai murna ake Taya ahalin Sanda Fulde ana Basu hannu suna gaisawa da mutane.

Su kansu iyayen Naufal dole suka tashi suka iso gaban ASH din suka miqa masa hannu cikin tsananin girmamawa suna masa Allah ya Sanya alkhairi da albarka.

Abdulhameed kasa gasgata dauruwar auren yayi da ASH sbd a yanzu bama Faisal dayake gabansaba yajiwa sai Haydar Talba Wanda yasan yanda yafi kusan kowa son Amatun.

Faisal da Daman yasan ASH TALBA bazai taba aura masa Amatu da hannunsa ba sbd magana Daya yake Kuma yayita atin lokacinda aka fasa aurensu farko da Amatun,

Amma Kuma Bai taba tinanin su kawu zasu barwa ASH komai a hannunsaba bare Kuma wannan mamakin na karshe Daya kashesa daga inda yake zaune.

Abdulhameed da Faisal dinne kawai Basu motsa ba kaf masallacin sbd shiga Mafi girman mamaki da tashin hankalin wannan auren.

Kawu Bello ne ya ankare dashi ya Dan waske ya iso inda yake da qafa ya shuresa Yana cewa

“Tashi zakayi ka nuna farin cikinka Koda kuwa bakayin farin cikin Dan kuwa wlh ko uwarku bazata kunce wannan aurenba ya dauru Se lahira tinda muka daurasa”

Kasa magana Abdul yayi sai miqewa tsaye da yayi Baya gane komai ya nufi gaban Dad din ya Dan ranqwafa zaiyi masa Allah ya Sanya alkhairi Amma ya kasa Bude Baki yace komai Saida kawu ashiru dayake kusa ya karbe zancen da cewa

“Abdulhameed Allah dai yayi muku albarka yaji qan mahaifinku Sanyawa wannan auren albarka da tsawon Rai”

Sai alokacin Abdul ya iya Bude Baki ya amsa da Amin Yana tofa tasa adduar shima cikin girmamawa ga Dad Wanda ya amsa Yana miqewa tsaye ya fito masallacin gaba Daya su kawu na biye dashi kowa bakinsa a Bude sai gasar nuna jajayen hakora sukeyi.

Acan cikin gida kuwa Abdulhameed ne yafara shigowa jikinsa na Dan rawa Amma Yana kokarin dannewa da nutsuwa ya qaraso gurinsu maamah wadda tinda ta gama sallah tana kan shimfidar sallan zaune Bata tashi ba, Husnah na gefenta kusan a maqale da jikinta, AmatulMaleek kuwa tana gefe kan shimfidar sallah a lokacin take sallar Azahar din.

Husnah ce ta dago daga jikin Maamah cikin sauri tana kallan Abdul din zuciyarta a qage da son jin idan an daura auren Kuma da waye.

Maamah Bata motsaba bakuma ta tambaya ba Dan kuwa zuwa yanzu ta fadawa Allah,ta sake fadawa Allah Dan haka ta San Allah zai dubi maraicinsu itada yayanta yayiwa Amatun zabi Mafi Alkhairi.

Abdulhameed na zuwa tsayawa yayi daga gefe Yana tauna yanda zai isar musu da wannan sabon lamarin da zai girgiza sauran nutsuwarsu.

Husnah ce ta miqe tsaye tana nufarsa muryarta na Dan rawa idanuwanta na cikowa da hawayen da batasan na Menene ba tace

“An daura auren ne?

Da Faisal aka daura?

Idanuwansa da suka sauya ya zuba mata Dan Jin ita Faisal ne kawai a gabanta ba damuwar kowa ba,

Kan maamah da baisan Yaya zata amshi lamarinba yayi kafin ya Maida kallansa kan Amatu Dake sallah a natse kafin ya Bude Baki zaiyi magana maamah ta dago ta kallesa sbd itama zuwa lokacin amsarsa take Jira hakama wainda suke dakunansu kusa dasu suna jinsu kasa kunnuwan abinda Abdul din zai fada sukai a qage.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda numfashi me dami kafin ya Bude Baki Kai tsaye yace

“An daura Auren…..

Shiru yayi ya sake Dan numfasawa kadan

Zuwa lokacin zuciyar Husnah takusa bugawa har rawa qafafunta keyi sbd son Jin idan Faisal aka daura dashi.

Miqewa maamah tayi ahankali tana kama Husnah da qafafunta ke rawa ta kalli Abdul din zatai magana ya rigata da cewa

“Da Dad dinsu Husnah din aka daur……”

Qarasa zubewa qasa Husnah tayi hawayen datake riqewa idanuwanta suna gangarowa.

Maamah kuwa Bata gama fahimtar wane Dad dinsu Husnah din ba Dan haka ta saki Husnah din tana dagowa idanuwanta jajir akan Abdul tace

“Wane Dad dinsu Husnah din?

ASH??

Gyada kansa yayi ahankali cikin sanyin jiki da damuwa sedai Bai gama jimaminba yaga maamah na Neman zubewa qasa

Kawu Dasuka shigo gidan cikin daga murya da sauri yace

“Karki yarda ki Suma bari a qarasa Miki Dalla Dalla tukuna ki sumen gaba Daya”

Kawu ashiru kuwa Abdul ya hau yiwa fada Yana cewa

“Abin farin ciki kukeson mayarwa na baqin cikin??

AmatulMaleek Dake sallah kasa riqe firgicinta tayi sbd sallarta ta riga ta lalace bayan duhu Babu abinda Idanuwanta ke Gani sai kawai ganin sukai ta silale qasa ita Kam a somen da Husnah da maamah suka kasa qarasawa.

Sakin maamah Abdul yayi yai kan Amatun Yana ambatar sunanta a cikin tsananin kauna da kulawa tareda firgici da tsoron kada Wani abun ya sameta.

Husnah ajiyar zuciya ta ringa jerowa a jejjere kaman me asthma sbd a mummunan bazatar da Bata taba tinanin shiga ba da Jin zancen Dad dinta yayi aure a yau bayan shekarun Daya dauka jiran mum dinta ta tashi

Hakama auren da AmatulMaleek wadda ko Haydar Bata taba hangowa aurenta ba Amma Dad dinsu gaba Daya shine ya aureta.

Maamah ma numfashin take fitarwa zufa na jiqata sosai sbd ciwonta kawai Daya yunquro Yana Neman tashi Dan haka amaryar kawu bello Tayo kanta da sauri tana mata fita taba ambatar sunanta.

Kawu bello Daya ga alamar wankin hula na Neman kaisu nesa batareda sun sanar da ita cikakken bayanin wannan auren duk Wanda yace bayayinsa wlh sedai ya mutu su binnesa Kuma a Dora inda aka tsaya ya Bude murya yanda maamah din zata jisa yafara cewa

“Amatu dai an daura mata aure da Me girma ASH TALBA Kuma wlh ko ciwo kika kwanta Se ta tafi Abuja ayau dinnan gwara ki daure ki danne ku tafi sbd Dake ya buqaci komawa ASH din,Idan Kuma kika kwanta ciwo saiki zauna anan jinyar aurenda bakiso dinba atafi ayi zamansa.,

Abdul Maza kamata ta miqe ku nemo ruwa a zuba mata zata qarasa dawowa daidai ku fara shiri.

Amatu Dake jikin Abdul har lokacin ya kalla Kai tsaye ya Kalli amaryarsa da matar kawu ashiru datakewa Amatun firfita yace ku zuba mata ruwa itama farfadowa zatayi ana jiransu komawa zasuyi.

Kan Husnah Dake fidda numfashi daqyar ya Maida kallansa yace

“Itama ciwon zuciyar ne da ita???

Ku kamata itama a Dan yayyafa mata ruwa ta dawo daidai.

Maamah duk yanda take cikin matsanancin halin tashin hankali da mummunan shock da rawar jiki sosai Saida maganganun kawu bellon suka Sakata Bude idanuwanta dasukai jajir batareda ta iya kallan kowaba a cikinsu sbd kirjinta Daya riqe Bata iya ko dogon motsi bare iya magana sai kawai wasu irin hawaye masu tsananin zafi da radadi suka gangaro idanuwanta.

Kawu ashiru ne yace

“Eh kiyi kukan farin ciki Allah ya cika Miki burinki yau an aurar da Amatun,

Allah ya Basu zaman lafiya karki lalata mana farin cikin aurar da ‘yarmu da mukai ayau din”

AmatulMaleek kuwa ruwa kawu bello Dayaga su saratu na sanyar zuba mata ruwan ta farfado kada ta firgici da tashin hankali ya aikata suga samu da rashi lokaci Daya da kansa ya debo ruwa zuba mata Yana ambatar sunanta cikin kulawa Yana cewa

“Abdulhameed Maza tayar da ita zaune kada ruwan ya shigar mata hanci”

Tayar da ita Abdul yayi zaune har lokacin Bata dawo hayyacinta ba tadai farfado ne kawai.

Shiru su kawu sukai suna kallanta cikin kulawar da ayau sukaji sunai mata me qarfi.

Kawu ashiru ne ya zauna kan tabarbar Da Amatun ke Akai Yana tattare babban tigarsa guri Daya yana kokarin fara jero bayanai ganin maamah da Amatun suna jinsa.

Kafin fara maganarsa babban yayansu Daya yashiga Mallam Shima gurin ya samu ya zauna sbd baisan abinda yake faruwaba Yana kauyen kusa dasu acan yake kasuwanci sai yayi wata Bai dawoba sai yau din cikin qanqanin lokaci kafin daurin auren akaje aka sanar dashi abinda yake faruwa a gigice Shima ya iso kada su bello da zalamarsu su cinye komai sedai Koda yaxo an daura auren tini Amma Jin Wanda aka daura dashi ya sakashi zubewa gaban ASH din a waje Yana zunduma Godia da Allah ya Sanya alkhairi harda hawayen cewan da Dan uwansu na duniya yau dayayi farin cikin ganin Yan uwansa sun aurar da ‘yarsa ga mutumin arziki.

Daqyar yagama gaisuwar ya nufi cikin gidan dayasan ana can ana kasafin sadakin Amatun Daya kusan kunce zariyar wandonsa sbd mamaki da farin ciki.

Zama yayi gefen kawu ashiru Yana gaisawa dasu sama sama Ya amshe zancen ashiru Dayake kokarin farawa na nasihar aure ga Amatun da uwarta datake da niyar daga hankalin auren.

Ganin hawayen da maamah ke tsiyaya bata iya magana ya Saka Mallam cewa

“Asama’u yanzu auren kikewa kuka?

Auren ne bakyaso kokuw mijin da aka daura dashi ne bakyaso?

Cikin mawuyacin hali da radadin zuci me girman gaske ta Bude Baki daqyar ta iya fizgo Kalmar “Babu aure tsakanin ASH TALBA mijin Abeeda da Amatu sbd bazan taba iya karban wannan auren…….

Cikin takaici me tsanani da zafin zuciya kawu bello ya katseta da cewa

“Uban waye ya haramta auren yarinyar data Riga ta zama mata mijinta…

Mallam da zuciya Shima ta siqesa dan idan maamah tace zata cigaba da maimaita maganar rusa auren a shirye yake da jefeta ta kurmance ta yanda bama zata iya maganarba bare harsu riqa jin wannan bayanin nata dayake Shirin musu ta leqo ta koma.

Kawu ashiru kuwa da baimaga dalilin tsayawa saurarontaba wa’azinsa yaci gaba da yiwa Amatu akan zaman aure wadda Babu abinda kunnuwanta ke ji mata dif take.

##MAMUH#

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

26

***************

Kawu bello gaba Daya Jin yakeyi ya qagara su tashi su fara Shirin fiddo kayansu su fito sbd ASH din yace yau zasu koma Abujan ko yolan bazasu kwana ba.

Maamah kasa dauka zuciyarta tayi da lamarin gaba Daya Dan haka jikinta yafara Neman rikicewa dole su kawu suka harhada sukaita kanta dole akace a kamota a fito dasu itada Amatun su harma da Husnah suka fito tafiya.

A mota Daya aka Saka maamah da Amatun wadda itama har lokacin bat dawo daidaiba dole Abdul motarsu ya shiga sbd suna buqatansa dukkaninsu.

Husnah mota Daya ta shiga da Dad dinta ta lafe gefensa batareda ta iya ko motsi ba bare magana kaman yanda Shima Babu abinda ya furta.

Faisal ma da kusan Shima a cikin shock yake Baya hayyacinsa dole motocinsu ASH aka taho dashi.

Manyan motocin na barin qauyen gaba daya su kawu suka kwabe manyan rigunansu Dan fuskantar junansu akan uban kudin da ASH ya Basu Dan kuwa tsakanin su da yayansu ba sauki kowa ya shirya abasa kasonsa musamman su uzaifa daya Bada kudinsu daban yace abasu suda suka so auren Amatun.

Hatta su megari babbar kyauta yayi musu

Su kuwa su kawu nasu baa magana ga sadakin AmatulMaleek din Yana hannunsu Dan haka kowa ya kasa ya tsare matse suke dasu Amatun su wuce Daman ayi kason kudin.

Tafiya ce akayo shiru Babu Wanda yake magana a duka motocin sai motar securities dinsa dasuketa murna da farin cikin aurensa tareda mamakin wadda ta zamo matar tasa.,

sai Kuma motar iyayen Naufal da kusan Suma dai suna tattauna yanda lamarin ya kasance ne uwa Uba uncle din dayaso Rabonta ya fado kansa yau shima ya dawo yayi kwanan Kwanciyar hankali da samuwar amaryarsa.

A motansu maamah kuwa daga ita har Amatu dai jikinsu ba sauki tafiyar kawai akeyi Dan haka hankalin abdul dayake gaba Yana kansu Akai Akai Yana juyawa ya kallesu.

Tafiya me Dan tsayi sukai zuwa lokacin duhun yamma ya Sako Kai Dan haka Koda suka shigo gari magrib tayi Dan haka Kai tsaye mansion dinsa Dake garin aka nufa su Kuma su uncles din Naufal masauki kawai Akai dasu Dan daman daga Nan zasu rabo zasubi jirginsu daga masaukin su wuce.

Koda suka Isa Daman akwai aiki a gidan Tini komai yake gyare Amatu  Abdul ya kamo ya shiga da ita har makeken bedroom din da aka ce akaita kafin yakoma ya shigo da maamah itama Wani bedroom din Daya kusan girman na Amatun.

Husnah da kanta ta shigo sbd Dad din tini yayi bangarensa sbd alwala ya fito sallah.

Dakin maamah ta nufa ta shige sbd batasan zuwa gurin Amatu tafison gurin maamah din.

Abdulhameed ma alwala yayi ya fito sallar kaman yanda Faisal ma yayi alwala duk suka nufi gurin sallan.

AmatulMaleek da kanta ke tsananin juyawa hakanan ta daure tana ganin jiri ta nufi toilet dayake dakin ta fada hannuwan na rawa ta tsaya jikin kofar lafiyayyan toilet din tareda rintse idanuwanta ko zata samu yar hankalinta ya dawo mata ko kadan ne sbd kanta daf yake da juyewa sbd tinanin komai ta kasa Dan Bata ganewa ma.

Daqyar ta Dan ji karfi ta daddafa ta Isa jikin ruwa Tayo alwala ta fito tana dafa Bango daqyar ta iya fito da kanta dakin tana lalabawa ta Isa Dayan dakin dasu maamah suke ta Bude idanuwanta basa Gani sosai.

Sallah Taga maamah na kokarin tayarwa daga zaune sbd bazata iya tashiba kaman ma ba qafafu a jikinta takeji.

Ganin inda suka kalla alqiblah yasata dawowa dakin itama ta tayar da sallarta sedai jiri sosai yake daukanta Amma ta daure sbd akwai har sallar Azahar a kanta.

Cikin dauriya da karfin zuciya tayi sallolin dasuke kanta tayi magrib ta zame a gurin ta kwanta zazzabi me qarfin gaske kawai Yana rufeta hawaye na bin gefen fuskarta masu tsananin zafi da sai yanzu nauyi da toshewan zuciyarta ke fara motsawa.

Abdul ne ya shigo dakin yayo kanta cikin kulawa da tsananin tausayinta ya tayar da ita zaune suka zauna a qasan dukkinsu tareda jingina da gadon dakin Idanuwansa na sauya zuwa ja sbd shi tako Ina damuwa suke sake nitsasa a cikinta ga bangare daya tinanin Haydar a cikin zuciyarsa dama yanda rana tsaka zaace Amatu ta zama matar ASH TALBA,

Ta bangare daya Kuma yasan Babu Wanda wannan auren zaizo masa a sauki sbd maamah hara abada bayajin zata iya karban wannan auren a yanda Bata hada komai da kaunar datakewa madame Abeeda ba yanzu Kuma ace yarta ta cikinta ce ta auri mijin Abeedan.

Kasancewar Abdul a tareda Amatun ya Sakata sakin kukan Daya taso daga qasan zuciyarta gaba Daya cikin sauti mara qarfi da qunci me tsanani.

Hannuwanta ya riqe mata sbd rawar da sukeyi cikin tausayawa Yana Bata hakurin da baima San meyake cewaba Dan Shima Yana cikin shock din sedai nasa me sauki ne Dan aure ne dai kamar kowanne aure aka daura hakama tinda anriga an daura Babu abinda tashin hankalin zai kawo bayan hakura a rungumi kaddara.

Kuka takeyi sosai duk Wani nauyi da quncin zuciyarta na saki.

Shi kansa Abdul kukanta hakuri da juriyar abin yake qara masa Dan kuwa ya gaji da ganinsu cikin wannan tashin hankalin da kukan daga ranarda duk wannan matsalar fyaden ta fado,

Shi saima yanzu yakejin gwara da auren ya fada akan ASH TALBA sbd aurensa ne zai zama duk wata kariyar da Amatun ke buqata daga cikin Mansion din har waje,

Daga yanzu data koma AmatulMaleek Talba Babu Wanda zai iya kallanta ya sake tina maganar fyade bare furta magana makamancinta Dan haka shi Kam alhmdlh,

A ransa Haydar shine Wanda yaso ya auri Amatun duk da tazarar shekarun sbd shine yake mata so tin baisan meye so din ba Kuma akan mutuncinta zai iya tsaye mata koina,

Amma Kuma a yanzu data zama mallakin ASH TALBA din gaba Daya kusan yamafi Jin nutsuwar zuciya ga yar uwar tasa Dan yanzu itace macen datake saman kowacce mace a TALBAs bayan Madame abeeda tinda sune matan shugaba.

Zazzabin Daya rufeta ne ya Saka Abdul din kamata ta kwanta kan gadon da tin anan sun San anfara samun banbanci Dan kuwa dakin shine matsayin dakin madame Abeeda duk da Basu tare gidan ba bama ta taba zuwa ba Amma dai shine matsayin dakinta Amma yanzu matar me gidan Daya ta shiga.

Fitowa yayi daki bayan rufeta da abin rufar Dake gadon me tsananin laushi ya nufi dakin dasu maamah suke Suma daga maamah har Husnah din zazzabi kowa yakeyi hakama Faisal tini nasa zazzabin yayi karfi yabar Mansion din ya tafi masaukinsa daga can jirgi zaibi a da safe ya koma Abuja.

ASH tinda yagamo sallan magrib din Shima shigewa yayi bangarensa tareda kashe wayoyinsa ya tsaya a dan qaramin closet dakin kayansa ya zare kayan jikinsa a natse tareda janyo towel Daya daga cikin towels Dake Jere a bangare daya kusan guda ashirin duk farare kowannen kalar farinsa da taushinsa zaisa ka bambamtasa da normal towels daka sani masu qarfi.

Toilet ya nufa ya shige hannunsa Daya akan towel din qugunsa Da Bai daure da kyau ba.

Wanka yayo ya fito toilet din gaba Daya ya cike da qamshin Aesop liquid soap daya biyo har dakin sbd jikinsa Dake fidda qamshin fatar jikinsa kuwa kaman wadda Bata taba shiga Rana ba fresh.

Baya Wani shafe shafe bayan body oil na Aesop din me shegiyar tsada sai body perfumes kawai.

Abinci lafiyayye da drinks dasu tea harma da snacks masu zafi aka jere babban dining table din Dake babban dakin cin abincinsu tareda sake tsaftace gurin kaman baa jima da sake tsafatace koina n gidanba.

Abdulhameed ne kawai yazo Palo ya tsaya jiran yanda zai sanar da ASH din halinda duka su Amatu suke ciki.

Masu aiki tini suka bace bat daga cikin ainihin palon cikin gidan sbd sanin kowane lokaci ASH zai iya fitowa.

Babu jimawa sai ga qamshinsa ya fara doso palon Abdul na Jin qamshin ya miqe tsaya Yana Dan saita kansa tareda nutsuwa.

Cikin wata tsadaddiyar silk jallabiyan da basai anfadaba kana gani kasan jallabiya ce ba muna jallabiya ba,

ASH TALBA matashin me kudin da yanzu ne yake kokarin shiga dattijantakarsa sbd auren gata na wuri da Akai masa hakama ‘dansa Haydar kana ganinsa kasan shine ya haifesa sbd kyansu ya banbanta Dana Husnah wadda nata mahaifin ta dauko itama Zak a kamanni Amma dayake Yana kama da ASH sai itama take diban kamannin da ASH,

Zuba masa idanuwa Abdul yayi Yana Yaba nutsatsiyar halittar da Allah yayi a gurin,

Mutumin da Babu Wanda zai kallesa baiyi fatan inama shine shi din,

Mutumin da Babu macen da bazata kallesa ba taji Ina Allah zai bata matsayin da zai kalleta da wata siffar sbd shedan da duniya tai masa na mijin mace Daya ne madame Abeeda Talba wadda bayan tafiyarta Allah ne kadai yasan matan da aka ringa basa ‘yayan manya da manyan matan Amma Yana dakatarwa sbd baitaba kallan wata macen da sunan macen so ko aure ba bayan matarsa,

Ita kadai ta ishesa a rayuwarsa yake gani hakama duk wuya duk rintse bazai taba iya kulawa ko kallan mace ko wace iri bace da sunan mace matiqar Abeedansa tana raye ba mutuwa tayiba Wanda Baya fatan ta mutu ko ahakan datake kwance yana fatan Allah ya bar masa ita karta tafi tabarsa.

Isowarsa tsakiyar palon yasaka shi dago fararen idanuwansa ya zuba akan Abdul din Wanda yayi qasa da nasa idanuwan Yana Bude Baki cikin girmamawa yayi masa barka da fitowa.

Amsawa yayi a natse Yana nufar dining room Abdul din ya biyo bayansa cikin nutsuwa yace

“Gaba dayansu maamah da anty Husnah basuda lafiya harma da AmatulMaleek,Kuma sosai”

Dago Idanuwansa dasuka Saka Abdul Dan shin shiru yayi ya Kalli hanyar dakunan nasu ya Bude Baki yace

“Ba damuwa likita zaizo ya dubasu yanzu kafin mu tafi da safe sun warware Inshallah”

Ok Abdul yace Yana kokarin juyawa ASH din ya basa izinin zama yaci abinci shikuma juyawa yayi yakoma Dan kira ya Bada umarnin a Aiko musu kwararran likita yanzu a Talba mansion.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

27

****************

Lokacinda likita yazo dubasu AmatulMaleek aka fara dubawa kafin su Husnah da maamah hakama dole aka Aiko da nurse biyu suka kula dasu har safe Daya Amatu dayar Kuma Husnah da Maamah.

Kafin safe ba laifi kowannensu ya samu kulawa me kyau sun samu kansu da sauki hakama Husnah ta riga su warwarewa ta fito da safe taci abinci tareda Dad dinta da Abdul a dining Wanda har lokacin Babu wata fuska ko damar maganar auren data Gani daga garesa Wanda shi bayajin a gurinsa akwai Wanda zaiba damar yi masa maganar auren ko tini akan maganar auren.

AmatulMaleek ma ankawo mata breakfast lafiyayye a dakin tareda jeresu kaman tareda wasu zataci.

Nurse dinta ce ta takurata tareda lallabata taci abincin dole

Tana gama ci taqara Bata magani Ta miqe ta shiga toilet wanka sbd Abdul yazo ya sanar dasu karfe 11 na safen zasu wuce.

Ko data fito wanka ankawo mata kayan sakawa dogayen Egypt abayas masu tsada sosai Huda uku an ajiye mata.

Kallan kayan tayi tareda dauke idanuwanta ahankali tanajin qarfin jikinta na sake tafiya Kuma Batada zabin Daya wuce sakasu tinda ko alamar an taho da kayansu Bata ganiba.

Black daga cikinsu ta Saka tareda mayafinta ko zama bataiba daga Saka kayan ta fito ta nufi dakinsu maamah lokacin Suma sun shirya ta gaida maamah a sanyaye cikin nutsuwa.

Maamah Bata iya dagowa ta kalletaba ta amsa gaisuwar,

Husnah ta kalla Taga yanda ta kafeta da idanuwa tana kallanta tareda fadawa tinani Dan haka sai batama tsaya yi mata magana ba ta fice sbd ganin yanayin maamah data qi ko kallanta.

Ta sani wannan auren duk qin da kowa zai masa qiyayyar da maamah zatai masa daban ce,

Idan kowa ya qi auren da sauki nata qin babbane,

To Amma ita meye laifinta tinda batason auren ita,Bazata iya auren Dad din Haydar ba,mijin mummy Abeeda,tayaya ma maamah zatayi tinanin ita Koda wasa zata iya son wannan auren.

Shigowar Abdul ne ya Saka Amatu dagowa ta kallesa harya iso ya zauna kan kujera Yana kallanta cikin kulawa yace

“Yaya jikin?

Zuba masa idanuwanta da suka fada cikin dare Daya tayi kafin ta amsa masa da taji sauki cikin sanyi.

Ganin yanayinta ya sanyashi tambayarta ko taje gurin maamah ne?

Sake kallansa tayi tareda gyada Kai ahankali zatai magana ya katseta da cewa

“Kowa maamah din Bata iya kalla bake kadai bace,

Bazata iya karban aurenki ba ayanzu sai zuwa gaba ahankali sbd wannan auren shock of her life ne aka Bata,dole zataji damuwa duba da yanda take da mummy Abeeda and shi kansa Dad dinsu Haydar din.

Fadan sunan Haydar dayayi shine ya sake narkar da zuciyarta tinawa da idan yaji wannan zancen kowane hali zai iya shiga Amma Kuma dole zatayi aure yaji Amma dai Bada Dad dinsaba,

Bazata taba so ko kaunar haydar yaji Dad dinsa ne ta zama matarsa ba,ko bayan Haydar dangin mummy Abeeda zasu iya qullatan maamah,

Ita kanta mummy Abeedan Koda Bata tareda su ahakan kaman baayi mata adalci bane.

Nasihar kwantar da hankali subi komai na rayuwa a sannu suga inda zata kaisu Abdul ya ringa wa Amatun tareda tinatar da ita wannan auren bawai shi kansa Dad din yana raayi ko buqatan auren bane,kawai yayi ne sbd biyan maamah alkhairinta garesa,yayi ne Dan kare mata mutuncin ‘yarta da akaso ketawa acikin gidansa,

Yayisa ne Dan karbo ki daga masifaffen auren dasu kawu sukaso yi Miki hakama yayi ne sbd Baki sunan matarsa ta yanda Babu Wanda zai Kuma kallanki ya Tina Wani abu hakama Babu Wanda ya Isa ya kalleki da wata manufar bayan ta girmamawa.

Ki kwantar da hankalinki ciki gaba da rayuwarki cikin nutsuwa da Kwanciyar hankali kaman yanda kika Saba Babu abinda zai canja a rayuwar ki bayan wannan auren.

Knocking kofar dakin Akai Abdul ya miqe yaje ya Bude.

Cook din gidan ne ya sanar dashi su fito lokacin tafiyansu yayi.

Abdulhameed ne yafara fitowa hannunsa riqe Dana AmatulMaleek din sbd tsananin sanyin jiki da damuwar datake ciki tana buqatan makusancinta a tareda ita.

Maamah da Husnah mota Daya suka shiga Abdul da Amatu suka shiga Daya Saida sukai zaman minti biyu a mota kafin ASH TALBA ya fito sanye cikin Wani tsadadden navy blue Switzerland cashmere Daya fitarda tsadaddiyar rayuwar Dayake cikinta,

Hasken fatarsa kawai AmatulMaleek ta iya hangowa lokacinda yake takowa cikin nutsuwa da kamewansa ta sauke Kai tana Jin jikinta na sake sanyi auren na dawowa mata cikin Kai da Jin Babu abinda takeso a rayuwarta daidai wannan gabar kaman rabuwar wannan auren.

Husnah kuwa Dad din nata ta zubawa idanuwanta ko kyaftawa Batayi,

A Koda yaushe Dad din ta komai nasa daban ne,

Tin daga kan iyayen mutane data Saba gani,masu kudi da masu kudin kudi sosai,harma samari da matasan da duka take Gani Babu kaman Dad dinta,

Dad dinta tamkar tauraro ne Gani daga nesa ga mata harma da mazan,

Dad dinta class/ajinsa dinsa daban ne,

Kwarjinsa da haibansa na musamman ne,

Kyansa da kyan jikinsa abin kallo ne

Mummy dinta ce kawai macen rayuwarsa,

Ita kadai yake kalla amatsayin macen data Kai,

Ita kadai ce a zuciyarsa

Tayaya Rana tsaka AmatulMaleek zata zama yarinyar da mutane zasu kira matar ASH TALBA bayan mahaifiyarta ce kawai me wannan sunan?

Tayaya AmatulMaleek zata samu girmamawa da mutuntawar da mum dinta ce kawai ta cancanta?

Tayaya AmatulMaleek ta samu mijin da ita tasan duk Wanda zata aura bazai Kaisa ba,

Faisal takeso a rayuwarta Kuma shi takeson aura to Amma Kuma Faisal Tako Ina be kama hanyar Dad dinta ba,meyesa AmatulMaleek zata fita ta wanna bangaren bayan itace a Baya take cire kayan sawarta tana Bata,

Jin tayi gaba Daya zuciyarta ta tsani wanna auren itama,

Sam Bata aminta dashi ba,

Kaman yanda Taga maamah Bata aminta ba Kuma batada niyar aminta dashi har abada yasata Jin zata tsaya a tareda Maamah bazasu taba aminta da wannan auren ba da Babu komai acikinsa bayan rashin kamata.

Hawaye taji suna ciko idanuwanta ta hadiye Wanda maamah ta lura da Hakan takuma San hawayen Menene tinda itama ASH TALBA din tayiwa kallo daya ta sauke idanuwanta sbd Jin abu biyu na danne kirjinta,

Na farko qin auren,.na biyu mijin AmatulMaleek ne tinda an daura kafin a warware batajin zata iya ko kallansa yanda ya kamata yanzu.

ASH da Babu abinda yake ransa gameda auren ko wainda ke tinanin auren Yana isowa aka bude masa mota ya shige aka rufe

 take aka tada motocin suka nufi gate da aka wangare musu suka fice tareda Hawa titi sai airport.

Ko isarsu airport dayake Babu Wani Bata time Akai abinda zaayi suka shige jirgi.

*********

Mum Aishi da Naufal da Shima tini ya dawo bayan tashin hankali Babu abinda suke cikinsa,

Tsoro da fargaban Kiran ASH takeyi taji ko andaurawa Naufal din aure da Amatun ne,

Hakama su Uncles din Naufal din Babu Wanda Bata kira numbernsa ba Bata shiga.

Shi kansa Naufal din yayita kiransu Amma Bata zuwa gashi shi harga Allah so yake yaji ance ai andaura masa Amatun shikenan ta zama tasa da hujja zaiyi zaman aure da ita Amma Bai bari mum tasan abinda yake ransa ba Dan haka ya bayyanarda damuwarsa ta qin son auren sosai.

Har dare yayi Babu bayanin komai haka suka kwana Babu kowanne zance Saida safe suna tashi Naufal ne yaci gaba da sake Kiransu cikin saa numbern Uncle Sulaiman dinsa ta shiga.

Ringing takeyi harta katse baa daga ba ya sake Saka Kiran harya Yanke baa dagaba.

Mum ce ta sake Saka Kiran da tata wayar Kiran farko ya dauka ransa a bace Dan Daman fushi sukeyi da Naufal.

Yana dauka mum Aisha daqyar ta iya tsayawa suka gaisa ta musu ya hanya tana dorawa da cewa

“Tin juya kuka baro kauyen ko?

Kun koma ne?ko Kuna yolan haryanxu?

Ya lamarin ya kasance?

An daurawa Naufal yarinyar kuwa?

Allah dai yasa baa daura ba sbd wlh har cikin Raina auren a yanzu Bai kwanta mun ba,Kuma dai daura musu auren batareda suna son juna ba bashine maslahaba……

Katseta uncle Sulaiman yayi da cewa

“Eh aure batareda suna son juna ba bashine maslahaba Amma ai yasan batasonsa Baya Sonta din yaje zai haiqe musu ‘ya,sai yanzu da zaayi musu aure yayi abinda yaga Dama da matar bisa ga Sunna shine rashin maslaha a gareki ko Aisha sbd son zuciya,

Yanzu duk wannan abin da yakeyi ke har kina iya ganin rashin maslaha a daura masa aure?

Kinfi shaawan yaje yayita lalata yayan mutane Yana zubarwa Wanda kuke karkashin alfarmarsa da mutunci,

To maslaha da rashin maslaha dai andaurawa yarinyar aure…..

Wani mummunan faduwa gaban mum Aisha yayi zufa na feso mata Dan kuwa qiyayyarta da auren Amatu ga Naufal dinta daga qasan zuciyarta ne,

Ace Danta guda Daya a duniya ya rasa macen da zata zama matarsa sai ‘yar me dafa mata abinci tana ci.

Naufal dayake Jin duk zancen na uncle Sulaiman Jin yayi zuciyoyinsa ta cike da Wani farin ciki da sanyi Dan kuwa yanzu da ya zama mijin AmatulMaleek din ko mum zata raba auren kaman yanda tayi rantsuwa wlh kafin ya saketa Saiya kwana Yana dirzan sadakinsa da aka biya kafin ya saketan da safe shi son yake ma yaji yaushe Amatun zaa dawo da ita.

Mum dinsa kaman tasan tambayar datake ransa ta Bude Baki zufanta na qaruwa tace

“To yaushe Amatun zata dawo idan har an daura auren ai dole ta dawo ko?

Dawowanta Kam tana hanya tareda Wanda take mallakinsa ayanzu,ma’ana mijinta,

Idan ba Basu Riga sun iso ba to suna hanyar isowa,

Dan haka saiki fadawa danki ya tattara kayansa yabar gidan Dan yanzu ko kallan matar me gidan yayi da wata manufar aka qwaqule idanuwansa a banza wlh karma ki nememu Dan bamuda da me wannan sunanma.

Kashe wayarsa yayi tareda kashewama gaba Daya sbd karsu damesa da kira Suma uban kudin da ASH ya Basu suke rabawa kafin Suma su dauki hanya Dan sukam motarsu zasu ja su koma ba jirgi zasu hau ba.

Naufal da mum Aisha kuwa juna suka kalla batareda fahimtar me uncle Sulaiman din yake nufi ba,

Naufal kalaman Uncle sun mata kama da bashine aka daurawa Amatun ba,

Wani zufan baqin ciki ne ya tsiyayo masa batareda ya tabbatarda Hakan ne ba,

Mum Kuma duk da Bata fahimta ba itama kalaman sun mata kama da Bada Naufal aka dauraba Dan haka take taji Wani sanyi na gauraya zuciyarta da ruhinta.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

28

************

Naufal Jin yayi zuciyarsa na daukan Wani zafi da takaici tareda baqin cikin idan har Wani aka aurawa Amatun ba shi ba bare yasan bazai wuce Barr Faisal uban naci da taurin Kai ba.

Mum Aisha ruwa ta ringa sha tana godewa Allah a Fili da zuciyarta Dan itama tasan bazai wuce Barr Faisal dinba tinda sun San Shima dole bazai iya zama baibi Amatun kauyen ba,.Dan haka itadai koma wanene su je su qarata Allah yasa auren bazai mutu ba sai mutuwa,

Allah yasa auren ya dauru Babu abinda zai tabasa sbd Amatun tayita zamanta acan Babu ranar dawowa rayuwar gidan sun huta

Shi kansa Naufal Daya qwallafa mata Rai tasan ranta yanzu zai samu Nutsuwan Bai ga Amatun ba bare ya Kuma janyo mata maganar da zata kaisu babbar halaka a hannun ASH.

Naufal miqewa yayi batareda yace komaiba zai bar palon mum Aisha ya kallesa da sauri tana cewa

“Ina zaka?

Kasan dai Tinda su Sulaiman sunbaro dole ASH Shima yabaro Kuma inda yake Yana hanyar dawowa gidan Nan ko?

Tinda Bada Kai aka daura ba Maza ka hada kayanka ka koma gidan zayyan kafin komai ya lafa sai na basa hakuri muga idan zaa samu sassaucin da kaima zaka iya zuwa Basa hakurin ya Sauko tukuna ka dawo.

Sai a lokacin Shima fargaban dawowan ASH din ya shigesa Dan haka cikin fargaba ya Kalli mum din yace

“Mum idan ASH ya sameni gidan Nan zai iya miqani inda sai kema kin manta kamanni na kafin a fito Miki Dani ki Ganni”

Miqewa tsaye mum din tayi tana cewa

“Muje kayi sauri ka hada kayanka ka fice sbd jirgi zai biyo kowane time zakaji ya iso.”

Fitowa sukai da sauri zuwa dakin Naufal din Shida mum din suna rige rigen Saka kayansa a akwatinansa da duka ya dawo dasu harya Jere kayansa Yana jiran amaryarsa.

Cikin sauri da gaggawa suke hada kayan batareda tsarawa ba Dan haka kayan kusan duk a hargitse suka gama hadasu suka janyo zuwa mota tana sake maimaita cewa

“Wallahi Naufal ka nutsu kafin na cire hannuwana a lamarinka,

idan zaka koyi dangana da iya hadiye kwadayika akan mata kafin mu samu sassaucin fushin ASH Wanda ba magana zaiyiba Amma hukuncinsa abin tsoro ne,

dan kaje ka sake debo Wani abin maganar da zai dawo kunnen ASH wlh fitarda hannuna zanyi tinda Kai bakasan ana koshi da gundura da komai na duniya ba”

Harabar gidan suke kokarin Isa aka Bude makeken gate din Mansion din motocin ASH suka shiga a Jere sukai parking.

Maamah da Husnah ne suka fara fitowa kafin Abdul Daya fito ya nufi bayan motacin Yana fidda Yan kayan dasuka taho dasu Dan kusan duk kayansu sun barosu a kauyen.

AmatulMaleek ce ta fito karshe kanta Bai juya koina ba sbd Bata iya kallan kowa itama hanyar sashensu take kokarin nufa Kai tsaye saiga mum Aisha da Naufal sun fito cikin sauri.

Cak kowannensu ya tsaya cikeda tsoro da firgici,

Naufal daya sauke idanuwansa akanta ya Sakata Jin gabanta yayi mummunan faduwa take jikinta ya dauki rawa da qarfi idanuwanta take sukai mata naufi ganinta na ragewa sbd komai dawo mata yayi musamman yanda yake kallanta da duka idanuwansa da abinda yake zuciyarsa.

Kasa daukanta kafafunta ke Neman yi tayi Baya ahankali se Jin tayi anyi mata katangar data hana jirin dubanta.

ASH TALBA ne da kansa ya tareta da kansa tareda miqa hannunsa Daya ya qarasa tareda batareda ya kalleta ba.

Mum Aisha da Naufal ya zubawa idanuwansa dasuka kusan Saka mum Aisha sumewa agurin yayi musu kallo daya Babu Kalma ko Daya ya juya da Amatu a hannunsa zuwa sashen dayake matarsa da yayansa.

AmatulMaleek gaba Daya Bata hayyacinta sbd firgicin ganin Naufal datai Dan haka Bata tantance waye ne ya hadata da jikinsa ba saima sake qanqamesa datai Bata ko ganin gabanta har suka bar harabar gidan gaba Daya.

A harabar gidan kusan duk Wanda yake da alaqa da ASH dakuma Wanda yakeda alaqa da AmatulMaleek kusan kowa mutuwar tsaye yayi cikin rawar jiki da tashin hankalin da baa Saka masa rana ba.

Mum Aisha da Naufal da duk Wanda yake gurin tsaye yasan Kai tsaye magana ce Mai hade da mummunan mataki ASH yafadawa mum Aisha da Naufal batareda Bude Baki ya furta ba cewan shine Wanda igiyoyin auren Amatu suke hannunsa.

Maamah da Husnah kuwa kusan kasa motsawa sukai sbd tashin hankali da mamaki me girma.

Abdulhameed da ganin Naufal tin farko ya sakashi baro inda yake da sauri zai nufi yar uwarsa ya Bata kariya kafin kyaftawan ido kaman daga sama kowannensu baiga isowan ASH dinba sai ganin Amatun sukai a jikinsa dakatawa yayi batareda ya qarasaba sbd da alama Amatun Bata buqatan kowa.

Mum Aisha kuwa jikinta ne ya dauki rawa gaba daya abinda tagani a gabanta din ya faru bame taba yiyuwa bane har abadan abada,

Naufal ma sakin kayan hannunsa yayi jikinsa na fito da zufa koina yana kallan mum dinsa Dan shi Kam komai ya kasa fahimta ita yake jiran ta fahimtar dashi Dan kuwa dai Shima hankalinsa ma ya kasa daukan abinda idanuwansa suka ganar masa AmatulMaleek a jikin ASH TALBA.

Maamah mum ta kalla bakinta da jikinta na rawa kalmomin a rarrabe tace

“Asmau Wa kika aurawa ‘yarki?

Kam Husnah wadda idanuwanta suka ciko da hawaye ta mayarda kallanta muryanta na sake rarrabewa tace

“Husnah me na Gani?

Me aka aikota a kauyen??

Waye ya auri Amatun??

Hawayen Dake cike da idanuwan Husnah ne suka gangaro kan fuskarta batareda ta Kalli mum Aisha din ba tace

“AmatulMaleek da Dad aka daura aurenta,

Amatu ta zama matar Dad…..

Jiri ne ya dibi mum Aisha ta fara ganin duhu qafafunta tini suka kasa daukanta ta zube a gurin tana rintse idanuwanta da budewa ko duhun datake Gani sai washe.

Naufal da wutar komai na jikinsa ta dauke rasa tinanin kamawa yayi sai rawa da jikinsa ya dauka tareda tiririn me qarfin gaske Amma dai abinda zai fara shine barin gidan tukuna sbd tsoro da firgici.

Ko mum dinsa baibi ta Kai ba ya ja kayansa ya Isa motarsa ko Gani bayayi sosai ya jefa kayansa ya fada motan yabar gidan jikinsa Babu inda Baya rawa da daukan zafi sosai.

Maamah data rasa abin fada ko yi itama ja idanuwanta sukai tayi gaba zuwa dakinta Abdul na bayanta da kayanta.

Tana shiga kayanta kawai ya ajiye mata ya fita da nasa zuwa dakin Haydar da yanzu shi kadai zaiyi rayuwa a cikinsa,.hakama kayan Amatu Bai aje a dakin maamah dinba dasu ya fito ya nufi cikin Mansion dasu.

Kai tsaye dakinsa yafara shiga ya aje nasa kayan kafin yayo ciki Dana Amatun.

A babban main palon ba kowa sbd Amatu Kai tsaye babban bedroom din Dake maqale Dana Abeeda Wanda ita na Abeedan Palo ne lafiyayye da bedroom a cikinsa Wanda bayajin akwai macen da zata maye gurbin komai na Abeeda a rayuwarsa.

Bedroom din ya kaita har bakin gadon dakin ya janye jikinsa daga nata batareda ya juyoba ya fice daga dakin zuwa bangarensa.

Saida ya fice daga dakin ta iya Bude idanuwanta har lokacin hannuwanta na rawa kaman yanda zuciyarta ke rawa cikin damuwa da tsoro.

Dakin datake ta dago ta kalla Tagane inda take take ta zame bakin gadon tana rintse idanuwanta da sai alokacin suka ciko da hawayen da batasan Kona ganin Naufal bane Kona shigowarta wanna rayuwar bace.

Abdulhameed ne yayi knocking dakin tareda Kiran sunanta ahankali yace mata ga kayanta.

Kasa tasowa tayi kaman yanda ta kasa iya Bude Baki Tayi magana dole shine ya shigo ya ajiye mata kayan ya fice batareda ya iya ce mata komaiba Shima sbd yanzu Kam kowa dole ya fuskanci sabuwar rayuwar Dake gabansa.

Mum Aisha dole su Farida masu aiki ne suka kamota suka dawo ciki da ita Dan kuwa jininta ya Haye sosai dole Abdul ne su Farida suka iya sanarwa Dan shine kawai suka ga fuskarsa a gidan

Shine ya kira likitan gidan yazo ya duba mum Aisha da take Takoma mara lafiyar qarfi da yaji Dan kuwa sosai jinin ya hau gashi yaqi sauka sbd tashin hankalin dayake zuciyarta yaqi sauka sai daka hada da alluran bacci da magani.

Su Farida aikin abincin sukahau duk da sun San Mai gidan Baya cin abincinsu baima taba Ciba maamah ce kawai ke masa abinci Amma yau maamah din ko dakinta Bata iya fitowa tinda suka iso ta shige tayi sallan Azahar da lokacinta yayi ta zauna shiru daki tana lazimi Dan idan ma ta fito batasan tayaya zata iya kallan gidan Aminiyarta yar uwarta da basuda tamkar juna Amma yau an wayi gari ‘yarta data Haifa ace itace zata zama kishiyar Abeeda???

Innalillahi wainna ilaihirrajiun” wannan kalman itace taketa firtawa a duk lokacinda ta ambaci auren.

Tsaf su Farida suka shirya lafiyayyan abinci da drinks a dining tareda cutleries masu tsadan gaske suka sake tsaftace koina a gidan duk da kusan duk bayan awanni ake sake gyarewa.

Gidan tsit har bayan laasar kafin kowa ya tashi daga baccin bacin Rai da rashin mafita sukai wanka da sallah,

Husnah ce ta fara fitowa kafin Abdul sai Amatun daga baya wadda Bata iya cin abincin ba drink kawai ta sha ta komawarta daki Dan itama ta rasa ta Ina zata iya wanna rayuwar ta auren kaddarar Daya sameta.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

29

Ga mamakin Husnah Dad dinta yafito yaci abinci tareda ita da Abdul Wanda kusan shine yake rage Mata kewan Haydar tin bayan tafiyar Haydar,

Ko a fuska ko a dama Husnah bataga ko Daya a gurin Dad dinta ba da zatai masa maganar auren nasa da bataso da AmatulMaleek data ganin Bai kamata ace tana auren Dad dinta ba hakama maamah bazata sake sakewa ba a gida sbd Bata kaunar auren har ranta itama to Kuma matiqar ba Dan sassaucin Daman magana suka Gani a tareda shi ba Babu me iya magana sedai suyita hadiye maganarsu da  damuwarsu har ya musu illa Kila.

Ba sosai yaci abincin ba sbd wannan shine farkon abincin masu aikin gidansa daga na matarsa saina cooks na gidan saina maamah su kadai yake ci Amma yanzu sanin gidan ba Normal yake ba yasa Bazai tsaya Bada Daman korafi ko magana ba.

A natse kaman wanda duk duniya baida damuwa yaci abincin kaman yanda ya Saba,

Yana gamawa ya goge bakinsa yabar dining din.

Abdulhameed hankalinsa kwance yaci abincinsa sosai iya koshinsa kafin Shima ya tashi.

Husnah ma dole abincin taci ta koshi ta tashi ta koma dakinta.

Har dare gidan ba motsin kowa sai masu aiki da suka sake tsaftace dakin cin abincin suka jere na dinner wanda ba abinci ne nauyi bane sedai kaman yanda suka jera kusan haka suka kwashesa Abdul ne kawai yaci abincin,

Husnah tea Tasha

AmatulMaleek ma tea Tasha hakama maamah tea din kawai Tasha shi me gidanma kwata kwata be fito cin abincinba.

Washe gari Babu Wanda ya gansa ya ficewarsa aiki Dan haka har kowa ya gama boyon kansa a daki ya fito sukaci abinci Husnah ce ta fara shiryawa ta ficewarta school Abdulhameed ma fita yayi zuwa Wani gurin.

AmatulMaleek bayan tayi wanka ta Saka doguwar rigar atampa fitowa tayi ta nufi gurin maamah wadda itama ta fito dole sbd sanin ASH din Baya cin abincin masu aiki ta shiga kitchen da kanta.

Amatun ta zuwa gaidata tayi tana tambayarta jikinta.

Amsawa tayi cikin kulawa tana cigaba da aikin dayake gabanta.

Hannu AmatulMaleek din ta miqa tana cewa

“Maamah kawo na tayaki ki huta sbd jikinki”

Numfashi maamah ta sauke tana kokarin hana zuciyarta ganin lefin Amatun akan aure sbd itama ba laifinta bane kaman yanda Abdulhameed ya mata nasiha akan lamarin sosai Kuma tabbas idan Taga laifin AmatulMaleek batai mata adalciba amatsayinta mahaifiyarta,

Abu ne da Akai Wanda ita Amatun kaman auren dole ne,auren kaddara,

Tashin hankali da fushi da qunci bazai kawo salamaba ga abinda suke kalla kaman haramun,Dan haka zatai amfani da zamanta uwa ga Amatun ta nesantata da auren cikin sauki batareda Rai ya Baci ba ko shiga damuwa.

Bata sakarwa Amatun aikin duka ba sedai sukai tare su Farida kuwa sai kaffa kaffa sukeyi da Amatun suna Bata girma ita Sam batama lura ba sbd aikin gabanta kawai takeyi cikin nutsuwa, maamah ce kawai ta lura da komai nasu ya canza gameda Amatun Amma dai itama tayi kaman Bata ganinba sbd kada abin yayi tsayi.

Aikin girkin sukai tare suna gamawa su Farida ne suka jere komai a dining maamah Kam batajin yanzu zata iya cigaba da zuwa cikin gidan sosai sbd kunyar ma ganin kanta takeyi a Mansion din kwata kwata.

Mum Aisha kuwa dai jinya takeyi sosai Dan ko wunin ranar a kwance tayisa cikin wahala da baqin cikin duniya dayake nukurkusanta tanajin kaman ta balbalawa gidan wuta ya cinye gaba daya harda mutanen Dake cikinsa Dan kuwa da Asmau da yarta su zama mamallakan duniyarta ASH gwara ya mutu tun Bai mayar da Amatun matarsa ba kowa ya rasa idan yaso Haydar ya gaje dukiyar ta ubansa duka tinda Husnah batada gadonsa sai abinda ya Bata kyauta tin Raye.

AmatulMaleek kuwa tana komawa dakinta wanka tasake yi tayi sallan Azahar tana idarwa ta fito taci abincin ta ta koma sbd itama kaman yanda Abdul ya sanar mata ASH TALBA ya aureta ne kawai Dan kwantar da kura da tashe tashen hankalin da aketa yi ba lallai zai zai ajeta matarsaba har abada Kila ya Bata Daman komawa karatu tana gamawa ta samu me Sonta yabata Daman yin auren Dan haka ba amfanin quntatawa rayuwarta komai zai wuce.

Tana cikin cin abincin a palon Husnah ta dawo sama sama sukai magana ta wuce daki ta fito cin abincin itama.

Tare sukaci AmatulMaleek tafara gamawa tana barin gurin Dad din Husnahn na shigowa sedai Basu gansa ba qamshinsa sukaji alaman yabita ta kofar palon Daya hada nasa palon da wanna ya wuce Dan haka Husnah ce ta sake gyare table din tsaf da kanta sbd yau abincin maamah ne zaice sosai Kila.

Da daddare ma ba dukansu sukaci abinci ba sbd Amatu bata fito ba sanin da dare tareda iyalinsa yake cin abinci Dan haka taqi fitowa tayi zamanta a daki tea Tasha tayi Shirin bacci ta kwanta.

Washe gari bayan Husnah ta fice makaranta tana fitowa ga mamakinta saiga Mr Jameel yazo ya sanar da ita ta shirya ga driver Nan zata ci gaba da zuwa school dinta.

Taji farin cikin Hakan amma nutsuwarta ta Sanya baiga hakan ba Godia tayi masa kawai.

Maamah ta fadawa itama Tayi mata addua Dan haka taje ta shirya 10 ta fito sanye cikin jallabiya maroon da yar handbag dinta kafin ta iso Daya daga cikin securities na gidan ya taso da saurinsa ya Bude mata motar Yana mata barka da fitowa Dan kuwa sukam ita suka sani tinda basusan tsohuwar matar the great ASH TALBA

dinba sbd tini aka sauya sabbin securities masu qarfi da tsanani Dan haka yanzune zasu San matan maigidansu ASH TALBA.

A natse ta shige motan tareda masa Godia driver ma cikin girmamawa ya gaidata tareda Jan motar suka fice zuwa makarantar tasu.

Koda suka Isa makaranta Daman ana kan karatu ne tai tafiyarta Dan haka kusan kwanakin kadan ne tayi missing Dan haka ta Dan maida hankali kawai tasan ba Wani sosai zai mata wuya ba.

Driver be tafi ba har yamma Saida tagama suka fito kusan tareda Husnah itama Saida tayi lectures din yamma kafin suka shiga motan tare batareda Husnah ta tsaya Kiran nata drivern ba.

Har suka iso baifi magana biyu ba zuwa uku sukaiwa juna kowa hankalinsa na kan abinda yakeyi, Husnah wayarta take dubawa

Amatun kuwa Wani littafi take dubawa.

Parking driver din yayi ya fito kaman Amatu tayi Wani yunqurin harya Bude mata motar Yana matsawa gefe.

Daga Amatun har Husnah shiru sukai da mamaki musamman Husnah data kasa yarda da abinda yake Shirin faruwa da rayuwarsu.

Fitowa Amatu tayi a natse tareda masa Godia tana wucewa batareda t Jira Husnah ba da itama ta fito ta nufi ciki zuciyarta na nauyi.

Koda Amatun ta shigo Bata wuce bedroom dinta ba gurin maamah tafara zuwa ta fada mata dawowanta tareda ajiye Jakarta anan dakin tayi alwala tayi sallan laasar tareda cin abincin suna Dan magana Sama sama da maamah din har magrib

anan tayi sallan magrib kafin ta fito ta nufi dakin mum Aisha tai mata ya jiki wadda ko amsawa batai ba Dan taji sauki Amma Babu Wanda tafara tankawa magana a gidan sbd shock din rayuwarta Bai gama sakintaba.

Juyawa tayi ta fice mum din ta bita da Wani irin kallon baqin ciki da tsana wutar zuciyarta na sake balbaluwa Dan kuwa akwai masifa a qasa kwance indai akan auren Nan tafison kowa ya tafi lahira ba shiri.

Amatu na Isa bedroom dinta wanka ta fara yi tayi Shirin bacci har zata kwanta ta Tina gaba Daya yau Bata ga Abdul ba Dan haka ta ziro takalminta ta fito.

Hanyar dakinsa take kokarin nufa taji motsi a dining room Dan haka ta juya ta nufi can din Kai tsaye Dan tasan shi kadai ne zai iya fitowa a wanna lokacin cin abincin dare.

Dayake kowa ya shige ba motsin kowa hakama kusan duk an rage hasken koina,

Kai tsaye ta shiga gurin cin abincin tareda ambatar sunan Abdul din da muryanta me taushi da nutsuwa…..

Dagowa yayi a natse daga tea dayake hadawa Batareda ya iya hadawan ba yayi mata kallo daya da fararen idanuwansa ya mayar dasu kan abinda yakeyi din.

Itama cak ta tsaya a gurin dataken tana sauke idanuwanta qasa tana rasa abin yi sbd taba tsammani ko tinanin shi din bane a daidai wannan lokacin.

Cikin nutsuwa ta Bude Baki ta gaidasa

Batareda ya dago ba ya amsa Yana nuna mata flask din Daya kasa budewa a natse yace

“Bude wannan abin Ina buqatan hot tea din yanzu”

Wani numfashi me Dan nauyi ta hadiye tareda danne rudewanta ta qaraso gurin a natse batareda tace komaiba ta miqa dogayen yatsun hannunta farare akan flask din ta dauka ta Bude a hankali tareda janyo cup ta zuba masa sedai Sam ruwan tea din Babu zafi sosai Wanda da alama tin na safe ne Kokuma Husnah ta Bude tabarsa Bude ya huce tinda baya yiyuwa ace masu aiki Basu kwashe komai suka sake jera wasu ba.

Rasa ya zatayi tayi dole ta Bude Baki kanta a qasa cikin nutsuwa da sanyin murya tace

“Ba zafi,zaa dafo Wani tea din”

Da hannu ya nuna mata kofa Yana mata alamar ta ta kawo wanin sbd Yana buqatan tea din sosai sbd yau be Wani ci abinci ba sbd Taron baqin da yayi akan hanyewarsa daga siyasan nan da Sam batai masa ba idan har sirrin gidanka bazai sake zama sirri ba sbd siyasa Dan haka Baya raayi tattara iyalinsa zaiyima subar qasar.

Kitchen din palon ta nufa ta kunna gas a natse ta sake dafa Wani ruwan tea din da kayan qamshi da lemun tsami kadan sai pure honey ta zubo a wasu gurin daban ta dauko ta kawo.

Har lokacin Yana dining room din gaba Daya qamshinsa har palonsu har kitchen ya gauraya koina sbd yar jimawansa a gurin.

Ajiyewa tayi tareda zubawa a cup ta sake ajiyewa ta juya ta nufi kofa.

Thank you” ya furta can qasan maqoshinsa cikin nutsuwa kafin ya dauko cup din ya Kai bakinsa lips dinsa na Hawa kan cup din ya Dan rufe ido sbd Jin qamshi da zafin tea din zai basa abinda yake buqata ataredi.

Tana baro dining din kasa wucewa tayi dakin Abdul ta koma dakinta ta nemi guri ta kwanta.

Washe gari Mr Jameel ne yazo da kansa tareda wata budurwa da zata girmeta sosai Amma dai batada tabbacin budurwa ce ko matan aure ya hadata da ita akan ita zata kula da ita kwana biyu.

Bata gane wace irin kulawa ba Dan haka Bata iya cewa komaiba Saida suka fita zuwa makaranta suna dawowa Kai tsaye ba gida suka nufa ba gurin siyayyan kayanta suka nufa.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

30

Siyayyan kayan sakawanta da handbags da shoes designers masu shegiyan tsada Taga Farha din nayi Wanda yasata mamakin inda kudin suka fito,

Suturar da aka Siya mata kuwa kasa tantance kudin dataci ana fadan musu tayi sbd gajiya da kanta dayayi Wani irin nauyi na mamaki me tsanani da tsoro.

Sai bayan magrib driver ya dawo dasu mansion su Farida ne suka shiga da kayan har bedroom dinta suka fice

Itama Farha Bata zaunaba ta fito driver ya tafi da ita kaita gidanta.

Wanka tayi tayi sallar magrib da ishi ta fito sanye da doguwar rigar yadi ta nufi gurin maamah dataita kiranta akan me takeyi a waje Bata dawoba.

Tana Isa dakin maamah na sallar ishai Dan haka abincin data Gani dakin ta Bude Taga tuwon semolina ne Akai da miyar zogala ta tsokan kaza da ganda da da egusi.

Ajiyar zuciya ta sauke sbd bdai taso cin abinci me nauyi ba Amma Kuma tana Jin yunwa Dan haka zataje taci kadan saita sha fruits suyi saurin narkar mata dashi.

Sama sama sukai magana da maamah dataga gajiya a tareda ita tace taje taci abinci ta kwanta ta huta.

Miqewa tayi ta fito ta biya sashen mum Aisha ga mamakinta Bata Nan tinda yamma ta fita kenan itama Bata dawoba.

Fitowa tayi ta wuce ciki Kai tsaye kitchen ta nufa ta samu fruits din ta debo kenan saiga Abdul ya fito hakama Husnah Dukkaninsu Babu Wanda yaci abinci Daman dan haka dole ta bisu zuwa dining din Badan taso ba sbd tasan Dad din Husnah na gidan Kuma akwai yiyuwar cin abincinsu a tareda shi.

Zaunawa sukai dukkaninsu Abdul na magana da Husnah tana murmushi sbd firar Haydar ne sukeyi dukkaninsu sunyi waya dashi yau din.

Basu fara cin abincin ba qamshinsa ya doso su Dan haka kowannensu ya dakata tareda juyawa ga hanyar shigowa Banda Amatun data kasa juyawa taji gaba Daya abincin ma kaman bazai shiga cikinta ba to Amma batasan tayaya zata miqeba tabar gurin bayan zuwansa.

Qarasowa yayi sanye cikin Balenciaga sweatset brown qafafunsa ma sanye da takarman zaman gida masu taushin fata sbd tsadansu.

Yana isowa ya zauna ahankali tareda amsa gaisuwar su cikin nutsuwa

Sai alokacin itama Amatun ta Bude Baki cikin sanyi da nutsuwa ta gaidasa.

Bai lura da ita ba Saida tayi magana ya Dan dago kadan ya amsa Yana daukan ruwan Dake gabansa marasa sanyi sosai yakai bakinsa yasha kadan ya ajiye.

Abincin da Husnah ta zuba masa Shima ya kalla

Yanason tuwo Amma yanzu dare yayi masa da cinsa sosai Dan haka kadan Shima yaci ya buqaci tea.

Husnah Bata iya dafawa ba Dan haka Amatu ta kalla wadda ita Kuma Daman hanyar barin gurin take nema Dan haka ta miqe ahankali ta bar gurin zuwa kitchen.

Tana aikin tana Shan fruits dinta Daman shi tuwon taci kadan a dining,

Tana gamawa ta juye ta dauko ta fito

Koda takai tea din daga Husnah har Abdul sun tashi ba kowa saishi a gurin Dan haka a natse ta iso ta ajiye tareda zuba masa ta juya tabar gurin.

Dakinta Takoma brush kawai tayi ta kwanta Dan baccin takeji sosai a yau din.

ASH kuwa Daman yace Abdul ya samesa bayan sun gama cin abincin Dan haka Abdul Yana kwatanta gamawansa ya fito a natse ya nufi palonsa tareda knocking cikin girmamawa da sallama ya shiga bayan ya basa izinim shigowa.

Zaunawa yayi bayan ya sake gaida Dad din.

A natse ya qarasa wayarsa kafin ya kasheta gaba Daya ya ajiye gefensa ya Kalli Abdulhameed din cikin nutsuwa yafara fada masa yafara shirye shiryen tafiya makaranta zaibi Haydar can inda yake zuwa nxt month Dan angama komansa kadan ne abubuwan dasuka rage.

Godiya sosai Abdulhameed yayi cikin bayyanarda farin cikinsa tareda adduar Allah ya Saka da Khairan.

Koda ya fito yasan Yan matan sunyi bacci Dan haka dakinsa Kai tsaye ya wuce cikeda murna da farin ciki me tsananin gaske ya ringa nafila yana godewa Allah tareda yiwa ASH addua da iyayensa babah da maamah.

Washe gari lokacinda ya sanarwa da Amatu kasa riqe farin cikinta yayi ta rungumesa tana Jin dadi sosai tareda yiwa ASH din addua Dan kuwa zuwa yanzu ta tabbatarda ba Wani maganar aurenta dayake gabansa Dan haka itama zata dage tayi abinda yake gabanta kawai,

Maamah ma sosai tayi farin ciki Kuma dole Badan tanada yanda zatayi ba ta tafi har palonsa tayi masa Godia ta fito

Husnah ma tayiwa Abdul din murna sbd Haydar ze samu na gida a tareda shi Koda maganar auren Amatu da Dad dinsu ta Isa kunnensa aqalla tasan Abdulhameed zai tsaya ya kula dashi batareda ya shiga Wani halin ba duk da dai su haryanxu soyayyar kuruciya ce yakewa Amatun.

Cikin farin ciki yau sukai breakfast dinsu a dakin maamah tareda ita suna gamawa Farha tazo tini Dan haka Amatu fitowa tayi ta Takoma bedroom dinta ta shiga wanka,

Kafin ta fito duk kayan da aka siyo jiyan Farha ta jera komai a inda ya kamata dakin ya sake sauyawa zuwa na budurwar da Bata rasa komaiba na duk Wata luxury rayuwa.

Dayake tayi latti ba Bata lokaci ta shirya kaman dai yanda kusan kayan duk dogayen riguna ne masu kudi

Acikinsu ta shirya suka fito Kai tsaye mota suka shige zuwa school.

Abinda yake bata mamaki da kawo mata Farha da Akai shine me zatai mata?

Haka kawai zata ringa rakata makaranta su dawo?

Bata tambayarba sbd batama ga Wanda zata tambaya ba hakama ita kanta Farha din yanda take kula da ita tana nuna mata wasu abubuwan da Bata saniba yasa take ganin ba takura sosai a yawonta da ita.

Kwana biyu duk suka fita sai anyi siyayyar abubuwan buqatanta harma da Wanda Bata buqatan,

Farha kaman designer ce kaman Kuma beauty designer,hakama abinda ta lura dashi shine kodai qanwar Mr Jameel ce Kokuma yar uwarsa sbd akwai kusanci a tsakaninsu hakama kusan komai shi Farha din ke kira Yana Bada kudin da kamar baisan zafinsu ba dayake kusan shine bankin ASH TALBA.

A cikin kwanakin dasukaita zuwa suna wucewa Farha ta Saka Amatu Dan fara sakin jiki da ita sosai duk kamun kan Amatun da rashin son mutanenta Saida ta sake da Farha duk da ta girmeta Amma Sam ba wanna tsakaninsu hakama a aynzu data fara sabawa da amfani da kayan da aketa siyowan taji tafi sakewa a cikin dogayen rigunan dasuka zama suturarta a yanzu,

Ta bangaren cikin gidan kuwa sosai kowa ya zama busy shiyasa kusan kowa a gajiye kowanne dare ake kwantawa,

Abdulhameed shirye shiryen tafiyarsa kawai yakeyi sosai hakama maamah duk Jin takeyi ta shiga sanyi sbd tinda ta haifesu Bata taba nesa dasu ba Koda na kwana biyu ne koyaushe tana tareda yayanta duk inda zasu Dan haka yanzu dazai tafi wata qasa duniyar Jin takeyi kaman bazai iyaba  sedai tinowa da Haydar na can Kuma zasu kula da juna sosai yake sata Jin hankalinta ya kwanta,

Husnah Kuma exams ne a gabanta shiyasa ta kasa gane kanta sosai ta dage sbd kusan Amatu sosai take kawo wuta a nata karatun Dan haka yanzu da Bata kaunar abinda ma zaisa Dad dinta ya duba cigaban Amatu akan nata Sam Bata kaunarsa.

*****Ta bangaren ASH TALBA kuwa kusan kullum da Amatu ta gane Yana shan tea da dare koyaushe kafin ta shige saita dafa ta Kai dining a flask ta ajiye ta shigewarta,

Shima Daya fahimci yanzu kullum ana aje masa sai ya rage fitowa cin abinci tareda su Sai ya gama komai zai fito yasha ya koma ya kwanta.

Mum Aisha tayi tafiyar dole wadda take Jin idan batai ba zata iya fashewa a cikin gidan sedai a Tararda gawarta Dan haka tayi tafiya kanta ya fara warwarewa kafin ta dawo tasan yanda zatayi da yar cin Amana maamah wadda taci amanar aminta da zumunci.

Tafiyar Abdul tazo daidai da tafiyar Husnah porthcrt mahaifiyar Faisal ta rasu Dan haka sosai hankalinta ya tashi haka itama Maamah sosai ta shiga damuwa ga exams sunayi a lokacin,

Ranar da Abdulhameed ya wuce AmatulMaleek Tasha kuka a jikinsa kaman shine yayan itace kanwar

 haka ya ringa rarrashinta Yana Bata qwarin gwiwan fuskantar rayuwarta batareda tsayawa kebe kanta ko takura kanta akan aurenda ASH Kila ya manta dashi.

Maamah ma taji dadin shawarar Daya bawa Amatun sbd so take Amatun itama ta manta da Wani maganar auren harsu samu Abeeda ta tashi Dan Tana tashi tasan ASH TALBA bazai qara ko kwana da auren Amatun ba zai sallameta asiri rufe batareda Abeeda ma tasan anyi auren an warwareba.

Abdulhameed ya tafi yabarsu da kewansa Dan haka maamah dole cikin kwanakin ta Maida kulawanta da tattalinta ga Amatu wadda ta shiga damuwa sosai na tafiyan Abdul sbd shine abokinta Kuma abokin shawararta.

Farha da maamah ne suka dage harta sake batareda ta Dade cikin damuwarba sbd exams dinta.

ASH TALBA tin washe garin rasuwar umman Faisal yaje yayi gaisuwa ya dawo,

Husnah ma itace ta riga Amatu gama exams dinta Dan haka babu Bata lokaci tayi Shirin tafiya porthcrt Kuma tareda maamah zasu itama tayi gaisuwa.,

A bangaren husnah da gangan ta da tafiyar maamah din sbd idan suka tafi gidan ze Kona ba kowa sai Amatu da masu aiki wainda suke bangarensu daban,cikin mansion dai ze kasance Amatu ce kawai Dan haka tsoro da firgici bazai taba barinta yin karatun da zatai exam me kyau ba sbd itama Bata karatun exam din ya lalace ne kwata kwata daga ranar da umman Faisal ta rasu.

Ita kanta Amatun da zasu tafi hankalinta tashi yayi sosai da barinta da zaayi ita kadai a gidan sosai ta shiga damuwa Amma batai magana ba sbd tasan ma ba lallai atafi da ita ba Kuma ko taje Yan uwan Faisal din da yawa basa Sonta ganin itace ta Hana ya auri Husnah ko gaisuwar rasuwar txt tai masa har so uku duk bayan awanni saita masa ta tura masa sbd bazata iya kiransa ba tin ranarda aka daura aurenta masu sake magana ba baice mata komaiba ko a waya haka itama batasan me zata ce masa ba,

A makarantar ma sosai suke wasan boyo da juna kaucewa juna sosai sukeyi basa son su Hadu.

##MAMUH#

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

31

Su Husnah na hanyar zuwa airport ta Ciro wayarta daga handbag dinta shedan na ingizata ta Dan shakka Amma Kuma zuciyarta na sake turata ta Nemo numbern Naufal ta tura masa txt din idan Yana son Neman gafarar AmatulMaleek ita kadaice a Mansion ko Babu kowa Se masu aiki hakama Dad dinta baya gari.

Tana tura sakon ta mayar da wayarta handbag dinta ta rufe tareda kallan maamah da itama itan ta kalla cikin kulawa ta saki murmushi tana Dan kwantawa jikin Maamah ahankali tace

“Maamah Allah yasa mum dina ta samu lafiya ta dawo cikinmu Ina kewanta sosai.”

Numfashi me dumi maamah ta sake tana amsawa da “Amin ya Allah” zuciyarta na Dan nauyi sbd duk lokacinda ta Tina da Abeeda da auren mijin Abeedan Dake kan tata ‘yar Jin takeyi hankalinta da duniyarta na jijjiga sosai cikin tashin hankali da damuwa.

Suna Isa airport Basu Wani jimaba suka hau jirginsu ya tashi Husnah na sauke ajiyar zuciya me sanyi.

Ranar da suka tafi din a school Amatu ta wuni Se magrib ta dawo gida cikin sanyin jiki tayi wanka ta fito taci abinci Takoma daki ta kwanta zazzabi na Neman rufeta sbd kadaici da rashin nutsuwar zuciya.

Bacci Rabi da Rabi tayi har tasamu asuba tayi ta tashi tayi sallah sai alokacin ta koma baccin kirki.

Bacci tayi cikin nutsuwa da Kwanciyar hankali har qarfe Tara kafin ta tashi tayi wanka ta fito daure da towel ta zauna gaban mirror ta shirya ta Saka undies kafin ta Saka doguwar rigar army green ta fito qamshinta na tashi ahankali cikin sanyi ta nufi kitchen Bata nufi dining ba Dan batajin zaa jera abinci tinda ita kadaice sedai ga mamakinta tini aka jera abincin breakfast dinta komai da komai Yana kan dining din dole can ta koma taci abincin tana gamawa ta miqe Takoma daki ta sake Dan gyarawa ta fito.

Dayake ko Farha kwana biyu Bata Nan ita kadai ta shiga mota driver ya jata zuwa school.

Acan ta wuni yauma sai yamma ta dawo tana gama komai ta shige ta rufe daki ta kwanta.

Kwana hudu da tafiyarsu maamah ta gama exams dinta ita Dan haka yau din data gama da wuri ta dawo tana shigowa mansion din ana Kiran laasar.

Wanka tafara yi Tayi sallah tana Jin nauyin dayake kanta kaman ya sauka tinda ta gama jarabawanta.

Abincin yau dinma baa dining taci ba a plate da trey aka kawo mata ta zauna Palo tana ci tana Dan kallo Sama sama.

Ko data gama da kanta takai kayan kitchen ta gyare gurin ta zauna tana Dan duba wayarta har magrib ta tashi ta shige daki tayi sallah

Tana idarwa Bata fitoba ta zauna a sofa tana waya da maamah suka jima suna wayar har Akai sallan ishai ta tashi tayi ta gama ta fito taci abinci kadan tareda Dan dakatar dasu Farida suka tayata fira a palon har 9 kafin suka tafi itama ta tashi ta shige bedroom dinta.

Tubewa tayi ta daura towel tareda shigewa wanka.

Tana cikin toilet taji kaman tashi Bude kofan dakin da rufewa

Gabanta yayi mummunan faduwa ta kashe ruwan wankan tana saurarawa.

Shiru Babu motsin komai Dan haka ta sake kunna ruwan tana qarasa wankan cikin faduwan gaba da mamaki.

Tana gamawa towel ta janyo ta daura tareda riqesa gamgam ta fito toilet din gabanta na tsananta faduwa.

Tana Bude kofar toilet din ga mamakinta sai Taga wutan dakin a kashe bayan tasan a kunne tabarta.

Hakan data Gani ya Sanyata sake qanqame towel dinta tana Neman juyawa toilet da sauri Dan ta rife kanta Amma taji mutum na kokarin fitowa daga gefen wardrobe na kayanta cikin matsanancin firgici da tashin hankalinta Dake barin jikinta ta qwalla Wani irin ihu me qarfin gaske da Gidan gabaki daya ya dauka.

Cikin sauri Yayi saurin sakinta jikinsa na rawa tareda nufar kofa ko Gani bayayi ya buge goshinsa da qarfi a kofa take ya saki Dan qaramin ihu Shima Amma Bai tsayaba ya fice da Wani irin sauri yabi ta kofan kitchen ya fita ya zagaya zuwa bayan sashen mum Aisha da akwai fence a gurin me tsayi da wire na wuta Amma dayake yasan inda ake zuwa ayi disconnecting Saida yayi disconnecting bayan shigowansa.

ASH TALBA after 9 na dare ya dawo gidan daga tafiyana Dan haka Yana shiga Shima wankan yafara shiga sbd rage nauyin tafiyar da yayo.

Fitowansa wanka kenan yaji ihun Daya ratsa kunnuwansa Bai fara kawo tinanin komaiba saida ya Tina da cewan akwai ‘yar mutane a gidan Kuma Sam ya manta da Hakan Dan haka da sauri ya janyo bathrobe blue ya Saka kan towel Dake qugunsa ya fito dagashi sai slippers dinsa masu taushi ya nufi hanyar palonsu da sauri Yana jefa idanuwansa kan agogon Dake palon yaga karfe goma sha Daya Dan haka da sauri ya qarasa Yana sake jiyo ihunta Wanda take ya sake shiga mamaki da qara sauri.

Yana isowa dakin Bai tsaye komaiba ya Bude tareda shiga Yana nufan inda take jikin kofan shiga toilet tanata ihu dukkanin jikinta na Wani irin rawar tashin hankali Tama fice hayyacinta gaba Daya.

Wutan dakin yafara kunnawa Kai tsaye tareda nufarta Yana kokarin kamota daga jikin bangon tana sake qanqamewa tana jikinta na jijjiga,

Kafin ma ya sake wata motsin zuwa gareta tini jikinta ya saki zata zube a gurin ya tarota da hannu Daya Yana Saka Dayan kan kirjinta ya dafe towel dinta dayake warware Yana Shirin sauka daga kirjin.

Numfashi ya sauke ahankali Yana kallan dakin ahankali Yana duba Menene matsalar,

A bayan jikin wardrobe yaga shatin takalmin babba a gurin sbd tsaftar gurin yasa shatin qurar qasa Dake jikin takalmin ya maqale.

Wani sarawa kansa yayi batareda ya gasgata abinda ya ganin ba bare tantancewa Dan bama zai yiyu ace Wani ya iya shigowa Nan dinba.

Kan fuskarta da take tayi ja ya dawo da idanuwansa ya sauke ya kalleta dakyau ahankali tareda dauke idanuwansa Yana daukanta gaba data Dan kuwa tabbas idan abinda yagani Kuma yake tinani mutum tagani Kokuma aljan.

Fitowa yayi da ita daga dakin ya nufi hanyar palonsa da ita har lokacin batasan ko matsi Batayi.

Kofar bedroom dinsa ya tsaya cak da ita sbd bayajin zai iya shiga da ita dakinsa Bai Dan haka ya juyo palonsa ya kwantar da ita kan kujera ahankali Yana dagowa towel dinta na fara zamewa da sauri yakai hannunsa ya dafesa Yana juyar da fuskarsa tareda miqewa gaba Daya ya bar gurin.

Bedroom dinsa ya shiga Kai tsaye ya Bai tsaya shafa komaiba ya Saka pyjamsa dinsa na bacci masu Dan kauri sbd bayason sanyi sosai ya dauki wayarsa ya fita Yana Kiran Jameel akan gaba Daya a bincike Mansion din ciki da wajensa.

Jameel na Jin Hakan ya sanar da securities Dan haka tini suka kunna shegun fitilinsu masu shegen haske duk da akwai haske koina gidan.

ASH din Bai fada musu abinda yake faruwaba Kuma baida niyar fadan Amma ya basu Daman duk abinda suka Gani su harbesa ko menene Dan haka suka hau dubawa a shiryensu ba sauki ba Imani suna gani zasu Ma koma Menene ko waye ruwan bullet dinsu.

Sosai suke bincike gidan ciki da waje Amma Basu ga kowa ba ko komaiba sedai sunga anyi disconnecting security electronic wire din gidan an kashe gaba Daya.

Ganin haka suka Ankara da dai Wani ne ya shiga gidan cikeda mamaki da bacin ran Wanda yakeda wannan qarfin halin suka sake bazama suna sakawa ransu koma waye wlh saisun kamasa.

AmatulMaleek cikin firgici ta Farka tasake Bude Baki zatai ihu sbd batasan inda ma take ba ga ba haske sosai a palon,

Tana Bude Baki yakai hannunsa na dama Dake kusa da ita ya Dora a bakin tareda sauke mata idanuwansa a karo na biyu Yana mata kallan da bana fizge ba,

Rawa jikinta keyi sosai ta Dora tafin hannuwanta akan nasa dayake kan bakinta zata janye hannun nasa tayi ihun sbd Bata ganesa ba a firgice take har lokacin,

Saukan hannuwanta akan nasa yasaka shi janye nasa hannun Yana kallanta zeyi magana ta fasa kuka me qarfi sbd gane waye a tareda itan tana Kiran sunan maamah da Abdul harma da Haydar.

Shiru yayi duk kuka da ambatar sunanyen datakeyi Bai motsaba kaman yanda Bai waiwayo ya kalletaba sbd dole tana buqatan kukan ta fita shock data shiga,

Ta bangare daya kuwa tinani be barkatai a ransa gameda lamarin,

Sedai Kuma anyi na karshe Dan kuwa Shima Saiya kama ko waye da hannunsa idan kuwa Wanda yake zargi ne tabbas zai Basu mamaki me girman gaske.

Kuka da tashin hankalin data shiga ya Sakar mata zafin jiki tana ji tana Gani yabarta a palon ya wuce ciki bayan ya rufe kofan palon duk da yasan koma waye ko wace giyar yasha kaddara bazata kawosa har palonsa ba.

yanda Amatu Taga Rana haka Taga Daren a firgice ta kwana,

A tsorace ta kwana,cikin rawar jiki da damuwa tareda tsananin buqatan mahaifiyarta ta kwana,

Sai guraren asuba baccin wahala ya dauketa me Dan karfi Dan haka Koda ya fito da asuba ganin tana bacci qyaleta kawai yayi ya koma ciki a cikin gida yayi sallan asubar ranar sbd bayajin zai iya fita yabarta bayan baa samu kama koma waye ba akwai yiyuwar Yana cikin gidan har lokacin Kokuma ya gudu.

Sai guraren 9 ta Farka gaba Daya jikinta ba qwari hakama kanta ciwo yakeyi sosai,

Jikinta ta kalla har lokacin towel ne a jikinta Dan haka Bata tsaya ko kallan kofar bedroom dinsa ba ta miqe daqyar Dan jiri na dibanta ta nufi kofa takai hannunta kenan zata Bude ta fice shikuma Yana Bude ta bedroom dinsa Wani sanyin AC tareda qamshinsa ya huro Bata juyo ba Bata Kuma tsaya ba ta Bude kofar ahankali ta fice cikeda kunya da baqin cikin yanda rayuwar ta take Neman komawa.

Sai data fice Shima ya fito Kuma meeting ne dashi Amma Yana Dan shakkan barinta gidan ita Daya duk da yasan da rana ne Babu abinda zai iya faruwa.

Saukowa yayi shirye cikin navy blue yadin cashmere haskensa da haibansa ya fito sosai hakama kamewa da nutsuwansa,

Qamshinsa Kawa bayar musu a palon Bai tsaya yayi breakfast ba ya fice.

Yana fitowa harabar gidan Tini aka Bude masa mota ya shige suke tada motacin suka fice bayan Jameel ya bawa securities tabbacin su Saka ido sosai kome suka Gani su kawai dashi.

#MAMUH#

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

32

*************

AmatulMaleek na fitowa bullowa palonsu su Farida na palon suna aiki shiyasa ta Jin Dan qarfin halin iya shiga dakinta har lokacin zuciyarta a Bata bugawa daidai ta Bude dakin ta shige.

Farida da karima Satan kallanta sukai ganin kofar data fito Kuma daga ita Se towel Amma ko dagowa su kalla Basu Isa ba sun sani.

Tana shiga dakin toilet ta nufa da sauri ya shige tareda rufewa Yana sakarwa kanta ruwa.

Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana Jan numfashinta Dake Neman shidewa cikin ruwan dayake saukar mata,

Ta jima a Hakan kafin Wani irin kuka me sanyi ya zuwar mata tana Jin kaman batada kowa,

Jin takeyi ko Husnah da Bata tareda mahaifiyarta Bata kaita maraicin uwa ba,

Bata taba Jin damuwan yanda maamah take fifita kulawan Husnah akanta ba sai yanzu,

Ina zata Saka rayuwart gameda wannan kaddarar Dake farautarta?

Batada tabbacin zata ringa tsira daga wannan mummunan kaddarar koyaushe,

Dan uwanta da Haydar dinta dasuke ture damuwar kowa su tsayu a tata basa tareda ita,

Mahaifiyarta Bata tareda ita Yaya zatai da wannan mugun abun dayake bibiyanta?

Da ASH TALBA Baya gidan a Daren zata iya mutuwa sbd tashin hankali da firgicin data samu kanta.

Kuka tayi sosai a toilet din idanuwanta suka kumbura sukai jajir kafin ta bawa kanta hakuri ta fito jiki ba qwari.

Dayake su Farida sun gyare dakin sunyi komai kafin ta fito sai Babu alaman komai na abinda ya faru jiyan

Sanyin AC da qamshin me dadi ne kawai yake tashi cikin dakin.

Batada karfin tsayawa shirywa gaban mirror Dan haka ko Mai Bata iya shafawa ba body mist kawai ta iya shafawa ta Saka Riga da wando masu Dan kauri ta koma kan gadonta ta Haye ta kwanta Dan ko apatite na cin abinci batada shi.

Daki karima ta kawo mata abincin ganin bata fitoba,

Yanda karima ta ajiye abincin har Azahar tayi Yana gurin ajiye Bata iya saukowa taci ba.

Sallan Azahar tai tayi addua sosai tana hawaye tana fadawa Allah damuwarta sbd batasan ma Yaya zatayiba.

Shiru shiru Bata fitoba duk ayyuka da abincin dasu karima sukaita kawowa suna jerawa Bata Ciba,

Kowacce daqiqa Daya idan ta wuce yammaci na kusantowa tareda dare tsoro ne yake cika zuciyarta.

Ana yin laasar ASH ya dawo gidan sbd hankalinsa Daya rabu biyu,Rabi akan aiki da tafiyan Dake gabansa a gobe Rabi Kuma akan Amatun Dake gida ba kowa hakama Yana tinanin tinda su Husnah Basu dawoba Kuma gashi kusan sati biyu koma fiye zasuyi yanason turata ta bisu Amman Kuma case da Akai na Faisal da familyn yasaka Bayajin zuwan nata acan yanada amfani,

Farha Kuma baijin tanada karfi ko iKon da zata iya tare Amatun idanma akace ta dawo gidan kafin dawowansu.

Jin shigowan motocinsa gidan ya Sakata Dan Jin sauki Sauki a tareda ita harta iya Dan daurewa taci abincin kadan Amma har lokacin ta kasa kunna wayarta sbd Batasan me zata fadawa maamah ba bayan tasan koma yayane itama tana buqatanta,

Ana yin magrib ta tashi jiki ba qwari Tayo alwala ta fito jikinta na tsananta sanyi hakama Kwanciyar hankalin zuciyarta na lalacewa sbd ganin duhu Dake Sako kai.

Kafin sallan ishai sbd ragewa Kai firgici da tashin hankalin datake ciki ta fita zuwa kitchen din dayake palon Dan dafa masa tea din data Saba dafawa a kwanakin.

Tinda ya dawo Bai fito ba sai da Akai kiran sallan magrib ya fito sanyeda dark ash jallabiya me tsananin santsi da taushi qamshinsa na Dan tashi ahankali ya nufi masallacin gidansa

 kana ganinsa kasan hutawa yayi yanda ya kamata shigarsa gidan sbd bacci yayi bayan ta tashi wanka yayi ya shirya ya fito sallan.

Ma’aikatan gidan nasa suna ganinsa duk suka miqe suna tasowa ya daga musu hannu Yana Dan girgiza Kai a natse Yana cewa

“No,muyi sallah tukuna shine a gaba”

Gaba sukai zuwa cikin masallacin suka bi sahu Dan tada sallah.

Naufal Dake dakin mum Aisha cikin azababben duhu da zafi sbd komai a kashe yake hakama baida iKon ko motsawa bare kunna Wani abu a dakin asan akwai mutum ciki,

Azababbiyar yunwa da tsoro ne fal cikeda zuciyarta sbd Bai tsaya tinanin komaiba ya shigo gidan gashi fita ta gagaresa hakama a kunnuwansa yaji umarnin ASH na a harbe duk abinda aka Gani mutum ko Dabba ko aljan,

Daqyar yake iya motsawa sbd wahala da yunwa da tashin hankalin yanda zai fita yabar gidan.

Kaman Wanda baida kafafu a iska yake tafiya haka ya fito dakin Dan Daman dakon su shiga sallan magrib yakeyi duk da yasan akwai christians a ciki securities din da basa sallah suna tsare da Gidan amman dai ficewan bazata masa wuya ba tinda sunsan shi Dan gidan ne Kuma basusan shine ya shigo jiyanba da aketa nemansa.

Yana fitowa ya fara Sanda zufa na jiqasa koina idanuwansa kaman zasu fado ya fito Yana nufo hanyar kitchen da zata basa Daman ficewa da sauri.

Adaidai lokacin ne ita Kuma AmatulMaleek tana kitchen din ruwan zafin dayake Kan gas din yakusa tafasa Dan haka ta juya ta dauko flask kenan sukai arba da juna ya shigo baisan da itaba itakuma ta juyo Bata San da Shiba.

Sakin flask din hannunta tayi gabaki daya jikinta na daukan rawa ta Bude Baki da karfi zata Saki ihu

A rikice ya fizgo butan ruwan zafin Dake kan gas din Yana watsa mata ruwan tayi saurin yin Baya tana juyawa ruwan ya sauka a bayanta cikin matsananciyar azaba ta saki ihu me karfi shi kuwa ganin komai na Neman lalace masa ya tafi lahira ba shiri ya sanyashi cikin rudewa da tashin hankali Yanke shawarar bankawa kitchen din wuta yanda kafin a biyosa sai an tsaya cetan Amatun ya samu ya gudu.

Qananun towels da aprons dake Jere a kitchen din ya fizgosu duka ya jefa kan wutar gas din Dake ci Yana sake kwaso wasu kayan duk ya zuba

Yayo kanta tana zube qasa bayanta da gefen wuyanta da ruwan zafin ya taba suna Wani irin azababben azaba baiyi wata wata ba ya daga hannu zai mareta karima data shigo kitchen din ta qwalla qara me karfin gaske tana ambatar wuta.

Hayaqi da duhu tini ya cike kitchen din hakama wutan sosai ta kama duk da ruwan Dake kokarin kashe wutar Amma Sam abin ya gagara ga gas.

Ihun karima ya Saka Naufal bangajeta Yana fitowa da gudu yayi Baya,

Daidai isowan ASH su Jameel da securities na bayansa Kai karima Dake rawar jiki tana kuka ya kalla yace

“Abeeda fa??

Shiru tayi tana zare ido a rikice sbd batasan waye Abeedan ba Dan haka Bai tsaya sake Batawa kansa lokaci ba ya fada cikin kitchen din da wutarsa ta fara yawa sosai.

Cikin saa a kofa yayi tintibe da ita ya sunkuya ya daukota gabaki dayanta Yana fitowa

Muryansa a Bude abinda kowa baitaba jiba yace

“Kota yaya karya fita gidan Nan ku harbesa idan yaqi tsayawa”

Aikuwa tini suka bi bayan Naufal a tsiyace kan kace me Yana Neman guduwa ASH da Amatu ke jikinsa har lokacin cikin sautinsa Daya sake gigitasu yace

“Ku harbi duka qafafun bastard din,duka biyun ku harbesu”

Aikuwa take suka sakarwa kafafun Naufal din wuta kowacce harbi daddaya sukai mata take ya zube a gurin bayan Wani mahaukacin ihun Daya saki Yana cewa ya mutu.

Jameel ne ya Bada umarnin a kira ambulance ta daukesa zuwa asibiti hakama a kira Police suyi handing case dinsa su sungama dashi.

ASH juyawa yake Neman yi zuwa cikin gidan da ita Amma tini wutar tayi qarfi Ashe Dan haka da sauri akai Baya ana kokarin zare cylinder na gas da wainda suke Jere a bayan kitchen din ana ficewa dasu.

Gobara dai sosai da sosai ta kama gidan Dan haka dole aka fitarda mota aka dauke ASH daga gidan tareda Amatun kafin asamu kashe wutar before ta kama koina gidan.

Kai tsaye gidansa Hilton aka wuce dasu sbd duka gidajensa Dake garin akwai mutane a cikinsu haya ne da dai sauransu,

Ko kafin su Isa Jameel yayi making reservation Dan haka suna Isa Kai tsaye batareda sunbi ta main hall ba suka hau lift zuwa suite da aka kama.

Kwantar da ita yayi Yana taba jikinsa wayarsa Bata tareda shi Dan haka dole da landline yayi amfani ya buqaci likita ko nurses.

Babu Bata lokaci nurse biyu suka iso dakin tareda Neman izinin shigowa.

Suna shigowa da hannu Daya ya nuna musu inda Amatun ke kwance tana motsawa a hankali ta farfado sedai radadin datake ji abayanta da wuyanta.

Dubata sukai cikin kulawa sosai sukaga konuwar bata Riga ta taso ba Dan haka cream na qonuwa kawai suka bayar tareda Dan maganin zazzabin dayake Neman rufeta jikinta na rawa.

Bayan ficewarsu daga shi har ita Babu Wanda ya motsa bare magana,

Bacin Rai da fushi me tsananin gaske ne a cikin ransa Amma a Fili Babu me iya gane Hakan.

Ita kanta rawar da jikinta keyi da azaban datake ji yasa ta kasa ko dogon motsi Se hawaye masu dumin dasuke bin fuskarta.

A haka lokaci me tsayi ya tafi kafin ya miqe ya shige toilet sbd alwalan sallar ishai da Akai tin kafin isowansu.

Yana idar da sallah Jameel na zuwa ya kawo masa wayoyinsa da duk abubuwan buqatansa tareda sanar dashi an kashe wutan hakama masu aikin suna Nan Babu abinda ya samu bangarensu.

Maganar tafiyarsu gobe da safe yakeson yayiwa ASH din Amma baiga fuska ba sbd ran Maza a bace yake shine kadai yake iya gane tsananin bacin ran ASH din.

Shiru yayi tareda yimasa saida safe ya wuce Yana fidda wayarsa Dan siyawa Amatun ticket itama tinda dai Babu yanda zaayi Takoma gidan a wannan halin din da Naufal angama da matsalarsa bayajin har abada zai sake tafiya da duka qafafun biyu sedai Daya idan anyi dace ma kenan.

Mansion din ya sake komawa ya Saka karima dubo masa handbag din Amatun me daukesa wallet nata na Id cards da komai Yana Karba ya fito Saida yafara siyan ticket nata na tafiyan nasu kafin ya wuce gida Dan tafiyar safe zasuyi zuwa Lagos kafin daga can su zasu wuce Ghana.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

33

***************

Sallah takeson miqewa tayi Amma gaba Daya qafafunta basa iya daukanta sbd halin datake ciki ko iya miqewa ta tsayun ma da qafafunta Bata iyawa dole ya juyo ya zuba mata idanuwansa a natse kafin ya taso tinda Babu yanda zaiyi da ita bayan taimaka mata dole,.

Tausayi take bashi sosai sosai sbd baitaba tinanin akwai kafiran aljanu mahaukatan acikin kan Naufal da zai iya tinanin taba matar aure ba,matan auren ma tasa da aurensa igiya uku yake kanta,

Tabbas zai basa darasin da mata duniya duka sun fita ransa kenan Koda ta aurensa ce kuwa.

Toilet takaita ya ajiye ahankali Yana kokarin juyawa idanuwansa suka sauka kan fatan wuyanta da Dan gurin da ruwan zafin ya taba ta ya Dan fara tashi kadan.

Dauke idanuwansa yayi daga kallan gurin tareda sakinta ya juya ya fice Yana tinanin likitan da zata Gani kafin ya wuce.

Kasa kuka tayi sbd hawayen nata kaman Suma sun gaji sun qafe Dan haka jiki a sanyaye hannuwanta na Dan rawa tayi alwala ta fito tana dafa Bango daqyar.

Ko data fito makeken lafiyayyan dakin  ta Dan kalla Taga batama San inda zata kalla tayi sallan ba gashi babu komai a tareda ita.

Kasa fitowa tayi daga quryan ta warware Dan kwalin kanta ta yafa ta Dan dudduba sai alokacin Taga inda yayi sallah abin sallan na gurin ta Isa gurin ta zauna sbd bazata iya sallan a tsaye ba jiri takeji sosai da zazzabin gaske.

Tana idarwa ko addua Bata samu damar yi ba ta zame a gurin ta kwanta tareda shigewa cikin doguwar rigar jikinta sanyi na dabaibayeta ta koina.

Jin shiru Bai shigo dakinba har Saida dare yayi sosai Yana zaune idanuwansa jajir Babu abinda yake cin zuciyarsa sai zafi da bacin Rai me tsananin gaske.

A natse ya Bude dakin ya shigo ganinta qasa a dunqule tana rawar sanyi cikin baccin azaba da dole.

Numfashi me dami mara sauti ya sauke tareda takowa ahankali Yana dauke kallansa daga kanta ya sunkuya a natse ya dauketa ya nufi gadon dakin da ita ya kwantar ahankali.

Abin rufa yaja ya rufe mata Rabin jikinta kaman zai miqe sai Kuma ya Dan dakata ya juyo tareda Kai hannun ya Dan juyar da fuskarta gefe ya Kalli wuyanta inda qonuwar take Dan sake tashi kadan kadan.

Idanuwansa dasuka Dan yi ja ya dauke daga gurin tareda Saka gadon ya nufi inda maganin da aka bayar yake ya dauko ya dawo.

Bude maganin yayi a natse tareda Dan matsowa kadan a yatsarsa ya nufi gurin Yana son shafawa a ciwon Amma baisan tayaya zai Kai hannunsa jikinta dinba batareda ta Farka ba.

Ganin ba Wani mafitan bayan Hakan ya sanyashi Kai hannunsa a fatar wuyan nata ya Dora yatsarsa ahankali ya shafa akan gurin…..

Azabar zafin maganin dataji cikin bacci ya Sanyata qanqamesa da qarfi jikinsu na haduwa sosai batareda tasan tayi Hakan ba.

Saukan numfashinta me zafi kan wuyansa ya sanyashi dakatawa daga shafawan tareda kokarin janyeta daga jikinsa Yana mayarwa kwance

Itama ahankali ta Bude idanuwanta cikin bacci da zafin zazzabi ta kallesa batareda ta iya cewa komaiba saima radadin datake ji gurin Daya shafa maganganin.

Miqewa yayi Yana Jan tissue Dake gefen gadon Yana goge yatsar hannunsa ya shige toilet.

Ko kafin ya fito ta sake komawa bacci me qarfi Dan haka Shima kan sofa yaje ya zauna Yana daukan wayoyinsa Dake kashe ya Kalli time Yana sake shiga tinanin yanda zaiyi da ita din,

Gashi baida niyar abari maamah tasan abinda yaso sake faruwa da ‘yarta hakama ya Hana abari duniyama kwata kwata tasan abinda ya faru a karo na biyun da ita Tako Ina yace a toshe zancen.

Asuba nayi yayi sallah ya kwanta a sofa cikin lafiyayyar duvet me taushi sai a lokacin bacci ya Dan daukesa sbd ciwon kan Daya kwana a zaune Yana yi Yana tashi dubota shiyasa baiyi baccin ba har Asuba.

Sai guraren 7 ta Farka a hankali jiki ba qwari ta yaye rufar jikinta tareda tashi zaune tana sauke numfashi ganin inda take komai na masifar jiyan na dawo mata.

Qafafunta ta ziro qasa ta miqe tsaye jiri na son dibanta sbd rashin karfin jiki.

Toilet ta nufa sbd batama dauka Yana dakinba kwata kwata,

Shiga toilet din tayi ta tsaya gaban madubi tana kallan wuyanta inda qonuwar take gaba Daya ta tashi.

Tsoro taji ya kamata sedai batada Wanda zai dubeta dole ta janye daga mirror din bayan ta dauki sabon brush tayi brush,

Fitsari da alwala Tayo ta fito tayi sallah bayanta da wuyanta na mata ciwo sosai.

Gadon ta koma ta kwanta bayan ta gama sallan sbd wutar ta tashi har ta bayanta.

Tana kwantawa hawaye suka fara gangarowa daga idanuwanta masu zafi,

Bata tareda wayarta bare ta kira Abdulhameed taji sanyi ko ta San matsayar rayuwarta,

Da Babu aurenta akan Dad dinsu Haydar da Yaya zaiyi da ita a irin wainnan lokutan da masifar rayuwarta take bibiyarta?

Shin dagaske dai yanzu shine mijinta da zai Bata kariya da kulawa tareda tsaya mata ake nufi ko me?

A wannan tinanin tayi Nisa tana hawaye har Wani baccin dole ya sake dauketa.

Bacci sukai sosai da lokacin tafiyarsa yazo kusa sosai batareda saninsa ba,

Dukkanin wayoyinsa Mr Jameel ya kira Amma basa shiga gashi flight din 10 zasubi.

Dole ya shirya komai na tafiyan tareda kawo masa kayansa itama Amatun dole Farha ya kira taje ta hado masa kayanta a qaramar lv luggage ta kawo masa ya taho musu dasu.

Bell din dakin mara qara yayi ringing ya tsaya jiran a Bude.

Shiru ba Wani motsi Dan haka ya sake dannawa a karo na biyu.

Time yake kalla ya sake dannawa.

Cikin bacci ASH yaji qarar na tashi kadan kadan ya Bude idanuwansa Yana Dan motsawa ahankali.

Numfashi ya sauke tareda ajiyan zuciya kafin ya janye rufarsa ya Sako qafafunsa qasa ya miqe tsaye Yana nufan kofan.

A natse ya Bude

Mr Jameel na ganinsa ya Dan dauke idanuwansa daga kansa cikin girmamawa yace

“Good morning,barka da safiya”

Da Kai kawai ya amsa Yana kallan kayan dayake janye dasu.

Cikin nutsuwa ya Dan tiro akwatinan ciki Yana cewa

“Kayan Ms AmatulMaleek ne,Se naka flight dinmu na 10 ne,naso cancelling mubi na yamma Amma can nayi magana nasu kafin Hakan Amma baqin sun Riga sun iso dole na 10 din zamu bi”

Juyawa kawai ASH yayi sbd kansa dayayi nauyin ciwo bazai iya tsayawa magana ba.

Mr Jameel kuwa qasa ya koma inda motocin Daukan ASH din suke suna jiran fitowan tasa.

Kai tsaye Yana shiga ita ya kalla yaga bacci takeyi Amma da alama tayi sallah ganin abin sallan a shimfide.

Wanka ya shiga da kayan amfaninsa da mr Jameel duk ya hado a luggage dinsa sanin komai na ASH din akan kaida da tsarinsa yake,

Shikuma ASH din gaba Daya kusan rayuwarsa tin daga lokacinda matarsa ta fara ciwo tsawon wannan shekarun Mr Jameel ne ke kulawa da duk wata lalurarsa,

Shine ya maye kusan duk Wani gurbi na bangaren kulawa da buqatun Daya kamata ace daga iyalinka kake samu,

Komai nasa Mr Jameel ne,

Duk wata buqatansa idan aka cire abincin dayake ci a cikin gidansa tareda iyalinsa to Mr Jameel ne yake kulawa da komai nasa,

Ita kulawa a rayuwarsa da tattali Wani abu ne da Sam a rayuwarsa yanzu baima San dasu ba bayan aiki,aiki,aiki kawai,sai tafiye tafiye su kawai ya sani,

Amma Jin dadin iyali, Kwanciyar hankali da hutawa a cikin familynsa Wani abu ne da Sam baisan dashiba a aynzu Kuma Bai damuba sbd Daman can baisan dadin Hakan ba bare rashin Hakan ya damesa.

Wanka yayi Bai fito ba Saida ya goge jikinsa da towel a bathroom din kafin ya Dan yi abubuwan da zaiyi ya fito ya shirya.

Qamshinsa Daya gauraye iskan dakin gabaki daya cikin sanyi da nutsuwa ya Sakata Bude idanuwanta da suka kumbura ahankali Basu sauka koina ba sai akan kyakkyawar fuskarsa dayake nufo gadon Dan tayar da ita.

Ganin Bude idanuwanta ya sanyashi dakatawa ya tsaya Yana kallan idanuwan sunyi kumburi sosai.

Yanda idanuwansa suke akanta ya Sanyata kasa ko motsawa tana yin qasa da idanuwanta.

Ahankali ya Bude Baki ya furta

“Yaya jikin?

Yaya pain na qonuwar?

Akwai zafi haryanxu?

Yanda ya jero tambayoyin ya Sanyata Dan dago idanuwanta datai qasa dasu ta Bude Baki cikin sanyi ta iya furta

“Da sauki”

Hakan kawai ta fada tana dagowa daga kwancen datake.

Akan wuyanta ya saukar da idanuwansa yaga yanda wutan ta tashi sosai.

Qonuwan ya kalla ahankali yaga ta gangara daga wuyanta har cikin rigarta,ya dauke idanuwansa ahankali daka gurin sbd ganin inda ta qonuwar ya nufa.

Juyawa yayi ya fice ya dauki wayoyinsa a inda ya kwanta batareda ta kunnasu duka ba ya dauka Daya y kunna sbd waya da zaiyi.

Toilet ta sauko ta nufa tayi wanka itama acan ta goge jikinta ta fito ta Sanya daguwar Riga mara Fadi sosai tana Dora gyalen akanta mr Jameel na sake ringing bell na dakin Dan haka Kai tsaye ASH ya miqe ya shigo yace ta fito.

Fitowa tayi a natse jiki ba qwari

Shi kuwa Mr Jameel shigowa yayi ya kama akwatinan yaja ya biyo bayansu.

Koda suka sauko kafin ma ya iso aka Bude masa motar ita yafara nunawa ta shiga kafin Shima ya shiga aka rufe Mr Jameel ya Saka kayansu a Bayan dayar motar suka ja cikin Dan gudu suka wuce sbd sunyi late sosai.

Mr Jameel Daya rasa tayaya zai tambaya ASH din maganar Amatun da yanda zasuyi da ita dole shiru yayi,

Shikuwa ASH gaba Daya tinda suka shiga motar waya yakeyi cikin nutsuwa da kalamai na Kai tsaye Dan haka shaf ya manta da dole ana buqatan sanin inda zasu Kai Amatun kafin ya dawo.

Kai tsaye airport suka nufa

Suna Isa aka fito da komai sai alokacin ya Kalli Amatun a hankali tareda kallan Mr Jameel kafin yayi kowace magana Mr Jameel cikin girmamawa da yace

“Na Siya mata ticket already sbd tinanin da ita zaayi tafiyan”

Zuba masa fararen idanuwansa yayi a karo na farko Dayaji Yana buqatan daga tafiyansa Amma Kuma ba halin Hakan sbd baqin dazai Gani nada mahimmanci sosai.

Juyawa yayi ya Kalli Amatun wadda aka budewa mota ta ziro qafafunta ta fito ahankali jikinta gabaki daya a sanyaye duk da gaba Daya tinaninta gurinsu maamah zaa kaita.

Kyakkyawar fuskarta tayi fayau sai kumburin idanuwanta dasuka bayyana.

A jikin jikinta zafi takeji na konuwarta gashi kusan inda hook na bra dinta yake akwai konuwa a gurin ma Dan haka a matse take takai inda zata ta xare kada azabar tayi mata illa.

Tana fitowa Mr Jameel ya Ciro kayansu suka ya biyosu suka jero ASH na sake amsa wata wayar a natse da rashin tada sauti sosai.

Dayake sunzo late ne suna shiga jirgin ya fara kokarin tashi.

A first-class suke Dan haka suna tashi breakfast aka kawowa Amatun shikuma tea kawai ya buqata Yana duba wasu bayanai a iPad.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

34

**********

Bata Wani iya cin abincin sosai ba sbd Dan takuren datake acikin jikinta zafin jiki data a ciwon takeji sosai duk da sanyin mara qarfi Daya gauraye gurin ba takura.

Tana gama Shan black tea da butterbread sai wasu abubuwan dama Bata damu da Cinsu ba su meatballs da lettuce tomato sauce Dan haka meatballs din Daya taci ya isheta aka tattare gurin ta lafe ahankali jikin inda take tareda lumshe fararen idanuwanta tana shaqan qamshinsa dayake kusa da ita ahankali.

Bai juya ya kalletaba sbd hankalinsa na kan abinda yakeyi Saida suka Isa ya ajiye iPad din hannunsa tareda juyowa a natse ya sauke idanuwansa akan fuskanta Da idanuwanta ke rufe tana bacci.

Yanda zai Bude Baki ya ambaci sunanta ne yaji bazai iyaba Dan Hakan ya Dan Kai hannunsa Daya a natse kan fuskarta ya taba ahankali yaji zafi sosai.

Da Dan mamaki ya sake juyowa da kyau ya kalleta Yana sake taba fuskan nata yaji zafin sosai ya tabbatarda zazzabi ne ajikinta sosai tanada qonuwa ya kamata ace Tasha magani da safen.

Rintse idanuwansa yayi a hankali ya Bude sbd rashin Shan maganin nata be kamata ba.

Miqewa yayi tareda tsayuwa gabanta ya ranqwafo ahankali zai taba fuskarta ta tashi Yana Dora hannunsa akan fuskan nata tana Bude idanuwanta ahankali cikin kasalan zazzabi ta zuba masa fararen idanuwanta da sukai laushi batareda ta motsaba.

Ganin Hakan ya tabbatarda tayi weak,

Ahankali ta motsa tareda miqewa tsaye suka nufi kofa,

Ko taku biyar bataiba jiri ya Dan debeta saijinta yayi ta riqe hannunsa.

Bai waiwayo ba hakama Bai Dena tafiya ba sedai dole tafiyansa da nata suka daidaita sbd hannuwansu dayake hade.

Mr Jameel Daya rigasu fitowa tini yayi gaba da kayansu

Motar da zata daukesu tini tana airport din Dan haka Kai tsaye driver da sauri ya fito ya Saka kayan a Baya Mr Jameel budewa ASH motan suna isowa ita aka fara shigarwa kafin shi ya shiga suka bar airport din.

Bata iya dagowa kallan koina bare tasani ko fahimtar inda take Dan haka har suka iso wani luxury lodge din dayake masaukinsa a lag Bata saniba.

Wannan Karan ma hannunta a cikin nasa suka fito Kai tsaye zuwa room nasa.

Koda suka Isa kwantar da ita yayi ya fito inda Jameel ya ajiye kayansu a palon yayi ciki dasu.

Alwala kawai yayi ya fito zasuyi sallah su wuce ana Jiransa.

Kafin ya fita nursu ya buqata aka Turo yabar kulawan Amatun a hannunta.

Bayan tafiyansa ita kanta nurse din buqatan Amatun ta cire kayanta tayi Daman a tsakanin matse take Dan haka ta cire kayan idanuwanta na tsiyayo da hawaye sosai ga zazzabi ga azaba tanaji ga batada kowa sai ASH din data kasa sakewa ko yarda da shine mijinta haryanxu Amma gashi ana tilastata karban Hakan Dan kuwa a lokacin da take Neman makusantanta shine kadai Wanda take samu.

Hatta bra Saida ta cire tayi wurgi da ita hawayenta na sake gudu

Kallan gurin data Dan Kone din nurse tayi tana mata sannu duk da ba wasu guri manya bane Kokuma da yawa Yan qananu qananu ne Kuma ba sosai ba Amma dayake boyayyun guri ne rufen dasuke shine zaisa ta wahala Amma da suna Shan iska sosai zasuyi saurin warkewa.

Dan gogggoge mata tareda Shafa mata magani tayi kafin ta Bata magani ta taimaka mata tayi sallah tana idarwa ta kwanta ta duqunqune sbd zazzabi.

Bata jima da Kwanciyar ba bacci ya dauketa,

Bayan baccinta yayi karfi nurse din ta sake shigo quryan ta Dan Saka hannu ta yaye mata bargon zuwa qugunta sbd a kife tayi Kwanciyar dole Dan haka ta yaye mata bayan har zuwa qugunta sbd bayan yasha iska.

Har yamma tana baccin nurse kuwa tana Palo tana gadinta.

Ahankali ta motsa tareda Bude idanuwanta tana sake motsawa ta tashi zaune kafin ta sauko da qafafunta ta miqe tsaye jiki ba qwari ta Isa toilet Tayo alwala tazo tayi sallan laasar da Akai tini.

Tana idarwa nurse na sake leqowa Taga AmatulMaleek din ta tashi Dan haka ta fito takira ta buqaci akawo abincin dakin Sir ASH TALBA din.

Babu Bata lokaci saiga abincin Anzo an Jere a dining kusan har abinda Baci zataiba ankawo an ajiye.

Sam batasan cewan tareda shi zasu zauna a dakinba ya Sanya da nurse tace kada ta Sanya kayan da zai taba gurin wutan sai ta Sanya vest mara nauyi kawai da wandon pyjamas dinta me santsi.

Sama sama ta Dan ci abincin tana gamawa lokacin sallan magrib nayi tayi sallan tareda daurewa ta sake dawowa ta zauna

Nurse lokacin tafiyanta yayi Dan haka tayiwa Amatun sallama ta tafi.

Bayan tafiyarta shiru ta zauna tana Dan kallan tv sama sama Amma hankalinta kusan gaba Daya Baya Kai.

Lokacin ishai na yi ta tashi tayi ta sake zaunawa shiru shiru

Zuwa 9 taji zazzabinta na Neman dawowa.

Miqewa tayi ta nufi daki tayi wanka tana fitowa ta Saka wata vest din mara nauyi ta kwanta.

Bacci na daukanta Yana dawowa,

Gurinta ya nufo Kai tsaye ya tsaya kanta a natse tareda Kai hannu ya taba fuskanta yaji har lokacin da zafi.

Dan Bata fuska yayi cikin mamakin ya Akai Hakan bayan yabada tabbacin nurse ta kula da ita yanda ya kamata Amma ace zazzabin be sauka ba.

Cire hannunsa yayi tareda juyawa yaje ya ajiye wayoyinsa tana zare takarminsa zuwa slippers ya nufi toilet.

A gajiye yake Dan haka ruwan dumi sosai yayi wanka dasu qamshin Aesop dinsa ya gauraye bathroom din gaba Daya har zuwa dakin.

Da bathrobe ya fito bayan ya tsane jikinsa daga can,

Body oil da qamshi kadan ya Saka ya Sanya pyjamas ya fita zuwa dining.

Abinci ya Dan ci kadan yasha ruwan zafi sosai kafin ya miqe sosai yake Jin gajiyan Tin shekaran jiya da kwanan sofa da yayi jiyan data yau.

Anan din Kuma Babu doguwar sofan da zai iya kwanciya akanta Dan haka Kai tsaye dakin ya nufa Dan ko a mafarki baimasan Yaya ake kwanciya a qasa ba bare ya kwanta and sosai yake buqatan hutawa afterall kwanciya gado Daya for now shine only mafita Kuma Hakan Baya nufin komai.

Hasken koina ya rage ya kashe wayoyinsa ya nufo gadon da kusan fadinsa ya cinye fiyeda Rabin dakin ya  zauna Dayan gefen batareda ya juyo ya kalleta ba kafin ya zare slippers dinsa masu taushi ya hau gadon a natse Yana mantawa da akwai Wani bayanshi Akai ya kwanta tareda lumshe idanuwansa bayansa na samun nutsuwa yanda ya kamata adhkar dinsa a zuci bacci ya daukesa ba jimawa.

Karfe uku saura na dare tafara kuka tana ambatar sunan maamah da Abdul da Haydar cikin zazzabi da zafin datake ji na konuwar sbd duk ta sabule Yan kananun konuwar da rigar jikinta cikin bacci.

Kukan datakeyi tana mutsu mutsu ya Sakasa Bude idanuwansa ahankali cikin bacci tareda motsawa kadan yana tabbatarda kukan nata ne.

Har qasan zuciyarta kukan ke fitowa tana ambatar sunayensu musamman Abdul da Haydar tana cewa Dan Allah su dawo tana buqatansu maamah ta tafi da Husnah ta barta.

Bayanta da wuyanta take tabawa cikin hawaye da kukan mara sauti sosai tana Jin batasan Yaya zatai da rayuwartaba.

Tashi zaune yayi ahankali tareda Dan kunna haske kadan yakai hannu ya yaye abin rufar a hankali yaga yanda takeyi da alama wutan ne yake mata zafi.

Haske ya Dan qara kadan ya Kalli time yagani,

Zuro qafafunsa yayi daga gadon ya zira slippers ya miqe tsaye tareda nufar Palo ya dauki waya yakira lodge din ya sanar musu Yana buqatan likita ko nurse.

Babu likita available sedai nurse Wanda namiji ne a yanzu,.shiru yayi kafin ya aje wayar kawai batareda Yama iya Basu amsa ba.

Juyawa yayi ya koma ciki.

Zuwa lokacin itama ta tashi zaune hawayenta na qara gudu.

Ganinsa ya Dan Sakata Jin sanyin ko zata mutu zata mutu a kwai na gida a tareda ita Dan haka tayi qasa da kanta tana safe fashewa da kuka kawai bakinta na son Kiran su Abdul Amma ta kasa.

Kukan datakeyi ne ya sakashi qaraso gurinta sbd Bai taba ganin kukan mace haka ba,

Matarsa Abeeda Bata taba kuka a gabansa ba sbd batasan yaga rauninta hakama tsarinta ne Bata yarda yaga kukanta ba,

‘yarsa Husnah kukanta a gabansa na Neman wata buqatan ne Wanda Shima sai akan mahaifiyarta dakuma buqatanta na son dawowan Asmau ne tayi kuka a gabansa Amma ayau kuka ita yanzu takeyi a gabansa tin daga zuciyarta.

Tausayi da sanin dole tana cikin tsananin Jin ciwo gashi tana Neman mahaifiyarta datake tare da tasa ‘yar tana tattalawa batareda tasan halinda yarta take ciki ba gashi ya Saka an toshe duk hanyar dasu maamah din zasu San komai suna can sedai idan sun dawo ya sanyashi qarasowa gurinta a hankali ya zaune gefen datake yakai hannu ya Dora a wuyanta a hankali yaji zafi har lokacin.

Gurin qonuwar ya saukar da idanuwansa ya kalla yaga yanda duk ta goge gurin da alama da rigar jikinta.

Bude Baki yayi cikin kulawa da sauti mara dagawa sosai yace

“Sorry”

Sorry” din Daya furta mata ya Saka kukanta Dan qaruwa.

Maganin wutar ya dauko ya dawo ya sake zaunawa bakin gadon ta inda take ya budesa tareda kallan wuyanta

A yatsa ya zubo maganin kadan ya nufi wuyanta dashi ya Dora Akai tareda shafawa ahankali.

Daukewa kukanta yayi ta dago hannunta ahankali ta Dora kan nasa Dake gurin ta riqe jikinta ba qwari ga tsananin zafin maganin Daya shigeta.

Yanda ta Dora hannunta akan nasa ta riqe ya sakashi dakatawa tareda dago idanuwansa ya kalleta ita Kuma ta rufe nata cikin sanyi tana qarasa gangaro hawayenta dasuke cikin idon.

Hannunsa Daya yakai kan nata din ya janye Yana sake shafa maganin a gurin..

Gaba tayi tana qoqarin janyewa ya tareta da Dayan hannunsa ta hanyar zagayota da hannunsa ya dawo da ita wannan karon bayanta saida ya Hadu da kirjinsa,

Daga shi har ita shiru sukai Babu Wanda ya motsa hakama Babu Wanda ya cigaba da abinda yakeyi.

Shine ya motsa ahankali tareda cigaba da shafa mata magani Bata janyeba sbd riqon da yayi mata sedai qanqame hannuwansa datai tana hadiye zafin man.

Hannunsa Dake zagaye da cikinta ya zame ahankali tareda dorawa akan  hannun vest din jikinta ya zamesa ahankali daga shi har ita kowannensu na dannewa da qarfin hali.

Saukar da hannun rigar yayi ya kama Dayan ahankali Shima ya sauke kafin ya dauke hannunsa rigar ta sauka daga jikinta zuwa cikinta da sauri ta hade kirjinta da bargon dayake Rabin jikinta tana rufe idanuwanta ahankali.

Farar fatar lafiyayyan bayanta ya zubawa ido Babu tabo ko Daya bayan konuwar dasuke gurin,

Dauke idanuwansa yayi ahankali daga Kai kafin ya fara shafa mata maganin ahankali tana tsiyayo hawaye sosai tana qanqame jikinta Wanda ya sake sakajin kaman ya rage mata radadin daga jikinta.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

35

**************

Kasa dagowa tayi a shafa maganin saurin gurin dayake ta gurin muyanta daga gaba zuwa kirjinta daga sama saman,

Shi kansa bayajin Yana buqatan shafawa har can din duk da ya lura akwai konuwar har agurin Amma Kuma bazai iya barinta taci gaba da Shan wannan wahalan konuwar ba,

Ahankali ya Dora hannunta a kafadanta zai juyo da ita tayi saurin rufe idanuwanta tana kasa juyowa sedai batada qarfi ko kuzarin iya Hana kanta juyowan.

Juyowan da yayi da ita har lokacin hannunta Daya nakan kirjinta data rufe da abin rufa.

Shi kansa Bai kalleta sosaiba gurin kawai ya kalla Yana Kai hannunsa ya shafa maganin ahankali,

Rintse idanuwanta ta sake yi tana juyar da kanta gefe cikin sanyi sedai juyawanta ya Sanya numfashin data fitar me dumi ya sauka acikin wuyansa a hankali.

Shiru yayi tareda dakatawa daga shafa maganin Yana dauke hannunsa daga jikinta batareda ya Kalli fuskartaba ya gyara mata Kwanciyar tareda saukowa a natse nufi toilet ya wanko hannunsa ya goge ya fito tareda kashe wutan dakin ya koma ya kwanta batareda kowa ya sake motsi a dakinbata suka koma bacci Wanda kusan Babu Wanda ya koma,sai guraren asuba ita ta samu baccin ya dauketa shikuwa Saida yayi asuba ya koma baccin.

Saida gari ya fara haske ta samu tayi sallah ta kasa komawa kan gadon ta fito Palo ta zauna shiru tareda Nisa a tinani daga qarshe a kan kujera bacci ya sake daukanta a zaune.

Qamshinsa Daya cika hancinta ya farkar da ita tareda tabbatarda Shima ya tashi Dan haka ta tashi tana Dan gyara zamanta ko gama wartsakewa bataiba ya fito a shirye kyakkyawar fuskarsa sai daukan ido takeyi komai nasa a tsare kudi ne kawai ke nuna kansu a jikinsa Tako Ina.

Idanuwansa akanta ya saukesu Ya kalleta tayi qasa da Kai cikin sanyi ta gaidasa.

Kafin ya amsa gaisuwar cikin nutsuwa jikinta ya fara tambaya ta amsa a natsen itama.

Abinci aka kawo zaa Jere ta miqe ta shige seda aka gama jerawa ta fito da kansa ya tsaya Saida Tasha magani bayan taci abinci kafin ya fice.

Bayan fitarsa ajiyan zuciya ta sauke ahankali ta Dan bari abincin ya fada mata kafin taje ta shiga wanka.

Ko data fito an gyare koina dakin sai qamshi da sanyi me dadi ke tashi koina Dan haka tana shiryawa da kanta ta shafa maganin inda hannunta yake kaiwa ta dawo ta zauna tana kallan dole sbd batajin rayuwartama gaba Daya Bata Kuma San me zatayi ba ga jikin nata da sauki ba laifi.

Ita kadai ta wuni idan lokacin sallah yayi ta tashi tayi ta dawo ta zauna ko ta kwanta ta tashi harsai yamma tayi yau da wuri ya dawo sbd jikin nata Dan haka Yana dawowa ta zauna Palo tasake shiga dakin ba Saida ya fito cin abincin dare.

A tare sukaci abincin ya sake Sakata Shan magani tana sha ta shige.

Wanka tayi ta kwanta take bacci ya dauketa,

Ya Dade be shigoba sai dare sosai ya shigo yayi duk abinda zeyi ya kwanta

Yau din Bata tashi ba Dan haka ya samu baccin nutsuwa.

Da asuba kusan tare sukai sallah Takoma Palo kaman jiyan Saida ya fita Takoma daki.

Yau dayake ya lura data ji sauki ba laifi bayan fitarsu mota aka Aiko ta fita da ita.

Batasan koina ba Dan haka yawon sama sama sukayo driver ya dawo da ita taci abinci kawai tayi wanka ta kwanta baccin Rana.

Ta Dena mamakin yanda maamah ta manta da ita zatace ko shareta hakama ta tsaya kallan rayuwar datake Kai a yanzu,

Abu Daya data tabbatar shine aure dai yahau kanta ko Bata so tinda har kaddara tasa ta kwana a guri Daya da mutumin da ko hanyar dakin baccinsa Bata taba bi ba a gidansa,.hakama Dad din Haydar  Kuma mijin amaniya yar uwar mahaifiyarta.

A cikin kwana biyu saima ta fara samun nutsuwa da Kwanciyar hankalin data rasa mansion,

Babu abinda takeyi sai hutawa duk da tana cikin damuwa wasu lokutan da kadaici tareda kewan maamah dasu Haydar.

Shi kansa yanzu ya gama abinda ya kawosa Dan haka tafiyarsa Ghana tana Dan Neman fasuwa Dan haka ya dakata tukuna su gama duba lamarin idan tafiyar zata yiyu ya wuce kada yayi saurin komawa Dan haka Baya fita koina hutawa yakeyi sosai Shima.

Bayan gaisuwa da serving dinsa abinci sai jikinta da kusan koyaushe shine abinda yake tambayarta Babu abinda yake hadasu.

Abu daya ne dukkaninsu suka kasa sabawa dashi ko sakewa dashi shine zama guri Daya da juna duk da shi a nasa bangaren me sauki ne Dan Sam mantawa yakeyi wasu lokutan da akwai wanzuwarta.

Ita kanta ta fahimci so da dama baya noticing na akwai mutum a tareda dashi Dan haka ta hutarda kanta daga takura na rakubewa.

Abu Daya ne yake Dan kokarin fara sabawa dashi a kwana biyun shine yanayin serving na abincinsa a natse datake da Kuma duk yanda ake kawo ruwan sanyi tana sauyawa masa zuwa mara sanyi batareda tasan cewan Daman bayason ruwan sanyin ba

Sai Kuma yawan kukan darenta da Shima ya fara sabawa dashi sbd haka kawai ko qaiqayi wutanta Daya fara warkewa yayi mata sai hawaye sbd ta Saba maamah kusan komai idan suna dakinsu ita ke Mata sbd a dakinsu ne kawai take uwarsu tana fitowa uwar Husnah ce Dan haka ya fara sabawa da wannan kananun motsin nata na dare Tana farawa farawa zai kama hannunta daya cikin nasa zatai shiru tana sedai Kuma shikenan baccinta ya Yanke haka nasa Se Kuma asuba shiyasa suna sallah suke baccin safe sosai abinda Sam Bai Saba dashi ba a rayuwarsa wato baccin na safe.

Ita Kuma a nata bangaren qamshinsa ne abinda hancinta ya fara sabawa dashi da kuka taushi da dumin fatar hannunsa da kusan duk dare yake kama Nata hannun.

Mr Jameel Dayaga Mai gidan nasa na samun hutun safe da Baya samu sai Hakan ya Sakasa Jin nutsuwa sbd babban farin cikinsa shine ASH din ya samu nutsuw ta rayuwa da Kwanciyar hankali,

Koyaushe rayuwarsa Babu kulaw daga inda y kamata sai aiki sai tafiya Dan haka ya ringa Jan maganar tafiya Ghana din bayan yasan ta lalace babuta Amma ya kasa tabbatarwa da ASH din haka Dan ya sake hutawa.

AmatulMaleek na buqatan kayan sawa Dan haka Koda mr Jameel yayi magana da Farha a waya ita ta zaba kayan da yayi shopping ta online aka kawo kallo daya Amatun tawa kayan ta ajiyesu.

Kayan baccin ciki kawai tayi amfani dashi dayake Riga da wando ne masu tsayi Kuma masu santsi duk da tasan zasuyi kudi sosai Amma dai basuda wani hayaniya.

Ahankali ahankali Saida suka share kwana Tara a lag din kafin suka dawo zuwa lokacin kusan duk yanda nesancinsu da juna yake ya Dan Ragu Dan kuwa so biyu tana waya da Abdul da wayar ASH din sedai bata iya magana da Haydar ba Shima Abdul din Bai bawa Haydar wayar ba sbd kada Haydar din yaga da wayar Dad dinsa Amatun tayi magana dasu.

Shi kansa Abdulhameed yayi mamakin jinta da wayar Dad din Amma Kuma ba Daman tambaya haka suka gama magana Sama sama.

Jirginsu ya sauka abuja kusan mota uku ce tazo daukansa daga airport din suka nufi sabon mansion dinsa Kai tsaye.

Batai mamaki ba sbd tayita jinsa a waya Yana maganar sabon mansion din da wasu abubuwan da Mr Jameel ke tambayarsa yanda zaayi.

Mansion ne me girma kaman wancan hakama wannan kusan shi kadaine ya  sama Se iyalinsa extra bedrooms din baqi da irinsu mum Aisha sune a qasa sai penthouse Dake can sama kwata kwata wannan gurin zuwansa ne shi kadai.

Maamah bangarenta na musamman Akai mata Palo and bedroom gefen bangarensu Haydar da Abdul idan sun dawo sai bangaren masu aiki a bayan nata.

Babu tsadaddiyar sabuwar rayuwar Jin dadin duniyar da baa Saka ba a mansion din,

Komai na cikinsa kudi ne suka daku kafin suka siyesa,

Komai na sabon mansion din ya doke na tsohon duk da tsohon ma kusan wata aljannar duniyar ne.

Komai an zuba Amma Babu Wanda aka daukowa kayansa kowa Saiya dawo ya dauko da kansa sbd Bai Bada Daman a shiga bedrooms na kowa ba abarwa kowa sirrinsa ya dauko da kansa.

Kayan Amatu ne kawai aka dauko sbd itama Babu abinda zaisa ya bari ta bi ko ta hanyar gidan Dan kawar mata da duk Wani memory mara dadi na gidan.

Farha ce tayi parking na kayan Amatu duka ta Kai mata aka Jere mata komai kaman tana Nan haka Suma su Karima tini aka kwashesu zuwa sabon mansion,

Khaltume ma andawo da ita bakin aikinta Dan haka ma aikatan suka Qaru,

Karima a iya me aikin AmatulMaleek take sauran ma’aikatan Kuma tini aka rarraba musu aiki Wanda wannan aikin na kulawa da duka masu aikin mansion din ya dawo hannun Farha Kuma bata daukan nonsense kana wasa da aikinka zata saukeka a dauki Wani Dan haka kowa ya sake shiga taitayinsu Daman Kuma sunsan baa wasa da aiki ko kadan a gidan Dan haka komai ya qara daukan tsanani.

Bedroom din Amatu a sama yake guri Daya da Husnah sbd palonsu Daya kowa da bedroom dinsa saina mum din Husnah din dayake gefen nasu shikuma Palo babba da bedroom set qaton dining room Wanda shine yakeda kofar da zata kaika palon Mai mansion din da komai nasa yake dabam.

Dawowan Amatu da Mai gidan ya sanya masu aikin sake nutsuwa kan ayyukansu,

Ganin Farha na gidan Bata wuceba ya Saka Amatu farin cikin ganinta tana cewa

“Anty Farha nayi missing fadanki kwana biyu”

Dariya Farha tayi tana kallan yanda tayi Dan fresh na hutun data samu zallansa Babu aikin komai tace

“Daga tafiya Se kashe waya Kuma Am”

Rasa abin fada tayi sbd ta rasa wayarta ne a wutan Daya faru batamasan Yaya aka qarasaba bare.

Su khaltume ne tareda sauran masu aikin duka suka shigo cikin girmamawa sukai mata barka da dawowa tareda mata sannu da jiki da fatan samun lafiya dorarriya.

Cikin nutsuwa da kulawa ta amsa tana gaidasu itama sbd Bata Saba da Hakan da suke mata ba.

Bayan ficewarsu sama ta Haye ta shiga bedroom dinta tareda ajiye handbag din hannunta tana Dan kallan dakin da ita kanta takasa yarda da nata dinne Amma Kuma zuwa yanzu tasan rayuwa ma koyaya tazo batada zabi bayan karbanta.

Alwala ta fara yowa tayi sallan laasar tana idarwa ta kwanta bacci duk da Bata tareda gajiyan komai.

Sai kusan magrib ta tashi

Toilet ta sake shiga Tayo alwala ta fito tayi sallah,

Bayan ta gama wanka tayi jikinta ya sake sakewa ta Saka straight gown black ta Roba me tsada ta Sako slippers ta sauko qamshinta me sanyi na tashi.

Yunwa takeji Dan haka kitchen take kokarin nufa saiga khaltume Farida na bayanta da kayan abinci zaa shirya abincin dare a dining.

Ganin Hakan ta nufi kitchen da kanta San ganin ko zata iya dafa masa tea din dayake sha din.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

36

********************

Ko data gama dafa tea din ta shirya a sabon tea set ta Jere ta dauko ta nufi dining room din

Shigarta yayi daidai da shigowansa dining din Shima bayan dawowansa daga sallan magrib sanye cikin black Armanis sweatsets fresh kaman saurayi abinci yake buqata sbd tinda suka dawo Shima Yana sama Yana hutawa cikin lafiyayyar bacci.

Kallansa tayi da idanuwanta farare tareda Dan dauke idanuwanta tana qarasowa tareda gaidasa a natse cikin sanyi.

Idanuwansa Shima ya Dan kalleta dasu kafin ya amsa Yana zaunawa a natse.

Green tea tafara zuba masa yakai hannu ahankali ya dauka Yana sha kafin tafara zuba masa farar spaghetti da kidney sauce sai lettuce da scotch eggs.

Tana gama zuba masa zata juya ahankali ya Bude Baki ya furta

“Ya jikin?

Dakatawa tayi daga inda take tsaye tareda sauke numfashi ahankali ta juyo ahankali idanuwanta na dagowa zuwa ga kallansa Shima daidai lokacin ya ajiye cup din hannunsa ya dago ya kalleta.

Sanyi jikinta yayi gabaki daya ta kasa daga kafafunta daga inda suke,

Jin shirunta ya Sakasa kasa dauke idanuwansa akanta Yana tinanin Bata ji saukin bane.

Miqewa tsaye yayi ahankali ya dosota ta Dan yi Baya kadan tareda dafa kejeran dining Dake bayanta tana sauke idanuwanta qasa tasamu kirjinta da bugawa ahankali hancinta Daya wuni yau din ba qamshinsa Yana shaqan qamshinsa cikin sanyi.

Shi kansa Saida ya iso gabanta ya tsaya Yana kallan wuyanta yaga gurin ya warke gaba Daya Dan bazaiso maamah dinta Taga wannan abin a jikinta ba.

Dagowa tayi ahankali zata kallesa ya juya ya koma inda ya taso ya zauna yafara cin abincinsa a natse.

Juyawa tayi batareda ta tsaya cin abincin ba ta koma dakinta zuciyarta Naci da bugawa.

Zama tayi tareda yin shiru tsawon lokaci Sai data tabbatarda ya gama ta miqe ta fito taje ta Zauna taci abincin ta taso ta dawo daki.

Sallan ishai tayi tai brush kawai ta kwanta.

Washe gari da safe ko fitowa batayiba Saida tayi wanka ta fito taci abinci tana zaune likita tazo dubata,

Batai mamaki ba Dan haka cire rigarta tayi ta duba koina na wutan Taga sun warke ta sake Bata cream da zata ringa shafawa a gurin ta tafi

Tana tafiya Mr Jameel ya Aiko mata da sabuwar waya guda biyu tareda layin MTN da Airtel.

Daya kawai ta Bude ta zabi na MTN din ta Saka ta ajiye dayar Dan Batada raayin amfani da waya biyu lokaci Daya.

Maamah tafara kira a take taji zuciyarta tayi sanyi lokacinda taji muryan maamah din.

Sallama tayi a cikin sanyi da nutsuwa tana cewa

“Maamah”

Ita kanta maamah din Jin Amatun ya Sakata miqewa daga kwancen datake tana ambatar sunan Amatun cikin tsananin kulawa da kauna tace

“Amatu,ansiya Miki wata wayar ne?

Mr Jameel yace wayarki kin yar ne a makaranta shiyasa bana samunki duk kwanakin Nan inata tinanin yanda zanyi magana Dake kafin na dawo,

Kina lafiya?

Zuciyata ta kasa nutsuwa Amatu,

Kina lafiya?

Numfashi me sanyi Amatun ta saki Jin abinda maamah din ta fada dan haka a sanyaye tace

“Lafiya kalau alhmdlh Maamah,ya Husnah,yasuke ta fama da hakurin rashin?

Alhmdlh”

Maamah yaushe zaku dawo?

Numfashi maamah ta sake tana cewa inshallah satin Nan zamu dawo Daman munata Dan jiran Husnah ta qara kwanakin data roqa ne Amma inshallah satin Nan zamu dawo.

Shiru Amatu tayi tana rasa abin cewa tace

“Allah ya dawo daku lfy”

Rasa abin fadawa juna sukai sai sukayi sallama.

Haydar tafara kira sbd tafi riqe numbernsa akan ta Abdul Yana dauka yaji itace abinda yafara fada shine

“10 days kenan bamuyi magana ba,tayaya zakiyi 10 Days ba waya,meyasa??

Batasan kwanakin data dauka ba rabonta da murmushi ya sauka kan kyakkyawar fuskarta sai yau din Dan haka murmushi me sauti ta saki tana cewa

“Zaka fara ko?

Rasa abin fada yayi sbd mamakin yanda za’a barta 10days ba wayan da gaske sai kawai ya hau tambayarta lafiyarta suna gaisawa dayake Abdul na tareda shi sun fita ne sai kawai ya Saka handsfree suka hau wayar su uku cikin samun nutsuwa da sakewa da juna.

Ta jima tana wayar dasu kafin ta kashe ta fito Dan batason zaman shirun ta nufi kitchen.

Da ita sukai aikin abincin Rana suka gama suka jere komai ta wuce daki.

Abinda batai tsammani ba shine dawowansa gida da wuri Dan haka a gidan yayi lunch ya shige.

Abincin dare kuwa kusan itace tayi sedai suka ringa taimaka mata da wasu ayyukan harta gama aka Jere komai ta sake shigewa.

Sallah tayi da wanka ta fito ta dafa ruwansa da baa dafawa sai lokacin cin abincin.

Tana kaiwa ta ajiye tana fita Yana shiga yasan lokacin ta fice sbd qamshinta Daya Dan fara noticing yaji ya shiga hancinsa.

Abincin yaci ya gama ya fice.

Yana ficewa itama ta shigo taci abincin da qamshinsa kawai Daya bari a dakin.

Sabuwar rayuwar kaucewa ganin juna suka fara Kokuma ace tafara dashi Dan shi ta nasa bangaren rayuwar Daya Saba ce yake Akai banbancin Daya fara samu shine kulawan dayake samu ta bangaren cimarsa datakeyi,Wanda itama ta Saba aikinsu ne Daman can itada uwarta,

Ta bangare daya Kuma dole tinda baa ware me kulawa da bangarensa ba itace dole tazama me aikin bangarensa,

Zata tafi gyare ne bayan ta tabbatarda ya fice zata gyara komai ta kunna qamshi da ac ta fito.

Shi da kansa yasan itace me gyara masa bedroom sbd Babu Wanda ya taba bin ko hanyar zuwa bangaren nasa Koda mr Jameel dinsa ne.

Bedroom dinsa shine Wanda yafi kowanne bedroom girma a Mansion din,

Luxury gadon Dake dakinsa a tsakiyar dakin yake hakama tsarin bedroom dinsa daban yake Dana Kowa.

*******Wani nauyi ne yahau kan Amatun a kwanakin dawowansu na aikinsa Daya hau kanta dole tinda ba know hakama Babu babba me fadan yanda zaayi din,

Masu aikin na jiran cewanta ita Kuma  batada me ce matan Dan haka Bata Ankaraba ta samu kanta da nauyin da duk matan aure take dauke dashi a gidanta na kulawa da komai na Wanda igiyoyin aurenta yake kanta.

A yanzu data samu kanta a wanna tsaunin hatta breakfast din dayake ci itace take fitowa tayi shiyasa duk safiya sai sun Hadu gurin hidimar cin abincin nasa.

Da farko Hakan Bai fara kamasa ba Saida tafara sabar masa da pen dayake amfani dashi idan ya dawo a tsare suke cikin tsari hakama komai nasa.

Maamah kusan kullum cewa takeyi zasu dawo Amma Basu dawoba Dan haka ta Dena ma tambayar yaushe zasu dawo.

Yau Bai fito ba tin safe sbd Babu inda zashi Amma Babu Wanda yasan yana gidan.

Ita kanta Amatun yau duk batada Wani kuzari sbd sanyi da akeyi Dan haka tinda suka gama breakfast ta dawo dakinta ta kwanta,

Masu aikin gidan ne kawai keta hidimarsu.

Mum Aisha ce ta dawo itama hankalinta gaba Daya baa kwance ba tafi sati biyu a cikin mummunan tashin hankalin rashin sanin inda Naufal ya shige,

Sam Bata samun wayarsa hakama zayyan yace Baya tareda shi,

Duk inda take tinanin samunsa ta bincika Amma Babu labarin inda yake Dan haka ta tattara ta dawo ba shiri saikuma ta tarar da sun dawo sabon mansion.

Kayan akwatinan sitirarta kawai ta kwaso itama Tayo sabon mansion din sedai tana zuwa securities suka dakatar da shigarta sai ankira mr Jameel yakira ASH idan ya Bada izinin shigowarta.

Mr Jameel bayan ankirasa Kai tsaye yaso Bada Daman abarta tinda ba itace ta aikata laifinba Danta ne Kuma haryanxu Babu ma Wanda ya sani sai Naufal din yaji sauki tukuna zaasan yanda za’a yi dashi Amma dai yace su Jira sai abinda ASH ya fada.

Kiran wayar ASH din yayi Amma duka biyun Babu Wadda aka daga Dan haka bazai cigaba da kiransa ya takurasa ba sai kawai ya kira numbern AmatulMaleek ya sanar da ita izinin ASH din ake nema akan shigowan Ms Aisha idan ya Bada dama.

Shiru tayi sbd batasan me zata ce ba hakama batasan tayaya zataje har bedroom dinsa ta samesaba.

Sake maimaita maganar Mr Jameel yayi Wanda Shima take tsananin ganin girmansa Dan haka ta sauko daga kan gadon datake ta zira slippers qafarta ta nufi hanyar dining room ta shiga kofar data zata shigar da ita palonsa.

Palon tsit Babu motsin komai daga qamshi me nutsuwa Se sanyi ke tashi Dan haka ta sauke ajiyan zuciya tareda nufar kofan bedroom dinsa kowanne takunta zuciyarta bugawa takeyi.

Tana tsayawa kofar bedroom din hannu Daya ta miqa zatai knocking kofar shikuma Yana Bude kofar hannunta ya Saka kirjinsa Dayake Bude Babu Riga a jiki sbd dogon wandon pyjamas ne tin na safe a jikinsa.

Fatar jikinsa Dake fara qal Babu tabo ko kurji kodaya tana daukan ido sbd lafiya da Hutu tayi saurin daukewa idanuwa gabanta na faduwa hakama tafin hannunta Daya sauka Akai ta dauke ahankali.

Shi kansa tsayawa yayi a gurin tareda kallan inda hannun nata ya sauka kafin ya dago idanuwansa dasukai ja da ciwon kan dayake fama dashi tin dazu ya zuba mata itama shi din ta dago a sanyaye ta kalla batareda ta motsa ba.

Fuskarta yake kalla a natse

Ta sauke nata idanuwan tareda Dan yin baya kadan.

Itace tayi qarfin Bude Baki a natse tace

“Mr Jameel na magana ne”

Bai iya magana ba Kai kawai ya gyada mata tareda juyawa ya koma ciki itama ta juya da sauri ta fice.

Wayarsa Daya ya koma ciki ya dauka yaga Kiran Jameel din ya Saka kiransa Kai tsaye.

Cikin nutsuwa Mr Jameel ya sanar dashi abinda yake faruwa a gate na mansion din.

Shiru yayi kafin ya Bada izinin shigowan nata aka Bude mata ta shigo.

Bayan shigowarta Babu abinda tafara cin karo dashi Daya girgizata shine sai dakin dasu khaltume suka Kai mata kayanta wato baa sama yake ba a qasa  dakinta yake duk da babba ne da palonsa Amma Sam baa qasa tazo zama ba,

Babban shock dinta na biyu shine tararta Babu kowa a gidan sai Amatu wadda take sama Kuma Bata sauko gaisheta ba.

Su sallah da abinci zataci ta huta sbd gaba Daya a kwanakin cikin rashin Kwanciyar hankalin Neman Naufal take.

Su karima da Farida ne suka hau shirya mata kayanta a wardrobe da sauran abubuwan inda zaa ajiye mata su.

Qanqanin lokaci sun gama suna kokarin ficewa ne Mum Aishan data gama komai ta zauna zata ci abinci ta kira sunan Farida tana cewa

“Meya samu old mansion din naga harda wuta Wani bangaren yayi,garin Yaya?

Kuma tin yaushe su Husnah sukai tafiya ne??

Kallan juna karima da Farida sukai kowannensu gabansa na faduwa da shiga firgicin tambayar.

Dagowa tayi ta sake kallansu tana fara cin abincin a natse tace

“Tambaya nayi,Babu amsar tambayata ne Kokuma dama kuka samu da sake bayan tafiyata”

Qasa sukai da kansu Wanda Hakan ya Bata tabbacin akwai abinda ya faru din kenan Dan haka ta ajiye spoon din hannunta tana hadiye abincin bakinta ta da tsawa ta sake maimaita tambayar

 cikin rawar murya da Farida tace

“Su Ms Husnah sunyi sati uku zuwa hudu da tafiya”

Abincinta taci gaba daci tana cewa

“Uhum gobarar Kuma fa garin Yaya?

Wannan Karan a tare suka amsa da cewa

“Sir Naufal ne ya kunnawa kitchen din wuta…..

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

37

*************

Abincin bakinta ne ya tsaya mata cak a maqoshi yakasa wucewa ta dago tana kallansu da matsanancin mamaki da tashin hankali tana sake hadiye abincin Amma yaqi wucewa Dan haka a shaqure ta Bude Baki tace

“Wane Naufal din?

Nawa?

Yaushe?

Garin Yaya?

Ta Yaya?

Ruwa farida ta dauka da sauri ta Bata

Ta bugesu da hannu tana sake jero tambayoyin a wahale.

Cikin tsoro suka fada mata abinda yafaru suna kaiwa inda akaiwa ‘danta ruwan bullet a qafa abincin ya dawo mata ta Baki gaba Daya idanuwanta na fitowa waje gaba Daya cikin matsanancin tashin hankali da rawar jikin Daya Saka su Farida yin baya suna sake shiga tsoro.

Mum Aishan kuwa jininta ne ya Haye take Dan haka jikinta ya dauki kyarma tana fidda idanuwanta Dake Neman fadowa tace

“Naufal dinne aka harbewa qafafuwan?

Naufal din?

Naufal din aka kashe akan matarda kilan karya take masa da sharri,

Waye yagansa?

Waye yace shine ya shiga a Daren kafin ranar?

Rawa jikinta keyi sosai idanuwanta na rufewa da Wani wutan tashin hankali da zafi zuciyarta na tsalle da tashin hankalin Danta ya mutu Dan kuwa Harbin bindiga ba wasa bane.

Magana su karima zasuyi ta Saka hannunwanta biyu ta turesu gaba Daya Bata Gani rawan tashin hankalin da jikinta yakeyi ya sa su karima rudewa cikin tsoro

Ta fito cikin ihu tana cewa inane dakin Amatun ta nufi hanyar saman tini duk suka fito suka tsatsaya hankali tashe khaltume ce kawai ta iya bin bayanta tana Bata hakuri su kuwa gaba Daya rudewa sukai.

Saman ta nufa tana Kiran sunan Amatun cikin qarfi da mummunan tashin hankalin datake ciki.

AmatulMaleek kuwa wanka ta fito sbd  Daman rashin kuzarin data tashi dashi na period ne,

Tagama saka undies kenan daga ita sai towel da bra a jikinta tana kokarin dauko kayan sakawa aka Bude kofan dakin da karfi tay juyo da sauri cikin mamaki da fargaba kafin tayi Wani motsin mum Aisha din Tayo kanta tana cewa tasa ASH ya kashe mata yaro.

Hannuwanta biyu ta miqa zata janyo Amatun ASH ya miqa hannunsa ya riga nata sauka ya janye AmatulMaleek din zuwa garesa Wanda Hakan ya Saka mum Aisha din shiga shock harma da khaltume sbd basusan dashi ba,

Basu ma San Da Yana gidanba shi kansa ihun Kiran Amatun datakeyi ne ya sakashi zuwa Dan fitowansa kenan zai zauna cin abinci.

Ita kanta Amatun da batasan da Shiba ganinsa ya Sanyata boye tashin hankalinta na ganin abin mamakin.

Mum Aishan ya kalla fuskarsa Babu inda Rahama ko sauki take a cikinta Kai tsaye yace

“Kina tinanin dukanta ne ko me?

Dukan matan aure Kuma?

Nine na harbe Naufal din ba ita ba ki sameni da damuwanki idan da gaske kikeyi din banason hayaniya a gidan nan”

Daga Hakan Bai qara ko Kalma Daya ba ya juya da Amatun a hannunsa ya fice itama Kuma Amatun Bata firgita sosaiba sbd Bata taba dauka dukanta mum Aishan zataiba Tim farko.

Kai tsaye hanyar palonsa suka nufa suna zuwa har bedroom dinsa ya jata Saida suka tsaya a tsakiyar bedroom din suka tsaya ya saukar da idanuwansa akanta sai alokacin yaga iya abinda yake jikinta itama juyawa tayi ahankali tareda basa baya ya zubawa farin bayanta idanuwansa yaga Dan sauran tabon konuwarta Daya kusa gogewa.

Juyawa yayi ya bar bedroom din.

Yana ficewa itama kofar ta nufo tana son fitowa sai Kuma ta dakata tareda Jan towel dinta sama ta Bude kofar ta fito.

Baya palon Dan haka ta nufi kofa ta fito Dan dole tana buqatan kayan sakawa a jikinta.

Tana fitowa mum Aisha Bata dakin ta sauka cikin matsanancin kuka Dan kuwa tasan inda Danta yake ma ASH bazai fada mata Dan haka kuka me tsananin baqin ciki da ciwo takeyi tana tsinewa Wanda ya haifi Asmau harta haifi Amatun da Danta yagani ya Hadu da wannan halakar hakama zayyan Daya bari Naufal dinma ya dawo gidan tsine masa ta ringa yi tana cewa duk sai kowa yaji abinda taji wlh.

Kaya Amatun ta Saka ta lafe a dakinta zuciyarta cikeda sabon tashin hankalin Wani bayan Wani.

Kaman gidan makoki haka gidan yayi tsit kowa Rai a tsorace da abinda Kuma zai bullo,

Duk roko da magiya da kukan son Jim inda Naufal yake mum Aisha tayi Amma Sam ASH ko ganinsa yaqi Bata damar tayi yana sama Kuma babu me iKon ko dosar hanyarsa bare.

Har dare Babu me dogon motsi.

AmatulMaleek daqyar ta iya saukowa ta dafa masa tea ta koma sama harta aje a dining saigashi sakon txt kawai ta Gani na cewan takai masa dinner dinsa palonsa bazai fito ba.

Tana ganin txt din ta gane shine

Itama Daman bazata iya zama cin abincinba tinda tasan mum Aisha zata iya zama cin abincin batada niyar zaunawa shigewa zatayi da wuri Dan haka ta hada komai ta dauka ta nufi hanyar dakinsa.

Ko data shiga kaman koyaushe shiru Babu hayaniya ba motsi Kwanciyar hankali ce kawai a duk inda yake din.

A C table Dake palon ta ajiye trey din tana miqewa ta koma ta dauko ruwa mara sanyi tana dawowa Yana fitowa daga bedroom dinsa yabita da kallo ita Kuma Jin idanuwansa akanta ya hanata dagowa ta ajiye ruwan a sanyaye ta Bude Baki cikin sanyi ta gaidasa.

Bai amsaba sbd karantar yanayinta na sanyi da fargaban dayake ranta a boye Dan haka Yana zaunawa harta Kai kofa cikin sanyi

Ya Bude Baki ya ambaci sunan Daya Sakata tsayawa cak a bakin kofar wato “Abeedah”

Tinda take a rayuwarta Babu Wanda ya taba ambatarta da asalin wannan sunan nata Dan kuwa har a takardunta da komai nata AmatulMaleek ne Se a yanzu din.

Juyowa tayi ahankali tareda kasa riqe idanuwanta daga kallansa ta kallesa a kasalance Shima ita ya kalla din.

Babu inda yakeda kuzari a jikinta ta dago ta dawo ahankali zuwa inda yake har lokacin idanuwansa na kanta sanyinta na bawa zuciyarsa mamaki Koda yaushe.

Tana isowa abincin data kawo masa ya kalla ya dawo da kallansa kanta da alama itama Bataci ba Kuma yasan fargaba zai iya hanata ci.

A karo na farko Daya ce mata ta zauna.

Zaunawa tayi ya sake kallanta yace Baya buqatan abincin tea kawai zesha ita taci abincin.

Babu musu sbd batada tinanin kanta alokacin ta zuba masa tea din ta miqa masa ta dauki spoon sedai bataiwa abincin ci uku ba ta koshi.

Tea yaci gaba dashi batareda yace ta tafi ba karshe aka bugo masa waya ya dauka Yana yin wayarsa hankali kwance.

Tin tana jiran ya gama har ta cire Rai da gama wayar tasa fargabanta Yana qaruwa Dan so tayi ta shige da wuri ta rufewarta Amma a yanzu data kai wannan lokacin na dare baa sakintaba tana fargaban fitowan gashi kaman yanda ita tasani Shima ya sani mum Aisha bazata iya rintsawa ba batareda ta gansa ba a tsananin buqatan ganinsa take Amma yaqi Bada damar.

Bai gama wayoyinsa ba sai guraren 1 daren dayake bama da Wanda yake qasar yake magana ba.

Waiwayowa yayi ahankali ya zuba mata idanuwansa gaba Daya Yana mata Wani irin kallan nutsuwa,

Bacci takeyi kaman baby duk da a takure tayi baccin Amma komai nata a natse takeyinsa har baccin ma,

Qananun kukan darenta ya Tina ko ta Dena tinda ta warke Kuma ta dawo gida.

Numfashi ya sauke ahankali tareda miqewa yazo inda take kwancen ya dauketa Kai tsaye ya nufi bedroom dinsa da ita har tsakiyan gadonsa ya kwantar da ita.

Yana kwantar da ita tana Bude idanuwanta ahankali cikin bacci ta saukesu a fuskarsa hannuwansa Daya sauketa baima Riga ya janye daga qarqashinta ba.

Dagowa tayi Dan ya janye hannuwan nasa daga bayanta kirjinta da nasa ya Hadu Wanda ya sanyasa Jin tidin kirjinta sosai a kirjinsa take ya zuba mata idanuwansa tayi rufe nata idanuwan ahankali Dan batasan cewan yajita sosai ba.

Ita kuwa qamshinsane dayake shigar hancinta direct yake Neman illata bugun zuciyarta Dan haka ta sake dagowa a karo na biyu tareda Dora tafin hannunta kan nasa Dan janyewa.

Kafin ta motsa ya janye hannunsa daga bayan nata ya juya ya shige toilet.

Yana shigewa kasa motsawa tayi sbd Batasan Yaya zatayiba bayan rufe idanuwanta tana komawa baccin da batasan ko zai dauketaba.

Yana fitowa hasken dakin ya fara ragewa gaba Daman sanye yake da pyjamas dinsa gadon ya nufo Kai tsaye ya kwanta.

Alarm na lokacin sallan asuba ne ya fara ringing a hankali ba wata hayaniya,

Dan haka ya Dan motsa kadan tareda miqa hannu ya kunna hasken dakin kadan kafin ya Bude idanuwansa ahankali daidai fuskarta data gap da tasa tana San fidda numfashi ahankali haka kawai zazzabi ya Dan dameta a lokacin Wanda kusan na firgicin data Kwana dashi ne.

Hannunsa Daya yakai ya wuyanta yaji da zafi sosai

Saukan hannunsa a wuyanta ya Sanyata Bude idanuwanta a Dan wahale ta kallesa ta mayar ta rufe cikin wani irin sanyi da sakala.

Hakan datai ya sanyashi lumshe idanuwansa tareda sake Kai hannunsa cikin wuyan nata ya tabo zafinsa.

Ta Dan sake rufe idanuwanta a karo na biyu tana motsawa,

Kaman tafiyan ruwa ahankali taji saukan muryarsa cikin kunnanta babu qarfi ba hayaniya ya furta

“Kin kwana da fever ne??

Yanda yayi mata maganan ya Sakata Bude idanuwanta Ashe nasa idanuwan akanta suke take idanuwansu suka shiga cikin na juna

Kallansa ya Sakata kasa Bude Baki ta gyada masa Kai ahankali tareda motsa hannunta ahankali ta nun cikinta amatsayin shine yake mata ciwo tinda bazata iya cewa mararta ba duk da ba Wani ciwo bane me tsanani.

Rashin maganar datai ya Sakasa tinanin sosai takejin ciwon Dan haka da ido ya mata alaman cikin na ciwo take nufi?

Gyada Kai tayi ahankali cikin sanyi.

Ba zata hannunsa ya sauka kan cikinta Daya Sakata dauke numfashi lokaci Daya tana qanqame hannunsa.

Hakan datai shine ya Sakasa sake zuba mata ido da mamakin har sosai haka cikin ke Mata ciwo.

Zamewa tayi tareda kokarin tashi zaune sedai hannunsa Dake cikinta ya Sakata dawowa Baya sedai akan jikinsa ta Baya ta dawo daidai shikuma ya taso Dan haka ta fado tsakiyan kirjinsa hannunsa daya na zagaye da ita kan cikinta.

Shiru sukai dukkaninsu kafin ya qarasa zagayota da Dayan hannun jikinsu na mannuwa da kyau.

Ajiyan zuciya me sanyi ta sauke sabanin shi dayaji Wani irin sanyin yanayi ya shigesa na nutsuwa.

Basu jima ahakan ba qamshin dayake wuyanta ya ringa shigan hancinsa Kai tsaye yana tinatar dashi yanda qamshin mace yake a hancinsa Wanda bazai iya Tina Yaya mace take qamshi bayan tsawon lokaci Sai yanzu din.

Ahankali yayi mata kyakkyawar rungumar data Sanyata Bude idanuwanta a kasalance ta duk da ta Baya ne yake rungume da ita din haduwa me kyau jikinsu yayi.

Saukan kansa cikin wuyanta ya Sanyata mayar da idanuwanta ta rufe ahankali bugun zuciyarta na qaruwa.

Qamshinta ne yake sake shigarsa Yana Saka Jin Wani irin yanayin daya kasa gane na Menene ma,

Hannuwansa Dake kan cikinta zagaye ya dago Daya ya shafi wuyan nata ahankali tayi saurin dago hannunta a kasalance ta Dora akan nasa Dan riqewa Amma ta kasa sai Hakan ya sakashi juyo da ita gaba Daya ya manne kirjinsa da nata yana lumshe idanuwansa da baccin cikinsu suka fita gaba Daya.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

38

******************

Cikin wuyanta ya Saka kansa ahankali hancinsa na samun nutsuwa da qamshin dayake fita a wuyan nata Yana fitowa daga jikinta Yana sake shigar da ita jikinsa fatarta jikinta dayayi dumi na warming nasa jikin ahankali cikin nutsuwa dumin jikinta ke shigarsa Yana rage dumama masa sanyin asuban.

Yanda yake shaqan qamshinta ita Kuma Yana sake Saka kansa cikin wuyanta fuskarsa na gogan fatan wuyanta zuwa gaban wuyan nata ya Sakata Jin tsokan jikinta na motsawa ahankali sunason tashi Amma Kuma shigarta jikinsa sosai na kashe jikin tsikan na komawa tana lafewa sbd Wani irin sanyi take samu a jikin nasa dayake rage zafin jikinta zuwa nasa jikin Dan haka gaba Daya ba notice jikinta ya mutu a cikin nasa ta lafe Shima lafewanta jikinsa kaman mage ya kashe nasa jikin ya Dan sake matseta jikinsa suna lumshe idanuwansu gaba Daya.

Shiru sukai a Hakan tsawon mintina yanajin bugun zuciyarta har akan kirjinsa tareda kirjinta Dake cikin bra dasuke manne a kirjinsa suna sake Bude kofofin jikinsa Dake karban zafin jikinta ba shamaki.

Saida aka sake Kiran sallah na biyu kafin ya iya zameta daga jikinsa ya kwantar da ita ya sauko Yana gyara rigar jiinsa ya nufi toilet Kai tsaye ya shige.

Bai jimaba ya fito ya fice sallah.

Bayan fitarsa kasa motsawa tayi daga kwancen datake sbd komai na jikinta qamshinsa yakeyi hatta wuyanta Daya saka kansa qamshinsa yakeyi

Lumshe idanuwanta tayi a kasalance tana Jin bugun zuciyarta na cigaba da qaruwa Yana sauyawa.

Tinane tinane take shiga kala daban daban cikin fargaba,shakka tareda tsoro zuciyarta har bacci ya Dan sake daukanta daga gurin kwance tinda ba sallan zatayiba.

Saida baccinta ya Dan fara Nisa ya dawo dakin daga sallah har gari ya fara haske kenan.

Ba Haske har lokacin a dakin Dan haka kwantawa yakoma yayi suna facing juna qamshinta na sake shigansa direct,

Cikin abin rufar me tsananin taushi ya shige Shima Wanda dole ya sake sakasu hadewa guri Daya.

Bacci sosai sukayi Wanda dagashi har ita rabonsu da irinsa tin Lagos,

Mr Jameel yayita Kiran wayoyin yayita yawon zuwa hanyar palon ta kofan da ASH din ke ficewa Yana Dan knocking a hankali Amma Sam Babu motsi Babu labari Dan haka ya saurarawa me gidan ya huta.

Itace tafara motsawa a kasalance tana juyawa cikin jikinsa datake nade kaman baby bayan natsatsen iskan da hancinta yake shaqan har acikin bacci Babu abinda yake sanyaya zuciya da jikinta.

Sake motsawanta ahankali ya sanyashi Bude idanuwansa Shima ahankali Yana saukesu a kanta cikin nutsuwa da kasalan da Shima baisan ta inda ta samesaba.

Qasa tayi da nata idanuwan ahankali numfashinta me dumi ya sauka akan fatan krjinsa datake ciki ta inda botiran rigar jikinsa suka Dan Bude.

Saukan numfashinta me dumi akan fatarsa ya sanyashi rufe idanuwansa dasuke da sauran nauyin bacci acikinsu Yana Dan motsa hannuwansa Dake zagaye da ita.

Numfashin nata sake sauka yaci gaba dayi ahankali ahankali cikin jikinsa Yana dumama jikinsa ahankali har zuwa cikin kansa,

Qarfin halin sakinta yayi ahankali cikin nutsuwa tareda zarewa ya tashi zaune sbd Neman sauyasa da ahakan ke yi.

Itama a hankali ta tashi zaune tareda kasa kallansa cikin sanyi ta Bude Baki ta furta

“Ina kwana”

Sanyin muryanta yayi yawan da duk lokacinda tayi magana Saiya juyo ya kalleta.

Idanuwansa ya zuba mata Wanda suke Sakata duk tsaka me wuyan data fara shiga akan lamarin auren Nan Dan haka tanajin saukansu akanta jikinta ya sake sanyi zuciyarta na narkewa.

Saukowa da qafafunta tayi daga gadan ahankali tareda miqewa tsaye Bata iya juyowa ba ta nufi kofa sbd tanajin qarfin idanuwansa akanta har lokacin.

Fitowa tayi ta nufi kofan ficewa daga bangaren ta Bude ta fice Kai tsaye ta dining ta bullo Babu kowa sai qamshi da tsit da Gidan ya sake dauka da alama angama komai harsu kariman sun koma kitchen aiki.

Bedroom dinta ta nufa tana shiga wayarta tafara nufa ta dauka ta duba Taga har goma tayi Ashe ga misscalls din Farha Dana maamah harma Dana Haydar da Abdul.

Ajiye wayar tayi tana zare kayan kayan jikinta da sauri ta fada toilet.

Ruwan dumi ta sakarwa kanta suna daukowa jikinta ta saki ajiyan zuciya tana shafa wuyanta.

Wankan tayi tana gamawa qamshin shower gel nata ya cika toilet din ta daura towel ta dauki brush ta tsaya tayi brush tana gamawa ta fito lafiyayyar farar fatarta na tsiyayar ruwan wankan datayo a hankali.

Goge jikinta tayi ta zauna gaban mirror ta shafa Mai da duk abubuwan da zata shafa ta miqe ta Saka pad da sauran undies dinta ta Saka Riga da skirt na atampar super brown acikin kayan da Farha ta kai ta Kuma karbo daga dinki qamshinta bame tashi sosai bane Amma a duk lokacin da ta zauna kusa da Kai ko rabarka ta wuce zaka ji nutsuwa,sanyi da dadinsa har cikin zuciyarka Dan haka ko data gama ta fito su farida Basu jiyo qamshin ba Sai data shigo kitchen din.

Kallo daya sukai mata dukkaninsu suka sauke Kai sbd kyanta me sanyin Nan ne da kana kallanta take shiga ranka a tsanake hakama Bata Saka kayan da suka wuce dogayen riguna yau ta Saka Riga da skirt Wanda ya fidda asalin shape dinta dayake boye koyaushe a cikin dogayen rigunan.

Gaidata sukai khaltume ma data fito daga gurin mum Aisha gurin Kai mata breakfast tana ganin Amatun kallo daya tayi mata ta tabbatarda Se Allah idan ba Amatun tabbata zatayi matar mansion din ba.

Cikin nutsuwa ta amsa gaisuwarsu itama ta gaidasu a mutunce tafara kokarin Dora tea din data shigo dafawa su karima na miqo mata kaya suna fada mata ai sun dafa Amma babu komai a ciki.

Khaltume ce tace

“Farida jeki ki dauko wancan din da aka Kai”

Hannu Farida ta cire daga ruwan robar datake jerawa a fridge tayi tazo ta wanke hannun da kyau ta dauki towel ta goge hannun kafin ta fice zuwa dining room din dayake sama.

Tana daukowa ta dawo ta kawo lokacin har Wanda Amatun ta Saka ya kusa Dan haka suka Dan ringa fira sama sama Dan ita Amatun haryanxu batajin Wani sauyin da zata iya nesanta kanta dasu tinda sun Saba aikin gidan tare ai bare su karima ko bayan auren suna sakewa da ita sosai dawowan khaltume ne suke Dan shakka bare yanzu da mum Aisha ta dawo gashi tin jiya Babu me iKon babban motsi a gidan.

Tana gamawa juyewa Tayi ta Jere komai ta sake goge komai sbd tabbatarda tsaftansu ta dauka ta juya ta fice zuwa saman.

Komai an Jere a dining already Ashe Dan haka ajiyewa tayi gaban kujeran da itace tasa tana kokarin juyowa Yana shigowa gurin qamshinsa tafara shaqa kafin takunsa dataji a bayanta Dan haka ta kasa juyowa Sai data sauke numfashi mara sauti a hankali kafin ta juyo ahankali daidai ya iso inda take daf zai zauna Dan haka juyowanta ya sakashi zuba mata mayun fararen idanuwansa sbd isowansa gap da itan qamshinta me sanyi ya shiga hancinsa.

Kasa dagowa tayi hakama Bata motsa ba,

Ahankali ya dauke idanuwansa daga kanta Yana zaunawa a natse cikin wata fitinanniyar tsadaddiyar soft milk yadi yake Daya bayyanarda zamansa billionaire,

Kyansa da kwarjinsa duk sun Sakata shiga Wani hali Amma dayake itama me tsananin nutsuwar ce sai Hakan Bai bayyanaba ahankali ta sake Bude Baki ta gaidasa.

Amsawa yayi Yana kallan dogayen yatsun hannuwanta Dake zuba masa green tea Wanda da ruwan zafi yake Bude cikinsa hakama dasu yake rufewa Hakan na qarawa ciki da jiki lafiya sosai.

Tana gama zubawa tafara zuba masa breakfast kenan mum Aisha ta shiga dakin cin abincin shirye cikin doguwar rigar tsadaddiyar lace pink fuskarta Babu damuwan komai hakama Babu alaman tashin hankali atareda ita kamar ba Babu abinda ya faru.

Dauke idanuwa AmatulMaleek tayi ahankali tana cigaba da serving nasa din.

Bai Kalli mum Aishan ba data shigo Saida ya juya idanuwansa akan Amatun ya Dan kalleta ya karanci yanayinta Sam Babu alaman daga hankali ko tashin hankalin saima nutsuwa duk da yasan akwai Dan firgici a cikin zuciyarta Amma tayaya ta iya hadiye tashin hankalinta da nutsuwa?.

Qarasowa mum Aisha tayi tana tsananin danne abinda yake ranta sbd ta tabbatarda har abada tashin hankali bazai Bata komai daga ASH ba Dan haka ta zabi sauya wasanta.

Cikin nutsuwa ta qaraso tana kallan Amatun kafin ta Kalli ASH din dayake Shan tea hankalinsa kwance fuskarsa sai cika mata ido takeyi.

Cikin girmamawa sosai da sakewa ta gaidasa kafin ta sake Maida kallanta kan Amatu kafin tayi magana Amatun ta Bude Baki itama cikin girmamawa ta gaidata.

Murmushi ta sake ahankali me sanyi kafin ta amsa gaisuwar Amatun tana cewa jiya ranta ya Baci ne Amma batada niyar yimata komai Daman.

Shiru Amatun kawai tayi tana qarasa gama zuba masa komai ta juya gurin mum Aisha din zatai serving nata ta dakatar da ita da cewa ta gode ta zauna kawai taci nata.

Tasan dole zasuyi magana Dan haka Bata zauna dinba ta juya zata bar gurin ba zato ya miqa hannunsa Daya cikin nutsuwa ya kama hannunta batareda ya dagoba a kame yace

“Sit”

Mum Aisha data qi kallan abinda ya faru din tana danne zuciyarta Dake tsananin ci da wuta da zafi Amatu ta Dan kalla Taga gaba Daya akan abincin dayake gabanta hankalinta yake.

Zaunawa tayi a natse tareda daukan choculate banana bread da aka gasa da safen tana kaiwa bakinta kafin ta fara zuba tea din itama tana sha ahankali.

Shiru gurin ya dauka Babu me magana Dan mum Aisha taso magana dashi Amma Amatun na gurin Kuma Sam Babu fuska kowacce iri daga ASH din gaba Daya tsoronsa sake shigarta yakeyi shiyasa ta canja salanta.

A gurin shi kadai ne yake cin abincinsa hankali kwance cikin nutsuwa ba damuwan komai sabanin AmatulMaleek datake a takure duk da itama cin abincin takeyi,mum Aisha kuwa da zaa Bude zuciyarta hayaqi kawai za’a ringa gani na tafasan da zuciyarta keyi Amma itama tura abincin takeyi cikin nutsuwa zuwa cikinta.

Yana gamawa tissue ya dauka ya goge bakinsa tareda hamdala cikin zuciyarsa ya miqe tsaye idanuwansa na dan sauka kan AmatulMaleek wadda itama ta Dan dago ta kallesa da idanuwanta dasuka sanyashi juyawa ya Kalli mum Aisha wadda itama San dagowa tayi tana kasa kallan cikin idanuwansa sbd girmamawa,

Baici komaiba bayan kallan da yayiwa mum Aisha ya juya Yana ficewa a qasan maqoshi Amatun tai masa a dawo lfy.

Mum Aisha dawo da kallanta kan Amatu tayi ta zuba mata su duka tana kasa motsawa sbd tasan kallo daya yayi mata ya fice batareda da Kalma ko Daya ba ta idan Taga dama ne ta taba matarsa ko yar mutane yake nufi hakama itama Amatun tasan tasani abinda yake nufi kenan da rashin maganarsa,

Ko Karan haukar Daya ciza Naufal ne yazo ya cijeta tasan bazata taba Amatun ba ayanzu Daya tsaya mata har ya iya sakawa a harbe mata ‘da Daya a duniya sbd Amatun to Babu abinda bazai iya faruwa ba idan tayi nata gangancin Dan haka miqewa tayi batareda ta iya cigaba da turawa cikinta abincin da daci ma yake mata a Baki ba.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

***********************

AmatulMaleek Bayan barin mum Aisha gurin lumshe idanuwanta tayi ahankali tareda sauke numfashi tana qarasa Shan tea dinta ahankali harta gama kafin ta miqe ta bar gurin su karima suka zo Dan tattarawa ita Kuma hanyar palonsa ta nufa Dan nata aikin.

Bedroom din ta gyara tareda sauya beddings da tsadansu take a bayyane farare dayake kusan komai na dakin fari ne Dan haka kusan closet na kayan beddings din dakin duka farare ne a Jere hakama gurinsa towels dinsama suke Jere a kusa da kayan shimfidar Suma duk kusan farare ne ba adadi qalilan ne masu kala Shima kala biyu rak blue Se brown Basu fi bibbiyu ba Amma sauran duka farare ne Se milk dasuka saje da farare.

Gyara kayan gadon data taba gurin dauko wasu tayi ta shimfida wasu tareda gyare dakin tsaf ta wanko toilet din nasa Wanda ko mace kafin a asamu me irinsa ba kusa ba Dan toiletries Dake bathroom din da abubuwan wankansa, shavings, mouth wash,facewash,shower creams bathmist da dai sauransu duk Saida tashiga mamaki sbd hatta towels na goge ruwan wankansa daban da wainda yake daurawa hakama na goge hannu qamshin toilet din da girmansa kawai Wani lamarin ne na daban.

Ba dauda Amma dai ta sake wankewa ta fito ta kunna AC tayi qasa dashi ta kunna qatuwar humidifier din Dake tsaye a gefen shigowa dakin ta fice.

Palon ta gyare Shima ta kunna ta fito da qaton zanin gadon dayafi karfinta ko a dauka ta kira Charlie Wanda shine yake wankin kayan dasuka fito daga bangaren ASH ya Karba ya wuce ita Kuma ta wuce sama dakinta.

Mum Aisha ko yau haka ta wuni a dakinta Babu me shiga ko babban motsi a gurin sbd batasan hayaniyar komai.

AmatulMaleek kuwa dakinta ta shige ta zauna tana waya sbd hutunta Dayake Shirin qarewa a satin tasan dole dai maamah zasu dawo yanzu tinda hutun Husnah itama ya qare.

Farha ce tazo gidan batama San mum Aisha ta dawo gidan ba Dan haka Bata tsaya nufar dakinta ta gaidata ba ta wuce sama.

AmatulMaleek Dake waya da maamah shigowan Farha yasa suka Dan taqaita tareda sallama ta ajiye wayar tana Dan murmushi me kyau na ganin Farha din tace

“Anty Farha sannu da zuwa”

Zaunawa tayi tana yar dariya itama tana cewa daga gurin karbo sauran kayan dinkunan Amatun take.

Bags din da anty Farhan ta ajiye masu girma ta kalla tana cewa

“Sannu da kokari anty Farha”

“Yauwa AmatulMaleek Amma dai Banda sannu sai wannan sanyin naki ya rage yafara yawa tinda haryanxu Baki zama cikakkiyar matan the great ASH TALBA ba,Mr Jameel abinda ya Saka ya daukoni daga office dina kenan dole nabarwa Yara aikin boutique’s dina nazo so yake Mai gidansa ya samu rayuwar da kowanne me Kwanciyar hankali yake samu fa.”

AmatulMaleek kasa cewa komai tayi sbd batasan me zata fada din ba Dan haka ta Dan yi Baya ta kwanta jikin sofa tana yiwa anty Farha din murmurshin karfin hali kawai.

Karima ce tai knocking ta shigo da trey ta qaraso a natse ta ajiye me dauke da drinks da vanilla cake da yanzu suke gasawa.

Juyawa tayi ta fice Suna Dan cigaba da firarsu wadda kusan duka anty Farha ce me zancen AmatulMaleek na binsa da idanuwa daga kwancen datake zuciyarta na Rasa wane matakin zata kama tsakanin zama matar ASH din ko janyewa ta tsaya a matsayin ‘yar Aminiyar matarsa.

Anty Farha kuwa kusan taqi qasa a gwiwa gurin sake shigar da zuciyar Amatun rudanin datake shiga ma idan Yana kusa a ayanzu.

A dakinta sukai wuninsu itada anty Farha cikin fira da sakewa da juna har yamma kafin suka dawo Palo anan suka qarasa wunin abincin Rana ma palon suka ci sa,

Sai gap da magrib da zata wuce suka sauko ta rakota har harabar gidan inda motarta take,

Ko motar Basu qarasa ba motocin ASH suka shigo mansion din.

Kallanta anty Farha tayi tana murmushi ita Kuma kusan gefen da ba ganinta zaayiba ta koma har sukai parking aka budewa ASH din ya fito yana amsa waya sedai idanuwansa dasuka Kalli inda take din ya sakasu fahimtar ya lura dashi Amma ya wuce yayi ciki kawai sbd har lokacin waya yake amsawa Kuma magrib tayi.

Mr Jameel ne ya qaraso da sauri yana kallan Farha fuska a sake kafin yace komai AmatulMaleek din yafara gaidawa cikin kulawa.

Gaidasa tayi itama cikin girmamawa tareda yiwa anty Farha sallama ta koma ciki.

Tana shiga sama ta Haye ta wuce bedroom dinta wayarta ta ajiye kawai ta nufi toilet batareda ta zauna ba.

Ko data fito lokacin karima ta shigo tana gyara dakin da kayan da anty Farha ta kawo duk da jere

Atampar jikinta ta cire tana sake komawa toilet Daman mararta ta rage.

Ta jima a ciki Dan haka Ko data fito Karima ta gama ta fice.

Zaunawa tayi a natse tayi komai nata tana gamawa ta shirya ta Saka Riga da wando masu tsanci na bacci ta zira doguwar hijab har qasa ta fito ta sauka ta nufi kitchen.

Cake din da itace me a kwaba komai tabar musu gashin ta fara dubawa tagani kafin ta Dora ruwan tea dinsa.

Tana kitchen din mum Aisha ta fito su khaltume suka gaidata cikin girmamawa

Itama cikin girmamawan ta gaidata sedai Bata amsa nata ba Suma kusan amsawa Daya tayi fuskarta Babu annuri ko Daya Wanda ansamu sassaucin tin safe da mr Jameel ya tabbatar mata da Naufal Yana Nan a Raye Yana asibiti ana treating dinsa.

Sama ta wuce Kai tsaye zuwa palon saman Dan jiran fitowan ASH cin abinci ta samu magana dashi.

AmatulMaleek ma na ganin Hakan tasan magana zasuyi Dan haka tana gamawa taje ta ajiye a dining ta baro palon gaba Daya ta shigewarta bayan Tasha orange juice da cake biyu ya isheta.

Zaman Jira mum Aisha ta fara a palon har Akai ishai yaje sallansa ya dawo ya shige batareda ta saniba tana zaune tana jiransa kaman zataita ihu tana debewa zuriar Asmau albarka data shigo ta tarwatse musu gidan.

Amatu tinda ba sallah takeyi ba bata Wani tsaya komaiba kwanciyarta tayi tana Dan chats dasu Abdul har guraren 10 ta ajiye wayar tareda miqewa ta shiga toilet ta sake fitsari ta canza pad tana fitowa ta kashe wutan dakin tahau gadonta kenan sakonsa ya shigo Wanda ya Dade da shigowa Bata lura bane sai lokacin Kokuma network ne Bata saniba.

Time ta kalla batai mamakin qin fitowansa cin abinci ba duk da ta dauka dole yafito kenan mum Aisha Bata samu ganinsa ba yau din ma.

Wata doguwar hijabin daban ta dauko ta zira tareda slippers ta fito ta nufi hanyar dining din.

Ga dibbin mamakinta mum Aisha na zaune palon saman tana jiransa har lokacin,

Dauke idanuwanta daga kallanta tayi tana sauke Kai qasa ta nufi dining room din zuciyarta na Dan shiga rawa.

Iya abinda zaici kawai ta hada a trey ta dauka tabi kofar dazata isar da ita palonsa ta dining room din batareda mum Aisha Tama San akwai hanya a gurin ba.

Tana isowa Kai tsaye ta Bude kofan ta shiga tareda turowa ta nufi inda zata ajiye kayan hannunta.

Baya palon hakama ba Wani Haske sosai apalon bayan Hasken flat screen Dake aiki Se sanyi da qamshin ne kawai dakuma Shiru me nutsuwa sbd akwai shirun da babu nutsuwa a cikinsa.

Ajiye abincin tayi ta nufi kofan bedroom dinsa ta miqa hannu a natse zatai knocking ya Bude kofan zai fito sanye da pyjamas farare tas dasuka lafe a jikinsa da fatan ke lafe itama.

Kujera ya nufa Yana kallan abincin data kawo yace tea kawai zesha dare yayi Baya buqatan abinci me tsayi.

Bayansa ta biyo hijabinta na Jan qasa yayi mata kyau sosai kaman yar islamiyya.

Zaunawa yayi a hankali tareda kallanta taba qarasowa hijabin jikinta ya lafe sosai a jikinta fuskanta Kuma fresh Babu komai Akai tinda tayi wanka body oil kadan ta shafa sai oil na tsadaddiyar oud din daya kama jikinta mara qarfi sosai.

Dauke idanuwansa yayi ahankali daga kanta Yana maidawa kan tea din da zata zuba masa.

Zaunawa tayi ahankali cikin nutsuwa ta zuba masa tea din tareda cake guda uku data Sako Dan Daman tasan zeyi wuya yaci abinci a daidai wannan lokacin.

Miqa masa tayi tareda dagowa ta kallesa da idanuwanta da bacci yafara shiga sun Dan narke.

Tea din ya Karba yakai bakinsa a kame ya fara sha ahankali kafin yace

“Kinci dinner naki??

Gyada Kai tayi ahankali tana sake kallansa a hankali Wanda Hakan ya sanyashi hadiye tea me zafi da qarfi saiga Tari.

Ruwa ta miqe ta dauko a fridge dayake palon me Dan sanyi ta dawo ta kawo masa tareda budewa ta miqa masa cikin sanyi tana furta

“Sorry,sannu”

Tea din ya miqa mata kafin ya karbi ruwan yakai bakinsa yasha ya miqa mata ta karba ta rufe tana sake furta masa sannu a hankali cikin kulawa.

Yanda ta tsayu sosai a kusa dashi har qamshinta na shiga hancinsa ya sakashi dagowa ya kalleta yaga damuwarta ta bayyana a Fili,

Karan farko kenan Dayaga bayyanar damuwarta Kokuma yace fahimtar Wani abu dayake ranta na damuwa ko firgici ko tashin hankali bare farin cikinta da Bai taba ganinsaba.

Ruwa tasake miqo masa ganin Yana kallanta cikin yanayin da itama batasan na Menene ba tana tinanin Yana buqatan sake Shan ruwane ne sbd tasan tea din akwai zafi sosai.

Bai dauke idanuwansa akantaba ita Kuma Bata janye hannunta daga miqa masa ruwan

Hakan datai shine yake sake kashesa da mamakin ita gaskiyanta kenan ya wine Yana cikin wuya ko me??

Hannunsa ya miqa ahankali ya Dora akan nata ya kama tareda janyota zuwa garesa a natse.

Hijabinta Dake Jan qasa Ya maqalu da doguwar kadan kujeran data taso Akai Dan haka ba Daman qarasowan nata.

Kallan hijab din yayi a natse itama bayan hijab din ta juya ahankali ta kalla sedai kafin ta juyo sai jinsa tayi a gabanta ya tsaya Wani irin ja numfashinta yayi sbd ba zata.

Hannunsa Daya yakai ahankali idanuwansa na kan fuskarta ya daga hijabin nata tareda zarewa gaba Daya ya saki a qasan sbd baimasan Menene ya riqe hijab dinba bare ya zare mata Dan haka ya zare mata hijab din kawai.

Bata taba tinanin hijab din zai zare mata ba Sai data samu kanta gaban nasa tsaye Babu hijab a jikinta.

Bata dago ba kirjinta takai idanuwanta cikin sanyi ta kalla Babu bra a jikinta hakama santsin kayan baccinta yasakasu lafewa jikinta kaman zasu hade da fatarta.

Abinda ta kalla shi ya kalla batareda yayi tsammanin ganin Hakan ba bayan zare mata hijabin.

Kasa motsawa tayi saima Dan sake shigesa datai kadan Dan tana yin baya zata basa Daman ganin kirjinta da babu shape dinsu dabai fito ba a rigar jikinta musamman saman da kaman a bayyane yake tsaban fitowan shape dinsa.

Yanda Tayo cikinsa kadan ya sakashi motsawa zeyi Baya sbd Hana kirjinsu haduwa a irin wannan yanayin.

Matsawa takeson yi Amma kunyar data dabaibayeta bazata iya barinta motsawa ba saima Jin tayi qafafunta na sanyi.

Qamshinta ne yafara masa yawa a hancinsa Dan haka ya Dan ja Baya kadan

 Yana yin Hakan tayi saurin juyawa zata durqusa daukan hijabinta ya kama hannunta ba zato tareda dawo da ita Baya ya hade bayanta da kirjinsa.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

*****************

Rintse idanuwanta tayi da sauri Jin hannuwansa na zagayeta bayan haduwar jikinsu numfashinta na kusan daukewa hakama zuciyarta na sauya dukawa a hankali.

Qamshinta shine masifar dayake tinanin tana Neman kamasa a duk lokacinda zai shiga hancinsa…

Kan shafaffen cikinta hannuwansa suka ya tsayar dasu Akai bakinsa Dayake gefen fuskarta ya Bude cikin sauti mara tashi ya furta

“Yaya cikin??

Qamshin butter mint mouth wash din da bakinsa yakeyi ne ya shiga hancinta ahankali ta sake rintse idanuwanta tana gyada Kai daqyar sbd hannunsa dayake shafa cikinta ahankali Yana Sakar mata zafin jikin da batasan daga Ina yake fitowa ba.

Yanda ta kasa Bude Baki ta amsa din ya sanyashi juyo da ita ahankali dukda baiso Hakan ba Amma qamshinta da sanyinta a jikinsa suna rinjiyar qarfin halinsa.

Yana juyo da ita ta manne da kirjinsa tana kasa barinsa ya ganta a wanna kayan sedai abinda bata sani ba shine data barin ya Gani yafi hada kirjinta datai da nasa sbd Jin tsinin saman kirjinta akan nasa ya sanyashi zagayota da hannuwansa biyu Yana zaunawa da ita akan jikinsa har lokacin kirjinsu a manne yanajin zafi na tasowa ta cikin kansa tako Ina.

Zamanta kan cinyarsa ya basa Daman dago idanuwansa dasuka fara sauyawa ya zubawa kirjinta da suka sake miqewa suna sukan kirjinsa tareda qara Bude kofofin zafinsa.

Hannunsa Daya ya sake zagayota jikinsa da kyau Dayan kuka cikin wuyanta ya Saka Yana shafawa ahankali kafin yakai kansa cikin wuyan ya shaqo qamshinta ya jasa har cikin kansa ya qanqameta Bata zato ya saukar mata da Wani fitinannen kiss din Daya Sakata qanqamesa numfashinta na Neman tsayawa Hakan ya sake kashesa ya sake cusa kansa cikin wuyanta Ya fiddo harshensa ahankali ya lashi tabon wutarta Daya kusa qonewa.

Miqewa tsikar jikinta tayi gaba Daya ta fidda Wani marayan numfashin Daya sauka gefen kunnensa ya tayar da tasa gashin jikin.

Dago fuskarta yayi ya zuba fararen idanuwansa Akai ta rufe idanuwanta ta kasa budewa ta kallesa.

Kan lips dinta ya gangaro da idanuwansa komai nata na fizgarsa zuwa gareta,

Goshinsa da nata ya fara hadewa Yana kokarin yaqar kansa da Hana kansa sedai duk fitan numfashinta Daya dayake sauka a fuskarsa kashesa sukeyi a cikin jininsa.

Ita kanta zuwa lokacin zuciyarta ta kasa hanata yarda da abinda yake faruwa,

Saukan lips dinsa akan nata Ya rusa sauran tinanin Daya fara shigarta a lokacin na guduwa ta Bude idanuwanta dasukai nauyi ahankali ta kallesa Shima nasa idanuwan da suka sauka akanta suke.

Jin harshensa na shiga cikin bakinta ahankali ya Sanyata rufe idanuwanta ahankali tana kasa kallan komai.

Qarasa hade bakinsa cikin nata yayi Yana kissing din bakinta tin daga cikin bakin har lips din.

Hannuwansa Dake riqe da bayanta ya saki Yana dawo dasu gaban Rigarta Yana zare maballan gaban rigar Daya bayan Daya ya zareta ya saketa ta zame zuwa qasa.

Qanqamesa tayi da sauri har lokacin bakinsa Yana cikin nata Wani irin kissing yake mata Wanda yake dumama jikinta Yana tada tsigan jikinta sbd nutsuwa da qwarewansa.

Haduwan kirjinta da nasa Babu komai a kirjin nata ya sanyashi kasa riqe qansa ya saki bakinta yafara kissing wuyanta zuwa kirjinta Dake Neman rabasa da notikan hakuri da juriyarsa.

Wuyanta suka kirjinta yake kissing Yana yawo da hannunsa tsakanin cikinta zuwa kirjinta.

Saukan hannunsa akan krjinta ya Saka hawaye gangaro mata sbd abune da Bai taba faruwa da ita ba ko a tsautsayin dayayita Neman afka mata.

Shi kansa zuwa baisan meyake Shirin faruwa dashi ba sbd komai na kansa ya Bude.

Yanda yake kissing nata Yana lasan lips dinta tareda yamutsa jikinta da tattausan hannuwansa ya Sanya hawayenta tsananta gudu hakama kuzarinta gaba Daya ya qare.

Bedroom dinsa suka nufa ya kwantar da ita kan gadonsa Dake tsakiyan gadon Yana kallan kyakkyawan fuskarta da idanuwanta ke rufe.

Bakinsa yakai kan idanuwan ahankali yayi kissing nasu tareda gangarowa har hancinta yayi kissing ya gangaro kan lips dinta ya shafesu da nasa lips din Yana Kai hannun Daya kan cikinta ya shafa,take taja Wani irin numfashi ahankali tana sake qanqame idanuwanta Dake rife,

Rigar jikinsa da cakuda tasaka botiranta budewa da kansu ya zame ya jefar bakin gadon tareda dagota kwance ya hade jikinsu

Daga shi har ita tare suka sauke numfashin Daya sakashi kwantawa tana kan jikinsa Bai tsaya komaiba ya kamo fuskarta ya sake hade bakinsa da nata Yana mata wani irin tsotsa hannuwansa na mata abinda yake sake tsananta fitar numfashinta cikin kunnuwansa Yana shigarsa da dumi Yana kuntosa gaba Daya.

Santsin fatar jikinta da qamshinta tareda Wani qananun kuka datakeyi ya sanya ASHRAF din dayake cikinsa bayyana ba ASH ba.

Kissing dinta yakeyi Yana zuqan duk Wani abu dayake cikin bakinta,

Hannuwansa gabaki daya sun samu kansu a inda suka fara cire Rai da sake sauka.

Juyar da ita yayi tareda mata rumfa ahankali Yana Kai bakinsa cikin Wani irin salon nutsuwa akan kirjinta kusan shine ya kusa rabuwa da numfashinsa ba ita kadai ba Dan na shiri ya dagota jikinsa ya qanqame Yana sake hade bakinsu kozai samu nutsuwansa ta dawo.

Ita kanta a tsorace take cikin firgici dan haka ta Dan qanqamesa Yana har lokacin kirjinsu a manne Babu me Riga a jikinsa.

Daqyar ya samu ya iya riqe kansa daga abinda yakeji ya rungumeta sosai cikin jikinsa tareda rufesu da abin rufa me taushin gaske Ya lumshe idanuwansa ahankali ya rufe Yana sake shigar da ita jikinsa.

Numfashi take fitarwa ahankali cikin sanyi a jikin jikin nasa itama idanuwanta a rufe.

Sosai yake yaqan abinda yakeji sbd kirjinta da babu kaya ajikinta dayake manne da nasa kirjin Yana Jin komai nasa na shigarsa Kai tsaye.

Kasa bacci tayi sbd tsoro har tsawon lokaci kafin bacci ya dauketa.

Sai Daya tabbatarda tayi bacci kafin ya zare jikinsa ahankali cikin nutsuwa ya sauka daga gadon ya nufi toilet ya shige.

Bai Wani jimaba ya fito ya rage hasken wutar dakin gaba Daya ya hau gadon a natse tareda gyara mata Kwanciya Yana rufesu da abin rufa.

Da asuba Yana fita sallan asuba

can itama ta Farka.

Tashi zaune tayi tareda ziro qafafunta ta sauko ta nufi kofa ta fita palon nasa ta dauko rigarta tasaka ta dawo ta zauna bakin gadon kenan kafin ta fara Saka botikan gaban Rigarta sai gashi ya dawo.

Akwai haske a dakin Amma ba sosai ba Dan haka kasa dagowa tayi ta kallesa.

Takowa yayi ya qaraso har bakin gadon ya zauna a natse Yana kallan abinda takeyi.

Saukan hannunsa kawai taji a kan gaban rigar tata numfashinta ya tsaya cak batareda ta dago ba har lokacin.

Hannunta ya janye yafara Saka mata botiran ahankali da kansa Yana kallan fuskarta dataqi dagowa ta kallesa.

Yana gama sakawa ta Dan dago kadan cikin sanyin murya tace

“Good morning”

Bakinta Daya furta kalmomin ya kalla ya saki murmushinda rabonsa da yinsa shi kansa ya manta.

A qataice ya amsa da cewa

“Kin tashi lfy??

Amsawa take kokarin yi ya Dan janyota jikinsa take maganarta ta koma ta dago idanuwanta Dake a sanyaye da narkewan tsoro ta kallesa shi Idanuwansa na zube a kanta shi Kuma.

Fuskansa gefen wuyanta ya Bude bakinsa dake bakin kunnenta cikin taushin muryarsa mara sauti ya furta mata kalman tafiya zeyi gobe.

Juyo da idanuwanta tayi ta kallesa batareda tasan tayi Hakan ba duk da saukan muryarsa cikin kunnenta ta kashe duk kuzarin jikinta.

Koyaushe saukan idanuwanta Wani sabon yanayi yake basa musamman datake kiyaye qin kallansa wasu lokutan.

Miqewa yayi ya shige toilet ba jimawa ya fito tana kwance lamo jikinta duk a sanyaye.

Jinsa cikin jikinta ya sanyata rufe ido ahankali kaman ta koma bacci Amma hankalinta na kan tinanin yanda zatayi rayuwa a gidan daga ita sai mum Aisha da masu aiki.

Bacci ya komawansa hankali kwance itama tin tana tinani kala kala har baccin ya sake tafiya da ita.

Da safen har 10 mum Aisha na jiransu breakfast Amma shiru,

Tinaninta da Mafi girman tashin hankalin mamakinta shine AmatulMaleek din tana dakinta ne Bata fito ba kokuwa?

Shi ASH Kuma wannan ne karo na farko rayuwarta a gidansa dataga yakai irin wannan lokacin ma Bai fitoba ya Dade da ficewa tini.

Tanason taje dakin Amatu ta duba Amma zuwanta dakin zaisa ASH idan yaji yayi tinanin taje da niyar yi mata Wani abin ne.

Ita kadai tayi breakfast dinta zuciyarta na tafasa ta gama ta miqe tabar dining din Tana zuwa dakinta ta shirya ta zari key na motarta ta fita zuwa dubo Danta Dan mr Jameel ya sanar mata asibitin dayake bayan ASH ya Bada Daman a sanar mata.

Sai 10:30 ta fito ta wuce dakinta Kai tsaye bayan ta Dan tsaya dining din ta dauki slice Daya na bread taci sbd yunwa sosai takeji ga jikinta na Dan mata ciwo.

Ko data shiga kaman koyaushe angyare koina,

Wanka ta tube ta shiga ta jima sosai sbd Dan ciwon da jikinta ke Mata ya sake.

Kodata fito a natsenta ta shirya cikin Riga da skirt dinma yau ta fito taje ta Dora tea dinsa Wanda yau milk tea ne Tayo dayaji kayan qamshi sosai da strawberry Lipton sai condensed milk me kyau da ta jero ta kawo.

Bata qarasa ajiyewa ba ya shiga dining din Yana fidda qamshinsa da nutsuwa da kamewansa sedai idanuwansa na kanta harta qaraso ta ajiye kan table.

Cikin sanyi ta sake gaishesa tana Dan qin kallansa.

Amsawa yayi bayan ya Kalli shigar datake jikinta wadda ta fidda shape dinta me kyau sosai.

Zama tayi bayan ta gama zuba masa duk abinda tasan zai buqaci a lokacin.

Yana fara cin abincin wayarsa tafara ringing ko kallan wayar beyiba bare nuna alaman Kiran nasa ne.

Suna gamawa ya miqe bayan ya goge bakinsa ya sauki wayoyinsa ya nufi kofa ahankali ta furta masa kalman Allah ya tsare cikin sanyi batareda ta dauka zeji bama.

Dakatawa ya danyi ya juyo ya kalleta kafin ya sake mata murmushinsa me sanyi da Bata taba ganiba a rayuwanta ya wuce yabar iskan gurin da qamshinsa.

Sai data dauki mintina zaune a gurin sosai kafin ta samu iya qarasa cin abincinta cikin sanyi tukuna ta baro gurin.

Tareda ita su karima sukai clearing table din suka Kai komai kitchen ta wuce bedroom dinta.

Batada abin yi bayan zaunawa tana wayoyinta yau takasa samun numbern maamah ma Dan haka tana gama waya dasu Haydar tayi da anty Farha da bazata samu shigowa yau dinba sai ta sauko kitchen Dan yin Wani abin zaman ya isheta.

Abincin Rana sukai Se Cookies da Wani cake din Dan ko na jiyan kadan sukai yau Kuma sai sukai choculate cake maimakon vanilla da sukai jiya,

Suna gamawa sama ta wuce lokacin har karfe biyu ta wuce.

Dakinsa ta nufa Kai tsaye tayi aikinsa tareda sauya masa tiraren cikin humidifier zuwa na oud me dadin qamshi ta kunna AC na palon kawai na dakin ta kashe ta fito.

Dakinta ta koma a matiqar gajiye ta zare kayanta ta shiga toilet Dan yin wanka.

Dayake harda wankan tsarkin gama period zatai ta jima sosai a toilet din kafin ta fito ta zauna tagama shiri ta miqe ta saka satin free size Riga da  palazzo pants na Versace ta daura silk scarf akanta ta Saka hijab tayi sallah tana idarwa ta fito ta dawo palonsu ta zauna tana cin abinci tana kallo Sama sama.

Su karima ne suka hawo saman janye da akwatinan Husnah gida biyu ita kanta Husnah din tana bayansu sanye cikin pencil jeans da free size long sleeve me Dan tsayi fara sai scarf sosai ta sake fresh abinta.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

41

***************

AmatulMaleek na ganin Husnah taji Wani sanyi na da nutsuwan zuciya na shigarta na dawowan mahaifiyarta Dan haka ta ajiye plate din da yake hannunta tareda daukan tissue tana goge Baki ta miqe tana zira slippers ta nufo hanyar saukan.

Husnah data tsaya kallan AmatulMaleek cikeda mamakin abinda takasa sanin tanawa mamakin sbd gaba Daya Amatun ta sauya Tako Ina,

Batai tsammani ko tinanin ganinta kaman wadda taje Hutu qasashen Jin dadin duniyaba,

A nata tinanin Amatun na Nan cikin damuwar rashin maamah da qunci da damuwa,

To kokuwa dai Daman baqin ciki da damuwa da kunci suna Saka mutum fresh da komawa kaman Wanda yake kwana Yana tashi cikin Madara?

Da kyakkyawan murmushi akan fuskan Amatun ta dakata tana kallan Husnah tana mata barka da dawowa,

Ganin Husnah ta kasa amsawa tana kallanta ya Sanyata wucewa ta sauka da sauri zuwa bangaren Maamah da aka ware mata na musamman tasan can su Farida sukai da kayanta ta bisu.

Tana Isa su Farida harsun aje akwatin maamah din anfara sake goge komai na dakin da tsaftacesa duk da komai sabone Babu Wanda ya taba shiga so Dole a sake tsaftacesa.

Rungume maamah din tayi batareda ta tsaya komaiba idanuwanta na cikowa da hawaye tace

“Maamah bayan wata kusan biyu Se yau kike dawowa ga ‘yarki,nayi kewanki kaman me,Kun barni ni Daya Basu Abdul ba kowa.”

Murmurshin farin ciki da sanyin Daya cika zuciyarta na ganin yarta a yanda ma batai tinanin ganintaba maamah ta sake tana kallan Amatun da kulawa tana cewa

“To ba gashi harmun dawo ba kaman ma bamu tafi ba mun sameki kalau ga Kuma sabon guri dasu Karima duk Kuna debewa juna kewa.”

Murmurshin farin cikin Dake cikeda ranta taketa sake sakewa tana zaunawa dakin maamah din da Bata ma taba zuwa ba tinda suka dawo gidan sbd baa ma budesa ba.

Itama maamah din zama tayi tana yaye mayafin jikinta tana sake kallan dakin tana tinanin girma da tsarinsa zai isheta itada Amatun basai tayi zaman can cikin Mansion dinba yanzu.

Amatu kuwa kayan maamah din da kanta tafara budewa tana cewa

“Maamah wai shikenan kukaje kuka zauna har wannan lokacin Sai yanzu,

Da Hutu be qare ba da bama yanzu zaku dawo ba kenan”

Miqewa maamah tayi tana cewa

“Bara dai na shiga bayi na fito sbd naga alaman ba Zaki Dena maganar Nan ta anqi dawowa da wuri ba Amatu”

Toilet ta shige sai alokacin Farida suka gama gyara dakin suka fice itama Kuma Amatu taci gaba da Bude kayan maamah tafara jera mata Wanda suke a wanke a Amma bataga alaman guga a taredasu ba Dan Daman maamah din Bata iya guga

Abdul ne me wanke musu kayansu ya goge musu gaban dayansu ita Kuma undies nasu kawai take wankewa nata data maamah.

Fasa jera kayan ma tayi ta sake Kiran karima ta miqa mata kayan tace a sake wankewa a goge tkuna a dawo dasu.

Karba karima tayi ta tana cewa to ta juya ta fice tareda Jan kofar bedroom din.

Maamah data fito lokacinda karima ke karban kayan kallan Amatu ta Dan yi tana Dan nazarin abinda tayi din kaman matan gida na bawa masu aiki umarni Amma dai batai magana ba sbd wannan Wani abu ne na daban bama wancan din ba.

Sallah ta shimfida dadduma tana kokarin yi bayan Amatu ta nuna mata gabas.

Fita Amatu tayi daga dakin ta nufi kitchen Kai tsaye ta hadawa maamah abinci da kanta a trey ta koma ta Kai mata su Farida ma hadawa Akai aka nufi dakin Husnah dashi wadda itama Saida aka sake tsaftace mata dakinta tsaf Wanda komai yayi mata yanda takesonsa sedai ganin hadeta guri Daya da Amatun Sam Bai mata ba tinda Anyiwa maamah daki me zaman kansa da AmatulMaleek din ta koma can kawai.

Koda Amatu ta kawo abincin maamah ta gama sallah Dan haka zaunawa tayi gefenta bayan ta ajiye abincin a qasa.

Abincin maamah ta Bude tana cewa

“Me kuka dafa ne?

Yanzu su waye suke aikin abincin tinda Kun koma makaranta ke bakya zama.”

“Hutun ne ze qare dai Amma banfara zuwa ba,su karima ne ke abincin Amma khaltume ma tadawo”

Abincin maamah ta fara diba zata ci batareda ta dago ba tace

“Ke Kuma sai kike zaman me to bakya zuwa aiki a kitchen din kunayi gaba dayanku?”

Tambayan ta Saka AmatulMaleek dagowa ta Kalli maaman sai tace

“Dani akeyi lokutan da dama aikin”

Shiru maamah tayi kawai tana fara cin abincin tana janyo Wani zancen Dan su bar wancan.

Firan su Abdul suka fara maamah na cin abincin itama Amatun spoon ta Saka sunacin tare da maamah sbd Bata Wani ci abincinta na ranan ba suka iso ta ajiye ta fito.

Zamanta tayi a dakin tareda maamah sunata fira da kewan juna da sukai na tsakani uwa da ‘yar har magrib.

Anan tayi sallah ta sake lafewanta anan har Akai ishai tukuna ta fita ta nufi kitchen ta Dora abinda ta San dole ne ta Haye sama Dan Shirin bacci ta koma tareda maamah zata kwana ayau.

Wanka tayi ta Saka Riga da wandon bacci marasa tsayi sosai tayi duk abinda zatai ta Sako hijab dogo ta fito ta juye tea din ta jera komai ta dauka takai dining ta ajiye ta juyo ta koma dakinta wayarta kawai ta dauka ta fice batareda ma Taga fitowan Husnah ba wadda itama hutawa takeyi a dakinta sai datai ishai ta fito zuwa dining daidai mum Aisha itama da batasan sun dawo ba ta dawo gidan ta fito zuwa cin abinci.

Husnah na ganinta taji farin ciki tareda fadawa jikinta tana ambatar sunanta.

Mum Aishan ma nata farin cikin ta bayyanar duk da akwai abinda yake ranta game da Husnah din Dan kuwa zayyan ya tabbatar mata da kaman Husnah ce last mutum da Naufal din yayita kira a wayarsa kafin ya rabu dashi Amma Bata daukaba,

So take taji komai Daya faru daga bakin Naufal duk Wanda yake da hannu a wannan masifar data afkawa Danta wlh Saiya biya Daya bayan Daya.

Cikin farin ciki da sakewa tace

“Husnah yaushe kuka dawo ne?

Yaya Su Antyn porthcrt din dasu Faisal anata fama da hakurin rashin hajiya,Allah de yaji qanta yayi mata Rahama.”

Amin”Husnah ta amsa tana sake fadan kowa lfy.

Dining room din suka nufa suna shiga Yana shigowa idanuwansa akan Husnah da itama shi take kalla cikin tsananin farin ciki ta qaraso gabansa ta ya miqa mata hannunsa a natse ta kamata tana cewa

“Ohh finally naga Dad dina yau,Dad barka da dawowa”

Fuskarta ya kalla cikin kulawa da kauna me zurfi irin ta Uba Yana amsawa da cewa Yaya suka dawo,Yaya maamah?

“Maamah na dakinta,lafiya muka dawo.”

Zama sukai a dining din Yana amsa gaisuwar mum Aisha da itama take miqowa cikin girmamawa da sakin fuska.

Tinda ya shigo idanuwansa Basu ganta ba seda ya zauna ganinsa ya sauka kan tea set Dake Jere a gurin ya fahimci ba dawowa zatai ba dole tana can tareda maamanta Dan haka a natse ya ci abincinsa batareda yasha tea din ba hakama Babu Wanda ya lura ko fahimtar wai Yana buqatan Shan ruwan zafin abincinsu kawai suke ci cikin kulawa da se Husnah Daketa magana akan abubuwan dasuka faru acan porthcrt dama son zuwa dubo mum dinta datai a wannan hutun Amma Bata samu zuwanba.

Yana gamawa ya miqe yabar gurin Husnah ma ta gama ta miqe tabi bayansa har palonsa anan ya zauna ta zauna suna magana sosai sbd tayi kewan Dad dinta kaman yanda yayi kewan yayansa duka Shima.

Sai 9:36 ta baro palon nasa ta wuce dakinta sbd baccin datakeji me Dan qarfi,

Wayarsa ya dauka ya tura Sako ya kashe wayar gaba Daya tareda miqewa ya nufi bedroom dinsa ya shige.

Itama Amatu sosai sukai fira da maamah kaman wanda sukai shekara da shekaru basa tare,

Fiyeda Rabin firar dukan cikinta ne maamah keyi cikin zance Dan Jin ko akwai Wani kusanci ko magana dayake shiga tsakaninta da me gidan Amma Sam Babu abu Daya data gane a maganganun Amatun Dan haka take Jin nutsuwa a ranta haryanxu Amatun nada Chance na rabuwa da auren duk da batasan tayaya zata raba wannan aurenba sbd ASH din bama zata iya tinkara ko iya furta ko Kalma Daya data danganci auren a gabansaba,Su kawu Kuma akan auren ko jefeta da asiri zasu iyayi tabi duniya ta bace bat Dan haka take cikin tsaka me wuya tareda damuwa me girman gaske har lokacin cikin ranta gameda auren duk da tsaban Babu ma komai na maaurata dayake cikin auren mantawa takeyi da auren kowama kusan mantawa yakeyi da auren sai can idan an Tina.

AmatulMaleek da Sam batasan me maamah ke nufi ba da mata wasu tambayoyin amsa mata tayi Kai tsaye sedai batajin ma ko a maganarta Wani zai iya fahimtar ma akwai shaquwa ko kusanci a tsakaninta da ASH bare mahaifiyarta datake ganin auren haramtacce ne.

Bacci ne yafara kokarin daukan maamah sama sama wayar Amatun tayi haske alaman shigowar Sako tana toilet.

Tana fitowa maamah tace

“Kaman ankira wayarki tanata kawo haske tana daukewa”

Nufo wayar Amatu tayi tana goge fuskarta da towel qarami sabo dayake toilet din sbd zata kwana anan karima ta daukosu guda uku tazo ta jera.

Zaunawa tayi bakin gadon ta dauki wayar tareda budewa ta duba.

Shiru tayi bayan ta karanta sakon,

Juyowa tayi a hankali ta Kalli maamah wadda itama ita din take kalla.

Numfashi ta sauke a boye sbd batasan ya zatai taje takai masa abinda yace Akai masa din ba.

Maamah kallan datake mata Sam ko a mafarkinta Bata taba kawo tinanin ASH a lamarin Amatun ba Dan haka ko lokacin kallan datake mata na daban ne sauyin datake Gani a tattareda Amatun ne yake Sakata shiga tinane tinane sbd ko fatan jikinta kadai abin kallawa ne a yanzu.

Miqewa Amatun tayi ahankali tareda nufar hijabinta sbd tsarguwa da kallan da maamah ke Mata a natse take cewa

“Zan turawa anty Farha Sako yana dakina”

Cikin murya me Dan bacci a ciki maamah tace

“To idan kinje kiyi zamanki acan din harda safe wannan yawon daga Nan zuwa can baida amfani da daddare”

Kasa cewa komai Amatun tayi sbd dole saita dawo ta kwana da maamanta a yau.

Hijabin ta Saka ta fice tareda rufo dakin ta nufi kofan kitchen ta Bude tabi ta Nan ta shige ta bulla hanyar hayewa saman.

Ko data hau tsit alaman Husnah ta shige Dan haka ko bedroom dinta Bata biya ba ta wuce dining room ta hada komai da zata Kai masa ta wuce.

Ko data Isa Baya Palo Kuma dayake tea ne kawai ba komai saita wuce Kai tsaye bedroom din nasa.

Budewa tayi ahankali bayan tayi knocking so Daya ta shigo Babu haske sosai a dakin hakama Baya dakin da alama Yana toilet Dan haka ta nufi inda zata ajiye Kai tsaye gurin makeken windon dakin Da kadan ya zama Kofa acan sofas guda biyu suke da table a tsakiya ta ajiye kenan hasken manyan wutan dasuke zagaye da Gidan suna ratsota ta window.

Bude kofan toilet da yayi yai daidai da lokacinda ta durqusa Dan zuba masa.

Tana gama zubawa kafin ta dago qamshin Aesop Daya cike dakinta ya tabbatar mata da wanka ya fito.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

42

***************

Kasa waiwayowa tayi sbd hannuwanta suka Dan fara rawa sbd yanda zuciyarta ke bugawa dan duk yanda dakin yakeda rashin haske

Hasken window da curtains dinsa suke gefe Yana haske dakin.

Yanda hannuwanta ke Dan rawa ya Saka tea din data zuba zubar mata a hijab ta ajiye tana Dan rintse idanuwanta ta Bude tareda daukan tissue Dake gurin tana gogewa hakama tana son tashi ta juyo Amma takasa Hakan Dan batajin ya gama shiryawa.

Zuban da tea tayi a jikinta kusan ya lura da Hakan yakuma San tea din nada zafi sosai Dan haka ya ajiye towel Dake hannunsa Yana goge jikinsa ya nufota Wanda duk takunsa Daya Dake nufota a cikin kunnuwansa zuwa zuciyarta yake sauka.

Yana isowa gab da ita tana miqewa tsaye batareda ta juyoba shikuwa gabanta ya zagayo ya tsaya tareda kallan hijab din Kai tsaye ya tattarasa ya cire mata tinawa da ko konuwanta na last time ruwan zafi ne.

Sakin hijab din yayi qasa tareda kallan fuskarta Dan karantar yanayinta ko akwai radadi a ciki.

Cikin kulawa ba zato taji kalmansa na cewa

“Kin Kone ne?

Akwai zafi?

Ruwan akwai zafi sosai ne?

Zaunawa yayi kan kujeran gurin tareda zaunar da ita kan qafafunsa a karonta na farko kenan kafin ta Bude bakinta tace masa ba zafin komai

Hannunsa ya sauka kan lafiyayyar cinyarta Dake bayyane sbd wandon kayan baccinta beda tsayi ko kadan.

Dubawa zaiyi batasan lokacinda ta Dora tafin hannunta kan nasa hannunba cikin Wani irin sanyin sauti tace

“Ba zafi…

Hakan data furta cikin Wani irin sautin da sanyinsa ya dakatar dashi ya sanyashi dawo da kallansa fuskarta itama shi din ta Dan dago ta kalla Dan tabbatar masa da Bata Kone din ba.

Fuskarta yake kalla a tsanake ita Kuma ganin kallan sai tayi qasa da nata idanuwan tana kasa kallan jirkinsa da Babu kaya Se towel hakama gata kan qafafunsa a zaune.

Numfashi mara sauti ya sauke tareda Maida idanuwansa gurin datace Bata qone din ba ya kalla

Fatan cinyoyinta Dake bayyane tana daukan ido duk da ba iya hasken window ne kawai.

Tea din dayake ajen ta miqe hannunta Daya ta dauko tareda miqa masa har lokacin tana qin kallansa.

Shiru yayi tsawon seconds Yana bin hannunta Dake dauke da cup din zuwa wuyanta da kallo kafin ya dauke hannunsa Daya daga kan cinyarta ya karbi cup din kafin yakai bakinsa ya Dan zubar masa a jikinsa Shima sedai ruwan tea din ya Riga ya huce ba Wani zafi.

Tissue ta miqa hannunta ta dauko ahankali ta Dora kan kirjinsa da ruwan ya diga daga ita harshi dagowa sukai suka kalli juna sbd abinda kowannensu yaji.

Cup din hannunsa ya ajiye sbd gap yake da subucewa daga hannun nasa.

Hannunta ya kama ya riqe tareda Saka hannunsa Daya ya zare tissue din hannun nata Yana janyota jikinsa dakyau Yana Jan qamshinta me sanyin dadi.

Fuskarsa Daya Sako ahankali cikin wuyanta ya Sanyasu sakin ajiyan zuciya a tare tana Dan Jan numfashinta dayake Neman daukewa a boye.

Fatan wuyanta ya dora lips dinsa ahankali yayi kissing take jikinta ya dauki Wani irin dumi tana narkewa a jikin nasa.

Sake kissing wuyanta yayi Yana zagayeta da hannuwansa zuwa cikin rigarta ya shafi cikinta hannunsa me Dan sanyi

Ba shiri ta ja Wani irin numfashi mara sauti tana Dora tafin hannuwanta a tsakiyan bayansa da babu kaya.

Wuta ya dauke na sakanni kafin ya qarasa cusa hannunsa cikin rigarta Yana Bude gaban Rigar daga ciki hakama fuskarsa na hadewa da tata Bai tsaya komaiba ya hade bakinsa da nata Yana hada bakinta da sauran taste na mouth wash dinsa Yana tsotsewa.

Rigar Dake jikinta ya qarasa zarewa ya jefar qasa suna gyara zamansu akan kujerar sbd girmama da lamarin yayi hasken window fes akansu Wanda ke basa Daman juyata a jikinsa yanda yaso cikin nutsuwa da Wani irin fitinanniyar romance din Daya juya qwaqwalwan kanta.

Kusan qaramin kukanta da yaqan kansa da yayi ya Sanya Babu abinda ya faru da ita a Daren sedai kusan jikinta Babu inda Bai amsa kowanne irin sakon da aka saukar masa ba.

Bacci sukai sosai har kusan makara yayi sallan asuba

Koda ya dawo itama tayi sallan

A jikinsa suka qarasa adduan datake yi kafin ta Dan dago tayi masa Ina kwana cikin murya me sanyi tana kallan hannunsa dayake sarqe da nata kaman Wanda shine ya tsarawa kansa komai,yatsin hannuwansa fresh dasu kaman basa komai kaman Seka wanke hannunka zaka iya tabasu.

Hannunta yakai bakinsa yayi kissing ahankali kafin ya amsa gaisuwar nata Yana tambayar ta qonuwan jiyan

Bata dago ta kallesaba ta sake tabbatar masa da Bata koneba.

Cikin sauti mara hayaniya ta Bude Baki tace

“Gobe ake komawa school”

Numfashi mara sauti ya sauke ahankali Yana zagayeta da hannunwansa yace

“Se next week Zaki koma”

Shiru tayi kafin ta dago idanuwanta tareda Dan juyowa zata kallesa bakinsu ya hade sbd fuskarsa Dake dap da bayanta.

Janye bakinta zatayi ya tareta ta hanyar zira harshensa cikin bakin Yana matseta jikinsa.

Kissing dinta yakeyi Yana shafa wuyanta hannuwansa na yawo cikin doguwar hijabin jikin nata.

Gari Daya fara haske ne ya Sanyata zamewa ahankali tareda miqewa tana kasa kallansa da idanuwanta da suka narke ta Kalli time Wanda Shima time din ya kalla Yana komawa cikin abin rufa kawai.

Kayan tea din ta tattara ta fice dasu tana fitowa palon tafara Jin fargaban haduwa da Wani idan ya a fita.

Ko data fito ba kowa sbd qarfe 6 ne lokacin,

Kai tsaye kan dining ta ajiye kayan ta wuce ta nufi palonsu ta shiga Kai tsaye bedroom dinta ta nufa ta zare hijabinta ta shiga toilet Bata jimaba ta fito ta Haye gadonta tareda shigewa bargo tana komawa bacci.

Bata Farka ba sai after 9 Dan haka Bata fito ba Sai datayi wanka ta shirya  cikin halfboubou da pencil skirt na Wani ash lace da tsadansa take a bayyane Kuma a boye Dan kuwa kudinsa ita kanta Amatun Bata saniba cikin kayan da aka Siya ne anty Farha takai mata dinkuna kaya guda Wanda Babu Wanda kudinsa idan su kawu sukaji bazasu Shiga shock ba.

Da wayarta a hannu ta fito Kai tsaye dakin maamah ta nufa tana Isa,

Maamah na kitchen Ashe sbd tace bazata iya zaman Bata motsa jiki ba.

Kitchen din ta dawo tana kallan maamah din zaune tana yanka cabbage suna fira da khaltume sama sama.

Gaidasu tayi tana kallan maamah din wadda itama ita take kalla tareda sutirar jikinta da batasanta dasu ba hakama batasan waye ya Dinka mata su ba Amma dai Bata ce komaiba.

Zama Amatun take kokarin yi gefen maamah Farida ta qaraso ta sanar da ita angama shirya dining Kuma kowa ya halarta dining din.

Shiru Amatun tayi zata juyo ta Kalli maamah sai maamah din ta dauke Kai tana ci gaba da abinda takeyi.

Miqewa tayi a natse tabi bayan Farida sbd khaltume Dake gurin yasaka daga ita har maamah kowa kasa cewa komai.

Ko data hawo ta nufo dining room din qamshinsa shine ya shiga hancinta ta tabbatarda Yana cikin dakin Dan haka tana Sako Kai idanuwanta Bata bari sun sauka akansa ba ta qaraso kafin ta zauna mum Aisha ta Dan fara kalla a natse da muryanta me taushi tace

“Ina kwana mum Aisha”

Amsawa mum Aisha din tayi tana qin kallan Amatun.

Gurinsa ta kalla a natse cikin girmamawa ta sake Bude Baki tai masa Ina kwanan Shima.

Wani kallan Daya dago yayi mata ya Sanyata Maida idanuwanta kan inda zata zauna ta zauna ahankali tana kallan Husnah wadda take kallan kayan jikin Amatun Dan kuwa sutura ce irin wainda mum dinta ce kadai take saka irinsu a cikin Mansion din ASH TALBA gaba Daya.

Laces ne da kusan order dinsu ake Badawa sbd tsadansu tayaya zaace Amatun tana sakawa,

Idanma fake ne to Ina ta samu fake din?

To kodai gobarar da Akai da parking ta samu cikin kaya tana sakasu to Amma Kuma jikin Amatun da mum dinta ba Daya ba.

Husnah ce tayi serving din Dad dinta Kuma Babu Wanda ya damu da Hakan bare nunawa harsukaci suka gama Babu Wanda yayi magana.

Itace ta dago ahankali Jin idanuwansa akanta Akai Akai

Ta kallesa tareda mayar da kanta kan plantain da sauce datake ci tana Jin zuciyarta na kasa nutsuwa da gurin sbd su mum Aisha da Husnah Dake gurin.

Yana gamawa ya miqe yabar gurin Husnah na bin bayansa cikin nuna shi Dad dinta ne tafi kusanci dashi fiyeda kowa Dake rayuwa a Mansion din yanzu.

AmatulMaleek kuwa Daman a takure take Dan haka miqewa tayi itama ahankali tabar gurin ta koma gurin maamah ta Saka musu aiki a abincin Rana da zaa fara aikinsa lokacin.

Mum Aisha kuwa ficewa ta sake yi

Husnah ma tana dawowa wanka tayi ta shirya ta fita da driver akwai guraren da zata.

Aikin abincin sukai suna fira suna magana maamah ta danne abinda yake ranta har suka gama kowa yaje yayi sallah Amatun ma tana dakin maamah acan taci abinci tayi baccin Rana ko data tashi da yamma harsun Dora girkin dare.

Bedroom dinta ta wuce bayan ta takura maamah ta koma dakinta ta huta zata kama su qarasa aikin.

Kayan jikinta ta sauya zuwa doguwar Riga tayi sallan laasar ta sauko suka qarasa aikin har magrib kafin ta koma sama.

Yauma kusan Bataci abincin tareda su ba Dan haka dole daga baya sai dataje dakinsa bayan kowa ya shige acan ta kwana bayan asuba ta dawo dakinta ta qarasa baccinta.

A darenma hakance ta faru dan kusan ma ranar lattin fitowa tayi sai bayan karfe 7 ta baro.

Babu Wanda Koda alama Koda tsautsayi ya taba ganin shigarta da fitowarta sedai mum Aisha datake lura da idanuwan ASH Sam basa iya controlling kansu matiqar Amatun na taredasu cin abincin,

Wannan shine babban tashin hankali da tsoron da mum Aisha ke shiga tana fatan Allah yabawa Danta lafiyar sanin inda kansa yake kafin Amatu tayi nasarar zama cikakkiyar matar ASH TALBA.

Husnah bata taba kallan Amatu da girma ko darajar da ko kallanta Dad dinta zai iyayi ba bare har sanin hanyar ma zuwa palonsa shiyasa ta kyaleta da iya arzikin sitirar data samu a qarqashin igiyan auren Dad dinta Wanda a yanzu tasake dagewa da addua ba dare ba Rana Mum dinta ta farfado ta yanda Dad dinta zaima Manta da wasu igiyoyin auren Amatun bare ita da haryanxu Bai gama gane kamannintaba.

Maamah kuwa ganin matsayin matar gidan ASH TALBA dayake Neman hawan Amatun ya sakata Saka ido sosai tareda tsananta dokokinta akan Amatun wadda ta hanawa zama cin abinci kwata kwata tareda su dakuma duk Wani abu dazaisa ko inda ASH TALBA ya bi zata iya bi ko qamshinsa taji,

Duk hanyar handuwansu maamah ta tosheta duk da Daman tasan bawai sanin kamannin Amatun yayiba,

Duk zasu gaisa da ASH din duk dare idan ya zauna cin abinci maamah tareda Amatun suke shigowa su gaidasa su fice batareda damuwan komaiba yake amsawa cikin mutuntawa da kamewansa.

Wannan matakin da maamah ta dauka shine abu Daya Da yayi wa ran mum Aisha sanyi Tin bayan dawowanta Dan haka ta sake budewa maamah din wuta da gori da maganganu akan taci amanar Abeeda taci amanar kauna da zumuncinsu duk ta bari yarta ta zama kishiyar Abeeda.

Maganganun na cin zuciyar maamah Amma hakanan take dannesu,

Ita kanta Husnah dagawa maamah din hankali tayi akan auren Dan haka Tako wane bangare maamah ta toshe rayuwar Amatu acikin gidan Se idan zata kwanta da daddare take barinta ta tafi dakinta.

Duk wannan tsananin da maamah ke Mata akan ASH TALBA har lokacin Babu Wanda yasan a tare suke kwana kowanne dare a gidan.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

43

*************

Naufal ya farfado cikin tashin hankali da kuka da baqin cikin ganinsa da qafa Daya dayar dole an ya keta sbd gyaran yaqi yi Neman lalacewa takeyi,

Kuka ya Ringa yi Yana tsinewa ASH TALBA da ‘yarsa Husnah qasa qasa sbd kada a jisu Amma zuciyarsa na cikin Mafi girman baqin cikin rayuwarsa,Babu Wanda ya cucesa ya kashe masa wannan rayuwar tasa bayan ASH TALBA da shegiyar ‘yarsa Husnah.

Mum Aishan ma tsinewa jinin data hada na uwa da ASH takeyi sbd ko moqiyinta bazai mata wannan abin da ASH yayi mata ba,

‘danta Daya a duniya datake dashi Wanda bayanshi har abada ansan bazata samu Wani ba tinda lokacin haihuwa Kam ya wuce mata,

Ko a gurin ubansa shi Daya ne namiji beda Wani Amma ASH sbd mace ya harbe mata qafafunsa,

Macen ma ‘yar me aikin gidansa sbd kawai Yana ikirarin Asmaun tamkar amanar Abeeda ce.

Ita Kuma asmaun ita da shegun ‘yayanta tana dauka Wani matsayin ne da ita ko mahimmanci basusan alfarmar Abeeda ce suke ci a zuciyar ASH din ba harma da ‘yayansa Dan kuwa da Abeeda zata dawo Husnah ko kallan inda maamah take bazata sake yi ba bare shi kansa ASH din.

Sam Bata fahimci tsinuwar sa Naufal kewa Husnah ba kota Menene a lokacin sbd kuka yakeyi sosai baqin ciki da tashin hankalin ganinsa a wannan halin dayake tafarasa zuciyarsa da jinin jikinsa.

kuka takeyi sosai Dan kuwa baqin cikinta da zafinta Baya bayyanuwa acikin Mansion din ASH Se ta fito, gashi qarfi da yaji kaman yanda ASH ya Saka aka Hana zancen fita hakama ana jinyar Naufal din cikin Sirri duk Kuma tasan sbd kare suna da martabar Amatun ne itama dole ta boye zancen Babu Wanda yasan abinda ya faru ko a dangin mahaifinsa bare Kuma mahaifin nasa da Baya ma kusa Yana bayelsa da zama tareda iyalinsa duk da Daman ya yafe mata Naufal din tini ya ciresa a jerin yayansa duba da rabuwar da sukai dakuma rikicin da Akai Akan yaso karban Naufal din tin Yana yaro.

Jinyar boyo itama ta shiga dole anai masa ko a cikin gidan su Husnah da maamah Basu San meyake faruwa ba kaman yanda basusan gobara Akai tsoron mansion din ba kawai dai sun dauka sauya aka samu tinda ba wani abin mamaki bane.

***AmatulMaleek ta koma hutunta tafara fita school Dan haka ma Se hankalin maamah ya sake kwanciya ta sake kiyayewa a fakaice cikin Sirri sa nutsuwa take sake nesanta Amatu da duk Wani abu Daya danganci wannan auren dayake kanta.

Ita kanta Amatun data far fahimatar maamah din gameda nesantata da shiga ma ko inda ake cin abincin gidan ne sai itama ta Dan fara kiyayewa tana kokarin nesanta kan nata da shi sedai ga mamakinta Hakan ya kasa yiyuwa sbd Wani irin sabo da shaquwa datai dashi din,

Sam shi kansa a yanzu ita kadai ce take iya kasancewa a tareda dashi yayi baccin Nutsuwa da Kwanciyar hankali bayan sun gama gigita mata Kai da wasu hot romances dinsa.

Hakama abincin kansa na dare daga shi har ita sun Dena ci Se takai musu suke cinsa a tare Wani a cinye Wani a lashe Wani Kuma duk a cikin bakinta yake qarasa cinyesa.

Abu na biyu Daya fara azabtar da ita shine tinanin ranarda maamah din zata fahimci abinda yake faruwa gashi Tako wanne bangaren yariga yayi mata illar da bazata iya qi ko gazawa komai nasa ba,

Baccinta harya Saba Baya zuwa sai tana cikin jikinsa

Shi kansa nasa baccin Baya zuwa Saiya gama lashe fatan lips dinta da wuyanta tareda yawun bakinta kafin ya Sakata jikinsa qamshinta na basa duk wani Kwanciyar hankalinda bacci me dadi yake buqata.

Ta bangaren zuwa school kuwa mota aka sauya mata wadda ta rabata da zuwa tareda Husnah Amma baqin cikin Husnah din ya Saka ta dakatar da nata drivern ta dawo bin motar Amatun sbd gaba Daya yanzu idonta da hankalinta ya fara dawowa kan Amatun kwata kwata hankalinta Baya kwance akan rayuwar data ga Amatun tafara samu ta walwala Bata so Kuma bazata taba so mutane su fara recognizing AmatulMaleek din a matsayin matar Dad dinta ba duk da tasan har abada idan har mum dinta na Raye ko tana cikin coma bazai taba noticing kowacce irin mace ba Dan haka ta sake dagawa Maamah hankali a fakaice gameda sakawa Amatun ido da tsananin doka.

Maamah ma kanta Daman Bata buqatan wasu sauye sauyen da zasu wuce misali na zaman Amatun ‘yarta a gidan Dan haka ta sake daurewa Amatun sosai gameda wasu abubuwan dole Amatu tafara shiga damuwa sbd hatta dakinta kusan idan ba baccin dare ne ze kaitaba maamah kusan Bata bari Dan haka itama ta Dena dawowa daga school da wuri gurin anti Farha take maqalewa suna fira da sauran abubuwansu Se kusan magrib take Dawowa kullum.

Hakan datakeyi ma still sai baiwa maamah din dadi ba dole ta hakura tana dawowa kan lokaci.

Yau satinta kusan hudu da komawa school a gajiye ta dawo gap da magrib Dan haka ana parking motan ta Bude ta fito batareda ta jira anbude mata motarba ta nufi ciki Kai tsaye ta kitchen tabi ta Haye sama zuwa bedroom dinta sbd tana buqatan gasa jikinta period yazo mata tanajinsa a hanyarta ta isowa gidan.

Shigarta bedroom dinta Jakarta ta jefar a kujera tana warware qaramin mayafin Dake nade a kanta tana zare doguwar rigarta ta dauko towel tana gama daurawa ta zare bra dinta ta jefa kan kayan data cire kenan karima na buga kofan dakin a tsanake tana shigowa.

Dauke take da ruwa da juice masu Dan sanyi ta ajiye tana sake yiwa Amatun sannu da dawowa.

Amsawa tayi tana tambayar Ina Maamah tana Ina?

Tana dakinta angama abinci da wuri ne yau din shiyasa ta shige da wuri inaga.

Gyada Kai kawai tayi tana nufar toilet.

Karima kayan da Amatun ya cire ta kwashe ta fita dasu.

Wanka tayi da ruwan zafi masu Dan warware gajiya sbd yau yawon da sukai da anty Farha yayi yawa duk da acikin lafiyayyar mota suke cikin AC Amma akwai gajiya.

Ko data fito wankan shiryawa tayi cikin kayan bacci Kai tsaye sbd anriga ma anfito sallan magrib.

Riga da wando ne masu taushi wandon har qasa yake sedai rigar kaman singlet ce Dan haka ta Saka bra kafin ta tashi Kwanciya.

Sosai take fidda qamshinta me dadi da sanyi Wanda dole maamah tafara sabawa da tantancesa hakama Husnah duk baqin cikinta akan tiraren koyaushe tsananta yakeyi musamman data kasa ganinsa bare ta bincika kudinsa taji Amma a saninta da tashinta duniyar kudi tasan dole me girman kudi ne wannan qamshin.

Dining room Kai tsaye Amatu ta nufa duk da lokacin cin abincin beyiba tana Isa ta shige kofan da zata shiga ta wuce palonsa.

Tana shiga kusan komai a fes kaman ko yau din ta sharesa bayan yau Bata samu gyara masa ba sbd lattin dasukai na bacci ta fita Bata dawoba.

Bedroom dinsa ta wuce Kai tsaye Dan gyarowa sharp sharp ta fice kafin ma ya dawo hakama kafin lokacin cin abincin yayi tabar bangaren gaba Daya tayi gurin maamah.

Tin a Palo ta ajiye doguwar rigar data doro akan kayan jikinta gashi ko hula Babu akanta hular Dake hade da doguwar rigarta Daman ta rufe kanta da ita.

Qamshinsa ne koyaushe yakewa duk Wanda ya Bude kofar bedroom din kyakkyawar tarba me sanyi da nutsuwa Dan haka tana shigowa gadonsa ta nufa duk da babi Wani gyaran dayake buqata sbd Ayanda ya kwanta haka yake tashi a gadon shinfidansa batai komaiba kaman ba baa kwantaba,yanzu ne wasu lokutan suke yamutsa gadon da dole sai ta gyara.

Tana gama gyara komai na dakin ta nufi kofan bedroom din tana fitowa Yana tsaye kofan zai shigo shikuma tayi Baya ahankali cikin yar firgita

Tarota yayi jikinsa Yana kallanta cikin kulawa me tsananin gaske Yana furta kalman

“Be careful” cikin sauti me cike da kulawa.

Numfashi ta sauke a boye tana Bude idanuwanta data Dan rintse ta Kalli fuskansa ahankali

Sanye yake da jallabiya me taushin gaske fuskarsa Wani irin sanyin kyansa da kwarjinsa na kashe jikinta.

Gyara mata tsayuwa yayi Yana sake matseta jikinsa Yana kallan idanuwanta Dasuka Dan shagala da kallansa.

Ahankali ya matso da fuskarsa zuwa tata yakai bakinsa kan idonta daya ya Dora lips dinsa yayi kissing idon ahankali.

Mutuwa jikinta yake Neman yi gaba Daya Dan haka ta Dan sake tsayuwa da kyau cikin jikinsa kada ta zube gurin.

Wuyanta yake shafawa ahankali Yana tambayarta meyasa jikinta yayi dumi sosai.

Sauke idanuwanta tayi daga kansa tana dago hannunta Daya ta Dora akan nasa Dake cikin wuyanta Yana shafawa Yana tayar da tsikan jikinta.

Ta Baki cikin Wani irin sanyin kasalan dayake Sakar mata zatai magana ya Saka harshensa ahankali ya lashi lips dinta Yana lumshe idanuwansa daga shi har ita

Kasa fadan abinda zata fada din tayi sbd qara lasanta da yayi.

Hannuwanta ta zira ahankali ta zagayosa dasu tana sake mannuwa dashi Jin saukan lips dinsa da harshensa har gefen fuskanta Yana Bata wasu silent kisses tana sake shigewa jikinsa cikin sanyi da kasalan.

A jikin kofan bedroom din ya suka gama yamutsewa kafin ya dawo da ita ya zaunar a kujeran palonsa da kansa ya dauko ruwa daga fridge Dake palon ya kawo ya Bude yabata a Baki

Sai data Dan dago ta kallesa kafin ta Bude Baki tafara Dan Shan ruwan sbd tana buqatansu kaman batada ruwan jiki takeji.

Tana gama sha ya Kai robar ruwan bakinsa ya Dora nasa bakin Akai ya sha ahankali tana kallansa zuciyarta na Rasa Ina zata Saka kanta da wannan halin data samu kanta aciki batareda ta San yausheba.

Itace ta miqe tana ya dauki rigarta Dake ajiye ya Saka mata tareda janyo hulan ya Saka mata ya Kai bakinsa ahankali kan lips dinta yayi kissing ya tsaya Yana kallanta harta Kai kofa ta fice batareda ta waiwayoba.

Karima ce kawai a dining tana jera ruwa da drinks data kawo lokacin a dining Dan haka ita kadaice ta ga fitowanta ta sauke Kai tana cigaba da aikinta.

Itama Amatun hankalinta Bai tashi sosaiba ganin karima ne Dan haka ta wuce Kai tsaye palon qasa Dan zuwa gurin maamah.

Tana saukowa su maamah da mum Aisha da Husnah Dake palon suna magana gabaki dayansu suka dawo da kallansu kanta hanyar saukowan duk da sunsan ita din ce Amma tinkarosu datakeyi yake sake basa qamshin Wanda Babu Wanda a gurin baisan waye mutum daya me wannan qamshinba a gidan.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

44

*****************

Husnah datafi kowa shiga mamakin abinda hancinta ke ji mata lokacinda Amatun tazo gefen maamah ta tsaya tana kallansu cikin boyayyan mamakin kallan da suke mata su dukan.

Maamah kuwa Sam hankalinta rabuwa biyu yakeyi tana tinanin ganin ta inda ASH ze fito sbd qamshinsa da suke Dan ji sama sama,

Mum Aishan baqin cikin Daya danne kirjinta tabbatarda Amatun ce me wannan qamshin takuma tabbatarda ASH TALBA fara taba AmatulMaleek din yayi Dan haka juyawanta tayi tana kasa magana sbd idan ba shirun tayi ba zata iya shaqe Amatun da Asma’un dasuke gabanta su mutu har lahira Dan haka ta zabi yin shiru kawai kafin wutan Dake cin kirjinta ta Dan rage.

Husnah kuwa maamah ta kalla kafin ta Maida kallanta kan Amatun tana sake Bude hancinta da kyau taji indai da gaske qamshin Dad dinta ne take Jin a tareda Amatun Amma Kuma sanin bama abinda zai yiyu bane sai itama tabi maamah suna satar kallan hanyar saukowa ko zasu ga ASH din Dan duk inda yake Yana kusa tinda suna iya jiyo qamshinsa.

AmatulMaleek da batasan me yake faruwaba a tsakanin su ukun da mum Aisha ke zubawa maamah maganganun dasuke gap da rabata da ranta tsaban ciwo da zafinsu gameda maganar auren tana sake cusa mata qi da tsanar auren.

Kasa magana Amatu tayi maamah kawai ta fara gaidawa maamah din ta amsa batareda ta kalleta sosai ba,

Mum Aisha ta juya ta kalla ta gaida itama cikin girmamawa,

Amsata tayi bayan ta Dan juyo ta kalleta.

Bata cewa Husnah komaiba sbd ganin irin kallan datake mata Fakaice dan haka ta juya tabar gurin gaba Daya.

Kitchen ta nufa Kai tsaye ta Dora ruwan tea dinsa Yana Kai ta dauko inda zata juye kenan sai ga maamah ta shigo kitchen din.

Qarasowa maamah tayi tana kallan Amatun a sanyaye kafin ta karbi kayan hannunta tana dauke idanuwanta daga kanta tace

“Ki tafi daga yanzu karki sake dafa tea din da ASH zaisa ni zan ringa dafawa Kokuma khaltume ki Dena kwata kwata,wuce ki tafi kici abincinki ki wuce daki ki kwanta tinda a gajiye kike”

Tsayawa Amatu tayi tana kallan yanda mahaifiyarta ke magana da ita Bata iya kallanta hakama bacin Rai ne da kusan fushi duka a hade cikin ranta lokaci Daya.

“Akanta maamah ke wannan fushi da bacin ran???

Hawayen da batasan dasu bane suka ciko idanuwanta ta kasa wucewa kaman yanda maamah din tace ta juyo tana kallanta ahankali muryanta na karyewa tace

“Maamah nayi Miki abinda ya Bata Miki Rai ne?

Maamah nayi Miki laifi ne?

Maamah kiyi hakuri bansan…….

Cikin bacin ran da Amatu Bata taba ganin mahaifiyarta ba maamah ta daka mata tsawan Daya Saka su karima da zasu shigo kitchen daka tawa suna juyawa.

Hawayen Dake idanuwan Amatun saukow suka fara yi suna gangarowa hannuwanta na rawa sbd yaune Karan farko da Hakan ya faru tsakaninta da mahaifiyarta tin rasuwar Babah maamah Bata taba hantarar ‘yayantaba.

Hawayen Amatu gudu suka qara tana kallan maamah

Maamah din taqi kallanta sbd zuciyarta Dake cikin bacin Rai da baqin cikin da batasan Yaya zatai dashi ba akan lamarin da ake Neman kasheta da baqin cikinsa.

Cikin sanyin jiki hawayenta na sake gudu Amatu ta matso zatai magana maamah din ta daga mata hannu sbd batason ta sake daga murya a jisu,

Cikin murya me nauyi tace

“Kije kawai sai da safe”

Juyawa Amatun tayi hawayenta na qara gudu tabar kitchen din ta nufi hanyar saman ta Haye zuciyarta na nauyi kuka takeji Amma tana dannewa Dan Hakan Bai taba shiga tsakaninta da maamah ba.

Mum Aisha da a kunnenta duk abinda ya faru din ya faru Wani numfashin takaici ta sake tana shiga mamakin kenan ma basai ta wahalarda kanta ta Wani bangarenbama da maamah zatai amafani ta lalata rayuwar gidan ASH TALBA gaba Daya,

A yanzu da Danta ya koma haka ta tabbatarda mafarkinta da burinta akansa yabi iska Dan haka Babu Wanda zai zauna cikin farin ciki a gidan kowa Saiya samu mummunan sakayyar data samu.

Wucewarta tayi bedroom dinta

Husnah ma da kusan taji abinda ya farun sama ta wuce dakinta itama.

Juye ruwan tea din maamah itama tayi ta Saka karima ta dauka taje takai ita Kuma ta wuce dakinta Dan zuciyarta nauyi take mata sosai.

AmatulMaleek na shiga dakinta Hana zuciyarta riqe abin tayi sbd tasan maamah dinta dole akwai abinda ya Bata mata Rai Bata taba fushi ko mata irin Hakan ba Dan haka zata danne dacinta ta roki maamah idanma Wani lefin tayi,Kokuma rashin zuwanta gurinta ne bayan dawowanta makaranta.

Duk yanda taso danne zuciyarta kasawa tayi wasu hawaye ne suke sake sauko mata.

Shigowan karima ya Saka ta share hawayenta tana Dan kallanta.

Abinci ne ta kawo mata har dakin ta jera mata tareda ficewa.

Zubawa abincin idanuwa tayi kafin tayi Wani motsi wayarta tayi ringing ta juya ta Kalli inda wayar take Taga sunan anty Farha.

Numfashi ta sake saukewa tareda miqa hannu ta dauko wayar tai receiving cikin sanyin murya tana cewa

“Anty Farha”

Amsawa anty Farha din tayi tana son sanar mata tayi Shirin Daya kamata tafiya zaayi da ita Amma Kuma ta kasa sbd Mr Jameel ya sanar da ita gargadin kar Wanda yasan da maganar tafiyar.

Bigewa tayi da kamo Wani zancen batareda ta saniba ta debewa Amatun kewan halinda take ciki sosai har taci abinci kadan batareda ta saniba suna wayar.

Ko da suka gama wayar har karima tazo ta fita da kayan Dan haka tashi tayi taje tayi brush ta wanke bakinta da mouth wash masu shegen qamshi da dadi da duk aikin anty Farha ce me siyo mata su musamman ake ware kudin siyayyarta ana bawa Farha din wadda ita gaba takaita sosai aiki da ASH TALBA.

Turare ta Dan sake shafawa jikinta ta Saka safa me taushi tana kokarin Hawa gadonta Amma Kuma tinanin tea dinsa na fado mata ta bangare daya Kuma mahaifiyarta na fado mata akan fushin datakeyi da ita batareda tasan lefin dataiba.

Harta kwanta ta kasa bacci ta janyo wayarta data Saka flight mode ta duba time Taga sha biyu ta wuce.

Saukowa gadon tayi sbd ta kasa Hana zuciyarta Kai masa Wani abin Dan tasan bazai taba Shan tea din ba daga lokacinda yayi masa Shan farko yaji ba itace ta dafasa ba bare Kuma ba lallai ya sha dinba Dan ya Dena sha idan ba itace ta zuba masa dinba shiyasa kullum take maisa dakinsa bayan kowa ya shige.

Ayau din bazata iya Kai masa tea din sbd umarnin maamah na cewa kada ta sake hada masa tea daga yau din Dan haka kitchen ta nufa Kai tsaye ta Bude fridge akwai orange juice datai jiya da daddare me orange sosai aciki kanasha kana taunasa Orange din aciki.

Daman shi ta hadawa Amma Bai sha ba sbd Bata Kai dining ba Dan haka ya fiddosa a glass jug me kyau ta zuba cikin Wani jug din da beyi girman wancan ba ta dauki cup Daya ta Dora akan trey din ta bar kitchen din.

Sama ta dawo ta wuce hanyar dining tabi hanyarta ta wuce Kai tsaye cikin sanyin jiki.

Ko data Isa bedroom dinsa Yana zaune kan sofa Yana facing window hasken waje Yana haske kyakkyawar fuskarsa Yana yi Yana kallan time Yana jiran 1 ta buga ya fita dakin da kansa.

Bude kofarta tareda shigowanta ya sanyashi Dan lumshe fararen idanuwansa batareda ya motsaba bare juyowa sedai zuciyarsa data amsa zuwan nata.

Qarasowa tayi ahankali har inda yake din ta ajiye kayan hannunta tareda juyowa ta kallesa ahankali cikin sanyi da mutuwar jikin datake cikinsa.

Yanayinta ya sanyashi kallanta a natse yana kokarin karantar yanayinta Amma ta Hana Hakan ta hanyar miqa hannu ta zuba masa juice din a cup ta dauko tana kokarin miqa masa ya miqa mata hannunsa Daya alaman ta zo din.

Sai data sauke numfashi a boye kafin ta miqa hannunta Daya ta Dora akan nasa din ya miqar da ita Yana janyota ahankali ya zaunar kan qafafunsa suna fuskantar juna.

Cup din hannunta ya kalla Bai karba ba har lokacin saima cikin idanuwanta dataqi barin ya kalla dayake kokarin kalla sbd damuwa dayake kaman Gani a cikinsu.

Rigarta ya fara zare mata ta zame qasa daga jikinta ya karbi cup din Ya dago bayansa daga jikin kujera ya Dora kansa kan kirjinta ya kwantar muryarsa na fita cikin kulawa yace

“Are you okay?

Wani abu Yana damunki right??

Shiru ta Dan yi tareda rufe idanuwanta ahankali kafin ta budesu tana qarasa hadiye sauran damuwanta dayake kokarin tonowa.

Cikin wata lazy murya mara karfi ko kadan ta furta masa “aa” cikin tsakiyan kunnuwansa.

Tasowa yayi ahankali daga jikinta idanuwansa akanta cikin Wani fitinannen yanayi tsikan jikinsa na tashi gaba Daya.

Batasan me maganarta tayi masa ba Dan haka kallansa ta Dan yi tana sauke Kai sbd ganin irin kallan dayake mata.

A Wani irin shaqe ya furta

“Kin tabbata?

Gyada Kai tayi daqyar sbd numfashinta dayake Neman yankewa da saukan hannunsa Daya cikin rigarta kan cikinta,Dayan hannun kuka cikin tsakiyan bayanta fuskarsa Kuma tana shafa wuyanta zuwa kirjinta Yana Neman fasa mata qaramin Kai.

Tsakiyar bayanta yayiwa Wani shafan Daya Sanyata manne kirjinta da nasa tana Jan numfashinta Daya kusa fita da qarfi cikin rashin sauti.

Yanda kirjinta ya mannu da nasa a lokacinda Bai tsammata ba shine ya Saka nasa numfashin barin kirjinsa na wasu seconds kafin ya Bude idanuwansa daqyar da sukai ja a take ya zubawa kirjin nata Yana masa Wani kallan maita.

Ahankali yakai hannuwansa biyu yafara warware gaban rigar baccin ya zareta ahankali ya jefar qasa

Farar padded strapless bra dinta ce ta bayyana akan idanuwasa

Numfashinta Dake sama Yan qasa ahankali sbd yanda zuciyarta ke bugawa yana sake sama da kirjinta Yana qasa dashi akan idanuwansa Dake sake juyewa kaman Wanda yasha motan wiwi.

Wuyanta ya kamo ahankali Aya Saka kansa ciki ya ja qamshinta sosai Wanda yake sake kashesa da ransa.

Fatan kunnenta ya dora lips dinsa ya Sakar mata Wani lafiyayyar kiss Daya rabata da numfashinta

Tanaji ya gangaro da harshensa ta wuyanta zuwa kirjinta hannunsa Kuma Yana sauka kan bra dinta ta Baya sai Jin tayi an balla bra din ta sauka daga jikinta tinda Daman ba hannu ne da ita ba.

Bayyanar komanta akan idanuwansa ya Sanyata shigewa jikinta cikin tsananin kunya idanuwanta a rufe.

Kasa hakuri da iya riqe kansa yayi ya dago fuskanta Bai tsaya komaiba ya hade bakinsa da nata yawun bakinta ya ringa tsosa a hankali Yana Jin kirjinta Dake tokale da kirjinsa na Neman kashesa sbd tini gaban rigarsa ya Bude Dan haka skin to skin yake Jin komai nata.

Zafi kissing din yayi harma da abubuwan Dake biyo bayansa,

Hannuwanta ta Saka ta zagayo wuyansa cikin Wani irin fitinanniyar yanayin Dake kokarin rabata da numfashinta a karo na farko data basa cikakkiyar Daman lasanta da yin komai da ita cikin sakewa.

Hakan da tai shine kisan karshen datai masa Dan haka ta a miqe tsaye da ita a jikinsa bakinsa na cikin nata kissing juna sukeyi hayaqi na fita ta kunnuwansa.

Lafiyayyar gadonsa ya kwantar da ita Yana qarasa cilli da Dan kayan dasuka rage a jikinta sedai komai ya tsaya ne lokacinda ta Tina da halinda take ciki na period Wanda Shima kasa cewa komai yayi sedai ya shige toilet Dan Baya fatan ta iya ganinsa a halinda yake ciki.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

45

*************

Ita kanta Amatun kasa dogon motsi tayi tana kwance idanuwanta a rufe harya dawo yayi wanka ya sauya kayan bacci masu santsi da taushi qamshinsa Daya kama jikinsa Yana tashi ahankali yazo ya kwanta tareda shigar da ita jikinsa sukai baccinsu.

Da asuba bayan ya dawo sallah tana cikin jikinsa ya sake tambayarta cikin nutsuwa da kulawa meyake damunta.

Batai magana ba sai hawayen da suka ciko idanuwanta tana son Maidasu Amma takasa,

Abdulhameed da Haydar ne kawai abokan shawararta Kuma yanzu Haydar wata shawarar Bata iya fada masa sbd haryanxu baisan da maganar aurenba.

Handkerchief dinsa Dake gefen gadon ya miqa hannu a natse ya zaro ya goge hawayen dasuka sauko mata ahankali Yana yin shiru Dan Bata Daman nutsuwa tukuna duk da ba cikin tashin hankali takeba Amma a ganinsa duk Wanda zaiyi hawaye Yana cikin tashin hankali me tsanani ne.

Shiru tsawon lokaci har lokacin tana cikin jikinsa kwance kafin ya sake tambayarta meyake faruwa.

Bazata iya fada masa ba Dan haka sai kawai tace lefi tayiwa maamah tana fushi da ita.

Qarasa fadan kalman tayi hawayenta na sake gangarowa.

Shiru yayi bayan ya share mata hawayen Yana kasa cewa komai kafin daga baya ya rarrasheta yace ta bawa maamah din hakuri koma lefin Menene zatayi hakuri Kuma itama ta kiyaye.

Gyada Kai tayi ahankali cikin kasalan datake tareda ita hakama jikinta duk yayi dumi sbd jikinta daya kasa komawa daidai daga kusan zama cikakkiyar macen datai a Daren.

Shi kansa jikinsa kusan a macen yake gashi yau akwai tafiyarsa gabansa.

Kafin ta fice ya sanar da ita tafiyansa Dan haka ta Dan sake narkewa batareda tasan tayi Hakanba shi kansa kusan Saida ya Hana kansa biyewa zuciyarsa kafin yayi sallamata da ita ta fice.

Issue na damuwan Daya Gani a tareda ita na maamah dinta dasuka samu damuwa ya sanyashi daukan wayarsa yayi Mr Jameel txt ayi cancelling nata ticket din Dan Bata Daman shiryawa da mahaifiyarta.

Tana fitowa bedroom dinta ta shige ta fada toilet.

Wanka tayi ta shirya cikin wasu kayan baccin daban sbd ko motsi tayi Babu abinda a jikinta ba qamshinsa yakeyiba,

Ita kanta fatan jikinta qamshinsa takeyi shiyasa tayi wankan da asubar ta sauya kayan baccin kaman zata kwanta saita fasa ta fito ta wuce dakin maamah.

Ko data shiga maamah din tayi sallah itama tana zaune tana lazimi cikin damuwa da sanyin jiki tinani kala kala a cikin zuci da kanta,

Kauye takejin tanason tattarawa ta koma da Amatun Amma Kuma tayaya ne zatai hakan bata saniba sbd auren ASH TALBA dayake kanta shine babban abin tashin hankalin da tsoron inda zatai wannan gangancin…

Idan Kuma tayi nasarar zuwa kauyen Kuma masifar da zata tarar acan tasu kawu saita dame ta Nan din ko batar da ita zasu iya tsaf su dawo da AmatulMaleek gidan ASH TALBA.

Cikin nutsuwa da girmamawa da sanyin jiki Amatu ta qaraso ta zauna ta gaida maamah din tareda Bata Bata hakuri akan duk laifin datayi din.

Kallanta maamah tayi tanajin tausayinta ta Wani bangaren sedai idan ba bayyanarda tsananin qinta ga auren tayi ba Amatun zata iya samun kanta a rayuwar auren da bazata iya fita ba Dan haka a yanda tasan Amatu na tsanar duk abinda ta tsana to tabbas Shima wannan auren zata cusa mata qinsa ta gujesa su samu su tattara ita yanzu Nan din ma gaba daya takeson bari da Amatun.

Nasiha maamah ta fara yiwa Amatun akan tsayawa matsayinka ka rungumi duk abinda Allah ya kaddara Maka a rayuwa ka tsaya inda ya ajiyeka.

Shiru Amatun tayi batareda tasan me maamah ke nufi da tsayawa ka rungumi kaddara ba,

Akan ta rungumi auren da Allah ya Dora mata ne kokuwa ta rungumi kaddarar rashin samun aure kaman irin na kowa.

Batasan me zata ce ba bayan gyadawa maamah din Kai tana Jin sanyin sassaucin fushin maamah din akanta.

Miqewa tayi ta Haye gadon maamah din tayi Kwanciyarta baccin da Bata samu ba a Daren.

Bata jima da Kwanciyar ba bacci ya dauketa a kasalance.

Maamah ma komawa baccin tayi tana fatan Amatun ta fahimci inda zancenta ya dosa akan aurenta ne.

Qarfe 8 Amatu ta fito Bata wuce sama ba kitchen ta tsaya da kanta hada Wani irin fresh juice me qarfi na ginger da pineapple Se ta zuba raspberry drink ciki me gas kadan tareda qanqara ta shirya a trey ta wuce sama dashi.

Kai tsaye dining room din ta nufa tana shiga mum Aisha da Husnah na zaune suna jiran fitowansa.

Gaida Mum Aisha tayi suka gaisa da Husnah sama sama tana ajiyewa kenan Yana Sako Kai cikin gurin sanyeda sky blue luxury Switzerland cashmere Daya kwanta a jikinsa ya qara fiddo Haske da kyau tareda hutun fatarsa,

Ta bangare daya gaba Daya fuskarsa Wani hasken kwarjini ta qara

Ko Husnah datake yarsa kallo daya tayi masa tai qasa da idanuwanta tanajin kishin Amatu data samu arzikin amsa sunan wadda igiyoyin aurensa suka hau kanta duk da a iya Baki ne auren Amma tayi arzikin da ita Babu Wanda zata aura tayi wannan arzikin idan ba Faisal da zata iya mutuwa akansa ta samu ba.

Idanuwansa akan Amatun kawai suka fara sauka ya Kalli abinda ta ajiye ta zuba ta dago tana kasa kallansa cikin sanyi da girmamawa tai masa Ina kwana ta juya ta tana nufar kofa.

Mum Aisha data ke ankare da kallan ASH cabdijm ta furta cikin zuciyarta tana kokarin daukan cup din gabanta ta kurbi ruwan sanyi ko taji sanyi.

Kan Husnah data gaidasa ya dawo da kallansa cikin kulawa a natse Yana amsawa tareda tambayarta karatu da lafiyanta da wasu abubuwan dasuka shafi kulawa sosai.

Abinda Amatun ta zuba masa a cup kafin ficewarta yakai hannu ahankali cikin nutsuwa ya dauka Yana kaiwa bakinsa yafara sha kafin cin komai.

Bai taba fara karyawa cikinsa da abu me Dan sanyi ba sai a yau din Kuma ga boyayyan mamakinsa hakan yayi masa daidai a Baki da ciki.

Sama sama yayi breakfast din ya miqe ya fice Husnah na bayansa sbd sanin tafiyan da zaiyi a yau din.

Har mota Husnah ta rakasa suka wuce kafin ta dawo ciki.

AmatulMaleek ta wayarta tayi masa text din adduan dawowa lfy Wanda kusan shine abinda ya sake Sakasa Wani irin yanayi komai nata kashesa yake Neman yi.

Wanka tayi ta shirya ta fito cikin Riga da skirt na lace mara nauyi Se kudi ta sauko a palon qasa tayi breakfast dinta tana gamawa taje tayi bankwana da maamah ta fice zuwa makaranta handbag dinta ta original Gucci na hannunta Se qaramin mayafinta da wayarta ahannu.

Kafin ta qaraso tini driver ya fito ya Bude mata ta shige suka bar harabar gidan.

Sai bayan tafiyarta Husnah itama ta fito ta fita da tata motar batareda ta bari driver ma ya jata ba da kanta ta ja ta fice.

Da wuri Amatu ta dawo tayi abinda zatai ta wuce dakin maamah tayi zamanta acan ba tinanin komai yau din a dakin maamah ta kwana,

Washe gari ma data tafi ta dawo anan ta kwana.

Cikin kwana biyu da ASH din Baya qasar sai ga maamah ta Dan sakewa ‘yarta Suma su mum Aisha da Husnah kowa ya Dan sake tinda baya Nan Saka sun samu sassaucin sakawa Amatun ido sosai Dan toshe kowane hanyar samun kusancinta da ASH.

Naufal tinda ya farfado bayan kuka da tashin hankali Babu abinda yakeyi Yana ihu sai anmasa allurar bacci sbd ya kasa yarda da qafa Daya zeyi rayuwa Dan haka tinda ya farfado mum Aisha bayan sabon tashin hankali Babu abinda take cikinsa da baqin ciki tareda mugayen qudiri kala kala Dake sake cike ruhi da zuciyarta sam ko wuni Bata Wani yi a mansion din sai dare take komawa tana tareda ‘danta gashi qiri qiri ASH ya Bada umarnin kar a sallamesa Saiya warke sarai bare ta daukesa ta fita dashi waje.

Kowanne dare sakonsa na shigewa take kwantawa bacci bayan ta karanta tana kwance kan gadon maamah batareda Maamah din tasan meyake faruwa a rayuwar ‘yarta ba kwata kwata.

Sati biyu yayi cif da tafiya Bai dawo ba hakama Batasan ranar dawowan nasa ba Dan Bata iya tambayar ba Kuma bazata iya tambayar ba.

******Yau da wuri ta gama da school ta kira anty Farha da suka kwana biyu Basu Hadu ba tanason biyowa gurinta Amma anty Farha din bata gida Dan haka ta tura mata location na inda zata sameta ta nufi can din.

Sabon guri ne da anty Farha din zata Bude spa na gyaran jiki.

Tayata murna tayi tareda tayata hidiman wasu abubuwan na gurin Wanda a ranar zaa Bude washe gari.

Dukiya sosai anty Farha din ta zuba sosai gurin gyarasa musamman kayan Dake cikin na gyaran jiki wainda kusan idan aka cire na waje masu kyau sauran duka daga Meerah aka Saro su aka tsara a shagon.

Se yamma suka gama komai

Komai na shagon ya kammala ya zama ready washe gari kawai suke Jira ayi bikin budesa.

Amatun ce ta farko da anty Farha din tace a fara gyarawa a yau din Dan gobe tana school Kila zaa fara Dan haka masu aikin suka zauna aka fara gyarata tareda gyaran gashinta da qafafu da komai kaman Wanda zaa canza a amayar wata duniyar.

Har bayan magrib Basu baro ba sai ishai suka fito bayan Amatun gaba daya ta sauya cikin qanqanin lokaci

Haskenta kaman an sake wankosa ne waje,

Daukan ido fatanta keyi gaba Daya ita kanta sai Taga abin ya mata yawa Dan haka tana dawowa gida wanka tayi ta Saka kayan bacci masu kauri da safa abinci kawai taci tayi sallolinta ta kwanta kada maamah ta Gani tayi fadan gyaran.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

46

**************

Dayake da wuri tayi bacci Bata tsaya duba massage dinsa ba sai washe gari,

Shirin tafiya makaranta tayi ta fice sbd bikin anty Farha tanason baro school da wuri Dan ta samu attending.

Su Maamah dai ta waya tayiwa anty Farha din Allah ya Sanya alkhairi

Husnah Kuma daga adduar har zuwan Babu Wanda takeda niyar yi bare mum Aisha da ko sunan Farha baa fada a gabanta bare shiga shaaninta.

Karfe uku ta baro school ta dawo gida.

Kadan ta huta tayi wanka tai Shirin tafiya bikin ta fice

Da kanta taja motan zuwa gurin waliman.

Ko data Isa anty Farha zuba mata idanuwa Tayi tana Jinjina kyanta da komai nata dayake da kyau da tsari musamman gyaran da Akai mata jiyan ya Sakata komawa kaman wata sabuwar ‘danyar amarya.

Fara waliman Akai cikin farin ciki da burgewa,

Manyan Yan mata da Yan matan Dake auren manyan qasa irinsu ash din kusan duk mutanen anty Farha ne sun halarto sosai anyi komai a tsari Se magrib aka watse.

Anty Farha riqeta tayi ta hanata komawa Saida suka gama komai taja motar Amatun sbd bazat iya barinta tayi driving da kanta ba magrib tayi.

Suna isowa aka bude musu gate din Mansion din suka shigo.

Anty Farha ce tana parking tace

“ASH TALBA ya dawo qasar kenan shine kika bari na riqeki har wannan time din Amah?”

Se a lokacin Amatu ta dago idanuwanta ta Kalli inda motocin ASH din suke suna kallan gate a maimakon yanda suke a Baya sun bawa gate din Baya ne alama ce ta ya dawo din anfita dasu anje an daukosa Kokuma ana jiran isowansa aje a daukosa.

Sanyi taji jikinta n Neman yi ta daure ta fito motan a natse tayi sallama da anty Farha wadda ta fito motar itama driver ze kaita gida da motan Amatun ya dawo.

Cikin gida Tayo ta kofan kitchen ma tabi sbd sanin Kila maamah na kitchen din Amma bata Nan.

Juyawa tayi ta nufi dakin maamah din ta Tararda ita tana sallah itama ta ajiye Jakarta da wayarta kan kujera ta nufi bedroom din maamah din ta shige toilet Tayo alwala ta fito tazo inda maamah din ta gama sallah tayi tata sallan.

Bayan ta idar da sallan addua tayi tana gamawa ta miqe ta dauko wayarta Dake ringing Taga sunan Haydar.

Murmurshi me kyau ta sake tana zaunawa tareda daga wayan tana ambatar sunansa Dan maamah data zuba mata idanuwan son sanin me wayar taji waye dinne.

Ta lura da yanda fuskan maamah ta sauya da Dan murmushi da farin cikin jin Haydar ne Dan haka taci gaba da wayarta da Haydar Wanda wasu maganganun ma maamah batasan me suke fada ma Dan turanci ne Da suka fara sabawa dashi yanzu sbd rayuwar can din basa iya dadewa suna magana da zallan Hausa.

Abdulhameed ma karban wayar yayi suna sake hayaniyarsu wadda idan Bada su din ba Se anty Farha yanzu Amma Babu Wanda zaaji Amatu na magana sosai dasu haka tana daga murya idan Basu ba.

Har Akai ishai Basu gama ga Saida ta Basu suka gaisa da maamah itama suna sake hayaniyarsu sukai sallama ta kashe wayar ta Nemo numbern anty Farha taji idan ta Isa gida lfy.

Wasu maganar da anty Farha ta fara yimata ne ya Sanyata Satan kallan inda maamah take gabanta na faduwa hakama tana rikicewa sbd kunya da tsoron maamah wadda ta zuba mata idanuwanta Amma batajin me anty Farha din ke fada Dan haka sallama da anty Farha din kawai Amatu tayi ta kashe wayarta batareda ta iya cigaba da sauraran abinda anty Farha din ke fada.

Maamah tashi tayi ta tada sallan ishai dinta

Itama Amatun miqewa tayi ta tayar da tata gajiya ma take Dan ji wanka take buqatan yi.

Bayan sun idar Amatu Bata Wani jik yunwa sbd sunci abinci taredasu anty Farha Dan haka batajin zata sake cin Wani abin.

Kallanta maamah tayi lokacinda take daukan banana data Gani a fridge dayake palon maamah din takai bakinta tace

“ASH ya dawo”……cak Amatun ta tsaya ayaban data Saka bakinta tana wuce maqoshinta batareda ta taunaba.

“kafin ki wuce dakinki muje muyi masa barka da dawowa ki wuce ki shige tinda fitan safe kikeyi.”

Danne yanayinta tareda boye faduwan da gabanta yayi Amatun tayi tana cigaba da cusa ayaban hannunta bakinta sbd kada maamah din tace tayi Wani abu akan auren Wanda shine abinda yake faruwa tsakaninsu yanxu.

A Dan matse ta gyada Kai tana Jin jikinta na sanyi Dan kuwa a ayanzu kaman tsaka me wuya ne take tsakanin maamah da ASH din gaba Daya.

Miqewa tayi tana fasa qara cin ayaban sbd Jin tayi cikinta ya cunkushe ba guri ma.

Fitowa sukai maamah na sanye da hijab har qasa ita Kuma Amatun kayan data dawo waliman anty Farha dasune a jikinta Riga da skirt na navy blue dry exclusive lace da mayafi Dan daidai irinta Yan mata marasa jiki.

Sama suka hawo maamah ce a gaba tasa Amatun ta biyo bayanta Dan haka a sanyaye take biye da maamah din ita da maamah dinma tabar gaisuwan zuwa gobe sayi.

Dining room suka nufa mum Aisha ma lokacin take shiga Husnah ce ta fara fitowa ta kofan palonsa fuskarta cikeda farin ciki da walwalan kasancewa da mahaifinta.

Husnah suke kalla kowa fuska a sake kafin suyi magana sai gashi ya fito Shima sanye cikin hoodie Riga da wandon rugby masu Dan kauri gaba Daya black hakama slippers dinsa dasuka bayyanarda hasken qafarsa da kaman Baya tafiya da ita black ne.

Fuskarsa idan akace Aiki yake zakai mamakin haske da hutun Daya bayyana tareda shi har wata kwantacciyar lafiyayyar gashin fuska ya Dan Tara Daya sauya kamanninsa gaba Daya zuwa Wani lafiyayyan matashin da bazaa ce ya haife saurayin ‘da Haydar ba da Husnah.

Qamshinsa kawai hancinta ya Shaqa taji jikinta ya mutu gaba Daya Amma bazata iya dagowa ta kallesaba sbd mahaifiyarta Dake gurin Dan haka numfashi me sanyi kawai ta sauke a boye.

Maamah da mum Aisha kuwa kasa iya kallansa sukai sedai gaisuwa da masa barka da dawowa.

Daga bayan Maamah ta iya Bude Baki itama cikin sanyin murya ta furta kalman

“Barka da dawowa”

Zama yayi bayan Jin saukan muryarta cikin kunnuwansa zuwa zuciyarsa data kasa hanasa kallanta duk da mahaifiyarta Dake gurin.

Fararen idanuwansa ya watsa gurinda maamah take tsaye dole maamah din ta janye sbd nauyin idanuwansa akanta tareda Jin nauyi saiga Amatun ta bayyana a bayanta tsaye.

Suturar Dake jikinta ya kalla saga qasa zuwa Samanta cikin nutsuwa kafin ya tsayar da kallansa kan fuskarta data kasa dagowa ta kallesa.

Maamah,mum Aisha da Husnah kusan kowannensu maida kallansa yayi kan Amatun Babu Wanda gabansa Baya mummunan bugawa da kallan tsaf da ASH din yayiwa Amatun cikin nutsuwa a gabansu.

Ahankali maamah ta juya ko ganin gabanta sosai Batayi ta fice daga gurin Amatu ta bi bayanta cikin kasalan da Idanuwansa tana jinsu a kanta suka sakar mata.

Maamah Bata iya tsayawa dogon maganaba ta raka Amatu har kofan dakinta tai mata seda safe ta wuce Dan idan Amatun ta biyota dakinta kwana yau din zata iya mata mummunan furuci akan abinda ya faru yanzu din bayan batasan mema zatace Yana faruwaba.

Jiki mace Amatu ta shige bedroom dinta itama,

Zaunawa tayi ta sauke ajiyan zuciya a Jere tana dawowa hayyacinta yanda ya kamata kafin ta miqe ta tube kayanta ta shige toilet.

Wanka tayi da ruwan zafi sosai jikinta ya sake kafin ta fito daure da towel ta zauna gaban mirror.

Body oil kawai ta shafa da turare ta miqe ya nufi kayan baccinta ta Ciro Riga da wando marasa nauyi masu santsi ta Saka.

Gadonta ta nufa tana kokarin kashe wayarta sakon daya Saka gabanta faduwa me qarfi shigowa wayarta.

Zaman tayi bakin gadonta tana sake karanta sakwan hakanan gabanta ke faduwa da tinanin zuwan kawai.

Kallan wayarta ta sake yi tana rasa tinanin kamawa na zuwa ko yiwa sakon shiru.

Lokaci me tsayi ta dauka tana shiga tinani da rashin sanin abinyi.

Numfashi ta sauke ahankali bayan kusan awa da shigowan sakon ta miqe tsaye jikinta ba qwari ta nufi wardrobe ta Dauko hijab ta Saka tareda daukan wayanta ta fice qafa ba qwari.

Kitchen ta nufa Bata dafa tea ba fridge kawai ta Bude ta zuba fresh juice da aka hada ranar na mango ta hada komai ta jera ta dauka ta koma saman  ta nufi hanyar palonsa Kai tsaye lokacin har 11 ta Dade da wucewa.

Tana Bude kofan palonsa Baya palon Dan haka ta nufi bedroom dinsa ta Bude ahankali cikin nutsuwa.

Akan dadduman sallah yake Yana sallah Dan haka table ta nufa ta ajiye kayan hannunta tana juyowa Yana sallamewa.

Idanuwansa ya zuba mata Yana mata kallon gaskia da gaskia na abinda yakeji a zuciyarsa Yana rasa Menene yake Jin din,

Menene suna ko ma’anar abinda yake ji cak a tsakiyan zuciyarsa game da ita da duk abinda ya shafeta.

Cikin sanyi da kasalan idanuwansa akanta ta dago nata idanuwan ta saukesu akansa Daman abinda yake jira kenan ko zai samu sassaucin abinda ya tsaya tsakiyar zuciyansa Amma still kallan nata kaman sake nauyin koma Menene yayi Dan haka a sanyaye Shima ya daga hannunsa Daya ya kirata ta Tako a natse tazo har gabansa.

Miqewa tsaye yayi ya kama hannunta Daya ya dago cikin sanyi yakai bakinsa yayi kissing din hannun tareda lumshe idanuwansa yanajin nutsuwa da sanyi na mamaye zuciya da ruhinsa ahankali.

Cikin sauti me sanyi da nutsuwa yakai bakinsa gap da kunnenta ya tambayeta tana tareda alwala.

Kasa dagowa tayi ta gyada masa Kai cikin sanyi.

Janyota yayi ahankali gefensa daga bayansa kadan ya tayar musu da sallah.

Nafila ce sukai wadda batasan ta Menene ba harsai da suka gama ya miqe ya zare mata hijabinta ya ajiye mata kan sofa ya janyota jikinsa ya rungume ahankali.

**Mr Jameel Dake Kiran wayoyinsa kaman zai Ari hauka a lokacin Jin yakeyi zufa da farin ciki da kuma rashin sanin mafita Yana Neman zautashi.

Cigaba yakeyi da sake Kiran wayoyinsa Amma Sam Babu Wadda ke shiga Dan haka ya kira ta Amatu itama tata a kashe Dan haka yakira Farha akan ta tura masa numbern Amatun Daya.

Tana tura masa yafara kira itama Bata dauka sbd wayarta Dake silent a lokacinda suke sallah.

Farha data kasa hakuri ta kira mr Jameel din ta tambayesa lafiya tana gama waya dashi text tayiwa Amatun Wanda ya shiga wayarta a lokacinda suka bar gurin da wayarta ke ajiye.

“Ankira Mr Jameel daga Greece Madame Abeeda ta Farka”

Shine text din data turawa Amatun tana Jin zuciyarta na Rasa itama murna zatayiwa TALBAs din kokuwa.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

47

**************

Anty Farha Jin tayi jikinta yayi sanyi duk da abu ne Daya kamata ace suna Taya ASH da ‘yayansa murnan farfadowan matarsa da duniya ta sheda Yana tsananin so,to Amma Amatun ta fa?

AmatulMaleek daya fara zama Wani bangaren na rayuwa,zuci da ruhinta fa,duk da shi mijin mata hudu ne Amma Kuma maganar samun guri ne a zuciyarsa akeyi ba wai aurenba.

Har cikin zuciyarta sanyi jikinta yayi taji da ba dare ne sosaiba tanason kasancewa da Amatun duk da Amatun bazaka taba sanin menene a cikin ranta ba ko menene tinaninta akan lamarin idan ya kama.

Shi kansa Mr Jameel kasa nutsuwa yayi da wasi wasi da rashin sanin abinyi a cikin Daren shiyasa yaso ya samu magana da ASH din sbd rubutacciyar umarni ce daga ASH din tin da dadewa cewan duk ranar da Madame abeeda ta Farka ko da wane lokaci labarin zaizo musu kar mr Jameel ya tsaya komai bayan Siya musu tickets da komai na tafiya,

Yanzu gashi sun dawo yau daga doguwan tafiya Kuma ayau din dole yasan ASH din na buqatan hutawa cikin sauran iyalin nasa,

Kashe wayoyin ASH na Daya daga cikin alamun Yana hutawa ne,

Gudun lefin rashin isar da sakon da wuri shi Kuma yake gudu ta Wani bangaren.

Anty Farha ce ta sake kiransa a karo na kusan uku tace Amatu Bata daga waya da alaman Kila tana tareda ASH din Kokuma tayi bacci Dan haka yawa Allah yabar zancen Nan harda safe sai a sanar masa tinda da Daren da safen duk Daya idan Rai yakai.

Shiru yayi tareda sauke numfashi da ajiyan zuciya Dan shi rudewama yayi Yana rasa Ina zai Saka kansa da wannan zancen Wanda da yanada hali ma boyewa ASH din zeyi kwata kwata Saiya huta daga wannan doguwar tafiyan tasu yanda ya kamata kafin ya sanar masa Dan yasan yana sanar masa Babu abinda zasu tsaya Jira sai sun bar qasar.

Baida zabin Daya wuce raba hannu ya dauko laptop cikin Daren ya cike komai na tafiyansu Wanda tsaban yawan zuwansu visa Bata musu wuya a qanqanin lokaci sun samu sun wuce.

Saida ya gama komai kafin ya aje ya miqe a kujeran Dake lafiyayyar palon gidansa Dan kuwa Jin yake bazai iya rintsawa ba hakanan Shima abin ya damesa sbd yasan damuwar da ASH dinsa ya fito zai iya komawa ta Maida lamuransa gaba Daya ga ciwon Madame Abeeda.

*****AmatulMaleek kuwa gama sallansu ya Sanyata tinanin komawa dakinta ta juya ta Kalli inda wayarta ke haske alaman shigowar Sako ko kira Dan haka ta juya zata nufi wayar a sanyaye sbd jikinta da yayi sanyi da Kuma gabanta dayake bugawa da irin sanyin data Gani a tattare dashi din yau kaman Wanda nutsuwansa ta ninku komai nasa a tsanake yake yi Yana bin kowanne motsinta da fitinanniyar kallan Dake kashe duk kuzarin jikinta Daya bayan Daya.

 Daqyar ta iya daga qafafunta zata Isa ga wayar sedai ko taku Daya bataiba ya riqo hannunta Daya ta Baya ta tsaya cak bugun zuciyarta na sake canjawa hakama jikinta na mutuwa Dan yau abinda zuciyarta ke ji akansa na daban ne,

Hawaye ne ke ciko idanuwanta tareda tsoro aduk lokacinda taji Wani irin Mafi girman yanayi cikin zuciyarta akansa.

Ahankali ya dawo da ita Baya zuwa jikinsa ya rungumota ta Baya suka matse jikin jikin juna suna lumshe idanuwansu a tare kowannensu zuciyarsa kaman zata fasa kukan abinda takeji.

Dukkaninsu jikinsu wata irin sanyi da nutsuwa ce suke ciki mara hayaniya da Kwanciyar hankali me sanyi duk da tanajin yanayinsa yau din na daban ne hakama tanajin fargaba da tsoro Amma mutuwan jiki da nutsuwan da abinda take ji akansa cikin zuciyarta me tsananin gaske ya Sanya nutsuwanta da kasalanta danne tsoro da firgicin.

Hijabinta data dauka a hannunta ne ya zame ya Fadi qasa lokacinda ya juyo da ita ahankali cikin nutsuwa suna fuskantar juna hannunsa Daya na zagayota tareda motsota jikinsa sosai suka manne yanda ya kamata tana Dan rufe idanuwanta.

Wuyanta Saka hannunsa Daya Yana shafawa ahankali Yana Jin Wani irin feelings masu karfi suna bawa komai nasa nutsuwa me sanyi hakama komai nata na fizgarsa ga kasa hakura da maidata cikakkiyar tasa takowane lungu da Sako.

Sake mannota da kirjinsa yayi ahankali Yana zira kansa zuwa cikin wuyanta Yana shaqanta Yana shafa fuskarsa a fatan wuyan nata hannuwansa na zare zip din gaban Rigarta ahankali cikin Wani irin slow me dauke Numfashi.

Yana Kai zip din karshe rigar ta zame ta Fadi qasa

Da kanta ta manne kirjinta ahankali da nasa sbd kunya me sanyi data saukar mata tana sanyaya jikinta.

Hakan datai ya sanyashi riqe numfashinsa Daya kusa barinsa ahankali Yana zagayota da tafin hannunsa Daya na yawo a fatan bayanta me laushi Dayan hannun na kamo fuskarta da idanuwanta ke rufe zuwa tasa fuskan ya fara zubawa lips dinta da idanuwanta Dake rufe mayun idanuwansa dasuka gama sauyawa cikin yanayin da komai ya gama kuncewa.

Wani yawu ya hadiye me sanyi kafin ya ya dawo da idanuwansa kan lips nata ya sake mayarwa kan hancinta da idanuwanta,komai nata kashesa yake yi Yana tada zaman lafiyan zuciya da ruhinsa.

Idanuwan yafara Dora lips dinsa yayi kissing ahankali kafin tsinin hancinta tukuna ahankali ya zaro harshensa Dake qamshin butter mint mouth wash ya Dora akan lips dinta ya lashesu cikin sanyi da nutsuwa tareda tsanani da feelings dinsa suke qarawa akanta.

Yanda ya sake lasan lips dinta ya Sakata Neman zubewa qasa ya tareta da kyau cikin jikinsa yanajin kirjinta na Neman qarasa kashesa da ransa tareda kunce masa notikan Kai.

Qanqameta yayi Jin komai nasa na kuncewa.

Kanta ya sake dagowa ahankali Bai tsaya sake lasa lips nata ba ya Dora bakinsa kan nata gaba Daya yana fara kissing dinta ahankali cikin sanyi da nutsuwa hannuwansa na sake qanqameta Dan Jin yake Kuma komai yazo ba komawa Baya.

Rigar jikinsa ta zare ya saki a qasa tareda sake hadeta da jikinsa Yana shan bakinta cikin salon Daya Saka hawaye masu dumi fara gangarowa daga idanuwanta Dake rufe numfashinta na Neman rabuwa da ita Dan saukan hannunsa kan wuyanta zuwa kirjinta Yana mata Wani irin shafa da abinda ya sake karye kuzarin qafafunta ta saki zatai qasa ya cirata sama gaba Daya Yana cigaba da Shan bakinta da wasa da jikinta ya nufi lafiyayyar gadonsa hayaqin dayake ji Yana fita ta kunnuwa da hancinsa harma da idanuwansa komai ji yakeyi kaman jininsa zai qone.

A tsakiyar gadon Bai tsaya ba cigaba yayi da tsotsanta cikin salo na nutsuwa sedai kanta Baya iya daukan wannan salon yayi mata karfi da girman da hawayenta gudu kawai suke qarawa sbd qarfi da zafin lamarin yau ya girmi kanta,

Shi kansa a cikin sanyi da nutsuwa yake komai Amma zafi da qarfin lamarin a jini da kansa yayi yawan da ya tashi daga ASH TALBA kwata kwata zuwa ASHRAF MUH’D TALBA Dan kuwa yanayi ne Daya manta Yaya mutum ke samun kansa a ciki sbd jimawansa Babu mace hakama ita nata abinda yake ji din daban ne Tin daga jininsa har zuciyarsa da Naman jikinsa yake Jin komai.

A daidai lokacinda komai yayi zafin da no going back rabata da komai nata yayi a lokacin hawayenta suka koma kuka me sautin da shigansa ma kunnensa qarasa bugar dashi yakeyi a mugun Mayen da bayaji baya Gani bayan son mayar da ita cikakkiyar mallakinsa da zatasansa a matsayin Miji itama.

Qanqamesa tayi cikin tsananin tashin hankali da tsoro me girman gaske kukanta na tsananta sosai jikinta na daukan rawa da mazari cikin rashin qarfi a lokacinda taji abinda yake kokarin daga rayuwarta daga budurwa zuwa Mace.

Wani abinda yake Neman haukata kansa yake Jin Yana ratsa koina da koina nasa take ya fice daga duniyar ASH ya fada duniyar datafi tasa,

Fitarsa hayyacinsa Ya sanyashi mantawa da komai da kowa harma da sauki da sassaucin da Amatun ke Nema.

Lokaci ya dauka Yana abinda ya kasa tantance shi waye,

Balai da masifan Daya ji ne ya sanyashi Kai hannu a zafafe ya daki bedside lamp Dake kan bedside drawer tareda yimata Wani irin damqan data fasa hannunsa jini yafara fita ahankali Amma Jin yake Bai samu sassaucin dayake buqata ba Wani irin irin numfashi da gurnanin Daya kusan sauka har qasan gidan ya saki Yana sakin lamp din da qarfin gaske tareda qanqame Amatun wadda tini ta jima da ficewa hayyacinta batasan meyake faruwaba.

*******Kusan awa Daya da mintina ya dauka qanqame da ita kafin ya samu jininsa Daya kusan konewa yafara dawowa daidai tareda zazzabi da Wani irin zafin jiki me qarfi ya motsa ahankali tareda Bude idanuwansa da sukai nauyi sosai jin kansa yake kwata kwata daban.

Fuskarta ya zubawa idanuwansa Yanajin abinda baisan me zaice akaiba,abu Daya yasani shine yau itace ranar da rayuwarsa ta taka Wani tsaunin da bayajin zai sake Kokuma buqatan sake taka irinsa har qarshen rayuwarsa Dan tsaunin Daya samu kansa Akai yau din ya ishesa tinawa tareda kafa masa Wani irin tarihi da shauqi na har abada.

Rawan da jikinta keyi sosai zafin jikinta na qaruwa Yana shiga nasa ya tinatar dashi da irin abinda ya sameta dole tana buqatan taimakon gaggawa Kokuma kulawa na musamman Dan kuwa har lokacin bata dawo hayyacinta ba.

Zamewa yayi ahankali cikin rashin kuzarinsa da Shima ya tafi ya sauko gadon tareda daukanta gaba Daya ya nufi toilet dasu gaba Daya.

Ayanda jikinsa yake shima yana buqatan ruwan zafin Dan haka tana rungume jikinsa ya Sakar musu ruwan zafi Yana kai fuskansa ahankali ya hade da tata Dan Bawa hancinta kariya daga ruwan da zai iya shiga hancin nata.

Numfashi take saukewa da qyar ahankali ahankali sbd Bata iya Jan numfashin da kyau hakama ko motsi,

Ruwan ya jima Yana sauka a jikinsu ya samu karfinsa ya dawo Dan haka ya gyara mata zama a jikinsa Yana Bude idanuwansa dasuke ja har lokacin Basu gama komawa daidaiba hakama hannunsa har lokacin Yana Dan fidda jini kadan kadan Amma San baima damu ba Dan baima lura da kyau ba.

Abu na farko Daya fara yi musu shine qasasu a ruwan zafi da kyau Shima qarfinsa ya dawo full,

Ita Kuma ta samu ta dan dawo hayyacinta ta iya Bude idanuwanta ahankali daqyar sedai zazzabi me qarfin gaske da rawar jiki suka rufeta.

Kayansa masu kauri dasukai mata yawa sosai ya Saka mata tareda safa ya sauya beddings sbd jininta da nasa na hannu duk sun lalata Wanda yake kan gadon ya kwantar da ita tareda rufeta cikin tsananin kulawan dayake jinta kaman babyn da aka Haifa yau.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

48

**************

Kaman yanda ake ganin wuni haka bacci ya qaura daga idanuwansa dasuka kasa komawa yanda suke kwance take cikin jikinsa duk zafin dayake jikinta a cikin jikinsa yake shigewa Yana jinsa Yana Kuma karba da nutsuwan zuciya,

Fuskarta ce kawai ya zubawa idanuwansa Yana kalla cikin hasken dakin da Babu yawa,

Baccin wahala da tsananin zazzabi takeyi Amma zuciyarsa Wani yanka takeyi na tsananin buqatan son sake kasancewa da ita Dan kaman bazai iya rayuwa idan Bai qarasa Maida ta macen ba completely duk da yasan ya Riga ya mayar da ita macen Amma bayajin yagama hudata tako Ina…..

Kome zai mata bayajin zuciyarsa zata samu cikewa daga abinda ayake ji a zuciyarsa game da ita Dan haka ya danne duk Wani abu da zuciya da ruhu harma da ganganr jikinsa keso sbd tsananin tausayinta da Jin zafin radadinta har cikin ransa da jininsa.

Kusan asuba zazzabinta ya Dan sauka sedai kukan datake yi sosai cikin jikin nasa na azaban datake Jin tana ratsata a jikinta wadda ta kasa magana bare fadan abinda take ji sai kukan kawai mara sauti da tsanani.

Kukanta raunana kuzarinsa yakeyi dan haka dole ya sake shigar da ita ruwan zafi Amma Sam Babu sassaucin dataji bayan ma Wani zazzabin Daya sake sauko mata,

Gaba Daya ta gama rikitasa Shima sai yaji kansa na sarawa da yanda take kukan dakuma zafin jikinta da yaqi sauka.

Har aka fara Kiran sallan asuba suna abu Daya na Neman yanda zai Samar mata sassaucin jikin kafin gari ya waye likitoci suzo su dubata.

Sai da Akai kira na biyu jikin nata ya Dan yi sauki har bacci ya sake daukanta a wahalce.

Sosai yake Jin kansa yayi nauyi hakama har lokacin idanuwansa idanuwansa Basu koma yanda suke ba,

Wanka yayi ya fito ya shirya cikin jallabiya fara qal me taushi ya zira takalmansa Yana qamshinsa me Nutsuwa da sanyi musamman yau din da kusan komai nasa ya sake nutsuwa da Wani irin kamewan class.

Wayarsa ya nufa ya dauki Daya ya kunna,

Tana kawowa wayar massage Kai tsaye ya rubutawa Jameel akan little Abeeda na buqatan likita yanzu yanzu.

Yana tura sakon ya mayarda wayar ya sake kashewa gaba Daya sbd Baya buqatan komai ko damuwa shi kansa kansa na buqatan hucewa daga abinda ya shigesa me girma a daren.

Goshinta ahankali ya shafa tareda kissing lips dinta da suka Dan Bushe mata duk da ruwan Daya ringa dauko mata a palonsa cikin Fridge tana sha.

Gaba Daya Daren Bai rintsa ba hakama itama baccin datake samu a yanken duk da wahala ne.

Bayan ficewansa sallah motsawa tayi ahankali tareda Bude idanuwanta dasuka kumbura sosai ko Gani sosai Batayi,

Babu inda Baya tsananin ciwo sosai a jikinta hakama zazzabinta har Wani fizga jikinta keyi.

Daqyar ta iya dafawa ta tashi zaune tana ganin jiri da radadi sosai a jikinta Amma batajin zata bari ya dawo tana dakin Koda da rarrafe ne dakinta takeson komawa Dan idan ya dawo Babu inda zai bari ta fita kowa zai wayi gari gidan yasan meya faru,

Maamah zata iya shiga mawuyacin halinda zata Sakata a tsaka me wuya Dan haka komai azaban datake ciki zata koma dakinta.

Daqyar ta iya saukowa gadon ta Isa inda wayarta take ta dauka Dan tana tsananin buqatan anty Farha kawai,

Hijab dinta ta Saka ko Gani Bata yi sosai tana dafa Bango ta fito,

Duk taku Daya idan tayi tanajin azaban datafi karfin kanta da kirjinta Amma hakanan ta daure tana rintse idanuwanta tana budewa daqyar ko hanyar Bata Gani sosai ta samu ta Isa bedroom dinta ta shiga ta tura kofan tareda faduwa qasa da rarrafe ta Isa toilet ta shiga ruwan safi tana fashewa da kukan radadi da azaban datake ji sosai.

Kuka takeyi sosai a toilet din takasa ko motsawa cikin ruwan taimako take nema Amma batasan waye zai taimaketa a wannan halin da ita kanta kunyar tinawa da abinda ya farun takeyi bare Wani yaji.

Jajir idanuwanta da farar fuskarta sukai tana kokarin cusa kanta cikin qafafunta taci gaba da kukan taji an Bude kofan toilet din Kai tsaye tareda shigowa…..

Cikin mummunan tashin hankali Daya dakatar da bugun zuciyarta ta dago Dan tasan maamah ce sedai ganin waye ya Sanyata fasa kukan da batasan na Menene ba tana sauke kanta qasa jikinta na tsananta rawa.

Qarasowa yayi ahankali har inda take Yana kallanta da tsananin Jin kukanta har ranta ya na isowa ya cirota daga ruwan gaba Daya Yana kallan fuskanta data qi kallansa tana cigaba da kukanta.

Daqyar ya iya samun kuzari tasa ya fita tayi wankan tsarkin itama ta daura towel ta kasa fitowa seda ya dawo ya dauketa ya fito da ita ya zaunar da kansa ya Saka mata doguwar Riga mara nauyi ba bra ba komai ta Saka rigar ya Saka mata hijab tayi sallah tana idarwa daga zaunen ta Bude Baki daqyar ta rokesa akan ya tafi.

Kallanta yayi zaiy magana ta fasa kuka tana sake rokonsa akan ya tafi.

Baida alaman tafiya likitan Daya Saka a Aiko yake jiran yazo ya duba sbd sosai take cikin azaban Jin jikin har lokacin rawa sosai jikinta keyi.

Kukan data ringa masa tana Neman shidewa ya sanyasa ficewa ya koma dakinsa dan kiran mr Jameel yaji abinda ya Hana likitocin zuwa har lokacin bayan tana Jin jikin sosai.

Bayan fitansa zubewa tayi qasan kwance tana kuka mara sauti jikinta na Jijjiga komai na jikinta kaman ana niqasa takeji musamman qasanta Jin takeyi azaban datake tai mata girma Dan haka kukanta yake sake tsananta.

Mr Jameel Daya kwana zaune Yana ganin sakon ASH akan buqatan likita take ya ajiye maganar rawar jikin isar masa da sakon Greece ya daga wayarsa ya kira asibitin dasuke komai ya buqaci likita mace da namiji.

Yana gama waya da asibitin Farha ya kira itama kusan kwananta Rabi da Rabi ne Dan haka tana ganin kiransa bayan asubar ta dauka da sauri tanason Jin idan yau zasu wuce kokuwa.

Gaisawa kawai sukai ya sanar mata da Amatu ASH ya buqaci a aikowa likitoci.

Dagashi har ita kowa da tinanin dayake ransa Amma dai sbd tsaro da Hana a Saka Amatun tsaka me wuya yace Farha din ta shirya gashinan yakusa isowa gidanta zai dauketa yakaita ta tsayawa Amatun idanma Wani matsalan ne ya sameta na rashin lfy.

Ko da suka iso Mansion din qarfe 6 da mintina Dan haka har Farha ta shigo ta Isa dakin Amatu Babu Wanda ma yakeda alaman tashi a jamaar gidan bayan su karima da suka fito Dan fara aiki.

Gaisawa kawai sukai ta wuce sama zuwa bedroom din Amatun Kai tsaye daidai ASH din ya fito lokacin ya sake dawowa ya dubata a karo na biyu.

Gaidasa Farha tayi cikin girmamawa idanuwanta na qasa

Ya masa Kai tsaye Yana wucewa tareda barin dakin da qamshinsa.

Shigowa tayi ko zama batai ba Dr beeba ta shigo tareda nurse Daya karima Tayi musu iso zuwa dakin batareda sunsan abinda yake faruwa ba.

Anty Farha kallo daya tayiwa Amatun ta fahimci abinda ya faru da ita Dan haka cikin sanyin Daya cika zuciyarta ta qaraso tana kama Amatun ta tashi zaune Amma Bata iya zama Dan haka Dr beeba ta qaraso bayan anty Farha ta rufe dakin bayan fitan karima.

Ita kanta Dr beeba Babu Shan wuya ta fahimci abinda ya faru Dan haka tace sai sun tafi da Amatun asibiti sun mata stitches.

Kuka mara sauti Amatun ta sake fashewa dashi tana jikin anty Farha wadda ke rarrashinta kada asan halinda take ciki musamman Husnah Dake kusa.

Anty Farha ce ta sanar da ASH abinda dr beeba ta ce.

Ga mamakinta shine da kansa yazo ya dauko Amatun bayan sun fice ya fito da ita ta kofan palonsa da Babu me ganinsa idan zai fita Yana fitowa mota na kofan palon yake shigewa

Itama ta Nan ya fito da ita ya shigar da ita mota Mr Jameel ne yau yaja motan suka Isa asibiti cikin qanqanin lokaci.

Isansu asibiti Babu Bata lokaci Akai mata dinkin Wanda ya sumar da ita bayan kukan azaba da wahalan datasha.

Allurai Akai mata tareda daura mata ruwa Bai dadeba ya qare sai lokacin ta dan farfado suka dawo gida lokacin karfe 8 na safe ya wuce Dan haka Koda suka iso ta kofan da aka fita da ita ta Nan suka ya shigo da ita tana hawaye ta nuna masa dakinta zata harya kaita ya kwantar ya rufeta ya fice Babu Wanda ya fito.

Kai tsaye bedroom dinsa ya koma Shima ya kwanta sbd baccin dazai samu ya koma shima wanda gaba Daya Bai rintsaba tin jiyan.

Wanka yayi da ruwan zafi sosai jikinsa ya sake hakama shi kansa Saida akai dressing na hannunsa.

Kaya marasa nauyi ya Saka ya shige bargon ya kwanta yaja sauke ajiyan zuciya da numfashi me sanyi.

A can dakinta kuwa baccin wahala ne ya dauketa itama anty Farha brush tayi ta sauko qasa taci abinci a kitchen ta nufi dakin maamah ta tarar da ita Bata tashi ba har lokacin Dan haka ta qyaleta ta koma dakin Amatun itama ta Haye gadon ta kwanta tayi baccin da bata samu yi ba Tin dare da Jameel ya sanar mata da sakon tashin Madame Abeeda Wanda haryanxu Bai sanarwa da ASH dinba ganin tashin hankalin da suka tashi dashi yanzu Kuma yabarsa ya huta musamman ganinsa da nasa raunin a hannu zai bari sai sun Isa office cikin Nutsuwa ya sanar masa da sakon duk da ya kamata ace an isar da wuri.

Kowa bacci yakeyi cikin mutanen gidan tsit kakeji bayan su karima da khaltume Dake aikinsu na tsaftace gidan da aikin breakfast kafin mutanen gidan su tashi,

Maamah ce ta fara tashi qarfe Tara da mintina ta shiga wanka tayi ta fito ta shirya tana kokarin fitowa Palo Farida ta shigo da breakfast dinta ta jiye mata a palo tareda gaidata ta juya ta fice.

Zaunawa tayi tana duba wayarta da sakwannin MTN sukai mata yawa tana son ragewa ta ajiye kafin ta gama karyawa tukuna idan Amatu ta dawo makaranta ta goge mata su ta dakatar mata da shigowansu.

Abincinta tafara ci hankali kwance tana Dan kallan tv da Farida ta kunna da tana sharan palon da safe.

Yau kusan kowa lattin fitowa yayi Se kusan 10 Husnah ta fito shirye cikin qananun kaya skinny jeans da black Fendi sweatshirt kanta daure da veil tana kokarin kunna wayanta Daya kwana kashe.

Sosai tayi mamakin ganin fitowan anty Farha daga bedroom din Amatu a lokacin dan kuwa garesu safiya ce karfe goman.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

49

*****************

Kallan da Husnah takewa anty Farha ya Saka anty Farha din kallanta tana sake fuska da kulawa tace

“Husnah kinfito kenan,barka da safiya,Yaya gidan?”

Cikin Dan kokarin boye mamakinta ta amsa da cewa

“Barka da safiya anty Farha,yau sammako kikai kenan keda ya kamata ki huta anty Farha kinyi hidima jiya”

Dariya anty Farha tayi tana qarasa zama a palon daukeda cup din custard me zafi data Saka karima ta hada mata tace

“Wlh Hutu Nan Ina buqatansa haryanxu Amma matar gidan Nan taku ce ba lafiya sosai shiyasa kika Ganni da sassafe a gidan,Amma inshallah tana Dan warwarewa zan tafi Nima na huta”

Kofar bedroom din Amatu Husnah ta kalla cikin takaici da mamakin yanda anty Farha din ta ambaci Amatun wai da matar gidan da Dan mamaki tace

“Me ya sameta ne?

Lafiya kalau fa ta kwanta jiyan da daddare.

Murmushi anty Farha tayi zatai magana kenan mum Aisha ta shigo palon maamah na bayanta dukkaninsu kallan Farha din sukeyi da mamaki dakuma ganin yanda Husnah itama take tsaye da mamakin tana jiran amasan anty Farha din.

Ita kanta kallansu tayi duk da mamakin ganin yanda kowannensu ke kallanta kaman wainda Basu taba ganinta ba.

Tamkar zakunan dasuka ga nama haka suke kallanta kafin maamah ta Dan juya ta Kalli hanyar dakin Amatu tana sake dawo da kallanta kan Farha wadda ta nutsu ta hadiye maganarta ta saki murmushi tana kawar da tinaninsu duka akan koma me suke tinani da son jin duk da Babu Wanda ko a giyar hauka acikinsu ya kawo tinanin da itama takeyi din akan nasu tinani ta Bude Baki fuska a sake Kuma cikin girmamawa ta gaida maamah kafin ta gaida Mum Aisha tana cewa

“Amatu ce ta kwana ba lafiya shine nayi sammakon zuwa sbd jiya Koda muka rabu Daman tana Jin zazzabi sosai da ciwon mara shine nayi sammakon zuwa da likita ta dubata Amma taji sauki”

Gaba dayansu a tare suke sake juyawa suka kalli kofan dakin Amatun maamah ma abinda Husnah ta fada ta maimaita cewa

“Lafiya kalau fa na rabu da ita jiyan da dare,wane ciwon mara Kuma a tsakiyan wata?

Mum Aisha dakin ta zubawa idanuwanta Bata ce komai ba kafin ta juya ta nufi bedroom din Kai tsaye sbd ganewa idonta ciwo da jikin Amatun.

Husnah ma kusan Daman dakin take kokarin nufa Dan gaba dayansu Hakanan sukaji ciwon nata na Neman Hana zuciyarsu nutsuwa.

Maamah ce a bayansu lokacinda suka Bude kofan bedroom dinta suka shigo dakin idanuwansu akan Amatun Dake bacci sosai fuskarta ta kumbura sosai alaman tayi kukan ciwon Kokuma kukan Wani abin.

Rarraba idanuwa kowannensu a fakaice yakeyi a dakin batareda sunga komaiba sedai hancin Husnah dayake Dan shaqar mata qamshin Dad dinta a dakin zuciyarta na harbawa Amma tana sake bawa kanta tabbacin ba Hakan bane shedan ne kawai da ke Sakata Jin qamshin dan haka Allah ya Bata lafiya kawai sukai mata fata suka fice Banda maamah data qaraso har bakin gadon na Amatu ta zauna a hankali tana kallanta cikin tausayawa ta dawo da kallanta kan Farha Data zauna kan sofa tace

“Menene ya sameta a dare Daya haka?

Likitan me sukace yana damunta?

Shiru Farha tayi tana shiga nazarin abinda zata fadawa maamah wadda ya kamata ace ta sanarwa gaskiyar maganar abinda ya samu Amatun Amma Kuma tasan fadawa maamah gaskiar zai kawo babban tashin hankali da baraka me girma tsakanin uwa da ‘ya Wanda bazataso Hakan ba musamman yanzu da Amatun take cikin wannan halin.

Numfashi ta sauke me sanyi wanda ya Saka maamah sake zuba mata idanuwanta tana jiran amsarta.

Kallan maamah din tayi ta Bude Baki a natse tace

“A yanzu dai taji sauki Se Dan abinda baa rasaba,ciwon mara ne kawai Se Kuma damuwa da sukace tana ciki tana buqatan kulawa…..

“Damuwa Kuma?

Damuwan me?

Akwai abinda yake damunta ne Wanda ban saniba?”

Cikin sanyi da damuwa Maamah ta jerowa Farha din tambayoyin wainda suke kashe jikinta da son fadawa maamah Amma Kuma tana danne zuciyarta da Hana kanta

Tace

“Damuwa bazai wuce na karatu da Kuma yanda kike kasa yarda da ita wasu lokutan maamah akan abinda ba laifinta bane,ba ita ta zabawa kanta Hakanba, a gabanki gaban kowa lamarin ya fada kanta Wanda kaman yanda kikaji haka tajisa maamah Amma kina ganin lefinta akan Hakan lokuta da dama,

Maamah Amatu na buqatanki sbd ke kadaice uwa Kuma abokiyar shawara da walwalanta,

Dan allah maamah ki Dena nesanta kanki da ita akan auren da Allah ne ya daurasa Dan kuwa shine ya qaddara ASH TALBA ne mijinta ba Itace ta kaddarawa kanta Hakanba…..

Kalmominta na karshe ne suka Saka maamah data fara yin sanyi da nasihar Farha din sauya zancen tareda dakatar dashi ta hanyar miqa hannunta ta dafa goshin Amatun daya huce Babu zafi a jikinta sbd alluran datasha da magani a asibiti ta Bude Baki tana cewa

“Allah ya Bata lafiya dai.”

Amin”Farha ta amsa dashi lura da maamah Bata son ko zancen auren Amatun da ASH tsaban zuciyarta ta bushe qyam akan auren batada Kuma niyar amsar auren.

Wayoyi anty Farha ta fara cikin nutsuwa da sakewa Wanda aket ayi mata na barkan waliman jiya

Maamah kuwa tana zaune tana kulawa da Amatun duk da bacci takeyi sosai batama San waye akantaba.

*****Qarfe goma sha Daya ya fito shirye tsaf cikin navy blue yadi me tsananin tsadan gaske hannunsa daure da agogon Rotary men’s Regent watch qamshinsa na tashi a cikin sanyin fuskansa fresh Wani irin nutsuwa ne ya bayyana a tareda shi duk da Shima a sanyaye yake baa ganewa sbd kasalan daya samu kansa acikinta.

Fitowansa yayi daidai da ihun da Husnah ta buga acikin gidan dukkaninta jikinta na tsananin rawa da farin ciki da rudewa harma da firgicin abinda bata taba tinanin zata ji ba arayuwartaba sbd tashin mahaifiyarta Wani abu ne da kusan kowa ya cire ya debe tsammani idan aka cire Dad dinta da Bai taba cire daga tashin matar tasa ba.

Aunt labiba Dake can qasar ce ta kirata ta sanar da ita wannan labarin Daya firgitata ta saki ihun da batasan tayi ba.

Ganin Dad dinta a gabanta lokacinda y Sako Kai palon nasu Dan isa dakin Amatun ya Sanyata qarasowa gurinsa ko Gani batayi Dan tasan ihunta ya sanyasa shigowa tana tsayuwa gabansa bakinta na rawa duk jikinta ma rawa yakeyi tace

“Dad,mum ta farfado, your wife is out of coma, she’s conscious Dad…..

Bata qarasaba kawai ta yanke jiki ta zube a ya tarota jikinsa komai nasa na dakatawa Shima cikin Wani irin mamaki da shock Dan bazai yiyu Hakan ta faru ba ace a bakin Husnah din yake ji ba batareda asibitin sun nemesa ba.

Maamah da Farha ne da ihunta suka fiddosa da gudu suka ganta some a jikin Dad dinta da sauri Maamah ta kamota tana dawo da ita jikin Farha suka kamata zuwa kujera shikuwa juyawa yayi ya fice idanuwansa na sauya batareda kansa ya dauki zancenba tsaban tashin hankalin idan ba Wani ne zai rikita masa qwaqwalwan ‘ya ba Amma tayaya matarsa zata Farka bayan shekaru a kwance ace ba shine na farko da zaa sanarwaba.

Mr Jameel Dake jiran saukowarsa a guest Palo Dake gefen security room da sauri ya fito ganin Kiran ASH din akan wayarsa.

Yana fitowa Babu mota Kai tsaye ya Bude masa ya shiga da sauri Shima ya shiga suka kama hanyar office Dan vcall yake buqata da Personal attendant na room din da Abeeda take.

Daga securities har mr Jameel take suka fahimci yau din yanayinsa a bayyane yake na bacin Rai da rashin sanin gaskiyar maganar.

Suna isowa office da sauri mr Jameel yabiyo bayansa cikin office dinsa kafin ASH din ya qara taku biyu cikin sanyi da damuwar jinkirinsa da Dan shakku yace

“Tin dare kanada pending call Daya Greece madame is conscious nayita Kiran…….

Dakatawar da ASH din yayi zuciyarsa na daukewa daga wutan bugawa ya Sanya Mr Jameel din yin shiru Yana qasa da kansa cikin damuwa.

Hannunsa Dake nade da bandage yakai ahankali ya dafa table Dake gabansa Dan jiri da nauyin da zuciyarsa ta Dan dauka da abinda Jameel din ke fada masa yanzu.

Ganin hakan Mr Jameel ya dago cikin son isar da sauran bayanin yace

“Nayi booking komai na tafiya zuwa can din komai a shirye yake ticket kawai za’a Siya”

Rintse idanuwansa da sukai jajir ASH din yayi kusan sanyi da Wani irin nauyi dayaji Yana sauka daga zuciyarsa yaji suna gangara jikinsa.

Qarasa zaunawa yayi Yana Bude laptop din da Mr Jameel yayi saurin kawowa ya ajiye gabansa Kai tsaye yayi Saka Kiran Kai tsaye me zuwa dakin Abeeda.

Mintina kafin Kiran yayi connecting aka basa Daman miqa Kiran zuwa dikinta Kai tsaye.

Abinda ya Gani ne ya sanyashi rintse idanuwansa Wani abu me nauyi da tarwatsewa daga kirjinsa idanuwansa sukai sauya take zuwa ja a Karan farko Dayaji yana kasa riqe yanayinsa na farin ciki da mamakin Daya girgizasa ganin Abeeda idanuwanta a Bude aunt labiba na tareda ita da nurse a dakin duk da kwance take Amma idanuwanta dasuke a Bude Kuma itama shi din Daya bayyana tv Dake dakin take kalla hawaye na gangaro gefen idanuwanta suna saukowa.

“Abeedah” ya furta cikin sautin Daya qarawa hawayenta gudu tana Dan motsawa ahankali.

Motsawanta ya Sanya aunt labiba fashewa da sabon kukan farin ciki shikuma Jin yayi Babu abinda yake buqata a wannan lokacin bayan ganinsa a Greece Dan haka Tim kafin ya dago ya Kalli Mr Jameel dayafi kowa sanin maanar ko motsin ASH da sauri ya juya ya fice Yana Ciro wayarsa daga jikin tsadaddiyar suit dinsa take yakira ya Siya ticket din da zasu Isa Lagos a ayau gobe su wuce.

Madame abeeda kuwa hawayenta ne suke qara gudu ganin fuskar mijinta datafi so fiyeda komai da kowa,

Shine hasken idanuwanta Kuma qarfinta kuzarinta da yayanta Dan haka hawayenta ke qara gudu tanajin tsananin son ganinsa a kusa da ita shi da yayanta.

A nasa bangaren kasa magana yayi bayan sunanta dayake ambata yanajin yau ranar itama ta musamman ce a garesa da rayuwarsa.

Mr Jameel kuwa tini ya fara clearing schedules din ASH din gaba Daya na wannan satin da satin gabansa Dan kuwa a yau zasu wuce Lagos.

A can gida kuwa a lokacinda maamah da anty Farha ke kokarin dawo da Husnah hayyacinta tana Bude idanuwanta abinda ta fara kallan maamah tana furtawa shine

“Maamah mum dina ta farfado,

Mum dina ta tashi,

Mum dina zata dawo gareni ga mijinta Dad dina,

Maamah mum Bata barmu ba ta dawo”

AmatulMaleek data farfado daga nata baccin a lokacin cikin Dan samun karfin jiki da kuzari ta tashi zaune ba zazzabi a jikinta Dan haka wayarta kawai ta miqa hannu ta dauka Dan Neman anty Farha a waya tazo sai alokacin idanuwanta suka sauka kan sakon anty Farha din tin na cikin dare.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

50

****************

Zubawa wayarta Dake hannunta idanuwanta Dake a kumbure tayi ahankali kalmomin Dake rubuce a cikin sakon ma shiga Kai zuwa ciyarta daki daki.

Nauyi idanuwanta suka fara qarawa ahankali tana kokarin ajiye wayar sbd nauyin dataji tana yi mata a hannu batareda ta kira anty Farha din data so Kiran ba.

Kofan bedroom din aka Bude da sauri aka shigo,

Kasa dagowa tayi sbd nauyin da komai yayi mata har ganin nata,

Anty Farha dakatawa tayi tsakiyan dakin tareda zubawa Amatun idanuwanta cikin tsananin tausayi da damuwa ganin halinda take ga wayar a gefen hannunta da alama Kila abinda tazo gogewa da sauri shine Amatun ta riga ta karanta.

Jin shiru ya Sanya Amatun dagowa ahankali tana danne dukkanin abinda take ji na ciwon jiki dana zuci dayake sauka ahankali duk yanda takeson yaqansa Hakan na Neman gagararta ta zubawa anty Farha idanuwanta suna sake sauyawa da dukkanin jarumtarta take danne hawayenta da sedai ganin kallan da anty Farha ke Mata cikin tsananin sanyi da tausayi harma da damuwa ya Sanya hawayenta gangarowa ahankali tana rufe idanuwanta.

Anty Farha da sauri ta qaraso tareda zaunawa gefen gadon tana rungumeta cikin kulawa da kauna me girma tana kasa magana itama.

Runguman da anty Farha tai mata ya Sanyata sakin sauran hawayenta tanajin zuciyarta na nauyi me nauyi sosai Wanda batasan na Menene ba Amma dai tasan tana cikin nauyin kirji da Kuma ciwon da ke damunta.

Ahankali anty Farha ta Bude Baki tana cewa

“Komai ze wuce,komai zai koma kaman baayiba,Zaki warke,Zaki iya fuskantar komai na rayuwa da sauki inshallah”

Batasan me take fahimta ba bayan abinda takeji kawai Dan haka hawaye sosai takeyi tana kokarin bawa kanta qarfin halin danne ciwon jikinta datake ji tareda zafi da radadin inda Akai mata dinki.

Share hawayenta tayi tareda dagowa ta Kalli anty Farha tace toilet zata shiga.

Kamata anty Farha tayi har bakin toilet ta shige ahankali tana tafiya a Dan ware ta rufo kofan.

Anty Farha kuwa fitowa tayi ta wuce maamah da Husnah Dake palon cikin tsananin rudu da farin ciki harma da gargaba da tashin hankalin ta inda maganar auren Nan zata fara bullowa Abeeda.

Qasa anty Farha ta sauka ta nufi kitchen ta samu khaltume na aiki tareda su karima,

Kariman ta kalla tace taje ta gyara dakin Amatun kafin ta fito wanka.

Dawo da kallanta tayi kan khaltume ta fada abinda takeso a dafa mata sharp sharp.

Tea me kauri sosai Wanda Milo yafi yawa ta hadawa Amatun ta wuce sama dashi tana Isa still bedroom din Amatun ta wuce ta shigewarta.

Amatu kuwa a cikin toilet din yakice komai take kokarin yi daga zuciyarsa Wanda shedan yake Neman cusa mata Dan lafiyanta da yanda maamah zata kasa gane halinda take ciki take nema.

Ruwan zafi sosai ta Tara a bathtub ta zare towel din data daura ta fara zira qafarta Daya kafin ta shigar da dayar ta shige ruwan ahankali ta zauna acikinsu.

Azaban dataji tana ratsata ne ya Sanyata rintse idanuwanta ahankali hawaye masu radadi suka gangaro mata Wanda take dangantawa da radadin ciwonta Amma Kuma daga zuciyarta radadin hawayen ke fitowa Dan nauyin kirjinta yakasa ko girgizuwa.

Qara Gudu hawayenta keyi tana kasa riqesu sai kawai ta saki kuka mara sauti tana rufe fuskanta da bakinta da tafin hannayenta ta can Kuma ruwan zafin na ratsata.

Ta jima a Hakan kafin ta share hawayenta ta Bude ruwan suka tsiyaye tana ciki batareda ta tashi ba

Suna gama tsiyayewa ta sake Tara wasu duk tana ciki zaune ruwan ya sake taruwa ta sake jimawa acikinsu kafin jikinta ya Dan samu karfi da kuzari tayi wankan daga zaune cikin bathtub din.

Tana gamawa brush ta sake yi ta sake goge fuskarta da towel me kyau kafin ta Bude kofa ta fito tana daurewa duk zafi tana tafiya daidai tinanin zata samu maamah a dakin amma maamah din Bata dakin.

Numfashi kawai ta sauke a boye kafin ta qaraso ahankali ta zauna gaban mirror tana Dan kallan kumburan idanuwanta da Jan su harma da fuskanta gaba Daya.

Bady oil ta daure sama sama ta shafa sbd anty Farha datake taimaka mata.

Turare ma kadan ta shafa anty Farha ce ta dauko mata kaya ta fara Saka undies kafin ta Saka doguwan Aleana katar gown mara nauyi Se kudi.

Tana gama shiryawa dawowa tayi kan shimfidan sallan da Akai mata ta zauna a zaune tayi sallan sbd bazata iya tsayuwa ba jiri take ji da rashin qarfin jiki.

Har ta idar da sallan maamah Bata shigo dakinba Dan haka ta miqe ahankali ta koma kan kujera ta zauna ahankali tareda hade qafafunta guri Daya qafarta sanye da safa me taushi.

Tea dinta aka sake qarowa zafi aka dawo mata dashi ta karba jikinta a sanyaye tace

“Thank you anty Farha”

Gyada mata Kai kawai anty Farha tayi tana nuna mata bowl na Naman da aka danderunsa tana cewa ta daure taci.

Dayake Bata iya magana bare gardamawa sbd zuci da gangar jikinta gaba Daya Babu me dadi.

Ahankali ta ringa cin Naman tana cusawa cikinta tana Shan tea din har ta Dan ci sosai ta shanye tea din gaba Daya Dan shine yafi mata dadi sosai a ciki.

Fitar da kayan Akai anty Farha ta Bata maganinta ta sha sai alokacin anty Farha ta zauna tana daukan wayarta tana Dan duba chats kafin ta turawa Mr Jameel txt na tambayar ASH TALBA zai tafi Greece dinne yanxu?

Mr Jameel dayake tareda ASH a lokacin Yana kammala Wani aikinsa ne da wasu baqinsa,

Satan kallansa yayi Yana sake karanta sakon Farha kafin ya Bata reply da cewan yau din zasu bi flight na dare zuwa lag,ya Dora da tambayar Yaya jikin Amatun.

Kasa basa amsar jikin Amatun Daya tambaya tayi ta ajiye wayarta tana Kai hannu ta dauko wayar Amatun Dan duba ko sakonsa idan ya shigo sai Taga wayar a flight mode Amatun ta Sakata.

Juyowa tayi ta Kalli Amatun Taga taqi kallo gefenta idanuwanta a rufe suke duk da ba bacci takeyiba.

******Maamah a Palo kuwa kusan da farko shock ta shiga na zancen farkawar Abeeda Daya shiga kunnuwanta,

Abeeda ta tashi?

Abeeda zata dawo garesu?

Abeeda ta rayu??

Hawayen farin ciki da tashin hankali da firgici ne lokaci Daya suka fara gangaro mata tana jikin duk jikinta na shiga rawa da sanyi.

Husnah ma hawaye takeyi cikin murna da farin cikin Dake Neman zautata,

Rungume maamah tayi tana murna tana maimaita mum dinta ta tashi.

Toshewa kan maamah yake Neman yi Dan kuwa Jin tayi kaman yau Abeedan zata dawo Dan haka ta shiga tsoro da tashin hankalin wannan data kasa rabasa Tin tini,

Wace kaddarar ce wannan?

Tayaya zata bari Abeeda taji wannan zancen auren?

Tayaya Abeeda zataji ‘yarta ce take auren mijinta da itace tasani Kuma ta sheda yanda take tsananin son ASH da kishinsa…..

Kasa motsawa tayi daga inda take zaune tareda shiga tinani da firgici,

Ga dai labarin farin ciki me girma dasuketa Jira tsawon shekaru Amma gashi murnarsu na rauni sbd wannan auren daya zama auren kaddara.

Husnah kuwa wayoyi tafara cikin murna da farin cikin data rasa Ina zata Saka kanta ta miqe ta wuce dakinta tana cigaba da wayoyinta tabar maamah din zaune a palon kaman Wanda ta shiga coman itama.

Maamah gaba Daya mantawa tayi da Amatu batada lafiya sbd halinda ta shiga Dan haka ta manta da komawa dakin Amatun ta koma dakinta zuciyarta na nauyi da shiga tinani me zurfi da nauyi sedai bangare daya na zuciyarta farin ciki me girma da sanyi sosai takeji na tashin yar uwarta Dan kuwa a rayuwa babban burinta baifi farfadowan Abeeda ba,

Bayan yayanta da mijinta itace a duniya tafi kowa fata da adduar Abeeda ta Farka yau Kuma gashi Allah ya amsa adduarsu ya tayar musu da ita.

Amatu kuwa a kwance ta wuni jikinta gaba Daya yaqi dadi anty Farha ce ta ringa kulawa da ita cikeda kulawa da tattali tana kokarin hanata shiga damuwan ciwon.

Zuwa yamma zazzabi ya sake rufeta sedai anty Farha tayi kokarin ganin ya sauka ta hanyar Bata magani da goge mata jikinta ta rage Mata zafin.

Sai bayan sallan magrib gidan kusan kowa ya Tina da ciwon Amatun har maamah,

Bayan sallah magrib maamah ta shigo dakin tana kallan Amatun tana zaune tsakiyan gadonta Rabin jikinta rufe tana sanye da halfvest sbd zafin jikinta ya Ragu anty Farha na zaune sai a lokacin ta gama sallan magrib dinta.

Qarasowa maamah tayi tana kallan Amatun yanzu cikin tausayawa gaba Daya ta koma kaman wadda tayi sati tana jinya gashi ta tafi tanata murna da farin cikin farkawar Abeeda Batazo ta sake duba ‘yarta ba.

Zaunawa tayi kan kujera tana kallan Amatun cikin tausayi da kulawa da kauna tace

“Amatu Yaya jikin naki?

Wai jikin har haka ne sosai Daman?

Kuka kikai ta yi ne fuskanki tayi Hakan Amatu?

Numfashi Amatun ta sauke ahankali tareda yin qasa da kanta kawai Dan batasan me zatace ba.

Anty Farha data miqe tsaye tana zare hijabin sallah tace

“Kuka taketa yi shiyasa duk ta sauyawa fuskanta kama Amma dai yanzu jikin nata yayi sauki,

Allah dai ya qaro afuwa ya Bata lafiya gaba Daya”

Amin” mamah tace tana dawo da kallanta kan Amatun tana cewa

“Meye abin kuka a ciwo Amatu,

Ai dauriya akeyi ba gashi yanzu kin samu saukinba..

Shigowan mum Aisha da Husnah ne a bayanta ya saka maamah da anty Farha kallan kofar banda Amatu da Bata Kalli kofan ba saima Dan lumshe idanuwanta tayi Dan batasan hayaniyar da zasu iya tadawa a dakin.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

51

**************

Daga Husnah har mum Aisha idanuwansu akan Amatun suke fatar jikinta na daukan idanuwansu sbd Babu Wanda ya taba ganinta a Hakan acikinsu,Basu dauka kyau da lafiyayyar jiki har haka ne da ita ba,

Mum Aisha kallan qurullan datake mata Se yanzu ne take jin tausayin Naufal Ashe abinda yasashi nacewa Amatun kenan sbd ganin asalin kyanta da Kila shine kadai ya taba ganinsa gashinan an sabauta mata shi sbd wannan kyan Dan macijin,

Husnah ma kuwa kasa dauke idanuwanta tayi daga kan Amatun Babu abinda yake jikin Amatun da Bai tsole idanuwanta ba ya tokare kirjinta Dan kuwa da ace Amatun da gaske zata zama matan Dad dinta kishiyar mum dinta zata iya zaucewa Dan Taya mum dinta kishi sbd da ba ita din yarinya ce ga zama matar Dad dinta ba da tabbas Amatun zata iya zautar da Dad dinta idan ya ganta ahakan,

Anty Farha ce ganin duk sun rude sunma rasa me ya kawosu bare magana ta nufi wardrobe zata daukowa Amatun rigar da zata Saka aka Bude kofar bedroom din cikin nutsuwa tareda turowa

Kaman a mafarki dukkaninsu qamshinsa ya sakasu juyawa ga kofar gaba dayansu.

ASH TALBA ne da kansa ya Bude kofar bedroom din Yana sanye da kayan Daya fita dasu tin safe hakama qafafunsa ba slippers bane Da Yana dawowa gida yake zare takarminsa ya Saka slippers dinsa masu taushi da tsada dasu yake yawon cikin gidansa Dan sakewa.

Da alama dawowansa mansion din kenan Kokuma daga mota Kai tsaye Nan din ya fara zuwa.

Mamaki ne a kan fuskan kowannensu Banda Farha data ji sanyi da farin cikin ganinsa zuwa duba Amatun dasuka cire Rai da zuwan nasa,

Maamah Amatu ta juyo ahankali ta kalla da idanuwanta dasuka cika da mamaki Amma tana boyewa,

Amatun kaman yanda Bata dago ta Kalli su Husnah ba bayan shigowansu hakama yanzu din Bata Kalli kofarba duk da qamshinsa ya bata tabbacin waye din y shigo dakin.

Mum Aisha Baki take Neman saki zarginta na son sake tabbata sedai Kuma itama dole ta danne nata mamaki da tashin hankalin tana boyewa kaman yanda maamah tayi.

Husnah ce ta kasa boye mamaki da firgicinta harma da baqin cikin dayake neman mamayeta na ganin Dad dinta a dakin Amatun,duk da tasan bedroom dinta zai tafi kila ya zo Nan din.

Cikin kokarin daidaita kanta kada ta bayyanarda abinda takeji a gabansa tace

“Dad ba Nan ne bedroom dina ba,

Kuma naji sauki sosai kana fita na farfado na…..

Idanuwansa Dasukai ciki ciki da pressure datai masa yawa ya dauke daga Amatun Daya zubawa su tin shigowansa ya watsawa Husnah ahankali ya furta

“Husnah kuje idan na fito zamuyi maganan zan duba Abeeda I have a flight to catch”

Yankewa maganar Husnah tayi tana sake matsowa tace

“Dad mum zaka duba yanzu? Ta Vconference?

I want to join too D….

Katseta yayi cikin nutsuwa da rashin son hayaniyar da cewa

“Little Abeeda”

Faduwa gabanta yayi da karfi tana Neman sarqewa da yawunta dataje hadiyewa ta juyawa da sauri ta kalli Amatu wadda taqi kallansu har lokacin saima sake rufe idanuwanta datai ahankali cikin sanyi da rashin kuzarin datake tare dashi.

Maamah wannan gabar kasa riqe mamakinta tayi ta zubawa AmatulMaleek idanuwa tana shiga tashin hankali da faduwan gaban itama,Ina take Jin little Abeeda, Amatun ce ya ambata Hakan??

Mum Aisha kuwa rikicewa ma tayi ta nufi hanyar fita maamah na bin bayanta da anty Farha data fasa dauko mata rigar sakawa tabi bayansu bayan takama hannun Husnah suka fito sbd Taga alaman bazata iya motsawa daga inda take tsayenba.

Anty Farha Jan kofar tayi bayan sun fito tana kallan maamah da batasan ma Ina take Saka kafartaba tsaban duhun da idanuwanta ke Neman yi sbd tinana da tashin hankalin meya hada ASH da zuwa duba Amatun ana zaune kalau,hakama waye ma ya sanar dashi ciwonta?

Hakama ciwon bama Wani me girma ba da zaace zaa zo dubiya a irin wannan lokacin.

Mum Aisha kuwa kujeran datake seti da bedroom din Amatun ta nema ta zauna a palon sbd ta hango ficewansa da lokacin da zai dauka a dakin.

Husnah anty Farha ce ta riqeta da kyau ta zaunar da ita tana cewa ta lura karta Fadi.

Ahankali ya Tako zuwa gadon datake a zaune din idanuwansa gaba Daya akanta Yana Jin pressure dinsa na raguwa kaman ana zazzage masa su suna bin iska.

Jin takowansa zuwa gareta ya Sanyata Bude idanuwanta ahankali batareda t dago ta iya kallansa ba Dan kuwa mutuwa jikinta yakeyi da zuciyarta akan matsayin da zata samu kanta yanzu da matarsa ta farfado,sedai Kuma tasan a Wani gabar ita Kanta tana murna da farin cikin tashin Madame abeeda bare shi dayake mijinta tinda dukkaninsu Babu Wanda qiyayya ta hada kowa kaunace ta hadasa da Abeedan daga ita har shi din.

Rashin saukan idanuwanta akansa ya Sanya jikinsa nauyi ya zauna ahankali cikin nutsuwa gefenta tareda miqa hannunsa Daya ya zagayota jikinta Dayan Kuma ya kama hannunta Daya ya sarqe da nasa din Yana sauke numfashi tareda ajiyan zuciya me sanyi a cikin kunnenta Wanda ya Sanyata Maida idanuwanta ta rufe tana riqe hawayen dayake son zuwa idanuwanta ta hanasu taruwa.

Cikin nutsuwa da kulawa ya sake sarke yatsunsa da nata ya zuba mata idanuwansa yace

“Yaya jikinki?

Are you still in pain kaman da safe?

Dr zaizo da Daren Nan ya sake dubaki before na wuce…..

Se a lokacin ta Bude idanuwanta ahankali ta Dan kallesa tana zuba mata idanuwanta dasukai laushi gaba Daya.

Jin yayi kansa na Neman kuncewa da kallanta sedai Bai nuna Hakan ba cikin kulawa a natse yana Kai hannunta bakinsa yayi kissing ahankali yace

“Zanyi tafiya a yau din Nan dole zuwa Lagos daga can Greece zan tafi….Abeeda ta farfado,I have to be there,akwai formalities and…”

Shiru kawai yayi batareda ya qarasaba ya dago ya zuba mata nasa idanuwan Shima Yana shafa wuyanta da fuskansa a natse Dan Jin zafin jikinta Daya sauka.

A handkali ta dauke idanuwanta daga kallan dayake mata ta Bude Baki cikin sanyi tace

“Allah ya tsare hanya,

Allah ya Bata lafiya yasa qarshen wahalan ciwon nata kenan”

Maganarta ya sanyashi zuba mata idanuwansa Batareda ya daukeba,

Jin yakeyi kaman bazai iya barinta ba a yanzu datake buqatan kulawa sosai sedai Kuma hankalinsa zai rabu ne zuwa da ita kaman yanda itama can Abeedan take buqatansa hakama little Abeedan bayajin tana buqatan ayi doguwan tafiya da ita a wannan halin datake ciki dayake ga kaman ko dogon motsi bayason tana shiga Dan shi kadai ne yasan irin yanda take buqatan zama guri Daya ta samu lafiya.

“Amin” ya furta ahankali kusa da kunnenta da sautin da bazai dametaba kafin ya Dora da tambayar taci abinci?

Gyada Kai tayi ahankali har lokacin Yana zagaye da ita da hannunsa Daya Dayan na sarke da nata.

“Ya maganinki,did you take them too??

Gyada masa Kai tayi tana dan dagowa ta kallesa take ya Kai bakinsa yayi kissing idanuwanta ahankali Yana sauke ajiyan zuciya me Dan nauyi.

Motsawa tayi zata gyara zamanta ya gyara masa da kansa Yana tambayarta Yaya dai,ko tanajin wani abin ne.

A Palo kuwa zaman jiran haihuwar gwaggo sukeyi gaba dayansu babu magana Se kallan kallo da Satan kallan hanyar bedroom din.

Maamah a jiqe take da zufa cikin rigarta Amma dai ta danne ta boye tinda dai bawai abinda suke tinanin bane na ASH din zai fara bawa Amatun matsayin matansa kawai dai dubiya ce sedai dadewan ne duk ya daga hankali da Sakata tinani da damuwa jiki a mace,harga Allah batason abinda zai hada Amatu da ASH ko kadan tinda Akai wannan auren.

Mum Aisha kuwa hankalinta rabuwa yayi uku akan makomar ‘danta da Kuma abinda yake Shirin faruwa tsakanin ‘yar Asmau da ASH dakuma farfadowan Abeeda datake fatan Allah yasa daga can ASH din na zuwa yafada mata yayi aure zuciyarta ta buga Cancer dinta ta haukace koina kaca kaca ta koma mutuwar kwancenta

 Dan kuwa matsalolin yawa zasu mata Bata gama data Asmau da ‘yarta ba yanzu Abeeda ta taso tace ta amince da auren shikenan Asmau da yarta sun zama masu gida,hakama shi ASH ya samu yanda yake so bayan ya kassara mata nata Dan tana ji tana Gani yakoma gurgu,

Wlh yanda batajin dadin rayuwar yanzu ita Danta Babu Wanda zeji dadi a mansion din TALBAs kowa Se yaji abinda bayason ji, Wanda zuciyarsa zata buga ta buga ya mutu, hakama Wanda ze haukace ya haukace hakama me Rabon sake komawa coma ya koma me mutuwa da ciwon so Shima Dan ubansa ya Dade be mutu ba.,

Itace zata sama yar sakon mugun labarin kowa kaman yanda kowa ya zama Dan isar mata da baqin cikin zuciya,

Fatanta yanzu ASH ya Maida Amatu matarsa ta fasawa maamah labarin tareda qarawa da Wanda ze fasa zuciyarta ta qara gaba ko itama tabi Aminiyar tata coma can su qarata ta samu taji da Amatun kawai Dan haka take Saka ido sosai akansu tinda alamun sun fara nuna Hakan na kusa a yanda ASH Baya iya Hana idanuwansa kallan Amatun.

Husnah kuwa asthma da basusan tanada shi bane yake Neman tashi ahankali ahankali

Mum Aisha ta Gani tayi mata banza tana hakama Aunt Farha ta Gani itama ta dauke Kai tana cigaba da wayarta na Dr beeba data dawo sake duba Amatun.

Maamah dai batama San me kowa yake cikiba ta sauko qasa kitchen ta zauna cikin sanyin jiki da tinani tareda damuwa me nauyi.

Dr beeba ce ta shigo palon saman karima data hawo da ita tana bayanta  kafin ta juya ta sauka.

Anty Farha ce ta miqe tana masa sannu da qarasowa kafin ta nufi bedroom din tayi knocking ahankali.

Bata sake buga kofanba ta dawo ta dauki wayarta ta kira Mr Jameel ta sanar masa ya fadawa ASH Dr beeba tana Jira a Palo.

Mr da Daman Shima a matse yake da ASH din sbd suna kokarin yin lattin zuwa airport Amma ya kasa kira dan yasan bama lallai ya dauka ba Dan yafara lura da idan Yana tareda Amatun samun daukan wayarsa dace ne.

Daurewa yayi ya turawa ASH din sakon Dr beeba na Palo zata duba Amatun kaman yanda ya buqata.

Daman shigowa ya bawa Dr beeba wadda ita kadai ce ta shiga dakin ta rufe ta qaraso ta zauna tana Dan kallansu cikin nutsuwa da shaawan kulawansa gameda iyalinsa.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

52

******************

Zaunawa Dr beeba tayi tana kallan Amatu cikin kulawa tace

“Yaya jikin naki?

Kin shiga ruwan zafi din Amma ba sosai ba Right??

Eh” Amatun ta Bude Baki ta furta kaman Wadda ke cikin sabuwan azabar ciwon.

Jin yayi Yana Neman shiga Wani tsaka me wuyar ganin yanda take magana kaman har lokacin tana cikin ciwo.

“Yanzu Yaya kikejin jikin harma da stitches din?

Kina Jin fever haryanxu?

Girgiza Kai tayi Kai tsaye.

“Are you sure?” Ya fada ahankali cikin nutsuwa Yana kallan cikin idanuwanta hannunsa har lokacin cikin nata.

Dauke idanuwanta tayi kansa tana gyada Kai kawai.

Numfashi Dr beeba ta sauke a boye Dan ita duk Neman rudewa takeyi daga duba Amatun Dan haka ta ce su shiga toilet zata Dan duba Amatun.

Dr beeba ce ta kamata da kanta suka nufi toilet din Yana bin bayan Amatun da Wani irin kallon yanda take tafiyar ahankali.

Basu Wani jimaba suka fito lokacin Dr beeba Kai tsaye Bata zaunaba ta sanar masa komai zai warke ahankali kulawa kawai take buqata.

Ficewa tayi sbd duk a rikice take da other side of ASH TALBA din da bata Saba gani ba ko tace jamaa Basu saniba.

Tana fita zaunar da ita yayi kan cinyarsa ahankali Yana matse tafin hannunsa da nata Yana kallanta yace

“Farha zata zauna anan ta kula Dake sosai is that ok with you??

Ko Zaki koma gidan Farha din kafin kiji sauki?

Wanne kikeso?

Ahankali ta Bude Baki tace

“Ta zauna anan din sbd maamah bazata bari naje koina ba harna kwana”

Wani irin murmushin da Bai san ya Akai ya sauka fuskansa bane ya dan sauko masa yana kallan bakinta Dake maganar.

Ajiyan zuciya ya sauke ahankali tareda kai bakinsa ahankali yayi kissing lips dinta yace

“Farha zata zauna anan din to Amma ki kula kema,zanyi kwana biyu kafin na dawo”

Sake kissing lips dinta yayi tareda tayar da ita ya tashi tsaye ya mayar da ita kan gadon zaune ya rufe mata Rabin jikinta yace

“Akwai sanyi ki Saka kaya me nauyi”

Kallansa kawai tayi batareda ta amsa da komaiba harya gama gyara mata rufan ya sunkuyo ya shafi wuyanta yai kissing idanuwanta ya mata sallama ya juya ya fice daga Dakin ta kasa bin ko bayansa da kallo sbd mutuwan da jikinta yayi gaba Daya idanuwanta na Neman cikowa da hawaye sedai ta danne ta hanasu cikowan.

Yana fitowa Kai tsaye baima lura dasu mum Aisha Dake palon ba ya fice zuwa hanyar palonsa.

Husnah kasa motsawa tayi Dan batama San ya fito ya wuce din ba Saida mum Aisha cikin muguwar gayya tace

“Ga ASH din na se yanzu ya fito daga dakin bayan Abeeda na can Rai hannun Allah tana jiransa Yana Nan gurin yar cikinsa ko me yake faruwa ne oho”

Anty Farha batama San me suke fada ba Dan waya takeyi tinda ta dawo daga raka Dr beeba.

Tashi tayi ta nufi bedroom din ta shige.

Mum Aisha kuwa ajiyar zuciya da numfashi ta ringa saukewa a Jere na rashin sanin meyake faruwa duk da zuciyarta na ingizata ga zargin abinda ya faru din na kodai ASH ya Maida Amatun mace ne to Amma Kuma bazai taba yiyuwaba take gani sbd yaushe har ya fara kallan Amatun da zai mayar da ita matarsa bayan Amatun ma ko kallansa bata iyayi har yanxu ko yaushe Kai a qasa tsohuwar munafuka data gada a gun uwarta.

Miqewa tayi ta nufi hanyar sauka Dan maamah na buqatan farkawa daga baccin kwadayi da burin da takeyi akan ASH.

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa cikin qanqanin lokaci yayi wanka ya fito sanyeda qananun kayan Balenciaga da fcap hannunsa wayoyinsa ne kawai Se luggage dinsa me tsadan gaske.

Husnah data kasa zuwa ganinsa hawayene masu zafin gaske take dannewa suna komawa cikin idanuwanta suna soya zuciyarta.

Qin tasowa tayi duk da Kiran da yayi mata a waya tana kallo taqi dauka sbd kanta Dake juyawa har Kiran ya yanke.

Sake kiranta yayi Bata daukaba Daman a kaidansa Baya wuce kira Daya sai iyalinsa kawai yakewa biyu Dan haka Bai sake kira ba sai maamah Daya kira a wayar y sanar da ita ya wuce ta kula da Gidan,su kudi Daman ba matsala bane a gidan idan Jameel Baya Nan akwai me kawo kudi ko duk abinda ake buqata a gidan ASH TALBA din.

Kai tsaye su Mr Jameel Dake jiransa kaman masu naqudar tsaye tsoron su rasa flight dinsu ga Kuma ba Daman kiransa Dan haka suna ganinsa suka taso gaba dayansu da sauri.

Mr Jameel yayi saurin karban luggage dinsa Yana Bude masa mota driver ya Bude bayan motar ya Saka kayan ya dawo ya fada motar da sauri ya tayar aka wangale musu gate suka fice da sauri.

Suna fita text ya rubuta mata akan Shan magani da kulawa sosai ya tura ya kashe wayar gaba Daya Yana miqawa mr Jameel daya karba yana Satan kallan time ahankali.

*******Bayan ficewansa daga gidan Husnah kasa riquwa kukanta yayi sbd zuciyarta zata iya bugawa Dan haka ta fasa Wani irin kuka Mai ciwo da zafin zuciya batareda ta motsa daga inda take ba.

Mum Aisha da maamah Dake palon qasa mum Aisha na fadawa maamah maganganun da suke Neman buga zuciyarta sbd damuwa da tashin hankali suka ji fasa kukan Husnah wadda yau ne ranar farko dataji tana Dana sani da baqin cikin takurawa dad dinta ya dawo da maamah kota halin Yaya.

Saman suka hawo suna kallan Husnah din maamah cikin damuwa

Mum Aisha Kuma cikin takaici.

Jajir idanuwanta sukai ta dago tana kallan maamah din cikin kukan da batasan mema zata ce ba bayan kalman “Maamah mum dina ta tashi bayan shekaru Amma Dad haryana da lokacin batawa a gida sbd ciwon Amatun data kasa fadan gaskiyar me yake damunta”

Anty Farha data fito daki taji abinda Husnah ke fada ta katseta da cewa

“Meye ruwan maamah to a zancen tinda itama yanda kikaga yanada lokacin batawar itama haka take Gani,

Da nice ke Kai tsaye zanje na tambayesa tinda kaf gidan keda Matar gidan ne kuka Fi kusanci dashi akan kowa”””

Mum Aisha bakin Farha take kalla kaman zata fasa mata shi da kwalba Amma ASH ya daure mata itama tinda yar amanar Amatu ce.

Maamah data kasa cewa komai tanajin kukan Husnah da maganganunta har cikin ranta suna yankar zuciyarta Amma ta hadiye sbd Husnah kaman yanda Abeeda bazatai fushi da itaba haka itama bazatai fushi da Husnah ba tinda kaman Amatun take a ranta.

Mum Aisha Dake jin kaman ta tarwatsa gidan da bomb barin gurin tayi ta sauka ta wuce dakinta tana tsinewa masifar data shigo gidan.

Anty Farha ma barin gurin tayi ta sauka Dan kawowa Amatun abinda zataci da daddaren.

Maamah ma jiki ba qwari ta ringa rarrashin Husnah data ringa rokon maamah din ta Saka Amatu barin gidan gaba Daya ma kafin mum dinta ta dawo taji maganar auren ta sake komawa coma.

Wannan maganar ce tafi daga hankalin maamah Dan haka ta qudurtawa ranta ko Abeeda ta dawo bazata taba barin ta tarar da wannan auren ba.

Husnah Bata samu sassaucin abinda take ji ba Saida maamah ta tabbatar mata da Babu abinda zaisa ma Abeeda ta tarar da auren bare saninsa tukuna ta samu Kanta ta silala ta shige daki kanta na juyawa kaman zata zauce takeji depression dinta na Neman tashi.

Maamah kuwa daurewa tayi ta shiga dakin Amatun dubata tana kasa kallan Amatun

Itama Amatun kallo daya tayiwa maamah jikinta yayi tsananin sanyi sbd karanto damuwa me girman gaske a tareda ita.

Zaman shirun sukai a dakin sai sama sama maamah din ke Dan magana

Ganin Farha da Kuma yanayin jikinta ya Sanyata barin maganarta kafin Amatun ta samu sauki Kuma farha ta tafi tukuna.

Har qarfe goma maamah na tareda Amatun da Farha Kuma ko da wasa Babu abinda sukai Daya Saka maamah zargin ciwon Amatun.

Ko da zata tafi dakinta Farha ce ta rakota Amatun Bata tashi daga inda take ba sai bayan ficewan Maamah din anty Farha ta kamata ta sake Dan shiga ruwa tayi wanka tai Shirin bacci ta kwanta cikin kayan bacci masu kauri.

Washe gari ko data tashi jikinta ya Dan sake samun karfi da sauki Dan haka ta daure tana nuna samun saukinta ahankali ahankali sbd kada maamah Taga abin yayi yawa.

Anty Farha ce ta tsaya take kulawa da ita sosai hakama suna iya kokarin Hana maamah fahimtar komai musamman yanzu da mum Aisha da Husnah suka qarasa gurbata tinaninta gaba Daya akan auren tsana take masa me nauyi Dan har cikin ranta tafison ‘yarta ta koma bazawara da Abeeda ta dawo ta tarar da wannan auren.

Husnah kwana biyu da tafiyar Dad din nata tabi jirgi ta tafiyarta porthcrt Dan ganin Amatu a yanzu Kawai suqar da ita takeyi Dan kuwa kishinta takeyi ta ko wanne bangaren,

Bangaren Taya mum dinta kishin Dad dinta me zafi,dakuma kishi da baqin cikin haryanxu Faisal Bai cire Amatun daga Rai ba Wanda ke Sakata shiga wasi wasin kada Amatun ta fito hannun Dad dinta Wani bangaren sbd tana fitowa Allah ne kawai ze Hana Faisal aurenta ga Haydar ta riga ta haramta garesa tinda ta auri Dad din bare ta fito a aura masa ita maimakon  Faisal.

Bayan tafiyar Husnah damuwa me tsanani maamah ta sake shiga sbd qarara a Fili sbd Amatu Husnah tabar gidan ta bangaren Daya Kuma sunyi magana da ASH dai Abeeda ta farfado Daram Amma Bata iya ko magana kusan komai nata Baya aiki yi mata komai akeyi.

Anty Farha ce kawai hankalinta kwance cikin rashin damuwa take kulawa sosai da Amatu wadda itama kusan cikin damuwar take sosai na yanda maamah ta sauya mata gaba Daya da Kuma yanda komai yake Neman juyewa a rayuwarta,

Taji sauki sosai ta warke Amma Bata cikin kuzarinta sbd damuwa duk da ta rasa Menene ma abinda yake Sakata damuwan bayan sauyin data samu daga mahaifiyarta,

Koyaushe ya kirata a waya Bata iya dauka Dan ta rasa tayaya zata iya magana dashi a lokacinda yake can din,

Rashin daukan wayarsa ya Sanya sedai yayi mata text kullum da dare.

Mum Aisha zaune take gaban Naufal Daya shiga shock na Jin tashin Madame abeeda ya Kalli mum dinsa da jajayen idanuwansa zuciyarsa na radadi yace

“ASH zai dawo da ita ne?

Kallansa mum Aisha tayi tana cewa

“Ta farfado me zata zauna acan tayi mijinta na Nan Yana rayuwarsa da sa’ar ‘yarsa”

Fadan kalman yarsa da tai ya Saka Naufal Jin zafin zuciyarsa ya qaru yace

“Yar Dan uwansa dai Dan da ‘yarsa daya Haifa da cikinsa ce bazata kirani ta turani zuwa ga matarsa ba gashinan Ashe tarko ta nada min Dan su……

Kallan da mum Aisha take masa ne ruwan datake sha suna kokarin biyowa ta hancinta ya sanyashi yin shiru kada ta mutu ya shige uku baida me tsaya masa.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

53

***************

Daqyar ruwan ya wuce ta maqoshinta kaman ta hadiye garwashi haka ta jisu tana kallansa idanuwa a wahale zatai magana ya dakatar da ita da cewa

“Mum ki nutsu fa karki halaka akan wainnan mutanen da Babu Wanda zai Gani da kyau”

Kallansa tayi sauran ruwan na qarasa dawowa ta hancinta

Shine ya zari tissue Yana goge mata ahankali zuciyarsa na tafasa tana zuba quna zaiyi magana mum din ta taresa da cewa

“Meye ne kake fada Naufal?

Me nake ji?

Ni bangane ba kamun bayani kafin na taka dungun qafar taka ka qarasa”

Jifar da tissue din hannunsa yayi Yana kallanta Shima ciwon ransa na dawowa sabo yace

“Mum kinaji fa nace Miki wannan tsinanniyar sauran haukar Husnah ce ta nadan tarkon zuwa mansion din fa,

Itace ta kira ne,

Sako ta turan akan naje mansion din ba kowa,

Dana ga sakonta sharesa nayi ban kulaba Amma ta sake Kirana ta Kuma sake kira…

Dan shiru yayi,

Mum da zuciyarta ta kawo maqoshinta kallan baqin ciki da zafi tana jiran sauran zancen a kufule da siqewa tace

“Kai Kuma mayen da maitarsa Bata kwantawa akan Amatun ta kwashi shegun qafafunka kaje ko???

Hade fuska yayi ransa na sake daukan zafi da radadi yace

“Daman akwai sauran abubuwana danake son dauka a mansion din Jin Hakan su naje dauka bawai Dan Amatun kadai ba sai gashi wannan tsinanniyar yarinyar tasa ASH yamun wannan rashin imanin”

Kasa magana mum Aisha tayi tana kallansa idanuwanta jajir kaman zasu koma cikin kanta tsaban bacin Rai

A kufule ta dauki roban ruwan data gama sha ta jefa masa a Kai hannuwanta suna rawan bacin Rai da baqin ciki me girman gaske data rasa Yaya zatai dashi,

Abu biyu take tsananin muradi a yanxu shine fasa kan Naufal din Taga idan jini zai fito ta samu tabbatarda kan mutane da qwaqwalwan mutane ne dashi Bata karfe ba,sai Kuma Husnah da zata buga kanta da stairs na gidan ubanta ta fada mata ASH din datake tayar da hankalin mutane akansa bama Ubanta bane qanin ubanta ne Kuma Mijin uwarta ko gadonsa batada shegiya me tabin hankali ‘yar gawa taqi Rami.

Kafin Taga Husnah Naufal din dayake gabanta zata fara cin ubansa taji toshewan kan data samesa da zai bi maganar Husnah sbd idonsa ya rife da kwadayin farar fatar Amatu.

Kallan mum din yayi lokacinda robar ruwan ta sauka kansa da zafi ya taba kansa Yana sake dawo da kallansa kan mum din tasa zaiyi magana cikin kunyar da baimasan yanada itama ta katsesa da cewa

“Ni kaddarata ta haihuwa acikin zuriar masu tosashen Kai ce,

Babu abinda yake cikin kanka daga mata Se mata,

Dana San haka zaka zama da a hannun ubanka zan barka ka tashi acan sai nasan baqin cikin labarin lalacewanka kawai zan riqa ji batareda nagani ba baqin cikin yamun yawa,

Uban meye ne Amatun take dashi da ka nace ka rufe ido da tosashiyar qwaqwalwanka harka qare da qafa Daya duk akan macen da gata Nan kanajin kana gani Se Hange shi Wanda ya rabaka da qafar Daya Ya mallaketa,

Duk wannan rashin hakurin naka da masifaffen kwadayin matan ya Saka Amatu ta samu Isa ga Daman zama ASH din,

Da ka hadiye kwadayinka da duk bamu zo Nan inda muke ba aynzu……

“Mum wlh yaudarata Husnah tayi nikuma kaya zan dauka a mansion din,wlh Bazan barta ba Husnah din ai……

“Kamun shiru da toshewan basirarka ka barni naji da komai,

Husnah dinma tafika hankali da tinani tinda har tasan ta inda zata cutatar da wadda bataso,

Kai kuwa idonka ya rufe maimakon data tura maka sakon ka tattara komai ka kaiwa ASH ka nuna masa Dan dawo da yardarsa gurinka ya yafe Maka akan abinda ya faru Baya Amma Se Kawai ka kwashi qafafunka kaje lalata masa mata ko? Ta barka da Arziki ka raso qafa Daya gurin rashin danganarka”

Shiru yayi maganganun mum Aisha din na cin zuciyarsa suna qara masa damuwa da baqin ciki me qarfi.

Katse shirunsa tayi da cewa

“Karka kuskura naji kayi Wani abun akan kowa,

Kabarni Daya bayan Daya kowa zaisan ya tabani, Husnah zatasan da was takeyi Dan ko uwarta nafi qarfin iskancinta bare ita,ba ta iya Kai labarin Azo ASH Baya gida ba?itama nata labarin zata samu bayan na fasa bakinta da kanta”

Sai alokacin ya sake dagowa ya Kalli mum din Yana Dan Jin sanyi a ransa Dan yasan ba sauki Husnah zata gurbi abinda tai masa.

Kasa zama tayi asibitin ta tattaro ta dawo gida Dan zuciyarta tafasan datakeyi ko Naufal din zata iya rufewa da duka duk girmansa da jinyar dayake kuwa sbd abinda takeci ya wuce bacin Rai tafasan zuciya takeyi.

Ko data dawo gida Babu ma Wanda yasan ta dawo bayan su khaltume ta shige bedroom dinta tana Ciro wayarta numbern Husnah ta Nemo ta danna mata kira zuciyarta na tsalle Dan kuwa da Husnah na gidan ayau da wlh sedai ASH ya Tararda Rabin Husnah din badai cikakkiyar ta ba Kuma ta fada masa abinda zai Sakasa yiwa shegiya auren Sadaka da duk Wanda ya samu.

Husnah na ganin Kiran mum Aisha taji gabanta ya Dan Fadi kaman bazata dauka ba sai kuka ta daure ta dauka cikin rashin son magana sosai.

Ko gaisuwarta mum Aisha Bata amsa ba tace

“Ki tattara komai naki ki dawo Abuja kafin ASH ya dawo Dan idan ya Riga ki dawowa shine zai fara Jin abinda kikai na turawa Amatu Naufal Dan ya la…….

Tashi zaune Husnah tayi da sauri daga kwancen datake tana satar kallan su mummyn porthcrt Dake tareda ita kafin ta miqe ta nufi bedroom ta shige tareda tura kofar tana cewa

“Mum Aisha ni Kuma?

Ni bangane me kike nufi ba?

Wane Uncle Naufal din?

Tsoki mara sauti mum Aisha ta sake tareda cewa

“Ki zauna porthcrt jiran bayani har ASH ya rigaki dawowa kisha mamakina”…kashe wayarta tayi tareda jefar da wayar Dan kuwa saita Maida Husnah abin tausayi da wannan maganar da ita zatai amfani ta juya kusan kowa a gidan yanda takeso.

*********

AmatulMaleek kuwa jikinta ya sake warwarewa kaman ma Bata taba yimata komaiba harda dinki Dan haka ta koma zuwa school Kuma ta Dan sakewarta sbd anty Farha na gidan Sam Bata barinta shiga damuwa ko tinanin dayake sanyaya jikinta duk da ta fahimci sosai maamah ta sauyawa Amatun takuma San dalilinta Dan kusan yanzu itace sirrin Amatun da maamah Dan ita kanta maamah din zuwa yanzu dole ta yarda Farha na kaunar Amatu da gaske haka Kuma hankalinta ya kwanta da alaqarsu sedai Sam taqi yarda da duk wata nasiha ko maganar da Farha ke Mata akan auren Amatun qarshe ma doka da rantsuwa tayi akan kar a sake Mata maganar duk da Amatu batama San anty Farha na kokarin yiwa maamah nasiha akan lamarin ba.

Ganin yanda Farha ta dauki auren Amatun da mahimmanci sai ta sauya mata kwata kwata ko fuska ta Dena sake mata Kuma daga Farha din har Amatun sun fahimci sauyin maamah din sai jikin Amatun yayi sanyi ta sake shiga damuwa.

Duk zata school tare suke fita da anty Farha su ajeta spa dinta su wuce idan sun dawo saisu biyo su dauketa su dawo gida.

A kwanakin duk da tana cikin damuwan maamah wasu lokutan Hakan Bai Hana hutun datake samu bayyana ba ga Kuma kulawa sosai da anty Farha ke Bata,

Komai nata ya sake upgrading zuwa babban matsayi Dan komai nata kusan an sauya ya sake zuwa babba,

Designer ne take bugu yanda ya kamata,kudinsu maamah Bata saniba da sai ta kusan kwanciya asibiti sbd damuwa,ita kanta Amatun bawai kudaden da ake kashe mata din ta saniba komai haka ake kawowa anty Farha ta jerasu inda ya kamata komai ya zauna.

Har wannan lokacin tinda ya tafi basuyi magana ba Dan batama kunna wayarta Se dare Kokuma idan zatai magana dasu Abdul ko Haydar Dake cikin farin cikin tashin mahaifiyarsa.

Tana kunnawa zataga text dinsa zata karanta ta rubuta masa lafiyanta kalau da thank you kawai ta sake kashe wayar.

A zuciyarta Babu ranar da tinaninsa Baya azabtar da ita Amma Kuma tana Jin jikinta na sanyi tareda mutuwa tinawa da a gurin matarsa dayake tsananin so ya tafi Dan murna da farin cikin son kasancewa da ita.

Ita kanta anty Farha Bata damu da rashin son kunna wayan da Amatun keyi Dan haka suka share suna abubuwan Dake gabansu kawai.

A wannan gabar maamah tafara matsuwa da Farha ta tafi sbd ta samu cikakkiyar Daman magana da Amatun akan abinda takeso tai mata magana kafin ASH ya dawo.

*****Husnah a porthcrt ta shiga tsananin tsoro da firgicin maganar mum Aisha Dan haka ta tattara zat dawo Amma su mommyn can din suka hanata dawowa Dan haka hankalinta yayi mummunan tashi Amma ba Daman fadan abinda yasa takeson komawan,

Tayita Kiran numbern mum Aisha Amma Bata dauka idan kira 100 zatai mata,

Hankalinta Bai tashiba tafara Neman haukacewa sai datai magana da Dad dinta taji a satin ze dawo Dan haka ta tattara ta Siya ticket sedai su mummyn suka wayi gari ta gudu Abuja Dan kuwa hankalinta ma Baya jikinta idan ba Isa tayi Abujan ba.

Ko data iso gidan ba kowa Se maamah da masu aiki Dan haka ko zama batai ba ta sake kiran mum Aisha Amma Bata dauka ba Dan haka ta zauna bakin gadonta jikinta na rawa ta tura mata sakon cewan ko dawo tana gida.

Tafiyar sakon befi da mintina biyu ba mum Aisha Tayo mata reply da sunan asibitin da suke.

Kallan sakon tayi a karo na babu adadi tana tinanin mezataje tayi acan din.

Shiru tayi tana Jin zuciyarta na shiga damuwa da tsoron maganar ta Isa kunnen Dad din duk da tasan bazai iya fushi da ita ba ko mata Wani hukuncin akan Amatu da ba ‘yarsa ba Amma Kuma batason yaji sbd Haydar ze tsaneta, Haydar ze iya fushi da ita Yama shareta.

Miqewa tayi tana daukan wayarta kawai Se qaramar chain handbag ta nufi kofa ta fito ta sauka ta fice batareda Maamah ma tasan ficewanta ba.

Da kanta ta karbi key taja motan sbd Bata buqatan kowa da zai iya ji Ko da tsautsayi cewan tanada Saka hannu a cikin maganar fyaden Amatu.

Tana ficewa mansion din su Amatu motansu na shigowa Amma Sam Batama lura dasu ba kaman yanda Suma Basu dauka itace ta dawo harta fita dinba.

###MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

54

************

Ko data Isa asibitin room number din dake tareda sunan asibitin cikin text din mum Aisha ta nufa gabanta na Dan faduwa tana Kuma fatan mum Aisha dince tayi hadarin motan da bama zata iya magana ba bare fadawa Dad dinta abinda takeson fadan.

Tana tsayawa kofan dakin Kai tsaye knocking tayi tareda Bude kofan dakin ta tura ta shiga idanuwanta na fara sauka kan Naufal Dake zaune Shima kofan yake kalla idanuwansa jajir da zafin zuciya da baqin cikin ganinta kaman zai tashi ya raba da ranta yakeji.

Rawa hannuwanta suka fara ta shigo tareda rufe kofar tana kallan Naufal jikinta na sake daukan rawan tashin hankalin ganinsa da qafa Daya.

Tsoro ne me qarfin gaske ya kamata ganin qafarsa Daya yanda take din Dan haka tayi saurin juyawa bazata iya kalla ba tsoro me tsananin gaske takeji Dan bata Saba ganin irin wannan tashin hankalinba.

Damqota mum Aisha tayi cikin zafin Rai tareda dawo da ita ta jefata gadon Naufal din gurin qafar Dan ta Gani da kyau.

Hawaye Husnah tafara jikin na sake daukan rawa sosai hakama bugun zuciyarta na tsananta har cikin zuciyarta tsoron ganin qafar takeyi hankalinta ya tashi sosai har ta kasa magana sai cewa tayi

“Mum Aisha banason Gani Ina tsoron ganin qafar uncle Naufal,tsoro nakeji banson Gani,Ina qafarsa Daya take Dan Allah karki…….

Cikin zafinta daya kasa dannuwa da tsananin bacin Rai Mai hade da baqin ciki mum Aisha ta falla mata Wani gigitaccen Marin Daya Saka Husnah fadawa kan qafar Naufal din jikinta na rawa tayi saurin janyewa daga qafar a rikice da azabar Marin sedai kafin ta qarasa janyewa mum Aisha ta sake dafe kanta a gurin kafar tana cewa

“Ki Kalli qafar da kyau yanda tsoro ze juyar Miki da qaramar qwaqwalwanki kafin ki fuskanci hukuncin abinda kikai daga Wanda ya Yanke masa qafa akan abinda kece kika haddasa komai”

Rawar masifaffen tashin hankali da firgici jikin Husnah ya dauka tana hawaye tana rintse idanuwanta daga kallan dungun qafar Naufal din dake fuskarta ta fashe da Wani irin kuka tana cewa

“Mum Aisha Dan Allah kiyi hakuri wlh zan Suma idan Ina ganin wannan qafar Dan Allah ki barni na tafi gida”

Cikin baqin ciki da takaici Naufal ya motsa qafar ya tura mata a fuska Yana buge bakinta da dungun duk da Yana Dan Jin zafi Amma baqin ciki ya hanasa Jin zafin sosai.

Kuka sosai Husnah keyi tana Neman shaqewa kafin mum Aisha ta dagota ta zubar qasa tana kallanta cikin zafin zuciya tace

“Yanda kika ga ya rasa qafarsa Daya akan abinda yayi to idan ASH din yaji kece kika turasa me kike tinanin ze Miki?

Kinsan ASH ne da kansa ya yankewa Naufal din kafa akan zuwansa mansion gurin Amatu kawai,

To idan shi ya Yanke kafarsa Dan yaje mata ke da kika aikasa kika ringa kiransa kina cewa yaje gidan me zaayi Miki?

Ke harma rigimar farko ta zuwan Naufal din dakinsu Amatun kece kikai mixing drink dinsa ma Dan yajewa Amatun……..

Cikin masifaffen tashin hankali Husnah ta dago jajayen idanuwanta ta Kalli mum din muryanta na rawa tace

“Wallahi tallahi banyi Hakan ba,ba nice ba,ban…..

“Kece kikasan ba kece ba mu bamu San Hakanba, ASH ma baisan Hakan ba…”

Rawa jikinta ya sake dauka hawayenta na qafewa tace

“Mum Aisha wlh banyi Hakan ba, Dad dina ba bazai taba yarda da zanyi Hakan ba,

Wannan na bayan ne kawai nasan na cewa uncle Naufal din yaje mansion ba kowa Se Amatun ya mata abinda yakeso….

Muryarta taji tana maimaita abinda ta fada yanzu a wayar Naufal din yayi playing recording din maganar tata.

Juyowa tayi ta kallesa idanuwanta na sake cikowa da wasu hawayen jikinta na mutuwa gaba Daya,

Kan mum Aisha ta dawo da kallanta hawayenta na saukowa ta Bude Baki a sanyaye tace

“Mum Aisha Dad dina bazai yarda da na aikata Hakanba,

Dad dina bazai iya yanka qafana ba kaman na uncle Naufal,

Dad dina bazai iya ko ganin bacin Rai na na bare yanka qafana….

Katseta mum Aisha din tayi da cewa

“Idan shine ya haifeki ba,

Idan shine ya haifeki daga tsatsonsa shine bazai iya Miki Hakan ba Amma tinda mijin uwarki ne kawai Kuma qanin mahaifinki mezai Hanasa ko aurar dake ga Daya daga cikin securities dinsa idan har bazai iya yanka qafarki ba bayan kin tura namiji yayiwa matarsa fyade,matarma wadda yakeso fiyeda Taki uwar Daya rufe babinta a rayuwarsa…….

Zuru Husnah tayi tana kallan mum Aisha da idanuwanta batareda ta fahimci Kalma ko Daya datake fada ba daga kalmominta na farko dasuka shiga kunnuwanta.

Naufal ne ya miqa hannu ya jijjigata daga zaunen dayake Yana cewa

“Abinda ake nufi ana shine ba ASH ne Wanda ya haifeki ba auran mamanki yayi dake a hannunta Dan rufa muku asiri ya Baki sunansa….””

Bata gane abinda suke fada ahankali taji jinta na daukewa bakinsu kawai take ganin suna motsawa suna fadan maganganun da Sam batajin komai.

Maimaita mata kalmomin suka ringa yi Daya bayan Daya har sai da jinta ya dawo zantukan suka ringa shiga kunnuwanta suna ratsasu zuwa cikin kanta,

Maimakon su Isa ga zuciyarta cikin kanta suke wucewa suna juya kan ahankali.

Zubewa tayi qasa take Neman yi mum Aisha ta tareda tareda kama hannunta kaman makauniyar da akewa jagora.

Harabar asibitin ta fito da ita Babu mutane sosai kowa abinda yake gabansa yakeyi.

Motarta ta Bude tareda kamata ta shigar da ita ta zaunar a mazaunin driver tareda saka key ta tada motar ta kama hannunta ta Dora mata kan steering ta kalleta tace

“Kije gida”

Rufe mata kofar motar tayi tareda juyawa ta koma ciki Dan tasan Babu yanda Husnah din zata iya Kai kanta gida a wannan halin itama yau zata dandani abinda ake nufi da azaban hadarin data saka Naufal a ciki ya rasa qafa ita Kuma kila ran zata rasa gaba Daya.

Tana juyawa Husnah taja motar a cikin mummunan gudun Daya Saka securities din asibitin tareta suka hanata fita sbd tsaro suka hau bincike motarta tana zaune kaman wadda Babu komai a tareda da ita bayan numfashin datake shaqanta kaman tana shaqan gas take ji sbd ficewa hayyaci.

Suna gamawa suka hanata fita Saida ta Dan dawo hayyacinta suka Bude mata gate ta ja motar cikin Wani irin tsananin gudun gaske me qarfi ta hau titi ko ganin gabanta Batayi sosai.

Ko data Isa mansion din TALBAs ganinta yafara qaranci sosai Dan haka   parking dinma Bata qarasaba ta fito motar tana hada hanya ta nufi cikin gidan.

Step din farko na stairs data Dora kafarta zata hau Sam sakon Naufal ya shigo wayarta Wanda yasata dubawa da idanuwanta Bata Gani sosai.

“Idan har kin samu Isa lafiya karki manta wadda ta fada Miki waye babanki itace takeda abin fadawa ASH TALBA abinda ya samu matarsa waye sanadi”

Qurawa sakon idanuwanta tayi hannuwanta na rawa sosai sbd idan ta fahimci abinda suke nufi shine idan ta fada Wanda ya fada mata ita ba yar ASH bace zasu fada masa abinda tayi.

Da dafa Bango ta Isa palon saman seda zuciyarta Dake kokarin bugawa ta kasa riqe abinda takeson riqewa ta Isa dakinta ba shiri Bata saniba ta zube tsakiyan palon tareda fasa Wani irin ihun Dayake dauke da tsananin girman baqin cikin da zuciyarta ke Neman fashewa akansa…

Gaba Daya mansion din sautin ihun nata ya dauka Wanda ya Saka kowa fitowa hankali tashe musamman Amatu da anty Farha da bedroom din Amatun yake palon sosai ihun yafi shiga kunnuwansu.

Maamah ma dasu khaltume duk a rikice sukayo saman sedai Koda kowa ya iso Husnah din ta sume a gurin hawayen Dake cikin idanuwanta suna gangarowa Babu abinda yake motsi nata.

Amatu ce tayi kanta cikin kulawa ta fara tabata tana ambatar sunanta cikin fargaban abinda ya sameta.

Maamah dasu khaltume kuwa harma da anty Farha Babu abinda yazo ransu Se Madame abeeda lokaci yayi ta cika kawai Dan haka kowa jikinsa ya dauki bari musamman maamah dataji zuciyarta na Neman tsayawa daga aiki tayi Baya Amatu ta miqe da sauri ta tareta tana kiranta a tsorace cikin damuwa da tsananin kulawa.

Zaunar da maamh din tayi su Kuma su khaltume suka kama Husnah din itama suka Kai kan kujera tareda debo ruwa suna zuba make Amma Sam ko motsawa Batayi.

Rawa jikin maamah ya sake dauka ta miqe da kanta ta karbi ruwan tana zubawa Husnah din Amma Sam Babu alaman zaa sameta.

Farha ce cikin tashin hankali ta dauko wayarta ta kira likita Amma Sam Bata shiga dan haka kawai suka kwasheta zuwa asibiti.

Maamah da Husnah dinne a Baya anty Farha na gaba Amatu ke driving sbd Basu tsaya cewa driver yakaisu ba.

Asibitin da suke zuwa aka nufa da ita suna Isa aka amsheta da gaggawa sbd kusan lamarin ya sake tsananta Dan numfashinta ma ya tsaya cak.

Maamah ma kusan dole suka buqaci likita ya dubata Dan kuwa itama zubewan take Neman yi Dan itama Amatun zuwa lokacin ta saddaqar da cewan Wani abu ya samu Madame abeeda ne.

Bayan an duba maamah itama an Bata gado ta huta na awanni hakama Husnah gadon aka Bata

Shiru Amatu tayi sai alokacin jikinta yayi sanyi da damuwan halinda ASH yake ciki idan Wani abin ne ya samu Madame abeeda.

Numfashi ta sauke ahankali tana kallan wayar anty Farha dake hannunta tanajin tanason Jin muryarsa Dan sanyaya damuwansa sedai zataso da tata wayar zata kirasa Dan haka ta danne abinda take ji a zuciyarta idan ta koma gida ta kirasa.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

55

************

Zaman rashin Madafa sukai a asibitin har kusan 12 na dare kafin aka Husnah ta dawo daidai aka sallamesu suka dawo gida Babu me magana sbd yanda Husnah din take kaman wadda tayi gamo komai batace ba Idanuwanta sunyi jajir Bata iya cewa komai sai hawayen dake ciko idanuwanta tana hadiyewa hakama zuciyarta kaman zata qone take ji,

Zafi take ji,radadi take ji,qunci me girman gaske take ji hakama damuwa da ciwon zuciya takeji duk lokaci Daya.

Har suka iso gida maamah ce kawai take Dan tambayarta abinda ta sameta Amma Sam taqi magana Dan tana Bude Baki kuka zata iya fasawa me gigitarwa Dan haka ta zabi yin shiru Dan kada kanta ya juye.

Farha ce ta tuqo su a dawowa gida Dan haka tana parking Amatu ta fito jiki a mace ta budewa maamah kofa zata kamota Amma maamah din Husnah take kamowa Dan taimaka mata ta fito.

Tsayawa tayi jiki a mace tana kallo maamah din ta fito ta kama hannun Husnah kaman mara laka ta jata suka wuce gaba.

Numfashi me sanyi ta sauke kafin ta daga nata kafafun itada anty Farha sukayo ciki Suma.

Dayake hankalinsu khaltume Baya kwance da abinda ya farun basuyi bacci ba kowa na zaune Yana jiran tsammanin abinda yake faruwa na madame Abeeda har Husnah din,mum Aisha ce kawai a bedroom dinta hankalinta kwance tana baccinta Babu abinda ya dameta duk da taji abinda ya samu Husnah din a bakin khaltume.

Ganinsu ya Saka su khaltume Jin yar nutsuwa suna yiwa Husnah din sannu har suka Haye sama itada Maamah,

Shigowan Amatu da anty Farha ya Saka su dawo da kallansu kansu Suma suna musu barka da dawowa.

Kallan khaltume anty Farha tayi tace

“A hadowa Amatu abinda zata ci akawo daki tareda ruwan zafi ta Dan sha”

Gyada Kai khaltume tayi tana juyawa Dan ganin abinda zaa hada akaiwa Amatun wadda ta Haye batareda ta tsaya ba jiki a mace.

Maamah dakin Husnah suka shige tana sake kulawa da Husnah din wadda hawaye suka tsinke mata masu radadi suna sauka har gaban Rigarta batareda ta iya Bude bakinta har lokacin sbd bazata iya fadan abinda yake tafasa zuciyarta Yana tarwatsetaba.

Zaunawa maamah tayi tana rungumota kadan cikin kulawa da tausawa

Husnah dinma kwantawa tayi jikin maamah din tana sake fasa kuka me qarfin gaske mara sauti jikinta na Wani irin jijjiga.

Maamah sake rudewa tayi tana rarrashinta tareda dena tambayarta abinda ya faru fahimtar shine ke sake gigitata.

AmatulMaleek kuwa tana shiga dakinta toilet ta wuce Kai tsaye Tayo wanka da alwala ta fito.

Sallan ishai tafara yi kafin tana gamawa tayi Shirin bacci sai alokacin ta janyo wayarta ta kunna tana zaunawa bakin gado lokacin anty Farha na toilet.

Time tafara kalla kafin ta Nemo numbernsa ta tsaya tana kalla gabanta na faduwa jikinta na mutuwa da sanyi ta Saka kiransa a Karan farko na rayuwarta.

Acan bangarensa zaune yake gaban Abeeda a lokacin ana sake gasa mata qashin hannuwanta da qafafunta sbd su dan fara motsawa tinda dai ta Farka Kuma daidai gwargwado da sauki ta farfado Dan kuwa rashin motsawan ne kawai Se Cancer dinta da shima Yana Nan Amma dai saukin yafara shigowa na samun qwarin gwiwan kuzari Wanda ganin mijinta ne ya Sanyata Jin tanason yaqan ciwon ta samu kuzari da Dan qarfin komawa ga ahalinta.

Wayarsa Dake hannun Mr Jameel ce tafara vibrating na shigowan Kiran Amatu Wanda ya Saka Mr Jameel Dan hadiye yawun mamaki Dan kuwa duk da ASH be fadaba Bai Kuma nuna ba yasan yana cikin yanayi na rashin Jinta dannewa yayi sbd bawa madame Abeeda tata lokacin nasa.

Kasa barin Kiran ya yanke yayi Dan haka ya Dan qaraso jikin kofar dakin yayi knocking ahankali.

Dayake angama har an rufe gaba Daya jikin Abeeda din sai nurses da zasu fice suka Bude kofan dakin tareda ficewa shikuma ya Dan shigo a hankali ya sake kallan Madame Abeeda da idanuwanta ne Kawai suke kallansa da kulawa sosai ya sake mata ya jiki.

Matsowa kadan yayi gurin ASH din da girmamawa yace

“Kanada call”

Kallan wayar da aka miqo masa din yayi yaga kalmomin L.A a rubuce Wanda yake nufin little Abeedah.

Hannu ya miqa ahankali tareda karban wayar Yana miqewa a natse ya San dafa hannun Abeeda ahankali cikin kulawa yana kallan ciki idanuwanta da sauti me sanyi yace

“Zan amsa kira zan dawo”  ya nufi kofa kafin ya Isa Mr Jameel yayi saurin Bude masa ya fice Shima ya fice tareda Jan kofar dakin.

Kiran tini ya Yanke Dan haka Kai tsaye txt ya tura mata akan zai kirata.

Dawowa yayi aka qarasa abinda zaayi na ranar ya wuce masaukinsa

Ko bayan Daya Isa wanka Shima ya sake yi ya zauna a natse ya sake Saka Kiran wayarta Amma tini ta kashe wayarta ta kwanta jiki ba qarfi.

Washe gari haka ya sake Saka Kiran Amma wayar a kashe hakama anty Farha Bata tareda ita tana spa ita Kuma tana school Dan haka kwata kwata Bai samu ji daga gareta ba.

Zuwa lokacin nutsuwarsa gaba Daya ta tashi daga kansa daurewa kawai yakeyi Amma kusan duk notin Kwanciyan hankalinsa sun kunce Mr Jameel ne kawai yasan Hakan Dan haka ya shirya tsaf umarni kawai yake jira ya Siya musu tickets din dawowa tinda madame Abeeda dai sedai ace alhmdlh ba laifi komai Normal ne.

***Husnah kwana biyu ta gama komawa kalan tausayi tausayi takaici takaici sbd ta gama ruda maamah ta daga mata hankali gaba Daya akan komai Daya danganci ASH da Amatu da Kuma mahaifiyarta sbd ta rasa ta inda zata fara ihu tana cewa Ashe ba ASH ne Dad dinta ba sbd tsoron abinda su mum Aisha zasu iya fadawa Dad din idan ya dawo dakuma firgita da abinda yayiwa Naufal akan lamarin fyaden Amatu tana tsoron itama abinda zai mata sbd laifinta babba ne.

Amatu data shiga damuwan ganin halinda Husnah ta jefa maamah na damuwa da kunci rokon maamah ta ringa yi akan ta cirewa kanta damuwa madame Abeeda na Nan lafiya kalau hakama Babu abinda zai faru inshallah.

Anty Farha dataga maamah na Neman Saka Amatun cikin tsaka me wuyar damuwa sai kawai ta tattara Amatun suke koma gidanta itama maamah din sai Bata Hana ba sbd ganin Amatun na sake rikita yanayin Husnah.

Komawanta gidan anty Farha itama shine natsuwan data samu gashi sun Dan samu break daga school Dan haka ta sake ta samu hankalinta ya kwanta.

Kwanansu biyu a gidan anty Farha ta Siya musu ticket suka wuce Lagos bayan anty Farha ta sanar da maamah din bikin auren qanwarta da suke uwa Daya Uba Daya zaayi,

Har cikin Rai maamah taji dadin tafiyan tasu Dan haka ta amince sbd a ranar suke tsammanin dawowan ASH gidan gwara Amatu ta tafi kawai har bayan kwana biyu.

Jirgin yamma suka bi Dan haka Koda suka Isa anyi magrib

Anty Farha ce a gaba sbd sanin zaa daukansu.

Amatun tana gefen anty Farha din sanye cikin doguwar Riga mara Fadi kusan daidai shape dinta me kyau kanta nade da mayafi mara nauyi,

 handbag dinta me shegiyar tsada ce kawai a hannunta sai wayarta

Hasken fuskanta me kyau da fresh ne kawai yake daukan idon Wanda ya kalleta.

Mr Jameel ne yazo daukansu airport Wanda ya Sakata cikin matsanancin mamakin Daya Saka gabanta faduwa jikinta gaba Daya na daukan sanyi lokaci Daya tana tabbatarda ASH Yana Lagos din kenan Kuma yasan da zuwansu.

Kasa cewa komai tayi bayan sanyin da jikinta ya qara lokacinda ta Bude Baki a natse ta gaisa da Mr Jameel din ta shiga mota batareda ta iya qara cewa komaiba.

Anty Farha ce ta shigo motar itama kafin Mr Jameel yashiga yaja suka bar airport din zuwa masaukin ASH da zasu ajiye Amatun su wuce inda ze Kai Farha nata masaukin itama gidan sister dinta.

Suna isowa shine ya Bude mata motar ta fito a hankali cikin nutsuwa har lokacin Bata iya cewa komaiba Se anty Farha datake kalla wadda ko a jikinta Dan itama hutun takeso daga pressure din gidan ASH TALBA da Bata qarewa Dan haka hutawa zatai a Lagos din sai ta kwana biyu.

Mr Jameel ne yake janye da luggage dinta ita da anty Farha na bayansa anty Farha na mata maganar da kwata kwata Bata fahimta sbd tinaninta da bugun zuciyarta dayayi Nisa da sauyawa.

Wata lafiyayyar luxury lodge ce Sukazo wadda take kusa da ruwa dan haka takeda sanyi a yanayinta.

Security da tsarin gurin kawai ze tabbatarda su waye da waye suka Kai matsayin zama gurin.

Babu hayaniya Dan haka har suka Isa dakin Babu motsi ko wulgawan kowa.

Mr Jameel ne ya Ciro card din hannunsa ya Bude dakin tareda juyowa ya miqawa Amatun card din ya tura mata luggage dinta ahankali zuwa cikin dakin.

Anty Farha ce ta Dan shafa fuskanta ahankali cikin kulawa tace

“Take care little Amah,sai munyi yawa”

A handkali tana Jin jikinta na sake mutuwa hakama zuciyarta na sake sauya dokawa ahankali ta shiga dakin Wanda yake suite ne na Wanda ko acikin masu kudin su masu kudin ne.

Tana shigewa Mr Jameel ne ya janyo kofar ya rufe tareda juyawa ya Kalli farha suna magana cikin murmushi suka bar gurin zuwa mota Dan itama yakaita.

AmatulMaleek kuwa tsayawa tayi a gurin ta tana kasa motsawa tsawon mintina komai Bata ganewa ma sosai sbd sanyin da jikinta yaketa sake yi.

A hankali ta daga qafafunta tareda nufar luxury sofas din Dake tsare a wadatacciyar tsararriyan palon,

Ko taku uku bataiba taji motsi a hanyar lungun da lafiyayyar gadon dakin take daga boye baa ganinta sbd cikin glass tsarin dakin turawan Russia.

Dakatawa tayi batareda ta juyoba sedai bugun zuciyarta dayake qaruwa ahankali ahankali sbd Jin takunsa Yana nufota Kai tsaye hakama qamshinsa dayake shiga hancinta bayan tsawon kwanaki.

Ahankali ya iso bayanta idanuwansa Dake cikin radadi da kasalan buqatan ganinta suna kallan bayanta Yana isowa taji hannuwansa ahankali suna zagayota ya rungumeta ta bayanta Yana lumshe fararen idanuwansa ahankali tareda sauke ajiyan zuciya me sanyi a bayyane.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

56

***************

Ita kanta ajiyan zuciyan ta sauke mara sauti tana rufe idanuwanta ahankali batareda ta motsa ba,

Saida yayi kusan mintina biyu a Hakan kafin ya juyo da ita ahankali ya  Bude idanuwansa ya zubawa fuskanta yanajin abinda baima San meye yake ji ba,

Kansa gaba Daya kuncewa yayi a kwanakin sbd rashin barin yaji muryarta ya raba hankali da nutsuwansa bangare bangare.

Yanda yake kallan nata batareda cewa komai ba cikik yanayinta tana jinsa a jikinta ya sanyata dago idanuwanta ahankali ta kallesa cikin yanayin daya Saka numfashinsa Neman yankewa Amma ya danne ya kanne Yana ci gaba da kallanta a natsatsen yanayi.

Ahankali ta Bude bakinta ta furta

“Ina wuni,barka da dawowa”

Wani sanyayyan ajiyan zuciyan ya sake saukewa tareda sake zagayota ya rungume cikin jikinsa kafin ya Bude Baki ahankali yace

“Meyasa kika Hanani jin lafiyanki?

Kinsan kin raba hankalina da Hakan?

Uhmmm kin San Hakan???

Girgiza Kai tayi ahankali tana yin qasa da idanuwanta

Dago fuskarta yayi ya kalleta Yana Jin zuciyarsa na sake kasa sukuni yace

“Amma kinsan Hakan is not right meyasa Zaki ringa kashe wayanki,kinason da dawo da wuri ne?

Dagowa tayi ta kallesa sbd abinda ya fada din Wanda ya Sanyata Jin Wani iri ta rasa amsar da zata basa gashi ya kafeta da Idanuwansa Yana mata kallan dayake tona asirin zuciyarsa.

Janyewa tayi ahankali daga jikinsa tana kaucewa kadan daga kallansa tana kawar da zancen da tambayar jikin Madame abeeda cikin kulawa da nutsuwa.

Shima amsawa yayi Yana zaunawa ahankali kan kujera tareda cigaba da kallanta Yana son karantar yanayinta Amma Sam taqi yarda da Hakan ta juya masa Baya tareda yin gaba ahankali tanason shigewa toilet sbd asirin zuciyarta ya kusa fallasa a gabansa.

Har ta wucesa ta shige toilet ahankali Bai dauke idanuwansa daga kanta ba cikin nutsuwa da sanyi yake bin komai nata da kallon nutsuwa.

Tana shiga toilet tsayawa tayi ahankali tana sauke boyayyan numfashi ahankali sbd ganinsa shine abinda Bata taba tsammata ba da zuwansu Lagos din.

Ta jima a toilet din kafin ta fito da alwalanta Dan yin sallah.

Baya dakin ya fice Dan haka sallah tazo tayi ta magrib,

Ko data gama lokacin ishai yayi Dan haka tayi sallanta ta ishai tayi addua ta miqe.

Karamar luggage dinta da kansa ya shigar mata da ita qurya,

Zaunawa take kokarin yi akai danna  ringing ta shigowa dakin mara qara sosai.

Kallan kofan tayi tareda nufanta ahankali tana budewa daga restaurant ne na cikin lodge din.

Abinci ne aka shigo dashi aka Jere kusan kala hudu Se snacks da gasashin wasu abubuwan aka Jere.

Juyawa sukai suka fice ita Kuma ta rufe ta wuce toilet Dan wanka sbd tanata son wankan Amma ta kasa.

Shigarta bathroom din brush tafara yi kafin tayi wanka ta fito daure da towel me Dan girma sbd nasa ne suna da girma.

Mai kawai ta shafa sama sama tareda turare kadan tanason ta saka kaya a jikinta kafin ya dawo.

Bra kawai ta Saka da underwear ya shigo cikin nutsuwa Yana amsa waya ahankali sedai Bai iya kallan inda take ba sbd zai iya loosing focus akan abinda yake tattaunawa.

Towel dinta na jikinta har lokacin Dan haka Riga da wandon bacci marasa tsayi da taushi kawai ta Saka ta nufi toilet ta mayar da towel din a hanger din dasuke Shan iska.

Tana fitowa Yana gama wayar ya taso daga inda yake zaune ya kama hannunta ya jata gurin abinci Yana cewa

“Yunwa Baya damunki ne?

Bata amsaba Saida suka zauna ta Kalli abincin sbd ba lallai akwai abinda zata iya ci ba aciki sbd batasan abinci me nauyi da dare.

Sake kiransa Kai a waya Kuma dole Yana buqatan daga Kiran Dan haka ya dauka Yana amsawa ahankali Yana Kuma tayata cin abincin datake ci cikin nutsuwa ahankali.

Brown chicken spaghetti ce takeci shikuma Yana amsa wayar Yana Dan share mata bakinta da tissue batareda ko a motsi wainda yake wayar dasu ba sun fahimci Wani abin yake yi daban.

Ko Daya gama wayar ta gama cin abincin Dan haka shima ahankali ya fara cin nasa tana kan qafafunsa har lokacin Yanaci Yana Dan tambayarta if she’s ok ko tana buqatan Wani abin.

A takaice tace Bata buqatan komai.

Harya gama tana kan qafafunsa Dan haka Yana gamawa itace dole itama ta goge masa bakinsa ahankali da tissue tana kallan dogon hancinsa me kyau da tsari.

Yanda take kallansa cikin tsananin son da zuciyarta ke masa da sanyi asirin zuciyarta na tonuwa ya sanyashi relaxing bayansa ahankali Yana Bata Daman kallansa yanda takeso batareda yayi abinda zai hanata Hakan ba.

Kan idanuwansa Dake kallanta ta Maida idanuwanta ta kallesu suna kashe dukkanin jiki da sonsa me qarfin gaske da batamasan yaushe ta samu kanta a cikinsa ba.

Gangarowa da idanuwanta tayi kan lips dinsa ta sake goge masa su da tissue ahankali tana dauke idanuwanta daga kan fuskar tasa tana miqewa daga jikinsa bugun zuciyarta na qaruwa.

Tana sauka jikinsa barin gurin tayi gaba Daya tanajin kallansa akanta harta shige.

Brush tashiga toilet Tayo ta fito,

Wayarta ta Ciro ahankali daga handbag dinta tareda zaunawa gaban mirror ta kunna tareda Nemo numbern maamah ta Saka kiranta

Tana cikin waya da maamah ya shigo ya shige toilet Kai tsaye.

Wanka yayi tareda brush da sauran abubuwan da zaiyi ya fito daure da towel din datai wanka dashi.

Kammala wayarta tayi da maamah ta miqe daga gaban mirror din ganin Nan ya nufo.

Tana miqewa ya iso gurin Yana kokarin gyara zaman daurin towel dinsa datake a qugu sauran jikinsa duk a bayyane,fatan jikinsa da jikinsa dayake a murde duk ya cika mata idanuwa Dan haka ta sauke kallanta tana rasa inda zata nufa sbd tsoron Hawa gadon dakin takeyi gabanta faduwa yakeyi.

Ganin yanda ta dan rikice duk da boyewan datakeyi ya sanyashi riqo hannunta ya dawo da ita lokacinda take zaunawa gaban mirror din itama ya dawo da ita tareda sake zaunar da ita kan qafafunsa yana kallan fuskarta dataqi kallan tasa.

Tambayarta yayi idan akwai abinda yake damunta.

“Babu komai” ta furta tana kallan tafin hannunsa dayake hadewa da nata cikin sanyi da kashe mata jiki.

Ruwan wankan dayake jikinsa ya hadeta da jikinsa yana shafa mata sauran Dan Wanda yake fuskansa a wuyanta Yana shafa wuyan nata da fuskansa.

Saurin Dan janyewa tayi ahankali sbd tsikan jikinta dayake miqewa ahankali da Hakan.

Kallanta yayi yaga fargaba a tareda ita  numfashi ya sauke me sanyi mara sauti Dan Baya buqatan fargaba a tareda ita.

Fuskarta ya kama da hannuwansa biyu Yana kallanta cikeda tsananin son da baisan iyakansa ba a sannu yace

“Me yake faruwa?

Kina Jin gajiyan tafiyan da kukayo Right??

Sai a lokacin ta Bude idanuwanta ta zuba masa tareda gyada Kai ahankali…..

Babban matsalan da aka samu shine kallan datai masa kafin ta basa amsa shine ya kunce masa notikan Kai ya zagayeta da hannuwansa Yana Saka kansa cikin wuyanta Yana Jan qamshinta Dake sake tabbatar masa da kewanta da yayi a kwanakin.

Ita kanta yanda ya Saka kansa cikin wuyanta Yana sauke mata numfashinsa ahankali me dumi ya Sanyata Jin tana narkewa a jikinsa batareda ta San tana Hakan ba.

Saukan lips dinsa a fatar kunnenta yayi kissing ya Sanyata rufe idanuwanta tana Jin bakin nasa na gangarowa zuwa wuyanta ya sauke mata wasu silent kisses dasuke sake kayar da gabanta suka kashe jikinta duk lokaci Daya.

A lips dinta ya tsaya Saida ya lasa lips dinta ahankali cikin Wani shegen yanayin data qanqamesa tana Bude idanuwanta daqyar kafin ya hade bakinsu Yana tsotsanta ahankali ahankali hannayensa Kuma na zare rigar jikinta zuwa qugunta.

Milk lacey pushup bra din Dake jikinta ce ta bayyana,

Wani Mayen kallo yabi bra din da ita kafin yafara zare hannunta Yana kallan sakam kirjinta Daya fara bayyana ta saman.

Hook din bra din ta gaba yake Kuma Daya ne Dan haka da hannu Daya ya ballasa Yana kallan idanuwanta tayi saurin rufewa ahankali cikin wata irin kasala.

Zarewa yayi tareda jefar da ita gefe Yana hade kirjinta da nasa tared miqewa da ita a jikinsa ya nufi lafiyayyar gadon Dake jiransu bakinsa na cikin nata Yana mata Wani irin tsosan Dayake sake firgita karamin kanta.

Lafiyayyar romance din Daya kashe duk Wani abu dayake jikinta dasu ne tareda sonsa Daya zama rauninta suka taru suka rage Mata tsoron data shiga harya Kuma maidata cikakkiyar mace a karo na biyu cikin sanyi da Kwanciyar hankali.

Taji zafi da wuya Amma ba kaman na farkon ba dan haka ya gyarata da kansa suka kwanta baccin nutsuwa da yar jinyar da batakai na farkonba.

Abinda ya Sakata babban jinya shine maimaicin Daya sake samu bayan asuba Wanda ya kasa controlling kansa kaman na dare Dan haka tini ta danyace masa ta zazzabi me qarfi da azaba ya kwantar da ita Saida aka kirawo dr da safe tazo ta dubata Amma Babu wata babban matsala sai magani kawai ta Bata ta tafiyanta.

Shi kadai yayi jinyarta a wunin batareda buqatan komai daga Mr Jameel Dan haka ko anty Farha batasan tayi ciwonba.

A dakin suka wuni Yana kulawa da ita har dare yayi ya daga mata kafa sbd ta warke yanda ya kamata bayason wahalar da ita ko jigata Tako wane hanya.

Da daddare kusan abinci ma shine ya Bata sukai wanka suka kwanta.

Washe gari haka ya sake tattalinta Yana Bata duk kulawan da Bata samu ba da bayanan.

Kwana biyu yayi Yana jinyarta ta warke sosai daga Nan komai ya sake daukan hanya yanda ya kamata sbd duk inda ake buqatan Maida yarinya mace ya maidata cikakkiyar matarsa ciki da wajenta,

Ita kanta duk yanda take Jin yar fargaba da tsoro a duk lokacinda Wani abu zai shiga tsakaninsu harta fara Dan sakewa a kwanakin Dan kuwa wata rayuwa ce daga ita har shi suka samu kansa wadda ta gama tabbatarwa da kowannensu bazai iya Rayuwa ba Dan uwansa.

Fitinanniyar tsadaddiyar soft soyayyarsa yake nuna mata hakama itama gaba daya ta lalace gurin narke masa da gigitasa da sanyinta Dan haka mantawa sukai da matsalolin duniya na Dan lokaci kawai zallan soyayya me sanyi suke gudanarwa.

Mr Jameel da anty Farha ma tini suka baje a garin suna tasu soyayyar da basumasan Suma sun faraba,

Kyale Maigidansa Mr Jameel yayi ya samu Hutu da Jin dadi yanda yakeso hakama anty Farha kyale qanwar tata tayi ta gama illata zuciyar the great ASH TALBA da soyayyarta.

Satinsu uku suka fara Shirin komawa Kuma zuwa lokacin kaman yanda anty Farha taso AmatulMaleek ta gama yiwa zuciyar the great ASH TALBA Barna Dan kuwa idanuwansa basa iya daukewa daga Bata kyakkyawar kallo ko a gaban waye Dan haka ma yake tinanin yanda zai iya barinta su wuce abuja shi daga Nan Ghana zai tafi sai bayan kwana biyu zai iso Abuja.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

57

**********

Daren ranar da zasu koma Abujan a jikinsa take kwance jikinta dayakeda dumi yake shafawa tana cikin jikinsa yanajin yanda dumin jikinta ke shigarsa ahankali.

Bacci ne a cikin idanuwanta Dake Dan son dauketa ahankali musamman yanda yake Dan shafa wuyanta zuwa bayanta Yana sauke mata dumin numfashinsa me Dan sanyi a kunnuwanta.

Cikin nutsuwa yake kallanta Yana sake tambayarta ta tabbata zata koma Abujan yanzu bazata bisa Ghana ba.

Gyada masa Kai Tayi ahankali tana cewa “eh” cikin kasala da qaramin sauti Batareda ta Bude idanuwanta ba kafin ahankali ta Dora da cewa

“Maamah tin shekaran jiya taketa fadan dadewana tace mu dawo Hakanan nida anty Farha”

Bakinta dayake maganar ya kalla Yana Dan lumshe idanuwansa Dan shi abinda ita kawai takeso yake ganin shine abin damuwan idan tanason komawa gidan baida damuwa da Hakan.

“Are you sure akan komawan naki??

Bude idanuwanta tayi ahankali ta zuba masa su cikin wata sanyi..

Idanuwanta wasu irin kaifin Yanke hakuri da kamewansa sukeyi Dan haka yake kaucewa kallanta wasu time din idan Mr Jameel Yana kusa Dan komai zai iya faruwa Amma takasa gane Hakan Dan haka ya kawo fuskarsa ahankali ya hade da tata ya shaqi numfashinta zuwa cikinsa yaji wutar datake cinsa ta mutu Ahankali.

Hancinsa ya goga da nata ahankali Yana zubawa idanuwanta data Bude ta kallesa a yanayin dayafi rikitasa ya sake hade fuskansu Yana shaqanta yanda yakeso a natse itama qamshinsa da dumin fatan jikinsa sake kashe jikinta sukeyi suna sake Saka idanuwanta rufewa cikin slow da da wata kasalanta Dake qaruwa.

Hannuwanta ta zira ahankali ta zagayo wuyansa tana sake mannuwa da kirjinta daga kwancen ta Bude idanuwanta tai masa Wani kallo da gangan Wanda ya Saka shi zarewa gaba Daya Yana kama lips dinta da bakinsa ya Bude bakinta Yana mata Wani irin tsotsan daya Sakata sake matsesa tana mannuwa da krjinsa da nata take ya kusan dauke wuta Ya saki bakinta ya riqo numfashinsa dakyau kafin ya mayar da bakinsa cikin nata suka fara kissing juna a tare cikin Wani irin sanyi Amma Kuma deep deep lamarin ke tafiya Dan kuwa kiss dinsa na daban ne,

Tsotsa ne me girman dayake kunce kanta hakama a sanyi da nutsuwa komai ke tafiya.

Rigar jikinta da kusan batada banbanci da Babu ya zare ya jeho qasa Yana Fizgota cikin jikinsa da daman shi Babu Riga sanye jikinsa.

A tare suka sauke numfashi da ajiyan zuciyan haduwan jikinsu tana Sakar masa jikinta gaba Daya shi ma Kuma Hakan yakeso take ya tarairayota jikinsa Yana fara mata abubuwan dasuke mantar da ita komai.

Kusan a Daren zallan romance ce da lafiyayyar love yake gudana a dakin me sanyi da tattala juna tareda fara kewan juna tin baa rabu din ba.

Da asuba tinda sukai sallah yake sake tarairayarta Yana kashe dukkanin jikinta da sonsa da Baya boyuwa a cikin idanuwanta duk yanda ta iya boye abinda yake ranta sonsa yayi girman da Baya boyuwa Dan hakama takejin tana shiga fargaban yanda zata iya controlling feelings dinta a gaban maamah wadda Se yanzu komai na yanda maamah ta tsani auren har ranta yake dawo mata cikin Kai da zuciya.

Jirgin 2 zasu bi su Amatun ita da anty Farha yayinda shi Kuma zaibi na 4 Dan haka kusan tare suka shirya bayan ya zaunar da ita taci abinci ta koshi Shima sama sama yaci abincin sukai sallar Azahar tana zaune jikinsa suna magana ahankali maganarta na sake kunce masa lissafi Amma Yana danewa cikin nutsuwa.

Gaba dayansu zasu tafi airport din Dan haka Koda su Mr Jameel sukazo daukansu hannunsa riqe da nata suka fito Yana amsa waya dukkaninsu cikin navy blue kaya shi Armanis da sun glasses Daya masifar fitarta haskensa da class dinsa ita Kuma doguwar straight Turkish gown qafafunta sanye da wedges black Se handbag dinta da sun glasses din itama.

Ma’aikatan lodge dinne janye da kayansu a bayansu.

Mr Jameel ne ya fito ya karbi kayan ya Saka mota Yana Satan kallan ASH din da gana Daya ya tashi daga the great ASH TALBA zuwa ASHRAF MUH’D TALBA Dan gaba Daya ya koma kaman Bai Haifa Haydar ba,

Freshness din is on another level and walwalansa ta sauya gaba Daya Kwanciyar hankali ya bayyana a tareda shi duk da kamewan na Nan.

Cikin girmamawa da sakewa yayi masa barka da fitowa Yana Maida kallansa kan Amatu itama suka gaisa tana Dan kasa kallansa sbd Jin nauyi dakuma ganin irin kallan da anty Farha ke Mata lokacinda take gaida ASH din itama.

Motan da ASH din da ita suke ciki daban da wadda Mr Jameel da anty Farha suke ciki Dan haka ko a cikin motar hannunsa Yana sarke da nata tana Neman rikita masa lissafin tafiyarsa gaba Daya Amma Kuma dole zai tafi sbd mahimmancin tafiyar.

Ko dasuka Isa airport kusan mintina da suka Bata cikin motan Saida Mr Jameel ya kwankwasa masa ya sanar masa zasuyi latti kafin ta fito Kai tsaye anty Farha ce ta kama hannunta suke wuce batareda ta waiwayoba.

Ko da suka shiga jirgi suka zauna anty Farha Bata Wani tsokane ta ba sbd itama Se yanzu hankalinta ya dawo jikinta tafara tinanin abinda zasu cewa maamah akan fadan dadewansu data ringa yi a wayar.

Amatun ma jikinta sanyi ya ringa yi akan abinda zasu tadda din na fadan maamah da Kuma fitinar gidan da Bata qarewa yanzu.

Koda suka sauka sunyi mamakin ganin mota daga mansion tazo daukansu.

Shiga mota sukai Kai tsaye gidan anty Farha suka fara nufa suka tattara sauran kayan Amatun Dake gidan itama anty Farha ta dauki abinda zata dauka suka fito aka wuce dasu mansion.

Ko da suka shigo ana sallan magrib Dan haka securities ne sukai musu barka da dawowa kafin suka shigo ciki ma su karima ne da sauran masu aikin suka fito suna musu barka da dawowa Amma mum Aisha ko jinsu bataiba hakama Husnah dataji motsinsu qin fitowa tayi tana Jin zuciyarta na nauyi baqin cikinta ta dawo gidan Dan da basa Nan Jin tayi naufin zuciyarta ya sauka duk da tana cikin baqin cikin rashin zamanta yar ASH TALBA Amma Kuma a yanzu itama ta zabi ta boye zancen cikin ranta sbd kada Amatu suji su San ba shine ya haifetaba.

Kayansu kawai aka wuce dasu sama Amma dakin maamah suka nufa Kai tsaye dukkaninsu.

Suna shiga tana tayar da sallah Dan haka bedroom dinta Amatu tafara wucewa ta shiga toilet.

Bata Wani jimaba ta fito da alwalanta tukuna anty Farha itama ta tashi ta shiga bayan ta kashe wayar datake tayi.

Gefen maamah dukkaninsu suka tada sallah

Suna gamawa Nan suka jiyo suna fuskantar maamah itama kallansu tayi da mamakin yanda suka iya zuwa sukai zamansu musamman Amatu datake da karatu a gabanta Dan haka kafin amsa gaisuwarsu fada Tayi sosai suna Bata hakuri hardai ta sauka suka sake gaisawa cikin nutsuwa tana amsawa tana tambayar Yan gidansu Farha din idanuwanta na kan Amatun data sauya gaba Daya ta koma kamar wata wadda taje Hutu da Jin dadi kawai sbd Hutu ne sosai ya bayyana a tattare da ita,

Ta ciko kadan,fatarta ta sauya,haskenta ya sake samun lafiyayyar kyau,hakama qamshinta ya sake zama na musamman..

Irin kallan da maamah kewa Amatun ya Sanya Amatun shiga firgici da bugawan zuciya ahankali sedai Bata bari ta iya hada ido da maamah din ba ta miqe tana nufar inda ta ajiye wayarta tana daukowa Taga tanada misscalls uku tana ganin numbers din ta tabbatarda waye me Kiran Dan haka text kawai ta iya turawa a lokacin tana Saka Kiran Abdul Dan kawar da kallan qurullan maamah a kanta ta miqa mata wayar suka fara magana daga Nan anty Farha itama ta sake shiga firar aka bar zancen kallo aka koma na fira duk da Amatun Bata cikin sakewa har lokacin zuciyarta a yanayi na yar fargaba take.

Su karima ne suka kawo musu abincinsu a Nan dakin aka Jere musu Daman suna buqatan abincin.

Ko fara ci Basu yiba husnah ta shigo dakin batareda tasan suna Nan ba da niyar magana da maamah akan dawowan Amatun sai Kuma ta gansu a tareda Maamah din.

Qarasowa tayi ahankali ta zauna sama sama ta gaisa dasu tareda zubawa Amatun idanuwanta dasuke jajir yanzu kullum sbd ciwon Rai dai yaqi qarewa kowa a gidan.

Yanda take kallan Amatun a qure hankalinta na Neman tashi cikin shakka da tsoro Dan kuwa ta kasa yarda da Nigeria su Amatun suka tsaya hakama hakanan taji takasa yarda da rashin dawowan Dad dinta Daya kamata y dawo a sati biyun da suka wuce gashi acan Greece ance yabaro.

Maamah ce ta lallabata tace taci abincin tareda su Dan haka ta zauna cin abincin tareda su Badan tanajin yunwa ba Dan kuwa Jin tayi cikinta ya cunkushe gaba Daya ya cika da baqin ciki har Babu gurin Shan iska.

Amatu kuwa abincinta takeci a natse cikin Kwanciyar hankali Dan yunwa takeji ba laifi, hakama anty Farha abincinta takeci babu abinda ya dameta da Husnah din bare maamah datake ta lallabata kaman yarinya qarama.

Sbd Husnah Dake gurin yasaka hirarsu batai Wani tsayiba bayan cin abincinsu tattarawa sukai suka nufi daki sbd suna buqatan wanka da Hutu Daman.

Saida safe sukai da maamah suka fice daga maamah din har Husnah suna bin Amatu da kallo kowa zuciyarsa na harbawa batareda yasan abinda yake zuciyar Dan uwansaba.

Su kuwa suna Isa daki Amatun ce tafara yin wanka Dan Koda suka shigo tini karima ta gyare dakin qamshi da sanyin AC ne kawai ke tashi.

Tana fitowa wanka Shirin bacci kawai tayi ta Haye gado Daman sun Riga sunyi ishai a gurin Maamah.

Wayarta ta kunna daga kwancen data ke ko minti uku baayiba kiransa ya shigo wayar ta dauka a hankali jikinta na mutuwa da Jin muryarsa cikin wata irin nutsuwa da kamewansa dakuma wahalalliyar so Dake dawainiya dashi.

Kaman yanda take amsawa a kasalance da sanyi kusan Shima ahakan yake mata magana Dan haka suka jima a shiririce suka gama wayar tayi bacci sbd bacci me nauyi ne yake cikeda idanuwanta.

Koda anty Farha ta fito har tayi shirunta ta gama tini ita tayi Nisa a bacci.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

And

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

58

******************

Washe gari kusan latti kowa gidan yatashi sbd bacci da suka jima sunayi,

Mum Aisha da safen lokacinda ta Hadu da Amatun gurin cin abincin mamakinta kasa boyuwa yayi a gaban maamah data hawo saman duba Husnah data ringa mata kuka bayan tafiyarsu Amatun akan ta taimaketa tasa a raba auren Nan kada mum dinta taji zata iya rasa ranta,

Mum Aisha bakinta Kai tsaye batareda itama tayi Kai tsaye da yawa ba tace

“Amatu Biki kuwa kika tafi Lagos kokuwa Wani gurin kuka tafi Dan Sam bakiyi kama da wadda ranar Lagos ma ta sauka akanta ba”

Daga Amatun har maamah data shigo palon a lokacin har Husnah data dago kowannensu shiru yayi cikin rashin sanin abin yi ko fada.

Anty Farha ce tahau kame Kamen zancen tana cewa

“Bikin Hutu ne ai bana wahala ba,Kuma tinda mukaje Amatun Bata fita koina ba Dan bazan bar matar ASH TALBA guda ba tana yawo ta jigata”” qarasa maganar tayi cikin Maida zancen wasa duk da Babu Wanda zancen yake wasa a gurinsa cikinsu,

Abincin ma kusan kowa Jin yayi cikinsa ya cika Banda mum Aisha datai maganar ko a jikinta.

Maamah jiki ba qwari ta koma inda ta fito Husnah ma Shan dole tayiwa tea din Dake hannunta tana danne zuciyarta Dake Neman dawo da abinda taci.

Amatu ce kawai ta qarasa cin abincin cikin sanyi batareda tace komaiba.

Suna gamawa Shirin school tayi ta ficewarta tareda anty Farha da itama tana buqatan zuwa shagonta Taga halinda ma’aikatanta ke ciki.

Bayan fitarsu kallan Husnah mum Aisha tayi cikin takaici Kai tsaye tace

“Ke kin yafe karatun kenan sbd baqin cikin wata zata fiki matsayi gurin Wanda kike dukan gaban mahaifinki ne.”

Kasa cewa komai Husnah tayi sbd Babu ranar da yanzu mum Aisha Bata tayar mata da ciwon depression dinta da maganganunta Wanda mum Aisha da gasken so take kafin ASH ya dawo ta jiyarwa da yar tasa qwaqwalwa kowa ya huta.

Amatu a school ta wuni sai yamma ta dawo gidan batareda anty Farha ba wadda Se dare zata dawo Dan haka dakin maamah tayi sallah tana idarwa taci abinci ta kwanta baccin yamma.

Sai magrib ta Farka ta shiga toilet tayi alwala sukai sallah tana idarwa waya ta fara da anty Farha dake Bata labarin abinda ya faru a shagonta yau din na wata yar matsala da itace ta Sanyatama dadewa Bata Dawo ba.

Maamah tanason yiwa Amatu magana akan auren ASH TALBA amma Kuma sai ta fasa sbd ganin kwata kwata Amatun rayuwarta takeyi a natse batareda ma tinawa da auren ASH dinba Dan haka sai takejin baima kamata tana maimaitawa Amatun maganar aurenba Koda da sunan gargadine Dan haka sai kawai ta hadiye maganarta koba komai yanzu ASH din tinda Abeeda ta farfado bawani zama zai ringa yi anan ba kafin a dawo da ita.

Cikin kwana biyu maamah ta sauyawa Amatun zuwa normal yanda suke hakama itama Amatun hankalinta ya kwanta ganin mahaifiyarta ta dawo mata daidai sai kawai take sake samun Kwanciyar hankali da nutsuwa ta bangare daya ma sosai take cikin nutsuwan zaman anty Farha tareda ita Dan tattalin datake nuna mata sai takejin kaman ASH din Yana tareda ita sbd komai na kulawan anty Farha datake mata bisa ga umarninsa ne da Kuma kaunar da anty Farha din ke Mata da zuciyarta Daya.

Mum Aisha ma da kusan abinda takeso ne yaketa Shirin faruwa a gidan na tarwatsewa Daya bayan Daya sai hankalinta yake Dan Kwanciya sbd tsaf ta hango kadan kadan Husnah Neman zaucewa takeyi a cikin gidan ubanta gashi ASH kaman Wanda baida niyar dawowa shiru Bai dawoba Dan haka Husnah ta sake shiga tashin hankali da damuwa ga barazanar da kullum mum Aisha da Naufal ke Mata akan fada masa abinda tayi idan har Bazata ringa abinda suka sakataba na son tarwatsa maamah da Amatu.

Damuwa da kadaici da barazanar mum Aisha ya Saka Husnah fara zarewa tana komawa ruwa na ciwonta Dan haka maamah hankalinta yafara tashi itakuma karshe ma kusan dakin Husnah din ta dawo da kwana Dan Husnah Bata iya bacci kowanne dare cikin kuka da buga kanta take gashi Sam duk wayar da ASH keyi da maamah din Dan Jin lafiyar kowa da Gidan Bata fada masa ba sbd kada ta raba masa hankali ga ciwon Abeeda da Kuma na yarsa,

Ita kanta Husnah din ta kasa barin ya gane halinda take ciki sbd Yana sani zai tabbatarda ya gano meya sameta anan zai San tasan ba shine ya haifetaba,kisan mummuke mum Aisha ke Mata tana Bata azabar boye Dan kuwa ko maamah Bata Saniba Dan ita kanta Husnah batason maamah ta sani tasan cewa itace ta tura Naufal yiwa Amatu fyade Dan kuwa tana sani zata iya juya Bata Baya bayan ita kadaice gatanta da bangon jinginarta a yanzu dakuma zamanta wadda kawai zata hurawa auren Amatu da Dad dinta wuta ya mutu batareda mum dinta ta dawoba.

Satinsu Amatu biyu da dawowa ASH TALBA ya sauka Abuja lokacin Bata gidan tana school Kuma Bata dawo ba Sai yamma Dan haka batama lura da motocinsa da aka fito dasu daga inda suke ba wainda suke nuna ya dawo a duk lokacinda zaka gansu a filin harabar gidan kusa kusa.

Ganin maamah a kitchen tareda su karima yasata tinanin me takeyi a kitchen ASH Baya gari tinda yawanci abincin dazai ci ne kawai take Saka hannu a ciki yanzu sbd sanin bayason abincin masu aiki.

Bata tsaya ba bayan maganarda tayi da maamah din sama sama ta wuce sama a Dan gajiye.

Tana shiga dakinta handbag dinta da wayarta ta jefar ta nufi toilet tana zare kayan jikinta.

Wanka tayi gajiyanta ya sake sosai ta fito ta zauna tana shafa Mai tana kallan time da aka fara Kiran magrib.

Wayarta datake flight mode ta cire tana ajiyewa ta miqe ta Saka kaya.

Ripped Skinny jeans ta Saka Wanda ya lafe jikin siraran cinyoyinta ta Saka  golden yellow freesize satin Versace shirt wadda material din ke kwantawa jikinka duk da fadinta.

Hula ta Saka qarama ta rufe gashin kanta da aka gyara mata shi jiya a shagon anty Farha.

Fitowa tayi farar qafarta sanye da slippers da suka Dan mata yawa ta sauko qasa ta dauki ruwa me sanyi a fridge ta koma sbd ruwan datake son sha idan bame sanyin sosai ba batajin ya cire mata kishin idan ta debo gajiyan school.

Tana komawa daki ruwan ta zauna Tasha sosai kafin ta rufe robar ruwan tana ajiyewa ta miqe ta tayar da sallar magrib.

Tana gamawa taji dawowan Husnah a lokacin sbd itama yau taje school duk da ita spll ne ma take shirye Shiryen farawa.

Itama Husnah Bata lura da Dad dinta ya dawo ba hakama Bata Tararda maamah a waje ba bare ta fada mata,su karima kuwa kowa a taitayinsa yake da Husnah da mum Aisha da dukansu zuciyarsu take a kusa.

Ana sallan ishai Amatu tayi ta fito cin abinci har lokacin Bata duba wayarta ba bare Taga misscalls din datake dasu da massages.

Tana fitowa Kai tsaye dining room ta nufa tana kallan abincin dayake Jere idanuwanta suka sauka kan tea set Dake gefe jere gurin zamansa.

Tsayar da idanuwanta tayi kan kayan tea din tana nazarin baa kawo tea akan dining matiqar ba ASH Yana gari ba,

Ya dawo ne ko me?

Yaushe ya dawo?

Juyawa tayi ahankali tareda komawa daki Dan duba wayarta sedai ko taku uku bataiba taji anriqo hannunta ta bayanta qamshinsa na cakuda iskan wajen cikin sanyi.

kasa riqe mamakinta tayi ta juyo da sauri tana kallansa cikin mamaki da sanyin dayake cike zuciyarta batareda ta saniba.

Dawo da ita yayi Baya ahankali Yana hade jikinsu fararen lazy eyes dinsa akanta ya sauke numfashi Yana cewa

“Ina kika shiga tareda kashe wayanki?”

Bata basa amsaba jikinsa ta qarasa shigewa tana sake Wani lafiyayyar murmushin da ya kashe jikinsa Yana Neman kunce masa Kai kafin ta Bude Baki tace

“Ina school tin safe and wayana Kuma Yana flight mode ne I dunno cewan zaka ki…””

Bata qarasaba ya kasa hakuri ya Dora lips dinsa akan nata ahankali ya sauke mata Wani light kiss Daya Sakata dago idanuwanta ta zuba masa tana sake gigita kamewansa Yana ma mantawa da inda suke din ya dagata ya zaunar akan dining din Yana ranqwafowa ya zagayeta da hannunsa Daya Dayan hannun Kuma ya kamo fuskanta ahankali ya sake kissing Yana cewa

“Akwai 2hours da zai wuce ne ban kira numbern L.A ba???

Qarasa mata tambayar yayi Yana Saka kansa wuyanta yayi kissing gefen kunneta tareda sake zagayota da hannunsa Yana Bata Daman shaqansa yanda takeso.

Bai tsaya Bata Daman amsawaba ya sake jefa mata wata tambayar data Sakata Bude idanuwanta akansa ba shiri tana amsawa da cewa

“Maamah tafi fada sosai fa na dadewan mu a lag da anty Farha”

A karo na biyu bayan tsayuwarsu gurin ya sake Sakar mata Mayen murmushinsa Yana sake ranqwafowa ya rufeta da kyau Yana sake Kai bakinsa wuyanta wannan Karan harshensa ya Saka ya lasa saman kirjinta Yana Dan Jin nutsuwansa na dawowa.

Lumshe idanuwanta tayi da lasan da yayi mata sbd waiwayi me qarfin gaske da Hakan ya Sakar mata ta Dan damqe hannunsa Daya dayake shafata Yana sake tambayarta lafiyanta da yanda tayi missing dinsa.

Amsawa takeyi a Yanke tana tana Dan lumshe idanuwanta tana kokarin riqe hannunsa sbd abinda yake faruwa Yana kashe dukkanin jikinta da kuzarinta hakama shi kansa numfashinsa Dake fita ahankali cikin sanyi Yana saukar mata ta tabbatarda yafara shiga kasala.

Ahankali ta Bude bakinta Dake setin kunnensa ta fara fidda numfashinta datake riqewa ahankali ya sauka cikin kunnensa har zuwa kansa take tsikan jikinsa suka miqe ya mannata da kirjinsa ta furta

“Kowa na gida fa and…..” Bata qarasaba ya dauketa gaba Dayanta ya rabata da dining din Yana komawa hanyar Daya fito da ita ita Kuma tana sake narkewa jikinsa duk da yunwa takeji abinci take buqata Dan haka batajin ma zai mata komai yanajin yinwa takeji.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

59

****************

Palonsa suka nufa Yana shiga da qafarsa daya ya tura kofar palon bayan sun shige,

Kan doguwar luxury console table Dake farkon shigowa palon ya zaunar da ita Bai tsaya komaiba ya hade bakinsa da nata

Itace tafara kissing dinsa tana susutar dashi gaba Daya missing din dayayi mata ya taso masa Yana qanqameta dakyau cikin jikinsa tana sake kashesa da yanda take kissing dinsa hayaqi kawai yakejin suna fita kunnuwansa.

Rigar jikinta ya yaga da hannuwansa ya zare ya jefar Yana bin milk Skims wireless embroidery bra dinta da kusan komai Yana Gani a ciki da matsiyacin kallo Yana ambatar sunanta cikin qasan maqoshinsa.

Abinda yake faruwa a gurin cikin sanyi me girma ne Dan kuwa numfashinsa ne kawai ke fita a gurin ahankali har sai daya tabbatarda bazai iya wahalarda ita a halinda take ciki na Jin yunwar da ko Bata fada masa ba yasan abinci tazo ci a dining din.

Sauko da ita yayi suka nufi bedroom dinsa ya zaunar da ita a bakin gado ya dauko mata wata shirt dinsa fara ya Saka mata sbd tata din bazata maidu ba Dan botiranta gaba Daya sun zube qasa Babu abinda zai riqe mata ita a jikinta hakama bra dinta Bata jikinta dole rigar tasa kawai ya Saka mata tareda mayar Mata da hularta ya rufe mata kanta suka fito Yana riqe da hannunta kaman basune suka gama abinda suka Gamo ciki din ba.

Suna fitowa zaunar da ita yayi ya zauna Shima kenan kafin yayi Wani motsin Husnah ta shigo gurin mum Aisha ma ta shigo Babu Wanda ya Kalli inda Amatu take shi suke kallo kowannensu a natse cikin girmamawa suka gaidasa suna masa sannu da zuwa Shima a natse ya amsa Yana kallan Husnah data sauya gaba Daya.

Cup din Daya dauka ya ajiye ahankali Yana kallanta cikeda kulawa Yana Dan kame fuskarsa sbd rashin Jin dadin ganinta ahakan yace

“Husnah,Wani abu Yana faruwa ne?

Kinyi rashin lafiya ne ko me???

Meyasa nake ganinki Hakan??

Shiru dukkaninsu sukai kowa gabansa na faduwa musamman Husnah din Se mum Aisha da kowannensu Baya fatan Koda tsautsayi ASH din yasan meyake faruwa a tsakaninsu.

Amatu ma shiru tayi tana kasa cewa komai bare dagowa Dan kuwa sosai ASH din ya zama serious da abinda yake fada amsar tambayarsa yake jira Kuma shirunsu ya Sakasa tabbatarda akwai abinda yake faruwa din.

Amatu ya juyo ya kalla yace taje ta kira masa maamah.

Tana Jin Hakan itama nata gaban ya sake faduwa Dan haka ta miqe a sanyaye sai alokacin idanuwan mum Aisha ya sauka kan rigar Dake jikin Amatun wadda ko zaa cire idonta ta shafa tasan ta ASH ce sbd kalan kayan dayake sakawa daban suke Dana Kowa duk mansion din da kewayansa kusa,hakama tayiwa Amatun yawa sosai rigar ga qamshinsa Dake tashi a jikinta….

Sarqewa tayi da qarfi tari me gigitarwa Yana taso mata tafara yinsa tana dafe kirjinta Dake Neman toshewa sbd Tarin tashin hankalin ta tabbata kenan ASH yafara ganin wannan yarinyar a boye ko me??

Ruwa ta dauka hannunta na rawa ta Bude takai bakinta tana sha da sauri sbd karta mutu a banza Asmau da yarta su samu ASH TALBA yanda suke so.

Amatu gaba Daya bata Tina da rigar dayake jikinta ba Kai tsaye maamah taje ta kirawo wadda itama Bata ma lura da meye a jikin Amatun ba suka dawo Saida suka shigo dining room din har lokacin kowa na zaune cikin zufa batareda sunce komaiba.

Maamah na shigewa ta tsaya daga gefen tareda Dan kasa kallansa suka gaisa ta sake masa barka da dawowa

 cikin mutuntawa a natse ya Bude Baki yace

“Meyake faruwa ne a gidan nan?

Husnah tayi jinya ne?

Akwai matsala ne a gidan daya kamata na sani?

Maamah ma shiru ta Dan yi sbd batasan me zata fada ba Kuma bayan abinda ta sani Wanda ita kanta batasan Menene matsalan Husnah dinba.

Numfashi ta Dan sauke ahankali ta Bude Baki tace

“Babu Wani matsalan bayan yanayin jikin Husnah Daya tashi sai Kuma kuka da tashin hankalin da nake ganin kaman dole akwai abinda yake damunta duk da Ina tinanin ko yanayin jikin Abeeda ne yake damunta”….shiru tayi daga Nan sbd Bata buqatan sanar dashi sauran tashe tashen hankalin da Husnah ta ringa sakasu da some somenta tinda ya wuce.

Shiru yayi Yana nazarin zancen maamah din sedai bayajin a yanzu da Abeeda ta tashi ciwonta zai Saka ciwon Husnah din tashi sedai Wani abun daban.

Kan Husnah Dake tsiyayo hawaye masu radadi ya Maida idanuwansa kafin ya Maida kallansa kan mum Aisha datake Dan sake shan ruwa tana Hana kanta sake sarqewa sbd fargaba Dan idan ASH yayi saurin ganota ya rabata da gidansa komai lalace mata zaiyi sbd Bata Riga ta Tara abinda ya kamata ace ta Tara ba a zamanta gidansa shekara da shekaru.

Kan Amatu ya Maida kallansa yaga itama duk tayi sanyi kanta akasa sai alokacin idanuwansa suka tinatar dashi da rigar dake jikinta Amma Bai damuba a yanzu damuwar datake Neman juyar masa da kan ‘ya yake Neman sani.

Sake maimaita tambayarsa yayi akan Husnah meyake damunta,

Dago kanta tayi ahankali zatai magana idanuwanta suka fara sauka kan AmatulMaleek da maamah ta tsayar a gefenta ta tareta daga zuwa cikin dakin da kyau,

Qurawa Amatu idanuwanta tayi tana kallan rigar jikinta da take ma ta hango Babu bra jikin Amatun,

Tsoshewa kirjinta yayi kafin idanuwanta suka fara Neman Dena Gani daidai tayi saurin rintse idanuaan sai kawai ta fashe da kuka Mai tsananin gaske tana kasa tantance abinda yake Shirin faruwa a cikin gidan ubanta da uwarta.

Kukanta ya Saka maamah Jin Babu dadi zuciyarta na sosuwa hakama tana mata nauyi lokaci Daya sbd tasan bakomai ne yake cin zuci da rayuwar Husnah ba sai irin abinda yake cin ranta na abinda zai iya biyowa bayan Abeeda tasan wannan auren na kaddara Dan haka itama cikowa idanuwanta sukai da hawayen ta Yanke shawarar yin magana dai a yau din komai ya zo karshe,

Dagowa tayi tareda dawo da kallanta kan ASH Dayake sauraron kukan Husnah har cikin ransa yake jinsa.

Bude Baki tayi zatai magana mum Aisha tayi saurin katseta sbd yanzu datake ganin alaman akwai abinda yake faruwa tsakanin ASH da Amatu batason a raba auren Se zancen ya Isa kunnen Abeeda Koda daga kwancen ne ta yanda zuciyarta zata buga ta mace,

Mutuwar Abeeda itace zata kawo mata komai datake so Dan mutuwarta zata buga mata zuciyar maamah,hakama mutuwarta zata qarasa juyar mata da kan Husnah haka shi kansa ASH din zai shiga Wani halin Dan haka so take kafin a raba auren kota Yaya ya Isa kunnen Abeeda koda shine abu na karshe da zata ji kafin komawa coman gaba Daya.

Hana maamah magana mum Aisha tayi ta hanyar cewa

“Husnah tana cikin damuwan rashin ganin mahaifiyarta ne bayan tashinta,

Kuka da damuwar datake ciki duk Hakan ne ya hanata walwala ganin takeyi akwai matsala babba da ake boye musu musamman dadewanka baka dawoba shine ya Bata tsoro sosai take shiga damuwa””

Husnah duk da tana cikin mummunan hali Saida ta dago ta Kalli mum Aisha tana kasa cewa komai sai qara kukanta datakeyi Wanda ya Saka ASH din kallanta da kyau ya tambaya idan Hakan dinne?

Gyada Kai kawai tayi sbd a matse take da son barin gurin kafin ganinta ya dauke gaba daya.

Sallaman maamah yayi Yana cewa ya gode taje,

Juyawa tayi takira Amatu ta bi bayanta suka bar gurin.

Kallan Husnah yayi itama cikin kulawa yace taci abincin idan ta gama ta samesa suyi magana.

Tashi yayi batareda Shima yaci abincin ba yabar gurin sbd ya tabbatarda akwai matsala a gidansa da baisan da itaba,.tsaf ta karanci kowa da abinda yake kokarin boyewa Dan haka zai gano koma Menene yasan abinda yake Neman daga zaman lafiya da Kwanciyar hankalin kowa a gidan.

Yana barin gurin abinda mum Aisha ta fara juyowa ta Kalli Husnah tana fada shine

“Lokaci yayi da Abeeda zata dawo Nigeria ta qarasa jinyarta a cikin Yan uwa da yayanta da mijinta tinda ta Farka idan ba haka ba lokacin da Zaki tattara ki bita can ASH ya dawo hannun Amatu da uwar Amatu”

Tana gama fada ta miqe tabar gurin tabar Husnah zuciyarta na tafasa kukanta na qaruwa,

Babu abinda take tsakanin buqata a yanzu bayan dawowan mum dinta Koda a kwancen ne dole zataje ko bada sanin Dad dinba ta dawo da ita sedai kawai su gansu tinda Neman mantawa yakeyi da mum dinta akan Amatun da ta kasa yarda ma da abinda yake Shirin faruwa Sam Sam bazai yiyuba.

Amatu suna fitowa da maamah komai maamah din Bata ce mata ba ta Sauka ta wuce bedroom dinta,

Shiru ta Dan yi a tsaye itama a palon saman kafin ta shige bedroom dinta ta zauna tana shiga damuwan shikenan maamah zata dawo da fushinta akanta.

Shiru gidan ya dauka yayi tsit bayan awa kusan biyu da lamarin.

Husnah palon Dad dinta ta tafi jiki a mace Dan sanar dashi tanason zuwa gurin duba mum dinta.

Cikin nutsuwa da kulawa ya kwantar mata da hankali tareda Bata tabbacin Daman tafiya Mr Jameel zai mata komai a cikin satin ta wuce.

Bayan sun jima suna magana miqewa tayi zata fice idanuwanta cikin kaddara da tsautsayi suka sauka kan bra din Amatu Dake jefe qasan gurin qaton console din dayake palon hanyar kofan ficewa da rigarta da suka watsar dazu.

Dafa Bango tayi tana Dan danne abinda yake taso mata tasamu ta Isa kofa ta fice batareda ma yasani ko fahimtar abinda ta Gani ba duk da shi baisanma kayan suna gurin ba.

Da dafa Bango ta Isa dakinta ta Bude ta shige ta rufo kofar ta Saka mata key ta Isa tsakiyar dakin ta zube qasa tareda fasa kuka me Qarfi tana rufe bakinta da hannunta tanajin ma har Dad din nata ta tsana Kuma tsana me tsanani.

Amatu tini ta kwanta sedai ta kasa bacci sbd batajin zata iya bacci batareda taci abinci ba Dan haka taketa juyawa kan gado a sanyaye cikin damuwa.

Kasawa tayi ta sauko gadonta ta zira slippers ta nufi kofar dakin ta fice.

Dining room ta nufa ta tarar da akwai abinci a Jere

Cikin Jin dadin Hakan ta dibi abincin a plate da drink da ruwa da abubuwan da zata iya ci duk a trey ta dauka ta juya zuwa dakinta.

Tana shiga dakin ta ajiye trey din kenan aka Turo kofar dakin tareda shigowa

Da sauri ta juya Se ganinsa tayi a natse hankali kwance ga mamakinta da drink a hannunsa alaman ya kawo mata sbd sanin Ba lallai taci abincinba.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

60

****************

Kallansa takeyi a kasalance da mamaki tana kallan hannunsa Shima ita yake kalla Yana qarasowa bayan ya tura kofan dakin.

Juyowa tayi dakyau a Dan kasalance tana kallansa harya iso inda take ya tsaya gabanta Shima kallanta yakeyi da idanuwansa dasuka Dan yi laushi na yunwa da damuwan halinda Husnah ta shiga a yau din.

Cikin sanyi Shima yau din ya Bude Baki yace

“Kinci dinner naki?

Maganarsa ta Dan sake motsa yunwar Dake cinta ta sake matsowa cikin jikinsa ahankali tareda zira hannunta ahankali ta zari Mango drink din dayake hannunsa ta dago tana kallansa itama cikin kulawa da tace

“Did you eat urs???

Tambayarta ta Saka shi lumshe idanuwansa Yana kama hannunta da drink din yake ya dago Yana kallan drink din yace

“How can i bayan nasan Babu abinda ya shiga cikin little Abeeda Talba….qarasa maganar yayi Yana bude drink din da hannunsa Daya Yana kaiwa bakinta ta Bude bakinta ahankali ta kurba tana lumshe idanuwanta sbd Jin dadin taste din a bakinta.

Itace ta kama hannunsa ta jasa suka qarasa suka zauna kan kujera Daya tana kallan abincin data debo kafin ta dawo da kallanta kansa ta Dan kama hannunsa cikin nata ahankali tace

“Zakaci wannan ko a kawo Wani abin daban?

Shiru yayi Yana kasa magana Se idanun Daya zuba mata jikinsa gaba Daya a mace.

“Tea??? Ta fada tana masa kallan tambaya kaman Wani qaramin baby wanda Hakan ya sakashi sakin murmushin da Bai shirya ba dariya me nutsuwa da sanyi na zuwar masa.

Itama murmushin ne yake saukan mata ganin yanda yayi nasa harda yar dariyansa da Bata taba ganiba.

Kaman yanda tai masa tambayar ta Yara Kai ya girgiza mata Shima.

Abincin ta Sakawa spoon Dan white rice ce da macaroni salad Bata Sako nama ba sbd Bata buqatansa sai soyayyar plantains da aka Soya tareda kwai da pepper.

Tayar da ita yayi ya Dora akan qafafunsa tafara cin abincin ahankali tanaci tana basa shima shikuma yana Bata drink din tana sha sbd duk bayan cin spoons uku ko biyu saita sha sbd Jin kaman Baya wuce mata saita sha abu me ruwa.

Babu yawa abincin Amma yanda suke ci suna Shan drink din sai gashi sun koshi sosai yabata ruwa Tasha yasha Shima ta tashi daga jikinsa taje takai kayan kitchen ta dawo.

Ko data shigo Yana zaune inda tabarsa Dan haka toilet ta wuce Dan yin brush.

Tana ciki ya shigo Shima brush din yayi da sabon brush data fasa masa suna gamawa alwalan bacci sukai suka fito tana tinanin tafiya zeyi dakinsa Amma ga mamakinta janyota kawai yayi jikinsa Ya Dan rugumeta ahankali suka nufi window din dakin nata ya janye curtains suna kallan waje Yana mata magana ahankali sbd abincin da suka ci ya Danyi digesting kafin su kwanta.

A jikin window din sun jima a tsaye har bacci ya dauketa a jikinsa kafin ya daukota suka dawo gadon ya kwantar da ita ahankali ya rufeta.

Toilet dinta ya sake shiga Bai jima ba ya dawo harda sabuwar alwalansa ya goge hannuwansa da towel harda qafafunsa da fuskansa sbd kada sanyinsu ya damesa harma da ita,

Rigarsa Dake da Dan sanyi ya zare itama ya ajiye dagashi sai dogon wandon kayan baccinsa ya Haye gadon ahankali ya janyota jikinsa kaman tana jiransa itama cikin bacci ta sake shigewa jikinsa tana lafewa cikin abin rufar baccinta na sake nauyi.

Shima Bai Wani jimaba baccin ya daukesa.

Bacci sukai na Kwanciyar hankali da nutsuwa,

Da asuba dayake yayi latti Dan Koda ya Farka ana kokarin sallame sallah Dan haka dole a daki yayi sallah Bai fita ba,

Tare sukai sallah suna gamawa itace ta fara miqewa ta zare hijab dinta zata kwanta sbd baccinta dawowa yayi.

Tana kwantawa ta zuba masa idanuwanta harya gama tana tinanin tafiya zaiyi sai kawai ganin tayi Yana Bude botiran gaban rigarsa zai sake cirewa ya kwanta.

Tashi tayi zaune ahankali tareda saukowa gadon tana Dora hannuwanta biyu akan hannunwansa tana hanasa qarasa Bude gaban rigar tasa idanuwanta da sauran bacci ke cikinsu ta dago ta zuba masa ta bude Baki cikin qasa qasa da murya kaman wadda ke bacci tace

“Gari zai fara haske kowanne time maamah or Husnah zasu iya fitowa”

Maganarta ta Sakasa kallanta cikin yanayin data kasa fahimtar Menene Amma Kuma Babu alamar maganarta ta shigesa koma samun gurin fahimtar Hakan.

Hannuwansa ya zare tareda zagayota ahankali ya manne da kirjinsa yana kallan idanuwanta Dake kasalance sbd bacci.

Yanda ya shigar da ita jikinsa kusan taban rigarsa Daman ta Bude Dan haka Kai tsaye lafiyayyar fatan jikinsa ne ya Hadu da tata duk da akwai yar fingilar rigar bacci a jikinta Amma kusan tinda Babu bra a jikinta sosai yaji haduwar jikin nasu Kuma Daman cike yake da kewanta

Kokarin Bude Baki tayi ta sake magana ya Dora bakinsa anata Yana dakatar da ita.

Tsotsan bakinta yakeyi ahankali ahankali cikin nutsuwa Yana sake zagayota da hannuwansa hannunsa Daya na shigewa cikin rigarta.

Shafan da yayi mata a fatan bayanta zuwa cikinta da kirjinta ya Sakata zagayosa da hannuwanta itama tana fara tsotsan bakinsa shima Dan haka take kansa ya kunce ya dauketa gaba Daya ya zaunar gaban mirror din dakin nata Yana Bude gaban Rigarta gaba Daya.

Lafiyayyar fatar bayanta datake fresh ba tabo ko Daya ya zubawa idanuwansa dasuka fara sauyawa ta cikin mirror din datake zaune akansa ta basa Baya kafin ya ranqwafo ya sake hade bakinsa da nata Yana dafeta jikin mirror din Yana bin duk abinda yakeso a jikinta da kisses masu zafin gaske.

Ganin suna Neman tarwatsa komai dayake gaban mirror din ya sanyashi dauketa cak ya nufi gado da ita yana qarasa zare rigarta ya jefar ya Haye gadon Shima Yana cigaba da abinda yakeyi zuwa abinda ma ya fisa.

Hankali kwance da nutsuwa da so me sanyi ya huta da matarsa yanda ransa yaso masa a dakin batareda da damuwan komaiba,

Suna gamawa wanka ma a dakin yayi tareda ita suna gamawa ta Saka Riga da wando na marasa nauyi shima kusan kayan jikinsa ya mayar ya kwanta tareda ita suka koma baccin safe bayan duk rokon datai masa akan ya tafi Amma yaqi Dan haka tasowa tayi ta sakawa dakin key ta dawo ta kwanta dole ba jimawa bacci me dadi da nauyi ya daukesu.

Baccin kusan awanni sukai tareda mantawa a inda suke sai guraren 10 ya Farka ya tashi ya sauko gadon itama lokacin ta Farka tare suka sauko.

Brush ta sake yi jikinta gaba daya mace sbd yunwa Dan haka tana brush din ta fito Shima brush yayi ya fito Kai tsaye kofa ya nufa sbd itama Bata dakin ta fice zuwa Neman abinda zata ci.

Yana kokarin fitowa daga dakin daidai dawowanta riqe da glass cup na Greek yoghurt me sanyi a hannunta tafara sha tin a hanya,

Batasan da fitowansa ba Dan haka saura kadan ta Fadi Daya Bude dakin Dan haka ya tareta tareda rungumota kirjinsa Yana kallanta Yana cewa ta kula sosai.

Bakinsa ya sauke idanuwansa Yana kallan yanda ta cika bakin da yoghurt din tana hadiyewa ahankali Yana kallan ya da yake wucewa ta maqoshinta idanuwanta na nuna yanda takejin dadinsa a Baki da zuwa cikinta.

Da ido ahankali ya tambayeta “meye wannan din take sha”

Kallan cup din hannunta tayi tareda sake kaiwa bakinta Tasha ahankali kafin ta Bude Baki cikin sauti mara karfi tace

“Greek yoghurt,do you want some?? Ta fada tana dago cup din tana nuna masa.

Gyada mata Kai yayi tareda Kai bakinsa ahankali ya ziro harshensa kan lips dinta ya lashi yoghurt din dayake saman bakin nata Yana lumshe idanuwansa ahankali.

Yanda ya lashi yoghurt din daga lips dinta ya Sakata sakin murmushi ahankali tana sake kurban yoghurt din Yana Bata bakinta gaba Daya.

Idanuwanta ya kalla Yana sakin Wani shegen murmushi tareda sake matseta da jikinsa Yana cewa

“Kina son yin kisa ne??

Murmushi tayi kafin ta Bude Baki ta basa amsa ya Dora bakinsa Yana yiwa yoghurt din kan bakin nata Wani irin lasan Daya kusan Sakata sakin cup din tana sake damqe cup din.

fitowan Husnah da mum Aisha data hawo palon saman ne idanuwansu yayi mummunan ganin Duk da kusan baa palon suke ba a dakin Amatun ne daga ciki bakin kofa Kuma sun Turo kofar rufewa ne bataiba batareda sun luraba.

Rawar disco qafafun Husnah suka dauka ganin abinda yafi karfin idanuwanta zuciyarta hakama itama mum Aisha rawa da tsalle zuciyarta keyi cikin tashin hankalin da baa Saka masa ranaba.

Bakin Husnah na rawa ta Bude zata fasa kuka me qarfin gaske mum Aisha tayi saurin Saka hannuwanta ta rufe bakinta da qarfi tareda Janta cikin dakinta ta saketa tareda juyawa da sauri ta fito ta sauko qasa Dan bazata yarda Husnah tayi kukan da zai Saka ASH sanin ‘yarsa ta San ya amshi Amatu matarsaba batareda Maamah tazo ta Gani da idanuwanta ba.

Dan haka tana saukowa cikin sauri har hada stairs takeyi gurin sauka Dan kirawo maamah yau Taga abinda zai Saka zuciyarta bugawa matsalanta tazo karshe.

Shikuwa Yana gama lashe yoghurt din sakinta yayi sbd komai zai iya faruwa a lokacin idan ba control na kansa yayi ba.

Fitowa sukai a tare suka wuce dining itace ta zauna shi Kuma ya wuce Hanyar bangarensa Dan sauya kayan jikinsa dasuke na bacci Kuma kusan rugar duk sun cire batiranta kaman Daya kawai ya Rage.

Yana wucewa bread kawai da cup dinta ta dauka ta baro dining din sbd Babu abinda yake gurin datake Jin zataci.

Bedroom dinta ta isa tana budewa maamah da mum Aisha na hawowa saman kallan Amatun maamah keyi da dukkanin idanuwanta sedai batama San me zata tambayeta sbd tsalle da zuciyarta keyi da zancen mum Aisha din cewan Amatu na tareda ASH a yanayin da Bai kamata ba,Bata Wani fahimci zancen mum Aisha dinba Dan haka Koda ta biyota suka zo ma batasan me zata ce ba.

Husnah ce da idanuwanta sukai Wani irin kumburan da ba kyan Gani ta fito dakinta tana ganin maamah ta sake fashewa da kuka ahankali tana sauke Kai qasa tace

“Maamah Amatu ta zama matar Dad dina dai kina kallo haka mum zata dawo ta tadda wannan mummunan lamarin…..

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

61

************

Ba maamah ba ko Amatun cikin faduwan gaba da firgici me girma a cikin zuciyarta ta juya ta Kalli Husnah din kafin ta dawo da kallanta kan maamah da sauri wadda zuciyarta ta buga da karfi sedai Kuma Sam zancen be shigetaba ba hakama batasan tayaya ma zata iya tsayawa tayi wannan maganar da Yara ba Dan haka shiru tayi tareda zubawa Amatu idanuwanta tsawon mintina Babu Wanda yace komai abinda maamah din zata fada suke Jira Amma ga mamakinsu sai kawai ta juya ta sauka batareda tace komaiba.

Amatu sanyi da firgici take Neman shiga Dan haka kasa bin bayan Maamah din tayi ta shige dakinta Husnah ma dakinta ta koma tana tsiyayar hawaye ta dauki wayarta a yau take son barin gidan ta tafiyarta sbd Jin tsanar Dad din takeyi tana shigarta tareda mamayeta.

Mum Aisha kuwa bayan Maamah tabi har dakinta ta zauna Babu magana mara dadin da Bata gaya mata tareda Bata tabbacin Amatu ta Dade da zaman cikakkiyar macen ASH TALBA Kuma wlh wannan cin amana ce Mafi girma Dan haka ta sani itace ta tarwatsa gidan Abeeda ta tarwatsa mata ‘yaya ta rabasu da ubansu sbd yanzu Husnah ta tsani Dad dinta hakama Haydar na ji zai tsanesa Shima Dan haka ta zama balai da masifa a rayuwar ahalin Abeeda.

Shiru maamah tayi har mum Aisha tagama ta fice daga dakin Bata iya cewa komaiba Bare motsawa,

Zuciyarta ce tayi mata Wani irin mummunan nauyi da ciwo tana buga mata ba daidai ba sedai bazata bari ta kwanta ba yanzu da duka gidan yake buqatanta Dan kawo karshen matsaloli.

Duk yanda taso riqe abinda takeji kasa riqewa tayi Dan haka ahankali ta fasa Wani irin kuka mara sauti tana rufe fuskarta da mayafin dayake jikinta jikinta na jijjiga sosai,

Bayan baqin ciki da qunci kusan a yanzu Babu abinda yake mamaye da zuciyarta da rayuwarta,

Bata cikin dadin zuciya,.ta Hana kanta walwala,ta Hana kanta Jin dadi da farin ciki duk akan kada auren Amatun da ASH ya zama cikakkiyar aure Amma Kuma yanzu ana fada mata zancen da Sam Bata yarda da zai iya yiyuwaba.

Amatu Kuwa tana shiga dakinta kasa cin abinda ta dauko tayi ta ajiye zuciyarta na shiga damuwa da fargaban abinda zai iya shiga zuciyar maamah da abinda Husnah ta fada gashi bama zata iya zuwa gurin maamah din ba Dan kuwa bama zata iya kallan fuskartaba bayan abinda aka furta din da Sam batamasan ta Ina zancen ya fito ba.

Babu Wanda ya fito breakfast Shima bayan shigarsa bedroom dinsa kirane birjik ya tadda a wayoyinsa Daya bari akunne ya tafi.

Shirin fita office kawai yayi ya fito ya Tararda ba kowa ya kira Husnah a waya ya sanar mata ta fito su fita tare sbd yanason Bata time dinsa sosai yanda ya kamata.

Qin daukan wayarsa tayi harya Dena Kiran,

Mr Jameel kawai yacewa bayan sun tafi driver ya kawo masa Husnah din office zasu fita.

Tsit gidan yayi kowa cikin damuwa da nauyin zuciya yake musamman Husnah da Maamah Dan Amatu yunwarta kasa riquwa tayi jiki ba qwari ta fito ta sauko qasa ta samu abinci a kitchen taci ta qoshi ta koma sama kenan zata shige bedroom dinta Husnah ta fito dakinta suka Hadu a tsakiyar palon

Kasa riqe zuciyarta Husnah tayi ta tsaya gaban Amatu tareda tarewa cikin daci da tsananin baqin ciki tace

“Menene sunan da zaa kiraki dashi?

Kafin ki jefawa mijin Aminiyar mahaifiyarki kanki ya kamata kiyi tinanin alaqan maamah da mum,

Menene su…..cikin Bacin Rai da baqin cikin maganar idanuwanta suka rufe bata tsaya komaiba ta kama hannun Husnah din da karfi ta fizgeta zuwa hanyar palon Dad din nata Dan Bata amsar maganarta a gabansa sedai ko taku biyu bataiba taji an riqo nata hannun tana juyowa Taga maamah tana mata Wani irin kallo idanuwanta jajir.

Magana zatai sbd idanuwanta da suka cika da bacin Rai da baqin cikin abinda Husnah din ta fada mata maamah ta katseta Kai tsaye da cewa

“Ina Zaki?

Ina Zaki jata kuje??

Sakin hannun Husnah din tayi tareda kallan maamah din bacin ranta Baya boyuwa tace

“Maamah kinji kalaman data jefeni dasu?

Kin….

Daga mata hannu maamah tayi cikin Bacin Rai da baqin ciki tana cewa

“Komai aka fada Amatu kece kikaja,

Meyene alaqarki da abinda suke fada din?

Shin kin menene ma ya hadaki guri Daya da ASH din harma wanna abin duka yake neman lalacewa?

Katseta Husnah tayi hawayen baqin cikinta na qaruwa tace

“Maamah wlh a dakin dad ta kwana….

Shiru maamah tayi jikinta na rawa tana kallan Amatun da dukkanin bacin Rai hakama Amatun sai alokacin hawayen baqin ciki me tsananin gaske ke ciko idanuwanta

 maamah tace

“Me Husnah ke fada?

Saukowa hawayenta sukai tana kasa cewa komai saima nauyi da zuciyarta tayi kafin tayi magana baqin ciki ya Saka idanuwanta Neman juyewa ta dafa Bango da sauri sbd jirin Daya debeta zai zubar Dan Bata dauka maamah zata jefeta da wannan tambayar ba.

Kuka Husnah ta sake fashewa dashi tana ihun mum dinta mutuwa zatai idan taji wannan mummunan labarin,

Hakama Amatu taci Amanar mum dinsu da Haydar.

Gaba Daya hargitsa gurin tayi da kukanta da maganganunta da suka Saka Amatu barin gurin zuciyarta na nauyi da tsananin damuwa da bacin Rai da fushin da batama San tanada shi ba.

Maamah kasa cewa komai tayi sai kawai ta bar palon ta kira ASH da kanta akan tanason magana dashi idan Yana gida.

Baya gida ya sanar mata Amma zai dawo da wuri a ranar.

Mr Jameel kuwa drivern da aka Saka ya kawo Husnah office din Dad dinta ya sake kira Amma driver ya sanar masa Husnah Bata fito ba.

Amatu bayan shigewarta daki kuka ta saki me ciwo da dacin Rai sbd lamarin yafara yimata yawa,

Ta rasa tayaya ta rasa so da kauna tareda yardar mahaifiyarta..

Kuka takeyi sosai Wanda ma batasan Yaya takejin Yana zuwaba Yana sake tayar da zuciyarta zuwa wuya.

Wayarta anty Farha keta kira Amma takasa dauka Dan haka ta kira khaltume wadda sukai tsit sbd ihun kukan da Husnah keyi tana fasa kayan palon saman ko zuciyarta Dake balbala da wuta zata sauka Amma Sam Babu abinda takeji a zuciyarta da jikinta bayan zafin baqin ciki.

Maamah Dake dakinta tana Jin ihun Husnah din da tashin hankalin datakeyi tana ambatar sunayen Amatu Dana mum dinta Amma Bata motsaba daga dakinta sbd yau lamarin ya isheta Babu abinda take buqata bayan barin gidan itada Amatun Dan ita yanzu bama zata iya bari Abeeda ta dawo ta tadda Amatun a gidan ba bare tasan meya faru.

Khaltume ce ta sanar da anty Farha abinda yake faruwa cikin damuwa gashi mum Aisha ta tattara ta fita batama gidan bare dakatar da Husnah wadda gaba Daya t zare Babu abinda take gani bayan Dad dinta da Amatu suna cin Amanar mum dinta.

Ita kanta Amatu datake dakin tana Jin duk abinda Husnah din keyi hakama kuka takeyi sosai Dan kuwa tasa bacin Rai da tsananin kukan da Maamah Tasha Koda Bata fada ba,

Ita komai ya isheta itama batason zaman kaman yanda Husnah take fadan bazata iya zama inda Amatu take ba itama Hakan takeji sbd abubuwan sun mata yawa.

Anty Farha Kam tashi hankalinta yayi Dan haka ta kira wayar mr Jameel ta sanar masa anata tashin hankali a Mansion din.

Satar kallan ASH yayi Wanda yake amsa waya ahankali yaga yanda yake wayar hankali kwance da nutsuwa.

Yanda Mr Jameel yake satar kallansa ya tabbatar masa da magana me mahimmanci Dan haka ya Dan takaita wayar ya kashe Yana kallansa yace

“Uhumm Ina ji”

Cikin damuwa da Dan sauke Kai mr Jameel din yace

“Ana rigima ne a mansion tsakanin Husnah da L.A”

Shiru yayi tareda dagowa ya zubawa Mr Jameel din idanuwansa Yana nazarin zancen sbd baijin akwai abinda zaisa ma ko hayaniya Husnah tayi da Amatu Bare rigima,

Wayar da maamah tai masa ce ya dawo masa.

Wayarsa ya dauka Kai tsaye maamah din ya kira.

Tana daf da katsewa ta dauka a natse sedai muryarta Sam Babu dadi da alamu kuka tai ko makamancinsa.

Baima yi mata magana ba sai kawai ya kashe wayar Yana nazarin abinda zai zama rigimar,

Idan har Husnah zatai hayaniya da little Abeeda akan maganar aurensa dayake kanta ne dakuma mum dinta hakama Asmau yasan Daman tanada damuwa da auren.

Idan maamah tana cikin wannan halin to little Abeeda na cikin Wanda ya fisa,

Dagowa yayi ya Kalli mr Jameel Kai tsaye yace

“Ayiwa Maamahn little Abeeda komai su wuce tareda Husnah Greece”

Kaman Mr Jameel na Jira ya gyada Kai da sauri Dan kuwa yau ba sai gobe ba zai tura su Lagos suna can zai qarasa musu komai su wuce.

Fitowa sukai Kai tsaye mota ya nufa da sauri aka Bude masa ya shige suka  nufi gida Yana kashe wayoyinsa tin a hanya.

Koda suka iso Husnah tafara gabalaita da kukan datakeyi da tashin hankalin hakama maamah dole tazo ta riqeta tana kokarin dawo da ita hankalinta cikin kulawa da damuwa me tsananin gaske.

Anty Farha ta riga su ASH isowa Dan haka ta ringa buga dakin Amatu wadda ta rufe kanta data cikin tayi kuka harta galabaita sbd maganganun da maamah ta shigo ta fada mata masu kama da tafiyarsu zasuyi subar gidan hakama batajin zata sake barinta ko fitowa daga dakin nata har su samu barin gidan.

Tashi hankalin anty Farha yayi musamman ganin palon kaman anyi damben balai a cikinsa sai tsoron ko Wani abin ya faru kafin su zo ya shigeta ta ringa buga kofar tana Kiran sunan Amatun,

Gasu maamah da Husnah a palon hakama su karima suna palon qasa a tsaye jiki duk yayi sanyi sbd Basu taba ganin wannan tashin hankalin a gidan ba bayan na gobarar da Akai.

Babu tsammani sukaga ASH a cikin palon kallo daya yayiwa gurin gaba Daya ya Kalli Husnah Dake jikin maamah tana kuka har lokacin ya nufi kofar dakin Amatun Kai tsaye daidai ta budewa anty Farha kofan dakin Dan haka anty Farha janyewa tayi ta basa kofa ya shiga Kai tsaye Yana kallan idanuwanta dasukai jajir ko tsayuwar arziki Bata iyayi.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

62

*************

Duk tashin hankalinda Husnah take ciki Bude jajayen idanuwanta tayi ta zubawa kofan dakin Amatun Daya shige.

Maamah ma kusan mutuwar zaune take Neman yi sedai kafin suyi Wani motsi mr Jameel dayake siqe dasu Kiran Farha yayi Yace tace su fito ga motar zuwa airport na jiransu ya fasa bari gobe su tafi yau ze ingizasu Lagos suje su Jira visa daga can su wuce hankalinsu suka ya kwanta Dan idan ba zuwa sukai suka dubo madame Abeeda sukaga halinda take ciki bazasu bari a zauna lafiya ba tinda yanajin komai dayake faruwa a cikin gidan a bakin anty Farha gameda auren.

Mum Aisha ma da isowanta gidan kenan Mr Jameel yace Maza Maza su fito jiransu akeyi jirgi ze tafi ya barsu.

Mamaki me tsananin gaske dukkaninsu suka shiga musamman maamah da mum Aisha da basusan da tasu tafiyar ba tsoro ma ne yake Neman kama mum Aisha Amma Kuma tinda mr Jameel yace tafiyar zasuyi to tabbas ASH ne ya Bada wannan umarnin gashi babu me ikon tambayar dalili sedai Babu Wanda yakeda raayi na tafiyar a cikinsu a dai wannan halin da ake ciki har gwara maamah tanason ganin Abeeda Kam Amma ba yanzu da ake cikin wannan tashin hankalinba sedai Babu gurin musawa ko fasawa.

AmatulMaleek dinma Basu samu Gani ba anty Farha itace ta hado kayan maamah tana sake tausarta da maganganun nasiha da Sam Babu me shigar maamah din tayaya zata bar Amatun a gidan bayan ASH Yana gari.

Kaman wasa sai gasu a mota an wuce dasu airport zuciya fal tashin hankali da mamakin Daya kasa barinsu tantancewa Saida suka daga zuwa Lagos suka tabbatarda dai kuwa tafiyar zasuyi ba Shiri ba sanarwa.

Basu dawo hayyacinsuba Saida suka samu kansu a Lagos tareda anty Farha wadda zata jagoranci tafiyar duk da itama ba shiri Amma ta yarda ta biyosu su tafi din Dan masifar kowannensu yawa ne da ita gwara akaisu gurin Abeedan idan qarasa ta zasuyi da masifarsu su qarasata acan din.

Maamah da mamaki da firgici ya tashi kasheta sai gata a kwance ciwonta ya tashi a Lagos anty Farha taqi fadawa ASH Dan kadama Amatun taji suka kwasheta zuwa asibiti zata warke ta tashi su tafi.

*****

AmatulMaleek kuwa batama San su an tattara su kaman kayan kunya ba anbar gidan dasu sbd zazzabi me karfin gaske Daya rufeta hakama Sam ta kasa Dena hawaye sbd tasan maamah yanzu zai yiyu tasan komai gameda mu’amalarta da ASH din.

Duk yanda yake rarrashinta da lallabata sbd zazzabin Daya rufeta Bata iya dawowa daidaiba Dan haka Koda magrib tayi dole aka kira likita tazo ta dubata Batai mata komai ba maganin zazzabi kawai ta Bata tareda rage Mata zafin jikinta ta wuce.

Su khaltume sun gyare gidan tsaf ya koma kaman Babu tashin hankalin da Kai cikinsa yau din sun kunna AC na koina tareda kunna qamshi dasuke tashi a hankali cikin sanyi da nutsuwa.

Abincin ranar ma a dakin Amatun aka Jere musu shi lokacinda ya fita Sallahn ishah.

Bayan dawowansa da kansa ya samu ya lallabata taci abincin kadan tayi wanka ta kwanta.

Kadan yaci abincin Shima ya koshi ya miqe tsaye tareda daukanta suka bar dakin zuwa bangarensa.

Suna zuwa kwantar da ita yayi ya rufe ya wuce toilet ya shige,

Wanka yayo hankalinsa kwance yayo brush da sauran abinda zaiyi ya fito ya shirya cikin kayan bacci da qamshinsa yazo ya kwanta cikin jikinta,

Jin jikinta da zafi sosai ya sanyashi zare rigarsa ya janyota ahankali ya shigar jikinsa ya rungumeta dakyau Yana Jin zafin jikin nata na shigarsa Yana Dan sassauta mata shi.

Bacci sukai a natse har safe tana fama da Dan zazzabin haka suka sake wuni batareda ya fita koinaba Yana kulawa da ita.

Sai da Rana ta fahimci Babu kowa a gidan ta sauko qasa Dan zuwa gurin maamah anan aka sanar mata tin jiyan suka wuce Lagos zasu Greece.

Da mamaki ta dawo sama ta dauko wayarta a bedroom dinta ta Saka Kiran wayar maamah gabanta na faduwa da tafiyar tasu.

Wayar Bata shiga dan haka ta rasa wa zata kira Dan daga mum Aisha har Husnah batasan waye zata iya kiraba tinawa da cewan anty Farha ma ance tana tareda su ya Sakata Kiran anty Farha din tana Jin zuciyarta na shiga damuwa.

Anty Farha Koda Amatun ya kira sun dawo gida da maamah Amma dai bacci takeyi Dan haka Bata sanarwa Amatun ba tadai ce mata tana bacci sbd dan zazzabin damuwa.

Shiru Amatun tayi sbd harga Allah tana tsananin gudun bacin ran mahaifiyarta da damuwarta,

Sam Bata son ganin maamah cikin damuwa da bacin Rai shiyasa ma takejin duk jikinta yayi sanyi da auren Wanda batama San tayaya zata iya cirewa kanta tsananin son ASH TALBA ba daya Riga yayiwa zuciyarta illan da Babu gyara,

Tayaya zata iya Rayuwa batareda shi din ba,gashi maamah da gasken gaske ta tsani auren bare alaqarsu.

Cikin nutsuwa da kulawa anty Farha ta kwantar mata da hankali akan maamah din da fushinta tareda nuna mata hankalin maamah din akan tafiyarsu yake yanzu komai abarsa saisun dawo tukuna.

Daqyar anty Farha ta iya kwantarwa da Amatun hankalin harta samu ta zauna taci abinci sosai Tasha magani ta kwanta zazzabinta Koda yamma tayi ya warke Dan haka Koda ya dawo daga yar fitan da yayi sosai yaji dadin ganinta.

Da daddare kwanan Kwanciyar hankali sukai Dan kuwa duk Wani kalan sanyayyan love ya nuna mata shi musamman data sake narke masa tana rikitasa da sanyin jikinta tana kashesa da idanuwanta.

Washe gari Bai fita ba sai 11 sbd baccin da Basu Wani yi ba da daddare sai bayan asuba suka samu baccin kirki.

Khaltume da sauran masu aikin gaba Daya sun Dena hawowa sama idan har Yana gida sbd sakewa yayi sosai a cikin gidansa Yana rayuwar da little Abeedan ce kawai zata iya fadanta.

Cikin kwanakin da suke gudanar da sabuwar rayuwar da daga shi har ita yanzu ne suke sake sanin matsayi da girman abinda yake zukatansu,

Su maamah kuwa duk kwanakin da sukai a Lagos kafin suka wuce Babu me walwala tafiya ce Akai ta bacin Rai da damuwa Dan kuwa ko Husnah datake Jin tana tsananin son baro gidan zuciyarta ta kasa nutsuwa daga baqin cikin baro Amatu kadai a gidan Kuma Dad dinta na gari,

Ita kanta maamah tashin hankalin dayake cin zuciyarta kenan duk da tana Jin sanyin son ganin Abeeda Amma murnarta a dishe take da baro Amatun Dan haka ta duqufa da fadawa Allah ya kawar da barnar datake gudun afkuwanta.

Mum Aisha dai kusan ita tafiyar tazo mata a biyu ne,

Tana son zuwa ta isarwa da Abeeda labarin auren haka Kuma tana gudun kafin su dawo Wani abu ya faru tsakanin ASH da Amatun Azo a samu ciki su shiga uku su lalace da wannan mugun labarin.

Maamah na amsa wayar Amatu sedai Sam Babu sakewa gaisawa kawai sukeyi tayi mata Se anjima ta kashe wayarta Dan hakan yasa duk tayi waya da maamah din take wuni cikin damuwa da qunci ASH na gane Hakan sai ya hanata kunna wayarta kusan lokuta da dama wayar a kashe take wuni.

******Satinsu uku da tafiya Shima tafiya ta kamasa zuwa South Africa Dan haka suka shirya tareda ita ya tafiyarsa Daga can Shima zai tafi gurin Abeedan Dan haka zasu hade acan dasu Maamah su dawo gaba Daya.

Tafiyansu South Africa ya Sakar mata da sanyin jiki sosai sbd sanyi Daya shigeta hakama zazzabin dare ke damunta kullum idan ba cikin jikinsa ba Bata iya bacci Shima kusan yasan Bata iya baccin sai ajikinsa Dan haka ya Saba kwanciya kwata kwata yanzu ba Riga sbd ita.

Satinsu biyu a South Africa suka fara Shirin wucewa Greece sedai jikinta yafara tsananta daurewa kawai takeyi.

Washe garin ranar da zasu wuce kira yazo masa daga Greece din jikin Abeedan ya tashi sosai haka kawai anrasa meya rikitar da jikin nata Dan haka hankalinsa ya tashi suka wuce ba Shiri.

Koda suka Isa itama Amatun jikinta sai ahankali sosai yake tarairayarta su samu Isa Taga likita duk da ta nace akan sanyi ne kawai.

Da daddare jirginsu ya sauka motan da zata daukesu na zuwa ta kwashesu suka Isa masaukinsa Wanda duka su maamah dasu Husnah acan suke gida ne me Dan girma da kyau da tsari sosai.

Suna isowa anty Farha ce tafara fitowa ta tarbi Amatun wadda tafara karfin halin daurewa tana Hana yanayinta bayyana duk da tanajin jikin.

Maamah Bata gidan tana asibiti itada Husnah Dan haka daga mum Aisha Dake dakinta tana bacci sai Farha.

Sanin anty Farha zata kula da ita sosai ya sakashi barinta a gurinta Bai Wani Bata lokaci ba wanka kawai yayi da salloli ya fito suka wuce asibi Shida mr Jameel ita Kuma ta samu sallah da wanka ta kwanta bacci me qarfi da wahala.

Maamah da Husnah zaune suke a asibitin jigum jigum hankalinsu a tashe da yanayin da Abeeda sai gashi ya iso.

Idanuwa Husnah ta zuba masa tana kallan Wani irin freshness da lafiyayyar hutun Daya qarawa komai nasa kyau da aji da kwarjini,

Maamah kasa kallansa tayi Saida ya iso cikin mutuntawa da girmamawa suka gaisa tana masa barka da zuwa Dan duk basusan da Amatu yazo ba.

Amsawa yayi tareda wucewa Kai tsaye zuwa gurin likitocin Dake Neman ganinsa.

Ya jima sosai a ciki kafin ya fito ya Isa gurin Abeedan wadda ta samu bacci sedai Kuma abinda likitoci suka sanar masa Daya Sakasa farin ciki shine tashin jikinta ya Saka wasu sassan jikinta sun fara aiki Dan suna Saka ran zaa iya fara Sakata wheelchair ana Dan zagayowa da ita.

Su kansu su maamah sunyi farin ciki da wannan cigaban da aka samu sedai Kuma abinda yake tsinkar dasu shine abinda aka fada na cewa duk tsanani kar abari ta shiga shock na Wani abu ko damuwa haka.

Wannan Kalmar itace kalman data Saka zuciyar Husnah tsananin farin ciki me girman gaske bayan tsawon lokaci Dan kuwa wanna gargadin na likitoci na nufin dole Dad ya dakatar da maganar aurensa daga zuwa Wani matsayi na gaba.

Maamah kuwa shiga damuwa da tinanin tayi me zurfi itama Dan kuwa tasan itama wanna gargadin na buqatan itama ta takawa Amatu mugun burki akan komai na gidan ASH da ASH din kansa.

Shi kansa ASH din shiru kawai yayi sbd baisan Wani abu ne zaisa su bawa Abeeda shock ba tinda so sukeyi ta tashi hakama Babu Wani damuwa a rayuwarsu da zasu ce zai Sakata shock.

Se tsakar dare suka dawo gida

Suna shigowa sama ya Haye maamah da Husnah Kuma dakin maamah din suka nufa ga Mafi girman mamakinsu Amatun suka tarar kwance har lokacin bacci takeyi.

Daga maamah har Husnah sakin baki sukai suka kallanta Husnah zuciyarta na harbawa da rikicewan ganin Amatun a daidai lokacinda akace baa buqatan mum dinta da bacin Rai ko labarin bacin Rai komai qanqantarsa sbd barazana ga rayuwarta duk da mum din Bata saniba Amma ai Dad dinta zai iya abinda zata iya fahimtar Wani abin.

Itama maamah nata tinanin kenan tayaya Amatu zata kasance inda Abeeda take duk da Abeedan Bata saniba Amma ai zaa iya samun matsalar magana ko tsautsayi.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

63

*******

Husnah saukar da idanuwanta tayi akan hasken Amatun Daya Qaru sosai hakama maamah ma Amatun take kallo kaman sabuwar baquwar da Basu taba Gani ba,

Har lokacin da Husnah ta qaraso bakin gadon tana kallan fuskar Amatu batareda ta gasgata Dad dinta zai iya dauko Amatun ya kawo har inda mum dinta take ba ta waiwayo Baki a sake ta Kalli maamah tace

“Wannan AmatulMaleek ce fa,

Dad ne ya zo da ita fa.” Kasa qara cewa komai tayi sbd kasa daukanta da kafafunta keyi ta silale ta zauna kan kujeran Dake dakin tana dauke kallanta daga Amatun zuciyarta na shiga Wani hali.

Maamah ma kusan silalewan tayi ta zauna tana kasa dauke idanuwanta daga Amatun Dan ita kaman ba Amatun data Haifa bace take Gani a gabanta Dan sauyawanta yayi yawa.

Anty Farha ce ta shigo dakin Dan sanin su maamah sun dawo dole ana Nan ana magana Kila sbd tin farko tacewa Amatun ta sauka a dakinta Amma tace dakin maamah zata sauka batasan Husnah na tareda maamah bane a dakin.

Tahowa tayi tana yi musu barka da dawowa tana kallan reaction nasu Daya kasa boyuwa da ganin Amatu.

Amatun tafara Dan kira tana tadawa baccin,

Husnah na ganin Hakan tayi hanyar toilet ta shige ta rufo kofar Dan zuciyarta zata iya tsayawa daga bugawa idan Amatun ta tashi taganta dakyau.

Tana shigewa toilet Amatun na farkawa ta Bude idanuwanta ahankali tana Dan motsawa cikin kasala da mutuwar jikin.

Tashi zaune tayi ganin maamah da anty Farha,

Kallan maamah takeyi tana sake gyara zamanta daga tashin datai daga kwance farin cikin ganin mahaifiyarta na cike fuskarta Yana bayyana ta Bude Baki cikin kulawa da kewa tace

“Maamah sannu da dawowa,nayi kewanki sosai”

zama maamah din tayi tareda sauke numfashi me nauyi tana danne tarin abubuwan Dake ranta da tarin tambayoyinta da mamakinta ta amsawa Amatun tana Dan sake mata fuskarta tana mata barka da zuwa itama tana Dan soka tambayar ya Akai haka kawai tazo din ba sanarwa Kuma tareda ASH ko har anyi hutu ne?.

Dagowa Amatu tayi ta zubawa maamah din idanuwanta sbd a bayyane tambayar itace abinda yafi farin cikin ganinta mahimmanci.

Bude Baki tayi a sanyaye tace Hutu takeyi Kuma ba kowa gidan ne shiyasa aka taho da ita.

“Daga Abujan kuka taho Nan Kai tsaye kokuwa Kuma Saida sukai kwanaki a Lagos dinne?

To a Ina kika sauke ke a Lagos din tinda ke Daya ce,nasan kin zamar masa dawainiya da kinyi zamanki ai muna kusa da dawowa tinda gasu khaltume a gidan dasu karima duk zasu debe Miki kadaici da kewa??

Numfashi Amatu ta sake saukewa tana bawa maamah din amsa Kai tsaye da cewa

“Banice nace zanzo ba cewa Akai na shirya shine aka taho Dani,Lagos din Kuma bamuje ba daga Abuja muka wuce”

Amsar data bawa maamah din ya saka maamah Jin Dan sanyi sanyi ta Kalli farha dake tsaye tana kallan iKon Allah tace

“Farha a dakinki zata zauna ko tinda Nan ni da Husnah ne zamu matsu kuka Kinga ba jituwa sosai yanzu tsakaninsu kuje can dakinki kaman zaifi Kwanciyar hankali.

Ita kanta Amatu tafi son komawa dakin anty Farha din sbd kallan da maamah ke Mata ko anan din ta kwana to bazata rintsa ba sbd tambayoyin da maamah zata ritseta dasu.

Saukowa Tayi daga gadon ta miqe tsaye tana kokarin nufar kofa maamah ta bita da kallo sosai ita gaba Daya Amatu ta sauya mata tsoro ma Hakan ke Bata tareda Sakata cikin firgicin irin Hutu da Amatun ke samu tana sauyawa zuwa kaman matar ASH din dai da gasken.

Fitowa sukai dakin har lokacin bacci ne cikin idanuwan Amatun gashi Daren yaqara tsalawa sosai.

Hanyar sama Farha ta kalla ta dawo da kallanta kan Amatu kafin ma tayi wata magana motsin saukowa saman sukaji.

Amatu bataji motsinba Dan haka ita hanyar kofar dakin anty Farha din take sake nufa kanta tsaye.

Anty Farha ce Taga saukowan ASH din Dan haka ta dakatar da Amatun tana Dan gaidasa a natse tareda sake masa sannu da hanya ta juya ta wuce hanyar bedroom din ta shige.

Cikin sanyi da kasalan bacci Amatu take kallansa tana Dan lumshe idanuwanta sbd qamshinsa Daya shiga hancinta lokacinda ya matsota sosai.

Shima kallanta yakeyi cikeda kulawa Yana kamo hannunta zuwa jikinsa Yana taba fatan wuyanta ahankali Dan Jin zafin jikinta datake yi da daddare cikin kulawa da sauti me tsananin taushi yace

“Yaya?ya kikeji yanzu?

Kina Jin damuwar jikin ne haryanxu?

Shud I call likita yazo yanzu ya dubaki?

Kinci abinci?

Zaki iya bacci a tareda agurin Farha dinne??

Shigewa tayi jikinsa da kyau cikin sanyi ta shaqi qamshinsa tana Dan lumshe idanuwanta tareda gayosa da hannuwanta kafin ta Bude Baki qasa qasa a sauti me laushi itama tace

“Naci abinci,banajin komai yanzu bacci kawai nakeji,no need a kira likita yanzu zuwa da safe zan warware”

Rungumeta yayi Yana Bata Daman sake shaqansa da kyau kafin ya Dora lips dinsa ahankali tsakiyar fatan kunnenta ya sauke mata kiss ahankali ya dago Yana kallan idanuwanta Dake Wani lumshewa yaji Wani irin duk kasala na cikesa ya Bude Baki yace

“Baccin fa?Zaki iya gurin Farha?muje sama ki kwana acan hankalina zai rabu da baccinki”

Tafin hannunta ta Dora akan gefen fuskarsa ta shafo cikin Wani yanayi na tsananin so da Baya boyuwa da shegen feelings tace

“Zan kwana gurin anty Farha,su maamah fa na gidan kaje ka huta da kyau tinda ka gaji baka huta ba tinda muka iso,Yaya jikin Mum Abeeda??

Bakinta ya fara kalla ya shafi lips dinta da yatsar hannunsa kafin ya amsa mata da jikin Abeedan alhmdlh sauki da cigaba ya fara zuwa.

Daqyar ya barta ta tafi dakin anty Farha ta shige kafin ya juya saman Shima bayan ya dauki ruwa.

Anty Farha da batai tinanin dawowan Amatun dakin ba kallanta tayi da mamaki tana cewa

“Yaya na ganki kuma?

gado dakin Amatun ta fada tana cewa

“Anty Farha kin manta maamah dasu mum Aisha na gidan Nan duka ne”

Daga haka batama iya cewa komaiba ta gyara Kwanciyarta baccin ta sake rufe idanuwanta sai numfashin baccinta anty Farha taji Yana fita ahankali.

Bata ce komaiba anty Farha Se takaicin su mum Aisha din Daya rufeta harma da maamah wadda ta Hana rayuwar Amatun yin gaba bare Baya,

Data rufe ido ta amsa auren da wata haukar su Husnah din sedai suyi bayan idonta tinda Koda auren Amatun a hannun ASH ko Babu kusan gidansa a hannun maamah din yake tinda matarsa ta kwanta Amma sun ishi kowa da masifar yau daban gobe daban,wlh suna tada rigima Mr Jameel zata fadawa a sake mayar dasu inda suka fito ko a tura su Umrah can suje suyita fama.

Washe gari da safe Mr Jameel anty Farha tafara kira tinda safe ta sanar masa su maamah zasu fara halinsu Dan kuwa da safe Kiri Kiri maamah ta hana Amatu fitowa daki har Saida ASH ya fito ya fice daga gidan.

Shiru Mr Jameel yayi Yana nazarin maganarta kafin ta Sako masa zancen turasu Umrah ko Maidasu gida.

Cikin mamaki yace

“Wace Umrah Kuma?suje har gaban dakin Allah su rokesa auren ya mutu kenan?

Suna tashin hankali Yola zan turasu gaba dayansu acan jirgi ze diresu su zauna gidansa na can shikenan acan zaa samu Yan aiki a zuba musu, Naufal ma dayake asibitin Abuja transfer zaa masa zuwa can din su qarata”

Shiru anty Farha tayi sbd idan antura su can madame Abeeda Dake kokarin dawowa Kuma Yaya zaayi da ita ga Kuma zancen Amatu tinda ana cewa maganar auren dole boye mata zaayi kota halin Yaya,ita Sam bataga Wani amfanin boye maganar bama tinda dai auren fa bame warwarewa bane gwara a fada kowa yaji me Rabon ganin Badi ya Gani me qararrun kwana Kuma haka Allah yaso.

Shiru me Jameel yayi Dan Shima dai yasan fadawa madame Abeeda tana wannan halin gaskia bame yiyuwa bane kaman yanda Kuma a gurin ASH boye aurensa ace ya ajesa gefe kwata kwata for now bame yiyuwar bane.

Bayan fitan ASH Amatu ta samu fitowa bayan riqeta da maamah tayi a daki da maganganu da Kai tsaye duka na bugun cikinta ne taji duka abinda ya faru da suka baro ta ita kadai mansion din.

Husnah tareda Dad din ta fice Dan haka har lokacin Bata Hadu face to face ba da Amatu.

Mum Aisha kuwa da safe Se ganin Amatu tayi a gidan itama kusan mamakinta Bai boyu ba ringa kallan Amatun tayi tana shiga tashin hankali da tsoro Dan kuwa Babu abinda yazo tinani da zuciyarta Kai tsaye Amatun ta gama zama cikakkiyar mace sbd komai nata ya sauya.

Tareda anty Farha da mum Aisha din sukai breakfast a dining tana kaucewa kallan mum Aisha dayayi mata yawa Dan kuwa mayyar kallan dole mum Aisha din ta koma tana rasa tinani da zargin kamawa.

Sai guraren 12 suka fito gaba dayansu aka tafi asibiti dasu suka je duba Madame Abeeda.

Koda suka Isa asibitin Amatun na sanye da doguwar glazisias pencil gown me taushin data lafe a jikinta kalar dark purple Se jacket me laushi ta Balenciaga kanta ma ba Wani kayan nauyi rolling ne mara nauyi Se glasses Dake fuskarta sbd Rana da haske sosai da bataso.

Ita da anty Farha ne a Bayan sosai suna magana Se maamah da mum Aisha a gaba sunyi musu Nisa akwai tazara a tsakaninsu sosai.

Suna Isa dakin Kai tsaye mum Aisha ta Bude batareda tayi knocking ba sbd sanin ASH na ciki fatanta ASH din na riqe da Abeedan Amatu ta Gani.

Suna shigowa Husnah Dake gefen Abeeda bayan angama dorata a wheelchair sedai Bata gama zaunuwa ba gyarata Husnah keyi Dad din ya shigo dakin a natse daga gurin gama ganawarsa da likitoci akan tafiyan Abeeda.

Mum Aisha kasa hakuri tayi ta qaraso ahankali daidai Husnah zata gyarawa mum dinta rigar jikinta ta Kara mata kafarta take Husnah din ta fada kan Abeedan da qarfin gaske Wanda yayi daidai da isowan ASH ya janye Abeedan Yana janye Husnah gefe wadda ta dago da sauri ta kalli mum Aisha din cikin mamaki me girma da tashin hankali sedai da ido mum Aisha din ta nuna mata kofa da su Amatu ke kokarin shigowa anty Farha na gaba Amatu na bayanta a natse.

Da sauri Husnah ta Maida kallanta kan Dad dinta Dake gyarawa Abeedan zama a natse da kansa cikin kulawa,da sauri ta dawo gurin Dad din ta marairaice fuska idanuwanta na cikowa da hawaye tana cewa

“Dad Babu abinda ya same ta?banganiba bansan ya Akai na fado kanta na daki fuskanta sosai bansaniba,ko zaa kira likita ya dubata idan…..

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

64

************

Katseta yayi Kai tsaye a natse Yana share fuskan Abeedan da handkerchief dinsa me qamshi yace

“Ba buqatan Hakan sbd Baki Riga kin fada mata din ba she’s ok”

Maamah ce ta fice dakin daidai Amatu na Sako Kai a dakin Yana zaunawa a hankali gefen Abeedan tareda kama hannunta Daya da nasa Yana kallanta cikeda kulawa ya furta mata sannu a natse da sauti me taushi na kulawa.

Anty Farha datake kallansa juyowa tayi a sace ta Kalli fuskar Amatu wadda ke kallan Madame Abeedan a natse tareda Bude bakinta cikin sanyi da kulawa ta ambaci sunanta da mum Abeeda kafin ta Dora da mata sannu da fatan samun lafiyanta.

Baisan da shigowansu ba Saida tayi magana yaji saukan muryanta cikin kunnensa ya dago idanuwansa ya zuba a inda take tsaye tana Maida kallanta kan fuskan mum Abeedan data dago ta zuba mata nata idanuwan tana kallanta.

Mum Aisha da Husnah ma Amatun suka zubawa idanuwa Dan ganin yanayinta da suka kasa karanta,

Anty Farha kuwa ASH din ta sata kallo kafin ta Maida kallanta kan hannunsa Dake riqe Dana madame Abeeda a sarke.

Dawo da kallanta tayi kan Amatu datake sake kallan mum Abeedan cikin kulawa tana mata sannu.

Har lokacin Madame Abeeda idanuwanta na kan Amatu datake kalla a natse duk da Bata iya magana kowa na iya ganin kallan mamaki ne takewa Amatun Wanda suke alaqanta Hakan da kallan mamakin girma dataga Amatun tayi sosai haka tana daukan ido duba da yanda Koda ta baro Amatun tana yarinyarta.

Shiru dakin ya sake dauka Se idanuwasa Dake kan Amatun wadda taqi kallansa qarshe ma itama bayan Maamah tabi ta koma Dake qaramar palan dakin ta zauna tana kokarin Ciro wayarta daga aljihun jacket dinta Duk da layinta bayayi Kuma batada layin qasar Amma tanason duba Wani abin ne.

Anty Farha ma fitowa tayi hakama mum Aisha wadda ba haka taso ba so tayi ASH ya rikice Amatu ta samesa Yana tarairayar matarsa,.itama Husnah Hakan taso AmatulMaleek da idonta Taga yanda Dad dinta yakeson mum dinta fiyeda kowa bare ita da itace take Kai masa tallan kanta.

Zaunawa sukai dukkaninsu Babu me cewa kowa komai sai wayoyinsu dasuke latsawa,

Shi kadai ne a dakin sai Abeeda dan haka Husnah ta kira mummyn porthcrt suna magana ta sanar mata da abinda likitoci sukace gameda dakatar da duk Wani abin dazai daga hankalin mum dinta zaa iya samun babbar matsala kafin ta Dora da yanda Dad dinta yake kulawa da mum din tana qarawa da duk abinda tasan zai quntata zuciyar Amatu daga qarshe Kai tsaye ta sanar da mummyn porthcrt din da suyiwa Dad magana Dan Allah ya aje maganar aurensa kwata kwata har sai mum ta samu lafiya da qarfin da zata iya karban zancen.

Dayake tana sane ta isar da sakon zancen a gaban maamah da Amatun harda hawaye ta ringa hadawa dasu tana rokon mummyn da su roki ASH din Shima a bari mum dinta ta samu lafiya.

Maamah Dake zaune kusan zancen shigarta ya ringa yi Kai tsaye itama Dan bama sai an roka ba abinda ya kamata ace ya faru dinne wato a kashe zancen auren kwata kwata ma sbd lafiyar Abeeda.

Amatu kuwa Sam Bata nuna alaman ma zancen ya shafeta ba duk da zuciyarta gaba Daya tayi Wani irin sanyi d nauyi lokaci Daya,zazzabinta ma taji Yana Neman dawowa Dan haka ta dago ta Kalli anty Farha a hankali batai magana ba anty Farha din ta rigata da cewa

“Muje tinda mun duba Madame abeedan anjima ko gobe saimu sake dawowa zazzabi nakeji da ciwon Kai”

Miqewa tayi itama Amatun jiki a mace ta miqe mum Aisha ranta fes take kallansu da walwala a fuskarta tace itama gidan zata suka wuce aka bar maamah da Husnah.

Suna barin asibitin Shima Yana barowa sedai Wani gurin ya tafi Se dare ya dawo gidan sbd ga dukkanin alamun jikin Abeedan da ita Kila zasu koma.

Su Amatu kuwa tinda suka dawo abinci kawai taci tayi sallah ta kwanta har bacci ya dauketa.

Anty Farha ce ta zauna Palo tana wayoyinta da sauran abubuwanta har yamma ta tada Amatu tayi sallah suka sake zuwa suka dubo Madame Abeedan acan sai dare Suma suka dawo gaba dayansu harda su maamah da Husnah da batawa Amatun magana har lokacin itama ko kallan inda Husnah din take Batayi.

Da daddare bayan kowannensu yaci abinci yayi Shirin Kwanciya duk sun shige Banda anty Farha dake Palo tana Aiki a laptop tana waya da Mr Jameel hankalinta kwance.

Shigowan ASH TALBA ya Sakata barin palon ta tattara ta koma daki duk da ya Haye sama.

Tana shiga dakin Amatu na fitowa daga toilet se alokacin tayi wanka sbd a kasalance tayi wunin gaba Daya zuciyarta ba dadi Sam.

Kallanta anty Farha tayi tace

“Yaya jikin naki?

Kinqi yarda kiga likita hakama kingi bari ASH ya Aiko likitan haka Zaki warke batareda magani ba?”

Kasa magana tayi ta shafa Mai kadan sbd sanyi da turare me sanyi ta dauki kayan baccinta Riga da wando masu Dan kauri ta Saka tana kokarin Hawa gado anty Farha tace

“Babu ruwan Shan ki na dare idan kin farko ban shigo dasu ba na manta kije ki dauko sbd ASH ya dawo Yana gidan bansan mu sake haduwa.”

Kaman bazata je daukowa ba sai Kuma ta daure ko takalmi Bata Sakaba sbd akwai socks a kafarta me taushi ta fita dauko ruwan.

Fitowarta Kai tsaye kitchen ta nufa ta Bude fridge ta dauko Roba biyu ta juyo kenan Shima Yana saukowa Kuma Kai tsaye kitchen din ya nufo Yana Sako Kai tana juyowa Kai tsaye a Fili ajiyan zuciyansa ta bayyana Yana kallanta kasalan rashin Jinta yau din gaba Daya Yana sake sakinsa.

Nufota yayi sedai itama din bawai ta tsaya bane tahowa tayi zata fice din sedai Hakan be samu ba sbd Yana isowa rungumeta yayi ahankali Yana sake sauke ajiyan zuciya Yana ambatar sunanta cikin qasan maqoshinsa wanda direct cikin kunnanta maganar ya shiga.

Damqe roban ruwan hannunta tayi dakyau Jin suna Neman subucewa sbd nauyin da kirjinta yake qarawa.

Janyewa tayi ahankali tareda Dan yin baya kadan tana dagowa ta zuba masa idanuwanta dasuke kashesa da ransa zatai magana ya tareta f da tasa maganar cikin kulawa da sanyi yace

“Yaya jikinki?

Meyesa yauma kika qi bari a dubaki?

Yaya kikai bacci jiya ma bari bari naji na Farha tace kinqi fitowa Kuma bakyason karba waya,Wani abin ya faru ne?

Jikin Yana damunki sosai ne?

Ruwan hannunta ya Maida kallansa Akai tareda kama hannunta ya sake janyota jikinsa ya zagaye da hannu Daya Dayan Kuma ya shafi cikinta ahankali Yana cewa

“Kinci abinci?

Qin amsawa tayi tareda dauke kallanta daga kansa tukuna ta gyada Kai ahankali tana dan motsawa kadan cikin jikin nasa.

Lura da batason kallansa ya sanyashi sakin murmushin da bai shirya ba yana daukanta cak ya zaunar kan kitchen island din Dake bayansu ya matseta jikinsa ahankali Yana kallan fuskanta Yana Saka hannunsa Daya cikin rigarta Yana shafa cibiyanta ahankali yana Kai fuskarsa daf da tata ya shaqi numfashinta Dake fita cikin sanyi da murmushi akan fuskarsa hancinsa na gugan nata yace

“ASHRAF yayi lefi ne??

Kokuwa ASH ne yayi lefin??

Uhmmm??

Dagowa tayi ta zuba masa fararen idanuwanta tana Jin Yana kashe zuciyarta da qamshinsa da yanda yake shafa cibiyanta zuwa fatar bayanta.

Ahankali ta Bude Baki tace

“Bacci nakeji”

Kan kunnenta yakai bakinsa ya fara Sakan mata numfashinsa me dumi kafin qasan maqoshinsa yace

“Kin tabbata??

Gyada Kai tayi tana janye idonta akansa.

Murmushi me sanyi ya sake saki kafin ya girgiza mata Kai alaman be yarda ba.

Marairaice fuska tayi tana narke masa tareda basa Daman Shima shaqan qamshinta Yana susucewa da wata muryan daya Sakasa ratsa nutsuwarsa gaba Daya tace masa yunka takeji Kuma.

Apple ya dauko guda biyu daga fridge da kansa ya Saka mata a Baki ta ringa ci ahankali tana sake juyar masa da Kai Yana binta da kallo a mace hannuwansa na yawo cikin Rigarta.

Yanda yake mata ya Saka daqyar aka cinye apple din guda Daya sukai jefar da Dayan a tsakiyar kitchen din tareda ruwan yafara kissing wuyanta zuwa kirjinta da kunnuwanta tini ta manta da nauyin kirjinta akansa.

Duk wata sabuwar ‘danyar soyayyarsu me zafi Saida suka baje kolinta a kitchen din kusan botiran rigarta da nasa duk a kitchen din suka watsar dasu rigunan ne kawai a jikinsu ya dauketa bakinsa cikin nata yana mata Wani irin tsosan Dayake sake kasheta suka Haye sama tana mantawa da inda suke.

Suna hayewa mum Aisha ce ta fara fitowa ta nufo kitchen abinda tagani na ruwa a qasa dasu apple da manyan botiran rigunan data tabbatarda na Amatu ne ya sata fitowa kitchen din da wuri tana kallan hanyar sama daidai Yana shigewa da Amatun a ajikinsa ya rufo kofar kai tsaye ta datse.

Mum Aisha yau dai ta tabbatarda abinda ya tabbata din Dan haka take kishirwarta ta Bace Bat kafafunta har zufa sukeyi ta nufi dakin Husnah da maamah Dake bacci ta tadosu batareda tace musu komaiba tace su zauna a palon.

Tana fadar haka Husnah hankalinta ya bata tabbacin akan Dad dinta ne Dan haka Kai tsaye dakinsu Amatun ta nufa ta Bude anty Farha na zaune tana kokarin kashe laptop dinta Dan haka ta dago tana kallanta kafin tayi magana maamah da mum Aisha ma suka shigo idanuwansu duka akan gadon dakin da Amatu bata Kai.

Kallon da sukewa dakin idanuwansu na Neman Amatu ya Saka gaban anty Farha faduwa tana kallan maamah datake kallan kofar toilet tana tsammanin fitowan Amatu.

Magana zatai maamah ta dakatar da ita Babu annuri ko Daya a fuskarta tace

“Ina Amatu??

Numfashi me sanyi anty Farha ta sauke zatai magana Husnah ta juya a fusace tabar dakin ta fito palon tareda fasa Wani irin kuka me Qarfi tana zubewa a gurin numfashinta na Neman daukewa a sume sbd zuciyarta takasa daukan Amatu na dakin Dad din suna tare bayan sunsan uwarta na garin asibiti a kwance kamanm zuciyarta ta buga.

Anty Farha na ganin Hakan wayarta ta dauka lokacinda maamah kan Husnah itama zuciyarta rawa takeyi kaman zata sume,

Numbern Mr Jameel tayi gaggawan kira ya fito daga dakinsa Dake kaman bq na gidan sbd yayi gaggawan zuwa idanma asibiti zaa kwashi Husnah din Akai.

Mr Jameel na dauka yaji abinda yake faruwa ya fito Yana Saka qatuwat jacket akan kayan baccinsa masu kauri Yana cewa su fito gaba dayansu da Husnah din batareda ASH ya saniba akaita asibiti kada hankalinsa ya tashi.

Mum Aisha zamewa tayi akan bazata asibitinba sbd sanin daga can Mr Jameel din zai iya kwasarsu zuwa airport sedai yanda maamah take kokarin rasa nata lafiyan yasa dole aka kwasosu gaba Daya suka fito.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

65

************

Suna barin gidan Babu Nisa suka Isa asibitin da zaa duba Husnah din duk da Mr Jameel har anty Farha sunsan ko ruwa aka zuba mata zata farfado Amma suna buqatan dai Taga likitan sbd yanzu ne zasu hargitsa gidan da tashin hankali cikin Daren gwara idan tashin hankalin zasuyi su bari da safe suyi saisu fuskanci ASH din gaba dayansu da kansa.

Yana miqasu asibitin ya tafiyarsa sbd yanda zuciya ke ingizasa Daya Siya musu tickets cikin Daren asubar fari subar qasar su koma inda suka fito.

Anty Farha kawai ya bari tareda su itama ta tsaya dinne duk da baa zama asibitin Amma sbd ta tare kowannensu daga komawa gida ta tsaya Dan har maamah din sukace likita ya duba Dan yanda numfashinta ke Neman yankewa sbd mummunan tashin hankalin datake ciki na kasa yarda ko gasgata Amatu Bata dakinsu a Daren Sam Bata yarda ba da abinda ake kokarin fada da tabbatarwa Amatu da ASH.

Mum Aisha kuwa gaba Daya hankalinta da nutsuwanta Bata taredasu a asibitin Yana gidan dasuka baro da abinda dai ya tabbata kenan Amatu ta zama matar ASH.

A gida kuwa tinda suka shige saman a palon ya fara zaunawa da ita a jikinsa suna fuskantar juna ya Ciro bakinsa daga nata Yana bin lips dinta dasukai Wani Dan ja da Kuma Hasken deep tsotsan daya musu.

Rigar jikinta yakeson zarewa Amma akwai sanyi bayason sanyin ya shigeta Dan haka gaban rigar dake Bude ya zira hannunwansa Yana mannota jikinsa kirjinsu ya hade da Dan karfi kadan,

Atare suka sauke ajiyan zuciya me hade da numfashi Yana ambatar sunanta kaman ransa na Neman fita,

Itama lumshe idanuwanta da baccin cikinsu ya gama tafiya gaba Daya tayi tana shafa bayan wuyansa ahankali kaman tsutsa na masa tafiya zuwa wuyansa da kirjinsa tareda sauke masa numfashinta masu dumi a cikin kunnensa na dama tini ya qarasa kuncewa.

Dago kanta tayi lokacinda ya sake ambatar sunanta ta Kalli fuskarsa kishinsa kawai taji Yana suka tareda mamaye zuciyarta tareda sonsa me tsananin gaske a lokaci Daya.

Cikowa idanuwanta sukai da hawayen galabaitan zuciyarta ta hade fuskansu tareda kama fuskansa da tafin hannuwanta ta hade bakinsa da nata wata irin fitinanniyar kiss me kunce Kai ta fara yimasa tana tsotsan lips dinsa da harshensa a lokaci Daya tana sake zagayo kansa da hannuwanta.

Kasa riqe kansa yayi daga rabata da rigarta gaba Yana shigarda ita jikinsa sosai Dan Hana sanyin shigarta ya miqe da ita har lokacin tana sake kashesa da nata salon kiss din.

A cikin bedroom din nasa kusan sabuwar duniyar suka Bude suna bajewa Dan kuwa Saida yagama susucewa gaba Daya tukuna suka Isa lafiyayyar gadon dakin suka hau suna watso kusan Rabin pillows din gadon ka suka Kai guda shiga qasa.

Lafiyayyar soyayyarsu suka sha ahankali kwance kafin tafara tinanin saukowa ta koma dakinsu kafin safe Wani ya fito yasan Bata Nan.

Bai bari ta koma din ba Dan Babu abinda ya shafesa da Wanda zai fito yaga Bata Nan din Dan haka wanka sukai ya kwanta cikin jikinta sbd gajiyansa da stress dinsa dayaji ya sakesa gaba Daya Wani baccin nutsuwa da Kwanciyar hankali ne ya daukesa itama dole tayi baccin a Nan sbd yanda ya kwanta jikinta bazata iya zamewaba Dan a zagaye da qugunta hannunsa duka biyun suke.

Babu Kiran sallah da alarm ake tashi sallan asuba dan haka Koda alarm din yayita yi ahankali qasa qasa Basu ji ba Saida sukai lattin sallah sosai.

Suna idar da sallah jikinta na Dan rawa ta silale ta sauko Jin gidan tsit tayi tinanin Basu tashi ba Dan haka tafara saukowa da sauri ahankali sedai ko gama saukowa bataiba ba aka Bude kofar shigowa dukkaninsu suka shigo gaba ki dayansu Banda mr Jameel da Bai shigoba.

Anty Farha ce agaba sai maamah da Husnah tukuna mum Aisha data shigo karshe ranta a hade sbd takaicin kwanan zaune kawai datai a asibitin.

Rawa jikin Amatun ya Dan dauka tana kallan maamah datai mata kallo daya ta dauke idanuwanta daga kallanta sbd zuciyarta zata iya bugawa.

Husnah ma zuru tayi tana kallan Amatun kallo na qurullan data iya gane ko yau din Babu bra a jikin Amatun hakama kusan gaba Daya qamshin Dad dinne yake tashi daga kayan jikinta.

Anty Farha ce tayi saurin yin gaba tana Jan Amatun da cewa

“Neman mu kikeyi ne?

Asibiti muka kwana Husnah ba lafiya lokacin kina kitchen kinje daukan ruwa Amma dai……

Maamah data kasa riqe bacin ranta da renin wayon da farha takeson kawo mata ta Saka hannu ta riqe hannun Amatun daga hannun Farha ta dawo da ita gabanta idanuwanta da sukai jajir akan Amatun data kasa kallanta har rawa da karyewa muryan maamah din keyi ta Bude Baki tace

“Amatu daga dakin ASH kike??

Qasa ta sake yi da kanta tana kasa cewa komai bayan hawayen Dake cikowa daga idanuwanta.

Magana anty Farha ta matso zatai Dan kare Amatu maamah ta daga mata hannu cikin tsananin bacin Rai tareda dawo da kallanta ga Amatu batace komaiba ta kama hannunta Rai a tsananin bace ta fizgeta zuwa cikin dakinsu ta Turo kofar.

Sakin hannun Amatun tayi Kai tsaye fushinta da tsananin zafin zuciyarta na qaruwa ta maimaita tambayarta tana tsoron amsar da zaa Bata Amma dai tanason Jin idan akwaima ko alalar gaisuwar datake shiga tsakanin Amatun da ASH batareda sanintaba.

Kasa amsa tambayar Amatu tayi idanuwanta na sauyawa zuwa ja hannuwanta na kakkarwa.

Cikin zafin zuciya Daya kasa boyuwa Maamah ta daga murya a zafafe tace

“Meya kaiki sama?

Menene alaqarki da zuwa saman?

Menene abinda su Mum Aisha suke fada???

Wannan Karan gudu hawayenta suka qara ta Bude Baki Babu abinda ta iya furtawa Se “kiyi hakuri maamah….

Wani ba zatan Mari ne maamah din ta dauketa dashi Wanda ya Sakata gigita sbd ba zatan saukansa da Kuma dukanta da baa taba yi ba.

Ita kanta maamah datai Marin rawa jikin ya dauka a fusace batama sanin me take fada tace

“Da gaske su Husnah suke kenan kina zuwa dakinsa ko me??

Kin taba kwana a dakinsa ne ko me nake Shirin Gani ko ji???

Kuka mara sauti ne ya kufcewa Amatu tana toshe bakinta da hannuwanta sake rawa tana kasa amsa tambayar maamah cikin matsanancin tashin hankali da tsoro.

A fusace maamah ta damqota tana jijjigata cikin fushinta Dake tsananta take sake maimaita tambayar da gaske ne tana zuwa dakin ASH?

Kukanta ke tsananta tana kasa amsa tambayar har lokacin hakama rawa jikinta keyi sosai sbd tashin hankali da tsoron Bata taba kaiwa wannan matakin ba da mahaifiyarta.

Maamah ma hawayen ne suka kufce mata tana fasa kuka sbd Bata taba tinani ba hakama Bata taba zata ba har lokacin ma ta kasa yarda da Hakan shiyasa takeson Amatun ta Bude bakinta da kanta ta fada mata.

Kukan maamah din ya sake gigita Amatun ta shiga tashin hankalin dayafi na farko tana fashewa da sabon kukan da Baya fidda sauti har lokacin sedai shesheka.

Cikin kukan maamah ta sake cakumo Amatun tana Neman illata sbd bacin Rai ta riqe hannunta Daya qam kaman zata tsaga mata shi tana Jin kaman karta tsaya Se tayiwa Amatun shegen dukan da zata Bude Baki ta fada mata gaskia duk da bazata taba yarda Amatun zata iya Hakan ba Dan haka cikin Nemo taurin zuciya ta share hawayenta tana kallan Amatun tareda Dan sassauta murya tace

“Amatu idan har kin yarda ni mahaifiyarki ce,nice na dauki cikinki na haifeki kimun alkawarin daga yanzu bazaki sake ko kallan ASH TALBA ba’a matsayin mijin yar uwar mahaifiyarki ba,kimun alkawarin babu alaqar da zata taba shiga tsakaninki dashi ba bare har abinda su Aisha suke magana ya tabbata,

Abeeda ta tashi bayan shekaru ko ke bazaki so abinda zai sake Sakata cikin Wani mummunan halinba tinda uwace a gareki,

Wannan auren na kaddara ne Kuma shi da kansa zai warware Miki shi ya sauke Miki nauyin auren tinda Abeeda ta tashi,

Abeeda kadai ce matar Dayake kallo a macen da zaiyi rayuwa da ita,

Babu abinda Zaki samu ko Qaru dashi da wannan auren zai lalata kuruciya da lokacinki sbd ke da ASH kaman sama da qasa ne akwai tazarar abubuwa da yawa da suka nesanta ku,

Ki dubi kauna da amincin dayake tsakanina da Abeeda ki tattara maganar ASH da aurensa ki aje a gefe kiyi rayuwarki,

Kimum wannan alqawarin Amatu,

Kimun alkawarin Nan Amatu ki tabbatar min da kin yafe auren Nan tareda ajesa a gefe kwata kwata kada yar uwata ta koma halinda ta fito…….

Amatu tinda take Bata taba gasgata da gaske mahaifiyarta data haifeta tafi son farin cikin kowa akanta ba,

Tafison Abeeda da yar Abeeda akanta,

A yau taji komai na duniya ya isheta ya fita kanta,

Ayau mahaifiyarta ce take rokonta akan ta koma bazawara sbd kada farin cikin ‘yar Abeeda Dan kuwa Abeeda yanzu Babu Wanda yasan me takeso meye bataso…

Katseta maamah tayi da sake maimaita mata kalmomin alqawarin datake son ta daukan mata idanuwanta jajir akanta.

Gudu hawayenta masu tsananin zafi suka qara tana dauke kallanta daga Maamah din kuka me qarfin gaske yana kufce mata.

Kukanta ya Saka maamah fahimtar alaqawarin data nema tai matan yayi mata tsauri Dan haka hankalinta ya sake tashi sosai sbd idan har Amatu batai mata wannan alqawarin ba to alama ce ta ASH din Yana cikin zuciyarta.

“Innalillahi wainna ilaihirrajiun” maamah din tafara furtawa tana Neman Yanke jiki ta Fadi Amatu ta tarota sedai da qarfi maamah din ta tureta tana daga mata hannu alamar ko tabata kada ta kuskura tayi.

Hakan datai ya Saka Amatu sake fashewa da kuka kafin tayi Wani yunkurin Husnah ta shigo dakin tana ganin halinsa maamah ke ciki da gudu ta iso gurin tana riqo maamah itama ranta da jikinta duk a mace hawaye kawai ke ciko idanuwanta tana hadiyewa.

Anty Farha ma shigowa tayi sbd takasa hakura tsoro da tashin hankalinta kada su tada balai da masifarsu su Saka Amatun a cikin Wani halin.

Suna dakin ASH ya fito a shirye sbd kiransa da Akai asibiti yanzu din akan yau zai dawo da Abeeda gida Dan haka ko breakfast Bai tsaya yi ba hakama mum Aisha Dake palon Bata bari yasan da akwai abinda yake faruwaba ta hanasa fahimtar komai harya fice daga gidan.

Yana fita mum Aisha ta shigo dakin tana sake rura wutan Dake cin zuciyar maamah da Husnah.

Anty Farha kuwa ayau maamah kasa riqe kanta tayi tai mata tas cikin tsananin bacin Rai duk da har lokacin kanta ya kasa dauka bare yarda da Amatun da gaske taje dakin ASH a Daren.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

66

***************

Mummunan halin da Amatu ta shiga ya Sanya anty Farha hadiye nata damuwan maganganun su maamah da mum Aisha dasuka ringa gasa mata masu zafi da ‘daci ta janye AmatulMaleek suka fito dakin jiki a sanyaye ta dawo da ita dakinsu.

Suna shiga dakin zaunar da Amatun tayi ita Kuma ta nufi toilet ta shige sbd maganganunsu sun Sosa ranta matiqar gaske musamman mum Aisha datake fadan nata cikin cin zarafi da quntatawa,

Ko Mr Jameel bazata iya kiraba a wannan lokacin sbd itama zuciyarta ta sosu matiqa idan ma ta kirasa bazata iya fadan komai ba kuka ne zaizo mata dan haka ta shige toilet ta rufo kofar batareda ta iya kallan Amatu ba da take nata kukan sosai itama.

Bayan ficewansu mum Aisha kan maamah ta dawo da maganganunta masu quntatawa ta qarasa damawa maamah din lissafi

Husnah kuwa takai matakin da idanuwanta Neman bushewa sukeyi qyam ba hawaye sai ja da radadin zuciya sbd ta kasa yarda da itam ace yau din wai Amatu ce da zuwa dakin Dad dinta da daddare bayan tasan mum dinta ance Koda wasa kar abari tasan da zancen auren bare wannan sabuwar tashin hankalin.

Abin baqin ciki da takaicinta shine yanda Dad dinta duk Isa,kamewa da class dinsa da manyan mata ke bibiya zai iya kallan Amatun ma a mace bare iya taba jikinta,

Babban buri,fata da adduarta shine duk rintsi kada Allah yasa Dad dinta ya Maida Amatu cikakkiyar matarsa,Allah yasa iya wannan da suka Gani ne abin ya tsaya yanda kawai gwara mum dinta ta sani Kila Hakan ne zaisa Dad ya bar Amatun ya dawo da dukkanin rayuwa da kulawansa harma da time dinsa gaba Daya kan mum din nata.

Maamah silalewa tayi zaune tana tare hawayenta sake saukowa kan fuskarta kwata kwata qasar ta fita ranta gaba Daya harma da rayuwa a cikin gidan ASH Dan haka Nigeria kawai take buqatan tattara Amatun su koma ta gaji bazata iyaba,

Zuciyarta bazata iya daukan wannan lamarin ba, bazata iya barin Abeeda ta tasan da maganar auren Nan ba tana guri Daya da ita gwara ta tattara Amatun su koma inda suka fito duk ranar Daya gaji da tafiyar tasu ya warware auren Amma tabbas ta gama zaman gidansa da Amatun.

****Duk wannan tashin hankalin da masifar baisan anayi ba daga shi har Mr Jameel sbd farha ce jinsa da ganinsa a cikin iyalinsa to itama tana cikin sanyin jiki yau din Dan haka wanka tayi ta shirya ta fice daga gidan gaba Daya ta fita kanta ya sake sbd taso fita da Amatun Amma Amatun bazata iya fita koina ba sbd kukan datasha gaba Daya kamanninta sun sauya ga zazzabi ya rufeta na take.

A asibitin kuwa duk wasu formalities na sallama da transfer din Abeedan zuwa Nigeria ta qarasa warware acan sun gama anso Basu nurse da zata ringa kulawa da ita Amma tinda tafiya zasuyi ha zama ba sai aka barta kawai akan zata ringa zuwa kullum nurse din tana dubata kafin tafiyarsu.

A motar ambulance ta asibitin aka kawo Madame Abeedan gida Dan haka suna Jin isowan motar kowannensu ya aro nutsuwar karfi da yaji ya yafawa kansa tareda fuskewa kada ASH ya gano abinda ya faru a gidan ko kadan.

Dayake Shima kusan hankalinsa gaba Daya Yana kan Abeedan da aka kawo gida sai Bai Wani fahimci komai ba hakama little Abeedan Dayaga Bai ganta ba hakama Farha sai yayi tinanin suna tare.

Husnah da maamah farin cikinsu duk da suna cikin dacin zuciya sun bayyana murnar dawowanta a Fili tareda rasa inama zasu ajeta.

Dakunan na qasa a cike suke sbd guda uku ne,

Mum Aisha Daya Se Husnah da maamah Daya sai anty Farha da Amatu Daya.

A sama Kuma bazai yiyuba sbd Hawa da saukan tinda ko motsi Bata iya yi sosai Se ahankali take Dan motsawa daga kallo sai motsi takeyi ko magana Bata iyawa sbd kaman paralyze ne a tattare da ita bayan ciwonta.

A dakin mum Aisha dole aka ajeta nan suka tare sunata dawainiyar murnar dawowanta.

ASH kuwa fita suka sake yi da Mr Jameel sbd so yake ba delay su koma Nigeria tinda Babu abinda zasu zauna suyi din anan Dan haka zai qarasa abinda zaiyi a qasar a ranar sai su Dan huta na kwana biyu kafin su wuce kawai.

Bayan fitarsa kusan yaqe da karfin halin danne ciwon ransu suka ringa yi a gaban madame Abeeda wadda ko Bata komai sunsan tana ji Kuma tana fahimtar komai din.

Wuni guda Amatu Tay a daki kwance cikin zazzabi me qarfi da ciwon damuwa Amma Babu Wanda ya Kalli dakin datake bare dubata sbd kowa a gidan ta ciki na cikinsa.

Anty Farha ma har dare Bata dawo gidan ba Dan haka daqyar Amatu ta iya tashi ta daddafa ta shiga toilet ta sakarwa kanta ruwan zafi sosai tayi wanka.

Dan karfi ta samu da kuzari na wankan datai Dan haka tayi brush ta fito a sanyaye jiki ba kwari ta zauna dole ta daure ta shafa Mai sbd sanyi ta tashi ta saka Riga da wando masu kauri sosai sbd sanyi ta Saka hijab tayi sallolin da suke kanta harma da ishai da lokacinta yayi.

Tana idarwa fitowa tayi Dan dole da yunwar da cikinta ya kasa riqewa kaman zata mutu.

Babu kowa a palon Dan haka Kai tsaye kitchen ta wuce ta Bude fridge ta dauko Coke me sanyi da biscuits ta zauna a kitchen din ta tura hakanan taci sbd bakin da ranta Babu dadi Sam.

Abincin dayake kitchen din ta duba Taga chicken noodles ce Akai duk da Bata Wani so haka ta daure ta zuba a plate ta tura tana ci tana Jin zuciyarta bataso Amma yunwar Bazata barta ba.

Ruwa Tasha me sanyi bayan tagama ta fito.

Husnah data fito daga dakinsu ce ta ganta ko kallan juna basuyiba Amatu ta wuce dakinta Kai tsaye lokacin kusan 10 ta kusa.

Rashin layin kasar yasaka ta rasa yanda zatai ta nema anty Farha Dan haka dole ta kwanta tana shiga damuwan rashin dawowan anty Farha din itama.

Harya kwanta ta manta Bata shigo da ruwa ba dole ta taso ta fito daidai Husnah ta sake fitowa wannan Karan bin Amatun da kallo tayi zuciyarta na tafasa da qunatata da tinanin Amatun dawowan Dad dinta take Jira waton yauma taje dakinsa ta kwana kenan bayan mum dinta tana gidan.

Wani baqin ciki da kishin Hakan ne ya danne kirjinta Dan haka batai tinanin komaiba ta nufi dakin mum Aisha gurin mum dinta.

Tana shiga har Madame abeeda ta fara bacci Amma ido rufe Husnah tafara kokarin dagata tana kokarin sakawa a kujera Amma ta kasa.

Mum Aisha ce ta fito toilet tana sauri ta gama tazo ta zauna ta qarasa warwarewa Abeeda komai na abinda ta fada mata asibiti kafin zuwan ASH.

Ta fada mata aure yayi Amma Bata fada mata wa yake aurenba jikinta ya birkice Dan haka yau zata qarasa cike aikinta.

Ganin Husnah na kokarin Saka Abeedan kan wheelchair yasata qarasowa tana kallanta da mamaki tana cewa

“Lafiyanki kuwa?

Kodai ciwon haukan ne ya motsa?

Kin dai San mahaifiyarki batasan kina samun juyewar Kai ba Akai Akai shine Zaki nuna mata Dan ta birkice bayan ance a guji birkicewan nata….

Dayake idanuwanta a rufe suke Husnah din Bata tsaya fahimtar tasirin da maganganun mum Aisha keyi ga mum din tata ba sai kawai taci gaba da kokarin Dora Abeedan harta samu zaunar da ita daidai Akai ta tura  ta Kai tsaye ta fice dakin tana Jin aranta gwara takai mum din tata sama ta kwana can zata Fi ma samun kulawa da wali a dakin Dad dinta.

Tana fitowa Palo da ita ta nufi hanyar Hawa sama Kai tsaye tana turawa daqyar tana dagawa sedai lamarin Yana Neman gagara sbd bazata iya turata ita kadai ba zuwa sama.

Maamah data fito itama Dan zuwa sake dubo Abeedan kafin ta kwanta tana fitowa akan kokuwan hayewa da Husnah ke kokarin yi da Abeedan idanuwanta suka sauka Dan haka da sauri ta qarasa ta kamata tana kallan Husnah da mamaki da tsoron yanda ta hawo da Abeedan stairs din tace

“Lafiya kika daukota?

Ina Zaki kaita kika hawo stairs dinnan masu tsayi da ita?

Cigaba da kokarin qarasawa da ita Husnah ta fara idanuwanta jajir suna Neman tara hawaye tace

“Zata Fi samun kulawa da sakewa a saman shiyasa zan kaita can kuma ko Dad ya dawo saman zai hawo da ita ma”

Da mamaki sosai maamah ke kallan Husnah din tana riqe Abeedan da kyau sbd sun kusa hayewa ko data fito ga Abeedan na Neman fin karfinsu a tsorace maamah tace

“Wanda baida lafiya irin haka meye zaisa a daukota zuwa Wani sama gaskia Sam wannan ganganci ne Husnah,kamata da kyau fa”

Amatu data fito daga dauko ruwa kitchen Dan bayan shigarta ta tarar Babu sauran ruwan sanyi a fridge sai ta Saka biyu ta Dan Jira suyi sanyi kadan ta dauko ta dawo.

Tana fitowa kitchen Taga abinda yake faruwa Madame abeeda da batama San andawo da ita ba Taga tana Neman gagararsu ta fado Dan haka ruwan hannunta ta jiye da sauri itama cikin mamaki me tsanani ta Isa Takai hannu zata kama musu Husnah tayi saurin tareta da hannunta Daya cikin zafin zuciya da baqin cikin yanda suke fama sun kasa qarasa hayewa da Abeedan tace

“Karki taba mum mahaifiya sbd kece silan wannan kakanikayi din da mukeyi da ita.

Mum Aisha ce ta fito tana kallansu da sauri ta hawo tana cewa

“Meye haka ne wai Husnah kikeyi,Sam ke bakyajin maganar kowa ne”

Hannu ta Saka suka qarasa cira wheelchair din zuwa stairs din sama na karshen gaba Daya suka ajeta sai alokacin maamah ta Kalli Husnah fuska ba wasa ko walwala ko kadan tace

“Banason Jin komai anan yanzu”

Tana fadar Hakan ta juya ta kalli Amatu zatace mata ta tafi kawai sai mum Aisha ta katse maamah din da cewa

“AmatulMaleek matar ASH ce Banga abin damuwa da daga hankalinda zaisa a dauko Abeeda tana fama da lafiyarta ku hawo da ita wannan tsaunin wahalar ba…….

Cikin Wani irin mugun shock dukkaninsu suka kalli mum Aisha din hankali tashe kafin suka Maida kallonsu lokaci Daya akan madame Abeeda data rufe idanuwanta ahankali tin kafin su juyo din gareta.

Maamah da Wani mummunan bacin Rai da fushin da basusan tana da shi ba ta kama hannun mum Aishan da qarfi tayi gefe da ita kadan duk da kowa na Jin abinda suke fada  fushinta na bayyana cikin zafin tace

“Me kike kokarin yi?

Wace maganar ne wannan??

“Akwai karya ne a abinda na fada Asmau?

‘yar ki Bata aure mijin Aminiyarki ba data tallafi rayuwarki?

Me yasa kika bari auren yazo har yanzu idan da gaske bakyaso?

Ita Amatun da kike ganin kin tsare kin killace akan auren so nawa ta kaiwa ASH din kanta?

Kuka da tashin hankali kuka ringa yi akan Naufal Akai masa sharrin fyade bayan shima ba yin kansa bane Husnah da kike bugun gaba da ita itace ta sirka maganinsa ta turasa yiwa Amatun fyade sbd Faisal,hakama a karo na biyu da gayya ta jaki zuwa porthcrt ta sake turasa yiwa Amatun fyaden da yayi sanadin gobarar tsohon Mansion da Kuma yankewan kafarsa da ASH yayi,

Ashe ba dadi rasa Wanda kakeso ni aka kassaramun ‘da sbd yarki?…

Wani mummunan jiri da zufan tashin hankali ne me tsananin gaske ya fara tsiyayowa maamah Nan take bakinta na rawar masifaffen tashin hankalin abind mum Aisha din ke fadan Husnah tasa ayiw Amatu fyade yasata kallan cikin idon mum Aisha din tace

“Ki maimaita abinda kika fada naji kyau”””

Kafin mum Aisha data shiga mamaki da shakkar fushin datake Gani me tsanani akan fuskar maamah tayi magana Husnah ne tayi kan Amatu zata shaqota sbd tasan shikenan mum dinta jikinta rikicewa zeyi ta rasata gaba Daya hakama maamah dinma rasata zatai Amatu ta zama balai da masifar rayuwarta.

Baya Amatu tayi tareda kaucewa Husnah din

 Husnah ta sake yi kanta ido rufe cikin tsananin fushi da rufewan zuciya da ido Wanda yasa maamah da mum Aisha sukayo kan Husnah din sbd qatuwar flower vase data dauka a haukace

Maamah ce ta tareta,mum Aisha kuwa kokarin kaucewa daga gurin tayi tana kokarin tura Husnah take flower vase din ta fada gurin wheelchair din da Madame abeeda take zaune idanuwanta jajir da abinda kunnuwanta ke ji mata take wheelchair din tafara wintsilowa kan stairs din kaman an jefo ball,

Gaba dayansu cikin gigitaccen tashin hankalin da baa Saka masa ranaba suka yo bakin stairs din Babu Wanda qafafunsa da hantarsa Bata tsalle a cikinsu.

Yanda ake gangarowa da kujeran daban madame Abeedan daban a stairs din ba kyan Gani daidai shigowan ASH da Mr Jameel Se anty Farha da itama atare suka shigo.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

67

***************

Anty Farha ce ta saki ihu cikin matsanancin tashin hankali da firgici

ASH kuwa taku biyu yayi ya Isa inda Abeedan ta fado Yana tarota jikinsa gaba Daya da sauti me girma yake Kiran sunanta Yana jijjiga fuskarta Dake fidda jinin da baimasan na Ina ne yake fitowa ba.

Mr Jameel kuwa Wani irin tafasa zuciyarsa da gangar jikinsa keyi sbd tsananin baqin ciki da tashin hankali harma Da bacin ran da shi kansa baisan yanada shiba lokacinda yake kallansu mum Aisha din da maamah s da Husnah din a jere a saman Wanda alamu da komai ya bayyana qarara dambe ne sukeyi a saman suka jehota Kokuma sainsa da tashin hankalin da suka Saba.

Husnah ce ta sauko da gudun datake hada stairs kusan hudu hudu ko uku uku hankali da ganinta na Neman gushewa,

Maamah kuwa zubewa tayi a gurin sbd ganinta Daya dauke lokaci Daya tareda bugun zuciyarta,

Mum Aisha hannu ta Dora Akai tana neman sakin ihu.

Amatu ma bayan tayi ahankali tana zamewa qasa zuciyarta na dauke bugawa da Mafi girman tashin hankali da balain dayafi karfin kwakwalwanta.

Ambulance Mr Jameel ya kira Yana tare Husnah da mum Aisha da suka nufato inda ASH yake da Abeedan a jikinsa Yana cigaba da ambatar sunanta Dan ta Bude idanuwanta Amma Sam Babu alaman zai samu Hakan.

Cikin qanqanin lokacinda ba’a dauka ba ambulance ta iso hankali tashe aka dauki Abeeda Akai asibiti da ita batareda da kowa yabi ta kansu ba ASH din da Mr Jameel ne kawai sukabi bayan ambulance din.

Suna wucewa anty Farha da kafafunta ke rawar tashin hankalin lamarin sama ta hau da sauri ta kamo Amatu Dake zube qasa idanuwanta a waje zuwa jikinta tana ambatar sunanta cikin tsananin kulawa da kokarin dawo da ita hayyacinta.

Dagota tayi takamo ta suka sauko Bata tsaya da ita palonba ta wuce da ita daki.

Husnah data kasa dawowa daidai sai alokacin ta fasa Wani irin kuka me Qarfi da ihu tana zubewa qasa zaune duka jikinta jijjigan tashin hankalin da Bata taba shiga ba takeyi Dan kuwa idan mum dinta ta mutu sune suka kasheta.

Maamah ma kaman mara laka ko Daya a jikinta ta sauko ta shige dakinsu ta zube tsakiyan dakin tareda fasa nata kukan me tsananin gaske cikin matsanancin tashin hankali da Wani irin gigita.

Mum Aisha kanta a gigicen take sbd bayyanar ASH a daidai lokacinda abin ya afku ita shine babban masifaffen tashin hankalinta da Bata tsoro.

Dan haka itama tini tafara rawar jiki tana sake gigicewan.

A daki kuwa anty Farha kokarin kulawa da Amatu takeyi ganin yanda ta shiga shock me qarfi Dan kuwa abin tashin hankali ne me girma mara lafiya irin Abeeda ace an jeho daga stairs.

Hawayen ne masu tsananin zafin gaske suka fara tsiyayowa Amatun kafin kuka me sauti da qarfin gaske ya zo mata ta silale qasa tana cusa kanta cikin qafafunta tana yinsa sosai tareda fatan Babu abinda ya samu mum Abeedan.

Duk anty Farha ma na cikin tashin hankalin lamarin Amma ta danne kokarin rarrashin Amatun takeyi tana Bata tabbacin babu abinda zai samu Madame Abeeda inshallah.

Gaba dayansu gidan Babu Wanda yake hayyacinsa bayan anty Farha datake iya kokarin ganin Babu Wanda ya zauce a cikinsu Dan kuwa kusan dukansu zaucewa kowa keyi gashi tsananin tsoron ASH ya Hana kowacce tinanin binsu asibitin dubo halinda Abeeda take ciki.

Anty Farha din da suka gama ciwa mutunci da safen itace dai ta ringa binsu Daya Baya Daya tana dawo da kowa hayyacinsa musamman mum Aisha datafi kowa shiga tsoron ASH Husnah da maamah kuwa tashin hankalin rasa Abeedan ne yake Dan kokarin fin tsoron ASH din Dayake cike da cikinsu duk da Shima din tsoron abinda zai iyayi sukeyi.

Dayake dare ne kusan kowa dakinsa ya shige suka zauna jigum jigum hankalinsu da idanuwansu a yanayi na rashin sanin Ina suka kwana.

AmatulMaleek kuwa zazzabinta cikin tsakar Daren har tsoro ya bawa anty Farha Dan haka Amai ta ringa yi Wanda ya Saka kowa fitowa daga dikinsa.

Daman Husnah neman dalilin fitowa takeyi sbd tashin hankalinta na Dayan bangaren maamah akan Jin itace tasaka ayiwa Amatun fyade,Sam maamah ko inda take Bata kallaba bare tinanin akwai mutum tareda ita,

A aynzu batada karfi ko bawa komai hankalinta sai taji yanda Abeeda take zatai tinanin Husnah da abinda tayi mata din.

Cirko cirko suka tsaya Babu Wanda cikin awannin da aka barsu din Bai fada ba yayi zuru zuru a dare daya lokaci Daya sbd rashin sanin meye zai faru.

AmatulMaleek ta galabaita sosai Dan haka ko zama daqyar anty Farha ta zaunar da ita taje ta kawo mata tea me zafin gaske ta fara Bata.

Banda Husnah daga mum Aisha har Maamah datake Neman shiga sabuwar shock of her life zubawa Amatu idanuwansu sukai mum Aisha ta Bude Baki murya na rawa tanason magana Amma ta fasa sbd yau tashin hankalin na musamman ne,

Magana ce a bakinta Amma ba damar furtawa sbd a wannan tsaka me wuyan dasuke tada Wani balain ba nasu bane Dan haka tayi shiru harsun samu fita daga wannan mummunan tashin hankalin Amma tabbas wlh ta tabbatarda ciki ne a jikin Amatun,Dan haka tana cikin sabon tashin hankali Amma dai tashin Abeeda yanzu shine fatanta Dan duk yanda takeson Abeedan ta mutu Bata so ya kasance ASH ya taddasu dumu dumu sun jeho masa mata ba da Bata saman Kokuma da Bai taddasu ba zata iya zame kanta Amma gaba dayansu ya taddasu Dan haka tasan Allah ne kadai zai fiddasu wannan masifar shine rashin mutuwar Abeeda a lokacin.

Maamah ma kusan tinanin mum Aisha ne yakeson shigarta Amma tashin hankalin datake ciki yasa Bata yarda da abinda idanuwanta ke ganar mata ba bare Kuma yarda da lamarin Dan haka a rude tayiwa Amatun sannu tabar dakin hakama mum Aisha tana ji tana Gani ga abin tada fitina da magana Amma yau ba dama.

Suna ficewa tana gama Shan tea ta kwanta ko baccin awa Daya bataiba lokacin sallan asuba tayi suka tashi sukai sallah Banda ita da anty Farha taqi tadawa sbd ta ganin yanda ta galabaita din tabarta ta samu baccin.

Qarfe 7 saura Amatun ta sake farkawa ta tashi ahankali sbd ta samu Dan kuzari ta nufi toilet Tayo fitsari da alwala tana fitowa ta tada sallah.

Tana sallamewa ko tashi daga inda take bataiba Mr Jameel ya shigo gidan  da sauran duhun asubar.

Baice komaiba ya buqaci su fito da kayansu jirgin da zasubi awa Daya ya rage ya tashi.

Hankali tashe suke kallansa Amma ba Daman magana shima Bai tsyaa komaiba Yana fada ya juya ya fice waje Yana jiransu sbd gaba Daya a siqe yake dasu kaman ya kwashesu yakaisu asibitin mahaukata yakeji yakai ya zubar ayita banka musu alluran hauka ko zasu huta da balainsu Daya ishi kowa har Yan aikin mansion din TALBAs sun dai gaji da masifarsu bare me gidan gashinan sun ja masa masifa Yana ganin ya samu Madame abeeda taji sauki.

Mum Aisha tasan zaayi Hakan Dan haka itace ta fara fitowa da akwatinta kafin maamah da Husnah dasuka so ko so Daya ne sunje sun duba Abeedan sunsan halinda take ciki Amma Sam Babu fuska Dan kuwa sanin wannan umarnin daga ASH ne Kila.

Anty Farha ce ta fito da nata kayan Dana Amatu suma suka fito Dan Mr Jameel cewa Yayi dukkaninsu kowa da kowa gida sukai su fito.

Babu me wanka a cikinsu bayan Amatu sbd itama ta sake samun qarfin jikinta ne anty Farha ta Sakata wanka da ruwan zafi sosai sharp sharp ta shirya cikin Riga da wandon Jean Se qatuwar jacket me tsayi da kauri tayi Rollin harda safa da facemask suka fito.

A yanda suka fito jikin kowa a mace idanuwa a jeme har lokacin Mr Jameel Babu wadda yacewa komai kawai kayansu ya zuba cikin babbar motar Daya zo da ita takaisu airport.

Tin a cikin mota ya bawa Farha tickets dinsu duka ta bawa kowa nasa da kanta tana kallansa cikin kulawa da sanyin jiki sedai ta kasa cewa komai sbd yanayinsa Babu walwala ko annuri ko kadan Kuma so da daman tin Madame abeeda na lafiya kalau kusan harma da duk me muamala Hulda da ASH ta Mr Jameel ake karanta ko gane halinda ASH yake ciki Dan kuwa mode din Mr Jameel shine yake bayyanar da mode din ASH Dan haka rashin annurin fuskar Mr Jameel da bacin Rai da damuwar dayake kwance a fuskansa yasa dukkaninsu sanin ba sauki ta gurin ASH din Dan haka Babu wanda ya sake ko Tari har suka iso airport suka sauka ko motan Bai fito ba farha ya kalla da idanuwasa Dake da Dan ja ahankali cikin nutsuwa yace

“Ki kula da L.A din,kema ki kula,Allah ya kaiku lfy”

Gyada masa Kai tayi a sanyaye itama zuciyarta na sake shiga damuwa.

Ko zama basuyiba aka kira flight nasu suka wuce kawai janye da kayansu Babu me qarfin jiki.

Kowa a zuciyarsa matse yake da son sanin halinda madame Abeeda take ciki Amma Babu dama Babu kuka alamar zama a bari su sani bare alamar sanin.

Jirginsu na dagawa mum Aisha ta sake ajiyan zuciya a boye Dan harga Allah a tsinke take ganin takeyi ASH miqasu zeyi ga hukumar qasar tasan sedai labarinsu ba dai su din ba.

Husnah hawayenta har sun bushe sun Dena saukowa sai jajir da idanuwan sukai,

Maamah ma dai kukan ya tsaya Se nauyin Daya danne mata kirji da zuciya.

Tafiyar zaman makokin wahala sukai me tsayin gaske har suka sauka Nigeria ga mamakinsu motan data zo daukansu daga Lagos sun dauka masauki zata kaisu sai kawai aka Sakasu motar zuwa Yola ba jirgi ba take hankalinsu gaba Daya ya tashi anty Farha ta zame da cewan Amatu batada lafiya zasu bari ta warware zuwa da safe su biyosu.

Mum Aisha ma take tace bazata iya bin mota ba hakama Husnah Amma Kiri Kiri aka sakasu mota sunaji suna Gani Husnah Se kuka take sbd tsoro da fargaban hanyar hakama mum Aisha jininta take yafara kokarin Hawa sbd tsoron hanya,maamah ce kawai Bata damuba sbd ba shine a gabanta ba tashin hankali biyu ne suke nukurkusanta,na yanayin ciwon da Amatun keyi da Kuma halinda Abeeda ke ciki.

Anty Farha suna wucewa ticket ta Siya musu suka hau jirgi duk da Yola sukai sbd Mr Jameel ya sanar mata can Akai dasu maamah sun Dena zaman Abuja gaba dayansu har Husnah.

Koda suka is mota Mr Jameel ya aika aka daukosu suka nufo mansion din ASH na Yola din.

Akwai masu aiki already a gidan sedai main gidan a rufe yake Dan haka bayan isarsu take aka bude koina masu aiki suka hau gyara,

Amatu daqyar ta iya tsayawa aka gama gyara koina gidan yayi fes qamshi da sanyin AC suka gauraya koina.

Dakinta data taba zama lokacinda suka baro kauye bayan auren suka sauka wanka tayi da ruwa me zafi sosai sukai sallah taci abinci sosai take ta kwanta bacci ya dauketa.

Itama anty Farha wanka tayi ta Saka kaya marasa nauyi ta kwanta baccin gajiya dana Daren jiyan da Basu yiba

Su kuwa su mum Aisha na can suna bugun hanyar lagos hankalinsu a tashe da tsoron hanya.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

68

**********

Bacci sosai anty Farha da Amatu suka samu Wanda ya Dan sassauta jikin Amatun Dan haka sai a lokacin ta dawo cikakkiyar hayyacinta ta tashi da asuba tayi sallah ta janyo wayarta Dan Neman maamah tajita sbd tsoro ma itama yafara shigarta na tafiyar tasu dan Koda anty Farha ta janyeta daga tafiyar Sam Bata kanta sosai Dan ko tsayuwa Bata iyayi yanda ya kamata Daman Kuma Bata cikin wainda zasuyi tafiyar mota a tsarin tafiyar.

Sam Bata samun wayar maamah duk Kiran datakeyi Dan haka ta hakura ta ajiye wayar.

Dauke wayarta anty Farha tayi tareda kashewa gaba Daya ta jefa Jakarta batareda Amatun ta saniba Dan hanata shiga ko samun Kiran da zai damar da ita Dan kuwa umarnin kukawa da Amatun datasan ko ASH be fada ba to Hakan yake expecting daga gareta.

Har dare yakuma yi su maamah Basu iso ba suna can suna dukan hanya Dan haka da wannan Daman anty Farha tayi amfani ta ringa kulawa da Amatun sosai tareda hanata shiga damuwar abinda ya faru din sedai Amatun ta kasa cire damuwar halinda ASH din yake ciki a yanxu.

Dare nayi da wuri Amatu tayi bacci anty Farha ce kawai ta rage a farke har kusan 12 na dare saiga su mum Aisha sun iso.

Securities na gidan barka da zuwa kawai sukai musu Babu Wanda ya amsar musu kayansu Kuma a napep suka iso Karan farko na rayuwar Husnah da mum Aisha dasuka hawo napep.

Gabaki dayansu su ukun Babu Wanda yake dubuwa sbd azabar hanya da yunwa da masifaffiyar wahalar dasuka sha,

Kowannensu kaman an tsomasa cikin yashi an fitar sbd qura.

Daqyar suka iso ciki barka da isowa anty Farha kawai tayi musu suka bita da kallan mamakin dayake Neman kashesu ta yanda suka riqasu isowa dakuma alaman cikin Hutawa Farhan take ba alamar mota suka biyo.

Kenan jirgi su suka biyo Kuma sun tabbatarda sbd Amatu ne aka sakosu jirgin sukuma aka jefawa hanyar Lagos su duk balain da zai cisu a hanyar ya Dade Bai cinyesu ba kenan.

Maamah ma Sam Babu qarfi a jikinta ga ciwon Rai ga ciwon jiki,

Daki kowannensu ya samu ya fada daqyar suka iya Kai kansu toilet suka sakarwa kansu ruwan zafi kowannensu yayo wanka Husnah ko abinci Bata iya ciba daga zaune tayi sallah ta zube a gurin tafara baccin wahala kaman ta mutu.

Mum Aisha kuwa abinci ta nema taci ta koshi kafin tayi sallah ta kwanta a watse.

Maamah Kam sallah tafara yi itama bayan wankan Bata iya cin abinci ba ruwan zafin tea kawai Tasha Wanda anty Farha ce ta kawo mata tana sha ta kwanta itama.

Kafin bacci ya dauketa Babu abinda takeji a zuciyarta Yana cinta da qunarta irin Jin rayuwar gidan ASH TALBA ta fita ranta gaba Daya,

Babu abinda takeso irin ta Dan tafi ta samu Hutu da Nutsuwar zuciya sbd takasa yarda da Husnah data Rena da hannunta zata iya turo Wani ayiwa Amatu fyade,fyadenma irin na wulaqanci tinda a cikin gida,a cikin gidan ma a lokacinda aure yake kan Amatun Koda kuwa baa son auren ai dai akwaisa Amma a Turo Wani Dan haiqe Mata…

Cikowa idanuwanta sukeyi da hawaye masu radadin gaske da baqin cikin zuciya me tsanani.

Koda gari ya waye Amatu sai ganinsu maamah din tayi sun iso taji tayi farin cikin ganin isowarsu lafiya sbd mahaifiyarta sedai Bata shigewa maamah din sosai ba sbd ganin kowa sedai kallan kallo musamman mum Aisha tanason magana Amma tana tsoron Wani tashin hankalin yanzu batareda sun San me ASH zaiyi dasu ba akan abinda ya faru ganin idansa a Greece.

Husnah qin fitowa tayi daga dakinta sbd kasa iya kallan maamah da batace komaiba akan abinda mum Aisha ta fada hakama Bata sake kallan ko inda take ba Dan haka Se takejin tana shiga shakku da fargaba ga Dad dinta da ko tinawa tayi da shi sai taji hankalinta na Neman gushewa da tashin hankali.

Haka suka wuni suka sake kwana gida kaman gidan mutuwa Babu me walwala kowa Motsawan ASH yake jira,

Babuwa Wanda ya iya kunna wayarsa sbd shakka da tsoro anty Farha ce kawai ke wayoyinta a gidan Kuma kullum sai tayi magana da Mr Jameel Wanda take bawa tabbacin lafiyar Amatu Dan tasan ASH na buqatan Jin Hakan Kodan samun qwarin gwiwan fuskan balain da suka Saka sa a ciki.

Case din dayake kusan police case ne shiyasa Sam Baya samun Daman komai da kowa daga karshe dai aka case din ya mutu ya samu Daman fuskantar Abeedan wadda tini ta sake komawa cikin mawuyacin hali me ban tausayi.

Mr Jameel ne ya duba footage na gidan Dan tabbatarda abinda ya faru lokacinda suke kokarin kashe case din ko zasu samu abinda zai Taimakawa kashe case din Amma abinda ya Gani din ya Sakashi shiga sabon takaicin tabbatarda tarin kolo mentals ne suke zagaye rayuwar ASH.

Mafi abinda yafi daga hankalinsa shine maganar fyaden da ake fada cewan Husnah ce ta aika Naufal,Tayaya zaace ‘yar ASH din ce zataiwa matarsa Hakan bayan a lokacin ma ko noticing dinta ASH din beyiba bare ta damu har da Saka wannan mummunan abin ya faru.

Rasa yanda zai fadawa ASH yayi sedai ya tura masa clip na video din ta wayarsa batareda ya iya fada masa da bakinsa ba.

Bayan ya turawa ASH clip din waya yayi a Yola take ya sallami masu ayyukan gidan guda Daya ya bari hakama securities tini ya sallamesu yabar Daya.

Su mum Aisha na zaune daki kwatsam suka ga wutar gidan ta dauke gaba Daya.

Mamaki ne ya Saka dukkaninsu fitowa Husnah Dake tsananin tsoron duhu tini tafara rawar jiki tana fitowa Neman Wanda zata raba amma ko maamah Bata Gani ba bare iya tinkararta mum Aisha kuwa zafi ne Sam bataso tini tafara Jin kaman zata siqe.

AmatulMaleek Dake daki ma zafin ne ya fara damunta Dan haka anty Farha ta fita Babu jimawa ta dawo mata da rechargeable fans guda uku da manyan fitila sbd tasan aikin Mr Jameel ne wuta a gidan Kuma Se abinda hali ya bayar.

Ko maamah Dake daki Kai tsaye tinaninta yake akan hukuncin abinda ya faru ne zasuyita amsa shiyasa Bata daga hankalinta ba saima sanyi da jikinta ya sake yi.

Tama Rasa tayaya zata fuskanci Amatu akan abinda dukkaninsu sukaji cewan Husnah data fifita akanta itace silan lalacewan ma komai na rayuwar tasu Suma suna zaman zamansu a bangaren masu aiki cikin rufin asiri da Kwanciyar hankali Amma ta tura Naufal ya lalata musu komai gasu yanzu a bagiren da bama Susan sunan alaqarsu ba Dan kuwa a yanzu Amatun gujewa raban maamah din takeyi sbd tashin hankalin da kullum Baya qarewa.

Kwana biyu sukai Babu wuta a gidan take suka fara Neman rasa nutsuwarsu,

Mum Aisha guduwa takeson yi daga gidan saiga Naufal an tattaro an kawo mata a boys quarters na gidan take ta sake shiga tashin hankali sbd tabbas hadesu guri Daya da Akai umarnin ASH ne to me Hakan ke nufi?

Ko dai ta dauke Naufal din su gudu ne to Amma batada gidan kanta ma Bare ta gudun,lalacewan Naufal ta hanasu Tara abinda ya kamata su Tara din gashi komai na Neman kwabewa.

Husnah zaucewa tafara yi,ga rashin sanin halinda mum dinta take ciki sbd ASH ya rufe duk wata hanyar da kowa zaisan me Abeeda take ciki,

Hakama shi kansa Babu Wanda zai taba gwada kiransa yace ya samesa,

Kudi dasuke yanda suke so da su kusan dama gurin Mr Jameel suke karba to Shima kansa shakkar kiransa sukeyi bare ASH da haukansu bema Kai can ba.

Dawowan Naufal ya Saka hankalin maamah fita daga gidan gaba Daya ba a kanta ba akan Amatu dan haka ta Yanke shawarar dauke Amatun su tafi daga gidan kafin ASH ya dawo ayi duk abinda zaayi.

Duk wannan tashin hankalin da kowa yake ciki na Amatu daban ne sbd rashin yin period dinta wata biyu harda Dori ya Sakata shiga mummunan tsoro da firgici,

Kewan ASH da tinanin halinda yake ciki Yana ranta gashi ya Hana kowa ji daga garesa to yanzu Kuma data fara fahimtar halinda take ciki Jin tayi itama tana Neman zaucewa Dan batasan tayaya zata fara tabbatarda idan ciki ne a jikinta Dan haka ma ta fara Hana kanta yawan fitowa itama tana rife jikinta sosai Dan Hana maamah ko kowa fahimtar halinda take ciki duk da Bata tabbatar ba.

Anty Farha Dake zaune tana waya a bedroom dinsu kallan Amatu datai shiru tayi Nisa a tinani tayi tana nazarinta.

Tana gama wayar Amatun ta kalla tana ajiye wayar gefenta tace

“Amatu meyake damunki ne?

Ni na Rasa wannan yawan tinanin da damuwan,

ASH ne??

Juyowa Amatun tayi ahankali tana kallan anty Farha din jikinta na sake mutuwa da yanda maamah zasu San ciki ne da ita ga ASH Baya Nan,tsoro ma takeji na maamah din.

Magana zatai anty Farha din ta katseta da cewa

“Abuja fa nakeson komawa sbd komai acan ya Dan tsaya ana buqatan zuwana gashi kina cikin wannan halin,.abinda ma yasa nayi tinanin tafiyar sbd ganin mutan gidan kaman kowa ya nutsu kafin dawowan me gidan Amma bazan…….

Shigowan maamah dakin ne ya Saka farha da Amatun kallan kofar suna kallanta a natse.

Itama a natsen ta qaraso har inda kujera take ta zauna

Amatu ta Bude Baki ta gaidata hakama anty Farha.

Amsawa tayi a sanyaye tana kallan Amatu data kasa dagowa ta kalleta,

Qurawa Amatun idanuwanta tayi sosai tana kallanta,

Ita duk lokacinda ta Kalli Amatu hankalinta mummunan tashi yakeyi sbd yanayi da kaman datake mata da masu ciki,

Da ace zaman aure Amatun keyi da tabbas zatace ciki ne da ita Amma Sam ta kasa tantacewa ita gaba Daya ma kanta neman juyewa yakeyi shiyasa zata dauki Amatun su tafi ganin gida acan zata gane idan ma Wani abin na jikinta su San abin yi kafin ma kowa ya sani.

Bude Baki tayi tana dawo da kallanta kan Farha tace

“Farha inaga ni da Amatu ganin gida zamu tafi kafin dawowan ASH…..

Wayar da farha ke kokarin dauka ta fasa tareda dawo da kallanta kan maamah din tana cewa

“Ganin gida Kuma maamah?

Ina kenan?

“Kauye zamu je inshallah”

Mummunan faduwa gaban Amatu yayi sbd tsoro da firgicin abinda zai kadaitata da maamah batareda ta tabbatarda da gaske cikin ne a jikinta ba,tsoro takeji su tafi suna zuwa zaa gane ciki a jikinta batasan me maamah zata mata ba.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

69

************

Ita Kuma anty Farha abinda ya fara zuwa ranta shine meyasa zasu tafi ganin gidan haka kawai ana zaune kalau hakama Bada sanin ASH ba Amatun zata iya tafiya ne harma ita maamah din.

Akan Amatu anty Farha ta dawo da kallanta Taga yanda tayi sanyi gaba Daya kanta a qasa.

“Maamah harda Amatun zaku tafi gashi Abuja yakamata ta koma sbd karatunta da zata fara exams satin Nan”

Maamah dagowa tayi tana kallan Farha din tace

“Jarabawa Kuma tana wannan yanayin na yau lafiya gobe ciwo?

Abari dai muje kauyen ko maganin zazzabin muyi tukuna saita dawo ku tafi jarabawan”

Gyara zama anty Farha tayi tana fuskantar maamah da kyau sbd taji ta gwara su koma da Abuja tareda Amatun akan a tafi kauyen da ita sbd abune dama Sam ASH din batajin zai bari wato daukan Amatu tayi tafiya da ita bayan uban girman lefinsu a gurinsa Dan haka cikin lallami tace

“Maamah kiyi hakuri da tafiyan Nan kibari muje tayi exams din ta kammalo tukuna sai mu dawo zuwa lokacin ma ta warware Kuma ko yayane yakamata ASH yasan zakuyi tafiya..

Shiru maamah tayi sbd ambatar ASH da Farha tayi yasata Jin tashin hankalinta dawowa tareda fargaba.

Rokonta Ant Farha taci gaba dayi har ta amincewa tafiyarsu Dan Daman zaman Amatu a Nan dinne Bata so a yanzu da Naufal yake kusa dakuma fargaban ganinta kaman me juna biyun datake Amma batajin zata bari su tafi batareda ta tabbatarda meye ciwon Amatun ba dayaqi warkewa.

Anty Farha na ganin maamah ta amincewa tafiyansu Bata tsaya Bata lokaci ba ta kira Mr Jameel ta sanar masa aka Siya musu tickets washe garin ranar suka tafiyarsu batareda mum Aisha ma ko Husnah ta saniba maamah ce kawai tasan da tafiyan nasu itama bawai a ranar ba ta dauka sai Wani satin Amma suka barta Baki sake suka tafi.

AmatulMaleek na baro gidan Jin tayi nutsuwarta data Dan rasa ta shigeta sbd zamanta guri Daya dasu gaba dayansu hanata nutsuwa yakeyi Dan hatta maamah data haifeta yanzu fargaban kasancewa takeyi da ita Sbd abinda take tinanin tana dauke dashi musamman alqawarin da maamah din ta ringa nanata mata akan kaucewa duk abinda ya shafi ASH har sai ankai karshen matsalar Abeeda data auren nasa.

Ko da suka Isa Abuja gidan anty Farha suka sauka Batada raayin komawa mansion a yanzu da batasan wane rikicin ne Kuma ke tafe ba.

Wanka tayi taci abinci sosai tai sallah ta kwanta bacci.

Anty Farha wanka tayi taci abinci tayi sallah ta zari motarta ta fice zuwa shagonta Dake buqatanta.

Se dare anty Farha ta dawo tareda karima data biya mansion ta daukowa Amatun.

Daki Daya aka warewa karima wadda taji dadin dawo da ita gurin Amatun da Akai Dan haka ba wasa ta fara kulawa da aikin gidan da girkinsu da komai duk da anty Farha na aikin gidanta Bata Wani bari anai mata gaba Daya.

Kaman Daman jiran tafiyan Amatu akeyi a gidan Yola din kusan har ruwan gidan suka tsaya sedai su debo a reservoir da kansu acan gate din Baya na cikin gidan.

Zaman bacin Rai da baqin ciki sukeyi a gidan sbd maamah ko cokali Bata iya fitowa ta taba a kitchen da sunan Wani aikin,hakama me aikin gidan Daya abinci guda takeyi a wuni ta tafiyarta Dan haka kusan ci Daya sukeyi sai kame kame tinda Babu me girkawa,

Husnah Neman haukatata zafi da duhu da wahala ke Neman yi Dan har lokacin maamah Bata ce mata komaiba kaman yanda Bata shiga sabgarta ko Daya.

Mum Aisha kuwa dawainiyar Naufal ce da itace takeyi da kanta sbd ba masu aikin ke Neman zautata gashi a yanda yake dinma baida magana shi Kuma sai ta shidai su tafi daga Nan din kada zafi da duhu su kashesa bayan yasan batada gidan kanta kaman yanda Shima baida gidan kansa din.

Daga karshe mum Aisha masu fixing wutan gidan gaban Daya ta kira Amma securities suka tabbatarda Baa Basu izini ko Bada Daman kowa ya shiga ko gyara komai na gidan ba Dan haka su mum Aisha din suka sake shiga tashin hankalin tsaka me wuya.

Daga mata hankali Naufal yayi dole suka kwasa suka koma hotel sbd masifar tafara musu yawa.

Daga maamah Se Husnah aka bari gidan itama maamah datai Shirin tafiyarta kauye ta kwana biyu tukuna ganin halinda Husnah take ciki ya Sanyata fasawa sbd duk abinda tai mata din bazata iya tafiya tabarta gidan ba kowa ba ba uwa ba Uba Yana budurwa.

Ko sati biyu su mum Aisha Basu qarasa rufawa ba suka dawo sbd kudin datake kashewa sunfara fita hankali kada ta qarar da Yan kudadenta ASH ya dawo ya koresu basuda komai gwara su dawo su hakura suci wuyar har lokacinda zai dawo.

**A Abuja hankalin Amatu ya kwanta kadan tana waya da maamah duk da ba Wani sakewa Amma dai yafi babun sbd har lokacin ta rasa meyasa maamah ta kasa dawo mata daidai,

Anty Farha Kuma tana kulawa da Amatun tana Kuma kulawa da business dinta sai Kuma ASH da koyaushe Yana Jin lafiyar Amatun agun Farha Amma ya kasa barin yayi magana da ita duk azabtuwar dayake yi na rashinta da rashin ji daga gareta sbd laifin da kusan yakeji harda ita kasancewar tana taredasu a lokacinda ya samesu da wannan mummunan aika aikan.

Ganin yanda yake hukuntar da kansa na Hana kansa Gani ko Jin Amatun ya Saka Mr Jameel sake tura masa clip din komai ya sanar masa Daya duba.

Duk wannan lokacin Daya dauka Bai dawoba jikin Abeedan ne sai addua kawai Dan haka baiji buqatan dawowan ba Saida kusan komai ya dawo daidai aka samu kanta sedai tana Nan kwance Amma ansamu Bata koma coma din ba Dan haka ya samu kansa ya dawo daidai ya shirya dawowa.

*******

Yanda ya shareta ya Saka Amatun itama Jin rashin dadi a zuciyarta sosai tareda Shiga damuwa da wasi wasin maganar Husnah ta cewan Babu macen daya damu da ita fiyeda mum dinta,

Tsaya mata a zuciya maganar tayi duk da tasan tabbas mum Abeedan na buqatansa hakama na yanda abin yafaru Bai kamata ya baro ba sai komai ya daidaita to Amma itama meyasa zai hanata jinsa Kokuma shi ya jita.

 Ga ciki dai a jikinta ya tabbata ta rasa Yaya zatai ta fadawa Wani hakama ta rasa Yaya zatai da tashin hankalin datake shiga akan cikin,

Yaya zatai idan cikin ya bayyana ma,

Gashi anty Farha tinda tasan da cikin ta tashi tsaye sosai akan kulawa da Amatun sosai sedai itama har lokacin Bata fadawa mr Jameel ba bare ya fadawa ASH sbd tafison ya dawo yagansa da kansa sbd fitowan Daya fara yi duk da Amatun na rufewa da kaya masu boye ciki yanzu datake sakawa.

Maamah ma nutsuwarta Dan dawo mata tayi sbd Jin shiru maganar komai na ciwon Amatun Bai bulla ba bare zargin da shedan ya Saka mata na cikin ya bulla Dan haka ta samu Dan kuzari da adduar fatan samun lafiyan Abeeda wadda suka San komai Kila yayi sauki tinda dai baa ce ta rasu ba to da sauki kenan lamarin.

Exams din su Amatu suka fara dayake ba Wani interval sai exams din nata suna sauri a satin qarshe da zata gama jikinta ya Dan ringa fara Bata Sabon laulayi zuciyarta na sake cika da radadi da damuwar fitowan da cikin keyi daga ita Se anty Farha ke renansa ba uwa ba mijin ba Yan uwa.

******Ranar Tuesday Wanda yai daidai da saura kwana Daya dawowansa Nigeria yana zaune Yana dubawa footage din da Mr Jameel ya tura masa Babu abinda Bai Gani ba Kuma Bai ji ba a rikicin da sukai suka jeho masa mata daga stairs.

Jajir idanuwansa sukai ya ajiye wayarsa gefensa ahankali Yana Dan lumshe idanuwansa Dan hadiye bacin ransa da zafin da ransa ya dauka sosai.

Shigowan kira a wayarsa ne ya sanyashi Bude idanuwansa batareda ya juyo ya duba me Kiranba Dan bama zai iya dauka ba kawai dai so yakeye ya wutar Dake cin zuciyarsa ta fara mutuwa.

Cigaba da Kiran aketa yi Wanda har lokacin Bai juyo ya Kalli wayarba karshe miqewa yayi tsaye tareda nufar window iskan wajen ya San kado masa sbd ba qaramar wuta da zafi ne yake ci a zuciyarsa ba Wanda Bai taba samun kansa a irin wannan Mafi girman bacin ran da zafin a rayuwarsa ba.

Mr Jameel daketa Kiran wayarsa Baya dauka kasa hakuri yayi sbd tashin hankalin abinda yake faruwa Wanda bazai iya barin ASH ya dandana radadin Dana sanin rashin daukan wannan wayarba har qarshen rayuwarsa ba Dan haka Kai tsaye saman ya hawo ya tsaya kofan dakin nasa ya fara buga kofan ahankali cikin nutsuwa da sanyi.

Bugun kofar ya sanyashi baro bakin window din idanuwansa Jan su na qaruwa ya iso kofar bedroom din ya Bude Kai tsaye ya zubawa Mr Jameel idanuwansa da suka sake sanyaya jikin Mr Jameel yayi qasa da Kai cikin mutuwar jiki da nauyin zuciya Shima ya furta

“Madame Abeeda… Shiru yayi Yana qasa da Kai batareda ya iya qarasawa ba..

Jajayen idanuwansa ya dago ahankali ya sake zubawa Mr Jameel Yana karance yanayinsa a sanyaye.

Ajiyar zuciya ya sauke tareda numfashi me tsananin dumi daya furxo nauyin da kirjinsa ya dauka tareda juyawa qatuwar jacket me tsayi sosai da kauri ya Sako akan kayan jikinsa ya fito Mr Jameel ya biyo bayansa a sanyaye jikinsa gaba Daya a mace.

Daga shi har mr Jameel Babu Wanda ya iya magana mota kawai suka shiga Mr Jameel din na satar kallansa cikin damuwa shikuwa Babu abinda ya iya furtawa asibitin kawai yake buqatan Isa.

Suna Isa asibitin Kai tsaye dakinta ya nufa bugun zuciyarsa na qaruwa tareda nauyin kirjinsa yana Isa ya Bude dakin Kai tsaye ya shige da saurin ya Isa kanta sedai hannunta kawai ya kama da nasa ahankali tareda kallan idanuwanta data Bude ahankali ta kallesa da ganinta Daya fara bacewa cikin Wani hali me sanyi ta Dan motsa hannunta Dayake cikin nasa ta Dan kama nasan itama.

Qanqame hannunta yayi ahankali zai Bude Bakinsa da yayi masa tsananin nauyi Bai furta abinda zai furta ta rufe idanuwanta.

Likitan dasuke kanta ne Basu saddakar ba zasu cigaba da Jan numfashinta Rai yayi halinsa.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

70

************

“P name Ms ABEEDA TALBA,

Time of dead 10:26 4th Dec”

shine abinda yake shiga kunnuwansa ahankali ya rufe idanuwansa ahankali hannunsa har lokacin Yana riqe da nata kafin ya Bude idanuwansa dasuka qarasa rikidewa ya zuba mata duk Wani jarumtarsa ta ciki tana tarwatsewa Dan kuwa Abeeda nata matsayi me kyau da girma a zuciyarsa na zamtowarta mata Kuma uwar yayansa hakama respect din dayake Jin tana dashi a gunsa yanada girma.

Hannunta aka zare ahankali daga nasa tareda ajiye mata shi straight gefen jikinta aka rufeta akan idanuwansa aka kashe komai na naurorin da duka suke jikinta bayan an zaresu Daya bayan Daya.

Mr Jameel Dake daga bakin kofa duk zamansa namiji kasa riqe hawayensa yayi Ms Abeeda mutum ce mai zuciya me kyau da sanyi daga karshe dai bayan jinyar shekara da shekaru ta rasu tabar mijinta da yayanta da duniyar gaba Daya.

ASH TALBA wannan Daren dare ne Daya girgiza duniyarsa tareda jijjiga zuciyarsa datake da tsananin jarumta sbd rashin Abeeda uwar yayansa dayake Jin tsananin tausayi da radadin jinyar datasha tareda azabar ciwo dakuma azabar dasu Husnah suka dandana mata a cikin Mafi azababbiyar hanya Dan kuwa ko daurirrikan da Akai mata na fadowar a jikinta sunkai biyar,Tasha wuya Tasha azaba gashi Babu karfi ko iKon motsawan da zata rage Mata azaban datake ciki.

Fitowa dashi Akai daga dakin aka bar gawan ta gama mintinan da ake diban mata kafin zuwa da ita inda zaa ajeta.

Mr Jameel Bai Taba ganin abinda yayi breaking ASH TALBA ba sai a ranar sbd har cikin ransa yakejin azabar da Abeedan ta shiga ciki a kwanakin na jinyarta data dawo sabuwa,

Daga shi har Abeedan sunsan tin farko bazatai surviving ba sbd stage na cancer dinta Amma Abeeda dashi kansa suka zabi Takoma gida cikin familynta ta qarasa jinyarta acan tayi spending days dinta ka karshe cikin yayanta da Yan uwanta Ashe batada Rabon ganin Hakan.

Basu baro asibitin ba sai kusan asuba suka dawo sallah yayi ya ringa yimata adduar samun Rahama Saida yazo shafa adduar wasu irin hawaye masu zafi suka tsinke masa ba zato kuka mara sauti ya kufce masa Dan kuwa nauyin zuciyarsa ya kasa riquwa.

Tausayin Abeeda da rashinta da tausayin yayansa sune suke yanka zuciyarsa suna tarwatsata.

Kafin safe zuciyarsa ta jigata sosai sedai Kuma haka Allah ya qaddara masa Yana fatan mutuwa gareta ta zama Hutu da Rahama Dan haka ya riqe jarumtarsa ya Saka Mr Jameel afara shirye shiryen yanda zasu iso da gawar Nigeria.

Shi kansa Mr Jameel Bai sanar da kowa ba sbd tinda Mai gidan nasa ya shige Shima yake cikin tsananin sanyin jiki da nauyin zuciya na rashi da Akai.

Asibiti suka tafi aka fara Shirin komai Dan tafiya yakeson suyi da ita ba Bata lokaci sbd a samu suturtata kan Lokaci.

Anty dinta dake qasar Greece din tareda ita dayake tinda ASH yazo qasar itama tayi tafiya ta huta bataji rasuwar Abeedan ba Saida aka gama komai na taho da gawarta ya kirata ya sanar mata take ta Yanke jiki ta Fadi sbd batama San Abeedan ta koma asibiti ba tinda tasan dai an koma gida da ita.

Ko data farfado aka fara Neman numbern ASH din sun Riga sun taso suna jirgi Dan haka baa samunsa take maganar rasuwar ta fara yaduwa zuwa porthcrt aikuwa take kowa jikinsa yayi sanyi duk da doguwar jinyarta tasa ake Saka ran rasuwar tata koyaushe Amma Kuma rasuwar ta daki kowa sbd Tasha wuyan jinya, ta tafi batareda ta dawo cikin Yan uwanta da yayanta ba datake ta fata da buri.

Kasa sanarwa Husnah rasuwar Akai sedai kawai aka aika musu cewan su koma Abuja dukansu Banda Naufal da suka bari gidan.

Dayake duk a matse suke cikin qunci a gidan take washe gari suka tattara Faisal ne da kansa yazo har yolan ya siya musu tickets suka wuce abuja.

Tinda suka baro jikin maamah yayi sanyi sbd abinda takeji a jikinta na ba lafiyan ba,

Ita kanta Husnah jikin nata a sanyaye yake sedai Kuma baro wancan gidan datai Yana Sakata Jin nutsuwa sbd kullum Bata iya bacci yanda Taga Rana haka take ganin dare Sam Kwanciyar hankalinta ya qare a qunci take wuni a qunci take kwana Se mafarkin mum dinta datake yawan yi gashi ba daman waya da Dad din bare taji Yaya take.

Koda suka iso Mansion din mutanen porthcrt sun rigasu isowa Dan haka take maamah jikinta fara Bata

Ita kanta mum Aisha zuwa lokacin jikinta yayi sanyi Kuma itama take tinanin Abeeda ta rasu yazo kanta

Husnah kuwa ganin dangin mum dinta a gidan ya Sanyata tsayawa cak tana kallansu tinanin dalilin zuwansu na tsinkar da zuciyarta sbd Basu taba zuwa dubasu ba tinda mum din tabar qasar sedai su suje duba su,Basu taka Tako kafarsu inda suke ba sedai idan sune suka je to meyasa sukazo dukkaninsu yanzu?

Maamah kasa riqeta qafafuwanta sukai ta zame qasa tana zauna qasan palon tana kokarin riqe abinda take ji a zuciyarta sbd fatan ba abinda tinaninsu yake Basu bane.

Mum Aisha ma a silale ta zauna tana kallan su mommyn porthcrt din da dukkaninsu suka kasa dagowa su Kalli Husnah.

Husnah dauke jajayen idanuwanta tayi daga kansu tareda Maidasu kan maamah sbd maamah dince zuciyarta kawai ke buqatan magana da ita bayan tsowan lokacinda maamah din ta dauka ko kallan inda take Batayi bare ta Bata Daman kare kanta ko musawa zancen mum Aisha data fada wanda kusan Hakan ne yake qara zarar da ita.

Qafafunta kasa daukanta sukai ta zube da rarrafowa ta iso gaban maamah ta kama qafafunta muryarta na rawa tace

“Maamah meyasa kike kokarin yin kuka bayan Babu abinda aka fada daga shigowanmu?

Gurin mummyn porthcrt ta rarrafa ta koma cikin murya me rawa tace

“Mummyn porthcrt me yake faruwa kuka taho?

Wani abu ya faru?

Kunyi waya da Dad dina ne??

Kasa magana mummyn tayi sai kokarin riqota datake yi zatai magana Amma Husnah din ta janye tana cewa

“Ku fadamun abinda yafaru kuka taho ni shi nakeson fara ji”

Faisal Daya shigo lokacin jikinsa a mace kallan Husnah din yayi zaiyi magana ta qura masa idanuwanta dasukai jajir Bata ko kyaftawa sbd tabbatarda abinda zai fada din.

Ahankali ya Bude Baki zaiyi magana jiniyar motan data dauko gawan ta shigo mansion din alaman su ASH din sun iso.

Gabaki dayansu kofa suka kalla Husnah jikinta Yana saki gaba Daya maamah kuwa kukan daya danne zuciyarta ne yake kokarin fitowa tareda idanuwanta Dake zuba mata radadi me zafi.

Juyawa Faisal yai ya nufi kofan palon ya fice da zuwa harabar gidan.

Husnah kuwa mummy ce ta riqota jikinta ahankali hawaye na gangarowa kowa Dake palon.

Isowar gawar matar ASH TALBA ya qara yada zancen rasuwar da jana’izan da zaayi Dan haka duk Wani abokin huldansa da muaamalansa suka shiga alhini da jimamin rasuwar.

Kusan Yan uwansa na kusa da dangin Abeedan tini suka iso duk suna mansion din Wanda hatta securities da masu Aiko kowa jikinsa a mace yake har aka shigo da gawar palon qasa aka ajiye take Husnah ta saki jiki a jikin mummyn porthcrt din a sume.

Maamah ma take zuciyarta ta fara Hawa sama numfashinta na kokarin daukewa khaltume ce sukai kanta suna kokarin ganin Bata shiga halinda take Neman shiga ba.

AmatulMaleek anty Farha Bata sanar da ita rasuwar ba sbd itama Saida su ASH din jirginsu ya sauka Mr Jameel ya sanar mata take ta shuga mummunan tashin hankali Dan haka Kai tsaye shagonta ta bari ta wuce school ta dauko Amatu data gama exams dinta a ranar.

Amatu kallo daya tayiwa anty Farha din ta fahimci damuwa da sanyin da jikinta yayi.

Jin tayi nata jikin yayi sanyi bare Daman ba Wani kuzari ne da ita ba Dan haka ta Dan sauke numfashi me sanyi a hankali tace

“Anty Farha lafiya dai kuwa?

Wani abu ya faru a spa ne???

Anty Farha din kasa juyowa tayi ta kalleta sai hanyar TALBAs mansion data dauka a hankali cikin sanyi tace

“Su maamah sun dawo suna mansion zamuje gurinsu ne”

Juyowa tayi ta Kalli anty Farha din da idanuwanta dasukai laushi cikeda mamaki da fargaban lafiya..

Kasa cewa komai tayi sbd tinanin data shiga tanajin jikinta na sanyi hakama anty Farha din ma jikinta a sanyaye yake.

Shiru sukai Babu me magana sai anty Farha din da ake kira Akai Akai tana amsawa Wani Kiran Kuma Bata ma iya amsawa sbd batajin dadin zuciya.

Yanayin anty Farha din ya sake Sakata cikin yanayin tinani da fargaban dole Wani abu ya faru kenan tinda tayi waya da maamah da jiya da safen Nan ne kawai basuyi waya ba sbd tinda safe ta fita exams dinta Kuma Bata sanar mata zasu taho Abujan ba,

Hakama idan sunzo anty Farha bazatai sanyi haka ba,hakama tayaya zata fuskanci kowa da ciki kwatsam a jikinta.

Harbawa zuciyarta tafara yi tanajin gefen cikinta Daya fito duk da ba sosaiba kana gani zakasan ciki ne na haihuwa a jikinta Yana daurewa.

Waiwayowa anty Farha tayi ta kalleta cikin kulawa tana Maida kallanta kan gefen cikin data Dan riqe cikin cikin kokarin kawar da damuwarta tace

“Lafiya dai?

Me kikeji?

Cikin na ciwo ne?

Karfa ki daga hankalinki sbd Kinga yanayinki.

Kasa magana Amatu tayi sbd zufan data fara hadawa lokacinda suka shigo street na gidan take taga alaman akwai abinda yake faruwa sbd securities din gidan kusan duk suna waje sbd motocin da suke harabar gidan.

Suna isowa aka Bude musu gate suka shigo Tin anan Amatu jikinta ya Dan fara rawa ganin Mr Jameel ya fito hanyar zuwa palon ASH na qasa Yana waya idanuwansa jajir take ta tabbatarda ASH ya dawo kenan.

Nauyi idanuwanta da zuciyarta suke sake shiga sbd fara fahimtar abinda ya faru,

Anty Farha dole riqe hannuwanta tayi suka nufi ciki suna Saka Kai a palon qasa din akan gawar da aka gama shiryawa ta Madame abeeda idanuwan Amatu suka fara sauka

Cak ta tsaya anty Farha na sake riqeta da kyau sbd jirin Daya dibeta idanuwanta na kan gawar.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

71

************

Cikin qarfin hali anty Farha ta sake riqeta da kyau tana Bata kariya daga jirin dayakeson dibanta tana Jin itama firgici Yana kamata sbd ganin gawa kwance gabansu.

Kama Amatu tayi suka qaraso cikin palon dakyau Wanda yasa wainda keda Dan sauran karfin hali juyowa suka kallesu Amma su maamah Kam da Husnah Babu me qarfi bare hankalin juyowa su kallesu.

Hawaye ne suka ciko idanuwan Amatun suna gangarowa rawar jikinta na bayyanuwa sosai sbd a take tasan Mum Abeeda ce ta rasu itace a kwance a shirye.

“Innalillahi wainna ilaihirrajiun” take furtawa daga bakinta Amma Sam kalman taqi fita sbd kasa tsayuwa da qafafunta datai sbd shock da tashin hankali Dan haka ta silale a gurin jikin anty Farha wadda itama ta bita qasa tana rungumota cikin tsoron kada Wani abun ya sameta sbd firgitan rasuwar.

Mum Aisha da tinda suka shigo ta zubawa Amatun idanuwanta tana kallan cikinta Da suna shigowa akansa Idonta ya fara sauka tini ta taso Dan tabbatarwa ta kamawa farha Amatun tana cewa

“Ciki ne ita??

Idan ciki ne Kam to kuyi sama dakinta ku zauna kada ya bare sbd tashin hankalin ganin gawa.

Anty Farha Bata iya amsa mum Aisha dinba kokarin bawa Amatu data rikice gaba Daya hakuri da kalaman da zasu dawo da ita daidai takeyi Amma gaba Daya Amatun ta rude sbd Daman kafin isowarsu a rude da tashin hankalin take sai gashi ta tadda abinda ya qarasa rikitata ga kukan Husnah Dana maamah dayake tashi cikin palon cikin Wani sauti me yanka zuciya Dan dukkaninsu ganin sukeyi sune silan rasuwar nata,

Maamah ganin takeyi da Bata biye tashin hankalinsu ba ta tsaya ta tare Abeeda da Kila Bata fado ba,

Husnah kuwa Kai tsaye tasan itace sanadin halakan mahaifiyartata hakama a lokacinda ya kamata ace ta tsaya ta gana sosai da mum dinta kafin lokacin rasuwar tata Amma gashi ta rasu batareda sun sake ganin juna ba.

Amatu Sam ta gagara taruwa gabaki daya ma Neman sumewa takeyi Dan haka dole mum Aisha din anty Farha ta Saka ta kama mata ita sukai sama zuwa bedroom dinta sauran mutane na binsu da kallo cikin tausayawa Amatun sbd ganin juna biyu a tareda ita duk da basu ganeta ba Basu San itace ‘yar maamah din da ASH yake aure ba.

Suna wucewa sama aka shigo daukan gawar Abeedan Dan ficewa da ita sbd anriga anmata sitira,

ASH dinne da kansa Se Haydar da Abdulhameed Wanda isowarsu kenan ko zama beyiba suka fito da gawar.

Husnah Wani irin kuka takeyi da ko fitowa ya Dena yi sbd wahala da tsananin Wanda taita yi tinda suka iso,

Maamah ma kusan siqewa take Neman yi kafin kace me zuciyarta ta riqe sedai aka kwasheta daga gurin da sauri itama Akai dakinta da ita su khaltume suna mata firfita kafin agama jana’izan a kira mata likita ko kaita asibiti sbd abin yafara Basu tsoro ma.

Husnah ma birkicewan tayi a gurin take ta sake somewa Akai kanta itama ana Neman cetan ranta.

Haydar kuwa kuka ne yakeyi sosai da da sosai sbd bayan tashin mum dinsu baa sanar masa komaiba hakama ko dayaje ganinta Greece yaga alaman sauki a tattare da ita harya tafi yabarsu Husnah da maamah baiga alaman ciwonta zai tashi ba sai kawai rasuwarta kwatsam.

Shi kansa Abdul yayi kukan rasuwar sbd tausayin Haydar da Husnah wadda kusan itace ma tafi basa tausayi tinda yasan depression datake fama dashi.

Anyi jana’izan Madame Abeeda Talba ankaita an rufeta aka dawo Karban gaisuwa Wanda akeyi a mansion din din cikin babbar palon ASH din Dayake qasa Wanda yake ganin baqi.

Acan cikin gidan ma a palon qasa ake karban gaisuwan,

Maamah da Husnah dole aka kira musu likita ya dubasu sbd suna dakunansu a kwance jikin ba sauki.

Amatu kuwa tinda suka kwantar da ita a gadonta hankalin anty Farha ke sake tashi sbd yanda gaba Daya jikinta ya rikice ga Mum Aisha ma ta tsaya tana nuna damuwanta sbd a yanzu data tabbatarda tasu ta qare a gurin ASH so zata nunawa Amatun da cikinta ko zata samu sassauci a gurinsa.

Kokarin saukar mata da zazzabinta anty Farha ta ringa yi kafin a gama jana’izan ta kira likita itama sbd yanzu ko ta kira Likita ana kokarin jana’izan ne bazata samu shigowa ba.

Mum Aisha ma haka ta ringa kaida kawo tsakanin palon qasa gurin karban gaisuwa da bedroom din Amatun har anty Farha ta gaji ta rufe dakin Dan mum Aisha din ta isheta bayan damuwan datake ciki na Amatun.

Dr beeba ta kirawa Amatun Se data Dan jima kafin tazo sbd tana asibiti ko da aka kirata Dan haka Koda ta iso Amatun ta gama galabaita harda ciwon mara har tayi baccin wahala Dan har kusan yamma ma tayi.

Dayake ba mutane sosai Tinda gaisuwan duk Wanda yayi ba zama yakeyiba wucewa yakeyi sbd kowa bayason zaman gaisuwar daga masu karban har masu zuwan tinda Wani lokacin zaman baida Wani amfani gwara kayi ka wuce.

Mum Aisha ce tayiwa Dr beeba jagora zuwa sama har dakin Amatu sukai knocking anty Farha ta taso ta Bude tana ganin Dr beeba ta saki ajiyan zuciya sbd ta fara saddakarwa da kawai ta dauki Amatun su tafi asibiti,

Bata kira Mr Jameel ba ta sanar amsa sbd kada a sanar da ASH a daga hankalinsa ayau dayake buqatan a barsa yaji da abu Daya tukuna.

Qarasowa ciki sukai Dr beeba na musu gaisuwan rasuwar tana nufar Amatu Dake kwance tana bacci a wahalce.

Zaunawa tayi tareda kallan Amatun tana kamo hannunta Daya Dayan Kuma tana Dan yaye rufarta ta Kalli Dan qaramin cikin tana dawo da kallanta kan Farha tace

“Meyasa Baki fadamun tana da ciki ba da bazan Dade haka ba ai zanyi kokarin zuwa kan time gaskia.”

Kasa cewa komai anty Farha tayi sai numfashi me dumi data sake jiki duk a mace sbd yunwa da damuwa dakuma ciwon Amatun.

Fara dubata Dr beeba tayi tana Ciro wayarta Dan Kiran asibiti akwai abinda zaa kawo mata.

Mum Aisha fita tayi Takoma qasa duk an watse sbd sallan magrib da Kai kusan duk Yan gidan ne suka rage Dan haka itama dakinta ta nufa ta shige qafafunta duk ciwo suke mata sbd Hawa da saukan benan data ringa yi,Ina dalili ta fada tana zubar da kayan data cire Dan wanka ko jikinta ya sake mata.

Dr beeba kuwa har bayan isha takai a gidan kusan after 9 ma Saida jikin Amatun ya Dan dawo daidai kafin ta fito ta tafi bayan ta sake duba Husnah da maamah wainda suka sai alokacin kowannensu ya samu baccin wuya ya daukesa.

Amatu kuwa wanka anty Farha ta Sakata tayi da ruwan zafi sosai jikinta ya Dan sake sakewa kafin ta fito ahankali ba qwarin jiki ta zauna ta Saka kayan sanyi kawai ko Mai Bata buqata.

Milk tea me kauri sosai da soyayyan  indomie me kwai da veggies anty Farha ta kawo mata Wanda itace da kanta taje kitchen ta dafa Mata ta dawo.

Duk da cikinta Baya hakurin yunwa yau hakanan ta wuni Bataci abincinba Dan haka ta daure daqyar take cusa abincin tana Shan tea din harta shanye tea taci kusan fiyeda Rabin indomie din ta aje.

Magani anty Farha ta Bata Wanda ba komai bane face su folic acid da sauransu,

Tana Shan maganin ta kwanta sbd gidan yayi tsit alaman kowa ya shige.

Anty Farha kanta wanka tayi taci abinci ta kwanta tareda kashe wayarta sbd itama zuciyarta daci take mata.

Kwanan damuwa da sanyin jiki Akai a TALBAs din Kuma kusan ba kowa ne yayi bacci ba kwance kawai wasu suke Amma baccin Kam bazai iya zuwaba.

Tinda safe kusan kowa a dakinsa yayi breakfast suka fito sbd baqi masu zuwa.

AmatulMaleek ma hakanan ta daure duk da tanajin jikin sukai wanka shirya suka fito itada anty Farha suka zauna palon qasa bayan tayiwa duka dangin mum Abeedan gaisuwa tareda Husnah wadda ko iya Bude idanuwanta dakyau Bata yi sbd nauyi da kumburinsu.

Dakin maamah da Bata iya fitowa sbd jikinta suka tafi itada anty Farha.

Doguwar Riga ce a jikinta da hijab har qasa Wanda ya boye Dan cikinta, fuskarta tayi haske sosai tareda Dan fadawa kadan duk da ta sauya sosai zuwa matar da Hutu ya gama ratsawa.

Itace a gaba kafin anty Farha suka shigo palon maamah Bata qaraso tsakiyar palon ba Idanuwanta ya sauka akan Haydar Dake zaune tareda Abdulhameed abincin breakfast ne Jere a gabansu Amma tea kawai suke sha Se Dan banana bread din dayake hadawa dashi shi kuwa Abdulhameed ita yaketa kokarin kira sbd tinda suka iso Basu ganta ba gashi ba Daman shigowa har sama sbd mutane Dake gidan da dare Kuma anty Farha ce ta sanar musu tayi bacci.

Cak ta tsaya jajayen idanuwanta da suka Dan kumbura akansu tana kallansu jikinta na sanyi hakama tanajin hawaye na ciko idanuwanta sbd batai tsammanin ganinsu ba adaidai lokacin da take tsananin buqatansu duk da Shima Haydar Yana buqatansu.

Haydar Daya ji tsayuwarta dagowa yayi ya zuba mata idanuwansa dasukai ja Yana kallanta batareda ya motsa ba sbd gabaki daya Jin yayi duniyarsa ta tsaya sbd ganinta ya fama raunin jarumtarsa na rashin mahaifiya Dan haka hawaye masu radadi suka ciko idanuwansa batareda ya sani ba sai gasu suna gangaro masa har lokacin idanuwansa na kanta.

Itama hawayen cikin idanuwanta ne suka fara gangarowa tanajin tausayinsa Yana danne duk wata damuwarta da quncin datake ciki daban daban.

Abdulhameed Dayaga Hakan da sauri ya taso Shima cikin tsananin tausayin Haydar dayasan shine itama a ranta dakuma damuwar dayasan tana ciki tinda komai nasu basa boyewa juna.

Rungumeta yayi ahankali itama qanqamesa tayi tana fashewa da kukan damuwoyin Dake kwance a ranta suna cinta batada abokin kokawa bayan anty Farha wadda take danne qarfin damuwarta a gabanta sbd kada ta Sakata damuwa da rashin walwala duk kokarin datakeyi da ita.

Runguman da Abdulhameed yayi mata ya sanyashi Jin tudun cikinta

 ahankali ya saketa tareda dagota daga jikinsa yana kallan cikinta Dayake cikin hijab,

Kan fuskarta ya dawo da kallansa cikin tsananin mamaki da kasa yadda da cikine a jikinta.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

72

*************

Kokarin boye mamakinsa Abdulhameed keyi sedai ya kasa boyuwa Dan haka ya zuba mata idanuwansa dasuke a bushe tin jiya sbd Radadin rasuwar,

Qasa tayi da kanta tana kasa kallansa hawayenta na tsananta gudu Dan kuwa Bata sanar masa tanada cikin ba sbd kunya.

Juyawa yayi ahankali ya Kalli inda Haydar yake zaune har lokacin idanuwansa akan Amatun hawayensa na saukowa ahankali.

Dawo da kallansa yayi kan Amatun tareda janyewa gefe Yana boye mamakinsa ya Bude Baki ya gaisa da anty Farha sukaiwa gaisuwan rasuwar kafin ya Kalli Amatun itama Yana mata gaisuwan rasuwar mum Abeedan.

Amsawa tayi muryarta a qasan makoshi da sanyi kafin ta daga kafafunta ahankali ta Isa gurin Haydar Wanda Bada tanada aure akanta ba aurenma na Dad dinsa da saita rungumesa ta rarrashesa sbd tana iya hango radadin dayake ciki na rashin uwa wadda duk girma da tsufanka ita uwa rashinta radadinsa daban yake.

Shi kansa Badan girma da yayi ba ya sake zama matashin gaske da Babu abinda zai hanasa runguman Amatun sbd ita kadaice a yanzu zata sassauta masa radadin da zuciyarsa keyi na rashin mahaifiyarsa.

Zaunawa tayi a gefensa ahankali a darare tana sake boye cikinta sbd idansa akanta suke.

Anty Farha ma da Abdul zaunawa sukai anty Farha na masa gaisuwa cikin kulawa da nutsuwa

Shima a natse ya amsa gaisuwar tareda Godia.

AmatulMaleek ma ahankali ta dago idanuwanta cikin nutsuwa da sanyin jiki ta Bude bakinta tai masa gaisuwa tareda yiwa Madame Abeedan addua da fatan samun rahamar ubagiji.

Amsawa yayi Yana dauke kallansa daga Amatun sbd adduarta ta sanyaya masa zuciya.

Shiru gurin ya dauka sbd kowa da abinda yake ransa,.anty Farha kuwa kallan Haydar din da kusan duk kamannin ASH ne a fuskarsa hakama jikin irin nasa ne kakkarfa ingarma hakama bazaka Kalli ASH Kai tsaye kace shine ya haifesaba sedai kace qaninsa ne,

Daga Haydar din har Abdulhameed Wanda shikuma kamansa da Amatu ne ya qara bayyana sosai sun zama matasa sosai Dan kuwa kusan bazaka gansu kace sune qannan Amatu da Husnah zaka dauka sune yannen su Amatun nesa ba kusa ba sbd zamansu a qasar turai sun sauya sosai geamin sukeyi Daya qara budesu ya sake boye shekarunsu duk da suka shekarun sun fara dagawa.

Kasa cewa komai tayi da Shirun yayi yawa ta miqe ta shiga dakin maamah Dake kwance ba bacci takeyiba Amma tana Dan jin jikin tai mata sannu harma da gaisuwan rasuwar ta zauna shiru tukuna ta fito.

Amatun duk da itama ba lafiyar ne da ita ba Haka ta Dan sake matsawa Haydar din yaci abincin dayake gabansa,.

Sama sama ya qara cin abincin kafin yafara ficewa ya tafi dakinsu yayi wanka ya fita gurin gaisuwa.

Abdulhameed ma sama sama sukai magana da Amatun a agaban anty Farha da tasan komai kafin ya fice Shima yaje yayi wanka ya fita wajen.

Suma anan palon maamah suka wuni sai bayan Azahar da zazzabin Amatun dai yayi Dan yawa suka koma suka dan sake zaunawa a palon sedai ko mintina arbain basuyiba ta kasa dole suka koma daki ta kwanta tana tsiyayar hawayen abinda takeji.

Yauma har dare mr Jameel kansa baiji daga anty Farha ba bare sanin ya Amatun take Dan itama anty Farha din tafara Jin zafin abinda akaiwa Amatun Dan haka Shima Mr Jameel din ta tattarasa ta aje Dan batajin shima Yana buqatan sanin me Amatun take ciki bare ubangidansa.

Maida hankalinta kawai tayi gurin kulawa da Amatun tinda kowa Wanda ya damu dashi yake kulawa.

Husnah dangin mum dinne suke kulawa da ita,

Maamah Abdul dasu khaltume ne suke kulawa da ita harma da Haydar Wanda Shi Kuma Abdul yake kulawa dashi.

Maigidan kuwa har lokacin Babu Wanda ya gansa sbd daga can yake shigewa sashensa.

Kwana bakwai da rasuwar kowa ya watse Dan haka aka bar mutanen gidan Se masu aikin gidan Dan haka gida ya sake daukan tsit.

Amatu sosai taji jiki a kwanakin Amma sbd anty Farha da Abdul dasuka tsayu akanta Taji sauki batareda har lokacin maamah tasan ciki ne a jikinta ba harya Dan bayyana,

Hakama Husnah batasan da cikin ba sbd har lokacin Bata dawo daidaiba Saida kowa ya watse ta Dan dawo daidai sedai tana cikin mummunan halin tausayi dan kuwa ko ruwa daqyar takesha abincima Daman turawa kawai takeyi.

Mum Aisha kuwa har lokacin ita dai a tsinke take da abinda zai biyo bayan watsewan zaman gaisuwar sanin sune sukai sanadin fadowar Abeedan Wanda ta tabbatarda ASH bawai mantawa yayi ba shiru yayi ne kawai Wanda Kuma Shirun shine abin tsoro da fargaban.

Anty Farha tana waya yanzu da Mr Jameel Amma Bata taba fada masa maganar Amatu ba hasalima ko shine ya tambaya lafiyar Amatun yi take kaman bataji ba,ita jin ma takeyi kaman ta dauke Amatun su koma gidanta tinda kaman babu me buqatanta a gidan bare kulawa da ita.

Ita kanta Amatun magana ne kawai Batayi zuciyarta a cike take da qunci da damuwa Amma Bata taba nunawaba zaman daki ma kawai ta koma yi koina bata fitowa taje har maamah ta Dan warware Bata sake zuwa dubota ba sbd itama jikin take ji.

Haydar kullum Yana shigowa ya duba Amatun Amma Bata taba barin yaga cikin dayake jikinta ba Shima kuka baitaba kawo tinanin samun ciki a jikin Amatun ba Dan haka sosai yake Bata kulawa da ita da Husnah wadda a yanzu Haydar ne abinda zuciyarta ke tsananin son kasancewa dashi Se maamah wadda Kuma tsoron ma zuwa inda take takeyi Amma a yanzu harda maamah take buqata sbd Dad dinta tsoron ma ganinsa takeyi.

Yau anty Farha zata koma gidanta duk da kwana Daya zatai ta dawo da karima da suka baro acan,

Hankalin Amatu Bai tashi ba sbd tasan anty Farha din tana kokari sosai Dan haka saita danne damuwarta ta nunawa anty Farha din ba damuwa zata iya zaman ko Bata Nan.

Bayan tafiyar anty Farha din babu Wanda ya sake leqowa inda take haka ta wuni ta kwana sbd su Abdul Basu wuni gida b da Haydar komawa zasuyi a kwanakin.

Washe gari da safe wanka tayi taci abincin da Farida ta kawo mata tana cikin ci anty Farha ta dawo gidan tareda karima wadda ta hawo da kayan Amatun Dake gidan anty Farha an tattaro andawo dasu.

Gama cin abincinta ko dauke abincin data gama ci ba’aiba amai ya taso mata Dan haka ta sauri ta tashi ta fada toilet tafara Amai me qarfi Wanda ya tafi da qarfinta sosai.

Ko data gama tayi laushi sosai rigarta kusan ta Dan lalace da aman Dan haka wanka ta sake yi ta fito daure da towel me Dan girma ta zauna kadan ta shafa Mai da tirare ta Saka doguwar rigar material me tsantsi da laushi me Fadi sosai da tsada duk da bazaka gansa kace me tsadan bane sbd na Shan iska ne.

Lafewa rigar tayi a jikinta kaman fata tareda bayyanar da cikinta sosai da sosai.

Kokarin zaunawa takeyi bakin gado aka Turo kofar dakin ahankali Bayan anyi knocking so Daya Dan anty Farha Bata dakin ta fita.

Husnah ce idanuwanta a kumbure hakama fuskarta Dan har ranar ta kasa Dena kukan mum dinta,

Zuciyarta ta kasa riqe tsananin buqatanta da kewan maamah Dan haka ta danne abinda takeji tazo bawa Amatun hakuri Dan ta shiryata da maamah sbd tana tsananin buqatanta a yanzu.

Juyowa gaba Daya Amatu tayi tana kallan Wanda ya shigo idanuwanta suka sauka akan Husnah wadda ta qame cak a inda take tana kasa daga qafarta ta qaraso tsakiyar dakin sbd abinda idanuwanta suka sauka Akai wato cikin Amatun da yake kusan wata hudu harma ya fita.

Rawan disco qafafunta suka fara yi tana Jin zufa Tako Ina Yana Neman jiqata,

Kasa dauke idanuwanta tayi akan cikin duk yanda taso sbd shock da rikicewan da ganinta ke Neman yi.

Amatu ma kasa motsawa tayi daga inda take tsayen cikin tsananin mamakin ganin Husnah a dakinta da Kuma shakkan kallan datakewa cikinta cikin mummunan halin tashin hankali.

Magana zatai Husnah ta rigata muryarta na yankewa a daburce da cewa

“Cikin haihuwa ne wannan Amatu??

Ciki gareki?na haihuwa ne kokuwa?

Na mutum ne ko aljanu Amatu?

Tambayoyinta ne suka Saka zuciyar Amatu daci da mamakin haukar Husnah da Bata warkewa,

Bazata iya tashin hankalin dasuka Saba ba sbd abinda yake gabanta ya isheta Dan haka batajin tanada lokacin amsa tambayar me kama da tabin hankali Dan haka zaunawa take kokarin yi ta nufi kujera tana cewa

“Lafiya kika zo nan din?”

Bata zaunaba Husnah din cikin ihun kuka jikinta na wata irin rawa tace

“Ciki ne wannan din da gaske?

Cikin haihuwan mutum da gaske??

Fasa zama Amatu tayi tana hana zafin dayake ranta fita sbd gaba Daya gidan da mutanen gidan itama sun isheta kaman yanda suke ganin ta ishesu itama ta gaji harma da Wanda duk akeyin rigimar akansa duk ta bar musu itama ta gaji.

Kallan Husnah din tayi tareda nuna mata kofa tace

“Ki tafi kiyi harkanki a inda Zaki samu me kulawa da ita ni na gama da matsalarku.”

“Wlh Karya kikeyi saikin bani amsata idan ciki ne wannan ko sakawa kikai kice cikin ne Dake…..

Kama hannunta Amatu tayi ranta ya gama Baci zuciyarta zafi takeyi batama San tanada karfin Jan Husnah din ba Sai data janyota kaman kayan wanki ta Turota waje zata rufe dakinta Husnah din ta tare kofar itama cikin tsananin radadin zuciya jikinta na rawa ta kasa yarda da mum dinta tana cikin ciwon mutuwa har Amatun da Dad dinta zasu samu damar yin ciki.

Ihun Husnah din ya Saka anty Farha sake kitchen gurin dafawa Amatun Wani custard din hawowa da sauri hakama mum Aisha datake palon qasa zaune tana waya tasowa tayi da sauri tana kashe wayar tana cewa

“Wannan mahaukaciyar zata ballo mana fushin ASH da suka samu rasuwar Abeedan ta kwantar ta ja musu balai ana zaune kalau”

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

73

*************

AmatulMaleek da sosai zuciyarta ke zafi itam da bacin Rai tsayawa tayi tana yiwa Husnah Dake ihu kallan takaici da mamaki me girma Dan Bata dauka da gaske Batada hankalin ba sai yau din.

Anty Farha na zuwa saurin janye Amatu Dake tsaye tana kallan Husnah tayi

 mum Aisha kuwa Husnah din ta riqe tana daka mata tsawa cikin tashin hankalin abinda zata janyo musu ana zaune cikin fargaba.

Ihun kukan baqin ciki da zafin zuciya da tafasan jini Husnah ke saki tana kokawan qwacewa tana ambatar ciki ne a jikin Amatun Kuma Bata yarda na Dad dinta bane.

Anty Farha data kasa daukan kalaman Husnah din hannu ta daga zata fizgo Husnah din a saketa tayi abinda zatai su Gani hannunta Amatu da idanuwanta suka rufe ta riqe tared daga nata hannun ta saukewa Husnah lafiyayyar Marin Daya Sakata dauke wutan mamaki da tashin hankalin ita Amatu zata mara,

Ita kanta Amatun yau ranta yakai maqurar Baci sbd maganganun Husnah din da tamkar karuwa ne take kiranta dashi da kalamanta.

Husnah qwacewa tayi daga jikin mum Aisha da itama mamakin Marin ya kasheta Dan abu ne da Basu taba dauka ba ko tsammata daga Amatu.

Qwacewan da Husnah tayi a fusace tana sake maimaita kalamanta yayi daidai da qarasowan maamah sama din hankali tashe sbd girman da balain yayi har bangarenta ana jiyosa.

Isowanta yayi daidai da kalaman anty Farha Dake tare Husnah tana cewa

“Wallahi hauka ya dibeki kika taba Amatu bayan kinga cikin Dad din naki dayake jikinta nice zan fara Baki mamaki kafin me cikin da kansa tinda ke haukarki batajin bari……

Kalaman ne suka raqe saurin qafafuwan maamah data qaraso gabansu ta tsaya tana kallan cikin Amatun dayake kallanta tana kallansa.

Rawa qafafunta suka dauka tayi saurin dagowa ta kalli Amatu da gaba Daya Jin takeyi kaman ta mutu ta huta da abinda take ji Dan kuwa mutuwarta kawai Kila zata kashe rigimar aurenta da ASH dayake haukata kowa harma da ita da auren yake kanta.

Maamah kokarin fahimtar komai takeyi a tsanake Amma Hakan ya kasa yiyuwa Dan kuwa cikin datake Gani a gaban Amatu shine Mafi girman shock data samu a rayuwarta bayan na rasuwar Abeeda.

Rikicewa tayi bakinta na rawa itama tace

“Cikin ne kenan da gaske a jikinki Amatu?

Cikin ne dai kike dashi?

Ciki fa Amatu?

Cikin haihuwar mutum fa Amatu..

Maganar maamah ya Saka tashin hankalin Amatun qaruwa mum Aisha kuwa maimaita ciki yayi wata biyar Kam da alama take fada Wanda yake sake juyar da kan Husnah Yana gigita maamah data kasa fitowa daga shock din ciki a jikin Amatun har ya fito haka…

Amatu rawa dukkanin jikinta ya qara dauka idanuwanta na yin ja

Maamah a rikice batamasan lokacinda tafara cewa

“Daga ina cikin ya fito a jikinki Amatu?

Cikin waye wannan nake Gani a jikinki Amatu??…….

Husnah sabon kuka me Qarfin gaske ta saki tana maimaitawa kunnuwan Amatu kalaman maamah din.

Mum Aisha data ga abin ya qarasa rikicewa sakin Husnah tayi tana Neman zamewa daga rigimar sedai ko Taku biyu bataiba maamah Tayo kan Amatun koina nata Yana rawa zata shaqeta taji inda ciki ya fito jikinta anty Farha tayi kan Amatu hakama Husnah kan Amatun tayi tana qarawa kukan baqin cikinta karfi mum Aisha ma ihun ta saki tana yowa kansu tsoron su taba Amatun takeyi sbd cikin…

ASH ne ya bayyana gurin Haydar da Abdul suna bayansa cikin mamaki da tashin hankalin meyake faruwa suke kallansu Abdul na yowa kan Amatun da anty Farha ta tarewa maamah kamowa,

Abdulhameed mamaah ya riqe sa sauri Haydar kuwa Husnah ya kamo kafin su furta komai Amatu Dake bayan anty Farha ta Yanke jiki ta zube a jikin ASH da taku Daya yayi ya tarota jikinsa jajayen idanuwansa akan qaramin cikinta Daya tsayar da komai nasa.

Duk Wanda yake gurin tsit yayi jikin Husnah Dana mum Aisha harma da maamah din Yana Dan daukan rawa

Hakama Haydar da idanuwansa suka sauka akan cikin dayake jikin Amatun sakin Husnah yayi jikinsa na Dan rawa kansa na sarawa ta ko Ina.

Anty Farha ce idanuwanta suka sauka akan jinin Dayake gangarowa daga qasan Amatu ta fasa Wani irin ihun salati tana Kiran sunan Amatun a ajikin ASH.

Abdulhameed ma maamah ya saki da sauri Yayo kan Amatun Yana kokarin taba ta Amma tana jikin ASH ba Daman Hakan Dan haka suka tsaya cikin tashin hankali da tsoron kada cikin ya samu matsala.

Miqewa ASH yayi da ita a ajikinsa ya dauketa ya nufi kofa da ita da sauri anty Farha ta bi bayansa hakama Abdulhameed da Haydar Daya rikice gaba Daya ya Dena gane komai a take.

Mr Jameel dayake jiyo hayaniyar cikin gidan Yana tsaye cikin baqin takaici da mamakin hankali irin nasu da bayan kisar da sukai Basu dawo hankalinsu ba haryanxu kenan gashi su kawu bello isowarsu kenan daga kauye sunzo gaisuwa kusan su ukun duka se uzaifa,

Suna tsaye suna gaisawa Yana musu barka da zuwa sama sama Dan hankalinsa Daya rabu.

Yana ganin fitowar ASH da Amatu a jikinsa yayi saurin Isa mota cikin mamakin yauma kisan suka gwada kenan ya Bude motar ASH din ya shigar da Amatun ya rufe motar tareda juyowa ya karbi key ya shiga motar Babu abinda ya furta ya tada motar yaja

Securities dake tsaye cirko cirko sukai saurin Bude masa gate ya fita da Wani irin mugun speed.

Rabonsa Daya ja mota da kansa harya manta baimasan yaushe ne ranar Daya tuqa mota da kansa ba sai yau din Dan haka Mr Jameel ya fada dayar motar tareda anty Farha suka bi bayansa Abdul ma key din wata motar ya Karba a hannun drivern Dayan motar Dake aje Shida Haydar suka bi bayansu.

Ba Dan sunso ba kowannen dole ya qarawa motarsa gudu sbd su samu Isa da ASH din Dan gudun dayake yi zai Isa ne harma a shiga da Amatun batareda sun isoba.

Su kawu iKon Allah suka tsaya kallo da mamaki da tsoron ganin abinda yake faruwan duk basu gane waye ASH din ya fita da ita ba jini duk jikinsa.

Tsoro ma kawu ashiru yaji shi Yana Neman kamasa daga zuwansu sai cin karo da mugun Abu saikace wainda suka taho da baqar kafa.

Mum Aisha da baqin cikin Husnah da maamah ya danne zuciyarta Dake tafasa kaman zata babbake ta kallesu tana Jin inama Wani balain ne ya samesu su taru su halaka akan sabuwar masifar dasuka tado musu akan Wanda haryanxu basusan meye hukuncinsu ba gurin ASH din.

Maamah ta kalla zuciya na tafasa tace

“Na dauka Husnah haukarta ta tabin hankalin data samu ne Ashe harda qarin gadon haukar uwar riqonta,

Ke yanzu da Abeeda ta rasu Bata duniyar meye naki na tada masifar ciki idan ya bayyana a jikin Amatun inace sbd Abeedan ne kike wannan haukar Ashe dai Daman can da ciwon rashin tinaninki kikazo,

Uban waye zai mata ciki bayan ASH din dasuke watsewarsu a tare,

 yanzu Dan Allah bakiji kunyar tambayar waye yawa yarki ciki ba bayan kina sane da tashin hankalin da Akai a Greece to na uban meye ne idan ba na kwanan datai a dakinsa ba,

Idan ba cikin ba to musulinci taje karba a dakin nasa kenan.”

Maamah rasa cewa komai tayi sbd maganganun mum Aisha din bama ta ganesu Sam hakama ita ta yanda Amatun zatai ciki harya fito haka batasan dashi ba shine yake girgizata Yana Neman buga zuciyarta,

Da Abeedan Bata rasu ba kenan haka zasu wayi gari kwatsam suga cikin ASH a jikin ba shiri.

Tayaya Amatu ‘yarta data haifa a cikinta zata boye mata irin wannan babban alamarin?

Shin yaushe Amatun ta janye daga gareta haka bayan ko Tari tayi Bata boye mata?

Meyasa ta munafurceta munafurci me girma irin wannan?.

Kasa daukanta qafafunta sukai tana Neman zubewa zaune kan kujeran kusa da ita khaltume ta shigo jiki a sanyaye da abinda yaketa faruwan basuda iKon ko kallawa ta Kalli maamah ta sanar da ita ana nemanta a waje baqi daga kauye sunzo gaisuwa.

Maamah na Jin Hakan gabanta yayi mummunan faduwa idanuwanta suka sake sauyawa zuwa ja ta Kalli khaltume bakinta na Dan nauyi tace

“Daga kauye?

Gyada Kai khaltume tayi tana juyawa ta sauka

Mum Aisha datake a qule kallan Husnah tayi tana cewa

“Wallahi tallahi tsaf zan sanar da ASH komai Babu gargada na abinda kikaiwa matarsa Dan bazaki sakani a masifar da ba hanyar fita ba, ubanwa ya Hana ki auren bare ki dauki cikin Duk da rasuwar mahaifiyarki Baki tuba ba kenan…

Juyawa tayi tana sauka gaba Daya zuciyarta tafasa takeyi shikenan tana murnar ASH Bai ce musu komaiba yanzu mahaukatan gidan sun debo musu sabuwar masifa batama San Ina zata Saka kanta ba da wannan mugun balain matiqar cikin Amatun ya zube.

A palon baqi na ASH dayake harabar gidan aka saukar dasu kawu suna zaune sanyin AC da qamshin arziki duk ya cikasu ga Kuma abubuwan sha duk an Jere musu saisha sukeyi ahankali suna tande Baki cikin sauti mara qara suna jiran fitowansu maamah da Amatun.

Mum Aisha ce ta shigo palon idonta a rufe da bacin Rai me tsanani

Suna ganinta suka ajiye lemukan hannunsu suna kallanta a mutunce cikin girmamawa suka fara gaisawa suna mata gaisuwan rasuwar.

Amsawa tayi tana kokarin fara magana maamah ta shigo itama jiki ba qwari ta zauna tana gaidasu a mutunce da girmamawa tana tambayar mutanen gida tana boyewa tareda danne damuwanta.

Amsawa sukai Baki a washe suna mata gaisuwan rasuwar itama kafin kawu bello yace Ina Amatu itama.

Shiru maamah Tayi,

Itama mum Aisha datazo da niyar miqa qarar maamah din gasu kawun fasa fada Tayi tana jiran amsar da maamah zata bayar.

Jin shiru yasa kawu ashiru Shima sake tambayar Amatu harma da Abdul duk da sunsan Abdulhameed shi Baya qasar Yana gurin karatu.

Shigowan khaltume da wayar mum Aisha dinne a hannu ya Saka mum Aisha kallanta tana kallan wayar Taga Kiran Naufal ne ta karba wayar tana ficewa duk a rude sbd tasan tasu tazo karshe Kila.

Tana fita kawu bello ya tsayar da kallansa da kyau kan maamah Yana cewa

“Asmau matsalan ciwon ji kika samu ne?

Allah sarki to Allah ya Baki Lfy

AmatulMaleek muka ce Ina take ne ita ma mu gaisa”.

Dagowa tayi tareda sauke numfashi da ajiyan me zafi ta bude Baki tace

“Amatu Bata Nan sun tafi asibiti”

Dukkaninsu kallanta sukai kawu ashiru ya amsa zancen da cewa

“Asibiti Kuma?

Waye ba lafiya?

Uzaifa ne ya katse kawun da cewa

“Baba Amatun ce fa aka fita da ita muna shigowa ni naso na ganeta gaskia”

Kawu yusufa da sai alokacin ya shiga zancen yace

“Amatun ce ba lafiya kenan?

Allah ya Bata lafiya to yasa dai da sauki”

Suka amsa gaba Daya suna shiga Wani zancen sbd sunso komawa a ranar Amma Nisan basusan yakai haka ba sosai gashi Kuma Basu samu ganin ASH din ba.

Fitowa Akai dasu aka kaisu Daya Daya Dake bq tareda Kai musu lafiyayyan abinci da abubuwan sha aka aje musu kafin su samu ganin ASH din ko yau din ko gobe.

#MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

74

*************

Asibitin Yana Isa parking yayi tareda fitowa cikin saa Dr beeba na harabar asibitin tana waya shigowarta kenan itama asibiti Bata qarasa shigaba Daman Taga motar gidan ASH din ta farko ta shigo saiga ta biyu kafin ta kashe wayarta saiga ta ukun take ta qaraso gurinsa daidai ya fito da Amatun

da sauri cikin daga murya tafara Kiran nurses suka fito da sauri akai ciki da Amatun.

Emergency dinsu dayake sama aka nufa da ita Kai tsaye aka shiga da ita Dr beeba din na tambayarsa meya sameta Bai iya cewa komaiba bayan ta dubata tareda tabbatarda Babu abinda ya samu cikin jikinta ko yayane su kokarta kawai.

Tabbacin zasu kokarta din ta basa tareda shigewa aka rufo kofar.

Mr Jameel da sauri ya nunawa ASH din gurin zaman Dake gurin Yana komawa mota Dan kawo tissues da wipes da zai goge jinin Daya taba kayansa sosai.

Anty Farha kuwa kanta har Wani sarawa yakeyi tana Jin da tanada Iko Amatu na tashi ba zata koma gidan ba gidanta zata tafi da ita.

Abdulhameed kuwa hannunsa yake Dan girgizawa a wuyansa cikin fargaba da tsoron Wani abu ya samu yar uwarsa ko cikin dayake jikinta.

Haydar har lokacin Bai samu kuzari ko nutsuwan tambayar abinda ya juyar masa da Kai ba kawai lafiyan Amatun yake fata kafin biyowar komai.

Ga Dad dinsa Babu ko fuska data bawa kowa Daman ko kusantosa bare tambaya.

Zaman shiru sukai a gurin harna kusan awa biyu kafin Dr beeba ta fito tana kallan Mr Jameel da anty Farha da suka Dan fara motsawa tukuna ta nufo ASH Dake zaune har lokacin bai iya cewa komaiba bayan idanuwansa da suka qara daukan Jan yanda zuciyarsa ke dauke da zafi me tsanani.

Dan sauke kallanta Dr beeba tayi daga idanuwanta tareda miqawa anty Farha takardar hannunta ta maganin data sauyawa Amatun ta Dan sake kallan ASH Daya dago idanuwansa ya zuba mata tana Neman rudewa sbd shakkar yanayin nasa tace

“Cikin ya Dan zuba ne Amma Allah yasa Bai fadi ba sai Kuma BP nata Da yayi mummunan Hawa sosai Wanda Bai kamata ace me ciki BP dinta Yana kaiwa Hakan ba kusan ma shine ya Sakata sumewa cikin na kokarin fita so,

Amma Inshallah komai is ok yanzu Se a kula sosai please musamman Daya fara zuba cikin komai zai iya faruwa idan aka sake ganganci”

Mr Jameel da anty Farha kusan a tare suka saki ajiyan zuciya a Fili abinda ya danne kirjinsu Yana fadawa,

Abdulhameed ma numfashinsa dayake a rikice ne ya sauka tareda dawowa daidai.

Haydar kuwa sai alokacin hankalinsa ya dawo daidai ya zubawa dukkaninsu idanuwansa tinaninsa na tsayuwa guri Daya shine cikin waye a jikin Amatun?

Yaushe tayi aure?

Dama zata iya aure batareda ya saniba duk tsawon lokacin Nan harma da qaruwar ciki??

Juyawa yayi batareda ya iya cewa komaiba yabar gurin Abdulhameed Daya lura da tafiyarsa juyawa yayi ya bisa jikinsa na sanyi.

ASH kuwa miqewa yayi ahankali daidai lokacinda aka fito da ita aka kaita Wani lafiyayyar dakin da kaman a luxury hotel room kake me nutsuwa.

Gadon da zaa maidata shine da kansa ya Saka hannuwansa biyu cikin kulawa ya dauketa ya kwantar bacci takeyi batama San waye akantaba.

Nurses din na ficewa ya zauna ahankali gefen gadon tareda zubawa cikinta idanuwansa Daya ji suna Neman tara ruwa a cikinsu na abinda yake Gani a gabansa.

Cikinsa ne a jikinta,

Haifar masa ‘yaya zatai bayan ya cire Rai daga sake samun wasu yayan,

Duk wannan lokacin Dasuka dauka nesa da juna ciki ne a jikinta batareda ya saniba,

Azabar Daya ringa bawa kansa na rashinta Ashe baida Rabon kulawa da jininsa dayake cikinta ne,

Da mahaukatan gidansa sun Saka cikin ya fita da shikenan yayi rashin tsatsonsa batareda ya San dashi ba ne ko me??

Meyasa farha duk tsawon lokacin Nan Bata sanar dashi Amatun juna biyu ne da ita ba,

Tayaya yarinyar da Bata taba ciki ba zaa barta da dawainiyar renan cikin ita kadai,

Yasan tayi kuka tayi rashin bacci ta shiga tashin hankali da fargabar maamah dinta gameda ciki Amma batada me Bata kariya da kulawa……

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na qara masa ciwon halinda ta shiga batareda saninsaba,

Duk wanna lokacin a cikin qunci sa radadin zuciya yake na rashinta Amma ya zabi hukuntasu su dukan akan lefin mahaukatan gidansa da sunyi Nisan da basa Jin kira.

Hannunta ya kama ahankali tareda hadewa da nasa tafin hannuwansu suka Hadu bayan tsawon lokaci da suka dauka batareda ganin juna ba ko jin juna.

Ajiyan zuciya me sanyi ya sauke Yana Maida idanuwansa akan cikin Dayake kasa gasgata shine ubansa,

Shine zai haifi Yaya da macen da tinaninta kawai ke dakatar da duniyarsa gabaki daya bare kallanta da idan tai masa yake Jin itace dalilin duk Wani farin cikin rayuwarsa.

Hannunsa Daya ya daga Ya Dora akan cikin take Wani numfashi me qarfin gaske ya kufce masa kowannen kofan zuciyarsa na budewa wasu sabbin feelings suna shiga suna narkashi.

Shafa cikin ya sake yi ahankali Yana kallansa sbd mamakin ganin cikina a cikin LA dinsa dayake Tina lokacin farko Daya fara ganinta a baby ya dauketa cikin zanin haihuwanta Bai dauka itace zata basa feelings da farin cikin ganin yayansa a cikinta ba sbd lokacinda Abeeda take da cikin Haydar nesanta kanta tayi dashi ta koma porthcrt gaba Daya sbd batason ya ganta da ciki kamanninta wai zasu Sauya batason ya ganta da kammanin masu ciki Dake kumbura komai Dan haka Sam bai samu dama ta kasancewa da ‘dansa lokacinda yake cikin ciki ba,hakama Bai samu Daman sanin dandano da dumin matarsa lokacinda takeda ciki ba.

Gaba daya Jin kansa yayi kaman sabon matashin saurayi Dan haka ya Jima sosai kafin ya fito suka tafi gida da Mr Jameel Dan wanka da sauya kayan jikinsa ba Farha kawai suka bari wadda itama hankalinta ya kwanta da samun cikin Amatun baiyi komaiba.

Haydar da Abdulhameed sun dawowa gida Haydar rufe kansa yayi a daki

Abdul yayita son magana dashi Amma Sam baya buqatan kowa a yanzu kansa yakeson ya sake,

Abinda yafi masa ciwo shine yanda Amatun ta iya boye masa aurenta da cikinta bayan basa boyewa juna komai.

Abdulhameed ganin Haydar din yaqi sauraronsa ya sakashi qyalesa ya tafi gurinsu kawu Dake bq Dan su gaisa.

Dawowan ASH mansion din ya Saka mum Aisha,maamah da Husnah shiga sabuwan sanyin jiki da fargaba.

Ga Abdulhameed ma Sam yaqi zuwa gurin maamah din bare taji lafiyan Amatun Dan Shima abin nasu ya ishesa ya rasa yaushe mahaifiyarsu ta Dena kaunar yayanta da Kwanciyar hankalinsu tareda rashin sanin inda tawakkalinta da hakuri da Nutsuwarta duk suka tafi tsoro ma yakeyi idan ba maganin Husnah takesha ba itama matsalan ke Neman tabata.

Gaisawa dasu kawu Abdul yayi ya zayyana musu abinda yake faruwa ba duka ba kawai dai iya qin amsar auren da maamah tayi sun gigita rayuwar Amatun gaba Daya gashinan yanzu tana asibiti ta kusa rasa cikin dayake jikinta.

Shiru dukkaninsu sukai cikin baqin mamakin duniya daya kashesu.

Kawu bello cikin mamaki yace

“Wato Asmau ciwon rashin tinani ya sameta kenan shine tazo ta zauna muka gaisa lafiya lafiya ta rufemu mu gama gaisuwa mu koma Se kawai ta kashe auren na da muka Hana kanmu zama muka Hana kanmu tsayi gurin yawon malamai a sake tsuqe mana shi karya balle Ashe muna zaune ganinta kawai zamuyi da Amatun ta kaso auren,cabdijm.”

Kawu ashiru kuwa rasa abin fada yayi sbd baqin cikin Asmaun da mamakinta Daya siqesa.

Kawu yusufa kuwa kallan Abdul yayi Yana cewa

“To ai shikenan tawa kanta Dan kuwa wlh kafarmu kafarta ba zaman da zata ci gaba da yi anan din,Banda rudun iska Daya shafeta a gidan sirikinta kamata yayi ace har mantawa ma ariga yi da tana gidan sbd kullen da zata ringa yiwa kanta ta zauna guri Daya Amma shine sbd samun guri har yawo takeyi koina a gidan hardasu dambe akan cikin siriki,

To zanga uban dazai Hana a Haifa cikin tinda sune sukai mata cikin.”

Shiru Abdulhameed yayi maganganunsu suna Dan Sosa zuciyarsa sedai Kuma Yana fatan akawo karshen matsalar tinda maamah su kawun ne kawai suke fada ta zaunu a gurinta sai Kuma ASH.

A cikin gidan kuwa a Palo suka zauna shiru kowa na jiran shigowan ASH Amma shiru sbd ta palonsa n qasa ya Haye zuwa samansa batareda sunsan ma ya shige din ba.

Wanka yayi da ruwan dumi toilet din na gaurayuwa da qamshin tsadaddiyar Aesop liquid soap dinsa me tsada da sanyin qamshi.

Yana gamawa ya fito daure da towel jikinsa na tsiyayar ruwan da kusan ke qarawa murdaddiyar jikinsa daukan hankalin Wanda ya Gani.

Goge jikinsa yayi da towel yana tsaye gaban mirror ya shirya tareda barin gurin ya Saka Fendi sweatsets ya fito sallan magrib da aka kira.

A gurin sallah su kawu suka samu ganinsa Shima sai alokacin yasan d zuwan nasu ya gaisa dasu sukai sallah

Bayan sun fito Kai tsaye palonsa na baqi da suka fara sauka ya Isa dasu suka zauna anan suka sake gaisawa dashi suna masa gaisuwa a tsananin girmamawa.

Bayan sun gama miqa gaisuwarsu ta rasuwar Abeeda kawu bello ne yafara jeho maganar jikin Amatu Yana mata sannu da fatan samun lafiya kafin suka sanar dashi sunji komai daga bakin Abdulhameed.

Fada sosai kawu bello da kawu yusufa sukai duk Yana sauraronsu har suka gama sai alokacin ya qara sanin wasu abubuwan na tashin hankalin da suke zubawa a gidan ya hada da Wanda yaji a bakin Farha yau din komai da komai.

 bayyanarda tafiyar da zasuyi da maamah sukai daga qarshe.

Sai da sukai shiru ya Kalli Mr Jameel dayake shigowa yace ya kira masa kowa duk suzo Yana nemansu.

Mr Jameel na ficewa ASH din ya Kalli su kawun Daya bayan Daya kowannensu yasha shaddarsa ta Roba da hulunansu da baimasan wane kalar Karin ne dasu ba Dan ta kawu yusufa kaman shape din jirgin kwale kwale.

Uzaifa ya juya Yana kalla Wanda Shima yake jikin shaddar robar green Shar da ba hula akansa Dan haka qananun gashin kansa Mai kama da gonar Aya yake bayyane.

Kawu bello yafara kalla bayan ya sauke numfashi ahankali Baya buqatan tashin hankalin dazai taba L.A ko lafiyan dansa dayake cikinta Dan haka Kai tsaye ya sanar dashi hukuncinsa da sauran bayanan abinda yake buqatan daga garesu.

Daga kawu bello har kawu ashiru da uzaifa kusan gaba dayansu Wani girmamman farin ciki me tsananin dadi ne ya rufesu Dan kuwa abune Daya samesu batareda tsammani ba.

Shigowar su mr Jameel dasu mum Aisha na bayansa ne harma dasu Abdul da Haydar ya Saka su kawu gaba dayansu zubawa kofar idanuwansu cikin tsananin farin ciki suna Dan washe Baki tareda boye murnarsu.

Zama dukkaninsu sukai kowa jikinsa na jiqewa da zufa musamman mum Aisha da Husnah harka da maamah,

Abdul da Haydar kuwa basusan meye dalilin Kiran ba tukuna.

Kallan inda su maamah suke Daya bayan Daya kafin ya tsayar da kallansa kan Husnah wadda take sake tsinkewa.

Bakinsa a natse ya Yana dauke kallansa daga kansu yace

“Dukkaninku ku shirya gobe za’a daurawa kowaccenku aure Kuma a goben zaku wuce.

Maamah ya kalla yace

“Malam bello yace ze mayar da aurensa na Kuma amince masa da Hakan,

Malam ashiru kuwa na basa auren Aisha,’dansa uzaifa Kuma auren Husnah,

Kowa ya shirya duka gobe ana daurawa zaku wuce.

Kowa ta tashi ya tafi shikenan.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

75

*************

Maamah ce take hawaye suka tsinke mata tana rufe idanuwanta zuciyarta na daukan nauyi me girma,

Mum Aisha kuwa gushewa hankalinta ya fara yi na seconds tareda jinta gaba Daya kafin ta ji ta Dan ji jinta ya dawo ta Kalli ASH din da dukkanin karfin ganinta hannuwanta na daukan rawar datafi rawar tela murya a rikice tace

“Auren addinin islama Wanda nasani???

Wani kallon Daya Sakata rikicewa ASH yayi mata da idanuwansa da har lokacin Basu koma daidaiba..

Rudewa tayi take tana rikicewa a rude ta fito daga bayan Maamah datake zaune bakinta na rawa hakama jikinta tace

“Ka yimun Rai ka dubi Allah ka dubi Annabi ka dubi maraicina Banda uwa Banda Uba Se Kai se Naufal,

Kaine uwata Kaine ubana wlh na tuba nabi Allah na bika ta tattara tashin hankali duk na aje Amma Dan Allah Karka auramun aure da girmana yanzu Kuma a kauyenda mota ma Bata shiga wlh rayuwata mutuwa zatai,haukacewa ma zanyi,Dan Allah kayi hakuri Karka min auren dole da girmana na tuba,Dan Allah kayi hakuri…..

Tsit palon yayi maamah ma hawayen takeyi tana sharewa kai a qasa Dan ita bama zata iya magana ba Dan Iya ganin mugun Abu yau shi take Gani sirikinta zai mata aure kaman na dole,tayaya ma zata rokesa tace Dan Allah karya mata auren? innalillahi wainna ilaihirrajiun.

Husnah kuwa Bata motsaba sbd Bata dauka ita Husnah din ake nufi sbd kwata kwata ma Babu abinda ya hadata da auren kowa yanzu bare,

Abdulhameed ne da Haydar suka shiga tashin hankalin hukuncin Husnah da maamah kawai da basason ta koma kauye Dan haka Haydar ya juyo Yana kallan Dad din nasu zaiyi magana ASH ya daga masa hannu kadan alaman bayason Jin komai.

Su kawu kuwa washe Baki suka hau yi suna sauke kansu qasa kawu ashiru sai kallan mum Aisha yakeyi yanajin shi gaba Daya ma Sonta ya kamasa a gurin.

Uzaifa ma Husnah ya zubawa jajayen idanuwansa masu girma kaman yalo ya taso saman manja

gaba dayama Jin yayi yawunsa na tsinkewa kaman zasu zubo masa da kallanta kawai,

Baitaba tinanin zai taba samun mata irinta ba koma a mafarkin duniyar aljanu aka Kaisa kuwa.

Ganin irin kallan da uzaifa kewa Husnah yasaka Haydar kasa shiru cikin tsananin damuwa da tashin hankali yace

“Dad dan Allah kayi hakuri ka sassauta musu hukuncinsu duba da yanayin rayuwar da ba Daya ba,Dan Allah Dad ka duba,ayi musu afuwa musamman Husnah da take yarinya, Dad…..

Kallan da Husnah ta jefawa Haydar din tana dagowa gaban Daya ne ya Saka Haydar dakatawa Yana kokarin hanata magana tace

“Dad ni aka bawa waye aure?

Dad aure ka bayar Dani?

Uzaifa na Jin haka ya washe Baki tana Dan motsawa tareda Shafa kansa dayake kaman gashin awaki daga nesa.

Juyowa Husnah tayi ta kallesa Yana sake washe hakoransa da miyar kuka ta Dafe

Wani ihu ta saki cikin gigicewa ma da ganinsa gaba Daya jikinta na daukan Wani irin rawa da kakkarwa ta rarrafo ta wuce mum Aisha Dake gabansa zuwa gurin qafafunsa tana fashewa da kuka me qarfin gaske komai nata rawa yakeyi tafara cewa

“Dad Dan Allah ka yafemun ka yafemun Karka kasheni,wlh mutuwa zanyi idan ka auramun wannan mutumin,ni tsoronsa ma nakeji Dad Karka Kaini Karka auramun shi na tuba,na tuba na Dena komai ma,na Daina fadan,na Daina ko fitowa daga dakina Amma Dan Allah Dad Karka hukuntani haka Dad bazan iya daukaba ni mutuwa ma zanyi Dad.”

Yanda ASH din fuskarsa take daure tamau ba sauki bare ya kallesu ya Sakasu qarasa dimaucewa gaba Daya Dan kuwa ba alaman ma Yana Jin zancensu bare sassauta musu Mum Aisha take itama kukan da batasan tanasa sauran hawayen yinsaba ya kufce mata tana tonawa kanta asiri da Neman tuba da yafiya akan karya aura mata kawu ashiru.

Husnah gaba Daya fita hayyacinta tayi tafara kukan fitar hankali tana rokonsa,

Haydar ta rarrafo ta kamata tana rokonsa ya roki Dad din cikin tsananin kuka da tashin hankali gaba Daya ta fice hayyacinta cikin mintinan da Basu Gaza biyar ba.

Kallansu kawu ASH yayi Yace su tafi kawai zai nemesu da safen kafin daurin auren.

Tashi sukai suka fice kowannensu ransa fes Dan shi kawu ashiru ma yanzu ne dadin tashin hankalinsu ya rufesa tinda gashi sunyita tashin hankalin Rabo ya samesa Yana zaune kalau tsuntsu daga sama gasashe.

Suna ficewa hawayen mum Aisha suka qara gudu tana rokon ASH da dukkanin zuciyarta da qarfinta.

Ganin halinda Husnah ta shigane kwata kwata kaman ta zauce gunjin kukanta kawai ke tashi a gurin ta saki Haydar ta kama Abdulhameed Shima tana rokonsa ya roki Dad dinta karya aura mata wannan mutumin kauyen.

Mum Aisha ma kuka takeyi sosai sbd tasan maganar ta gudu ma Bata taso ba Dan batada gurin zuwa har ita har Naufal gwara ta tsaya ta roko ASH ya sassauta ya dubi maraicinta ya janye hukuncinsa.

Yanayin Husnah tini ya karya zuciyar Haydar gabaki Daya harma da Abdulhameed Wanda yakejin radadin hukuncin da tausayinta sbd yasan ko kwana Daya bazata iya a rayuwar kauyen ba.

Haydar jajir idanuwansa sukai Yana kallan Dad dinsu cikin tsananin damuwa da qasqantar da Kai duk da yaji laifukan da su Husnah din suka aikata musamman ita din a bakin Mum Aisha gashinan tanata fada Amma duk girman lefin nata aure a kauye da Miji irin wannan qarasa zauncewa ma zatai.

Qarfin Husnah take ya fara qarewa ta rarrafo gurin Haydar ta qanqamesa tana sake kuka sosai da yake jinsa har cikin ransa ya rungumeta Yana kokarin rarrashinta Amma Sam taqi tsayawa kukanta tsananta kawai yakeyi tana cewa ta tuba ta Dena komai.

Abdulhameed ne ya zuba mata idanuwansa da sukai jajir yanajin Shima bazai iya barin akaita kauyen aure ba kaman yanda bazaiso Amatu tayi zaman aure a kauyen ba,

A Baya Amatu ta samu kanta a irin wannan halin ya tsaya Kuma ASH dinma ya tsaya suka qwatota Dan haka ko Husnah duk laifinta rayuwar kauyen da auren uzaifa kashe rayuwarta gaba Daya zatai.

Juyowa yayi ahankali tareda dago kansa daga duqen dayake ya kasa kallan ASH sbd nauyin da kirjinsa yayi ya Bude Baki cikin girmamawa da nutsuwa yafara rokonsa Shima tareda basa hakuri zuciyarsa ta sanyaya.

Husnah Da qarfinta ya fara qarewa rarrafowa tayi gurin Abdulhameed da sauri ta riqe hannunsa Daya da hannuwanta biyu a rude ta Kalli ASH tace

“Dad Dan Allah idan kayi alkawarin bazata barni ba ka auramun Abdulhameed na yarda zan zauna dashi shi akan wancan mutumin wlh tsoronsa nakeji,

Dad dan Allah ka auramun Abdulhameed wlh inaso zan zauna dashi zan masa biyayya zan shiryu,Dan Allah Dad.”

Abdulhameed kusan mutuwar zaune yayi sbd mamaki me tsananin gaske da tashin hankali,

Dagowa yayi da sauri tareda kallanta cikin yanayi na rikicewa ma dayake Neman yi sedai kallan da ASH ke masa da yanda take kuka sosai har batada karfi ya sanyashi yin shiru.

Sake qanqame hannunsa tayi tana maimaitawa Dad dinta zata auri Abdul din zata zauna dashi ko inane.

ASH sai alokacin ya zuba mata idanuwansa da suka sake sauyawa sbd duk kukan datakeyi a cikin ransa yake jinsa sbd harga Allah Yana son ‘yar tasa kawai hukuncine dole yayi mata idan yanaso ta dawo daidai.

Haydar Dora idanuwansa da sukai jajir yayi akan Abdul Yana masa kallan fatan hakan ta kasance Dan Shima zaiyi farin cikin Husnah ta auri Abdul sosai fiyeda uzaifa din.

Irin kallan da Haydar ke masa hakama da yanda Husnah ke zake kuka sosai a jikinsa ya sanyashi Jin zai iya auren nata Dan kubutar da ita daga auren da bazai taba son ai mata ba.

Dagowa yayi ya Kalli ASH cikin girmamawa da jarumta yace

“Eh inasonta zan aureta,Dan Allah a auramun ita zan kula da ita ta Dena dukkanin urin wannan lefin,ayi mata afuwa ta tuba”

Duk tashin hankalin da mum Aisha take ciki da kukan datakeyi Saida ta dago tana kallan Abdulhameed din da Husnah ta maqalalewa gaba Daya batama hayyacinta,

To tayaya ma zaa bari Husnah ta kaucewa hukuncin zuwa kauye bayan itace duk ta ja musu wannan masifar.

Haydar cikin damuwa me girman gaske ya fara rokon Dad din Daya tausaya ya sassauta Husnah abawa Abdul din Dan Allah tinda yace zai aureta din.

Maamah ma dagowa tayi ta Kalli Abdulhameed din da Husnah kafin ta dawo da kallanta gurin ASH batareda ta iya kallansa ba murya a shaqe sbd kukan datasha ta fara rokonsa akan karya aurawa Husnah uzaifa a aurawa Abdul din Dan Allah.

Mamakin tashin hankali mum Aisha tace Bata yarda ba sbd Husnah dince duk me girman lefi a duk abinda suka aikata din hakama itace ai ta Saka Naufal zuwa yiwa Fyade Dan haka itace tafi kowa cancantar zuwa kauye.

Babu Wanda ya kula mum Aisha din duk da daga ASH har maamah, Abdul da Haydar Babu Wanda zuciyarsa Bata quna da yanka akan maganar Husnah dince ta tura a yiwa Amatun fyade sedai Kuma duk da Hakan bazasu bari rayuwarta ta mutu gaba daya ba ta hanyar miqata hannun zuriar Sanda Fulde a kauye,zasu hukuntata ta wata hanyar Amma wannan din Kam bazasu iya bari ta tafi ba.

Abdulhameed ma da kansa ya qasqantar da Kai ya ringa rokon ASH din hakama Haydar,

Husnah dinma kanta a cikin kukan da qarfinta ya gama qarewa rokonsa takeyi tana maimaita ta tuba bazata sake tada hankali ba ko rigima da Amatun.

Numfashi ASH din ya sauke ahankali tareda Jin nauyin da kirjinsa ya tokale dashi ya Dan fada Dan haka ya Kalli Abdulhameed din a natse cikin kamewa yace

“Ka tabbatarda kana Sonta zaka aureta?

Gyada Kai Abdul din yayi kansa a qasa

 kusan itama Husnah din gyada kan takeyi kaman ita aka tambaya jikinta duka rawa yakeyi sosai.

“Zaka iya tsayawa akan tarbiyanta?

Zaka iya tsayawa akan kulawa da ita da gyara halayenta?

Zaka iya tsayawa kayi hakuri da ciwonta?”

Sake qanqame Abdulhameed din Husnah tayi tana kallansa da jajayen idanuwanta dasuka gama shiga rauni tana fatan yace zai iya duka sbd ita gaba Daya shi din ma takeson aure a ayanzu ta yafe Faisal.

Numfashi Abdulhameed ya sauke ahankali tareda zubawa Husnah din idanuwansa ahankali Ya kalleta kafin ya Maida kallansa inda ASH yake zaune cikin nutsuwa da sanyi yace

“Eh inshallah duka zan iya.”

Haydar Wani sanyi da ajiyan zuciya ne ya ringa saki cikin ransa Yana godewa Allah da Jin sabuwar kaunar Abdul din Dan kuwa ya ceto masa yar uwa daga abinda bazai iya qara rayuwa cikin dadi da farin ciki ba da anyi Husnah din auren kauyen.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

76

*************

Mum Aisha na Jin ASH ya amince ya bawa Abdulhameed din Husnah ta fasa sabon kuka tana cewa Bata yardaba itama bazata iya auren kauyen ba.

Baice komaiba ya Bata kyakkyawan zabi akan ko tayi auren Daya zabar mata ko ta tattara tabar masa gidan harna Abuja harna Yola ta tafiyarta itada Naufal su tafi Babu ruwansa ko hadinsa da ita.

Wani irin kukan baqin cikin rayuwa ta sake fasawa tana barin palon ko Gani batayi jininta na hayewa gaba Daya.

Maamah ya kalla da alaman kema kinada magana ne?

Ta miqe a silale ta fice zuciyarta a nauyaye itama Dan kuwa yau tagama ganin qasqancin rayuwa ga baqin cikin auren kawu bello,

Idan suka ce Basu yarda ba a sake tada Wani rigimar Azo ayita tashin hankali a gabansa sauran mutuncin ya qarasa zubewa.

Tana ficewa Husnah jikinta da qafafunta na rawa ta miqe sedai bama zata iya Kai kanta cikin gida ba sbd barin da jikin keyi sosai Kuma har lokacin hawayenta Basu tsaya ba.

Abdulhameed dinne ya miqe ya kama hannuwanta ta sake qanqamesa tana tsiyayar hawaye suna fice palon aka bar Haydar Se Dad din Mr Jameel ma ficewa yayi ya Basu guri Dan suyi magana sosai.

Suna fita Husnah ta fasa kuka mara sauti tana Neman zubewa qasa Abdul ya riqota da kyau jikinsa tareda tsayawa cak Yana kallanta a natse kafin ya Bude Baki yace

“Kukan Kuma yanzu na Menene tinda bazaki auri uzaifa din ba?

Sake fasa Wani kukan tayi tana fadawa jikinsa ta qanqamesa cikin kuka take cewa

“Nidai kace gobe a daura damu kar abari saika dawo Dad zai iya sake fushi ya auramun mutumin, Dan Allah a daura mana auren muma tareda su mum Aisha gobe

ku tafi dani bazan iya zama anan ba Nima zan Biku”

Numfashi me sanyi ya sauke ahankali tareda Dan dagota daga jikinsa sbd gaba Daya a rude take shiyasa takeda maqalqalesa din.

Cireta daga jikinsa yayi gaban Daya tareda kama hannunta suka qarasa cikin gida sbd ta huta ta nutsu.

Sama yahau da ita har bedroom dinta ya zaunar da ita bakin gadonta tareda daukan tissue Dake gefen gadonta ya share mata hawayenta cikin kulawa yace ta Dena kukan ya Isa haka.

Daqyar ya samu ta dan dawo hayyacinta ya sake kwantar mata da hankali da kalmomin rarrashi da kulawa kafin ya fice ya barta kwance.

Daga dakinta Kai tsaye dakinsa ya wuce sbd nauyi da kansa da zuciyarsa sukai sbd baitaba tinanin yin aure a yanzu ba hakama yanada budurwarsa dayake tinanin aure bayan sun dawo gaba Daya itama acan take karatu tareda su.

Yana Isa daki toilet ya shige da kayan jikinsa ya sakarwa kansa ruwan sanyi sbd harga Allah lissafinsa ya kunce da lamarin duk da Baya Dana sani ko baqin cikin Hakan sbd da gaskiyarsa kaman yanda bazai iya kalla ya bari rayuwar Amatu ta lalace ba zai iya bari rayuwar Husnah ta lalace ba sbd ‘dan uwanta Haydar dayake kaunar Amatu da zuciya Daya bakuma zai iya barin AmatulMaleek ta shiga irin wannan halin ba kota halin yaya,

dakuma Dad dinta ASH dayake yiwa Amatu son da har zai iya hukunta ‘yarsa irin haka akanta Badan zuciyarsa bazata quntata da hukuncin nasa ba shi kansa,

Saikuma mahaifiyarta mum Abeeda datake tsananin kaunar tasu mahaifiyar da zuciya Daya kauna Kuma me tsanani batareda sun hada jini ba tin yarinta,,

Wannan dalilan ne yasa Bazai iya barin rayuwar Husnah ta lalaceba zai aureta Kuma zai kula da ita sbd tana Neman me kulawa da ita ne ya dorata a hanyar dangana da tawakkali bawai so qarara ba da rashin kwaba kaman yanda maamah tayi mata shiyasa duk ta koma batada lissafi ko tinanin daukan abu da sauki.

Gidan tsit ya dauka kusan kowa tasa ta ishesa ta tashin hankali da masifa,

Haydar ko Daya dawo daga gurin Dad dinsa ciwon Kai ne da toshewan zuciya gabaki daya a tareda shi sbd Kai tsaye Dad dinsa ya sanar masa AmatulMaleek shine me aurenta Kuma uban cikin dayake jikinta sbd toshe wata sabuwar hanyar fitinar ko tashin hankalin.

Abdulhameed na fitowa toilet shima ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyin da kaya a jikinsa Dan samun sanyi da sassaucin zafin Daya rufe jikinsa duk da kusan ba auren ne yafi masa ciwo ba kaman yanda aka boye masa Kuma Amatun yafi Jin zafin boye masan datai Dan kusancinsu kusan yayi karfin da basa fa boyewa juna komai.

Yana fitowa kaya ya Saka na bacci ya hau gado ya kwanta gefen Abdulhameed Wanda Shima ba bacci ko alamansa a idanuwansa sbd daki Daya suke amfani dashi tin zuwansu tinda ba wani dadewa zasuyiba su koma.

Bangaren su kawu bello kuwa farin ciki ne fal a zukatansu sun kasa zaune sun kasa tsaye musamman kawu ashiru da uzaifa sbd shi kawu bello kome ne zaayi duk da komen ne Yana farin cikin Shima Dan maamah din Hutu da Jin dadi ya sauyata hakama ASH TALBA bazai barsu hakanan ba aike da kayan arzuka Akai Akai Sunday auren sirikarsa,da qanwarsa da ‘yarsa tilo a gida Daya,Aiko kayan arzuka sai sun ture duniya sabuwa.

Kawu yusufa da Sam shi aure auren be damesa ba kudi dai kudi dai kawai kallansu yakeyi bakinsa a washe yace

“Kai ashiru sai farin cikin sabon auren jar fata kakeyi kana mantawa da laraba da zafin kishinta da tashin hankalinta kana Kai matar mutane kauye laraba zata iya fasa mata hanci da langa fa,ko sati aurenka bazaiyiba Kila zai mutu Dan wlh Babu me iyawa da haukar laraba sai Kai Saka aurota,

Ga sauran matan ka Nan duk ta Maidasu bayinta Yan wahala ya zakai da matar binnin idan ka Kai??”

Dariya kawu bello ya saki Yana cewa

“Tin anan idan kasan bazaka iya karya laraba akan matar binnin ba wlh kace ka hakura bazakaiba Dan Babu ruwana a lamarin laraba ba mutunci ne da ita ba”

Uzaifa dayaji ana ambatar uwarsa shiru yayi Yana Jin ba dadi wa babansa idan har ya rasa wannan matar binnin datai jajir ta nuna kaman mangwaro.

Kawu ashiru shiru yayi Dan kuwa Shima yasan balain laraba Amma Kuma bayajin zai fasa amsar auren Aishan binnin akan laraba suna Isa zai saketa tabar gidan ya Saka Aishan wajenta tinda Daman baida gurin Saka Aishan binnin.

Kayan jikinsu kawai suka zo dasu gashi akwai daurin auren da safe basuda wasu kayan Dan haka suka cire kayan suka nade suka ajiye da niyar sakawa da safen karsu kwana dasu su yamutsasu,

Sanyin AC Dana garin duk a cikin qashinsu ya shige a Daren sbd kwanan da sukai ba kaya ajikinsu.

*******

Cikin dare sosai Amatu ta Farka daga baccinta jikinta duk yayi mata nauyi Amma dai Bata Jin ciwon komai bayan na nauyin.

Anty Farha Dake waya har lokacin da Mr Jameel ya gama fada mata duk abinda ya faru Dan kawai ta Dan sassauto masa sbd ya lura da ba lafiya ba yanda take masa a kwanakin.

Gama jinsa tayi batareda ta sauko din ba yanata lallabata tana amsa masa a taqaice saiga Amatun ta tashi kashe wayarta kawai tayi ta ajiye gefe tareda miqewa ta nufo Amatun.

Tashi zaune Amatun tayi anty Farha na mata sannu tana cewa

“Kina buqatan wanka dan jikinki ya sake na hada Miki ruwan zafi sosai ko?”

Gyada Kai Amatun tayi tana Bude Baki a ahankali tace

“Amma Ina Jin yunwa sosai anty Farha abinci nakeso”

Murmushi anty Farha tayi tana cewa

“To Abar wankan sai kinci abinci kenan.”

Tea ta hada mata me kauri mara sugar kafin ta zubo mata macaroni da aka dafa tareda potatoes da nama kadan Se carrot a ciki Wanda karima ce Mr Jameel da kansa ya kawota ta kawo musu da magrib.

Sosai Amatu taci abincin tasha tea taji jikinta ya sake samun karfi ta sauko gadon ta nufi toilet Kai tsaya tana tafiya a hankali.

Ruwan zafi sosai ta gasa jikinta dasu kafin ta fito kayan sanyi ta Sanya tayi duk Yan abubuwan da zatai ta koma ta kwanta anty Farha ta rufeta take bacci ya dauketa me dadi.

Qarfe 6 na safe tana bacci Akai knocking kadan tareda budewa Kai tsaye Mr Jameel ne ya budewa ASH din lokacin anty Farha na sallame sallarta ta dago ahankali tareda yiwa ASH din barka da asuba tana miqewa suka shigo.

Amsawa yayi a natse idanuwansa akan L.A dinsa Dake bacci kaman baby kafin ya tambayi jikin nata

Anty Farha ta tabbatar masa da lafiya kalau ne yanzu.

Anty Farha ce tafara ficewa daga dakin Mr Jameel ya bi bayanta Yana Jin kaman ya rungumeta har sai ta sauko daga fushinta gabaki daya.

Suna ficewa ya qaraso bakin gadon ya  tsaya Yana sake zuba mata idanuwansa masu kyau tsawon mintina kafin ya Maida idanuwansa kan cikinta duk da Yana rufe da abin rufa Amma tinda yasan da abinsa Yana iya ganin tudinsa.

Hannunsa Daya ya Dora a cikin cikin kulawa kafin ya ranqwafo ahankali ya Dora bakinsa kan lips dinta yayi kissing dinsu Yana Jin Sonta kaman zai faso kirjinsa ya fito.

Tasowa yayi Yana kama hannunta da nasa hannun ya sarkesu tafin hannuwansu na haduwa cikin dumi da sanyi.

Cikin baccinta ahankali taji qamshinsa na shiga hancinta har cikin kanta,

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali cikin baccin lokacinda qamshin yaketa sake shigarta sai gashi ta motsa ahankali tana kokarin farkawa.

Numfashi me sanyi ta sake tareda Bude idanuwanta ahankali sbd Jin mutum kusa da ita.

Akan kyakkyawar fuskarsa Dake kallanta nata idanuwan suka sauka ta Dan sake lumshe idanuwanta ta Bude akansa.

Numfashi mara sauti ta sauke a zuciyarta kafin ta dauke idanuwanta daga kansa ahankali batareda ta motsa ba tukuna ta zare hannunta Dayake cikin nasa ahankali tana Dan gyara Kwanciyarta.

Jin yayi jikinsa na Neman mutuwa da yanayin nata Dan haka ya sake kamo hannunta ahankali zaiyi magana ta rigasa da Bude Baki ahankali cikin sanyi da rashin kuzari tace

“Ina kwana”

Mamaki ne ya Dan kamasa sbd gaisuwar kaman daga sama ya jita bayan shi ba gaisuwan yake buqata ba a lokaci Jin lafiyanta Dana babynsa yake buqata.

Amsa gaisuwar yayi a tsanake Yana son yin magana ta lumshe fararen idanuwanta alaman bacci takeson komawa Dan haka dole yayi shiru Dan kada ya hanata baccin Kila tana buqatansa.

Tinda ta Maida idanuwanta ta rufe bacci Bai zo mata na hakama Bata motsa ba bare Bude idanuwan har tsawon lokaci kafin ta Bude ahankali tareda tashi zaune tana kokarin sauka gadon ya kalleta tareda miqa hannu zai riqo hannunta ta Dan dago ta kallesa da idanuwanta a sanyi tace zata iya ta gode.

Toilet ta wuce ahankali ta shige tareda rufo kofar.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

77

*************

Tana shigewa toilet ta jima Bata fito ba sai ga dr beeba ta shigo dakin tareda wata nurse da anty Farha.

Gaidasa sukai cikeda girmamawa suna Dan mamakin ganinsa a wannan lokacin danma itama Dr beeba ta kwana asibiti ne yasa tashigo dakin a lokacin.

Fitowa tayi daga toilet din a natse cikin sanyinta batareda ta dago ta Kalli kowa ba bayan Dr beeba Dake mata yaya jikin ta amsa a cikin sanyi tana zaunawa a hankali bakin gadon.

Tambayoyi Dr beeba din Tai mata tareda fada mata ta kula sosai ta cire damuwa sai Kuma kiyayewa da yanayinta tace ta sallamesu su koma gida.

Rubutawa tai a folder din Amatun kafin ta miqawa nurse din dake tareda ita tana fadawa ASH din dole sai ankula sosai sbd samun BP ga me juna biyu baa cika so ba Gaskia.

Dr beeba na ficewa Amatu Dake zaune ta Kalli anty Farha tace ta Bata hijab ta Saka tana Dan Jin sanyi.

Doguwar hijab anty Farha din ta miqawa Amatun ta Saka a natse har qasa kusan ma cikin idan ba Wanda yasan dashi ba Baya ganinsa.

Basuda Wani kaya Dan haka Yan abubuwansu Mr Jameel ne da kansa ya dauko ya fito dasu suka fito.

ASH dinne a gaba batareda yace komaiba sbd ko kallansa ma LA din taqi yi bare ya samu Daman yin magana.

Suna isowa mota dayake akwai mota Daya a asibitin a tareda dasu kafin wadda ASH da Mr Jameel din suka zo da ita yanzu.

Kai tsaye dayar motar Amatu ta nufa tana cewa anty Farha gidanta takeson su tafi Batason koina.

Shiru anty Farha tayi tareda tsayawa tana kallan Amatun cikin Dan mamaki kafin ta juya ta Kalli Mr Jameel Dayake tsaye Shima yaji abinda ta fada.

ASH Daya Bude mata mota Yana jiran qarasowarta kafin ya juyo da sauri mr Jameel ya qaraso cikin girmamawa da kare zancen ya sanar masa LA din tace a motan Farha zasu koma gidan.

Juyowa yayi ahankali ya kalleta yaga harta Isa motan Farha din batareda ta waiwayo ba ko alaman ma zata waiwayon.

Baici komaiba ya barta suje a motan Farha din sbd kada ya takurata ko kadan.

Mr Jameel da duk yake Neman rikicewa shiga motarsu yayi bayan ya rufewa ASH din kofa bayn shigarsa motar ya tada Basu fice ba Saida sukaga motar su Farha din ta fara ficewa.

Mr Jameel dayake yasan ba mansion sukaiba sai ya bari suka bace musu Dan kada ASH ya lura da hanyar da zasu bi daban.

Anty Farha Kai tsaye hanyar gidanta ta kama su Kuma Mr Jameel ya dauki hanyar mansion Yana shiga tinanin wannan sabuwar lamarin Kuma.

Ko da suka Isa mansion su kawu sunyi breakfast sun shirya tsaf abinsu sai kyallin Mai sukeyi da suka Saka aka kawo musu suka shafa sbd yanda duka fuskokinsu suka bushe kaman anyi hayaqin yashi suna zaune.

ASH na dawowa suka fito suka qaraso gurinsa suna gaidasa cike da girmamawa suna tambayar jikin Amatu.

Amsawa yayi Yana sake Basu tabbacin karfe goma sha Daya zaa dauka auren Amma Banda na uzaifa zai masa kudi ya samu mata acan kauye ya aura Husnah zai daura mata auren da Abdulhameed idan sun amince da Hakan.

Matse fuska uzaifa yayi sedai su kawu Basu bari ya nuna ba suka hau washe Baki suna cewa ai da Abdulhameed din da uzaifa duka Daya ne duk Wanda aka nawa nasu ai.

Ciki ya shige yabarsu suka koma masaukinsu suna tausar uzaifa Dayake Jin baqin ciki a karo na biyu ana masa ta leqo ta koma haka Akai masa lokacin Amatu yanzu Kuma Yana murna ya samu zuqeqiyar lafiyayyar yar Madara anzo an Hana masa zaa bawa Abdulhameed Dan anga ya fisa jikin girma da cika ido.

Dayake su kawun Basu rasa nasu ba Kuma sun San kudine dai zasu ta shigosu Dan haka suka taru suka danne uzaifa suka hanasa magantuwa akan maganar har su koma.

Husnah gari na wayewa ta fito Kai tsaye dakin maamah Dake daki itama tin jiyan ta kasa fitowa abin duniya ya isheta ya sha mata Kai,

Ga wannan auren na kaddada baqa da zaa daura mata,ga rashin sanin halinda Amatu take ciki ga ASH din Babu Wanda ya sake ganinsa ko Jin idan ya janye hukuncin nasa ko ansamu sassauci ga Abdul Rana tsaka da zaa daurawa aure ba shiri.

Husnah na shigowa ta zube gaban maamah din tana fasa kuka sosai tana rokonta ta yafe mata tace a daura aurenta da Abdul ayau din itama kada daga baya Dad ya sake fushi da ita ya aura mata uzaifa ko Wani daban Wanda bataso.

Shiru maamah tayi mata sbd itama cikin tsaka me wuyan take Amma kukan Husnah da yanda take rokonta har cikin ranta take jinsa dan son datake wa Husnah din Allah ya Gani har qasan ranta take kaunarta kaman itace ta haifeta.

Karyewa zuciyarta tayi ta rarrasheta akan suyi addua kawai Allah ya musu zabi Mafi Alkhairi Amma ita yanzu ko fitama daga dakin batajin zata iya bare zuwa rokon ASH.

Kasa fitowa daga dakin Husnah tayi ta rakube gefen maamah din tana Jin zazzabin tashin hankali na rufeta Dan duk ta sake shiga firgici idan ba ganin tayi Yan kauyen sun kwasa sun tattara sun tafi ba hankalinta bazai taba dawowa jikinta ba.

Tana zaune zuru Abdulhameed yayi sallama dakin ya shigo cikin nutsuwa sanye da Ralph Lauren sweatsets black da suka fito da haskensa sosai slippers ne a qafarsa masu tsada.

Baisan Husnah na dakin ba Saida ya shigo ya ganta zaune gefen maamah din duk a firgice gwanin tausayi.

Tana ganinsa taji sanyi da nutsuwa na San shigarta ta taso ta nufosa tana kokarin shige masa ya riqe hannuwanta tareda tareda Yana kallanta cikin nutsuwa yana cewa ta nutsu.

Nutsuwar take kokarin yi Amma bazata iyaba ta kasa.

Janta yayi suka dawo Palo ya zaunar da ita tareda sakin hannuwanta Yana kallan fuskanta data kumbura gaba Daya ta sauya kamanni.

Magana zaiyi Haydar Shima ya shigo palon Yana ganinsu ya qaraso a natse ya zauna gefen Husnah din tareda zuba mata idanuwansa baice komaiba itama kasa cewa komai din tayi ta fada jikinsa tana fashewa da kuka sosai Wani irin maraicin rashin uwa da Uba takeji Yana daibaiyeta Haydar ne kadai sanyin datake samu a rayuwarta sai Abdulhameed idan ta samesa to Kila ta samu me rarrashinta.

Shi kansa Haydar hawayen tausayinta da kaunarta yake ji na Neman cika idanuwansa Amma Yana buqatan nuna jarumtarsa ya tsayawa yar uwarsa sbd Shima a yanzu auren yakeso a daura mata da Abdul su tafi da ita ya Bata kulawan datake buqata hakama yasan Abdul din zai Bata kulawan da zata buqata ta dawo daidai kaman yanda itama takeson binsu din can.

Abdulhameed miqewa yayi ya Basu guri ya fice zuwa kitchen ya buqaci khaltume ta Aiko Farida ta kawo breakfast dinsu a dakin maamah.

Yana juyowa Farida ta biyo bayansa da katon basket Dake cike da kayan abincin nasu.

Suna shigowa ya tarar da Haydar ya nutsar da Husnah din da maganganun nutsuwa da kulawa ya kwantar mata da hankali sbd saita nutsu ne zata samu abinda takeso idan Dad yaga ta nutsu.

Ajiye basket din Farida tayi ta fara fidda komai ta Jere musu akan table din tsakiyan palon taje ta dauko sauran kayan ta qarasa jerawa ta fice.

Kallan Husnah Dake jikin Haydar har lokacin Abdul yayi Yana cewa tazo taci abinci.

Kaman yarinya qarama haka ta taso a sanyaye ta zo ta zauna kusa dashi har Saida ya Dan matsa kadan sbd taji fada da nasihar Haydar dayayi mata duk Tayi sanyi.

Abdulhameed ma maamah yaje yayiwa nasihar me shiga jiki duk da anriga anbata Gini tin tan Zane Amma dai lokacin gyara Bai wuce musu ba,

Fitowa yayi da itama cikin sanyi tazo ta zauna tareda su.

Haydar da Abdul ne suka sake musu nasihar a tare kafin suka sakasu cin abinci sukaci gaba dayansu kowannensu jiki a mace Babu Wanda ya iya cewa komai sun koma kaman sune ‘yayan su Abdul da Haydar din yanda suka nutsu da maganganun su Abdul din.

Abincin sukaci kaman marasa lafiya suna gamawa kowa yaje yayi wanka ya shirya ya kwanta baccin da Bai samuba tsakar dare kaman yanda su Haydar suka sakasu.

Bayan sunyi baccin dayake kaman na dole ne Haydar da Abdul fitowa sukai suka wuce asibiti dubo Amatu sbd sun shiga gaida Dad din bayanan ya fita Kuma sun tabbatarda asibiti ya tafi.

Suna Isa asibitin suka Tararda su Amatun basa Nan Dan haka Abdul ne ya kirata yaji suna gidan anty Farha,

 Haydar na Jin an sallameta ta samu sauki kenan sai ya fasa zuwa gidan anty Farha din dubota ya wucewarsa gida Abdul ne kadai ya wuce can din.

Yana Isa gidan anty Farha ya Tararda Amatun zaune a Palo tayi wanka harta Saka doguwan Riga mara nauyi Daya sake bayyanarda cikinta karima data kawo mata fura da yoghurt me tsami datake so tana gefenta tana fada mata yanda Akai ta Samo me tsamin.

Zubawa Amatun idanuwansa yayi cikeda kulawa da kauna da farin cikin ganin zata fara hada zuriar kanta tareda mijin dayake tsananin Sonta da kaunarta.

Jin yayi Yana sake samun qwarin gwiwan kulawa da Husnah ya Bata kyakkyawan rayuwa da kulawa kaman yanda Dad dinta ke kulawa da tasa yar uwar.

Zaunawa yayi bayan ya amsa gaisuwar karima tana ficewa daga palon,

Anty Farha na ciki tana baccin gajiya.

Cikin kulawa ya tambayeta Yaya jikin nata tana kallansa ta amsa tana tambayarsa maamah.

Numfashi ya fara saukewa Yana fara zayyano mata abinda yake faruwa na auren maamah din da mum Aisha harma da Husnah dakuma auren Husnah din Daya dawo kansa ya Dora da tambayarta raayinta akan aurensa da Husnah Yana kallanta.

Shiru tayi cikin mamaki me girma da fargaban auren maamah din Dan kuwa abun yayi Wani iri Amma tana magana maamah zata ga laifinta musamman yanzu datake cike da fushi da ita akan cikin.

Maganar aurensa da Husnah kuwa rasa abin fada Tayi Dan kaman yanda Abdul din ya fada ko ita bazata taba So Husnah taje gidan nasu aure ba Dan kuwa mutuwa kwata kwata rayuwarta zatai Dan haka batajin zata Hana Abdul aurenta sbd kubutar da ita duk da abubuwan Dake tsakaninsu wannan Wani lamarin ne daban.

Ajiyan zuciya ya sauke da amincewan Amatun Dan kuwa bazaiso ya auri Husnah batareda yar uwar tasa na kaunar alaqar ba har cikin rantaba.

Shiru sukai kafin ta kallesa tana ajiye cup din hannunta ta tambayesa Haydar murya a sanyaye.

Bayaninsa yayi mata akan fushin da yayi Amma dai zai sauko sbd duk Basu kyauta masa ba zasuyita basa hakuri harya hakura din.

Maganar maamah ya fara yiwa Amatun itama Yana mata nata nasihar akan maamah uwa ce baa fushi da mahaifi komai zeyi maka Dan haka ta tabbatarda tayi magana da mamaah ta Bata hakuri duk da batada laifi.

Shiru tayi sbd Bata taba fushi da mahaifiyarta ba hasalima tsoro ne yake Sakata yin nesa da ita sbd kada ta shiga tashin hankali ta Saka maamah din cikin Bacin Rai.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

78

*************

Karfe goma Abdulhameed yabar gidan ya koma bayan sun jima suna magana sosai tsakaninsa da Amatun.

Mum Aisha har guduwa daga mansion din taso yi Amma Sam securities sun Hana kowa fita Dan haka dole ta dawo da motarta tayi parking ta dawo cikin kaman mahaukaciya Dan kuwa tin kayan jiya ne a jikinta gashi Naufal Se kiransa takeyi wayarsa kashe sbd har lokacin gidan Yola din baa mayar da wuta ba daqyar yake zuwa ya samo caji a gun masu caji da kekensa ta qafa Daya.

ASH ko breakfast ya kasa yi a cikin gidan sbd rashin dawowan su little Abeeda har lokacin Dan haka ya fahimci gidan Farha ta wuce kenan Bata dawo Nan din ba.

Numfashi ya sake me dumi Yana Dan Jin sanyin jiki na shigarsa ya daure ya kame ya shirya ya fito qarfe goma da Rabi lokacin Kuma Abdulhameed ya dawo gidan yayi parking mota ya fito kenan Mr Jameel Shima ya shigo harabar gidan yayi parking tasa motar ya dauko tsadaddun shaddodi da yadikan manya masu tsada ready made kusan duka size din Abdulhameed din ya wuce dasu ya miqawa Abdul din ya wuce gurin ASH Dake jiransa.

Abdul su kawu ne suka kirasa da kansu suka isar masa da sakon ASH din na yau din duka zaa daura auren harda nasa Dan haka Saiya shirya zama magidanci Kuma wlh ya riqe yar mutane da kyau tinda Shima gashinan tasa yar uwar ta samu guri har uban yar masu gida akeci akanta.

Shiru kawai Abdul yayi sbd Bai dauka tinda ya amince ba zaace zaa daura auren yanzu ba.

Fitowa yayi yaje ya sanar da maamah wadda itama zataso Daman a daura auren Husnah ta samu me kulawa da ita yanda ya kamata tinda su dole yanzu zasu bar Nan din.

Albarka ta sakawa auren tana danne damuwarta da halin datake ciki ita tareda fada masa ya riqe yar mutane da kyau da kulawa.

Mum Aisha na ganin lokaci ya sake matsowa ta fito a rikice ta koma gurin ASH ta ringa kuka tana rokonsa Amma Sam baima Kalli inda takeba Saida su kawu suka shigo kallo daya tayiwa dukkaninsu batareda ma tasan waye nata angon a cikinsu ba ta fasa kukan baqin ciki sbd ganin su dukan kaman baqin aljanu kowannensu karnin shaddarsa kawai zai iya sumar da ita,ita datake shafa turaren da kudinsa zai ciyar da kaf gidan Sanda Fulde din na tsawon kwanaki koma satittika Amma ace aure zatai da wainnan fataken.

Ficewa tai tana Jin Hawan jininta na tashi da baqin cikin ganinsu kawai.

Tana ficewa kawu ashiru ya bita da Satan kallo Dan shi gaba Daya Sonta ma qara shigarsa yakeyi,

‘dan nata ma da ake fada shi taje dashi agolanci zai amshesa ya hada da nasa manyan yayan ya riqe.

Husnah na daki ta rasa meyake mata dadi,ta rasa wa zata kira wa zata kama gashi Haydar yace tayi zamanta daki karya fito sai komai ya kammala sunga abinda ya faru tukuna.

Maamah ma tana dakinta zaune yanzu tinanin Amatu ne Kuma yake rufeta gashi dai ma zata koma kauye tabar Amatu anan karshe abinda taita tashin hankali Akai tana ji tana Gani Amatu zata cika gidan da yayan ASH batada ta cewa,

Amma Kuma har lokacin mamakin samun cikin Amatun Bai Dena jijjigata ba,

Tayaya ASH ya iya kebewa da Amatun har cikin ya samu?

Suna cikin gida Daya yarta tayi ciki harya bayyana Bata saniba,

Kunyar kanta da damuwa me nauyi ce ta sake danne zuciyarta gashi yanzu kiri Kiri tana kallo zata tafi tabarta zaman auren da Basu shirya ba.

Karfe goma sha Daya da mintina aka fara daura auren Abdulhameed Sanda Fulde da Husnah Ashraf Talba akan sadaki Naira dubu dari biyu Wanda Abdulhameed dinne ya biya abinsa da kansa mutane qalilan ne suka sheda a masallacin gidan nasa,

 sai Kuma na maamah da kawu bello akan sadakinsa da Shima shine ya biya abinsa dubu Tara.

Na mum Aisha da kawu ashiru shine na qarshe da aka daura akan sadakinsa Shima Daya biya dubu Tara Dan dubu goma goma aka yanka musu sadakin.

Mum Aisha ko da aka gama daurin auren ciwonta ya tashi gaba Daya na hawan jini dole aka kwasheta zuwa asibiti,

Maamah kuwa kukan datasha kaman qaramar yarinya ita kadai cikin daki tana Jin baqin cikin su kawun Dan batasan ma inda zata fara zama da matansa ba da Babu hakuri ko hankali a cikinsu ba ko kadan,

Da anbarta ba aurenma zata iya komawa kauyen tayi zamanta Amma auren baida Wani amfani da girmanka.

Husnah na daki duk tayi zuru cikin matsanancin halin tsoro da fargaban Menene makomarta,

Yanda zuciyarta ke bugawa kaman zata fado da tsantsan tashin hankali ya Saka hannuwanta ma rawa sukeyi tana dai zaune cikin fita hayyacinta aka Bude kofar bedroom din nata aka shigo…

Haydar ne cikin cikin fararen manyan kaya da Dan adonsa Dan inganta auren yar uwarsa da nuna farin cikinsa Koda kuwa ana cikin damuwa ne.

Ganinsa ya Sakata juyo da jajayen idanuwanta ta zuba masa bugun zuciyarta na tsananta har yayi yawan da ba’a cika so ba.

Qarasowa yayi da sauri Dan ganin ta kusa rasa bugun zuciyarta yana isowa ya riqeta Yana cewa

“Andaura aurenki da Abd…..

Bai qarasa ba Idanuwanta suka juye tana sauke numfashi me qarfi ta sume a jikinsa Dan sanyin Daya ratsa kunnuwanta da zuciyarta haryafi karfin bugun zuciyarta a lokacin.

Tarota yayi jikinsa hankalinsa na tashi ya fara Ambatar sunanta da qarfi Yana Dan jijjigata.

Daukota yayi gaba Daya a ya Sauko zai fita da ita zuwa asibiti Abdulhameed Daya baro gurinsu kawu ya gansa da sauri ya qaraso Yana tambayar abinda ya sameta.

Kasa amsawa Haydar yayi Yana kallan fuskanta.

Hannuwa Abdulhameed din ya Saka ya karbeta daga jikin Haydar din Yana cewa

“Mu koma a kira likita yafi zuwan asibiti tinda kaman Suma ne”

Juyawa sukai suka koma saman tana jikin Abdul Daya daukota kaman Bai dauko budurwa ba kaman yarinya ya dauko.

Bedroom din nata suka koma ya kwantar da ita khaltume ta kawo ruwa da sauri tace a fara yayyara mata a Gani.

Abdul dinne ya Karba ya zuba mata a fuska Yana ambatar sunanta har lokacin tana jikinsa.

Ajiyan zuciya tafara saukewa tana jerowa kafin ta Bude idanuwanta ahankali tana sake sauke ajiyan zuciya Wani bayan Wani.

Khaltume na ganin Hakan ta sauke numfashi itama hakama Haydar shi kansa Abdul din ajiyan zuciya ya sauke.

Akan fuskar Abdul ta sauke idanuwanta ko kyaftawa Batayi jikinta gabaki daya ya matu Bata iya motsa ko hannunta ahankali ta Bude bakinta kuka na Neman kwace mata tace

“Thank you”

Kalman data furta ya Yanke zuciyar Haydar gaba Daya har hawaye suka ciko Idanuwansa ace tana yiwa namiji godiya Dan ya aureta.

Shi kansa Abdulhameed kalman yankan zuciyarsa tayi Dan haka ya dora hannunsa ahankali kan bakinta tareda girgiza mata Kai yana kallan cikin idanuwanta yace

“Dad dinki Bai Bani aurenki Dan kice thank you ba Ya bani ne sbd yasan kinada mahimmanci me girma a zuciyarsa da bazai iya Bada ki kauyen ba”

Kalamansa suka Saka hawayen cikin idanuwanta saukowa tana Jin zuciyarta na samun nutsuwan fara dawowa hayyacinta idan har da gaske tanada sauran mahimmanci a zuciyar Dad dinta.

Haydar juyawa yayi ya fita Dan amsa wayar iyayensu na porthcrt da yanzu ne suka gama magana da ASH ya sanar dasu auren Husnah din.

Bayan ficewan Haydar Shima Abdulhameed din sake rarrashinta yayi da magana ta sake dawowa hayyacinta kafin ya fice daga dakin tabi sa da kallo tana Jin yanzu Kuma da aka daura nata auren dashi batasan tayaya zasuyi zaman aurenba da Wanda ta girma duk da mantawama tayi da Hakan kwata kwata Amma dai koma yayane zuciyarta tana samun Nutsuwa da kulawansa tin kafin su zo yanzu tun suna Yara.

Ana gama daurin auren da duka Wani gaishe gaishe Akai Sallahn Azahar ASH ya shige.

Abinci yaci sama sama ya shige sashensa Babu Wanda ya sake ganinsa sai laasar ya fito cikin Shirin fita Bai buqatan driver sbd Mr Jameel Baya Nan da kansa yaja mota ya fita Kai tsaye gidan Farha ya nufa.

Ko Daya Isa motar Mr Jameel tana gidan Shima yanata ganin shege a gun Farha da gaba Daya ya rasa gane kanta duk ASH din ya ja masa.

Ganin Mr Jameel ya Saka ASH Dan kamewa Shima Mr Jameel din ganin ASH ya sakashi mamaki Amma ya boye ya danne mamakin tareda masa barka da zuwa ya masa jagora zuwa ciki Dan shi yafi awa Daya a harabar estate din Amma Farha taqi fitowa Dan haka zuwan ASH zai basa Dama da saukin lamarin tinda shi dole a iso dashi ciki sbd matarsa datake ciki.

Kofar palon yayi knocking tareda danna door bell lokaci daya

Karima na palon Dan haka Koda taji door bell din zuwa kawai tayi ta Bude

Gani Mr Jameel da ASH da kansa ya Sakata saurin yin gefe kanta a qasa cikin tsananin girmamawa ta musu sannu da zuwa tana gaidasu.

Lafiyayyar Palo ne me girma Daya Hadu sosai Dan haka guri Mr Jameel ya nunawa ASH din ya zauna Yana sake Saka kiran numbern Amatun a karo na kusan dari da Wani abun Bata dagawa karshe ma wayar a kashe.

Anty Farha na dakinta tana Shirin fita tareda karima siyayyar wasu abubuwan buqatan Amatun Dan Mr Jameel din dayake waje zata Saka ya kaisu ya dawo dasu Dan haka Bata San da baqin ba Saida ta fito a shirye sai ganin the great ASH TALBA tayi zaune palon Ya gauraya musu numfashin palon gaba Daya da qamshinsa me sanyi da gigitarwa.

Rikicewa tayi sbd ba zatan ganinsa da kwarjinin Daya cike musu gurin dashi Dan haka murya duk a rude ta Dake suka gaisa tace bara ta kira Amatu.

Shiga tayi dakin Amatun ta Tararda tana wanka ta fita ta sanar masa tana wanka.

Mr Jameel da duk ya gama susucewa da ganin Farha din fita yayi daga waje itama Farha din text tayiwa Amatu cewan ASH TALBA na gidan ta bi bayan Mr Jameel karima na bayanta suka fita bayan ta sanar masa Amatun zata fito.

Suna fita Mr Jameel ya juyowa Yana kallanta ta daure fuska tana sake Jin zafinsa na qin sanar mata tareda ASH din sukazo bare Amatu ta sani.

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

79

*************

Amatu na fitowa wanka a natse ta zauna ta goge jikinta tareda Shafa Mai da turare ta Saka Riga da wando na bacci masu santsi da tsada ta Saka huka mara nauyi ta ziro slippers ta fito Dan Jin shiru gidan da Kuma ruwan datake buqata ta Bude kofar dakin ta fito tana Jin qamshin dayake shiga hancinta Yana Sakata mamakin jinsa sbd tasan bame yiyu bane Jin wannan qamshin a gidan nan Kuma a daidai wannan lokacin.

Tsakiyan palon take sake kusantowa tareda Bude Baki cikin sautin muryanta me nutsuwa ta qwalla kira Kiran Karima.

Tinda ta ya jiya Karan Bude kofar bedroom da rufewa ya dago kansa a natse ya zubawa hanyar dayaji motsin idanuwansa Dake galabaice da buqatan ganinta harta fito daga hanyar bedroom din tana shigowa palon dakyau idanuwansa akan cikinsu Dayake gabanta ya koma Yana Jin Yana sake macewa akanta kowane lokaci da zai ringa Dora idanuwansa akanta.

Bata lura dashi ba Saida ta kawo kusan gab dashi idanuwanta suka sauka akansa cikin sauri ta tsaya cak tareda yar razana sbd Bata taba tinani ko tsammanin ganinsa ba Tako Ina a gidan.

Juyawa tayi ta Kalli kofar kitchen tareda kallan hanyar bedroom din anty Farha kafin ta Dake Dan janyewa gefe daga gabansa tana dauke kallanta akansa shikuma Yana sake zurfafa nasa kallan akanta tareda miqa hannunsa Daya cikin sanyi da nutsuwa yayi mata sallama Yana sake miqa mata hannun idanuwansa akanta.

Bata Kalli hannun ba ta Dan koma gefe daga nesa kadan dashi ta zauna a natse tareda dagowa ta gaidasa kaman yanda take gaidasa a Baya Babu sakewa Babu alaman sabo ko wata shaquwa da kulawa.

Hannunsa data bari a gurin kaman ma Bata Gani ba ya kalla tareda dawo da hannun Yana kallanta ya amsa gaisuwar tareda tasowa ya dawo inda take ya zaune sosai jikinsu na haduwa ya kamo hannunta Daya a sanyaye ya Bude Baki yace

“Girman laifin Ashraf yakai har haka ne?

Hukunci Zaki masa?

Ba Zaki sassauta ba ko kadan ne?

Hannunta Daya kama ta zare ahankali cikin nutsuwa batareda ta dago ta kallesaba ta girgiza masa Kai kawai ahankali alaman ba komai datakewa fushin.

Tsayawa yayi kallanta sbd gaba Daya ma taqi kallansa hakama taqi nuna fushin nata ko bacin ran nata yasan yanda zai Bata hakurin ya rarrasheta.

Miqewa tayi tana kokarin tafiya kitchen ta dauko abinda ya fito da ita ta koma daki,tana taku Daya ya riqo hannunta tareda sauke numfashi da ajiyan zuciyan masu sanyi jikinsa na mutuwa ya miqe tsaye a hankali ya dawo gabanta ya tsaya cikin kulawa ya janyota jikinsa tareda ya Bude Baki da Wani irin sauti mara hayaniya ya furta

“m sorry”

Rintse idanuwanta tayi ahankali tana Jin radadin zuciyarta na raguwa sedai Kuma batajin zata iya barin ya Ragu din tinawa da quncin data shiga akan shariyarsa.

Sai data Dan sauke numfashi a zuciyarta kafin ta dago idanuwanta masu rudasa ta kallesa cikin sanyinta kafin ta janye jikinta gaba Daya tana Dan dauke idanuwan nata akansa ta Bude Baki tace meyasa yake cewa sorry ita Babu komai fa daya mata.

Hakan data fada ya sakashi sake shiga damuwa Dan maganan yakeso suyi Amma tana toshe masa hanya.

Kitchen ta juya ta tafi ta dauko ruwanta ta fito har lokacin Yana tsaye hanyar dakinta take kokarin nufa ya sake takowa ya kamo hannunta tareda rungumota ta Baya cikin sanyi yace

“Please LA””

Shiru tayi batace komaiba

Ya sake zagayota da hannuwansa Yana fora hannuwansa akan cikinta Yana shafawa Yana Jin kaman ya Bude kirjinsa ya Sakata cikin zuciyarsa ko zuciyan ta samu sassaucin azaban Sonta take ji.

Ajiyan zuciya ya sauke hannunsa na kan cikin a sanyaye tace

“ASH is really sorry”

Hannunta ta Dora akan hannunsa ahankali Wanda Hakan ya Sakasa Jin sanyi da Wani irin nutsuwa sedai kafin ya Bude idanuwansa yaji ta janye hannunsa daga cikin nata tana janyewa gaba Daya daga jikinsa ta juyo batareda ta kallesa ba ta sake maimaita masa ba komai ya Dena damuwa da maganar.

Wannan Karan kusan abinda yake ranta na fushi ya Dan bayyana tareda hawayen da suka ciko idanuwanta masu radadi duk yanda taso dannewa da boyewa.

Ganin fushin datai Yana son bayyanar masa ya Sakata wucewa kawai bedroom dinta ta shige ta rufo kofar sbd batason yasan tana cikin quncin abinda ya mata Dan Bata buqatan basa Daman wanke kansa.

Hanyar data bi ya zubawa idanuwansa da suka sauya take sbd ganin hawayen Idanuwanta sun rikita masa lissafi.

Baya keta iyakar da Bata kamata ba da Babu abinda zai hanasa shiga dakin ya sameta Amma ba gidansa bane ko da tana matarsa bazai iya shiga kuryan ba.

Zaunawa yayi cikin tareda daukan wayarsa yana Sake Kiran wayarta Amma taqi dagawa Dan haka ya rubuta mata Sako Amma still ba reply ba motsinta.

Shiru yayi kansa na daukan nauyi kaman yanda zuciyarsa tayi nauyin.

Bazai iya sanin zaman awa nawa yayi ba a palon har sai da su anty Farha suka dawo itama anty Farha din tayi mamakin ganinsa shi Daya a palon Dan haka suna shigowa ficewa kawai yayi.

Yana fitowa harabar gida mr Jameel Dake tsaye kaman an dasashi a inda yake sbd abinda Farha ta masa Yama rasa inda zai Saka ransa,

Kallansa ASH yayi da idanuwansa da sukai Dan ja Shima ASH din ya dago ya kalla da nasa idanuwan kowannensu na kokarin boye damuwarsa.

Sai da safe Mr Jameel yayiwa ASH din bayan sun shiru kowa ya rasa abin fada.

Mota ASH din yaja yabar gidan ya kama hanyar gida.

Mr Jameel ma tada tasa motar yayi ya nufi gida.

ASH na Isa gidan Kai tsaye shigewa bangarensa yayi Daman Kuma dare yayi tinda kusan goma ta wuce.

Husnah da daddaren Haydar ne yazo da kansa suka ci abinci tare sbd idan ba Wani ya tsayu akanta ba ba lallai ta iya cin abincin ba sbd har lokacin tana cikin damuwa da sanyin jiki.

Maamah kuwa Abdul ne yaci da ita mum Aisha kuwa da aka sallamo tana daki a rufe Babu Wanda yasan halin datake ciki.

Su kawu kuwa a matse suke da su koma kauye amarci kawai suke Jira su fara darza.

Bayan ficewan ASH anty Farha dakin Amatu ta nufa Kai tsaye ta Bude tana ambatar sunanta ta ganta zaune tsakiyan gadonta idanuwanta sunyi jajir da alama kuka tayi sosai sbd Radadin abubuwan da suka dawo mata na wahalan datasha a wannan Dan lokacin da ciki.

Qarasowa anty Farha tayi tana rarrashinta tareda Bata hakuri akan ASH din ta sauko Hakan tinda yace ayi hakurin.

Shiru kawai Amatun tayi sbd haryanxu bataji zuciyarta ta sassauto akansa ba.

Hakanan anty Farha tayi rarrashinta da ban hakurin ta fito ta wuce dakinta

Ita Kuma kwantawa tayi duk da baccinta ya qaurace tin dazun.

Washe gari da zazzabi Amatun ta tashi sbd kukan datai da daddaren dakuma rashin samun baccin Daren Dan haka ko data tashi sai ciwon Kai yazo kafin daga baya zazzabin.

Dr beeba anty Farha ta kira sai gashi Dr beeba din Tai kira Mr Jameel ta sanar masa sbd ASH ya Bada umarnin komai Daya danganci Amatu da cikinsa ya ringa sanin komai koma Menene.

Ganin ba shine ya kirata akan taxo Amatun ba lafiya ba yasa ta kira ta sanar kafin ta tafi din.

Mr Jameel na Jin Hakan ya taho mansion din Dan dama Yana Shirin tafiya can dinne sbd su kawu dasu mum Aisha da zasu wuce Yola.

Yana isowa kusan komai na tafiyansu ya kammala su kawu har sun fito mum Aisha da maamah ma kusan duk sun fito lafiyayyar motar mansion dince zata kaisu Yola.

Mum Aisha jiran kawai takeyi su Isa yolan subar Nan ko kallanta kawu ashiru yayi saita Saka Yan Sanda sun makantar dashi Dan kudinsa na sadaki harda qari Mai yawa zata basa ya saki auren ya qara gaba.

Maamah kuwa abinda ta sani shine zata koma gida ne ta zauna Amma ba Wani zaman auren da zatai da kawu bello sbd tasan ko gurin Sakata baidashi.

Husnah tayi kuka sosai na tafiyan maamah din hankalinta ya tashi ta yanda zata zauna ita Daya a gidan yanzu ba kowa.

Yanda ta daga hankalinta ne Haydar yace su shirya gaba Daya su rakasu maamah din Yola su biyo jirgi gobe su dawo.

Dayake Daman da Abdul zaa tafi tin farko sai tafiyar ta qara yawa Jin su Haydar dinma zasu tafi.

Mr Jameel ya sanar da ASH Dr beeba ta sanar da Amatu ba lafiya Dan haka bayan sun fito yayi sallama da su tareda sallaman su kawu da abinda ya wuce tinaninsu suka ringa Godia hakama su mum Aisha da maamah sanyi jikinsu yayi da sabbin motocin Daya Basu kowaccensu daddaya bayan yasan a kauye zasu zauna Ina gurin bin mota ma bare Janta.

Har lokacin Husnah a tsorace take da Dad din nata ta kasa zuwa inda yake duk da ta zama matar Abdul idan ba ganin tayi su uzaifa sun bar gidan ba hankalinta baa kwance yake ba.

Shine ya fara ficewa mansion din tareda Mr Jameel dayake jansa zuwa gidan Farha.

Shiru sukai Mr Jameel na drivern yanason ya tambaya Yaya ake rarrashin mace ta sauko daga fushi a gurin Mr Jameel Amma Kuma dai ya fuske ya kame batareda ya tambayar ba zai sake gwada sa’arsa yau yagani idan little Abeedan zata sauko.

Suna Isa Dr beeba ta riga ta Isa tana gidan Dan haka anty Farha ce da kanta ta fito tayiwa ASH din jagora bayan ta gaidasa cikin girmamawa batareda ta Kalli ko inda Mr Jameel yake ba tareda su.

Suna shiga palon Dr beeba na fitowa daga dakin tareda gaida ASH tayi masa bayanin ba Wani matsala bane kawai rashin hutun bacci ne da yar damuwa wadda ya kamata ace ta cire daga ranta koma ta Menene.

Shiru yayi tareda yiwa Dr beeba din godiya a taqaice kafin ya Kalli dakin anty Farha tayi saurin yi masa ison Isa dakin duba Amatun sbd bazata Wani iya fitowa ba.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

80

*************

Karima Daman tana kitchen a rufe tana aikinta tinda ASH din ya shigo gidan,

Anty Farha kuwa Dr beeba ta juya rakiya Shima Mr Jameel din bayansu ya bi Yana Dan sake yiwa Dr beeba Godia.

Acan mansion kuwa su kawu sun Yanke shawarar akaisu su biya su duba Amatu kafin wucewansu hakama maamah dole zatai magana da Amatun kafin wucewarta Dan haka bayan motocin sun fito Kai tsaye hanyar gidan Farha suka kamo.

ASH a natse ya Bude dakin ya shiga duk zuciyarsa ba dadi da zancen Dr beeba na fadin damuwa ne yake damun Abeedan.

Tura kofar dakin yayi bayan shigowansa idanuwansa akanta tana zaune tsakiyan gadonta sanye da Riga da wandon jeans Daya lafe jikinta sai rigar Ralph Lauren fara data Dan kwanta jikinta duk da freesize ce Rigan.

Kyakkyawar fuskarta ya zubawa idanuwansa datake jinsu a kanta Amma Bata dagoba ta kallesa kafin ya Maida kallansa kan cikinta ya Tako a natse ya zauna ahankali gefen gadon tareda janyota baice komaiba Saida ya shiga da ita gefen jikinsa ya rungume ya saki ajiyan zuciya kusan guda hudu a Jere kafin ya Bude Baki yace

“Good morning LA”

A natsenta ta amsa masa itama da ce masa…”Good morning”

Hannunta ya kama ahankali yakai bakinsa yayi kissing kadan kafin yace

“Yaya jikinki?

Did you eat your breakfast?” Yaqarasa fada Yana kallan abincin da aka aje mata Jere a trey kan bedside.

Gyada masa Kai tayi ahankali tana Dan Bude Baki tace

“Naji sauki”

Hannunsa ya Kai ya Dan dago fuskanta Yana kallan doguwar hancinta zuwa idanuwanta da suka nuna alaman kuka tai sosai sbd idanuwan sun Dan kumbura hancin Kuma yayi ja.

Tafin hannunsa ya Saka ahankali ya shafi idanuwan nata Yana Jin baisan Yaya zaiyi ya Sakata Bude masa zuciyarta ya wanke duka damuwa da bacin ran Daya Sakata a ciki ba.

“Meyasa kike damuwa bayan kinsan yanayinki Baya buqatan duk Wani damuwa?”” Yafada kalmomin cikin muryar Dake bayyanarda damuwansa akan yanayin nata.

Hawayen da batasan da su bane suka ciko idanuwanta kafin su sauko ya Ciro handkerchief ya taresu Yana kallanta da tsananin kulawa da damuwa yace

“Zaki hukunta ASH ne ta Hakan?

Wannan yayi tsauri sbd kukan naki Yana sakaki ciwo ne”

Fasa masa kuka kawai tayi take ya qarasa rikicewa cikin zuciyarsa Yana rasa abin yi sai kawai ya rungumeta Yana maimaita kalman sorry a sauti me bayyanarda damuwansa da halinda take ciki.

Kukan taci gaba da yi Yana sake shigar da ita jikinsa Yana rarrashinta kaman zai maidata cikinsa.

Ganin bazata Daina kukan ba Kuma kukan yankan zuciyarsa yakeyi Dan haka ya dagota Ya zaunar a qafafunsa yana share mata hawayen Yana sake Saka mata magana da sautin da ita kadaice take jinsa sbd qasan maqoshinsa da maganar ke fitowa.

Daqyar ya samu tayi shiru ya goge mata fuska ya kamata sukaje har ciki toilet din dakin ya rakata ta wanko fuskanta suka fito Yana riqe da hannunta duk bayajin dadin ransa.

Zaunawa suka sake yi yana kallanta Yana Dan sarqe hannunsa Daya da nata Yana sake rarrashinta.

Dago jajayen idanuwanta tayi ta Dan kallesa ya Bude Baki zaiyi magana Akai knocking kofar dakin anty Farha ce ta sanar dasu su maamah sunzo ganin Amatun.

Shiru yayi Yana kallan Amatun Dan ganin yanayinta idan Hakan yayi mata dadi kokuwa,

Ita Kuwa gabanta faduwa ya Dan yi tareda Jin tana Dan shiga fargaban haduwa da maamah sbd cikinta da rikicin da Akai akansa dakuma samun ASH din da sukai a gidan.

Kallansa tayi Taga Babu Wani yanayi na rashin Jin dadin samunsa da Akai Kokuma damuwan zuwan nasu da kunyar su gansa duk Babu ko Daya a tareda shi hasalima shi itan yakeson sanin idan zata iya fitan.

Numfashi ta sauke ahankali tareda saddaqarwa da komai sbd tinda cikinta ya bayyana ga duniya batada mafita ko zabi bare tinanin gardamawa ko boye waye uban cikin,

Ko maamah dai batada yanda zatai ta ci gaba da boye mata ko guje mata akan duk hukuncin da zatai akan cikin sbd kaddara ta riga fata.

Tashi tayi daga qafafunsa datake Kai a zaune tareda nufan dagowan hijab dinta ta dauka,

 shine ya Saka mata hijabin da kansa Yana kallanta cikin kulawa ya furta

“Zaki iya fitan??

Gyada masa Kai tayi a hankali tana daidaita kanta ta nufi kofar dakin ta fito Yana gefenta suka nufo palon gidan Wanda kusan dukkaninsu kawun dasu maamah da kowa na palon.

Anty Farha ce ta fara ganin tahowar tasu ta juya da sauri ta kalli maamah da mum Aisha harma da Husnah da Haydar kafin ta dawo da kallanta kan ASH din sbd Bata dauka zai iya biyo Amatun su fito tare ba asan Yana gidan duk da motarsa Dake harabar gidan dasu Haydar zasu gane Amma ai ganin Mr Jameel zaisa su dauka shine yazo da motar ba ASH din ba.

Husnah,mum Aisha da maamah a tare suke kallan ASH din mamakin ganinsa da inda ya fito Yana Saka jikinsu gabaki daya sanyi,. Mum Aisha hawayenta kasa riquwa sukai suka fara gangarowa tana sharewa jiki ba qwari.

Husnah ma nata idanuwan cikowa sukai da hawayen sedai tana shanyewa batareda ta bari sun saukoba Wani ya Gani musamman Dad din nata.

Maamah qasa tayi da kanta itama nata idanuwan kaman zasu ciko da hawayen ta danne,

Haydar kuwa kallo daya yayiwa Amatun ya sauke kansa ganinta tareda Dad dinsa.

Abdulhameed Husnah da maamah yake kalla Yana fatan sun Dena Jin abinda suke ji abaya.

Su kawu Dake gefe rakube kuwa jajayen hakoransu suka ringa washewa suna Jin zamzam da ganin ASH guda Yana bin ‘yarsu.

Zaunawa yayi dukkaninsu kowa na sake gaidasa bai Wani tsayaba ya tashi suka bar gidan da Mr Jameel da shidai har lokacin Bai ganewa komaiba.

Bayan ficewansa tsit palon yayi Babu Wanda ya motsa bare magantuwa sbd kowa da abinda ya kashe jikinsa yayi sanyi laqwas.

Anty Farha ma shiru tayi sbd batama San ta Ina zata fara kame Kamen zancen ba ga Amatu ma duk tayi zuru ta rasa abin fada bayan gaisuwar da taiwa kowa harda maamah dasu kawu.

Abdulhameed ne yafara Dan gyaran murya Yana katse shirun da tambayar anty Farha ya jikin Amatun dakuma Dan tsokanarta Bata tayasa murnar aurensa ba.

Itama anty Farhan cikin sauri tana San sakin dariyar qarfin hali ta amshi zancen da Sako maganar auren tana tayasa murna tana yiwa Husnah ma congratulations kafin ta Kalli mum Aisha tanason tayata murna da fatan Allah ya Sanya alkhairi Amma tana gudun yanzu gidan ya rikice da sabon tashin hankali Azo asake laifin da baa San Ina abin zai tsaya ba.

Kan maamah ta Maida kallanta tana son magana itama Amma bazata iya ba Dan haka ta Maida fitarta ga su kawu da suketa washe Baki suna ta sambadawa Amatu albarka da fatan ta haihu lafiya.

Mum Aisha gaba Daya komawa tayi kaman an tsoma ta ruwa itada Husnah da hawayenta ke cigaba da cikowa tana hadiyewa seda Abdul ya lura da Hakan ya miqe hannunsa Daya ahankali ya Dora akan nata Daman itace a kusa dashi Dan yanzu kaman cingum take Neman zaman masa shi da Haydar sbd tsoro.

Dago idanuwanta tayi ta kallesa Shima ita yake kalla cikeda sanyi da kulawa akan ta kwantar da hankalinta karta sakawa zuciyarta komai.

Qura masa idanuwanta tayi tana Jin hawayenta na komawa,

Hannunta ya kama ya sarke da nasa Yana Dan sake bata nutsuwa batareda yayi magana ba.

Anty Farha ce ta cewa maamah ta shigo daga ciki suka miqe suka shige harda Amatu wadda Haydar kawai dayaqi kallanta take kalla sbd damuwan fushin datasan itama yanayi da ita.

Maamah da Amatu da Abdul ne suka shiga dakin Amatun harma da anty Farha wadda Bata Wani jima ba ta fito tabarsu suka qarasa magana bayan sun taru sun bawa maamah hakuri su  ukun ita da Amatu da Abdul sun Kuma rarrasheta tareda tabbatarda ta nutsu ta yarda da kaddara akan komai Taga Allah ya kaddaro.

Sun Dan jima kafin suka fito mum Aisha dai tana zaune kaman ma Bata hayyacinta Dan Nisan datai a tinani.

Suna fitowa suka dauki Shirin tafiya Amatu na gefen maamah tanajin Sam hankalinta bazai taba Kwanciya da zaman maamah a kauye ba Dan haka batajin zata yarda da Hakan.

Har waje suka rakasu suka wuce bayan su kawu sun sake wa Amatun nasihan aure hakama maamah a karo na farko yau din data mata adduar samun farin cikin rayuwar auren.

Haydar ne dayaqi kulata har lokacinda zasu wuce ta kalla idanuwanta na cikowa da hawaye tai masa magana.

Tsayawa yayi tareda juyowa ya kalleta ya mata fatan samun lafiya ya wucewarsa.

Ko da suka wuce ta dawo cikin gidan Jin tayi Wani nauyi na zuciyarta ya sauka sbd mahaifiyarta data shirya da ita duk da ba fada sukeba Amma a zuciya sun kasa samun Nutsuwa da juna sai yau din.

Abdulhameed ticket ya siyawa kansa da Husnah da maamah Amma su kawu suka rufe ido sukace a mota tareda su maamah zata tafi.

Mum Aisha ma ticket dinta ta Siya tabi su Abdul din suka bi jirgi ba tareda sanin ASH ba suka wuce.

Haydar Daya ga an Hana maamah bin jirgi Saiya fasa siyan ticket din shi ya bisu a motocin sbd Abdul dayace Husnah da maamah subi jirgin shi zaibi su maamah sai Haydar yace ya tafi dasu Husnah din shi yabi su maamah din.

Su Abdul da Babu Bata lokaci ko wahala suka isa Yola Kai tsaye TALBAs mansion suka nufa da motan datazo daukansu.

Kafin su Isa an gyara wuta da ruwan gidan da komai harma da masu aikin duk sun dawo Dan haka Mansion din ya rayu.

Ga mamakinsu Koda suka Isa anata aiki ana tana Manson din biyu Daya maamah Daya mum Aisha.

Mum Aisha data Tararda Hakan Wani kukan farin ciki da sanyin zuciya ta fasa tana Jin asirinta ya rufu sbd da niyar guduwa tazo akan ta tafi kauyen Kuma idan ta gudu ba gurin zuwa ne da ita ba Dan haka taji ta Dan dawo hankalinta.

Su kawu dayake tin acan daman ASH ya sanar musu dasu maamah din ya Basu gidansa na yolan zaa Raba musu su zauna anan Kuma sun amince Dan haka ko zama Basu yiba duka wuce kauye sbd duk hankalinsu baa kwance yake ba Suma da tarin dukiyar da suka samo a matse suke dasu Isa kauye su raba su adana ko su siya gona da dabbobi Dan haka suka wucewarsu akan sai angama gyara an natsa zasu ringa zuwa gurin matayen nasu suna musu auren dangan Sanda.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

81

*************

Sbd gyaran da akeyi a mansion din ya Saka babu Wani gurin saukan mutane  natsatse Dan haka dole Abdulhameed lafiyayyar hotel ya kama daki yakai Husnah can ya tafi kauye tareda su kawu ya Kuma dawo a ranar sbd yasan bazata iya zama gidan ba sbd maamah kwata kwata batajin dadin zuciyan buqatan kowa a tareda ita.

Ita kanta Husnah bayan ya barta a dakin ya tafi Jin tayi tana samun Nutsuwa sbd su kawu sun tafi da wahalarsu ta tabbatarda ta samu kubuta kenan.

Haydar ma a hotel din ya sauka inda Husnah take dakin kusa da ita kafin Abdul din ya dawo ya kula da ita.

Ko bayan isarsu Abdul kauye Saida ya sake bawa su kawu kudi da mutanen gidan sosai suka ringa tayasa murnar aure da fatan alkhairi sai yamma sosai ya juyo Dan haka Koda ya iso dare yayi sosai.

Numbern Haydar ya kira ya sanar masa dakin dayake ya sauka acan kafin su juya da safen Amma ya kashe wayar ya kwanta Dan haka baida zabi dole dakin Daya kama din farko ya nufa Yana taba kofar idonta biyu ta tashi zaune cikin tsoro tana kallan kofar kafin t dauki wayarta da sauri ta sake Kiran Haydar taji wayarsa a kashe Dan haka ta Abdul din ta Nemo ta saka Kiransa.

Yana kofar dakin Yana sake knocking yag kiranta a wayarsa ya dauka cikin nutsuwa yace shine ta Bude masa kofar.

Numfashi ta sake cikin rawar da jikinta ya fara dauka ta tsoro ta kashe wayar ta ajiye gefen gadon ta sauko ta nufi kofar ta Bude masa har lokacin hannuwanta rawa sukeyi bugun zuciyarta Bai dawo daidaiba.

Shigowa yayi a gajiye tareda dauke idanuwansa daga kallanta sbd kayan baccin Dake jikinta dogaye masu santsi dasuka Dan lafe jikinta gashi da alama ba bra a jikinta.

Ciki ya wuce Kai tsaye Yana ajiye wayarsa da key din motar Daya dawo da ita ya wuce toilet Kai tsaye Dan Wankan da zai rage masa gajiyansa yake buqata.

Yana tubewa ruwan zafi ya shiga jacuzzi ya sakarwa kansa Yana lumshe idanuwansa dumin ruwan na ratsasa.

Ya jima a ciki kafin ya fito daure da towel a qugunsa Yana goge jikinsa da Wani.

Yana shigewa toilet Husnah Takoma kan gadon ta kwana tareda rufewa tana kokarin riqe zuciyarta Dake harbawa har lokacin dakuma tinani da damuwan yanda zatai rayuwar aure da Abdulhameed qaninta.

Tana Jin fitowarsa bata motsaba idanuwanta na sauka a jikinsa dayake a murde fresh ta rufe idanuwanta ahankali tana jin kaman zata fasa kukan wannan sabuwar kaddarar data sameta duk da Bata regretting Amma dai Kuma batasan tayaya zatai rayuwar ba sedai Kuma idan ta Tina idan har Amatu datake tsararta zata iya aure da hada shimfidar aure da Dad dinta Wanda itama ya Isa haihuwanta to itama zata iya rayuwar auren da hada shimfidar auren da Abdulhameed qaninta Kuma kanin Amatun Dan itama ta dauki cikin qaninta idan ita ta dauki cikin ubanta.

Abdulhameed harya gama shiryawa ya Bude DKNY jakar kayansa ya dauki kayan bacci masu kauri ya Saka ya nufi fridge ya Bude ya dauko Apple Daya yaci yasha drink mara gas ya nufo gadon Kai tsaye ya hau gefenta ya kwanta Yana kashe wutar dakin qamshinta na shiga hancinsa itama nasa na shigar mata hancin a hankali.

Baccin gajiya ne ya daukesa kafin itama daga baya nata ya dauketa,

Cikin dare tayi mafarki me ban tsoro na an raba aurenta da Abdul din an daura mata da uzaifa ya tafi da ita kauye Yanata kokarin Kwanciyar aure da ita tana qin yarda Yana dukanta sosai.

A firgice ta tashi hankalinta tashe jikinta na Wani irin rawa ta fasa kuka tana Neman rikicewa Abdul din dole ya janyota jikinsa ya rungumeta tsamtsam Yana mata adduoi Yana shafa bayanta Yana rarrashinta kaman qaramar yarinya.

Kukan datakeyi na yanda gaba Daya take Neman rasa nutsuwar rayuwa da walwala ne gaba Daya Dan haka ta ringa nanata masa cikin kuka akan kada ya rabu da ita duk wuya duk rintsi.

Share mata hawayenta yayi Yana Bata tabbacin bazai rabun da ita ba inshallah.

Qanqamesa tayi tana cigaba da gangaro da hawaye Shima yana sake share mata Yana son janyeta daga jikin nasa sbd yanda suka manne din Yana damunsa haduwan jikinsu na Neman Sakasa halinda Baya buqatan shiga tin yanzu da daga shi har ita Basu gama fahimtar juna ba.

Kukanta ya Saka dole yabarta a cikin jikin nasa Yana cigaba da rarrashinta cikin kulawa sosai da tattali.

Har tayi bacci tana qanqame dashi Dan haka Shima dole ahakan ya barta sukai baccin Yana sake rufesu da abin rufa.

Koda asuba tayi kusan lattin sallah yayi Saida lokacin sallan ya gota ya tashi ya janyeta daga jikinsa yayo alwala yazo yayi sallah itama ya tadata Tayo alwalan tayi sallah ya zaunar da ita tayi karatun Al’Qur’an sbd ta samu Nutsuwan zuciyarta dayaga alamun ta dade da rasawa gaba Daya.

Sun jima suna karatun kafin suka tashi suka koma bacci sai gashi ta samu baccin ma me nutsuwa da Kwanciyar hankali tareda Jin nauye nauyen dake zuciyarta sun Dan Ragu.

Sai qarfe goma sha Daya suka baro hotel din suka tafi gidansu maamah da aka gama aikin gidan kawai sabbin furnitures da ake sakawa ne ya rage Dan haka fita Abdul din yayi da Haydar yabar Husnah din na gurin maamah,

Mum Aisha kuwa tin jiyan take masifa da fada tsakaninta da Naufal Dayaji aurenta ya ringa tsinewa Husnah data kaisu wannan babban balain da basuda yanda zasuyi Dan shi yanzu baimasan makomarsa ba shikenan ahakan zai zauna Yana Gani Wani tsohon shegen kauye na zuwa gidan wai gurin mahaifiyarsa da sunan mijinta,

Shi ba gwara idan auren zaai mata ba a mayarwa da ubansa ita Kokuma a aura mata Wani a Abujan Amma wainnan mutanen Daya Gani ya dauka mahaukatane suka shigo gidan ace Daya daga cikinsu ne mijin mum dinsa.

Mum Aisha zaginsa ta ringa yi Daya fara zagin ASH tace karya jawo mata wata masifar,tinda anbata gidan zama halak malak da sabuwar motar Hawa ga tsohuwarta hakama an zuba mata komai na Jin dadi ga kudi ma zai ringa Basu ba laifi sun isheta tinda Allah ya tserar da ita daga zuwa kauye ta tuba ta dawo hanya,shi kansa kawu ashirun duk yazo kudi zata ringa basa Yana komawa harta samu ya saki auren batareda ta batawa ASH Rai ba taqi bin umarninsa salin alin zata lallaba lamarin.

*********

Da daddare ASH da Mr Jameel suka iso gidan Farha wannan Karan mr Jameel ne yayi masa iso yai knocking anty Farha datasan sune ta Bude kofar tana masa barka da zuwa tana wucewa qurya tabar musu palon sbd Amatun na zaune palon tana shan watermelon Mai Dan sanyi da aka yanka mata aka zuba condensed milk sosai Akai.

Kayan bacci ne a jikinta black kanta Babu ko hula sai gashinta dake da kalba qananu.

Mr Jameel daman Bai qarasa shigowaba yaja kofar ya rufe ya juya ya koma waje Yana Saka Kiran farha dataqi dauka.

Zaunawa yazo yayi a gefenta Yana kallan abinda take sha batareda ta dauke idanuwanta daga tv datake kalla na tana Shan melon din ta Bude Baki a natse ta gaidasa.

Kasa amsawa yayi sbd wannan rashin kallan nasa datakeyi Yana kashesa Dan haka ya Dora hannunsa kan hannunta datake Shan dashi ya karbi spoon din Yana Bata da kansa Yana tambayarta Yaya jikinta da babyn?

Amsawa tai a taqaice tana qin kallansa har lokacin.

Shiru yayi tsawon mintina Yana ci gaba da bata tana gamawa ta miqe daga Kai bowl din kitchen ta shige dakinta tabarsa zaune ya fito Yana saukowa Mr Jameel ya Bude masa mota kafin Mr Jameel ya tada motar Kai tsaye ASH ya kallesa yace

“Meye matsalan mata ne wai???

Fushinsu Baya sauka ne??

Kaman an ciza Mr Jameel ya juyo cikin rashin sanin mafita yace

“Situation din danake ciki kenan ranka ya Dade ni nawa lamarin yayi nauyi ma”

Shiru ASH din yayi tsawon mintina sbd Jin gaba Daya ta hanasa samun Nutsuwa da Kwanciyar hankali da fushin da Tama qi basa daman ya wanke kansa harta sauko masa.

Ajiyan zuciya ya sauke ahankali tareda Bude motar ya fito Kai tsaye ciki y koma Yana Isa kafin ma ya taba kofar aka Bude ita Karima ce zata zagaya Baya kwaso kayan data shanya kada su Kwana waje.

Da sauri tayi gefe tana gaidasa Bai amsa ba ya wuce ciki kawai.

Kai tsaye dakin Amatun y shiga daidai fitowanta toilet baice komaiba hijabinta ya dauka ya saka mata tana kallansa cikin tsananin mamaki bayan ya gama Saka mata hijabin ta janye daga jikinsa ta Bude Baki zatai magana ya kasa riqe kansa tareda hanata maganar ya kamo fuskarta ya Dora bakinsa kan nata ya kamo harshenta yayi masa wata irin tsotsa me kyau da lafiya kafin ya Ciro bakinsa ahankali yana kallan idanuwanta datake Budewa cikin sanyi can qasan maqoshinsa maganar na fitowa cikin kasala ya furta

“I love you Abeeda AmatulMaleek,

Zakiyi kisa idan Baki Dena wannan fushin ba,

I can’t take it anymore,

M sorry,

Ki yafewa ASH da ASHRAF din duka,

I love you LA,

I love you””””ya qarasa fada Yana mayar da bakinsa cikin nata Yana tsotsewa ahankali cikin sanyi da Sonta Daya kashe masa jiki.

Sanyi qafafunta sukai har suka kasa daukanta ta sake tana Neman faduwa ya tarota dakyau jikinsa tudun cikinta Yana taba cikinsa da matarsa yaji son nata Yana ninkuwan da baimasan kalman da zata iya fadan matsayin abinda yakeji a Ransa game da ita ba Dan ganin yake I love you dinma formality ce kawai Amma Babu kalman dazata iya fadan matsayinta a ransa.

Daukanta yayi gaba Dayanta tareda nufar kofa da ita batareda sanin anty Farha ba ya fice da matarsa daga gidan.

Mr Jameel Dake tsaye Shima Yana tinanin abin yi yaga ASH ya fito dauke da matarsa sakin baki yayi cikeda mamakin kenan ASH yakai qarshen tasa matsalar yabarsa da sauran aiki.

Bude masa motar yayi da sauri ya sake Amatun ya karbi key yace zaija da kansa.

Basa key Mr Jameel Yana masa a sauka lafiya.

Suna barin gurin Shima wayarsa ya fidda take ya kira qanin mahaifinsa ya sanar dashi a shirya gobe aje a nema masa auren Farha ya shirya kawai.

###MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

82

*************

Kallansa ta juyo tayi kadan lokacinda yake driving din sbd Bata taba ganinsa Yana yi da kansa ba hakama ta kasa dawowa daidai daga kalamansa da suka narkar da zuciyarta da jikinta ma gaba Daya.

Hannunsa Daya Yana sarke da nata hannun Daya yake driving har suka Isa Wani lafiyayyar super market yayi ordern manya manyan water melons masu girma aka fito aka Saka masa bayan mota tareda condensed milk kusan cartons biyu tana kallansa Bata kala ba har suka iso Mansion din.

Security Daya ne ya fidda kayan daga bayan motar ya kira su khaltume suka shiga dasu ciki

ASH din kuwa tini ya shige ciki da Amatun hannunsa na riqe da nata.

Su khaltume kuwa Daman kaman jiran tafiyarsu mum Aisha din sukeyi daga gidan Tini aka sake tsarin gidan akai masa gyaran Daya tabbatarda gidan Amatu ne dai komai yayi tsit yaji gyara daga kukan AC a hankali sai qamshi ke tashi koina sai motsin masu aiki a qasa.

Ta palonsa na qasa suka bi suka haye samansa Kai tsaye batareda tabi ta can cikin gidan ba Dan haka su khaltume basuma ganta ba ba Amma dai sunsan ta dawo Dan haka suka hawo da Yan abubuwan da zata iya buqata na abinci suka jere a dining suka fice tareda rufe koina suka koma bangarensu.

Suna shiga palonsa na saman ta nufi kofar datake kaita dinin zuwa palonsu Dan wucewarta tana Jin zuciyarta na sanyi haka kawai tana samun Nutsuwa.

Baice mata komaiba ya kyaleta ta fice ya sauke ajiyan zuciya Shima Yana Jin Nutsuwa da Wani irin sabon feelings suna shigansa na ganin ta dawo gidansa.

Juyawa yayi ya shige bedroom dinsa Kai tsaye wanka ya sake yi Yana fitowa yayi Shirin bacci sbd 11 tayi harta Dan gota.

Kashe wayoyinsa yayi yabarsu a dakin ya fito Kai tsaye bedroom dinta ya nufa bayan ya tsaya dining ya daukan mata ruwan Daya fahimci duk dare tana sha.

Bude dakin yayi ya shiga Kai tsaye tareda rufe kofan ya nufi bedside ya ajiye roban ruwan guda biyu ya ajiye Yana kallan fuskanta da Dan haske kadan Daya rage sbd ta Kai hasken dakin qasa sosai.

Zaunawa yayi ahankali atareda zare slippers dinsa ya hau gadon cikin nutsuwa sbd kada ya tadata daga baccin dayake tinanin tayi Nisa ita Kuma tana jinsa shiru kawai tayi kaman me Jin baccin.

Shigar da ita jikinsa yayi ya rungume ahankali cikin nutsuwa da kulawa Yana Jin cikinta a tsakaninsu feeling din na sake kashesa a koyaushe yaji jikinsa a jikin nata Jin yake kaman ya tabbata a wannan yanayin.

Wata sanyayyan ajiyan zuciya a kasalance suka saki duka su biyun lokacinda kowannensu ya shaqi qamshin Dan uwansa dayayi tsananin kewa zuciyoyinsu na nerkewa ita idanuwanta har hawaye Saida suka ciko dasu sbd allah ne kadai yasan yansa tayi kewan ASHRAF din nata sbd ASH ne yake mata lefi ba Ashraf ba.

Bacci sukai me nutsuwan da rabonsu dashi harsun manta musamman tashe tashen hankalin da akaita shiga da rashi da Akai.

Anan sukai sallan asuba suka sake komawa bacci har kusan 9 na safe yunwa sosai ta tayar da ita ta tashi daga jikinsa ta sauko ta shiga toilet ta sake yin brush ta ziro slippers ta fito sanyeda rigarta da wando na bacci da Dan cikinta qarami a gaba ta sauko qasa sbd tini su Farida suka gama gyara saman suka sake nunna qamshi suka sauka Dan yanzu ko baa fada masu ba sunsan saman idan ba kiransu akaiba suna gama aikinsu shine kan basa qara Hawa.

Ko Daya sauko palon qasan Kai tsaye kitchen ta nufa ta Tararda suna qarasa aikin breakfast dinsu da zaa Kai sama sbd baayi da wuri tinda ansan basayi da wuri din a qaidar Gidan.

Gaisawa tayi dasu tana kallan yi musu sannu da aiki kafin ta Kalli khaltume tace

“Akwai kankana da aka shigo dashi jiya da Madara shi nakeso Yana Ina shi zanci kafin breakfast din.”

Fuska a sake khaltume tace

“Yana store wasu Kuma an Saka a fridge bara a dauko na fridge din,

Yankawa zaayi?

“Eh” tafada tana nufar fridge din ta dauko da kanta Farida ta karba tana wankewa Dan yankawa ta hada mata sbd sunsan yanda takeso tin farkon cikinta bama tareda sunsan ciki ne da ita ba.

Fitowa tayi kitchen din ta zauna Palon qasa tana Dan kallan tv har Farida ta wanke ta yanko mata a bowl tareda tsiyayo mata condensed milk Akai sosai koina.

Karba tayi tareda godewa Faridan ta wuce sama tin a hanya tafara sha tana lumshe idanuwanta sbd tana tsananin son hakan.

Bedroom dinta ta nufa tana shiga ta tarar da Baya dakin ta dauka ya fita sai data zauna tana Shan kankanan ahankali taji Bude kofan toilet dinta ta juyo ahankali ta zuba masa idanuwanta dasuka sakashi zuba mata nasa idanuwan Yana kasa daukewa akanta ya qaraso ya zauna gefenta tareda daukanta ya zaunar a qafafunsa ta Bude bakinta me kankana a ciki a hankali tace

“Good morning”

Wanda ya taba gefen bakinta yafara Kai hannu ya goge mata kaman bayason gogewan kafin ya amsa gaisuwar tata Yana dorawa da cewa

“Yaya?Yaya kikejin jikinki and the baby??

“Lafiya kalau” ta amsa tana nuna masa kankanar da idanuwanta alaman zaisha?

Wani murmushi me kyau da daukan hankali ya sake mata Yana Kai bakinsa kunnenta cikin qaramin sauti yace

“Zansha Amma na cikin bakinki zansha,Zaki ban??

Dagowa tayi tana kallansa Shima ita yake kalla fuskarsu gap data juna suna Jin dumin nimfashin juna na sauka akan fuskokinsu,

“Uhummm?”” Ya sake fada alaman me tace Yana kallanta.

Rasa abin fada tana kallansa sonsa na karya duk jarimta datake tinanin tana da ita ta sharesa.

Dauko Daya tayi da fork takai masa bakinsa tana Hana murmushinta fita sedai ya Riga ya gansa Dan haka tana Kai masa bakinsa ya riqe hannun a tsanake tareda mayarwa bakinta ya Saka mata tana Bude bakin ya Dora nasa Yana qarasawa da kankanar ciki Yana hadawa da ita da harshenta Yana tsotsewa sanyin kankanar da zagin Madara da taste din bakinta suna Basu Wani daddadan yanayi na daban.

Tsotsewa yayai Yana sake matsota jikinsa har suka shanye ta bakin nasu kafin ya sake daukowa ya Saka bakinsa ya kamo fuskarta ya sake hade bakinsu wannan Karan itace ta tsotseta tas tana kashesa gaba Daya tareda tayar da duka tsikar jikinsa musamman data zagayo kansa da hannuwanta tana tsotsansa ahankali ba garagara.

Dagowa tayi tana kallan idanuwansa da suka fara sauya ta Bude Baki a kasalance cikin kunnensa ta furta masa

“Ka koshi?

Girgiza Kai yayi kaman mara laka a jiki Yana sake matsota jikinsa Yana mata Wani Mayen kallo.

Murmushi ta sake ahankali tareda sake dauko wata kankanar ta Saka bakinta ta nufi bakinsa kafin ma ta qarasa ya kamota ya hade bakin nasu Yana shayewa kansa duk yafara kuncewa.

Wuyansa tafara shafawa tana sake rudasa.

Wuyanta yafara kissing ahankali Yana yawo da hannunsa zuwa cikin rigarta yafara shafa cikinta tana lumshe idanuwanta kaman zata sume a gurin sbd saman da yayi da hannunsa Yana Wani irin abun Daya Sakata sakin Wani sanyayyan Nishi me dumi a cikin kunnensa Yana sake kunce masa notikan Kai gaba Daya.

Rigar jikinta ya balle gaba gaba Daya sbd bazai iya tsayawa cire botiran ba.

Cikinta Dake tsakaninsu ya fara zubawa idanuwansa yanajin zuciyarsa na sake mutuwa akansu kafin ya dago idanuwansa ya sauke a kirjinta zuwa wuyanta,

Fatarta da komai nata ya qara Haske sosai suna sake gigitasa.

Zame rigar yayi ya wurgar Yana kai bakinsa wuyanta Yana dora lips dinsa masu sanyi ahankali ahankali har zuwa kirjinta Yana kokarin rabata da numfashinta da abinda yake mata Mai tsananin nutsuwa da sanyi.

Rigar jikinsa Shima ya farke ya zare ya jefar daga zaunen da suke din Yana sake manne kirjinsu take numfashinsa ya kusa daukewa ya Bude idanuwansa dasukai nauyi sun gama sauyawa ya lashi lips dinta Yana  mata shafan dake Sakata sallama masa kanta gaba Daya.

Duk yanda yakai ga kunnuwa Bai manta tana Jin yunwa ne ya Sakata Shan kankanan Dan haka ahakan ya ringa Bata kankanar Yana tsotseta yana rikitasu har sai dasuka shanye Wanda kusan ita ya ringa bawa ta koshi kafin ya zafafa Romance din yana daukanta gaba Daya suka nufi gadonta suna hade bakinsu har suka Isa ya kwantar da ita a gadon.

Sabuwar yanayin daya sake samun kasan a duniyanta ne ya sakashi kusan fasa kunnuwanta da zafafan numfashinsa masu qarfi.

Wani nutsatsiyar Jin dadi da Kwanciyar hankali ya samu tareda sanyayyan love dinta Dana cikinta ya samu,

Kusan cikinta Bai hanasu komaiba duk da farko yanata kiyayewa sbd cikin nata Amma sai gashi Daya rasa control still Babu abinda ya faru din.

Ita kanta ta San ta jigata sosai daurewa kawai tayi Bata nuna dinba sbd ganin nutsuwan da yasamu sosai ya Kuma nuna Hakan.

Wanka sukai sai Daya Bata abinci da kansa a dining taci ta koshi Shima yaci kafin suka sake komawa bacci sbd gajiyan Dake tareda ita da kasala Shima kusan baida Wani buqatan fita koina sbd bayajin zai iya bawa komai hankalinsa.

Sai karfe kusan Daya na Rana ya fito sallah shirye cikin Armanis Navy blue Yana qamshinsa me sanyi fuskarsa fresh da wayarsa Daya a hannunsa wadda ya kunna batareda ya kunna dayarba.

Mr Jameel daman Shima aranar Bai yi gangancin shigowa aiki ba Dan yasan Hutu zasuyi sai Azahar yazo daidai Kuma lokacin ASH ya fito sallah kallo daya sukaiwa juna kowa na fuskewa Dan Shima Mr Jameel ya riqe wutarsa bakin Rai auren ya tashi yi.

Sallah suka fito Mr Jameel ya sanar masa da maganar zuwa Neman aurensa Wanda da ASH din zaa tafi.

Sun Dan jima suna magana da Mr Jameel din kan maganar zuwa Neman auren kafin Kiran Haydar ya shigo wayarsa suka fara magana cikin kulawa da nutsuwa Dan kusan Haydar din komai na Dad dinsa ya dauko.

Bai koma ciki ba Saida ya Dan yi wayoyi har laasar kafin ya shigo tana daki tana waya da anty Farha sanye cikin qaramar Riga mara nauyi ko hannu batada sai qamshinta me sanyi takeyi komai nata kyau yake qarasa masa ya qaraso Yana zama kusa da ita Yana sarqe hannuwansu dole tai sallama da anty Farha din ta aje wayar tana jifansa da kallanta me sanyi zatai magana ya rigata Yana shinshinata zuciyarsa na cika da sanyi yace

“Zamuyi tafiya gobe da safe”

Yanda yake shinshinata din duk ya kashe mata jiki ta zame tana kallansa tace

“Gobe?

Ina?

Bakinta da yayi maganar ya Dan shafa da yatsarsa Yana cewa

“Auren Jameel zamuje nema tinda keda Antynki Kun Hana sa zaman lafiya shi da Maigidansa”

Saka kansa yayi cikin wuyanta ya Saka shakan kamshinta Yana cigaba da cewa

“Me kikaso yiwa ASH ne?

Kinso kiyi kisa ne?

Kinsa me kikai kuwa?

Murmushi kawai tayi batareda ta juyo ta kallesaba sbd yanda yake matan dariya da waiwayi abin yake Sakata dariyar datake riqewa ne ya fito mata tana ce masa

“Please stop”

Kasa dainawa yayi sai Dayaga dariyan ya mata yawa kafin ya saketa Yana cewa ta shirya goben tare zasu tafi Lagos din.

##MAMUH#

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

83

************

Su kadai suka wuni a gidan hankali kwance Yana juyata yanda yakeso suna zuba soyayyansu abincin ma kusan duk a shiririce suke cinsa har lokacin bacci yayi sukai wanka yamata Shirin bacci suka kwanta.

Bai mata komaiba sai bayan sallan asuba suka zuba lafiyayyar soyayyarsu Yana Jin gaba daya baisan ta ina zai fara iya rayuwa idan tana fushi dashi.

Da safe dole da wuri suka shirya sbd tafiyar suka bi jirgi suka wuce bayan ta fadawa anty Farha komai sun jima suna magana.

Harda Mr Jameel din sukai tafiyar shiyasa suna Isa Basu Wani Bata Lokaci ba Saida ya tabbata taci abinci tayi wanka ta kwanta baccin Hutu kafin ya Hadu da qanin mahaifin Mr Jameel din suka tafi Neman auren.

Se yamma ya dawo wanka yayi shima ya huta suka zauna fira tana basa abinci Yanaci sama sama sbd wayan dayake amsawa.

Da daddare fita sukai acan suka ci abinci Wani lafiyayyar restaurant taci abubuwa kala kala datake so sbd shi drink kawai ya sha Amma Saida suka kashe kudinta zai ciyarda Wani gidan Taron na tsawon sati nawa a gurin ciye ciyen nata kawai.

Se dare sosai suka dawo wanka sukai suka kwanta bacci me dadi take ya daukesu sbd zazzafan love din da sukai making me sanyi da nutsuwa cikin so me qarfin dayake zuciyar kowannensu.

Washe gari anty farha ta iso Lagos din sbd Yan uwa da iyaye daketa murna da farin cikin itama lokacin nata auren yazo bayan ta jima din batai aure ba.

*****Ranar da su Amatu suka wuce Lagos a ranar su Haydar suka dawo Daman Kuma yayi magana da Dad dinsa zasu tafi porthcrt da Husnah kafin wucewansu Dan haka kwana Daya sukai Suma suka wuce porthcrt din shi da Husnah sbd acan zaayi hidiman bikin aurenta da anriga an daura.

Suna Isa aka fara Shirin Biki duk da iya walima da Salalle za’ai mata da Kuma gyaran Amare tinda dai an daura auren to dole suyi mata hidiman da akewa kowacce Amarya.

Abdulhameed Bai dawo ba Yana Yola tareda maamah wadda gidanta yake daban Dana mum Aisha sbd an rabasu kowa da gate dinta daban Kuma kowa sama da qasa ne tsarin nata gidan hatta me aiki kowannensu nada daddaya da me gadi so babu Wadda ke cikin tashin hankali da masifar da suka hangowa kansu farko ga abinci da komai an zuba musu.

A waya sukaji Amatu suna Lagos maamah naji tayi kaman bataji ba sbd Jin lamarin banbarakwai haka suka gama magana a wayar sukai sallan tana yiwa farha fatan alkhairi tareda cewa zata kirata tai mata barka din.

A porthcrt ba hidima sosai akaiba bayan Salalle da waliman akaita mata nasiha da fadan kwantar da hankali kada ta sake hargitse rayuwarta ta nutsu ta gyara mu’amalarta da Dad dinta hakama ta nutsu ta sake Dora rayuwarta kan tirba me kyau.

Gyara ake mata sosai Wanda ya sauyata ciki da wajenta kaman ba ita ba duk da ta rame sosai sbd damuwa da sanyi datai.

Haydar kuwa Daman ya Dade baizo cikin dangin mum din tasu ba Dan haka ya saki jiki Yana shiga cikinsu sosai.

Kwanansu bakwai a garin suka fara Shirye shiryen dawowa Amma Haydar yace ba yanzu zai koma ba Dan haka dole Abdulhameed da kansa yazo porthcrt din kwanansa Daya ya gaisa da family sosai suka juya tareda Husnah din zuwa Abuja.

Koda suka koma Bata dauka Amatu da Dad dinta basa Nan ba da bazata dawo ba sbd kadaici na Bata tsoro ga Dad dinta duk Kiran datake masa suna gaisawa batasan Baya Abuja Dan Saida su mummyn porthcrt Suka kirasa aka basa hakuri ya sauko daga fushinsa akanta Dan Daman tana cikin ransa a kwanakin yasan tana cikin damuwa.

Su khaltume cikin murna da farin ciki suka tarbeta suna mata sannu da zuwa sune sukai sama da kayanta kafin ta Abdul yahau sama da ita hannunta na riqe cikin nasa har bedroom dinta kafin ya fice zuwa nasu dakin.

Wanka yayi ya fito zuwa masallaci sallah cikin qananun kaya

Itama wanka tayi tai sallah ta Saka kaya marasa nauyi ta kunna wayarta tana waya da mutanen porthcrt daketa kira suna mata barka da sauka.

Sai da yayi sallan ishai ya shigo gidan abincinsu a dining room din palon kasa aka Jere musu Yana zaunawa ya kirata a waya ta fito cin abinci.

Saukowa Tayi jikinta duk a sanyaye da fargaban yanda zata kwana cikin. Mansion din ita Daya duka masu aiki suna bangarensu Shima Yana nasu bangaren.

Kallo daya yayi mata tana saukowa ya dauke kallansa daga gurin yana takaita wayar dayake yi da Amatu sbd kayan jikinta Sam basuda nauyi doguwar Riga ce pencil ta lafe jikinta sai hula Dake kanta.

Tana zuwa zaunawa tayi tana kallansa ta gaidasa kaman yanda aka ce mata a porthcrt.

Da Dan mamaki ya zuba mata kyakkyawan idanuwansa ya Kalli fuskarta tukuna ya amsa Yana dorawa da tambayar Yaya dai ya ganta kaman da damuwa.

Numfashi ta sauke tana cewa bazata iya kwana a gidan ba ita tsoro takeji ya kaita gidan anty Farha kawai zata kwana acan itama.

Cikin sabon mamaki yace

“Anty Farha din Bata Nan itama tana Lagos sbd hidiman aurenta ne yasaka su Amatun tafiyan ai”

Shiru tayi tana zuba abincin tana rasa abin yi.

Har suka gama zaman cin abincin Babu Me magana Saida ya gama ya miqe yana kokarin barin gurin ta Bude Baki tace

“Zaka fita ne?

Juyawa yayi ya kalleta Yana fasa Saka Kiran da zaiyi yace

“Akwai Wani abin ne?

Akwai abinda kike buqata ne?

Numfashi ta sauke ahankali tareda girgiza Kai kawai.

Ficewa yayi

 itama kasa qarasa cin abincin tai tana barin dining din.

Tana zuwa daki brush kawai tayi tai Shirin bacci ta kwanta a takure.

Duk yanda taso bacci cikin Daren kasawa tayi Dan haka Koda asuba tayi kanta tsananin ciwo yakeyi ko abinci Bata iya fitowa ci ba Shima da safe fita yayi Bai dawo ba Se yamma.

A daki ta wuni sama sama kan ke damunta harma da zazzabi,

Bata bari yasan Halinda take ciki ba haka ta sake kwana cikin yanayin damuwa da ciwon Kai

Koda gari ya sake wayewa zazzabinta yayi karfi Dan haka dole yasan Halinda take ciki ya tafi da ita dakinsa ta kwana acan Yana kulawa da ita har safe.

Da safe shiryawa sukai yakaita Taga likita ba Wani matsala bane kawai ciwon Kai da zazzabi.

A cikin gidan haka ya ringa kulawa da ita cikin kwanakin yana tattalinta harta warware amma Bata dena kwana a dakin nasa ba Dan haka ya fara janyewa daga gareta sbd yanda lamarin ke kokarin tabasa sosai Dan ita Sam Bata Wani damu ko Tina yawan haduwan jikinsu da yanda take shigarta ta bacci yanda ta Saba zai iya tabasa ko Wani abin ba daban.

Ita Kuma ganin ya fara janye mata sai duk tafara Dan shiga damuwa sbd rashin sanin abinda yafaru.

Shikuwa sosai ya sake janye mata Dan yaga zata iya Sakasa mawuyacin hali Dan haka har baccin ma da daddare sai ya Dena kwanciya gado Daya da ita gari na wayewa zai bar gidan Baya dawowa Se dare sosai.

Rikicewa tayi da wannan sauyin Dan alamunsa sosai sun nuna itace din bayason tana rabarsa Dan haka ta ranar wata talata ta zauna ta ringa kuka sbd rashin sanin wane abin tayi Shima Daya gaji da ita harya Yana janye mata.

Ko Daya dawo da daddare tayi Shirin baccinta tana zaune tsakiyar gadon tayi kuka har idanuwanta sun sauya sosai Dan haka dole bayan yayi Shirin bacci ya zauna gefenta tareda kallanta zaiyi magana hawaye suka gangaro daga idanuwanta sbd shi kadai take dashi a yanzu da Dad dinta da Haydar basa Nan Amma Ya janye mata kwata kwata ko inda take bayason raba.

Tissue ya janyo Yana share mata hawayenta cikin kulawa yace ta Dena kukan ya Isa hakanan.

Rarrashinta yahau yi dole harda Dan janyota jikinsa Yana sake rarrashin nata harta Dena kuka ta lafe jikin nasa tana yar nutsuwa na dawo mata.

Dole ya sake mata Yana tarairayarta har tayi bacci a jikinsa tana lafe harda qanqamesa.

Hakanan ya daure Shima yayi bacci Rabi da Rabi sbd uwar haduwan dasukai dakyau har safe.

Washe gari duk yanda yaso kame kansa daga gareta Hakan Bai samu ba sbd zazzabin ciwon kan data tashi dashi haka ya lalace gurin kulawa da ita,.

Abinda Bata saniba shine yanda take shiga jikinsa sosai yayi masa illan da ita kanta bazata so ya kasa riqe kansa ba,

Da daddaren ranar haka ta jiqa masa aiki gaba Daya ya kasa riqe kansa yayi mata kyakkyawar runguma Yana kama fuskanta cikin sanyi ya hade bakinsa da nata ya mata wani irin kiss me sanyi Yana qanqameta jikinsa.

Qwacewa take kokari yi Amma yanda yake kissing din nata cikin sanyi Yana zagayota gaba Daya tared qanqameta jikinsa ya Sakata kasa kwacewa Se hawayen Dake ciko idanuwanta suna gangarowa.

A daren duk yanda taso qwatan kanta daga gurinsa Bata iyaba haka tanaji tana Gani ya mayar da ita cikakkiyar matarsa halak malak,

Taci wuya taci azaba me tsanani sbd qarfin samartaka dake tareda sosai gashi da maji karfin namiji,

Shi kansa yasan Tasha wuyan dan Saida suka tafi asibiti sai gata harda Dan stitches.

Bayan sun dawo shi da khaltume ne sukai ta aikin kulawa da ita Yana tarairayarta kaman sabuwar babyn da aka Haifa ranar,

Dayake Allah yayita me shegen raki haka ta ringa kuka damuwa kala kala a ranta harta warke ya bita da kulawa da tarairaya ya sake maidata tasa cikin sanyi.

Da farko ta shiga damuwan zamansu Daya din Amma ahankali da yanda ya ringa binta kwana biyu Yana tattali da kulawa Saita cire damuwan.

Sati biyu da kwanaki suka share suna cikin yanayin amarcinsu kafin Haydar ya fara dawowa Dan haka ta koma dakinta ya rabasu bayan sun fara sabo da Kwanciyansu cikin nutsuwa da tattali harma da soyayyarta Daya fara shigarsa me tsafta.

Kwanan Haydar hudu da dawowa su ASH suka dawo Suma bayan uban sabuwar rayuwar dasuka Bude a Lagos suna bazawa.

Dawowansu Husnah ta sake bawa Dad din hakuri ya hakura hakama Abdul ya shiryata da Amatu da kansa sbd bazaiso matarsa da yar uwarsa basa shiri ba.

Bayan dawowansu Dad dinta Husnah naji tana Gani Takoma zaman daki sbd rayuwar da idanuwanta ke Gani saikuma idan Abdul ya dauketa sun fita sbd kusan sune rage cin abinci sosai a gida guraren hutawa suke zuwa matsu tsada suci su dawo.

Dawowansu ASH da sati uku su Haydar da Abdulhameed din suka koma Banda Husnah sbd visan ta Bai samu ba sai daga baya zata bisu.

Kaman karsu rabu harda kukanta sbd yagama sauya mata rayuwa gaba Daya da kulawa da tattalinsa Dan haka bayan tafiyarsu koyaushe suna kan waya.

Bayan tafiyarsu da wata biyu Ciwon laulayi ya bayyana a jikinta take kunyar bayyanarsa ya Sakata shiga damuwa ta fadawa Amatun suka ringa boyewa ASH sbd batason ya sani sai ta tafi.

Tattarawa tayi bayan da cikin yafara kokarin bayyana ta koma Yola gurin maamah daga can visanta ya fito ta dawo ta tattara ta tafi Daman mijinta a matse yake da ganinta da cikin nasa Daya Riga ya sani Dan ta sanar masa.

Haydar mamakinsu hanasa magana yayi Saida murnar cikin dayayi sbd ganin Husnah din ta zama daidai a rayuwarta.

AMATULMALEEK ta haifi baby boy dinta lafiyayye ranar da aka gama bikin anty Farha kenan,

Allah yasa maamah tazo bikin hakama mum Aisha ta samu halartowa sbd Neman yawo takeyi ido rufe,

Dayake a Lagos Akai bikin acan ta haihu dole aka fasa tarewan Farha ranar sai washe gari suka tattaro suka dawo Abuja da amarya anty Farha.

Farin cikin the grt ASH TALBA da mr Jameel kusan bazai fadu b sbd kowannensu lokaci ne farin cikin rayuwarsu Dan haka Suka tafi hutun aikinsu gaba Daya.

Mr Jameel sabuwar rayuwar Kwanciyar hankali ya Bude da amaryarsa Farha gashi suna cikin double farin ciki Dana haihuwar masoyansu wato ASH da AmatulMaleek.

Maamah hakanan ta zauna ita da mum Aisha har Akai suna baby yaci sunan FAROUK ASH TALBA da sati Daya kafin suka koma Yola din gaba Daya harda Amatun sbd ASH din zaiyi tafiya Shima a satin.

Bayan tafiyarsu Yola da kwana biyu ya wuce Cyprus.

Zaman haihuwanta a Yola na gata da kulawa sosai ne daga maamah hakama mota biyu daga kauye kusan Rabin Yan gidan suka zo ganin farouk harda ganin matar kawu ashiru da baa taba Gani ba.

Maamah sosai ta kula da gyaranta har tayi arbain da sati biyu tukuna ASH ya dawo Basu Wani zauna ba suka koma sbd aikinsa kusan shekara zeyi acan Bai kammala ba gashi dole Baya iyawa seda Mr Jameel Dan haka mr Jameel tini ya samarwa matarsa visa suka wuce Koda Amatu ta Isa anty Farha farin cikin ganinta kaman me.

Sabuwar babin rayuwar Jin dadi suka Bude abinsu hankali kwance daga su sai babynsu saisu anty Farha da itama cikin ne da ita qarami.

Husnah na haihuwan baby boy itama mamaki ya kusan daure kan ASH da baisan ‘yarsa nada ciki ba Dan haka da kansa suka tafi UK din taredasu Amatu ganin baby wanda Husnah harda kuka shagwaban kunya ta ringa wa Dad din Daya bayyanarda mamakinsa.

Abdulhameed kuwa hankalinsa kwance murna da farin cikin zamowa Uba kawai yakeyi ga Haydar ma yayi murnar ganin qaninsa da kusan Shima kamanninsa Dana Dad din yayo.

Maamah ce kawai ta samu zuwa sbd kulawa da Husnah din sai mummyn porthcrt da itama tazo baby yaci sunan ASHRAF little.

Ana 2 weeks ASH da Amatu suka koma.

#MAMUH#

ALHMDLH!!

PLEASE KADA KUCE BAI KAMATA A GAMA BA YANZU KOKUMA YAKAMATA A QARA MUKU TSAWONSA SBD BABU SAURAN ABINDA YA RAGE A RUBUTA IDAN BA NISHADINSA ZAMU RAGE BA,

ABINDA NA MANTA BAN SAKA BA KO BAN WARWAREBA KOKUMA NA RUBUTA BA DAIDAI BA PLEASE AMUN UZURI SBD AJIZANSI,

ALLAH YA YAFE BARNAR DA MUKA AIKATA A CIKI YA BAMU LADAN NA KHAIRIN.

GODIA MARA ADADI GA DUKA WAINDA SUKA BIBIYA LABARIN AMATULMALEEK DAGA FARKONSA HAR QARSHENSA,

NAGODE SOSAI SOSAI.

ALLAH YABAR KAUNA.

SAI MUN HADU A NEXT BADA DADEWA WANDA INSHALLAH INA MUKI ALBISHIR DIN ZA ZAIFI WANNAN TAKO WANE SIGA INSHALLAH.

YAN BATI KUMA SANNUNKU DA KOKARIN BIBIYA DA KUMA ZAGI.

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

Series Navigation<< Amatulmaleek Chapter 4Amatulmalik Chapter 5 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *