Fadwaah Part 2

This entry is part 2 of 3 in the series Fadwaah by Asmy B Aliyu

FADWAAH

ASMY B ALIYU
Free book

2…
Tozali tayi da Mami wadda ke tsaye jikin kofa murmushi dauke a fuskarta rungume Mami tayi ta saki ihun murna,
Wayyo ddi!Mami sannu da zuwa Mami ina kika baromin sahlaah ?fadwaah ta qarasa mganar gamida bin bayan mamin da kallo matashin saurayine Wanda ba zai wuce shekaru talatin da hu’du da biyar ba a dunia.kallo daya zakayi masa , zakasan matashi ne mai Jida kansa wurin kyau haka ga kudi sun zauna ta koina ,da sauri fadwaah ta dauke kanta akansa cikin ranta take fadin yana da kyau !Amma yyi kato da yawa ko ina jikinsa a murde.to ina Mami ta samu wannan baturen?bata taɓa ganin sa gidan Mami ba.mom ce ta harareta ,baxaki gaisheda yayan ki Abhi ba ?Dan fiddo ido  waje  tayi gamida dafe kirjinta haka tana fuskantar abhi take faɗin Am sorry mom ban dauka shi bane amma mom yafi su sahlaaa kyau .”ta faɗa gamida sakin daria a hnkali haka lokaci ɗaya Abhi yaji ta riqo hannunsa binta kurum yakeyi da ido ,qoqarin zare hannunta yakeyi cikin nasa. Yaga Mami na qallonsa a hankali fadwaah ta shiga Jan sa cikin falon ,haka tana zuba masa surutu yah Abhi kana da kyau?”wani ya taɓa faɗa maka haka kuwa?”
“Dan Allah Mami ce ta haifeka da gaske ,tayi maganar cikin muryar rada zama yayi batareda yayi magana ba ,
ga mamàkin sa sai yaga ta zauna gaf dashi tana kallon (quarter million )din da ya kewaye nan qaramin bakinsa mai dauke da red lips, hnnun ta tàkai a wurin inason wannan abun !Amma Areef dina baya dashi ,plsss fadamin me zai Shafa ya fito masa kibari idan muka tashi tafia zan dauko maki  A mota ae kina so ko?”woww muryarka so cwt.
Murmushi ta saki gamida haɗe hannayenta wuri daya haka ta saka su acikin cinyoyinta ,take fadin ina so mana.”ta qarasa maganar cike da tsantsan yarinta ,mom ce ta katseta kinxo kin wani tsaresa   da shegen surutu ko ruwan sha baki kawo masa ba,mikewa tayi tsaye tana fadin am sorry yah Abhi bara na kawo maka lemu da gudu ta nufi kitchen ,yayinda mom ta zauna gefensa tana tambayar sa ya aeki ya kuma ya baro azeezah? Cike da kunya yake fadin lfy qlau take Mom tana gaisheki…..cike da fara’a mom ke fa’din ina amsawa tana Abuja?
Ko tare ku kazo?Dan Sosa qansa yyi tare mukaxo mom,masha allahu!
Haka fadwaah ta cika gabansa,da kayan  ciye-ciye Mami da mom na acan gefe suna ka’llo su  kansa yana a kasa ko kallonta baiyi ba ,lokaci ɗaya yaji an warce wyar binta yayi da ido ,ka zauna kaci abinci mana !kai baka magana irin Yah Aliyu plsss kayi magana da daria kamar yadda yakeyi ta faɗa gamida miqa masa juice a cup glass haka ta wani hade rai Amsar cup din yayi zama tayi a gefensa gamida bin wayar da ido pic dinsa dake gaban wayar take ka’llo yana sanye da kakin police yayi masifar kyau acikin su murmushi dauke a fusakarsa.qallonsa tayi gamida qallon pic din .”kai!
dama kai Dan sanda ne?
Tayi maganar cikin fuskar damuwa ,tsaki Abhi yayi aransa yaji yagaji  da surutun wannan yarinyar ,
Kwace wayarsa yayi haka ya haɗe rai cikin sanyin murya yake fadin idan baki rage wannan surutun naki ba!…..baxamu shirya ba ,haka baxamu zama friend’s ba bana friend da mutum Wanda ya fiye surutu ,
da sauri ta kama bakinta wallahi na daina!
Plsss karkace baxamu zama friend’s ba ,ta qarasa maganar cikin fuskar tausayi.

murmushi Abhi yyi gamida miqa mata sauran lemun da yasha to amsa kisha naji.”

bata qarbi lemun ba ,take faɗin to mu zama friend’s mana”

ba yanzu ba Fadwaah!”

cike da mamaki take kallonsa zatayi magana ,yayi saurin damqa mata cup glass din hannun sa ,Yayi hanyar  barin cikin falon da alamr wayaa xai amsa Dan taga yaki amsa wayar a gabanta ,da alamar kira ne mai muhimmanci.

Mami ta maida kallonta gurin mom gamida , faɗin Amina Ina tsoron rasa Abhi ne tunda yayi auren nan gaba daya yabi ya canja ,dama can ni ban yarda da yarinyar nan ba,kin san yaro Idan  yanason abu sai kibarsa ,dama kuma yaga daddy na goyon bayansa ba dole ba.idan bani na daga waya na kira Abhi ba,baxai daga waya ya kirani ba,sai ya kwashe watanni ukku baizo Gombe ba.”

bazan zuba ido su mallakemin Yaro ba.”

Azeezah ba ya’r gidan mutunci bace !haka bata dace da Rayuwar Omar ba!
Akwae cutarwa sosae acikin Rayuwar aurensu!”

Dan haka nake Neman taimakon ki Aminiya ta haka ina Neman amincewar ki,Fadwaah baxa ta cutu ba ,inason ganin ya’yan Abhi a dunia!inaso naga zuri’ar Abhi Amina!Hawaye ne suka fara sauka a fuskar Mami a hankali,hannu mom ta saka tayi saurin taresu meyayi zafi haka Maman Raheema!
Indai ta wuri nace bana da matsala ,dama a kullum ina addu’ar Allah yabaiwa Fadwaah na gartaccen miji, sai gashi addu’ar nawa bai tafi a banza ba.”Ashe kice zumuncin mu zai qara dorewa Maman Raheema ,nayi farin cikin Jin wannan maganar ,
Share hawayenki babu abunda xai sami Abhi ,abunda yasa kika fiye damuwa da Abhi ,
Ya fiye ,zurfin ciki ne baka taba gane cikin farin ciki yake ko bakin ciki!
Zanyi magana da kawun Fadwaah zanyi maki bayanin komae a waya.
Amma Dan Allah karki qara daukar damuwa ki saka ma ranki.Allah dai yabar zumuncinmu.”

“Amin.

Mami ta fada cike da wani irin farin ciki ,Wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyar ta.

Kusan 12 miss call ta gani kuma daga Areef dinta ,tana riqe da wayar wani kiran ya shigo da sauri ta dauki kiran nasa murya can ciki yake fadin my flower kina wahalar dani da yawa”.ki shirya gani nan zuwa xan fadawa mom ina sonki Dan Allah tabani ke na aureki”!
fiddo ido waje tayi zuciyar ta na mugun bugawa.” cikin rawar murya take fadin karufa min asiri Areef mom zata kasheni ne ,bata taba bani damar kula wani ba plsss karkaxo komae na iya faruwa!tayi maganar cikin rawar murya ,Wata doguwar ajiar zuciya ya sauqe. kin fiso muyi ta zama a haka fadwaah  ko?”kullum idan xan ganki sai da dabara ,ko kina son na rasaki ne.?ko kina son  Wani yayimin shigar sauri? da qarfi take faɗin no don’t say dat Areef plss!ta qarasa maganar cikin rawar murya ,Anjima zan kiraka mom na kirana ok. Idan baki kirani ba Allah zuwa zanyi ,xan ma kira ka .”ta karasa maganar cikin rawar murya ,I love yhu!ya fa’da a hnkali cikin sanyi take fadin  I love you too..

karfe Tara na dare tana  bedroom din mom ,rigar body hook ce ajikinta wadda ta tsiya iya gwiwarta white colour sai hular kanta da ta kasance light pink ,gwada kayan da Mami ta kawo mata takeyi sai murna takeyi sosai.

A hankali taji mom ta kira sunan ta zuwa tayi ta xauna gafda mom cike da farin ciki.

FADWAAH.!!”
Mom ta kira sunan ya’rtata a hankali .da mamaki fadwaah ke qallon mom bata tàba jin mom dinta ta kirata haka ba tafi yawan kiranta da baby.” tun tasowar ta.

Gabanta taji ya fadi! cikin sarkewar murya take fadin na’am mom!

Am sorry”!
Haka mom ta fada a karo na biyu,a daburce Fadwaah  ke fadin ,sorry for wat mom?,dana qarya maki alkawarin cewa baxaki yi aure …in dis age ba ,sai kin kammala digree dinki .Hajia salma wato Mami taxomin da alfarmar da bazan iya qinta ba,nan take hankalin Ikram ya tashi ,mom bata kula da yanayin ya’rtata ba.ta cigaba da zayyane mata maganganun da suka tattauna ,da Mami bani da kowa sai ke Fadwaah  sai uncle dinki wato ,
Kanin mom mahaifinki ya rasu tun kinada shekara biyu a dunia ,ni kaina bazan so na kaiki gidan da zaki wulakanta ba.Mami tayi min alkawarin ,
Zata cigaba da daukar ki y’ah a wurinta tamkar yarda kk y’ah acan baya ….nasan babyna bata taba tsayawa dawani ba,da sunan soyayya Dan ban taba baki wannan damar ba ,amma bazan tilasta maki ba .idan bakison Abi baxa ayi wannan auren ba ,Dan Mami tace a fara jin ra’ayinki tukuna.”

Hankali fadwaah yayi mummunan tashi hawaye a hankali suka fara sauka akan fuskarta ,taya zata fahimtar da mom dinta akwae Wanda takeso?idan kuma har ta faɗawa mom dinta Tana da Wanda takeso ta yaudari mom dinta ta haince ta tayi mata qarya !A hankali fadwaah  tayiwa mom dinta kyakkyawar runguma gamida fashewa da wani irin kuka, Wanda ke fitowa tun daga karkashin zucuyarta.baxata iya fadawa mom ba !baxaza iya ba ,itakam ta shiga ukku!wannan wace irin qaddarace ,ta fada masu haka?”
Tasan muddin Areef yaji wannan zance ,zuciyarsa na iyayin bindiga tana son Areef tana matuqar kaunar sa.

Areef shine mutum na farko da ya fahimtar da ita meye so Areef ya sota,tun kafin ta zama cikakkiyar budurwa tun tana ya’r secondary skull .Areef shine mutunen da ya fahimtar daita meye so ?”akansa ta fahimce meye soyayya Areef mutum ne mai tausayin gaske ,mutum ne Wanda ya Riga ya karanci halayyarta da har taxamo bata bata masa rai ,muddin babu Areef acikin rayuwarta bata ga amafanin Rayuwar taba.

“Mom bani da tacewa nikam kinfi kowa sanin ciwona ,baxaki kaini inda zan wulakanta ba ,amma sai dai mom zan yi kewarki banason abunda zai  rabani dake mom ,takarasa zance gamida shigewa jikin mom ta saki wani marayan kuka.”Wanda itakanta batasan kukan meye ne ba!
A hankali Hajia Amina ke Shafa bayan ya’rtata ,
Karki damu da hakan baby zan riqa zuwa ina dubaki duk week end.Allah yay maki albarka.

Amin mom .”
Taqarasa maganar cikin shesshekar kuka.
Tanajin Areef na kiranta a waya ta kasa ,dauka.
Acan bangaren Areef kuwa hankalin sa yayi mummunan tashi haka ,yanajin wani irin feelings strange,
Saqo ya tura mata alamr gashi nan zuwa bazai Iya jurewa bà,
Ta bu’de masa qofar baya ,
Lokacin da taga saqon sa ya shigo a wayarta,
Hankalin ta yayi balain tashi,
Tasan Areef xay iya zuwa .
Idan mom ta gansa fa?
duba agogo tayi qarfe goma da Rabi na dare ,da sauri ta shiga kiran lambarsa amma bata shiga ,
Atsorace ta sauqo daga down stairs ta hanyar kitchen na nufa zuwa balcony Dan cikin balconyn su akwae wata ya’r qaramar qo’fa ,Wanda bbu Wanda yasan da zamanta ,daga Fadwaah  sai mom ko maigadi da masu aikin gidan basu San ,da zaman ta ba.
Koina tsit wani irin tsoro taji ya shigeta ,tanayi tana waige-waige .

Wayarta ce ta fara ringing da sauri ta da’ga ,budemin ko’fa taji ya fada cikin wani irin murya,bakada hankali ne Areef !”kabari sai da safe plsss mu haɗu a skull I promise you.”.
Ta qarasa maganar cikin fashewa ,da kuka baxan iyaba Fadwaah  idan baxaki buɗe ba zan ba’lla kofar !
Jiki na rawa,ta saka key ta bu’de tsaye ta gansa ,
da farar Jallabiya ajikinsa ,idonsa sun kada sunyi wani irin Ja..dauke kanta tayi akansa ,
hanya tabasa ya shigo ta maida kofar ta rufe ,bata da zabi ta fada Jikinsa ta kankamesa sosae gamida ,
Fashewa da wani irin kuka mai Sosa rai,
Tunda take da Areef bata taba Rungumar sa ba ,
Haka shima  koda wasa baita riqe hannunta  ba ,shima tsoro abun yabasa,
Bbu musu ya riqeta sosae tanajin yadda ,zuciyarsa ke wani irin halbawa.tamkar zata fito waje…

A hnkali yajata cikin balcony fararen kujorune daga gefe aka kawata wurin dasu,har lokacin tana cikin jikinsa tana sauke Ajiar zucia .zaunar daita yayi maimakon ya zauna sai ya zube gwiwon sa a qasa ,cikin sanyi jiki ya kamo hannayenta duka biyu har lokacin Fadwaah bata daina zubar hawaye ba.

FADWAAH!!”
Ya kirata cikin wani irin tone ,Wanda bata tabajin sa dashi ba haka akwae wahala sosae ya kirata da wannan ,sunan hawayenta na diga akan hannunsa a hankali ,qara matse hannayen yayi yana Jin hawayenta tamkar ana zuba masa, ruwan dalma.

shin menene danuwar ki? meya saki kuka ?”baki da lfy ne?’lokaci daya ya jero mata tambayoyinsa haka yana kallonta ,da idanunsa da suka rine daga farare zuwa Ja .”kwace hannunta tayi haka taji wani kuka ya qara xo mata babu shiri ta toshe bakinta.cike da  tashin hnkali Areef ke kallonta bai taba ganinta haka ba!akwae wani Abu mai muhimmanci da ya faru daita,a karo na biyu ya qara riqo hannayenta ,cikin rawar murya yake fa’din kiyiwa Allah ki daina kukan nan haka  ,kukan ki yana tafasa min zuciya na rokeki plsss .kansa ya Dora akan cinyar ta gamida lumshe idonsa,mom ce ba lfy ?
Yyi mganar cikin sanyin murya ,sai yanxu ta qula da yadda tafito,
Atsorace ta miqe tsaye .
Areef muyi magana zuwa gobe dare yayi ,bata jira amsar saba,
Ta rugu da gudu zuwa cikin gida.
Ido Jajur yabita da kallo qafafunsa sun qasa daukarsa ,sannu a hankali ya zube gwiwon sa a qasa.
Yafi minti ashirin a wurin jiki sabule yabar gidan ,
Koda ya koma mota daura kansa yay akan sitiyari.
yana tunanin mai ya gigita fadwaah haka?”kowane irin abune yaji ajikinsa ya shafesa,
Ko rasata zai yi?’wata zuciyar ta fada masa haka,da sauri yake fadin nooo!haka baxai taba faruwa ba ,Jiki sabule yaiwa motar key yabar unguwar lokacin karfe goma sha daya dai-dai na dare.

kankame pilo tayi sosae ajikinta ,tana wani irin kuka mai taba zuciyar duk mai saurare ,
Karo na farko da tafara tsanar kanta akan qin gabatar da Areef a wurin mom ,da wane ido zata kalli Areef?
Baxata iya Jure rasa saba ,tana son Areef tana matuqar qaunar sa Wanda baki kadai bazai  furta hakan ba .ta ina zata fara ?”
Adaren bata iya yin barci ba ,
Kashe phone nata tayi gudun karta dagawa Areef hankali!
Kashen wayar kuwa ya qara daga hankalin Areef fiye da tunani mai karatu……………..A kasan rug  yay kwance farin boxer ne Ajikinsa ,
Bbu ko Riga ajikinsa haka yasa qirar mazan takar sa taqara fita sarari,
Duk da Areef din black beauty ne amma kyakkyawan karshe ne ,
Wanda ya’mmata ke hauka akansa,
Dan Areef ya ha’da duk wani  qualities din da ake nema agurin namiji .”
Riqe yake da phone nasa ,
Yana Juyata a hankali ,Katon pic din Fadwaah ne manne agaban wayar sa ,Riga da skirt ne na body hook Ajikinta ,Rigar fara ce sai skirt.din ya kasance dark blue Wanda ya Dan baje A qasa ,
Sai hular kanta ta net wadda ta qasance dark blue ,
Idonta yasha kwalli sai Dan qaramin bakinta Wanda yasha red Jan baki pic din yayi matuqar yin kyau ,murmushi kwance a kyakkyawar fuskarta.
Samun kansa yay da shigar vedio din wyar ,anan ya danna play din wani vedio…….Tsaye take a kitchen ,
Yayinda sahlaah ke bayanta riqe da wayar ,
A hnkali Fadwaah ta juyo tana qallonta .”rolling din manyyan  eyes nata tayi akan sahlaah wadda ta saita ,camera!
Oh babe meye haka?”
Sai kace wata ya’r wasan kwaikwayo zaki riqa yimin vedio,plss beb stop this nonsense dramar naki taqarasa zance gamida haɗe rai .daria sahlaah tayi karki damu kanki ya’mmata areef naki zan turawa ,yaga yadda kike aeki a gida tamkar a gidan sa !
cigaba da aekinta tayi tana fadin ko bai gani ba sahlaah wataran ma ae zay gani nidai ki tayani addu’ar samun Areef kawae besty”ina yimasa wani irin son da banayiwa kaina shi ,baki wangalau sahlaah ta saki tana qallonta.
Cikin zolaya sahlaah ke fadin kin fison shi da mom?
da sauri fadwaah ta kama baki bakiji abakina ba ,karki yimin sharri ,OK naji kin fison sa dani?”
Fuskantar ta Fadwaah  tayi ,
Kowa Dana shi matsayi a zuciyana,plsss tambayr ya isa haka daria sahlaah tayi.”

samun qansa yay da yin murmushi duk da yana cikin damuwa ,yana son FADWAAH yana Jin sonta na yawo acikin ko wane gaba ta jikinsa.

ABHI KURFI PLACE…………aeki sosae yakeyi da laptop nasa kirar Apple daga kai yayi ya qa’lli agogon dake manne a  ba’ngo dakin ,qarfe sha daya harda rabi tsaki Yaja ,
A qaro na farko yarasa Azeezah wace irin macce ce allah yabasa?’ tun qarfe goma da rabi ya kirata a waya Dan ta ha’do masa coffee ,kusan awa day’a har yanxu ba alamr ta kuma tasan duk yana irin wannan aekin sai da coffee agabansa,
Hakane kaidar sa tun kafin suyi aure ya Riga yasaba da hakan ,
A fusace ya ture laptop din gefe ,black tree quarter ne ajikinsa sae kuma farar vest duk sanyi Ac. Dake mamaye da qatafaren da’kin nasa komai na dakin nasa off white ne . best colour dinsa ,kenan Wanda yay matuqar tsaruwa. qallo day’a zakayiwa da’kin kasan kudi sun zauna ta koina,
(Casual slippers)ya saka a kafafunsa  ya nufi part din azeezah ,
Wanda bbu wadataccen haske a falon na farko ,yana Shiga na biyu yaji qarar TV.Wanda komae na falon brown ne ,
Tsaki yayi aransa yake fa’din .”she is so careless !ya dauki remote ya qashe TV. Kai  tsaye  bedroom dinta ya nufa ,
Akan soofa ya hangota kwance tana amsa waya tana sanye da sleeping dress masu daukar hankali,da lumsassun idonsa yake binta da qa’llo murya can ciki yake ,
Fadin
Azeexah kin manta da coffeen nawa ne?ko rainin ,hankalinki ne ya tashi?”
Duk da cikin sanyi yake mganar amma maganr na tattare da fushi,
da sauri ta miqe zaune ta haɗe rai  take qa’llonsa gamida qarosawa gabansa,aah Meyayi zafi haka Abhi?
Nifa ba ya’rka bace da zaka riqa fadamin magana son ranka !haka ni ba ya’r aekin ka bace da zaka Juyani yadda kakeso ,baxan haɗa coffee ba.!
Ta qarasa maganar cikin zafin rai ,
Wani mugun kallo Abhi ke binta dashi ,gamida fadin Alright ae nan ba gidan Ku bane!
Haka bake kike aure na ba,
Ni nake aurenki Dan haka dole kiyimin abunda nakeso!!”haushinta takeji daga shi har uwarsa tun lokacin da ya bullo da maganar aure.
A fusace take ka’llonsa gamida riqe kugunta ,Ashe ko akwae balai Agidan nan .
Mr.Abhi salman kurfi !
Wlhi baxan haɗa coffee din nan ,ba ka koma gurin wacce kuke kulla munafurci daita ta h……sauqar mari taji akan fuskarta ,kafin ta dawo hayacinta ya shimfida mata ,wani !karki kuskura ki qara gigin aibanta min mahaifiyata a gabana !ko bayan idona Azeezah!
Zan fisge son da nake yimaki ,
Na wulakanta ki Azeezah!
Abhi ya qarasa zance cikin wani irin fushi ,hawaye na zuba a idonta take bin mijin nata da qallo tsoro mamaki suka lullube zuciyar ta lokaci ɗaya cikin zafin zuciya yabar mata room din ,gamida bugo mata qofa.

ASMY B ALIYU

Abhi Kurfi

Azeezah kurfi

Fadwah

AY saraki

Series Navigation<< Fadwaah Part 1Fadwaah Part 3 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *