Gama Duniya Babi na uku

Gama Duniya Babi Na Biyu

This entry is part 2 of 3 in the series Gama Duniya by Binta Umar Abbale

°°°GAMA DUNIYA
BINTA UMAR ABBALE 🍒

BABI NA BIYU
Cikin k’asaita alhaji Badamasi yake tuk’a motarsa har isa wani hotel mai kyau da ‘kayatuwa. Ya gyara parking ya fito yana gyara babbar rigar dake jikinsa. wayarsa ya d’auko daga aljihu ya fara neman lambar Ladi. Sai ya hange ta tana zuwa gurinsa cikin salon tafiyarta mai tafe da girgiza . Lokaci guda hankalinsa ya tashi. dawowarsa kenan daga Lego’s ya ji ba zai iya jurewa ba sai ya ga Ladi gimbiyar mata. Ya dinga bin ta da mayataccen kallo har ta k’arasa kusa da shi. “Alhaji na babyna gaskiya na ji dadin ganin ka yau na yi kewarka.” Alhaji Badamasi ya sauke ajiyar zuciya ido jazur ya ce.” Babu lokacin magana A halin yanzu muje ciki kawai.” Da sauri ya yi gaba Ladi ta bi bayansa tana hararar ‘keyarsa. Ba don komai take bin sa ba sai don kud’insa, zuciyarta ta namiji d’aya ce. Suna shiga dakin ta jefar da mayafin dake rataye a wuyanta. Alhaji Badamasi ya bararraje kan gado yana bude mata hannuwansa wai ta je. Ba tare da bata lokaci kuwa ta rungume shi, ta fara rikita shi da salonta da yake bala’in kid’ima shi.

**
Luba da Ashanty suka fito daga d’akin bayan sun kammala ta’asarsu. Luba ta ce.” Wallahi zan yi kewarki kawata, bana gajiya da wannan lamarin, lusarin mutumin nan zai katse mana hanzari sam ban ji dad’in dawowarsa ba.”
Ashanty Ta ce.” Ai sai da na fadà miki aure sam bashi da fa’ida takurawa ne zallan. Idan biyan bukata ki ke nema ni meye amfanina, ki ka ce ke dole sai kin aure shi. Ko da yake Muna samun kudin biyan bukatanmu.”

“Shine dalilin da yasa nake zaune dashi har yanzu. Amma idan ba haka ba ni wallahi babu abinda zan yi dashi tunda ba ya iya tsinana mini komai.”
Ashanty ta fashe da dariya tare da bata hannu suka tafa.


GIDAN NASIRU.

“Ayyara iye alagidogo, ala gidigo baba rudo, ala gidigo!” Aliya kenan dake zaune a kan kujera ‘yar tsuguno tana rera wak’ar alagidogo, tana sanye da wani uban leshi mai tsada ta yi d’aurin ture ka ga tsiya yatsunta sanye da manyan zobunan gwal wuyanta ma sarka ce a kwance.
Kayan miya take gyarawa tana rere wak’a da alama duniyar ta yi mata dad’i. Tun kafin ya shigo take jin zage-zagensa yau ya waiwayo gida da wuri kenan.” Tab’e baki ta yi ta cigaba da rera wak’arta. Ya shigo gidan yana bal da abinda yake kan hanya. Daidai bakin kofar shigowa ya tsaya yana kallonta wadda da ta’ki ta d’aga kai ta kalle shi saboda mugun haushinsa da take ji. Nasiru ya lashe bakinsa yana sakin murmush ‘Dole ne fa ya sauke tsiyar da ya shigo da ita cikin gida ya kwashi gara domin wannan kwalliyar da Aliya ta yi ta mutu’kar tafiya da imaninsa, bayan haka kuma ga kayan miya nan tana gyarawa ya san yau za kwashi jar miya ko da kuwa za ta tsine masa sai ya ci.

Nufar ta ya yi yana washe baki ya ce.” Aliya manya mata Aliya ta Nasiru ikon Allah! Aliya farincikin Nasiru tauraruwar Nasiru, yau kwalliyarki ta burge ni Aliya ashe gwara dana zagayo gida yau akwai soyayya a tsakaninmu.” Maganar yake yi yana kusantarta.
Ta kalle shi a banzace kafin ta girgiza kanta sai kawai ta cigaba da abinda take yi kuma bata fasa rera wak’arta ta alagidigo ba. Ya tsake matsawa jikinta kamar zai rungumeta da sauri ta zabura! tana nuna shi da wu’kar da take hannunta ta ce” Wallahi kar ka shafa min warin gyanye da tabar wiwi na shirya tsaf zan shiga cikin Jama’a kasa ana guduna.” Nasiru ya b’ata fuskarsa ya ce.” Waye yake warin ganye? Wallahi ki shiga taitayin ki ko ki ci ubanki a gidan uwarki na sha tabar wiwi.” Dariya Aliya ta yi har da tafa hannaye kana ta ce”Nasiru kenan a tafin hannuna kake wallahi duk abinda kake yi nasa ni don haka go gefe don Allah kada ka bata mini kwaliyata. Duka ya kaiwa bakinta a fusace yana huci ya ce.” Za ki yi mini rashin kunyar ne da ki ka saba ina a matsayin mijinki na sunnah.” Da sauri ta tashi tsaye ta d’auki d’an bokitin da ta gyara kayan miyan “Wallahi ban ji dad’i shigowarka gidanan ba ina cikin nishadi da farinciki ka zo ga rusa mini jin dadina.” Nasiru ya zabura kamar zai kai mata duka ya ce.” Gidan ubanki ko nawa?”
“Ahayye nanaye!” Aliya ta fad’a tana girgiza ta ce.” Allah yasa kasan a inda ka je ka auro ni ballantana ka yi mini gori ka san gidanmu ya ci wwar wannan akurkin.” Ya girgiza kansa tare da cewa .”Wallahi na yi rantsuwar babu inda za ki je yau domin hutawa zan yi a gidana.” Kafin ya rufe bakinsa ta katse shi ta hanyar fad’in”Baka isa ba wallahi, fita kamar na yi na gama. ” Kanta ya yi gadan-gadan. Da gudu ta nufi dakinta, ya fizgota da k’arfi had’e da k’wace bokitin kayan miyar ya yi cilli dashi bakin rariya, matse ta yayi jikin bango yana kokarin hada bakinsu guri guda wai shi kiss zai yi Aliya ta daki gabansa da kafarta guda da sauri ya sake ta ya fad’i a gurin, yana ihu! D’akinta ta shige da gudu tana hakki. sakata ta zura ta jingina jikin kofar ta da dafe kirjinta gabanta sai fad’uwa yake yi. Nasiru da ‘kyar ya dawo hayyacinsa, ya mike da sauri hade da kaiwa kofar duka da k’afarsa yana fadin”Aliya mutu’kar na kamaki Wallahi sai na yi miki rashin mutunci sai na ragargaje ki shegiya mayya ni za ki nakasta ki hanani na jin dad’i n mori kuruciyata to ba zan lamunta ba sai ci ubanki Wallahi.”
“Ba ka isa ba wallahi na yi kwalliya ta ka b’ata mini da warin jikinka, yo ni idan ba kaddara ba me zan ci dakai d’an shaye- shaye.” Ihu! ya yi ya k’ara kaiwa kofar duka yana fad’in”Ni kike fad’awa wannan maganar Aliya? Ihuhu! cau! wallahi yau zan sake ki don ubanki ki je ki auri wani yanzu kuwa, ke nama sake ki saki uku ni tsayayyan namiji ne da ba’a nuna ni da yatsa ki je na sake ki saki uku.” Aliya dake cikin daki ta ji abinda yake cewa gabanta ya fad’i! saboda tunawa da alk’awarin da ta dauka a gidansu cewar auranta da Nasiru babu saki babu yaji. Da k’arfi ta ce”Wallahi ban sako ba Nasiru zama cikin gidan ka daram ko saki dari za ka yi min babu inda zan je.”
Ya ce.”Zan kuwa ci uwarki wallahi tunda ke mayya ce saunawa ina fad’in na sake ki kina zauna mini a gida, shikkenan za ki ga iskanci da zan yi miki.”

Aliya dake cikin d’aki a rufe ta ce”Sai dai naga alkairi wallahi ai ni nake ri’ke da kaina a gidan, baka sauke nauyin kanka ba babu abinda kake yi mini saboda haka babu inda zan je wallahi.” Yana kokarin fita daga gidan suka yi karo da Atine ta ci uwar kwalliya sai kamshi take yi. Atine ‘kawar Aliya ce tare suka tashi. Wani irin kallo ya yi mata na sha’awa ya ce.”Atine dama ana ganin ku?” Fari ta yi da ido tare da fad’in “Gani kuwa ka Nasiru ina fatan dai Aliya tana nan don unguwa zamuje.” Lasar bakinsa ya yi, yana yi mata kallon kurrulla. Ya ce.” Tana ciki ‘yar gidan mutsiyata, yanzu take k’okarin kassarani ta kai mini duka a makarfafa.” Atine ta fashe da dariya har da tafa hannu “Wato dai har yanzu kuna nan kuna abinda kuke yi ko wai yaushe za ku yi hankali ne don Allah.” Nasiru ya ce.” Babu ranar hankali idan ina tare da Aliya domin ba matar rufin asiri ba ce.
Atine ta dinga dariya tana fad’in “Aliya an yi ‘yar iska wallahi amma na ji ta ce wai baka gamsar da ita a shimfid’a ko shiyasa take so ta nakastaka ba, to in banda abin Aliya duka a makarfafa ai sai ta kashe ka.” Ya ce.” Ki rabu da ita wallahi zan nuna mata ni cikakken namiji ne tunda yawo take yi da ni a duniya tana fad’in. Gaza sauke nauyinta Lallai Aliya ba ta da mutumci wallahi.”

Atine ta dinga k’yalkyala dariya tana kallonsa. Ya mika hannunsa zai cafko ta, cikin shakiyancin da suka saba ya ke fad’in.” Ke ma ai ba gagarata za ki yi ba Atine.”
Bakinta ta ri’ke da sauri ta shige gidan tana cewa” Rufa mini asiri Nasiru na mutu maza su kai ni, ai ni na fi karfinka ba za ka iya da ni ba.”

FREE BOOK NE GA KOWA DA KOWA.

Series Navigation<< Gama Duniya Babi Na DayaGama Duniya Babi na Uku >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *