Amatulmalik Chapter 5

Amatulmalik Chapter 5

This entry is part 6 of 6 in the series Amatulmalik na Mamuhgee

5

Abeedan bazata iya daukanta ba Dan haka dole masu aikin ne suka dauki AmatulMaleek din maamah Kuma tana dauke da jakarsu suka dunguma zuwa ciki.

Kai tsaye sashen masu aiki aka nufa dasu dayake akwai daki na musamman acan aka Bade musu Daya aka kwantar da AmatulMaleek din gefen Abdulhameed Daya farfado shi Amma baida karfin iya motsawa sai tsoro Mai karfin gaske Daya shigesa ganin inda suke kaman baa duniya ba duk da baisan yanda aljanna take ba da lahirar.

Abeeda da kanta ta fice tana bawa masu aikin umarnin su fara yaran kafin a kirawo likita yazo ya dubasu cikin gaggawa.

Abdulhameed suka fara yiwa wanka fes suka dirji uwar dauda da kurar jikinsa kafin suka fito dashi.

AmatulMaleek kuwa kasa barinsu maamah tayi da kanta ta daure ta wanketa tsaf ta fito da ita.

Kaya aka Basu suka Saka Wanda AmatulMaleek din take aka karbo kayan Husnah Talba daga bangaren iyayen gidan aka Bata maamah ta Saka mata hakama Abdulhameed kayan haidar aka Saka masa take suka Dan yi kyan Gani Babu Bata lokaci likita tazo ta fara dubasu Duk da shi Abdulhameed ana basa tea me tsananin kaurin gaske ya shanye katan Kofi yafara Dan samun kuzari.

AmatulMaleek kuwa ana Bata tea din haka ta amayosa Dan haka dole aka sake gyarata kafin likitar tazo.

Ita kanta maamah ta tsaftace kanta cikin ‘yar suturar da aka Bata Dan baayi qasa a gwiwar Kai kayansu store ba aka ajiye sbd Babu Wani sutirar arziki acikinsa.

Da farko sosai hankalin Abeeda ya tashi da ciwon na yaran Dan Bata dauka yunwa da wahala ne tareda iska Dasuka wuni suna sha a hanya ba tin asuba ya jijjigasu gaba Daya.

Likita Abdulhameed ta yara dubawa dakyau ya tabbatarda gajiya ce da azabar yunwa a tareda shi Dan haka ruwa kawai ya daura masa Dan karfinsa Daya tafi ya Dawo.

AmatulMaleek kuwa bayan yunwa iskane ya shigeta sosai Wanda Bata Saba sha ba sbd basa zuwa koina koyaushe suna kauye cikin gida a zaune,Se yunwa da wahalar hanya ta doguwar tafiyar da tinda tayi wayo Bata taba ba.

Itama ruwan ya daura mata tareda allura kafin ya tafi yace basa buqatan magani da sun samu hutawa sosai sukaci abinci wadatacce zasu warware Inshallah.

Sai bayan tafiyar likita Maamah ta iya dagowa ta Kalli Abeeda datafi nuna damuwarta akan ciwon nasu sbd Bata taba ganinsu a wannan halinba bayan ciwo ga wahalalliyar yunwa Nan a tareda su bayyane a jikinsu.

Kan maamah ta dawo da kallanta tareda qurawa Maamah din idanuwanta tana sake kallan qashin wuyanta Da kamar turosa Akai waje duk koina jikinta qasusuwanta a bayyane,

Jin tayi hankalinta ya ninka tashi tareda shiga tsoro Amma tayi kokarin dannewa tareda boyewa sbd kada ta muzanta Maamah din da kallanta dakuma mamakin.

Fitowa tayi maamah na biyeda ita kaman yanda ta umarta suka nufi sashenta sai alokacin maamah ta Dan saki numfashi sbd sanyin AC Daya gama kame koina na sashen da Wani irin kamshi na gidan kudi da basai anfada Maka ma.

A palonta na farko ta zauna ahankali kan kujera tana nunawa Maamah gurin zama tareda sakawa aka kira me aikinta ta kusanta.

Khaltume na zuwa ta Dan tsaya daga gefen Abeedan cikin girmamawa tace gata tazo.

Abeeda Dake kokarin dauke kallanta daga Maamah sbd kallan yafara damunta da alama ta Dan juyo ta kalli khaltumen Kai tsaye tace a hadawa Maamah abinci a dining.

Dawo da kallanta tai kan Maamah din cikin yar kulawa tace

“Asmau meye kikeson ci??

Me zaa dafa Miki kici a cikin gaggawa?

Dan dagowa Maamah tayi tana kokarin Hana damuwa da sanyinta bayyana ta saki Dan numfashi tareda yaqe ta Bude Baki tace

“Kowanne irin abincin ma yayi basai sun wahala ba”

Juyawa khaltume tayi da kallanta kan Madame dinsu tana jiran umarnin abinda zaayi din.

Abeeda Bata juyoba ta kalleta tace

“Kije koma me Akai a ajiye mata ta taso taci batareda Bata lokaci ba.”

Murmushin yaqe Maamah ta sauke tana dagowa ta zubawa Abeedan Idanuwanta cikin kulawa da ganin yanda itama Abeedan ta fada sosai tayi Wani irin haske kamar na Wanda beda jini ko kadan.

Numfashi ta sauke kafin ta Bude Baki cikin kulawa tace

“Abeeda Yaya muka sameku?

Yaya Husnah da Haydar?

Duk suna lafiya?

Yaya labarin su hajiyar porthcrt?kowa lafiya dai ko?

Numfashi Abeeda ta sauke kawai fuskar Asmau take kalla wadda magana takeyi Amma bakin dayake bushe da wuyanta ne suke kashe mata jiki Dan haka Bata iya Bude Baki sosaiba ta gyada Kai ahankali cikin sanyi tace

“Kowa lafiyansa kalau,

Asmau meya sameku haka keda yaran kuka koma kamar wainda ke rufe a kejin wahala?

Meyake faruwa ne?

Kuma cikin qunci da wahala ne?

Bakwa samun abinci ne?

Andena Kai Miki abincin da ASH yasa aringa kaiwa duk wata ne?

Shiru Maamah tayi tareda Dan sake sakin murmushin yaqe tana cewa

“Ana kaiwa kinsan gidan taro dakuma rayuwar kauye baka samun abu ka ringa cinyewa Kai Daya Se iyalinka,Idan ankai ana bawa kowa ya  Dan Saka albarka,Allah dai yaci gaba da biyanki keda Mijinki har karshen rayuwarku,ai Kunata kokari….

Katseta Abeeda tayi da cewa

“Asmau bayan yunwa wane masifar kuke ciki haka da kika koma kaman wadda take kwance tana jinya??

Asmau Kin ganki kuwa?

Kinga ‘yayanki kuwa?

Sake sauke numfashi maamah tayi tana Dan son Hana kanta da zuciyarta bayyanarda abinda zai damar da Abeedan Dan haka ta sauya tambayar ta Abeeda da jefa mata tata tambayar idanuwanta akan Abeedan tana cewa

“Yaya maigida ASH TALBA? Yana lafiya?

Yakuma akaji da hakurin rashin Alhajin??

Numfashi itama Abeedan ta saki sbd sanin zurfin ciki da iya shanye damuwa da duk abinda ya wuce na Asmau Dan haka tasan ba komai zata fada mata ba ayanzu din sai kawai tayi Baya ahankali ta gyara zamanta a lallausan Luxury kujeran Dake palon nata tana cewa

“ASH lafiyansa kalau yau da safen Nan yayi tafiya Dan Daman rasuwar Nan ta tsayar dashi,

Alhaji kuwa lokacin yayi Se fatan Allah yayi masa Rahama da samun Jin qansa.

Shiru sukai dukkaninsu kowanne zuciyarsa a sanyaye Banda Abeeda Dake jin bazata iya fadawa Asmaun damuwarta datai niyaba a duk randa suka Hadu sbd Bata taba tinanin ganinta a wannan mummunan halin itada yayantaba kamar wasu gawar dataqi Rami.

Ita Kuma maamah Jin tayi itama jikinta na sanyi tareda Jin nauyin fadawa Abeedan damuwarta sbd kada ta damu sosai gashi da alama Sam rayuwarta da alama batasan meye ma damuwaba Dan haka bazata lalata mata komaiba da tata damuwar zasuyi kwana biyinsu su koma salin alin zata bar damuwarta a cikinta ta duqufa da yiwa yayanta addua.

Abincin da akace a jera mata khaltume ta gama jerawa ta matso ta sanar musu angama jerawa.

Kallan maamah Abeeda tayi tace mata taje taci abinci tukuna.

Miqewa maamah tayi ta nufi inda abincin yake a Jere cike da table din da tasan zamansa yafi karfinta Dan haka sai kawai ta Kalli khaltume Dake ajiye kulan farfesun qaton catfish akan dining cikin nutsuwa da mutintawa tace bazata iya cin abincin anan ba akaita kitchen ko can dakin da aka saukesu taci.

Abeeda Dake waya cikin nutsuwa da Wani irin sanyi na Wanda Hutu kawai ya sani batasan me suke fada ba har khaltume din ta fita da Maamah din suka dauki kayan suka fito dasu har zuwa sashen masu aikin.

A lokacin AmatulMaleek tayi bacci hakama Abdulhameed Amma shi suna shigowa dakin ya Farka Yana ganin maamah din ya tashi zaune Yana kallanta tareda matar Dake bayanta Yana Jin son komawa gida gaba Daya na shigarsa.

Ajiye kayan sukai a qasa gefen Dan madaidacin gadon Dake dakin tayiwa khaltume data juya zata fice Godia sosai cikin Nutsuwa.

Bayan ajiye kayan da ficewar khaltume kallan Abdulhameed maamah tayi tana qarasowa gadon dayake kwance shida AmatulMaleek ta miqa hannu ta fara taba AmatulMaleek taji jikinta zafin Kai a sauka sosai ba laifi take ta sauke ajiyan zuciya me sanyi kafin ta Maida kallanta na Abdulhameed Shima ta tabasa taji ba zafi Sam Kwata kwata a nasa jikin Dan haka ta kamosa ya sauko gadon Yana kallan kayan abincin Dake ajiye kasa Yana cewa

“Maamah yaushe zamu koma gida?”

Zaunar dashi tafara yi a qasa kafin itama ta zauna tana cewa

“Kwana biyu zamu insha Allah mu koma,

Kaci abincin dai tukuna kafin Amatu ta tashi itama taci.”

Doya da dankalin turawa ne da aka cakudasa da kwai dasu pepper sai kamshin spices yakeyi.

Wani mugun yawu me kaurin gaske Abdulhameed din ya hadiye harda ita Maamah din Amma dayake sunada dangana sai jikinsu Bai Wani dauki rawa ba.

A natse ta zuba musu kafin ta sake Bude dayar kulan sukai arba da farfesun kifin Shima ta zuba musu duk a cikin guri Daya sbd kada su Bata plates din dasuke qal tasan Se sunyi tsada,

abinda ma ita Bata saniba shine ko spoon da matar gidan take amfani dashi baa bari Koda wasa yazo bangaren masu bare kayan abincinta Wanda wainnan din daga yau sun tashi daga kayan cin abincin madame Abeeda sedai Kuma a ajiyesu Dan baqin da basuda wani mahimmanci,

Shi oga kwata kwata kuwa Sam bama kowa ke taba kayan da ake masa amfani dasu ba sbd Wani irin qyanqyaminsa da tsaftarsa data Baci tayi yawanda idan Yana gari aikinsa na musamman ne da ake taka tsantsan da kiyayewa dashi.

Abdulhameed duk da Yana cikin kulaficin son komawa gida a take harma da tsoron inda yaga sunzo din  Amma sosai ya saki cikinsa ya ringa cin cimar da Bai taba cinta arayuwarsa ba Dan kuwa baitaba ganin ko dankalin turawa da idanuwansa ba bare ci hakama doya har gwara kifi suna Gani a masu siyarwa na kauyensu da masu zuwa ruwa su kamo.

Dadin dahuwar wadda take ta musamman Dan kuwa duka masu aikin gidan wainda suke da karatu akan aikinsu ake dauka Dan haka masu girkinsu komai nasu kamar a 5star restaurants kake,

Hakama masu aikin tsafatace gidan Suma kusan sai wainda suka samu training me kyau ake dauka sbd kusan gaba Daya rayuwar taurawan datake cikin ASH TALBA tagama kama iyalinsa da kusan gidan komai a daki daki akeyinsa kan tsari da rashin tarkacen da zai damesa.

Ita kanta maamah taci abincin sosai ba laifi suka sha Wani homemade drink da ko zaa kulla musu bomb ya watse dasu basusan dame dame acikinsa duk da fruits ne zalla Amma dai Sam basusan meye shi din ba sudai sunci Kuma sun koshi.

Suna gamawa ta rabe kayan gefe sbd na Amatu da suka rage Mata.

Toilet dayake dakin suka shiga

Dayake ta iya amfani duk da irin wainnan abubuwan sbd tasowa gidan masu arziki Dan haka Bata manta yanda ake amfani da wasu abubuwan ba da yawa.

Wanke musu hannuwansu tayi nata Dana Abdulhameed daketa lashe hannun.

Sabulun tasaka ta wanke masa hannu da kyau itama ta wanke nata kafin ta goge musu bakinsu suka fito tana ce masa ya koma yayi bacci kafin azahar ta qarasa yi ya sake warwarewa.

Hayewa yayi gadon Yana cewa

“To Amma bazaki fita koina ki barmu anan ba ko?

“Babu inda zani Ina Nan zaune harku tashi Nima Dan rintsawa zanyi kafin lokacin yayi.”

Yana Jin Hakan ya sauko daga gadon Yana cewa

“To zan kwanta a gurinki”

*_AMATULMALEEK_*

By Mamuhgee

AMATULMALEEK

Mamuhgee

#ZafafaBiyar

Join our WhatsApp group here

Series Navigation<< Amatulmaleek Chapter 6
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *