Fadwaah Part 1

This entry is part 1 of 3 in the series Fadwaah by Asmy B Aliyu

FADWAAH

ASMY B ALIYU

Page 1

Idonta cike da kwallah take gyara masa  zaman italyn  suit coat din dake jikinsa. haka Abhi ya lura da yadda sanyin azeezah din yayi yawa lokaci ɗaya. sai dai baice komai ba ,kishine kurum ke cinta lokaci ɗaya ta sake sa gamida zubewa akan gefen bed ta saki marayan kuka jikin Abhi lokaci ɗaya yayi sanyi yasan dole Azeezah tayi kuka ,
Abunda ciwo ace macce ko shekara daya aurenta baiyi ba ace xa’ayi mata kishiya dolema ne taji ciwo zaunawa yayi gefen bed .gamida jawo matar tasa ya saka ta cikin fadeden kirjinsa .
Kukanta yakeji har cikin ransa ,
Am sorry baby !
“Ke kanki kinsan auren nan ba sonsa nakeyi ba ya na iya da Mami ,kin ga yarda takeso ayi auren nan mistake daya xanyi a yanxu Mami xata hau fushi dani.”cikin shesshekar kuka take faɗin haba umar menayiwa mami haka? menayi mata
da zata yimin wannan mummunar sakayyar?
Anya kuwa akwae sauran tausayi acikin zuciyar Mami?
Lokaci daya taga abhi ya saketa ,cikin wani irin fushi yake fa’din.”mind your language azeezah!
Kin xo wurin da baxan iya jurewa ba,
Baxan yarda da wannan ba!
Naji Mami bata da tausayi ,shikenan .”
Ya qarasa mganar cikin fushi da zafin rai!
Hawaye na zuba a idonta take kallonsa da sassarfa yabar mata room din gamida ,bugo mata kofa ,hannu azeezah ta saka akai gamida sakin wani irin
  kuka tasaka a  haukace ta shiga watsi da komai na dakin.

da sasarfa yake tunkarar mamin sa wadda ke zaune a bayan motar (Ranjer Rover)da driver zaune a gefe,da alamar shi kadai ake jira yarda yaga mamin ta hade rai yasa yasha Jinin jikinsa da sauri driver ya fito daga motar gamida bude masa bayan motar  ya shige sai da ya zauna driver ya rufe marfin motar, gamida komawa mazauninsa .da sauri yayiwa motar key ,horn ya danna da sauri maigadi ya wangale katuwar get suka fice daga cikin gidan.

sai da suka dau hanya sa’annan Abhi ya kalli mamin  nasa cikin sanyi jiki wadda ta hade cikin less dark green da kuma ra’atsin red ajikinsa,sai kuma Red din hijab mai hannu   glass din medical ne sanye a idonta , qallo ɗaya zakayi mata zaka san suna Jin dadin rayuwa ,haka kudi sun zauna ta koina.hnnunta ya kamo a raunane yake fadin Mami kinyi kyau .”harara ta watsa  masa gamida dauke kai ganin haka yasan mamin fushi tayi a hankali ,ya saki hannun Mami gamida Jingina bayansa ajikin kujera, lokaci day’a kuma ya saki ajiar zuciya.

Ana gaf da kawowa gidan su tayi saurin dakatar dashi da qarfi take fa’din AREEF! Nan ma ya isa!
So kake mommy ta kasheni!”
Kallonta yyi gamida sakin murmushi haka lokaci daya Ya gangara da motar gefen hanya gamida yin parking.Dan bude idonsa yayi akanta irin ,wannan ihu haka my flower. sae kisa na saki sitiyari batareda na sani ba.”
Folding din hnnunta tayi akan kirjinta gamida turo masa Dan kyakkyawan bakinta.alamr tayi fushi lakace mata hanci yyi gamida sakin daria ,buge hannun tayi gamida balle marfin motar tafice da Dan gudu ,
Fitowa yayi shima da Dan gudu yana kwala mata kira .
da gudu ta fada cikin gidan su ko waiwaye .murmushi yyi gamida komawa mota yanajin son FADWAAH yana huda ko wace gaba ta Jikinsa.
Mom! Mom!
Haka ta dinga kwalawa mom din nata kira a tsakiyar kayataccen parlorn nasu Wanda yaji kayan Alatu.ganin tayi mery tafito dauke ,da kulolin abinci zuwa dinning area.
Hi marry!
juyowa Mary tayi tana ka’llonta .
Mom fah?
Hanyar kitchen ta nuna mata kai tsaye kitchen din ta nufah,
Tsaye tayi tana qallon mom din tata wadda ke hada Orange juice hugging dinta tayi gamida fadin sannu da aeki mom!

“Am back “
tayi mganar cikin sanyi murya ,mom bata kalleta ba take fa’din hop yamaki dinki mai kyau?rolling manyyan eye’s nata tayi gamida dawowa gaban mom din ,dolen sa ma mom !yamin mai kyau mana oya kije kiyi wanka ki shirya Su Abhi na kan hanya shida mami ,bata fuska tayi gamida fadin waye kuma Abhi mom?_

“I don’t know him!
” shima Dan gurin Mami ne,zatayi magana mommy ta katseta oya jeki kiyi wanka ,Anjima mayi magana.”badan Fadwaah taso ba ta juya tabar kitchen din.

Adai dai bakin (makey super market) yaji Mami tayiwa driver umurnin yayi parking motar su a wuri na musamman, da aka ware Dan parking  motoci.
cikin sauri ya fito daga motar zuwa side din Mami yasa hannu biyu ya bude mata motar gamida amsar handbag din hannunta .bayan ya rufe motar Mami ta miqa masa hannu alamar yabata handbag din ,cikin sanyi murya yake fa’din Mami barshi na riqa maki shige mutafi haka zaka shiga da handbag a hannu mata na qallonka?”girgiza kai yayi Mami ina ruwana da mata ,ai lada zan samu!

Yanda yayi maganar yasa Mami tayi murmushi gamida qarbar Jakarta ta saqala agefen kafadarta ,taqara gyara zaman gilashinta .Haka kawae sai kasa mata su rainamin babana! To bazai yuyuba!
Shige mutafi baice komae ba yabi bayan Mami ,dama tasan baizai ce din ba.kasancewar sa bayada yawan magana.

Tsaye yayi yana qallon yadda mamin ,ke kwasar kaya Dan juyowa tayi tana qallonsa Abhi karaso ka zabarwa Fadwaah  perfumes mana,kamar yayi kuka yake qallon mamin shi taya za’ayi yasan turaren mata sabida Allah ?”ko Azeezah lokacin da tana gidan su sae dai suje tare ta zabi kalar da takeso……haka yata kwasar kalolin turarukka  batareda yasan dadim su ba,ko akasin hakan .samun kansa yayi da Juyawa gefen chaculate masu tsadar gaske ya shiga  kwasar mata su yayinda yabar mamin gurin tarkacen kayan kwalliyya .sae da aka hada kayan akayi bill ,sa’annan ya lura da kayan sunyi yawa wai duk na mutum daya ne nan aka bada bill,sai yaga mamin ta miqa card nata.anan suka ciri kudinsu aka daukar masu kayan zuwa mota.

Kai tsaye unguwar (orji Quartz), suka nufa.

Ta hade cikin wani tsadadden less dark purple da ratsin pink ajikinsa  ,mery ce take taimaka mata da  daurin Dan  kwali tayi wani irin kyau na musamman duk da kasancewar ta black beauty chaculate ce salon make up din dake fuskarta yayi matuqar yimata kyau ,bayan  mery tagama Daura mata Dan kwali ta kalleta gamida fa’din thank yhu mery.

plsss kawomin abincina anan ,ta amsa da to .gamida ficewa daga dakin.

Akan soofa ta koma ta zauna ta daga wayarta sai taga honey boo dinta ya kira kusan 10 miss call ,Dan fiddo ido waje tayi  a hnkali ta furta oh my god!

dialling numbersa tayi ring daya biyu ya daga dama kamar Jira yakeyi ,ajiar zuciya  ya saki.
Ina kika shigane hayatiee  ina ta kiran wayar ki baki daga ba?am sorry baby ina wanka ne!
My flower ina son na ganki ya xa’ayi ?”
Ido ta Dan zaro kamar tana ganinsa ,Ka rufamin asiri mommy zatayi ba’ki kawae Ka hakura sai gobe!
Bazan iya ba!
Yayi magnar cikin shagwababbiyar muryar dake sakata jin wata irin kasala ,Jin ana qoqarin shigowa dakin nata ,yasa tace honey ,
Muyi magana zuwa anjima mom!
Bata Jira mezaya fada ba tayi saurin katse  kiran dai dai lokacin da  mom ta turo qofar da’kin na’ta.”masha Allahu!_
Abunda mom din ta fada kenan itama tana sanye cikin shiga ta alfarma kasancewar ta mai qaramin jiki sai ka rantse da Allah ba itace ta haifi Fadwaah ba.

‘Juyi Fadwaah  ta shigayi a gaban mom din gamida riqe kugunta tana  Dan karkada idanunta ,take fadin  mom ya kika ganni nayi kyau?”daman  kuma Fadwaah akwai iyayi oh my princess!”
You look so cute ,gorgeous stunning Preety angel,and take away,just can’t stop suprising.”
Yeehhh!
Stop !stop plss mom karkisa na riqa ganin nafi kowa kyau a dunia!ta qarasa mganar cikin ,ihun murna daria mom tayi baxata iya da Shiriritar Fadwaah  ba .zatayi magana taji ana dannan door bell ,ae da gudu ta nufi qofa tana wlhi mom ga Mami nan!Allah yasa tare sukaxo da sahlaa.
da haka ta bude qofar tafita da gudu…….

ASMY B ALIYU

Fadwaah

Areef Yusuf saraki

Abhi kurfi

Azeezarh kurfi

Series NavigationFadwaah Part 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *