*GISHIRIN*
      *ZAMAN*
*DUNIYA*
  _Daga Alâkalamin_
_Badiâat Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR đ€đ» TAKUN FARKO
Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace ya ke bayarwa ga alâumma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin zamantakewar Aure.
Kashi na farko
Babi na 1~2
Shinfiâdađ
Kano 7/2/2010 gidan cike ya ke dam da âyan Uwa da abokan arziki, wanda su ka amsa gayyatar biki na, daga gari gari. âYan uwan mahaifina da su ka kasance su ne jigon bikin, kab âdinsu sun halarci wannan biki nawa. Daga âbangaren maza a waje âyan daurin aure kuma, Kawu Sulaiman wan mahaifina shine madâaurin aure na. An cika maâkil a kâofar gidan mu dan gudanar da wannan âdaurin aure. Ni kuwa ina cikin kawayena da su ka kasance manyan mata. Dan kab kawayena babu budurwa, daga matan aure masu yara, sai zawarawa. Kasancewar na samu jinkirin aure. Shekaruna talatin da biyar a duniya. Daga gari gari a ka halarci wannan biki dan na yi gayya sosai. Abokan aikina na asibiti ma duk sun hallara, kasancewata maâaikaciyar kiwon lafiya, bangaren anguwar zoma. Farin cikin da na ke ciki a wannan ranar bai da abun misali. Sanye na ke cikin riga da siket na atamfar Soso, mai kalar green da wani ganye ganye mai ruwan madara a jikin atamfar, na yi kyau sosai, sai busa kamshin turaren humra na ke yi. Kawayena sai tsokana ta su ke ta faman yi. Aminiyata makociyarmu Amina ce ta shigo dâakin da mu ke ni da kawayena ta na haki. Dubanta nai da mamaki nace.
Ke kuma lafiya ki ke ta haki kamar wacce jaki ya ka da ita?â Ba ta ce da ni komai ba, hannuna kawai ta ja, tare da kirawo kawata Hadiza wacce ta zo bikina daga katsina. Fita mu ka yi zuwa bayan gidan mu, in da akwai rangwamen taron mata. Ta ce da ni.
âSadiya akwai fa gagarumar matsala a wannan karon ma.â Murmushin yaâke na yi, domun zuchiyata har ta gama yi mun hasashen abunda amina ta ke so ta ce.â
An fasa auran wannan karon ma ko Amina?â Murmushi na sa ke sakar ma Amina, amma cikin zuchiyata ci take da wuta babababah. Hadiza ta ce.
âAmina dukkan mu ba yara bane. Ina tunanin kwakwalwarmu za ta iya shanye komai. Ki sanar da mu abunda ke faruwa.â Yawu Amina ta haâdiye ta miâkomun wata kalanda. Hannu nasa na amsa jikina na rawa. A hankali na warware wannan kalandar. Abunda na gani shi ya tsananta bugun da zuchiyata ta ke ta faman yi, take hawaye su ka gama wanke mun âyar fuskarta. Kalanda ce mai dâauke da hoton Ahmad mijin da zan aura yau, tare da kawata Fatima. Ko da na duba date sai na ga the same date da nawa daurin auren yau. Amina na duba na ce. Ina ki ka samu wannan kalandar Amina, Ahmad dâin dama soyayya su ke yi da Fatima ban sani ba, tare zai haâda ya aure mu ko kuwa ita kaâdai zai aura, ni ya fasa aure na?â Dukka Waâdannan tambayoyin a gigice na jeroma Amina, cikin dimuwa da tashin hankali mafifici. Sau uku ana kawo sadaki na, ana fasa auran, sabida kawai na yi ilimin boko mai zurfi har ina dâaukar albashi daga asusun gwamnati. Amina jiki a mace ta ce.
âMaman mu ce, ta je bikin jiya. Shine aka rarraba kalandar, yau da na zo sai na soma shiga gida kafin in shigo nan, sai na tarad da mama bata nan, ta na nan gidan. A kan gadon ta na ga wannan kalandar. Sadiya iyakar abunda na sa ni kenan.â Lumshe idanuna na yi, ina jin son Ahmad na ninka kanshi a zuchiyata. Na ce.
Babu komai nagode. Koma mai Ahmad ya ke nufi ai zan ji zan gani, tunda yau ne daurin auran, kuma ma yanzu. A wajan na barsu na shiga ciki, ina ta gauraye hanya dan ba na jin daâdi sam, zazzabâi me mai zafin gaske ya ke shirin kwantar da ni. Kwanciya na yi a dâakin da kawayena su ke. Sai liyafar cin abinci da shan lamon kwalba su ke yi. Ni kuwa na zama kurma sai duba siririn agogon fatan da ke manne a tsintsiyar hannuna na ke yi. Zainab kawata ta ce.
âSadiya ta wajajen ina gidan da Ahmad zai sa ki ya ke?â Duban ta na yi a sanyaye na ce.
Ta wajajen Dâorayi gidan ya ke, amma bansan layin ba gaskiya.â Hadiza ta ce.
âRabu da ita Sadiya, bayan anjima anjimannan tare da ita za mu je jere, ko wannan dinma mai gidan na ki bai barki bane?â Ta jefa ma Zainab tambaya. Dariya Zainab ta yi tace.
âAhh haba dai, shima bazai hana ba, ya fa san yanda mu ke da Sadiya. Shima ya na waje cikin maza âyan daurin auren ai.â Ni dai sai bin su da kallo na ke yi. Kanwar umman mu ce Goggo Hansatu ta leâko dâakin da mu ke tace.
âKawayen amarya da su wa da su waye za su je jere ? Dan Allah ku fito ga iyaye can a wajan mota ku ake jira.â Gabana ne ya sa ke sabon bugawar da sai da na runtse idanuna. Su Amina, da Hadiza, da Zainab, ne su ka miâke tare da bin bayan Goggo Hansatu. Ni dai ina kwance ina jiran tsammanin abunda zai je ya zo.
Su Goggo su na wajan motar kayan da zata kai kayan amarya. Kawu Sulaiman da kawu Bala ne, su ka iso wajan Motar. Goggo Safiya, da Goggo Mariya âkannenshi ya ce da su. Su shiga gida ya na da magana.
Bin bayan su, su ka yi zuwa cikin gidan âdakin da ke zauran gidan, in da anan su ka sauka su maza mazan. Sawa ya yi a ka kirawo Yaya Asabe Babbar yayarsu a mata, da kuma mahaifiyar Sadiya, da kanwarta Goggo Hansatu.
Bayan duk sun hallarane, Kawu Sulaiman yace.
âToh alâamuran daurin auran yarinyar nan komai ya jagule ya damalmale. Aisha kin cuce mu da ki ka bar mana yarinya a gida harta riâka ta riâke. Ki ka kâi fur ki ba mu yarinyar nan lokacin da âdan uwanmu Adamu ya rasu. Amma Aisha ki ka yi fur ki ka hana, wai ke âyar ki karatu za ta yi, Adamun ya baki wasiccin ki bar yarinyar tai zurfin karatu. Toh yaro dai iyayenshi sun gama bincike sun ce âdan su bazai auri yar boko maâaikaciyar gwamnati ba, âyan bariki masu budadden idanu. Shine ni da Bala wan mahaifin Aliyu âdan gidan Yaya Asabe, mu ka yanke shawarar a âdaura auran da shi Aliyun kawai âdan wajan ki Yaya. Kuma Alhamdullah, Malam Bala shi ya amshi Auren har da sadaki nera dubu uku ga su.â
Yaya Asabe ta soma rabka salati tare da fashewa da kuka tace.
âShikenan ni Asabe na shiga uku. Sai da yarinya ta zama âyar duniyar da a Birni ma ta kasa auruwa, sau uku wannan ne na huâdu ana fasa aurenta. Shine Bala za ka cuce ni ka Aura ma Kâusar Yaki ita? Aisha fa sai da ta tabbatar ta raba Adamu da kab danginsa da asirinsu irinna mutan katsinawa, wacce iriyar azaba ce ba ta bamu ba, amma yanzu kâusar Yaki aka aura ma Sadiya? Wallahi bazan yarda ba.â Kawu Sulaiman ya ce.
âYaya ki yi hakâuri, ni kai na na ji abun. Kuma kinga Sadiya ta girmi Aliyu da kusan shekara biyar. Goggo Safiya tace.
â Ai juya shi za ta yi, tai ta yi mai wayo. Ni na tabbatar sai abunda Sadiya ta ce da Aliyu. âYan boko fitsararru da ba zaman aure su ke yi ba. Sun fi so a barsu sakaka sui ta cuâdanya da maza wai abokan aikinsu. Kawu Bala ya ce.
âYanzu dai bakin alkâalami ya bushe, ni ne dai Wan mahaifin Aliyu kuma ni ne madaurin Auran shi, ni kuma na amshi Aurannan domun a rufa ma Adamu asiri, shi da ya mutu ya bar baya da kâura. Yarinya ta yi kwantai kowa na gudun na shi ya aure ta. Asabe hakâuri za ki yi dan Allah. Goggo Asabe ta ce.
â yaronnan fa, da rana a kan shi. Daya dawo da wata dâaya zaâayi auran shi da Khadija âyar gidan mai gari, yarinya ga mai dambu Aminiyata. Wallahi aure kuma ba fashi.â Kawu Sulaiman. Ya ce.
âWannan ba zai gagaraba yaya Asabe, yaro zai yi auran shi duk macen da ya ke son Aure.â Goggo Asabe tace.
âShikenan yaya zan yi, cuta ce dai an riga da an cutar da ni. Yaro sai da ya zama mutum tukunna, duk wata kadarata, da gadon da shi kan shi yaron ya samu, duk ya kâare a wajan naiman ilimin addini shine har Madina. Amma zai dawo ya samu mummunan labari, wallahi bazan yi wuyar renon Kusar yakâi, da gina shi, Sadiya ta hanani cin arzikinshi ba. Tunda Adamu ya faâdi ya mutu, Aisha ita da âdiyarta ne kaâdai su ke amshe kuâdin pension dâin nashi da garatuti. shikenan na yi Allah ya sanya alkhairi.â Cikin kuluwa da takaici Goggo Hansatu tace.
âAn dâaura auran yarinya, babu wani shawara. Toh ya maganar aikinta da take yi na asibiti, daga can kauyan za ta dinga tawowa ko yaya? Sannan ya yarinya zata rayu a maraya, wayayya, mai ilimi, maâaikaciya, sannan ita ba yarinya ba. Kawai a dâaura auranta da wani Wai shi Aliyu. Ai ta na da hakki ya kamata aji ta bakinta, koma meye sai a yi daga baya. Sannan Sadiya ba yarinya bace, ta girmi Aliyu nesa ba kusa ba, wanne irin zaman aure za su yi to? Aure ba soyayya, kuma a kaita kauye shikenan a durâkusar da rayuwarta, ba zaâa barta ta amfanar da al âumma da ilimin data karanta ba? Wai me yasa ake ganin illa ne mace ta yi ilimin boko ta yi aiki, dan ta kare martabarta ta mace, da martabar kâasar ta. Mu gidanmu âyan boko ne, kuma dole Sadiya za ta ci gaba da aikinta.â Kawu Sulaiman yace.
âKe dakata Hansatu, wannan ba huruminki bane, ko Aisha bata isa ta tanka mun ba kan batun Sadiya. Domun ni ne uban Sadiya, duk duniya bata da gatan da ya wuce mu. Yarinyar nan zumunci mu ka yi ma, har aka ba ma shi Aliyun domun naga anan taki auruwa, ga shi sai girma take yi, shakaru takatin fa da biyar ai ta gama tsofewa a gida. Maganar aiki ma ajjiyeshi za ta yi, mu abunda muka sani shine âdâakin mace shine darajarta. Mu daraja mu ka ne ma mata.â Yaya Asabe ta cabke cikin daga murya tace.
âZancan kauye kuma da kuke yi, ai Adamu daga wannan kauyan ya fito kuma Aisha ta aureshi ta raba mu dashi, ko san zuwa ganin gida ba yayi. Itama dole ta je ta yi zaman aure.â Goggo Hansatu za ta yi magana Aisha ta dâaga mata hannu, dole ta yi Shiru, zuchiyarta na yi mata kâuna. Cikin raunin murya tace.
âYaya sulaiman Sadiya âyar ku ce, kuma kune gatan ta. Ni ba ku da matsala dani, Allah ya sanya albarka a wannan auran, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gare mu baki dâaya.â Ta na kai wa nan ta fice a dâakin. Goggo Hansatu kuwa ba karamin rikici su ka yi da su Goggo Asabe ba. Har sai da âyan Uwa aka shiga zancan sannan fa aka yi sulhu. Kawu Sulaiman yace.
âSafiya ina ga kuje ku tafi kai kayan Sadiyan ko? Kawayen ita Sadiyan suna wajen motar su na jira. Hansatu kuma ki kirawo ta ku tafi tare. Barayin Dauda daya gina zai sa amaryar sa nan da wata biyu shi
Za ku yi ma Sadiyan jere in yaso shi Dauda ya gina wani. Kui maza rana na yi.â Goggo safiya ba ta ce komai ba ta bi umarnin Kawu Sulaiman. Goggo Hansatu ta dubi kawayen amarya tace.
âToh
Su waye âyan kwana domun in fa mu ka je acan zaâa kwana waje ba kusa ba?â Hadiza ta ce.
âAi ina ga ni kaâdai ce zan kwana, sai Amina ko?â Zainab tace.
âGaskiya kam ni kam sai dai gobe ma bi ayarin âyan budar kai mu zo ganin dâakin amarya.â Goggo Hansatu ta yi ma su Hadiza jagora cikin motar da za su ta fi. Da ita sai Goggo Safiya, sai Hadiza, da Amina. A gaban mota kuma daga direba sai Anas wan Aliyu. Motar su Goggo Hansatu na gaba. Motar kaya na biye da su a baya.
Mahaifiyar Sadiya na dakinta, hawaye kawai ta ke ta faman sharcewa wa. Hankalinta yai matukâar tashi, shin wacce rayuwa Sadiya za ta yi a kauye, gashi an aura mata miji yaro, maganar aikinta kuma fa, shin karatun da su ka daâde suna wahala domun samuwarshi, yanzu gashi ya samu har ta kai matsayin maâaikaciyar asibiti, shikenan dangin mahaifinta sun dakatar mata da cikar burinta da manufarta kan karatun dâiya mace?.
âYa Allah kai ne ubangijin kowa da komai, ya Allah ka saukar ma da Sadiya nutsuwa da dangana, ya Allah ka sa aurannan na ta ya zame mana alkhairi, ya Allah ka raba Sadiya da makiyanta masu son ganin bayanta, Allah ka kawo mata sauyin alkhairi.â Sauke hannayenta da ta âdaga tayi, ta na zubar da hawaye. Ta rasa dalilin da yasa dangin mijinta su ka tsane ta. Dan kawai ta zama âyar boko kuma maâaikaciyar gwamnati. Shin shi ilimin Mace laifi ne, ko kuwa kasancewarta maâaikaciya zunubi ne?â Miâkewa ta yi, ta share hawayenta. Cikin dakewar zuchiyata ta tura dâakin da Sadiya take a kwance.
Sadiya
Idanuna na runtse domun har zuwa lokacin a cikin fargaba da taraddadin abunda ka je ka zo na ke. Bansan me ke faruwa ba, kuma bansan a wanne matsayi na ke ba a yanzu, matar auran da igiyoyi uku su ka rataye rayuwarta, ko budurwar da ta gaji da kwanciya a gado ita kaâdai, cike da matsananciyar shaâawa da shaukin jin dumin mijin halali a tare da ita?â
âSadiya!!! Ki sa me ni a dâaki yanzu.â Juyawa ta yi ba tare da ta ji amsar da zan bata ba. Jiki a mace tamkar kazar da ta taka wuâka haka na miâke.kawayena su kuma sai aikin zolayata su ke yi. Wai tun kamun a kaini har na riga da na karaya. Da dariyar yaâke kawai na bisu. Ahankali na dinga ratsa jamaâar biki ina bin sawun mama. Kallon da jamaâar bikin su ke bi na da shi, sai na lura ya wuce gaban misali. Take zuchiyata ta shiga kokawar fitowa da kâarfin tsiya.