Gama Duniya Babi na uku

Gama Duniya Babi Na Daya

This entry is part 1 of 3 in the series Gama Duniya by Binta Umar Abbale

°°°GAMA DUNIYA!
BINTA UMAR ABBALE 🍒

BABI NA ‘DAYA

Join our WhatsApp group here


‘Katuwar makarantar Allo ta Malam Dauda mai al’majirai, ta yi shuhura a garin Kano inda mutane daga garuruwa suke kawo ‘ya’yansu karatu makarantar saboda yanda take da horo da bada karatu na al’kur’ani mai girma. Makarantar Malam Dauda ba ta tsaya anan ba har gagararru, wad’anda suka gagari iyayensu, tana maganinsu da izinin Allah duk taurin kan yaro mutu’kar aka kawo shi tsangayar Malam Dauda to ubangiji zai shirye shi. D’aliban dake cikin makarantar suna da yawa saboda kullum kawo sabbi ake yi dayawa daga cikin tsofaffin d’alibansa sun yi aure sun tare a garin suna neman kud’insu, sai dai su je gurin iyayensu da sunan ziyara.
Duk yawan d’aliban Malam Dauda bai sa ya mance ko guda ba, sai yanzu da tsufa ya cimma sa. Amma a shekarun baya duk shige da ficensu yana gani, kuma ko d’aya ne bai dawo daga bara ba, sai ya gane.
Malam Dauda yana da mata hud’u da ‘ya’ya ashirin da takwas duk suna cikin k’aton gidansa mai dauke da d’akuna Goma sha biyar, bayan manya-manyan shaguna goma da suke wajan gidan.
Akwai wasu manya-manyan filaye uku duk mallakinsa ne kuma a cikinsu ya kafa rumfar kwano suke karatu da d’alibansa.

D’alibansa da ya yaye sune suke d’aukar nauyin gidansa da duk abinda ya shafi iyalansa kuma duk cikin gidan shi suke rayuwa da ‘ya’yansu shiyasa gidan ya zama tamkar wani gidan haya rayuwa suke kamar ta dabbobi kowa na yi Abinda ya dame shi, band’aki biyar ne a gidan ko wanne a kwai gurin tsuguno a ciki, sai su fi shekara basu wanke ba ko wacce tana ganin ‘kyashin ta shiga ta wanke. Matan Malam duk k’arfin su ya k’are sauran ‘yan matan ‘ya’yansu sune suke yi musu aikace-akaice ko wacce ranar girkin ta, ‘yayan ta ne zasu d’ora k’atuwar tukunya a gidan, iyakacinsu kawai ‘bagaran almajiran malam da ‘yayansu dake aure a gidan ko wanne tukunyarsa daban. Gidan Malam Dauda kamar bariki haka yake dalilin rauni da tsufan da ya kama shi. Kowa a gidan abinda ya ga dama yake yi.
Wata dattijuwar mata na gani zaune cikin wata k’atuwar rumfa mai zurfi tana zaune kan tabarma jikinta sanye da hijabi da carbi a hannunta tana ja da alamu ta idar da sallar walha ne, kanta ta d’aga tana kallon ‘yar ta da ta fito daga uwar d’aki, taci uwar kwalliya tana sanye da doguwar riga ta wani irin yadi mai sharara ta yi rolling da wani siririn mayafi hannunta rike da ‘yar k’aramar pose sai taunar cingam take yi kas-kas. Mahaifiyar tata ta kalle ta a nutse ta ce”Yanzu Ladi ba kya yi wa kanki fad’a ba ki je ki cire wannan kayan na jikin ki, kuma ki cire wannan gashin da kika sanya a idonki da wannan siriryar sarkar dake k’afar ki guda d’aya, shin kin san kallon kuwa da jama’ar gari suke miki?”
D’aga kafad’u Ladi ta yi tana wani irin fari da idonta ta yi k’as!k’as da cingum din dake bakinta, ta ce” Kinga Uwale ki k’yale ni na mori k’uruciya ta da Lokacina wai me yasa duk abinda nake yi idon ki a kaina mtsss ni wallahi ba na son irin wannan abin da kike yi mini.” Ta fad’a tana murgud’a bakinta.

Cike da mamaki mahaifiyar tata take kallonta ta ce”Yanzu Ladi ni kike fad’awa magana? Har da tsaki ni fa mahaifiyar ki ce.” Dariya Ladi ta sanya harda tafa hannu “To shikkenan saboda kina mahaifiya ta sai ki hana ni na more k’uruciya ta saboda kina mini bakinciki da irin kyau da hallitar da Ubangiji ya yi mini lallai Uwale akwai aiki a gaban ki.” Ta k’arashe maganar tana dariyar iskanci. Uwale ta sunkyar da kanta cikin bakinciki da takaici ta ce”Ladi ba zan yi miki baki ba kan dukanin abinda kike yi Allah ya shirye ki.” Ladi tana dariya ta ce” Yanzu kika yi magana Uwale ni sai na dawo.” Tana gama maganar ta tabar gurin cikin wata irin ‘yar iskar tafiya.

GIDAN ALHAJI BADAMASI.
“Hajara ke Hajara! wai ba kya ji ne ina kiran ki?” Matar da aka kira da suna Hajara ta fito daga kicin da sauri ta zo ta tsuguna gaban mijin nata dake tsaye cikin wata lafiyayyiyar shadda sai maiko take yi ya murza hula zanna bukar a kansa yana uban k’amshin turare. Kallon banza ya yi mata yana wani ya mutse fuskarsa kamar wanda ya ga kashi ya ce.” Wato saboda baki da mutumci kina ji ina kiran ki kika yi mini banza ko?” Hajara jikinta na rawa “Wallahi ban ji da wuri bane ka yi hakur…. Kafin ta karasa ya tufa mata miyau a fuskarta, yana ya mutsa fuska ya ce.” Wallahi ki kiyaye ni idan ba haka ba zan auna ki gidan ubanki mutsiyaciya kawai.”Hajara ta sanya hannunta cike da bakin ciki ta goge abinda ya tofa mata a fuska muryar ta na rawa ta ce”Ka yi hakuri Alhaji.” Tsaki ya ja ya zura hannunsa cikin aljihu ya ciro gudar dari biyar sabuwa dal! ya jefa mata tare da fad’in “Gashinan ki san yanda za ki yi ku ci abinci ke da yara ni zan fita kuma ina zaton sai gobe zan dawo domin tafiyar gaggawa ta same ni yanzu.” Jiki a sanyaye ta dauki kud’in tana jin tsoron ta fada masa maganar dake bakinta. Da kyar dai ta ce”Alhaji dama Jiya mun karb’i taliya Leda biyu gurin Nura mai kanti d’azu da safe da na aiki Sayyid ya siyo min sukari yace a bashi kud’insa.” Wani irin bahagon mari ya zabga mata a kumatu da masifa ya ce”Don ubanki ni na aike ki ki ci mini bashi a unguwa? wato kina so ki tona mini asiri ko? da arzikina da mutumci na ki je kina ci mini bashi Hajara ni za ki tozarta ?”
Ta ri’ke kuncinta tana hawaye had’e da bashi hakuri, da sauri ya shiga dakin da ya fito ya ciro wayar redio kai tsaye kanta ya nufa ya fara lafta mata yana d’ura mata ashar iri-iri.

Hajara kuka take yi tana bashi hakuri shi kuwa ko a jikinsa dukan ta kawai yake yi ta ko ina kamar wanda Allah ya aiko shi, sai da ya yi mata lilis! sannan ya jefar da wayar yana hakki! Ya ce” daga yau ki ‘kara ci mini bashi a waje wallahi sai na karya ki na zubar shegiya ‘yar mutsiyata.” Rigar shi ya buge ya tsallake ta ya fice daga gidan yana hura hanci. Garejin da motarsa take ya bud’e ya fito da ita ya bata wuta ya bar unguwar.
Hajara kuwa kuka take yi sosai ta rike gefan kunnenta da take ji yana yi mata wani irin k’uda dummmm! kawai take ji a cikin kunnan nata kuka take tana k’okarin tashi daga gurin ta kasa saboda jiri sai ta koma ta kwanta tana addu’a cikin ranta. Cikin wannan hali yaranta suka dawo daga makaranta suka same ta.

GIDAN AUWALU

Wani irin buge-buge na dinga ji a cikin uwar d’akin. Lamfu na yi ina saurara. Tabbas rikici ne tsakanin ma’auratan guda biyu, kafin na ankara naga sun fito da daga dakin a guje!
“Amina ki sake ni kar ki yaga min riga ta, ki sake ni nace miki in sha Allahu yau idan na shigo da daddare zan baki kud’in ki wallahi na yi miki alk’awari.” Ya k’arashe maganar tasa cikin sigar rarrashi.
Matar da aka kira da suna Amina cikin rashin d’a’a da rashin tarbiyya ta ce”Billahillazi Auwalu idan kaga na sake ka a gurin nan to tabbata ka bani kud’in mutane domin na gaji da wannan jirgin! da kake min yau kace kaza gobe kace kaza ni zaka rainawa hankali!” Ta k’arasa maganar ta a zafafe! Auwalu ya karyar da kansa gwanin tausayi ya ce.” Wallahi na yi miki alk’awari zan baki kud’in ki yau.” Da hayaniya ta ce. Baka Isa ba Auwalu ba za ka sanya ni na yi kaffara ba!” Hannu tasa ta fizge hular da take kansa, jifa ta yi da ita tsakiyar rumfar ta fizge tubarau d’in da ya kafa a fuskarsa ta jefar. Kwalarsa taci sosai tana wata girgiza cike da bala’i ta ce”Sai naga inda zaka je kuma wallahi idan ka yi wasa zan keta wannan sabuwar rigar taka yanzu nan.” Auwalu da takaici da b’acin rai ya ingije ta fad’i a gurun da sauri ya sunkuya ya dauki hularsa bai tsaya sawa ba ya ri’ke a hannu yana kokarin fita daga gidan. Amina ta yi kukan kura ta mik’e da sauri ta nufi inda take aje kwalaban manja da mank’ulun da take siyarwa kai tsaye kwalbar manja ta dauka da sauri ta watsa masa a bayansa lokacin da yake kokarin fita. Auwalu ya juyo da sauri yana duba jikinsa, manja ya gani a jikin sabuwar farar shaddarsa da yake bala’in ji da ita, duk cikin kayansa itace sabuwa, Kuma ya saye ta da tsadar gaske. Kamar zai fashe da kuka ya kalle ta dake tsaye a bakin k’ofar ta tana girgiza jikinta Yace.” Amina ni kika watsawa manja a jiki ko?” Da sauri ta ce”Na watsa maka d’in Auwalu ka yi abinda za ka yi, aikin banza aikin wofi kawai, wallahi sai ka bani kud’in mutane banza da kai, mazanbaci ma ha’inci kawai!” A fusace! Auwalu ya yi kanta. Ta ruga d’aki a guje ta zura sakata tana auno masa zagi!

Auwalu zuciyarsa babu dad’i ya bude d’akinsa ya shiga domin sanja wasu kayan yana nazarin matakin da zai d’auka a kanta.


“Kai! yane! bani sigari guda biyu mana.” D’anladi mai kanti ya d’ago kansa da sauri yana kallon k’wage dake tsaye bakin k’ofar kantinsa yana fito! Irin nasu na gagararru! cike da tsoro D’alladi ya ce.” Akwai kud’in Sigari uku baka biya b…… K’wage ya zaburo masa, cikin gadara da cijewa ya ce.” Kai yawa! kake malam idan za ka ba ni sigari ka bani na ware! ko an fad’a maka zamu cinye maka kud’i ne?” ‘Danladi mai kanti ya yi saurin ciro sigari kara biyu ya sanya a farar leda ya mik’a masa da sauri. Wafcewa ya yi yana wani zare jajayen idonsa! Hannunsa ya zura cikin wandonsa 3qutar yana laluben ashana babu. Sigarin ya zura a bakin sa, ya kalli Danladi me kanti tare da fad’in “Kai! e yane fa! na manta leghtar a gida kunna mini sigarin mana.” Danladi ya d’auko ashana da sauri ya kyatta ya kaita daidaita bakin K’wage.
wani irin zuk’a ya yi wa sigarin ya cika bakinsa da hayak’i ya fesa a fuskar Danladi, yana fito ya bar gurin.
tari ne ya sark’e Danladi ya rike k’irjinsa da had’e da yin zaman dirshan gurin.
BA SABON LITTAFI BA NE, YA KWANA BIYU, NA DAWO MUKU DASHI ZAN SABUNTA SHI SABODA MASU TAMBAYATA YAUSHE ZAN FARA SABON LITTAFI. KYAUTA NE GA KOWA DA KOWA, AMMA IDAN NA GA ANA COMMENTS DA SHARING KENAN. IDAN BA A YI ZAN DAINA POSTING

Series NavigationGama Duniya Babi Na Biyu >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *