Tabarmar Kashi Chapter 6

This entry is part 8 of 6 in the series Tabarmar Kashi by Safiyya Huguma

Page 06

Sai data fara busar da kanta da ya jiqe,sannan ta shirya cikin wasu cotton kayan bacci masu tsananin taushi,riga da wandon da bai sauka har qasa ba,kadan ya rage yakai idon sahu,ta mulke kanta da turaren gashi kamar yadda ta saba ya zame mata al’ada,hakanan ta shafe jikinta da nau’ikan turarukan da sai zatayi bacci take using nasu.

            Cikin sofa bed ta kalmashe qafafunta bayan ta rage haske dakin,ta ja wayarta ta kunna data,tanason shiga media ta karanta news ko zata rage tsahon daren sai taji ana knocking,ta daga manyan idanunta da suka rusuna zuwa lokacin ta kallo qofar sannan ta bada izinin shigowar. Baraka ce,cikin girmamawa ta isar mata da saqon farheen na ta fito taci abinci,kai ta girgiza

“Am okay,kice mata saida safe ma hadu” kai ta jinjina sannan ta juya zata fice

“Ammm,amma idan zan samu black tea ko coffee ina so”

“Babu amma yanzu yanzu saina hada miki”

“Na gode” ta fada a tausashe,baraka ta juya ta fita tana ja mata qofar.

             Tana shirin buda wayar saiga kira ya shigo mata,tsaiwa tayi cak tana kallon numbers din dake faman harbawa saman screen din wayar,baquwar number ce don babu ita cikin kaf ‘yan tsirarun contact da ta adana cikin wayarta. Ba kowacce number take saving ba,sai number dake da matuqar muhimmanci da amfani a tattare da ita. Wannan yasa taqi daga kiran,har ta gama ruri ta katse,saita sake kunna data din ta shiga abinda tayi niyyar yi tun farko.

             Ba’a dauki dogon lokaci ba kiran ya sake shigo mata,taja qaramin tsaki tana jin kamar tayi rejecting,amma saita fasa,taci gaba da kallon yadda wayar ke neman a kawo mata agaji,harta gaji da ɓurari ta sake yankewa,katsewarta da minti daya kacal saqo ya shigo

_”please……do me a favor,ki daga kirana koda na second biyar ne,zan gode da hakan,mahmud abba gana”_

          Wani dogon tsaki ta saki kamar zata cire halshenta,wani abu mai tauri yazo ya tsaya mata a wuya,ta lumshe ido tare da danne makashin wayarta yana kasheta gaba daya qirjinta na wani irin dokawa,kenan afifa ta raba number wayarta?,me yasa afifa zatayi mata haka,ta rufe ido kamar batasan komai ba……kamar komai bai faru ba?”. Ita daya cikin dakin amma bacin rai ya cikata,haka ta dinga hararar wayar dake ajjiye a gefe kamar itace mahmud din,cikin ranta tana qiyasta gamuwarta da afifa,a haka farheen dake cikin shigar wasu lafiyayyun kayan bacci masu matuqar kyau da daukan hankali ta turo qofar ta shigo dakin, hannunta dauke da coffe din sãahar.

           Da kallo sãahar din tadan bi farheen,zamanta da ita ta koyi abubuwa masu tarin yawa,ta kuma gane ashe a baya ita din amsa sunan mace kawai takeyi ba tare da tasan ma’anar hakan ba,sai data zauna da farheen din na tsahon shekaru biyu da Wani abun,taci gaba da kallonta cikin rai da zuciyarta tana jin inama itace farheen din,bata da wata damuwa kaf rayuwarta,Allah ya bata miji irin yaa muhyi dinta,ya kuma azurtata da zuri’a yara lafiyayyu har guda biyu,gidanta tamkar ita ta zabawa kanta shi,duk ko me takeso tana samu,inda itace ita me zata nema kuwa a duniya?.

“Gayamin ta yaya zakiyi kumari,kin kama black tea da coffee kin riqesu tsam” farheen ta fada tana dire cup din saman bedside,idanunta akan fuskar sãahar tana qoqarin karantar yanayinta da take shinshinar kamar ya sauya.

        Karamin murmushin da yafi kama da yaqe ta dan saki

“Bana jin yunwa,bazan iya cin abinci kuma banajin yunwa ba” kallonta farheen tayi tayi murmushi

“Koda bakiji yunwa ba ki kamanta ci koda babu yawa” lumshe ido kawai tayi ta gyada mata kai

“Ba wani abu da kike buqata ko?” Kai ta sake gyadawa tana qoqarin zama sosai saman sofa bed din

“To sai da safe”

“Khalipha fa?” Waiwaya kadan farheen tayi

“Kina buqatar dan tayin kwana ne?” Kai ta gyada

“Kin manta ne tare muke kwana dama duk sanda nazo?”

“Haka ne,zan sa baraka ta kawo miki shi,saida safe”

“Allah ya kaimu” ta amsa tana miqa hannu ta jawo mug din tana kaiwa bakinta.

           Ba jimawa baraka ta shigo da khalipha wanda keta faman barci,an shirya shi cikin kayan bacci da alama ya jima dayin baccin,ta kwantar mata dashi saman gadon taja mata qofar. Ko rabin coffe din bata sha ba taji ya isheta,ta maidashi saman qaramin plate din tangaran din da farheen ta hado mata dashi,ta miqe a nutse ta shiga toilet tayi brush sannan ta dawo ta rage hasken fitilun dakin,ta hanye gado tana lullubesu da bargo ita da khalipha bayan taja yaron cikin jikinta tana jin tamkar ita ta haifeshi.

           Ajiyar zuciya ta saki mai nauyi sanda ta lissafa shekarun yaron,yazo dai dai da shekarun faruwar wani abu daya sameta a baya,ta gyarawa yaron kwanciyar cikin jikinta,tana iya jinsa sanda yake sauke ajiyar zuciya,sai wasu hawaye masu dumi suka ratso ta idanunta,ta sanya tafin hannunta da sauri tana gogesu,qasa qasa bakinta na furta

“Aamantu billah, Alhamdulillah ala kulli haal” ta qarashe maganar ne tare da rintse idanuwanta hadi da tilastawa zuciyarta kauda dukka wani abu da zai kawowa mata hutu da nutsuwa cikin sassanyan daren da wata iska me dadi wadda ke dauke da hadari take kadawa. Sai Allah ya taimaketa bata jima a duniyar tunani tana bulayi ba bacci yayi nasarar daukarta yayi awon gaba da ita.

           Washegari tun bayan sallar asuba bata koma ba,wannan din kusan dabi’arta ce,tana zama ne saman abun sallah har sai alfijir ya keto gari ya danyi haske. Ko yau dinma tana zaune,tana dab da kammala addu’o’in ta khalipha dake barci farka,ya miqe ya zauna sosai saman gadon yana murza idanunsa,a nutse ta waiwaya tana kallonsa,suka dan zubawa juna ido na wasu sakanni,sai ya sauko daga saman gadon da sauri,ta bude masa hannayenta ya fado ciki ta maida ta rungumeshi tsam tana sakin murmushi

“Kaji dadin ganina?” Ta tambayeshi har cikin ranta zuciyarta na mata sanyi,sanyin daya hadu dana hasken azkar din data gama yi,ya kuma gauraya da iskar safiya me dadi dake kai kawo tana kutsowa harta windows din dakin bayan ta samu nasarar daga labulen dake maqale a jiki kadan kadan. Kai ya jinjina yana dariya

“Na cewa daddy dama ya kaini,yace sai weekends,i missed you small mom” kyakkyawan murmushi ya qwace mata,tasa hannu taja kumatunsa

“I missed you too my little dad”. Tun daga lokacin bai barta ta huta ba,akwai sabo sosai tsakaninta da khalipha din,wanna yasa yake sakewa sosai da ita fiye da momynsa farheen,yayita mata hira da tabara ita kuma tana biye masa. Allah ya halicci zuciyarta da matuqar soyayyar yara da kuma qaunarsu,duk inda taga yaro hankalinta yana kai,haka tayita hidima dashi,tayi masa wanka itama tayi,ta kintsa dakin da kanta ba tare data jira su baraka ba,taja hannunsa suka wuce kitchen abinda ta jima batayi ba,tana tambayarsa me yakeson ci,ya gaya mata ta soma fiddo kayan da zata hada breakfast din dashi.

          Mamaki ya kama lubabatu sanda ta samesu a kitchen

“Da kinyi magana saina taso na hada miki abinda kike da buqata,yau din hutun qarshen mako ne,nasan masu gidan basa tashi da wuri,shi yasa banyi safkon fitowa ba”

“Karki damu” ta amsata a taqaice,saita miqa mata abinda zata tayata dashi taci gaba da hidimar hada break din tana sauraren khalifa. Ita kanta a jikinta yau dadi takeji,ko ba komai tadan motsa jikinta,don ta jima batayi girki ba,duk da yana daya daga cikin hobbies dinta,amma wani dalili mai nauyi ya kasheshi murus daga ruhinta.

         Awa biyu ta gama komai ta zubawa khalipha komai a plate daya,yanata murna yau an hada mishi delicious,yaqi yarda ko lubabatu ta dauka masa plate din takai masa Parlor. Sãhaar na murmushin wauta da dadin quruciya irin na yaro ta sakashi a gaba suka fito.

            Suna fitowar sukayi kacibus da farheen,a shirye tsaf tana zuba qamshi,hannunta dauke da aleena da tayi mata kwalliya da wata designer overall kusan shigarta ta ko yaushe kenan

“To bismillahi,shi yasa yau banji ifce ifcensa a parlor ba,ashe an tafi inda akafi kauri” farheen ta fada tana kallon khalipha,wanda tuni shi ya samu guri yayi zaman dirshan abinsa. Sãahar dake kallon khalipha tana sha’awar rayuwarsa,bashi da wata matsala ko damuwa,abinci kam zaici duk wanda aka bashi a sanda kuma yaso,baisan ma mommyn nasa nayi ba,ta maida idonta ga aleena daketa bangala mata dariya tana kuma dago mata hannu alamun tanason ta dauketa ne

“Beauty na baxan daukeki na bata wannan kwalliyar ba,banyi wanka ba”

“A hakan?” Farheen ta fada

“muna tashi kitchen muka shiga,bari na watsa ruwa nazo muyi hira” sãahar din ta fada tana juyawa da dan hanzari

“Dubiya ma zaki rakani,kada ki jima,so nake muje mu dawo daddyn khalipha yacemin da azahar zayaje daurin aure”.

          Batason zuwa yau ko ina saboda jiya ta fita,to amma dubiya ce tasan daga asibitin ba wani gurin zasu wuce ba. Minti kusan talatin ta kwashe a toilet din sannan ta fito,ta tsane jikinta ta fara mulke fatarta da lotion.

            Cikin qasa da minti talatin ta shirya cikin vintage bubu gown ta chiffon material,ta yane kanta da dan siririn veil din da yazo hade da rigar tayi rolling dashi, kyakkyawar fuskarta ta fita ta tsakiyar mayafin,siririn agogon casio ta daurawa tsintsiyar hannunta wanda yazo ne tare da qaramar barimar data sawa kunnuwanta,don ba kasafai takeson kaya masu damu ko nauyi ba,saidai idan ya zamana ba yadda zatayi. Bata dauki komai ba banda wayarta data riqe a hannunta bayan ta feshe jikinta da turarukanta na dindindin guda biyu masu tsananin sanyin qamshi da jimawa a waje basu bar gurin ba,ta zura takalmanta masu matsakaicin tudu Golden goose brand ta fita a dakin.

           A tsaye ta samu farheen tana serving yaa muhyi dake sanye da jallabiyya,da alama tashinsa a barci kenan yunwa ta fiddo shi,don ba kasafai yake cin abincin a sassan ba.

            Tana juya masa tea ta dago ta kalli sãahar

“Tabarakar rahman” farheen ta fada tana murmushi,saboda har ga Allah ta gaza jurewa kyan da sãahar din tayi,cikin ranta da zuciyarta ta cika da fatan ubangiji ya shiga lamarinta. Daga kai yaa muhyi yayi ya kalli farheen din

“Me ya faru?”

“Bakaga auta ba?” Idanunsa ya maida ga sãahar sannan ya dawo dasu kan farheen bayan ya karbi tea din daga hannunta,shi kansa kowacce rana sallolinsa biyar tana cikin addu’o’in sa,ajjiye mace kamar sãahar din a gida abune da bazaiyiwu ba,duk kuwa girman jarrabawar data fuskanta,gidan aure shine solution.

             Cikin girmamawa ta qaraso ta gaida yaa muhyi din,cikin ranta tana addu’ar Allah ya kauda hankalinsa,kada ya sake tayar mata da dukka wata magana data shafi aikin company din nan,saidai addu’artata bata ci ba,suna gama gaisawa ya jeho maganar

“Kiran wayar professor ne ya tasheni……yanamin tuni game da batunki” shuru ne ya ratsa saboda ta rasa amsar bashi,shi kuma kamar bai kula ba ya dora

“Kiyi qoqarin hada amsarki nan kusa,don kusan nashi shirin ya kammala,cikin satin nan ko sati na gaba zaku kama aikinku”

“To,in sha Allah” ta amsa masa a sanyaye,gabanta yana dan faduwa,zasu kama aiki ko ita dawa dawa?,ta tabbatar harka ce data shafi mu’amala da maza,magana ake ta company wanda bazaiyiwu ace mata bane zallah.

           Wannan maganar ita ta sake sanyata ta zama so silent sanda suke hanyar asibiti ita da farheen,duk da cewa ita ke driving,amma yadda ta bawa kwalta dukka hankalinta ya isa ka fahimci tana wani nazari ne da daban.

             Page 07

         “yayanki ya saka hope da yawa a kanki,ya kambamaki da yawa,Allah yasa dai zaki fishsheshi” sãahar dake tsakiyar duniyar tunani ta tsinciki maganar farheen kaman daga sama. Kadan ta waiwayo ta dubi farheen,kamar zatace wani abu sai kuma ta fasa,ta sake maida kanta ga tuqin,wanda har suka isa asibitin bata kuma cewa uffan ba.

            Tunda suka shiga dakin suka gaisa da mara lafiyan da relatives na anty farheen,sai ta kama hannun khalifa suka fita a dakin,saboda idanun mutum biyu da suka fara uzzura mata,zata iya cewa tasan daya,saboda tana ganin pictures dinsa cikin hotunan farheen,dayan ne batasan daga ina yake ba,amma tana kyautata zaton dan uwan mijin thurayya me haihuwar ne.

             Ta bayan asibitin suka bi ta fara shawagi cikin asibitin,dukka guraren da take bi din gurare ne da babu yawaitar mutane sosai,sai majinyata jifa jifa,abinda ya sake karya mata zuciya,tana sake godewa ubangiji da ya barta da lafiyarta bata salwanta ha,tabbas inda burin ADAM yakai ga cimma gaci,tayi imani dari bisa dari cewa har kamar wannan lokacin itama tana cikin jerin sahun wadanda zasu qulla kyakkyawar alaqa da asibiti,idan ma bata samu gurbin zama a cikinsa ba,zaman da ba wanda yasan ranar yankewarsa da ubangijin daya qaddara mata komai.

           Tafi tafi sai gata ta bulla ta bangaren ‘yan haihuwa,cikin jiki da zuciyarta taji tana mararin shiga ta basu gudunmawa,don ta tabbatara akwai tarin mata masu raunin gaske a wajen,saidai ta manta cewar yau din bata riqo koda purse ba bare ta fito da kudi. HIBBA HASHIM ta tuna,wata qawa ga afifa dinta,idan bata manta ba kamar ta taba jin afifa na maganar anan take aiki,saita koma gefe daya ta tsaya,ta kunna wayarta wadda tun daren jiya take a kashe. Bata gama daidaita ba saqonnin kar ta kwana suka fara turereniyar shigowa da baquwar number da bata sani ba. Qaramin tsaki taja ta share saqonnin ba tare data duba ba,ta kira afifan.

          Ta bata tabbacin a nan take,kuma ana samunta a yau din,cikin minti biyu ta kira mata ita,sai gata a bakin gurin,fuskarta fal fara’a. Tanason sãahar,tana masifar burgeta,gayunta kyanta da kuma iliminta,macace me ajin da jerawar mutum kadai da ita ya isa ya sake siya maka daraja da aji,don haka cikin girmamawa ta yiwa sãahar jagoranci zuwa gurin.

           A hankali take takawa,jiki da zuciyarta gaba daya sun raunana,tsohon ciwon dake danqare a zuciyarta ya fara balle kansa,wannan ya qaranta walwala sosai daga fuskarta.

            Muryar wata nurse shine abu na farko daya fara dukan dodon kunnenta,fada take sosai kamar me shirin antayawa matar dake tsaye a gabanta dauke da tulelen ciki zagi,ba abinda jikin matar keyi sai rawa,tana kuma share hawayen dake zarto mata

“Nidai don girman Allah malama kiyi haquri,ki bani gado,idan na haihu koma meye sai ayi,amma yanzu inajin haihuwata a kusa,koda yaushe zan iya haihuwa”

“To ina ruwan wani?,ki haihu din mana,wanda yayi miki cikinma bai damu ba bare mu da rana tsaka muka ganki dashi” saita juya tana niyyar wuce matar.

           Cak sãahar tayi a wajen,ta gagara zama samam kujerar da hibba ke mata tayin zaman,a nutse ta dauke manyan fararen idanunta daga kan matar zuwa kan hibba

“Me ya samu waccan matar” baki hibba ta tabe

“Kin ganta nan,ta kawo kanta asibiti da sunan haihuwa,amma ko pant din da za’a sakawa jariri babu,bare ayi maganar katin da tayi awo kudin gado da sauran abubuwan da ba gwamnati ce take biya ba,da aka tambayeta ina mijin sai tace ta baroshi gida yana bacci,muka ce lallai sai yazo,saboda yaronta breach ne,zamuyi qoqarin gyara masa kwanciyarsa,idan an samu nasara shikenan,idan ba’a samu ba dole sai ya biya kudi anyi mata C.S. Dajin haka hankalinta ya tashi,muka bata aron waya ta saka numbers dinsa ta kirashi,wallahi sai data kusa kiransa sau goma kafin ya daga,da gasken kuma baccin yakeyi abun mamakin,daya daga yaji itace sai cewa yayi ‘dalla malama meye?’ tayi masa bayanin komai,amma budar bakinsa cewa yayi,kada ta dameshi,idan ya gama baccin zaizo,idan zata iya jiransa ta jirashi,idan ba zata jirashi ba tayi duk yadda taga zata iya,sai ya kashe wayarsa…..kinsan abun takaicin?” Kasa cewa komai sãahar tayi bare ta amsa mata ba,duk da hakan hibba bata damu ba ta dora

“Dukka kudin matar nan idan tayi aikin tayi wahalar mijin take bawa wai a taru a rufawa juna asiri,wallahi duk da abinda yayi matan nan muna ta masifa amma bashi kariya takeyi a fakaice,abinda ya bamu haushi kenan mu duka,har yanzu kuma in gaya miki baizo ba,maganar da nake miki tun jiya fa abun nan ya faru,kudin data tara inda a hannunta ta ajjiye ba yaro daya ba ko biyar zata haifa zai mata komai ba” idanunta sãahar ta mayar ta rufe tana jin wani radadi tun daga cikin idanuwan nata har zuwa zuciyarta

“Allah ya tsinema makahon so” kalmar ta subuce daga bakinta ta fita da wani irin zafi da amo me motsa rai da zuciya.

“Wallahi kam” hibba ta amsata ba tare data lura bada ita take ba

“Kuyi mata komai ni zan biya,ku bani number wayar mijin nata,he must pay na duk neglect dinsa akan matarsa,ba baiwa bace d’iya ce kamar yadda yake d’a ga wasu” ta fada a mugun zafafe. Har yanzu maza suna bautar da mata?,har yanzu maza suna amfani da raunin ‘ya’ya mata suna cutar dasu,suna illata su,wadda ke kan wani doro mai matuqar hatsari ga dukka rayuwar kowacce d’iya mace na mutuwa ko rayuwa ma basu barta ba bare me lafiya?. Ta daga idanunta da suka canza launi daga inda take zaune tana duban inda matar ke tsaye,kallo daya zakayi mata ka tabbatar tana cikin tsananin tashin hankali,kuka kawai takeyi,bata ko duba da cewa ita din ba qaramar yarinya bace,taimako da agaji kawai take nema,ya manna mata abinda zai iya zama ajalinta ya kuma gaza bata kulawa a sanda tafi buqatar hakan,koda da kudinta ne wanda ta hada da guminta da qarfin jiki dana zuciya,ba tare datayi la’akari da nauyinta yana bisa wuyansa ba

“Ina danginta?”

“Ba ‘yar nan qasar bace,aurota yayi,kamar nijer naji tace” daidai sanda hibba ta gama bawa sãahar information matar ta kama qugunta ta durqushe tana murqususun dake nuna ciwonta ya fara kankama da gaske. Sãahar din na tsaye sanda nurses din suka kamata bisa jagorancin hibba suka shiga labor room din da ita. Kasa zama tayi,wani tsumammen bacin rai yana taso mata kamar zai shaqeta,wasu abubuwa da suka shude mata cikin rayuwarta a yau suka fara motsawa,suna son dawo mata da abinda ya shude a baya, situation din da matar ke ciki yayi mata baban famin data kasa shanyewa,saida wasu hawaye masu zafi suka sauko mata,ta saka tissue din data riqo a hannunta saboda khalifa ta daukesu a mugun sanyaye.

           Muryar farheen ce ta katseta,ta waiwaya daga sashen da takejin amon muryar tata

“Nayita nemanku ban ganku ba,inason nace ku dawo ciki,dakin babu kowa” farheen ta fada tana karantar wasu abubuwa masu zafi dake fita daga qwayar idanun sãahar. Kai ta girgiza

“Zan shigo,amma saina gama wani dan aiki a nan”

“Patient dinki ta sauka fa,ta samu baby girl” muryar hibba dake qarasowa gurin da hanzari ta katse tambayar da farheen ke shirin jefawa sãahar

“Alhamdulillah” sãahar ta fada tana lumshe idanunta,har cikin ranta tana jin bacin ranta yana raguwa,wanne irin sa’a akayi haka komai ya daidaita cikin hukuncin ubangiji?,ba tare da ankai ruwa rana ba duk da babyn ba’a dai dai take ba?.

        Tun kafin farheen ta jefa tambayarta ta gama karantar komai, saita harde hannuwa tana saurarensu ita da hibba har suka gama maganganunsu,hibba ta koma dakin ta gani idan an gama gyara babyn ta dauko musu ita.

“Amma……daga haka ba wani abun zaki sake aiwatarwa ba?” Farheen ta tambayi sãahar sanda taga tana latsa wayarta. Karamin murmushi kawai ta fidda ba tare da tacewa farheen komai ba,ta riga ta qudirta a ranta,sai kuma ta aiwatar. Bugu biyu aka daga wayar daga can bangaren,suka kuma fara magana da matar dake riqe da wayar a daya sashen.

           A nutse farheen ta dauke dubanta daga kan sãahar dake shigar da qorafi tamkar aleena ko afifa aka yiwa hakan ta juya ga bayanta,inda muryar magidancin da duka duka bazai wuce shekara arba’in ba a duniya ke tashi cike da hayaniya da kuma hargowa,cikin nuna zallar gogewa a rashin mutunci.

Page 08

        Daga shigowarsa zuwa isowarsa gurin duka duka mintuna qalilan amma ya cika wajen da hayaniya da fadace fadace,sãahar ta lumshe idanunta tana jin wani bacin rai yana sake ratsata,ko ba’a gaya mata ba ta tabbatarwa kanta wannan shine mijin matar,sai taja kujera kawai ta zauna tana qare masa nazari hankali kwance,domin tayi imanin babu abinda zai hanashi karbar hukuncin dukka wannan haukar tashi.

*_Bayan awa d’aya_*

          Duk da yadda lamarin ya zamo mata Wani babban fami a rayuwarta,amma sai ta dinga jin nutsuwa tana shigarta da aikin data aiwatar yau cikin asibitin,duk kuwa da cewa bata da Wani relation da matar,amma tana jin tayi abinda ya kamata na ceto ta daga azzalumin namiji data tabbatarwa da kanta ire irensa suna da yawa a duniya,wasu matan da yawa saidai a lahira ubangiji zaiyi wannan hisabin,don basu da gata basu da me tsaya musu,babu kuma me qwato musu yanci da haqqunansu da mazan suka sanya takalma suka tattake. Karon farko taji tana da sha’awar bude qungiyar da zatayi aiki akan ire iren wadan nan zalunci da akewa mata,to amma gaba daya bata da wannan qwarin gwiwar a yanzu,ita kanta akwai sauran tarin matsaloli da qalubale,wasu sun shude wasu tana cikinsu,wasu kuma jikinta yana bata suna gaba suna jiran isowarta

“Sannu da aiki” farheen ta fada sanda sãahar ta saka key tana qoqarin kunna motar bayan ta kammala duk abinda ta qudirta yi a asibitin.

            Waiwayowa sãahar tayi ta kalli farheen din,qaramin murmushi yana subuce mata,duk da yadda zuciyarta ke wani irin zafi,tanason lallai saitayi mata bitar tata rayuwar,yayin da ita kuma ya sanya dukkan wani qarfi nata tana tanqwarata,tare da gaya mata bata da wannan buqatar,sãahar din bata amsa ba ta tayar da motar cikin nutsuwa tayi reverse suka fice daga harabar asibitin,anty farheen na sake jinjina mata qoqarin da tayi,da kuma yabawa sãahar din kan hannun wadanda ta danqa me gidan matar,ta tabbatar matat zata samu adalci.

           Saboda raunin da zuciyarta ta samu wannan ya sanya takejin jikinta gaba daya ba qwari,don haka suna isa gida ta fidda kayan jikinta ta watsa ruwa,ta sanya wata riga me taushi da akayita da zallar auduga,ta rage ribbom di kanta tabar wani siririn band.

           Tana zura slipper a fara sol din qafarta wayarta dake yashe saman madubi ta dauki tsuwwa,a kasalance ta isa gaban madubin tana kallon wayar. Baquwar number ce dai still,sai ta kauda kanta daga kallon wayar,sai a sannan ta tuna da saqonnin da ta gani a dazu,taja qarami tsaki tana barin gaban madubin,ta wuce Parlor abinta.

           Kadan ta taba abincin ta baro anty farheen acan ta dawo daki,idanunta akan agogo,tanason ganin lokaci zai bata daman yin baccin awanni biyu kafin sallar magrib,sai qarar wayarta ta sake mata kutse cikin tunaninta. Wannan karon tun batakai ga wayar ba ta fara jan tsaki,tana jin haushin kanta da bata sake kashe wayar ba.

               Sai data daga sannan ta lura da sunan BESTIE,tadan karyar da kanta gefe tana maqala wayar a kunnenta,ta koma bakin gadon ta zauna qafafunta zube a qasa tana sallama cikin lallausar siririyar muryarta

“na gode sosai bestie,na gode,kin gwadawa mahmud iya matsayina a wajenki,na gode”

“Oops……” Sãahar ta fada a hankali tana dora yatsunta saman goshinta,she really need a rest……ga afifa da tata rigimar a gefe

“Dama munyi haka dake?,ko ya nemi izinin kirana?”

“Oh sorry,na miki shishshigi ko?,am so sorry” afifa ta fada tana gimtse wayar. Siririn murmushi ya qwacewa sãahar,ta sani sarai rigima afifan keji,dakuma son cusa mata mahmud din qarfi da yaji,batasan yaushe ya samu wannan fadar haka a wajen afifan ba,har takeson mata tutsu saboda shi.

          Aje wayar kawai tayi gefe ba tare data bi bayan afifa ba,tasan zata gama fushinta ta huce ne,infact ma a yanzu hutawa takesonyi,idan ta tashi koma meye taji dashi. Ta sauke ajiyar zuciya ta kwanta sosai a tsagin hannun damanta kamar yadda ta saba,ta lumshe manyan idanunta a hankali,eyelashes dinta masu tsaho da baqi suka yiwa kyawawan tsagar idanunta rumfa.

*********K’arfe takwas da mintuna na dare agogon dake maqale a bangon falon ya nuna,farheen na tsaye daga dining area tana hadawa yaa muhyi fruit salad,daga qasan falon kuma,can saman qawatacce kuma lallausan carfet din da aka yiwa Parlor din ado dashi,sãahar ce zaune,sanye cikin wata farar long sleeve shirt turtle neck da aka yiwa adon flowers qananu daga wajen qirjin da pink flowers,kanta babu dankwali sai band data matse gashinta daketa qyalli yana daukar idanu,duk da cewa dare ne,amma hakan bazai hanaka jin sassanyan qamshin da jikinta yake fitarwa ba,wanda ya riga ya gama runewa a jikin fatarta komai gumi da zafi,fuskarta tayi wani fresh farinta me surkin ja ya bayyana sosai,duk kuwa da cewa ko dan kunne babu a kunnuwanta amma hakan baya hanaka hango baiwar kyan da Allah ya bata. Aleena na zaune tsakiyar qafafunta,khalifa kuma yana zaune daga gefanta tana masa homework. Lokaci lokaci farheen na daga kai tana dubansu sannan taci gaba da aikinta,yanayin yadda sãahar din ke matuqar son yara zai baka mamaki,a haka a ido sam batayi kama da meson yara ba.

           Sallamar yaa muhyi cikin Parlor din ita ta tashi karatun,khalipha yayi gurinsa da gudu aleena ta fara daga masa hannu tana bangale masa da dariya,dole ya qaraso ya dauketa,ya zauna saman kujera yana ji dasu duka su biyun,da khalipha dake surutu,da aleena dake gwaranci.

“sannu da zuwa yaa” sãahar ta fada tana miqewa tsaye da zummar barin falon. Waiwayowa yayi yana dan karkata hankalinsa a kanta

“Barkanki khadijatou”

“Ya aikin?” Ta sake fada tana duqawa ta dauki wayarta

“Alhamdulillah…..zan shiga ciki yanzu zan watsa ruwa,after one hour ki sameni”

“Okay” ta fada tana jinjina kai,sai ta juya ta wuce zuwa dakinta tana jiyo ‘yar hayaniyarsu da yaran.

             Saman sofa bed ta zauna tana gwada kiran afifa wadda ta dauki fushi da ita,bugu biyu ta daga

“Me kika kirani kice min?”

“Relax mana” ta fada very calm

“Dadina dake hayaniya sa saurin daukan temper”

“Eheeen,ya muke dake?” Maganar ta saka sãahar sakin qaramin murmushi saman kyakkyawar fuskarta,tasan magana ce kawai afifa keson gaya mata

“Koma ya muke din ba wani abu bane,nayi miki laifi kiyi haquri,am sorry” ajiyar zuciya afifa ta sauke,sãahar din tana da wata baiwa cikin halaye da dabi’unta,tasan dukka hanyar da zata zauna da kowa da zamantakewa ya hadasu,hakanan tasan hanya mafi sauqi na sauke mutum daga kan fishinsa nan take

“Is ok”

“Everything will be alright……but for now please,ki manta da issue dinsa…. mahmud ko?” Ta fada calmly. Idanu afifa ta fidda kamar tana gabanta

“Ya salam…… you can’t remember his name sãahar,Allahu yahdik” ta qarashe maganar tana dafe goshinta

“Whatever afifa,i need space don Allah,ki dakatar dashi”

“Zan gwada”

“Zaki gwada….. like how?”

“You are more than you think,ya dauki al’amarinki da girma sãahar,ba lallai don na mishi bayani ya fahimta ba”

“Ya rage nashi” ta fada very careless tana dage kafadunta. Ita gaba daya al’amarin maza baya burgeta sam,ko meye zasuyi,shin meye bata gani ba?,wanne hali nasu ne yayi mata saura?,hirar gaba daya bata burgeta don haka ta sako wani topic din daban.

              Sai da suka cinye awa dayan da yaa muhyi din ya bata sannan ta ajjiye wayar,ta shiga bandaki ta daura alwala,ta dawo ta fidda abaya ta dora saman rigar jikinta,ta yane kanta da mayafin abayar.

             Duk da agurguje ba tare kuma da nufin tayi kwalliya ba ta shirya,amma kyanta ya fita sosai,zakayi tsammanin zama tayi tayi wata kwalliya ta musamman,tana da baiwar komai ta raɓa a jikinta yi mata kyau yakeyi.

            Cikin takardu ta sameshi,gefansa ta zauna tana wasa da yatsun aleena dake zaune jingine da pillow don kada takai ga faduwa,ya dubeta yana ture takardun gabansa,ya zaro wani file mara nauyi,saidai ya banbanta da dukka takardun wajen,bangonsa fari ne tas,anyi masa ado da zaiba,kallo daya zakasan na musamman ne ko kuma yana dauke da wasu muhimman bayanai.

            Budawa yayi daya bayan daya yana dan dubawa cikin nazari,daga bangon farko har zuwa bangon qarshe,sannan ya maidashi ya rufe,ya ajjiye shi a tsakaninsu yana kiran sunanta idanunsa a kanta

“Na’am yaaa”

“Kiyi haquri na miki laifi,na karba takardun amsar aiki daga MT GROUP OF COMPANY,ba tare dana jira jin hukuncin da kika yanke ba,am sorry na miki katsalandan” kanta ta daga a hankali,ta sauke dubanta ga yaa muhyi din tana jin wani abu me nauyi yana sauka saman kanta zuwa qirjinta,wani abun kuma da bata tantance meye ba yana mamaye qirjinta,maganganun nasa sunyi mata nauyi qwarai,saboda bata zaci jinsu a wannan lokacin ba,saidai abu daya da take tunawa,yaa muhyi din yafi qarfin komai a wajenta,ta tabbatar shi din masoyi ne me qaunar dukka wani abu da zai baiwa zuciya da rayuwarta farinciki,bijirewa saka hannun karbar aikin dai dai yake da ta tozartashi

“Ga file din ki wuce dashi daki,ki duba sosai ki saka hannu a duk inda ya dace,amma kafin sannan,har yanzu kina da chance,idan kikaji baki nutsu ba ko baki gamsu ba,kada ki damu ki dawo da dukka takardun” ya fada yana miqa mata su.

            Hannu ta miqa itama ta karba,sannan ta miqe cikin sanyi da mutuwar jiki,kamar wadda aka bibbigewa gwiwoyi ta doshi qofar fita,yaa muhyi din ya rakata da kallo har sai data bacewa ganinsa. Kansa ya jinjina,cikin ransa yana fatan saituwar al’amuranta,yana jin kamar ya runtse idanu ya bude yaga sãahar dinsu ta baya ta dawo,ba wannan sãahar din da duk wani buri na rayuwa ya fice daga rayuwarta sa tunaninta ba da mugun gudun tsiya,sanadin wani abu daya shude shekara biyu baya.

           Kamar wani abun tsoro haka ta ajjiye file din saman madubi,ta koma gefan gado ta zauna,ta dafe gefe da gefe da dukka tafukan hannayenta tana kallon file din daga inda take zaune tamkar wadda ke nazarin karatu daga allon computer,tako ina tana jin sanyin jiki,mutuwar jiki dama rashin karsashi,saidai ko daya cikin istikharar data sanya a gaba takeyi bataji a ranta ta fasa aikin kota watsar da tayin yaa muhyi ba.

Page 09

           Kwana file din yayi a nan,bayan sallahr asuba ta kammala azkar dinta ta jawoshi tana zaune daga saman abun sallarta,ta buda a hankali ta fara karantawa kamar yadda yaa muhyi yace tayi din.

            Very interesting,komai na kamfanin a tsare yake cikin wani tsari mai burgewa,banda batajin son aikin cikin ruhinta zata iya cewa company din ya burgeta,kuma kamar tana da gudunmawar da zata iya bayarwa tabbas gurin saitashi. Tsayawa tayi cak da biron dake hannunta bayan ta kammala signing tana duban sunan CEO din dake rubuce cikin ruwan gold daga gefen takardar MUHAMMAD TAUFEEQ. Zame hannunta tayi a hankali daga saman takardar tana kallon sunan,a hankali tunaninta ya koma can baya,sai yanzun ta tuna yaa muhyi ya gaya mata zasuyi aiki ne tare da yaronsa

“Jaffal qalam” ta fada can qasan ranta tana maida file din ta rufe,ta riga ta saka hannu,tabbas data janye,batason a kaita sashen da zatayi aiki tare da kowa,amma ya zatayi?,yaa muhyi ya riga ya daureta da jijiyar jikinta.

          A gaggauce ta isa parking lot na gidan sanda yake shirin shiga motarsa,ya dakata ya waiwayo yana dubanta tana dan haki saboda saurin da takeyi,file din ta miqa masa

“Ya akayi?” Ya tambayeta tun kafin ya buda bayan ya karba

“Na cike yaaya” ta fada tana langabe kanta,sosai murmushi ya wadaci fuskarsa,alamun maganar tayi masa dadi sosai,ya fara buda file din ya duba sannan ya dora idonsa a kanta

“Thank you sisi,na gode da baki bani kunya ba baki kuma watsa min qasa a ido ba” yadda yayi appreciating nata saita kasa neman komai daga wajensa,ta saki qaramin murmushi ta gyada kai kawai

“Next week on Monday zaki fara shiga office dinki,komai da kike buqata kiyimin magana baki da matsalarsa in sha Allah,already shi partner din naki ya fara shiga cikin wannan satin” yana maganar yana danne danne a wayarsa. Daga kai yayi

“Na saka miki kudi ko zaki buqaci yin siyayya”

“Oh no yaaya,ina da kudi a account dina fa,sannan last week yaa Saifullahi ya sakamin shima”

“I know,hal jaza’ul ihsani illal ihsan” kai ta jijjiga a hankali,sai taji cikin ranta tana jin dadin abinda tayi masan,tunda shima har qasan zuciya da fuskarsa abun ya faranta masa.

           Ciki ta koma ta fara shiryawa don wucewa gida,already dama tana da intention na zuwa yin shopping din,akwai kayayyakin amfaninta da sukayi low.

**********Lafiyayyun motocine qirar range rover baqaqe sidik ke wulwula gudu saman kwalta wata nabin wata har guda hudu a jere. Tun daga inda suka taho wato cikin filin sauka da tashin jiragen saman malam aminu kano wato aminu kano international airport har zuwa cikin rukunin gidajen dake unguwar nasarawa GRA,duk inda suka gifta daukan idanu da kuma hankulan al’umma sukeyi tare da saka kokwanton cikin zukatan al’umma na tunanin mamallakan motocin da babu cikakkiyar number a jiki kamar ta kowanne abun hawa,sai wasu qididdigaggun haruffa da kuma lambobi da sukazo a jere data sauran kowacce mota dake bin ‘yaruwarta.

         A hankali suka nutsa cikin nasarawa,sannan kai tsaye suka fada titin guda abdullahi road,kafin su tsaya qofar bristol palace. Cikin gaggawa kuma security din dake tsaron qofar gidan suka wangale musu gate ba tare da tsananta bincike ba,dukka motocin suka shige ciki,suka kuma samu wajena gurbin da aka tanada don ajjiye motoci suka faka. Cikin qasa da minti daya dukka qofofin motar suka bude banda guda daya tak,mutanen dake ciki sanye da baqaqen suit suka firfito,kowa ya samu guri ya tsaya,biyu daga cikinsu kuma suka bi hanyar da zata sadasu da reception na hotel din cikin sassarfa.

          A qalla mintuna biyar kyawawa sai ga mutum biyu daga cikinsu ya dawo,cikin azama da zafin nama ya isa ga motar dake tsaye dukka qofofinta a kulle yayi knocking baqin glass din motar,aka dan zugeshi kadan,yayi magana ta mintina sannan yabar wajen,ya koma bayan motar ya dage,yasa hannu ya fidda wasu kyawawan luggage guda biyu,biyu daga cikin mutanen dake tsaye daga bayansa suka matso,kowa ya riqe guda daya,sannan ya sake zagayawa right side na seat din bayan motar ya bude qofar,yaja baya cikin girmamawa don bawa mamallakin motar fitowa.

           Sakanni sittin cif kafin qafarsa ta fara fitowa,Sannan ya zuro qafarsa cikin kyakkyawan takalmi qirar kamfanin hermes na qasar france,sai daukar idanu yake saboda tsananin kyau da tsafta,ya sake daukar wasu sakannin kafin ya zuro dukka jikinsa zuwa waje. Zara zara yatsun hannunsa ya sanya yana qoqarin cire wayar dake maqale a kunnensa,kyakkyawar fuskarsa mai cike da wani irin kwarjini haiba da cikar zati a dinke tsaf!,babu alamun fara’a ko kadan tattare da ita.

             Fari ne,amma ba zaka kirashi kar ba,wani irin fari da bai cika haske da yawa ba,me murjajjen jiki da babu wani waje da yake a rame ko ya nuna alamun qashi,saima qaqqarfar siffarsa da cikakken zatinsa daya nuna kansa da kansa ta jikin lallausan yadin vicuna mai asalin kyau da tsada dake jikinsa,wanda aka yiwa wani irin dinki na musamman mai jan hankali,duka duka tsahon rigar bai wuce gwiwarsa ba,dogon hannu ne da rigar daya bai qarasa tsintsiyar hannu ba,an qawata hannun rigar da wasu irin links masu zubin gold,daga qasansu kadan kuma kyakkyawan agogon hannu ne baqi qirar kamfanin Casio daya kwanta luf saman fatarsa dame lullube da gargasa baqa sidik mai santsi,wadda ta fito har zuwa saman hannunsa da kuma saman kowanne yatsa nasa,zobe ne qwaya tal daga tsakiyar hannun nasa na wani irin qarfe mai daraja,wanda shi ba gold bane,hakanan ba azurfa ba.

              Yadda sumar kansa take baqa sidik a nannade sannan kuma a kwance,hakan gashin daya qawata gefe da gefen fuskarsa,zaka iya kiransa qasumba,saidai baiyi kama da qasumba hakanan baiyi kama da saje ba,saboda wani irin gyara na musamman da akayi masa,wanda yasa yafi qasumba kyan gani,yafi kuma saje tsari da qawatuwa,tun daga kumatunsa zuwa habarsa,ya kuma hade da qasan hancinsa. Baqar sumar da baqin yadin dake jikinsa suka hadu suka haska farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Eye glasses din daya sanya kuma ko kadan bai boye kyawawan qwayar idanunsa ba dake da wani irin shape mai matuqar fusgar hankali,idanun dake cike da wani irin kwarjini mai tarin yawa,kwarjinin da a kullum yake lullube da fushi da kuma fusata.

           Ko yaya ka qara taqi kadan kusa dashi kana iya shaqar daddadan qamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaqeshi,ya kuma qara kwarjini ga ma’abocin qamshin.

            Dukka hannayensa ya zube a aljihun lallausan yadin jikinsa,ya kuma daga kai yana kallon tsororuwar ginin hotel din cikin kamewa da nutsuwarsa,tamkar wanda yake nazarin wani abu,yayin da dukka mutanen suka zamana a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Iska ya furza ya taka zuwa gaba,abinda ya sanya mutum biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi,yayin da daya daga gefansa wanda ke riqe da wani babban folder ya matso gefansa kadan

“May I continue sir” ya fada cikin matuqar girmamawa a russune,da hannu yayi masa nuni da eh,yaci gaba da takawa shi da sauran mutanen,yana biye dashi yana karanto masa komai daki daki. Dukkansu suka fara kutsa kai zuwa cikin main entrance na hotel din.

            A gaggauce suka wuce zuwa lipter da zai sadasu da dakin da zai sauka,cikin mintunan da ba zasu wuce sakanni sittin ba ta tsaya,suna biye dashi har a sannan ta bude dukka suka fito. Kai tsaye har zuwa qofar dakin. Daga daga ciki yayi scanning card a bakin qofar,tayi qaramar qara alamun samun izinin shiga.

           Palace suit,babban dakin dake da aqalla zai iya daukar mutum bakwai cif,two ensuite bedroom da kuma master bedroom guda daya,living room dining room kitchen da kuma corridor. Wannan shine cikakken zabinsa ga masauki,bayason takura bayason matsi,duk sanda tafiya ta kamashi zuwa wani gari da bashi da gida nashi mallakin kansa,ko kuma yake buqatar kebewa ko sauka ya huta sosai ba tare da kowa yasan ya shigo ba.

           Yadda yayi cak a tsaye yana sauraron bayanin da inyamurin ke kwararo masa haka sauran mutanen da suka shigo tare dashi suke a tsaye,dukkansu na jiran wani umarni nasa ne. Sosai ya kafe mutumin da idanu,duk da cewa bai kalleshi ba amma tsantsar kwarjinin da idanunsa ke dashi ya hudashi,tun daga fatarsa har zuwa jinin jikinsa ua harbawa kwanya da zuciyarsa,take muryarsa ta fara rawa,ya fada kwan gaba kwan baya cikin bayanansa,sai ya lumshe kyawawan idanunsa kawai, qwaqwalwarsa ta fara kaishi inda yake zato ko hasashe.

“Where is musaddiq?” Karon farko da muryarsa me taushi da wani irin amo a cikinta ta bayyana cikin sigar tambaya da alamun gajiya da jin soki burutsun bayanan da ake masa. Daya daga cikin mutanen ya matso da hanzari ya amsa masa

“Sir…..on his way”

“Ka kirashi,ka gaya masa yayi sauri,idan yazo ya karbi dukkan folders din dake hannun peter kafin ya nemeni,you can go” ya fada a taqaice yana sanya kansa ciki.

             Gaba daya gumi ya rufe mutumin da aka kira da peter din,tabbas yasan qaryarsa ta qare,tun daga watan da aka sanar da yiwuwar zuwansa kamfanin,yaketa shige da ficen ganin ya binne komai,ya kuma rufe bakin dukka wanda zaiyi ruwa da tsaki wajen kawo tarnaqi cikin walwalarsa,sai gashi a karon farko……tun ba’a je ko ina ba alamu sun fara nuna kansu. Ya san yaron sarai,bawai tun yau ba,aiki ya taba hadasu sau daya tak dashi kafin su suma ya karkata hankalinsa zuwa wata qasar,bai kwashe da dadi a hannunsa ba,yaji babu dadi qwarai,sai gashi wata mummunar qaddarar ta sake dawowa tana neman budadeshi.

Page 10

          Har yayi taku biyu mutumin da yafi yawan magana dashi yadan sassauta muryarsa

“Am sir,am sorry…..akwai mutum biyu dakeson zama dakai,yanzu haka suna zaman jiranka”

“Who and who?” Kadan ya buda wani dan qaramin abun rubutu dake hannunsa sannan ya gaya masa sunan

“Mr Paul and mr isaac” fara takawa ya sakeyi zuwa ciki sannan ya amsashi

“Tell them to give me an hour,I will take a bath”.

              A nutse ya tura daya daga cikin dakunan daya fi zabar zama a ciki,rabin hankalinsa nakan wata qaramar wayar hannu ‘yar firit me qarancin tudu yana latsata. Ya lalubo wata number ya fara kira,dai dai sanda ya zauna gefen sofa bed,idanunsa na bisa fuskarsa data fito tarwai ta babban madubin dake dakin,sai kayi tsammanin ita yake kallo,saidai ko kadan,tunaninsa ya lula wata duniyar daban.

             Ba dadewa na’ura ta gaya masa layin a kashe yake,yaja tsaki yana sauke wayar a kunnensa,ya sake laluba wata number,wadda ita din bugu daya ta shiga.

            Muryar dattijuwa ce ta bayyana cikin wayar,muryar dake nuna zallar dattijanka da kamalar mamallakiyar muryar

“Barka da dare yallabai” shine abinda ta fara fada bayan amsa mata sallamarta da yayi

“Barka,kuna lafiya?”

“Lafiya qalau walhamdulillah……yanzun nan tayi barci ko mintuna goma batayi ba” lumshe idanunsa masu kyau da daukan hankali yayi

“Alright……a shafamin kanta” kafin ta sake cewa komai ya katse wayar,ya durqusa a mugun kasalance yana zare takalmin qafarsa zuwa socks yana cillarwa waje daya,gaba daya yayi loosing duk wani interest akan aikin,abban bai taba nufarsa da wani aiki da yaji sam bayaso ba irin wannan,baisan me yasa ba.

           Sai daya cire kayan jikinsa tsaf ya daura babban towel ya wuce bathroom. Wanda a qalla sai da ya shafe mintuna nasu dama kafin ya fito,tamkar wanda yake sauya fatar jikinsa.

            Lokacin daya fito din ya samu na’ura na gaya masa yana da baqi a living room,ya kauda idanunsa da suka dan canza launi sakamakon shigar ruwa cikinsu ya mayar ga madubi yana qoqarin tsane sumarsa data jiqe da ruwa,abu guda daya tak da zai fara gaya maka shi din ba asalin bahaushe bane,yana da jibi da wani yaren da aka sansu da irin wadan nan sumammakin.

            Kamar babu wanda yake jiransa haka ya kammala shirinsa a nutse cikin wasu farare qal din pajamas,ya zura dogayen qafafunsa wadanda kamar basa taka qasa cikin wasu lausasan baqaqen flip flops,sannan ya kwashi wayoyinsa ya wuce zuwa living room din.

            Mutum biyu ya samu a zaune,daya yasan da zuwansa,dayanne baiyi tsammanin zuwan nasa ba a dai dai wannan lokacin. Dukkansu suka miqe,daya matashin dake sanye da wata danyar shadda getzner daketa faman maiqo da qyalli ya miqa masa hannu kai tsaye sukayi musabaha,cikin salon da kana kalla zakasan akwai sanayya da shaquwa me qarfi a tsakaninsu,duk da fuskar dayan bata nuna hakan ba,har yanzu dai tana nan a yanayinta na dazu,daurewa da kuma rashin walwala. Matsowa daya matashin yayi,cikin girmamawa ya russuna

“Barka da yamma” kai yadan gyada masa sannan yace

“I hope ka karbi komai kamar yadda nace?”

“Eh na karba,but yace na gaya maka…..” Kasa qarasawa yayi yana dan sosa kansa kadan,a nutse ya zauna,ya kuma zuba masa idanu bayan ya dora qafarsa daya akan daya,yayi relaxing sosai cikin kujerar,abinda ya sanya musaddiq ya sake diriricewa kenan,ya kuma yi nadamar karbar saqon peter

“Idan baka da abun cewa get out,i don’t have time to wasted” salin alin musaddiq ya sanya kai zuwa waje,don bayajin zai iya qarasa fadin saqon,kwarjininsa yayi masa yawa,yana saka kai zai fita,daya daga cikin ma’aikatan dake aiki a restaurant din dake hotel din ya sako kai dauke da dukka nau’in kayayyakin buqata naci da nasha,wanda daya daga cikin aikin ma’aikatansa ne wato jibril,he’s very serious akan dukka abinda yakeso,kafin ya fada anyi,wannan ya sanya yake ji dashi matuqa,baya kuma rabo dashi duk inda zashi.

              Tsaf aka shirya komai,jibril kuma ajjiye masa wanda zaici a dining room,sannan ya sanar masa

“Saina gama da mr isaac first,but before…..” Sai ya waiwaya gareshi

“Kana da buqatar wani abu ne?” Kai ya girgiza

“No,banajin gaskiya”

“Okay,i will be back,zan sallamesu……ban cup daya na coffee” ya buqaci hakan.

          A duniya idan ka cire mahaifinta da yayyenta maza guda uku da Allah ya bata,babu wata sauran halitta ta d’a namiji data yarda dashi,babu wani d’a namiji da take masa kallon me imani,babu kuma wani d’a namiji da take dubansa a mazaunin nagartacce,dukkansu tana aunasu ne kan mizauni guda,ma’auni guda da kuma dabi’a guda daya,suna kuma tafiya ne a nata ganin kan tafarki guda.

            Su biyu ne cikin motar kan hanyarsu ta dawowa daga shopping ita da ya zaid,suna tafe a hankali yana qoqarin cusa mata ra’ayin aikinta,ta bashi aron kunnuwanta kawai,bawai don tana jin qaunar abun ya shigeta ba,abinda ta lura dashi dukkansu suna supporting aikin,suna kuma so tayi,ta karanci a nasi ganin suna hasashen hakan zai rage mata zaman kadaici ne,yayi attaching nata sosai da mutane,ya dawo mata da dukka yarda aminci da walwala da kuma mu’amalarta da kowa yadda take a baya.

            Signal din da taga ya saka yana niyyar shiga guda abdullahi road bayan suna kan hanya dai dai shi yadan ja hankalinta

“Yaa zaid…..ina zamu qara zuwa?”

“Oh my goodness” zaid ya fada yana dariya harda dukan sitiyarin mota

“Anya zancan afifa bai zama gaskiya ba?” Saita waiwayo da hanzari

“Da tace me?” Yadda ta tambayeshi da sauri tana narke fuska ya sake bashi dariya

“Tsoron duka mutane kikaji,you didn’t trust anyone”. Tabbas gaskiya afifa ta fada,idan kai tsaye akace ta tsani maza ba’a yi mata qarya ba,ita kadai tasan abinda ta fuskanta,wani abun bazai fadu ba. Sai taji zuciyarta ta tabu,har hakan ya bayyana baro baro saman fuskarta,ya zaid yadan juya kadan ya kalleta kafin ya maida hankalinsa akan tuqin da yakeyi,cikin sigar lallashi da kwantar da murya yace

“Ba duka aka taru aka zama daya ba,dole duk runtsi duk tsanani akwai mutane na haqiqa,akwai nagartattu fiye da tunaninki,akwai masu soyayya saboda Allah,suke kuma nemanta ido rufe,banason wannan kudin goron da kike mana,saboda saka hakan da zakiyi a ranki zaiyita hunting dinki to the rest of your life idan har baki canza ba”

“Bazan maka musu ba ya zaid,amma I doubt gaskiya” ta fada da karyayyar zuciya da kuma karyayyar murya,har taji kaman hawaye suna tsatstsafowa daga qwayar idanunta. Murmushi ya saki kadan,baisan ta yadda zasu sauya tunaninta ba a kullum,amma suna fatan watan wataran HASKE zai bayyanar mata. Yasan duk yadda zai kwatanta mata a yanzun babu lalallai ta miqa hankali nazarinta da tsinkayenta zuwa wajen,don haka ya rufe chapter din ya dauko wani batun na daban,saidai ya riga ya karya zuciyarta,ta kasa sakewa.

              Riqe da glass coffee mug din a hannunsa da yake kurba time to time,yana zaune daya daga cikin kujeru hudu dake gurin,sauran biyun baqinsa ne a kai,idanunsa akan takardun dasu Mr Paul suka gabatar masa yana irga adadinsu da idanunsa ba tare da yakai ga tabasu ba. A nutse ya ajjiye mug din yasa hannu ya rufe file din

“We will contact you after two weeks” kai suka jinjina cikin fara’a suka miqa masa hannu,saidai kafin yakai nasa hannun muryarta ta ratsa dodon kunnensa

“Hi……” Ta furta, cikin qasa da second biyar kuma ta bayyana a gabansu.

           Dukka su ukun suke kallonta,saidai kowannensu da irin kallon da yake mata,mr isaac da Mr Paul kallo suke mata na zallar burgesu da tayi,kyawunta kuma ya ratsa har cikin jininsu,yayin da nasa idanun suka cika da tsananin bacin rai da haushi mara misali. Idanunsa ya janye daga kanta ya miqa musu hannu sukayi musabahar da basuyi din ba,sannan ya miqe yasa hannu daya ya dauki mug dinsa,daya hannun kuma ya fara danna wayarsa yana son kiran jibril yaso ya shiga masa da file din. Cikin second kadan ya iso,ya masa nuni da takardun,yasa hannu biyu ya dauka ya wuce dasu.

              Tana tsaye a gurin,ta zuba masa dukka idanuwanta,tana jin wata mahaukaciyar qaunarsa tana tasiri a jikinta da zuciyarta,tana jin kamar ta taka da gudu ta rungumeshi cikin jikinta,ta kwantar da kanta saman ingarman qirjin nan nasa,ta kuma shafi gefan fuskarsa dake dauke da lallausan gashin da tana iya hango gyaran da yasha ya kuma kwanta luf. Saidai inaaaa,tasan hakan shine babban kuskuren da zata tafka a rayuwarta,tasan wayeshi qwarai da gaske,ko a yanzun ma tana cin albarkacin wani abu ne,tabbas!,da bata isa ta bibiyeshi har haka ba.

           Ganin ya fara barin inda take din ba tare daya nuna wata alama na sanin wanzuwarta a wajen ba yasa itama ta cira qafarta dake sanye da high heels ta fara binsa

“Hello” ta gada da muryarta mai yauqi,shuru ba amsa,wannan ya sanya tadan qara daga qafa

“Muhammad” tayi kiransa da ainihin zallar sunansa. Shi kansa a karan kansa yasan girma qima da martabar me asalin sunan,mahaifinsa ya dauka ya bashi shi,zaiyi wuya ka kirashi da sunan zalla ya iya tafiya ya barka a guri saboda girmamawa ga sunan kansa,batasan hakan yana masa tasiri ba,tana kiransa ne kawai duk sanda taji nishadin kiran nasa da sunan nasa. Ya tsaya cak,har zuwa sanda yaji qarasowarta bayansa dab dashi,cikin deep voice dinsa yace mata

“Ki juya ki koma inda kika fito”

“Saboda me?,don kai fa nazo”

“Ba matsala bace……i said ki juya ki koma inda kika fito,if not…..” Maqale hannayenta tayi a qirji,alamun gargadinsa ko a jikinta

“Idan nace a nan zan kwana fa,kuma a kusa dakai?”

“You are mad,ki gwada ki gani” ya fada yana jin zallar tsanarta tana shigarsa,cikin second kadan tasa kansa ya fara ciwo,duk duniya ita daya ta isa ta tsaya haka a gabansa a matsayinta na MACE ya fada sau daya ta maida masa,ita dimma tana cin wata daraja ne guda daya,sai ya fara yin gaba ba tare daya waiwayo ba.

           Baisan daga ina ba,baisan ya akayi ba……saiji yayi an masa wawar runguma ta baya,he was shock beyond the words,bai taba zata ba bai taba kawowa ba,bai taba tunani haukan LABIBA yakai haka ba. Wani irin mahaukacin fushi ya yunquro masa,yana waiwayo ya zube mata yatsunsa guda biyar saman fuskarta.

             Hannu bibbiyu ta saka tana dafe dukka kuncinta guda biyun hadi da rintse idanu tamkar ita aka mara bayan ta saki wayar hannunta da take dannawa don rage tsahon lokacin jiran yaa zaid,sai kuma ta bude idanun nata a hankali tana laluben daga inda wannan zazzafan marin ya fito,dai dai lokacin da ya fara magana cikin deep voice dinsa data cika da tsananin fushi

“Shashasha wawiya, I can’t tolerate it, next time kika sake gwada irin haka kiyi tsammanin abinda yafi haka” yayi wurgi da mug din hannunsa ya hadu da qarfen dake riqe da fitilun gurin ya tarwatse,baiko bi ta kansa ba ya wuce yana taku da sassarfa duk da hakan kuma majestically.

            Mutuwar zaune sãahar tayi,kunnuwanta suna bitar mugayen maganganun da yanzun nan kunnuwanta suka saurara,duk da cewa bataga fuskarsa da kyau ba amma muryarsa ta fita clearly kamar a gabanta yake maganar,a hankali kalaman suka fara mata suya a qirji tamkar ita aka gayawa,me yasa maza suka raina mata?,itace tambayar data dinga yi mata sukuwa cikin tsakiyar kanta,idanunta nakan labiba data sulale a gun tana kuka,kukan nata ya dinga taba sãahar,ta lumshe ido tana jin kamar ita ya zaga. Me tayi masa ne da har zai daga hannu saboda zallar rashin sanin darajar mace ya zabga mata irin wannan marin?,bata iya shiga abinda babu ruwanta ba,da ta qarasa ta daga labiba data zube a gun tana kuka sosai,ta bata haquri tare da bata shawarar ta manta dashi koda ba zata iya rama abinda yayi mata ba.

           Kasa jure sautin kukan nata tayi,saboda yana son taso mata da nata tsohon ciwon,don haka ta miqe a gaggauce ta zagayawa zuwa inda yaa zaid ya ajjiye motarsa,tayi amfani da key din daya bata ta bude motar ta shige tana maida numfashi ranta a matuqar jagule.

Page 11

          A gaggauce yake komawa cikin hotel din cikin sassarfa da wani irin bacin rai kwance saman kyakkyawar fuskarsa da bata da annuri tun asali ko kadan,jibril dake biye dashi yana maida qafarsa duk inda ya ajjiye,tabbas yasan yau an taboshi fiye da ko yaushe,saidai baiga laifin fushin nasa ba,don shi kansa yarinyar ta fara gundurarsa bare kuma shi da ake bibiyar.

               Suna shiga lobby ya waiwaya ya dubeshi,zuwa sannan fuskarsa harta fara yin ja,musamman hancinsa,abinka da farar fata

“Ka kiramin dukka wadanda muka shigo wajen nan tare,su sameni a living room now!” Yana fadin haka ya qara sauri ya wuce zuwa elevator.

             Da sauri matashin daya bari zaune cikin living room din ya daga kai yana dubansa,yasan yana da matuqar zafi da rashin fara’a,amma yana saurin gane canzawarsa idan wani abun ya sameshi,kamar dai yanzun daya kasa zama,sai iska mai zafi da yake furzawarwa daga bakinsa

“What’s going on?” Ya jefa masa tambayar yana binsa da kallo,kai ya girgiza masa ba tare da ya iya ce masa komai ba

“Come on please,take it easy mana man” yayi maganar yana sauke qafafunsa dake harde qasa,tare da yunqurin cooling temper din da hanga cikin idanunsa,dai dai lokacin da aka nema izinin shigowa living room din.

           Dukkansu suka dinga shigowa daya bayan daya,kowanne a yanzu wasu kayanne a jikinsa ba baqar suit din dazu ba,da alama kowanne yana dakinsa ne yayi shirin kwanciya. Da wani zazzafan kallo ya bisu,dakin ya dauki shiru na wasu yan daqiqu,sannan ya buda bakinsa da zuzzurfar muryarsa data qara nauyi saboda bacin rai

“i regard one of you was betrayal” yayi furucin da gasken gaske,babu alamun sassauci ko wasa ko kadan saman fuskarsa. Tsit dakin yayi,jikin kowa ya amsa,aka rasa me motsawa bare ya bashi amsa

“Who told her I was there?” Dif dakin ya sakeyi,yayin da yake sake bin fuskarsu da kallo daya bayan daya,yana hucin bacin rai yana fita daga fuskarsa,ya dauke kansa daga dubansu,ya maida hannayensa cikin aljihun wandonsa ya soma takawa a hankali zuwa gaba

“I will not repeat my question…..” Ya fada bayan ya basu baya

“Nine” daya daga cikinsu dake rakube acan gefe ya fada,zufa tayi wani irin wankeshi,yasan sakamakonsa,babbar asarar ce zata sameshi wadda ba lallai ya maida gurbinta,sai ta ninka abinda ya samu daga gareta bayan dogon lallashin data masa ta ciyo kansa ya shaida mata sun sauka a bristol din.

           A nutse ya waiwayo ya kuma zuba masa idanu,zuciyarsa tana tafasa

“All this while…….” Sai kuma ya kasa qarasawa saboda bacin ran dake sake taso masa idan ya tuna yadda ta rungumeshi,yanajin kamar ya zauna ya daye fatar wajen,ko ya maido da lokacin ya goge faruwar hakan

“You’re fired!” Ya fada kawai bayan ya duqa ya dauki wayarsa yana nufar qofa

“Anyone who deliberately does what he has done deserves to be fired from his job” statement dinsa na qarshe kenan,yasa kai ya fice daga dakin ba tare daya sake waiwayar kowa a cikinsu ba.

         A nutse saurayin SAJJAD ya miqe yabi bayansa,yana shiga dakin shima yana sanya qafarsa

“Me kake aikatawa ne TAUFEEQ?,firing a person from work is not a joke”

“Did I tell you I was kidding? I really mean what I said,i dismissed him,idan kuna tunanin wasa ne na ganshi cikin maaikatana gobe” yayi maganar yana bude fridge,ya cire ruwa me sanyi ya balle murfin gorar yana tuttulawa cikinsa ba tare daya nema koda cup ba.

          Da kallo SAJJAD ya bishi,tabbas shan ruwa me sanyi sam ba dabi’ar taufeeq din bane,idan kaga hakan ya faru to alamu ne na tsananin bacin ransa,ko meye zai gaya masa a yanzun bazaiyi tasiri ba,sai yaja qaramin tsaki

“since that’s how you choose to be,sai kaci gaba,sai da safe”

“Ka sallamesu ka rufemin qofofina” ya fada masa a taqaice yana cillar da robar ruwan gefe,ko a jikinsa na fushin da sajjad din yayi,bazaita zama bai takawa yarinyar burki ba ita da duk wanda yake bata information na wanzuwarsa a waje ba,tabbas muddin akaci gaba da haka to babu shakka watarana zata zubar masa da mutunci kima da kuma martabarsa,tunda har ta farajin takai hannu jikinsa,the worst part ma a waje na jama’a irin wannan,daya daga cikin dalilan da yasa yake sake tsanar mata a ransa,zasu iya yin komai…….zasu iya aikata komai da gajeran tunani da qwaqwalwarsu.

          Qarar wayarsa ce ta dakatar dashi,ya fidda hannayensa daga aljihunsa ya taka a hankali zuwa inda ya ajjiye wayar,kiran dake shigowa ta cikin wayar me muhimmanci ne,ya ajjiyeta ne kawai saboda ire iren kira masu muhimmancin da suka shafi family dinsa.

             Wani abun mamaki qaramin murmushin daya ratsa murtukekkiyar fuskarsa har labbansa suka motsa,wani irin sirrintaccen kyau ya bayyana kan fuskarsa,ya dauki wayar yana daga kiran

“Daddy” siririyar muryar qaramar yarinyar ta bayyana cikin wayar,ta kuma ratsa kunnensa,ya lumshe idanunsa ya budesu a hankali,yana jin duk wata damuwa da bacin ransa suna narkewa

“Daddy’s angel” ya maida mata a tausashe

“Wai da gaske kazo?”

“Ki fara gaisheni tukunna” ya gyara mata bayan ya bude dukka idanunsa yana kallon gabansa

“Good evening daddy”

“That’s my girl……kina lafiya?”

“Lafiya lau daddy,da gaske kazo?” Gyara zamansa yayi ya zauna sosai sannan ya amsa mata kanshi tsaye,don bai saba yi mata qarya ba,bare ma kwata kwata shi din yana cikin jerin mutanen da komai tsanani komai wuya basa barinsa yayi qarya,tun daga yarinya har kawo yau,komai girman situation din da za’a shiga

“Na dawo angel,but wani aiki ya riqe daddynki,i really miss you, I can’t wait to see you,but in sha Allah gobe komai dare,you will be next to your daddy,please apologize me” dariya ta qyalqyale dashi cikin nishadi da siririyar muryarta sannan tace

“Apology accepted daddy”

“Thank you princess” ya fada cikin nuna kulawa.

            Sosai zakayi mamakin yadda ya saki jiki yana hira da ita cikin kulawa,a hankali kuma bacin ransa yana narkewa,ita din duniyarsa ce,wata qwayar halitta guda daya dake da mazaunin komai na rayuwarsa,baya wasa da dukka abinda ya shafeta,matsayinta da qaunarta a ransa ta zarta komai. Bugu da qari lalurar dake tattare da ita tana sake sanya masa wata qaunar yarinyar tare da mugun tausayinta,tattalinta da kuma bata dukkan kulawar daya kamata,idan ba tayi mugun takewa ba,baya bari ko kadan yayi nisa da ita.

*_F R I D A Y_*

          K’arfe d’aya da rabi na rana suka fito daga town hall meeting,wanda ya sake maida kowanne ma’aikaci cikin nutsuwarsa,ya kuma girgiza zukatan duka wasu marasa gaskiya. Iya abinda aka tattauna a gurin kawai tsaiwarsa da yadda ya tsara abubuwa ya tabbatarwa da kowa ba wasa yazo yi ba,daga nan suka wuce sallar juma’a da dukkan Wani ma’aikaci musulmi,sannan ya sallami kowa da zazzafan gargadin haduwarsu da fara aiwatar da komai ranar litinin.

           Suit coat dinsa ya cire yana ratayeta,sannan ya jawo kujerarsa ya zauna bayan ya nade hannun rigarsa zuwa sama kadan,yakai hannu ya dauki drink din da jibril ya ajjiye masa yana duban mutum biyun dake zaune,ya tsaya ya saurari dayan ya sallameshi,sannan ya maida dubansa ga sajjad

“Who is my new president?”

“she didn’t come” komawa yayi baya yayi relaxing jikin kujerar,idanunsa a lumshe yana jin kansa ya dauki caji da yawa

“Is she a female?”

“Eh” ya amsa masa yana kallonsa,don yasan anzo gurin,idanunsa ya bude tarwai,ya zubesu kan fuskar sajjad

“A female president? why?”

“it’s dad’s choice” shuru ya danyi,kamar bazai sake magana ba,sajjad ya kafeshi da ido,sai ya janye nasa idanun,ya janyo system dinsa yana budewa

“If she is not ready to work with us, we will replace her with someone else,let her know,dole ta zama serious,ba zamu dinga biyanta tana abinda taga dama ba”

“Za’a gaya mata,but wannan dogon statement din yayi yawa sir” ya fada yana bincika jerin sunaye da address phone number da email address na ma’aikatan dake hannunsa,duk wasu ayyukan ba nasa bane basa a wuyansa,amma sanin hali ya sanya abba ya hadashi dashi,yace kuma ya dinga zama by his side lokaci lokaci,yana monitoring wasu abubuwan,yasan taufeeq din da zafin kai qwarai.

        Bazai iya challenging daddy din ba,amma tabbas da ya sauya ta da namiji,matsayine da yake ganin mace sam ba zata iya riqeshi ba,koda zata iya din ma,zuciyarsa bata basu wannan amincin na riqe babban matsayi har haka ba,rashin amanarsu kadai ya sanya baya qaunar wani hulda a tsakaninsu,bare har akai ga zama na aiki da musayen ideas.

       Kwata kwata ma basu cancanci dukka wata mu’amala data qunshi aminci ba,yana musu kallon wata halitta ta daban,KUDI shine abinda sukafi bawa daraja kima mutunci da muhimmanci,zaifi kyau su tsaya iya nan.

Page 12

          Tunda yaa zaid ya sauketa a jiyan abun yaqi barin ranta,kusan zata iya cewa dashi ta kwana,wanda ya haifar mata da wani irin bacci mara dadi,da mafarkai barkatai wadanda suka shafi wasu al’amura dake da alaqa da rayuwarta. Cikin dare ciwon kai ya saukar mata,wannan ya sabbaba mata makara a sallar asuba,kuma ko bayan tayi sallar wani baccin ya sake daukarta,sam ta mance da batun fara zuwa aikinta a yau,wanda dama zataje ne kawai don ta fara karantar yanayin yadda abubuwan suke.

          Kwata kwata bata tashi farkawa ba sai qarfe goma na safe,ta tashi da sauqin ciwon kan,ta miqe daga gadon tana shirin shiga toilet akayi knocking qofarta.

            Maama ce ta shigo,cikin kamalar nan tata wadda kusan a nan da wajen abba sãahar din ta gadota

“Kina lafiya kuwa?” Tayi mata tambayar tana kallon qwayar idanunta tare da fatan ba damuwarta ce ta sake motsawa ba

“Ina kwana maama” ta maida mata da gaisuwa

“Lafiya qalau,kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah,na dan tashi da ciwon kaine,bayan asuba kuma saina samu bacci”

“Subhanallah,Allah ya sawwaqe,ko zaki asibiti?,banason zama da ciwo” ta fada cikin damuwa,saboda tasan yanayin ciwon kan sãahar din,baya yi mata da sauqi idan ya tashi,saboda ciwo ne da ya samo asali ta Wani dalili,ba hakanan ta sameshi ba

“Alhamdulillah naji sauqi yanzu,wanka kawai zanyi na sauko”

“To alhmdlh,yayanki ne ya dameni da waya tun dazu,yace yana kiran wayarki bata shiga ba”

“Ya muhyi” ta fada kai tsaye,tasan yanason jin ta fita aikinne ko kuwa

“Zan kirashi idan na fito a wanka”

“To madalla,yayi” saita juya tana shirin fita

“Abbanku ya fita,amma shima ya tambaya kafin ya fita din”

“Zan kirashi shima” ta sake fada tana yunqurin zare rigar baccin jikinta

“Don Allah maama,baba rabi ta kawomin ruwan dumi a cup”

“Shikenan” ta amsa tana qarasa fita a dakin.

              Da ruwa me dumi sosai tayi wankan nata,ta fito fatarta na wani irin sulbi da qamshi daya hade da tururin ruwan dumin da tayi wankan,ta fito ta tsaya gaban mudubi tana kallon fuskarta dake subul kamar ta jariri,babu tabo babu komai,sai tsananin taushi da sulbi da take sakeyi,alamun product din da take amfani dashi ya karbeta. Tasa hannu ta dauki mug din ruwan dumin da baaba rabi ta kawo mata ta aje ta soma kurba a hankali,saboda muhimmancinsa a jiki bata skipping shansa kowacce safiya kafin taci komai,koda kuwa ta makara bata tashi da wuri ba.

             Da wani irin sauri sautin marin jiya ya gilma a kunnenta,ta runtse idanu kamar a sannan abun ya faru,ta cire cup din da takai bakinta a hankali ta ajjiye saman madubin sannan ta bude idanunta tarwai tana kallon fuskarta. Tsantsar rashin sanin darajar dan adam ta tabbata ga duk mutumin da zai iya shimfida yatsunsa akan muhallin da yafi ko ina daraja a jikin dan adam,wani abu yazo ya tsaye mata a wuya,ta saka hannuwanta biyu saman kuncinta,tana tuna wani lokaci can baya daya wuce,tana tuna marukan da tasha saman fuskarta,wanda batasan iya adadinsu ba.

           Sauke hannuwanta tayi taja da baya tana barin gaban madubin ganin bacin ran da bataso tana yawan ji yana qoqarin taso mata,sai ta koma gefan gadonta ta zauna tana hadiyeshi,idanunta suka sauka kan ledar siyayyarta data shigo da ita jiya,ta miqa hannu ta janyota,ta fara buda kayan ciki tana sake dubawa,bawai don batasan me ta siya din ba,a’ah tanason kore bacin ran dake taso mata ne.

          Sai data shirya kayan cikin walking closet dinta sannan ta fara gyara jikinta,ta shirya kanta cikin wata sassauqar gown fara,alamu suna nuna ita din ma’abociyar son fararen abubuwa ne,musamman kayan zaman gida da qananun abubuwan amfani irin haka. Cikin qasa da awa daya ta sauko qasan riqe da system dinta tana amsa wayar afifa,ta saka system din a chargy,ta leqa ta gayawa maama ta fito wadda ke saman abun sallah zata tayar da salatud duha(sallar walaha),sannan ta nufa kitchen ta samo abinda zata iya ci.

            “Barka da fitowa” baba rabi ta fada cikin girmamawa,tadan murmusa kadan,baba rabin ba zata taba daina gaisheta ba

“Ina kwana?”

“Kin tashi lafiya farar d’iya” suna ne da takan kirata dashi lokaci lokaci

“Lafiya qalau,me zan samu?” Fara bude mata abubuwan da suke dashi da safen a kitchen tayi,kusan duka ba cimarta bane,amma batason bawa kowa aiki da safen nan,ita kuma qyuyar aikin yau takeji,don haka sai ta jawo plate ta tsakuri iya abinda take ganin zata iya a plate daya,ta fice zuwa Parlor din.

           Tana cin abincin kamar wasan yara ta kunna laptop din nata,gidan gaba daya ya mata shuru ba dadi,afifa bata dawo ba kwata kwata wannan satin,shi yasa takeson yara,bata rabo da dauko ‘ya’yan yayyen nata,to wannan karon su fadil suna umra duka gidan,khalifa na exam,aleena tayi qanqanta don ko yayeta ba’ayi ba,ya zaid kuma ya maidasu na’eem canada,cikin satin nan shima zai bisu,dole ta zauna zaman kadaici,idan taji ta matsu da yawa kuma tabi afifa.

              Sai data gama duk uzurinta sannan ta shiga ma’ajiyar saqonnin email dinta da nufin share saqonnin da suke kai ko zata ragewa computer din nauyi,har ta fara marking idanunta suka kai kan sabon saqon daya shigo mata daga MT GLOBAL COMPANY,ta dan tsaya tana tunanin inda tasan sunan,kafin daga baya hankalinta yakai kai,takai arrow din kai tayi clicking ta shiga.

          Dogon tsaki taja bayan ta gama karanta abinda saqon ya qunsa,and so what don zasu canzata da wata muddin bata shiga aiki ba on Monday,ko an gaya musu aiki da su damuwarta ne?,ko basusan alfarma zatayi musu ba saboda darajar masu daraja?,cikin jin haushi ta soma rubuta musu reply na basu damar sanya watan,cikin ranta tana jin ta samu hanya mafi sauqi ma da zata sabule wannan alaqaqai din aikin,saidai tana kammala rubutawa kafin ta tura taji muryar yaa muhyi yana magana da masu aikin gidan dake harabar gidan,saita dora hannuwanta saman fuskarta tana jin ba dadi,a sanyaye tayi highlight na duka rubutu tayi cutting dinsa,ta goge email din ta sauka daga ciki,tayi shutting down na system din,dai dai lokacin ya sanyo kansa cikin parlor din.

           A nutse ta amsa sallamarsa,tayi masa barka da safiya sannan ta miqe ta yiwa maama magana,ta kuma wuce kitchen ta hado masa dan abin motsa baki,ta kawo ta ajjiye masa

“Ya na ganki gida,nayita kiran wayarki kuma bakiyi picking ba,kada dai ace tun ranarki ta farko kin fada wasa da aikinki?” Yaa muhyi ya fada yana kallonta hadi da dan kada key din hannunsa.

          Fuskarta ta tattare tayi alamun tausayi ta zauna daga kujerar dake gefansa

“Da ciwon kai na tashi yaa,kuma ma Allah……” Kasa qarasa masa tayi,tadan lanqwasa yatsun hannunsa

“Eheenn,Allah me?” Ya tambayeta kai tsaye yana dubanta bayan yadan tsuke fuskarsa kadan,don bayason jin wani zance sabanin wanda sukayi da ita

“Yaa ko zaka taimakamin su sauyamin position din da suka bani,bana son president din nan wallahi” ta qarashe fada tana narke murya. Ajiyar zuciya yadan sauke yana furzar da iska daga bakinsa sannan ya sake maida dubansa kanta

“Dr yana da matuqar kirki da sanin ya kamata,haka d’an nasa,yana da kamewa da sanin ya kamata,na tabbatar ba zaki taba fuskantar wata matsala wajen yin aiki dasu ba,inda nasan akwai matsalar kema kin sani,bazan karba miki ba,so please accept it,kiyi aiki tuquru,ko don saboda ni” qas tayi da kanta,tanason tilastawa zuciyarta da har yanzu taqi jin nutsuwa aminci wa aikin kan ta karba buqatar dan uwanta,sake gyara zamansa yayi sannan yace

“Shi da kansa Dr yin ya zaba miki position din,ya fimu shekaru da hangen nesa,yana ganin kin cancanta ne,ko abba dana gaya masa baice wani abu ba,kuma koni din nasan you can do it,so please kada kiyi discouraging kanki,you will made it in sha Allah” Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya qasan ranta,bai fahimceta bane,bawai ba zata iya bane,ita sam harkar da duk zai hadata mu’alama da jama’a ne bataso. Ganin ta shiga tunani sau ya katse tunanin nata ta hanyar miqa mata key din mota

“Gashi,gift na fara zuwa aiki,daga ni da kuma Saifullahi” hannu biyu tasa ta karba tana masa godiya,saidai sanda ta duba sunan motar sai da zuciyarta ta tsinke,motace sabuwar qira me kyau ta mata,tana kuma da dan tsada,lallai da gaske sukeso sai tayi aikin nan,zatayi addu’a ta kuma roqi Allah ya dafa mata,kada ya bata ikon watsa musu qasa a ido.

***********Duk daga inda ka daga kanka cikin layin,daga farko ne qarshe gaba ko baya na layin kana iya hangen katafaren ginin mansion house din daya amsa sunansa ta kowacce fuska a idanun me kallo,saidai daga ainihin cikin zuciyar gidan akwai naqasu me tarin yawa a ciki,birnannen tarihi da memories masu daci tsananin quna da soya zukata,memories da suka dakushe jin dadi da walwala mafi rinjaye ta dukka mutumin daya shafi gidan,gefe guda kuma akwai wani boyayyen muhimmin al’amari wanda yake sarrafa duk wani motsi da rayuwa ta al’ummar gidan.

          Idan nace al’ummar gidan kada ka dauka wasu jama’a ne masu yawa,a’ah……dai daikun mutane wanda rayuwa cikin gidan ga zame musu lazim.

            Kamar kowanne lokaci,qarfe takwas da wasu mintuna na dare,lafiyayyun hamshaqan motocin nasa suka tsaya babbar gate din gidan me kama da qofar masarauta ko shiga wata kasuwar duniya,cikin qasa da second biyar aka soma motsa qofar gate din bisa sahalewa da sarrafawar daya daga ckin security din gidan dake tsaron qofar,wanda ke tsaye daga gefe kusa da na’urar dake tura gate din cikin uniform din da dukka ma’aikatan gidan suke amfani dashi,wato baqin wando da farar riga,sai baqar hula me kama da hular ‘yan sanda.

             A nutse suka kutsa kai lafiyayyar harabar gidan me matuqar girma da tsari,wadda aka qawatata qwarai da shuke shuke,fitilu masu tsananin kyau da haske,da kuma ainihin fuskar gidan dake manne da wasu gilasai tamkar dasu akayi bangon gidan. Tun daga harabar tsarin gidan zai fara tafiya da imaninka,tsaftatattun tsirrai masu bada wani irin iska qamshi da koke koken tsintsaye daban daban,wasu siyansu akayi aka ajesu don bawa gidan dukkan ni’imar data kamata,wasu kuma daga Allah ne,sukanzo su wuce,kosu samawa kanau gurin kwana cikin tsirran dake wajen wadanda suka dace da tsarinsu,hakan sai ya sake qawata wajen,ya wadatashi da wani irin yanayi me sanyaya zuciya.

            A nutse ya fito daga motar kamar kowanne lokaci cikin tsananin kamewa da izza,yauqi da aji irin na hadaddun mazan da suke ji da kansu suka san kuma waye su. Yana sanye da wani yadi da aka samar dashi daga merino wool dan asalin qasar spain me asalin kyau da tsada,wanda wani qwararren telan ya zauna ya shiryawa dinki na zamani daya sake qawata yadin fiye da kima,ya kuma qawata kwalliyar mamallakin suturar. Yana daya daga cikin jerin mutanen dake da tsari da kuma zabi a dukka sutturar da zasu sanya,hakan sai ya cakudu da baiwar dacewa da kowacce shiga keyi da jikinsa,koda kuwa pajamas ya sanya,duk da wasu matan dake da qarancin kunya a idanunsu……sun sha gaya masa yana da kyau ne,hakanan komai nasa me kyau ne,wannan ya sanya kome zai raba a jikinsa yake dacewa dashi,ya kuma sake qara masa kwarjini da cikar haiba da kamala.

           Daya daga cikin yaransa ne ya matso da sauri yana masa bayanin wasu tarin takardu dake hannunsa,sai ya masa nuni da matashin dake tsaye a gefansa,yayi handing over dashi sannan ya taka a hankali yana nufar ainihin main entrance na gidan,ya barsu a wajen kowa yana qoqarin hattama aikinsa na ranar.

              Duk taku daya yana jin yana qara masa kwadayin isa gareta,zuciyarsa ce ita,rayuwarsa ce,hakanan farincikinsa.

             A nutse ya buda qofar lafiyayyen falon farko da zaka soma tararwa,falon da dukka kalolin kayan ado da qawa da aka zuba masa warm beige color ne da ratsin rusty red,tun daga manya manyan curtains na alfarma,kujerun da aka zuba carfet da aka malaleshi dashi ac da paint na ainihin bangon,hatta da frames dake parlor din masu dauke da ayatul kursiyyu falaq da nas da sauran ayoyin tsari color din dake jikinsa kenan,sai ratsin gold kadan a jiki.

            Iya dubansa tsaf ya qarewa falon,ya sanya qafafunsa a hankali ya saka kai ciki hannayensa cikin aljihun wandonsa yana ratsa falon,wani yanayi yana saukarwa gangar jikinsa har zuwa zuciyarsa,wasu emotions da baisan yadda zai raba kanshi dasu ba,yayita kokawa da kansa yana danne fushin dakeson motsa masa yana ci gaba da saka kai ciki.

Page 13

           Wani Parlor din ya tarar wanda baikai wannan girma ba,duk da dama abinda ya rabasu da wannan din babbar qofar glass ne da zaka turata,sai kuma labulaye na alfarma da aka zubawa qofofin duka,saidai wannan Parlor din nashi kalar daban da wancan,don komai da aka shirya a cikinsa minty blue green ne da ratsin creamy white. Dan matsaici ne da bai cika girma sosai kamar wancan ba,amma ya tsaru yadda jiki da zuciya zasu samu hutu yadda ya kamata. Shima shuru yake babu kowa,saiya taka zuwa hannun damansa,ya yaye labulen daya sadashi da wani tsararrren corridor wanda ya qawatu da wasu gold leaf picture frames,fentinsa olive green ne saboda qarawa idanu qarfin gani,kalar kuma ta dace da wajen sosai daya qawatau da fitilu masu haske tarwai,sai flowers a maqale a kowacce corner daga jikin bango,wanda suke bada qamshi na musamman da kuma samun kyakkyawar iska fiye da iskar da na’urar bature dake kafe a wajen zata bayar.

             Qofofin dakunan bacci ne guda hudu a wajen,kowacce da dan taqi kadan daga qofar dake kusa da ita,biyu na kallon guda biyun,sai yaci gaba da takawa a nutse kamar mai nufar full length mirror din dake maqale a bangon qarshe na wajen,ya isa qofa ta qarshen dake daura da madubin daga hannun damansa,yasa hannu ya murda ya tura sannan ya shiga.

           A nutse yake qarewa dakin dake a tsaftace kallo,yana watsa idanunsa tare da laluben daga inda zai hangota.

           . Daga saman gadonta ya hangi tattausan bargonta milk color me matuqar taushi cure waje daya,ya zubawa gurin ido sosai,alamun motsin da ya gani shi yaja hankalinsa,ya daga qafa da wani irin hanzari ya isa bakin gadon,bai tsaya jiran komai ba ya sanya hannu ya yaye bargon take ta bayyana.

             Kyakkyawar yarinya ce da duka duka shekarunta ba zasu haura biyar zuwa shida ba,fara ce qal siririya sosai,gashinta me tsaho da sulbi yana daure tsakiyar kanta da wani siririn ribbon pink color,kalar riga da wandon dake jikinta kenan. Cure take waje daya,ta qanqame ilahirin jikinta kamar wadda taga wani mummunan abun tsoro,saidai yadda bakinta yake rawa kawai ya isa gaya maka ta hadu ne da mummunan zazzabi.

          Da hanzari ya haura gadon gaba daya,jikinta na rawa,lokaci daya tashin hankali da rudewa suka bayyana qarara saman fuskarsa tamkar ba ingarman namijin nan da yanzu yanzu yake shigowa cikin gidan ba,cikin takun dake cike da karsashi ba.

“Ya salam……ya salam” ya fada fuskarsa na wani irin sauyawa,tare da rungumota gaba daya zuwa jikinsa yana fadin

“Zazzabi ne a jikinki fadeela?,ina baaba rabi?” Ya fada yana lullubeta cikin jikinsa tamkar yana shirin maida ciwon jikinsa ne. Bude qofar dakin sai ya zama kamar amsar tambayarsa,kamilalliyar matar tayi sallama,wankan tarwada ce,sanye take da atamfa riga da zani,sai kakkauran mayafi data yane kanta dashi,hannunta dauke da carbi

“A’ah lafiya?,me ya sameta?” Ta fada cikin nuna tsantsar kulawa,itama fuskarta na nuna zallar alhini tana matsowa zuwa bakin gadon

“Yanzu yanzu na fita nayi sallah,na barta tare da julia tana qoqarin bata kayan bacci ta saka” baaba Rabi ta fada cikin tsantsar alhini tana qoqarin karbar fadeela daga jikinsa,saidai yaqi sakar mata ita

“Itace sabuwar nanny din da aka kawo?” Ya jefawa baaba rabin tambaya yana kallonta da idanunsa da suka kada suka canza launi,cike fal da wani irin zazzafan bacin rai

“Itace” ta amsa masa dukka hankalinta yana kan yarinyar,kafin yace komai aka buda qofar dakin aka shigo.

           Matashiyar budurwa ce ‘yar qabilar yoruba,sanye da uniform irin na ma’aikatan kamar kowanne ma’aikaci dake aiki cikin gidan. Cikin mugun razana taja da baya tana sauke idanunta qasa,gabanta yayi masifar faduwa,dukka jikinta ya dauki rawa,cikin matuqar kaduwa ta sulale ta duqa a wajen

“You are welcome sir” Idanunsa fal da masifa da kuma tashin hankali yake kallonta,ya zare yarinyar daga jikinsa ya miqawa baaba rabi ita,cikin harshen turanci ya fara magana cikin masifa tamkar zai bugeta,saika dauka bai cikin hayyacinsa

“Kin fadi adadin abinda kike da buqata na kudi,nasa an biyaki amma hakan bai hanaki kiyimin sakaci da rayuwar yarinya ba?,zaki barmin ita har zazzabi irin wannan ya sauka a jikinta ba tare da kin sani ba,banga amfaninki ba,ki tattara komai naki kibar gidan nan,na sallameki” ba ita kadai ba data rasa aikin da tayi mugun saka a rai kanshi ba,hatta baaba rabi tayi mugun kaduwa da hukuncin nasa,julia itace me aiki ta goma sha daya daya kora cikin qanqanin lokaci,kwata kwata baya daukan sakaci akan yarinyar,komai qanqantarsa shi ganganci ne a wajensa,duka masu aikin basa wuce sati daya suke rasa ayyukansu,masu nisan zango ne sukeyin sati biyu.

            Yana da mugun kwarjini da haibar da bazaka iya tsaiwa roqonsa ba,don haka tana share hawaye cike da baqinciki rasa aiki me gwabi da tarin albashi me tsoka,da kuma fita daga daular wannan gidan,wanda iya cima da AC din dake karakaina a lungu da saqo na gidan kawai ta isa sanyaka ka mallaki lafiyayyar fata me sheqi,ba tare da kana amfani da mai ko sabulu ba.

            Wayarsa ya ciro a aljihunsa cikin hanzari yayi kira na wasu sakanni,sannan ya matsa da sauri ya dauke yarinyar cak daga cinyar baaba rabi ya rungumeta cikin jikinsa,ya juya cikin kamewarsa da fushi ya bayyana a tsakiyarta yana fita a dakin.

             A nutse yake takawa da ita zuwa sashensa,yana jin kamar ya maido ciwon jikinsa,tana ruqunqume dashi itama duk da zafin zazzabin jikinta,yana takawa idanunsa na sauya launi,wani abu da yafi kama da bacin rai yana motsa zuciyarsa,yana jin wata qaqqarfar tsana ta wata halitta na sake haifuwar sabuwar yabanya a zuciyarsa.

             Da hannu daya ya bude qofar bayan ya ratsa wani hadadden balcony da aka qawatashi matuqa fiye da tunani,kyakkyawan falo ne na alfarma wanda ya kerewa dukka falukan gidan,komai da komai na cikin falon,hatta da door mat dinsa kalar creamy white ne me matuqar daukan hankali da burgewa,fararen fitilu qal da suka haska falon tarwai kamar safiyar da aka tashi da tsananin hasken rana sun taka rawar gani wajen qawata falon,tako ina qyalli yake,komai fes qal kamar rai bata rayuwa a ciki,duk inda ka waiwaya sai kaga kamar zaka ga fuskarka. Ba abinda falon yake bayarwa sai Wani irin ni’imtaccen qamshi dake cakude da qamshin air conditioner din dake tsaitsaye a kusurwoyin falon yadda zata wadaceshi tako ina saboda girman da yake dashi. Tsaf ya laqume saitin kujeru biyu na alfarma,iya wanzuwarka cikin falon ya isa ya baka wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali,saidai banda taufeeq wanda babu abinda ya sauya daga abinda yakeji cikin zuciyarsa.

“Welcome sir” ma’aikatan dake aiki a sassansa mutum biyar dukka maza suka fada cikin rusunawa da kuma girmamawa,baiko amsawa kowa daga cikinsu ba,sai hannu daya daga musu alamun ya sallamesu,suka juya da daya da daya suka fice a parlor din bayan kowa ya tabbatar aikinsa ya kammala,jibril ne qarshe,ya zube files din hannunsa da komai da komai ya juya shima ya fice.

            Ta hannun damansa ya bulla wani matsakaicin hallway da aka qawatashi sosai shigen na daya sashen,ya tura qofar dake a wajen,babban bedroom ne shima da komai na cikinsa creamy white ne kamar falon,tsararrren gado dan qasar italia da yasha shimfidu da lallausan farin zanin gado saqar qasar dubai,qarasawa yayi ya kwantar da ita akai cikin tsananin tausayawa,shi da itan duka yana jinsu shi da ita tamkar marayan da mahaifinsa ya rasu kafin haihuwarsa,mahaifiyarsa kuma ta rasu ta barshi yayin haihuwarsa,yakanji duniyarsu tayi musu fadi kamar babu wani me jibantar lamarinsu,bawai don sun rasa masoyan dake nuna kulawa da soyayya mara iyaka a kansu shi da ita ba,a’ah…..akwai wani boyayyen abu,wani internal love da dukka su biyun suke buqata,wanda suka rasashi,kuma shine sila sannan musabbabiyyar jin wannan kadaicin dake lasar zukatansu ta can ciki.

Page 14

          “Daddy” ta fada da siririyar muryarta da zazzabi ya jigata ta qara laushi ainun,Hannuwansa yaji ta kama ta riqe tsam,sai ya waiwayo ya kama hannuwan nata ya sanya cikin nashi,idanunsa suna canza launi saboda bacin rai da damuwa,ya miqa hannunsa zuwa gefen wuyanta don sake jin adadin zazzabin,har yanzu dai kamar dazun

“Am sorry angel,yanzu likita zaizo ya dubaki,zaki samu sauqi in sha Allah” da ido kawai take binsa,ya durqusa a tausashe yayi kissing bayan hannunta yana sake riqe hannun nata da kyau,yanajin kamar ya maidata cikinsa. Qararrawar falo ce tayi qara dai dai sanda wayarsa tayi qara itama,ya fara duba kiran

“Ku shiga dashi waiting room” ya fada a taqaice,sannan ya zare bluetooth din kunnen nasa ya ajjiye,ya sunkuya ya sake daukan fadeelan suka fita.

           Qaramin clinic ne da ya kasance mallakin gidan,wanda ke dauke da dakin magunguna,dakin jinya guda biyu da gadajensu,da daki guda na gwaje gwaje da sauran ayyuka wato mini laboratory,kusan duk wani qaramin ciwo da zai samu iyalin gidan a nan ake dubasu bisa jagorancin likitan gidan wato Dr anwar ko kuma Dr raheema. Dukkan wasu kayan amfani da suka shafi magunguna na clinic din ana yawan dubasu da sabuntasu qarqashin jagorancin likitan amana Dr anwar bisa kulawa da kuma qwarewa,zallar karamcin MT jarma ya shafe idanunsa,ya kuma bashi dukkan wani matsayi da martabawar da baya iya tsallake kiransa shi da dr raheema kowanne irin aiki sukeyi,matuqar bai wuce gaban tasu buqatar ba.

          Cikin lokaci qanqani ya gama checking dinta,ya soma hada allurai zaiyi mata

“Yanzu yanzu zazzabin zai sauka in sha Allah,ba wani ciwo bane me zafi,don’t bother sir” a nutse ya gyada kansa,dukka idanunsa da damuwarsa suna kanta.

           Mutsu mutsu ta fara yi,qaramin murmushin da bai shirya zuwansa ba ya kufce masa,yasan anzo gurin dama,muddin idanunta suka qyalla akan allura to yanzu zata daga hankalin kowa,a tausashe ya matsa kusa da ita,ya dagata cak ya sanyata a jikinsa,ya dora hannunsa saman lallausan gashinta yana shafawa a hankali

“Relax angel….. relax,bazaiyi miki da zafi ba” ya fada yana tausasa muryarsa sosai,saita tsaya cak din,ta runtse idanu tana jin shigar allurar a jikinta,ta kuwa matseshi gam har aka gama.

         Da kansa ya isa dining room bayan zazzabin ya saukar mata,ya dudduba abinda cook dinsa ya dafa,ya zari plate ya debo dai dai iyakar abinda yasan tanaci.

           Cikin tsantsar kulawa ya zauna ya dinga diban abincin da spoon yana bata,yana yi yana janye tab din hannunta,don daga saukar zazzabin har ta yiwa game dirar mikiya,tana masifar qaunar game,babu abinda yake bata nishadi kamar ita,idan ta kalleshi ta tabe baki zata sa masa kuka saiya kada mata yatsansa alamun a’ah.  Yafi fahimtarta fiye da mahaifiyar data haifeta,ya gama haddace duk wani abu data fiso da wanda bai dameta ba,harma da wanda bataso,sai daya tabbatar ta qoshi sannan ya barta,ya miqa mata tab din yace mata zaije yayi wanka,ta gyada kai ta kuma waving masa hannayenta alamun bye

“See you soon dad” qaramin murmushi ya fita a fuskarsa,ya kada mata nasa hannayen,sannan ya juya a hankali ya wuce bedroom dinsa,hankalinsa da tunaninsa yana kanta.

            Kayan jikinsa ya fara ragewa,yanayi yana kokawa da tunaninsa,hutu yake da buqata a yanzu,bawai tuna wasu tarkacen abubuwa marasa muhimmanci ba,tunasun da bazai haifar masa da komai ba sai zallar bacin da kwana cikin damuwa,damuwar da a wannan yanayin da al’amura suka cushe masa abubuwa sukayi masa yawa bashi da buqatarta,gobe ranar hutunsa ce,yana da buqatar ya wuni tare da ita,ya debe mata kewar data jima tanayi tasa. Babban towel fari qal ya daura iya qugunsa,faffadan qirjinsa dake cike da gargasa da murdaddun damtsensa ya bayyana sosai.

*M O N D A Y*

         Tun qarfe biyar na asuba data kammala salla tana saman abun sallarta,koda ta gama azkar dinma saita samu kanta da sanyin jiki da kuma sanyin gwiwar kasa tashi tabar wajen,don haka ta buda qur’ani tayi tilawar wasu shafuka daga ciki sannan ta maida ta rufe. Agogo ta kalla,har yanzu akwai sauran lokaci kafin fitarta,sai ta jawo wayarta ta kunnata daga kashetan da tayi. Har yanzu cikin jikinta tana jin wani yanayi mara dadi,wanda duka baya rasa nasaba da fara fitarta aiki.

            Saqon barka da asuba daga wajen mahmud gana ta fara cin karo,ko da wasa bata taba gwada saving number dinsa cikin wayarta ba,to amma yadda yaketa binbininta,da yawan cikata da yakeyi da saqonni safe rana dare yasa ta fara shaida number din tasa a idanu. Qaramin tsaki taja,bata koda bari ta buda saqon taga cikakken abinda ya qunsa ba ta shareshi daga wayar tata gaba daya,kusan hakance take faruwa dama,duk sanda saqonsa ya shigo wayarta bata tsaiwa dubawa bare ta karanta,ta riga ta quna daga lamarin maza,batajin akwai wani abu nasu guda daya da zai burgeta,dukkansu a wajenta tamkar hankaka suke,gabansu fari bayansu baqi,kamar hawainiya dake iya canza ainihin launinta zuwa dukka launin da takeso,babu wani abu daga garesu da yayi saura wanda zai dauki hankalinta ko yaja ra’ayinta,tafi ganewa ita dasu din ya zamana kowa yana daga nesa yana sabgarshi.

             K’arfe takwas saura ta fito a wanka,tadan makara kadan saboda wani littafi data soma dubawa wanda ya dauki hankalinta har taso gota lokaci,babban towel ne daure ajikinta daya bayyana fararen fatar dake qirjinta zuwa bayanta da kuma sambala sambalan hannayenta. Gaban madubi ta tsaya tana tsane jikinta da towel,sannan ta saka hannu ta zare shower cap din dake kanta,take gashin kanta ya warwatsu a kafada da kuma gadon bayanta,ta ajjiye towel din,ta jawo wata qawatacciyat stool ta zauna a kai,sannan ta jawo cream dinta ta fara shafawa. Batayi nisa da shafan man ba kiran afifa ya shigo,wanda shi ya qara mata nauyin shiryawar,sai data cinye kusan awa guda sannan ta kammala komai.

              Ta fito d’as cikin wani atamfa me asalin tsada da taushi,wadda ta yane atamfar da wata tsadajjiyar laffaya ruwan golden yellow da brown,kalolin da suka hadu sukayi masifar fidda kyanta.

         Kanta irin daurin nan da ake kira zahra buhari ne,wanda ya baiwa gashinta data nannade damar fitowa ta qasa,tsadadden agogon rolex ne a hannunta da wani sisirin zobe me qananun fararen duwatsu masu walwali,ta zura fararen qafafunta cikin wani lafiyayyen takalmi me matsakaicin tudu qirar kamfanin gucci mahadin qaramar handbag dinta. Bata wani tsaya batawa kanta lokaci wai ta duba komai yayi perfectly fine ba ta fesa lallausan turarenta ta dauki wayarta ta fito.

            Kamar ko yaushe muddin bawai baqi ne dasu ba falon gidan nasu shuru yake,ta duba agogon hannunta taga dai dai yake aiki da na falon,saita maida dubanta ga dining dinsu. Dan qaramin murmushi ta saki,baaba rabi kenan,komai ta shiryashi cif,saboda tasan yau zata fara fita aiki,duk da cewa tasan ita ba ma’abociyar cin abinci bace koda rana tayi ma sosai bare yanzu da sassafiyar nan,don ko tara na safe batayi ba.

            Tana shirin bullawa sassan maama,idan bata sameta ba ta qarasawa wajen abba don tasan bata wuce can saiga baaba rabi

“Allahu akhbar kabiran,dawisu gwanar ado,ummin abba uwar masu gidan,wannan kyau wannan kyau,hohoho” ba kasafai takeson wannan kodatan da baaba rabi takeyi ba,to amma ya zamewa baba rabin sara da dabi’a yabi jikinta,uwa uba kuma suna martabata saboda dadewarta dasu,suna bata wani girma na musamman

“Barka da warhaka baaba”

“Barka kadai uwarmu,an fito kenan,to ubangiji yasa a fara a sa’a,ya kauda dukkan abunqi,ya kuma kade fitina”

“Ameeen ya hayyu ya qayyumu,maama fa?” Ta tambayeta har cikin zuciyarta tana jin dadin addu’ar da tayi mata

“Ta shiga wajen alhaji” saita juya a nutse tana nufar can.

             Sai data tsaya ta ware igiyar takalminta a nutse tayi sallama ta shiga falon. Dattijon da fuskarsa me cike da kamala da kwarjini yana zaune cikin couch,hannunsa riqe da takardun qur’ani da yake zuwa pieces. A gefe ya ajiiye qur’anin cikin martabawa,ya daga kai yana dubanta tare da amsa sallamar tata,qaramin murmushi na fita saman fuskarsa,can qasan zuciyarsa kuma cike yake da fata,fata da buri me tarin yawa akan rayuwarta gaba daya.

            Daf da qafafunsa tazo ta rusuna har qasa

“Barka da safiya abba” gyara zamansa yayi yana dubanta

“Barka kadai ummin abba,an tashi lpy?”

“Alhamdulillah abba ya qarfin jiki?”

“Muna godewa Allah”

“Allah ya qara lafiya da nisan kwana me amfani”

“Ameen don nabiyyur rahmati,an fito aikin kenan?” Kai ta gyada a sanyaye

“Eh abba”

“To Allah yasa a fara a sa’a,yasa ya zamewa dukiyarki da lahirarki alkhairi,ki kare mutuncin kanki da kyau,don ke din ba yarinya bace qanqanuwa,duk da bani da haufi akan tarbiyyarki,amma dan adam saida tunasarwa da nuni,ki tsare gaskiya da amana,ki riqe aikinki da muhimmanci sai Allah ya dafa miki”

“In sha Allah abba,na gode Allah ya qara girma” kafin wani a cikinsu yace wani abu an turo qofar falon an shigo,maama ce da afifa da alama wani saqon ta kawo mata suke magana akai. Tayi mamaki da taga afifa din,ta dauka da wasa take mata sanda tace ita zata zo da kanta ta kaita office a ranarta ta farko,ta duqa gaban maama suka gaisa,al’adarta ce ba kasafai take iya gaida babba a tsaye ba,musamman mahaifanta,saita juya ga afifa daketa kallonta,bakinta fal da magana,idanun su abba ne kawai ya hanata cewa komai,har zuwa sansa suka fito.

       Bayan sunyi addu’a sun shiga sabuwar motar sãahar din saita waiwaya tana dubanta

“Bestie,kinga kyan da kikayi?,don Allah ki sassauta,karkije ki dinga hada ma’aikata fada a kanki” sosai sãahar ta tsuke fuska,saita sauke madubin gaban motar tana kallon kanta. Tabbas tayi kyau qwarai,komai data saka ajikinta ya haskata sosai,sai kawai ta sanya hannu zata balle murfin motar. Da sauri afifa ta tayar da motar tana dariya,saboda ta gama karantar abinda take da nufin yi

“Kome zakiyi,ke koda kashi zaki shafawa jikinki hakan bazai hanaki yin kyau ba sayyada” harara ta watsa mata

“Kinzo ne to spoiling my whole day afifa da maganganunki?” Ta fada manyan idanunta dake kan afifa kamar zasu fado. Kai ta girgiza tana dariya

“Ni na isa?,kefa yanzu amanar mahmud ce a wajena” fuska ta tsuke sosai tana kallonta

“Waye mahmud?,amanar me?”

“Ba zaki gane ba,amma dole na kula dake don amana ba wasa bace” ranta ya sosu sosai,saidai afifa tafi gaban haka

“Wai kasuwanci na kika fara afifa?” Dariya sosai afifa ta qyalqyale dashi har tana dan duqawa ga sitiyarin motar

“Idan ma shi na fara aiba laifi bane,tunda hankalinki yaqi dawowa gangar jikinki har yanzu” rasa me zatace da afifa tayi,sai kawai ta dauke kanta ta maida gefe tana kallon hanyoyin da suke wucewa,hanyoyin kano da safe wandada suke da qarancin kai kawo na jama’a,maganar duniya afifa tayi mata amma ‘yan miskilancin sun motsa,taqi koda waiwayowa bare ta tanka mata.

*************

         Kamar ko yaushe daya bayan daya motocin masu kama daya suke kutsawa kan titin da zai sadasu da katafaren kamfanin MT GLOBAL COMPANY,duk da cewa cikin combo suke,amma mota guda dayaa a ciki ta fita zakka,mercedes maybach s580 sand color dake masifar daukan hankulan jama’a duk inda ta gifta.

Page 15

        Kofar tafkeken gate din kamfanin suka tsaya,kafin sukai ga sanar da isowar CEO OF MT GROUP OF COMPANY har jami’an tsaron dake kai kawo a qofar company din sun ture musu gate din gefe,sannan suka qame dukkaninsu suna sara musu har zuwa sanda suka gama shigewa tsaf,suka maida qofar suka rufe.

          Cikin nutsuwa da sanin doka da order dukkaninsu suka faka a matsayar motoci ta company din,saidai daga gefe guda dake nuna waje ne kebantacce saboda ajiyar ababen hawa na musamman,don akwai qarfen daya raba tsakaninsa da ragowar filin ajiyar motocin.

           Yadda motar ke daukan hankalin kowa haka ta dauki hankalin afifa data taqarqare a dazun tana zubawa sãahar bayanin da yasa takw kallon afifan kamar wata statue

“Wai ta riqe amanar mahmud?,to shi mahmud qanin maama ne ko qanin abba?,yaushe ta karba amanar tasa da har zatayi mata roqon riqewa?,banda afifa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata wannan zancan ta barshi tana kallonshi haka.

            Saida suka gama fakawa sannan ta maida dubanta ga sãahar

“Kinga abinda na gani kuwa?” Ta jefawa sãahar tambayar cikin zallar mamaki,da kuma tafiya da hankalinta da motar tayi.

          Ido kawai sãahar din ta lumshe tare da budesu lokaci guda ba tare data amsawa afifa ba

“Wow….wow…..mybatch vigil abloh fa?,kinsan mutum 150 ne duka duka suka mallaketa a duniya gaba daya?”

“Zan iya tafiya?” Sãahar ta jefeta da wannan tambayar,cikin bawa maganarta rashin muhimmanci,saidai afifan ci gaba tayi da koro mata bayanin zallar tsadar motar da darajarta,sai kawai tasa hannu zata buda motar.

           Caraf ta riqo tsintsiyar hannunta

“Don Allah ki barni naga wanne me sa’ar ne ya mallaki wannan motar,wanne DON dinne?” Idanu ta kafe afifa dashi tana mamakin qaunar da afifa kewa motar,already tasan halinta,she’s a classy ladie,amma me yaja hankalinta haka?. Ido ta zuba mata tana kallon yadda ta natsu tana mata bayani tare da kallon sashen da motar take.

           A qalla an kusa kwashe minti biyar bayan fitowar duk mutanen dake cikin sauran motocin kafin motar ta bude a hankali ya kuma zuro jikinsa zuwa waje,zuwa sannan idanun sãahar nakan wayarta tana dannawar dole,saboda ta cika maqil da takaicin afifa data hanata fita,ga saukar yayyafi da aka fara samu siri siri,wanda ita kuma kwata kwata bata qaunar ruwa ya taba jikinta

           cikin shigar wata lafiyayyar suit ta zallar cashmere wool,charcoal color yake,idanunsa manne da baqin eye glasses,wanda zaiyi wuya ka iya ganin qwayar idanunsa,hannuwansa duka cikin aljihun wandon suit din,yana takawa da sassarfa sosai yana kuma magana a waya ta Bluetooth din kunnensa.

“Tabarakallahu ahsanul khaliqeen,don Allah dago ki tayani ganin wani kyau a nan” afifa ta fada tana tabo hannun sãahar,tana kuma qunshe dariya a cikinta,ya tafi da ita matuqar tafiya,amma tanasl ne itama ta rama ta qunsa mata takaicin yin shuru da tayi sanda taketa babatun mata batun mahmud.

            A maimakon ta kalla inda afifa keson kalla saita kallo afifan

“Na kalli me?,kedai da kika zabawa kanki ganin kyan dan maciji na d’a namiji ai sai nace miki bismillahi,Allah ya bada sa’a” ta fada wani fushi yana motsawa daga qasan zuciyarta,kai afifa ta girgiza

“Ba haka bane sãahar,ban taba ganin irin wannan a zahiri ba Allah i swear,there was no denying that the handsome man was charming,he was elegant in every way Allah,don Allah ki kalla ki gani,zaki tabbatar ba qarya nakeyi ba” haushi ya sake qure sãahar,takaici da bacin rai yasa ta daga kai zuwa sashen da take roqarta ta kalla din,dai dai sanda yake wucesu cikin tarin ma’aikata zuwa main entrance na building din kamfanin.

           Siririn tsaki sãahar taja,ta kuma watsawa afifa harara

“Wai me ya shiga kanki ne yau?,lallai ya zama dole na gayawa su maama suyi gaggawar aurar dake,tunda kin fara sumbatu”

“Ba sumbatu nake ba,don Allah bakiga abinda na gani ba?,haduwa iya haduwa?,he was striking,no one could take their eyes off his good look”

“To ina ruwana?” Ta fada tana jin ta fara hasala,sai afifa ta qwace da dariya,tasan tayi mata abinda tafi tsana a rayuwarta,zancan d’a namiji,kuma har ta zauna tana kodashi haka,duk sa cewa YES wannan din yakai ya wuce ma yadda idanun me kallo zai ganshi,yana da wani irin kyau me sanyi haiba da kuma kwarjini na musamman.

         Kafin afifa ta sake cewa komai sãahar ta buda murfin motar ta fice abinta

“Zan wuce da motar,zan bayar a dawo miki da ita sanda zaku shiga lunch break” gyara yafen laffayarta tayi kawai,ta soma takawa a nutse zuwa ciki ba tare data amsa kota waiwayi afifa ba,yayin da afifan ke binta da kallo,murmushi na fita akan fuskarta. Komai na ‘yar uwarta me kyau ne,komai na ‘yaruwarta me aji ne,iyakar dukka inda mace takai ga aji da kyau takai,amma abu daya ya tsaida duniyarta cak,saita girgiza kai ta tashi motar bayan taga shigewarta building din.

          Cikin nutsuwa da kamewarta take takawa,a  nutse kuma ba kai tsaye ba tana karantar yanayin kamfanin da kuma inda take takawar,tun daga wajen ta sake karantar girma da tsarin kamfanin,kusan kowa ya duqufa yana aiki sosai,tun lokaci baiyi nisa ba,amma kowa yana mazauninsa ya riqe aikinsa.

“You are highly welcome madam” taji an fada daga gefanta,saita waiwaya a nutse. Matashi ne sanye da shirt da trouser lime green da baqi,yayi maganar cikin zallar girmamawa yana dan rusunawa kadan

“Fourth floor zaki sauka,akwai ma’aikatan dake jiranki a can,zasuyi guiding naki akan komai” ya fada cikin girmamawa,saita jinjina kai ta kuma taka zuwa bakin elevator,ta danna ta shiga,tayi kuma selecting number din floor din da takeson sauka,sannan ta koma daya daga cikin corners din dake cikin elevator din ta goye hannayenta a qirji,idanunta qyar akan numbers din dake jere daga bakin qofar shiga na’urar, zuciyarta na fara ayyana mata ko yaya zamanta cikin wannan babban company zai kasance?.

              A second floor elevator din ya tsaya,da alamar akwai wani dakeson shiga shima,idanunta akan bakin qofar,har zuwa sanda ta bude. Fes ya bayyana daga gaban qofar,fuskarsa na kallon gefansa yana magana da wani cikin nutsuwa da kamewa,duk da cewa baka iya jin abinda yake fada,amma yadda yake maganar cikin izza da kamewa zai gaya maka umarni yake bayarwa.

          Yana gama maganar yayi taku biyu don isa cikin elevator din,karon FARKO idanunsa ya sauka a kanta,kamar yadda itama karon farko nata idanun suka shiga cikin nasa,tsahon tsaiwar da elevator din yayi sai a sannan ta dubi wanda ke bakin qofar da nufin shigowa ciki suyi tarayya na wasu sakannin da zasu kai kowa inda yayi nufin zuwa. Lokaci guda kuma a tare kowa ya janye idanunsa,ta kauda kanta gefe guda tana tsuke fuskarta,ta gane fuskar,fuskar mutumin da a dazu afifa ta cikata da zancansa,saita sake tsuke fuskartata,tana jin qyamatar hada guri dasu,kamar yadda takeji a ranta game da duk wani DA NAMIJI.

            Sanda taji anyi releasing elevator din ya wuce ba tare da an shigo ba sai taji mamaki kadan ya kamata,ta maida dubanta ga qofar taga taci gaba da hawa zuwa saman,saita yarfar da hannunta tare da tabe bakinta,ita dama hakan takeso,bata buqatar hada numfashi da jinsi irin nasu.

           Fitowarta daga ciki yayi dai dai da matsowar sajjad dake cikin aiki kace kace,amma Dr girema ya tasheshi takanas saboda ya marabci sãahar din,ya kuma tabbatar ya bata duk abinda take da buqata da zai sake jin ta gamsu da aikin da kuma kamfanin gaba daya.

           Kamar wancan data baro a qasa haka shima yayi welcoming nata,sannan cikin sanin kima da darajar dan adam daya sanyata tadanji zuciyarta ta saki kadan yace mata

“If you don’t mind……i will show you your office” kai ta jinjina kadan,yayi gaba tana biye dashi,sannan sauran ma’aikatan da suke qarqashin kulawar office dinta.

            Kusan kafin ya fita sai daya gabatar mata da komai da take da buqatar sani,tana zaune saman kujerar da sai da tayi addu’a sannan takai ga zama,ta bada dukka hankalinta ga bayanansa,abinda zai nuna maka zallar seriousness dinta,yanayin yadda kyakkyawar fuskarta ke a tamke ya isheka shiga taitayinka da tabbatar maka ba zata dauki wargi ko wasa ba,har ya kammala,saita dan lumshe kyawawan idanunta kadan sannan ta budesu

“Inason a sanarwa suk department din dake qarqashin wannan office din akwai general meeting a gobe”

“In sha Allah” ya fada sannan sukayi mata sallama suka fita don bata damar duba ayyukan da aka tsaya akai don ta dora.

           A nutse ta fara buda computer din dake gabanta,ta soma aika saqon email zuwa ga sauran department dake cikin kamfanin da sauran dukka board members,tare da introducing kanta,email guda daya daya rage zata turama,wani saqo ya shigo mata ta email,abinda ya janye hankalinta kenan ta shiga Wani aikin daban,sai kuma ta shiga binciken dame dame aka aiwatar cikin office din.

              Cikin qwarewa tare da amfani da zallar basira take sarrafa na’urar,da wani irin qwarin gwiwa da karsashi da batasan ya sauko mata ba. Ta kusan kashe awa biyu cur,kafin ta zame hannunta daga kan computer din,ta kuma maidasu saman fuskarta ta rufe fuskartata da kyau tana fidda numfashi me dumi daga bakinta. Ta fuskanci akwai jan aiki a gabansu,da kuma wasu al’amura na rashin gaskiya masu tarin yawa da aka aiwatar,wadanda sune suka taka rawar gani wajen kawowa company din naqasu da kuma koma baya,ta tura kujerar ta baya tana hade yatsunta da suka gaji guri daya ta lanqwasasu da kyau,dai dai lokacin kiran afifa ya shigo wayarta.

            Har ta saka hannu zata daga wayar saita fasa,ta jefawa wayar harara kamar itace afifa din,saita miqe bayan ta zare takalman qafarta,ta taka saman lallausan carfet din da zai sadata da qawataccen fridge din dake office din tana sake nazartar office din,komai an shiryashi base on her favourite colors,har ta soma zargin anya ba tare da yaa muhyi aka zuba furniture na office din ba?.

          Komai an tanadeshi,don hatta fridge din cike yake da kalolin drinks,ruwa kawai ta dauko,ta dawo ta zauna saman couch masu laushi da aka shirya daga gaban table dinta bayan ta dauko wayarta.

            Sms guda biyu ne suka shigo kusan lokaci daya,na afifa ne a sama,shi ta fara budewa

_”I hope you are enjoying your work?,god bless you dear,All the best”_. Dole murmushi ya subuce mata,afifa ta wajenta,ayi dadi ayi tsiya,saita maida mata amsa a taqaice

_”All is well bestie,thank you”_. Komawa tayi ta duba saqo na biyu

_”assalam gimbiya,iam wishing you a joyful day,i hope you will remain blessed,fatan nasara,mahmud A gana”_ dogon tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,saita goge saqon kamar yadda ta saba,ta bude gorar ruwan ta zuba a glass cup ta fara sha tana tunanin next abinda zata aiwatar.

Page 16

          Dogon tsaki taja kamar zata tsinke harshenta,saita goge saqon kamar yadda ta saba,ta bude gorar ruwan ta zuba a glass cup ta fara sha tana tunanin next abinda zata aiwatar.

        Tun daga sama zuwa qasa ta tsaya ta qarewa kanta kallo da kyau,tayi taku biyu gaba ta sakeyin taku biyu zuwa baya,taja rigarta baya kadan yadda zata dauki hankalin duk wani daka iya kallonta ko yakai idonsa kanta bisa tsautsayi ko kuma dace. Ta waiwaya kadan jikin wata qofar glass dake baka daman ganin fuskarka tamkar madubi,ta fito full hakanan dressing nata,saita saki siririn murmushi tana maida gashin kanta baya wanda tasa gantalallen scarf ta lullube rabin gashin dashi.

           A nutse ta koma ta zauna saman kujerarta ta zauna tana sake sakin murmushi,ita kadai tasan farincikin da takeji cikin ranta,tayi matuqar samun sa’ar da bata zata ba data zama secretary dinsa,bayan dogon hanyar da tabi me cike da tangarda kafin cimma muradinta. Tasan cewa a gata dukiya ilimi da kuma kyau na halitta da take dashi dukka tafi qarfin matsayin zama secretary,to amma….muddin akan MUHAMMAD TAUFEEQ ne,ta shirya zama massinger ma bawai iya secretary kawai ba. Maida qafarta tayi ta harde daya saman daya,ta bude computer din ta soma sarrafata.

      Cikin qasaita da izzar nan tasa data zame masa jinin jiki ya sanya kai zuwa babban office dinsa daya kasance na daya duk fadin company din,sauran ma’aikatansa da na biye dashi.

         Jibril ya buda qofar,dukka suka dataka ya fara shiga sannan suka rufa masa baya. Da sauri ta daga kanta tana duban qofar,saita miqe cikin sauri saidai kuma cikin salo na yanga da yauqin da take amfani dashi wajen farautar hankulan maza. Gabanta na wani irin faduwa,zuciyarta tana bugawa da qarfi sanadin ganinsa da tayi.

          Mamaki ya kusa daskarar da ita sanda taga baiko kallo koda sashen da take tsaye ba,tamkar ma baisan da wanzuwar wata halitta a wajen ba,dole ta tattare guntun iyayin kalamanta data tsara yi masa magana dasu,ta zare jikinta daga kujerar tabi sauran ayari zuwa cikin office dinsa gaba daya,gabanta na faduwa,tana fatan duk wani shiri nata ya dinga zuwa mata da sauqi fiye da yadda take tsammata.

             Kamar wanda tsaiwa ta zamewa dabi’a,ba kasafai ya fiya damuwa da zama saman kujera ba,yanzunma haka ce,daya bayan daya ya sallamesu,ya rage saura sajjad da jibril. Jibril din ya duqufa da duba wasu takardu,yayin da sajjad suke magana qasa qasa da ita,duk da cewa gaba daya hankalinta yana a kanshi,yayi mugun tafiya da ita,shigarsa ta yau ta dabance dake nuna aiki zallah.

“Ehnnnn” ya fada a taqaie yana jingine da mulmulallen table dinsa dake tsare da files da suke jiran isowarsa,ya zuba duka hannayensa a aljihun wandonsa,yayin da yayi crossing qafafunsa.

           Da sauri jibril ya dago kansa,sannan ya fara magana

“Sir,muna expecting ziyara daga gurin Dr at any moment” kyawawan idanunsa ya lumshe yakuma budesu a lokaci guda

“Okay,the meeting has been postponed,a canza date zuwa gobe”

“Zan sanarwa kowanne department” tayi caraf da zancan,ganin cewa dukka wannan abun aikinta ne,ita ya kamata ta sanar masa da kowanne tsari,amma jibril yana aiwatarwa,hakan na nufin ita ‘yar kallo zata zama kenan?. Ta yiwa kanta tambayar da bata da amsarta.

            Har yanzun bai nuna alamun yasan da wanzuwarta a wajen ba,bare maganar da tayi,yaci gaba da magana da jibril ya sallameshi. Sajjad ma ya ajjiye masa dukka files din daya kamata ya juya ya fita,cikin zuciyarsa tausayin SAIMA yana kamashi,tabbas SON MASO WANI qoshin wahala ne,yayi imanin babu abinda zata tsinta daga wajensa face tsantsar bacin rai da kuma batawa kai lokaci,inda zata dauki shawararsa,abu daya zaice da ita,ta kama kanta,ta kuma kama martaba da kimarta ta diya mace,shine kadai abinda zaisa ta tsira a idanun TOUFEEQ din.

            Kujera yaja ya zauna har yanzu dai bai bata hankalinsa ko da na second guda ba,wannan duka bai sanya ta sare ba,ta tako zuwa gaban table din a hankali ta tsaya,dai dai sanda yake rubutu saman wani file

“Sir…..akwai wani abu da kake buqata?” Tayi maganar tana dan zame rigarta kadan don ta bawa qirjinta damar fitowa,ko Allah zaisa ya daga kansa gareta,sai daya bude page din gaba na file din sannan ya fara magana,cikin muryar sa din nan dake cike da zallar qasaita da kuma izza

“Banason yawan magana,bana kuma son shishshigi,kiyi qoqarin cire kanki daga dukkan abinda ban gayyatoki a ciki ba,karki soma wuce limit dinki,any moment kuma kamfani zai iya sauyaki idan aikinki baiyi ba,these are my conditions,you can go”. Wani abune yazo ya tsaya mata a wuya,ta dan zuba masa ido tana jin sonshi yana ninkuwa a ranta,amma bata taba kawowa zaiyi mata irin wanna yankan qaunar da wuri ba haka,tasan halinsa,fes zai iya yanka mata jan card idan ta tsallake abinda ya gaya mata yanzun,dole ta miqe jiki a salube ta fita a office din,tana saqawa ranta abinda zai fishsheta,ba zata taba iya jure irin zaman da shi ya tsara zasuyi ba.

          K’arfe daya na rana zuwa biyu shine lokacin break na kamfanin,masu cin abincin rana da masuyin sallah ga musulman ciki,wannan kuma duk umarni ne na CEO,ya sauya fasalin abubuwa da yawa cikin sati guda a kamfanin,da yawan ma’aikatan abubuwan sun musu dadi,amma ga wadanda sharholiya kadai suka sanya a gabansu wasu abubuwan basu yiwa tsarinsu dai dai ba.

         Bata da ra’ayin zuwa kitchen,wanda aka tanadeshi musamman saboda manyan offices kamar nata,don haka ta umarci miss sameera ta samo mata coffee kadai. Ba kasafai take sakewa taci abinci ako ina ba,shi yasa ma baaba rabi taso shirya mata wani abun ta taho dashi,duk da tasan babu lallai ta maida kai taci yadda ya kamata.

          Cikin toilet dinta dake office din ta daura alwala,ta dawo corner ta musamman da aka tanadarwa office din don yin sallah,ta gyara lullubinta ta tayar da sallar. Kafin ta idar miss sameera ta dawo,ta ajjiye mata coffee din,ta koma ta tsaya tana jiranta ta idar da sallar.

         Cikin girmamawa ta matso bayanta kadan bayan ta idar

“Akwai email da aka turo miki daga ceo office,kusan minti talatin kenan,ina kyautata zaton baki gani ba” kai ta gyada mata a nutse tana dubanta

“Boss ne ya iso,yana office na ceo,he wants meet you” jim tayi na wasu ‘yan mintuna,sannan ta maida dubanta ga miss sameera,kai ta gyada mata a natse,ita kuma ta jinjina kai ta juya ta fice.

             Fuskarta da daurinta ta gyara kamar yadda yake,kamar bata sanyawa fuskarta ruwa ba,tanana da qyallin nan da gogewar fatarta,saika dauka tayi amfani ne da powder. Ta gaban table dinta ta tsaya ta danyi sipping coffe din,bata ma iya shanyewa ba ta fito ta cimma miss sameera na jiranta a farfajiyar data fi kama da parlor wadda zata sadaka da office dinta.

          A nutse take takawa cikin shigar tsadaddar laffayar data lullube ilahirin jikinta,duk inda ta gifta sai tayi gaba da hankula da kuma idanun kaso mafi yawa na ma’aikatan kamfanin,walau maza ko mata,ko ina akwai shige da ficen ma’aikata,kasancewar lokaci ne na hutu. Ko daya babu wanda ta baiwa hankalinta,cikin kamewa da nutsuwa har suka isa qofar office din,mr sameera ta tura qofar tayi gaba,sãahar tabi bayanta.

          Wani irin katafaren office da babu irinsa kaf kamfanin,wanda ke dauke da sassa biyu zuwa uku,waitin parlor wanda saima ke ciki ita da tarin takardu da kujerun da aka qawata gurin,sai rest room daura dashi kuma main office din da zaka gudanar da ayyukanka. Idan ka kira office din da aljannar duniya akai tsaye sam bakayi laifi ba,saboda ya amsa sunan,wasu irin colors da design me matuqar tsari da aka qawata kowanne sashe na office din.

          Sallamar miss sameera ya sanya saima daga idanunta daga kan computer,maimakon idanunta su sauka kan sameera,sai suka fada kan sãahar dake qoqarin daga kiran daya shigo wayarta

“Zaki iya sanarwa da sir isowar president?” Sameera ta yiwa saima tambayar,lokacin da ta tattara dukkan hankalinta akan sãahar da nata hankalin yake kan khalipha dake mata complain na tafiyar da tayi baya nan,lallausan murmushin dake masifar qawata mata fuska ne kwance saman fuskartata,har jerarrun fararen haqoranta da suka zama tamkar hasken lu’ulu’u suna fitowa,wani luguden abu taji ya saukar mata,tana da labarin dukka sabbin ma’aikatan kamfanin a yau zasu kama aiki kamar dai ita,tabi diddigin kowacce mace dake cikinsu,musamman wadanda ya zamana mu’amala zata iya hadasu da office din TOUFEEQ dinta,to amma ita din ita kadai tak! Ta kasa samun komai a kanta,ta gaza cimma wani bayani daya shafeta har zuwa lokacin data taka qafarta ciki kamfanin,sai yanzu,karo na farko

“Excuse me,ko ta shiga ne?” Sameera ta fada cikin girmamawa da kuma zaquwar ganin yadda saima ta kasa amsa maganarta ta farko.

         Iska taja sosai a cikin hunhunta,ta qanqance idanu tana duban sameera,duban da zataso ace president din da kanta ta yiwa shi,saidai ba zatayi garajen aikata hakan ba,don batasan wace ita ba,kada ta aikata abinda zai zame mata matsala,ya kuma zama silar cisgeta daga bigiren data dora buri akai

“Sir yana tare da babban baqo wato mahaifinsa,saidai ku dawo wani time din,kafin lokacin na sanar masa” tayi maganar tana ci gaba da dannan system dinta,dai dai sanda sãahar ta gama wayar,ta zameta daga kunnenta tana kallon sameera dake jiran ta kammala wayar tayi mata bayani. Kafin tace wani abu sãahar ta rigata

“Thank you,na gode da rakiya,zaki iya komawa office” tayi maganar kanta tsaye tana kyakkyawar qofar da a samanta take liqe da takardar dake bayanin inane nan gurin ba tare data waiwayi saima ba.

Page 17

         Wani abu ne ya tasowa saima,yayi mata tsaye a wuya,ta riga ta saka hannu kan dokar yin biyya ga wanda yake sama da office dinka,me yasa bata nema matsayin president ba?

“Neman kusanci da taoufeeq” zuciyarta ta bata amsa kai tsaye,ajiyar zuciyar baqinciki ta sauke,ta koma tayi relaxing cikin kujerarta tana qarewa qofofin guda biyu dake facing dinta kallo, zuciyarta na wani irin tsalle cike da luguden kishi,har tsahon wani lokaci toufeeq din zai kwashe kebance da wannan kyakkyawar halittar data bar mata sassanyan turarenta na yawo cikin dukka qofofin hancinta?.

           Cikin nutsuwa kuma dauke da sallama ta tura qofar office din. Kyakkyawan dattijone da shekaru sam basu samu nasarar ture kyakkyawan fuskar da Allah ya mallaka masa ba,fari ne sol,farin dake gwada tashen kyau da farin daya zuba zamanin quruciya,yana zaune saman sofa qwaya daya dake cikin office din,ya dora qafarsa daya kan daya,system dinsa na saman qafar tasa yana dannata cike da qwarewa.

           Cikin kamala ya waiwayo yana amsa sallamar tata,idanunsu suka gauraya,kwarjininsa da kuma kamalarsa suka cika idanun sãahar,yayin da murmushi ya wadaci fuskarsa

“Lale maraba da ‘yata,president dinmu” dattijon da shekarunsa suka suka rufa sittin ya fada yana sauke qafafunsa qasa. Da dan sauri ta daga kanta daga sunkuyar dashi din da tayi da farko tana duban dattijon duba na mamaki,ita dai zata iya cewa kaf rayuwarta yaune karon farko data fara ganinsa ma gaba daya,sani kuwa saidai na fatar baki kawai wajen yaa muhyi,to amma shi din ya akayi yasan wace ita

“Daina mamaki diyata,kamanninki da d’ana muhyiddeen ta bayyana sosai a fuskarki…..” Cikin girmamawa qaramin murmushi ya subuce mata,bata taba jin ance suna kama da yaa muhyi ba sai yau,tana shirin gaidashi ya tareta

“Koma ki shiga resting room ku jirani keda d’an uwan naki” ya fada cikin kulawa.

“Dan uwana?” Ta tambayi kanta cikin mamaki,waye cikin gidansu yazo company din ba tare data sani ba?,kodai yaa muhyi ne bai nutsu ba sai daya biyota?,bata sani ba,saita juya a nutse taja masa qofar ta fito.

           Qofa ta biyun ta dosa tana takawa a nutse,zuciyarta na qawatuwa da karamcin tsohon da kuma kirkinsa. Tsaiwa ta danyi kadan tana sauraren muryar dake fita daga dakin,wata irin husky voice me zurfi da wani irin amo,cikin fada da kuma tsawa muryar ke fita,saidai kuma a nutse sautin yake fita kuma a jejjere,cikin ginshiri da wani abu da yayi kama da QASAITA.

        Hannunta ta sauke daga kan handle din,tadan yamutsa fuskarta kadan,zuciyarta na mata fatan Allah yasa ba halittun maza aka tara a dakin ba,muddin hakan ta kasance bata jin zata iya dogon zama a tattaunawar tasu.

          Cikin bawa kai qwarin gwiwa ta sake dora hannunta saman handle din,kalmar da taji ta fita a bakin mamallakiyar fusatacciyar muryar me zurfi yasa ta sake dakatawa

“You are fired,stupid woman” cikin qasa da second biyar qwaqwalwarta tayi mata rewinding,sak irin muryar da taji tana magana da wata mace cikin tsawa a bristol palace kwanakin da suka wuce,daga bisani kuma qarar mari ya biyo baya,qarar marin da ko a yanzun sai data sanyata rintse idanunta kamar a lokacin ake yinsa,ta kuma damqe hannunta abinda ya sanyata murda handle na qofar ba tare data shirya ba,saiji tayi ta tafi kai tsaye zuwa cikin dakin.

         Cak ta tsaya daga bakin qofar,idanunta yana nutsawa ga tsakiyar dakin. Kallonta bai sauka a ko ina ba sai akan budurwar dake sharban kuka,kyakkyawar budurwa wadda zubin dressing dinta ke nuna zallar iya gayunta da kuma wayewarta. Dauke idanunta tayi daga kanta tana jin zuciyarta na zafi,ta sauke a hankali a kansa. Tsayyayen namiji sosai mai cikar haiba izza da kuma kamala,hannunsa daya yana sanye a aljihun wandon suit dinsa,daya hannun kuma yana danna wayarsa da zafi zafi. Dai dai sanda yake sanya wayar a kunnensa ya juyo,idanunsu suka sarqe guri daya.

          A tare suka sake janye idanunsu kamar dai wancan karon,zuciyar sãahar cike da wani irin tsanarsa da kuma jin haushinsa,ko kadan maza basu da tausayi bare imani,suna amfani da raunin mata suna cutara musu,hakan wani karatu ne da take yawaita bitarsa a kwanyarta a duk lokacin da taga ire iren wadan nan rashin imanin na maza akan mata,saidai a yanzun shi din tamkar yana sake jaddada mata cewa haka tunaninta yake,karo na biyu data taba saninsa a rayuwa,amma duk sanda zata ganshi din cikin wulaqantawa da wofantar da kimar mata yake

“Ka sallameta da albashinta na wannan watan,ka hada dana watan gaba,banason ka nemeni akan wannan issue din,case closed” ya fada da murkakkiyar fuskarsa wadda ko kusa batayi kama data mutumin daya taba gwada yin dariya ba arayuwarsa,ko da yake a wajen mutane da yawa da suka sanshi haka suke kallonsa,sukan tambayi kawunansu harma da abokan huldarsu

“Wai shin yana dariya?”

“Shin wai ya taba dariya kuwa?”

“Ka taba ganin dariyarsa?”.

           A nutse ta taka ta yiwa kanta mazauni saman daya daga cikin couches din dake zagaye da qawataccen dakin,wanda aka yiwa tsari me ma’ana da baiwa ruhi kwanya harma da zuciya hutu. Dai dai lokacin daya kammala wayar,a karo na biyu ya sake daga kai ya sauke sexy eyes dinsa a kanta,wani fushi ne ya sake taso masa,wacece ita da har zata shigo masa dakin hutawa a sanda yake da buqatar hutu ba tare da izininsa ba?,wacece ita da zata shigo dakin da ba kowa yake baiwa izinin shigowa ba,har ta yiwa kanta da kanta mazauni ba tare data nemi yardarsa ba?,me ta dauki kanta?,dukka wadan nan maganganun dake ransa,shigowar Dr mahmud JARMA ya datsesu daga kwanyarsa,sai ya maida dukka hannuwansa cikin aljihun wandonsa,ya tattara hankalinsa ga mahaifinsa.

           Sosai yake mata kwarjini da wani irin haiba dake bayyana a fuskarsa,don haka ta miqe tsaye sanda yake shigowar,cikin nuna girmamawa

“D’iyata ina fatan ban bata lokacinki ba ko?” Kanta a qasa tana murza zara zaran yatsun hannunta,cikin siririyar muryar nan dake da wani irin taushi da amo tace

“Babu komai abba” a hankali ya lumshe idanunsa yana zuqar numfashi da kyau zuwa hunhunsa,lokaci daya yaji wani abu me kama da rashin jituwa ya darsu a ransa,fitar sautin muryarta kawai yaji a ransa yarinyar batayi masa ba kwata kwata

“I hate it” ya fada can qasa yana sauraren muryar tata sanda take magana da abban nasa a karo na biyu. Haka kurum yaji zuciyarsa tana zafi,sai ya koma a hankali ya yiwa kansa mazauni akan daya daga cikin kujerun da aka tanadesu domin hutawar,wadanda zasu bawa gangar jiki qafafu da kuma baya daman zama Sosai su samu nutsuwa.

         Yana jinsu sanda dr mahmud yake zama saman daya daga cikin sofa din dake dakin,har zuwa sanda yake umartar sãahar data zame ta zauna saman lallausan carfet din da aka ajjiye tsakanin kujerun

“Tashi ki zauna saman kujera mana,wannan meeting ne zamuyishi tamkar sa’anni,bawai na uba da ‘ya’yansa ba” yayi furucin sãahar din na sake shiga zuciyarsa,d’a’arta nutsuwarta da tarbiyya girmama na gaba data samu suna sake saka mata qaunarta tare da jinta a zuciyarsa tamkar TOUFEEQ dinsa. Murmushi ta danyi kadan,sannan ta koma saman kujerar kamar yadda ta buqata.

            A nutse ya waiwaya ya dubeshi,sai ya zuba masa idanu,yadda yayi kamar baya gurin da lumsassun idanunsa da eyelashes suka yiwa ado ya tabbatar ‘yan halin sun motsa ko suna kusa,don haka yayi gyaran murya,ya kuma kirayeshi da sunansa na aihini

“Muhammad” kiran sunan da ya sanyashi ware idanunsa a hankali,a nutse ya rabo bayansa da jikin kujerar,ya zauna sosai hadi da crossing qafafunsa dake sanye da wata shiny black socks guri daya

“Ga khadijatou,itace sabuwar president na kamfanin nan da zakuyi aiki a tare,nake kuma fatan zaku kai kamfanin zuwa tudun mun tsira,inaso ka dauketa tamkar NADEEYA,infact….na damqa amanarta a hannunka kamar yadda yayanta na damqamin” idanunsa yadan lumshe kadan sannan ya budesu lokaci guda,yana jin maganar abban nasa wani iri,ba aiki tazoyi don a biyata ba?,ko raino aka kawota da za’a buqaci a bata kulawa?,kudi tazo nema fa,an yarda za’a biyata ita kuma ta yiwa kamfani aiki,fine…….ba shikenan ba?.

“Na yarda da kaifin basirarta,na tabbatar kuma idan kuka hada gwiwa,kuka hada qarfi da qarfe za’a samu kyakkyawan result din da akeso” maganar abban a gaba ta biyu ta sake katse masa tunaninsa. Baiko tsaya din ta bakinsa don yasan halin kayansa,ya waiwaya ga sãahar data nutsu tana sauraren maganganun dattijon,duk da tafin hannunta take murzawa a hankali

“Khadijatou,ga MUHAMMAD nan,a matsayin yayanki yake,kada kiji nauyi,idan kina da buqatar wani abu,koma meye ki tambayeshi,bashi da maraba da muhyiddeen,kinji ko?” Kai ta gyada masa,a taqaice tace

“In sha Allah,we will do our best”

“Barakallahu lakuma,zanyi alfahari da hakan”.

           Duk su biyun ya saka a gaba yana nuna musu wasu muhimman abubuwa da suka shafi company din wadanda su basusan dasu ba,toufeeq na hannun damansa,ita tana daga hagunsa,a lokacin idan ka shigo zaka dauka duka ‘ya’yansa ne,shi kansa cikin zuciyarsa sai daya ji hakan.

           Tsahon wasu mintuna kusan arba’in da wani abu sannan ya dakata yana dubansu bayan ya kalli tsadajjen agogon hannunsa,ya dan saki murmushi saman dattijuwar fuskarsa

“Inajin a nan zan tsaya,kusan muhammad kasan komai,zan barka da khadijatu,sauran abinda ya rage saika qarasa nuna mata kayi mata bayani,for the first time zatayi aikin kamfani,but tana da talent sosai,zan wuce kada nayi missing flight” ya furta yana miqewa. Dai dai lokacin da daya daga cikin guard dinsa yayi knocking qofar bayan ya samu alert dake nuna Dr din yana buqatarsa. Komai ya tattarawa uban gidan nasa,dr ya miqe yana duban toufeeq da shima ya miqe

“Koma ka zauna,ku qarasa kada lokacin tashi yayi” yadda yayi masa sallama haka itama sãahar,cikin girmamawa da ganin kimarsa,ya juya ya fita a office din,yana jin farinciki har cikin zuciyarsa.

           Shuru ne ya ratsa office din tamkar babu sauran wani me rai,shi din yana daga saman kujerarsa,yayin daya dora sambala sambalan qafafunsa akan leg rest na jikin kujerar,yana kuma sarrafa computer dinsa cikin qwarewa da hannu daya. Ko sau daya bai dago kai ko yayi wani motsi da zai nuna yasan da mutum cikin office din ba,dai dai lokacin da sãahar ke zaune don cika umarnin dattijon,wayarta itama take sarrafawa,lokaci lokaci tana duba agogon hannunta,tana jiran kuma lokacin data dibawa kanta ya cika tabar masa office dinsa.

          Kowanne a cikinsu jin kansa ya hanashi ya fara tankawa dan uwansa,cikin zuciyar sãahar tsanarsa da haushinsa ne fal suka danqare mata,ba tun yau ba tasan baisan darajar diya mace ba,bai martaba kimarta sam,a nasa sashen kuma ji yake sam batayi masa ba,tunda suke da Dr bai taba ganin mutumin daya jawo jikinsa har haka ba,farat daya ya maidashi tamkar ahalinsa,ya bashi dukkan yarda ya bude masa sirrinsa,yasan halin mata sarai,basu da kirki ko kadan muddin suna da wata manufa akan abu……tofa basa ji basa kuma gani harsai sun cimma muradinsu,suna iya komai,hakanan suna kuma iya jure komai har sai sun cimma gaci,musamman akan KUDI DA DUKIYA,suna sa masifar son kudi,tamkar wata halitta ce aka dasata cikin jininsu,basayin komai don Allah,bayason shi ko wani nasa ya sake fadawa MASIFA DA TARKON MACE,wannan wani HUKUNCI ne nashi da ya jima da yankewa akan kowacce mace idan ka debe MUTUM UKU RAK cikin rayuwarsa.

          Sai da ya mula don kansa sannan ya janye hannuwansa da idanuwansa duka daga kan computer din,ya sarqe yatsunsa cikin na juna yana fitar da sassanyar siririyar iska daga bakinsa,ya maida shanyayyun idanunsa dake da wani irin qarfin fusgar hankali a muhallin da take sai kuma ya janye yana jin wani qyashi yana kamashi,dai dai sanda take miqewa a nutse cikin nata jin kan,ta zura takalmanta a nutse ta fara takawa zuwa bakin qofa

“Hey,da alama bakisan policies na aikin kamfani ba” ya jefa mata magabarya nutse ba tare daya kalli inda take ba,tsaiwa tayi cak,sautin muryarsa data tsana tana ratsa kunnuwanta,kamar tayi gaba,sai taga ya kamata atleast ta tsaya ta fuskanci wannan izzar tasa,don haka ta waiwayo cikin nutsuwa ta zube idanunta fes cikin nasa

Page 18

      “Eheenn” sãahar ta furta a taqaice da alamun dake nuni da neman qarin bayani takeyi,sake zare hannunsa yayi daga kan system din,ya sanya idanunsa cikin nata a hankali kamar masu narkewa,wani abu me kama da fushi yadan ratsa ta tsakanin zagayayyun qwayar idanunsa

“Waye ya sallameki?” Ya fada kansa tsaye yana qanqance idanunsa cikin nata. Sai data kalli agogon hannunta sannan ta amsashi,tana jin kamar ta bude idanu taganta ba cikin office din ba,inda yasan yadda ta tsani hada hulda da maza da bai bari ta zauna tsahon mintunan da tayi a tare dashi ba,tana qoqarin hadiye fushinta ta amsa masa,saidai hakan bai boye tata izzar ba

“Lokacin daya kamata naci gaba da zama ya cika,inajin babu wani sauran abinda ya kamata na sani,inda akwai da ka sanar dani din”  yadda take maganar with confidence ya bashi mamaki,karon farko da wata diya mace ta taba tsaiwa a gabansa cikin nutsuwa irin wannan ta bashi amsa takai tsaye,ta kuma amsa masa da abinda ya fito kai tsaye daga zuciyarta. Hannu yasa ya jawo wani file dake gefansa

“Inason nayi alerting naki abu daya,ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun Dr ya rudeki,kina da naki limit din,so do not exceed that limit,right?”

“Don’t bother” ta amsa masa a taqaice,duk da tanason ta gaya masa sama da hakan,to amma a yanzun bata da buqatar doguwar magana,sannan bai kamata ta take maganganun dattijon da bai dade da gama gaya mata su ba,bata sake bata koda second biyu ba ta juya ta fice abinta ba tare data tsaya jiran abinda yakeson gaya matan ba.

           Sanda ta koma office sai abubuwan suka yita dawo mata,tanason taci gaba da aikin,amma kuma abinda ya faru cikin office din yana ta dawo mata a rai,a hankali sai zuciyarta ta fara zafi,ta dinga jan tsaki a jejjere,daga qarshe ta tabbatarwa kanta ba zata iya ci gaba da aikin ba,sai ta ture komai ta fara hada tarkacenta,ta dan debi wasu files da take tsammanin may be zata iya dubasu a gida,tabar office din bayan ta yiwa miss sameera umarnin ta rufe,ta dan bita da kallo tana mamakin yadda ta tashi abinda duk da lokacin tashi baiyi ba,bayan qaqqarfan jan kunne da CEO ya ajewa kowanne ma’aikaci akan makara da kuma tashi kafin cikar lokaci,a taqaice ma dai a kwanakin kusan kowanne ma’aikaci yana d’ara lokacin tashinsa,saboda yadda kowa ya maida hankalin wajen kawo daidaito da gyaruwar lamuran kamfanin.

           Tana driving a hanya zuciyarta tana dada yin zafi,ta yaya zata iya aiki da wannan mutumin?,ta yaya zata jure aiki dashi?,kwata kwata nashi da manners,baisan darajar mutum ba,koda wayeshi,kowanne irin matsayi yake dashi,itakam ba zata taba jure ya takata ba,ba zata dauki kowanne banzan hali daga wajen kowanne d’a namiji ba yanzun.

          Da wannan fushin da zafin zuciyar ta isa gida,tayi parking ta fito tana tattaro files din data taho dasu,fuskar nan a dinke na walwala taji takun afifa.

        Ta cikin motar ta daga kai ta dubeta sanda take tahowa tana amsa waya,sanye da wata free gown,da alama tun dazun ta taso daga nata aikin,saita maida kanta taci gaba da abinda takeyi.

        Tana isowa gurin ta gimtse wayar tana dariya qasa qasa

“Oyoyo mr president,bari na kwashi tabarraki” ta fada tana murmushi tare da qoqarin karbar folders din hannun nata,batayi jayayya ba ta sakar mata,ta fara kulle motar,afifa na gyara zaman folders din a hannunta tace

“How was your day today?” Yi tayi kaman ta cilla mata harara amma sai ta fasa,ganin cewa ba ita takar zomon ba,don haka ta amsa mata cikin miskilancin nan nata

“Bad” ta fada a taqaice tana soma takawa zuwa ciki,afifa tabi bayanta da hanzari

“Kaman yaya?,your first day at work fa” kai ta jinjina mata kawai tana lumshe ido ba tare da tace mata komai ba,sai afifan itama bata qara tambayarta ba,sukaci gaba da takawa zuwa ciki.

        Maama ce zaune cikin falon,saman cinyarta wani dan bowl ne dake dauke da strawberry tana gyarawa,cikin kulawa ta amsa sallamar tasu idanunta akan fuskar diyar tata

“Barka da gida maama” sãahar ta fada tana isowa gabanta gami da duqawa,ta kuma dora saman cinyarta kadan. Murmushi ta sauke tana dubanta,gaba daya jiki da zuciyarta sun nuna gazawa xda gajiyawarta,saita zare hannunta daga cikin strawberry din ta dora saman kanta

“Barka kadai president dinmu,ya aikin?” Tabe baki tayi kamar wadda zata saki kuka,itako sunan batason a tuna mata,don da alama yaa muhyi ya bata aiki me wahala qwarai

“Ba dadi maama,ya muhyi yayi punishing dina ne kawai da wannan aikin” dariya afifa ta saki yayin da maama tayi murmushi

“Ba haka bane,da sannu dai zaki saba,qila ma ki dinga jin dadin aikin nan gaba kadan fiye da yadda muke tunani” miqewa tayi tana dan tura baki

“Anya maama zanso wannan aikin?”

“Ba wanda yasan gobe sai Allah” kai tadan jinjina

“Abba bai iso ba?”

“Ya kusa,inajin sai an idar da sallar magrib”.

            Zasu wuce baaba rabi ta iso zata karba strawberry din da zata markada,cikin fara’a da girmamawa ta amsa barka da gidan da sãahar tayi mata

“Barka dai farar d’iya,tun dazun nake dakon isowarki,abincinki ya kammala”

“A shiryamin dan kadan,bamai yawa ba,ina fitowa yanzu”

“A fito lafiya ummin abba” ta fada cikin nuna kulawa,maama dake zaue ta kalleta

“Rabi kece kike sake sakalta sãahar naga alama”

“Idan bamu tattalawa alhaji diya ba hajiya ai bamuyi halacci ba” sai kawai maaman ta bita da murmushi,kasancewar itadinma ba maison yawan magana bace.

            Tare suka shiga dakin ita da afifa,ta zube mata takardunta a kyakkyawar kusurwaf da aka shiryama wani kyakkyawan table da kujerarsa,dan qaramin study room a maqale da bedroom din nasu,gurin an masa shiri na musaman da zaiyi dadin karatu,ta koma parlor ta barta a dakin.

           A nutse ta cire kayanta ta watsa cikin laundry basket,ta daura wani lallausan farin towel,gab da zata shiga toilet din wayarta ta soma tsuwwa,dakatawa tayi tana duba number dake yawo saman screen dinta,zubawa numbers din dake jere reras idanu tayi,sai taja da baya ta wuce bandaki abinta,saboda number tayi mata kama da number mahmud,wadda a qalla kusan kullum tana ganin gilmawarta cikin wayarta da tarin saqonninsa da ko sau daya bata taba tsaiwa dubawa ba bare ta bashi amsa.

          Mintina kusan ashirin da biyar sannan ta fito,ta tsaya gaban madubi ta tsane jikinta,ta shafe lallausar fatarta me sulbi da mayuka sannan ta mutstsike jikinta da turarukanta masu taushin qamshin da kwantar da zuciya.

         Wani budadden cotton trouser ta saka,da wata free over size shirt me taushi,ta kama gashinta ta daure da band,idanunta suka sauka ga fuskarta da tayi wani irin fresh,babu alamun tabo ko qwarzane ko daya a kanta

_”ki tsaya iya matsayinki,kada maganganun dr ya rudeki,kina da naki limit din_” ido ta lumshe tana jin maganar na mata zafi kamar yanzun ya furta mata su,waye ya gaya masa buqatar kanta ce wai ta kawota companynsu?,baisan aikin tamkar wata tursasawa bane da karan tsaye ne da aka yiwa rayuwarta ba?,batason shafe maganar dattijon,hakanan batason zubda yaa muhyi a idanunsu,dole wani abun ta kauda masa kai,amma bafa komai ba,kuma muddin zasuci gaba da hada hanya da guy din ta tabbatar babu jimawa zasuyi batacciya,don ba zata iya shanyewa irin wadan nan halayen nasa ba,yadda yakema mata ita ba zata iya dauka ba,don ba abinda take nema daga wajensu.

            Dogon tsaki taja,sannan ta juya tana fita a dakin bayan ta dauki wayarta,ta kuma goge duk wani miscall na mahmud da saqonsa da ya shigo bayan taqi daga wayar.

          Still maama da afifa na zaune suna hira a parlor din,saita wuce saman dining tana duba abincin da baaba rabi ta ajjiye mata. Cikin wanda ta zuba din ta sake tsakurar wani,duk da bashi da yawa amma ba zai iya shiga cikinta duk ba,hakanan yanayinta yake,sanda tana qarama maaman tasha kaita asibiti,ayita bata multivitamin ko cikinta zai bude a samu cin abincinta ya qaru,saidai babu wani ci gaba,dole aka rabu da ita hakanan bayan sun fahimci halittarta ce a hakan.

            Sanda ta kammala itama qasan ta sauko ta saka baki a hirar tasu,duk da kusan rabin hankalinta yana kan wayarta,ta shiga Instagram account dinta tana dubawa.

          Har ta gota wani post saita dawo da baya a hankali. Hoto ne da aka yiwa cikakken daukan daya bala’in fita tarrrr,kana ganin hoton zakasan cewa da babbar waya akayi,irin wayoyin da sukasan haqqin fidda hoto da kyau.

_i’d never met anyone so quiet and beautiful simultaneously like him,his personality match his beautiful face MT JARMA_ Rubutun dake qasan photon kenan,sai tarin comments rututu,wanda kusan rabinsa na mata ne.

         Wani bacin rai ne yazowa sãahar iya wuya,ta fita gaba daya daga Instagram din,wasu abubuwan ba shakka laifin mata ne,irin comment data dinga gani a qasan photon kwata kwata babu tsari babu kuma aji bare kamun kai irin na ‘ya’ya mata,kamar a duniya shi daya Allah ya bawa baiwar kyau?,ba dole ya dinga buga wannan iskancin ba, muddin a zahirance irin wannan rawan kan da digimin matan suke masa,ranta ya baci sosai,har afifa ta kula ta tambayeta,amma sai tace ba komai,ta jawo saman wayar ta kashe data dinta gaba daya,dai dai sanda yaa zaid yayi sallama cikin falon,yana riqe da jakar abba,abban yana biye dashi a baya.

          Cikin girmamawa kowa ke qoqarin masa sannu da zuwa,mutum me cikar kamala da kuma nuna qauna da sakewa da iyalinsa,yana da faran faran sakin fuska da kuma barkwanci,amma muddin zakayi ba dai dai ba da gangan da ganganci to fa baya lamunta,a nan ne zaka ga aihin Color dinsa.

           Sassansa ya wuce daga nan ta qofar data hada sassan biyu,maama tabi bayansa ta barsu da zaid din yana tambayar sãahar ya aikin

“Lafiya” ta amsa masa a taqaice shima,afifa dake zaune daga gefanta dariyar da taketa dannewa ta taso mata

“Adai dinga jin tsoron Allah ana fadin gaskiya,atoh” waiwayawa tayi ta kalli afifan,kaman zatayi magana saita fasa ta maida idanunta ga wayarta

“Tell me,me ya faru?,da alama akwai magana tunda permanent assistant dinki ke dariya” shuru ta danyi kamar ba zatayi magana ba,sai kuma ta buda baki sound na bacin rai yana dan fita kadan a muryarta

“Bashi da kirki yaa zaid,he was trying to insult me as kamar ina neman wani abu da kamfaninsu” dan zuba mata ido zaid yayi sannan ya saki murmushi

“Try to relieve your anger dear,ki nutsu ki fuskanceshi,ki kuma fuskanci aikinki,ba don shi kadai kike zaune a kamfanin ba right?” Kai ta gyada

“So no need ki damu kanki,do all the right things,amma don’t be rude to him,ya girmeki,show some respect zaki samawa yaa muhyi din mutunci,ki zama me kawaici yadda na sanki,kada ki bari qananun abubuwa su dinga bata ranki,kin fahimta?” Nutsuwa taji tana saukar mata,Allah ya sani yadda yayyenta suke nuna qauna da kulawa a gareta ya sanya itama take qaunarsu,take kuma qoqarin bin dukka umarninsu,yanzun maganar da sukayi da yaa zaid din ya samar mata da relief sosai,sai ta dan sake sukaci gaba da hira,har zuwa sanda akayi kiran magrib,ya fita masallaci shida abba,su kuma suka wuce ciki ita da afifa.

          Ba kasafai take tashi daga saman abun salla da wuri ba duk bayan sallar magarib har sai tayi isha’i,kamar yadda takeyi bayan asuba har alfijir ya keto,saboda gurabene na amsar addu’a sosai.

        Afifa na kwance rub da ciki a saman gadonsu,tana kallo ta system din sãahar din,furera mataimakiyar baaba rabi ce tayi knocking,afifa dake kallo tayi mata izini,ta turo qofar dakin a shigo,cikin girmamawa tace

“Maama tace a gayawa ummee,alhaji yana nemanta a sassansa” sãahar da takai ayar qarshe cikin surar da take karantawa ta maida qur’anin ta rufe

“Gani nan zuwa” ta amsawa furera,ta miqe zata fice,afifa ta nuna mata plates din da sukasha kankana tace ta wuce kitchen dashi.

             Qur’anin ta mayar gurinsa,ta nade abun sallar sannan ta zura wasu slippers masu taushi a qafafunta tana mamakin kiran abban a irin wannan lokacin. Ko hijabin jikinta bata cire ba ta juya ta fice,afifa ta bita da kallo tana dariya qasa qasa,yau akwai daru kenan,sai ta gyara kwanciyarta sosai tana jiran dawowar rigimammiyar tata.

          A nutse tayi sallama abban ya bata umarnin qarasowa,ta zare slipper dinta ta shigo,ta zauna daga qasa gefe guda. Dubanta yayi ba tare da ya ajjiye wayarsa dake hannunsa ba

“Ummin abba,ki duba setting room,kina da baqo”. Jin maganar tayi kamar anyi jifa da abu ne nauyi cikin zuzzurfan rami,ya fada kansa tsaye ne ba tare da wata damuwa ko ganin nauyin maganar a tattare dashi,saita shiga ko kwanto,kodai bataji da kyau bane

“Na’am abba?,afifa dai ko?” A natse ya dago ya kalleta sosai wannan karon cikin idanunta

“Khadijatou nace” jikinta ne ya sanyaya gaba daya da yadda abban ya kira ainihin sunanta,wanda ta manta rabon daya kirata hakan,dukka gabobinta kamar an bi an doddokesu haka taji,ta tattara dukka qwarin gwiwarta,ta samu ta yunqura ta miqe,tana jin kamar iska na yawo da ita daga hagunta zuwa dama,daga gaba zuwa baya. Har takai qofa muryar abban ta sake cimmata

“Idan kinje ki dawo zamuyi magana dake” kai ta gyada masa kamar me ciwon baki,ta zura takalminta da a yanzu takejin kamar qafafunta ba zasu iya riqesu ba ta fice.

           Minti daya ma ya isa ya kaita setting room din gidan,wanda babban qayataccen parlor ne dake farfajiyar gidansu,wanda a nan abban ke ganawa da baqinsa,to amma a yadda jikinta ya zama wani matacce,sai data debi mintuna biyu harda doriya sannan ta qarasa,zuciyarta cike fal da mamaki da kuma tunanin waye wannan?,me kuma yazoyi mata?.

         Muryar ya zaid ta fara ji sanda take dage labulen parlor din,suka hada ido dashi,yana zaune hannun kujera suna hira da baqon dake saye cikin wata dakakkiyar shadda,qamshin turarensa ya cika falon,a sake sosai suke hira da ya zaid kamar sun dade da sanin juna,suna hada ido ya miqe

“Gata nan ma ta iso,sai nace ka gaida gida” ya furta yana miqa masa hannunsa sukayi musabaha,sannan ya zagayeta ya fice daga parlor din.

             Shuru parlor din ya dauka,yayin da taci gaba da tsaiwa a wajen kamar an dasata,bata fita ba bata kuma qarasa shigowa ba bare ta samu muhallin zama. Hakan ya baiwa mahmud abba gana damar kallonta da kyau,duk da cewa cikin hijab take amma sassanyan kyawun nan nata bai gaza fitowa fili ba muraran,wata qaunarta ta qara linkuwa cikin ransa,batayi laifi ba idan tayi jan aji me yawa,ta cancanta,tako ina ta cancanci dukkan wata izza da ginshira,saidai inda dubban matan dake binsa zasuya wahalar da yakesha akanta,tabbas da sun dara,da kuma yasha kunya

“Me kake buqata?,me kake nema a gurina?” Ta tambayeshi kanta tsaye,don ta gundira da kallon da yake mata,kamar yadda taji ta tsani zaman falon.

          Murmushi ya saki sannan ya miqe tsaye yana mata nuni da kujera

“Inaga zaifi kyau ki samu guri ki zauna,karki gaji da tsaiwar” ya fada yana murmushi,har cikin ransa yana jin dadin ganinta da wanzuwarsu guri guda

“Kada ka damu da tsaiwata ko zamana,kai tsaye ka fadamin abinda kake ya kawoka, inason komawa ciki,nabar ayyuka da yawa ” murmushi ya saki yana goye hannayensa a qijinsa

“Ayyah,sorry,ina fatan ba aikin office ne ya gajiyarmin dake ba” idanunta tadan lumshe sannan ta budesu,ta gundura matuqa,da zai taimaketa daya taqaita komai da komai ya sallameta ta wuce ciki abinta

“Have a seat please” ya fada yana karyar da murya. Bata fiyason ayita roqonta abu ba,hasalima tun asali mutum ce da bata qaunar mita da kuma jan magana,don haka ga qarasa ta zauna a hannun kujerar da ya zaid ya tashi a kai

“Na gode” ya fada yana jin dadin yadda ta girmama buqatarsa,sai ya koma kan kujerar da ya tashi shima,idanunsa a kanta,abinda ya fara sanya ranta baci kenan,batason yawan kallo kwata kwata.

“Basai mun dawo da doguwar magana ba, tunda na fuskanci abinda bakeso kenan,kaina tsaye zan gaya miki,sonki nakeyi sãahar,so kuma irin na aure,qauna ta fisabilillah,bance ki soni yanzu yanzu ba,a’ah ina son ki bani dana zuwa wani lokaci,har zuwa sanda zaki aminta a karan kanki da soyayyar da nake miki,ki kuma gamsu da cewa ke din zaki iya aurena” ya fada yana hade tafukan hannayensu biyu waje daya,kamar me neman gafara.

          Ji tayi kamar ya sanya wuqa ya yanki naman zuciyarta,tun bayan rabuwarta da adam yaune karon farko data zauna har kunnuwanta suka saurari kalmar soyayya daga bakin wani namiji,kalmar data jima dayin jana’izarta a kaf littafin rayuwarta,kalmar da takeji a ranta zuwa yanzu cewa qarya ce,babu wani so na gaskiya,saidai SON RAI da SON ZUCIYA da kuma SHA’AWA,sune zallarsu,ake musu ado da fenti a kirasu da soyayya.

           A ranta taji kawai mahmud din yazo ne don ya bata mata lokaci,eh….bata lokaci mana, tunda bazai taba samun abinda yakeso daga gareta ba,sai ta miqe tsam

“Zanyi shawara” tayi furucin don ta samu ficewa a dakin,bawai don tana nufin yin shawarar bane da gaske,shawara akan abinda baida muhimmanci?,abinda ta riga ta sani ko sama da qasa zasu hadu bazai samu wannan buri nasa daga gareta ba

“Alfarma ya biyu,don Allah badon ni ba” yayi hanzarin fada ganin ta doshi qofar fita,dole ta tsaya ba tare data waiwayo ba

“Ko sau daya ne tak a rana ki dinga daga wayata”

“Banyi alqawari ba” ta fada kai tsaye tana qarasa ficewa harda ‘yar sassarfa wannan karon,kamar wadda akace za’a kama.

          Hanyar yabi da kallo harta bace masa,ya dunqule hannunsa ya kaiwa iska naushi,saidi fuskarsa murmushi ne a kwance,ko iya hakan yaji dadi a ransa,koba komai sunyi musayar kalamai duk da ba masu tsayi bane,a qalla an samu improvement ko yaya yake,zaici gaba da trying,bazai gaji ba,ya daga tsadajjen agogon rolex dake hannunsa ya duba lokaci,sai ya taka yana fita daga setting room din,wanda kafin ya iso tuni ya yiwa guard dinsa umarni sun shigo da uban siyayyar da yayo dukka domin sãahar din,karon farko daya fara tad’i da ita a cewarsa.

            Rana ce da kuma lokaci na musamman a rayuwarsa da bazai taba mantawa da ita ba,duk da ba wani abun kirki ta gaya mishi ba,bai samu hankalinta da lokacinta yadda yakeso ba.

         A wani mugun quntace take komawa zuwa falon abban,gaba daya ta shiga rudani da firgici,hankalinta a tashe yake kamar wadda wani mummunan abu ke shirin samunta.

          Tana sallama dr mamman ya zuba mata ido bayan ya dauke kansa daga kan takardar dake hannunsa kafin yakai ga amsa sallamar tata,yana sauke qafafunsa dake harde waje daya qasa tare da binta da idanu,yanason karantar yanayinta da gaske.

           Kanta a qasa ta tako lallausan carfet din dake shimfide a falonsa,madadin marbles din da aka qawata fiye da rabin qasan ginin gidan,ta zame a hankali cikin matuqar mutuwar jiki da wata fargaba ta zauna daura dashi

“Gani abba” zama ya sakeyi sosai,ya ajjiye takardar yana dubanta

“Ina kyautata zaton ba yau ne karon farko da kika fara ganinsa,nasan kuma zakiyi mamakin yadda akayi ya samu izinin ganinki direct daga wajena…..ya nema izinin soma ganawa dake ne kamar yadda shari’a da kuma al’ada ta tanadar,ya cika dukkan sharudda da akeson mai neman auren diyarka ya cika,wannan ya sanya na bashi izini,zaici gaba da zuwa har zuwa lokacin da zaku daidaita kanku,ku kuma aminta da junanku,kije kiyi addu’a,Allah yayi miki albarka” ya qarqare maganar ba tare daya bata damar cewa komai ba.

“Ameen” tayi qarfin halin kalato jimlar daga kowanne sashe na bakinta ta hadata sanann ta furtawa abban.

         Sai da tayi namijin qoqari sannan ta yunqura ta miqe,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,haka ta dinga ji tun daga zuciyarta zuwa gangar jikinta a birkice.

           Kasa qarasawa tayi cikin gidan,ta biyo ta farfajiyar gidan,sanna a hankali ta karkata zuwa sashen hagu na gidan,inda aka kebance wajen da wasu qawatattun kujeru domin hutawa musamman da yammaci,irin yammacin da zafin rana ke damun dan adam.

            Kujera daya taja ta zauna akai,daidai sanda take fidda wata ajiyar zuciya me nauyi da zafi,tasa dukka hannayenta biyu ta dafe kanta da taji yana niyyar fara mata ciwo saboda nauyin da maganar ta yiwa qwaqwalwarta. Ko da wasa bata taba sanyawa a ranta mahmud zai iya zama saua daga cikin matsalolinta ba a rayuwa,kwata kwata ma bata taba daukar batunsa da muhimmanci ba,shi yasa bata ja masa layi tunda wuri ba,ashe tayi sake,gashi yayi mata shigar burtu,yakai wani guri da idan batayi da gaske ba zai iya sawa a tanqwarata tayi abinda bata da niyya ko lissafin yi.

       Shurun da afifa taji yayi yawa sãahar din bata dawo ba,shi ya sanyata kashe laptop din ta sauko daga gadon,dakin maama ta leqa,ta sameta ta fito a wanka tana shiryawa

“Bata shigo ba,tunda kuka wuce daki tacemin ta taho da ayyuka daga office zata rage banga ta sake fitowa ba” sai afifan ta juya zata fita,har takai qofa maaman ta kirata

“Ko abbanku yayi maganar da ita?” Kai afifa ta gyada

“Haka nake tunani maama” jinjina kai tayi fuskarta na bayyanar da damuwa

“Dubata don Allah” juyawa afifan tayi ta fice itama jikinta yana bata lallai akwai damuwa.

           Ta jima lausasan tafukan hannuwanta kife saman fuskarta,tanason ta daidaita yanayinta ne ta kuma ragewa kanta damuwa kodon ayyukan data debo masu yawa daga office. A nutse taji an dafa kafadarta,ko bata juyo ba tasan wacace,amma sai tayi burus,a wannan gabar itama afifan ta shafeta,haushinta takeji sosai,ko banza ta taka muhimmiyar rawa wajen faruwar wannan abun,tasan babu ta inda mahmud zai samu cikakken information a kanta sai wajen afifan,inda ta barshi kamar yadda ta bashi tsaye a wajen….. tun a ranar,da tuni an wuce wajen,batajin zata sake bashi damar ganinta ma bare wani abu makamancin wannan ya biyo baya.

         Zagayowa tayi ta zauna ganin taqi waiwayowa gareta duk da ta tabata,tasan fushinta akanta,wannan din kuma da tayi alamace na tayi fushi. Sai data zauna sosai sannan tayi kiran sunanta,tsahon wasu sakanni ba tare data motsa ba,kamar bata jita ba,daga bisani kuma ta fara sauke hannuwan nata idanunta fes akan afifa.

            Kallon kallo suka yiwa junansu,kafin ta miqe a nutse tara ture kujerarta baya

“Don’t say anything……kinsan kome tunda kece silar faruwar komai din” ta fada calmly tana niyyar wucewa. Murmushi ne ya subucewa afifan,amma tasan cikin bacin ran da taketa kokawar dannewa take,don haka bata bari taga murmushin nata ba,ta miqe kawai tabi bayanta

“A shirye nake na fuskanci kowanne irin hukunci,nidai na shirya sauya rayuwar ‘yar uwata ta kowacce hanya me kyau,wannan karon tare nakeson a daura mana igiyoyin aure uku” kamar ta sanya waigi ta tsaida sãahar din,ta dakata da tafiyar da takeyi,sannan ta waiwayo ta zubawa afifa fararen idanun nan nata,ta motsa siraran labbanta a hankali

“Aiba watanni shida masu zuwa ba,nan da shekara shida ma,ki rubuta ki ajjiye nan daura damaran yin aure ba” dukka girarta biyu afifa ta dage cike da tsantsar mamakin yadda kullum take dada zurfafa wajen tsanar maza,da kuma nisanta kanta da yin aure

“Ahhh…..kice mun kusa bada sadakar wata yarinya a gidan nan”

“Bismillah” ta fada a taqaice ganin afifa nason maida batun wasa,bata tsaya saurarenta ba ta wuce ciki.

            Aiki biyu ta hadawa kwanyarta kusan lokaci guda,damuwa ga aikin office din data debo,haka ta yita yaqi da kanta,har Allah ya bata nasarar wancakalar da wancan batun,tunaninta da hankalinta ya karkata sosai ga files din da take dubawa,tanayi tana hada wasu bayanai a system dinta tana saving. Ba ita ta tashi a wajen ba sai sha biyu saura,ta fahimci abubuwa masu yawa tarin naqasu da kuma gyare gyare,tana kuma saka ran daga gobe zata fara gudanar da aikinta da dukkan fikira da baiwar da Allah ya bata,kafin ta kwanta ta hada dukkan wasu bayanai masu muhimmanci,printing dinsu as document zatasa kawai ayi idan ta isa office.

*_W A S H E G A R I _*

        Ta tashi a miskilarta sosai,har ta kammala shirinta,yau dimma cikin wata lafiyayyar lafaya me bala’i kyau da asalin tsada,wadda ta dace da takalmi da qaramin band bag dinta samfurin kamfanin Hermes,tayi wani masifar kyau,daurewar fuskar tata ta sake qara mata kyau da kuma kwarjini na musamman,tayi wani irin sassanyan kyau,sulbi da laushin fatarta a ido kawai kana iya fahimtarsa. Sarai afifa ta fuskanci fushi takeyi da ita,yau da alama ‘yan miskilancin har a kanta suka sauka,don haka tana tsaka da nata shirin fita gurin aikin,hannunta riqe da towel tana goge jikinta

“A sister like no other” ta fada tana kanne ido alamun tsokana,duk da cewa so take ta tsokaneta,amma har cikin ranta shigar ta sãahar tayi kyau sosai. Waiwayowa tayi ta jefa mata harara

“Ki samu wanda zakiwa dadin baki” qaramar dariya afifa ta saki, sãahar ta gama daura agogon hannunta,tana fesa lallausan turarenta afifa ta sake cewa

“Ki duba mudubi sosai fa kafin ki fita,gudun samun matsala” ta qarasa maganar tana qunshe dariya,datakawa sãahar tayi daga zuge zip na hand bag din nata,ta juyo tana duban afifa

“Matsala?,kaman yaya?”

“To ai wabillahi any moment za’a iya samun matsala,wannan kyan dake fita daga fuskarki kowacce safiya,kina zaton akwai namijin da zai iya gani ya kau da kai karon farko bai kawo kanshi ba?” Maganar ta fusgi hankalinta,saita waiwaya tana duban kanta da kanta a mudubi,tsahon wasu sakanni sannan ta dawo da dubanta ga afifa dake danne dariyarta,yanayinta yayi wani irin sanyi,kamae wadda ke shirin sakin kuka. Dukka kafadunta afifa ta dage ta yarfar da hannu

“No way out fa malama,indai ba shafa kashi zaki koma yi ba,just kawai ki bawa mahmud kai bori ya hau,shine zaki zama cikin aminci”

“Saiki auramin din mamata” ta fada adan fusace tana fusgar jakarta ta nufi hanyar fita,afifa ta saki dariyarta sosai

“Yo kwana nawa ne” banza tayi da ita,tabbas da biyu afifa ke mata hakan,amma inda tasan yadda maganar ke sanyata cikin firgici da razani da bata dinga tsokanarta da hakan ba.

            Kamar kowacce safiya,a sassan abba ta samu maama,saidai ta taras ya Saifullahi yazo,suna breakfast tare da abban,ganin tayi musu sallama zata tafi bataci komai ba ya Saifullahi din ya tsaidata kan lallai sai taci wani abun,tsaiwar da zatayi tayi breakfast din zai iya bata mata lokaci,tana kuma son su shiga meeting din akan lokaci ko don cikar martaba da kamalarta,to amma sam ba zata iya ce masa a’ah ba,dole ta ajjiye hand bag dinta,taja kujera daya dake kusa da abban ta zauna ta hada tea.

        K’arfe tara saura mintuna goma na safiyar ranar motocinsa suka isa gurin ajjiye motoci na kamfanin,cikin hanzari cika aiki da sanin makamar aikin,daya daga cikin guards dinsa ya buda murfin motar,a yau din ba tare da wani tsaiko ba ya zuro baqi sidik din takalminsa kafin gangar jikinsa dake sanye tsadaddar suit charcoal color ta biyo baya,kunnuwansa manne da waya,ya waiwaya yana miqawa jibril daya wayar tasa,sannan ya fara takawa zuwa cikin kamfanin,cikin takunsa dake nuna zallar kuzari da kuma izza ta cikar mazantakar d’a namiji.

           Duk inda ya gifta ma’aikatane ke zubewa,kowa yana qoqarin miqa gaisuwarsa cike da girmamawa,saidai har a sannan waya yake amsawa,baya samun damar amsa gaisuwar tasu,hakan kuma bai sanya sun daina ba,har ya isa ga elevator,ya shiga shida jibril da mr samson,sauran kuma suka suka biyo bayansa.

           Har ya isa ga office din nasa waya yakeyi,wayar dake hannun jibril dince ta dauki tsuwwa,ya duba kiran sanna ya miqa masa da hanzari,sunan dake saman screen din yasa ya katse waccar wayar da yakeyi ya daga daya wayar,yana musu nuni da hannu. Rusunawa sukayi sannan suka juya cikin girmamawa suka fice.

         Yadda ya sake yana wayar kadai ya isa ya gaya maka da mutum me muhimmanci yake wayar,ya bata a qalla mintuna goma kafin ya lallabata sukayi sallama,ya sake kallon fuskar wayar yana furzar da iska daga bakinsa,a duk sanda zaiji sautin muryar yarinyar,sai qauna da kuma zallar tausayinta sun cika masa zuciya,inama ace ana iya sauyawa mutum uwa,ba shakka da tuni ya biya,komai tsadar uwar muddin zata maye gurbin waccan,zata shafe sunanta,jininta zai fita daga nata jinin fita ta har abada,lallai da zai iya sarayar da dukka abinda ya mallaka indai hakan zata tabbata,saidai inaaaa…… KADDARA TA RIGA FATA. Wannan tunanin kawai ya motsa zuciyarsa qwarai da gaske,har sai daya fidda baqin glass dinsa ya sakaye qwayar idanunsa a ciki,cikin hanzari kuma ya danna kiran jibril,gwara yayi hanzarin aiwatar da dukka schedules dinsa na yau kafin tunanun yaci galaba a kansa.

            Tsam saima ta miqe ta biyo bayan jibril dake yunqurin shiga office din,bata jin zata bari tayi asarar dare da wunin data bata taba zaben kaya da shigar da zatayi yau,ta lura,ko lokacin da ya shigo office din tana welcoming nasa,amma ko kusa ko alama bataga alamun ya ganta ba,bare ta sanya ran yaga dressing dinta.

             A nutse ya motsa labbansa yana amsa sallamar jibril,idanunsa sunga saima din dake biye dashi,kallo daya yayi mata ya janye qwayar idanunsa ya maida ga system din,yana qoqarin binciken ganin kowanne department sunsan da meeting din yau?.

“Banason meeting din nan ya wuce nine thirty,a sanarwa dukkan board members din,banason makara,ina buqatar kowa a wajen on time”

“Yes sir” jibril ya amsa yana rusunawa,sannan ya juya zai fice

“Sir,am sorry,sai nake ganin dukka aikina ne fa?,so no need ka dinga kiran jibril,i can do it” ta fada gabanta yana dan faduwa,tana tunanin kalar amsar da zata samu daga wajensa.

           Kamar baiji abinda ta fada ba har jibril dinma tuni ya fita,dauke hannunsa yayi daga kan system din,ya zare gilashin idanunsa,qwayar idanun nasa da suka dan canza launi ta fito tarwai,ya kuma zube dukka wani nauyi da uban kwarjinin dake cikinta saman fuskar saima,wadda a take taji tana neman faduwa,cikin dabara ta qarasa ga ma’ajiyar kayan sanyi dake office din ta jingina kadan don hanawa qafafunta rawar da suka fara yi

“Bake zaki tsaramin abinda ya kamata da kuma wanda bai kamata ba,aiki kika nema kuma an baki fine……wannan ya zama karo na qarshe da zanyi warning dinki,duk ranar kuma da kika sake……ki irga kanki a mazaunin korarriya” iya abinda yace da ita kenan ya maida gilashi fuskarsa ya sake tattara hankalinsa ga abinda yakeyi,kai ba zakace shi yayi wannan maganar ba a yanzu.

           Mutuwar tsaye tayi,kafin ta samu ta tattara dukka qwarin gwiwarta,ta juya a hankali ta fice.  Cikin tsananin bacin rai ta zauna da qarfi saman kujerarta tana maida numfashi,sai kuma ta jawo jakarta dake saman teburinta ta ciro mudubi takai ga fuskarta,so take ta hango wani aibu nata da ya hana taoufeeq bata koda lokacinsa ne bare akai ga hankalinsa,tanason gano wanne irin naqasu take dashi da har ta gaza samun kansa,ta kasa samun soyayyarsa.

           Ba abinda ta hango sai doguwar fuskarta ne dauke da siririn hanci da kuma manyan idanu masu girma qwarai,ita kanta tasan tako ina bata da wani makusa ko aibu,KE KYAKKYAWA CE,kullum abinda tarin mazan da take tare dasu suke gaya mata kenan,taji hakan daga bakunansu ba sau daya ba ba sau biyu ba,amma a yau dukka wannan kyan nata ya gaza amfani a kansa?.

          Maida dubanta tayi ga shigar jikinta,kayan data kashe kudade masu nauyi ta siya,tasa aka zauna aka tsara mata dinki na jan hankali,amma ko sau daya,ko bisa kuskure bai kalli gangar jikinta ba bare tayi tunanin ya kula har hakan yaja hankalinsa. Madubin ta wurgar cike da bacin rai da kuma zallar takaici,ta kifa fuskarta saman jakar tata,tana jin kamar fa fashe da kuka ko zata samun sassaucin wannan musibar.

           Tare da miss sameera secretary dinta suka shigo office,ita ta riqo mata jakarta har ciki,tana shirin zama cikin dan sakewa tayi magana da sameeran

“Ina fatan kowanne department a shirye suke?,qarfe goma dai dai zamu shiga” kai ta jinjina

“Abinda na fara yi kenan ina shigowa office”

“Alright,ki tattara dukkan bayanan nan ki fidda minsu as document,ko basu samu duka kafin lokacin ba ina da buqatar mafiya rinjaye”

“Ok madam” sai ta amsa ta fice,yayin da sãahar din ta soma rage wasu ayyukan kafin cikar lokaci.

          Cikin girmamawa jibril ya dawo,yayi sallama ya amsa masa ba tare daya daga kai daga abinda yakeyi

“Sir,akwai wani taron daga office din president,all employees daga dukkan departments,ten o’clock” da mamaki ya tsaya da abinda yakeyi din,ya zubawa jibril idanunsa

“Akwai wani meeting da za’a yi irin wannan ba tare da an shaida min ba?”

“May be an tura email zuwa ga secretary,shaida maka bane batayi ba” a nutse ya maida bayansa ga kujera ya jinginar,a yadda yasan halinta ya tabbatar ba zata kasa gaya masa ba

“Koma daga office din waye a sanar nayi cancelling dinsa,wannan taron shine most important”

“Yes sir” ya fada sannan ya juya ya fita don ya fara sanarwa saima,dole idan suna buqatar isar saqon akan lokaci ta tayashi tura sanarwar.

            Siririn tsaki yaja,ya tsani wannan power din da Dr ya bata,a wajensa kamar bata cancanceta ba,a matsayinta na baquwa,wadda batasan komai akan aikinsu ba,batasan kuma komai da ya shafesu ba,sai ya miqe yana cire suit jacket dinsa,yayi hanging dinta,sannan ya taka zuwa bakin qawataccen books shield da aka jera takardunsa da kuma litattafan cikinsa a tsare gwanin burgewa,ya zuge ya debo wasu takardu,dai dai sanda sajjad ya shigo.

           A nutse ya amsa sallamar tasa ba tare daya waiwayo ba,ya dauki abinda zai dauka ya rufe sannan ya tako zuwa inda sajjad ke tsaye. Hannu kowa ya dunqule ya miqawa dan uwansa kamar zasu daki juna,wani salon gaisuwa da suka saba yi a tsakaninsu,kafin daga bisani kowa ya ware hannun sukayi musabaha sosai,ya fara takawa zai koma kan kujerarsa

“Tun jiya naga sanarwar general meeting daga office na president,yau kuma katsam sai gashi kayi cancelling ka maye gurbinsa da naka” sai daya zauna sosai sannan ya aza zagayayyun manyan idanunsa a kansa

“Yes,anything else?” Kafada yadan dage yana samawa kansa gurin zama

“Eh……kamar bai dace ba,bai kamata kayi cancelling ba dab da lokacin yin meeting din” ya qarashe maganar yana daukar wata calendar dake dake gefansa yana dubawa,baiyi maganar dama don ya bashi amsa ba,don yasan dama ba lallai bane ya amsa masa din.

         Shuru tayi tana duban Miss sameera bayan ta shaida mata anyi cancelling meeting nasu gaba daya daga office din CEO,an kuma maye gurbinsa da board meeting,ranta yadan baci kadan

“Amma for what reason ne sameera?”

“Madam,ban gani sun fada ba,amma dai i think wani babban uzuri ne ya taso” shuru ta sakeyi kafin daga bisani tace

“Alright,ki shiryamin takardun da zan fita dasu” ta amsa mata a aladabce ta fice.

             Delay din da aka dan samu kafin miss sameera ta gama hada komai,shi ya kawo tsaikon fitarta on time,ta tsaya ta gyara yafen laffayarta,ta dauki wayarta da system dinta sannan ta fito,sameera na biye da ita

“Madam,idan ba damuwa zan rigaki isa gurin” ta fada cikin girmamawa,kai sãahar ta gyada mata,dom ta fuskanci me take nufi,miss sameeran hard worker ce sosai,hatta da yanayin tafiyarta irin me gab gab din nan ne cike da sauri,ita a iya nata yanayin halittar iya saurinta kenan,amma ta tabbatar ya yiwa sameeran kadan,shi yasa ta bata wannan damar.

           A floor din dake qasan nasu za’ayi taron,ta isa gaban elevator ta bude ta shiga,ba kowa a ciki sai ita daya,wannan ya bata damar sakewa. Saidai qofar na shirin rufewa,sai taga ta tsaya,abinda ya sanyata dago kai kenan a nutse tana duban bakin qofar.

           Kafarsa dake saye cikin rufaffen baqin takalminsa ya sanya daga bakin qofar,abinda ya hanata rufewa kenan saboda na’ura na aikata da saqon akwai mutum dake shigowa ciki,duk da cewa yana magana da wani dake tsaye a bayansa,amma hakan bazai hanaka ganin gefan kyakkyawar fuskarsa wadda ke kwance lamban da suma ba,sumar dake baki sidik ta kuma kwanta da kyau saman farar lallausar fatarsa,sassanyan qamshinsa dake kai kawo har zuwa cikin elevator din ya karade gurin.

         Ido ta janye a hankali tana goye hannuwanta a qirjinta,ta lumshe idanun nata can qasan ranta tana addu’ar idan ya ganta ya koma kamar yadda suka saba,duk yadda takai ga qin hada hulda da maza,ba kasafai takejin tsanarsu ba indai ba harkarta suka shiga ba,amma shi wannan din,tana jin tsanarsa ne naturally daga qasan ranta,banda yana tsaye ne ta bakin qofar,ita kuma tana jin qyashin ce masa ya matsa,da tuni ta fice daga elevator din,ta gwammace ta jirayi wata,koda zata sake bata lokaci fiye da wanda ta bata dazun.

           Dai dai sanda tunaninta ya yanke ya kammala magana da mutumin,ya matso da niyyar shigowa idanunsa ya fada a kanta,ta karkatar da kanta daga fuskantar qofa ta maidashi left side dinta kamar me kallon wani abu na daban,sai ya janye shanyayyun idanunsa,yana tsuke fuskarsa da kyau,cikin ransa yanajin ya kamata a raba elevator din maza da mata a company,bai kamata aci gaba da cudanya haka ba,ya isa ga madannin ya bata umarnin inda zata saukeshi.

         Ganin ya gama shigowa kuma qofar bata kai ga rufewa ba,saita sauke hannunta,ta kuma nufi qofar da niyyar ficewa ta sauya wata,sarai ya ganta,ya kuma fuskanci fita zatayi saidai hakan bai dakatar dashi daga dannan madannin ba,wanda gab da zata fita qofar ta rufe ruf,sannan kuma ta fara sauka dasu zuwa qasan da sasarfa cikin cika umarnin da aka bata.

             Saukar data fara yi cikin ba zata babu zato wani jiri ya fusgeta,qaqqarfan tsoro ya mamayeta,ta runtse idanunta cikin hanzari ta dafe qarfen dake kusa da ita,tun asali ita ba me yawan son hawa lifter ko wani iri bane,ta sauke boyayyar ajiyar zuciya tana sauke numfashinta a hankali,har zuwa sanda taji tsaiwar elevator,saidai abun takaicin tun bata bude idanunta ba taji floor din da suka sauka ba nan zata je ba,ta bude idon a hankali ranta yana baci. Daga bakin qofar ta ganshi a tsaye yana magana da daya daga cikin guard nasa.

           Sosai ranta ya baci,do meye zai maida elevator din jirgin yawo?,bayan yasan bashi kadai bane a cikinta,koda baiyi hakan ba already tasan shi din ba mai sanin darajar dan adam bane,yana da izza, izzar da a kallo daya zakayi masa ta karanceta tasss saman fuskarsa da motsinsa.

          Bata sake motsawa ba daga gurin,ta bawa banza ajiyarsa har ya gama abinda zaiyi,ya sake takowa ya zabi floor din da zata ajjiye shi tamkar baisan da mutum a ciki ba. Tana iya jin sanda kira ya shigo wayarsa,ya daga ya kara a kunnensa,saidai bata iya jin abinda yake fada clearly,taja tsaki qasan ranta kamar zata tsinke zuciyarta saboda haushi da kuma takaicinsa.

Page 21

         Tana da tabbacin meeting hall din ya nufa,dole yana gaba tana biye dashi. Tun daga nesa dukka guards nashi suka zama ready da isowarsa,daya daga ciki ya iskeshi a hanya riqe da suit jacket dinsa,ya taimaka masa ya saka,sannan ya karba komai dake hannunsa suka take masa baya har zuwa bakin madaidaicin hall na musamman da aka tanada saboda ganawa me muhimmanci irin wannan da manyan masu ruwa sa tsaki cikin company din.

             Dai dai sanda ta iso dab dashi ya gama magana dasu,kusan lokaci daya suka tura qofar,suka kuma sanya qafafunsu,sai ya zamana tamkar dama a tare suke.

              Hankula da idanuwan dukka board members din dake hall din yayo wajen, kasancewar shi kadai dama ake jira,a hankali kallon dake saman fuskokinsu ya canza,idanuwansu na karakaina saman kyakkyawar fuskar sãahar dake cike da fushi,baquwar fuskar dake dauke da wani irin sassanyan kyau me jan hankali,wasu kuma cike da mamakin wacece ita?,meye alaqarta da CEO dinsu?,wanne irin matsayi gareta da har sai daya jirata suka taho tare?,take wutar kishi ta kunnu a zukatan matan dake zaune a wajen,harda wani sashe na mazan gurin,saura kuma zukatansu suka cika da wasu wasi,take wutar jita jita ta fara tsiro a wajen,aka fara qus qus a tsakanin juna,ko kusa daga shi har sãahar da ranta ke abace basu ma lura da hakan ba.

           Kujerarsa ce qwaya daya tal daga can saman qololuwar table din,daga gefanta ya tsaya ba tare daya zauna ba,sannan cikin husky voice dinsa dake da wani irin amo na zallar kwarjini yace

“I apologize for not arriving on time” a nutse sãahar dake zaune cikin tata kujerar dake daura da tashi ta daga kanta,tanason kallon qwayar idanunsa ne cike da mamaki,bata taba tunanin zai iya apologizing wani akan wani abu ba

“let’s start for what brought us together here” ya kuma fada yana zube hannayensa cikin aljihun wandonsa,fuskarsa cike da seriousness dake cakude da kwarjini.

            Cikin wani irin salo na tsari meeting din ya fara gudana,tsarin da kana gani kasan ya samo asali da tushe ne daga wajen CEO din yasan abinda yakeyi,dukka tsahon zaman nan yana tsaye ko sau daya bai zauna ba, saidai time to time ya durqusa ya danyi rubutu a system dinsa ya same miqewa,duk kuwa da cewa saima tana wajen,kuma aikinta ne ta nadar masa dukka bayanai.

          Tunda aka fara tattaunawar batace komai ba,a nutse take sauraren komai tana kuma sake samun ideas sosai,saidai gaba daya a takure take,hakanan ranta kuma a bace yake.

          Tun daga sanda ta shigo gurin ido yayi yawa a kanta,daga mazan har matan wanda ita batasan meye dalilin kallon ba,bayan ta zauna ta samu raguwar idanun da sukayi mata caaa,saidai har kawo yanzu idanuwan mutum biyu hudu sun hanata sakat. Biyu daga cikinsu mata ne,don haka kallonsu bai wani dameta ba,sauran biyun kuma dukkansu sun fito daga jinsin da basa ga maciji watonJINSIN MAZA. Dayan ta fahimci shike riqe da muqamin chief financial officer (CFO) a bayanan daya gabatar,dayan kuma batace ga nasa muqamin ba,saidai tunda har yake cikin board members wani ne tabbas cikin kamfanin.

             A nutse ta maida dubanta ga takardar da take kusan hannun kowa dake wajen,wadda tsari ne na abinda za’a tattauna a wajen. Yadda tattaunawar ta dauki zafi,sai take ganin kamar ana shirin sauka daga kan ainihin abinda ya tattarasu,zuwa sanda MT jarma ya dan buga table din gabansa,dakin ya dauki shuru,ya gyara tsaiwarsa da take qara fidda zatinsa,cikin qwarewa da fasahar iya magana dake cakude da taushin muryarsa me zurfi ya fara nasa bayanin. Shuru gaba daya hall din ya dauka,maganganunsa da iya sarrafa harshensa sunja hankalin kusan kowa dake gurin,har zuwa sanda ya kammala ya rufe da fadin

“Ina buqatar tattararren bayani daga kowanne member personally,you can ask question if anything seems unclear or confusing” ya qarashe fada yana sauke dubansa akan kowa dake cike da gamsuwa akan bayanansa,a hankali har idanunsa suka fada a kanta,lokacin da ta bude folder dinta tana dubawa,tamkar ma bata a wajen ake dukka wannan zazzafar tattaunawar. Janye idanunsa yayi,ransa na baci,baiga amfaninta cikin kamfanin ba har yau ,wannan zaman yana daya daga cikin tattaunawa me amfani da zata iya zama tushe na fitar company din daga matsalar da yake shirin afkawa,yaja qaramin tsaki,yana shigar da wannan bayanan cikin system dinsa.

         Cikin jikinta taji kamar ana kallonta sama da idanuwan da suke kallon nata a dazu,don haka ta rufe folder din nata a hankali ta daga kanta,ta jjiye folder din daga gefe ta gyara yafen laffayarta,dai dai sanda suka sake hada idanu dashi karo na barkatai. Qasa qasa taja tsaki tana gyara abun maganar dake ajjiye a gabanta,tunda suka zauna gurin yake qare mata kallo iya son ransa kasancewar yana zaune ne kujerar dake fuskantarta

“Akwai muhimman abubuwan daya kamata ace anyi magana a kansu,saidai ba wanda yayi magana akansu din duk tsahon zaman, though dai we’ve got ten minutes left…” A nutse ya daga kansa daga system ya saukesu a kanta,a take idanuwansu suka gauraya waje daya,cikin qasa da second uku kowa yayi saurin janye nasa,saita juya ga abun maganarta ta fara nata bayanin a taqaice.

            Kamar sanda yake magana,ko a yanzunma shuru ne ya sake wanzuwa a dakin taron,amon muryarta da nata salon turancin tatacce kamar nasa,mintuna shida kacal ta tattara komai A taqaice,sannan ta miqa file ga mr sameera tace a sadar dashi ga office na ceo,suna buqatar sanya hannunsa don aiwatar da aikace aikacen da team dinta suka tsara.

“Any questions?” Ya tambaya kai tsaye,saidai ba wanda yace komai,hakan ya tabbatar da zuwan meeting din qarshe.

           Tana zaune saman kujerarta bata motsa ba har sanda mutane suka fara fita,kusan hakan al’adarta ce,bata yunqurin fita daga guri irin wannan me hadakar maza da mata ba,har sai an samu ragowar cunkoso gudun hada jiki dasu.

“Madam,banga kinsha komai ba” taji an fada daga gaba da ita kadan,a nutse ta daga kai tana kallon mai maganar,shine dai na dazun,me shegen nacin kallon tsiya,CFO,ya kafeta da mayun idanunsa yana jifanta da murmushi

“Thanks” ta fada masa a gajarce,saita fasa ci gaba da zaman,ta miqe tana daukar hand bag dinta tare ta yima Mr sameera inkiya,ta fara takawa a nutse,nutsuwar data haifarwa da takun tafiyarta wani irin salo da zaka dauka tsabar yanga gayu da kuma yauqi ne,saidai ita din tun asali naturally haka halittarta yake.

         K’arfe shida da mintuna motocinsa suka dauki hanyar gida dashi,a mugun gajiye yake jinsa,kowacce gaba ta jikinsa tana da buqatar hutu,banda hutu na gangar jiki,harma da hutu na zuciya.

          Tare da sajjad suke cikin motar,duk da suna hanya amma sajjad din na hirar yadda taron ya gudana

“But…… sabuwar president din nan,ta bani mamaki beyond my expectations,she’s very talented”

“I don’t know” taoufeeq da hankalinsa ke kan qaramin screen din dake liqe a kujerar gaban seat dinsa ya amsawa sajjad a taqaice,sam baya son zancanta,tunanin da yaketa kokawa dashi kenan tun dazun,abubuwan data gabatar ne sukata yi masa yawo akai,to ko su din bayason tunawa,haka kawai zuciyarsa ke gaya masa ta fiya zaqewa,kamar tanayi saboda ta sake samun shiga jikinsu da sanin abinda yake mallakin dr ahmad jarma din.

“She’s the best president da companyn nan ya taba samu I think” zuwa yanzu maganar ta fara gundurarsa,ba a bakin sajjad ba,kafin sajjad din yace wani abu kusan mutum biyar daga cikin board members din abinda ya barosu suna tattaunawa,bashi da sauran shaida data rage akan diya mace,banda mutum uku zuwa hudu daya ware,don haka yasa hannu ya ciro headphone ya toshe kunnuwansa dasu yaci gaba da abinda yakeyi. Sam sajjad dake bin tsarin aikin nata yana dubawa gami da ci gaba da yi masa zancanta bai lura ba,sai daya waiwayo da nufin nuna masa wata agenda sannan ya gani,baki kawai ya sake yana kallonsa,ya gaji da jinsa,amma bazai buda baki ya fada masa ba,ya gwammace ya toshe kunnuwansa da bututun sauti?,sai kawai ya rufe folder din ya adanata cikin wata ma’ajiya dake jikin kujerun me kama da akwatu,ya maida gurin ya rufe. A yadda ya nuna baida interest muddin bai adana folder din ba yasan bashi da asara na koma meye da zai sameta,bazai damuwa ba,illa iyaka yace yayi cancelling,ko ya sasu wahalar sake tsara wani jadawalin.

            Su biyu ne rak a babbar farfajiyar gidan a zaune,kamilar dattijuwa baaba rabi na zaune saman couch din da aka qawata gurin da ko ruwan sama bai sauka,sai daddadar iska me sanyi,qamshin furanni da koke koken tsintsaye kala daban daban.

            Saman cinyarta kyakkyawar farar yarinya ce, siririya sosai mara jiki ko kadan,sai zallan madarar kyau da Allah ya zuba mata,wanda tayo gadonsa ne daga gurin mahaifinta,matashin attajirjn dan kasuwa MT jarma.

          Fararen kaya ne sol a jikinta,dogon lallausan wando da rigarsa me dogon hannu,saidai akwai zanen pink din teddy daga gaban rigar,da siririyar sarqa me ruwan gwal a wuyanta,sai dankunnen barima shima da yafi kama da na gold din,sosai mayalwaciyar sumarta ke a gyare kuma a daure cikin farin ribbom,yankan farce baba rabin takeyi mata,gefe daya kuma tanata qoqarin karbar surutun da take mata cikin nuna kulawa babu gajiyawa ko kadan saman fuskarta.

             Hon din motocin kadai taji ta gane dawowar mahaifinta,mahaifin da duk fadin duniya baaba rabi takance,ta jima bataga irinsa ba shida diyarsa,wata irin shaquwa da qaunar juna ce a tsakaninsu me tarin yawa,duk da nakasu me tarin yawa dake tattare da rayuwar kowannensu,kamar a duniya basu da kowa sai junansu.

22

       Baaba ramatu bata hanata janye qafafunta da take yankewa farce da take qoqarin yi ba,ta sakar mata amma ta miqe tana cewa

“Yi a hankali,gidan fa zai shigo gaba daya fadeela” baaba ramatu ta fada cikin tausayawa,ganin yadda taketa zirgillo,ta kasa tsaiwa guri daya,har sai data isa ta kama hannunta suka nufi gurin da yake ajjiye motarsa duk sanda ya dawo daga office.

            Ita dince mutum ta farko daya fara gani kuwa,don motar na tsaiwa,bai tsaya jiran guards sun bude masa ya buda da kansa ya zuro qafafunsa waje,dai dai sanda itama taketa kutsawa ta tsakanin ma’aikatan mahaifin nata,har sai data iskeshi,ya buda hannayensa dukka biyun ta fada ciki cikin matuqar farinciki,zakayi zaton ba dazu dazu bane yabar gidan,tamkar matafiyin da yayi watanni bai cikin ahalinsa.

             Ba wanda ya katse musu walwalarsu,domin idan da sabo dukka wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya saba da ganin hakan,saida ya fidda mata dukka wani nau’in kayan ciye ciye data lissafa masa tana so kafin fitarsa,ya damqa mata sannan ya samu ta barshi ya fito daga cikin motar,suna saqale da hannun juna suka doso hanyar ainihin cikin gidan.

           Dab da zai isa kusa da baaba ramatu ya dakata,cikin girmamawar da har yau har kwanan gobe bata gajiya da bashi ita tayi masa barka da zuwa

“barka,ya gida,ya fama da me rigima?” Kusan wannan tambayar ta zame masa tilas,kullum sai ya yiwa baba rabin ita tare da yi mata sannu,abinda ke qara mata ganin kimarsa kenan.

         Murmushi ta saki,itakam a duniya rigimar fadeela bata taba damunta ba,idan ba’a tausaya mata ba bai kamata aga laifinta ba,duk da hakan yarinyar tana da wani irin hankali sanyin rai da kuma nutsuwa,kawai dai bata iya nutsuwa muddin taga mahaifinta

“Alhamdulillah,mun yini cikin qoshin lafiya” wannan kusan itace amsar da tafi masa kowacce amsa dadi a rayuwarsa,hakan yana nufin fadeela bata hadu da hatsarin da kowacce rana,tun daga bullowar rana zuwa faduwarta zata iya fuskanta ba,lalurar dake sanyawa duk wanda suke tare dashi fargaba,suke kwana su kuma tashi cikinta.

“Hajiya qarama ma ta dawo” baaba ramatu ta fada a ladabce,abinda yasa ya dakata daga tafiyar da yakeyi,sai ya sauya akalarsa zuwa sassan da ‘yan aiki suketa kai kawo,da alama suna aikin gyaran sassan ne.

            Fadeelan na biye dashi tana ci gaba da bashi labarai,wanda ayanzun ta sauya akalar labaran nata ne kan MOMMY QARAMA,kayan wasan data kawo mata da sauran tarkacen wasan yara.

            Daya daga cikin tafka tafkan sashe ne cikin sassan dake gidan,wanda kusan a manne yake da sashen da fadeela da baaba ramatu suke rayuwa a cikin sa.

           Kamar kowanne sashe na gidan,shima masu aiki ne mata ke kai kawo tsakanin makeken falon da yayi girman wasu gidajen kitchen,dining area zuwa balcony din da bedrooms din sassan suke a tsare,har ya zuwa upstairs din sassan da  nasa falon.

           Tun daga qofar falon suke zubewa suna gaidashi,ba tare da damuwa da cewa ko sau daya bai samu amsawa kowa ba a cikinsu. Sun riga da sun saba da wannan yanayin nashi,zasu iya cewa tsahon shekarun da suka dauka a tare dasu,basu taba katarin ganin koda murmushi akan fuskarsa ba bare akai ga dariya.

“Hajiya qarama fa?” Ya tambayi matar data fito a kitchen ta kuma zube a gabansa cikin ban girma

“Tana sama” bai amsa mata ba,ya fiddo wayarsa ya fara kiran wani layi. Bugun farko aka daga cikin qasa da second daya ya amsa da

“Okay” ya maida wayar aljihu,ya zauna saman daya daga cikin kujerun yaja fadeela jikinsa ya dorata saman cinyarsa yana ci gaba da bare mata chocolate din.

            Minti daya tal motsi ya fara tashi daga upstair din,kafin daga bisani sautin takalmi dake bada d’as d’as ya biyo baya.

              Farar macace doguwa sambal,ma’abociyar tsaho da kuma qibar da batayi yawa ba,koda batayi kama da toufeeq ba,amma tun kallon farko zakasan cewa akwai alaqa ta jini me qarfi a tsakaninsu,dukkansu kuma babu qarya……a duban farko kadai zaka gane ainihin yare da qabilar da suka fito wato SHUWA.

“Marhaban Muhammad” tayi maganar murmushi kwance akan fuskarta,muryarta ta sanya fadeela zamewa daga jikinsa ta doshi stairs din tana murmushin itama

“Basai kin hauro ba,saukowa zanyi UKTIE” dai dai sanda ta qarasa saukowar,saita miqe hannunta duka ta riqe fadeelan da kyau,cikin wani irin duba me cike da zallar so qauna da kuma kulawa.

         Kujerar gefansa ta samu ta zauna tana bashi duka hankalinta

“Yanzun kake shigowa?,sanda na dawo ai baaba ramatu tacemin baka jima da fita ba” kai ya jinjina,cikin nutsuwarsa yace

“Barka da dawowa,i hope komai lafiya” murmushi ta kuma sakewa,tamkar kumatunta basa gajiya da fidda murmushin

“Barka kadai jarma,lafiya alhamdulillah,inacan inata kewarku,hankalina gaba daya yana kan uktie,ina fatan tun tafiyata ba’a sake samun wata matsala ba?”  Kai ya jinjina yana lumshe idanunsa hadi da budesu,da alama hakan kusan wata dabi’a ce tasa a duk sanda yake magana

“Komai an samu sauqinsa, alhamdulillah” ya furta cike da fatan hakan taci gaba da kasancewa. Zai iya cewa komai na jin dadin duniya ubangiji ya mallaka masa shi,saidai ita rayuwa bata taba tafiyarwa bawa a yadda ya sota dari bisa dari,hakanan bata taba kubuta daga tarin qaddara da jarrabawa,lalurar fadeela na dukka abinda ya sameshi a can baya ya aminta na daya daga cikin qaddarorinsu,kuma sila na samun tawaya daga cikar jin dadin duniyarsa.

“Na dawo na tarar julia bata nan” ta fadi fuskarta na nuna tsantsar fushi

“Na sallameta” ya amsa mata a taqaice,don shi din mutum ne da bayason doguwar magana sam sam sam

“Shine dai dai hakan da kayi,ta yaya za’a dauki a ninka miki salary dinki na asali sannan ki kasa aiwatar da abinda aka daukoki dominshi?,wannan ai tsantsar yaudara da kuma cin amana ne,naso ina nan,daa kafin tabar gidan nan ba shakka sai na hada mata da hukunci” sumarsa ya shafa da hannunsa daya sannan ya miqe

“Ya wuce”

“Allah ya tsare gaba,zan saka madam Stella ta sake lalubo wata,tsayayya da zata iya kulawa da ita” tayi maganar tana shafa sumar fadeelan cikin kulawa

“Yayi,but idan aka sake samun kuskure kusa dana baya,itama zata rasa aikinta ne kamar su”

“In sha Allah wannan shine karo na qarshe,masu aiki duka babu aminci,kowacce da irin nata sakacin” tayi maganar cikin salon fada. Dai dai sanda labulen daya lullube qofar balcony din dake falon qasa ya bude,budurwa dake ciki ta fito.

          Labiba ce sanye da kayan bacci,guntun wandon da iyakarsa cinya,sai wata fingilalliyar rigarsa wadda da kadan ta dara saman cikinta,cup hand ne da ita maqallalle iya dantsen hannunta,kanta baby dankwali,sai gashinta dake daure a ribbons,kusan kowacce sura ta jikinta a bayyane take. Ganin taoufeeq ciki falon sai ya qarasa kashe mata jiki,kowacce gaba ta jikinta ta amsa,amma kuma kallon daya watsa mata ya dakatar da ita daga tahowar da take izuwa gurin,ta tsaya cak tana tuna gamuwarsu ta qarshe,marin da fuskarta tasha da kuma irin zazzafan gargadin da yayi mata.

          Bai sake duban inda take ba ya juya ya fice abinsa daga falon a nutse cikin qasaitaccen takunsa.

           Wata ajiyar zuciya me qarfi ta sauke,sai daya fitan sannan ta samu sukunin qarasowa,idanun hajiya qarama a kanta har ta zauna

“Lafiyarki ke kuma?” Sake sakin ajiyar zuciya tayi,tana karbar ruwan tea da fried egg da daya daga cikin masu aiki ta kawo mata

“Muhammad”

“Me yasa kullum tunaninki da dukkan furucinki ko yaushe a kansa yake?” Kai ta girgiza tana ajjiye cup din da tayi niyyar kaiwa bakinta ta fasa

“Mommy,wani irin fitinannen so nakeyi masa,ba zaki gane yadda nake jinsa a raina ba,i can’t imagine my life without him” wani irin duba na tsanaki hajiya qarama take binta dashi tsahon wasu sakanni ta ajiiye numfashi,sannan ta gyara zamanta.

“Kiyi qoqarin ragewa,kinfi kowa sanin halinsa,bayasin shishshigi bayason kuma a fiya shige masa da yawa”

“Zan kwatanta” ta fada badon tana jin zata iya ba,wani sashen na kwanyarta kuma na tuna mata marin da tasha a haduwarsu ta qarshe. Taji babu dadi amma bataji haushinsa ba,daga qarshe ta tattara laifin ta azawa kanta,saboda tasan kuskure ta tafka ba qarami ba,tafi kowa sanin halinsa,ita kanta batasan zata iya aikata hakan ba,amma SO DA ZUCIYA saidai a barsu kawai.

              Sanda ya isa sashensa cook dinsa ya gama shirya table dinsa,gurin kawai zaka dauka wani gurin cin abincin shugaban qasa ko wani governor ne,ya samu sajjad har yayi wanka ya sauya kaya daga cikin bedrooms din dake sassan,a nan yabar fadeela ya haura sama shima don ya watsa ruwan.

          Minti talatin da wani abu ya kammala shima ya sauko,cikin fararen pajamas marasa nauyi masu ratsin baqi kadan,mutum ne meson amfani da fararen kayayyaki,kusan first choice dinsa a color fari ne.

         Tare da tab dinsa ya sauko,ya samu tuni sunyi ready saman dining sai yayi joining dinsu. Yau kam babu laifi a sake yake,hakan kuma sajjad yasan baya rasa nasaba da alamun dorewar lafiyar fadeela.

            Suna kammala cin abincin aikin kamfanin da bayanan da jibril ya turo masa na taron yau ya saka a gaba yana dubawa. Shima sajjad din aikin yake ragewa,kowa hankalinsa yana kan na’ura,don haka falon ya dauki shuru.

          Sajjad ne ya fara motsawa,ya jawo wata folder ya tura gabansa,ya daga kai yana dubana alamun neman qarin bayani

“Folder din president ce” qaramin tsaki toufeeq yaja,ba tare da yabi takan folder din ba yaci gaba da aikinsa. Tsam sajjad ya dakata yana dubansa

“Wai me kake nufi?,wannan folder din ita ya kamata ka fara dubawa kafin ka duba komai fa”

“Bani da lokaci” ya sake amsa masa a taqaice,sai kawai ya qyaleshi bai sake cewa komai dashi ba.

           Ba jimawa bacci ya dauki fadeela,ya tattara komai ya ajjiye,ya dauketa da kansa yabi ta siririn balcony da shi da fadeelan kadai ke amfanin dashi,ya bulla sassansu.

          Cikin falon ya samu baaba ramatu,su uku ne,ita da mai gyaran dakin fadeela zuwa sashen wato mabruka,da kuma wadda ke musu girki wato zuwaira,suna zaune suna hira,da alama daukewa baaba ramatu kewa sukeyi.

          Shigowarsa a sabe da fadeelan sai duka suka miqe,zuwaira da mabruka kawunansu a qasa suna masa barka da dare,baba ramatu kuma ta qarasa tana karbarta daga hannunsa. Idan da sabo ta saba,muddin yana gari ba kasafai fadeela ke zama suci abincin dare tare ba,yawanci sai dare idan tayi bacci yake kawota,idan kuma dare yayi sosai kwana takeyi a wajensa. Kafin baba ramatun ma ta gama karbarta zuwaira da mabruka tuni sun fece,mugun kwarjini yake musu,girmansa kuma suke gani sosai da har basa iya tsaiwa guri daya da shi idan ba shi ya nema hakan ba.

            Da kansa ya rarrage kayan wutar dake falon kafin ya juya ya fice shima.

         Inda yabar sajjad ya dawo ya tarar dashi,sai ya duqa ya tattare kayayyakinsa ya wuce daki bayan sunyi sallama.

             Saman bedside table ya ajjiye komai dake hannunsa yana dan sauke numfashi na alamun gajiya,ya cire bedroom slippers din qafarsa ya doshi qofar toilet. Alwala ya daura,sannan ya shimfida abun sallah ya tayar da sallahn.

          Cikin awa guda ya kammala komai,a maimakon ya hau saman lafiyayyen gadonsa dake lullube da tattausar shimfida,sai kawai ya jawo manyan duvets din dake kai har guda biyu ya shimfidasu a qasa ya sanya pillow,saidai yana kwanciyar yaji kaman ya kwanta akan wani abu. A nutse ya miqe yana duba wajen.

        Ido ya lumshe sannan ya bude yana furzar da iska

“Sajjad……inda maye ne ya kamani bazai sakeni ba” ya fada can qasa,ya zaro folder din,har zaiyi jifa da ita ya fasa,ya jawo bedside drawer ya jefa a ciki ya rufe ya maida kansa ya kwanta.

           Baiyi cikakken awa uku ba ya farka a firgice sosai,saidai duk da haka bakinsa yana dauke da kalmar

“La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” wani irin birkitaccen yanayi,hautsinannen mafarkin da baya rufa wata biyu baiyi shi ba. Ci gaba yayi da maimaita addu’ar,har ya samu dukka nutsuwarsa ta dawo,saidai jikinsa ya jiqe sharkaf da gumi har ta tsakiyar gargasar dake kwance a hannunsa qirjinsa zuwa qafafunsa,ya miqe a hankali ya doshi toilet.

           Alwala ya daura bayan ya kama ruwa,yayi tsaye a gaban madubin bandakin yana ci gaba da watsawa fuskarsa ruwa,sunayen mutum biyu suna masa yawo aka tare da mafarkin daya gama yi yanzun nan a kansu

“Maji,ameesha”

Page 23

           Ya motsa bakinsa a hankali yana maimaita sunan,me yasa yake yawaita maimaita mafarkinsu?,ameesha tuntuntuni ya gama rufe babinta a rayuwarsa…..maji fa?,yasan babu ta yadda zai iya cire jininta daga jikinsa,amma yawaita mafarkin nata a yanayin da yasan a zahiri ba haka rayuwarta take ba shine abu mafi daure kai a wajensa.

             Har sai da yaji idanunsa suna dan masa yaji yaji sannan ya kulle famfon,ya jawo towel ya goge fuskarsa data qara wani haske,ya fito a hankali daga toilet din zuwa bedroom dinsa,baccin da bai samu ya koma ba kenan,daga qarshe ya matsa ya koma saman sallayarsa ya sake kabbara sallah…..boyayyar rayuwarsa kenan da ba kowa bane yasan hakan.

           Washegari da wani irin weakness ya tashi,babu karsashin nan da kuzarin da ya saba wayar gari dashi duk safiya,saidai makara da yayi bai fito lokacin daya saba fitowar ba,don a sanda ya fito din tuni fadeela ta wuce makaranta.

            Cook dinsa yana tsaye yana serving dinsa,yayin da shi kuma yake danne danne a wayarsa,sallamar hajiya qarama ta karade falon,sanye take da wani lace na alfarma,wanda ke nuni da zallar tsadar da yake dashi,a kallon farko zaka karanci mutum ce me izza tare da son komai na alfarma da kerewa sa’a,don a iya takun tafiyarta ma kawai ya nuna haka.

             Kujera daya taja ta zauna cikin kujeru shiddan dake zagaye da mulmulallen dining table din me wani irin siffa da tsari,a gurguje Noah cook din nasa ya kammala zuba komai bayan ya zube a qasa ya gaidata,ya sauka da sassarfa yana barin parlor din zuwa kitchen don ya tsaftaceshi hadi da kammale komai kamar yadda ya saba a duk sanda ya kammala girkawa uban gidan nasa abinci,daya daga cikin dokokinsa daya kafa masa akan tsafta ne,baya qaunarta sam sam,sai kuma akayi sa’a shima Noah din gwanin tsafta ne dama.

“Kunyi waya da maji kuwa a kwanan nan?” Ta tambayeshi da kulawa,kamar ya dago kansa ya kalleta saboda ambatar sunan da tayi,wanda hakan ya tuna masa da mafarkinta da yayi a daren jiya,sai kuma yaci gaba da diban chips da yakeyi a fork

“Bamuyi ba,bata kirani ba”  boyayyar ajiyar zuciya ta sauke,duk da hakan batajin nutsuwa a tattare da ita,shurun maji ta tabbatar bawai yana nufin tabar mata toufeeq bane,hakanan a duk sanda shurunta ya tashi maido da amsa……yana magana ne cikin amo da amsa kuwwa me qarfi,irin qarfin da ita kanta takejin sautin saman jiki da zuciyarta. Ta sani,ba sanin jiya ko yau ba……itadin jarumar macace,wadda bata yarda da faduwa saarewa ko gajiyawa ba,wannan dalilin ne ya sanya har yanzu burinkan mommy qarama ya gaza kaiwa ga gaci,duk da ta cimma nasara da galaba masu yawa a kanta

“Ka qoqarta kayi kiranta” kai kawai ya gyada mata,shuru ya sake ratsa tsakani,tana mamakin yadda har yau bai iya doguwar hira da ita ba,duk da tana data cewa da yawa cikin al’amuran rayuwarsa

“Nace ba” ta sake fada tana fifita masa tea din don ta saisaita zafinsa,qwayoyin idanunsa kawai ya daga ya kalleta ba tare da yace komai ba har zuwa sanda ya janyesu. Janyesun da yayi ne ya qara mata qwarin gwiwa,idanunsa na dabanne,haka kallon dake cikinsu,suna da kwarjini wanda har yau idan ya dubeta tana jin hakan sosai yana tabata

“Yaruwarka HASEENA,nace kuna gaisawa kuwa?” Sosai tambayar tata ta bashi mamaki,ita kanta daya kalleta sai taga tambayar kamar bata hau dai dai ba,tunda tasan kome yake akwai tsakaninsu

“Bani da lokacin biyewa shirmenta” ya amsa a taqaice. Yanason ya bawa hajiya qaraman haske amma kuma shi din bame sanin yadda zaiyi magana me tsaho bane,a ko yaushe yakanyi magana ne a dunqule,indai bamai matuqar muhimmanci ba,shine zai zauna bayani.

          Murmushi hajiya qarama ta saki tana tura masa cup din tea din

“Me kakeso na gayawa daddynka?” Ta sake jefa masa tambayar tana dubansa. Bai amsa ba har sai daya kusa cinye abinda ke bakinsa sannan ya miqe alamun ya gama kenan

“Ya kamata ya fahimceni don Allah” shine amsar daya bata,saiya ciri tissue guda daya ya soma sauka,da kallo ta bishi,sannan daga bisani tace

“A dawo lafiya,Allah ya tsare” taci gaba da kallonsa har ya fita daga dining room din. Dubanta ta dawo dashi inda ya tashin,ta jijjiga kai,sai kuma murmushi ya kubce mata,tadan daki table din kadan sannan itama ta miqe ta fice a nutse cikin qasaitaccen takunta.

***********Kamar kowanne lokaci,yau yadan saba lokacin dawowarsa,don bai shigo gidan ba sai bayan sallar magariba,bayan sun tsaya sunyi sallah a masallacin dake gine daga farkon layinsu.

            A kullum itace mutum ta farko da yake fara nema idan ya shigo gidan,yau dinma hakanne,sassansu ya wuce kai tsaye,ya samu baaba ramatu tana gyara kayan ruwa lemo da ice cream kala kala da yake zubewa fadeela a fridge din.

“Barka da dawowa yallabai” tafada cikin mutuntawa,cikin girmamawa shima ya amsa mata,tun kafin ya tambaya kuma ta amsa masa

“Tana ciki ita da hajiya qarama” ta nuna hanyar da zata sadashi da bedrooms dinsu,baice komai ba yaci gaba da takawa da ‘yar sasaarfa zuwa dakin,yanajin yadda gajiya takebin gabbansa.

           A nutse tare kuma da sallama ya tura qofar dakin,hajiya qarama na tsaye goye da hannayenta,fadeela da sabuwar nannynta na daga bakin toilet,nannyn tana tsane mata jiki da towel.

         Sallamarsa kadai ta zaburar da ita,ta watsar da towel din ta tako da gudu,sai ya durqusa mata kamar yadda ya saba,ya bude mata hannayensa ta shige tana fadin

“Oyoyo” murmushi hajiya qarama ta saki

“Shikenan,mun huta da complain din daddy yayi late” siririn murmushin da ba kasafai ake ganinsa akan fuskarsa ba ya saki,wani irin sirrintaccen kyansa ya bayyana

“An dawo lafiya?,ina nan ina sake nunawa nannynta yadda zata dinga kula da abubuwa,bana fatan a sake samun matsala daga kanta” hajiya qarama ta fada,sai ya jinjina kai,yana maida hankalinsa ga fadeela data dauko wani kwali ta miqo masa

“Mommy qarama ce ta bani,kai nake jira ka dawo ka hadamin” karban kwalin yayi hannu bibbiyu

“I hope kince mata kin gode?” Kai ta gyada cike da zumudi

“Good,me zai hana ki bawa mommy ta qarasa ladanta?” Kafada ta noqe,kafin tace komai ma mommyn ta daga hannunta sama

“Inaaa,wannan kuma aikinku ne,nidai na gama nawa tunda na cika alqawari” ta fadi tana dariya gami da nufan qofa

“Allah ya bamu alkhairi tunda tsohonki ya dawo ai kuma shikenan” ta fadi tana ficewa daga dakin.

             Duk yadda yaso fa barshi yaje yayi wanka yaci abinci sannan a hada qin yarda tayi,abu daya ta bari akayi,ta kira nanny din nata,tazo ta saka mata kaya,tana riqe da kwalin suka fito zuwa sassansa.

           Ta harabar gidan suka sake fitowa maimakon yayi Linkin ya bulla ta sassan nasu,tana gaba yana biye da ita,dai dai sanda qaramar motar da aka gama parking dinta yanzu ke budewa.

            Labiba ce ke fitowa,sanye da wani skinny jeans da shirt mai gajeran hannu, high heels ne a qafarta me azabar tsini kamar idan ka takashi da kyau zai iya karyewa,yalolon mayafi ne saman wanda baida maraba da mayafin yaran da shekarunsu ba zasu zarta tsakanin uku hudu zuwa biyar ba

“Hi fadeela” abinda ta fada kenan,idanunta a kansa tana jin wani qunci a ranta,duba daya yayi mata,kallon da bata tunanin ya b’ata second uku yana yi mata shi,ya dauke kansa kamar yaga wani abun qyama

“Hi” yarinyar ta maida mata,sannan ta taka da hanzari tabi bayan babanta da yayi gaba tuni tana kiran ya jirata. Tsaye tayi a wajen har suka bace mata,sai a sanann ta samu qwatar kallonta daga kansu,taja wani dogon tsaki

“Yarinyar sai shegen rashin saurin yarda da sabo fal cikinta,ta kwashe halin tsohonta tsaf” tayi maganar cikin salon mita tana maida murfin motar ta rufe,sannan ta saka mata key tana takawa cikin gidan,zuwa yanzu ta fara tuqewa,zuciyarta ta fara gazawa daga yadda ganinsa yake neman fara yi mata wuya,ta jigata sosai da yadda a yanzun ya sake daure mata fiye da baya. A baya koda zai watsar da ita,koda bazai kulata ba,koda bazai kalleta ba amma bazai kyaret ba,bai kuma taba shata mata layin zama inda yake ba,saidai yayi kamar baisan da ita a wajen ba,ita kuma ko babu komai iya hakan ma tasan wata alfarma ce ta samu,wadda dubban matan dake yawo,suke kamar zasu mutu a kanshi basu samu hakan ba,ko babu komai tana samun daman zama ta kalleshi iya son ranta.

          Sai daya tsaya ya hada mata komai,ta sake tubure masa sai daya zauna suka fara yi tare sannan ta barshi ya shiga ciki,wanka ya fara yi,ya dawo ya shirya cikin gajerun pajamas.

           Yana tsaka da taje kansa wayarsa ta dauki tsuwwa. A nutse ya jawo wayar yana duba me kiran,MAJI shine ya bayyana saman screen din,sai ya ajjiye comb din hannun nasa,ya jawo stool ya zauna akai yana daga kiran.

          Sassanyar muryar dattijuwar,dake cike da wani irin amo dake nuna zallar sanyinta koda a yanayi na halitta ma,tayi cikakkiyar sallamar data saka zuciyarsa dokawa,ya lumshe idanunsa yana amsa sallamar tata,tare da qoqarin tuno watannin da ya shafe ba tare daya kirata din ba

“Ka manta dani ko moha?” Ta kirayeshi da sunan da ita kadai ke kiransa dashi,kuma koda a wani guri yaji wannan sautin ya tabbatar ita dince,ko kuma wani dake da alaqa da ita.

          Cikin tsananin jin kunya da nauyinta ya motsa labbansa

“Kiyi haquri” ya fada a sanyaye,qaramin murmushi ta saki,ta saba da jin wannan kalmar ta ban haquri daga bakinsa,har batasan iya adadi ba,bada haqurin da kuma ba wai yana nufin ya daina bane,wani abu ne da yake faruwa tsahon shekaru masu yawa,wanda batasan ranar yankewarsa ba,duk da cewa idan har ta bugi qirji ta kuma daga hannuwanta da sunan samun nasara ba shakka batayi laifi ba.

        Cikin wani irin rashin sakewa da kuma rashin sabon da baisan daga ina yake taso masa ba a duk inda suke waya ya fara gaisheta,saidai kuma cike da girmamawa ne

“Ina fatan komai yana lafiya?”

“Alhamdulillah”

“Ma sha Allah,kada kayi wasa da addu’a a dukka wani gaba ta rayuwarka,komai yana da lokaci,kuma nan kusa nake fatan samun wani haske da fatahi daga rayuwarmu gaba daya,ina jikata?” Ta tambayi fadeela cike da shauqin son jin muryarta,wata irin qauna me gauraye da tausayi takewa yarinyar. ‘Yar halak din kamar tasan ita ake nema kuwa,sai gata ta buda qofar dakin riqe da games dinta tazo kawo qorafi. Kai tsaye ya miqa mata wayar

“Maji ce” ya fada qasa qasa,saita ajjiye kayan hannun nata duka a qasa,ta tako da sassarfa ta karbi wayar.

        Gefe ya koma ya harde hannayensa yana kallon yadda suke waya da maji,kamar sun san juna sosai da sosai,duk da batasan maji ba,amma akwai wanda wani irin sabo tsakaninsu qwarai da gaske,tasan maji a baki kamar me. Lokaci kadan tama manta da daddyn nata dake tsaye,hira suke abinsu,kamar ba daga wata qasa maji din ke kira ba,bata jin katinta sam da take yawan qonawa akan fadeela.

Page 24

           Lokaci kadan tama manta da daddyn nata dake tsaye,hira suke abinsu,kamar ba daga wata qasa maji din ke kira ba,bata jin katinta sam da take yawan qonawa akan fadeela.

           Sun jima kafin daga bisani suyi sallama,ta kawo masa wayar,fuskarta qunshe da murmushi

“Daddy,wai a ina maji take?” Ta jefa masa tambayar da baiyi zaton jinta daga bakinta ba

“Bata a nan qasar angel”

“Tana ina?” Ta sake tambayarsa,da alamar da gaske tanason jin a inda take din

“Algeria”

“Yaushe zamuje daddy?,tanason ta ganni nima inason na ganta” ta tambayeshi a shagwabe. Ido ya zuba mata sosai,shi kansa a yanzu bazai iya kai kasa kai tsaye inda maji take ba,tun haihuwarsa har girmansa bai taba zuwa,a baya yana da kwadayin zuwan,amma a yanzun kwata kwata babu wannan cikin ransa,baisan kuma yaushe hakan ta faru ba,kawai dai ya tashi ne dare daya yaji yayi loosing interest akan dukkan abinda ya shafeta,kafin daga bisani kuma ya yakan yawaita samun mantuwa akan komai daga danganceta.

“Zamuje angel”

“Daddy yaushe?” Ta sake tambayarsa tana kafeshi da idanu,idanunsa ya janye daga kanta,murmushi kadan yana subuce masa,ya fuskanci rigima takeji

“Wata rana” ya bata amsa yana sanya hannuwansa ya dauketa cak hadi da cewa

“Muje muci dinner” zata sake magana ya dora yatsansa akan lips dinsa gami da cewa

“Shshshsh,ya isa” duk da qanqantarta amma tana gudun abinda zai bata masa rai,tana matuqar jin maganarsa fiye da tunani,saita kwantar da kanta a kafadarsa,a haka suka qarasa dining room din.

         Sallamar cook din nasa dake jiran ya iso yayi serving nashi yayi,da kansa ya zuba musu iya abinda zasu iya ci shi da fadeelan yabar sauran.

*********Karfe daya na rana ne,lokacin da kowanne ma’aikaci dake qarqashin company din yake morewa lokuttansa na break. Dai dai lokacin da sãahar a cikin nata office din ta duqufa wajen ganin ta gama hada dukka bayanan data samu daga financial team na company,tana duba yiwuwar yin magana akan document dinta dake office na CEO,batason tayi aikin banza,tanaso ta aiwatar da dukka tsare tsaren da tayi,don ta tabbatar zai kawo gagarumin ci gaba da kuma sauyi cikin company din.

          Buda qofar da akayi ya sakata daga fararen idanunta tana kallon bakin qofar,mr sameera ce,ta bata izinin qarasowa bayan ta janye hannuwanta daga kan system din

“Ranki ya dade,sir hamza ne ya sake dawowa” idanunta da suka dan daure saboda kallon allon system din tadan juya kadan,qaramin tsaki taja,hamzan yanason shiga rayuwarta,kaf fadin company din a yanzu bata da wata matsala saishi,yaqi fahimtar inda tasa gaba,gaba daya sake shige mata yakeyi a kowanne lokaci,don kawai office dinta yana da alaqa da department dinsa,don ko yanzu report din da take dubawa daga office dinsa ya fito,banda haka da tuni ta yanke dukkan wata alaqa da zaya bashi damar ganinta

“Ki gaya masa ba yanzu ba,aiki nakeyi,ya tura kowanne saqo ta email din office,zan duba sanda na zama available” jinjina kai sameera tayi,ta juya ta fice.

          Cak ta tsaya da aikin da takeyi tana sake jan wani dogon tsakin da yafi na farko,saita tura kujerarta baya tana dan fidda iska daga bakinta,da alama wani tunani ne ya darsu a ranta lokaci daya. Yatsunta tasa tana murza goshinta dasu,tana tuna shigowarta company a safiyar dazu,yadda ta tadda employee a dan hautsine,sakamakon korar wasu ma’aikatan guda uku da ceo yayi a safiyar

“wanne irin mutum ne shi?,me izza da dagawa?,he doesn’t give excuse to anyone?,abu kadan kora?,kowa ma yana iya kora ko yayi masa fada?” Tayi maganar can qasan zuciyarta,haushinsa da kuma tsanarsa suna huda zuciyar tata,abinda ta lura dashi ma,gaba daya yafi zafafa al’amuransa akan mata. Sake jan wani dogon tsakin tayi karo na uku,gaba daya tuna abin da ya farun yasa tayo loosing interest akan aikin,ta duba baqin agogon dake daure a tsintsaye hannunta qirar kamfanin Casio,akwai ragowar mintuna talatin kafin lokacin komawa bakin aiki yayi,coffe take da buqata,amma batason takura mr sameera,don haka ta tsugunna a hankali ta daura igiyoyin baqon takalaminta daya mugun haska farar qafarta me dauke da dogayen yatsu,ta miqe a nutse ta dauki iya wayarta ta fita a office din.

         A nutse take takawa a farfajiyar gurin,cikin girmamawa ma’aikatan ke gaidata,saboda Suna respecting nata sosai,duk wanda yayi mu’alama da ita kuma kusan sai ya fadi halinta ya kuma yi mata shaida me kyau.

         Ko kusa ko alama bata ga koda inuwarsa ba,saijin maganarsa tayi a bayanta

“Ranki ya dade,barka sa fitowa” mr hamza kenan,wanda ke biye da takunta yana son ya cimmata cikin zumudin da katarin ganin fitowarta da yayi. Kadan ta waiwaya ta aje masa kallo daya

“Ya kake?” Ta fada a daqile,hamza na daya daga cikin mutanen dakeson zame mata barazana cikin company din,tare da yi mata kutse cikin walwalarta da al’amuranta,duk wani hanya da zatayi avoiding nasa tayi,amma ta karanci kamar baya fahimta,da alama yana sahun mazan dake da shegen naci da kafiya ne

“Lafiya amma ba qalau ba,please ki taimaka ki gayawa secretary dinki,ta daina min shamaki da ganinki,wallahi it really hurts me” sunzo bakin qofar kitchen din,kuma bata da buqatar yaci gaba da binta,don haka ta dakata,ta juyo gaba daya tana dubansa

“Excuse me mr hamza…..ko zaka taimaka ka juya,saboda banason ka shigarmin lokacin nawa hutun,na gaya maka idan maganar office ce ka tura ta email zan duba,idan kuma bata office bane, please i beg you,banason wani abu da bashi ya taramu a nan ba ya hadani da kai,bama kai ba,koma waye bana buqatar wata hulda ko alaqa” da hanzari ya buda baki zai maida mata da martani,amma sai taji yayi dif,batasan dalilin daukewar wutarsa haka lokaci guda ba,amma koma meye sanadi ita ba damuwarta bane,don dama tafi buqatar shirunsa akan amsarsa,don haka ta juya ta shige kitchen din kanta tsaye.

          Wayam din data gani a kitchen din babu kowa da kuma qarancin haskensa bai sanya ta zaci akwai wani abu ba,saboda wannan shine karon farko data taba shigowa kitchen din. Coffe dama kadai tazo nema,don haka ta nufi mini coffee maker din data gani a jone,data duba sai taga akwai saura a ciki,don haka ta ciri mug guda daya,ta cikashi dashi,yawunta yana tsinkewa,saboda wani qamshi da taji yanayi na musamman,uwa uba kuma kana kallonsa zakasan ya hadu iya kwadayinka da shan coffee.

        Dan qaramin murmushi ta sauke,saita gyata tsaiwarta tana kai mug din bakinta,dai dai sanda ta juyo. Babu zato ta saki mug din,cikin razana taja baya,fararen idanunta suna sake girma hadi da fitowa waje. Tsoratar da tayi yasa bata iya tsaiwa ta tantance waye ba tayi qofar waje da sassarfa,saidai kuma tana dab da isa ya rigata isa gurin,ya saka hannu ya tura qofar ya rufeta bam,taja birki a mugun hautsine tana sauke dubanta a kansa,sai a lokacinne ta gane waye.

             MT jarma ne da kansa,cikin shigar suit dinsa ta ko yaushe,saidai kuma a yau din babu suit jacket din a jikinsa,alamu suna nuna ya barota a office,hannun rigar ciki da ya kasance dogo ya tattareshi ya barshi iya gwiwar hannunsa,wannan ya bawa murdadden hannunsa dake cike da gargasa da wasu irin jijiyoyin da yawan shiga gym ya haifar dasu. Kwantacciyar sumarsa me santsi a dan hargitse take kadan,lips dinsa sundan sake yin jaa saboda zazzafan coffee din da yake sipping a hankali.

         Ko a yanzun ma da yake tsaye ci gaba yayi da sipping abinsa cikin nutsuwarsa da kamewarsa,kamar bashi ya tsorata ta ba,sanann yasa hannu ya garqame musu qofa haka kawai ana zaune qalau. Ranta ne taji yayi mummunan baci,tadan motsa fuskarta kadan saboda yadda zafin coffee din data saki ya dan taba qafarta yake mata zafi kadan kadan,wannan wacce irin dabi’a ce zai samu guri ya zauna a kitchen,a corner din da ba lallai kai ka iya ganinsa ba?,saita janye idanunta ta taka zuwa qofar don ta bude ta fice,don bata qaunar hada rufi daya dashi bare taci gaba da zuqar qamshin turarenta da yake neman sanyaya dukkan wani zafi data dauka akan abinda yayin.

           Table din dake daura dashi ya matsa kadan ya dora cup din,cikin zuzzurfar muryarsa dake cakude da wani irin amo me ya soma magana

“You must learn saying salam a duk wajen da zaki shiga,saboda nan din mudai musulmai sunfi yawa……sannan bari na taimakeki na tuna miki wani abu daya,nan masana’anta ce,kayi aiki a biyaka da gwargwadon wahalarka na wata daya,ba waje bane da aka bude saboda soyayya ba,saboda haka ki kiyayi bawa wani damar ganinki a office da kebantacciyar buqatarku wadda bata da alaqa da company,idan ba haka ba,you will loose your job” ya qarasa maganar yana dora hannunsa a mariqin qofar,ya budeta sannan yace

“Dont try to do this again……inda kin fita a yadda kikaso fita,wani ya ganki me kike tunani zai zata” bai jira amsarta ba ya taka zai fita, zuciyarta tazo mata iya wuya sosai. Yama gama raina mata hankali,yaso qona mata qafafuwa,sannan kuma ya bita da wasu sharuddansa marasa amfani a gurinta,tunda dai ai ita ba yarinya bace,tasan meye ya dace da ita. Ji tayi idan ya fita ba tare datace masa komai ba tabbas yaci bulus,duk da zuicyarta na qoqarin tuna mata maganganun yaa Saifullahi da yaa zaid na ta girmamashi,gaba yake da ita

“Shi kuma wannan kullemu da kayi fa?,idan wanin ya gani yace me?” Ta fada tana jin takaicin yadda tayi dogon zama a guri daya dashi,harta shaqi turarensa da kyau,ya shiga kowacce kafa ta hanci da kwanyarta.

          Waiwayowa yayi ya zube mata manyan kewayayyun idanun nasa dake da wani irin magnet da kwarjini,har sai dataji kamar zata zube,yayo taku biyu ya dawo baya kadan

“Kina iya gayawa duk wanda ya tambayeki….. nayi raping naki ne,don wanann din kadanne daga aikinku”.

“Ya salam” ta fada can qasan zuciyarta hade da wani mugun bugawa da zuciyar tata tayi,ba kuma tare data shirya ba ta koma da baya ta zauna saman kujerar dake kusa da ita,wanda tayi yaqinin banda taimakon Allah kujerar tana kusa da ita lallai zata iya faduwa qasa. Kamar baice komai ba ya juya a nutsensa ya fita a kitchen din.

Page 25

         Wasu hawaye masu zafi taji sun cika mata idanu,qarshen cin zarafi yayi mata shi,FYADE ai ba qanqanuwar kalma bace da furtata zai zama abu me sauqi har haka ba,kadan daga aikinsu me yake nufi kenan da ita?,kawai saita kasa riqe hawayenta,ta barsu suka silalo ko zata samu ganin gabanta da kyau,tun bayan abinda adam yayi mata…..ba wani mahaluqin daya taba mata kalma me tsananin daci zafi da qasqantarwa irin haka ba,sai ta miqe kawai a gaggauce tana fita a kitchen din,har ranta tana jin tsanar shi kansa kitchen din,da kuma dalilin daya kawota.

           Tana fitowa a hanya suka hadu da sameera,ta tareta da yanayi ya dan rudani kadan

“Ance kitchen kika tafi,inata qoqarin tsaidaki saboda time ne na shigan sir kitchen din yayi lunch,karkije a samu matsala”

“Ba’a samu ba,gashi na dawo” ta bawa sameera amsa a taqaice tana wuceta.

          Toilet dinta ta fada tana sake rage qwallar takaicinsa data sake taruwar mata,sai data kusan minti goma kafin tayi controlling kanta,ta daura alwala ta fito ta tayar da sallah,tana sake jin tsanarsa qwarai a ranta,tana kuma sake tabbatarwa da kanta shi din wani irin mutum ne mara iya mu’amala da gautsin harshe.

         Ko bayan ta idar zamanta taci gaba dayi saman abun sallar,duk da akwai sauran ayyukan da takeson gamasu a yau din,a haka miss sameera ta nemi izinin shigowa.

“Boss ne yake neman izinin ganinki” tunda tace boss ta gama fahimtar waye,abun sai ya girmame mata,dr Ahmed da kansa yafi qarfin neman izini wai don zai shigo office dinta,da sauri ta tashi saman abun sallar tana dubanta

“Yafi qarfin neman izini miss sameera,maza bude masa qofa” saita juya a gaggauce tana murmushi,tabbas sãhaar din batasan waye boss ba,da batayi mamaki ba don ya nemi izinin shigowa ba.

         Cike da tarin haiba kwarjini da kuma kamalarsa yayi sallama,saita miqe tsaye tana masa sannu da zuwa tare da nuna masa gurin zama,da kanta ta bude qawataccen fridge din dake office din ta ciro masa ruwa da lemo masu matsakaitan sanyi,kasancewar ita dinma ba mai yawan shan abu me sanyi bace

“Na gode sosai diyata” ya fada yana yaba dattakonta,da yadda take da girmama manya tare da sanin kimarsu. Ita kunyar godiyar ne ya kamata,tana neman gurin zama yace da ita

“Ya ayyukan?,ina fatan kina jin dadin aiki da yayan naki?” Qaramin murmushi ta kuma saki,kanta a qasa tace

“Alhamdulillah abba”

“Ma sha Allah,na sanshi sarai,wasu lokutan bashi da kirki,yana da zafin zuciya,amma kuma yana da tausayi” kai ta jinjina tana kokwanton tausayin da Dr yace toufeeq yana dashi.

        Ruwa kadan yasha,sanann suka fara tattaunawa kan sabbin ci gaban da aka samu cikin company din,daga bisani yace

“Sajjad ya gayamin,akwai kundin da kika bayar,ya gamsu da ayyukan ciki,ya kuma yimin bayani,amma har yanzu banga an aiwatar da komai ba”

“Tuni na miqa su ga office din ceo muna jiran sign dinsa”

“Kina da copy dinsa a gurinki?” Miqewa tayi a nutse,ta buda computer ta kawo masa gabansa. A nutse ya dinga karanta komai,

“Ma sha Allah,ma sha Allah” kawai bakinsa yake furtawa,baiko kai ga qarasawa ba ya dago kai

“Akwai ideas masu kyau da muhimmanci a nan,zaifi kyau a saka hannun da wuri,inaji a jikina za’a samu cimma gaci yadda akeso” sosai taji dadin yadda ya yaba mata din,har ta rakashi yana mata addu’a gami da sanya mata albarka.

            Lokacin tashi yana cika ta baro office dinta,kai tsaye ta sauka zuwa qasa,tana daga cikin sahun farko na ma’aikatan da suka baro office dinsu,don haka gurin ba cikowar masu daukan ababen hawansu. Hakan dama takeso,tayi ta fice kafin wancan mayataccen ya isketa,sam baya yin fushi ko kuma zuciya game da dukkan abinda zata gaya masa.

           Sau uku tana qoqarin kunna motar amma taqi kawo wuta gaba daya,abun ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,tunda dai tasan lafiya lafiya ta tafi ta barta. Ta gwada dukkan wata dabara amma taqi,dole ta fito ta rufe motar,ta fidda wayarta tana gwada kiran mechanic dinsu,tana masa bayanin abinda ya faru,tare da kwatanta masa kamfanin,kamfanin ba wani boyayye bane,don haka yace yana zuwa nan da minti arba’in zuwa awa daya.

           Sauya akalar kiran nata tayi zuwa ga number afifa,bugu biyu ta daga

“Bestie,kin tashi daga aiki ne?”

“A’ah,sai sixs,wani abu ne?” Lumshe idanunta tayi cikin damuwa

“Motana yaqi tashi,baisan meye damuwarta ba,kuma banason fita neman abun hawa na haya”

“Subhanallahi,to ba damuwa,bari zan iso kamar nan da awa daya saina daukeki,kinga na rage time din tashin kada ya zamana na fito da wuri”

“Okay,thanks” ta fada tana tsinke kiran. Da isowar mechanic din dana afifa tana sanya ran yayi lokaci daya,ta dubi agogon hannunta sannan ta sauke tana duban building din,ma’aikata sunata fitowa kowa yana kama gabansa,batason komawa can saman nan,don haka ta yanke ta wuce executive garden dake kamfanin ta zauna ta jirasu a can,da wannan shawarar ta karkata akalarta zuwa can din.

          A nutse ta durfafi gurin,yanayin wajen yana sake burgeta,da alama yana samun kyakkyawar kulawa. Sanya qafafunta kenan sautin muryarsa shine abu na farko daya fara ziyartar kunnenta,kafin daga bisani idanunta su sauka a kansa,dai dai lokacin da shima dan motsin da yaji ya sakashi daga kai,idanunsu suka sarqe waje daya,yana daga tsaye hannunsa guda daya cikin aljihunsa yana magana da wasu mutum biyu da bata gane ko su waye ba,saboda suna dan gaba kadan dashi.

            Qaramin tsakin da batasan meye dalilin yinsa ba ta saki,kawai dai tasan taji haushin ganinsa a wajen,ya kuma bata mata budget din da tayi na sakewa ta zauna a wajen ta jirayi afifa,saita juya a nutse tana fita a wajen.

         Dif maganar da yakeyi ta dauke,ya lumshe idanunsa a nutse yana jin wani irin bacin rai na taso masa,idan har dai dai kunnuwansa suka jiye masa,sautin tsaki ya jiyo,wanda yaga alamun fitarsa daga dan qaramin bakinta data turoshi gaba lokacin da take hada sautukan tsakin.

          Ransa ne yaji yayi wani mugun baci,tunda yake zai iya cewa ba wata diya mace data taba masa tsaki,tsakinma mara dalili,haka siddan saboda ganin araharsa?,nan take yaji bazai iya tolerating ba,don ya gama fahimtar kamar tana daukan kanta wani abu,tana da ji da kanta over.

             Sam basu lura da barin wajen yakeyi ba har sai da yakai qofar fita,cikin daga murya sajjad yace

“Hi man……ya kamata mu gama kafin mu wuce fa”

“One minute” kawai ya iya ce masa,idanunsa na biye da ita,duk da cewa ta danyi masa nisa kadan. Sai ya qara yawan takunsa,mutum ne ingarma me yawan kuzari,ga kuma tsaho da yake dashi,wannan ya taimaka masa nan da nan ya rage tazarar dake tsakaninsu,wanda sam bata sani ba,ta yanke shawarar ta buda office dinta kawai ta zauna ta jirayesu acan,ko hawa na nawa ne ta gwammace ta koma ta jirasu,akan dai ta sake ganin fuskarsa.

             Hankali kwance elevator ta bude mata ta shige,tana shirin komawa ta rufe shima ya shigo,ta koma ruf ta rufe sannan ta fara aikin haurawa dasu zuwa saman.

Page 26

         Haka kawai taji gabanta yayi mummunar faduwa,kowanne sashe na jikinta yayi sanyi saboda yadda ya zuba mata mayatattun idanunsa,yana jifanta da kallon tsana. Tayi tunanin zata iya jurewa kallonsa kamar yadda ya ritsata da nasa idanun,amma tun ba’a yi nisan zango ba taji ta gaza dauke nauyin zagayyun idanunsan nan masu tsananin haske,kamar ba idanun namiji ba. Gaba daya sai ta jita kamar wadda aka nannade aka jefa cikin wani keji,kamar an sanya igiya an daureta,ta dinga fatan na’urar ta sauketa da inda ta umarceta tayi ta fice ta bashi guri.

            Saidai kuma suna isa floor din ya matsa gurin madannan ya sake bata direction na dawowa dasu floor din qasa,a sannan ta waiwayo ta sake dubansa da fararen idanunta karo na biyu,still har yanzu ita yake kalla,kallon dake sake bayyana fushin dake kwance a zuciyarsa. Sake janye idanun nata tayi ta maida dubanta wani wajen,gaba daya kallon da yake mata ya wuce qa’idar da jarumtarta zata iya dauka,uwa uba kuma shirin rikicewa takeyi gaba daya,saboda yadda qamshinsa yake sake cika elevator din. Tattara hankalinta tayi tana jiran jin sun isa,ta riga ta gama ayyanawa a ranta suna isa zatayi hanzarin ficewa,don ta fuskanci kamar ya shirya tayita yawo dasu daga sama zuwa qasa,can can qasan ranta tana tuna tsakin data sakar masa.

               Da wani irin hanzari ta nufi qofar da zummar fita,amma kuma kafin ta isa har ya maida qofar ya rufe,ya kuma sake sakata ta lula sama dasu. Wannan karon tsaiwa tayi daga bakin qofar yana lumshe idonta,ranta itama ya soma baci da rainin hankalinsa,ta yaya zayazo ya sameta a waje ya kuma dinga mata wasa hankali?,na meye?,zata tsaya gab da qofa,zataga gudun ruwansa,idan ta fita yasa qarin tuwo ya dawo da ita.

           Duk yadda taci buri kuwa suna isa sai gashi tsaye bakin qofar,abun yayi matuqar bata mamaki,batasan wanne irin zafin nama gareshi ba

“Excuse me mana,fita zanyi” ta fada da siririyar lallausar muryarta

“Wa kika yiwa tsaki?” Ya jefe mata tambayar kansa tsaye cikin izza da qasaitarsa kamar wani basarake,duk da yadda yayi mata matuqar kwarjini,amma motsawar tata izzar ta bata qwarin gwiwar amsashi

“Da wanda ya tsargu” ta amsa masa tana qoqarin kaucewa qwayar idanunsa,don har yanzu tana cike da takaicin abinda yayi mata dazu a kitchen.

“Ko?” Ya fadi wani miskilin murmushin gefen baki na subuce masa,duk da cewa ba murmushi bane na kyautatawa ko jin dadi,amma wani irin sirrin taccen kyau ya bayyana muraran kan fuskarsa,fuskarta yake duba,yanason gano daga inda ta samo wannan qwarin gwiwar tsaiwa ta gwada masa rashin kunya,yayi imanin batasan wane shi ba,amma a yadda ya lura akwai quruciya sosai tattare da ita,qaramin abu kawai zaiyi da zai bata zazzafan warning,ta yadda ba zata sake marmarin maida masa martanin magana ba.

            Bata taba kawowa ba ko kusa ko alama,kamar a mafarki taji an take dogayen yatsunta da qarfi,sosai zafi ya ziyarceta,ya kuma ratsata tun daga saman qafarta zuwa qwaqwalwarta

“Wayyo Allah na” ta fada a jigace

“Wa kika yiwa tsaki nace?” Ya sake maimaita mata tambayar wannan karon da wani irin zafin rai,har hakan na bayyana kan fuskarsa

“Sa’anki ne ni?” Ya kuma jefa mata tambayar,duk da bata samu damar amsa masa tambayar farko ba

“Ko don kinga Dr ya baki damarmaki da yawa kike tunanin kanmu daya dake?” Ya kuma fadi a mugun tsawace,sautin tsawar tasa tana ratsa mata kunne

“Bakizan tsaki zagi bane a gurin wanda ya girmeka?” Still dai ya tambayeta yana kallon fuskarta,wadda zufa ta fara wanke goshinta dake lullube da wasu irin gashi masu matuqar santsi

“Lemme warn you……daga yau,duk randa kika kuskura kika qara yimin tsaki ko…….” Sai ya murza yatsunsa akan fuskarta

“Bazan koreki ba,bare kisa Dr yaga baqina,amma sai na ɓarka bakin tsakin,ki zama me d’a’a ga wanda yake sama dake” yana qarasa fada ya dage mata qafar,ya kuma kauce ya bata hanya yana jira ta fita.

         A wahalce ta tashi daga tsugunnawar da tayi,hawaye sun jiqa mata fuska,wannan shine qarshen cin zarafi da tozarcin da zaiyi mata,ba tare data kalleshi ba ta juya ta fita daga elevator din tana jan qafarta da tayi mata nauyi.

            Floor din qasa ya sanyata ta maidashi,yana tsaye yana kallon yadda take sauka qasa dashi,sai furzar da iska yake daga bakinsa,yana son ya fifita zuciyarsa daga zafin data dauka. A wajensa wannan din zallar raini ne,ba abinda ya tsana a duniya sama da tsaki,tsakinma a rasa daga gurin wanda zai fito sai mace?,macenma yarinya qarama wadda ya girmewa da shekaru masu dan dama,kuma ma ma’aikaciyarsu dake qarqashinsu,wanda kaf rayuwarsa ba yarinyar data taba masa irin hakan,kawai don ta samu dama daga gurin Dr,ko don tana ganin tana da kyau?, abinda ya gani dazu tsakaninta da hamza ya fado masa a rai,ya dunqule hannu ya kaiwa iska naushi,yana jin tsanar mata na nikuwa a ransa. Ya tsani mata totally, especially masu kyau irin haka,tabbas koda yaushe basu rabuwa da shaidan,babu wani alkhairi sam a tattare dasu sai tarin sharri,bazai bar mr hamza yaci gaba da barar musu da mutunci ba. Har ya saka dayan qafar zai fita yaji ya taka wani abu,sai ya dawo da baya yana duban qasa,wani abu me qyalli ne ruwan azurfa,ya duqa a hankali yasa hannu ya dauke,ya wulla a aljihunsa ya fice.

             A daddafe ta samu ta isa office dinta,tana budewa ta zube saman sofa ta saki wani nannauyan kuka me cin zuciya,tunda take apart from abinda adam ya aikata mata,ba’a taba tozartata irin wannan ba,saita koma ta kwanta sosai saman sofa din,tana jin zama yayi mata kadan,ta saki kukanta sosai tana share qwalla.

         A qalla ta kusan minti ashirin a haka sannan taji zuciyarta tayi sanyi,ta miqe ta zauna,dai dai lokacin kiran mahmud ya sake shigo mata,wanda wannan shine kira na biyar da yayi mata. Bata ko saurari wayar ba,ta miqe ta nufi toilet,ta wanke fuskarta da kyau,sannan ta dawo ta tsaya cikin office din ta dauki wasu qananun abubuwa nata ta zuba a jaka,da zummar har abada tabar aiki da kamfanin MT JARMA GROUP OF COMPANY,dama can sunci darajar yaa muhyi da bazata taba iya cewa a’ah ba.

            Tana shirin jefa wayar a jaka kiran nasa ya sake shigo mata,tuna tayi cewa a yanzun yanayin komai ne bisa iznin daya samu daga gurin mutumin da yafi kowa kima da martaba a wajenta,wanan ya sanya ta daga wayar,ta kuma mara a kunnenta ba tare da tace komai ba

“I hope kina lafiya ko?,ko zaki turomin full address na companyn,zan qaraso sai nayi dropping naki a gida idan an bani dama” bacin rai kan bacin rai,tadan cije lebanta tana jin sha’awar sakeyin wani kukan bayan wanda tayi,ita afifa zata yiwa haka?,haka sukayi da ita?,salon kawai ta zubda mata qima da mutunci zata kira wani mahmud wai yayi dropping nata

“Karka damu,ina hanyar gida,thanks” tayi maganar a gajarce,saboda batason tayi tsaho har bacin rai da fushin da bashi ya haddasashi ba ya shafeshi.

           Yau gaba daya sai takejin kamar ba ranar saarta bane,ranta a mugun jagule ta iso farfajiyar company din,kiran mechanic din ya shigo a dai dai,yace mata yana bakin gate din farko,sai tace ya qaraso ciki,ya sameta parking lot na company din.

            Tun daga nesa ta fahimci motocinsa da motarta ne kawai ya rage a gurin, zuciyarta na sake motsa mata da bacin ransa tana danneta har ta qarasa gurin. Ta matsa kusa da motarta tana amsa kiran wayar musa mechanic,ta gama ta jefa wayar a jakarta tana qunquni. Gaba daya guards dinsa sunyi carko carko a gurin kamar zasuci babu,kowannesu cikin shigar baqar suit ya qame,suna jiransa sanda yake tsaye yana sallama da baqin da ya gama ganawa dasu cikin garden din company din.

             A gaggauce ta yiwa musa bayani,don ta matsu taga ta fice daga companyn

“Idan ka gama ka kaimin ita gida,saika fadamin kudin gyaran”

“To idan ba damuwa,bari na fita na taro miki abun hawa mana” ya fada cikin girmamawa

“Meye ya samu abun hawan diyar tawa?” Dattijuwar muryarsa ta bayyana a gurin. Waiwayawa sãahar din tayi tana dubansa sanda ya tsaya daura dasu,masu tsaron lafiyarsa na tsaye daga bayansa,hannunsa dauke da mini laptop,yana dubanta cikin kulawa.

           Har abada yana da wata kima da martaba a gurinta, saboda dattakonsa da kuma girmama dan adam da yake dashi,cikin mutuntawa irin ta uba da d’ansa tace

“Yadan baci ne abba,amma yanzun in sha Allah nasan zai gyara”

“Subhanallah,ashshsha,to yayi,ammm…..amma ame zaki koma gida?”

“Zan qarasa titi,zan samu abun hawa” kai ya girgiza,sannan ya yafito daya daga cikin guards dinsa ya masa magana qasa qasa,ya zabura da hanzari don cika umarnin ogansa yayi gaba.

             Rusunawa yayi daga bayan toufeeq daketa amsa waya,ba tare daya katse wayar ba ya waiwayo yana dubansa,tsaf har ya gama gaya masa saqon BOSS

“Okay” ya fada yana sauke wayar,ya taka a hankali don amsa kiran mahaifin nasa,masu tsaron lafiyarsa suka motsa da zummar binsa,ya tsaidasu ta hanyar umarni da hannu.

           Yana takawa zuwa inda suke tsayen ita da Dr ahmad jarma,idanunsa zube fes a kanta,can qasan ransa yana mamakin dalilin tsauwarsu haka shi da ita,dr din kuma na magana da ita cikin kulawa,tamkar yadda zaiyi magana da shi ko NADEEYA.

“Abba….akwai wani damuwa?” Toufeeq din ya fada a girmame yana duban fuskar mahaifinsa. Waiwayawa yayi ya dubi sãahar,wadda a sannan takejin kamar ta rufe ido ta bude ta ganta a gida,ta samu nasarar tsere musu sannan ya mayar da dubansa gareshi

“Ta yaya matsalar mota zata samu president dinka sannan ka tayar da dukka motocinka ku tafi ba tare da an kula da buqatarta ba?” Hannunsa ya murza kamar kadan,yana jifanta da wani irin bahagon kallo,dr din bai jira amsarsa ba yace

“Ka dauketa ku sauketa a gida,ka tabbatar kun ajeta har cikin gida kamar yadda muka karbo amanarta”

“In sha Allah ” ya fada da lallausar muryarsa dake cike da bacin rai,shi yarinyar zata yankema schedules kawai saboda buqatar qashin kanta?.

              Dai dai lokacin sajjad ya qaraso gurin,akwai banbancin halaye masu yawa tsakaninsa da toufeeq,don shi din cikin sakin fuska yake tambayarta akwai matsala ne tayi late na komawa gida?.

“Dole haka wataran dama ta faru,tunda kunyi sakacin kula da buqatun ma’aikata,maza a sanyata a mota a kaita gida, motarta ce ta samu matsala”

“Yanzun nan abba” sajjad din ya fada gami da ce mata bismillah bayan yayi gaba,tabi bayansa. Tun isowar sajjad taoufeeq din ya wuce mota ya zauna abinsa,yasan tunda har ya iso wajen,abinda abban ma baice ayi ba sajjad din zai sake ruruta abun,ya fuskanci yana wani mugun bata girma na musamman,abinda ya kasa ganewa mene shi?.

            Kansa tsaye ya bude motar da toufeeq din kadai take dauka,saikumma shi idan tafiya ta hadosu tare

“Bismillah ko?” Ya sake fada cikin girmamawa fuskarsa a sake.a nutse ta fara sanya qugunta a motar,sannan ta dauke qafafunta a hankali saboda ciwon da ‘yan yatsunta sukeyi mata. Tun bata waiwaya gefanta ba,qamshin turarensa shine abu na farko daya sanar mata da wanzuwarsa a gurin,sanann dukka jikinta ma ya bata. Ya hakimce a owners corner yana danna wayarsa hankali kwance,tamkar baiga shigowarta ba,amma can qasan ransa yana tsara yadda zai cimma sajjad ne,don ya qona masa rai matuqa. Muryar dr ta sake wanzuwa a gurin,ya tako da kansa ya qaraso bakin motar

“Akwai ciwo a qafarta fa …..taoufeeq,ka sauketa asibiti a dubata da kyau kafin ku wuce gida,kai kuma sajjad muje ka tayani ganin baqin can,Allah ya sawwaqe,ki miqamin gaisuwa gurin girema”

“Zaiji” ta fada softly,tana mamakin shin yasan abbanta ne dama?.

Page 27

         Shuru motar ta dauka,sai sanyin ac da qamshin turarensa daya cika motar,ko sau daya bai motsa ba,sai aikin danna wayarsa da yakeyi,har zuwa sanda motar ta motsa tana fita daga cikin company din,cikin wani irin yanayi da ba lallai ka fahimci ma tafiya motar takeyi ba,iya wannan kadai ya isa shaida maka zunzurutun kudin da aka narka kafin a siya motar.

          Wani qaramin sassanyan ringin wayarsa tayi,ya dauke manyan idanunsa daga wayar hannun nasa ya maida ga qaramar wayar dake gefansa,sai ya ajiiye dayar ya daga wancan kiran bayan ya sanya earpiece a kunnensa.

             Tuni ta lumshe idanunta ta hade jikinta tsam a waje daya,duk da tazarar dake tsakaninsu,amma sai takejin kamar idan tayi qwaqwaqwaran motsi jikinta zai taba nasa,kamammiyar muryarsa me wani iri amo dake da taushi da dadin sauraro ce ke fita cikin nutsuwa,har kamar baka tantance abinda yake fada cikin wayar.

          Bai jima sosai ba ya ajiiye kiran,ba dadewa wani kiran ya sake shigowa,tadan gyara zamanta tana sake jin yadda ta takura a zamanta tare dashi cikin motar,tana son taja tsaki amma karon farko zuciyarta ta tuna mata abinda ya faru da ita dazun sanadin hakan,duk da haka bata haqura ba,cikin zuciyarta tayita mita gami da tura baki gaba,kamar ta bude idonta ta ganta a gida.

             Ringing wayarta ta fara yi,sai a sannan ta bude idanunta,ta zaro wayar daga jaka,afifa ce ke kiranta,wani haushin afifan ya kamata,kamar itace tayi mata laifin,sai tayi rejecting ta dora wayar saman cinyarta.

          Sake kira tayi,amma harta katse bata daga ba,a karo na uku yayi magana cikin izza

“whether you answer your phone call or turn it off, I don’t want noise” yayi maganar kamar ba da ita yake ba,don bai kalli inda take zaune ba. Tanason ce masa ya sauketa kawai,amma tana tuna idan ta aikata hakan kamar bata girmama tsohon daya tako da qafafunsa don kawai a bata kulawa ba,sai ta zabi kawai ta shareshi,tayi kamar bata jishi ba.

          Ci gaba da kira afifan tayi,mahmud yana tayata,a qalla sai da suka kira sau bibbiyu,ba zato ba tsammani taji ya saka hannu ya suri wayar dake ajjiye saman jakarta data dora kan cinyoyinta,yayi switching nata off,ya jefota saman wani dan abu me kama da akwati dake a tsakaninsu.

“Wannan shine karo na qarshe da zan gaya miki dole ki dinga yimin biyayya,you must remember that i am your boss”

“And then what?!,zamowana ma’aikaciyarku bawai yana nufin zamana baiwarku bane!”

“What’s the difference?,kina aiki ne domin kudi,kina kuma aiki domin a biyaki” murmushin takaici ne ya qwace mata

“You are too proud mr jarma,sannan fahimtarka bata baka dai dai ba,am not one of the women who can lose their dignity saboda kudi ko qyale qyalen duniya,drop me please” ta fadi wani abu na zabalbala daga cikin zuciyarta,tsanarsa na ninkuwa a ranta,tana jin a duniya bayan adam,shine namijin da tafi tsana a rayuwarta”

“you can say whatever you want,but…..babu abinda zai canzaku daga yadda kuke…..and bazan saukeki ba,don baki isa bani umarni ba,amma doing it for the sake of  Dr jarma,umarninsa ne” tamkar ya watsa mata wuta a fuskarta haka taji, hawaye suka cika idanunta fal,to amma batason ya gansu har ya fuskanci rauninta,don ta rantse ta daina gwadawa kowanne d’a namiji rauninta,bare ya samu hanyar takata tare da illata rayuwarta.

          Titi ta zubawa ido tana jin kamar ta balle murfin motar ta fice abinta,to amma kwata kwata komai na motar ba irin wanda ta saba gani bane,tilas taci gaba da rintse idanunta,don bata qaunar ganin koda shatin inuwarsa,idan kuma tace zata ci gaba da bashi amsa,may be ta amsa masa da maganar da zata zunda kimar yaa muhyi a idanunsu,dama familyn Dr mamman girema gaba daya.

            Tana daga cikin motar amma tana iya hangen tsaruwar asibitin da suka shiga,umarni yayi a duba masa likitan da yake on duty,cikin gaggawa da son cika umarni suka fita,yadda baice mata ci kanki ba,haka bata motsa ba,har zuwa sanda suka dawo suka shaida masa

“Dr raheema ce” kai kawai ya gyada musu,ya musu wani sign da batasan na meye ba,sai taga daha driver har security din nasa sun fita daga motar.

           Hannu ya sanya ya dauki suit jacket dinsa ya zura,ya daidaita zamanta a jikinsa,ya danna Lock password na qofofin,suka bada ‘yar qara alamun sun bude,ya tura ya zura qafarsa sanann yayi magana a qasaice

“Follow me”

“Allah ya kiyaye na jera da kai” maganar dake qasan zuciyarta kenan,tsananin yadda ya bata mata rai ya kuma cikata maganar ta fito ba tare data shirya ba.

         Cak ya dakata daga nufin fitar da yakeyi,ya maido qafafunsa ciki,ya kuma sake maida lock din ya rufe,maida jikinsa yayi makarin kujerar yana furzar da iska me zafi daga bakinsa,for the first time da wata mace tayi disgracing dinsa,why?,me yasa yarinyar taketa karya masa record?,who is she?,ya qare da tambayar da bashi da amsarta. Banda darajar Dr jarma,banda shi din ubane a gareshi da bai taba saba umarninsa ba,yarinyar sam bata isa ya hada koda hanyar wucewa da ita ba,bare ta samu daman maida masa magana.

         Bluetooth din kunnensa yadan taba da dan yatsansa manuni,sannan yace

“Tell dr raheema to meet me in the car,ina tare da patient” abinda ya fada kenan a taqaice,ya bude tafukan hannayensa yana kalla hadi da murzasu guri daya. Me zaiyi mata wanda zaiyi matuqar bata mata rai?,ya kuma kashe wannan bakin me kama da gidan tsutsa na rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da ita?.

          Knocking glass din akayi,hakan ya tabbatar masa da isowar dr raheema din,qasa yadan sauke glass din,muryarta me cike da fara’a da matuqar kirki tace

“You are welcome sir,kaine yau da kanka?” Ta qarasa maganar tana sauke dubanta akan kyakkyawar balarabiyar fuskar sãahar dake cike da fushi.

“Yes,please come in” ya fada yana dage glass din window sama ya rufesu ruf kaman dazun.

         Daya daga cikin guard dinne ya shigo,ya juyo ma dr raheema da kujerar gaban sãahar,ta zamana tana facing dinta,ya qara mata fadi da zurfi yadda dr zataji dadin zama.

“Gud evening madam” dr raheema ta fada da fuskarta da bata rabo da murmushi. Idanu sãahar ta daga ta kalleta,saita gaza tankwabar da gaisuwar tata,ta maida mata a taqaice

“good evening dr” abinka da likita,nan da nan ta fahimci ba meson dogon magana bane,don haka ta maida dubanta ga jarma

“Sir,i hope ba wani babban abu bane ya faru ba,naji kace na taho da kayan aikina” gyara zamansa yayi bayan ya cire suit jacket din nasa

“Yes,yau car service zakiyi,ga patient din nan,ta gaya miki damuwarta” daga haka ya maida hankalinsa ga dan qaramin computer din dake maqale da seat din yana ci gaba da duba aikinsa na dazu daya katse.

“Sannu madam,meye damuwar?” Ta sake tambayarta da dakakkiyar fuska. Qafarta ta daga mata,dr raheema ta kalli qafan,sai ta kalleta cikin sauri,abinka da farar fata,fatar wajen tayi jajur

“Sir,me ya samu qafarta hakanan”

“Ask her” ya amsa mata carelessness. Wannan karon batasan sanda ta jefa masa wata muguwar harara ba,tana jin tabbas inda tana da dama sai tayi masa mugun duka. Dr raheema data gani sai murmushi ya qwace mata,abun ya burgeta sosai,har ta kasa yin shuru

“Baka kyauta ba sir……you must show your care and concern,kasan mu mata bamason rashin nuna kulawa”

“Do your job dr…..am in hurry please,banason jira”

“Okay sir”ta fada cikin girmamawa tana ajjiye maganar a gefe.

         Saida tayi mata allurar anti tetanus saboda batasan dame taji ciwon ba,sannan ta bata pain killers,tace kuma zata iya gasa gurin da lukewarm water,sannan ta hada kayan aikin nata ta fito. Tana fita suka dawo,dukka motocin suka dauki saiti suka sake fita a asibitin.

        Ko sau daya bai tambayeta address dinsu ba,tadaiji yana magana a waya,amma zugin da qafarta keyi bai barta taji abinda yake fada bama,daga bisani taji yana basu umarnin yin amfani da map dake jikin motar. Sanda motar ta tsaya data bude idonta sai gata qofar gidansu,ta boye mamakinta ta dauki jakarta cikin kamewa da takatsantsan da qafafunta ta fice daga motar,tana jin kamar an zareta daga cikin tarin qayoyi.

           Afifa dake tsaye jikin motar mahmud ta nufota da hanzari,wanda sam bata lura dasu ba,saboda Allah Allah take ta isa gida ta sake rage kukan dake cin zuciyarta karo na biyu. Gwanar kuka ce sosai,duk wanda ya santa ya santa da wannan dabi’ar,kuka baya mata wuya

“Bestie,lafiya?” Afifa ta fada tana qoqarin riqeta,hannu ta daga mata

“Ki barni don Allah,koma meye ke kika jawomin”

“Da nayi me?, Ta tambayeta cikin mamakin bacin ran data gani a fuskarta

“Mahmud yaje har kamfanin akace boss yasa a kawoki,sai musa ya samu yana gyaran motarki,tare muke dashi tun dazun a nan muna jiran isowarki,ganin kinyi delay yasa muka fara kiranki,kuma daga qarshe wayar a kashe, hankalinmu ya tashi” dai dai sanda takai qarshen maganar mahmud shima ya iso,dukka jikinsa a sanyaye,bayan ya gama kallon motocin da suka sauke sãahar din yanzu,wadanda suke dauke da number MT JARMA tun daga 01 har zuwa 05

“I hope she’s fine” ya tambayi afifa,don tuni ita ta soma shigewa gidan ma

“I don’t think so,naga yanayinta kamar akwai damuwa” idanunsa ya sake mayarwa kan shacin tayoyin motocin,kamar a nan zaiga amsar tambaya da kokwanton da suka cika masa zuciya,tun daga dannowar motocin street din nasu,har zuwa fitarsu

“Don’t bother,zan shiga naji me ya faru,koma meye i will let you know”

“Thank you afifa” ya fada yana zube hannayensa a aljihun rigarsa. Yana yabawa gudunmawar da take bashi wajen samun soyayyar sãahar din

“No worries” ta bashi amsa tana gaggawar cimma sãahar din,sauqin abunma daya,anty farheen na ciki,koma meye tasan zata tari matsalar,tunda tasan halin ‘yan kayanta sosai.

            Da sallama ta shiga parlor din,ba kowa sai maama dake gyarawa aleena socks dinta,khalipha kuma ya gaggwafe a qasa yanata qoqarin hada wani maths puzzles,tun dazun ya fara,har yanzun kuma bai hadasu dai dai ba

“Maama,sãahar fa?” Dan tabe baki kadan tayi

“Suna ciki ita da uwarta” juya akalarta tayi zuwa dakin,tana cewa khalipha dake kiran tazo ta duba masa ya kasa hadawa

“Drop it aside son,i will be back”.

        A hankali ta tura qofar dakin nasu,daidai lokacin da sãahar din ke zaune gefan gadonsu,ta zuba hannayenta saman fuskarta tana sheshsheqar kuka,anty farheen na zaune saman stool tana fuskantarta,tana tallafe da bayan hannunta tana dubanta kawai ba tare data hanata kukanta ba. Tun daga sanda adam yayi breaking heart dinta,yayi breaking dukka wani trust nata akan kowa,saita zama me raunin zuciya,wanda a times kuka ne kawai yake sanyawa ta samu tayi controlling anger dinta. Ko yanzun ma ta fara gaya mata amma ta kasa ci gaba ta fashe da kuka,farheen tasan crying is the one way to calm her self,wannan ya sanya batayi qoqarin hanata ba.

           Taji motsin shigowar afifa,saita bude fuskarta wadda harta hada jaaa

“Me kika shigo kiyimin?”

“Afifa fita please” anty farheen ta fada. Harara afifan ta watsawa sãahar

“Ba inda zani,inkinso ki hadiye zuciya,duk wanna fushin nasan kawai don kinganni da mahmud ne,to zama daram a dakin nan” tasan halin afifa da kafiya wani lokacin,batason suyi ja’inja da ita alhalin tana cikin irin wannan bacin ran,afifa means alort to her,ba zata taba iya bata mata rai ba,wata sashe ce ta rayuwarta,don haka ta wuce toilet,ta qarasa matse hawayenta ta dauro alwala. Tun kafin ma ta gama alwalar taji sanyi yana sauka a zuciyarta,ita kanta wannan tsananin fushin bata sonshi,to amma yata iya?,wata qaqqarfar qaddara ta keto tsakiyar rayuwarta ta sauya mata abubuwa da dama.

             Ta sake yarda afifa da anty farheen din wasu mutane ne na musamman Allah ya ajiye mata,duk cikinsu babu wadda ta tashi,idan ta lura kamar damuwa ce saman fuskar kowannensu,duk da afifa ta maze tanata danne danne a wayarta,kamar komai bai sha mata kai ba. Wannan caring din data gani tattare dasu yasa ta kasa sauya kayan jikinta da tayi niyya,ta koma inda ta tashi dazu ta zauna,anty farheen na ankare da qafarta da tayi jazur

“Daga yau na ajjiye aiki da companyn MT JARMA,don Allah anty ki tayani fahimtar da yaa muhyi” ta fada a raunane,tana jin dacin abubuwan da yayi mata a yau.

        Furucinta dukkansu yaja hankalinsu,har afifa tabar danna wayar da takeyi,ta miqe ta zauna sosai tana kallon sãahar din.

Page 28

         Dif dakin yayi na wasu mintuna,kafin anty farheen ta tattara hankalinta sannan tace

“Me ya faru daya kawo wannan ajjiye aikin rana tsaka haka?” Qwalla idanunta suka kawo,tayi qoqarin maidasu ta kuma kawo dakiya ta azawa ranta,sannan ta fara basu labari daki daki,daga qarshe ta qarqare da fadin

“I can’t take it anymore anty,how can he humiliate me like that?yana tunanin ina da interest ne akan dukiyarsu?,ya dauka ni na kawo kaina nayi begging a bani aiki,kamar yadda sauran wulaqantattun matan dake mutuwar masa soyayya sukayi aka basu gurbin aiki yanzu haka a company din ba,baisan tilastani yaa muhyi yayi ba shima don kawai yayi alfarma wa mahaifinsa?” Shuruu anty farheen tayi tana jinjina kai,sosai taga zallar bacin rai saman fuskarta,afifa zatayi magana tayi saurin dakatar da ido,sannan ta fara magana

“Gaskiya bai kyauta ba,baisan mace ‘yar tarairaya bace?,so amma duk da haka,ina roqar masa afuwa ummin abba,sannan on my own view akwai dalilin da yasa yake behaving haka…..but kafin sannan,dole na gaya miki gaskiya ummin abba,kema kina da naki laifin”

“Yes” afifa data kasa jure rashin saka bakinta ta fada,har sai da sãahar ta waiwaya ta dalla mata harara da fararen idanunta dake da raguwar danshin hawaye. Juyawa farheen tayi

“Afifa,i beg you…” Yatsunta tasa ta kame bakinta,sanann ta koma ta kwanta,saidai duk da haka kunnuwanta da hankalinta yana kansu din tana ci gaba da sauraron abinda anty farheen din taci gaba da gaya matan.

              Mai da kai farheen tayi ga sãahar tana dubanta cikin kulawa

“Don ba dai dai ba anyi miki,ya bata miki rai na yarda,kuma ya miki laifi,tunda har abun yakai ga taba lafiyarki……to amma abinda nakeson ki sani,shi babba duk inda yake babbane,koda babban nan ba musulmi bane Christian ne,abu na biyu ko babu komai ai ya girme miki ya kuma baki shekaru sãahar,ina cewa ma zaid ya miki magana akan kiyi haquri kiyi aikinki?,ki kuma bashi girma ko don daddyn aleena?,sannan karki mata,namiji ako yaushe sarki ne,ke macace dole ko yaushe a qasansu kike…..”

“Ni ba a qasan wanan nake ba anty,ni a qasan abba dasu ya muhyi kawai nake a yanzun,amma babu wani namiji a samana” ta fada da sauri,da alama an tabo mata bangaren da tafi adawa dashi. Karamun murmushi ta saki

“To shikenan,amma dai kamata yayi ace,tunda kinsan halinsa kici maganin zama dashi ,magana ta Allah kuma babu namijin da yasan abinda yakeyi wanda zai yarda da wannan,kina qasa da shekarunsa,sannan kina qasa dashi a aiki sannan kuma ya dauki rani?,bazai yiwu ba,kiyi tunani da kyau,a yanzun kina cikin fushi,yanke hukunci ba naki bane” taji duka maganganun farheen,amma batajin akwai wata sauran shawara data rage,gaba daya ta gama tsanarsa da dukkan wani abu da ya shafeshi,ajjiye aikin shine kawai maslaha a wajenta saboda muddin zasu ci gaba da haduwa,zaici gaba da yi mata haka,ita kuwa ba zata taba jura ba,saita maida masa dai dai da abinda yayi matan.

***********Tun washegarin ranar da abun ya faru bata sake batu ko yunqurin zuwa aiki ba,sunyi waya da miss sameera,tana tambayar lafiyarta jin shuru bata shigo ba,tace mata bata jin dadi ne. Cikin alhini tayi mata sannu,tare da shaida mata zata shigar da report

“Da kin barsu ma sameera,basai kinyi reporting ba”. A kan hakan suka rabu,amma duk da haka bata fasa yin report din ba,duk sai taji ba dadi rashin zuwan sãahar din,kirkinta yana da yawa,tana kyautata mu’amala sosai a tsakaninsu.

             Tun daga ranar har zuwa satin gaba gaba daya tayi qaura daga zuwa aiki,duk da cewa zuwa lokacin ma qafar ta warke sumul,koda maama ta tambayeta dalili ce mata kawai tayi hutu ta dauka,sai bata sake yi mata zancan ba.

**********Karfe hudu na yammacin ranar litinin ne,wanda ya kama shigarta sati na biyu rabonta da MT JARMA GROUP OF COMPANY. Tana zaune cikin farfajiyar gidan,guri na musamman da aka kebe saboda hutawa. IG ta shiga tana duba hotunan styles na dinkuna da takeso takai,tayi scrolling down kenan hotonsa ya mamaye fuskar laptop din nata. Faduwa gabanta yayi,cikin sauri ta furta

“A’uzubillahi minash shaidanir rajim” ta sake maimaitawa kusan sau uku,kafin daga bisani ta bude idanun nata a hankali tana jan tsaki,ji take kamar ta fasa computer din gaba daya,sam bata qaunar ganinsa har can cikin zuciyarta,ko yanzun data aje aikin ta daina zuwa ji takeyi kamar tayi nesa da wani baqin maciji. Tana shirin sauka daga IG din gaba daya idanunta ya fada kan sunan me account din MEENAL YA’AQOUB AJI(AJI).

“Banzaye marasa kishin kansu” ta furta tana qoqarin karanta rubutun dake qasan hoton nasa. Kamar dai wancan karon,itace wadda ta wlafa hoton nasa tare da kalmomi na yabo tare da nuna zallar madarar soyayya da qauna a gareshi,sauran ‘yammatan da suka zube comment sama da dubu uku suna sake yaba kyanshi haiba da kamalarsa,tare da sake kodashi. Baki sãahar ta tabe

“Ko meye abunso a nan?,a green snake under green grass kenan”

“To tunda bakison kalla ki sauka mana,naga kema kallon nasa kikeyi” muryar afifa taji daga bayanta. Wani irin fatali tayi da system din kafin takai ga waiwayowa ga afifa wadda ta rugo tana fadin

“Subhanallahi” ta daga system din tana fatan batayi komai ba,saboda tasan nawa ta sanya ta siyeta,system ce me tsada ta kamfanin apple,kuma ko shekara batayi ba sukayi order dinta ita da afifan.

           Sai data tabbatar ba abinda ya sametan sannan ta fita ta kashe mata ita gaba daya,kafin ta maida hankalinta akan sãahar din.

            Manyan idanunta ta kafeta dasu,bacin ranta yana bayyana sosai saman fuskarta,suna hada ido tadan kauda idon don ta samu damar gayawa afifan abinda yake ranta

“Bestie….”

“Me yasa kika tsaneshi har haka sãahar?” Afifan fa katsi numfashin sãahar din daga abinda tayi niyyar gaya mata,ba tare da ta barta ta bata amsa ba ta sake cewa

“Ina jiye miki tsoron hadisin ma’aiki yayi aiki a kanki fa?,yace kada ku zurfafa soyayya don tana iya juyewa qiyayya,kamar dai tsakaninki da adam,sannan kuma yace kada ku zurafaf qiyayya saboda watarana zata iya juyewa zuwa soyayya”.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,bestie bansan bakya qaunata ba sai yau” sãahar ta fada da muryarta data canza saboda tsananin bacin rai,duk duniya afifa dince kawai take zata iya gaya mata hakan ta qyaleta. Kowanne yana shirin sake magana qarara wayar sãahar dake kan cinyoyinta ta katseta,maida dubanta tayi ga wayar tana tsammanin mahmud ne,amma sai taga mutumin da bata taba zaton kiransa ba,Dr mahmud JARMA.

          Cikin matuqar mamaki da kuma girmamawa ta daga kiran hadi da yin sallama

“Waalaikumus salam diyata”

“Barka da yammaci abba”

“Barka kadai,kin yini lafiya?”

“Alhamdulillah abba”

“Ayimin afuwa,inata son na kirayeki naji ya qafar taki,sai kuma sabgogi suka riqeni,to amma shekaran jiya munyi waya da muhyiddeen,yace kin warke tun cikin wancan satin ma” cikin jin nauyin afuwar da yake bida a wajenta tace

“Na warke abba,alhamdulillah”

“To ma sha Allah,nayi zaton ciwon ne ya hanaki komawa aiki,ina fatan za’a daure a koma din”

“In sha Allah” ta samu kanta da furtawa saboda yadda yayi mata kwarjini take kuma jin nauyinsa,duk da cewa babu plan na komawarta aikin kwata kwata. Addu’a sosai yayi mata,cikin jin dadin irin girman da take bashi,qaunarta da kimarta data iyayenta suna sake qaruwa a ran Dr mahmud JARMA.

           A sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta tana tuhumar kanta dalilin da yasa ta amsawa dr jarma cewa zata koma bakin aiki?,me yasa bata gaya masa cewa tabar aiki ba?.

“Yanzun nan ya zaid ya shigo,nayi masa zancan ankon bikin fatima,yace cikin week din nan container dinsa da yayi order laces daga china zata iso,akwai wasu colors guda goma na musamman da su kadai ne a ciki,zai cire mana”

“Yayi,amma duk wani event da tasan akwai maza a ciki a cireni” ta fada tana gyara zamanta,can qasan ranta alqawarin komawa bakin aikin da tayi ba tare data shirya bane yake damunta.

              Sanye yake da yadin lallausan yadi da aka saqa da ainihin zaren guanaco me taushi da tsada,an shirya masa dinkin da yayi masifar dacewa da darajar yadin da martabarsa,ya kuma dace da jikin mamallakin yadin. Rufaffen takalmin qasar italy ne a qafarsa me asalin kyau da tsada,wanann kusan al’adarsa ne,komai nashi designer ne,komai nasa na musamman ne. Kansa babu hula,sai sassalkar sumarsa daketa qyalli,da wani irin gyara dake nuna tana samun kulawa,hakanan yana amfani da tsaftatattun tsadaddun mayukan gyaran gashi na maza. Zallar kyau da kwarjinin dake shimfide a fuskarsa dake da qarancin fara’a a bayyane yake muraran,kwarjinin da yake hanawa mata da yawa kallon fuskarsa kai tsaye.

          Shi da angel din nasa suke takowa zuwa inda motocinsa suke jiransa,akwai baqi da sukazo daga qasar tokyo da zasu karbesu shida daddyn nasa,wanda a yanzun haka suke bristol suna jiransu.

            Daga daya bangaren nasa kuma hajiya qarama ce,riqe da wata doguwar takarda

“Zaki bani aron lokacin daddyn naki muyi magana kuwa?” Hajiya qarama ta fada tana duban fadeela. Siririyar dariya yarinyar tayi tana dora kanta saman hannun daddyn nata da yake riqe da nata hannun,sai ya saka hannunsa ya dauketa cak ya a zata saman kafadarsa,wani miskilin murmushi na fita daga labbansa.

“Wannan sune list na mutane cikin dangi da za’a bawa zakkar wannan shekarar” hajiya qarama ta fada tana duban takardar. Kadan ya waiwaya ya kalleta,sannan yace

“Mu qarasa ki bawa jibril ko elyas”

“To yayi” ta fada tana ninke takardar.

           Dukkanin motocin an shiryasu kamar yadda aka saba,ya qare musu kallo a nutse sanann yace

“Da mota biyu kawai zamu fita yau”

“Me yasa?,baka tsoron lafiyarka?, idan baka qara guards ba ai ba zaka rage ba,yadda yanzun duniyar nan ba amana ba gaskiya” kai ya kada,shi dukka guards da yake fita dasu badon komai bane,don kawai ya samu sauqin tafiyar da aikinsa ne,bashi da wata alaqar gaba da kowa, hakanan dukiyarsa da guminsa ya tara,halas dinsa ce,so bayajin akwai wata barazana da zaiji tsoron fuskantarta

“Ba komai,fi amanillah” ya furta calmly,baki tadan kyabe kadan,yana da wani irin tauhidi da wani lokaci yakan bata tsoro,zata sake magana cook dinsa ya iso,yadan tsaya daga nesa nesa yana jiran izinin qarasowarsa,sai yasa hannu ya yafitoshi,wannan ya bashi damar qarasowar yana cire zungureriyar hular chief dake kansa

“Sir,you didn’t choose what you want to eat” yayi maganar yana miqawa jibril takardar dake dauke da jadawalin abincin wata guda.

“Bashi takardan mu wuce,i want something lite,banason abu me nauyi yau,coz zan dawo gida late” yayi maganar yana sauke fadeela. Dai dai sanda wayarsa ta dauki tsuwwa.

            Sunan Dr mahmud din da ya gani ya sanyashi daga wayar da hanzari

“Ka taho ne?”

“On my way dad”

“Good,ka tsaya ta gidan Dr Mamman girema,ka duba jikin president dinka,ya kamata ka dinga kyautata mu’amala da employee dinka toufeeq”

“Alright dad” ya amsa masa yana sauke wayar daga kunnensa. Zazzafar iska ya furzar daga bakinsa yana zube hannayensa cikin aljuhun wandonsa,me yasa dad zaiyi masa haka?,wannan umarnin da ya bashi dai dai yake da yace masa yabi jirgin sama ya kamo masa shi,wannan yarinyar maras kunya?,me dagawa da izza zai taka ya sake zuwa gidansu a karo na biyu da sunan dubata?,bayan wancan karon dad din ya sakashi kaita asibiti ya kuma kaita har gida ya sauketa?. Duk yadda yaso ya qirqiri wani uzuri da zai hanashi wannan zuwan amma abun ya faskara,sun riga sunyi magana da dad din yace masa ya gama komai yana hanyar zuwa,so babu wani excuse ya tabbatar da zai bashi ya karba.

Page 29

          Duqawa yayi yayi kissing goshin fadeelan,ita kuma tayi masa addu’a kamar kowanne lokaci

“A dawo lafiya abby,Allah ya tsareka ya bada sa’a” wannan addu’ar yana ji da ita,yakanji kamar ta fita ne daga bakin mahaifiyarsa sometimes

“Wannan yarinya akwai iyayi,ko iyayin waye kika kwaso haka oho” hajiya qarama dake kallonta tana qaramar dariya ta fada,shima yana jinsu,sun saba irin wanann wasan dake kama da wasan jika da kaka,do haka ko waiwayosu baiyi ba ya wuce ya shige motar da tuni jason ya bude masa. A ciki ya samu sajjad yana jiransa,ya kalli agogonsa sannan ya dubeshi

“Dr yace muje shagari quaters tukunna ko?,nasan zamu kashe kamar awa daya a can din” wani kallo ya watsawa sajjad din bayan ya zauna sosai cikin kujerar

“Awa dari zamuyi” fashewa da dariya sajjad yayi har yana duqawa,yadda yayi maganar ya tabbatar masa a wuya yake

“To ai shikenan,ba laifi,saina gayawa Dr kana buqatar awanni dari,ayi postponing meeting din zuwa wasu kwanakin a gaba”

“Will you keep quiet sajjad?” Ya fada a nutse yana lumshe idanunsa hadi da budesu

“Afwan” ya fada yana dariya,sannan ya maida kansa ga google da ya shiga,yana duba sabbin kayayyaki da sauran companies suka saki a satin,gudun kada suyo kaya iri daya,amma can qasan ransa cike fal yake da dariya da kuma annashuwar abinda Dr ya yiwa toufeeq din,bayan shekaru kusan biyar,yau dr ya karyawa toufeeq record,abinda yasan cewa duk duniya banda shi ba wanda ya isa ya masa hakan.

          Ko cikin motar shuru yayi kamar wanda ke tunani,bini bini ya duba agogon hannunsa,shi ko hanyar unguwar bayason bi bare ya isa ga gidan,ya danna wani madanni daga gefansa,wanda saqo zai kaiwa driver din dake gaba na buqatar ya qara speed na motar.

         Cikin mintuna qalilan suka isa qofar tafkeken gate din gidan, driver din yana shirin dannan hon don a basu damar shiga farfajiyar gidan toufeeq ya dakatar dashi

“Inaga ta fito kawai mu dubata,no need sai mun shiga har cikin gidan” waiwayowa sajjad yayi ya kalleshi

“What kind of dubiya is this?,ka taba jin ance wanda za’a duba shi zai fito?” Kafin yayi wani yunquri sajjad ya bawa driver din umarnin shiga ciki.

         Hon biyu kacal me tsoron qofar ya buda gate din yanason ganin su waye,Dr mamman dake zaune daura dasu yana duba jarida yace ya bude,kosu waye da alama sanannu ne. Wanann din dabi’arsa ce,lokaci bayan lokaci yakan zauna a bakin gate din da kansa tare da me gadin,ya girmi baaba habu,amma shi dinma dattijone kamar shi,zaman nasa a wajen lokaci lokaci yana yiwa baaba habu din dadi,akwai kyakkyawar mu’amala da fahimtar juna a tsakaninsu,sannan hakan yana sake baiwa dr girema damar fahimtar matsaloli da kusakurai da za’a iya gyarawa.

            Rufe news paper din yayi sanda motar ta gama tsayawa,toufeeq da sajjad suka fito,miqewa yayi sanda suke sajjad ya nufoshi toufeeq na biye dashi a baya.

“Barka da yamma” shi da sajjad din suka fada kusan lokaci guda

“Barka kadai yan samari daga ina?”

“Daga kamfanin MT JARMA muke,munzo duba jikin daya daga cikin ma’aikatan mu ne Khadija”

“Ma sha Allah,amma kai din yaron Dr ne?” Abba ya fada cikin sakin fuska yana duban sajjad, murmushi sajjad yayi ya juya yana dubam toufeeq

“Ga dansa nan” matsowa taoufeeq din yayi,abba ya miqa masa hannu sukayi musabaha,sannan ya waiwaya ga jamilu wanda ke aikace aikace a gidan

“Yi musu jan gora zuwa setting room,sai ka yiwa ita sãahar din magana”

“Muna kan hanya ne abba,ko zamu samu ganinta?” Toufeeq ya datsi hanzarinsa,kai ya jinjina

“Babu damuwa,rakasu ta can baya,naga wucewar ‘yar uwarta gurin,na tabbatar suna tare” godiya sajjad yayi sannan sukabi bayan wanda aka kira da jamilu.

           Sake zurfafa ganinta afifa dake zaune tana fuskantar sãahar tayi tare da son tantance abinda idanunta ke gane mata,a youngest handsome millionaire,a business tycoon Muhammad toufeeq jarma. Yana takowa majestically,takun da ya banbanta dana sauran maza,koda a yanzun yanayin tafiyarsa daban da tasu sajjad da kuma jamilu.

       Sãahar ta bada baya,ta tabbatar ba zata iya ganin meke faruwa a bayanta ba muddin ba ita ta tabota ba,so amma tana gudun reaction dinta,kada taje tayi misbehaving,don haka ta maze,taci gaba da kurbar mamakinta ita kadai,har zuwa sanda suka qaraso gurin.

         Sallamar jamilu ta saka sãahar waiwayawa,abinda ya bata damar ganin abinda ya sanqarar da tunaninta,lokaci guda idanunsu suka gauraya cikin na juna,a take kowa izzarsa ta motsa,haushin dan uwansa kuma ya sake motsa musu. Me wannan dan izzar yakeyi cikin gidansu?

“Alhaji ne yace a rakosu” jamilu ya fada cikin rusunawa,gamar fadar tashi kuma tayi dai dai da miqewar sãahar,ta fara dauke wayarta headphone da sauran tarkacen da tazo gurin dasu,don ba zata iya hada numfashi da mutumin nan ba,bare har magana ya shiga tsakaninsu. Tana gama debewa ba tare data waiwaya ba tayi gaba da zummar dauke system dinta a inda afifa ta ajjiye mata,ta duqa takai hannu,saidai kafin hannun nata yakai ga sauka a kai wani hannun ya dauketa ya aje gefe.

          A nutse ta dago da fusatattun idanunta,ta zubesu cikin nasa sanda yake tsaye a gabanta,hannunsa guda daya zube a aljihun wandonsa,shima ita yake kalla

“Nan fa ba MT JARMA COMPANY bane,bare kace zaka sakamin doka ko iyaka daga yin duk abinda nayi niyya” gyara tsaiwarsa yayi,yana jinjina qarfin halin yarinyar,da qwarewa wajen rashin kunya da tsiwa

“Koda ba MT COMPANY bane,amma anan din,cikin tsakiyar gidan naku ina iya ladabtar dake iya yadda naso……tunda qafafun naki sun warke,ina tunanin wani sabon tabon kike da buqata daga wajena…….Me kike a gida bayan kin warke?” Ya jefa mata tambayar cikin izza yana kafeta da ido. Mamaki ne ya cikata,tayi kasaqe tana kallon qarfin hali irin nasa,ya tsareta da tuhuma kamar wani ubanta. Zare idanunsa yayi daga kallonta,ya duba agogon hannunsa minti goma sha biyar kacal yayi niyyar qonawa a dubiyar da Dr ya tirsasa masa yayita,kuma ta cika,dago idonsa yayi ya sanya hannunsa a aljihun rigarsa,ya fiddo wayarta data bari a mota ya cilla mata

“Ki tabbatar kin dawo aiki ranar Monday,ko kuma ki rasa aikinki” abinda ya fada kenan,ya zagayeta ya wuce.

          Da kallo ta bishi cikin tsananin bacin rai,ya isheta ya kaita maqura,ita ba yarinyarshi bace da zai dinga yi mata irin wannan izzar,tabbas a yau dai baici bulus ba,zata koma aiki amma kuma saita rama abinda yayi mata,tabbas zai biya da farashi me tsada.

           Ta qofar baya ta wuce ta bulla sassansu,a parlor ta samu afifa da maama a zaune,bata tsaya ba sai tayi wucewarta ciki,tana kuma shiga daki ta maida muqulli ta rufe qofar,ta zauna tana fidda zazzafan huci daga bakinta,tsanarsa na sake ratsa mata jininta.

           Sai da suka daidaita akan hanya sajjad ya dubeshi

“Da ka sanya muka bar gurin,ina fata ba wani abu mara kyau ka yiwa yarinyar mutane ba”

“Kanta na yanke zan siyar” ya amsa masa a taqaice

“A yadda kake da zafin rannan,idan ka fara yankan kai an mata sun shiga uku,kafin shekara ‘yammatan garinku sun qare inaga” maganar sajjad din taso bashi dariya,sai kawai yadan murmusa kadan da iya labbansa yana girgiza kai,sajjad din yana ci masa tuwo aka yadda yaga dama,amma ba komai,shi da shi kar tasan kar ne.

***********Cikin karsashi da tare da maido dukka azamarta gangar jikinta ta shiga company din ranar monday,abu na farko data fara yi shine hada dukkan documents da report data fara aiki a kansu,ta tattara dukkan wasi bayanai,harda hardcopie data aikawa office din ceo din bai saka hannu ba,ta zauna cikin kwanaki hudu ta tura zuwa email din Dr ahmad jarma,tace ya duba musu,idan komai yayi,suna buqatar sanya hannunsa zasu fara aiwatar da komai.

          A dare daya ya duba dukkan bayanan,bai samu gamawa ba sai kusan qarfe uku na dare. Sosai ya jinjinawa kaifin basira da qwaqwalwa irin na sãahar din,yayi saluting nata sosai,tunanukanta da yadda ta iya tsara abubuwa sai yake masa yanayi da tsari da ra’ayin toufeeq dinsa,tsarikan nata sunyi bala’in burgeshi,don haka baiyi jinkiri ba ya sanya mata hannu a gaba daya guraben da ake buqatar sahalewarsa,don aiwatar da ayyukan da kuma fidda kudade daga asusun kamfanin.

           Sanda documents din suka isketa murmushi ta saki,sai taji kanta sakayau,kamar Dr din ya share mata wani fage da zata aiwatar da dukka ayyukanta hankali kwance ba tare data bi ta office dinsa ba har ya samu damar da zai bata mata rai,taci alwashi!,kuma tana da yaqinin wannan itace hanya guda daya da zata qona masa rai.

             Sati na gaba ta fara gudanar da komai,aka fitar da kudade akayi hiring mutanen da zasu bada gudunmawar farfado da kamfanin,cikin sati guda ta sauya komai ta kuma fara gudanar da al’amuranta hankali kwance.

            Wata guda kacal company ya fara ci gaba,kawo yanzu kusa duk wanda ya kwana ya tashi cikin company din yasan da zamanta,ta maida kanta busy sosai ta yadda zatayi abinda ya dace,wanda zai faranta ran Dr,ya kuma daga kima da martabar yayanta, she’s very hard worker,wannan ya qarawa ma’aikatan qwazo da karsashin aiki,ta kuma samu soyayya sosai daga garesu hadi da martabawa,wannan ya fara sanya mata so da qaunar aikin cikin ranta kadan kadan ba tare data farga ba.

********Cikin satittikan da suka biyo baya gaba daya aiki takeyi tuquru cikin kamfanin,duk wani abu daya zama nauyinta ne akafadarta yake tayi qoqarin ganin ya tafi dai dai,gaba daya bata sake bi takan abinda ya danganci office din CEO ba,duk da tana sane da file dinta dake gurinsu,ta zuba idanu ne taga ko zata samu saqo daga gurinsu,yau ne ko gobe ne,shuru dai.

           Ba jimawa ta fara samun soyayya daga wajen employees sosai,duk wanda yaga yadda take tafi da aikinta yasan cewa tasan abinda takeyi,da yawa ta tafi da zukatansu,mafi yawansu sun fada a soyayyarta,saidai kwarjininta da yadda bata sakewa mutane fuska musamman maza ya sanya suke shakkar tunkararta. Ta kame kanta sosai,ta kuma sake shata layi ga duk wanda ta fuskanci dan rawar kaine. A hankali sai aikin nata ya fara shiga jikinta,ta fara jin qaunar aikin,saita samu kanta da daura damarar yin dukkan wani abu da zai kawoma kamfanin ci gaba,ko don albarkacin Dr mahmud da ya dauketa kamar diyar cikinsa,don cikin watanni biyun da tayi sai hudu yana kiranta,ya shaida mata yana samun bayanin yadda aketa samun ci gaba daga bakin sajjad. Ba wani sanin sajjad din tayi cancan ba,amma zata iya shaida fuskarsa da kuma nasa muqamin.

          Ta bangaren toufeeq aikinne yaso hadar masa,nasa company din da yake shirin kafawa daya baro ana processing budeshi abubuwa sunyi nisa,ana da buqatarsa,dole yayi wani irin busy sosai,yake kasa hankalinsa gida biyu yayi aikin MT JARMA GROUP OF COMPANY sannan yayi na MAHFAD FACTORY,kwata kwata baya samun kansa sai dare,nan ma lokutan baccin nasa bame yawa bane sosai,yana qoqarin yakicewa ya dawo gida ne kadai saboda fadeela bayason abinda zai sanya ta dinga jin kewa,ko ta nemi wani abun ta rasa bata samu ba.

Page 30

       *_RAI DANGIN GORO_*

        Yadda ayyuka suka dauki zafi cikin company din,da yadda hadin kai ke samuwa daga dukka ma’aikatan ya sanya cikin satin basu damar samar samar da wasu games don nishadi a kowanne department.

          Ranar Monday bata wuce awa daya da shigowa office ba,miss sameera ta shigo,fuskarta dauke da murmushi tace

“Kin samu gayyata daga CSO Chief security officer na MT JARMA COMPANY,yau zasu gabatar da nasu game din na hack day,during break hours”. Hannu ta miqa ta karba mini computer din da miss sameera ke duba saqonni irin wannan tana duba saqon da aka aiko din. Kai ta gyada kadan sannan tace

“Babu matsala,ki tunamin idan time yayi”

“In sha Allah”  ta fada tana dan russunawa cikin girmamawa,sannan ta juya ta fita. Fitar tata da yayi dai dai da shigowar kiran ahmad gana wayarta.

          Har ta dauke kai taci daga da aikinta kamar ba zata daga ba,sai kuma wata zuciyar ta nuna mata kamatuwar yin hakan,koda batason tayi wayar dashi a qalla ta bashi uzurin da zai sanya ta zamewa amsa wayar tasa,tun ranar da yazo gidansun har yau bata sake daga wayarshi ba bare ya sanya ran samun damar sake ziyartar.

           Lokacin data daga wayar a zaune yake,amma sai gashi ya miqe tsaye saboda farinciki,maganar gaskiya ya kira ne kawai,bawai don yana da wani tabbacin na zata daga ba, sassanyar muryarta ta saukar masa da kasala lokaci daya,ya koma ya zauna yana dafe wayar qamqam a kunnensa

“Am so sorry,na katse miki aiki ko?,nasan yanzu lokacin aiki ne” ya katsi hanzarinta tun kafin ma tace komai

“Ayimin afuwa,na kasa daina kiranki ne,amma ko iya haka Am really grateful “

“Why did you call me?” Ta tambayeshi kai tsaye

“I want hear you,i missed your sweet voice” ko kadan maganar tasa bata burgeta ba,saima bata mata rai da tayi,ko kadan bata jiran jin yabo daga bakin kowanne namiji a yanzu

“Okay,It’s working hours now,can you turn off the phone?”

“Can i call you later please?” Ya fadi cikin kwantar da murya,hakanan taji yau din ta kasa musa masa,sai kawai tace masa

“Allah ya kaimu” daga haka bata tsaya jiran jin amsarsa ba ta datse kiran. Tana ci gaba da aikin amma rabin hankalinta yana kan hanyar da zata bi ta yakice mahmud daga rayuwarta,ta fuskanci wani banzatar da lamuransa da takeyi sam baya damunsa,kamar ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,qara qaimi kawai abinsa yakeyi. Duk kuma yadda yakai ga sonta bata jin ko kusa ko alama zata iya aurensa,bama shi kadai ba,ta tattara al’amarin aure gaba daya ta rufe shafinsa,bata sani ba ko sai a qiyama.

              Sanda miss sameera ta shigo ta gaya mata lokaci yayi saita duba agogo,ta tsaya tayi sallar azahar,duk da cewa akwai sauran lokaci,farkon muhtarinta ne a sannan. Coffee tasha rabin cup,sannan ta gyara yafen mayafinta daya zauna sosai a kanta,ya dace kuma da doguwar rigar atamfar jikinta,wadda dinkin yabi jikinta kamar domin ita aka halicci atamfar da dinkin gaba daya,jikinta sai fidda sirrintaccen qamshin nan nata yakeyi,saika dauka yanzu yanzu ta gama fesa turarukan nata,kabbasa ce me dan karen qamshi data dade da bin jikinta,bayan body mist da sauran turaren kaya da take using dasu masu dan karen tsada da kyau,tana iya kashe ko nawa ne ta siya turare,ba kamar sauran tarkacen makeup ba da har yau saidai a siya mata,don ba wani damunta sukayi ba,gwara gwara powder ma.

         Tare suka taho da miss sameera,suna dan tattaunawa akan abinda ya shafi aikinsu. Dab da zasu gifta office dinsa idanunta ya sauka a kansu,can qasan ranta tayi qwafa gami da duke kanta,don ko ta qofar office din bason gifatawa takeyi ba bare wani abu ya kaita,har ya hadata mu’alama da mamallakinsa.

          Babban hall din company a nan ta taras da ma’aikata masu yawa,kowa yana saman kujerarun da aka warwatsa a gurin, gurin sama na musamman aka bata ta zauna tana maida hankalinta ga babban allon majigin dake iya nuna yadda kowanne abokin aiki ke qoqarin yin kutse a na’urar dan uwansa amma wancan yana tosheshi. Tun bata jima da zama ba wasan ya dauki hankalinta sosai,bama ita kadai ba,kusan duk wanda yake wajen abun ya matuqar qayatar dashi,mayun na’ura aka hada team dinsu guda kowa yana qoqarin baje fasaharsa.

              Sosai wasan ya dauki zafi,ya kuma dauki hankula,har haka ya sabbaba tashin ‘yar hayaniya a hall din saboda ana gab da gangara a wasan.

              Ba zato ba tsammani sai gashi ya bayyana a gurin,da yawa basu lura da shigowar sa ba,har sai daya fara zuwa tsakiyar hall din,sannan kowa ya fara shiga taitayinsa,cikin girmamawa kowa ya fara duqar da kansa yana miqa masa gaisuwa. Ko gaisuwar mutum daya bai amsa ba,yaci gaba da takowa ciki,cikin izza da qasaitarsa,hannayensa zube a aljihun suit dinsa,fuskarnan a dinke tsaf kamar ko yaushe,murtukewar kuma da bata taba hana bayyanuwar kyansa.

          Bai tsaya ba har ya isa ga kujerar da CSO yake tsaye a gabanta,yadan russuna cikin girmamawa

“You are welcome sir” ya fada a ladabce,yana mamakin yadda akayi yasan da game din,bayan basu tura takardar gayyata office dinsa ba. An rasa zaququrin da zai tura ne saboda zallar shakkarsa da sukeyi,dukkansu jikkinansu sun basu bazai dauki wannan da muhimmanci ba bare ya halarta.

         Idanunsa masu kaifi ya zube masa yana jifansa da kallon da ya sanyashi qas da kansa,cikin husky voice dinsa data qara wani zurfi da bacin rai a cikinta yace

“what nonsense are you doing here?” Kadan ya dago ya saci kallonsa,yadan sosa kansa sannan yace a ladabce

“Ba shirme bane sir,and It’s not a joke, it’s a game to strengthen the security team”

“Who gave you permission to do it?,a tsakiyar ranakun aiki saboda rashin sanin muhimmancin ayyukanku?”

“Sorry sir,munyi requesting wa office din president,da muka samu tabbacin zuwanta munyi tunanin wannan ya wadatar……”. Ambatar sunanta yasa ya gama fahimtar inda komai ya dosa,tunda ya shigo da safen yaci karo da sabbbin ma’aikatan da baisan da zamansu ba dama,yaga kuma aikace aikace masu yawa da shi yasan bai sanya hannu don a gabatar dasu ba,saboda yana da nashi plan din da yakeson ya kammala a qaddamar dasu duka a tare kuma lokaci daya.

              Waiwaya yayi yana duban sashen da take,tana zaune akan seat dinta,har zuwa yanzu bata tashi ba,hakanan bata motsa ba,tana ci gaba da latsa system din gabanta,duk da cewa an dakatar da komai amma ta shiga wani sashe daban,zakayi tsammanin batasan me yake faruwa cikin hall din ba.

         Kafeta yayi da idanu,ransa yana sake baci,wato she doesn’t care?,me yasa Dr zai saurin aminta da ita ne ma wai?,meye dalili?,baisan sharrin mata ba,they can do whatever don suga sun shiga jikinka,sun samu aminci da yardarka,sannan daga bisani su cutar da kai,bayan dogon lokacin da suka dauka tare da kai,bazai sake barin haka ta faru ba!,har abada!!.

           Matsawa yayi gaba kadan yana fuskantarta,cikin izza ya motsa bakinsa yana magana da ita da wani irin zafi

“Where did you get all this courage mr president?,me yasa kikeson ki dinga yin gaban kanki bayan baki cancanci hakan ba?” Cikin matuqar mamaki ta daga kai,kanta tsaye ta saka idanunta cikin nasa birkitattun idanuwan wadanda ke cike fal da memories masu zafi dake sake zafafa kansa

“What are you trying to say?” Ta tambayeshi itama kai tsaye

“Kin fahimci komai,dukka wadan nan abubuwan da kike gudanarwa me hakan yake nufi?,baqin fuskar ma’aikata da kika kwaso babu cikakken bincike tantancewa ko tattaunawa da wadanda suke da haqqi da abun,me hakan yake nufi?” Wani irin kallo ta jefa masa,zuwa lokacin tana jin takai geji,ta kuma gaji da sauraron maganganunsa masu kama da ya shirya ci mata mutunci,saita miqe tana fuskantarsa kai tsaye cikin rashin tsoro da kuma rashin shakka,saidai kafin tace komai muryar sajjad ta mamaye gurin.

           Tun sanda ya shiga office dinsa saima data tura masa information na cewa ana can ana game din,a nufinta na b’ata sãahar da kuma kawo rigima a tsakaninsu,tace masa ya fita zuwa hall din yaji hankalinsa bai kwanta ba da fitar tasa ba,saboda tun daren jiya yasan cikin mugun bacin rai yake,saboda kiransa da NADEEYA tayi ta gaya masa saqo daga AMEESHA,ita kanta nadeeyan tayi nadamar kiran,ta dauka komai yana zuwa ya wuce,ta zaci zuciyarsa ta sassauto ashe ba haka bane,ta tafka kuskuren daya dami zuicyarta,tun jiya kuma take kiransa amma har zuwa yanzun bai daga wayar ba,abinda yasa ko kamfanin da zafi zafinsa ya iso yau,sai Allah kuma ya kade azal bata sauka kan kowa ba har ya isa office dinsa,shi yasa yanzun da yaji ya fita sai yabi bayansa,don shi yasan da game din,ya jima ma zaune cikin hall din yana kallon yadda suke abun cikin gwaninta sa qayatarwa.

“everybody outside please!” Nan da nan employees din kawunansu ke a qasa cikin d’ari d’ari da rashin jin dadin maganganun da yake gayawa president din tasu suka fara qoqarin fita cikin gaggawa,kamar basu da buqatar dama gani da jin abinda yakeyi matan,banda wasu tsiraru cikin mata da basu so hakan ba,dama su din ta shige musu hanci da qudundune,tako ina ta sha gabansu,sun rasa yadda zasu fatota,ciki harda saima dake lafe a bakin qofa.

Page 31

       Da hanzari sajjad ya tari numfashinsa,don bayason yace komai kada al’amuran su qarasa jagulewa

“Please toufeeq Calm down,don’t make harsh words” bai ko waiwayo ba ko ya saurareshi ba ya tako zuwa gabanta,ya bada kusanci sosai a tsakaninsu irin wanda bai taba yi ba. Ranqwafawa yayi yayi mata rumfa saman kanta yana dubanta

“Nawa ne kasonki?!” Ya fada da wata irin kakkausar murya. A birkice take kallonsa,sosai maganarsa ta daketa,sai yanzu ta fahimci inda ya sanya gaba ma gaba daya,yana nufin wani ha’inci ta qulla ko ko meye?,kamar yasan me take tunani saiya sauqaqe mata ta hanyar sake bayyana mata abinda yake nufi

“Nace nawa ne share dinki?,tsakanin kawo ma’aikata da sauran ayyukan!,nawa kika tsara samu!,nawa kika samu!,ki gayamin zan ninka miki,amma ki fita daga rayuwarmu!” Duk da cewa bata shirya zubda hawayenta ba amma ta gagara riqesa,a take ya zarto daga idanunta ya sauka saman lallausan fuskarta da bata iya riqe komai ma ballantana ruwan hawaye saboda santsi da sulbinta,ta kafeshi sosai da ido kamar wadda ta warke daga ciwon makanta,cikin matsanancin fushi tace

“wanne irin mutum ne kai mara kirki?,mara iya mu’amala?,wanda baisan kima da martabar dan adam ba?,me yasa dukka zancanka kudi!,me yasa kake hangen kudi sune gaba da komai?,kana tunanin aiki daku na nufin in zama baiwa?,ko mara ‘yanci?,ko kuma aiki daku na nufin zan mallaki wata dukiya?saboda kun mallaki yanke talauci?,Mr Muhammad………idan baka sani ba yau ka sani,banyi aiki daku bisa radin kaina ko kuma don ina nema ba…..nayi aiki daku ne bisa dole da kuma takura neman alfarma da kuma ganin kimar yaaya na, karamcin mahaifinka kuma ya zama silar wanzuwata a nan gurin……baka da matsayin da zan nema sa hannunka akan ayyukan kamfanin nan,duk abinda kake tunanin na aikata…..yes na aikata din,na samu kaso me tsoka wanda hankali bazai dauka ba,na tara arziqin da yafi na mansa musaa dukka a jikinku,do your worst,I don’t care or fear……ba dai dukka taqamarka kora ga ma’aikaci ba?,zaka iske resigning letter dinku a wajen sameera,ka riqe tsiyarka ka bawa wanda kaga dama” ta qarasa fada kuka sosai yana qwace mata,sannan ta soma fita daga hall din da sassarfa kuka na sake qwace mata.

              Da sassarfa sajjad yabi bayanta shi da mr hamza,saidai cikin rashin sa’a ta rufe office din,a yanayin da take sun tabbatar ba zata sauraresu ba,sai suka barwa miss sameera dake tsaye saqon idan fa bude ko tazo fita don Allah kar ta barta,ta tsaidata ta sanar dasu.

             A office ya sameshi yana kai kawo,ya cika ya batse kamar zai fashe

“Burinka ya cika,hankalinka kuma ya kwanta” sajjad ya fadi shima cikin bacin rai

“Stop sajjad,don’t aggravate my anger,bakaji me ta fada bane?,I will surely punish her” ya qarasa fada yana dukan bayan kujera da hannunsa a zafafe. Kallonsa kawai sajjad yakeyi,yama rasa abun fada,wanne irin tashin hankali ne haka suka tashi dashi yau,sai kawai ya zaro wayarsa ya fara dialing number Dr.

             Tana kuka tana rubuta resigning letter din,bawai tana kuka kan barinta aiki bane, a’ah,tozartata da yayi a gaban mutanen da suke ganinta da kima da mutunci,maganganun daya gaya mata,wanda shine mutum na biyu a duniya daya taba gaya mata magana masu zafi irin haka. Ta kammala rubutawa kai tsaye ta turawa sameera,tace bayan ta tura musu a rubuce tayi printing as hard copy,ta riga ta yanke har abada ita da companyn,bama iya kamfanin kadai ba,duk wani aiki da yayi kamanceceniya da wanann ta barshi har abada.

          Da hanzari take tattara dukka wasu kaya da suke da alaqa da ita tana hadasu a wata jaka,ta taka zata cire wata calendar dinta kanta yayi mummunan sarawa,ta koma da baya babu shiri ta dafe kanta da hannayenta biyu tana kiran sunan Allah,idan batayi wasa ba alamu sun nuna ciwon kan da taketa gujewa motsawarsa a yau zai motsa din. Batason ciwon ya sameta a nan,don haka ta bude qofar,ta leqa ta kira sameera. Yanayin da taga uwargidan nata ya sanya hankalinta tashi,nuni tayi mata da iya kayan data samu cirewa ta miqa mata key tace ta saka mata a mota. Sameeran na fita ta miqe da qyar,ta yafa mayafinta ta zura takalminta ta taka a hankali tana ficewa daga office din,zuciyarta na karyewa,wani sashen na zuciyar tata tana ban kwana da dukka abinda ya shafi MT JARMA,bankwana na har abada.

_uhmmm,ko shin da gaske bankwanar ne?,ko kuma akwai sauran kallo?,masu karatu,ku gyara zama da kyau,akwai fa sauran kallo,zamu shiga gaba ta biyu na labarin,gaba me matuqar muhimmanci,muje zuwa_🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️🏃🏽‍♀️

Da kallon mamaki maama kin bita sanda ta shiga gidan

“Ke kuma me ya faru na ganki a gida a irin wannan lokacin?” Idanunta fal da hawaye da taketa qoqarin shanyewa tace

“Ba komai maama”

“Qarya kike ban yarda ba” ta fada tana tattara hankalinta a kanta tare da barin duk abinda takeyi. Hawaye ne ya zarto a fuskar sãahar din,tasa bayan hannunta ta share

“Na ajjiye aiki maama” fuska tadan baata kadan

“Dalili dame?” Kai kawai ta shiga girgizawa,bakinta ya kasa furta komai,tana jin daci da ciwon abinda yayi mata har saman harshenta,ga kanta da yake sara mata sosai kamar zai rabe gida biyu

“Jeki,Allah ya kyauta” maama ta fadi saboda yadda taga ta gaza furta komai,koma meye tasan zataji idan yayunta ko afifa sukazo.

          Komai ta zube a qasan daki ta isa gado ta kwanta rub da ciki tana fashewa da kukan da takeson saki tun dazun, idanunta a lumshe tana bitar maganganun daya yayyaba mata,tayi nadama da dana sanin sanin kamfanin ma gaba daya bare wasu mutane dake da alaqa dashi.

              Sai data shafe kusan awa daya sanann ta laluba magani tasha, tayi kuma sallar azahar don tasan zaiyi wuya batayi bacci ba,idan kuma tayin lokacin yana iya kubce mata. Kamar yadda ta zata din kuwa,lokaci kadan baccin yayi awan gaba da ita,saidai dukka cikin barcin ba komai sai mafarkai,wadanda dukka toufeeq ne a ciki da tarin cin mutunci da cin zarafinsa a gareta.

             Knocking din baaba rabi ne ya tayar da ita

“Hajiya tace ki fito hakanan kici abincin rana”

“To” ta amsa mata,ta sa hannu ta shafi fuskarta,tana tuna yadda ya zabga mata mari a mafarki,kwatan kwacin marin da ta taba ji ya zabgawa wata,kai ta girgiza ta miqe a hankali ta wuce bandaki. Alwala ta dauro,sannan ta dawo ta cire kayan jikinta. Wata sof cotton shirt ta saka me gajeran hannu royal blue,me adon furanni da gold colour,sai spaghetti skirt daya dace da rigar,tasa comb ta sake gyara gashinta daya hargitse saboda baccin da tayi,ta qara turare a jikinta ta dauki wayarta dake da tarin miscall ta kashe ba tare data tsaya duba kiran waye da waye ba,ta tabbatar dai harda kiran dan anace mahmud a ciki.

             A parlor ta samesu,maama da baaba rabi dake gyara freezer din parlor din

“Barka da fitowa farar d’iya” ta fada tana murmushi

“Barka baaba rabi,ya aikin?

“Alhamdulillah “

“Ma sha Allah ” ta fadi tana qarasawa kusa maama ta zauna,wadda har yanzun binta take da kallo

“Me za’a kawo miki?” Baaba rabi ta tambaya

“Barshi baaba,zan dan huta ne kadan sannan naci abincin,zan zuba da kaina” ta amsa mata tana daukar remote ta canza channel.

          Bayan wucewar baaba rabin kallonta maama tayi

“Kunyi waya da yayanki ne?” Saida gabanta yadan fadi,tasan yaaya muhyiddeen take magana a kai tabbas,batason ko sau daya ya roqeta ta koma aikin nan,don ba zata iya ba muddin wannan mutumin yana a cikin kamfanin

“Bamuyi ba,ko ya kira din inajin bacci nake a sannan” kai ta kada

“Me ya sanya kika ajjiye aiki sãahar?” Shuru ne ya biyo baya na ‘yan sakanni,tanata qoqarin hadiye bacin ranta sannan ta motsa bakinta

“Bazan iya ba maama,dansa bashi da kirki sam,baya ganin kima da girman kowa,duk wata mace dake aiki a kamfanin kallon baiwa yake mata,ko wata mara daraja da batasan martabar kanta ba”  shuru maama ta danyi sanann ta numfasa

“Amma dai kinsan qarfe daya baya amo ko?,kuma ko meye halin mutum sai k………” Qarar wayarta ya katse mata maganar,sai t maida hankalinta a kai ta daga wayar ta sanyata a free.

          Dr mamman girema ne,wanda kafin su gama wayar sun sanya sãahar din cikin tunani,tabbas inda dukka maza irin mahaifinta ne,su kuma mata duka zasu kasance kamar mahaifiyarta ba ko tantama da ba’a samu mutuwar aure ba,koda an samu din ma saboda sabanin da baya wucewa tsakanin bayi,to zaiyi matuqar qaranci.

             Tuwon alkama yace yanaso miyar danyar kubewa,batason ta zauna tayita zaman tuna mutumin da a wajenta bashi da wani amfani sam,banza ma ta fishi,don haka sai ta wuce ta debi abincinta taci,tana kammalawa ta shiga kitchen da kanta ta dorawa abban nata tuwon.

           Tunda akayi sallar magariba taji yaa muhyi din tare da abba suka shigo gidan ta qule a daki taqi yarda ta fito,saidai ana gama sallar isha’i saiga maama da kanta

“Ki dauki abincin can ki kaiwa abbanku,zan shiga wanka” hakanan ta miqe jiki a sabule,ta fidda hijabinta ta maida gurbinsa da dan qarami ta fito ta debi kayan abincin ta wuce sassan Dr mamman.

           A ladabce ta zauna ta gaidasu dukkansu,don yau kafin ta fita basu hadu da abban ba,ta zauna sosai ta fara serving nasu duka su biyun da suketa tattaunawa akan harkokin da suka shafi kasuwancin da suke na hadin gwiwa a tsakaninsu. Ta ajjiye musu komai tana shirin miqewa abba daya gama wanke hannunsa yace

“Dawo ki zauna mana ummin abba” murmushi kadan tayi,ta dawo ta zauna din,sai da ya fara cin abincin sannan yace

“Me ya faru ne yau a MT JARMA?” Kanta ta sunkuyar tana jin rauninta yana dawowa,kamar yanzun abun yake faruwa,amma dole ta bude baki tayi magana da harshen da zasu fahimceta

“Na ajiiye aiki yau abba,ku  yimin afuwa abba kai da yaa muhyi na rashin neman sahalewarku kafin aiwatar da hakan,abun yazo a gaggauce ne,sannan kuma a gabar da bazai bada damar yin hakan ba”

“Me ya faru?” Abban ya sake jefa mata tambayar. Bata rufe komai ba ta zayyane musu,tun haduwarsu ta farko har zuwa abinda ya wakana yau din. Ta qarashe maganar tana hawayen takaici.

          Ga mamakinta sai taga abban ya saki murmushi yana girgiza kai

“Dake dashi dukka quruciya ce take damunku da kuma zafin kai,tare da wasu memories da suketa hunting rayuwarku,shikenan dai,bakin alqalami ya riga ya bushe,dr jarma ya kirani da kansa,yace bazai tilastaki ba akan ajjiye aiki da kikayi,yace a baki haquri a madadinsa da dukka ma’aikatan,sannan ya tura kudi a baki saboda hobbasar da kikayi kika daga kamfaninsa zuwa matakin gaba,kika gyara matsalar da suke fuskanta kaso sittin cikin d’ari” ya qarashe fadi yana duban fuskarta. Batace komai ba sai kai data girgiza,taji dadi da bai nema alfarmar lallai ta koma ba,don bataso ya roqeta abinda ba zata sake iyayi masa shi ba.

“Dama aiki ba dole bane,aure ne dole” abban ya sake fadi,maganar data bugeta sosai,ta kuma sakata dago kanta da sauri ta kalli abban,shima idanunsa yana kanta,ya jinjina kai alamun tabbatar mata da hakan

“Tunda taqi tsayawa ta fahimci kowa abba bazaiyiwu taci gaba da zama babu auren kuma ba aikin ba,Allah baya barin bawa babu aikin yi,akwai irin aikin da takeso din abba,idan na dawo daga tafiyar nan ta wata daya zuwa biyun nan zan applying mata” kai ya sake jinjinawa yana tsame hannunsa daga tuwon

“Banqi ta taka ba,amma duk da haka ta maida kai ta fidda miji,saboda lokaci tafiya yakeyi,kuma har yanzu ke din yarinya ce qanqanuwa ballantana kice kin girmi yin aure a yanzu”. Gaba daya babu abinda maganganunsu sukayi sai dagula mata lissafi,dan ciwon kan data samu ya ragu sosai ya dinga qoqarin dawowa saboda damuwa,ga gidan babu kowa bare ta samu me debe mata kewa,tanaso tayi magana da anty farheen to amma tasan tabbas yaa muhyi yana gidan,don tafiyar tasa sai zuwa wani satin,sai kawai ta hada kayanta a washegari tabi afifan nata zooroad.

            Ranar da taje qin cewa afifan komai tayi,itama bata matsanta ba sukaci gaba da hutunsu,har sai data huce,ranar suna ta raka afifa gyaran farce da fuskarta,suna hanya tana driving ta bata labari. Sosai afifa bataji dadin ajjiye aikin ba,duk da itama taji ba dadi akan yadda abun ya faru tsakaninta da toufeeq din,saidai itama ta gaya mata

“Ba kowanne namiji ke iya fuskantar mace ya bata uzuri ba,ya kuma banbance rashin kunya da tsaiwa akan haqqinta ba,bare mutum irin MT da Allah ya yiwa baiwar kyau kudi da ilimi da kwarjini…..”

“To hell with his kudi da kwarjinin,ya dauka ina cikin shirgin wawayen ‘yammatansa ne da zan dauki irin wannan?,ki daina yabonsa please kina batamin rai afifa…..bakisan wayeshi bane,saboda baki taba mu’amala dashi ba,he was arrogant beyond belief,good look don’t always signal kindness” dariya afifa tayi

“Wato kin fahimci kyansa ya janye hankalina sosai ko?”

“chapter close a beg” yatsunta biyu ta sanya tayi signal na zipping bakinta,bata kuma sake cewa komai din ba,sai suka shiga wata hirar ta daban.

Page 32

*********K’arfe kusan takwas ne na dare,saman titin dake wadace da fitilu yake tuqin yau da kansa,kuma shi daya,abinda ba kasafai yake faruwa ba. Sanye yake da wata maroon and golden hoodie captan abaya na maza saqar qasa turkiyya,dogon hannu gareta,ya saki hular a bayansa,hakan ya bawa kyakkyawar fuskarsa damar fitowa sosai,cike da wannan turbunewar da kuma rashin fara’a daya zame masa dabi’a.

          Kiran dr jarma ne ya fito dashi,don yana zaune shida fadeela a part dinsa suna buga game data tubure itakam yau tare zasuyi,da qyar ya lallabata ya maidata gurin nanny dinta sannan ya fito,tare da alqawarin zai dawo da wuri su qarasa. Baisan kiran na meye ba,amma alamu sun nuna a gaggauce yake neman nasa.

            Cikin rukunin gidajen dake sharada NNDC QUARTER,mayalwacin layin dake shimfide da kwalta da kuma fitilu a jere reras,kowanne gini dake layin abun kallo ne,wannan yana wane wancan,a haka yaci gaba da tafiya bayan ya ragewa motar gudu,da alama ya kusa isowa gidan daya nufaci zuwa.

            K’ofar wani mansion house dake dauke da ginin bene hawa biyu ya tsaya,ya danna hon na farko, kafin yayi na biyu security din dake sanye da baqaqen uniform da suke kama dana police ya buda masa qofar,a nutse ya sanya hancin motar zuwa cikin makekiyar harabar gidan. Biyu daga cikin security dinne suka bude masa qofar cikin girmamawa da qauna me tarin yawa suke gaidashi,ya amsa musu yana rufe motar,ya jefa key din a aljihun rigar tasa,ba tare daya ciro hannuwan nasa ba yaci gaba da takawa zuwa cikin kamar maijin sanyi. Bawai sanyi yakeji ba,kawai yana jin wani iri ne da yanayin yadda dr din ya kirashi.

           Kai tsaye ya kutsa zuwa hanyar da zata sadashi da falon gidan,ya tsaya yayi knocking,duk da cewa gidan mahaifinsa ne,amma hakan ba sakashi shiga kai tsaye ba,duk sanda yazo gidan sai ya tsaya ya nemi izini don cikar dokar addinin musulunci.

          K’ofar aka bude,labiba ce,sanye da wata doguwar riga da tasha tattara daga qirji,ta bude daga qasa sosai,kanta cike da qananun kitso da gashin doki,sao farata zaqo zaqo data sanyawa hannayenta tamkar wata dabbar daji,amma ita a gurinta hakan ado ne na wayayyun mata masu aji(wallahi wallahi wallahi muddin kinsan daya daga cikin wadan nan abubuwan dabi’unki ne to kiyi gaggawar dainawa tun kina raye kina da lafiya,qarin gashi haramunne koda mijinki zaki yiwa,ko meye zaki sanyashi a kitsonki a qara miki tsahon gashinki haramunne,hakanan saka farce shima haramunne,haramunne haramunne,koda faratan hannunki bai halasta ki tarasu ki barsu baki yanke ba,haramunne barin farce yayi zaqo zaqo bare har kije ki biya kudi a dora miki shi,kina ‘yar adam amma kinason kiyi kamanceceniya da dabba?,suke da wanann siffa ta akaifa ko qumba masu tsaho,acikin tsarki na addinin musulunci,bansa aske gashin maara dana hammata harda yankan farce sai yiwa yara shayi(kaciya), ma’aiki baya taba fadar magana wallahi wallahi ta tashi a banza,idan yace abu haramunne mu yarda mubi,ba wani kwaskwarima da malaman zamani masu son zuciya zasuyi ma maganarsa ta koma halak,haram haram ce,halal halal ce,Allah yasa mufi qarfin zakatanmu👏🏽👏🏽).

             Sau daya tak ya kalleta ya kauda idanunsa,sannan ya gewayeta ya sanya jikinsa zuwa falon

“Sannu da zuwa yaa toufeeq” ta furta tana bin bayansa hadi da binsa da wani mayen kallo,bai amsa mata ba yaci gaba da kutsa kai,masu aikin dake kai kawo a parlor din suka yi masa barka da zuwa sannan suka kauce daga gurin.

“Abban yana samansa” ta fada cikin yauqi da kwarkwasa,wanda sau tari wani lokaci ita kanta batasan hakan tana faruwa ba,tsabar yadda zuciyarta ne ta afu ason samun soyayyarsa.

“Ya toufeeq” ta kira sunansa,waiwayowa yayi ya watsa mata wani irin kallo daya takura zuciyarta guri guda ya sanyata harbawa,saita duqar da kanta qasa tana wasa da yatsunta

“Yaa toufeeq,am sorry for what happened last time,tsautsayi ne in sha Allah hakan bazai sake faruwa ba” qaramin tsaki yaja,yayi gaba ya fara takawa zuwa stairs din dake cikin falon.

         Binsa tayi da kallo har ya bacewa ganinta,hannuwanta ta yarfar kamar zata saki kuka,ta tsani wanann miskilancin nasa,yana matuqar dafaata da dagula mata lissafi,sai ta koma ta zauna saman daya daga cikin qayatattun kujerun falon tana dafe da kanta,dai dai sanda daya daga cikin masu aikin gidan ta qaraso cikin rusunawa

“Ranki ya dade,abincin daren,na kammala fa”

“Dalla matsa ki ban guri” ta fada mata cikin tsawa tana jan tsaki

“Allah ya baki haquri” ta fadi tana janye jikinta daga gurin tunda ragowar mutuncinta,tasan tsaf zata iya ci mata zarafi,ta juya ta koma cikin kitchen din,cikin ranta tana Allah ya qara da yadda toufeeq din yake wajiga rayuwarta. Sake daga kai tayi ta dubi stairs din,gurin mommynta takeson zuwa,to amma ta sani,tunda ya iso ko ruwan giya tasha bata isa hawa saman ba har sai ya sauko,saita kwashe qafafunta ta mayar saman kujerar ta kwanta tana dakon fitowarsa,a ranta tana tsara yadda zasu kebe ita dashi ko na minti talatin ne kacal.

           Da sallama a bakinsa ya shiga falon bayan dr yayi masa izini,tana duqe tana zuba masa lemo a cup,kakkaurar mace wankan tarwada me tsaho da jiki,wanda kana dubanta zakasan ba hausa fulani bace.

          Da fara’a a fuskarta ta dago tana cewa

“Wata sabon gani,kaine yau a gidan namu?” Dan binta yayi kadan da kallo yana mamakin furucinta,A GIDAN NAMU,sai baice mata komai ba,ya taka a nutse ya isa daura da mahaifinsa,kwata kwata baisan me yasa bai taba jin matar ko daukarta da wani daraja ba,duk da tsahon shekarun data kwashe tana amsa sunan MATAR MAHAIFINSA,sannan dai dai da rana daya bata taba gwada masa wani hali ba,amma haka kawai take takenta baiyi masa ba.

“Ina ka baromin kishiyata?” Ta sake fada cikin fadada fara’arta,maimaikon ya amsa mata tambayarta sai ya buge da fadin

“Barka da dare”yayi furucin kamar ba da ita yake ba,yana maida dubansa ga mahaifinsa,cike da kulawa tace

“Barka kadai Muhammad,ya ayyuka,ya akaji da kacaniyar jama’a” ta tambayeshi cikin nuna kulawa.

“Alhamdulillah” ya amsa mata a taqaice,sam bata damu ba,don ta saba da irin wanna halayyar tasa,saita fara kwashe kayan abincin dake gurin tana dubansa

“Me za’a kawo maka?” Kai ya girgiza,baisan sai yaushe zatayi fushi ba ta daina tambayarsa abinda zaici ba duk sanda yazo gidan,bayan tafi kowa sanin baya cin abinci daga hannun kowa kuma a ko ina ba,sai a wasu kebantattun hannuwa da gurare.

“Alhamdulillah,basai na saki hidima ba” murmushi ta kumayi

“A’ah kace dai ba zakaci ba kamar kullum”

“Yi tafiyarki ki rabu dashi,kada Allah yasa yaci din” Dr ahmad ya fada,wanda tunda ya shigo lemonsa yake kurba yana kuma kallon labarai daga NTA network news.

“Zaici ne wataran ai” ta fada da dariyarta tana yin gaba. Sau daya tak kalmar ta shiga kunnensa amma ya gama fahimtar abinda take nufi ba tare da ita tayi zaton zai fahimta din ba.

“Barka da warhaka” ya fada cikin girmamawa,sauke qafafunsa dr ahmad yayi qasa yana ajiye cup din hannunsa gami da bashi amsa duka lokaci guda

“Kai ya kamata a yiwa barka ai,irin wannan aikin da kayi na cin zarafin yarinyar dana nema alfarmar a bani aronta,ka kuma sanya tabar aiki lokaci guda,to kaga kai ka cancanci a yiwa barka” bai barshi yace komai ba dr din ya tsinke da fada,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba,daga qarshe yace

“Ka ajjiyemin komai daya shafi company dina kaima na sallameka,na gode da iya taimakon daka bani,ka koma bakin taka dukiyar” daga haka ya miqe ya wuce bedroom dinsa yana bar masa falon.

           Kasa motsawa yayi daga gurin,yanajin tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu,tsahon tasowarsa bayan shudewar matsalolin da suka sanyo kai a rayuwarsu tun zamanin quruciyarsa,bazaice ga lokacin daya zauna yayi masa fada me zafi irin haka ba,sai yanzu?,a dalilin yarinyar?,ya jima a gurin sannan ya miqe a nutse yana sauka qasan,fuskarsa cike fal da fushi da kuma bacin rai,ta zama silar gurbata kyakkyawar alaqar dake tsakaninsa kenan da mahifinsa lokaci guda?.

            Suna zaune a falon,hajiya mansura(matar dr ahmad jarma) tare da labiba,ganin yazo zai wucesu ba tare daya kalli kowa a cikinsu ba,kamar ma baisan da zamansu ba hajiya mansura ta magantu

“Harka sauko?,kun gama kenan?” Da so samu ne yayi wucewarsa,to amma ko babu komai ita din mata ce ga mahaifinsa,zata iya cin darajar mahaifin nasa koda qanqani ne

“Eh” ya amsa bayan ya waiwayo yana dubanta hannayensa zube a aljihun rigarsa. Kwarjini ya mata sosai,tadan daburce amma saita maze ta hanyar sakin murmushi

“Ammm,tafiyarku daya da qanwarka,nace ko ta bika saiku tafi tare?” Ido kawai ya lumshe wanda ke nuna ya amsa kenan,ya juya ya fita a falon.

          Da mugun gudu ta sauko daga saman kujerar,ko ina na jikinta yana rawa

“Mommy,ki bada kayana gobe usaina ta kaimin”

“Ki tsaya ki tafi da kayarki,goben akwai inda zan aiketa”

“Tsaf zai tafi ya barni idan na tsaya jiran hada kaya” tayi maganar a lokacin ma takai bakin qofa.

         Lokacin data isa tuni ya tayar da motar,abinda ya tabbatar mata inda ta qara wasu mintuna saidai tazo ta tarar da wajen wayam. Gaba ta bude zata shiga,cikin kaushin murya yace

“Koma baya!” Jiki a sanyaye ta maida murfin ta rufe,ta koma bayan ta zauna,ranta ba haka yaso ba,taso zaman kusa dashi,ta yadda duk maganar da zatayi masa ta tafi cikin kissa da kuma jan hankali.

“Yaa toufeeq” ta kira sunansa sanda suka dauki hanya sosai

“I don’t want to hear anything from you har mu qarasa gida,if not kuma,i will drop you” kallonta ta maida ga titunan da suke wucewar,yadda suka dauki shuru saboda daukewar qafa da ababen hawa sakamakon dare daya fara yi,marufar asirinta yin shurun,don tasan kadan ne daga aikinsa ya sauketan kamar yadda ya furta. Ranta ya quntata sosai,dukka wani plan nata ya rushe,manufar da yasa tacewa Mommy tayi masa magana ya sauketa ma ya tashi a banza.

Page 33

          Shuru ne ya wanzu cikin motar,sai satar kallonsa da take tayi ta cikin madubin motar a duk sanda zasu gifta wani guri dake da wadatar haske,ji takeyi kamar taje ta rungumeshi tsam tsam ko zata ji sassaucin yadda zuciyarta ke azalzala da qaunarsa,burinta da fatanta a yanzu shine Allah ya mallaka mata toufeeq din kota halin yaya ne ma.

           A nasa sashen kuwa hadiyar wani abu ke tauri kawai yakeyi daya tsaya masa a wuya,tabbas ya sake amanna da kaidin mata babba ne,babu abinda ba zasu iya aiwatarwa ba,fada da kalmomin da Dr ya gaggaya masa kawai ke yawo a kunnensa,yayi qwafa can qasa yadan daki sitiyarin motar kadan yana jinjina kai,ji yake dama ya buda idanu ya ganta yanzun a gabansa. Dan qara speed na motar yayi saboda wani faduwar gaba da yaji ya ziyarceshi,wani yanayi ne da yakan samu kansa a ciki muddin wani abu zai afku ga fadeela,sai duka ya samu kansa tunaninsa ya koma gida.

            Tun kafi ya kammala parking yace mata ta sauka,ta fidda ido tana ganin yadda motar ke slow bata qarasa tsaiwa ba,saita langabe kai zatayi masa salo

“Yaa toufeeq idan na karye fa?”

“Keep quiet,will you drop ko sai na fiddaki da kaina?” Jin haka ya sanya ba shiri ta tattare ta tsallake,Allah yasa motar a sannan ta kammala tsaiwa, zuciyarta kamar zata fashe saboda baqinciki,batasan me yasa yake tozartata haka ba,tanason tayi zuciya ta kuma yi fushi dashi amma ta kasa,shi din fushinka banza ne,rashinsa banza a wajensa,wannan bacin ran ya sanya tayi wucewarta ba tare data tsaya ta kalli inda baaba ramatu ke zaune ita da fadeela ba,wadda ta damu baaba ramatun ta rakota su fito su jira dad dinta,dole ta taso suka bar nanny dinta a ciki.

           Yana fitowa daga motar fadeela din ta miqe da sassarfa tayi gurinsa cikin murnar ganin ya dawo da wuri

“Daddy……dadddd…….” Maganar ta kasa fitowa gaba daya,saboda yadda harshenta ya lanqwashe,haruffan suka sarqe cikin na juna,a take kuma kowanne sashe na jikinta ya fara wani irin kakkarwa ta soma lanqwashewa zata kai qasa,kafin takai qasan har ya risketa,ya kuma tallafota ta fada jikinsa ta zube gaba daya,ta fara wata irin jijjiga me qarfin gaske. Duk da cewa ba yau ne ciwonta irin haka ya fara tashi ba,amma har yau har kwanan gobe ya kasa sabawa da irin wannan tashin hankalin da yake tsintar kansa a ciki a duk lokacin da EPILEPSY din fadeela ke fuskanta a rayuwarta ta motsa,komai qwace masa yakeyi,kamar yanzun daya rude gaba daya yana kiran sunanta,wanda zuwa sannan ta zama unconscious.

         Tuni baaba ramatu dake qwalla ta kirayi hajiya qarama,ganin dosowarta gurin yasa yayi hanzarin yiwa kansa saiti tare da qoqarin dawowa da kansa dai dai,bai jira isowarsu ba ya dauketa don ya sama mata gurin da zata zama comfortable ya wuce sassansa da ita da wani irin sassarfa yana monitoring numfashinta yadda yake kai kawo yana wani irin riqewa.

           Sosai ya kwantar da ita saman lallausar sofa,ya kuma tallafi kanta da pillow me laushi yana kallon numfashinta,a duk sanda take irin wannan abun,sai ya dinga ganin kamar zai rasata,kamar zata tafi ta barshi,hannunsa ya sanya ya juyata barin hannunta na dama don daidaituwar numfashinta da yakeyi kamar zai dauke,yaci gaba da kallonta,yana jin inama ace yana da qarfi ko wata dama da zai iya fidda wannan ciwon daga jikinta?,a ko yaushe saidai ya zauna ya kalleta helpless,har sai ta gama ta dawo hayyacinta.

            Maida dubansa ga agogo yayi bayan shudewar wasu mintuna,dai dai sanda hajiya qarama data iso tace

“Ta tashi?” Kai ya girgiza ya jawo wayarsa a gaggauce yana neman number Dr anwar,har yanzu idanunsa nakan agogo yana irga mintunan,bata taba daukar mintuna irin haka ba tare data dawo dai dai ba,abun ya fara daga masa hankali.

           Kira daya tak ya daga

“Fadeela ce?” Dr anwar ya fada,saboda layi ne da yasa aka tanadar masa saboda matsala irin wannan

“Gani nan” ya fada kawai

“Kada ka matsa daga inda take,ka barta a right side dinta kaci gaba da monitoring dinta da kuma mintunan”

“Alright” ya fada yana ajjiye wayar da sauri,zuwa lokacin hajiya qarama ta koma kujerar kusa dasu ta zauna,ta hada tagumi hannu bibbiyu tana maimaita kiran sunan Allah cikin nuna tsananin tashin hankali,kauda hankalinsa yayi daga maganganun da takeyi,saboda qara masa tashin hankali da kuma karaya kawai sukeyi. Mintuna biyar kacal Dr anwar ya iso,saboda basu da nisa,layi biyu ne kadai ya rabasu. Shi ya dauketa zuwa clinic na cikin gidan,dab da zasu shiga ta motsa tana bude idanunta a hankali bakinta dauke da sunan

“Daddy” miqa masa ita yayi yace ya qarasa masa da ita ciki,suna hada ido ta saki ajiyar zuciya ta qanqameshi sosai,sai taji zuciyarsa na karyewa,tausayinta da tausayin rayuwarta da kuma tsanar mahaifiyarta data jefata a wannan mummunan yanayin yana sake ratsa kowanne sashe na gangar jikinsa.

              Sosai Dr anwar yayi checking dinta don gano abinda yasa jijjigar tata ta dauki lokaci fiye da yadda ta saba,ya ajjiye kayan aikinsa gaba daya yana duban toufeeq,hajiya qarama na zaune daga gefe,baaba ramatu kuma na tsaye daga saman kan fadeelan

“Ya kamata gaskiya a qara ninka kulawar da ake bata,akwai factor’s da zasu iya ta’azzara epilepsy din,ta qaru daga adadin mintunan da aka saba yinta” idanunsa da suka sauya launi ya mayar kan baaba ramatu

“Ina fatan nanny dinta tana aikinta?” Dan sunkuyar da kanta tayi,ta fahimci me tambayar tasa take nufi,idan ta bayyana masa gaskiya zai kori yarinyar ne daga bakin aikinta,idan kuma ta boye masa taci amanar mutanen da suka bata yarda,har yanzu batajin yarinyar ta samu kulawa dai dai da wadda Dr anwar ke magana akai,ita din ba komai take iya aiwatarwa ba,kamar kula da magungunan yarinyar da sauran wasu kayan qarin lafiyar,abune na wadanda sukayi karatu,ita kuma bata taba halarta boko ba,iya bakin qoqarinta tanayi wajen kula da fadeela tamkar jikar data fito daga jininta,kowa ya shaida hakan,wasu abubuwan hajiya qaraman ne ya kamata tayisu,to amma ita din ba mazauniya bace,koda mazauniyar ce ma,bata ganin alamun………

“Ko yaushe ciwon zai iya worsening,me zai hana kayi haquri a jarraba yi mata aiki?” Maganar dr anwar ta katse tunanin baaba rabi. Yayi susa ne a inda yake mata qaiqayi,kullum cikin sallolinta na dare addu’arta tafi qarfi akan ciwon fadeela,Allah ya yanke mata,idan da alkhairi Allah ya fahimtar da mahaifinta mahimmancin aikin nan ayi mata ta huta ta rabu da wannan ciwon,tana matuqar qaunar yarinyar kamar jininta.

“Haba likita?,ya zaka ce haka?”

“Hajiya” baaba ramatu a wannan karon ta sanya baki

“Nima ina ganin abarwa Allah a gwada jarrabawa din,ba’a san inda za’a dace ba”

“Dakata ramatu,ashe baki da hankali kema?” Ta fada cikin fushi

“Ke kinsan ma me ake nufi da yiwa mutum aiki a qwaqwalwa?” Shuru baaba ramatu tayi tana sadda kanta qasa

“Allah ya baki haquri” ta fada a sanyaye tana jin ciwon maganar data yaba mata,shi yasa sai ayi abu dubu cikin gidan bata tofa tata ba,wannan shi ya siya mata kima ya kuma sanya ta dade sosai cikin gidan.

“Relax please” toufeeq dake riqe da hannun fadeela ya fada yana rage girman idonsa,dole hajiya qarama ta koma ta zauna tana huci harda qwafa

“Dr,banason azo ayi abinda zai zama nadama a garemu,kaso mafi rinjaye a aikin nan bashi da tabbas na dawowarta normal,if akayi rashin dace ma abun yana iya qaruwa ko kuma a sake samun wata matsalar bayan ya qarun haka ne?”

“Yes,duka akwai probability na samun hakan”

“Mubar zancan”

“Is ok” kansa ya mayar ga takardar ya sake rubuta mata qarin wasu magungunan ya miqa masa

“Aci gaba da kula da magungunanta da muhallinta,and someone who is very knowledgeable is the one who can takes care of her”

“Thanks” ya furta yana bawa dr anwar din hannu sukayi musabaha sannan yayi musu sallama ya fice.

         Matsowa hajiya qarama tayi tana shafa kanta a nutse

“Sannu uktie” daga kai yarinyar tayi ta kalleta,saita sakar mata wani dan malalacin murmushi wanda zai nuna maka jikinta duka ba dadi,qarasowa toufeeq yayi ya bata hannu,ta kama hannunsa ya dagota,ya dauketa cak ya azata a kafadarsa

“Ka bani ita mu wuce sashena ta kwana gurina mana?” Hajiya qarama ta fada

“I can take care of her, don’t mind it”

“Okay,ke ramatu,ki tattaro magungunanta ki kawo su,a hado mata da kayan baccinta,ki cewa nanny dinta tazo part dina ta fara mata wanka ta shiryata saina miqo maka ita”

“No,tell her to pack her things,gobe driver ya sauketa a inda aka daukota,she’s no longer needed,zan canzata with someone better” yana gama fada ya fara takawa a hankali yana fita daga clinic din,yana jin zuciyarsa kamar zatayi melting down,wani irin yanayi na tsananin kewa da tausayin kawunansu yana tsarga masa.

          Shi yayi mata komai kamar yadda yace,ya shiryata cikin fararen kayan bacci masu taushi,ya bata abinci taci,tana ci ta kalleshi da fararen idanunta

“Dad,kaima kaci” kai ya girgiza yana qoqarin sauke murmushi akan fuskarsa

“I can’t eat” sai ta bata fuska ta rufe nata bakin,ya fahimci me take nufi don haka yace

“Later angel”

“Sure?” Sai ya gyada mata kai yana lumshe ido.

          Ci gaba yayi da kula da ita,har bacci yayi awon gaba da ita,ya zauna a gefanta yana qare mata kallo cike da tausayi,zuciyarsa na gaya masa ya ajjiye komai da komai,ya zauna yayita kula da ita tsahon rayuwarsu.

             Qarar wayarsa ta katse masa tunanin daya zurfafa a ciki,yanzun yake shirin kasheta, saboda baya buqatar wata hayaniya kuma,ajiyar zuciya ce ta qwace masa sansa yaga sunan MAJI yana yawo saman screen dinsa,sai ya daga wayar a sanyaye ya kaarata a kunne hadi da yin sallama da muryarsa da tayi laushi qwarai

“Bakayi bacci ba?” Ta tambayeshi bayan sun gaisa da hausarta da ta gauraya da sirkin larabci,cikin wani yanayi na nauyin qirji da kuma tausayi dake can qasan zuciyarta yana cinta

“Yanzu nake shiri”

“Ina fadeela?”

“Tayi bacci” shuru na rashin sabo ya gifta a tsakaninsu sannan tace

“Ka yawaita addu’a tare da miqawa Allah al’amuranka,kana buqatar matar aure ta gari kamar yadda fadeela take buqatar UWA” shuru yayi yana saurarenta,ta saba yi masa wannan maganar dake kama da wasiyya,amma kuma a yaudin tayi masa maganar da bata taba yi masa irinta ba. Shurun da yaji yasa ya gane kiran ya yanke sai kawai ya ajjiye wayar gefe,ya zame daga gefan fadeelan ya kwanta rub da ciki yana sauke idanunsa akan innocent baby face dinta.

Page 34

******Tamkar wadda aka yiwa dukan tsiya haka take dawowa cikin dakin,duk wani karsashi data fita dashi babu shi afifa sam bata lura da sauyin yanayinta ba,saboda lokacin da ta dawo din tana amsa waya ne,tana gamawa kuma ta dora mata da hirar da sukeyi dazun kafin ya fita

“Epilepsy duk bahaushen asali yana mata kallon farfadiya,ciwon da aka dangantashi da aljanu,amma kuma mu a likitance ba aikin aljanu bane,aikin daga gazawar qwaqwalwa ne,na gaya miki dalilan dazu da irin yadda akeson a basu kulawa…..yanzu kuma bari kiga w……” Maqale mata maganar tayi,saboda waiwayowa da tayi taga sãahar din dafe da kanta hannu bibbiyu. Da sauri ta ajjiye system din hannunta dake dauke da zanen qwaqwalwa ta nufi sãahar din

“Me yake faruwa?,kin fita lafiya kuma saiki dawomin a haka?” Ta fada tana dafa kafadarta. Kanta ta dago da idanunta da suka cika da qwalla,cikin matuqar sarewa da mutuwar jiki tace

“Inajin kamar na fara gajiya da rayuwar nan”

“Me kuma ya faru haka ana zaune qalau?,ko yaa muhyi dinne?” Kai ta gyada tana sharce qwallar data ziraro mata

“Shine,yana maganar na sake duba akan hukuncin ajjiye aikina,ni kuma wallahi Allah afifa bazan taba iya sake taka kamfanin MT jarma da sunan ma’aikaciya ba,bazan iya daukan cin fuska ko cin kashi daga gurin kowanne d’a namiji ba a yanzu,na fuskanci iya abinda zan iya dauka,ina buqatar nutsuwa,inason nayi nesa daga dukkan wani namiji da abinda ya danganceshi,wai har kun manta da irin abinda na fuskanta ne?” Kai afifa ta girgiza,ta kama hannuwan sãahar din dukka biyun

“Cool down mana bestie,taya zamu manta da wadan nan baqaqen ranakun a rayuwarmu?,yaa muhyi ba cewa yayi ki koma ba lallai,cewa yayi kiyi tunani, kina iya cewa ba zaki iya komawa ba ya baki uzuri,na tabbatar bazai sake cewa komai ba,please kada ki ja ciwon kanki ya tashi,calm down bestie” kai ta jinjina tana jin sassauci natsuwa na saukar mata kadan kadan,sai ta lumshe ido ta dafa hannun afifa

“Thank you for always being with me afifa” murmushi ta saki tana jin tausayi da qaunar ‘yar uwarta

“Ba buqatar ki godemin,domin kamar na aikata dole na ne…..yanzu ki kwanta kawai,dare ya farayi,gobe zan qarasa miki bayanin” bata musawa afifan ba,don a yanzun itama ba abinda take buqata irin ta zauna silent ko hayaqin da takeji cikin kanta zai sauka.

            Ta kwanta ne kawai ta kuma rufe ido,amma duk wani motsi na afifa tana jinsa,har afifan ta gama abinda zatayi ta rage musu hasken fitilar dakin zuwa kala me duhu ta kwanta.

           Cikin duhun dakin idanunta keta walainiya,ba abinda ke gilmawa qwaqwalwata irin abinda ya faru da ita,rayuwarta ta baya data shude kamar zuwa da tafiyar ruwan sama,ta runtse idanunta da kyau tana girgiza kai,saboda bata shirya tuna irin wannan abun ba cikin daren daya fara nisa,saidai duk yadda takai ga toshe tunanin sai daya fara dawo mata da kansa.

*_WACECE SÃAHAR?,ME YA FARU DA ITA?,ku biyoni muje mu gani_*

*NAMIJI tabarmar k’ashi*

           Madaidaicin gida ne dake dauke da dakunan bacci manya guda biyu a qasa,da kuma mayalwacin parlor dake dauke da dukkan wani nau’i na kayayyakin da rayuwa ke buqata ga masu qarfi da kuma wadatar abun hannu.

               Qawataccen dining area da aka zubawa dining me kyau da daukar idanu na gilashi,da kuma qofar qawataccen kitchen din mamallakiyar gidan, kitchen din daya tara dukkan wani abu daya kamata ace akwaishi ga kitchen din diya mace.

         Tun daga manyan hotunan masu gidan dake manne a bango hudu na gidan kadai ya isa ya gaya maka irin gidan daka shigo,hotunane da aka daukesu bisa tsari da burgewa,gogewa da kuma sanin ilimin zamani,hotunan dake fallasa zallar soyayya qauna kulawa da kuma shaquwa tsantsa daga idanun mutanen da siffofinsu ke manne jikin taswirar.

           Duk da akwao banbancin siffa da kyau daga barayin mutumin dake jikin hoton zuwa ga matar dake tare dashi,amma wannan bazai zama cikas zuwa ga burgewar da zasu yiwa zuciyarka ba,hakanan bai zama cikas ga bayyanuwar soyayyar dake idanun kowannensu ba.

            Komai na falon a kammale yake a tsaftace hakanan a kintse,cikin wata irin tsafta kulawa da kuma sassanyan qamshin dake gauraye da sanyin ac din dake karakina cikin falon da kuma kewayensa,wani irin yanayi daka iya karyar da zuciyar dake da rauni,ya kuma bawa kowacce irin rai nutsuwa da gamsuwa.

              Daga saman gidan shima Parlor ne dauke da bedroom guda daya,saidai yafi dukka bedrooms din gidan girma da yalwa,shine kuma yake a mazaunin master bedroom,saidai shi parlor din baikai girman na qasa ba,saidai yana da jan hankali da alatu sosai har kamar ma yaso yafi falon qasan,hakan kuma baya rasa nasaba da kasancewarsa falon me gidan,wanda daga shi sai matarsa ke mu’amalantar sa.

           Cikin daya daga cikin bedrooms na gidan,dakin baccin dake da wani irin tsari da aka shiryashi cikin unique colors,qofa guda daya tal dake cikin dakin baccin ta bude a hankali.

         Sambaleliyar matashiya ce ta fito,doguwa mai matsakaicin tsaho,murjajjen jikin da ya hana bayyanuwar tsahonta,ya sanya tsahon ya zamana ado a gareta,fara ce sol farin dake da surki surkin ja a cakude dashi.

           Sassalkar sumar kanta mai tsaho santsi da kuma cika kadai ta isa ta gaya maka cewa ita din ba BAHAUSHIYA bace,saidai wani yaren daga cikin yarukan da Allah ya albarkaci qasata nigeria dasu.

            Kai tsaye zaka iya kiranta da KYAKKYAWA cikin mata dake da kyau a ajin farko,wani baiwar kyau da Allah ya bata tun tana ciki zuwa isowarta duniya,kyan dake iya zama barazana ga rayuwar diya macen da bata samu kyakkyawar tarbiyya ba,ko bata hadu da iyayen qwarai ba,wani irin kyau mai sanyi da tsayawa a rai,wanda ya cakuda da tsafta iya kulawa da kai da kuma gayu sannan ilimi ya hada dukkansu yayi masa ado na musamman.

           Towel ne kawai daure a qirjinta,cikin wata irin nutsuwa take takowa har ta iso gaban makeken mudubinta,har ta miqa hannu zata dauki daya daga cikin tsadaddun mayukan shafawarta saita fasa,ta daga kai tana kallon agogon bangon dake manne saman mudubin wanda yayi wata qaramar qara dake nuna awa guda cif ta cika.

         Zagayayyun fararen idanunta ta janye daga kan agogon cike da mamaki,saita dauki man ta bude,ta dan tsaya tana dubansa kamar yaune rana ta farko data fara ganinsa,ba zata iya tuna when last da ta bari man shafawarta ya qare ba,hakan yana nufin dole gobe taje shopping kenan,saita lakaci man ta fara shafe lafiyayyar fatarta cikin hanzari,tana yi tana duban wayarta dake ajjiye a gefe.

            Kasa daurewa tayi,gani takeyi kamar ta kasa saurin da ya kamata ace tayin,ta jawo wayar tana loda wasu numbers dake alamta ta jima da haddace su,suka cika cif ta danna kira,SOULMATE sunan ya bayyana baro baro kan screen din wayar tata.

              User busy ta saka mata,mamaki ya kamata,ta sake maimaita kiran aka sake sanar mata ana amfani da layin,saita aje wayar kawai ta mayar da hankalinta kacokam akan shiryawar da takeyi din,saidai can qasan zuciyarta bata daina mamakin wasu abubuwa da take gani cikin satin nan ba,wanda kai tsaye zata iya kiransu da BAƘIN ABUBUWA.

           Kamar ko yaushe ta shirya tsaf cikin wata lafiyayyar rigar bacci da ta saka kudi masu nauyi ta siya duk don saboda ta burge mijin nata,masoyin da duk duniya idan ka dauke iyaye da kuma AFIFA bata da kamarshi,tayi checking kanta da kanta ta tabbatar komai yayi fiye da yadda ADAM keson ganinta a kowanne dare,saita saki qaramin murmushin da ya sanya dimple din dake dukka kumatunta lobawa,ta kawo qaramin baby hijab ta saka,sannan ta dauki wayarta laptop da sauran wasu tarkace da takeson dubawa na sauran aikin office da bata qarasa ba,ta zura slippers a qafarta ta fito.

             Sai data kashe kowanne qwai da sauran kayan electronics dake aiki a qasan sannan ta haura saman cikin takun nan nata kamar tafiyar wahainiya,wanda ya zame mata halitta cikin jininta yake.

           Ba kowa a falon,sai butar shayin data barshi yana sha a dazun da sautan cups da suka bata,dukka sai data killacesu sannan ta dawo zuwa babbar qofar da zaga sadata da bedroom din nasa,tana mamakin yadda akayi duk motsinta na yau baiji ba.

              Da sallama a bakinta ta tura qofar,yana zaune sosai saman lafiyayyen gadon,ya jingina bayansa da fuskar gadon,saman cinyarsa kuwa na’urar laptop ce daya zubawa dukkanin idanunsa,yakuma bata hankalinsa dari bisa dari,koma me yakeyi da alama yaja hankalinsa matuqa.

             Sautin muryarta ya sanyashi daga kai a hankali ya watsa mata manyan idanunsa,sai ya fidda qaramin murmushi daga labbansa idanunsa nadan lumshewa saboda yadda ta dauki hankalinsa,har yaji ma komai ya fita daga kansa,shi kansa yasan Allah yayi masa baiwar kyakkyawar mace,Allah ya bashi macen da yasan qarfin ikonsa ko wani qoqarinsa…. dukiyarsa ko iliminsa,wayo da dabara dukka basu isa su bashi SÃAHAR ba face tsananin rabo da kuma irin sa’arsa,wadda tunda ya fara gwagwarmaya a rayuwarsa ya fahimci shi din me sa’ar ne.

            Kyawawan idanunta masu zubin gold ta narke masa tana kallonsa cikin salon kallon tuhuma,takuma maqale kafadarta tana kebe baki,sai ya daga hannayensa dukka biyun sama

“Am sorry baby” saita sake kafadarta ta fara takowar saidai har yanzu bata saki fuskarta ba.

             Kai tsaye tayi qoqarin shigewa jikinsa sanda ta iso abinda zai zata ba,tana shigewar ne tare da qoqarin kai idanunta kan allon computer dinsa,saidai tun kafin kwanyarta ta gama tantance komai ya saka daya hannun ya rufe system din ba tare daya kasheta ba,yasa daya hannun kuma ya riqota cikin jikinsa sosai yana jifanta da wani irin kallo

“Bansan lokaci ya tafi har haka ba baby” ya qarasa maganar yana kissing goshinta,a shagwabe tace dashi da muryarta dake da wani irin zaqi da taushi

“Duka cikin satin nan haka kake mun,bansan yaushe na koyi bata lokaci akan computer da waya ba…… nidai ka gayamin,ko wata ka samo?”. Tsam ya janyeta daga jikinsa yana duban qwayar idanunta,yanayin fuskarsa ya canza daga walwala zuwa wani yanayi na daban,idanunsu suka sarqe waje daya,sai ya girgiza mata kai

“Banason na qara jin wannan kalmar daga bakinki,ina dake ta yaya idanuwana zasu iya ganomin wata macen?,kinsan matsayinki a raina kuwa?,kinsan yadda kike a zuciyata?,beside ma…..mu da muke qoqarin ganin munkai rayuwarmu wani mataki na kwatance……ina nake da lokacin da zan kalli wata diya mace?,wai kina tunanin a duniya ma akwai macen data kai kyanki kuwa?” Kanta ta cusa a qirjinsa dariya tana subuce mata,a duk sanda adam yake gaya mata irin wadan nan kalaman,tana jin kanta acan qololuwar sama,tana jin duk duniya babu macen da ta kaita sa’a,babu macen da tayi dacen mijin qwarai kamarta,tana jin cewa zata iya tsayawa takarar macen da tafi kowacce mace sa’ar miji a duk fadin duniya,zuciyarta kuma na sake nutsewa cikin shauqin son adam da kuma qara amincewa dashi da kuma sallama masa rayuwarta gangar jikinta dama komai data mallaka.

           Saman kanta ya dora nasa kan yana shafa sumarta da yake matuqar so yana kuma sake fito mata da abinda yake zuciyarsa a kanta,tayi shuru tana saurarensa,kowacce gaba ta jikinta tana saki cikin zallar shauqin so.

           Sun jima a haka kafin ya umarceta ta bashi ruwa a parlor,ta sauka a hankali ta fice tana takawa tana jinta kamar tana yawo a gajimare,yayin da shi kuma ya bita da kallo,yana jin sha’awarta na sake fusgarsa da wani irin shauqi a kanta.

             Kafin ta dawo ya kashe system din yama yi ready din kwanciya,ta hauro gadon ta tsiyaya ruwan ta miqa masa.

             Sai daya kammala sha sannan ya bata cup din yana cewa

“Wannan watan ya akayi salary dinku yayi delay?” Maida cup din tayi ta ajjiye,sanna ta juyo gunsa

“Sun shigo fa tun kwana uku,kawai na dan ari kudin ne na siya wasu abubuwa dasu,amma gobe nake sa ran zan tura main account din gaba daya”.

Page 35

        Fuskarsa tadan canza kadan har hakan ya bayyana qarara

“Me kikayi dasu da yafi abinda yake gabanmu muhimmanci baby?” Kai ta yada gefe tana dan murmushi kadan,adam da gaske yake,so yake yaga tabbatuwar mafarkinsu,ya bawa abin muhimmanci qwarai da gaske fiye da yadda ita din ta bashi,kodon akwai banbancin muhalli gidaje da yanayin rayuwa da dukkaninsu suka fito daga ciki ne?,batason gaya masa Afifa ta arawa,don babu jituwa ko kadan tsakaninsu,don haka tace

“Wasu gyare gyare namu na mata nayi dasu” a tausashe ya kamo hannunta ya sanya cikin nashi yana duban qwayar idanunta

“Idan kikaji ana batun ready made to kece,ke din baki buqatar wata kwaskwarima ko sauran gyara,ko yaushe cikin kyau da daukan hankali kike baby,so please mu maida hankali mu tara abinda muka tara mu gabatar da qudurinmu kafin cikar shekarun da muka dibawa kanmu” kai ta gyada tana dubansa,zuciyarta na qara aminta dashi,ci gabansu yakeso da gasken gaske ita da dukkan abinda zasu zo nan gaba ta tsatsonta,akwai masoyi sama da haka a rayuwa?.

“In sha Allah,hakan bazai kuma faruwa ba” kai ya jinjina yana sakar mata murmushin nan nasa gami da gyada kansa.

             Suna shirin kwanciya ya saka hannunsa da sauri ya jawo locker din bedside dinsu ya ciro wani dan kati,sai ya fiddo idanunsa duka waje

“Kaiiiii!” Ya fada yana dafe kai,ta daga idanu tana dubansa sanda take zura santala santalan qafafunta cikin duvet

“Me?” Ta jefa masa tambayar tana kallon yadda ya dafe kai

“Yau ya kamata ace kinje allura,ni dake duka mun sha’afa” ya qarasa maganar yana ritsata da idanu jikinsa adan sanyaye,ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi,tadan juya qwayar idanunta sannan tace

“Shine duka hankalinka ya tashi haka?” Fuskarsa yadan sake hadi da qaramin murmushi sannan yace

“Banaso a samu matsalane baby”

“Matsala kuma?,kamar ba miji da mata ba?,kana tunanin duk babyn da zamu samu a yanzu ba zamu iya daukan nauyinsa ba?” Kansa ya girgixa a nutse ya maida katin saman drower din ya ajjiye yana duban idanunta

“Ba haka nake nufi ba…..amma kinsan komai yana da lokaci,kuma komai idan aka tsarashi yafi zuwa ta dadin rai” iska ta furzar daga bakinta tana dubansa,duk cikin tsarukan adam wannan ne kadai baiyi mata ba,wannan ne kadai takejin rawar zuciya da rashin tsaiwar hankalinta a kansa,har yau har kwanan gobe ta gaza sabawa,ta kasa jin gamsuwa da nutsuwa da hukuncin,duk kuwa da cewa ta gaza musanta masa ko qalubalantarsa,tasan koda tayi yunqurin hakan yana da tarin hujjojin da zai bata da zasu mamaye tunaninta

“Ko baka da wanann halin na tabbatar ina da gatan da bazan rasa komai ba” kansa ya fara girgizawa da sauri

“Noooo…..Allah ya kiyaye,ta yaya hakanma zata faru?,ya za’a yi nabarwa wasu hidimarki?,har abada,meye amfanina baby?,karki qara fadin hakan,inason na nunawa duniya ne i can make it happen,i can do it,we shall live happily,wannan din akwai lokaci na musamman dana tanadarwa zuwansa” kyawawan idanunta na saman fuskarsa tana dan lumshesu da budesu, zuciyar ta na bata mabanbantan ra’ayi,ta yaya zaka tsarawa kanka abinda Allah ne kadai yake da ikon tsarawa bawa?,ta buda baki a hankali zatace wani abu,sai yasa tafin hannunsa ya rufe tausasan labbanta yana girgiza kai,sannan daga bisani ya birkitota jikinsa yana lullubeta da soyayyarsa.

*_W A S H E G A R I_*

         Shirye take tsaf cikin wata lafiyayyar lafaya wadda ta kusan zame mata al’ada sanyatan,a duk sanda ta sakata din kuma sai kamanninta su canza,ka rasa fahimtar da wanne yare zata dangantata,wani irin kyau shigar take mata mai daukan hankali.

           Golden yellow ce da aka yiwa ado da brown color,dukkan takalmi jaka da dan kunne zuwa sarqa da tayi amfani dasu sunyi matuqar dacewa da shigar tata.

           A nutse suke takowa ita da adam din suna hira qasa qasa,sanye yake da joggers pants dogo har qasa da kuma wata shirt me gajeran hannu,hannunsa yana riqe da hand bag dinta,daya hannun nasa kuma yana riqe da key din motarta,cikin kulawa tamkar wani bodyguard dinta.

         Da kansa ya bude mata motar ta shiga ta zauna,sannan ya zagaya ya ajjiye mata hand bag din a kujerar me zaman banza,ya kuma durqusa saitin window din yana jifanta da wani narkakken kallo

“Karfe nawa zaki dawo?” Murmushin nan dake qarawa fuskarta kyau da daraja ta saki

“Zan iya kaiwa yammaci,inason na biya ta gidan momee” kai ya jinjina

“Banjin yau zan fita,inaso na huta,naso mu kasance tare,amma ba damuwa,da yammar ki zauna zan shigo gidan saimu wuce tare” kai ta jinjina masa,yayi kissing hannunsa ya hura mata iskar sannan yaja da baya,ta saki murmushi ta maida masa martani,ta kunna motar yaja baya ta tasheta ta fice a gidan a hankali.

          Ajiyar zuciya ta saki idanunta nakan titi,kwanya da zuciyarta gaba daya ba abinda take bita sai kyakkyawan xaman dake tsakaninta da adam,wani irin zama me cike da fahimtar juna qauna tausayi da zallar soyayya,iyakar zamansu na shekara biyu ba zata iya tuna ranar data bata masa rai ko ya bata mata ba,kullum ita dashi cikin tattalin junansu suke.

           Lallausan sautin wayarta ya katse mata tunaninta,ta dan dubi wayar kadan dake gefanta,sunan BESTIE A ya bayyana kan screen din wayar,ta saki murmushi har qaramin bakinta yana motsawa,ta miqa hannu ta daga wayar ta sakata a handsfree.

            “Zaki shigo kuwa?,ko oga adam ya hanaki?” Murmushi ya qwacewa Saahar

“Hooo afifa ta adam…..”

“A’ah…..adam dai na saahar,bar wannan zancan” ta katsi numfashinta,da alamu batason zancan

“To shi kam baice komai ba,infact ma ina kan hanya,ina fatan kina gida baki wuce zoo road din ba”

“Eh bankai ga tafiya ba,daman yau sai dare nake da niyyar tafiya”

“Okay saina qaraso” daga haka ta gimtse wayar ta ajeta a gefe tana dora dukka hannuwanta kan sitiyarin ta dafeshi,ta sauke ajiyar zuciya sosai,tana mamakin irin wannan rashin jituwa tsakanin adam da afifan,ta sani adam yana tsananin sonta,yana kuma yin komai don ita da kuma girman qaunar da yake mata,yayin da afifa take challenging duk wani tsari ko shiri na adam din,komai nasa baiyi mata ba,bai kuma dace da tsari da kuma hasashen da takewa rayuwar saahar din ba,saidai dukkaninsu ta yiwa kowa uzuri,ta tabbatar dukkaninsu qaunarta a zukatansu ne ta kawo wannan sabanin a junansu.

            Tafiyar mintuna talatin kacal ta sadar da ita da shagari quaters,ta gangara layin dake shimfide da kwalta,gidajensa bisa tsarin da kana kallo kasan kusan dukka mazauna wajen suna da sukuni na rayuwa.

            Gida me lamba 0009 ta tsaida motarta ta danna horn,babu jimawa mai gadin gidan ya bayyana,ya kuma dage qofar gidan cikin gaggawa sakamakon gane motar da yayi,ya maida qofar ya rufe bayan shigewarta da sauri yabi bayanta.

            Duk da kasancewarsa ya fara manyanta amma hakan bai hanashi bude mata qofa ba yana fadin

“Barka da zuwa uwar dakina” yayi maganar yana dariya,ita dimma murmushi takeyi

“Baaba habu barka kadai,lallai yau nazo a sa’a,kamar kowa yana gidan ko?” Ta fada tana bin rumfar adana motocin dake gidan da kallo,wadda ke dauke da motocin uku na baqi,sauran kuma duka motar mai gidan da matar gidan ne

“Aikuwa duka basu jima da shigowa ba,sunzo alhaji dr ne” idanu ta fiddo adan rude

“Me ya samu abban?”

“Ba komai fa,jiya ne yadan kwana da zazzabi” da sauri ta fita a motar baaba habu ya kulle mata,ta bude jakarta ta cire kudi ta miqa masa

“Ayiwa iyali cefane” hannu biyu yasa ya karba yana kwarara mata godiya,bata tsaya saurarensa ba,don idan da sabo ta saba da godiyar baaba habu da bata qarewa.

“Allah ya tsareki ya kareki daga dukkan abunqi da kuma sharrin me sharri” ya furta yana juya kudin a hannunsa,ya jima baiga mutane masu kirki da karamci ba irin ahalin gidan Dr Mamman girema ba.

“maama” ta fada da hanzarinta sanda take shiga falon,saika dauka sun dauki wasu shekaru basu hadu ba,zallar kewa da kuma qaunar ganin mahaifiyarta ya bayyana muraran a muryarta,kiran kuwa ya iske matar har cikin kitchen dinta dake falon,tayi hanzarin daukar butar shayin data cika da zazzafan baqin tea wanda yasha hadin kayan qamshi masu kwantar da hankali ta fito tana cewa.

           Fara tasss kamar diyarta saahar din,doguwa ce itama,amma shekaru da girma sun sanyata tayi jiki,duk da bamai yawa bane amma ya hadiye tsahon nata kaf,saita shiga jerin sahun mata masu matsaikatan tsaho kamar saahar din,kallo daya zakayi mata kasan cewa ta zuba tashen kyau qwarai da gaske zamanin quruciya kamar yadda diyarta a yanzu take.

“Eheeennn….aifa saike saahar,bansan ranar girmanki ba” ta fada murmushi na fita a fuskarta.

         ƙanƙameta tayi sosai kamar zata koma cikinta

“I miss you maama”

“Sakeni saahar,kayan ruwan zafi ne a hannuna” sakin nata tayi tana gaidata,sannan ta karbi kayan hannun nata suka jera zuwa falon Dr,cikin sakalci take qorafi

“Yanzun abba baiji dadi ba amma maama a rasa me gayamin,banda Allah ya kawoni?”

“Bafa wani ciwo bane,zazzabi ne da ciwon kai,kuma hakan baya rasa nasaba da stress da rashin hutu”

“Amma ya kamata zuwa yanzu abba ya zauna ya huta,me yake nema Allah yayi masa komai” dan kyabe baki maama tayi

“Naji su yasir na magana akai,ban sani ba ko yanzun zai yarda ya huta din” daidai lokacin da suke isowa qofar falon,maama na gaba saahar din tana biye da ita.

           Dattijon da duka duka shekarunsa ba zasu haura hamsin da takwas ba,zaune saman luntsuma luntsuman sofa’s dake zagaye da qawataccen falon.

Page 36

         Daga gefansa Aafiya ce durqushe saman qafafunta,matashiyar da suke sa’anni ita da sahar din,baqar fata mai haske gareta sabanin saahar dake fara tasss,saidai komai nasu kusan daya ne,kama daga tsahon da girman jiki,sanye cikin wasu gray material da aka yiwa dinkin riga da skert budaddu,tarkacen takardun abban take hadawa,daga daya hannun nasa kuma yaaya saifullah ne yake zare abun auna bugun zuciyar daya cusa qasan abun awon jinin daya nada a hannun abban,wannan kusan ba sabon abu bane,kusan duk bayan wani lokaci yana yima abban irin wannan gwajin,na hawan jini dana suger saboda kula da lafiyar abban,duk da bashi da komai daga jinin har sugar din,Allah ya bashi cikakkiyar lafiya.

           Daga saman daya sofa din kuma yaaya muhyiddeen ne zaune,gefansa yaaya zainul-abideen da suke kira da yaa zain,dukansu hira suke a tsakaninsu,fuskar kowa qunshe cikin walwala da farincikin dake nuna zallar sukunin rayuwa da kwanciyar hankali daya samu matsugunni cikin rayuwar kowannensu.

           Hawaye taji yadan tsatstsafo cikin idanunta,sai taji tayi missing gidan dama kowa da kowa,harda rayuwarta ta baya,ada ita keda wannan matsayin,ko yaushe tana daga gefan abban tana kula da buqatunsa,yanzu kuwa aure ya nesantata da komai dama kowa.

          A shagwabe ta qarasa shigowa falon,ta kuma isa gaban abban daya tarbeta da dukkan kulawa,abu na farko ta fara qorafi akan rashin sanin rashin lafiyarsa

“Jiya ne kawai amma kinga yadda suka sanyani gaba”

“Me zakizo kiyi to,bayan gamu duk munxo?” Yaaya zain ya fadi,duk da ya girmeta,infact itacema qarama,amma time to time sai ya dan xungureta sunyi fadan sako da sako.

         Baki ta tabe ashagwabe

“Ni kaina na sani da abbana kawai”

“Gaskiyarki auta ina bayanki” yaaya  muhyiddeen ya fada yana murmushi,ta waiwaya tana sake masa murmushi

“Yauwa yaaya na na kaina” yaaya saifullah ne baice komai ba kasancewarsa shine babba,sai ta waiwaya tana gaidashi bayan ta gaida abban tayi masa sannu da jiki,ta gaida kowa ta waiwaya ga Aafiya

“Babu ko maraba bestie”

“Goyaki kawai zanyi yanzun nan,shine abinda ya rage ki gane nayi murna da zuwanki” dariya duka falon aka saki,don tsakanin Aafiya da saahar babu me shiga.

           Shigowar saahar ya sake jinkirta tafiyar yayun nata,a nan suka sake sabon breakfast gaba dayansu,duk kowa ya cika cikinsa a gidansa kafin fitowarsa,basu watse sunbar falon ba sai kusan qarfe daya saura bayan abba Dr yasha maganinsa yadan kwanta.

            Suna isa dakin aafiya dake gidan ta fara warware lafayar jikinta gami da warware agogon dake daure a tsintsiyar hannunta

“Bestie….bari nayi alwala nazo ki gyaramin kaina don Allah,ya dameni wallahi kwana biyun nan” idanu Aafiya ta fiddo

“Hala kin manta santsi da tsahon gashinki,sai yaushe zamu gama aikinsa” karyar da wuya tayi

“Haba mana bestie…..”ta fada a karye

“Ya na iya dake,ina hutun sallah,idan kin fito sai muyi” Aafiya tayi maganar tana nutsewa cikin sofa din dakin gami da jan wayarta ta soma dannawa.

          Tana idar da sallah Aafiya ta fara gyara matan,tanayi suna taba hira,abunda ya daukesu mai tsaho,sanda suka gama data duba agogo saita fidda idanu waje,ita da zataje asibiti allura?,lokaci ya qure tasan yanzun haka nurse din dake mata allurar ta tashi,batason kuma yauma su sake missing allurar kamar jiya,ta fuskanci hankalin adam bazai kwanta ba sai ta tabbatar masa tayin

“Bestie taimaka kiyimin allura mana” sosai ta waiwayo tana duban saahar

“Allura?,baki da lafiya ne?” Aafiya ta jefa mata tambayar dai dai sanda take amsar allurar daga hannun saahar.

            Juya allurar ta fara yi tana kuma qoqarin karantar allurar meye,dukka idanunta ta fitar waje,cikin mugun gigita ta watsasu kan fuskar saahar

“Wannan allurar kice?,ko acan pharmacy din sukayi mistake din baki ita?”

           Janye idanunta saahar din tayi daga kallon tuhumar da Aafiya keyi mata,bayan ta tsareta da dukkan kallo na idanu da kuma kunnuwanta,sam ta sha’afa cewa wani babban sirri ne,sirri ne da suka tsarashi tsakaninta da adam,bata tunani duk duniya akwai mahaluqin da yasan da wannan babban sirrin idan ka dauke  mommee din adam din

“Allurar planning bestie?,tun yaushe kika fara?” Aafiya ta jefawa saahar tambayar tana tsareta da dukkan wani kallo dazai nunawa dan adam tsantsar tuhumar da ake masa mai tsananin qarfi da kaifi.

            Shuru saahar tayiwa Aafiya ba tare data amsa mata ba,yayin da Aafiya taci gaba da tsareta da kallon tana jin wani daci yana ratsata har saman harshenta,kwanyarta ta cika da nau’ikan tani iri daban daban,zuciya nata yi mata hasashe kala kala.

          Tasan saahar sosai har fiye da yunwar cikinta,shurun da tayi yana tabbatar mata da cewa batayi shirin amsa mata tambayarta ba,kuma muddin ta kafe akan abu,la shakka bata isa ya juyata kota sauya mata ra’ayi ba,don haka ta kwantanta yin barazana gareta ko zata samu taji bayanan da zuciyarta keda muradin ji daga bakin ‘yar uwartata. Wannan ya sanya ta miqe tsam da allurar a hannunta tayi qofar fita a dakin.

          Cikin wani irin zafin nama da dukkaninsu basusan saahar din tana dashi ba ta miqe,cikin matuqar sa’a ta samu nasarar cafkar hannun Aafiya

“Ina zaki?” Waiwayowa tayi ta watsa mata wani kallo

“Zanje na nunawa maama da abba abinda kike aikatawa kanki”

“Baki da hankali ne?”

“Nice bani da hankali ko kuma kece saahar?” Ta kirayi sunanta kai tsaye abinda ba kasafai take yinsa ba.

          Ta fahimci Aafiya takai qololuwar fushi,kuma bata da sauran zabi illa ta gaya mata abinda take da buqatar ji din

“Zauna sai muyi magana a nutse”

“Bazan zauna ba har saikin gayan komai,yaushe kika fara wannan allurar,keda ko bari baki taba yiba tsahon shekara biyu da aurenki,muna nan munata addu’ar ganin qwanki a duniya?”

“Satin farko na aurena” sosai maganar ta daki Aafiya,har sai data dan ja baya kadan,to amma tana buqatar samun cikakken qarin bayani daga bakin saahar din don ta samu makama

“Satin farko kuma?,shi adam din ya sani ko munafuntarsa kike?” Gyara zama tayi tana jin tambayoyin Aafiya sunkai mata ko ina,ta gaji da jera mata tambayoyin da taketa faman yi

“Kin fiya takura da zaqule zaqule,xama mukayi mukayi shawara muka yanke hakan ni dashi,duka duka saura watanni kadan watannin da muka diba su cika na dainayin allurar gaba daya,so please don Allah banason kowa yaji zancan nan,tunda dai mun kusa kammalawa”.

             Tashin hankali sosai ya shigi Aafiya,ita da tayi karatun lafiya tasan illar da hakan zai iya haifarwa da saahar,ta sani…..saahar ta saya ne kawai,ba zancan tare da adam sukayi shawarar aikata hakan,tunda duk mahaluqin daya kwana ya tashi yasan saahar din mada mugun son yara kamar me,tana iya yin komai saboda yara,tana kuma iya barin komai saboda yara,naturally ma akan ce dukka wani ko wata auta suna da son yara,to na saahar har ya wuce misali,abun kamar cikin jininta ne,ada maama ta dauka iya na quruciya ne,saidai har girmanta har zuwa aurenta abun yana nan tare da ita,to ta yaya koda dukka jikinta kunne ne zata amince saahar zatayi planning bisa radin kanta?.

          To amma koma meye a yanzun tashin hankali ba nata bane,idan illa take gudarwa saahar kome meye zuwa yanzu allurar ta dade dayi mata,fada tashin hankali da masifa ta tabbatar ba zasuyi tasirin komai ba,ta sauke ajiyar zuciya bayan dabara ta fado mata,ta dawo a hankali jiki a sanyaye ta zauna daga gefan saahar,ta kamo dukka hannuwanta ta sanya a nata

“Idan wani ya fahimceku bestie wani bazai fahimceku ba,idan wani bai zagi adam ba wani zai zageshi,don me kina da buqatar irin wannan allurar kinsan zan iya yi miki amma baki nemana nayi miki asirinku a rufe basai sun fallasa sirrinku ba?” Sosai maganar ta bawa saahar mamaki a yadda tasan hali da dabi’ar Aafiyan tata,ta kafeta da idanu,wani sashe na zuciyarta ta gaza gasgata zancan afiyan,wani bangaren kuma na gasgatata,tunda ita din kaifi daya ce,bata qarya don a sota,hakanan duk yadda magana takai ga rashin yi maka dadi zata gayamaka ita muddin dai gaskiya ce.

             Hannuwanta ta kamo cikin son gamsar da saahar din tayi yadda takeso

“Wannan din sirrinku ne,kuma sai amintaccenku ya kamata ya sani,tashi nayi miki” ta qarashe maganar tana sakin hannayen saahar din,ta soma zuqe ruwan allurar cikin syringe tana mita

“Shekara biyu amma bestie ace kina da wani sirri da kike boyemin,duk yadda muke dake,na sake yarda adam ya shiga tsakaninmu” sai zuwa sannan tadan saki murmushi,idan da sabo ta saba jin wannan tababar da suke akan juna,aafiya na qorafi akan adam koda yaushe,kamar yadda adam ke qorafi akan aafiya,batasan yadda zata hada kawunansu su fuskanci juna ba.

          “Next month idan kin tashi zuwa ki sameni a asibiti,don banason maama ta gani ta tambayi ba’asin yin allurar”

“Wai meye ya sanyaki saukowa haka da wuri bestie?” Saahar ta jefawa aafiya tambayar da tun dazun take cin zuciyarta,ta kuma shiga cikin kokwanto

“Saboda inason abinda bestie na takeso,kinason adam,kinason duk abinda yakeso,ni kuma inason bestie na,kuma dole na tayata son duk abinda takeso muddin da gasken ina sonta”ta amsa mata kai tsaye idanunta cikin qwayar idanun saahar.

          Janye idanunta tayi daga na Aafiyan tana son gamsar da kanta da gasken aafiya take,don ita din kaifi daya ce,dadi ko wuya basa sakata canza ra’ayinta.

               Tana jin kamar kada ta tafi tabar gidan saboda tsananin sabo da kuma soyayyar dake tsakaninta da familyn ta,amma dole qarfe uku da rabi ta yiwa maama sallama

“Da wuri haka bestie?” Aafiya ta tambayeta sanda ta isketa tsaye a falo bayan shigarta kitchen kenan ta hada musu banana smoothie

“Munyi da adam zai sameni gidan momee da yammar nan,daga can saimu wuce gida” tabe baki Aafiyan tayi

“Ya kamata,muje na taka miki”

“To bani smoothie din na shanye mana kafin na tafi,kinsan akwai amana tsakanina dashi”

“Na zaci ai sauri bazai barki kisha ba” qaramin murmushi kawai saahar din ta saki,batasan me yasa duk Wani abu daya shafi adam ba aafiya bata maraba dashi,zuwanta daya tsahon shekara biyun nan gidansu adam din,ta kuma yimata rakiya da qyar,bayan sun fito kuma tayi shuru cikin mota kamar wadda ruwa ya shanye

“Yadai bestie?”

“Mamar adam din nan sam bata yimin ba,wai yaushe ta fara sonki ne bestie?” Aafiyan ta jefawa saahar dake driving tambaya.

            Dan qaramin bakinta ta bude cikin alamun mamaki sannan ta bushe da dariya,ta san halin Aafiya ba kowanne mutum bane yake mata a karon farko

“Ni banga aibun momee ba,bata da matsala,tana daukata kamar wata qawarta,bata taba takuramin ba,hasalima bata iya boyen duk wata damuwarta,so kuma ni dama bata taba nunamin qiyayya ba”

“K’nnnnn,haka ne” Aafiya ta fada a taqaice tana jawo wasu takardu dake ajjiye gaban motar sahar din ta tara dubawa,shuru ya ratsa motar kafin ta sake dago kai

“Waye zai bude joint account kuma?”

“Adam ne ya karbosu,bai gayan na waye ba yace na ajjiye masa kawai” saita gyada kai ta maida takardun da ba’a kai ga cikewa ba inda ta daukosu,ta gyara zamanta tana dauko wata hirar daban.

           Har bakin mota Aafiya ta rakota,saahar tanata mita

“Wallahi wallahi kin bani mamaki,ban taba zaton aure zai nesantamu ba,tsahon shekara biyu cur amma zan iya irga zuwanki gidana da yatsun hannuna?,wanne laifi mukayi miki?,tun adam na min qorafi har ya koma gorantamin kan cewa baki damu dani ba,ni daya na damu dake,ko yaa zain da yake namiji ya fiki zuwa gida na fa” qaramin murmushi Aafiya ta sake

“Ke kuma sai kika yarda da zancan adam?,ki rabu dashi so yake ya hadamu,aiki bestie kema kin sani,amma na miki alqawarin zuwa in sha Allah ending next month” hannu kawai saahar ta sanya tana rufe qofar motarta

“Kice kawai baki shirya zuwa ba,basai kin fitomin ta haka ba”

“Seriouse,Allah da gaske nake miki” ta fada tana dariya bayan taja ta bata hanya,tana nan tsaye har saahar dake galla mata harara ta mirror din motar ta fice daga gidan,Aafiya ta saki ajiyar zuciya sannan ta juya a hankali tana komawa cikin gidan.

             Minti ashirin kacal suka kaita unguwar sharada. Saboda ta danyi gudu ba laifi,bataso taje ta samu adam ya isa yana jiranta.

              A farfajiyar gidan ta tsaida motarta ta kasheta ta fito,ta fara takawa cikin nutsuwa da takuntan nan zuwa cikin gidan tana gyara laffayarta.

              Gab da zata qarasa qofar da zata sadata da ainihin falon gidan mata biyu suka fito,daya a gaba daya a baya,sai tadanja da baya ta tsaya don basu damar wucewa.

Page 37

         Ta farkon macace da aqalla ta doshi shekara hamsin da biyar,saidai a ido ba zakace haka ba,saboda yanayin yadda take,kallo daya zakayi mata ka fuskanci gogaggiyar macace wadda tasan kan rayuwa sosai,idanunta fes suke,akwai wayewa mai tsanani a tattare da ita,gajeriya ce mai gogaggiyar baqar fata,tana da manyan idanuwa da dogon hanci,wannan ya qawata mata fuska sosai,ta bayan nata kuwa doguwa ce,wannan itace momee din adam,wadda suke kama sosai ta fuska.

            “Kina hanya ashe?,har na fidda rai?” Ta fada cikin madaukakiyar fara’a,cikin kunya da kara irin wadda kowacce diya keji ga surukarta saahar tadan duqar dakai

“Ina hanya momee…..barka da yamma,ina wuni?” Ta gaida baquwar dake tare da momee din wadda ta kafeta da idanu cikin wani irin kallo na qurilla,har saahar din na jinsa har cikin jininta.

             Da sauri ta murmusa cikin nuna kulawa

“Lafiya lou,kina lafiya?” Ta amsa da hausarta data dan baci kadan,da alama su momee din sun fita qwarewa nesa ba kusa ba

“Lafiya lau alhmdlh”

“Ki shiga ciki bari na rakata na dawo” momee ta fada suna juyawa da baquwar

“Ina mamakin yadda adam ya samu kyakkyawar yarinya haka,kyanta na bani tsoro k……” Saahar ta jiyo muryar baquwar,wadda bata qarasa jin abinda take fadi din ba,katsewa tayi ko nisan data fara yi mata ne bata sani ba,ta sanya kai cikin parlor din momee din,wanda a yanzun ya zama abun sha’awa cike da kayan alatu.

             ‘yar budurwar da ake kira da raihanatu ta amsa sallamar saahar din cikin mayalwacin murmushi da kuma tarin kirki da girmamawar da takewa saahar,ta qaraso da sauri tana karbar ledar hannunta hannu bibbiyu har kamar zata kai qasa tana cewa

“Sannu da zuwa anty” cikin fara’a Sahar din itama ta maida mata

“Sannu raiha sarkin aiki,ya gida ya aiki?”

“Alhamdulillah anty,bari na kawo miki ruwa” ta yiwa ledar guri a wajen,ta juya da sauri ta doshi kitchen dinsu dake manne da parlor din,saahar ta bita da kallo.

         Yarinyar diya ce ga qanwar momee,momee din ta dauko riqonta,itake mata komai,kamar yadda yarinyar itama itace komai na gidan,yarinyar nada wani irin hankali kirki da kuma nutsuwa,bata da surutu sam,hakanan bata da shiga shirgin da ba nata ba.

         Cikin mintin da bai gaza daya ba raiha ta gabatar ma da saahar drinks masu sanyi hade da ruwa,tana murmushi tace

“Mun cinye abincin rana anty,bamu gama kuma na dare ba kiyi haquri” murmushi ya subuce mata

“Ni ba baquwa bace raihana,kada ki damu” ta girgiza kai tana murmushi itama,har cikin zuciyarta tana jin qaunar anty saahar din,saboda sauqin kai kirkinta kyauta da kuma kyautatawarta,matsayinta dana mahaifinta,kyawunta ko iliminta sam bai sanya mata girman kai ba ko jin ita din wata bace,uwa uba kuma yadda ta dauki momee din a matsayinta na surukarta.

         Bata taba komai a ciki ba,don ta fito gida a qoshe,har zuwa sanda momee ta dawo parlon ta zauna tana cewa

“Sannu da zuwa,har na cire rai ai” a kunyace saahar ta saki murmushi,tadan sunkui da kai tana murza zoben hannunta

“Ina sane momee,ga saqon nan” sosai ta washe baki cikin fara’a,ta miqe tsam ta dauko ledar da kanta tana budawa.

          Manyan kaji ne broilers da suka qanqare saboda dadewa cikin freezer,cikin ma’aikata gidansu ta sanya wata cikinsu ta ciro mata

“Allah dai yayi miki albarka,ai baqi nayi,duka naman gidan ya qare,gashi ni kuma banason girki babu nama ko kadan” saita qwalawa raiha kira,cikin minti daya ta iso gurin,harara ta jefa mata

“Kina abu kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,dauki wannan naman,ki cire wani daga ciki kiyimin farfesu”

“Tom momee” ta amsa a ladance,ta sukunya ta dauki ledar ta wuce kitchen din.

           Kamar ko yaushe hira sosai momee ke janta da ita,harda abinda saahar ke ganin bai shafeta ba,to amma tana baiwa momee din uzurin banbacin al’ada da yare dake tsakaninsu,sannan kuma irin wayewarta daban da wayewar sauran surukai data sani.

            Mafi yawa saidai ta amsa da eh ko a’ah,ko kuma tayi murmushi wani lokacin,tun tana zuba idon ganin adam har aka kirayi sallar magariba,a sannan raiha tayi mata jagora zuwa dakinta,duk da momee din tayi mata tayin shiga nata dakin tayi sallar amma sai tace a’ah,don ba zata iya sakewa ba.

             Sai a sannan ta samu sukunin kiran adam din,amma harta qaraci ringing dinta bai daga ba,ta haqura ta ajjiye wayar zuciyarta na gaya mata yana sallah ne hala.

              Tana idarwa ta sake gwada kirannasa,cikin sa’a ta shiga,ta bada dukkan hankalinta ga wayar tana jira ya daga.

             Dab da zata tsinke ya daga din,muryarsa can qasa yayi sallama,ta amsa masa cikin kulawa

“Nayita jiranka dear…..kuma baka shigo ba” dan gyaran murya yayi kadan

“Ban samu na fita din bama,throughout yau ina gida” hankalinta ya sake kaiwa ga muryarsa

“Lafiya kake?”

“Me kika gani?”

“Muryanka was so cool…..kaman jikinka ba qwari”

“Yeah…..bacci nayi ban tashi ba har yamma,shi ya kashemin jiki”

“Alright,na taho kenan?”

“No,ai nayi alqawari,zan shigo saimu dawo tare”

“Okay”

“I missed you” ya fada cikin tsananin kulawa, murmushi ya subuce mata

“I missed you too,saika qaraso” daga haka sukayi sallama ta ajjiye wayar taci gaba da lazuminta,lokaci lokaci tunani yana waftar hankalinta ya kaishi ga wani abu na daban,bata bar dakin ba har sai datayi sallar isha’i.

            A falo ta samu momee,ta baje dabgen kajin tana kaiwa ciki,tayi d’ai d’ai saman kujera kamar ita daya ta rage a duniyar.

            Raihana ta qwala kira har kusan sau uku a jere

“Maza hadawa diyata abinci taci” ta amsa a aladabce,ba jima ta dawo da babban tray ta ajjiye gabanta

“Zauna mana muci” saahar ta yiwa yarinyar tayi,saita girgiza kai,tamkar taga hararar da momee din ke watsa mata ta gefan ido

“Zanci nawa yanzu anty,wannan naki ne”.

             Batayi nisa dacin abincin ba ta qoshi,dama ita tun tale tale bata cikin sahun mutanen da abinci ya dama,tana rufe warmers din adam na shigowa.

          Hannayensa zube a aljihun wandonsa,cikin wasu shirt da trouser yake sanye,shi din gwanin wanka ne,akwai iya daukan ado me jan hankali,idanunsa a kanta,haka yake mata irin wannan kallon ko gaban waye.

          Kallo daya tayi masa ta dauke kanta daga sashensa,yayi mata kyau amma jikinsa babu kuzari kamar yadda taji dazu a waya,sai daya iso cikin Parlor din sannan yayi sallama yana laluben wajen zama,saahar din ta miqe tsam da tray din bayan tayi masa sannu da zuwa ta nufi kitchen dasu,duk da yadda momee ke cewa ta zauna raiha tazo ta kwashe.

              A kitchen din ta sameta ta gama cin abincin tana wanke plates din,da hanzari ta karba kwanukan tana mata sannu, murmushi saahar din tayi ganin yadda ta tarbeta kamar wadda tayi wani aiki me yawa

“Aike za’a yiwa sannu”sai kawai taja kujerar plastic ta zauna tana bin yadda raiha ke gudanar da aikin nata cikin nutsuwa,batabar kitchen din ba har sai da adam ya  leqo yayi mata magana.

             Sunyi gaba shida momee din,ta tsaya tana tattara jakarta data gani a bude,ta danyi mamaki,don tasan a zuge tabar jakar,to amma sai wata zuciyar ta bata may be ta manta ne,a buden ta barta,tunda babu wani baqo cikin gidan bare parlor din bare ta zargi wani abun.

           “C’mon momee,please kibar maganar nan” muryar adam kenan dake fita a kasalance idanunsa nakan saahar dake fitowa,waiwayowa momee din tayi kafin ta maida dubanta ga adam

“Okay,amma kayi tunani akai ka gani,think twice kafin yanke hukunci”

“Nasan abinda nakeyi fa” ya amsa mata kai tsaye yana dosar motar saahar da key din ke hannunsa,ya buda mazaunin mai zaman banza yana jira isowarta.

            Sai data yiwa momee saida safe,ta rakata da addu’o’i kamar zata rusuna mata har qofar motar,saahar din ta shige a kunyace kan yadda momee din ke mata,sannan ya zagaya shima ya shiga seat dinsa,ya tayar da motar suka fice a gidan.

            Shuru ne ya ratsa motar,tunanin saahar ya dauketa ya wulwula da ita can baya,wasu watanni masu dan dama da suka shude cikin rayuwar aurenta da adam,koda cikin tarin mafarkai,bata taba tsammanin zatayi mafarki guda daya da zai nuna mata nan gaba momee zata sota ba,zata amsheta hannun bibbiyu a matsayin suruka ba,sai gashi a yanzun……cikin wani hali da yafi kama da juyin juyi momee ta amsheta har fiye ma da yadda take nunawa adam qauna da kulawa,duk da kasancewarsa tilon d’a a gareta.

            Saukar hannun adam saman nata hannun ya fargar da ita,ta waiwayo ta zube masa kyawawan idanunta da suka tilasta masa lumshe nasa idanun

“Yaadai?,akwai matsala ne?” Tattausan murmushi ta sakar masa tana girgiza kai

“Babu” sai yaja hannun nata zuwa bakinsa a tausashe yayi kissing bayan hannun,wani abu ya sauka a zuciyarta,ko yaushe adam baya gajiya da ita,hakanan baya gajiya da bayyana zallar soyayyarsa a gareta.

********Misalin qarfe shida ne na yamma,dai dai lokacin babu abinda gidan yake fitarwa sai daddadan qamshin turaren wuta daya wadaci kowanne lungu da saqo na gidan,sai sauran burbushin qamshin daddadan abincinta da tuni ya gama zama ready saman dining table.

            Saahar din irin matan nan ne da suka kai sunan mata ta kowanne fanni na rayuwa,suka kai qololuwa gurin iya zamantakewar gidan aure,suka kuma qware tare da ci gaba da neman sani cikin kowacce rana ta ubangiji ga dukkan macen data amsa sunanta,ta kuma qware gami da sanin dukka hanyoyin kyautatama miji,tare da zama tauraruwarsa.

           Tun daga abinda ya shafi kyan sura,gayu dake cakude da ilimi da kuma tsantsar tsafta,kawaici haquri da iya mu’amala,uwa uba iya girki da kuma gyaran kai kowanne lokaci lungu da saqo,ta yadda zata dace da muradin adam,tasan yadda zata hadawa kanta nau’in dukkan wani abu da zai daga martabarta da darajarta na diya mace awajen miji.

          Idan ka shigo gidan ka sameta kaga yadda take tafiyar da gidanta cikin tsari da nutsuwa ba tare da ta buqaci me aiki ba zakiyi matuqar mamaki,duk da tarin gata da dukiyar da mahaifinta keda ita,amma wannan sam bai sanya ta dauki kanta takai wani bigire ba,tana ganin cewa cinyewar rayuwar mace a gidan aurenta shine ta bautatawa mijinta,tayi hidima cikin gidanta da dukka jikinta da hannuwanta.

             Kamar yanxun data kammala komai,tana sanye da wata gown ta wani farin material me santsi qal dashi,ta daure sassalkan gashinta cikin farin ribbom daya dace da rigar jikinta,jikinta na fidda wani sihirtaccen qamshi da babu lallai ka iya tantance ainihin turaren da tayi amfani dashi kai tsaye,qamshine mai tafi da zuciya da tsayawa arai,tana qaunar qamshi har batasan iyaka ba,zata iya saka ko nawa ne ta siyi turare muddin qamshinsa ya dace da tsarinta.

             Tana shirin zama ta tuna bata hada ruwan wankan adam din ba,saita aje wayar hannunta,ta juya cikin tafiyarta me kama da na me tausayin qasa ta wuce dakinsa sannan ta zarce toilet dinsa.

             Daga ciki ta jiyo qarar sautin wayarta,ta goge hannunta jikin rowels din dake rataye a bandakin cikin tsari,wanda da kanta ta zabarwa kanta tsarin duka toilets dinsu,take kuma kula dasu kamar ba muhallin qazanta ba saboda yadda suke samun kulawa.

               Special tone ta sanya masa,don haka kafin ta qaraso ta fahimci wanda yake kiran, murmushi ya subuce mata,ta juya qwayar idanunta sannan ta daga wayar ta kara a kunnenta

“Amincin Allah ya tabbata a gareka”

“Tare dake mace daya tamkar da dubu…..nazo wuce wani fish park ne naga suna gashin kifi,kina da buqata ne?” Take taji yawunta ya tsinke,ta tuna wanda taci shekaran jiya kamar ta tsinke harshenta,tunda take bata tana craving na kifi irin wannan karon ba

“Na gode qwarai da gaske dear,ina buqata idan har zan samu”

“Kin samu ma matar aljanna,kinfi gaba haka,kinfi qarfin ki nema abu ki rasa” ya fada a tausashe,sautin murmushinsa yana isa kunnuwanta,idanunta ta juya dadi yana dada ratsata,idan tace duk duniya babu miji kamar nata to ba shakka batayi kuskure ba,batajin a wannan lokacin akwai miji kamar nata,ko yaushe soyayyarsa a gareta sabuwa ce,kulawar data tabbatar mata da yawa sun rasata,wasu kuma suna kewarta,batasan dame zata amsa masa ba,saidai farincikin da takeji wanda a kullum baya gajiya da sanyata a cikinsa,a haka ya barta da waya a hannu tanata smiling,kafin daga bisani ta zame wayar daga kunnenta,ta koma ta zauna saman kujerar ta zauna,sannan taja wani english novel tana dubawa qafarta daya saman daya tana jiran qarasowarsa.

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 38

          Horn dinsa kadai ya isar mata da saqon dawowarsa,ta ajjiye littafin a gefanta ta miqe a nutse tana takawa zuwa farfajiyar gidan.

            A tsakiya suka hade, yasa dukka hannayensa biyu ya tarbeta,ya dagata sama cak yana dariya

“Na jima banga macen da bata da nauyi kamarki ba”  dubansa tayi sosai da dukka idanunta,saiya lumshe idanunsa yana jinjina mata kai

“Ka jima kuma?,akwai wata ne bayan ni?” Idanunsa dukka ya ware yana dubanta gami da girgiza kai

“Babu,har abada kuma ba za’a samu ba,idan mutane na cewa kada ki yarda da mijinki muddin zaice miki bayanke babu qari,banda adam a ciki,ki rubuta ki ajjiye,ina miki magana ne kan qanne na da nake dasu wanda momee ta riqesu kafin daga baya ta aurar dasu tun a ghana” murmushi ta saki tana saqalo wuyansa

“Nima nafison na zauna a haka,don banason ka daina daukata” ta fada tana langabe kai.

             Dariya ya saki yana duban idanunta

“Kina tunanin akwai qibar da zatayi sanadin da zan daina daukan matata masoyiyata?,babu ita,muje ciki na baki kifinki” daga haka ya taka da ita zuwa ciki suna hira qasa qasa.

            Tun hankalinsa baikai kan yadda take cin kifin hannu baka hannu qwarya ba har ya ankara,ya tsaya da abinda yakeyi yana kallonta,sai ya kama hannunta da take qoqarin kaiwa baki ya riqe yana dubanta cikin kokwanto,suka hada idanu saita sakar masa murmushi

“Please dear,don Allah ka barni na qarasa mana”

“Yaushe kika zama hadamammiya ne?” Wuyanta ta langabe tana kallonsa

“Nima ban sani ba,kawai dai na wayi gari inason kifi fiye da komai” hannun ya sakar mata,sannan ya koma da baya ya zauna yana fuskantarta,yanayin fuskarsa yana dan canzawa kadan bada wani alamu me yawa ba

“Tun yaushe?” Ya jefa mata tambayar,wanda ita tuni taci gaba da cin kifinta,ta daga kai suka hada ido

“Dearrrr…..ka bari na gama tukunna,ban qoshi ba Allah” shuru ya danyi yana ci gaba da kallonta,kafin ya miqe yana zare kayan jikinsa saboda wanka da yakeson shiga.

            Tun daga shirinsa zuwa zaman cin abincinsa da shirin kwanciya baccin da sukayi ta lura kamar kuzarinsa ya ragu,da tayi complain sai yace

“Yau nayi overwork baby,jikina duka ciwo yakemin” tsam ta miqe,ta shiga kitchen ta hada masa ruwa me dumi,daga gefansa ta zauna ta miqa masa mug din

“Ga wannan kasha,yana sauke gajiya” kurba daya yayi ya miqa mata,saita langabe kai tana kallon fuskarsa

“Ai baka sha ba dear” kansa ya girgixa yana dan qaramin murmushi

“Cikina ya cika fa,ko kin manta abinci na gama ci yanzu?,ba space,hakanma is okay,thank you”.

           A sanyaye ta sauka daga saman gadon,yadan bita da kallo sannan ya gyara zamansa sosai saman gadon yana dubanta

“Yauwa kafin ki fita kiban wancan briefcase din,ki dawo a kitchen din kizo ki gani” miqa masan tayi taje ta ajjiye mug din a kitchen din sannan ta dawo,ta zauna daga gefansa tana kallon takardun daya fito dasu.

           Biyu daga ciki ya zaro ya miqa mata,ta karba amma tana masa duban neman qarin bayani

“Wadan nan filayen ne da mukayi zamu siya ni dake,an gama cinikinsu kamar sauran,ga takardun ki saka hannu” a nutse ta karanta rubutun dake jikin takardan,kamar kullum kamar kuma ko wanne lokaci,duk sadda suka siya wata kadara tare dashi,maimakon sunansu su biyun sunanta yake sanyawa,tasha masa qorafin shi da ita duk daya ne,koda sunansa ya saka dinma ai babu laifi.

             Motsa bakinta tayi,yasan qorafin data saba zatayi masa,sai ya saki murmushi ya daga mata hannu

“Bazan fasa saka sunanki ba fa,karkiyi ma magana,don na saka sunanki sai meye?,komai dana mallaka naki ne fa,bare ni dake din mun riga mun zama abu daya,saka hannu kawai” ya fada yana miqa mata biro,cikin sanyin jiki tare da jinjina qauna soyayya da kuma fahimtar juna me zurfi dake tsakaninta da adam din ta yi signing da signature dinta,wata irin sign me matuqar kyau da tsari,ta miqa masa takardun tana cewa

“Allah yasa musu albarka…..ina alfahari da irin tunaninka da qoqarinka” ta fada tana jinjina kai,tsarin daya kawo musu naci gaba ita sam bata taba kawowa ranta tayi hakan ba,daga aurensu zuwa yanzu suna da filaye masu suna filaye da suka hada kudi suka siya masu yawan gaske,hakanan zunzurutun kudin dake join account dinsu dake maqare da kudin da suke zubawa duk wata daga cikin albashin kowannensu,wanda dashi suke saka ran amfani da filinsu da yafi kowanne girma su tayar da ginin katafaren kamfani.

            Murmushi yayi bayan ya mayar da takardan cikin takardunss,ya sanya hannunsa ya rungumeta tsam cikin jikinsa yana shaqar lallausan qamshinsa

“Ni yafi dacewa nayi wannan godiyar” saita kwantar da kanta saman qirjinsa tana sakin murmushi,zuciyarta fes,cike da zallar farinciki hadi da samun nutsuwa da cikakkiyar gamsuwa da kalar mijin da take da.

***********Tsaye tayi bayan gama wanke mata kan tana goge ruwan kan nata da qaramin towel don dake saman kanta wanda ke dauke da tambarin katafaren gurin gyaran kai da jiki na mata Thairaphy saloon and spa,zare towel din tayi ta ajjiye,afifa dake zaune tana duba wani magazine ta daga kai tana dubanta

“Ya dai”

“Kifi zanje nemowa,nan haka nasan ba za’a rasa ba” ta fada tana maida rolling Vail dinta saman gown din jikinta da hanzari, rufe magazine din afifa tayi tana kallonta

“Amma kinsan ba’a yi gyaran jikin ba ko?,karmu bata lokaci fa”

“Manta kawai,yanzu zan dawo” ta fada tana zaro key din motarta daga jakar,cikin sauri ta nufi qofa

“Bansan qaunar data shiga tsakaninki da kifi ba”

“Nima haka”ta bata amsa a qagauce,sai afifan ta bita da kallo,wani abu ya darsu a ranta, murmushi ya qwace mata tana jinjina kai

“Allah ameen”ta fada tana ci gaba da gyada kai kamar qadangaruwa,kafin muryar daya daga cikin ma’aikatan dake wajen ta katse mata tunani,ta miqe tana zare nata dankwalin,gashinta me cika da tsaho ya bayyana,ma’aikaciyar taja mata kujera ta zauna aka fara gyara mata nata gashin.

           Afifa na zaune daga saman kujerar tana karantar yadda saahar kema kifin wani irin ci,zargin dake ranta yana sake tabbatuwa,iya saninta da asaahar bame ciye ciye bace,hasalima ko yunwa zatayi mata meye bata yarda taci abinci a waje, especially idan wajen na jama’a ne kamar haka,tana da wani irin halayya dda dabi’a ta daban data banbanta data koww,batace mata komai ba har sai data gama,ta wanke hannunta da kyau ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi tana kallon afifa,sai afifan ta tabe baki tana kau da kai

“Wanda yaci shi kadai dai shi kadai zai mutu” murmushi mai sauti ya kufcewa saahar,tasa hannu tana rufe bakinta

“Am sorry bestie,na manta gaba daya,gaskiya ban kyauta ba,but zan fanshi kaina,zan siyo miki wani harfa sai kinci kin ture”

“Banso” ta fada tana jefa mata hararar wasa,cikin zuciyarta cike fal da wani irin farinciki kyakkyawa fata da kuma zato me qarfi akan saahar din.

              Awa biyu suka gama abinda sukeyi sukabar wajen suka wuce  zoo road gidansu afifa,tun cikin mota ta fara jin jikinta yayi laushi,kasala duka ta rufeta,ga wani yanayi da yake saukar mata kamar zazzabin cikin qashi.

              Afifa dake tuqi ta waiwayo ta kalli saahar din

“Anci kifi anyi dam baki ya mutu” ta fada cikin salon tsokana,wannan ya bawa saahar damar muskutawa tana yatsina fuska

“Jikina me a mace kaman fever keson kamani”

“Ya salam……aiko mu qarasa gida nayi miki test na gani,amma me zai hada madam adam da maleria ma?” Fuska ta yatsina tana jin jikinta sosai babu dadi

“Ba wani test fa,kusan last two weeks ina jin hakan,ko aiki ma daurewa kawai nakeyi,nafi zaton maleria din na kwaso,kinsan munje wata ziyara da momee munyi kwana daya” tsaki afifa taja cikin ranta,yadda bata qaunar d’an matar haka uwarma,saidai ba yadda zatayi sun riga sun zama daya a yanzun,tunda suna auren ‘yar uwarta kuma aminiyarta tun daga quruciya har zuwa girma,sai bata sake cewa saahar din komai ba,har zuwa sanda suka qaraso gidan.

           A harabar gidansu ta tsaida motar,saahar ta rigata fita ta wuce ciki,sai data kashe motar ta kulleta sannan tabi bayanta.

             Saman kujerar falo ta sami saahar din a zaune,ummi mahaifiyar afifa tsaye a kanta suna magana,matar data debo dukka kamannin Dr mamman girema,wanda ko ba’a gaya maka ba zaka fuskanci JINI DAYA ne ke yawo a jikinsu,ba zaka kirata da yayarsa ba,saboda shekarun dake kwance a jiki da fuskarta basu kai na dr mamman din ba,don haka zaifi dacewa ka bata matsayi na qanwarsa.

“Ki duba saahar afifa kafin ku shiga shiriritar taku” abinda ummi ta fada kenan tana wucewa kitchen.

            Dakin afifan da bashi da maraba dana saahar suka kwasa suka wuce,dukkansu tun kafin auren saahar ba zaka banbance dakin waccar da waccar cikin gidansu ba,kowacce tana iya amfani da dakin ‘yar uwarta,ta kuma yi tasarrufi dashi yadda taga dama,har zuwa yanzun da duka dakunan afifa ke amfani dasu,duk da ita dinma ta kusa kaucewa tabar gaban iyayenta,don akwai kudin khalifa idress a kanta,akwai abinda ya kawo tsaikon sanya rana da mahaifin afifa ya roqa a daga masa,yanason kammaluwarsa kafin saka ranar.

            Kan yalwataccen gadon afifan saahar ta zube tana fidda iska daga bakinta,tana daga kwancen tana kallon afifa ta gama hada komai da zata buqata sannan ta kalleta

“Taso mu gani” miqewa tayi tana cire dankwalin kanta da takejin ya mata nauyi ta ajjiye a gefe

“Amma da ki fara da yimin allura ta ko?”

“Waime?,allurar planning?” Kai ta gyada mata a kasalance,wani abu mai tauri yazo ya tsayawa afifa a wuya,ta allura ma take ana batun duba lafiyarta?,duk da hakan afifa ta shanye bacin ranta,don tasan zaiyi wuya idan ramin data ginawa adam din baiyi zuruf ya afka ba,don ba zatace ramin data ginawa saahar ba,domin a gareta ba rami bane wannan,abinda tayin dai dai yake da tudun muntsira data ja hannun saahar din ta kaita ba tare da ita kanta ta sani ba

“To madam biyayya vice’s qauna,taso na fara duba lafiyarki tukunna,tunda itace gaba da komai” duk da jikinta ba dadi sai data saki qaramin murmushi ta girgiza kai,tabi qaramar robar da afifa ke miqa mata da kallo

“Me zanyi da wannan?”

“Fitsarinki nake buqata” dan kafe afifa tayi da kallo kamar me tunani,sai kuma tasa hannu ta karba ta shige toilet din afifan.

Page 39

            Bata jima ba ta fito da fitsarin,ta miqawa afifan ta koma ta zauna tana lumshe idanunta,tana jin yadda jikinta yake qara zama weak,ita kanta tana mamakin wanann sauyin da bata taba jin irinsa ba.

           “Yes!!!!” Afifa ta fada da wani irin madaukakin sauti

“Alhamdulillah Alhamdulillah” ta maye gurbin furucin nata da sauri tana murza tafukan hannayenta waje daya.

             Sai a sannan saahar ta bude idanunta a hankali ta zubesu akan afifa dake tsaye tana ta faman buga murmushi,dukka hankalinta da idanunta nakan saahar

“Me wai?” Ta tambayeta a gajarce,sai fuskar afifan ta sake fadada da farinciki,abinda ke nuni da cewa farincikin dake danqare a zuciyarta ba kadan bane a wannan lokacin

“Congratulations mrs adam,congratulations” ido saahar ta fidda tana duban afifa

“Meye a kanki bestie,da ciwon kikemun murna ko kuwa?” Dariya ta saki a nishadance

“Wannan ciwon ai irinsa muka dade muna nema miki,you are pregnant bestie” cak komai ya tsayawa saahar saboda yadda maganar tazo mata a bazata na farko,na biyu kuma yanayin yadda cikin yazo,murna zatayi ko akasin hakan?,duk da tana da tsananin buqatarsa,tana cikin kewa da qishirwar samun yaro a kusa,tana qaunar yara qwarai da gaske har batasan iyaka ba,to amma kuma har yanzu basu cimma plan dinsu da adam ba,hakan na nufin cikin yazo a lokacin da basu shiryama zuwansa ba ko kuwa?.

“Bestie banason wasa,kina magana ne akan rayuwata fa” batace mata komai ba sai dauko strip din datayi mata test din dashi ta ajjiye mata a gabanta,layuka biyu gasunan sun bayyana radau kamar ma sunfi fitowa a jikin nata tsinken fiye da yadda suka saba fitowa,hakan yana nufin cikin ba na satin jiya ko yau bane.

            Kanta ta dago jikinta a sanyaye ta kalli afifa

“How comes afifa?”

“Min indillah” ta amsa mata kai tsaye tana goye da hannyenta a qirji,tana qarewa saahar nazari da karantar yadda ta karbi cikin a ranta.

                Akwai farinciki shinfide can qasan fuska da zuciyarta,amma ta karanci kamar akwai wani abu mai nauyi dake tasowa yana danne wannan,wanda jikinta yake bata koma meye baya rasa nasaba da adam

“Ciki dama yana iya samuwa ana tsaka da yi maka injection na planning?” Dukka girarta ta daga kafin ta amsa mata

“Yes mana saahar,akwai wanda ya isa halittar Allah wanzuwa aduk sanda yaso?,allura fa just wani qaramin garkuwa ne da bai isa ya hana Allah yin yadda yaga dama da bayinsa a duk sadda yaso ba”

“That’s absolutely true” ta furta a hankali tana gyada kai,bata iya sake cewa komai ba saahar din,sai ta samu kanta da cika da farinciki,dukkan wani kwadayinta da son haihuwarta yana dawowa sabo fil cikin ranta,farinciki takeji yana mamayarta irin wanda bata taba tsammanin zata tsinciki kanta a ciki ba,lallai haihuwa ni’ima ce,’ya’ya kuma rahama ce da babu kamarta(Allah ya azurta masu nema da samu,ya bayar dame albarka ya albarkaci diyoyin musulmai gaba daya).

“Ni ya kamata na yiwa mr adam wannan albishir din,ki kwanciyarki,zan prescribing maki wasu magunguna idan yazo zaku wuce sai ya tsaya ya siya miki,don’t mind any changes da zakiji a jikinki,you will be alright in sha Allah soon” kai ta gyada tana lumshe idanunta,afifa ta dauki wayar saahar din da zummar kiran adam din yazo ya dauketa,tabar saahar da ido a lumshe,hannunta saman plate tummy dinta tana shafawa a hankali,tunani fal kwanyarta,wai ita din itace zata zama uwa,itace wata halitta yanzun haka ke rayuwa a jikinta,murmushi ya subuce mata,wata qaqqarfar soyayyar abinda duk ke kwance a marar tata ya fara sauka cikin zuciyarta.

           Afifa bata sanar da saahar zuwan adam ba,ta sanya an saukeshi a Parlor din baqi na gidan,ta sanya me aikin gidan takai masa ruwa da lemo,sannan ta shiga daki ta zura dogon hijabi ta fito.

          Ta iskeshi zaune a falon,cikin shigar qananun kaya,ya cika falon da turarensa,hannunsa riqe da wayarsa yana chart.

            Baki afifa ta tabe sannan tayi sallama,ya daga kai yana amsa mata sallamar,fuskarsa kadaran kadaham,haka kawai jininsa bai taba zuwa daya da yarinyar ba ko sau daya,kamar yadda itama nata jinin da nasa bai haduwa sam,kawai dai kowa yana dakewa ne saboda darajar saahar dake a tsakaninsu.

           Hannun kujerar dake daura da qofar fita ta zauna tana cewa

“Sannu da zuwa mr adam” zamansa ya gyara,ya maida wayar aljihunsa,ba tare da ya amsa mata ba ya jefa mata tambayar

“Ina baby?”

“Babynka tana ciki,yanzu zata fito…..” Sai tadan dakata,ta fidda iska kadan daga bakinta,bayan ta sake canzawa fuskarta yanayi,babu sauran sassaucin data shigo dashi

“Na fara iskeka ne don nayi miki kyakkyawan albishir din cewa ka kusa zama uba,babyn naka na dauke da wani babyn naku……i mean matarka nada juna biyu” ta qarashe maganar tana zube dukka idanunta akan fuskarsa,tana fatan ko yaya ta fusgi wani reaction nasa,wanda shi zai bata kowacce irin dama da takeson samu daga gareshi.

             Cak komai ya tsaya a falon tsakaninta da adam din,kafin daga bisani ya sakar mata murmushi yana juya key din motar dake hannunsa

“Ban taba zaton ke mutuniyar kirki bace irin yau,kin iya kawo kyakkyawan albishir,duk da naso na fara jin hakan daga bakin baby…… anyways…..ke da ita duk daya ne,ina taya junanmu murna” ya qarashe maganar yana tsareta shima da nasa kallon.

           Murmushi ta saki tana murza hannunta

“Haka ne abinda ya kamata ya fito daga bakin kowanne magidanci na qwarai…..shikenan daga yau allurar planning ta qare,saika maida hankali ga kula da abinda yake cikin nata,yadda kake kula da duk wani kudi da zai shigo ko ya fita ta account dinta,da yadda kake kiyaye lokuttan yin salary dinta da sauran komai nata…..ina fatan yaron da ba’a shirya zuwansa duniya ba….. ubangiji ya qaddari zuwan nasa ta silar innarsa afifa……zai samu kulawa matuqa da qauna hadi da soyayya,kwatankwacin wadda ake iqirarin ana yiwa mamansa……yanzu zan turo maka babyn naka,ku sauka lafiya” daga haka ta miqe tana ficewa daga falon,yayin da adam ya miqe tsaye yana rakata da ido,zuciyarsa na suya sosai.

            Ya akayi yarinyar ta rainashi har haka?, waye ya gaya mata sirrin rayuwarsu da yadda suka tsara zasu tafi da ita tsakaninsa da matarsa mallakinsa?,me yarinyar ke nufi akansa?,wanne kallo takeyi masa?,akwai maganganu da yawa da yakeson gaya mata don tasan shi din ba sa’anta bane,to amma kuma ta riga tayi nisa ba ta yadda zai iya amayar mata da dukkan abinda yakeson fada din.

            Sosai Zuciyarsa ke quna,ransa yayi matuqar baci da maganganun afifan,a zafafe ya fita a falon,ya bude motarsa ya zauna yana jiran fitowar saahar,ya tabbatar banda saahar na sonshi so na gasken gaske,yayi amannar da tuni afifa ta dade da tarwatsa kyakkyawar mu’amala ta fahimtar juna kyautatawa da girmamawar dake tsakaninsa da ita.

           Sallamar saahar din kawai ya iya amsawa,ba tare daya waiwayo ya dubeta ba ya tayar da motar ya figeta suka fice daga gidan,saahar da batasan abinda ke faruwa ba ta bishi da kallo galala cike da mamaki

“Na dauka zaka shiga ka gaida ummi ne ai” ta fadi a sanyaye tana mamakin abinda ya canjashi da matsanancin fushi haka lokaci guda.

            Shuru baice mata komai ba,sai mamaki ya sake kamata,ta gaza dannewa saboda bata saba ganin irin wannan yanayin a tare dashi ba

“Dear……lafiya kuwa?,ko wani abu ya faru?” Da wani irin gudu ya gangara gefan titi ya tsaida motar,cikin tsawa da hargagi ya soma magana

“Saboda zallar rainin hankali ma ni kike tambaya lafiya?,bayan kinsan komai?,kinsan abinda ya farun?,ki aiko ‘yaruwarki ta cikin mutunci ta wulaqantani,ashe yawo kike dani kina bayar da labarin ina karbar dukiyarki,kina gayawa duniya nidin makwadaici ne?,to ki sani ba abinda zanyi da dukiyarki,ki kuma gayawa wannan banzar ‘yar uwarki taki afifa ta fit…….”

“Ya isa!!” Ta fada da qarfi zuciyarta na wata irin suya,mamakin adam yana cikata,ta dinga kallonsa sosai waiko zataga wani sign na fara shaye shaye a tare dashi,tunda take dashi ko kallon banza bai taba hadata dashi ba bare tsawa har irin haka ba, zata iya jure komai amma banda zagin afifa,don ita din Wani sashe ce ta jikinta

“Ta yaya zaka zo kana hukuntani akan al’amarin da bansan dashi ba?,har kana qoqarin zagin afifa,afifan da bata nufinmu da komai sai alkhairi?”

“Kedai!,amma banda ni,yadda ta tsaneni nima haka na tsaneta,i hate her with passion,idiot…..” Saiya finciki motar da kyau,har saahar nayin gaba zata daki gaban motar ta kare da hannayenta, hankalinta ya tashi sosai,bata saba ganin tashin hankali ba,kamar yadda bata taba ganin bacin rai makamancin haka daga gurin adam ba,duk da tasan yana da fushi amma bai taba kwatanta mata ba.

           Kuka ta fashe dashi tana dora kanta saman cinyarta,wanne abu afifa dinta ta yiwa adam da zai dauki irin wannan mugun fushin?. Suna isa gidan yaci burki,ya fita yabarta a motar bayan ya kashe. Da hanzari itama ta fita a motar tabi bayansa,saidai bata cimmasa cikin falo ba,tana niyyar binsa daki da take jiyo motsinsa da qarfi sai gashi ya fito,hannunsa dauke da wani file.

Page 40

        Yana daga tsayi ya wurgoshi kusa da ita,abinda ya baiwa dukka takardun ciki damar fitowa suka warwatsu a falon

“Ga komai naki nan,ki duba dukka abinda babu a ciki ki rubuta zan biyaki,sauran abinda mukayi hadaka kuma ki lissafa nawa ne na cire miki naki” ya qarashe maganar cikin fushi. Iya wuya zuciya tazo mata,sai taji ba zata iya jurewa wannan abun nasa ba,bayan batasan me tayi masa ba,ta miqe a fusace karo na farko a tarihin zamansu data taba maida masa magana

“Basai ka fake da abinda afifa tayi maka ba,zaka iya cin mutuncina duk ta yadda kaso adam,na gode” kuka ya qwace mata ta juya da hanzari ta nufi bedroom dinta.

            Sautin kukanta bai hanashi wucewa dakinsa ba yana jan mugun tsaki,amma tsakanin awa daya zuwa biyu sai wayarsa tayi qara,ya kalli wayar yaja tsaki,banda me kiran nada muhimmanci a wajensa ba abinda zai sanyashi daga wata waya a yanzu,shi daya yasan iya adadin yadda ransa yake a bace da kuma irin rudanin daya samu kansa a ciki a iya ranar yau,komai yazo masa a bazata,ya miqa hannu ya daga wayar yana maqaleta a kunnensa.

*_BAYAN AWA DAYA_*

          Ajjiye wayar yayi,ya shiga toilet dinsa ya fidda kayan jikinsa yayi wanka,ya dawo ya shirya cikin armless riga da boxer dinta,ya feshe kansa da turare sannan ya wuce dakinta.

             Yayi mamakin tarar da ita tana kuka har sannan,yayi tsaye a kanta yana kallonta,sai yaji zuciyarsa ta karyo,ya qarasa kusa da ita ya dora hannunsa saman bayanta

“Awa nawa kikayi kina wannan kukan da bashi da amfani?,bayan kinsan bake kadai bace?” Maganar tasa tazo mata a bazata,sai kukan nata ya tsaya cak,yadda yayi maganar juna biyun dake jikinta kadai ya tabbatar mata shima yana maraba dashi,sabanin yadda tayita tunanin da yadda zata fahimtar dashi. Bata gama wannan tunanin ba taji ya sanya hannunsa duka biyun ya dagota ya rungumeta yana fadin

“Am sorry,raina ne a bace” ajiyar zuciya ta saki tana narkewa a qirjinsa,cikin lokaci qalilan komai ya wuce a tsakaninsu kamar komai bai faru ba,kasancewar basu saba samun sabani a tsakaninsu irin haka ba,sai ya bude sabon shafin tattalinta tare da nunawa abinda ke cikinta zallar qauna muraran,wannan ya wanke komai daga zukatansu.

*********Cikin kwanakin da suka biyo baya komai ya koma normal,hankalin saahar ya sake kwanciya sosai da yadda adam ke tattalinta yana nunawa cikin jikinta qauna,har excuse ya nema mata daga wajen aiki saboda laulayin da take fama dashi,laulayi takeyi sosai,yau lafiya gobe babu lafiya,gaba daya hankalin ‘yan gidansu yana kanta,tun daga kan abba har ya zaid da take bi,kowa tattalinta da kuma riritata yakeyi,kamar itace zata haifa musu jikan farko. Saidai duk irin riritar da suke nuna mata bata kai rabin wadda adam ke mata ba.

********Zaune take saman couche,ta miqe qafafunta sosai yadda zata sake,chiffon armless short gown ce a jikinta,wanda rashin tsahonta ya bawa sambala sambalan kyawawan qafafunta damar bayyana.

              Waya suke da momee,wadda kullum kwanan duniya sai ta kirata tayi mata sannu da jiki,tun abun yana sata jin kunya da nauyi harta fara sabawa,sukayi sallama da ita dai dai sanda adam ke fitowa daga kitchen,hannuwansa duka biyun riqe da mug dake dan fitar da tururi,qamshin kayan qamshi na tashi a ciki.

           Tun kafin ya qaraso ta miqe ta zauna sosai,shima ita yake kallo fuskarsa tana fitar da murmushi,ya soma takowa a hankali saita maqale kafada a shagwabe

“Jan rai ko?”

“Yes” ya amsa mata kai tsaye yana dariya qasa qasa. Kunnuwanta ta kama tana dariya kadan kadan

“Na tuba,don Allah a bani nasha” idanu yadan zubata,yadda tayin tayi masifar burgeshi,kyanta kuma ya sake fita muraran,sai yaji jikinsa yadan saki amma kuma ta wani sashen wata zuciyar ta qara masa qaimi tare da karsashi,ya qarasa gabanta yadan russuna ya miqa mata cup din

“Thanks dear” ta furta da sassanyar muryarta bayan ta saka dukka hannuwanta guda biyun ta karbi mug din cikin zallar kwadayin shan tea din,ta sanya bakinta ta kurba,saita lumshe ido tana sakin murmushi saboda dadin da ya ratsa ta sosai

“Na yarda yau kadai…..ka fini iya hada black tea” murmushi ya sakar mata ba tare da yace komai ba,ba kuma tare da ya dauke kallonsa daga kan fuskarta ba,ta sake kai cup din bakinta ta sake sipping,dai dai lokacin da qaramar wayarsa dake kan wani dan teburin gilashi tare da babbar wayarsa dake charge ta dauki qara,ya qarasa a hankali,ya zareta daga charging ya karata a kunnensa idanunsa har yanzu akan fuskar saahar

“Yanzu?….kamar dai gobe…… alright on my way” ya fada a hankali,saiya cire wayar daga kunnensa ya tako inda saahar take.

            Rusunawa yayi yayi kissing goshinta

“Ayimin afwa baby,fita ce ta kamani yanzu,just one hour zanyi zuwan da dawowar…… I hope ba damuwa?” Kai ta jinjina masa tana lumshe kyawawan fararen idanunta

“Babu dear” ciki ya wuce,ba jimawa ya fito,ya canza kaya zuwa qananun kaya,sai zabga qamshi yakeyi,ya mata kyau sosai,ya sunkuya ya sake kissing dinta,har ya wuce ta kira sunansa

“Kayi kyau da yawa,Allah yasa ba zance zaka je ba” ta fada tana langabar da kai. Dariya sosai ya saki,sai ya dawo ya tsugunna a gabanta

“Bayan ke babu wata,idan akwai ma Allah yasa ta makance ta gurgunce koma ta mutu…..”baki ta kama tana dariya

“Nidai ba ruwa na,irin wannan mummunan fata haka”

“Eh kuma har zuciyata na fada ba,bazan wuce hour dayan ba zan dawo in sha Allah” ya fada yana miqewa da dan hanzari sanda wayarsa ta qara yin qara alamun ana sake kiransa. Hakanan ta samu kanta da binsa da kallo har ya fice.

            A nan falon taci gaba da zama tana kallon wani film da mbc2 suke haskawa,film ne daya shafi soldiers battle,tana son irin films din sosai.

              Kamar daga sama taji qarar waya,a mamakance ta waiwaya tana duban daga inda sound din ke fita. Wayar adam ce a wajen,tadan zubawa wayar ido tana mamakin yadda akayi yau ya manta wayarsa,shi da kwana biyun nan baya sake da waya,ko yaushe tana hannunsa,bini bini ya dauka ya duba,har wani sabon suna ta saka masa saboda maitar riqe waya daya koya,ko cikin dare idan ta farka da yake a kwanakin nan bata fiya kwana da qoshin lafiya ba sai ta ganshi riqe da waya,tun tana daukan abun da wasa har taga ya zama gaske,tayi masa complain sai yace akwai wata sabuwar harka ne da yakeson ya gwada shiga,so ana wayar masa dakai ne yadda business din yake,wanda kuma yake masa bayanin ba qasar nan yake ba,yana china, akwai tazarar 7hrs tsakaninmu,darensu shine ranarmu,lokacin shi kuma yana office bazaiyu ya maida hankali ba akan waya ya ajiye aiki,ranarsu kuma shine darenmu,a sannan shi yana da chance nayin chart,shi yasa yake tashi a daren.

              Ta gamsu,saboda ya yarda da adam din,bata taba kamashi da wani laifi da zai sanya zuciyarta tayi ɗar ko rawa a kansa ba.

             Kira bayan kira haka ya dinga shigowa,hakanan taji qarar wayar ta dameta,saita yanke shawarar sanyata a silent,don ita din ba gwanar daga masa waya bace,koda za’a kira wayarsa sau dubu bazata waiwaya ta kalleta ba,ada har qorafin hakan yake mata

“Idan kirane mai muhimmanci ko kuma samuwa ce kinga shikenan ta wucemu” dariya kawai takeyi,saboda bata jin zata iya,tana da dabi’a na tsame kai daga abinda ba huruminta bane bai kuma shafeta ba.

              Da sauri ta koma ta zauna sanda ta miqe da nufin cimma inda wayar take saboda wani hadadden ciwon mara na tashin hankali da taji ya soketa,ta runtse idanunta ta kuma dafe mararta da kyau tana kiran sunan Allah tana jujjuya kanta saboda azaba. Akalla ta kusa kwashe minti biyar a haka tana juya kanta hagu da dama,gefe guda kuma qarar wayar naci gaba da cika mata kunnuwa. Ta bude idanunta a hankali bayan ciwon ya lafa tana share gumin daya tsatstsafo mata a goshi,qafafunta babu cikakken qwari ta miqe ta nufi wayar.

             Tana isa wayar ta danyi blinking light alamun shigowar saqo,ba inda idanunta suka sauka sai kan fuskar wayar. Da sauri ta zare idanunta daga fuskar wayar tana lumshe su,gabanta na wani irin dokawa labbanta na furta

“Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis” tana fatan ta bude idanunta taga ba abinda suka gane mata bane da farko. Saidai a wannan karon data sake bude idanun nata abinda ta gani ya zarta wanda ta gani da farko,dukkan jikinta ya dauki rawa,taji a sannan bata da sauran zabi da ya wuce ta dauki wayar.

            Tana daukan wayar qafafunta suka gaza daukarta,dole ta zame ta koma da baya ta zauna saman kujera, hannuwanta kamar ba zasu iya riqe wayar da kyau ba,ta fara qoqarin gwada password din dake kan wayar.

            Duk password din da ta saka sai yace mata wrong,daga qarshe ta gwada saka qarshen number wayarsa,a take ta bude,saqon da bai gama fitowa ba ya bayyana muraran.

            K’azaman kalmomi masu munin gani bare kuma kunnuwa su iya jumurin sauraronsu,wani gumi mai zafi ya shiga tsatstsafo mata ta kowacce kafar gashi dake jikinta,zuciyarta ta ninka bugunta kamar zatayi tsalle ta fito daga qirjinta,kanta yayi wata irin sarawa ta fara gani dishi dishi sanda ta fara bin charts din dake inbox din da number wayar da babu suna a kanta. Wasu irin qazaman saqonni da ko ita da take halalin adam bata tunanin sun taba musayar irinsu a tsakaninsu,hotuna na kowanne sashe na jikin yarinyar,harda muhallin da ko mahaifiyar yarinyar tana tunanin zaiyi wuya ta sake katarin ganinsa tun bayan da shari’a ta hau kanta. Ganin abun take kamar al’mara,ganin abun takeyi kamar ba adam dinta bane,kamar ma ba wayarsa bace,ba abinda ke kaikawo cikin kwanya da zuciyarta da sunan adam din da kuma fuskarsa. Video na qarshe da idanunta suka gaza kalla wayar ta sulale a hannunta ta fadi tare da wani hadadden ciwon mara da bata taba jin makamancinsa ba,sai kawai ta cure a wajen tana jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta.

               Wannan yayi dai dai da bude qofar falon da adam din yayi cikin gaggawa,har yayi nisa ya tuna yabar wayarsa,duk da yasan baida matsala,kuma bashi da haufi matarsa bata taba wayarsa,amma haka kawai yau din yaji ya kasa samun nutsuwa,yaji bashi da gamsuwar tafiya,dole ya juyo da kan motarsa ya dawo ya dauki wayar sannan ya koma.

         Sam bai lura da inda ya aje wayar ba,idanunsa akan saahar dake cure guri daya kamar alkaki suka fara sauka. Da hanzari ya qaraso yana kiran sunanta,duk da azabar ciwon da takeji a mararta amma hakan bai hanata daga kai ta watsa masa wani kallo da jajayen idanunta ba. Sosai yasha jinin jikinsa amma zuciyarsa na gaya masa komai normal ne,ya miqa hannu gareta,ta tattara dukka ragowar qarfinta ta miqe tana jin mararta kamar zata rabe biyu

“Kada ka yarda ka tabani,karka qaraso inda nake……” Bata kai ga qarasawa ba numfashinta ya soma sarqewa,tana jin wani abu me dumi ya ratso ta jikinta ya soma bin qafafunta yana gangarowa,duk da yanayin gushewar hankali da take kan gabar yi,amma hakan bai hanata qoqarin ganin abinda ke faruwa da ita ba,idanunsu shi da ita suka sauka lokaci daya akan jinin dake malala saman tiles din falon,bai jira cewarta ba ya qarasa gareta da hanzari yana riqeta,zuwa lokacin itama tuni ta qarasa ficewa daga hayyacinta,saboda qarin tashin hankalin fitar jinin da ta gani daga jikinta.

Page 41

*******Daga lokacin data fahimci cewa ta farka,ta dawo cikin duniyar da batayi tsammanin dawowarta ciki ba,sai ta fara qoqarin bude idanunta don ta tabbatar da inda take din. A lokacin da kwanyarta ta fara yi mata bitar al’amari na qarshe daya faru da ita saita rasa dukka qwarin gwiwa karsashi da kuma sha’awar bude idanun nata,ta sake runtse idanun nata cikin jin zafi,wani abu me tsini na sukar qirjinta kamar an fiddo zuciyarta an shanyata tsakiyar qwalleliyar rana.

           Hannunta data daga a hankali takai saman cikinta ta shafa bayan ta tuna yadda taga jini yana bin qafafunta a kallo na qarshe data yiwa jikinta. “Saahar,kin farka ne,sannu” muryar anty labiba matar yaa saif dake zaune a gabanta ya ratsa kunnuwanta,bayan zuwa yin salla da maama ita da afifa suka fita yi. “Sannu saahar” anty labiba ta fada tana riqe hannunta dake saman cikin

“Ki daina motsa hannun, cannula din dake hannunki zata goce” ta fada cikin matsanancin jin tausayinta,daga yadda taga tana shafa cikin lallai shine abu na farko daya fara zuwa mata kenan a rai bayan ta farfado din,wanda tuni ya fice daga jikinta ta cikin jinin data dinga fitarwa me yawan gaske.

              Tare maama suka shigo ita da afifa,dukkansu rige rigen isowa gareta sukeyi

“Menene abun kukan kuma?,Allahn daya baki shi zai sake baki wani” abinda maama ta fada kenan cikin muryar lallashi,a nata zaton saahar din ta fuskanci babu cikin a jikinta.

           A mugun karye ta daga kai ta kalli maaman,xancan yayi mugun dukanta,wasu tawagar hawayen masu zafi suka kunno kai,saita maida idanunta kawai ta lumshe,abinda ya bawa hawayen damar saukowa da kyau.

            Tsahon zaman da sukayi tare da ita suna lallashinta idanunta na a rufe ba tare data iya budesu ba,taji ciwo sosai na rasa gudan jininta da tayi,amma a yanzun hankalinta yafi karkata ga mummunan ganin data yi a wayar adam din. Ciki tasan ubangijin da ya bata shi zai sake bata wani,ko a kusa ko a nesa kamar yadda ya kawo mata wannan,to amma kuma wannan baqon al’amari daya shigo rayuwar adam fa?,wanda kai tsaye zata iya kiransa da neman mace koda bata ce neman mata kai tsaye ba,iya maganganunsu kawai ya gama gaya mata adam ya jima da yarinyar,sunyi mugun sabo,kuma sun saba kasancewa da juna da irin mu’amalar dake iya wakana tsakanin ma’aurata

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta furta har ta fito fili ba tare data ankara ba,sai sautin muryar maama da tace

“Yauwa,ita zakiyita maimaitawa” sake motsa bakinta tayi a karo na biyu tana sake maimaita kalmar,hawayen na sake bin kuncinta.

             A matuqar sanyaye afifa ke sanya tissue tana dauke mata hawayen,saahar dinta jaruma ce da take da wani irin juriya dakiya da kuma cinye abu,irin tashin hankalin da take gani dimuwa da halin qunci sai take ganin kamar ya zarta yadda ya kamata ace an gani a fuskar macen data jima bata samu haihuwa ba ta hadu da miscarriage,saidai bata ga wani abu guda daya da zai dasa mata kowanne irin zargi a zuciyarta ba bare ta sanya ayar tambaya.

            Dai dai lokacin likitan yayi knocking qofar ya kuma tura ya shigo shida wata nurse dake riqe da file na saahar din

“Yauwa ta farka?”

“Ta farka dr” anty labiba ta amsa masa

“Ma sha Allah” ya fada yana tsaiwa daga gefan saahar din

“Sannu ko?” Ya sake fada yana duban fuskarta,sai a sannan ta bude idanunta a hankali da suka tasa saboda hawayen daketa fita daga cikinsu akai akai

“Ya da kuka kuma madam?,sorry for the lost…..kiyi addu’a,next year kamar war haka sai kiganki saman gadon nan rungume da babynki alive and healthier” idanunta ta mayar kawai ta lumshe,abinda takeji cikin zuciya da qirjinta ta tabbatar babu me iya fahimta,da rufaffun idanuwan nata ta amsawa likita dukka tambayoyin sa,sai ya rufe file din nata yadan dubi afifa

“Idan me gidanta ya shigo a turomin shi,inason magana dashi kafin na fita duty”

“Okay,in sha Allah” ta amsawa likitan bayan ta daga kanta daga wayar da take dannawa, zuciyarta duka babu dadi,duk sanda daya daga cikinsu ya shiga damuwa ko tashin hankali,kusan su biyu suke raba wannan damuwar da dukka sakamakon da zai biyo baya.

           Yanayin yadda taga kukanta yana tabasu tare da sake sanyasu damuwa ya saka dole ta tattara abinta ta cinye ta hadiye tana kiran sunayen Allah can qasan ranta,don ita kadai tasan qunci da bala’in da zuciyarta take ciki,dukkansu sun sanyata a gaba kowanne tambayarta yake me takeso?,me yake damunta?,bisa taimakon afifa da anty labiba ta shiga bandaki ta gyara jikinta tayi wanka,ta fito afifa ta shiryata sannan ta zauna yaa zaid yana ajjiye mata plate din abinci a gefanta

“Banason naga komai a cikinsa” wani marayan busashen murmushi ta saki,ta karyar dakai zuciyarta na karyewa,bata jin a yau maqogoranta zaiyi wani amfani,don bata tsammanin akwai wani abu me tauri kamar abinci da zai iya wucewa ta gurin saboda tsabar quntacewa da gurin yayi. Ganin da gaske ba zata iya cin abincin ba dole suka haqura,afifa ta hada mata kakkauran tea,ita da yaa zaid suka sanyata a gaba,aka samu tasha rabin cup,ta buqaci zata kwanta,shuru take da buqata,kadaici takeson samu ko zatayi wani tunani me amfani kan bala’in dake tunkaro rayuwar aurenta koma kai tsaye tace ya tunkarota,tashin hankali da musibar da ko wanne lokaci hankalinta ke tashi, tsigar jikinta ke zubawa idan taga wata mace cikin irinsa,yau gashi AKAN KANTA…..tamkar almara……tamkar cikin tarikicen tarkacen mafarkai,saidai kash……wannan din a zahiri ne,gaskiya ne,ba mafarki hikaya ko tatsuniya ko almara bace.

           Dukkaninsu sun dauka bacci ne ya sake dauketa,don haka yaa saif da yaa muhyi suka dauki iyalansu suka wuce gida,ya zaid shima ya wuce bayan maama ta sanyashi ya dauki masu aikin gidan biyu da suke tare anan tace su tsaya su karbo abincin dare,hamisu driver ya dawo dasu zuwa magrib.

            Shuru dakin yayi,daga afifa dake faman research a wani website sai maama dake jan carbi counter,sallamar adam dake gaba momee na biye dashi shi ya ratsa shurun da dakin yayi.

           Har tsakiyar kanta taji saukar muryar adam din,bata motsa daga yadda take ba har suka qarasa shigowa,tana jin sanda maama ke gaisawa da momee cikin surukuta tare da bata kujerar zama,yayin da adam ya matso dab da gadonta,ya miqa hannunsa a hankali ya sanya shi cikin nata yana kallon kyakkyawar fuskarta data fada tayi wani fayau da ita.

             Ji tayi kamar ya manna mata wuta,da da hali abinda tafiso a yanzun shine ta zare hannunta daga cikin nasa,to amma bata son tayi wani abu da zai fuskanci idanunta biyu,don bata shirya kallon fuskarsa ba a yanzu.

            Kamar afifa ta shiga zuciyarta sai kuwa ta isarwa da adam din saqon likita,ya zame hannunsa ya juya ya fita zuwa office din likitan.

            Ya sameshi yana shirin fita daga duty,to amma shigowar adam din ya sanyashi tsayawa da hada takardunsa da yakeyi ya masa izinin zama,ya zauna kujerar da take fuskantar dr,ya bashi hannu sukayi musabaha. Gyaran murya kadan yayi sannan yace

“Kaine me gidan saahar girema ko?” Kai ya jinjina yana dubansa

“Ma sha Allah,kasan cewa zubewar cikinta nada alaqa da shan tablet na zubda ciki?” Sosai fuskar adam din ta nuna zallar mamaki da alhini

“Tablet kuma dr?,haka kuka gani?” Kai ya jinjina masa cikin yanayi na tabbatarwa

“Yes,and after that ma…..mahaifarta ta dan samu rauni gaskiya sanadiyyar injection na planning da kuma wannan tablet din masu qarfi da tasha”

“Nasan da zancan injection,infact ma da yardarta aka fara”

“But haihuwarta nawa?” Likitan ya jefa masa tambayar yana kallonsa cikin mamaki

“Ko daya,duka duka ba bamu cika two years da aure ba until now” mamaki qarara ya bayyana kan fuskar likitan

“Amma….sorry mr adam,waye ya baku wannan shawarar?,bakusan allurar planning koda ka haihu bata masu haihuwa daya ko biyu bane?” Iska adam ya furzar daga bakinsa,dr yadan lumshe ido sannan yace

“Am sorry kada na zaqe da yawa,duk da cikin aikinmu ne mu bada shawara ga hanyar da zata bulle ma mara lafiyarmu don samun ingantacciyar lafiya kuma cikakkiya……a likitance kada ta sake ta’ammali da wani qwaya ko allura na zubda ciki ko hana haihuwa,don a yanzu haka mahaifarta ta samu rauni sosai,koda a gaba fa sake samun ciki sai an bashi special care matuqar inason juna biyunta yayi surviving har zuwa haihuwa” shuru adam yayi yana gyada kai,kafin ya sauke ajiyar zuciya yana kallon likitan

“Akwai wanda yasan dukka wadan nan bayanan?” Kansa ya girgixa cikin halin ko in kula

“Babu,but sister dinta taso taji wani abu daga gareni,so amma kuma tunda kaine ka kawota kuma kaine mijinta, that’s why bance komai ba,coz kaine kafi cancanta mu tattauna maganar da kai”

“Okay dr,na gode,inason please kada wanda yasan da wannan,zanyi qoqari in sha Allah na kiyaye lafiyarta,zan kuma bincika abinda ya kawo wadan nan matsalolin”

“Hakan yayi kyau” daga haka sukayi sallama da likitan ya baro office din.

              Tsahon zaman da sukayi a dakin shida momee din taqi koda bude idanunta bare su gaisa,har suka gama zamansu sukayi sallama suka wuce gida ita da adam din.

             Wata irin jinya saahar takeyi me wahala tare da qoqarin danne abinda ke cikin zuciyarta,jinyar ta zame mata guda biyu,ta zuciya data gangar jikinta,tayi masifar kewa tare da rashin jin dadin rasa abinda ke cikinta,saboda yadda ta qwallafa rai a kansa,ta kuma aza dukka burinta a kansa,sai gashi rana daya sanadin kuskuren adam tazo ta rasashi,abu na biyu mummunan ganin da tayi a wayar adam din,wanda ya zama silar tarwatsa wani sashe mai girma na farinciki da walwalar rayuwarta,banda Allah yasa kota ina tana da matallafa,da family me qarfi dake tattalin farincikinta.

            Da farko baccin qarya ya tsira duk sanda adam yazo har kuwa ya tafi koda awa nawa zaiyi,daga bisani ta fahimci abun yayi yawa,kuma har kamar an fara fahimtar ta,wannan yasa ta canza salo,zaizo kuma har ya tafi bata barin kowacce kalma ta hadata dashi,koda kuwa kallon fuskarsa batayi,rabon data dora qwayar idanunta akan fuskarsa tun randa fa kalli fuskar wayarta,duk sanda tayi yunqurin kallon nasa saita hangeshi cikin qazamin hoton da ya dauka shida yarinyar da bata gama tantance kamanninta ba cikin wani qazantaccen yanayi da ko a mafarki bata taba tunanin ganin hakan akan adam ba,dukka wani yarda da aminci daya samu daga zuciyarta sai taji a hankali a hankali yana sulalewa. Yanayin da yaga saahar din ta koma yayi matuqar girgiza adam din hadi da sanyashi cikin matuqar tashin hankali,yanason ko yaya ne ta bashi dama da zasuyi magana amma ta hana hakan faruwa,har zuwa randa aka basu sallama.

              Kai tsaye ta wuce motar yaa Saifullahi,yaa saif din ya ranqwafo yana kallonta

“Ki koma matar mijinki mana,ina cewa ke ya budewa motar yana jiranki ki shiga?”. Kanta ta langabe,idanunta nason kawo ruwa amma kuma tana hana hakan faruwa,su dukka basu sani ba,sam a yanzun bata da sha’awar komawarta gidan adam,to amma kuma idan tace ma ba zata koma din ba tasan bata isa ba,dole saita bada gamsashshiyar hujjar da zata zame mata garkuwa,ta kuma zama silar da zasu karbi uzurinta suyi mata yadda takeso,su barta a gida ta gama warkewa,ta kuma yi nazari a tsanake kan makomar zamanta da adam,ta gano daga ina kuskuren yake?,sakacinta ne ko nasa?,amma hakan dukka ba zata samu ba,don duk da yadda suke gatantata,suke kuma shagwabata ba shakka basa lamuntar wasa da harkar aure,ba kanta farau ba,ta gani daga kan yayarta wadda ya zaid yake bi Anty ANUUM.

            Tana fita a motar yaa Saifullahi adam ya nufo gurin da sassarfa,yamatso da nufin tallafa mata ta isa motar duk da tana takawa sosai amma saita zame,ta matsa gefe kadan dashi tayi gaba ta barshi.

          Bai sare ba ya bita,ya kuma cimmata tana kici kicin bude motar,sai ya bude mata front seat,sabanin ita dake qoqarin bude back seat.

          Karon farko ta daga manyan fararen idanunta ta zube masa su ba tare da tace komai ba. Wani abu yaji ya dakeshi sosai,kwarjini tayi masa sosai,haryaji yana shirin narkewa a wajen,saiya kauda nasa idanun,bai sake dubanta ba har zuwa sanda tashige ya maida qofar ya rufe ya zagaya ya tashi motar suka fice daga harabar asibitin.

             Shuru ne kawai ya baqunci motar,kaiba zaka ce akwai mai rai a cikinta ba,karo nafarko tun aurensu da irin hakan ta faru. Saahar din wata irin macace ta daban da take da matuqar qoqari wajen iya kula da miji,taka tsantsan tare da qoqarin barin dukkan wani abu da adam bayaso,bata daukan fushi dashi koda ya bata mata,tafi gane ta sanar masa su tattauna su yiwa kansu sulhu,a tsahon zamansu na wannan shekarun babu wanda ya taba jin kansu,sun zama wadansu irin ababen koyi da kwatance ga kowa.

Page 42

“Saahar” adam din ya kira sunanta kai tsaye da wata irin murya dake shaking,sarai ta jishi amma saita lumshe idanu kawai batare data amsa ba. Sake kiran sunanta yayi amma kamar dazun,ya fahimci ba zata amsashi ba koda zai kwana yana kiran sunanta,a duk sanda take cikin maquracin bacin rai, dabi’ar miskilanci itace abokiyarta a sannan. Samun tabbacin ba zata amsa masa ba sai ya fada jero mata kalamai na kare kai da kaifin harshe da kuma zaqin iya tsara kalamai da Allah ya bashi. Wata irin baiwa ce dashi kansa yake alfahari da ita,baiwar da yasan cewa ta siyo masa abubuwa masu yawa masu tsada da daraja…..cikinsu kuwa harda ita saahar din.

             Dukka wata kalma da yasan zata iya tasiri a zuciyar saahar din a lokacin ya arota yayi amfani da ita,to amma ko gezau,kamar ma bata wajen,abinda yayi matuqar karyashi,don bata taba gwada masa irin wannan dabi’ar ba.

          Har suka isa gida,bata tada kai koda sau daya ta kalleshi ba,ta sani muddin ma tace zata kalleshi to ba abinda zata hango tattare da adam din face baqinsa da zuciya da idanuwanta zasu dinga gani,hakanan matuqar tace zata bude baki tayi wata magana…..to lallai kalmar da dukka zata fita a bakinta muninta zaiyi yawan da zata iya haifar da faruwar komai.

            Yana tsaida motar ta budeta ta fice a gaggauce,cikin zafin nama shima ya bude bangarensa ya take mata baya,yakuma yi nasarar cimmata a tsakiyar falon gidan,ya sha gabanta yana kallon fusatattun idanuwanta da suka tashi daga ainihin launinsu na fari qal da baqi sidik din qwayar idanuwa,zuwa pink da surkin red. Wani mugun kwarjini tayi masa da ya qarasa karyashi gaba daya,sai yayi qasa da qwayar idanuwansa yana cewa

“Dukkan laifin da kike tuhumata dashi saahar na yarda na aikata…..amma ban aikata babban laifin da zuciyarki ke miki hasashen na aikata din ba,ban taba yi ba na rantse miki da girman Allah”

“Ka bani guri na wuce adam!” Furucin ya fita daga bakinta da wani irin madaukakin sauti daya canza tone na muryarta,karo nafarko data taba tanka masa tun daga waccar ranar da abun ya faru

“Bazan matsa ba saahar,kiyimin dukka kalar hukuncin da kikeso muddin zaki tsaya muyi magana koda ba zaki fahimceni ba”. Juyawa tayi kawai ta doshi hanyar fita ba tare data sake koda motsa bakinta da nufin tankawa maganarsa ba. Yayi wata muguwar zabura yabi bayanta,don ya tabbatar tana nufin ficewa daga gidansa,wanda faruwar hakan yana nufin faruwar komai da komai,yana nufin tonuwar asirinsa,yana kuma nufin subucewarsa daga kafatanin rayuwarsa,abinda a yanzun bai shirya masa ba.

          Hannu yasa ya maida qofar parlor din ya rufe,ya kuma murza key ya zare key din ya jefa a aljihun rigarsa,sai yasa dukka hannuwansa ya hade a nasa,ya kuma sulale a wajen ya tsugunna bisa gwiwoyinsa,sannan ya buda tafukan hannayen nata ya saka fuskarsa a ciki ya rufe ruf tare da kubcewar kuka.

         Duk da a yanzun batajin adam din bisa kowanne matsayi a zuciyarta,bata jinsa kwata kwata daga guraben da a baya yakai,amma kukansa yazo mata a bazata,ya kuma bata mamaki,kuka koda ga qaramin yaro abune me cin rai da zuciya gaba daya,bare ga babban mutum da yakai munzalin magidanci kamar adam,saidai wannan ko daya bai kashe wutar dake ruruwa cikin zuciyarta ba.

“Na roqeki kiyimin alfarma ki yafemin,kiyi haquri kiyimin dukka kalar hukuncin da kikaga dama,amma karki nesanceni,kada ki gujemin,ina mai hadaki da girman Allah……ki yafemin,na miki alqawari ba zaki sake samuna da wani laifi kwatankwacin wannan ba,sharrin zuciya da na shaidan ne,duk sanda kika sake kamani da laifi mai shigen wanan bama wannan din ba,na amince na kuma lamunce miki kiyimin dukka irin hukuncin da kikaga dama” duk yadda taso ya sakar mata hannu ya barta da abinda takeji a zuciyarta amma yaqi bata wannan damar,yaci gaba da amfani da baiwar iya sarrafa kalamai da yake da ita,ya dinga zaftare tsananin fushi da bacin ran da suka kafa sansani mai girma da qarfi a zuciyarta,har sai da yayi nasarar ture kaso mai girma daga cikinsa

“Ka sakarmin hannu…….har yanzu bansan makomar zamana ni dakai ba….”

“Har sai yaushe saahar?,me kikeso nayi miki wanda zai wanke wannan mummunan laifin da na aikata?”

“Sai nayi tunani” ta fada kanta tsaye. Da gaske tana buqatar nutsuwa,tana buqatar tayi tunani me kyau,tana buqatar su zauna ita dashi su tattauna,tana kuma da buqatar lalubar daga inda matsalar take. Lamarin babban abun tashin hankali ne daga gurin diya mace,ba kowa ke iya jurewa ta fuskanci irin wannan babban qalubalen ba.

           Ya qyaletan kamar yadda taso,ba kuma wai ya qyaleta bane dukka yadda ta buqata,yayi kane kane tsakanin dakinta da nasa,wunin ranar gaba daya bai zauna guri daya ba,dukka hidimar gidan ya dauka ya aza a wuyansa,dukka wani abu da saahar din keda buqata shi ya dinga yi mata,duk da bata buqaci komai daga wajensa ba,daga bisani da taga bashi da niyyar bata space kamar yadda ta buqata,sai ta murza key ta rufe dakin.

            Tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi,tayi addu’a da dukkan iyawarta da nau’ikan addu’o’in data sani,ta nema ubangiji ya shiga lamarinta ya kuma bata juriya,taji ta muzanta da yawa ta kuma qasqanta,ta kalli kanta a madubi har sau babu adadi,tanason zaqulo abinda ta rasa,tanason zaqulo inda ta gaza,tana kuma son gano wanne GURBI ne da bata cikewa adam ba har ya tsinciki kansa cikin irin wannan qazamin sahun?. Saidai a dukka hasashe da dogon nazarin da tayi,bata tsinkayi abu daya da ta kasa cikawa adam ba.

           Babu wanda yasan halin da take ciki,babu kuma wanda tayi niyyar gayawa koda afifa kuwa,tanaji har cikin zuciyarta ba zata iya tonawa adam asiri ba,sun fara hawa matakin fara samun zuri’a,ko taqi ko taso,a yau ko kuma gobe ana iya kiransa da uban ‘ya’yanta,shike da matsala ita ke zaune dashi,su tattauna a tsakaninsu su kamo bakin zaren tare tana ganin shine hanyar da zasu samu mafita.

          Tun washegarin ranar data dawo momee ta bata aron rahina a cewarta har sai jikinta ya warware tunda ita din bata da ra’ayin me aiki,yarinyar itake komai na gidan tamkar saahar ba a kwance take ba,ita din bata iya hassala komai,daga kwanciya sai kwanciya,damuwa ta farmaketa ta cimmata a lokacin da bata taba hasashen wata matsala ko damuwa cikin rayuwarta ba,tana ganin komai nata ya cika cif cif,gibi guda daya daya ragema rayuwarta na rashin haihuwa shima ya cikashe!,ashe qalubalen yana gaba!.

             Sati guda bata ko yarda sun sake hada hanya da adam ba,har sai zuwa ranar data gamsu a karan kanta lokaci yayi daya kamata ta fuskanceshi da dukka tarin tambayoyi da tuhume tuhumenta. Ranar tun da safe bayan ya fita itama ta fito ta qwarara jikinta,rahina nata murnar ganin fitowar saahar din,kusan wunin ranar tare sukayi komai da ita,har zuwa magrib inda saahar ta wuce dakinta.

            Qarfe takwas da wani abu na dare tana gaban madubi tana daure dogon gashinta mai santsi da baya rabo da gyara adam ya turo qofar dakin ya shigo,idanu suka hada saita janye nata idanun ta maida kan mudubin,yayin da shi kuma ya kafeta da kallonsa cike da kewarta,jikinsa fes da alama tun daxun ya shigo,yayi wanka ya canza kayansa cikin wasu qananun kaya da suka amsheshi qwarai.

          Hannunsa ya cire daga aljihunsa,yaji bazai iya ci gaba da jurewa shariyarta ba,ya tako zuwa inda take,ya tsaya dab da bayanta yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubin,ta sake haske,fuskarta tayi fayau.

          Jikinta ta zame daga wajen,ya bita da kallo,ya motsa bakinsa zaiyi magana,ta rigashi ta hanyar masa nuni da wajen zama,sannan itama ta koma daga gefan gadonta ta zauna.

            Dukka idanunta ta zuba masa,wani bacin rai yana motsawa daga qasan zuciyarta zuwa saman fuskarta,idan tace ta taba jin tashin hankali mai gauraye da bacin rai irin wannan tayi qarya,tayi namijin qoqari qwarai,ta tattare dukkan abinda ke taso matan,ta jefa masa tambayar data dade tana son amayar da ita,ko zata samu sauqin radadin dake yankar naman zuciyarta kowanne dare zuwa rana

“Yaushe ka fara neman mata adam?” A hargitse ya kalleta,don tambayar ta dakeshi qwarai,yanayin fuskarsa ta sauya yayi wani mugun laushi

“Idan kikace neman mata…..kina nufin zina fa kenan?” Kai ta jinjina kai masa

“Qwarai kuwa,domin abinda idanuwa suka karanto kenan,qwaqwalwata kuma ta fahimta”

“Subhanallah,wa’iyazubillah” ya fada fuskarsa na nuna girman yadda furucin yayi masa radadi a zuciya,tsahon wasu sakanni sannan ya iya daga kai ya dubeta

“Ba neman mata nakeyi ba,duk da tarayyar da mukeyi akwai sabon Allah a ciki,tunda zataga tsiraici na zanga nata….. Ta rudeni watanni uku baya da suka shude,banda ita na rantse da Allah ban taba neman kowa ba,ban taba tarayya da kowacce mace ba,kuma tun daga ranar ban sake kulata ba,ban sake bi ta kanta ba”

“Ta ina na gaza maka adam?,ko akwai wani waje da na gaza maka daka rufeni ka kasa gayamin?” Kai ya girgiza da sauri

“Ke din ta kowacce fuska kin kerewa kowacce mace,idan nace kowacce mace…..ina nufin nau’in kowacce mace daga kowanne jinsi da yare na duniya ni a wajena” wayarsa dake aljihunsa ya ciro,ya kuma fidda layukansa gaba daya ya lanqwashesu suka karye,sannan ya qarasa gabanta ya ajjiye mata wayar

“Idan kinso daga yau ni adam na ajjiye wayatama gaba daya sai sanda kika lamunce min,kiyi haquri ki yafemin,kici gaba da zama dani,sannan ki lullube sirrina,na miki alqawari saahar,muddin na sauya ko naci amana,na yarda amanar Allah ta cini nima” kalmarsa ta qarshe tayi masifar yi mata nauyin da har sai data tilasta mata rufe idanuwanta,amanar Allah ta cishi?,lallai da gaske yake mata,ba shakka ya canza ya kuma shiryu da gasken gaske.

              Ta dauki wannan kalmar ta azata bisa babban ma’auni,ta bata matsayi me girma,irin matsayin daya zarta ta qiyasceshi,a nata dabi’ar da kuma kyakkyawar tarbiyyar data samu,girman ubangiji ya wuce wani dan adam yayi wasa dashi,ko ya fake a bayansa ya aiwatar da dukka abinda son zuciya da qaawar duniya zai sawwarawa mutum. Ta dauki wannan kalmar a matsayin madogara,ta fifitata ta karbi nadamar adam,cikin sati guda ta fara qoqarin daidaita kanta tare da daidaita dukka lamuranta,ta dinga kokawa da kanta da yaqi da kanta tana son komawa ainihin saahar,tare da qoqarin maida komai a tsakaninsu ya koma bisa mizanin daidaito.

             Cikin lokaci qalilan ya sake canza mata,ya zame mata tamkar bawa dake qarqashin ikon uban gidansa,sai abinda tace shi zai aiwatar,sai abinda ta zaba,ya ninka dukka kyautatawa da kuma soyayyar da yake nuna mata,kulawa da tattali marasa misali,cikin wata guda kacal ya mantar da ita komai,ya kuma sake amintar da ita,ya nisanci dukka abinda zai kawo zargi da kokwanto a tsakaninsu shi da ita. Rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali,wannan amincin…..wannan yardar…..wannan hadakar da wannan gamayyar dake a tsakaninsu tana ci gaba da wanzuwa.

Page 43

*_WASA FARIN GIRKI_*

         Totally adam ya sauya mata,ya sake zama wani me mugun sanyi tare da takatsantsan da damuwarta da duk wani buqata tata,a tsakiyar wannnan,watanni biyar da rasa wancan cikin wani cikin ya sake samuwa. A wannan karonma itama hankalinta baikai kai ba,tana dai yawan jin jikinta babu dadi sam,adam ne ya fara ganowa,ya kuma kaita asibiti da kansa don tabbatarwa. Irin girman farincikin data gani a idanu da fuskarsa ya ninka nata ya shanye,harda qwallarsa,ya rasa inda zai sakata. Lokacin da take gayawa afifa cikin murnar yadda adam ya karbi cikin,haka kawai jikinta ya sanyaya,amma ta hadiye abunta,cikin farinciki ta taya sãahar din murna. Komai adam ya hanata yi a gidan,shike komai,yayi hidimarta yayi tasa,ya kuma shirya ya fita aiki,bashi ma da wani cikakken lokacin kansa,ya dawo dakinta gaba daya ya tare,yabar nasa bedroom din,sai kuma ya fara bata tausayi,tayi qoqarin komawa dai dai itama,tare da sake saisaita tsarin gidanta,saidai duk da haka bai fasa yi mata hidima ba.

*******K’arfe sha daya na safe ta fito daga wanka,daure da babban towel daya rufe jikinta sosai,tana a tsaye gaban madubi tana ware gashinta daya jiqe don busar dashi da hand drayer,tana ware gashin tana kallon fuskarta,tayi fresh sosai ta kuma fara dan cikowa. Cikinta ya shiga wata na uku har ya fara nisa,wannan ya sanya ta fara samun sauqin laulaye laulayen da take fama dashi,taji jiki iya jin jiki,ta gasu,don kusan yafi cikinta na baya bata wahala.

          A nutse aka turo qofar dakin nata,ta maida dubanta ga qofar,adam ne ke shigowa da innocent face din nan nashi,yana sanye da shirt turtle neck me dogon hannu da trouser dinta data zauna masa a jiki sosai tayi masa kyau,idanunsa akan sãahar,yana jifanta da wani iri kallo dake cike da tarin soyayya,kamar zai cinyeta.

         Har ya iso ya ajjiye madaidaicin tray din hannunsa idanunsa na a kanta,sai daya daidaita zaman tray din saman madubin sannan ya sanya hannuwansa ya jawota jikinsa yana dora kansa a gefan kafadarta

“Qara kyau kike kullum my heart” dan qaramin murmushi ta saki

“Shine kaketa wani kallo na kamar zaka cinyeni?” Ta fada shagwabe sosai,sai ya saki dariya me qaramin sauti

“Bakisan matsayinki bane a zuciyata,da ba zakiyi mamakin irin kallon da nake miki ba” shuru tayi tana jin saukar numfashinsa a wuyanta,kowacce rana sake jinjina soyayyarta dake ninkuwa a zuciyar adam takeyi,a duk sanda kuma ta tuna da incident dinsu na watannin baya sai taji tana sake gayawa kanta tabbas sharrin shaidanne da kowacce irin zuciya bata iya tsallake masa idan yazo da qaddara.

            Dan janye jikinta tayi daga gareshi jin shurun nasa yayi yawa,ta waiwayo tana duban fuskarsa,damuwar da take hanga tun jiya ta sake ganinta muraran kwance saman fuskarsa,duk sai taji babu dadi,don ta tabbatar inda shine da tuni ya sakata a gaba da tambaya,har sai yaji menene?,ya kuma tayata sun magance abun koda da shawara ne

“Damuwa naketa gani fa a fuskarka” murmushi ya sake saki yana girgiza kai,tare da saka hannu ya maida gashinta dake son tsole mata ido baya

“Ba wani damuwa fa,kawai sauyin yanayi ne” fuska tadan bata

“Amma ko da ban cika mace ba,mata na rako duniya,almost three years amma ace na kasa gane damuwa a fuskar mijina?, c’mon,tell me kawai,ba’a boyewa abokin kuka mutuwa” ajiyar zuciya ya saki me nauyi dake alamta lallai akwai damuwar sosai a ransa,ya koma gefan gado ya zauna yana goye da hannayensa,idanunsan nan dake cike da wani irin kallo a kanta,sannan ya fara magana

“Momee ce……” Sai yayi shuru yana duban wani gurin

“Uhmmm,me tayi momee din?” Kansa ya girgixa sannan cikin damuwa yaci gaba da magana

“Wai lallai saina canza mota motar da take hawa,jarinta kuma yayi qasa,saboda ta tana kudinta sosai wanna zuwan da tayi Ghana,tana buqatar wasu kudi ta dora jarinta” qaramin murmushi sãahar ta saki,duk da taji maganar wani iri,saboda motar momee din ba wani dadewa tayi ba,hasalima tata ce adam din yake hawa,momee ta nuna sha’awarta,sãahar din tace yabar mata,gif ne ya Saifullahi ya bata. Bataji komai ba,don iyakar kirki matar tana dashi,hakanan soyayyar da take nuna mata ko adam data haifa baya samun ire irenta ma,bata qaunar bacin ranta ko dis!. Uwa uba kuma ita din tana comparing momee da maama dinta,ta tabbatar yadda adam yake sonta yake kuma girmama iyayenta……ba shakka zai iya yiwa abba da maama komai muddin yana da dama

“To meye abun damuwa a ciki dear?,uwa ce fa?,ko ranka tana ce kana so ba zaka iya cirewa ka bata ba?” Kai ya girgiza da sauri

“No heart…..ba haka bane,kinsan a yanzu babu agenda na taba kudaden dake hannuna….infact ma ni banason taba abinda yake ba mallakina bane ni kadai” ido tadan fidda tana kallonsa,sai kuma ta bata fuska tayi kicin kicin

“Kanason gayamin momee bata haifeni ba,kai kadaine danta” dariya sosai ya saki

“Nidai bance ba,kawai dai banason taba kudin ya kawo delay wajen cikar burinmu,inason kafin babymu ya iso duniya,yazo ya samu mahaifinsa wanda yake tsaye saman qafafunsa,sai raɓi inuwa ko alfarmar kowa ba” ya qarashe maganar bayan ya iso gabanta,ya dora hannunsa plate tummy dinta da har yau yake mamaki da kuma tantamar tabbatuwar samuwarsa.

         K’awataccen murmushi ta saki,ta dora nata hannun saman nasa,wannan ya bashi damar dago fuskarta yana kalla

“An soso miki inda yake miki qaiqayi ko?,na lura kafuwar kamfanin ma bata dameki ba kamar yadda kika damu da zuwan babyn nan” kai ta jinjina

“Allah ya jarabceni da son yara,inajin ranar dana haihu bazan iya bacci ba,har ina rayawa a raina,wannan tsananin son yaran kada ya zama tawa jarrabawar kenan,na mutu ban haihu ba”

“Komai lokaci ne,gashi yanzu yana hanya?”

“In sha Allah” ta fada tana jin wani farinciki yana lullubeta,ta jarabtu da son wannan cikin fiye da cikinta na baya.

           Zame jikinta tayi daga nasa,ta matsa zuwa side bed drawer dinta,ta budeta,sannan ta jawo safe dinta,ta ciro wani bangul guda biyu me kyan gaske daketa daukar ido,ta qaraso wajen adam dake tsaye daga bayanta, hannayensa cikin aljihun wandonsa yana kallonta. Miqa masa tayi

“Abun hannun nan yana da matuqar muhimmanci a wajena,amma duk muhimmancinsa baikai na miji na gari irinka ba,na amince ka siyar dashi,ka siyawa momee duk abinda takeso,idan da saura a zuba a kudaden da suka rage mana na gininmu,koda foundation a fara sakawa na ginin” baya yaja yana zare idanu

“What?, a’ah,ba za’a yi haka dani ba,Allah ya sawwaqe”ya fada yana yarfar da hannu,fuska ta bata tana kallonsa,sai shima ya tsaya ya zuba mata ido yana kallon yadda rashin jin dadi ya ratsa har cikin zuicyarta

“Ni ba kyauta na baka ba,ka rubuta idan komai na kamfani ya kammala zaka biyani” dariya ya saki sosai

“Matata me wayo,to godiya nake” ya fada yasa hannu biyu ya karba yana juya abun hannun,wanda ya tabbatar idan aka kaishi kasuwa kudade ne masu nauyi za’a karba. Ya sani yayi kuma imani sãahar ta dabance ko cikin mata,tana cikin sahun mutanen da idan suka soka qaramin abu bai sanyawa su gujeka,zasu iya sadaukar maka da dukkan farincikinsu muddin zasu samu soyayya da kulawa daga gareka,hakanan idan suka qika,zaiyi wuya wani abu yasa su soka.

             Da hannunsa ya dinga bata breakfast din har taci ta qoshi,ya tattare plates din zai fita dasu yana cewa

“Bari na watsa ruwa,inason zan dan fita,sai naga waya kamata ya siya banguls din” miqewa tayi a nutse tana daure lallausan gashinta da wani qaramin scarf kalar english wears din jikinta

“Yaukam ko ladan hada maka ruwan wanka ka barni na samu please” ta fada a shagwabe,kai ya girgiza

“Indai nine na yafe” tsaiwa tayi tana dubansa,kamar me tuna wani abu

“Amma,yau kusan two weeks kana hanani shiga dakinka,why?” Ta fada tana bata fuska, murmushi ya sakar mata,ya kama kumatunta yaja

“Banason kiyi dukkan wani aiki bare ki wahala,idan kika shiga da zummar hadamin ruwan wanka,zakice zakimin gyaran daki ne,don dakin yayi qazanta da yawa,abinda ni kuma bana so kenan” kanta ta kawar gefe cikin nuna tata rigimar

“Wannan gatan yayi yawa,ba’a kaina aka fara samun ciki ba,gidanmu cike yake da ‘yan aikin da idan na buqata za’a kawomin,amma banason,saboda me?,aure nazo bautar Allah,ba zaman jin dadi da baiwa zuciya da rayuka abinda sukeso ba,ina fatan samun dacewa” ta qarasa maganar tana zube idanunta a kansa.

           Kai ya jinjina,shi kansa shaida ne,gata kyau ko wani matsayi na rayuwa bai sanyata ta dakaki kanta a gidan aurenta ba

“Shikenan,let’s go” ya fadi yana bata hanya,saita miqe tana harararshi

“Da ladan kakemin buqulu?”

“Ban isa ba” ya fada yana daga hannu sama alamun surrender.

           Koda suka shiga dakin bataga wani datti me yawa da yake magana a kai ba,ta hada masa ruwan yayi wankan a gurguje ya fito ya shirya,tana zaune daga gefan gadonsa suna hira har ya kammala,sannan suka fito tare,sai taga yana saka key yana kulle dakin,abinda ya maidashi dabi’a kenan a kwanakin,to amma da yake tana da nata bedroom din,kuma ba wani abu take ajjiyewa cikin dakin ba,sai bata taba damuwa ba,yayi kissing nata lightly a forehead dinta sannan ya wuce.

          Ba abinda zatayi,yau ko aiki ba zata fita ba,don haka tayi zamanta a Parlor,ta kunna kallo,jita jifa tana taba chart a wayarta.

            Sallar azahar ce kadai ta tasheta,tayi sallar ta duba fridge ta dauko fresh samosa da adam din ya mata order ya cika mata fridge dashi wai saboda yunwar dare,ta soyata,ta hado da hollandia me sanyi ta dawo ta zauna.

             Tana tsaka daci kiran afifa ya shigo wayarta

“Uwar biyu” ta fada cikin salon tsokana

“Allah yasa,tabbas da kin samu kyautar kujerar umra daga adam” zuciyar afifa daga can ta tsinke,batasan wanne suna zata bawa adam ba,har yanzu zuciyarta bata taba nutsuwa da komai na adam ba,ta rasa me yasa?,duk da cewa ya bada dalilai masu yawa da yaci ace kowa ya gamsu ya kuma aminta dashi,amma ta nata bangaren hakan ya gaza samuwa

“Allah yasa” ta amsawa sãahar din

“Kudaden nan sunzo ko?” Kai ta girgiza tana sipping madarar

“A’ah,anya?,banga alert ba”

“Haba?,amma tun jiya da dare fa,kuma sunyi debiting dina,receipt din na manta banyi generating ba”

“Karki damu,zan duba balance,nasan sunzo ma”

“A’ah,duba dai yanzu ki gayamin,amana ce ya zaid ya bani kuma kafin na gaya masa na saka sai nayi confirming ya shiga Account dinki” qaramin murmushin dake qara mata kyau tayi

“Bestie koni kika siyar kikaci kudin kinci halak”

“Na sani,amma yanzun ki duba tukunna” ta fada tana katse kiran,ta ajiye wayar a gefe tana jiran kiran sãahar,akwai abinda takeson takai sãahar din gashi,addu’a kuma take takai gano.

         Tana murmushi ta soma checking balance dinsu ta USSD CODE,tayi na farko yayi cancelling,ta sake gwadawa har sau uku yana cancelling,tayi duk wami qoqari na checking din amma yaqi yiwuwa,abinka dame ciki,haka kawai abun ya zafafeta,sai ta soma trying number wani ma’aikacin banking da suke ajiyar.

             Sanda ta gama masa bayanin cewa yayi

“It seems like anyi disconnecting duk wani details naki daga Account din,to amma kuma ina doubting,saboda indai za’a yi hakan saida saninki da yardarki,anyway,gobe zan shiga bankin,zan duba miki komai in sha Allah” godiya tayi masa ta sauke wayar,duk da cewa wani bangare na zuciyarta cike yake da mamaki,amma wani sashen kuma cikin tantama yake,kanta ya kulle dason gane gaskiya da kuma meye dai dai?,ganin zata batawa kanta lokaci saita ajiye komai,don bata da tabbacin gaskiyar ko rashinta akan duk abinda zuciyarta zata raya mata,taci gaba da cin samosa dinta.

           Takai plates din kitchen kenan ta fito taji ana knocking,ta fasa zaman da tayi niyya,ta isa qofar falon ta budeta.

           Mamaki ne sosai ya kamata ganin raihanatu,don tsahon aurensu da adam batajin yarinyar tazo gidan yakai sau uku,duk da yadda takeson yarinyar saboda hankali da nutsuwarta,da kuma yadda take girmamata.

Page 44

          Ta taba yiwa momee din complain akan hakan,tabe baki tayi

“Na rabaki da wannan,wannan me baqin halin,sumumu kasau” murmushi ta danyi kadan,can qasan zuciyarta cike da mamaki,bata taba ganin wani abu na rashin kyautawa raihanatu tayi ba,duk tsahon zuwanta gidan kullum cikin hidima takewa momee,bata tana tsallake umarninta,tausayi da nutsuwarta yake qarawa sãahar qaunarta,wannan ya sanya koda kayan bayarwa zata fitar,raihanan take baiwa,ko yanzu kayan jikinta na sãahar dinne,don ba kasafai momee ke mata dinki ba,takance tana yi mata, yarinyar ce kamar ba mace ba,batason kwalliya bata sawa, sãahar dai bata taba ganinta cikin qazanta ba,ko yaushe fess take da tsaftatattun kaya.

“Shigo ciki mana” sãahar ta fada ganin wani abu me kama da tsoro a fuskar raihana dake tsaye daga bakin qofa,hannunta dauke da ledar dake nuna aikenta momee tayi ta biyo nan,sau biyu tana waigawa tana kallon bayanta kafin ta fado falon.

          A qasa ta zauna, sãahar ta tasheta tace ta koma saman kujera

“Ya gida yasu momee?” Ta fara tambayarta ganin har yanzu batace komai ba tana nufar qofar kitchen,hannunta taji an riqo,saita juyo,fuskarta ta sauka akan raihanatu. K’walla ta gani cike fal da idanun nata,yanayinta ya sake sauyawa qwarai,kowanne lokaci zata iya sakin kuka

“Ki zauna anty don Allah,magana nakeson zamuyi,gida nakeson komawa da sauri,kada momee ta fahimci na biya wani gurin” kai ta jinjina,saita dawo da baya ta zauna dab da raihanatu ta zuba mata ido,jikinta yayi wani mugun sanyi da kuma mutuwa,wanda batasan dalilin hakan ba,sai taji gabanta yana faduwa kadan kadan lokacin da taga raihana ta sad da kanta qasa,qwalla tana diga.

             Tsahon zamanta da yarinyar bata taba zama irin haka da ita ba,zuciyarta ta shiga fargaba da taraddadi,kafin tace wani abu raihanatu cikin rawar murya ta fara magana

“Kafin rasuwar mamana ta gayamin duniya a yanzu cike take da mutane azzalumai,marasa amana,marasa kuma saka alkhairi da alkhairi,na sake tabbatarwa a yanzu akan yayar mahaifiyata,na kuma sake tabbatarwa a yanzu a zamanki da yaya adam da momee. Bazan taba nutsuwa ba,bazan taba samun kwanciyar hankali ba idan har na bari akayo miki wannan zaluncin,bayan kunnuwa na sunji amma na gagara gaya miki” sai tayi shuru hawayen naci gaba da zuba tana hadiyar zuciya

“Na baro yaya adam a gida yanzu suna shirya yadda zasu qarasa murqushe dukiyarki” ta tsaya da zancan tana kallon sãahar. Ido sosai sãahar din ta zuba mata,maganar tana neman matsugunni a kunnuwanta sannan ta isa ga kwanyarta,tsahon wasu sakanni sannan ta danyi murmushi tace

“Ba murqushewa zaiyi ba ba raihanatu,nina dauka da kaina na bashi,ba bangula guda biyu ba?” Kai ta girgiza alamun a’ah

“Duk wata dukiya dake hannunki da wadda take hannunsa,bama wannan ba anty…..kinsan yaa adam yana da wata matar bayan ke?” Wani irin mugun hautsinawa kanta yayi,mararta kuma ta damqe guri guda kamar curarren alkaki,amai ya taso masa me bala’in zafi tare da tashin hankalin daya daki zuciyarta,saita miqe da mugun gudu ta nufi kitchen wanda shine yafi kusa da ita.

             Sosai ta dinga kwarara amai,har sai dan samosa da madarar da tasha babu jimawa suka fice gaba daya,a sannan raihanatu tana tsaye a bayanta tanayi mata sannu cikin tashin hankali,a wahalce sãahar ta gama kuskure bakinta tana maida numfashi ta juyo tana duban raihanatu data gama tsurewa gaba daya,zuciyarta kuma ta fara shiga tsoro da nadamar abinda yasa ta gaya mata wannan babban sirrin

“Kiyi haquri anty,ban gaya miki don na daga hankalinki ba,na gaya miki ne saboda kina da kirki,ke din mutuniyar arziqi ce,barin wasu mutane masu mummunar zuciya su cutar daku babban zunubi ne” hannu ta dora a kafadar raihanatu

“Karki damu raihanatu,jikina yana bani da dukkan gaskiyarki kikayi maganar nan” saita jawo yarinyar jikinta tana jin zuciyarta tana karyewa,duk da a yanzu tana gayawa kanta ba rauni take buqata ba,tana buqatar qarfin hali da dauriya me tarin yawa don ta gano ainihin gaskiyar maganar,duk da wani sashe na zuciyar yana mata tantama,anya adam?,adam da momee?,zasu aikata?.

“Na gode raihanatu” ta fada sannan ta janyeta daga jikinta,hannuwan sãahar duka biyun raihanatu ta kamo ta riqe,abinda bata taba yi ba,cikin rawar murya tace

“Amma don Allah anty kiyimin alqawarin ba wanda zaisan ni na gaya miki maganar nan”

“Komai rintsi komai tsanani raihanatu,na miki wannan alqawarin” tana nan tsaye kamar statue har raihanatu ta fice a gidan. Gaba daya ji tayi kamar an yashe komai daga cikin kanta,ta rasa dukkan wata idea da matakin daya kamata ta fara dauka,babu abinda yake mata amsa kuwwa a kunne sai YAYA ADAM YANA DA WATA MATAR BAYAN KE,ta yaya hakan zata kasance?,ta yaya hakan zata yiwu?,bayan ko yaushe suna tare da dam?,shiba matafiyi ba ba komai ba bare tace yayi amfani da wannan damar yayi auren a wani garin bata sani ba?,sai ta sulale ta zauna a wajen,tasa hannunta guda biyun ta dafe kanta wanda taji yana sara mata,kanta taji yana cushewa,zai buga da kalar tunanin da take takurawa kanta dashi,saita fara karanto sunayen Allah,da haka ta samu taja jikinta ta koma falon ta zube saman kujera.

          Tunda ta kwanta bata tashi ba sai da akayi sallar la’asar,kana kallonta zakace bata da lafiya,dab da kiran magariba adam ya shigo,tana daga kwancen ta daga kanta tana kallonsa,fuskarsa cike da walwala da wani irin nishadi wanda batasan daga ina ya samo asali ba,saita samu kanta da qarewa fuskarka kallo da kyau,zuciyarta tana nazartarsa,nazarin da bata taba yinsa a kan adam ba.

            Ganinta a kwance yasa ya sauke hannayensa daya ware mata yana jiran ta shigo ya rungumeta,duka sai walwalarsa ta koma,ya tako da sassarfa cikin nuna damuwa me yawa ya iso gareta

“Heart,what happened?” Yayi maganar yana dagota zuwa jikinsa

‘banajin dadi” ta bashi amsa a taqaice

“What?,kada dai ace a kwance kika wuni?”kai ta sake gyada masa

“Ya salam,me yasa baki kirani ba?,amma baki kyautamin ba, please please karki qara yimin haka,idan wani abu ya sameki fa?” Yayi maganar kamar zai fashe da kuka,sai ya kwantar da ita,ya ciro waya,saiji tayi yana kiran wani likitansa. Drip yasa aka daura mata,wai tafijin qwarin jikinta,ya kasa zaune ya kasa tsaye,bayan fitar likitan ya shiga kitchen ya dora abincin dare,yayi yayi ta fada me takeson ci tace masa babu komai.

            Wanzuwarsa a kitchen din ya bata damar sake zurfafa cikin tunaninta,ta dinga hango mode dinsa tun daga shigowarsa gidan kawo yanzu,tarin qauna kulawa da kuma riritawa ce zallah,sai zuciyarta ta cika da kokwanto,amma kuma ta rasa meye yake bata qwarin gwiwa da tabbaci.

        Karin ruwan babu abinda ya qara mata,saboda wata irin narkakkiyar damuwa ce dake kwance qasan a zuciya,a haka suka kwana. Washegari tunda wuri ya hada mata breakfast ya shirya yace mata zai fita,amma azahar ko la’asar zai dawo. Har ya fita saita miqe ta bishi,a qofar dakinsa sukaci karo,yasa hannu ya jawo qofar yana kullewa da dan sauri,yayin da idanunsa ke a kanta yana kasheta da murmushi.

“Akwai wani abu ne?,ko kinaso na taho miki da wani abun?” Kai ta girgiza

“A’ah,zan dan fita strolling ne idan na gaji da kwanciyar”

“Ba damuwa,amma ko nasa momee ta kawo miki raihanatu?”kiran sunan kawai yasa gabanta ya fadi,saboda tuna gagarumin abun da muddin ta samu tabbacin afkuwarsa,zai zama sila ta guntulewar alaqar auratayya tsakaninta da adam,duk yadda take da kai, muddin kai din maha’inci ko maciyin amana ne…..to tana shata layi me girma a tsakaninka da ita.

“Ka barta,na danji dadin jikin ai” ta amsa masa.

     Kasa komawa dakinta tayi bayan fitarsa,taja jiki ta zauna saman kujera,kamar kuma wadda aka mintsina saita miqe da sauri,kai tsaye ta doshi dakin adam. Tambayar kanta takeyi me zataje tayi a dakin?,tunda ta tabbatar ya rufe dakin a gabanta,kuma bata da sauran spare key da zai bata damar shiga?,amma duk da wannan tunanin sai ta gaza tsaida kanta daga dosar dakin da takeyi.

               Sau daya ta murda dakin bawai don tana tantama ko tana da masaniyar bai rufe ba,amma cikin iko da qudurar ubangiji taji ya bude,mamaki ya cikata,ta tsaya tana duban qofar bayan ta bude,ta leqa sai ta fahimci yana sauri ne bai murza key din da kyau ba,lock din bai gama shiga ba ya zare ya dauka ya shige. Sakin wannan tunanin tayi ta wuce dakin da gaggawa.

           Cak ta tsaya tana qarewa dakin kallo,tana nazarin ta ina zata fara binciken da zai bata shaida ko tabbacin abinda take zargi?,shikam adam ma bashi da safe irin nata,saboda yasha gaya mata ya yarda da ita. Wani tunani ya fado mata,a dazu da suka shiga dakin taga yanata kaffa kaffa da wardrobe dinsa,tun bata ankara ba har hankalinta yakai kai,amma bata kawo komai a ranta ba ko kadan,saboda tasan zuwa yanzu ya wanke dukkan wani zarginsa a ranta.

          Cike da fargaba ta buda wardrobe din,cikin ranta tana addu’ar Allah yasa komai ya zama hasashe ne,Allah yasa komai ya zama tunani ne,muddin ta samu adam da cin amanarta,batasan ta yadda zuciyarta zata iya dauka ba.

            Tsaf ta bincike wardrobe din,saidai bataga komai ba,tasa hannu tana shirin rufewa idanunta ya sauka daga can qasanta,wani abu me kama da jaka ta gani a jingine daga can gefe,saita tsugunna ta jawo,jakace baqa mai cike da zips kala kala,tunda take da adam bata taba ganin jakar ba,wannan ya qara mata qaimi da karsashi,ta fara bude zips din,take kudade masu tarin yawa daure cikin kyauraye da kuma takardu masu yawa suka fado.

Page 45

           Kafafunta ne taji sunyi wani irin sanyi suna kamar zasu lanqwashe da kansu kai kace narkakkiyar roba ce,sai ta zame ta zauna sosai a qasa,ta ajjiye kudaden da suka kasance dollars masu tarin yawa bandir bandir gefe guda,ta zube takardun da kyau,ta soma dauka tana dubawa.

              Wani irin gumi ne ya fara yanko mata,tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafafunta,kowacce takarda da original copy dinta,da kuma wadda aka sauya a manne da ‘yar uwarta,indai idanunta dai dai suke gane mata……takardun dukka filayenta da sauran kadarorinta ne dake wajensa aka sauyasu da wasu sunaye na wasu mutane da batasansu ba,affidavit na court dake bada tabbacin sunayen da kuma mallakar dake jikin takardun na asali,takardun withdrawal da akayi daga joint account dinsu,statement of account gaba daya,dama rufe account din da akayi kwata kwata.

                   Tashin hankali wanda ba’a saka masa rana,komai ya canza,ya tashi daga mallakinta zuwa mallakar ADAM ADAM,FAINUSA ADAM da kuma WARISHA KHADIRI,mutanen da batasan su waye ba banda sunan adam din dake maqale a jikin sunan kowannensu.

               Kamar wadda aka tsinkawa jijiyar hannu ta zaro takardar gaba, certificate of birth ne me dauke da sunayen dake a sama,FAINUSA ADAM da ADAM ADAM,kanta ya sake kullewa da kyau,wani irin tashin hankali ya dira a tsakiyar zuciya dama kwanyarta tunanin da ya darsu a ranta ya sanyata ci gaba da birkita takardun gabanta cikin hanzari,caraf hannunta ya sauka akan takardar shaidar zama ma’aurata ADAM/WARISHA.

                 Sosai hannuwanta suka fara rawa,da gaske ne ashe?, abinda raihanatu ta gaya mata da gaske ne?,adam yana da wata matar bayan ita?,da gaske ne adam ya shirya cin amanarta?,indai waccan matarsa ce su kuma yaran fa na waye?, tambayar data sanyata surar passport din data gani guda hudu a gabanta,wanda budeshi ya zame mata tamkar madubi ko amsa na dukka tambayoyin dake karakaina a tsakiyar kwanyarta zuwa zuciyarta,suna barazanar fasa mata tunani.

                  Fes kamannin yaran suka bayyana kansu da kansu,adam sak!,kamar yayi kaki ya ajjiye,ko kamar karan da aka samu gwanin iya rabo ya tsagashi gida biyu.

                 Dif komai ya tsaya mata,ta dinga jujjuya korayen fasfunan da suka kasance baqaqe wuluk a idanunta,fasfunan dake dauke da visa ta qasar england,visa din da zata basu damar zama a qasar na shekaru ɗai ɗai har shekaru biyar cif!. Da qyar ta qwaci kanta ta fusgi harshenta ta kawowa kanta da kanta dauki ta hanyar furta

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, la’ilaha illa anta subhanaka inji kuntu minazzalimin” ta fara maimaitawa wasu hawaye masu zafi suna malala daga idanun nata.

                Qoqarin hanawa kanta tashin hankalin kanta takeyi da gasken gaske,saboda yadda taji mararta tana qullewa,bata shirya asarar abinda yake cikinta ba,don haka tayita kokawa da numfashinta tana jansa tare da fitar dashi da sunan Allah,wata ‘yar qaramar nutsuwa ta sauko mata,saidai zuciyarta na mata wani irin ciwo da zafi tana jin inda za’a dubata a yanzu qila a tarar ta kumbura.

            Miqewa tayi jiri yana dibarta ta wuce toilet dinsa,ta tsaya gaban sink ta kunna famfo ta daura alwala tana fatan tiririn yaji da zafin dake fita a fuskarta ya tsagaita,ta kusa kashe minti goma tana daura alwalar tana kuma maimaitawa,ita kadai tasan dimuwa da razanar da zuciyarta take ciki,daga bisani tilas ta daure famfon ta fito zuwa bedroom din.

              Gefe guda ta zauna,ta zubawa takardun da kudaden da fiye da rabinsu haqqinta ne ido,shi yasa ta daina jin alert?,ya zare duk wani kudi data nema da guminta?,ya yiwa matarsa da yaransa wadanda batasan da zamansu ba visa na barin qasar?,ya dauke duk wata dukiya tata ya maidata mallakinsa?,ya hanata haihuwa,ya hanata morar komai nata,ya yaudareta yaudara mafi muni,ya shiga rayuwarta a lokacin da taqi baiwa kowanne namiji fuska,yayi amfani da iya kalamansa, kyakkyawar mu’amala da kulawa mai matuqar nauyi da zurfi,irin kulawar da komai taurin kai da kafiyarki dole ki amshi soyayyar mutum,ya hada da wayo da dabara irin wanda itadin qarancin shekarunta basukai kansu ba,ya cusa mata soyayyarsa ya mallaketa yake kuma neman sanyata cikin musiba mara misali,me ta yiwa adam haka na cutarwa tsahon rayuwarsu da zaiyi mata wannan mummunar sakayyar?.

           Ji tayi kamar zuciyarta tana narkewa,kukanta yanason fitowa fili ta yishi sosai,amma zuciyartata tana tunasar da ita

“Lokacine daya kamata ace kinyi abinda ya dace,ba lokacin kuka bane yanzu” maganar data fito daga can qarqashin zuciyarta kenan,ta kuma zaburar da ita,ta barota daga inda take zaunen,ta dawo ta tattara takardun da kudin,passport din da komai da komai yadda suke a tsare a jakar,bayan ta gama ta zuge jakar,ta daukota ta fita daga dakin,bayan taja kowacce qofa ta maidata yadda take,tamkar ma bata shiga dakin ba.

              Doguwar riga me sulbi ta zura saman kayan jikinta,ta yane kanta da mayafin rigar,bayan ta shafa fuskarta da hoda ta zizara kwalli daya qarawa idanunta haske,duk da yawan kukan da tasha,sannan ta wuce zuwa farfajiyar gidan,ta bude motarta ta jefa jakar a ciki,ta tashi motar ta fice a gidan da gudun tsiya.

          Kai tsaye gidansu ta nufa,tanason ta yiwa jakar ajiya a muhalli me kyau,tanason taga iya gudun ruwan adam,tanason ya kama kanshi da kanshi ta hanya mafi sauqi da dacewa.

            Qasa da mintinan data saba isa gida a yau ta isa,don gudu tayi sosai saman titi,tanason ta riga adam komawa gida,batason yasan cewa ma tafita kwata kwata daga gidan.

          Biyu cikin ma’aikatan gidansu ne suka taso suna mata sannu da zuwa,a yau din bata cikin dukkan wani yanayi na walwala ko sakewar data saba yi musu,don haka sama sama ta amsa musu,ta bude baya ta dauki jakar,saita barwa marwa key din motar tace ta rufe mata,ta wuce gidan dauke da jakar.

              Gidan babu kowa sai masu aikin daketa kaikawo,ko maama ma a sannan tana daki a kwance tana hutawa,da kallo ta bita lokacin data shiga dakin,ta miqe ta zauna tana ci gaba da nazartarta

“Ajiya na kawo miki maama,wasu kaya ne masu muhimmanci,don Allah karki barsu nan kusa,nima ajiya aka ban,ina tsoron tabasu ko kuma nayi sakaci wajen ajiyarsu” abinda tace da maama din kenan,sai tabi jakar da kallo sannan ta sake maida dubanta ga sãahar

“To shikenan,amma dai,kedin lafiya lau kike kuwa?” Wani abu me nauyi ya sauka a qirjinta,tana jin kamar ta budewa maama zuciyarta taga tsantsar damuwa da kuma tashin hankalin da take ciki,to amma idan ta aikata hakan tasan zata jefata ne a damuwar data ninka tata. Dukkaninsu wani irin so suke mata,sam basu ajeta nan kusa ba a zukatansu

“Ba komai,kawai yau inajin weakness ne,gida ma zan wuce nadan kwanta,zan samu relief in sha Allah idan na tashi” kai tadan jinjina tana dan jin tantama,amma dai bata sake hango komai dazai bata hujja ba

“Allah ya qara lafiya,ya raba lafiya,kinqi bari a kawo miki me tayaki hidimar gida,ke kadai a family kin fita zakka sãahar,ba wanda babu me aiki a gidansa sai ke” murmushin da yafi kama da yaqe ta saki

“Maama saina haihu in sha Allah”

“Dolenki ai” ta fada tana miqewa da jakar a hannunta.

            Kamar a zuwa haka a komawa ta dinga tsala gudu,cikin mintuna qalilan ta isa gidan,ta qarasa da motarta parking lot ta kasheta ta fito zuwa cikin gidan.

           A parlor ta zube,dauriyarta tana nan qarewa,ba abinda ke mata yawo a idanu sai hotunan yaran dake jikin passport din,da sunan ADAM a matsayin ubansu,da kuma matar dake a mazaunin matarsa, kuma mahaifiya ga yaran kamar yadda ta gani a sauran takardun dake dauke da gurbin da ake buqatar sunan mahaifiya. To hakan me yake nufi?,tun asali adam baya sonta kenan?, auren jari yaso yayi da ita?,ko cin amana ne zallah ya sauka zuwa zuciyarsa?,mummunar zuciya suka hadu da iblis sukayi masa muguwar kururuwa?,adam da d’a?,wanda ba ita ta haifa ba?,adam da mata bayan ita da duniya ta gama sani?,ya maye gurbin kowacce kadara tata da dukiyarta da sunan ‘ya’yansa?,wanann wacce irin azzalumar duniya ce muke rayuwa a cikinta?.

             Duk yadda taso ci gaba da jurewa abun ya faskara,kuka ta zauna tanayi wiwiwi a falon,tafukan hannayenta shinfide saman fuskarta. Karar shigowar motarsa harabar gidan ya sanyata miqewa,kai tsaye ta wuce dakinta,ta kuma zarce bedroom ta fara hada ruwan wanka tana zare kayan jikinta,sam batason adam ya fuskanci komai bare wani abu ya darsu a ransa,don haka ta hada ruwa me dumi sosai,wanda tana gab da fara wankan ya Murda qofar dakin ya shigo, muryarsa cike da wani irin nishadi da a karon farko sãahar ta fassarashi,cikin muryar shauqi da nuna zallar soyayya yake kiranta

“Heart!,heart kina ina?” Lamarin da ya sakata lumshe idanuwa,wasu hawaye masu dumin gaske suka sulalo mata

“Har tsahon yaushe zai dauka yana yaudararta kafin ya gaya mata gaskiya?,ko kuma har sai lokacin da zata bude ido ta laluba sama da qasa babushi?,ya tattara komai nasa da ba nasa ba sun bar qasar shida iyalinsa?.

            Gyaran murya tayi masa,saiya murda qofar bandakin

“Budemin nayi joining dinki mana” bata iya furta komai ba saboda ta tabbatar muryarta ta shaqe,saita sakeyi masa gyaran murya,dai dai sanda kira ya shigo wayarsa,saiya maida hankali kan kiran ya juya yana ficewa daga dakin tare da daga wayar duk a lokaci guda.

Page 46

         Sake fashewa tayi da kuka cikin bathtub din,tanajin kamar ana matsa zuciyarta,ta jima a hakan sannan ta fito daga bandakin,tana takawa a hankali saboda yadda mararta ta riqe, idanunta suka sauka akan ledar daya shigo da ita ya ajjiye mata,wadda kullum yake kawo mata dukka abinda ta zabi ci kafin fitarsa,a yau sai taji ta tsani ledar da kuma tsani wanda ya kawo ledar,ta matsa gaban madubi tana goge ruwan jikinta,bata da karsashi ko sha’awar komai,kawai zata daure tayi komai ne don batason ya fuskanci wani abu,batason bashi qofar da zai dago akwai wani abu daya faru bayan fitarsa,tanason ta kamashi ne red handed,tana son ya kawo kanshi da kanshi,a dole ta shafa mai,ta zaro wata doguwar rigar ta zura,dai dai sanda taji an budo qofar da qarfi,har sai data hadu da bango ta bada wani bammm!.

           Da sauri ta daga kai tana dubansa,shima ita yake kallo,ta tsirashi da idanu,wani lafiyayyen tashin hankali ne a kwance saman fuskarsa,ta hadiye wani abu me daci da tauri,nata bacin ran yana son yin tasirin da taketa danne masa tun awannin dazu,amma kuma sai tayi wani qaqqarfan yunquri ta kauda shi gefe,ta maye gurbinsa da lallausan murmushin da idan kayi masa nazari me kyau zakasan cewa zallar yaqe ne takeyi me masifar ciwo

“Sannu da zuwa,ka dade kuma cemin kayi da wuri zaka dawo” ta fada a shagwabe kamar yadda ta saba. Wani abu me matuqar girma ya hadiye a maqoshinsa,wanda ita kanta dake tsaye tana iya ganin yadda maqwallatonsa maqogaronsa yayi sama sannan yayi qasa,mummunar faduwar gaba da kokwanto suka lullubeshi,yayi namijin qoqarin qaqaro murmushin da yafi kama da kuka,cikin sanyin murya yace

“Eh……na dan tsaya ne,momee na raka wani guri” murmushi ta kuma saki tana gyada kai,amma kuma zuciyarta na wani irin qonewa,ba zata iya ci gaba dayi masa wannan murmushin tana kallon fuskar da take da mugun baqi a idanunta ba,don haka ta waske ta hanyar juyawa zuwa ga ledar tana cewa

“Let me see me aka kawomin” baice komai ba sai cika qofar da yayi ya juya ya fita a dakin,ta daga kanta a hankali tana sakin ledar ta fadi qasa,tabi qofar daya bar mata a bude da kallo,ruwan hawaye suna cika idanunta,dukkan wani tabbaci da yaqini yana sake samuwa a tatttare da ita.

          A daren babu wani abu data iya ci,hakanan bata sake ganin adam ba,sai sintiri da motsinsa me qarfi data dinga jiyowa daga dakinsa zuwa parlor,haka ta duqunquna cikin duvet,idanunta a runtse zazzabi yanason kamata.

             Sai wajen sha biyu saura sannan ya shigo dakin,har a sannan tana kwance ne kawai idanunta sun soye,babu wani alamun bacci,tana ga monitoring motsin adam din. Yana kunna fitilar dakin ta miqe tana hamma tamkar daga bacci ta tashi,ta kalleshi suka hada idanu tana mutstsuka ido

“Kada kacemin sai yanzu ka shigo?,har nayi baccin farko?” Ta fada tana qare masa kallo,daga shigowarsa gida zuwa yanzu har wata rama taga yayi,fuskarsa ta fada,ya firgice gaba daya

“Eh sai yanzu……ina wani aiki ne”

“Maimakon ka kirani na tayaka saika barni nayi bacci ni kadai?” Ta saje fada a shagwabe,kamar amma gasa zuciyarta,bata iya jin amsar daya bata ba,sai kansa daya shafa.

           Saukowa tayi da niyyar zuwa tayi fitsari sannan ta daura alwala ko zataji sauqin zuciyarta,amma mararta ta riqe gam,saita zauna daga bakin gadon tana cije lebe,kanta a qasa tana ambaton sunan Allah

“Yau su waye da waye sukazo gidan nan kam?” A hankali ta daga kai ta kalleshi,yana zaune gefan gadon ko kayan jikinsa baiyi nufin cirewa ba,kai ta girgiza

“Ai yau ni kadai ka bari a gidan na wuni kamar tsohuwar mayya” ta amsa masa tana kafeshi da ido,sai ya danyi jim sannan ya zame ya kwanta kamar wanda zazzabi ke shirin saukar masa.

          Koda ta dawo kwanciyar ta tayi,ta kuma saki jiki sosai kamar wadda ke bacci,tana jinsa yanata juyi,ta kwanta ya tashi ya miqe ya fita ya dawo,har zuwa sanda addu’a taci qarfin idanunta baccin da takewa kanta fata yazo.

             Washegari bayan ta farka daga baccin daya dauketa bayan sallar asuba baya dakin,data fito falo sai taji motsinsa a bedroom dinsa,koda fa leqa ya yiwa komai na dakin filla filla

“Halan furniture zaka sake mana?” Ta fada tana dariya,ba fara’a ko daya a fuskarsa,sai kai daya girgiza

“Sanitation nakeyi” ya amsa mata a taqaice

“Ya kamata, shikenan yau bari na fansheka na hada mana breakfast” bata jira cewarsa ba ta juya ta fice.

           Tana girkin tunani fal zuciyarta da ranta, sauqinta daya tun jiya bata fasa kiran sunan Allah a baki da zuci ba,tana samun raguwar quncin sosai da sukunin zuciya,tanason gayawa afifa,to amma ta tabbatar yadda afifa keda haushin adam komai ma zata dagulashi,ashe akwai abinda ‘yaruwarta keji a jikinta shi yasa ta tsani adam har haka?,me yasa ita bata taba jin komai a kansa ba?,sai tarin yarda da aminci?,ko don ita za’a jarraba?,shi yasa komai nasa yayi tasiri a kanta?,bata taba manta yadda haduwarsu da adam ta samo asali,a b u k,yana level 400 gab dasu fara final exam,tana level 200.

            Sam adam ba ajinta bane,hasali ma sãahar din tun a sannan da take da shekaru qanana she has a CHARISMA that attract many people to her,ba kowanne namiji ke iya tararta da sunan soyayya ba,amma adam din ya daukarma ransa saiya siya soyayyarta,yana da baiwar BAKI da IYA TSARA MAGANA(abubuwa biyun dake cutar ‘yammatan wannan zamanin kenan game da maza),tun daga randa ya bayyana mata soyayyarsa tayi gaba a wajen ta barshi kamar sauran samarin dake yawo a kanta,ya shiga ya fita yasan komai a kanta,ya zaqulo dukkan wani abu dake burge sãahar,abinda tafiso da wanda bataso,ya maida kansa irin wannan mutumin sak,a duk inda yasan zasu hadu,sai yayi wani abu daya tabbatar zai burgeta ko kuma yana cikin likes dinta.

       Ya jima yana bibiyarta da rayuwarta kafin ta daina ganinsa tsaf,abinka da zuciya da akace tanason me kyautata mata,tana kuma qin me munana mata,tun bata damu ba har ta fara jin babu dadi,basa makaranta daya da afifa,afifa na northwest a sannan,a b u k din da take kuma ita bamai kule kulen qawaye bace,tana da mugun miskilanci sosai,idan kaga sakewarta to irin iyayen nan masu zuwa da qananun yara,a nan ne zaka ga jerarrun fararen haqoranta,wannan din kuma sai ya sanya mata farinjini sosai gurin matan,gefe guda ga mazan dakeson miqa soyayyarsu a gareta,wadanda sukasan ita din me ajice kuma tafi qarfin ajin ajinsi,suna fatan koda abota ko qawance tayi dasu uwa uba tana da wata irin basira,tana da brain qwarai da gaske,wadan nan su suka sanyata zama sananniya sosai.

             Sai bayan wani lokaci sannan ya dawo,ko a sannan bata sake masa yadda yakeso ba,saidai an samu improvement akan yadda suke a baya,da wannan ya samu qofa ya kuma baje duk wata basirarsa,wadda sai data kusa qarewa tasss kafin ya samu dasa qaqqarfar soyayyarsa a zuciyarta.

          Bai mata qarya ba ya gaya mata wayeshi,su din ba masu shi bane,yana rayuwa ne da mamansa wadda ita ke daukar nauyin karatunsa da komai nasa,yana fargabar gidansu kamar ba zasu bashi aurenta ba,amma da yake Dr mamman girema dattijone,duk da yadda ya muhyi da yaa Saifullahi sundan nuna basaso,abinda ya tsayawa adam a rai kenan,amma dr mamman ya tsaya akayi komai,ba takurawa ba tsawwalawa,abinda ya girgiza kowa ya bawa kowa mamaki. A irin zallar kyau tsarin halitta gata da kuma aji na sãahar,ba wanda ya taba kawowa zata auri mutum me qaramin matsayi da matakin wadata a rayuwa irin ADAM. Sam ita ba wannan take dubawa ba,mutum ce da bata dauki rayuwarta da zafi can can ba, soyayya da kulawar da momee din adam ke nuna mata kawai ta isa ka kalla ka qara kalla,duk da cewa farko farkon aurensu,wata irin tsana ta yiwa afifan,qiri qiri ta nuna bata sonta,wanda ba wanda yasan meye dalili,amma dare daya komai ya canza,ta sata a jikinta da soyayyar da ko adam din bai sameta ba.

         Tun asali haka kawai wata irin rashin jituwa ke a tsakanin afifa da adam,wanda sai a wanann lokacin sãahar din wasu abubuwan suka fara zuwa kanta,ta fara tariyar dalilin da abubuwan daka iya jawo haka,ciki harda wannan yanayin data tsinci kanta a ciki a yanzu.

      A sauqaqe ta hada simple breakfast,ta samu ta durawa cikinta tea da chips ta miqa masa ta wuce nata dakin.

          Wanka tayi ta shirya kanta cikin sauqaqan kaya,tana cikin hutu ne data dauka a gurin aiki saboda yanayin laulayinta me dauke da ciwo,don haka ta shirya kanta cikin wata simple gown,ta koma saman gado tayi kwanciyarta ba tare data sake koma masa ba,zuciyarta cike da tunanuka iri daban daban,duk da yadda taketa qoqarin hana kanta,ko don lafiyar abinda yake cikinta.

           Tana jinsa yana waya sama sama amma bata iya tantance ainihin abinda yake fada,sai kai kawonsa lokaci zuwa lokaci,kusan awa biyu cikakku sannan ya tura qofar dakin nata,tana daga kwancen ta daga kai ta kalleshi,gaba daya yayi wani hajaran majaran dashi,suka hada ido,yau ko yaqen da yake ta qoqarin mata tun daga jiya zuwa yau ya kasa,sai haqora daya bude mata kawai

“Ko zaki tashi kema ayi miki sanitation din?” Idanunta tadan juya kadan,baqincikinsa yana sake cikata,ta gama fahimtar inda ya dosa tsaf,don haka hankali kwance tace masa

“Ka manta kowanne wata daga gida ina kiran masu aiki suyimin irin wannan gyaran?”

“Na sani,yau ni nake sha’awar nayi miki” ya fada adan diririce da kuma alamun zaquwa,bata sake ce masa komai ba,ta miqe tsam ta kwashe duvet dinta tayi hanyar falo,don wani sanyo sanyi takeji dake nuna alamun zazzabi yana tafe.

           Tun idanunta suna kan tv tana sauraren motsinsa daga dakinta har baccin da bata samu isashe ba daren jiya yazo ya sureta,baccin da babu komai cikinsa sai takura da mafarkai marasa dadi,wannan ya sanya batayi nisa ba ta farka,mararta ta cika da fitsari,ta yaye duvet din ta sauke qafafunta qasa ta nufi bedroom dinta.

           Yana zaune saman bedside drawer dinta,ya aza dukka hannayensa guda biyu saman kansa ya dafe,kamar wanda mummunan ciwon kai ya cimma,ya maida komai inda ya jawoshi,saidai dakin ba abinda yayi face hargitsewa,ta san za’a rina,don bashi da cikakkiyar nutsuwar maida mata dakinta yadda yake,kawai ta barshi ne don taga iyakacin gudun nasa ruwan,ta kuma sake badda tunaninsa.

Page 47

          Toilet din ta wuce abinta,sai da tayi fitsarin ta sake daura alwala sannan ta fito,zuwa sannan ya sauke dafe kan nasa da yayi,ya goge hannuwansa a qirjinsa,suka hada ido,ta janye nata idanun tana bin dakin da kallo kafin ta sauke a kansa

“Wannan ai wani aikin kawai ka bani,ka sake hautsinamin daki” iska ya furzar daga bakinsa yana ritsata da idanu,yana jin kamar ya yaye duk wani hijabi dake tsakanin kowanne dan adam da abokin maganarsa,ya gano inda ta ajiiye masa jakar,yana jin wani irin tashin hankali yana saukar masa,fargaba da wani irin firgici,wani sashen zuciyar tasa kuma tana cike ne da tantama,don yasan tabbas sai daya kulle dakinsa kafin ya fita,kuma tuntuni ya kwashe dukka spare keys din,suna gurinsa,kowanne kuma a cike yake babu guda daya daya bata,to amma ai jakar bata da qafafu,zata tafi da kanta ne?,ko kuwa fiffike tayi?.

“kasala ce ta saukarmin” abinda ya fada kenan ya miqe yana jan qafafunsa ya fice,ta rakashi da kallo,taja tsaki hawaye nabin idanunta,mutum har mutum,amma yaudara ha’inci gami da cin amana sun ratsashi,itakam me zatayi da adam?,batajin har abada zata sake yarda dashi.

         Cikin kwanakin gaba daya ya gama zama wani iri,babu cikakken kuzari kwata kwata a tattare dashi,tuni dafa abinci ya zama tarihi a gidan,don dama shine yakeyi,ita bata iyawa sai jifa jifa,to daga ita har shi din a yanzu babu wanda yake da nutsuwar da zai tsaya yaci abincin ma gaba daya. Saidia yayita sintiri a kanta,ita kam koda wasa taqi nuna masa tasan komai kota gane abinda yake wakana,ta kawo idanu ta zuba masa,ta rungumi addu’a kawai,tana jiran ganin abinda hali zaiyi,murje idanunsa ne zai kawo kansa ko kuwa?.

            Shi da ita gaba daya sukayi rama cikin kwanakin,basa wata doguwar magana a tsakaninsu,duk da tana ta qoqarin yin komai kamar yadda ta saba,saidai yadda zuciyarta ke mata ciwo,wani lokacin tana buqatar kebewa,sai tayi masa qaryar batajin dadin jikinta,baya cewa komai shima,saidai hakan na sake dulmiyashi cikin kogin kokwanton ita ta dauke jakar koba ita bace.

*_K A C I Ɓ U S (M U G U N G A M O)_*

            Wai bahaushe yace kaciɓus mugun gamo,sau da dama akwai zazzafar  jarrabawar da zata fado rayuwarka,har wasu lokutan idan bakayi da gaske ba ta kusan zama silar rabuwarka da imaninka(wa’iyazubillah)amma kuma sai ta zamewa rayuwarka MABUDIN ALKHAIRI,sanin gaibu sai Allah,tabbas haka yake,batuna kuma da bashi canzawa.

           A cikin wannan yanayin da rayuwarsu ke tafiya a kai,cikin huwacewa ta ubangiji Allah ya qaddara tafiya aikin hajji ga dukka familyn Dr mamman girema,matarsa,yaransa harma da jikokinsa,da ‘yan uwa na kusa da sukan biyawa,ciki harda afifa. Tun asali an tsara za’a yi tafiyar harda sãahar,amma samuwar cikin jikinta ya kawo zare sunanta daga cikin masu tafiyar.

           Taji ba dadi sosai,saboda tafiya ce da sau daya suka taba yinta wannan shine karo na biyu,ko wancan karon da akayi tafiyar gab da bikinta ne,taji dadin aikin hajji qwarai cikin familynta,kuma abune dama da yakan yiwa kowa dadi idan ka gudanar dashi cikin tawagar iyalinka.

          Tun ranar da sukayi waya da maama ta sanar mata tafiyarsu zata iya kamawa next week taji gana daya jikinta ya sanyaya,sai takejin kamar idan sun tafi ba zasu dawo ba,ko kuma ba zasu dawo su tarar da ita ba,cikin jikinta ta dinga jin kamar akwai wani babban abu mara dadi dake tunkarar rayuwarta,don haka cikin satin ta dinga ziryan zuwa gida. Wuni take a jikin maamanta,afifa na gefe suna hira,dukkansu sunga yanayinta ya canza,ga ramewar sa tayi,maama ta fara tambayarta

“Ko akwai matsala ne tattare da cikin?” Kai ta girgiza

“Nima bansan me yake sakani ramar nan ba maama” saita jinjina kai

“Allah ya raba lafiya,karki dinga zama haka,ki kula da kanki da kyau don Allah”

“In sha Allah” ta amsa tana maida kanta ta kwantar,tana jin kamar kada ta koma gidanta,kamar tayi zamanta tare dasu. Afifa dai tana gefe batace komai,har maama ta gama abinda takeyi ta fita ta barsu a dakin,afifa ta ajiiye nail cutter din hannunta ta kira sunan sãahar,tana daga kwancen ta kalleta

“Ban yarda da cewar babu abinda yake damunki ba,kamar yadda maama ma na tabbatar bata gamsu da xancanki ba,kawai don ita din me kawaici ce,wadda kuma bata cika takurawa sai taji sirrin da mutum ya yanke ya barwa cikinsa ba” shuru sãahar tayi idanunta a runtse tana jin heart beat dinta har cikin kunnuwanta,hawaye masu dumi suka ciko idanunta da suke runtse amma taqi basu damar zubowa,tsahon wasu mintuna,batace komai ba itama afifa bata sake magana ba,ta buda bakinta a hankali

“Tabbas akwai abinda yake damuna,babbar matsala ce da take gab da rabani da gidan aurena,idan har shuru yaci gaba da wanzuwa a bakinsa ba tare da kowanne irin sauyi na bayani ko bayyana kai daga gareshi ba,to komai zai bayyana,zan bayyana komai da kaina da kuma bakina” ta qarashe zancan tana bude idanunta akan afifa.

              Sosai afifa ke kallonta kamar meson karanto matsalar data kira din

“Amma kinsan barin kashi a ciki baya maganin yunwa?” Ta fadi bayan ta rasa wacce kalma zata fada din,don gabanta wani irin faduwa kawai yakeyi da yadda taga fararen idanun saahar din sun canza launi. Wani malalacin murmushi ta saki,ta saukar da kanta qasa

“Na sani,amma komai yana da lokaci” shuru ya sake ratsa dakin,afifa ta jima tana karantar fuskar sãahar din,sanann taja numfashi ta sauke

“Allah yasa muji alkhairi” bata amsa mata ba,tadai maida kanta ne kawai ta kwantar, Allah ne kadai yasan me gobe zata haifar,Allah ne kuma kadai yasan ya rayuwa zatayi da ita a gobenta.

           Randa ake sanya ran tashinsu tayi niyyar kwana a gida ne,don haka da shirin kwana ta taho,cikin ikon Allah wajen sha daya na dare saiga kira mahajjatan qaramar hukumarsu su fito,cikin qanqanin lokaci gidan nasu yadan cika da masu sallama da kuma wasu daga cikin wadanda za’a yi tafiyar dasu,wasu kuma daga gidajensu sun wuce airport din,ba jinkiri suka fito,motarsu daya da maama da kuma afifa,jikinta a sanyaye tana kwance jikin maaman

“Ni ina ganin idan ba dama ku koma asibiti ayi miki checkup,hankalina ba’a kwance yake ba sãahar tun ranar nan,bana ganin alamun lafiya a tattare dake,idan mukaje muka dawo still babu sauyi,zan yiwa yayanku magana ya siya mana ticket muje Egypt ko india a dubaki da kyau,jiya jiya abbanku ma yakemin qorafi” kamar maama din ta xungureta,saita sake lafewa a jikinta tana sakin siririn kuka, zuciyarta sam ba dadi,rayuwarma jinta take kawai gata nan gata nan,kukan da ya tashi hankalin maama din sosai

“Anya ba damuwa?,anya zan tafi na barki a haka?,me yake damunki?” Yadda taga hankalin maama ya tashi ya sanya ta sassauta kukan,tana kuma qoqarin daidaita kanta,batason tayi asarar aikin hajji guda saboda ita,wataqila dukka ayyukan hajjinta a wannan ne zata samu cikakken karbabbe me cike da da cewa da rahamar Allah,ba zatayi mata wannan asarar ba

“Lafiyata qalau maama,zanyi kewarku ne,duk kun hada baki kun tafi kun barni” ta fada tana kebe fuska

“Ba zamuso wani abu ya sake samun abinda yake cikinki ba,idan Allah ya saukeki lafiya zakuje umra keda adam din,hajj kuwa zagayowar shekara kamar yaune,zuwa sannan ma zaki iya yayemin jikana saiki ajjiyemin abina ku tafi” kiran sunan adam da tayi kamar wani fami ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta,saita sake lafewa jikin maaman ba tare da ta sake cewa komai ba.

           Tana tsaye ita da sauran ma’aikatan gidansu da ba dasu za’a je ba wannan karon har jirginsu ya tashi,zuwa lokacin qarfe sha biyu dai dai na dare,kubra daya daga cikin masu aikin biye da ita suka koma inda motocin gidansu ke fake,ta shige daya daga ciki,drivern yaja suka bar airport din.

          Tun a motar ta hada kai da gwiwa cike da damuwa,tana jin kamar ita daya tayi saura cikin duniyar,suna isa gidan ta wuce dakin maama,gadonta ta haye ta lulluba da duvet dinta tana jin wata matsananciyar kewarta da bata taba jin irinta ba tunda suke tafiye tafiye,saboda akwai adam a gefanta,a lokuttan qauna da soyayya da kuka tsantsar kulawar da take kashe mata kewar duk wani makusancinta,a lokacin da yake nagartaccen miji tsayayye da baya gajiya da nuna mata zallar soyayya da kulawa,amma ayanzun daya zame mata tamkar wani shirgegen maciji dake dauke da uban dafi a bakinsa,dafin da takejin taqin dake tsakaninta dashi bashi da yawa,wanda da ace ya kai ga tsarta mata shi da wani zancen ake ba wannan ba.

             Cikin daren tayi wani irin kuka da yafi dukka sauran kukan da tayi a baya ciwo da yawa,ta tabbatar a rayuwa babu abinda yafi maraici d’aci da kuma ciwo,irin ciwon dake da tsananin wahala,kamar tasan qarin MUMMUNAR QADDARAR da take sake jiranta a washegari.

          Wannan kukan ya sanya tun asuba taji jikinta ba dadi,ta laluba magungunanta na anti natal ta barsu a gida,ba yanzun ta shirya komawa gida ba,to amma ya zama dole,don tana buqatar magungunan,don haka da safe bayan ta karya da abincin da take samu tana sanyawa cikinta da qyar saboda dan tayin bawan Allahn dake cikinta,tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar da a yanzun kusan suta maida kayan sawarta,kamar wata me takaba,kyakkyawar fuskar nan ta kode saboda kukan data kwana tanayi,saidai har a lokacin wannan sassanyan kyan bai gushe ba,ta karba key na daya daga cikin motocin,a yau fushin dake cinta a zuciya da tashin hankalin da rayuwarta ke ciki ya gaza boyuwa,ba fara’a ko alamun sukuni sam a fuskarta,wannan yanayin yasa cikin kulawa kubra tace tazo ta rakata?,kai kawai ta girgiza mata ta fice a gidan.

*_Turqashi!!!!,shin me zata tarar?_*😭😭😭😭

Page 48

          A qofar gidan ta tsaida motar,da nufin ta fita ta bude gidan,tunda ta sani,ya gaya mata shima zaiyi tafiya ta kwanaki uku.

             A hankali take takawa zuwa qofar gate din,saboda yadda mararta ta sake qullewa,ta saka key ta buda qofar,ta tura qaramar qofar dake maqale jikin gate din ta shige.

           Bata ankara da motarsa dake ajjiye a farfajiyar gidan ba har sai data kawo tsakiyar gidan,mamaki yadan bayyana saman fuskarta,batayi tsammanin ganin motarsa ba,to amma sai zuciyarta ta bata wataqila tafiya ce ta team,a abun hawar ma’aikata suka tafi,ko kuma yabi jirgi ne ohon masa,duk da cewa tana tsammani zaiyi wuya indai ba biya masa akayi ba ya iya samun kudin biyan kudin ticket da sauransu. Tun daga sanda ya tattara komai ya kammale,idanuwanta suka kai ta kwashe,alamu da yawa suna nuna mata sauyin al’amura da yawa a tattare dashi,akwai abubuwa da yawansu da a yanzu baya iya aiwatarwa,hakan kuma yana nuni da cewa,dama can cikin kudadensu yake dukka birgima da facakarsa. Yage wannan tunanin tayi taci gaba da shiga cikin gidan.

           Mamakinta ya sake qaruwa lokacin data bude qofar falon,kaya ne a warwatse a qasan falon,ba watsewar kayan bace abun mamakin,gamayyar kalolin sutturar mace da namiji,daya dai tabbas kayan adam ne,yadin data siya masa a dinke a matsayin gift ranar zagayowar shekarar haihuwarsa,sauran kuma ba zata iya tantance suturar waye ba,tasan dai ba tata bace.

           Wani abune ya daki zuciyarta,amma saita matse zuciyar tata daga zarge zarge da tunane tunanen data fara debo mata,koma meye a yanzun bata rayuwar adam take ba,ta kanta da tata rayuwar da rayuwar abinda yake cikinta takeyi,koda tana buqatar sanin wani abu akai,tasha maganinta a yanzu shine abinda yafi zame mata me muhimmanci,tanajin mummunar fargabar da kuma mugun bugun zuciya,amma haka ta dauke idanunta daga kan kayan,ta kuma dauke idanunta daga kan sashen dakin adam dinma gaba daya ta nufi dakinta,saidai tana zura key da nufin budewa qofar ta tura kanta da kanta.

          Wani irin gurnani da sautin nishi ne abu na farko daya fara kaiwa ga idanunta,kafin daga bisani idanun nata su iya dauko mata hoton abinda ke wakana a tsakiyar gadonta na Sunnah,tare da mijinta na sunnah,cikin gidan aurenta na sunnah.

            Ba qaramin dan gajeran yaqi akayi tsakanin ido da kwanyarta kafin qwaqwalwar ta yarda ta kuma tantance mata gaskiyar abinda idanun suka hango mata. ADAM mijinta,tare da wata mace da ba zata iya gane ko wacece ba,suna aikata fasiqanci akan tsakiyar gadonta,dukkansu haihuwar iyayensu,dagashi har ita,ko duvet basu kaarantawa kansu sun rabawa jikinsu ba bare akai ga batun sutura.

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ta fada da qarfi sanadiyyar fusgota tayi daga cikin bakinta qarfi da yaji lokacin da numfashinta ke niyyar katsewa daga gangar jikinta.

         Dif taji sautuka marasa dadin dake tashi sun katse,ta daga kanta da yayi mata wani mugun nauyi tana sake qoqarin bude idanunta a karo na biyu. Tayi zaton ganin kowannensu a wani muhallin na daban yana neman sutura ko maboya,a’ah…….sabanin haka sai ta sake ganinsu a tare da juna,suna ci gaba da aikata alfasharsu hankali kwance,kamar ma basusan ta shigo ba.

“ADAM!!!” Ta kira sunansa da wani irin sauti kamar na mutuwa,waiwayowa yayi yana duban tsakiyar qwayar idanunta da rinannun idanunsa,ba kuma tare da ya fasa aiwatar da abinda yakeyi din ba. Wani irin mummunan fushi da tashin hankali ya rifto mata,ta daga qafarta da zummar kaiwa cikin dakin don ta dakatar dasu,saidai taku biyu kacal tayi!,wani abu me dumi taji ya tsarga daga mararta yana bin qafafunta,abinda ya sanya mata waigi,ta dakata a firgice tana binsa da kallo.

         Jini ne jajir yake saukar mata, shigen jinin data gani a wancan lokacin na baya,wanda ganinsa ya tabbatar mata da zuwan qarshen zaminin cikinta,a yanzun kuma me yake shirin alamta mata?. Da wacce jarrabawar zubarsa zaizo mata?, qwaqwalwarta batayi nisan kiwon da zata lalubo mata amsar tambayarta ta fara kokawa da numfashinta,a hankali ta soma gani dishi dishi,dukkan wani jarumta ta gabban jikinta ta fara zagwanyewa,saita fara sulalewa tana yin qasa,inda daga bisani ta kife kif a akan fuskarta kuma saman cikinta.

*******Ba zata iya cewa ga iya adadin awannin data dauka kafin dawowarta duniya ba,iya abinda zata iya tunawa kokawa data fara yi da zuciya da ruhinta,kokawar da batasan a gaske take yinta ba,har sai lokacin da taji ana bada umarnin riqeta,ba jimawa taji an daddanneta,bawai iya hannuwanta kadai ba,harda qafafunta,ta kasa motsa koda yatsarta,a sannan ta yanke shawarar buda idanuwanta taga ko cikin kabari take wannan al’amarin yake faruwa da ita?.

          Ba cikin kabari bane,cikin dakinta take,saman gadonta data tabbatar  an gama yamutsashi da qazantaccen al’amarin da idanunta suka gani a dazu,hannunta guda daya qarin ruwa akeyi mata,wani dogon baqin mutum dake sanye da lab coat yana tsaye kusa ruwan yana qoqarin zuba wasu allaurai,daga daya bangaren kuma adam ne,wanda ya haye fiye da rabon gadon,kuma shike daddanne da ita.

            Wani azababben bacin rai tsana da kuma mummunar qiyayyarsa ce ta zarto tun daga asalin qasan zuciyarta har zuwa saman fuskarta,wani irin qarfi yazo mata,tayi yunquri me qarfi sai gashi tayi nasarar ture adam din gaba daya gefe,saboda ya saki jikinsa,bai dauka zata iya aiwatar da hakan ba.

         K’arin ruwan da ake mata tasa hannu ta fincike,take ruwan ya soma zuba a qasa,jini kuma ya ballewa hannun nata,kafin takai ga miqewa adam din ya miqe tsaye yana dosowa inda take

“Karka sake ka matso inda nake,karka kuskure ka qaraso kusa dani,mugu azzalumi,macuci fasiqi,na gama zama dakai har abada wallahi,nayi nadamar saninka a rayuwata,nayi nadamar hada jikina da nayi da naka qazantaccen jikin” tana gama fada ta diro qafafunta qasa cikin fushi qasa,saidai tana miqewa ta jita fayau,kamar iska zata kayar da ita,jini me dumi ya sake zarto mata,amma duk da haka bata dakata daga fita da take niyyar yi ba. Ta tsani ganin koda inuwar adam bare ta hada daki daya dashi,ballantana kuma har suyi musayar numfashi,burinta kawai ta ganta ba a cikin gidan ba kota wanne hali,saidai tana kaiwa bakin qofa taji an fincikota an watsar,kafin ta gama gane ainihin abinda yake faruwa,an saukewa kyakkyawar fuskarta lafiyayyun mari guda biyu,wanda saida kunnenta ya dauke ya daina ji na wucin gadi,idanunta kuwa wasu irin taurari ta gani sun gifta,bata dawo hayyacinta ba adam ya bayyana a gabanta.

           Wata irin tsaiwa yayi a kanta,ya raba qafafunsa biyu a tsakiyarta yana duban qwayar idanunta da kyau

“Ina zakije da?,ai yanzu aka fara wasan,wasa ne me kyau dake nuni da kyakkyawan shirin bugashi da kikayi,wanda inda kinsan true color din abokin buga wasan naki da baki tarki yin irin wannan wasan dashi ba” mamaki ya sanya ta daga fararen idanunta da suka taruwar jini a gefe tana kallonsa

“Eh,idan kuma har baki shirya ci gaba da buga wasan ba……..hanya guda daya ce gareki,ki fiddomin jakata da kika dauke” kai tsaye babu wani bata lokaci ko dogon ta fahimci abinda yakeson fada

“Jakarka?” Ta fada bawai don tanason musawa ko kokwanto ba

“Yes jakata,wannan ne zai sanya na baki damar tafiya salin alin,ina tsananin sonki sãahar,don ban taba samun mace me zallar madarar kyau da cikakkiyar ni’imar da take iya gamsar dani,da wani irin dandano da dadi na musamman kamarki ba,amma wallahi wallahi nafison kudi fiye dake,kuma nayi imanin su zasu sake samarmin wata macen wadda ta fiki ma wala’alla a wata nahiyar duniyar,matata ba zata taba hanani yin duk harkokin da nakeso ba,saboda itama bai hanata tayi tata rayuwar ba,amma ke muddin zanci gaba da zama dake,duk wata shaqatawata da jin dadina saidai na ajjiyeshi a gefe saboda wai kiyaye mutuncin addini da kuma samun dorewar soyayyarki da zaman lafiya a tsakaninmu,kamar yadda nayi tsahon uku babu kadan a zaman da mukayi……wanda nikam bazan iya ba,inason rayuwa” ya qarashe maganganun nasa yana sakin wani mugun murmushi.

           Saita zama speechless,ta narke a wajen tana kallon adam din cikin tsantsar mamakin daya gama daskarar da ita a gurin

“Me kike kallo?,zaki ban jakata na sallameki ko saimun ci gaba da buga game din?”

“Da kudadena halalina zakayi wannan shaqatawar?” Ta jefa masa tambayar da tafi qona mata rai,tafi kuma yi mata ciwo a ranta

“Really,kin fini tarawa da yawa ai,sannan acan gida ma an tara miki wasu ana kan tara mikin ma kinga ya kamata naci gadonki tun kina raye,tunda na taqaita miki wahala ban bari kin haihu dani ba,wancan cikin na saka miki tablet yabi rariya salin alin,wannan ma yana fara girgidi na sanya aka zaquleshi aka watsar,don haka ina binki ladan aiki ma” sosai ta sake razana da bayanansa,ta miqa hannu ya shafo jinin dake bin qafafunta har yanzu ta kawoshi dai dai fuskarta tana kalla,wasu zafafan hawaye suka fara bin kuncinta,shikenan,shima ta rasashi. Wata irin dakiya taurin rai da zafin zuciya ne suka saukar mata a lokaci guda,ta daga fararen idanunta da a yanzun suka rine zuwa jajaye ta kalleshi da muryarta data qara kauri ta kuma cakude da sautin kuka

“Yadda idan mutum yabar duniya sunyi bankwana da ita kenan har gaban abada…….haka nan wannan jakar tabar hannunka har abada,koda hakan yana nufin rasa numfashina ne” miqewa yayi zumbur yana dubanta saboda girgiza da yayi da jin furucinta,yasan halinta tsaf fiye da kima,KHADIJA tana da matuqar taurin kai a wasu lokutan,hakanan ita din kaifi daya ce,idan tace YES tofa YES dinne,hakanan idan tace NO zaiyi wahala ta dawo tace YES. Da qyar ya tattara qwarin gwiwarsa,ya saki dariya ya qara taku biyu zuwa gabanta kamar zai take yatsun qafarta

“Nasan halinki fa,shi yasa na shiryawa dukkan wani taurin kan da zakizo min dashi,wuya da kuma azaba babu abinda bata sanyawa a barshi ko a aikatashi,idan ke qwararriyar ‘yar wasa ce to kin hadu da qwararren me buga wasan”

Page 49

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 49

     Juyawa yayi ga likitan dake tsaye a gefe abinsa kamar ma baisan abinda yake wakana ba

“Me kake jira likita?,ci gaba da aikinka” sai ya waiwaya gareta

“Kika musanta ko kikace zakiyi taurin kai…..zakici gaba da shan baqar wahala ne a hannuna,babu kuma wanda ya isa ya qwaceki”. 

      Zumbur ta sake miqewa ganin likitan ua dosota,har batajin ciwo da zubar jinin jikinta,da gudu ta doshi qofa,amma kafin ta isa adam din ya rigata,ya kankane qofar,daga bayanta kuma likitan yana tsaye yana jiranta,ta duba hagu dama babu ba wani gurin tsira sai qofar toilet,don haka ta kwasa ta nufa can da gudu.

      Harta wuce drawer dinsa ta hangi wayarta akai,ta dawo da baya ta finciki wayar ta qara gudu zuwa toilet din,idanun adam suka kai kai,ya baro bakin qofar da wani irin mugun sauri ya biyo bayanta,kafin ya iso ta samu nasarar shigewa bandakin,ta tura qofar,ta kuma danneta da bayanta. Hannunta na rawa ta kunna wayar,ta fara laluben wanda zata kira,zuciyarta tayi mugun karyewa sanda ta tuna a yanzun kusan dukka wanda take saka ran samun daukinsa baya qasar baya tare da ita,daga qarshe ta yanke shawarar kiran ummin afifa.

      Wayar tana ringing adam dake bakin qofa yana dannota iya qarfinsa tare da qoqarin bankadeta ya bude qofar,ta runtse ido tana sakin kuka,bakinta fal addu’ar kada Allah ya bashi ikon cimmata har sai ummin ta dauka,muddin bata dauka da wuri ba tasan cewa kashinta ya bushe,a yadda ta zubar da jinin nan,babu wani cikakken qarfi yanzu haka a jikinta da zata iya ci gaba da tare qofar.

       Ringing din ya tsaya,muryar ummin ta bayyana radau tare da yin sallama

“Zasu kasheni,zai kasheni” abinda ta fada kenan cikin qaraji,saboda nasarar bankado qofar da adam din ya samuyi,dalilin da ya sanyata faduwa gefe qasa warwas,taku biyu ya isa gabanta,yasa hannunsa ya damqe bakinta da kyau,ta inda babu damar da zatayi magana,ya zubamata ido da wani irin kallo na zallar rashin imani yana duban fuskarta tare da ja mata zazzafan gargadi da idanun nasa,sannan ya miqa hannu ya dauki wayar da har zuwa lokacin ummi ke fama cewa hello hello jin shuru ba’a sake magana ba.

      Kiran ya kashe sannan ya sakar mata baki,ya koma saman toilet ya zauna yana maida numfashi,ransa a matuqar bace

“Kin ginawa kanki da kanki rami,zakisan cewa bani da imani” yana fadin hakan ya kamata,saidai taqi miqewa tsaye sam,bai damu ba ya riqe hannunta da kyau ya fara janta a qasa kamar kayan wanki,bai ajjiyeta ko a ina ba sai a gaban likitan

“Kayi mata allurar bacci,ka hada mata data ‘yan shaye shaye me qarfin” tana ji tana gani ya danneta aka hada ruguntsumin alluran aka dirka mata,a hankali jikinta ya fara saki,saidai idanuwanta basu daina zubar da ruwan hawaye ba,hakanan bakinta bai fasa fadin

“Allah ya isa,Allah ya sakamin,Allah ka yimin sakayya”.

     Bai ko dubeta ba ya jawo stool gabanta ya zauna,yayi kiran ummi. Bugu daya ta daga a matuqar rikice

“Me yake faruwa da sãahar din?”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,muna cikin mummunan tashin hankali” ya fada da muryar kuka wadda a wajen ya qirqireta

“Me ya faru?”

“Ibtila’i ne ya samemu,na fita lafiya na dawo na tarar da ita cikin wani yanayi,ina shigowa kawai ta cakumeni ta fara fadin mugu azzalumi,ka cuceni zaka kasheni,Allah ya isa,Allah ya sakamin,ina tsammanin mummunan gamo tayi,don cewa tayi waita ganni da wata muna aikata alfasha,bayan kuma ni dawowata kenan daga tafiya,kwanana uku bana garin,yanzun haka gata ta sume,da qyar na samo kanta,duk tayi fashe fashe a dakinta” salati ummi ta saki tana sallalami cikin matuqar tashin hankali

“Yanzun tana ina?”

“Gamu a gida,amma na yiwa wani malami waya yana kan hanyar zuwa”

“Ganinan nima” ta fada a gaggauce tana kashe kiran.

      Iska ya furzar daga bakinsa,sannan cikin hanzari ya fara kiran wata number wayar daban. Bugu uku aka daga,sai ya miqe yana fita a dakin,yana amsa wayar a gaggauce.

     Sake lumshewa idanunta sukayi hade da wani zazzafan hawaye,zuwa lokacin sama sama takejin komai,hakanan dishi dishi take ganin abubuwa,amma duk da haka kwanyarta bata daina aiki ba,bata kuma daina haska mata girman cin amanar da adam yake Shirin aikata mata ba,wadda tafi abinda ya aikata mata a baya girma da muni. Kafin ya dawo bacci tuni yaci qarfinta.

       Sanda ta farka ta ganta ne kawai kaca kaca cikin shirgi da shara,tana yashe a qasa cikin dattin,gaba daya dakin ya kacame,hatta da mirror da wanda ke jikin sif din a farfashe yake,duk wani kayan ado da qawa dake dakin wanda hannu zai iya kaiwa gareshi a fashe yake.

    Cikin mamaki ta miqe ta zauna tana jin kallon ko ina,ita daya ce qwallin qwal a ciki,saita zabura ta miqe ta sauri ta nufi bakin qofa,tana fatan ta samu qofar a bude.

       Tana isa bakin qofar muryar ummi ta fara jiyowa,wannan ya sanya da azama ta dora hannunta kan handle din ta fara jijjigashi tana fadin

“Ki taimakeni….. kasheni yakeson yi,ki budemin,ki tafi dani don Allah” ta furta iyakar budewar muryarta,wadda bata da wani amo sam sam kasancewarta mai sanyin murya tun asali.

     Adam dake zaune qasan kujera wurjajan ya daga jajajyen idanunsa da sukayi jajur ya kalli qofar,kamar yadda idanun ummi dake sharce hawaye itama suke duban qofar

“To hajiya kinji irin takeyi,kuma duk sharrinsu ne” cewar wanda ke zaune daura da adam din,cikin babbar rugar malum malum harda rawani,da kuma tsayayyen gemun da wala’alla ciko ne akayi masa yayi irin wannan cikar,hannunsa kuma zabgegiyar tasbaha ce yake ta janta daya nabin daya

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,wannan wacce irin jarabawa ce ta saukarmiki sãahar da qananun da ko ashirin basu haura ba?” Ta fada cikin kuka

“Hajiya kar ayi sabo,shi lamarin ubangiji haka yake,jarrabawa kuma babu ta inda bata saukarwa bawa” malamin qaryar ya fada yana shafa gemunsa cikin nuna zallar taqawar da babu ita ko kusa ko alama cikin zuciyarsa

“Yanzu ba yadda za’a yi na ganta?” Da sauri ya girgiza kai

“Ai hajiya muddin aka rabata da wannan dakin ba abinda bazai iya faruwa ba,zasu iya dauketa ma a nemeta a rasata,shi kansa likitan da kikaga ya fita yanzu saida Allah yasa bacci ya dauketa ya iyayi mata gwaje gwajen da yayi,shima kuma yaga alamun tabuwar kwanya kadan,duk da hakan na iya yiwuwa duk cikin sharrinsu ne”.

      A yadda suka tsara komai abune mawuyaci ka fahimci cewa shiri ne irin na adam da muqarrabansa,cikin kwana daya tal ya maidata mahaukaciyar qarfi da yaji,kusan kullum a nan ummi ke yini,gudun tonuwar asirinsa yasa aka dinga yawaita yi mata allurar bacci da aka cakudata da allurar sanya maye,abinda ya qara nakasta garkuwar jikinta,ya zamana ko cikakken zama bata iyayi,data zauna din sai bacci,kota dinga bin kowa da kallo kamar sokuwa,sukayi amfani da wannan damar sukace maganin da malamin yakeyi mata ne ya fara aiki a jikinta.

     Fadin irin tashin hankalin da iyalan Dr mamman jarma suka shiga a qasar saudiyya sakamakon mummunan labarin tabuwar qwaqwalwar sãahar da suka samu bata baki ne,kada ma afifa taji labari,wadda a jikinta ta dinga jin cewa ba haka bane,hauka yana da sila da kuma sanadi idan ma har haukanne,koda ta sanadiyyar jinnu ne suna nuna wasu alamomi kafin sukai ga taba lafiya kwanyar mutum,tunda suke da sãahar basu taba ganin wani abu na daban tattare da ita ba da yake da alaqa da irin wannan lalurar.

     Mutane ne masu tsananun dattako da yarda da Allah wahidun ahadun,sun yi imani suna qofar waraka,qofar karbar dukkan addu’ar me neman,wajen biyan buqatar duk wani mabaraci,dukkaninsu sai suka duqufa da addu’a ta nema mata sassauci da waraka,tana da gata me yawa da soyayyar iyaye da yayye,hakanan qananun yaran da suka kasance ‘ya’yan ‘yan uwanta suna tsananin sonta,saboda ita din mutum ce me son yara qwarai,akwai soyayya da sabo sosai a tsakaninsu.

       Kwanakin da suke gabansu na ranar dawowa Nigeria sai suka zame musu kwanaki mafiya tsaho,duk da haka basu bari sunyi asarar kwanakin ba,sunci gaba da addu’a da ibada,tare da samin information na halin da ake ciki a wajen ummi.

**************Ta fuskanci duk wani abu da zatayi babu abinda zai hana adam aiwatar da abinda ya shirya mata,hakanan a yadda ya tsara din ta tabbata cikakkiyar mahaukaci ga idon kowa,tana jin muryoyin ‘yan uwa makusanta daga parlor din gidan masu zuwa dubiya gurin ummi,saidai ta zame ta kwanta lamo tana jinsu,don zuwa lokacin tayi kukan da batasan iya adadinsa ba,bai kuma qara mata komai ba hakanan bai rage ba,don ba abinda adam ya fasa,saidai yana gaya mata a kullum,zabin fitarta daga wannan yanayin ko tabbatuwarta a ciki yana hannunta,ta sallameshi shima a ranar zai sallameta kowa ya kama gabansa.

       Kwata kwata daina tanka masa tayi,saidai ya qaraci maganarsa ya tashi ya miqe ya fice,abinda yake sake dugunzuma ransa kenan tare da qara masa bacin rai a kanta

“Banda ina tsoron na qarasa gawar daba tawa ba,tabbas da sai nayi miki dukan da zaki raina kanki,amma ko a hakan ma muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura” ya miqe yayi fatali da gantalelallen abincin da ya kawo mata,ya samu kyakkyawan mazauni akan qafafunta,zafin abincin ya ratsata,amma bata iya janye qafafun nata ba saboda wani azabtaccen ciwon kai da take fama dashi,ko gani bata iyayi sosai. Da zugin ya isheta saita zame kawai ta kwanta a wajen tana maida numfashi,babu abinda zuciyarta ke ayyano mata sai irin rayuwar da sukayi ita da adam a baya,yadda ya kula da ita ya tattalata,amma zuwa wannan lokacin ya juye ya koma mata wani irin baqirin shaidanin kumurcin maciji me cike da guba da kuma dafi.

       Lokacin data fuskanci jinin cikin da cisge mata ta qarfi da yaji ya dauke,sai tayi wanka ta daura babban towel tayi sallah,baya rufe bandakin,don bazai iya jigilar gyara gurin ba idan ta bata. Darajar sallar data fara yi sai ta fara samun nutsuwa cikin ruhinta,daga mugun likitan har annamimin malamin,duk sanda sukazo saidai tabisu da ido,kowa ya gama mugun alkaba’insa ya fice,me allura yayi,me kawo tofin qarya ya kawo ya ajjiye saboda adam din yanason ya tara evidence na cewa yana kula da ita,kuma tabbas lalurarta akwai aljanu a ciki.

       Ko sau daya bata taba bata ba a lissafin kwanakin daya ragewa ahalinta su dawo,ranar da take sanya ran kwanaki biyu ko daya suka rage musu su dawo,bayan likitan ya gama dirka mata allurar ba tare da sunbi takan matsanancin ciwon kan dake gallabarta ba,wanda ya sake sanyawa ta zuqe ta rame ta koma ‘yar firit,sai sassanyan kyantannan da har yanzu yana nan shinfide a fuskarta.

Page 50

    Idanunta a lullumshe,tana ganinsa dishi dishi,amma ranta cike fal da baqinciki da kuma zallar bacin rai na hana mata samun salla,don tana gama alwala kafin takai ga tayar da sallar suka shigo mata

“Kaji tsoron Allah” ta samu ta fusgi kalmomin daga bakinta,cikin sautin galabaita,a fusace ya dawo gabanta ya tsaya,ya sa hannu ya matse fuskarta cikin hannunsa da kyau,wani zafi ya ratsa fatarta,ta runtse idanunta a galabaice

“Ke zan cewa kiji tsoron Allah,muguwa wadda bataso a qaru da ita,kina ta sakani ina sake asarar ragowar kudin hannuna gurin siya miki alluran da zasu ladabtarmin da ke,na rantse miki da Allah bazan taba barinki ki kubuta ba har sai kin fiddomin da jakata” yana kaiwa wannan ya jefar da ita ya fice yana huci.

      Duk da hankalinta ya kusa gushewa amma bata gaza tantance dacin kalamansa a kanta ba,a sannan tarwai take iya tuno sanda afifa dama maama ke jaddada mata tayi iskhara kafin ta bawa adam damar turo magabatansa, murmushi kawai tauiy,tana ganin tunda har Allah yasa abba ya karbeshi ya amince ya turo,duk da su ya Saifullahi basu gama gamsuwa ba,to ba shakka shi din Allahn ya zaba mata,bata kokwanto,bata kuma buqatar qarawa da istikhara din,kada taje hankalinta ya kasu biyu. Kuka takeson yi amma ruwan allurar yabi jikinta,haka tayi shame shame a gurin,ita bame rai ba,hakanan ita ba gawa ba.

       Abu daya da bata sani ba shine,yadda take lissafin ranar dawowar su maama haka shima adam yakeyi,ya kuma gama shirya komai,da dukka wasu allurai masu qarfi da za’a sauya mata dasu,wanda zasu sake sakata cikin bacci da maye mai qarfi,su kuma zabura qwaqwalwarta,ta yadda komai qwaqwafi da hasashenka baka isa ka fahimci lafiya qalau take ba.

      A washegari aka shiryo raihanatu aka kawota gidan da sunan zata dinga kula da sãahar,saidai duka hakan wani shiri ne da akayi don amintar da zukatan iyalan dr mamman girema. Da qaqqarfar gargadi momee ta tsare raihanatu akan babu ruwanta da dukkan abinda zata ji ko zata gani a gidan adamu,iyakar abinda akace tayi shi zatayi,wanda ba’a sanyata ba kome zai faru kada ta tsoma hannu ko bakinta,sabawa wannan umarnin nata,dai dai yake data rasa rayuwarta gaba daya,maganar datayi mugun daga hankalin raihanatu kenan,fitsari ya balle mata,ta roqi momee kan tayi haquri,kada ma ta kaita,saboda ta fahimci akwai abubuwa masu muni dake faruwa da anty sãahar din mutuniyar kirki me qaunarta,duk da bata gama fahimtar komai dari bisa dari ba,to amma jikinta da zuciyarta sun bata,kumnuwanta kuma sun tsinci kadan daga cikin wasu qulle qullen da momee din keyi tare da adam din.

“Bakin alqalami ya riga ya bushe,tunda har wannan gargadin nawa ya shiga kunnenki dole zargi xai darsu a ranki,tunda zargi ya darsu kuma dole kici gaba da rayuwa damu harmu cimma gaci” tana ji tana gani aka tattarata aka kaita gidan.

      Cikin kwana daya tak ta dinga jinta kamar cikin maqabarta take rayuwa,gunji da buge buge hadi da fashe fashen da takanji duk bayan wasu lokuta daga dakin anty sãahar din yana mugun dugunzuma mata hankali tare da daga mata hankali,kamar afifa,itama a jikinta ta dinga jin cewa tabbas sãahar ba zata haukace ba,Allah bazai taba barin mace me kyakkyawar zuciya irinta ta samu tawaya da naqasa irin wannan ba,idan tace ga sau nawa tayi kuka a kwana biyun nan saboda tsananin tausayin sãahar to tayi qarya,cikin dare bata iya bacci,har cikin ruhinta takejin tashin hankali da kuma damuwa da yanayin da sãahar din take ciki,don haka ta dinga shimfida abun sallah tana miqawa ubangiji kokenta akan ya kubutar da sãahar din daga dukkan kaidi da sharrinsu. (Ita kyakkyawar mu’amala da kuma kyakkyawar dabi’a yado takeyi,a yayin daka shiga tsanani,sai dukkan wanda yake tare da kai ko kuma ya sanka sai ya shiga damuwa me tsanani,wanda bai sanka bama sani na haqiqa labarinka yakeji,sai shina zuciyarsa ta shiga tayaka damuwa da kuma alhini,wannan duka sirrin kyakkyawar zuciya da kyakkyawar mu’amala ce,wannan soyayyar daga ubangiji take,a yayin da ya soka saboda nagartarka,sai ya sanya wannan soyayyar taka a zuciyar dukka bayinsa,suyita qaunarka ba tare da kun hada komai dasu ba,wasu ma baka taba yi musu wani abu na kyautatawa da zasu iya nunawa duniya ba,amma dai kawai suna jin labarinka,sai suji soyayyarka ta shiga ruhinsu,ya Allah,kayi mana baiwa da tsarkin zuciya da kuma kyakkyawar mu’amala 👏🏽 da daukacin bayinka)

*_RANA BATA ƘARYA_*

      Inji bahaushe,tunda ya samu labarin a gobe ne ake sakaran isowar jirgin KABO AIR da mahajjatan da suka hada da iyalan Dr mamman girema adam ya kasa zaune ya kasa tsaye,a ranar sãahar taga izaya nau’i daban daban,wata allura data sake birkitata akayi mata,tun safe bata farka ba sai yamma liqis,babu azahar ba la’asar,abinda yafi komai qona mata rai. Tana yunqurin tashi yana sanya muqulli ya bude qofar dakin,idanuwansa da suka canza launi suka kuma zuzzurma saboda bala’in da yakeji rayuwarsa tana ciki ya zuba mata,ya tako ya tsaya a kanta,sai kuma ya kalli agogon hannunsa,ya girgiza kai da sauri

“Nafison allurar da tafi wannan qarfi” ya fadi kansa tsaye,saboda ba tun yau ba,baya shakkar fadin dukka wani shiri nasa a kanta,ta dade da gama haddace koshi waye,ainihin tarihin rayuwarsa da komai nasa da yadda ya shirya faruwar komai kawo yau.

     Stool ya jawo zuwa gabanta ya zauna,sai ta miqe taja baya da sauri,duk sanda ya zauna gab da ita tana jin kamar ta cinnawa kanta wuta ne saboda tsabar tsanar data yi masa,duk ranar kuma da yayi kwanciyar aure da ita,ikon Allah ne kawai yake sanyata taci gaba da rayuwa. Takanji zuciyarta ta wani irin kumbura kamar zata buga,saidai bakinta baya rabo da kiran sunayen Allah,ta haka kadai take samun sassauci.

      Wani mugun murmushi ya saka ganin yadda taja baya

“Kwantar da hankalinki,yau da gobe bana neman komai daga guriki,so nake sai sha’awata ta taru nayi miki wankin babban bargo,ta yadda tafiyama zata gagareki,da haka sai na sake lanqayawa aljanunki nace sun fara ma kwanciya dake,hanya mafi sauqi da zan rattabamiki sakinki uku qwarara bayan na karbe jakata daga gurinki” maganganun nasa sune abinda suka sake fusata qwarai da gaske,karon farko data saki murmushi ta zauna sosai tana kallonsa.

“indai har yanzu wannan jakar tana cikin mafarkinka,ba shakka ba zaka gushe ba cikin buri da fata har qarshen rayuwarka,kayimin duk iya sharrin da zaka yimin,ka laqabamin dukka ciwon dakaga dama,kayimin dukka iya muguntar da kake jin ka iya,amma karka manta,Alla baya bacci,kuma baya barin zalunci,kuma alqawarin ne yayi rantsuwa sai ya taimaki wanda aka zalunta,bani da baqinciki koda ta sanadinka na mutu,amma ina me sake jaddada maka,daukan fansa daga ubangiji tana nan tafe zuwa kanka,a kusa ko a nesa” dariya sosai ya saki,ya dawo gabanta ya tsugunna

“Waya gaya miki inason ki mutu?,kuma ma a hannuna?,har yanzu ina sonki,ina qaunarki,kodon wannan kyakkyawar surar taki da bata gushewa,bin qwaqwafinki da bincikenki ya sanya kika tono wuqar yanka kanki,idan da ace baki zurfafa bincike ba,cikin biyu za’a yi daya,ko muci gaba da rayuwarmu a gefe ina tawa irin rayuwar dana zabawa kaina na kuma saba da ita,ko ki tashi dare daya ki nemeni ki rasa,amma zaki ci karo da takardar sakinki,salin alin koma gaban iyayenki ba tare da kin cutu da komai ba illa dukiyar kawai da zan kwashe,dukiya kuwa ana iya maida madadinta” kamar yau ta fara ganinsa haka ta zuba masa ido,ta karanci cewa yayi wani mugun nisan nisan da ko kira baya ji,tana zaune a nan idanunta suka fara lumshewa,ya miqe ya tsallaketa ya fice abinsa.

   *_W A S H E G A R I_*

     Tun daga airport su da motocin da suka daukosu basu saukesu ako ina ba sai gidan sãahar din,tun kan hanya afifa ta fara kuka tana jin tsinkewar gaba da tashin hankalin yadda zata riski ‘yar uwarta,hakanan maama daurewa kawai takeyi. Iya su yasu ne,yayyenta maza dukkansu sun wuce Egypt suna laluben asibitin da za’a kawota ayi mata magani,don sunce ba zasu iya dawowa su ganta a haka ba.

     Mutum biyar ne a falon nasa,malamin bogin da yake kira da sheik usama,sai almajiran daya hayo guda hudu,bude da qur’ani suka karantawa,shi kuma da baisan ko bihim ba yana zaune a qasa,ya tanqwashe qafa yana faman can tasbaharsa me dubu.

     Shine ya fara miqewa da sauri sanda su maama ke shigowa falon ya daga musu hannu alamun suyi shuru.

Page 51

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 51

     “Mahalan,mahalan(ku kwantar da hankali)” ya fadi da sigar lallashi

“Aiki mukeyi,kuma kukanku zai iya bada matsala,ayi haquri da qaddarar Allah,mijinta yana bakin qoqarinsa qwarai da gaske,kuma ko yanzu ma an fara ganin nasara,son ba ko yaushe suka sakata surutan da bige bige ba”.

       A nan suka zauna cikin matsanancin halin kuka da jimami,shi kansa gidan gaba daya ya sauya yayi wani iri,dama raihanatu tana bakin qoqarin tsaftaceshi da kula dashi,ita kanta tana zaune rakube daga gefe,tausayin iyalin duka ya kamata ganin tashin hankalin da suka shiga da cutar bogin da aka laqabawa matar da bataji ba bata gani ba.

“Ko zan iya ganinta?” Maama ta fada cikin zallar alhini da tashin hankali. Kallon juna adam da malam usama sukayi,sai ya maida dubansa ga maaman

“Bako yaushe ake shiga gurinta ba,saboda hakan yana sakata yunqurin guduwa,da kuma surutai marasa kan gado,amma yanzu barin na fara shiga nayi mata wasu addu’o’i,yadda ba zata cutar da ku ba koda kun shiga din” ya fadi hakanne saboda allurar da aka danqara mata sunason ta fara aiki,jikinta ya saki gaba daya,yadda ko magana ba zata iya dasu ba barw ta fadi wani abun da zata shanshano ainihin batun.

      Lokacin da ya shiga dakin ya isketa allurar ta fara mata aiki,ya hadiyi wani yawu muqut yana qare mata kallo,kullum yaga yarinyar sai ransa ya biya,tana da wani mugun kyau da kyakkyawar suffa,Allah Allah yake wataran ya samu dama kamar hakan nan sanda bata da sauran qarfi shima yadan dandanata,ya rage qishirwar dake ransa,baisan ma wanne irin rashin rabo bane ya sanya adam din yake mata wannan izayar,shikam inda shine ya mallaki zuqeqiyar mace irin wannan,baisan wanne asarar bace zata sakashi yayi sakacin da zai rasata ba,ai shi kam zai iya cewa ma Allah ya sallameshi a duniya dai.

      Kamar masu cutar rashin kuzari haka suka shigo dakin,su hudu ciki harda afifa da maama,gaba daya dakin a hautsine yake da fasassun abubuwa,wanda duka setup ne. Wani irin kuka afifa ta saki,ta kuma durfafi sãahar a gigice ganin yadda gaba daya ta koma zararriya sak,dakatar da ita malam usama ke shirin yi yana fadin

“Subhanallahi,karki qarasa gareta,na samu nayi musu addu’o’in kashe jiki,karki zaburar dasu” saidai kafin ma ya qarasa bayaninsa tuni ta isa. Rungume sãahar din tayi cikin jikinta,dumin afifan yana ratsata ta sauke wata iriyar qaqqarfar ajiyar zuciya,ta lumshe idanunta da suka kasa sauka daga fuskar maama dinta,tanason koda motsa labbanta ne ta fadi kalmar da maama zata fahimci diyarta lafiya lau take amma ta kasa furta komai.

       Irin kukan da suka wuni sunayi zai baiwa dukkan me imani tausayi,don ko raihanatu haka ta dinga boyewa a kitchen tana tayasu kukan, tare da jin qaqqarfar tsanar momee da shi kansa adam din,duk da kasancewarsu jininta. Abinci kuwa ba wanda ya iya sakawa cikinsa dukkansu,har zuwa dare suna zaune a gidan,daren da ya riski sãahar batasan ma me akeyi ba,tana can wata duniya ta daban da adam da likitocinsa suka kaita.

      Da qyar Dr mamman ya lallabasu maama da afifa suka wuce gida,da nufin gobe sa dawo. Hankalin adam ya tashi sosai jin su yaa Saifullahi suna can neman asibiti me kyau da zasu dauketa su kaita,hakan ya tabbatar masa asirinsa yana gab da tonuwa,sannan kuma yana gab da tafka asarar da gwara mutuwar sãahar a wajensa akan yayi wannan asarar ta dukiyar daya narka zuwa dollar,ga passport dinsa na yaransa dana matarsa duka a hade. Kwana maama tayi tana kuka,tana ganin abun kamar almara, innocent sãahar dinta,wadda duka duka shekarunta tsakanin ashirin ne zuwa ashirin da daya,idan tayi wuta sa biyu amma wannan mummunar qaddarar ta afka mata.

      A daren gaba daya afifa bata samu bacci ba itama,duk inda ta juya fuskar sãahar take gani,kamar yadda adam baiyi bacci ba shima,yanata juya yadda zai matsa sãahar din ta sallameshi salin alin,tun bata ritsa dashi ba.

      Wannan tunanin ya sanya washegari ya yayyaba mata maganganun da suka qona mata rai yasa kuma akayi mata allurar maaye da kyau waiko zata magantu,wannan yasa ta zabure,ta dinga fashe fashe tare da surutai a dakin saboda qarfin allurar,hakan kuma sai yayi dai dai da zuwansu afifa. Abun ya yiwa adam dadi ganin tashin hankulan dake kan fuskarsu tare da sake yarda da cewa eh lallai sãahar din ta haukace,wani irin mawuyacin yini sukayi a gidan, qwayar shinkafa babu wanda ya kaiwa cikinsa sai zallar ruwa. Sãahar na kwance daga bakin qofar dakin inda allurar ta bugar da ita daga qarshe tana jin muryoyinsu jifa jifa,wannan yasa ta yita motsa bakinta tana magana dasu,amma babu me jinta kasancewar sautin baya fita,taji muyar maama dinta na addu’ar Allah ya yaye mata ya bata lafiya yafi sau shurin masaki, furucin dake qonawa gami da soya mata zuciya,ya tabbata dai da gaske adam yaci galaba a kanta,ya kumma manna mata haukan dai,sannan ya sauya mata suna zuwa MAHAUKACIYA, sunzo sun taddata tana attitude na mahaukata tuburan.

*_W A S H E G A R I_*

       *_waiwaye_*

“Ina sonki…..kuma banajin zan daina sonki,saidai kin shiga hurumin daba naki ba,kin shigar gonar daba taki ba,kin tsallake iyakarki,kuma a yanzu nafi buqatar wadan nan abubuwan fiye dake,ki daukominsu ki damqamin,ke kuma na barki kici gaba da rayuwarki cikin salama” kai take girgizawa tana hawaye,wani irin mamakinsa tana jin kamar zai kasheta, kowacce rana da zata bullo zuwa faduwarta cikin shakka da kokwanto take,anya wannan din ADAM NE?,anya adam dinta ne?,anya musanyensa akayi mata ba?,ko kuma wata rundunar mugayen shaidanun aljanu ta shige jikinsa ne ta samu mafaka?,don abinda yakeyi a yanzun da ainihin wannan suffar tasa ta yanzu…….bata taba ganinta a tattare da adam dinta ba,koda kuwa cikin mafarkan bacci bare a kai ga rayuwa ta zahiri,adam din da ko quda baya qaunar ya sauka a kanta?,adam din dake kuka da idanunsa idan bata da lafiya?,adam din da yake kasa bacci saboda ta shiga damuwa?,adam din da yake kasa sukuni idan tana da buqata har sai ya adar mata?,dole ta shiga shakka…..amma kuma kullum yana qara tabbatar mata da cewa shi dinne fa,bawai kama ko musaye bane,to me yake faruwa?.

“Bazan taba baka ba…..burinka bazai taba cika ba,saidai na rasa rayuwata,kayi duk abinda kaga dama” ta fada tana jin bacin rai yana taso mata,tare da wani irin qwarin gwiwar tunkarar duk nau’in kalar azaba tuggu da makircin daya shirya mata.

      Wani murmushi ya kuma saki yana dubanta,da wani irin kallo na qasa qasa mai cike da tarin mugunta

“Ke kike jawa kanki koma meye,tunda ke muguwa ce ba zaki iya sallamamin abinda kikafi qarfinsa ba tako ina,to nima bazan sassauta miki ba har sai sanda kika gasu,kikaji cewa zaki iya sallamawa” daga haka ya miqe,ya fara fidda kayan jikinsa yana zubarwa a wajen.

      Idanu ta bude da kyau cikin tsananin tashin hankali tana dubansa,kada dai ace haqqinsa na aure yake shirin karba kamar yadda ya saba?,zallar rashin imanin da yake gwada mata bai sanya ya daga mata qafa ba,yakance

“Har yanzu fa a sunan matata kike,ban saki igiyar ba,wannan abun dake faruwa wani issue ne na daban daya shafi interest dina da kuma naki”. A duk lokaci irin wannan idan ya rabeta tana jin inama zata bude idanu taganta kwance cikin ramin qabarinta?,banda addininmu ya haramta kisan kai,naka ko na Wani,tabbas da tuni ta tsufa da kai kanta kiyama.

      Da gaske so yake ya kusanceta alhalin yasan cewa cikin jinin al’ada take,rashin imanin nasa qara gaba yake,dole tace rundunar shaidanun aljanu ne suka shigeshi,don lamarinsa yafi qarfin shaidani guda daya.

    Kansa tsaye ya nufota gadan gadan,kamar ba adam din nan da abaya a lokutta irin wanann yake sanyata taji babu ya ita cikin ‘ya’ya mata ba,ya sanyata taji duk duniya babu macen da tayi sa’ar abokin rayuwa irinta ba,a yanzu ya koma mata wani tsohon annamimin ifritu mashayin jinin bil’adama da ko motsinsa bataso ji bare ya rabeta,bashi da maraba da qaton shaidani a idanuwanta.

     Ringing din wayarsa ya dakatar dashi daga sake tunkarota,sai ya koma cikin aljihun wandonsa da ya yasar yana lalubar wayar. Cikin hanzari ya karata a kunnensa,sai kuma yace

“Ok,yanzu yanzu?,tom” ya latse wayar da sauri ya maidata,sannan ya soma mayar da kayan jikin nasa tana daga zaune tana kallonsa.

     Ga mamakinta sai taga yana bi yana balle button na rigarsa yana watsarwa,ya kama gaban rigar da qarfin tsiya ya ciccisge,sannan ya tsugunna ya jawo plate din tangaran din dake ajjiye gefe wanda ya kawo mata abincin da bata budawa bare ta taba,ya dagashi har abincin ya tamfatsa shi da qasa ya tarwatse,ya dauki wani yanki daga ciki ya yanki jikinsa ya kuma shashshafe maiqon a jikinsa.

      Sake miqewa yayi ya fara fatali da kayan dake saman madubi da duk wani abu na glass dake dakin yana cewa da matuqar daukaka murya

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,ki tsaya……ki tsaya don Allah,ya salam,karki jiwa kanki ciwo, Hasbunallahu wa ni’imal wakeel,ya hayyu ya qayyumu ya baki lafiya” yana fada hawaye na sauka a idanunsa,yana kuma ci gaba da tarwatsa dakin tare da sake hargitsashi,bayan tsaiwa da tayi tayi masa gyara na nutsuwa,waiko hakan zai sanya wani daga cikin ahalin nata su ankara da cewa akwai hankali tattare da ita.

      Sanqamewa tayi a zaune,tunaninta ya dinke cifff kan meye manufar adam na aikata haka?,saidai koma meye tasan halinsa,ungulu ne baya jewar banza,ba shakka akwai abinda yake shirin sake qullawa. Kafin takai ga lalubo abinda ke shirin faruwa sai ta tsinci muryoyin mutanen da a kullum take addu’ar isowarsu gareta,qila akwai wani haske da zai risketa,ya kuma zama silar fitarta daga duhu zuwa haske.

     Da mugun qarfi ta yunqura zata dira daga gadon,yayi caraf ya tsallako ya damqeta ya cukuikuyeta da kyau yana sake yamutsa rigata da yamutsatsen gashinta.

      Ya mata mugun riqon da bazata iya qwacewa ba,saboda banbancin qarfi da kuma qarancin garkuwa jiki dake tare da ita,don haka ta bude baki da zummar kiran daya daga ciki

“Koda kin kirasun ma sun shigo sunanki bazai canza ba a idanunsu,sunanki mahaukaciya har yau har gobe,sai ranar da kika fanshi kanki,ni kuma zan wankeki a idon duniya” daga haka yaci gaba da qaraji da ambaton sunan Allah yana mata kyakkyawan riqo,ita kuma taci gaba da yunqurin qwacewa hawaye na gudu bisa fuskarta, kokawa ta barke a tsakaninsu duk da cewa ba wata nasara a hakan sai azabar riqon da yayi mata da takesha,dai dai sanda aka turo qofar da sauri aka shigo,ya saki wani lafiyayyen murmushi daga can qasan zuciyarsa,burinsa ya cika,plan dinsa ya tafi a dai dai,dama abinda yakeso kenan,shigen abinda ya faru jiya,yau ma sun sake samunta a mahaukaciyarta.

Page 52

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 52

    Afifa ce wadda ta kasa jurewa ci gaba da jin muryar sãahar din cikin wannan birkitaccen yanayin,da sassarfa ta nufo sãahar dake riqe a hannun adam da yayi wata irin wajiga,yayi hajaran majaran

“Karki ce zaki tabata, qoqari nake a yanzun ma kada ta yiwa kanta illa,don ko kanta bata ganewa bare wani”

“Komai girman haukan da bestie takeyi jikina ya bani ba zata taba illatani ba,saketa” afifa ta fada da wani irin zafin zuciya. Tashi zuciyar shima tazo wuya,amma dole ya sakar mata sãahar din saboda su maama dake a tsaye daga bakin qofa,can qasan ransa kuwa yana sake cika maqil da afifa din,baya qaunar mu’amalarta sam sam da sãahar,saboda ita din sãahar ba mai damuwa ko maida hankali akan abubuwa bace,tana da mugun kawaici da kuma sanyi akan abubuwa,duk da zazzafa ce ta fannin miskulanci da kima qin daukan raini wulaqanci ko qanqanci daga gurin kowa.

     Talau haka tayi a jikin afifa,maama ta taimaka mata suka kwantar da ita saman gadon,tanata buda baki da zummar yi musu magana,saidai kalma ko daya ta kasa fita daga bakinta,don allurar da aka shimfida mata ta fara aiki a jikinta.

     Shurun dakin ya dauka saboda bacci daya kwashe sãahar,afifa ta dauke dubanta daga fuskar sãahar tana jan majina saboda kukan da tasha,ta maida dubanta ga adam dake tsaye jikin qofa,gaba daya fuskarsa babu komai kwance a samanta face zallar tashin hankali

“Zan samu qur’ani?” Ta tambayi adam din,sai ya daga kai da sauri

“Eh,akwai,amma karki ce zakiyi karatu ne,an samu ta samu bacci ba kuma wani matsalan ya biyo baya” kai ta girgiza tana kafeshi da ido

“Ba inda karanta qur’ani yake zama matsala,saidai waraka,ka daukomin” ta fada tana miqewa zuwa toilet din sãahar din don ta daura alwala.

    Tayi alwalar tana fitowa ta taka wani abu,sai ta tsaya taja baya da sauri tana furta

“Subhanallah” ganin kwalba ce,ta sunkuya ta dauketa ta cillata a dust bin din,ta shimfida abun salla kusa da maama wadda ke zaune tun dazun,riqe da hannun sãahar,ta zuba mata ido tana mata wani irin kallon qurilla,cike da zallar tausayinta,time to time tana tofa mata addu’o’in da taketa karantawa.

       Sanda ta idar da sallar saita dauki qur’anin da adam ya kawo ya ajjiye ya fita,ta zauna dai dai saman kan sãahar din ta bude ta fara karantawa. Sai data shafe awanni uku cur sannan ta miqe ta sauka daga gadon,ta ajjiye qur’anin,ta sake juyawa da nufin komawa bandakin don tayi fitsari.

      Kamar gilmawar walqiya hasken kwalbar data yar dazu ya gifta mata,saita tsaya ta koma da baya,ta tsaya gaban sharar tana duban kwalbar wadda takewa kallon sani.

      Duqawa tayi ta sanya hannu ta cirota kusa da syringe din dake nuna dashi aka zuqe ruwan aka zubawa duk wanda aka sakawan ma,ta soma bin rubutun jiki tana son tantance allurar data sani din ce?. Wani irin dimuwa firgici da kuma tashin hankali ne suka shigeta farat daya,ta waro idanunta kamar zasu fado qasa,saita juya da sauri fa koma saman gadon. Gaba daya jikinta rawa yakeyi,zuciyarta na ayyana mata abubuwa kala daban daban,babban burinta a yanzu sãahar din ta farka,akwai abubuwa da alama masu tarin yawa,akwai wasu abubuwa a lullube a kima binne babu ko shakkaMaimakon karatun da taso yi,saita kasa aiwatar da komai,ta koma ta zauna saman gadon tana riqe da hannun sãahar gam kamar wadda zata bacewa ganinta,kwanyarta nason hakaito mata abinda yake faruwa da sãahar amma gaba daya tunaninta yaqi aminta da hakan. Ta jima a cikin wannan yanayin kafin taji an budo qofa. Maama ce tare da Dr mamman,dukkansu suka tsuguna a gaban gadon sãahar din,kowanne fuskarsa a narke zuciyarsu cike da rauni.

      Addu’a yayi mata kamar ko yaushe,sannan yace su shirya su wuce gida,duk da ya gama karantarta sam batason tafiya gidan

“A nan yau zan kwana” afifa ta fada kanta tsaye,saboda zuciya da gangar jikinta suna bata abubuwa da dama da takeson tabbatar dasu,akwai qaqqarfan zargin daya shiga zuciyarta

“Anya?,zaki iya?” Dr mamman girema ya fada yana kallon afifan,kafin ta bada amsa adam da yake shigowa yayi caraf da zancan cikin tashin hankalin daya bugi qirjinsa na jin cewa zata kwana da sãahar

“Gaskiya abba banajin zata iya,zan iya ci gaba da kwana da ita kafin randa zamu wuce asibitin,babu abinda ta rasa,zan kuma ci gaba da kulawa,ba zata rasa komai din ba in sha Allah har zuwa lokacin da Allah zai bata lafiya”

“Kana qoqari kam,mun shaida mun kuma yaba sosai,a qalla yau kaima ka kwanta kayi bacci sosai yadda ya kamata, saboda haka yau ni zan kwana da bestie in sha Allah,don na tabbatar koda nice irin hakan ta sameni,ba zata gujeni ba koda na kwana daya ne” ta fada tana sakin qwalla,don tanason karya zuciyar dr mamman ya qyaleta ta kwanan. Ta samu nasara kuwa,don dukkansu qas sukayi da kansu,yayin da maama ke share hawaye

“Gaskiya ne,kaima ya kamata ka huta koda iya yaune, ubangiji yayi maka albarka bisa qoqarinka”

“Ameem ya Allah abba” ga fada kansa a qasa yana murza yatsunsa,zuciyarsa na wani irin bugawa da zallar tashin hankali tare da tunanin mafita,don ba shakka zuwa nan da awa daya zuwa biyu sãahar din zata iya farkawa,farkawarta kuma dai dai yake da tonuwar asirinsa da tashin ballin dukkan wani rufaffen asirinsa.

     Har motarsu dr mamman ta tashi yana tsaye kamar wanda aka kafa a wajen,daga qarshe dabara ta fado masa,ya fada motarsa kai tsaye yabi bayansu ya wuce gurin likitansa. Allurar da ake mata me sanya nannauyan bacci har fiye da wadda aka saba yi mata,da kuma wadda ke sanya birkicewar kwanya ya karbo,dukkansu yasa aka sauya musu gida,tunda yasan me afifan ta karanta,harkar kafiya ne,a yanzun tana cikin matasan likitoci masu qarancin shekaru da jahar kano ke dasu,yanason yayi wasa ds hankalinta,ta kuma yiwa ‘yar uwar tata da take mutuwar so take aibatashi sabods ita allurar da zata sake mata illa tako ina.

      Tana zaune tana karanta qur’anin ya tura qofar,ta daga kai a hankali ta qare masa nutsatsen kallo amma a fakaice,sai a yanzun ta lura da wasu abubuwa a tattare dashi,cikin son nuna kulawa ya qaraso ya ajjiye ledar hannunsa,sannan ya matsa gaban gadon ya shafi wuyan sãahar din dake baccin mutuwa,ganin bata motsa ba ya tabbatar akwai ssuran lokuta kafin allurar ta saketa

“Alhamdulillah,Allah ya qara lafiya” ya fadi da sigar dake nuna damuwa da kuma kulawa. Waiwayawa yayi ya kalli afifa

“Ina ganin kije kici abinci sai ki buda daya dakin ki kwanta ko?” Qaramin murmushi ta sake

“Banda abinka mr Adam,ai ba hutawa nazo yi ba,jinya nazo yi,yau kaine da baccin nan,kada ka damu” tsaki yaja cikin ransa yana tsinewa afifan,yassn tunda har ra dawo dole ne aikinsa a yanzu ya hadu da qalubale masu yawa,amma idan tasan wata ai batasan wata ba,zaiji da ita

“To yayi,yanzu ga alluranta nan,za’a yi mata su kafin ta farka,hakan yana taimakawa wajen farkawarta ba tare da buge buge ko surutai ba”

“Okay” ta furta tana ajjiye qur’anin,ta buda ledar tana fiddo ruwan alluran hade da syringe din.

      Duban farko ta yiwa alluran tasan cewa ba ainihin mazubinsu suke ba,abu na biyu kenan daya qara qarfafa zarginta,ta fitar dasu kaf ta zuqe ruwan allurar a syringe,ta matso ta dora tsinin allurar saman hannun sãahar da batasan abinda akeyi ba.

Page 53

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 53

Sai kuma ta daga kai ta kalli adam din dake tsaye qyam a kansu yana duban alluran

“Bani tissue mana” amsawa yayi da to cikin hanzarin da baiso ta aiwatar da wani abun da zai kawo kuskure wajen yin allurar,ya ciro tissu din ya bata,ta karba ta dora a bakin tsinin allurar,ta fara zirarawa ruwan zuwa cikin tissue din data linkata,sai data qarar da ita a ciki tas sannan ta zare allurar,tayi hanzari danne tissue din a qasan cinyarta gudun kada ya fahimci jiqewar da tayi.

Sanda yaga ta kammala wani dadi ne ya kamashi,ko yanzun hankalinsa ya samu ya kwanta,yaukam zaiyi bacci abinsa sosai,yasan har gobe zuwa wajejen azahar tana cikin bacci da tambele idan ma ta farka din kafin sannan,wala’alla ma ya gayyato wata cikin ‘yammatansa idan kowa yayi bacci ta tayashi debe kewa,da wannan tabbacin gaibun daya samu ya fita a dakin abinsa hankali kwance.

Kwanciyar hankalin da afifan ta gani a fuskarsa sanda yake fita din ta sake dasa qaqqarfan zargi a ranta,sai ta bude alqur’anin cikin nutsuwa ta fara karantawa da madaidaicin sauti me cike da nutsuwa.

Kusan awa guda cur ta shafe a hakan,a hankali taji wani sassanyan hannu ya dafa hannunta dake saman qur’anin,kafin ta daga kai taji ta kira sunanta da wata iriyar siriryar galabaitacciyar murya

“Bestie,kema wai kin yarda ni din mahaukaciya ce?,na haukace?” Wasu irin birkitattun hawaye ne suka shiga silalowa afifa,banda ta sanya hannunta ta toshe bakinta da kuka mai qarfi zata barke dashi,hannunta na saman bakinta tana girgiza kai,sai kawai ta rungume sãahar din a jikinta tana sakin kukan data boye sautinsa

“Bazan taba yarda ba bestie,koda ma da gaske ne ina qaunarki a hakan” kuka dukkansu suka saki rurus,suka dinga rerashi babu wani me rarrashin wani,har tsahon wani lokaci kafin afifa da idanunta sukayi jazur ta magantu

“Bestie,wanne irin mummunan abune kika yiwa adam ya yanke hukuncin mai dake haka?” Ido ta lumshe ragowar hawayen dake maqale a idanunta masu zafi suka gangaro,tabba inda ace ruwan hawaye yana qarewa da tuni nata ya jima da qarewa

“Wannan damuwar da kika tafi kika barni a cikinta,wadda nayi alqawarin gaya miki ita,ashe itace zata zaftaro bisa kaina,tayi shirin kaini lahira koda ban shirya ba” a nutse ta rattabawa afifan komai. Wani mugun birkicewa afifan tayi,ta miqe zata sauka a gadon da zafi zafinta, fuskarta gaba daya ta sauya kamanni.

Da sauri sãahar ta cafko hannunta,don tasan halinta sarai komai ma zata iyayi

“Ina zaki?”

“Adam din zanje na samu ayita ta qare,tsinanne matsiyaci dan wuta” girgiza kai ta hauyi da sauri

“Tunkarar adam a irin wannan yanayin abune me hatsarin gaske,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawon ya kamaka,sai kinbi ta takatsantsan da hikima sosai kafin ya zamana mai laifi red handed,baki tsoron kema yace dalilin kwanan da kikayi kin shafi aljanuna ko ciwon haukata?” Sanyaya jikinta yayi,lallai a yadda idanun adam suka rufe babu abinda bazai iya aikatawa ba,yadda ya matsu da jakar koma meye akace zaiyi zaiyi din,saita koma ta zauna tana ci gaba da kukanta,zuciyarta kuma ta zurafafa da tunanin daukan fansa.

Da qyar suka lallashi juna,ta kama sãahar da jikinta sam ba qwari ta rakata toilet,ta daura alwala tazo ta rama sallolin da ake binta,afifa na gefe tana kallonta tana kuka, sãahar din da bata wasa da sallah?,duk tsanani duk rintsi bata yarda lokacin sallah ya wuceta ba ba tare da ta yita akan lokacinta ba.

Abincin da raihanatu ta bayar adam ya shigo dashi tun dazu ta buda,ta saka sãahar din a gaba akan sai taci,da qyar tayi cokali biyar,saboda cikinta ya sake wani mugun tsukewa,baya iya daukan abincin sam me yawa,dama kuma tun asali na gwanar abincin bace.

Daga ita har sãahar ba wanda ya rintsa a daren,sãahar din nata bat labarin irin azabobin da adam ya gana mata,tayi kuka tayi kuka har ta bawa uku lada,a daren ta gama shirya yadda komai zai tafi,tsarin kuma ya yiwa sãahar din itama.

Washegari da adam din daya kwana da wata macen suna holewa kan gadon aurensa ya shigo ko a fuska bata nuna masa komai ba,saima zallar tsoron kwana da sãahar din data nuna masa ta dinga ji. Murmushin jin dadi da samun cikakkiyar nasara ya saki yana sauke dubansa ga sãahar daje kwance shame shame kamar dai yadda take a jiya,a yanzun sauran tsoronsa ya kau,abinda ya rage masa ya sake matsa qaimi kawai ta bashi jakarsa kafin yayyenta su iso su wuce da ita wani banzan asibiti. Afifa ce dama tsoronsa,yasan halinta tsafff, za’a iya fuskantar matsala ta sanadinta,amma a yadda yaga tayi firgai firgai ta kuma ce a jiyan batayi bacci ba,alamu sun nuna ba zata iya sake kwana ba(baizan qarfin aminci da soyayyar dake tsakaninsu ta ginu sosai bisa tubalin Allah da ma’aiki ba,ba abota irin ta wannan zamanin ba,iya fatar baki). Ilai kuwa yadda ya zata hakance ta afku,afifa ta hada kayanta tayi musu sallama bayan ta gama tsara komai ta fice a motarta.

Ba gida ta wuce ba,can cikin kasuwar qofar ruwa ta zarce,ta kuma sauka kai tsaye gurin mutumin da yafi kowa qwarewa wajen yanka muqullin da zai dace da kowacce qofa, cikin lokaci qanqani aka gama yanka mata saboda kudin data zuba ta biya,ta karba ta dawo gida,ta hada wasu kaya ta baiwa maama dake shirin tafiya gidan,tace ta ajiiye mata dakin sãahar din gobe zata koma ta sake kwana da ita

“Kada ta barnatar miki fa” hawaye ne suka ciko idanun afifan,mutum da hankalinsa amma ya sanya kowa yana mata kallon tabbabiya

“Ba zata taba ba in sha Allah” shuru maaman tayi tana juya kayan

“Na rasa abinda yasa har yanzu naqi ji a jikina sãahar ta samu tabin qwaqwalwa,jiya muna hanya da abbanku dana fada yace shaidan keson yimin wasa da imani na,na yarda da qaddara ne kyau ko akasinta”

“In sha Allah nan kusa bestie zata dawo cikinmu muci gaba da rayuwa kamar kowa” abinda afifa ta fada kawai kenan tana sharce hawayen fuskarta.

Fitar maama daga gidan ya baiwa afifa damar shiga dakinta ta dauke jakar ta canza mata muhalli,saboda gudun abinda zaije yazo,ta gama sarawa girman sharrin adam,tasan bazai taba rasa kawowa a ransa jakar na gidan ba,zai kuma ya tsara komai da zai sanya a aminta dashi a damqa masa ita.

Kuka sosai ta zauna tana yi sanda ta gama qarewa kayan dake cikin jakar kallo,burinta kawai taga ta watsawa passport din wuta da sauran takardun,to amma suna buqatar evidence,don haka tayi haquri ta tattarasu ta kaisu cikin motarta.

Kamar ko yaushe bayan kowa ya tafi yaja qofar ya kulleta,don ba kwana dakin yakeyi ba sai idan yana da buqata. Cikin sanda ta bude kayan da maama ta ajjiye cikin drower dinta,wanda tunda ta shigo dasu take ankare dasu tare da fatan kada hankalin adam yakai kai. Ta warware kayan a nutse ta ciro muqullin ta maidasu gurinsu,ta duba daya bangaren kayan nata ta ciro hijabi ta sakawa jikinta, sannan ta fara takawa cikin sanda da takatsantsan,qirjinta yana wani irin bugawa,bakinta dauke da tarin addu’ar samun nasarar ficewa daga gidan ba tare da kowa ya ganta ba,tana takawa iska na yawo da ita saboda jimawa da tayi rabon da tayi doguwar tafiya,ga ciwo da uban allurai rashin cin abinci da uban tashin hankalin da yasa ta zabge ta rame.

Cikin nasara ta bude qofar dakin da muqullin,ta budeta a hankali ta fara takowa ta falon,motsi taji me qarfi daga bayanta,abinda ya kada hantar cikinta kenan ta waiwaya da sauri har tana shirin kaiwa qasa saboda tsananin razana.

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

54

    Raihanatu ta gani a tsaye,itama jikinta rawa yakeyi,plate din data debo suna shirin watsewa a hannunta. Bud baki sãahar tayi zatayi magana raihanatu tayi saurin dora yatsanta saman labbanta alamun sãahar din tayi shuru,sai ta maida plates din saman dining,ta sauko da mugun hanzari cikin wani taku na sand’a,ta qaraso inda sãahar ke tsaye ta finciki hannunta da mugun sauri ta bude mata qofar parlor din suka fice.

     Tsakanin baranda da farfajiyar gidan suka ja cak suka tsaya,dukkansu kowa yana maida numfashi,qirjinsu yana wani irin dagawa

“Mai gadi…..yana nan anty,bari na dauk….ke masa hankali” bata tsaya jin ta bakin sãahar din ba ta lallaba tabi ta cikin flowers din ta zagaya bayan dakin me gadin. Dutse ta samu me dan girma ta jefa ta saman roofing din ya bada sauti qwaalll,sautin da ya dan ja hankalinsa,sai yayi tsaki yaci gaba da abinda yakeyi. Sake daukan wasu dutsunan har biyu tayi ta sake jefawa,ya sauka kuwa a tare,sai ya fusata ya miqe don ya zagaya ya duba daga ina jifan yake,kafin ya qaraso tuni ta fita ta koma wajen sãahar,ta sake jan hannunta gudu gudu sauri sauri,ta bude mata qofar gate din tana magana cikin ruwan hawaye

“Jeki anty,Allah zai dafa miki,ubangiji yayi miki sakayya,duk da ban gama sanin kan komai ba amma zuciyata da gangar jikina sun gama gayamin me yake faruwa,ko yanzun yana dakinki da wata,ko iya wannan sakayyar Allah ne kadai zaiyita” tana gama fada ta maida qofar cikin matuqar takatsantsan ta rufeta ta koma cikin da sauri ba tare data bari me gadin ya ganta ba.

    Bibbiyu ta dinga gani cikin qwayar idanunta,jiri sosai ya dinga dibanta ta fara hada hanya. Da hanzari afifa dake zaune tana jiranta tsahon sa’a guda ta buda murfin motar ta fito da mugun sauri,ta tarbeta a hanya ta riqeta qam ta sanyata cikin motar,dai dai lokacin da numfashinta ya fara sauyawa,alamu suka fara nuna tana neman suma ne,wanann ya saka afifa tayar da motar da mugun gudu suka bar layin.

     A lokacin babu wanda ta gayawa abinda ke faruwa,saboda bataso a sani din,don taci alwashin saita wujijjiga rayuwar adam din. A yanzun da sãahar ta sume mata dole ta nemi taimakon wani. Kai tsaye anty farheen ta kira,ta gaya mata asibitin da take tace tazo yanzu don Allah

“Wa kikai wannan asibitin me nisa?,duk hospitals din da muke zuwa na kusa damu”

“Ba lokaci anty don Allah ki qaraso yanzu,its urgent”

“Ba laifi,gani nan” ta fadi maganar tana ajjiye wayar. Muhyiddeen baya nan already,don haka ta barwa masi aikinta duka yaran,ta tayar da driver suka fito daga gidan cikin motarta.

     Ba qaramin razana tayi ba lokacin da afifa ta gama zayyane mata komai,kuka sosai ta saki ita kanta anty farheen tana tsinewa adam din

“Dole mu dauki mummunan matakin shari’a a kansa,tabbas baici bulus ba” kai afifa ta girgiza

“A’ah anty,mubi komai a sannu kamar yadda sãahar ta shawarta,ni kaina yanzun tsoro yake bani,kaidinsa ya wuce tunaninmu,duk yadda nakai ga tsanarsa da qin jininsa……ban taba kawowa zai iya aikata haka ba,so sai mun iya takunmu,tsaf zai iya wanke kansa a wajen iyayenmu maza da ‘yan uwanmu,bari kiji plans dina” a nutse ta warwarewa farheen shirinta,shirin ya yiwa farheen din sosai,kuma itace hanya guda daya da zata iya sanyawa adam ya tona asirin kansa da kansa.

     Anty farheen bata bar asibitin ba sai kusan qarfe daya saura na dare,tace gobe zata dawo asibitin secretly ta kawo musu breakfast,don so samu a gobe ta maida sãahar gidanta aci gaba da yi mata treatment a can,don batason rashin ganin gilmawar afifa ya sanya adam ko wani cikin ‘yan gida ya fahimci akwai wani abu,basason hakan ya kasance,har sai zuwa sanda suka tsara faruwar hakan.

^^^^^^Sam adam bai waiwayi dakin sãahar ba tun bayan tafiyar afifa,duk da yasan afifan a yau ta tafi gida,sai ya tattare shi da karuwarsa suka qule dakinsa sukaci karensu babu babbaka. Kwata kwata bai doshi dakin ba sai bayan sallar asuba,ya miqe yana jiri saboda buguwar da yayi a daren jiya,da kuma masha’ar daya aikata son ransa.

     Zama yayi a bakin gadon yana jiran fitowarta,amma sai yaji shuru,don haka ya miqe ya nufi bandakin yana zage zage

“Na kusa kawo qarshen matsalata,tsaf zan iya hallakaki muddin kikace zakici gaba da boyemin jakata,ke kiyi asarry rayuwarki ni nayi asarar dukiyata” wata muguwar razana yayi lokacin da yaga bandakin wayam,ya fidda idanunsa waje kamar yana shirin zurarosu qas,ya waiwaya da sauri yana tuna cewa lokacin da yazo shiga dakin baifa budeshi da maqulli ba,yana turashi yaga ya bude,a zabure ya fito yana kwarara ihu kamar hauka sabon kamu,yayo falo yana qwalawa rahinatu kira.

     Tunda ta idar da sallar asuba take zaune tana zaman tsammanin jiran jin makamancin wannan kiran,sai da tayi addu’ar neman samun tallafin nutsuwa daga ubangiji ta shafa sannan ta fito,a sannan har ya gagara zaman jiranta ya bankado qofar dakin,kadan ya rage ta daki fuskarta

“Ina sãahar take?” Ya tambayeta cikin tsawa

“Tana dakinta yaya” ta amsa masa a nutse,kamar da gaske batasan komai ba,ido ya zaro waje

“Tana dakinta zanzo ina tambayarki inda take don ubanki?” Cikin nuna zallar mamaki tace

“Bata dakinta kuma yaaya?,to ina ta tafi?, innalillahi wa inna ilaihi raji’un” duk sai ta nuna rudewarta a fili

“Ni tunda ka shigo kacemin na wuce dakina,kada ka sake ganin gilmawata ai ban sake fitowa ba yaaya sai yanzu daka kirani” yadda yaga ta rude shine ya sake gigitashi ya kuma rudashi,ya saki qofar da sauri yana barin wajen hadi da kama gashin kanshi da hannunsa bibbiyu kamar wanda yasha cocaine ya bugu da kyau,haka ya dinga zirga zirga kafin ya afka dakinsa.

     Tana nan tsaye taji hayaniyarsu shi da kilakin tasa,kafin zuwa wani lokaci taji yana jibgarta,ba jimawa sai gata ya jawota kiiiii zuwa falon gidan da wasu gantalallun kayan bacci da basu da maraba da tsirara

“Tsinanniya mitsiyaciya,ke kika jawomin,saida na gaya miki kada ki bani abun bugarwa,a situation din da nake ciki bani da buqatar sa amma saida kika bani,yanzu kina shirin jazamin masifar da tafi kowacce girma,fita ki barmin gida” haka ya korata ko kayan jikinta bai bari ta canza ba.

     Dawowa yayi yaci gaba da yin safa da marwar cikin tashin hankali

“Ya akayi ta fita daga dakin dana kulleta?,ina ta tafi?” Tambayoyin daya dinga yiwa kansa daya gama cakewa kenan,sai ya juya a gurguje ya durfafi me gadi yana tuhumarsa,saidai ya tabbatar masa yau din banda afifa data fita a gaban idanunsu dukka ba wanda ya sake fita daga gidan.

     Qaramin hauka ya dinga yi tuburan, raihanatu na maqale tana hawaye,gami da janjantawa kanta game da muhallin da rayuwa ta jefota,dangin uwa marasa saiti,marasa imani jahilai masu shegen son kansu da kwadayin abun duniya fiye da komai.

      Sanda ya kirata yace itama ta fito tabar gidan yana auna mata zagi,hakan dadi yayi mata,don duka tsoro ya kamta,ganin gidan ba kowa sai ita dashi yanata kuma wani abu kamar me tabin hankali,don haka a gurguje ta zira slippers dinta bata ma tsaya daukan komai nata ba ta qara gaba.

*_BAYAN AWA UKU_*

      Mutum takwas ne cikin falon,ciki harda afifa maama da dr mamman sai yaa muhyi da yaa Saifullahi,wanda ba wanda yasan da zuwansu a yau din,sai kuma gashi sunzo sun tarar da tashin hankalin rasa sãahar.

      A falon saika rasa tantance waye yafi wani shiga tashin hankali?,maama Kuka kawai takeyi wiwiwi wanda yake taba ran afifa,yakeson kuma ya karyar mata da gwiwarta. Duk bayan mintuna saita saci kallon adam da yake shirin zaucewa,ya kasa zama ya kasa tsaiwa,sai kai kawo kawai da yakeyi yana kiran sunan Allah,ta sake sarewa,ta kuma sake jin tsoron kaidin mutum,lallai dan adam me buhun sharri ne,ba wanda bai tausayawa adam din ba a falon yanayin da suka ga ya shiga,ba tare da sanij cewa shine ummul aba’isin faruwar komai ba

     Zaman da sukeyi a yanzu na zaman jiran tsammani ne,bayan sun bada report na batanta a kafafen yada labarai da kuma police station guri guri.

“kayi haquri adam,in sha Allah za’a ganta cikin aminci” abba ya fada cikin son qarfafawa adam din gwiwa,duk sa cewa shi dinma bawai yana da qwarin gwiwar bane

“Abba bansan ya akayi ta fita ba,ina ta tafi?, innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya fada da madaukakiyar murya,kai afifa ta kawar ta tabe baki,tabbas bawai yana cikin tashin hankali bane saboda batan sãahar,yana cikin tashin hankali ne kawai saboda jakarsa.

      Wuni sukayi ranar a haka,har zuwa dare,ba wani labari ko alamun samun sãahar.

     Ta fannin afifa duk da tanason komawa gidan yaa muhyi su kwana da sãahar din wadda tuni anty farheen ta samo likita ya fara bata kulawa ta musamman,to amma zamanta tare da maama dake cikin tashin hankali yana da matuqar amfani,tunda tasan ko ba komai zata debe mata kewa ta kuma kwantar mata da hankali,don haka ta bita gida,amma tana tuntubar anty farheen akan duk yanayin da ake ciki,ta shaida mata tana samun sauqi da kuma kyakkyawar kulawa. Lokaci lokaci take satar jiki taje taga sãahar din. Sosai sãahar din ke murmurewa tana sake samun lafiya,saboda kulawa ta musamman da anty farheen din take bata,duk da cewa sãahar din bata da aiki sai koke koke,saboda matuqar dimuwa da kaduwa ta shigeshi akan abinda adam yayi mata,gaba daya so take ta zama depressed,amma dagewar anty farheen da jajircewarta yanata aiki a kanta,baji ba gani haka take bata kulawa da shawarwari

“Um um ummin abba,baki godewa Allah ba kenan?,baki godewa ni’imarsa ba?,ya kubuto dake daga sharrin da bakisan iya zurfinsa ba?,da yawan koke koke zaki sakawa ubangijinki?”

“Dole nayi kuka anty,ashe dama haka maza suke?,dama masoyi yana iya komawa maqiyi mafi ban tsoro me muni?,ashe su din basusan halacci ba?,basusan soyayya ta ainihi ba?,basusan tausayi imani da jin qai ba?,ashe adam zai iya yimin haka anty?,me yayi saura kuma a duniya?,tunda har adam zaiyi haka,wanne masoyi ne bazai iya cin amanar masoyi ba?” A lokacin dukka bayanin da zata yi mata bazaiyi amfani ko tasiri ba,don haka sai kawai taci gaba da lallashinta cikin hikima da kwantar da kai.

KOMAI NISAN JIFA

      Bayan zamun tabbacin warwarewar sãahar,suka tabbatar ta dawo cikin hayyaci da nutsuwarta,da taimakin likitansu dake duba mafi akasadin matsalar data shafi familyn gaba daya. Ba abinda afifa ta boyewa Dr usman,ta kuma nemi taimakonsa ya zama jagora wajen zama MABUDIN tonuwar asirin adam,ba tare da jinkiri ba ya amince,don shi kansa al’amarin yayi masifar tsimashi tare da tayar masa da hankali matuqa da gaske.

       Tun cikin satin ta tayar da maganar zuwa duba filaye da kadarorin sãahar,tace

“Ya zaid,ya kamata a duba,kasan mutane babu amana, qilan wasu suji labarin batanta suje suyi rub da ciki a kai” zaid din ya gamsu da zancanta,yace zai samu lokaci yaje ya dudduba din.

      Lokuta lokuta sukanje gidan,basu barshi hakanan ba,kamar ko wanne lokaci,yau ma sun je gidan kusan su dukansu,banda zaid da yace zai fara wucewa duba filayen sãahar din,abinda yayi matuqar yiwa afifa dadi,ta dinga kallon adam da yaketa mazari irin na rashin gaskiya a tsakaninsu,tana jiran jin dawowar zaid.

       Maama na tsaka da jajensa kan ya dade ya iso gidan,cikin wani irin yanayi daya tabbatarwa afifa boom din data dana ya soma tashi

“Lafiya?” Maama ta tambayeshi

“Akwai matsala maama,lokacin dana isa na fara da duba filayenta daka bakin titi,amma ga mamakina kusan fiye da rabinsu an tada gini a cikinsu harma anyi nisa,ko dana zauna na fara bibiyar lamarin,na nemi haduwa da ainihin masu filin,na samu ganin mutum uku a ciki,don suna gurin suna duba aikin da akeyi musu,kuma dukkansu sun shaida min siyan fili sukayi,kowanne kuma ya nunamin takardar shaidar mallakar filin original copy” wani irin sauti cikin adam din ya bayar,wanne irin sabuwar masifa ce kuma take shirin afko masa bayan yana tsakiyar wannan dumu dumu bai gama fita daga cikinta ba?,dakiya da qarfin hali ya aro,cikin nuna bacin rai gami da mamaki yace

“Kai,wanne irin rainin wayau ne wannan?,me yasa mutane masu da kirki basu da imani?,daga batan baiwar Allahn sai kawai su hau gine mata filaye?”

“Basu x laifi,kuma suna da gaskiya,don kowanne ya shaidamin a hannun mijinta ya samu damar mallakar filin,ya tabbatar musu kuma babu wata matsala” ai baisan sanda ya miqe ba,ya soma fada yana yarfa hannu,sam ya manta a gaban su waye yake

“A gidan ubanwa suka sanni?,ni zasu yiwa sharri saboda sunga Allah ya rufamin asiri?,muna zaman lafiya da soyayya da matata?,ko su waye wlh bazan qyalesu ba,tabbas saina kaisu qara kotu” relaxing ya zaid yayi yana qare masa kallo

“Ka kwantar ds hankalinka,ko nima bazan qyalesu ba sai nayi shari’a dasu,so shi yasa a gobe na yanke hadaku ku duka acire me gaskiya da mara gaskiya,tun kafin ta ritsa da wanda baida laifin komai” mummunar faduwa gabansa yayi,amma ya maze

‘”hakan yayi,ko baka hadamu ba ni zan nemesu,na kuma nemi fansar batamin suna da sukeso suyi” sai yaci gaba da fada,ya kasa shuru hakanan ya kasa nutsuwa ya zauna guri guda.

      Daren ranar bacci barawo duk qwarewarsa bai iya satarsa ba,ya dauki wayarsa ya kira momee ya zayyane mata komai

“Kada ka wani damu,kuje din,iyaka ka murje idonka kace baka sansu ba,zanma shigo gidan goben saboda ka samu supporting ” akan hakan suka samu matsaya,saidai abinda basu sani ba,tuni afifa ta gama nata shirin na goben,don ko da suka tashi zuwa,tare da Dr suka taho,bisa shawarar adam din ya bada report na duka lalurar sãahar din ya duba da kyau. Tace hakan yana da kyau,idan da yiwuwar suyi attaching nasa cikin cigiyar neman sãahar da akeyi,qila wannan ya sauqaqe samunta da wuri.

Page 55

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 55

A nutse ya zauna a falon gidan yana duba report din qarya da Dr din bogin da adam yayi hiring ya hada,ga duk qwararren likita yana kallon abun zai fahimci an tsarashi ne kawai,saboda babu gaba babu baya,bayanan babu wani cikakken abun kamawa.

Nannauyar ajiyar zuiciya ya sauke,wannan mutumin bayan qwarewa da yayi wajen hada plan,harda sa’a ma daya taka cikin al’amarinsa,ko kuma qaddarar da bahaushe yakewa take da bata wuce rana da lokacinta,saboda ya duba ya dubo,family irin na dr mamman girema,ba abu bane me sauqi kayi musu irin wannan abu lokaci guda hankalinsu bai kai kai ba,duk da akwai tasirin boko sosai a tattare dasu,amma suna da ilimin addini a tattare dasu. Daga qarshe ya rufe file din yana sauke ajiyar zuciya,lallai banda ma wannan……sun bashi amana qwarai,ta yadda tunaninsu bai taba kawo musu wai adam din zai aikata wani abu makamancin wannan ba.

A nutse likitan ya maida dubansa ga momee dinsa data iso tanata kumfar baki akan case din filayen,tana ta fada akan duk wanda ya murqushe dukiyar,ya kuma bi d’anta da sharri bazasu qyale ba. Duba daya yayi mata ya karanci ‘yar bariki ce tsantsa,amma dattako da karamci irin na iyalan dr mamman girema yasa basu taba nuna mata komai ba face zallar karamci da mutuntawa.

Afifa dake dakin sãahar tana tattaro dukka kwalaben alluran da aka dinga juyewa gangar jikin ‘yar uwartata,tana jiyo dukka kumfar bakin momee,tun ranar tasan cewa komai da hadin bakinta ake aikatashi,tsanar da take wa matar ta sake ninkuwa cikin ranta. Qoqarin dauke hankalinta tayi akan maganganun amma kuma ta kasa,bala’i biyu ne ya hade mata,na farko qarfin alluran da aka dinga dibgawa sãahar din,wanda tasan banda ikon Allah,babu abinda zai hana kwanyarta juyewa,na biyu kuma yadda momee din ke magana kamar mutuniyar arziqi,wannan yasa ta miqe a fusace,ta daga inda ta yiwa jakar ajiya ta musamman ta cirota ta kuma fito daga dakin da wani irin hanzari,tana huci kamar ta hadiyi kunama.

Yadda ta buda qofar da qarfi har tana dukan bango ya dawo da hankalin dukka mutumin dake falon kanta,yaa zaid yana shirin tambayarta lafiya?,saita miqa kwalaben ga likitan

“Dr,dubamin wadan nan kwalaben,allurar meye?” Hannu biyu yasa ya karba ya fara dubasu daya bayan daya. Wani gumi ne ya yanko masa shima,ya daga kansa ya zubawa adam idanu.

Tun baice komai ba ilahirin jikin adam din ya dauki rawa,ko kadan baisan da zaman kwalaben ba a dakin,yasan duk sanda akayi allurar indai ya tuna zai kwashesu ya fita dasu,to waye ya tarasu?,ba shakka sãahar dince,hakan yana nufin duk lokacin da akayi mata allura tana fakar idonsa ta dauki kwalbar kenan ta adana?,lallai ta shiryama zuwan wannan ranar

“Wanne dan wutar ne cikin likitoci yake iya zuqar wannan ruwan allurar ya zubesu ga jikin dan adam?” Abinda likitan ya fara tambayarsa kenan cikin matsanancin bacin rai.

Duk yadda yaso ya shirya qaryar da zata sanyashi ya bulle amma bakinsa yaqi bashi hadin kai,saboda rawa kawai labbansa sukeyi,da qyar ya fusgo kalmar

“Bansan a inda aka samosu ba,don wannan kwalaben ni ban taba ganinsu bama”ya tabbatar qarya yake,tunda ya riga yasan da komai,sai kawai ya maida dubansa ga ya zaid ya fara karanto masa aikin da allurar takeyi a jikin dan adam,da kuma girman illarta.

Kuka kawai maama ta fashe dashi tana kiran sunan Allah,yayin da adam ya jiqe jagab kamar an masa wanka da ruwa,jikinsa yana bashi yau ba ranar sa’ar sa bace,yau ranar tonin sililinsa ce,momee ce mai qarfin halin miqewa,cikin borin kunya ta fara maganganu

“Dama dai kawai kun shirya ci mana mutunci da wulaqantamu,saboda talakawa ne mu bamu da komai,banda haka ta yaya yaron da bashi a zaune bashi a tsaye game da al’amarin diyarku amma ku rasa sharrin da zaku jefeshi dashi sai wannan,idan banda shi da yasan girman halacci ma waye zai zauna da mahaukaciya…..”

“Ke tsohuwa,ki iya kalamanki” afifa ta dakawa momee tsawa da muryar da ita kanta batasan tana da irinta ba

“Tunda har kuna da bakin kare kanku,ai waqa a bakin me ita tafi dadi” saita fidda waya tana kiran anty farheen

“Muna hanya afifa,muna gab da shigowa layin”

“Saikun qaraso” sai ga juya gasu dr mamman

“Abba,don Allah ku jira minti uku,ga raba gardamar nan isowa” jin kalmar afifa ta qarshe ta kada hanjin cikin momee,zatonta ya bata jami’an tsaro kawai suka kira musu kai tsaye,sai ta kama hannun adam tana cewa

“Tashi mu tafi,Allah zai saka mana da wannan qazamin qazafin da sukayi maka saboda kana auren diyarsu”

“Ina zaku?,ku koma ku zauna,ai bakwa tafi muna zarginku ba,gwara a warware gaskiya ko hajiya?” Cewa dr mamman girema.

Jikinta ne ya dauki rawa ta fara kame kame,saidai kafin ta dire kame kamen nata sallamar sãahar ta dauki hankalin kowa.

Sanye cikin wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin doguwar riga,da gyale mahadinsa,fuskarta har yau bata cika ba a yadda take a baya,saidai sassanyan kyan nan da baya gushewa kwance saman fuskar tata. Akwai alamu na samun nutsuwa a tattare da ita,sabanin satittikan baya da dukka wata natsuwa tayi qaura daga rayuwarta,ake shirin haukatata,a maidata mahaukaciya zalla,idan ta yiwu ma yazo da qarar kwana,bataga abinda zai hanata ta baqunci lahira ba.

Cikin azama tare da son nunawa duniya shi din wankakke ne,kuma masoyi ga matarsa ya miqe cikin zallar mamaki ya nufeta yana qwala kiran sunanta. Rungumeta yayi nufin yi,saidai kafin yakai ga aikata hakan ya samu tsarabar wani lafiyayyen mari saman fuskarta,sannan ta tattara dukka qarfin data shigo dashi ta ingizashi baya ya fada saman momee dake zaune cikin kaduwa da tsurewa.

Zumbur ya miqe yana shafa wajen,sannan ya maida dubansa a kanta,sanda take tsaye ta kafeshi da fararen manyan idanunta dake dauke yau din da wani irin matsanancin fushi da bai taba ganin irinsa tattare da ita ba

“Baki warke bane sãahar?,subhanallahi”

“Kaine zaka shiga taka haukar yanzun nan,mayaudari maciyin amana,ina neman tsarin Allah daga kai” sai ta fashe da kuka ta soma sulalewa a gurin zata zauna,anty farheen ta riqeta da kyau tana bata baki. Tuni maama ta qaraso bayan ta tabbatar ba mafarki takeyi ba,ta rungume ‘yarta tsam tana jero addu’o’in godiya ga Allah

“Ya kamata kowa ya samu waje ya zauna” yaa Saifullahi ya magantu cikin nutsuwarsa,domin ya karanci akwai babban al’amari dake shirin faruwa,komai ya fara bayyanar masa saman fuskar adam da babarsa,sannan ya akayi sãahar take a gidan muhyiddeen duk da tsahon lokacin da aka dauka ana nemanta ba tare da kowa ya sani ba?,ga adam da momee suna matsawa daga bakin qofa?,tamkar yaa zaid ya lura,sai ya matsa yayiwa kansa mazauni daga can hanyar qofar,suka zamana a tsakiya.

A nutse afifa ta qaraso tsakiyarsu ta dire jakar. Lokacin da idanun adam suka sauka a kan jakar sai ga fitsari ya balle masa yana daga zaunen,zazzafar gudawa ta soma qoqarin kufce masa amma ya matseta da kyau,gurbatacciyar ziciyarsa tana gaya masa akwai sauran dama adam,kada ka karaya,muddin baka amsa ba ba wanda ya isa ya tilastaka,koda kuwa a kotu ne.

A gaban kowa sãahar ta matso,ta daga jakar ta zazzage komai ya tarwatse a qasa,wani zazzafan kuka ya taso mata,amma ta danneshi. Daya bayan daya ta soma basu labarin yadda suka fara hadaka a rayuwarsu,yarjajeniyar rashin daukan ciki,canjin halayensa,kamashi da tayi a waya da zuba mata tablet da yayi na zubda ciki,bayyanar ha’incin da yake mata ba tare amma data kama sunan raihanatu ba,azabar daya dinga gana mata har zuwa sanda Allah yayi fitarta daga gidan da taimakon afifa da kuma raihanatu. Kamar wani mahaukacin zaki ya miqe ya soma zage zage,yaa zaid baisan sanda yasa qafa ya kwasheshi ba cikin matsanancin fushi,sai gashi kif a qasa

“Idan ka sake mana magana sai na cire maka harshe” kota ina jikin momee rawa yake,duk sauran qwarin gwiwar da take dasu sun kwaranye sunbi ruwa,don itama wasu abubuwan batasan dasu ba.

Jakar ta fara musu bayani,tana zazzage abubuwan ciki tana nunawa kowa,sai maama ta kasa daurewa,ta rufe fuskarta da hannunta kuka mara sauti yana qwace mata. Duka duka nawa sãahar din take da har zata fuskanci irin wannan cin zarafin cin fuska da zallar cin amana daga gurin da namiji?,ko ita data kawota duniya bata taba fuskantar wani abu da yayi kamanceceniya da wannan ba

“Duk abinda ta fada gaskiya ne,ni shaida ce” muryar raihanatu ta ratsa falon,sai suka waiwaya suna kallonta, idanunta cike fal da qwallar tausayin sãahar din,don itama wasu abubuwan sai yanzu takeji.

Mamaki ya cika momee qwarai,wato raihanatu zata zame mata ‘yar kuka?,ta raini makashiyarta?

“Ki daina mamaki momee,ko kina tunanin bansan ba don Allah kike riqe dani ba?,bayan bautar da nake muku kina lissafin sake maidani machine din tatsar kudinki?, bayan kin cinye dukka abinda mahaifiyata ta mallaka,tun tana raye bata da bakin musa miki?” Maganar ta sake zuwarma momee a bazata,lokaci guda ta nemi sukurkuta mata runani,ya akayi yarinyar tasan wannan

“ni zaki butulcewa raihanatu?”

“Dalla malama ki rufewa mutane baki” yaa Saifullahi ya fada cikin muguwar tsawa,ransa baqiqqirin,tamkar zai kifawa momee din mari,hannu Dr mamman ya daga masa,saboda shi wani abuma ya tsaye masa a wuya ya kasa magana,idanunsa qirrr saman fuskar adam,yana tuna girma da nauyin karamcin da ya yiwa rayuwarsa,tarin alkhairai wanda ko sãahar da take matarsa ya hana ya gaya mata,yakance masa

“Nayi maka ne fisabilillahi saboda Allah,ko ummin abba banaso ta sani,kasan su mata,wani qaramin tunani garesu,qanqani abu zai hadaka dasu sai su goranta maka”.

Sam basu farga ba,ashe tuni yaa zain yayi kiran mopol,kafin kace wani abu sai isowarsu akaji da sanyo kansu cikin gidan

“Waye yayi hakan a cikinku?” Dr mamman ya tambaya

“Kayi haquri abba,nine” ya zaid ya fada yana miqewa,yanason a hukunta masa adam da mahaifiyarsa hukunci Mafi tsanani da radadi,irin hukuncin da har su koma ga Allah ba zasu mance dashi ba.

“Amma ina zaune ba zaka fara neman shawarata ba zain?”

“Kayimin afuwa abba” yana gama fada ga fita,cikin second biyar suka cika falon.

“Wait please” ya Saifullahi ya fada,ya miqa hannu ya ciro paper,ya zaro pen daga aljihunsa ya dorawa adam da ake qoqarin cukuikuyewa

“Maza rubuta mata takardarta” kai ya girgiza cikin taurin zuciya da taurin kai

“Matata ce,kuma ina sonta har yanzu,don haka bazan saketa ba,saidai…….” Bai qarasa fada ba ya Saifullahin ya daukeshi da wani kyakkyawan mari

“Mu zaka gayawa maganar banza da wofi?,wato saboda baka daku ba har kana da qwarin gwiwar yi mana musu ko?” Duk da marin amma sai ya sake girgiza kai

“Saidai ta mutu da igiyar aure na”

“Ba zata mutu ba kuwa,saboda mudin ba jahilai bane,kawai kotu akwai shari’a kuma” ya muhyiddeen da mamakin adam ke sake kasheshi ya fada. Saidai yana rufe bakinsa mopol din ya saukewa adam din wani irin zazzafar mahangurba da lokaci guda ta sauke masa jini ta hanci da labbansa,ta kuma tara masa wani lafiyayyen jini a gefen idanunsa. Ihu momee ta saki tana neman taimakon wai za’a kasheta ita da danta

“Saketa,ka saketa nace karsu kasheka baka da gata” koda momee din bata fada ba zai rubuta,shi kadai yasan kalar azabar da yaji,idanunsa a rurrufe ya rubuta mata saki daya. A fusace ya Saifullahin ya duba

“Don ubanka qarashe mata sauran biyun” dr mamman ne da nasa mamakin ya qarasa daskarar dashi ya daga masa hannu

“Rabu dashi” ya basu umarni a taqaice,daa yaso ya hana a tafi dasu,amma yadda suka nuna rashin nadama kwata kwata bisa fuskarsu yasa ya kasa hana mopol din tafiya dasu.

“So nake a azabtarmin dasu yadda ya kamata,a sassaba masa kamanni shida uwarsa,banason kowa yasan inda suke,kada kuma a daga musu qafa ko na kwana daya,zamuyi waya” yacewa da shugabansun

“Karka damu,sakamakon mummuna ai mummuna ne” shima ya fada cike da jin takaicin adam da uwarsa.

Ko minti biyar basu qara a gidan ba suka tattara nasu ya nasu suka fice a gidan,sãahar ce tabi raihanatu da kallo wadda ta hada nata kayan ta fara yin titi

“Abba bata da kowa a qasar nan,kuma ko yanzun bata da wajen zama,dama suke riqe da ita,na tabbatar kuma ba zasu ci gaba da riqonta ba” wannan yasa suka dauki raihanatun,abban kuma ya tabbatarwa sa sãahar zai kula da nauyinta da rayuwarta,zuwa gaba kadan kuma zasuje ghana a binciko danginta na qwarai,don susan irin riqon da momee tayi mata. Ajiyar zuciya sãahar ta sauke

“Allah yasa su iya wani abu,saboda momee ta cikasu da kyaututtuka,a yanzu kuwa lalacewa ta tattaru a cikin dangi,duk lalacewarka izgilancinka da rashin ganin girman mutane,taka mutane da mugunyar halinka kaida iyalinka,muddin kana ungo ungo,sai idanun ‘yan uwa su rufe daga aibunka,a rasa wani tsayayyen da idan kayi ba daidai ba za’a tsaya a tsawatar maka a kuma hukuntaka dai dai da laifinka” kai abban ya jinjina,maganar sãahar tana kan hanya

“Wannan shine yake kawo lalacewar zumunci da tabarbarewarsa,dole sai an hadu za’a gyara,dole sai an hadu an hukunta me qarfi ko mara qarfi,ya zamana kowa baifi qarfin doka ba,Allah ya kyauta,yasa mufi qarfin zukatanmu”

_NOTE:wadannan matsalolin da suke babbar masifa ce suna nan suna ruruwa cikin al’umma,a yanzu dan qanwarki ko dan yayarki yana iya cin zarafinki,uwarsa ta goya masa baya,saboda suna yiwa dangin nan dan ihsanin da bai taka kara ya karya ba,su kansu masu fada aji a dangin sai kaga sun zama hoto,basu da wani amfani saboda ba kowa suke iya juyawa ba,sun wulaqantar da kansu saboda suna tsoron wasu sashe,idan sunyi ba dai dai ba basu isa su hukuntasu ba,ke kuma uwa wallahi wallahi kanki kikewa baqar dabara,kin nunawa ‘ya’yanki kowa baida mutunci,babu me gaya musu suji,saboda kema a haka kika taso,kina ganin kinfi qarfin a baki shawara ko a tsawatarmiki,kin ruguza iyalinki da hannunki,bayan babu ranki haka zasuci wahala,saboda masuyi don ganin idanunkin guduwa zasuyi su barsu,kina qabari ke kuma kina amsar query akan tarbiyyar da kika yiwa yaranki,kina qabari ana nan duniya ana alawadai da halin yaranki,abinda kina raye babu me iya fada,kin mutu kin barwa dangi masifa,qila akwai mata a cikinsu,sai kiga yarinya ta kasa zaman gidan miji,ta kasa biyayyar aure saboda a tarbiyyar da uwarta tayi mata batasan biyayya ba saidai ita a bita,sai tsananin rabo yake zaunar dasu,to duka mu sani,dake uwa da kika zama shashasha sauna,wadda ke iya bari diyan cikinta su wulaqanta ‘yan uwanta saboda yunwar ilimin addini da qarancinsa,dasu dangi da suke ganin barna su kasa tsaiwa a gyara saboda kowa yana tsoron fadin gaskiya,ta silar haka zumunci ya gurgunce,wallahi wallahi kowa sai ya tsaya yayi bayani gaban Allah,da wanda aka cuta da wansa yayi cutar,Allah ka bamu dacewa,ka bamu ikon tsaiwa akan gaskiya akan mutum ko wayeshi,komai girma da matsayinsa,ka rabamu da kwadayin abun hannun kowa,ka wadatamu da wadatar zuci daga gurinka👏🏽_

Page 56

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 56

    Cikin lokacin kowa qoqari yake ya faranta ran sãahar,tamkar rige rige akeyi,kowa yana bakin qoqarin ganin ya sanyata walwala,dukkansu sun fahimci depression ya fara kamata,ta soma wasu attitude da suke bayyana hakan. Anty farheen ita ta tashi tsayin daka a kanta,daga qarshe ta karbeta daga hannun maama,duk da maaman taso a barta da diyarta,to amma farheen din nada wani irin kirki da tausayi,dole ta haqura ta bar mata ita.

      Zamanta hannun farheen yasa ta qaru da abubuwa masu tarin yawa,sannan ta taimaka mata wajen mantawa da wasu abubuwan,tare da fara dawowa cikin saitinta. A lokacin ya muhyiddeen ya samu wani aiki a Scotland,sai duka suka tattara har sãahar din suka wuce can. Koda sukaje din asibiti me kyau farheen tasa yaa muhyi ya duba musu suka fara zuwa ita da sãahar din,akwai sashen guiding and counselling masu kula da matsaloli irin wadan nan da hanyoyin kubutar da tunani daga wannan damuwar,abinka da qasashen da sukaci gaba,watanni kadan saiga sãahar din ta koma dariyarta da walwalarta,ta sake murjewa,gayu ya sake zama a jikinta fiye da kima saboda tasirin zamanta da anty farheen,idan ka ganta saita bala’in burgeki ke da kika diya mace ma,nan da nan anty farheen tayi amfani da wannan damar ta nema mata makaranta da kanta,ta dora karatun mastering degree dinta.

      Cikin shekarun komai yazo ya wuce,saidai babu ta yadda za’a ji ciwo sannan a warke ba tare da ya barwa mutum tabo ba,koda a gangar jiki ne bare kuma a guri me matuqar muhimmanci da sammatsi irin ZUCIYA,zalincin adama gareta yasa ta hadu sa ciwon kai mai matuqar tsanani sanadin alluran da aka dingayi mata ba bisa qa’ida ba,wanda inda ace anci gaba da yinsu,tsaf kwanyarta zata juye cewar likita,wannan tabon shine abinda ya haifarwa da sãahar tsanar maza,tsana me tsanani,babu halitta da takewa bahagon kallo irinsu,ta tsani taji kalmar soyayya,kalmar AURE kuwa tana sanyata jin wani tashin hankali,kwatankwacin mutumin da yaqi ya tunkaro shi,duk wani abu da zai sanyata hulda da maza ta datseshi,wannan ne yasa tunda suka dawo Nigeria tayi zamanta wajen anty farheen dake ji da ita,take kuma sake maidata macen da idan aka kalla sai an sake juyawa an kalla cikin hikima. Batason kowa yayi mata zancan aiki,shi yasa taqi fidda results nata data samu,results me kyau da yayi bala’in burge yayyenta,duk da dama tunda can sunsan ita din bata da wasa ta fannin karatu,hakanan tana da kwanyar da dukka cikin gidan ita da yaa Saifullahi keda irinta,duk da sauran suma ba daga baya ba,wannan yasa kowanne yake riqe da wani babban matsayi,ya kuma tara dukiyar da a qananun shekarunsu idan aka gaya maka yawanta zakayi mamaki,dukka cikinsu babu rago,babu kuma koma baya.

      A wancan lokacin sati guda dr mamman yace su zain su saki adam,su barshi da halinsa,yayi imanin bazai gama rayuwa a daron duniya ya wanye qalau ba tare da Allah ya hukuntashi ba,duk kuma yadda sukaso hukuntashi hukuncin Allah shine gaba da nasu. Hatta da afifa bata bayar da goyon baya ba,ita inda son samu ne,akai adam din muhallin da hatta hasken rana baya shiga gurin ayi masa daurin rai da rai.  

      Sun bar dr mamman aka cewa an sakeshi,amma basu barsu ba saida sukayi watanni uku cur suna karban hukunci a hannun sajoji,kafin sannan kuwa gaba dayansu ba wanda baiji a jikinsa ba,duk wani abu da sukasan ya mallaka ta silarsu sun karbeshi,ciki harda gidan da momee ke zaune,da wanda suka rayu shi da sãahar,sai a sannan suka gane cewa gidan ashe shima ya saidashi,ta yadda idan yabar qasar saidai sãahar taji ana batun ta tashi ga masu gida. Tuni suka sayar da gida,su kuma ainihin wadanda suka siya a wajensa dama baikai ga basu takardun ba,ya karba kudinne kawai,nufinsa sai ranar da zasu bar qasar ya danqa musu ya qara gaba,sukace ba zasu yarda ba,yaa zain yace su nema kudinsu a hannun dan damfarar da suka bawa. Sunsan tako ina family din dr mamman girema ba abun wasa bane,sunfi kuma qarfin wannan gidan bare suce cuwa cuwa sukayi,don haka suka karkata akalar tuhumarsu ga adam wanda a sannan ko gidan da zai kwanta a ciki ya huce tarin gajiyar da sojojin suka hada musu ya kuma yi jinyar raunukan jikinsa bashi dashi.

      A sannan tuni abba ya samawa raihanatu karatu a maryam abacha American university dake garin maradi a jahar nijer,tana can ta dora karatunta daga inda ta tsaya,babban burinta kenan a rayuwa,wanda momee tasha gaya mata bazai taba cika ba,ba zata dinga adashin da batasan ranar kwasarsa ba.

*Dama hausawa sukance ALHAKI KWAIKWIYO NE,ME SHI YAKE BI*

     Juyawa ta sakeyi a karo na babu adadi bayan gama dukka wannan bitar da qwaqwalwarta tayi,gefan da afifa ke kwance ta kalla,kusan wasu matsalolin tare suka fuskancesu ita da afifan,amma sau tari sai taji inama itace afifan?,inama bata taba sanin wani adam ba bare ya shiga rayuwarta ya cutar da ita haka ba?. Tsaki taja qasa qasa bayan fargar da ita da zuicyarta tayi,saita miqe ta sauko daga gadon a hankali ta nufi toilet,cikin ranta tana sake jin yaqini da qwarin gwiwar cewa,ya zame mata tabbas tayi wani abu,har yanzu batajin cewa tayi warkewar da zata doshi wani aikin ko kuma aure,dole tayi hobbasar da zata sake nesantata daga dukkan wata mu’alama da zata sake hadata da azzalumar halittar maza,marasa tausayi da jin qai,marasa amana kuma,dole ta yiwa kanta wannan aikin.

      Daren gaba daya ta raya,da tarin addu’o’in ta da buqatunta jingim wajen Allah,ko kafin ta kammala ma wata irin nutsuwa ta maye gurbin bacin rai da fargabar dake motsa zuciyarta,albarkacin wannan kuma a nan saman abun sallar daddadan bacci ya saceta.

     Afifa ta rigata tashi sallar asuba,batayi mamakin ganinta a kwance a nan ba,saboda ba kowanne dare ne take iya kwanciya ta shareshi dukka tana bacci ba,saita qarasa cikin tausayawa da qauna ta tabata tana kiran sunanta. Idanunta ta bude tana kallon afifa

“Ya shehiya sãahar,a tashi ayi sallar asuba,Allah ya amsa addu’ar nan,ina fatan kin sakani a ciki,Allah ya kawo masoyi na gari” qaramin murmushi tayi duk da cewa daga bacci ta tashi,hakan kuma ya sake qarawa fuskarta kyau,sai da tayi brush ta daura alwala ta fito sannan ta amsa mata

“Allah ya kakkawo,saidai ita afifa akwai wanda take jira” bata tsaya jin amsarta ta tayar da sallah ta barta da baki a bude tana cewa dariya nason kamata

“Kajimin yarinya zatamin sharri?”.

     Dukka wani azkar data saba yi sai data yishi,haka kawai taji idanunta babu wani sauran bacci,duk da cewa ba wani baccin kirki ta samu ba adaren jiyan,don haka ta shafa addu’o’inta ta nade abun sallar,ta dauki wayarta ta koma saman gadon su,tana kallon afifa da idanunta ke rufe,da alama bacci ne sosai a kanta, saita ja duvet itama tana shirin rufa,dai dai lokacin da tex din ahmad ke shigowa wayarta.

     Ko bata buda ba tasan saqon barka da safiya ne,taja qaramin tsaki,tana tunanin sai yaushe zai gaji da naci yace ya haqura da ita?,ba amsa,don haka ta share saqon bayan ta buda wayar.

     Watsapp tahau zata buda wani qaramin document na addu’o’i da anty farheen ta turo mata,yana da dan nauyi,don haka da tayi clicking akai,sai ta fita da zummar rage jira kafin ya kammala buduwa.

      Haka kawai ta samu kanta da buda jerin list na mutanen da sukayi status a safiyar ranar,duk da cewa kuwa ba dabi’arta bane hakan. Sunan mr sadeeqa yana sama sama,auntie din su nurain ‘ya’yan yaa Saifullahi. Sam ta mance da matar a rayuwarta,duk da cewa tana da kirki qwarai,tun kafin tayi aure lokacin da takanje gidan yaa Saifullahi din,wani lokaci ita ke kaisu school da safe,a nan suka dan saba da ita saboda matuqar kirkinta,sai kuma dabi’arsu tason yara tazo daya,wannan ya sanya suka dan saba suke gaisawa,har sukayi exchanging numbers.

      Batasan ya akayi ba hannunta ya taba status din mrs sadeeqa,take ya bude,hotone na wata baby girl,duk da cewa hoton ya danyi blurry kadan,amma hakan bazai hanaka iya gane kyan yarinyar ba,tayi rubutu a qasan hoton kamar haka

_she has being suffering and battling epilepsy,she is looking for a good nanny,praying for an easy recovery my class cute angel_😥😥.

      Epilepsy qwaqwalwarta tayi mata tariyar maganarsu ta jiya da sukeyi da afifa kenan kafin ta fita,take tausayin yarinyar taji ya taba zuciyarta duk da bata iya ganin fuskarta sosai,fingers dinta guda biyu ta saka tayi zooming hoton,still dai it was blurry,hakanan kawai tayi replying status din da cewa

_”is that serious?,she’s looking for a Nanny”_ sai data tura saqon kuma sai tayi shuru,ita kadai tana tunanin meye amfanin tambayar data tura. Da sauri ta koma ta jerin charts dinta da zummar gogewa,amma sai ta tarar mrs sadeeqa din tuni ta gani,har ma tana typing wani abu,hakan yasa ta haqura ta koma duba document dinta da take budewa,amma kuma hankalinta nakan inbox din mrs sadeeqa.

     Har zata buda taga shigowar saqo daga mrs sadeeqa din. Sake fita tayi ta duba

“Yeah,she’s my student,ina tausayinta sosai,akwai wata ne daga bangarenki?” Tausayin data darsu a zuciyarta taji ya sake motsawa,a taqaice ta tafa mata

“No,but zan bincika,i will back to you idan na samu Allah ya bata lafiya”

“Ameen,thanks for your concern”. Kashe data din tayi,ya dudduba addu’o’in sosai,zuwa lokacin garin ya fara haske,sai ta kashe wayar gaba daya ta sake gyara kwanciyarta ta kwanta tana rufe idanunta da fatan samuwar baccin.

       Bacci tayi sosai,har na kusan awanni hudu,wanda qarshen baccin yazo mata da mafarkin da ya sanyata farkawa. Miqewa tayi ta zauna sosai tana duban gefan afifa,bata a gurin,tabi dakin da kallo,da alama ma harta gyara dakin,gadon da take kwance a kai ne kawai bata gyara ba. Hannunta ta sanya ta tattare gashinta daya zame daga band din data matseshi dashi saboda santsinsa,ta daureshi gudi daya tana sauke qaramar ajiyar zuciya,tunaninta na komawa baya kan mafarkin da shine silar farkawarta a yanzu,zuciyarta cike fal da mamaki,to meye hadinta da yarinyar da bata taba ganinta ba sai dazu a status din mrs sadeeqa da har zata yi mafarkinta?,ko a dazun ma bata gama tantance fuskarta ba,kamar yadda a mafarkin ma bata gama ganin fuskarta sosai ba.

“La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin” ta fada a hankali,sannan ta zamo ta sauka daga gadon,har yanzu zuciyarta bata daina mamakin yanayin data ga yarinyar a mafarki ba. Kuka takeyi sosai tana riqo hannunta,yayin da ita kuma take qoqarin zame hannun nata ta tafi ta barta,daga bayan yarinyar kuma wata matace take biye da ita da sharbebiyar wuqa tana son caka mata. Da wannan tunanin ta isa toilet din,ta ciri brush ta matsa toothpaste ta fara wanke bakinta,har yanzu tana nacin son gano abinda mafarkin ke nufi amma ko daya tunaninta bai iya hasaso komai ba,to shin me ma zata hasaso din?,bayan batasan wace yarinyar ba,daga qarshe sai ta tattara tunanin ta watsar,ta barwa ranta cewa tsabar son yara da take dashi a jininta ne,da kuma yadda zuciyarta ke da rauni akan dukka abinda ya shafi yaro.

       Wanka tayi gaba daya sannan ta dawo dakin tana shiryawa,afifa ta shigo da dan tray data shiryo breakfast dinta a kai,hannunta daya riqe da waya tana amsawa. Idanunta akan fuskar sãahar din harta qaraso,sai ta miqa mata wayar muryarta can qasa tace

“Please” hadi da karyar da kai gefe daya alamun roqo. Kafeta tayi da idanu tana son nuna mata bata kyauta mata ba da zata sanyata yin abinda batayi niyya ba,sai kuma daga bisani ta miqa hannu ta karba wayar,don afifa ce tafi qarfin komai a wajenta,ta kara wayar a kunnenta tana qoqarin tsane jikinta da qaramin towel.

Page 57

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 57

      Kamar yadda tayi tsammani mahmud ne,ajiyar zuciya mai nauyi ya fara saukewa

“Kiyi haquri,duk yadda naso nayi miki yadda kikaso,zuciyata ta gaza bani hadin kai,na mugun jarrabtata da sonki har bansan iyaka ba” bakinta ta tabe,tana jin kamar ta saki wayar ta tarwatse,da wadan nan kalaman nasa gwara ya sakar mata ihu a kunnenta yafi mata sauqi,amma hakanan ta daure ta amsa a taqaice

“Is okay,bana dan jin dadi ne,that’s why na kashe wayar”

“Ya salam” ya fada cikin nuna kulawa

“Me ya sameki?”

“Noo,lite headache ne,amma i feel better”

“To alhamdulillah,kibar wayar a kashe ki samu ki huta sosai,idan inason jinki zan kira ta line din afifa,bata wayar zamuyi magana” batace komai ba ta zare wayar ta miqa mata tana harararta,tana danne dariya ta karba,batasan me ya gaya mata ba,taga ta miqe ta fita,ta bita da kallo tana tabe baki taci gaba da shiryawa.

      Tana cikin saka kaya afifan ta dawo,ta koma ta zauna tana ci gaba da cin abincinta,saita fasa daurin dankwalin da tayi niyya,dama can dankwali asara ne cikin dinkunanta,ta qaraso gaban afifan bayan ta jawo stool ta zauna ta sanya hannu suka fara ci tare. Har suka danyi nisa babu me cewa da dan uwansa wani abu,afifa ta karanci yau mutanen ne a kusa,ita kuma bakinta magana ce fal,don haka ta koma ta zauna sosai tana kallon sãahar

“Na baki shawara?” Dubanta sau daya tayi sannan tace

“Bani mana,is ether na dauka ko na bar miki kayarki”

“Alright,ammm……magana ta gaskiya na jima banga soyayya me zafi irin wadda mahmud yakeyi miki ba…..”

“Tam, contract din kuma da kika karba kenan da safen nan,ko azahar batayi ba?” Dole ba tare data shirya ba dariya ta qwace mata sosai

“Allah ya isa bestie,wait……wai me kika mayar dani?”

“Me dalili,naga alama sana’ar da kikeso ki koma kenan” wannan karon ma saida wata dariyar mai sauti ta kufce mata har tana shirin qwarewa,a nutse sãahar din ta tsiyaya ruwa ta miqa mata

“Maza karba kisha kada ki wuce gana ya rasa campaign officer dinsa” tana dariyar tana sha,har taji dai dai ta ajjiye,tayi gyaran murya kadan tana dubanta da idanunta da suka tara hawaye

“Seriously nake miki magana,amma naga kinason ki maida abun wani joke,don Allah bestie ki manta da komai,ya kamata kiyi moving forward mana,kina tunanin zamanki a haka adam bazaiyi tunanin shi kike jira ba?,har yanzu soyayyarsa ta hanaki kallon kowa bare ki aureshi?”

“Soyayya?” Ta furta kalmar kamar ranar ta fara jinta,kai afifa ta jinjina

“Yes” wani qaramin murmushi me ciwo sãahar din ta saki,sai kawai ta miqe

“Banda bayan soyayya dake tsakanin namiji da mace,kawai nau’ikan soyayya kala kala, kamar wadda ke tsakanin ‘yan uwa da iyaye,da nace Allah ya tsinewa soyayya albarka” ido afifa ta zaro,ta kuma hangame baki yana kallon sãahar,wadda tayi furucinta hankalinta kwance,saima ta gyada kai ta juya tana nufar qofa

“Naga alama tunda kika samu annual leave din nan rashin aikin yi ya sameki,shi yasa kika amsa contract daga wajen gana,to wallahi ke dashi ba wanda zaya matsamin” tana kaiwa qarshe ne dai dai sanda take fita a dakin gaba daya.

     Gurin ummee tayi tafiyarta,wunin ranar gaba daya taqi tsaiwa sauraron bayanan mahmud. Saidai wani abun mamaki,duk bayan wasu mintuna sai yarinyar da ko sunanta bata sani ba ta fado a ranta,hakanan maganar da sukayi da mrs sadeeqa,wunin ranar har yamma,batayin minti arba’in cikakke bata fado mata a rai ba.

      Ta idar da sallar la’asar tana yiwa ummee din gyaran wardrobe dinta kiran yaa Saifullahi ya shigo wayarta,cikin girmamawa ta daga kiran ta kara a kunnenta,ta gaidashi a aladabce,saboda shine babba duka gidan,kuma hatta da yaa muhyi yana bashi girma,duk da cewa shike binsa,akwai girmama na gaba sosai a tsakaninsu

“Kina gidan inna ummee dinne?,akwai baqo da zayazo ya sameki,abba yace a shaida miki” gabanta ne ya fadi,rudewa kuma ta sameta lokaci guda,har ta kama sunansa ba tare data shirya ba

“Mahmud?”

“Eh fa,da wani abu?” Ya tambaya kai tsaye da seniority din nan nasa

“A’ah,daman…..dama munje therapy saloon ne”

“Alright,zai kiraki yanzun saiki gaya masa” daga haka ya yanke wayarsa abinsa.

     Wayar ta jefar gefe kamar zata saki kuka,da qyar ta tsara qaryar gashi kuma da alama haqanta bai cimma ruwa ba. Bata gama wannan tunanin ba kiran mahmud din ya shigo,kamar ta dora hannu aka tayi kuka haka ta daga kiran.

      Akwai wani irin farinciki sosai cikin muryarsa

“Can I get the address?,saina sameku a can?”

“no,mu hadu a gida kawai after one hour” kamar zai zuba ruwa a qasa yasha haka yaji,cikin madaukakin farinciki yace

“Thank you,thank you so much” bata tsaya jin qarashen godiyar tasa ba ta yanke kiran tana gunaguni,ta ajjiye wayar gefe tana dafe kanta.

      Ko kwalli bata sanyawa idanunta ba haka ta fito,afifa tayi tayi amma tayi biris da ita,daga baya ma cewa tayi

“Idan kika matsamin Allah sai na fasa fita”

“Allah ya baki haquri masifaffiya” sai taja bakinta tayi shuru,tasan kadan daga aikinta.

     Tun kafin ta isa afifa tasa an cika shi da kayan motsa baki kala kala,tahowarta ya sanyashi miqewa,bai zauna ba har sai data zauna sannan ya zauna yana mata barka da fitowa,ta danne zuciyarta ta gaidashi,abinda ya masa dadi sosai. Duk yadda yasan zai sha kanta sai da yayi,tana zaune tana saurarensa har ya gama,sannan ta motsa labbanta

“Inda zakayi haquri da hakan yafi,saboda tuni na rufe babin soyayya daga rayuwata” kai ya girgiza

“Banajin zan iya,banajin zan iya daina sonki,kiyimin alfarma ki amincemin ki aureni,zan iya zama dake a hakan koda ke baki sona” tsam ta miqe,saboda ta fuskanci mahmud din yayi nisa,kuma bayajin kira sam. Ta bude bakinta da niyyar magana ya zaid ya iso wajen.

      Yanayin yadda taga suna gaisawa da shi cike da sanayya mutunci da girmama juna ya daga hankalinta,sanda suka gama gaisawan da tambaye tambayen juna sai zaid din ya kalleta

“Ki riqeshi da kyau,mutumin kirki ne sosai” maganar tayi mugun tabata,har kuma mahmud yayi mata sallama ya wuce bata sake fahimtar abinda yake fada ba. Haka taci gaba da kasancewa har zuwa dare,tabbas!,ba shakka komai zai iya faruwa,muddin mahmud yaci gaba da samun irin wannan soyayyar daga wajen ‘yan gidansu,idan tace komai,tana nufin komai din,ciki harda tausata ta karba aurensa ba tare data shirya ba!. 

     Wannan sautin da ya tsarga daga cikin kwanyarta shi ya sakata miqewa zumbur ta zauna saman gadonsu,afifa dake gaban system tana wani aiki ta waiwayo tana dubanta,saita maida kai tana ci gaba da aikinta ganin ta dauko wayarta itama ta bude. Tun bayan tafiyar mahmud ta fahimci tana cikin damuwa,ta riga da tasan damuwarta na meye,so shi yasa ma bata tambayeta akan komai ba.

     Kai tsaye ta kirayi layin mrs sadeeqa,bugu daya tal ta daga,da alama tana kusa da wayar,cikin mamakin ganin kiranta da kuma zumudi hadi da girmama suka fara gaisawa,tana tambayarta tsaffin dalibanta su fadeel

“Basu dawo qasar ba har yanzu…..” Ta furta cikin son yankewar tambayoyin ta kuma isar da nata saqon

“Ma sha Allah” mrs sadeeqa ta fada

“Inason tambaya ne naji,your student,ta samu nanny din nan kuwa?” Kai ta girgiza

“Kai,gaskiya i don’t think so”

“So if you don’t mind nace akwai me buqatar aikin” murmushi ta saki

“Ma sha Allah,so far dai banajin akwai wadda tayi musu,duk da hajiyan tata tace akwai wadanda aka yiwa screening,amma basu cancanta ba” duk da batun screening wa nanny’s din ya bawa sãahar mamaki,amma ba wannan bane yanzun a gabanta

“Alright,hakan yayi”

“Naji dadi,nasan ko wace za’a samu daha bangarenki she wil be the best among others in sha Allah,wace a ina take?,sai na yiwa hajjajun magana”

“Nice” ta fada da qwarin gwiwa. Ba mrs sadeeqa ba,hatta afifa dake aiki batasan sanda ta tashi ta zauna sosai tana duban sãahar da wani irin madaukakin mamaki ba,tare da tantamar abinda kunnuwanta suke son jiye mata

“Na’am madam,me kika ce?” Mrs sadeeqa ta tambayeta cike da kokwanton abinda taji daga bakinta

“Yes,nice,ni zanyi aikin” dan murmushi mrs sadeeqa ta saki

“Madam,ko baki kula sosai da wanne irin aiki bane ake magana,ba aikin company ko na banki ko lecturing bane……raino ne,na yarinya me lalura,duk da ba qarama bace sosai,amma dai raino ne” ido sãahar ta lumshe sannan ta budesu lokaci guda

“Ya salam ya Allah” ta furta a qasan zuciyarta,batason ta fara da samun matsala tun yanzu,saboda ba zata iya jurewa ba,zuciyarta ta karkata matuqa,ta kuma kwadaitu da buqatar aikin

“I Know,na fahimta,just……ina sha’awar yin aikin ne” shuru mrs sadeeqa tayi cikin kokwanto matuqa, kafin daga baya tace

“Zaki iya kuwa madam,wouldn’t it be a disgrace?”

“Surely mrs sadeeqa,ko ba komai aikin lada ne” ta fadi hakan har zuciyarta

“Gaskiya ne,i will talk to hajiyan,zan miki magana,kin gama samu ma in sha Allah,you are not the kind of people to be ignored”

“Thank you ma’am” sãahar ta fada tana gintse kiran

“Thanks for what sãahar?,wanne mummunan tsari ne wannan?,a nanny?” Afifa ta furta kamar zatayi kuka,kalmar na sukar ranta.

     A nutse abinta hankali kwance take kallon afifa din harta gama,saita sauka daga inda take zaune,ta dawo kusa da afifan ta zauna sosai tana fuskantar ta

“Wannan shine burina a yanzu, abinda kuma nakeso,bazan iya boye miki komai ba bestie,shi yasa nayi wayar ma a gabanki,jikina yana bani mahmud nason yin galaba akan su abba dasu ya Saifullahi,idan banyi wasa ba kuma komai yana iya faruwa,so I want to be far away from him for a while that’s why na nemi wannan aikin,banason mahmud afifa,bazan iya aurenshi ba,zanyi nesa dashi,duk sanda na samu tabbaci da yaqinin iya zama da wani namijin…..koda shi mahmud dinne zan dawo a kurkusa,i won’t be longer,support me please bestie”

“What a bad idea sãahar?,you mean….zaki koma ‘yar aiki fa kenan?,wait…. idan na yarda ma su abba kina tunanin zasu yarda da ke?” Murmushi ta saki kadan

“A yanzun nafi sha’awar zama ‘yar aikin bestie,ko banza babu ruwana da kowa da matsalarsa,zan zauna guri daya nayi rayuwata da yarinya qarama,zan cika burina na raino wanda adam ya dakushe min…….zan samu ladan yarinyar dake dauke da cutar epilepsy,ban sani ba,kota silar jinyar Allah ya yayemin tawa damuwar bestie,don Allah ki maaramin baya,kada ki watsamin qasa a ido” shuru afifa tayi tana jin yadda sãahar ta riqe hannunta da kyau,da alama tana buqatar yin hakan,kanta ya kulle sosai,ta yaya zata mara mata baya ta mayar da kanta nanny?,bayan da gantanta?,duk randa maganar ta bayyana me zatace da su abba da maama?. Sosai sãahar din ya tsareta da ido cikin laushi da salon rarrashi,sai ta rasa amsar da zata bata,daga bisani Allah ya kimsa mata,ta waiwayo ya dubeta tana sauke ajiyar zuciya

“Ni dake duka muje muyi istikhara,idan mun samu nutsuwa akan abun,zan maara miki baya”

“Kin tabbata da gaske kike?” Murmushi ta saki

“Da gaske nake,amma ki tanadi abinda zaki gayawa su abba,don ni bazan iya musu qarya ba” miqewa tayi daga tsugunon da tayi ta zauna sosai

“Kinfi kowa sanin ba dabi’ata bace,so nima ba qaryar zanyi masa ba”.

      Akan haka suka samu matsaya ita da afifa din,sannan kuma dukansu suka shiga istikhara din kamar yadda afifa ta shawarcesu. Cikin kwana ukun kuma baki dayansu ita da afifan,kowanne ya samu nutsuwa cikin ransa,rudanin dake ran afifa ya kau,haka dan kokwanton da ita sãahar din kanta takeyi game da aikin sai taji babu shi,taji har cikin ranta zata iya,fatanta daya kada abba yace ba zatayi ba.

*_TOFA😂,me yake shirin faruwa kuma?,GUDUN K’ADDARA sãahar ke shirin yi ko kuwa?,ku biyoni dai muje zuwa_*

Page 58

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 58

     Kwana biyu kacal Mrs sadeeqa tayi kiranta,ta gaya mata cewa hajiyan tayi accepting nata,saboda haka ta shirya kwana uku masu zuwa zasu zo da mota a dauketa ta kama aikinta.

     Taji dadin hakan,amma kuma fargaba ta lullubeta na yadda zata tunkari abban,wuni tayi cikin rashin sukunin,afifa na kallonta taqi bata shawarar komai

“Na gama aikina ai,tunda har nace bazan gayawa abba manufar komai aka aikinki ba”

“Haba bestie”

“Da gaske nake” ta sake jaddada mata,sai daga bisani ta samu qwarin gwiwa,bayan wata idea ta fado mata,ta dauki wayarta da sauri ta fara kiran anty farheen.

“anty,zan sameki yau a gida?”

“Eh ba inda zani yau,akwai wani abu ne?”

“Saina iso kawai” tace da ita,saita ajjiye wayar ta fada toilet kawai ta fara wanka,so take ta gama da kowacce matsala a yau,tayi shirin tafiyarta hankali kwance.

     Cikin lokaci qalilan ta shirya cikin wata doguwar rigar abaya qirar qasan oman mai sulbi da kuma tsarin zubin duwatsu masu daukan hankali,fuskarta ta sake wani fresh da wani irin haske me kyau,kalar abayan na charcoal color ya karbi farar fatarta sosai,sassanyan qamshinta na bin kowanne sashe na dakin har zuwa falon da batakai ga fitowa ba.

       ‘Dan abinda take da buqata ta dauka a wata qawatacciyar qaramar jaka me jikin mage,dai dai lokacin da afifa ke kitchen tana duba girkin abbansu da basu aikin gidan suka dora ta dawo dakin,ta murza qofar ta shigo,idanunta akan sãahar

“Madam nanny” ta fada tana murmushi hadi da tabe baki, zagayyun fararen idanunta ta juya tana goya jakar a bayanta

“Yes,daga yau sunana kenan” qaramar dariya afifa tayi tana zama saman stool

“Kinsan Allah zaiyi wuya ma su karbeki as nanny,shin wai ke baki kallon kanki ne?,wace zata daukeki ‘yar aiki muddin tana da aure?,wace wawiyar ce?…..”

“Don Allah afifa tsaya,kiyimin fatan alkhairi mana,wannan duka fatan tsiyan na meye ne ha’an”

“Baqinciki nakeyi, bestie na zata zama ‘yar aiki”

“Okay,that’s fine,kici gaba da fada” saita fara zura dogayen qafafunta cikin wani lallausan plate din takalmi

“Ina zakine ma babu ko gayyata?” Ta jefeta da tambayar bayan ta dakata daga danna wayarta

“Gidan yaa muhyi”

“Jirani don Allah na shirya” ta fada tana miqewa da gudu bayan ta cillar da wayar tata ta shige toilet ba tare data tsaya jiran jin abinda sãahar din zata ce ba. Iska me zafi ta fitar,afifa dole saita bata mata lokaci,tanason ta gama komai da wuri ta iske abbanta a gida,ta kalli agogon dake daure a hannunta dan india dan kamfanin Daniel Wellington,saita maida dubanta ga qofar bandakin

“Ki sameni a wajen ummee,don’t stay longer please” saita tsugunna ta dauki laptop dinta me tambarin apple ta fice daga dakin.

•••••••••”daga ina kuke halan da yamman nan?” Farheen ta fadi tana zama saman kujera,bayan ta fito musu da plate din snacks,me aikinta dauke da daya try din data shirya musu smoothie,don ita din gwanar girki ce kala kala,fridge dinta kawai idan ka bude zaka samu fresh snacks sosai,a nan din sãahar ta koyi girki masu yawan gaske

“Nanny sãahar ce ta tasomu,ni fa amma gayyar sodi nazo,don bata gayyaceni ba nace ta tsayani mu taho tare” afifa tayi maganar tana duban sãahar daketa ji da rigimar khalipha shi da aleena data qara wayo sosai

“Nanny kuma?” Farheen ta fada tana dan dariya,a zatonta fadan da suka dan saba tabawa ne da shaqiyanci ma juna ya motsa tsakaninta da sãahar din

“Eh mana anty,koda yake dai ance waqa a bakin me ita yafi dadi” ta qarshe zancan tana jawo cup din da smoothie din yake,ta gyaran zaman straw din jiki ta fara zuqa a hankali tana lumshe ido,zaqi da dadinsa yana ratsata

“Uhmmmm,ta yaya don Allah ya muhyi zai iya qara aure ana masa wannan delicious din” qaramar dariya farheen tayi,tasan afifa qwarai badai iya tsokana ba,amma hakan na mata dadi,don babu komai tsakaninta da dangin mijinta face tsantsar girmama juna da zaman lafiya hadi da qaunar juna

“Basu da tabbas fa,iya girki ko qwarewa a wani abun baya hanasu qara aure idan sunso,koda kuwa ke din hurul’eeni ce,saidai kawai dai ki iya din don ki amsa sunanki na mace,sannan saboda lafiyarki yaranki dashi kansa me gidan,yaranki mata kuma ki zame musu makaranta,sannan koda wata zatazo din ya zamana ba’a fiki da komai ba,kin wuce kiyi kwaikwayo saidai keda ita ku goga,kowa ya baje hajarsa” kai sosai afifa take gyadawa cikin gamsuwa,zaiyi wahala ka zauna da farheen baka qaru da ita ba ta kowanne fanni na rayuwa.

“Ke kuma yaushe kika zama nanny?” Ta maida tambayarta ga sãahar,daga kanta tayi,sai kuma ta zaunar da aleena sosai tsakanin qafafunta

“Shi mutum idan gulma tayi masa yawa sai addu’a,da kin barta ta qarshe miki labarin….. bestie naga alama bazaki rufan asiri ba” dariya sosai afifa keyi harda kwanciya cikin kujera,abun yana bata mamaki yadda sãahar lokaci daya ta daukaki batun aikin da zahiri tafi qarfinsa,ita kanta a gidansu ‘yan aiki nawa ne?,so amma a yanzun ita bata jin komai akan aikin,tunda suka tsaya sukayi addu’a a tare.

“To nayi miki qarya ne,ba nanny din bace?”

“Ban sani ba…..am anty don Allah alfarma nazo nema” ta qarashe maganar tana maida hankalinta ga farheen

“Ina jinki,Allah yasa bata fi qarfina ba”. Komai ta zayyanewa farheen shi,saboda babu ‘yar boye boye a tsakaninsu,sannan ta qarashe da cewa

“Matsalata daya abba zaice zaiyi bincike akan inda zani aikin,abu daya nakeson kiyimin,zance masa kin sansu,sannan wata uku kacal zanyi na dawo” shuru farheen tayi tana jinjina kai,tana qaunar sãahar har cikin ranta tamkar qanwarta uwa daya uba daya,zata iyayi mata kowacce alfarma,to amma kuma akwai matuqar girmamawa da ganin mutuncin juna tsakaninta da surukanta,batason tayi musu qarya

“Zan iyayi miki kowacce alfarma,amma bazan iya shaidar abinda bani da tabbaci ba,inason ki bani address dinsu na gani,zan aika ayimin binciken ingancin halayyar mutanen gidan”

“Alright” ba wani jinkiri ta kira Mrs sadeeqa kai tsaye,ta kuma tura mata komai da komai.

     Address din ta tura mata,ita kuma ta miqawa farheen wayar. A fili ta karanta address din

“Wannan layin ai kamar layin gidan qawata sauma,bari nayi confirming” khalifa ta tura ya dauko mata wayarta,saita tashi tabar gurin. Duk da hankalin sãahar nakan yaran,amma kuma fiye da rabin tunaninta yana kan farheen data fita a falon.

     Ta kusa mintuna ashirin sannan ta fito,ta koma ta zauna a inda ta tashi

“Yanzu kuma ina da qwarin gwiwar bada shaida,layin gidan qawata ne,tasan gidan,sanann me gidan ma tacemin sananne ne sosai,mutumin kirki ne qwarai da ya samu yabo da shaidar al’umma,ko jiya shine wanda ya qaddamar da committee na tsaro na unguwar,kusan ko yaushe suna tare da me gidanta tsakanin sallar magrib da isha’i,duk da ba mazauni bane,yakanyi watanni ma baya gari,yarinyar ce tace bata santa sosai ba,tunda ba inda take fita,amma tace eh tabbas yana da diya guda daya. Ajiyar zuciya sãahar ta sake,sai ta sake jin nutsuwa tana ratsata,yanzun kam ta samu qwarin gwiwar tunkarar abba,muddin farheen tace ta san gidan,tana da yaqinin babu lallai abba ya zurafafa ko yace zai hanata,yana ganin kimarta sosai cikin surukansa.

       Ana idar da magriba sãahar din ta miqe

“Zan wuce gida bestie ya za’a yi?”

“Kije kawai,drivern anty farheen sai ya saukeni”

“Ba wata damuwa?”

“Babu miss nanny” harara ta watsa mata,ta dauki qaramar hand bag dinta ta tsugunna tayi kissing aleena a cheeks dinta.

      A kan hanya ita kadai tana driving tana tsara zantukan da zata tunkari abba dasu,wani lokacin takanji abban me sauqi ne akan maama,amma tasan muddin abban ya amince,maama din ma komai zaya zo da sauqin in sha Allah.

    Mintuna talatin kacal suka kaita gida,saboda tana tuqin tana duba lokaci,tanason ta saita lokacinta dai dai da sanda zata riski abban yana hutawa.

     Baaba habu ne mutum na farko daya fara yi mata barka da zuwa bayan ya dage mata gate din gidan ta wuce zuwa ciki,ya iso gaban motar sanda take fitowa

“Barka da zuwa farar d’iya” qaramin murmushi dake qawata fuskarta qwarai ta saki tana fitowa a motar

“Baba habu,baaba rabi ta koya maka ko?” Murmushin dake dauke da dattijanka yayi

“Sunan ya dace da me shine ai,kedai Allah yayi miki albarka keda sauran ‘yan uwanki”

“Ameen ya Allah baba habu,Allah ya qara girma” kamar sauran lokuta,bata fiya wucewa ba tare data yi masa alkhairi ba,tun tasowarta yake cikin gidansu yake kuma musu aiki bisa gaskiya da amana,ko sau daya bata taba jin wani yayi kuka a kansa ba,hakanan baaba rabi,ba kasafai gidansu suke sauya me aiki ba,saboda suma masu aikin idan suka fara,basa barin gidan haka siddan saidai mutuwa ko kuma aure.

     Hannu biyu yasa ya karba yana godiya,ba kasafai ta fiyason yawan godiyarsa ba,ko ya dinga sanya hannu bibbiyu idan zai karba abu daga wajenta ba,to amma koda zatayi maganar ma bazai canza ba,ya riga ya saba

“Ameen ameen,baba habu ayi min addu’a” ta fadi tana rufe jakarta

“Kullum cikin yi muku nake,amma a yanzun ma bazan fasa ba,Allah ya tabbatar miki da dukkan alkhairi a rayuwarki”

“Ameen ya hayyu ya qayyumu,na gode sosai” cikin wannan girmamawar da mutuntawar ta nufi entrance na gidan,bakinta dauke da

“La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem” don taga motar abban nata,hakan kuma ya tabbatar mata yana gidan,koda ya fita to masallaci ne kawai.

      Falon nasu ba kowa,ta danja qaramin tsaki,ta tsani wannan loneliness din na gidan sam,shi yasa bata cike sati guda a gidan,kwanaki taji maama tana batun zuwa nijer cikin ‘yan uwa ta dauko yara biyu mata,batasan inda zancan ya kwana ba har yanzu.

     Dakinta ta duba don sanar mata da isowarta amma bata risketa a can ba,saita zarce kitchen tana tafe tana yaba tsafta da kulawar da gidan nasu yake samu,wannan ya sanya ta taso da dabi’a ta masifar tsafta qwarai.

      Sallamarta ya sanyata waiwayowa sanda take juye tea a flask

“Daga ina da daren nan?”

“Gidan ya muhyi” ta fadi tana zagayowa ta rungumeta ta baya

“Yau kuma?,sakeni to kada na qone”

“Da kin barta ai hajiya,auta ce fa” cewar lariya me aikinsu

“Wannan gansamar?” Ta fadi dai dai sanda sãahar din ta zagayo ta karbe qaramar rariya da cup din da take tace shayin taci gaba da aikin

“Amma na hanaki tafiyar dare irin haka ko?,abbanku ma kuma bayaso”

“Za’a kiyaye in sha Allah maama”

“To Allah yayi albarka”

“Ameen maama na”. Tsaf ta gama hada mata komai sannan suka fito tare bayan taji abban yana masallaci,ita tayi dakinta ita kuma ta wuce sassan abban.

     Kayan jikinta ta fidda,ta shiga wanka,ta wanke jikinta da kyau da ruwa me dumi sosai,sai data fara yin sallar isha’i sannan ta shirya cikin riga d wando masu laushi,rigar ta kawo mata har cinya me gajeran hannu,sai wandon shima daya saukar mata har qasa,ta kama gashinta ta hade da pink ribbom sannan ta shafe jikinta da lallausan turarenta. Wani kyau tayi sosai,kayan sun karbeta kamar bana barci ba,idan ka ganta a lokacin zata dauka duka duka shekarunta sha takwas ne zuwa sha tara. Remote din ac ta dauka ta rage qarfinta,ta ajjiye saman bedside table sannan ta dauki hijab dinta me hannu ta saka,ta zira slippers dinta ta fito daga dakin.

      Tana takawa qirjinta yana dukan uku uku,addu’o’i fal bakinta,daga jiya zuwa yau ta wani mugun damuwa da aikin,damuwar da ita kanta takanji mamaki,batasan dalili ba,tafi danganta hakan da abubuwa biyu,neman mafaka da kuma tausayin yarinyar da ya sauka tun daga saman zuciyarta har ciki tun jiya.

      Da sallama ta shiga parlor din abba,ya amsa mata yana dauke dubansa daga kan zain dake zaune a gabansa ya mayar kanta,ta qaraso cikin nutsuwa tana zama a gefansu. Abban ta fara gaidawa sannan ya zain,sai ta karbi maama dake qoqarin serving nasu abinci ta fara zuba musu,data kammala sai ta koma gefe ta lafe kawai,hankalinta yana rabuwa gida biyu, rabi a hirarsu,rabi kuma tana tauna yadda maganar zata fita a bakinta

“Yadai ummin abba?,akwai labari?” Dr mamman ya fada sanda ya gama tauna lomar abincin dake bakinsa,murmushi ta saki,tayi qas da kanta tana murza yatsunta

“Babu abba”

“Ban yarda ba,bari mu gama cin abincin tukunna” ba abun mamaki bane sam don ya fahimci damuwarta lokaci daya,shi din wani irin mutum ne daya samar da shaquwa da sabo sosai tsakaninsa da iyalinsa,akwai fahimtar juna da kuma sakin fuskar da bai haifar da raini ko rashin girmamawa ba a tsakaninsu ba.

      Ba jimawa zain yayi musu sallama ya wuce,falon ya zama daga ita sai abban,don maama ma ta wuce bedroom dinsa tana sanya turaren wuta,wanda hakan din dabi’arta ce,duk da ko yaushe gidan ma gaba daya cikin turare yake,amma muddin abban yana gab da kwanciya sai ta kunna burner ta saka wani turaren,wanda yawanci yana riqe dakin har zuwa safiya,a gurinta sãahar ta koyi wannan,yana qarawa bacci dadi da armashi sosai.

“Ummi na,ma yake faruwa?,kada kiji nauyina,ki gayamin” sake takurewa tayi kadan tana jin fargaba,ta saci kallon abban,abinda ya alamta masa da gaske akwai magana me muhimmanci da takeson gaya masa

“Ehmmm,ina jinki ummi na”

“Abba…..” Sai ta kasa ci gaba

“Ina jinki,fell free mana ummi”

“Abba don Allah wata alfarma nazo nema,wadda nake da tabbacin indai ka amince tafi dukkan wani aiki da zanyi kyau da samun lada me tarin yawa,abba…..inason ka saurareni,sannan kayimin alfarma”

“Ina jinki” ya fada yana tattara hankalinsa a kanta.

Page 59

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

    “na samu aiki abba…..amma ba irin aikin da kuke tunani zanyi ba,aiki ne na kula da mara lafiya”

“Kula da mara lafiya kuma?” Ya tambayeta cikin mamaki,kai ta jinjina

“Banda abinki ummi,ai ba sai kinyi da kanki ba,idan kikayi bayani,sai na biya a daukowa mara lafiyan me kula dashi har zuwa sanda Allah zai bashi lafiya” kai ta girgiza alamun a’ah

“Ba jinya bace ta kullum kullum da ake kwance ba,abba yarinya ce marainiya,wadda take fama da epilepsy,tana buqatar kulawa ta wasu watanni daga gurin tsayayyar nanny da zata iya kulawa da ita da kyau”

“Ikon Allah” kawai dr mamman ya fada,ya gyara zamansa yana kallon sãahar din,abinda ya bata damar dorawa

“Zanyi aikin nan abba idan lamuncemin,bawai don neman kudi ba,sabida babu abinda na rasa daga wajenku,zanyi ne kadai saboda kwadayin lada wajen Allah,wanda na tabbatar hatta ku zakuyi tarayya a cikinsa,don Allah abba ka lamuncemin,haka kawai na tsinci kaina cikin kwadayin wannan ladan” kai ya gyada,maganarta gaskiya ne,saidai abun ya masa banbarakwai,diyarsa da aikin nanny a wani gidan?.

“Duk maganarki haka take,to amma banda abun ummin abba,ko biya kikayi akayi kina da wannan ladar ai” zamanta ta gyara

“Abba suna da wadatar da zasu iya biyan kowanne mutum,amma kudi basa iya taba siyan nagarta da cancanta” kai ya jinjina cikin dogon nazari

“Abba bazan jima ba,tana samun lafiya shikenan” ta yanke masa tunaninsa ta hanyar fadin haka. Dole murmushi ya kubce masa saboda yadda tayi maganar cikin kwantar da murya tana langabe kai,da alama da gaske har cikin zuciyarta takeson tayi aikin.

“Shikenan,kiban address,zan sa fahad ya yimin bincike akan nagartar mutanen gidan,don bazan bawa wani cikin yayyenki bama”

“Kana iya tambayar anty farheen,ita ta fara bincikawa ma, neighbors na qawarta ne,kuma Alhmdlh basu da matsala,shi yasa aikin ya sake kwanta min a raina” fadin farheen din ya sake sanyawa hankalinsa ya dan kwanta

“Zan nemeki” ta miqe tayi masa sai da safe ta wuce sashensu.

      Washegari da safe taga sauyin fuska daga wajen maama,sai tasha jinin jikinta,abban yana fita kuwa ta kirata,sababi ta fara tare da gaya mata itakam bataga dalilin wannan aikin ba,sosai ta kwantar da kai tana kwatanta mata amma maama tayi biris. Wuni guda ana abu daya har dare,shima abban ya gaza shawo kanta,sai da tayi kiran afifa. Itama afifan qin zuwa tayi da farko,ko da tazo dinma sai ta hadasu duka ta fatattakesu,daga bisani afifan tabi bayan maama,batasan ya suka qarke ba,tadai shigo tana harararta

“Burinki ya cika new nanny” murmushi me kyau ya subucewa fuskarta,yadda tayi maganar ya tabbatar mata da ta shawo mata kan maama,saita rungumeta tana cewa

“Allah ya barmin bestie na” murmushi itama ta saka

“Ba wani dadin baki fa,bawai ance kije ki manta da mahmud ba” baya taja tana hade rai,afifa ta bita da kallo tana jan qwafa,itadai batasan sai yaushe sãahar zata dauka daga kan wannan aqidar ba,tana addu’ar Allah ya kawo mutumin da zai sauya wannan tsattsauran ra’ayin nata.

*****Cikin takun nan nasa me cike da tsantsar qasaita da kuma wani irin aji suke nufar sassan hajiya qarama. Sanye yake da yadin baby cashmere me tsada dan qasar indai,wanda aka tsarawa wani irin dinki shi ba dinkin suit ba hakanan ba style na Pakistan ba,sosai dinkin ya qara masa kyau da kwarjini,ya kuma fidda qirar jikinsa qwarai dake dauke da siffar qarfi,duk inda ya gifta sai ya bada ajiyar sassanyan qamshin turarensa me masifar tsada daya sanya qamshin baya bajewa da wuri. Hnunsa riqe da siririn hannun fadeelan suke takawa zuwa sassan momy qarama,daga kan fuskarta har idanunta shabe shabe suke da hawaye,wanda rabi na shagwaba ne,rabi kuma tana ji har cikin zuciyarta yadda zatayi kewar mahaifin nata. Qasa qasa yake magana da ita tamkar wata babba

“Calm down my angel,ipad dinki na wajen momy qarama,nayi alqawarin kiranki kullum through video calls,i will do my very best na dawo da wuri,new nanny dinki na nan zuwa” kafada ta maqale tana zirara da hawaye

“Nikam banason wata nanny kuma,kai zanbi” murmushi ya saki saman miskilar fuskarnan tasa,sai ya sanya hannuwansa ya dagata ya azata zuwa kafadarsa yana ci gaba da takawa hadi da lallashinta cikin hikima. Duk duniya ita daya yake iya tsaiwa ya lallasa haka,banda a kanta,baisan koda hanyar yadda ake rarrashi ba.

      Suna shiga falon momy qarama na fitowa daga kitchen,hannunta riqe da mug dake cike da tea

“Badai har ka fito ba?” Agogonsa ya duba yana amsata

“Am ready to go,banason na wuce haka kada nayi missing flight”

“Gaskiya ne” ta fada tana neman wajen zama,sai shima ya zauna saman daya daga cikin qawatattun kujerun dake falon

“Na sanya jibril yayi magana da mutanen can,za’a kawo food stuff,idan akwai abinda babu ki gaya musu kawai,zan saka elyas yayi transfer ta account dinki,naki ne keda fadeela,shikenan koda wani abu?” Qasaitaccen murmushi ta saki,a duniya idan akwai wadda ta shigo rayuwa a sa’a to tana cikin sahun farko na jerin wadan nan matan,tana jin dadi,kanta kuma yana sake fasuwa a duk sanda toufeeq ke treating nata haka

“Eh to,batun nanny din fadeela ne,yau in sha Allah zatazo,wannan karon ina saka ran an samu wadda zata iya kula mana da fadeelan in sha Allah,duk da naso ka ganta kafin ka wuce” miqewa tsaye yayi

“Ba damuwa,indai tayi miki fine,just ta kula da aikinta shine abun buqata,and then ta fadi nawa takeson salary dinta,every month ko qasa da haka,duk ba damuwa indai zata kula da qa’idoji da sharuda”

“Karka damu in sha Allah” tare suka sake fita da fadeelan,still tana maqale dashi. Kuka ta saka masa sosai security dinsa ya buda masa motar ya shiga,sai da yasa akayi kiean baaba ramatu,da wayau da dabara ta rabata da gurin tana kuka.

      Har suka fita a gidan yana jin sautin kukanta cikin kwanyarsa,ya lumshe manyan idanunsa da suka sauya launi saboda wani bacin rai daya sokeshi,sannan ya budesu sosai yana jin wani ciwo cikin ransa,sam wannan ba itace kalar rayuwar daya tsarama kansa da kuma ‘ya’yan da zaya haifa ba,wannan din wata bahaguwar rayuwa ce da qaddara ta tsago da ita cikin nasa shirin da tsarin ta kuma wargaza komai

“AMEESHA” sunan da bazai taba gogewa cikin tarihin rayuwarsa ba,koda ace ya fita daga zuciyarsa da dukkan wani abu daya danganceshi. Cikin hanzari ya watsar da tunanin,ta hanyar ciro wayarsa ya laluba wata number da yayi alqawarin kira ya kira din,ya fara amsa wayar cikin wani irin sanyi bayan ya maida bayansa yayi relaxing a jikin kujerar.

     Koda ya gama wayar shuru yayi yana juya wayar a hannunsa,kamar wanda take sabuwa ga idanunsa ranar ya fara saninta,yau din gaba daya duk wanda ya kalleshi yasan yanayin komai ne cikin sanyi,yanayin da sam bashi a halittarshi.

     Tsaiwar motocin ya janye hankalinsa,ya daga kan nasa yana duban driver dinsa

“What’s happening?”

“I don’t know sir,but…. lemme check” ya fada,sai driver din ya bude ya fita ya barshi shi da guard dinsa guda daya dake zaune a gaban motar.

      Ko minti uku baiyi ba ya dawo da gaggawa

“An samu matsala sir,harith ne ya bige wani tsoho……”

“Ya salam” ya furta da sauri,ba tare da ya bari ya kammala bayaninsa ya bude qofar motar da kanshi ya sanya qafafunsa ya fito wajen,cikin sakanni guard dinnasa dukka suka fito suka take bayansa.

     Har a sannan tsohon yana zaune a qasa yanata bala’i,harith din da wadanda suke mota daya suna tsaye a kansa. Tsawa daya ya daka musu cikin bacin rai dukkansu sukaja baya suna sunkuyar da kai,ya ratsa ya tsakaninsu ya isa gaban tsohon,ya duqa zai dagoshi suka matso da nufin karbarsa,ya daga musu hannu alamun dakatarwa,ya tsugunna gaban tsohon bayan ya tadashi sosai.

“Kayi haquri baaba,am very sorry,bada niyya bane na tabbatar,amma kayi mana afuwa gaba daya” dukka wani fushi da fada daga dattijon sai ya sauka,saidai idanunsa suna zube cikin na toufeeq din yana kallonsa,ya saki ajiyar zuciya

“Shikenan,ba komai”

“Ina fata baiji maka ciwo ba ko?” Ya sake fada yana kamashi ya miqar dashi ya tayar dashi tsaye yana kade masa jiki,cikin matuqar martaba da mutuntawa,duk da alamu da suka nuna babu wani sukunin rayuwa me yawa tattare da tsohon

“Ba komai yaro,banji ciwo na,buguwa ce kadan a hannu na”

“Dole a dubaka kada ya zame maka matsala baaba” cancel din mota daya yayi cikin jerin gwanon motocin,yace su miqashi asibiti a dubashi,sannan su kaishi ga iyalinsa, yayi kiran elyas da hannu,y qaraso cikin girmamawa,ya gaya masa abinda yake da buqatar a bawa tsohon

“Okay sir” ya fada a ladabce.

“Yaro!” Yaji muryar tsohon ta kirashi dai dai sanda yake shirin saka qafafunsa a motar,ya tsaya cak ya waiwaya yana dubansa

“Ban taba tsammanin mutum me arziqi har haka zai iya tsaiwa ya saurari talakan da bai mallaki komai kamata ba,na gode qwarai da karamcinka,a duk lokacin da kaji tasowar fushi daga zuciyarka,ka yawaita ambaton A’UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM, HASBUNALLAHU LA ILAHA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL ARSHIL AZEEM” Shuru toufeeq yayi yana kallonsa har ya shige motar harith ya rufe,ya zagaya ya tayar da motar

“Sir….. it’s getting late,we should leave” jikinsa a wani irin mace ya shiga motar yana maimaita kalmomin da dattijon ya gaya masa,daidai sanda jibril ya rufe qofar kira ya shigo wayarsa

“Maji” sunan daya bayyana kenan wanda furtasa ya hade masa da faduwar gaban da baisan dalilin saukarta ba.

      Tattaro dukka nutsuwarsa yayi sanda motar ke dagawa ta dauki hanya sosai,cikin muryar da ita daya duk duniya yakewa magana da ita,duk da baisan hakan yana faruwa ba yayi mata sallama,sannan ya gaidata,ta amsa masa da wani irin kulawa

“Ina fadeela tah?” Ta tambayeshi a sanyaye. Wani nauyi yaji ya saukar masa,ya shirya yana hanyar barin qasar,tun da bai shaida mata ba sai a yanzu?,a yanzun ma da itace tayi kiranshi?,yaya zataji idan ya gaya mata hakan?

“Ko baka gida nayi kira da layin da zan sameta?” Ta jefa masa tambayar. Sosai nauyi ya sake kamashi,ya sani tana da wancan layin na baaba ramatu,to amma takan tsallake kowa tayi kiransa koda lokuttan da take da yaqinin baya tare da fadeelan,tun da jimawa ya fahimci tana hakanne don taji tasa muryar da lafiyarsa,tunda har yanzu hannayenta sun gaza iya koyar daukar wayar suyi kira a nata lambobin da layin domin suji lafiyarta,koda wasa…..koda sau daya……koda da gwaji. Wani al’amarine da yake damun qwaryar zuciyarsa qwarai cike da wata irin damuwa,amma ya gaza ta kowacce fuska…..ya gaza kawo gyara koda qanqani ne…….sau tari yanajin naqasu,gazawa da kuma kasawa,hadi da wata cikakkiyar tayawa me wawakeken girma daga rayuwarsa,amma baisan ta yadda zai gyara ba…..ta ina?,kuma a yaushe?,rashin matallafine ko kuwa?,duka shima bai sani ba.

“Allah ya kiyaye,ya tsare, ubangiji ya bayar da dukka sa’a da kariyarsa,fatan alkhairi” ta fada a taqaice ta kuma gimtse wayar.

     Wani abune ya sauko ya daki zuciyarsa,take tayi wani irin rauni,yanajin wata irin kunyarta na mamayarsa, kunyar da dukka d’a na qwarai yakeji a lokacin da yayi wani abu na sabawa ga iyayensa,duk da a karan kansa yasha gayawa kansa shi din ba na gari bane……yanajin wani irin karyewa a tata muryar,kamar wadda kuka ke shirin subucewa,amma duk yadda yaso ya juya zuciyarsa ta bita don taji meye damuwarta ya kasa,sai ya soke hannayensa guri guda yana matsesu da wani irin qarfi,kamar yana shirin ballasu.

⚜️⚜️⚜️ Kebantacce falo ne wanda ke dauke da wasu qasaitattun kujeru da suka zama cikamakin cikar adon falon,bashi da wani girma,amma yana da tsari me matuqar kyau tare da jan hankalin me kallo.

      Saman daya daga cikin kujerun falon sãahar ce zaune,cikin kamilalliyar shigarta ta jilbab,wanda yake hade da doguwar rigarsa me dogon hannu,gefe da gefe na dan qaramin hijabin madin rigar a tsage yake,an masa wani irin ado daga bakin tsagar,farar kyakkyawar fuskarta ta fita sosai ta tsakiyar fuskar hijabin da wani irin kwantaccen kyau me daukan hankali.

     Tun farko shigowarta gidan take nazarinsa daya bayan daya,ta kowacce fuska gidan ya amsa sunansa,ya kuma sake bayyana mata tarin dukiya tare da arziqin da masu gidan suka mallaka. Ta taso cikin gata soyayya kulawa tsakiyar nasu arziqin da dukiyar,tun daga kan mahaifinta zuwa yayyenta,hakanan dangi na mahaifi da mahaifiya,amma a yau daya,cikin mintunan da basu gaza goma ba kanta yana shirin kwancewa ta zama ‘yar qauye cikin gidan.

     Ba iya wannan ba,ta lura akwai tarin doka da bin tsari daga dukkan ma’aikatan gidan,kula gami da takatsantsan da tsoron kaucewa qa’ida,tun daga mai gadi,zuwa wadda ta rakota qofar sassan hajiyar gidan,kawo wadda ta kawota wannan falon da take zaune a yanzun tana jiran isowar matar,don ta ganta ta kuma karbeta gami da sake mata bayanin aikinta cikin gidan.

     Wayarta na hannunta a lokacin tana shaidawa afifa ta iso,afifan da tace sam ita ba zata iya rakota ta ganta a bigiren ‘yar aiki ba,saidai duk da haka batayi fushi ba,tana maqale a online tana bibiyar dukka motsin bestie din tata.

      Qarar takalmin da ya fara ratso falon yaja hankalinta,saita kashe data dinta,ta kuma ajjiye wayar tsakanin qafafunta,ta daga kai tana aje dubanta daga guraben da sautin tafiyar yake fitowa.

      Guri guda idanunsu suka hadu nata dana hajiya qaramar. Daidaita kallonta ya sakeyi kan fuskar sãahar duk da bata kai ga qarasowa gurin ba,wani abu yana sauka a zuciyarta,tanason ta karanceta irin karatun kallon farko,tanata qoqarin daidaita zuciyarta da taji kamar ta tsaya guri daya,ta gaza wanzar mata da kowanne feeling akan sãahar din,ba kamar yadda takanji ba akan sauran dukka nannys din fadeela na baya da sukabar gidan.

Page 60

*H U G U M A*

*_TABARMAR ƘASHI_*💔

Page 60

     Cikin takunta na qasaita da nuna isa ta qaraso,ta dauke filon dake saman kujerar dake fuskantar sãahar din ta zauna,tana maida filon saman cinyarta,bayan ta dora qafarta daya saman daya

“Sãahar ko?” Hajiya qaraman ta jefeta da tambayar sunanta kai tsaye,kai ta gyada mata cikin tabbatarwa gami da furta

“Eh nice,barka da yamma”

“Barka kadai” ta amsa mata tana qare mata kallo a fakaice,zuciyarta cike fal da mamaki irin sassanyan kyan da yarinyar ke dashi,babu alama ko digo dake nuna wahala ko buqata daga jikinta,asalima ko ita din sãahar din fatarta tafi tata nuna jin dadi da hutu,to amma ta wani bangaren tasan zata samu nutsuwa,zata samu sauqi itama,ilimi zallah ya nuna kansa tattare da sãahar din.

     Gyara zamanta tayi tana sauke qafafun nata,har yanzu idanunta akan fuskar sãahar din,kyanta yana sake bata mamaki

“Nasan mrs sadeeqa ta gaya miki komai,so amma koda zata gaya mikin ba komai zata iyayi miki bayani ba kamar yadda ni zanyi miki…..da farko kina iya kirana da hajiya ko hajiya qarama ko mommy qarama,kusan nice shugabar gidan nan,kowa da kika gani ya kwana ya tashi cikin gidan nan qarqashin ikona yake,hatta dashi me gidan kansa da abinda ya mallaka ya kuma haifa……aikinki guda daya ne tal cikin gidan nan,kula da jikata tamkar ke kika haifeta,munason ta samu kulawa fiye da yadda zaki bawa kanki kulawa,saboda yanayin ciwonta,bamason kiyi nesa da ita,saidai idan tayi bacci ne, kuma koda kin koma naki dakin zakici gaba da dubata ne gudun faruwar wani abun,wankanta da tsaftarta yana wuyanki,abinda zataci kuma wannan ba dolenki bane” sai Tayi shuru tana maida numfashi. A nutse sãahar ta daga kai tana dubanta tare da nazarin kalamanta,wanda suke cakude da sautin izza a cikinsu

“Fadeela…..ita daya muke da ita,itace sanyin idaniyarmu,farincikinta shine namu, sabawa daya daga cikin ayyukankin nan suna iya zama silar rasa aikinki” ci gaba kawai sãahar tayi da nazarin mommy qarama tana kuma kallonta

“Kin fahimta?” A nutse kuma a hankali ta gyada mata kai

“Da kyau,gidan nan yana da tsari,bawai zama bane kamar na sauran gidaje da kika sani,abu na gaba kowa aikinsa ya sanya a gaba,ba ruwan wani da shiga sabgar wani,ban yarda da zama tsakanin ma’aikata ana hira ba,kowa yayi abinda ya kawoshi ya wuce mazauninsa” shuru ta sakeyi tana kallon yadda sãahar ta kame,ta kuma bata hankali tare da manyan fararen idanunta tana kallonta

“Magana ta qarshe” ta furta tana zama serious sosai

“Nasan kinsan kalar ciwon da yake damun shelelenmu,right?” Kai ta jinjina tana ci gaba da sauraronta

“Yauwa,akwai magunguna da takesha,so gaskiya banason yawan qwayoyin da yake yawan bata,saboda haka duk lokacin da ya dace tasha magani zan shaida miki,kota waya,ko na tako har zuwa sashen da kaina,ban yarda ba ko sau daya ki dauki magani ki bata ba tare da sanina ba” wanann maganar ita ta zowa sãahar din a hagunce,sai ta gyara zamanta itama,ta kuma dora qafarta daya saman daya ba tare da tasan tayi hakan bama

“Amma why not ki yiwa likitan magana,idan zai yiwu da kansa zai fada,zai kuma rage mata,idan wasu kuma za’a yi exchanging dasu duka zai fadi”

“Look!” Hajiya qarama ta fada tana fidda idanunta waje

“Ina cewa ko minti biyar banyi ba da gaya miki rule’s na gidan nan,who are you da zaki shiga lamarin da bai shafeki ba daga zuwanki?,na gaya miki hakanne don na taimakeki,bijirewa hakan zai iya shiga list na dalilan rasa aikinki” mamaki ne ya kama sãahar,tadan yamutsa fuska kadan tana juya maganar a ranta,kaf cikin maganar bataga inda tayi wani lafazi da bai dace ba

“Ke ba kowa bace face nanny da zatayi aiki a biyata” zuciyarta da kwanyarta suka tuna mata matsayinta cikin gidan,sai ta zame qafafunta data dora saman na juna a hankali lokacin da taga hajiya qaraman na kallon yadda ta hade qafafun

“Am sorry,zan kiyaye in sha Allah”

“Kin samawa kanki lafiya” ta furta tana sake tsuke fuskarta,saida can qasan ranta tana cike da mamakin yarinyar,kwata kwata batayi kama da masu aiki ba,koda kuwa makaho ne ya shafa zaiji hakan,duk da sun nema well educated amma kuma wannan kamar ajinta ya d’ara wajen.

      Waya ta dauka tayi kira na qasa da second goma sha biyar,cikin minti daya tak matar ta iso,daya daga cikin masu aikin gidan,wanda basai ka tambayi hakan ba,saboda uniform da take sanye dashi,ta rusuna cikin girmamawa

“Sabuwar nanny din uktie,a kaita sassansu,ki damqata a hannun baaba ramatu”

“An gama ranki ya dade” ta fada cikin rusunawa,luggage din sãahar din ta dauka tayi gaba,don dukka nanny din data kasance ta fadeela ce a gidan,tana samun wani respect da kyautatawa darajar fadeelan,wannan haka tsarin gidan yake.

      Har takai qofa momy qarama na rakata da kallo,batasan me yasa yarinyar ke jan hankalinta har haka ba,yadda take takunta a nutse daya na bin daya kadai yana nuna mata kamar akwai wata extra qasaita a jinin yarinyar

“Sãahar” ta kirayi sunanta da dan kaushi kadan,dakatawa tayi sannan ta waiwayo tana dubanta

“Mrs sadeeqa nada matuqar kirki,tana kuma da darajar da zata baki dukkan wata kima da martabawa a gidan nan,ba tare da ko na miki screening ba na dauki aikin kula da ‘YAR SO na baki,ki kula da kyau,kada kuma ki gota iyaka” har yanzu kalaman matar basu daina bata mamaki ba,sai ta saki wan siririn murmushi ta jinjina kai kawai,sannan ta juya a nutsenta tana barin falon,tabi bayan ma’aikaciyar.

       Kamar ko yaushe katafaren ni’imtaccen falon nasu a tsaftace yake sannan killace,iskar na’urar sanyaya daki tana busawa ta kowacce kusurwa na falon tana cakuda da qamshin fresheners.

      Sau biyu me aikin tana sallama kafin qofar glass ta falo na biyu ta bude,baaba ramatu ta fito cikin kamalarta da carbi a hannu,da alama tana azkar din yammaci ne

“Qaraso mana,ke da baquwa ce?” Tayi tambayar idanunta akan sãahar dake tsaye a baya

“Nanny din fadeela ce hajiya tace a rakota” juyawa baaba ramatu tayi tana duban sãahar,sai kuma ta sakar mata murmushi

“Maraba,sannu da zuwa,Allah yasa tana jin hausarmu” tayi maganar cikin tantamar sãahar din tasan zo na kasheka da hausa. Murmushi ne ya subucewa sãahar din,karon farko tun shigowarta cikin gidan,yadda dattijuwar tayi magana cike da barkwanci yana burgeta

“Ina yini?” Ta fada a nutse don kore shakku daga zuciyar baaba ramatu,a mamakance riqe da baki t juyo ga sãahar

“Ma sha Allah,lafiya alhamdulillah,sannu da zuwa”

“Yauwa sannu” ta maidawa baaba ramatu

“Shigar mata da kayan nata ciki,dazu dazu aka kammala kintsa dakin muje ko ‘yata?” tayi maganar da sakakkiyar murya tana yi mata jagora ga tsararren hallway din da zai sadaka da dakunan baccinsu.

     Daya daga cikin qofofin dake kulle baaba ramatu ta tura ta shiga tana cewa sãahar

“Bismillah” sai tabi bayanta,bakinta dauke da addu’ar shiga sabon guri ko zama a baqon guri. Daki ne me yalwa wanda yake dauke da qawatattun kayan gado ‘yan asalin qasar turkey,komai na dakin kwantacciyar kalar yellow green ne me kyau da daukan hankali,kalolin dake qarawa idanu qarfin gani,dakin nada wani irin tsari me burgewa,bai cika girma ba,hakanan bai cika qanqanta ba.

“To ga dakinki nan,idan kina da buqatar wani abun kina iya magana a kawo miki,aikinki kawai ki kula da fadeela” baaba ramatu ta fada cikin murmushi. Murmushin itama tayi

“Bana buqatar komai,amma ina ita babyn?,inaga ita ya kamata na fara gani ko?” Qaramin murmushi ya sake sauka a fuskar baaba ramatu,haka kawai kallon farko taji sãahar tayi mata,fadeelan bata tana nanny irinta ba,yawancinsu tun daga hanyar shigowarsu gidan zuwa hanyar isowarsu dakin suke rudewa da kalle kalle da kuma santin tarin dukiyar dake jibge a gidan,hakanan duka cikinsu babu wadda ta taba tambayar a kaita gurin wadda tazo gidan aiki dominta,har sai baaba ramatun ta buqaci hakan

“Tana dakinta,tun dazun taqi fitowa rigima takeji,tunda babanta yayi tafiya dazun ya barta take fushi da kowa harda ni dana daukota daga waje,ko abinci taqi ta karba” baaba ramatu ta fadi tana dan dariya.

      Kai sãahar ta girgiza tana dan murmushi

“Ayyah,tana kewarsa ne tun yanzu,muje na gani ko zata yarda ta fito” gaba baaba ramatu tayi tana dan yi mata hirar fadeelan,yadda halayyarta da dabi’unta suke. Qofar dakin dake facing ta sãahar din baba ramatun ta tura ta bude, tsararren dakinta cikin kalolin white cream ya bayyana,wani irin daki da yafi kama da dakin hamshaqiyar mace me aure,dakin dake aka sanya masa dukkan wani abu na buqata jin dadi da kayan qawa,wanda hakan bai sanya ya cika tarkace da yawa ba,sai wani irin kyau da tsari na musamman daya bayar,ga tasirin tsafta sosai a tare dashi,ko ina qal qal yana fidda qamshi me dadin gaske.

“Fadeela” baaba ramatu ta ambaci sunanta sanda suke shiga dakin. Tana nade cikin duvet,ko motsi batayi ba

“Ki tashi ga sabuwar me kula dake tazo ganinki” kafadarta ta maqale,ta kuma bubbuga qafafunta

“Bana sonta” idanu baaba ramatu ta zaro waje tana kallon sãahar cikin rashin jin dadin kalaman fadeela,sãahar din da siririyar muryar fadeelan ta sanyata dariya tare da qarin dariyar zallar quruciyar data fuskanta tattare da ita

“Kul na qarajin kince bakiso wani,bakya sonta?”

“Eh ta koma,saboda nima daddy ya tafi….” Ta fadi tana yaye duvet din da sauri,sai kuma ta tsaya cak tana rarraba kallonta akan fuskar sãahar dake jifanta da murmushi. A hankali ta zame duvet din duka daga fuskar tata tana ci gaba da kallon sãahar.

     Waiwaya sãahar din tayi ta kallo baaba ramatu

“Baaba a kawo abincin nata”

“To shikenan” ta fadi tana juyawa ta fice daga dakin,cikin ranta tana jin cewa sãahar din zata bada fiye da abinda ake zata.

     Bata taka ba taci gaba da kallon fadeela tana murmushi,har sai da yarinyar ta miqe ta zauna sosai da kanta,sannan ta sauke hannuwanta ta taka zuwa bakin gadon ta zauna daga gefanta

“Kiyi haquri” sãahar ta fada tana kallonta,tana iya ganin sanda ta waiwayo da sauri tana kallonta,saita sake mata murmushi

“Ummmm”

“Ba abinda kika yimin fa amma kike cewa nayi haquri”

“A’ah,kince bakya sona,na dauka nayi miki wani abun” kai ta girgiza da sauri,saita shagwabe mata

“Abby ne ya tafi ya barni,bayan yace bazai sake tafiya ba dani ba” siraran hannuwan yarinyar ta kamo tana kallonsu,babu wata qiba sam,kamar bata cin wani abu da zai gina mata jiki,duk da daular da take ciki,saidai kyau da gogewar fata kawai

“Abbynki ba zaiyi qarya ba,lallai uzurin da sai yayi tafiyar ne kuma ba tare da ke ba ya kamashi,but na tabbatar bazai dade sosai ba” murmushi ya qwacewa fadeela

“Shima haka yacemin”

“So….you must trust him” kai fadeela ta jinjina tana murmushi

“Wait…..yanzun kinci abinci?” Kai ta girgiza fuskarta na sake narkewa,ido sãahar ta zaro

“Eehhhh,bakyason abby ya dawo yaga kin zama qatuwa?,baby fadeela ta zama ‘yar lukuta?” Dariya fadeelan ta saki,yadda sãahar din ke bubba hannayenta tana mata sign na qiba

“Inaso auntie,inaso”

“Good,chubby fadeela”

“Yes anty,not slimy,a chubby,a daina tsokanata a school”

“Aha,oya gate up” tayi furucin tana miqa mata hannunta,sai tayi hanzarin dora nata hannun,cikin kulawa sãahar ta riqeta sosai ta sauko da ita tana karantar yadda walwala da farinciki ya maye gurbin bacin rai data dawo ta sameta a ciki,wani irin nau’in tausayinta ya sake saukar mata,saita ajjiyeta saman lallausan carfet din dake gaban gadonta,itama ta zauna akai,ta fara diban abincin tana bata a baki.

“Kin iya feeding mutum like my abby” murmushi sãahar tayi

“Really?” Kai ta gyada mata

“Okay,nayi alqawarin zaifi na Abby din naki gaba kadan. Wani dariya me cike da nishadi fadeelan ta saki, sãahar ta tsaya kawai tana kallonta,an gaya mata tana da wuyar sabo sosai,nannys dinta suna jimawa kafin ta fara sakin jikin dasu,duk da ba wani dogon zango sukeyi ba a gidan,amma sai gashi ita lokaci guda ta sake sosai da ita.

uhmmm,ga sabuwar nanny a sheqar da batasan ta waye ba, za’a dore kuwa?,to lokaci shi zai nuna mana,asha hutun weekend lafiya,fatan alkhairi a gareku gaba daya,masu comments ina gani na gode sosai,gurin amsa comment dinne baya dannuwa,but am really appreciating

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

Page 61

Tsaf ta gyara gurin bayan ta gama bata abincin,duk da akwai wadda ke da alhakin hakan amma bata jira ba,ta shiga toilet dinta ta wanke hannunta,ta zari towel din dake ajiye musamman saboda goge hannu tana gogewa

baaba ramatu ta shigo.

Tayi mamakin yawan abincin da taga taci

“Ke ai baki iya bayarwa ba,new nanny ta fiki iyawa” baki ta kama tana dariya “‘yeee,zakici qaniyarki,yau nice ban iya bada abinci ba?,tun kina koyar yadda akecin abincin to ni nake baki don gidanku” dariya ta saki tana buga tsalle a gadon,abinda yasa sãahar murmushi kenan tana dan binta da kallo,abinda ta karanta,yarinyar nada sauqin kai,sanann irin mutanen nan ne masu son abinda zai nishadantar dasu,a yadda ta karanta gasa da minti arba’in a tarayyarsu,tana bugatar kulawa da zata dace da hankalinta.

A dakin ta barsu,ta dauki excuse don ta kintsa kanta da dakinta. Tana shiga ta zare mayafin jikinta ta ajjiye saman gado tana furzar da iska daga bakinta,yarinyar ta shiga ranta lokaci guda fiye da yadda tayi zaton zata kasance,wani abu takeji game da ita a ranta,tana jin kamar daga jininta ta fito.

Sai data gama shirya kayanta a wardrobe tsaf ta fidda komai ta ajjiyeshi a muhallinsa,bath stuff dinta ta kaisu bandaki,sannan ta zare kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka. Koda ta fito cikin wata doguwar riga ta lallausar auduga ta shirya,ta

gabatar da sallah,zuwa lokacin dakin ya fara

kama qamshin turarukanta masu sanyin

qamshi.

Hijabinta ta zare ta tsaya bakin mudubi

tana taje gashinta,ta gama tana hadeshi akayi

knocking,ta qarasa a nutse ya yafa qaramin

hijab ta bude gofar.

Me dafa abincin sashence,itama sanye da

uniform dinta,saidai su nasu akwai banbancin

color dana sashen hajiya qarama dana sauran

ma’aikatan dake gidan,nasu din fari ne qal da

ratsin bagi

“Its time for dinner maa” ta fada cikin

rusunawa

“Alright,thank you” ta fada cikin sauqin kanta da ba kasafai yake bayyana tattare da ita ba.

Ciki ta koma ta fidda slippers din da aka bata cikin wata jaka,wanda qa’ida ne na dukka ma’aikacin da zai fara aiki cikin gidan,ta sanya a qafafunta,saita kashe wayarta ta jona a charge da nufin sanda zata dawo ya cika,sai tayi kiran dukkan wanda ya kamata,don batason suyi kiranta bayan bata nan,ta maida qaramin hijabin daya sauka har kusan qugunta sannan ta fito a dakin.

Kai tsaye dakin fadeela ta koma,ta sameta sunata rigima da baaba ramatu akan kayan da zata sanya, kowa da yake gidan ya saba da wannan agenda din nasu,sosai take maidata kamar kakarta. Cikin hikima da dabara ta fidda mata wasu kayan,da lallashi ta sakata ta sanyasu,bayan tayi mata alqawarin bata zabin kayan baccin duk da takeson sakawa,sannan suka fito cin abincin ita da fadeela da baaba ramatu.

A gasa sãahar ta sauko musu dasu,sabanin yadda suka saka ci a saman table. Sãahar ta buda abincin tana gare masa kallo. Abinci ne yankunan Europe da Asia,saita ajiye murfin warmer din tana duban fuskokinsu. Ba wani karsashi a fuskar baaba ramatu,amma fadeelan har zumudin a zuba mata takeyi. Damar zubawa ta bawa baaba ramatu,ita kuma ta zubawa fadeela,sannan ta zauna ta bata da kanta kamar wancan lokacin,sai data tabbatar ta qoshi sannan ta zauna sosai,kadan ta tsakura ta ture,don ba jituwa tsakaninta da abinci, especially ma abincin dare, tafi qaunar coffee fiye da komai a rayuwarta.

Suna daki tana shirya fadeelan wadda taketa gogarin bata labarin abby dinta, magana daya biyu saita sakoshi, murmushi kawai sãahar ke binta dashi,tunda batasan komai a kai ba,kawai dai tana ji a zuciyarta cewa yarinyar ta rabauta da uba daya san darajar diyarshi,yake bata dukkan kulawa,ya kuma damu da damuwarta. Ruwa me dumi sosai tayi mata wankan dashi,ta shiryata cikin wasu kayan bacci masu taushi dai dai da shekarunta,ta sake mata gashinta yadda zatafi in dadin kwanciya.

Har wani lumshe idanu fadeela keyi,tana jin dadi sosai a jikinta

“Aunty nanny kin iya wanka wallahi” dole dariyar da saahar batayi niyya ba ta qwace mata,ta rige siraran hannuwan fadeelan

“‘Wankan ma akwai wanda yafi wani dadi?” Kai ta gyada

“Sosai,na abby da naki yafi dadi, amma shi abby sai ya daina yimin, waina girma,sai randa na fadi bani da lafiya shine yakemin” ta garasa maganar cikin karyewar murya dake nuna itama tasan halin ciwon da take ciki

“Aunty nanny,abby yace wai zan warke watarana hakane?” Qwalla ce ta cika idanuwan sãahar,saita jawo ta ta zaunar da ita saman cinyoyinta

“In sha Allah, kina addu’a?”

§ . 865 4C16

“‘ Ai ban iya ba” fuskarta ta dago ta shafa, komai nata siriri,saita saki murmushi

“Zan koya miki,zamu dinga sallah abby’s chubby” magaleta tayi tana dariya saboda sunan ya mata dadi. Dai dai lokacin aka turo gofar dakin fadeelan.

Dukkansu suka daga kai suna duban me shigowar,mommy qarama ce,cikin wasu kayan bacci da suka zubu,tayi rolling da wani qaramin mayafi kalar kayan,ikinta sai fidda qasaitaccen qamshi yakeyi. Miqewa fadeela tayi ta isa gurinta,saita miga hannu ta ruqota suka qaraso cikin dakin

“Mummy amma abby bazai kori wannan nanny din ba ko?,ita ina sonta sosai” ta fadi tana dora kanta akan cinyar hajiya garama. Hannu ta dora saman kanta tana shafawa,idanunta akan fuskar säahar

Нд

“‘Indai ta kiyaye doka da qa’idoji,sannan ta riqe alkinta ta kula dake yadda akace mata”

“Mommy tana kula dani sosai” tayi maganar da accent na quruciya a muryarta

“Okay,jiki wajen baaba ramatu kice ta baki kayan dana bata ajiya”, fellawa tayi da gudu ta fice, saita tattaro hankalinta kan säahar.

Idanu tadan kafeta dashi,wasu lokutan takanji shakka da kokwanto akan yarinyar,tana da wani irin kwarjini da bata ganinsa saman fuskar kaf ma’ikatan gidan sai ita,sannan daga shigowarta zuwa yanzu ta fahimci kwata kwata bata rawar jikin da dukka maaikacin daya shigo gidan yakeyi,kamar zai kwanta a hanyarta tabi ta kansa,dazu data kira mrs sadeega ta gaya mata haka yanayin ta mrs sadeeqa ta gaya mata haka yanayinta yake,bata da son yawa surutu da kuma hayaniya,MISKILA CE.

Ад

miskilar data fadi shi yafi qara kwanta mata,saboda tasan muddin tana da wanna dabi’ar ba zata saba da kowa ba,ba kuma zata zauna tayi hira da kowa ba akan abinda ya shafi gidan ba,aikinta kawai zata yita yi babu waiwaye ba duban kowa.

Wata jaka ta ajjiye mata tana Kallonta

“Ya lafiyar fadeelan?”

“Alhamdulillah” ta amsa mata a taqaice tana kwashe cosmetics din yarinyar data bazasu a gasa

“Madallah,wadannan…

…sune magungunan

ta,zaki dinga bata da safe da rana bayan ta dawo daga school sai da dare idan zata kwanta,kamar yanzun kenan,ba’a son fashi ko daga qafa,ki kula da kyau,ba kowa ake nunawa maganinsu ba,idan ya qare ni kadai zaki gayawa,zan sake kawo wasu,a ciki akwai tablet dinta,u are educated a yadda aka bani information dinki,so koda baki taba amfani da ita ba zaki iya hada mata ita,na sanya an dora komai daya dace a kanta,so amfani kawai zata fara yi da ita” kai ta gyada kawai

“Ki kular mata da tab,na tabbata bakisan darajarta ba,abace me tsada daga kamfani me daraja ta daya a duniya” sam sãahar din batasan murmushi ya subuce mata ba sai da taga hajiya qaraman na kallonta sosal,saita buge da gyada kai

“In sha Allah ” ta fada hankali kwance,cikin ranta tana mamaki,haka ‘yan aiki sukeji?,haka ake dizgasu? ta godewa Allah data rayu a gidansu taga yadda ake karrama masu aiki,ta godewa Allah da bata taba sha’awar dauko me aiki a ravuwarta ta baya ba,ashe suma suna jin babu dadi idan aka fadi wani kalma na qasqanci a kansu,suma mutanene kamar kowa,a yanzun abinda yasa itan bataji wannan ciwon ba,saboda tasan daga inda ta fito, tablet zata iya cewa dai dai take da ‘yartsanar wasanta,batasan nawa ta lalata ba tun kafin tayi hankali,ta yayunta da maaminta kafin ta mallaki nata kala kala.

“Muddin wani abu ya sameta zan cirene cikin albashinki” wata dariyar taso taso mata amma saita danne ta sake gyada kai. Dauke idanunta hajiya qarama tayi daga kanta,tana mamakin yadda maganar bata dameta ba,ta fada ne don ta mata ciwo,amma bata alamun wannan a tare da ita ba.

“Nawa kika yanke salary dinki,monthly ko weekly?” Hajiyan ta fada bayan ta miqe tsaye

“Wannan ba matsala bane,aikin yafi salary din muhimmanci” da sauri ta waiwayo tana dubanta,maganar taba fusgar hankalinta,sai ta dawo da baya tana tsareta da ido

“Ban gane ba,meye alaqarki da yarinya da aikin yafi miki kudin muhimmanci?,ana aiki don kudi ne haka ne?” Kai ta gyada tana lumshe ido. Ta girgiza kanta a nutse

“Ba haka nake nufi ba,shi kula da yaro lada gareshi me tarin yawa,koda ba’a biyaka a nan duniya ba,ladanka na qiyama yana jiranka,abinda ubangiji zai maka sakayya dashi,yafi kudin da za’a baka” qogarin dai daita yanayinta hajiya qaraman tayi tana jinjina kai,sai ta juya ta fice kawai ba tare da tace mata komai ba.

Da kallo ta bita har ta fice,saita dauke dubanta daga kan hanyar tana qoqarin fidda abinda zuicyarta keson suranta mata,ta jawo ledar ta buda kayan da suke ciki. Tashi tayi ta yiwa tab din gurin ajiya me kyau,sannan ta dawo ta zazzage magungunan.

Zama tayi sosai tana binsu da kallo,mamaki yana dan kamata,wasu irin tablet da babu rubutu a jikin robobinsu bare kaga bayanin da kowanne magani ke zuwa dashi. Ta jujjuya mazuban dukka plain fararen mazubi ne, abun sai ya daure mata kai,ta dinga juyasu daga gaba zuwa baya har batasan adadi ba,kanta ya daure sosai,gefe guda na zuciyarta kuma ya cika wa wasi wasi da fargaba. Motsin shigowar fadeela ya sanyata ajiye bottle din,ta daga kai tana dubanta,hannunta riqe da wata babbar sweet,cikin sakalci da salo na shagwaba ta zauna gefanta

“Uncle dina ne ya kawomin,yace gobe shima zaibi abby na,munyi waya da abby ta wayarshi, yace a barmin tab dina a bude zai dinga kirana kullum ta google meet muyi video call” cikin dauriya ta saki murmushi

“In sha Allahu” ta fada tana tattare kayan magungunan,ta maidasu cikin ledar,ta sake kadema fadeela gadonta ta saisaita sanyin ac din dakin da kuma hasken,ta rakata toilet tayi brush suka dawo tare. Sai data tabbatar tay bacci sannan ta zauna gefanta tana kallon doguwar fuskarta,abubuwa da yawa data taras a gidan suna dawo mata kanta,tun daga shigowarta gidan kawo yanzu,haka kawai jikinta yake bata akwai wani qalubale,akwai wani abu tattare da rayuwar yarinyar,ina mahaifiyarta?,don daga baaba ramatu har hajiya qarama tasan sunyi girman da ba zasu haifi kamar fadeela ba,to amma tana da mahaifi,shi din me yasa bazai zauna kusa da yarinyarshi ba? ko don babban lalurar daka iya zamewa naqasu ga rayuwar mutum?. Da wannan tunanin ta tashi daga gurin ta fita a dakin bayan ta tofeta da addu’a ta shafeta da ita,ta rufe dakin ta shige nata ba tare da tabi takan magungunan da hajiya qarama ta bata ba,haka kawai ranta da jikinta taji basu aminta data dauka ta bawa yarinyar ba. Zuwa lokacin wutar dake bada haske a hallway din ta sauya launi,alamun dake nuna lokacin baccin yayi kenan.

Sai da tayi sallar shafa’i da wutiri sannan ta zare wayarta a charge,ta zauna sosal saman gadon ta shafe jikinta da addu’o’i sannan ta kunna wayarta tana duba time. Taso shigowa da wuri ta kira kowa amma lokaci ya qwace mata sanadiyyar shigowar hajiya qarama,yanzun kam dare yayi ba zata iya kiran kowa ba a cikinsu.

Wayar na gama daidaituwa saqon

mahmud ya shigo har guda uku a jere,yau kam dai ta duba,saqon fatan alkhairi ne tare da nuna zallar kewarta da zaiyi,afifa ta gaya masa ta samu aiki amma ba’a kano ba. Ko data gama karantawar batayi reply ba ta soma kiran afifa,bugu biyu ta daga

“Nanny bestie,me ya faru da wayarki tun dazun switched off?,ko gidan basa bari a daga waya ne?” Ta garashe maganar cikin shaqiyanci da zolaya

“Ban sani ba,mu hadu a WhatsApp” daga haka ta gintse kiran,ta sani ai tunda ta zabi wannan aikin ta shiga uku gurin afifa,qilan sai tayi kamar zata zautata da tsokanarta.

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

Page 62

Bata sake tsokanar tata ba bayan sun hau online,suka gaisa saidai ta tambayeta ya vanayin alkin

“There’s is something terrible a cikinsa” ta amsa mata har zucivarta tana in akwai wani abu

“‘Kaman yaya?” Afifa ta tambayeta cikin fargabar kada ta sake fadawa wata cutarwar kwatankwacin na baya. A nutse ta gaya mata komai,ba jimawa voicenote me yawa. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta gama saurara,dukka maganganun afifa akan hanya suke,kuma taji dadin yadda ta qwarara mata gwiwa

“But afifa how she can survive without medication?”

“Yes,her illness needs treatment,idan ba haka ba abun zaiyita worsening ne,so that zanyi prescribing miki wasu magunguna,su zata dinga sha zasu taimaka mata in sha Allah,but kafin sannan ki samo history na ciwon nata,yanayin yadda yake mata idan ya tashi da kuma asalinsa,ki ajiye wadancan,tunda babu sahihanci a cikinsu”. Sosai suka tattauna da afifan,sai taji dadin shawarwarin data bata game da yadda zata kula da fadeela din,shawarwarin da afifan ta bata saita tsinci kusakurai da yawa game da yadda ake kula da yarinyar.

Basu rabu ba sai can dare,don daya ma ta kusa,ta sauka ta daura alwala ta gabatar da sallar dare kamar yadda ta saba,ta miga bugatunta wa ubangiji idanunta cike fal da hawaye. Wannan din wani sirrin rayuwarta ne da babu wanda ya sani sai afifa. Data kammala fita tayi ta dubo fadeela,ta sake gyara mata kwanciya da rufa gaba daya sannan ta jawo gofar dakin ta fice,a ranta tana jin rashin kamatar barinta ta dinga kwana ita daya alhalin tana da irin wannan lalurar,anytime zata iya far mata.

*WASHEGAR I*

Komai na gidan ta fuskanci cikin tsarin yahudanci zata iya cewa yake tafiya,safiya a garesu tamkar dare ne,don ba da wuri suke tashi ba sam,fadeela ce kawai za’a yiwa abincin tafiya makaranta,a kuma shiryata ta wuce. Kowa rayuwarsa yakeyi,saidai idan an hadu a gaisa,kowa yayi aikinsa kuma ya kama gabansa,sai idan wani aikin ya sake hadaku.

Tun bayan data shirya fadeela driver ya dauketa saita shiga dakin yrinyar,da kanta ta yiwa dakin gyara,ta fidda duk wani sharp objects da zai iya cutar da ita idan ciwonta ya tashi,ta gyara komai ta sanyashi a muhallin da koda faduwa tazo mata ba zata cutu ba

Teddy’s manya tayi list cikin abubuwan da fadeelan ke bugata,tanason aje mata agurare mabanbanta ya zama ko ina dakin bai cika da wani abu me tsini ko tauri ba,tashin ciwon unexpected abu ne,tanason tayi abinda zai zame mata first aid koda ba wani a kusa da ita.

Tana tsaka da aikin me gyaran dakin ta shigo,sai kawai ta sallameta,da kanta ta shiga walking closet dinta,cike yake da kaya masu kyau da tsada na alfarma,saidai alamu sun nuna akwai kayan da ba’a sanya mata su,ko ba’a damu da saka mata su din bane oho ta gyarata fes ta sake jera komai. Bata fita a dakin ba sai garfe daya,sai sukayi clashing da baaba ramatu.

Baya ta jaye mata cikin girmamawa,fuskarta da fara’a tace

“Naji shurun yayi yawa nace bari na dubaki” murmushi tayi

“Ina ciki ina aikin gyaran dakin fadeela”

“”’ah,ina mabaruka?”

“Ni na sallameta,akwai gyaran da na yiwa dakin ne”

“To madalla,sannu da qoqari” baaba ramatu ta fada,har cikin ranta tana jin cewa yanzun fadeela ta samu nanny din da zaiyi wuya korarta,tun daga jiya zuwa yau taga tarin banbamce banbamcen da sauran masu kula da itan da tayi a baya.

Cikin sati guda kacal ta gama fahimtar

dukkan wasu tsare tsare na gidan,sannan

itama ta gama tsarawa kanta yadda zata rayu

da kowa. Cikin sati guda din nan kacal suny!

wani mugun sabo da fadeelan,yarinyar tana da

wani irin shiga rai da kuma masifaffen wayo

dake da alaqa da kaifi basirarta a makaranta.

Sannu sannu dukkan wasu ayyuka da sauran

ma’aikatan gidan kewa yarinyar,kama daga

abincinta,gyara dakinta,hada kayan wankinta

a bayar zuwa laundry room duka ta qiya

kowa yayi mata,dukka sun koma wuyan

sãahar. Wani irin girma take bata,tana jinta a

ranta ta zarta mata kowa a gidan,kafin tayi

wata guda sai ya zamana sun koma tamkar

ya da uwa,hatta da dakinta idan zata koma

sai bayan yarinyar tayi bacci,data farka ta

sauko a gadonta komai asuba zataji ana

mata knocking,indai taji wannan bugun tasan

fadeela ce,tare xasu qarasa kwanan,ayi shirin

makaranta. Ayyukan makaranta kuwa shima

ya koma aikin sāaharlesson dinta da ake mata

still dai shima taqi malamin,a nan ne fadeela

ta lura kamar akwai rauni wajen karatun

addininta,da kanta ta zauna ta tsara yadda

zata fara koya mata,duk da ason ranta yarinyar

ta shiga islamiyya,to amma batasan yadda

zata tunkari masu gidan da maganar ba.

A nata bangaren ayyukan fadeela gaba daya nishadi suka sanyata,sun debe mata kewar yara sosai,sun kuma nesantata da dukkan wani namiji kamar yadda take da muradi,tana jinta kamar a killace,babu idanun kowa a kanta,ta samu cikakkiyar nutsuwa da gamsuwa cikin gidan,hajiya qarama da takejin kamar zata zame mata matsala ko akwai wani illa tare da ita,saita fuskanci ba wani damuwa tayi da sassan ba,saita share kwanaki ma bata shigo ba,sai idan fadeela taje mata. To amma,shin da gaske fadeelan jikarta ce?,idan jikarta ce ta yaya mu’amala irin wannan zata wanzu tsakanin jika da kaaka?,tanason sanin labarinsu,tana son sanin ainihin wacece hajiya garama a wajen fadeela,to amma ita din bata cikin sahun mutanen da suke shiga lamuran da sukayi yaqinin basu shafi rayuwarsu ba.

*****K’arfe biyar da wasu yan mintuna na yammacin ranar ne,dai dai sanda madaidaiciyar motar me kyau ke shigowa cikin gidan,wanda da shigowarta da isowar masu aikin gidan duka duka bazaiyi minti biyu ba,cikin gaggawa kowanne ya iso,saboda sanin mamallakiyar motar,kowa yana gudun tsira da mutuncinsa.

Bude murfin motar tayi,sannan ta qwalawa daya daga cikinsu kira,matsowa tayi da gaggawa,bakinta dake tauna chewing gum ta motsa

“Daukarmin hand bag dita”

“Tom” ta fada tana buda daya side din da jakar take ta dauka ta riqe

“Kai jama’a,mutum ba uban kowa ba sai shegen ji da kai da izzar banza” tayi gorafi gasa qasa,saidai ya fidda sautin gunaguni

“Me kike cewa?” Labiba ta tambaya taba juyowa,murmushi tadan saki a rikice

“Bab…..babu komai,cewa nayi maraba da dawowa” bata sake cewa komai ba ta fita a motartabar musu aikin kashewa da rufeta hadi da rigo mata key din. Cikin jin kai take takawa,sanye da wani skinny jeans da yabi jikinta sosai ya lafe, kamar a jikin nata aka dinkashi,manyan mazaunanta da suke da wani irin dan banzan tsini sun fita sosai,saidai kuma shafaffen qirjinta dake boye a t shirt din jikinta ya kawo cikas waien cikar adon da akesonyi da bayyana abinda akeson a bayyana din. Kitson attache ne a kanta daya zuba har gadon baya,ya bullo da qasan gantalelallen mayafin data yane kanta dashi wanda iyakarsa wuyanta.

Har ta doshi sassan hajiya qarama suka shaida mata ta fita, amma ba nisa tayi ba,saita sauya akalarta ta wuce sassan fadeela,tanason ta saba da yarinyar,to amma matsalar ita batasan yadda zata shawo kanta su shaqu ba.

Dai dai lokacin da sãahar ke zaune a madaidaicin falonsu na biyu,suna zaune qasan carfet ita da fadeelan, ita tana cin abinci sãahar din na monitoring dinta,a daya bangaren tana duba homeworks din da aka basu ranar a makaranta.

Sanye take da brown din chiffon gown budaddiya sosai,sai kanta data yafawa vail na plain chiffon din shima brown da bai garasa na jikin rigar haske ba, kyakkyawar fuskarta tayi fresh,tes take fatarta na nan da glowing dinta,babu digon ko tabo ballantana qurji,pink lips dinta sai shegin lips balm sukeyi,zara zara yatsunta take sanyawa tana buda book din page by page tana ganin performance din fadeelan a homeworks dinta na baya.

Sau biyu tana buda baki da niyyar yin magana tana dora mata yatsa akan lips tace

“Shshshsh” tasan tanason yin Santi ne akan abincin da takeci, wanda säahar dince yau ta dafa. A karo na uku data hanata saita langabar da kai

“Please aunty ki barni nace wani abu mana” yadda tayi maganar yayi masifar baiwa sãahar dariya,saita rufe littafin tana murmushi idanunta akan fadeela

“Say it fadee”

“Wallahi anty ban tabacin abinci me dadin wannan ba,kamar daga aljanna aka kawosa” ba shiri dariya sosai ta kubcewa saahar,saita miga hannu ta dauki pillow ta saka mata daga gefanta

“‘Bari na tareki kada santi yasa ki fadi” dariya itama ta saki sukaci gaba da yi tare

“Please aunty nanny,zaki ci gaba da dafamin abinci?,harda wanda zanje school dashi don

Allah,nasan abincina sai yafi na kowa dadi” idanu ta lumshe tana gyada kai,a yadda takejin fadeela kamar jininta babu hidimar da bazata ivayi mata ba

“Alright,amma idan satin nan ya wuce baki gama haddace suratul a’alah ba,to zan daina,kin yarda?”

“‘Na yarda aunty,nayi algawarin jibi zan gama” ido ta ya fidda tana dubanta da mamaki

“Really?” Kai ta jijiga mata alamun da gaske take.

“Hi fadeela” muryar labiba dake tsaye a kansu ta ratsa kunnuwansu,dukkaninsu babu wanda yasan da shigowarta bare wanzuwarta a gurin.

Daga kansu sukayi kusan lokaci guda suka

dubeta,dai dai lokacin idanunsu suka gauraya

da juna ita da sãahar.

Dan ja baya kadan tayi cikin yanayin dake

nuna qaramar razana

“Ya salam” ta furta can gasan ranta,tana

hadiye wani abu me tauri a maqoshinta,a

ina aka samo wannan cikin gidan?” Ta yiwa

kanta tambayar da batasan amsarta ba,zataso

ta jefa tambayar ga baquwar fuskar,amma

idanunta zuwa fuskarta suna fidda wani irin

kwarini.

Sãahar ce ta fara janye idanun nata daga

kanta,ranta yana dan baci da yadda ta riskesu

gatsau kai tsaye tayi musu kuma tsaye a

ka,saita maida idanunta ga duba littafin

hannun nata ba tare data sake dagowa ta

dubeta ba,saidai a jikinta tana jin kamar tasan

fuskar,kamar ta taba ganinta a wani waje.

Tana jinta ta isa gaban fadeela ta zauna

tana ta janta da surutu,lokaci lokaci idanunta

suna satar kallon sãahar,wadda bata sake

duban sashenta ba,koda ace suna da dabi ar

yahudawa,a qalla tunda musulmi ne su tay!

musu sallama sanda ta riskesu

“Na gama anty” fadeela ta fada bayan ta ajiye

gorar ruwan hannunta

“Good bari na dauko miki hijab,qur ani zamu

fara yi” saita kife littafin ta mige zuwa dakin

fadeelan. Kallo labiba ta bita dashi hankalinta yana tashi, ko ita da take mace ta tabbatar

ta kuma yaqini hakanan ta sallama wannan

din ta cika mace wani abu me cakude da

kishi da tashin hankalin wanzuwarta a gidan

yazo yayi mata tsaye,sai ta maida dubanta ga

fadeela dake qoqarin dauke plate din da taga gama cin abincin tana tattare inda ta bata da

tissue,abinda bata taba gani yarinyar tayi ba “Wacece wannan uktie?” Duban labiban kawai

tayi,da yake itama miskilar kanta ce,kafin tace

komai baaba ramatu ta shigo falon,hannunta

dauke da humidifier da tasan sãahar na

yawan ajjiyeta a gurin saboda tsananin son

qamshinta,waccan ta lalace ta sauyo musu

wata,tana respecting duk wasu buqatu na

sãahar din,don zata iya cewa tsahon zamanta

a gidan,bata taba jin dadin zama da wani

mutum a gidan ba kamarta

“‘Barka da dawowa” baaba ramatu ta fadi tana

duban labiba

“Yaushe akayi baquwa a gidan nan?” Ta jefa mata tambayar ba tare data amsa marabar ta

ba

“Ba baquwa bace,kawai ita ke kula da fadeela

yanzun” a take fuskar labiban ta washe,ta saki

garamar dariya.

“A’ah ramatu,kice nanny ce kawai,basai kin

wahalar da harshenki ba” tayi furucin dukka

a kunnen säahar data qaraso gurin hannunta

dauke da gogaggen hijabin fadeela,cikin

wadanda ta dinko mata da kudinta,saboda

tazo ta risketa bata da jiba ko daya,sai wani

fingilalle V shape na uniform dinta.

Hada idanu sukayi da labiban,sai sauran

maganar ta magale mata a magoshi,ta mige

daga zaman da tayi tana fadin

“Zan jira mommy a sassanta, fadeela enjoy

your new nanny” saita dan daafa kan

fadeelan ta soma takawa tana barin falon.

Ran baaba ramatu ba dadi ta ajjiye

humidifier din,tasan halin kowa a gidan,don

kusan kowa a gabanta yayi girmansa, ta samu

guri ta zauna lokacin da sãahar ke sanyawa

fadeela hijab din nata,daga can qasan

zuciyarta tana fassara kallon da kalaman labiba. Ta fahimci ma’anarsu fes,to amma abinda ya bata mamaki daga haduwar farko ko maganar farko babu a tsakaninsu me ya haifar da wannan matsanancin kishin cikin qwayar idanunta?

“Wannan itace labiba, kuma za’a iya cewa ita din ganwa ce ga mahaifin fadeela,wato

‘yar matar babansa ce,tana da wasu halaye marasa kyau wani lokacin,sai kinyi haquri da ita” a nutse ta daga kai ta kalli baaba ramatu,saita saki kyakkyawar murmushin nan nata da ba kasafai take yinsa ba,ta taka tana debo litattafansu

“Karki damu baaba ramatu,haquri da ita bai zama dole ba,tunda bani da case da ita” jinjina kai baaba ramatu tayi,tasan sarai tana da kawaici da kuma sanyin hali,hakanan bata da kwaramniya ko hayaniya,amma labiban fa?,tayi imanin koda bata shiga gonarta ba ita zata shiga tata,saidai fatan Allah ya kiyaye.

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_**

Page 63

Sasai wuyanta ke cike da wani qatoton abu,sashen hajiya qaraman taso wucewa amma saita kasa,ta samu kujera ta zauna a nan farfajiyar gidan tana jan numfashi tana fesarwa,ba abinda ke gilma mata cikin idanunta sai kyakkyawar surarta,kamewarta da uban kwarjin da zai hana ta takata yadda taso. Ta yaya zaman wannan cikin gidan zai yiwu?,kuma a matsayin me kula da halittar da toufeeq yafiso duk duniya fiye da komai da kowa?,ta yaya zata bari su dinga gwama numfashi tare dashi?,anya idanun hajiya garama ba rufewa yayi ba kuwa harta amshi wannan surar a mazaunin nanny?.

Qafa daya kan daya tana kadata makeken gate din gidan dake da rassa biyu daya daga cikin reshen(enter) wato shigowa ya bude,ta zubawa gun idanu tana fatan hajiya qarama dince ta dawo. Ita dince kuwa,bata iya haqurin jumurin tsaiwar motar bama ta miqe ta bi bayan motar har zuwa parking lot na gidan,dai dai sanda motar ke tsaiwa,tasa hannu ya bude seat din baya wanda tasan a nan hajiya qarama din ke zama driver yana tuqata,ta shiga ta zauna idanunta akan hajiyan dake amsa waya da dukka hankalinta

“Nooo. karki damu MY BABY,duka duka watannin guda nawa ne? ki kwantar da hankalinki ki kammala karatunki,na miki algawarin duk lokacin da nazo bikin yayeku dake din zan taho,na miki wannan algawarin” girjin labiba ne ya buga,a duk sanda taji tana waya da BABY din,sai ta samu fargaba irin wannan,sunan da ita kanta me sunan ba qaramin barazana bane ga kunnuwanta da rayuwarta

“Alright…..kada ki damu da wannan,ki maida hankali kiyi karatu sosai ki fita da result din da yafi qarfin raini… okay,bye,i love you” saita katse wayar murmushi me kama da dariya kwance akan fuskarta,soyayyarta tana sake ratsata,burinta a kanta yana sake hauhawa,lokaci kawai take jira,kuma mutuwa ce kadai zata shiga tsakaninta da cikar wannan burin nata

“‘Ya akayi labiba?” Ta waiwaya gareta bayan ta saka wayar a jakarta, numfashi ta ja ta hadiye yawu

“Mommy, nazo na samu andauki wata me kama da aljanu wai a mazaunin nanny”

“Shine me?” Tavi tambayar hankalinta kwance

HA

“Mummy bakiga irin kyau da halittarta bane?,bakya tsoron ta rudi yaa toufeeq da kyan nata?” Qaramar dariya hajiya qarama ta saki

“Toufeeq..

. toufeeq dai? ke bakisan halinsa

bane halan har yanzu?,kin taba ganin idanunsa bisa fuskar wata mace da zummar so ko sha’awa?,bare har yaji tayi masa? inama yake toufeeg din?” Shuru labiba tayi tana juya maganar mommy din. Tabbas ko ita din iya tsahon rayuwarta zata iya irga sau nawa ya daga kai ya kalleta,kallon da mafi yawan lokuta yana mata shine don hukuntata idan tavi wani abu daya saba da nasa ra’ayin,sai taji wannan case din kamar ya mutu ne

“Mommy haseena zata dawo ne?” Sai data buda murfin motar ta saka qafarta waje sannan ta amsa mata Ад

“Ba yanzu ba” ta fara qoqarin fita sai kuma ta dakata,shuru tayi kamar me nazarin wani abu,sanann ta fara magana da labiban a hankali

“Toufeeq allura ce cikin ruwa,me rabo ka dauka,so ki dinga sassautawa kanki wasu abubuwan kinji daughter” daga hakan ta saka gafafunta waje ta fita a motar tabar labiba a ciki.

Shuru tayi gumi na dan tsatstsafowa daga goshinta,mommy din tayi magana cikin kwantar da murya da kuma nuna kulawa,to amma kalaman dake qunshe cikin maganarta….sunyi mata wani iri,me rabo ka dauka?,allurar cikin ruwa?,duka me hakan yake nufi?. Shuru ta sakeyi tanason lallai saita fahimtar da kanta,amma ta gaza gano komai,tunda tace dawowar HASEENA ba yanzu ba,ta toshe duk wani kafa ta tunaninta,dole ta jawo qafafunta ta fita a motar don ta bawa driver din damar rufe motar,saidai a ranta tana jin ya kamata ta kira

hajiyarta ta gaya mata ko ita din zata gano abinda ta gaza ganowa.

Da daren ranar suna saman gadon fadeelan,bayan ta tabbatar ta bata magungunan da afifa ta rubuta ita kuma ta fita da kanta ta siyo. Ta shiryata cikin kayan bacci,kan fadeela na kwance saman cinyarta,gashinta me tsaho da santsi irin na saahar din ya baje saman gafafun sãahar din,ta nace wai sai sãahar din tayi mata kitso.

Itama ba iya kitson tayi ba sai kalba,don haka kalbar taketa qoqarin kitsawa amma tana warewa, kunnuwanta suna kan fadeelan daketa complain din rashin kiranta da Abby din nata baiyi ba. Kusan duk wayar da zaiyi matan tana gurin baaba ramatu,a can suke wayarsu su gama

“Abby yayi busy ne tabbas,amma ayi masa uzuri kinji,ki daina complain da yawa fadee,he cares about you fadee,you have to appreciate his efforts kinji” ta fadi ne don kawai kwantar mata da hankali tare da nuna mata muhimmanci haquri da kau da kai. Kai ta gyada a sanyaye,bata sake cewa komai ba.

Kamar jira kuwa akeyi tayi shurun sai tab din ta fara gara, zamewa tayi da gudu ta dira a gadon ta nufeta,ta iya karatu sosai,don haka ta karanta sunan me kiran

“Aunty,budemin google meet dina,abby ne a nutse ta sauka a gadon,ta dauko mata headphone da fold up stand,ta fara bata headphone din ta saka a kunnenta,sannan ta ware fold up din ta dora mata tab din a ciki don taji dadin amsa wayar,ta koma daga bayan camera din ta saita mata Google meet din.

Cikin qawatacce kuma tsararren balcony din nasa yake a zaune,wanda aka rabashi sassa biyu lounge and eating area qawace yake da wasu irin stone tiles da kuma couch masu tsananin laushi hade da table din dake da kujerunsa guda hudu,sai swing bench daga can gefe guda daya dake mahadin furniture din. Da wasu irin fitilu aka yiwa gurin ado,hakanan aka wadatashi da potted plants a kowanne sago da kuma qasan gurin,tsirran dake iva garawa gurin kyau iska me dadi da kuma qamshin furannin dake magale dasu.

Pajamas ne a jikinsa,farare tas tas dasu,rigar me gajeran hannu ce qwarai,v shape neck dake iya baka damar hango lallausar gargasar dake kwance lambam a girjinsa,hakanan gajartar hannun rigar yasa kake iya ganin dantsensa dake da wasu irin muscles,daga can gasa zuwa tsintsiyar hannun kuma gargasa ce itama me santsi baga sidik.

Wandon jikinsa iyakarsa gwiwa,yayi crossing gafafunsa yana jiran kiran da ya yiwa halittar mafi soyuwa a gareshi ya shiga,hannun damansa coffee dinsa yake sipping kadan kadan. Duka duka bai cika awa guda da dawowa daga office ba,ya sake maida kansa busy qwarai da gaske da tunanin hakan shi zai zame masa abokin debe dukka wata damuwa da kewa.

Miskilin murmushi ne ya subuce a labbansa sanda innocent face din fadeela dake zaune tsakiyar gado da hargitsatsen gashinta ta bayyana

“Assalamualaikum abby” sallamar tata ta ratsashi qwarai,ta kuma dace sosai da muryarta

‘Waalaikumus salam,daddy’s angel ta girma da gaske,an iya sallama da kyau‚barakallahu fiik”

“Abby,aunty nanny ce ta koyamin” sai ya jinjina kai yana murmushi

“Tace min tafi lada akan ace hello”

“‘Da gaske ne” ya amsa mata yana gyara zamansa,ya buda baki zaice wani abu,saidai kafin yace komai din ta rigashi,ta barke da bashi labarin aunty nanny,abubuwan da take koyamata,abubuwan data hanata yi da wadanda ta gyara mata,karatunta da sauransu. Shuruuu kawai yayi yana bin bakinta da kallo tare da sauraren bayananta,yana tsintar abubuwa masu yawa game da labarin nanny din da take bashi,a hankali ya samu kansa da furta

“Alhamdulillah” a gasan zuciyarsa,tana sake gaya masa abubuwan da suke gudanarwa nutsuwa na sake saukar masa game da hannun da diyar tasa ta fada a wannan karon,abinda yake ta taraddadi kenan,sai ya gara sakewa sosai ya bata dukka hankalinsa yana sauraronta,cikin ransa yana jin mai yiwuwa Allah ne ya dubeshi ya share masa damuwarsa ya hada sanyin idaniyar tasa da nanny ta gari

“Kanason ka ganta? daddy na nuna maka ita?” Tayi gasa gasa da muryarta harda dan sunkuyowa screen din wayar alamun quima,tana maganar kuma tana satar kallon säahar dake tsaye bakin mudubi tana

taje kanta tare da gogarin hadeshi cikin

ribbon,fadeelan ce ta watsa mata kan a dasu garin cewa lallai saita koyi kitso itama a kanta.

Yadda tavi maganar da sunkuya da yin qasa qasa da murya ya bashi dariya,ya daga hannu yana shirin dakatar da ita,amma

inaaa… bata tsaya jin ta bakinsa ta juyar da screen din zuwa sashen da sãahar din ke tsaye tana daure gashinta da ya zuba har bayanta.

“aunty na juyo miki da camera kizo ku gaisa da abby na…” Wani muguwar faduwa gaban sãahar din yayi,tamkar wadda aka dasa taci gaba da baiwa camera din baya ba tare data juyo ba,ba abinda take tunawa sai kayan jikinta,inda Allah ya taimaketa doguwar rigace sakakkiya a jikinta,amma duk da hakan tasan tudun mazaunanta da kuma gashinta dake sake a baya yana lilo bazai kasa ganuwa ba,lallai ta yarda quruciya na damun fadeela sosai, banda haka ba wanda zaiyi irin abinda tayi.

Da sauri ya janye idanunsa daga kallon abinda baiyi niyyar gani ba,ya dunqule hannunsa sosai yana fadin

“Angel,move the camera,basai mun gaisa ba” kasancewar akwai headphone a jiki ya sanya ita daya take jin abinda yake fada,saita kyabe fuska tana fadin

“Anty na dauke camera din,yace basai kun gaisa bama” ido ya zubawa fadeelan sosai yana kallonta,can qasan magoshinsa yana qogarin harhada abinda zai fada mata,saboda ta sanyashi kallon abinda bai shiryawa ganin ba,dole ya mata bayani cikin hikima yadda zata fahimta,don ya fahimci ita kanta matar batasan zata juyar mata da camera ba. Zama yayi sosai yana fuskantarta,ya maida fuskarsa serious da zummar mata bayani da kyau,kada wataran ta sakashi ganin abinda baiyi niyya ba

“Fadeela”

“Abby”

“Kina iina?”

“En daddy”

“Daga yau idan na kiraki,idan bance ki bawa wani waya ba kada ki sake yin hakan kinji?” Kai ta gyada a sanyaye

“Kome zaka yima mutum saida izninsa,kinga yanzun ba hijab ko dankwali a jikinta,kuma ba kyau aga mutum a haka,kin saka mata camera,kinga ba zataji dadi ba ko?” Kai ta sake gyadawa da alamu jikinta ya mutu

“Good girl,idan mun gama waya ki bata haquri”

“In sha Allah” sai murmushi ya sake subuce masa,in sha Allah din kamar a bakinta aka radata,bai taba jin ta fadi ba,kamar wata babba,amma yanzun data fada sai yaji wani sanyi a ransa

“Khairan in sha Allah” ya fada a ransa yana jin hope sosai akan sabuwar nanny din fadeelan.

Tunda ta fahimci ta janye camera din sai ta koma gefe ta zauna tana maida numfashi, wani abune da bata taba zata ba shi yasa ta razana,wayarta ta jawo ta buda don rage zaman da bugawar da zuciyarta keyi akan abun,tana danne danne tana kiran sunan

Allah,har batasan fadeela ta kammala wayar ba,saijin mutum tayi tsugunne gabanta

“Aunty,am sorry,abby yace na baki haquri,na juya miki camera without your permission” ido ta zuba mata,sai ta murmusa ta sanya hannunta ta dagota ta dorata kan cinyarta

“Abby yace babu kyau kada na sake” kai ta jinjina

“Abby dinki is a good person,gaskiya ya fada,na haqura nasan kema ba kina sane bane ko?”

Kai ra gyada mata tana murmushin jin dadin yabon da ta yiwa mahaifinta,riqe hannunta tayi suka miqe

“Oya,muje a kwanta,gobe da school,next week kuma zaku fara revision,sai C.A then exams ko?

“Yes” ta fada tana murmushi

“Abby yamin alqawura da yawa,yace ya gaji da ganin third position,da second yakeson ganina,if possible ma first,idan na kawo first din kuwa,sai ya gyada kai,nasan abby naidan ya gyada kai baice komai ba…..hmmmmm,zai baka mamaki ne,anty ki tayani addu’a na samu first position” ta garasa maganar tana

marairaicewa dai dai sanda sãahar ke lullubeta

da duvet.

Murmushi ta saki,ta kama hannunta ta rige

cikin nata

“Kiyi karatu sosai kiyi addu’a da yawa,you will pass in sha Allah, kuma duka zan tayaki fadee”

qanqameta tayi tana dariya cikin jin dadi

“Na gode aunty nanny”

Shuru yayi idanunsa akan system dinsa

bayan sallama da fadeelan,hannunsa rige da

dan qaramin spoon yana ta juya tea din da

already ya riga ya gama juyuwa,ya rasa me

yake tunani,hirarsu da fadeela….abubuwan

da yaji.

.ko abinda ta nuna masa bai shirya

gani ba?, Sai kawai ya zame hannunsa daga

tea din,ya mige yana zuba hannuwansa dukka

biyu a aliihun wandonsa yana furta “La haula wala quwwata illa billah” tattaki yayi kadan ya matsa gaban balcony dinsa,ya zube idanunsa a gurin yana kallon jerarrun tsirran dake gurin suna rayuwarsu hankali kwance,duhun dare da hasken fitilu suna sake qawata ganin mutum. Qarar wayarsa ta sanyashi waiwayowa,ya zubawa wayar ido yana karanta sunan NADEEYA cikin ransa,sai data kusa katsewa sannan ya daga ya sanyata a kunnensa yayi shuru ba tare da yace komai ba.

*HUGUMA*

64

* TABARMAR KASHI_*

Page 64

“barka da warhaka yaa toufeeg” daga can daya sashen aka fada cikin d’ari d’ari,kamar me tsoron yin magana

“Barka” ya fada a dake kuma a taqaice

“Ya aiki yaa?”

“‘Alhamdulillah” ya sake amsa mata a taqaice,duk sai taji ba dadi,saboda ba haka suka saba yin waya ba,ba kuma da irin wannan yanayin yake magana da ita ba,duk da ta saba da miskilancin sa,amma yanayinsa na yanzu ba dashi suka saba magana ba

“Yaaya upper week zan dawo gida,finally na gama exam dina,zaman canada ya qare”

“Good…..ina miki murna” ya sake amsa mata a taqaice. Marairaicewa tayi zuciyarta na karyewa,tamkar tana a gabansa

“Am sorry yaaya”

“Sorry for what?” Yayi tambayar hankali kwance kamar dai da gaske baisan abinda yake faruwa din ba

“Yaaya,nasan kasan nayi maka laifi,amma wallahi it was not my fault,tanata sakamin pressure akan tanason ganin FADEELA..

“Ki gaya mata,ta sanya a ranta bata haifi wata ‘ya ba a duniya kwata kwata,fadeela a yanzun ba jininta bace” yayi maganar cikin zafi tamkar itace a gabansa. Laqwas NADEEYA tayi cikin toro da firgicin jin sautin muryarsa mara hayaniya lokaci guda ta cika da kauri.

Iska yadan furzar yadda nadeeya din tayi shuru ya tabbatar masa ta tsorata da yadda yay maganar ne,sai ya lumshe idonsa yana gogarin yiwa kansa saiti,bayan ratsawar shuru na wasu sakanni sal yace

“Ticket din wacce rana kikayi booking?”

“Sunday” ta fada a sanyaye

“Alright,zan dawo miki da abinda kika kashe,don nayi fushi bashi zai baki lasisin yiwa kanki wata hidima ba,don’t tray to buy anything da kudinki,as long as iam alive”

“In sha Allah” ta amsa masa a sanyaye, zuciyarta cike fal da qauna da kuma soyayyarsa,irin zallar soyayyar yan uwantaka,wadda babu algus a ciki. Labarai kadan ta bashi suka katse kiran,don ta fuskanci yanayinsa kamar he’s not in mood.

Ya jima da wayarsa a hannu yana jujjuyata ba tare da iya yin komai ba,haka kawai wasu abubuwa na rayuwa suke dauko kansu suna kawo kansu da kansu gabansa,rayuwarsu yadda ta gudana shi da

‘yaruwarsa,shekara kusan ashirin da biyar baya.

Ajiyar zuciya hade zazzafar iska ya fesar,ya sake juya wayar a hannunsa sannan ya lalubi number hajiya qarama.

Tashi tayi ta zauna sasai tana cire hankalinta daga lissafin ribar kayan data kawo daga china da suka samu qarewa,ta

bada dukka hankalinta akan wayar ganin me sunan,tayi gyaran murya sannan ta saka wayar a kunnenta.

“Barka da dare”

“Barka kadai,yanzu yanzu na shigo daga gurin mutuniyar,suna can ita da nannynta suna shirin bacci”

“Ummm,yayi,batun nanny dinne dama na kira,nawa ta buqaci albashinta?” Wuyan rigar lace din jikinta ta gyara

“Har yanzu taqi fadin nawa,ni bansan kalar nanny din da muka samo ba wannan karon,nayi mata zancan kudin amma sai tacemin ba komai,aikin yafi kudin muhimmanci” gyara zamansa yayi,shima maganar ta dan bashi mamaki

“‘Noo,ta fadi ko nawan ne,sai a yiwa elyas magana,a dinga cire mata on time ” yayi maganar ne har qasan zuciyarsa, yana lua hangen canji qarara daga fadeela,a yadda zuciya da ransa sukayi masa dadi,yana ganin ko nawa ne ta bugaci a biyata baiyi tsada ba

“Okay,i will talk to her’

“Yayi’ ya amsa a kasalance,tanaso su tattauna wasu abubuwa amma ya bata uzurinta,sai tayi masa addu’a sosai sannan ya katse wayar,ya jefara gefe yana jin dukka gabban jikinsa suna sake zama weak,don haka sai ya kwashe wayoyinsa yabar dukka sauran tarkacen a gurin, saboda akwai wadanda xasu gyara gurin,komai kuma su sanyashi a muhallinsa.

Wanka yasoyi daya dawo amma saboda ya kira fadeelan baiyi ba,don haka yana shiga ya zare kayan jikinsa,ya lullube murdadden jikinsa da babban lallausan towel. Minti talatin kacal ya fito yana qamshin shower gel,da hair shampoo dinsa me tsada da yake amfani dashi waien wanke sassalkan gashinsa da ko yaushe yake cikin daukar idanu da hankulan tarin matan da shi kansa baisan adadinsu ba,saboda mafi yawansu bashi da masaniya akan fadawar da sukayi cikin matsananciyar soyayyarsa. Mintuna sha biyar ya gama shirinsa,a hakan yayi sauri akan yadda ya saba,don shirinsa yana daukar lokaci,sosai yake bawa jikinsa da fatarsa kulawa da mayuka da turaruka masu shegen tsada,ko nawa yana iya kashewa ya siya turare zuwa mayuka,ko a yanzun kudin wasu turarukan nasa sun isa jari a waien mutane da dama. A gurguje ya feshe gashinsa da turaren ka,hakanan beard dinsa da nasa turaren na musamman tamkar wani mace haka yake a wannan bangaren.

Guri na musamman da yake gabatar da ibadunsa ya shimfida lallausar dadduma,cikin daidaituwa da miga dukka tunanin damuwar duniya izuwa bayanka ya fuskanci alqibla,cikin cikakkiyar tsaiwa da daidaito ya kabbara sallarsa.

Dukka raka’o’in daya saba yi babu wadda ya rage a ciki,ya dade saman abun sallah yana addu’o’in sa,bayan ya kammala yana nade abun sallar akayi masa knocking,sai ya waiwaya yana duban wata maqalalliyar na’ura dake nuna masa fuskar wanda ke knocking din. Jibril ne,matsawa yayi gaban bedside drawer ya ciro wasu files,sannan ya zura wasu lallausasan takalma da aka yi da wani gashi me laushi ya buda gofar da zata sadashi da setting room na gidan.

Cikin girmamawa ya rusuna yana gaidashi

“Sir… bakaci dinner dinka ba,ina fatan lafiya” kai ya girgiza yana miga masa files din

“Am too tired,ina bugatar hutu,gobe inaso mu fita da wuri,zan kwanta yanzun,ko meye please kada wanda ya tasheni,zan nemeka idan ina da buqatar hakan” hannu biyu yasa ya karba cikin girmamawa

“Yes Sir,have a goodnight”

“Allah ya tashemu lafiya” sai ya juya a nutse yana komawa dakin.

Saman lallausan carfet din dakin ya yada pillow,ba kasafai yake iya kwana samam shimfida me laushi ko katifa ba,yayi rigingine idanuwansa na kallon roofing din dakin cikin dim light din daya saki,ya kammala addi’ o’insa ya shafe jikinsa,ya koma riginginen ya kwanta yana sauraren zuwan bacci.

A hankali jinsa da ganinsa ya fara nisa da wannan duniyar da muke ciki,ya haurawa zuwa duniyar bacci,irin baccin da kake tsakanin wannan duniyartamu da duniyar baccin,zuciya da ruhinsa suka fara haska masa wani abu da ya faru zahiran dazu dazu cikin rayuwarsa ta ainihi. Tana tsaye ta basu baya kamar yadda ya gani a mafarkinsa, dogon gashinta me tsananin duhu da sheqi daya raba tsakiyar bayanta,hips dinta da mazaunanta da suka fita ainun ta shape din doguwar rigar.

A mugun firgice ya bude

idanunsa,sannan yayi wani irin tsalle ya miqe ya zauna sosai saman carfet din,hannunsa ya sanya ya tallafi goshinsa da ya dan fara hada zufa,a hankali labbansa suka motsa da fadin

“Hasbunallahu la’ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azeem” ya maimaita ta kusa sau goma,sannan a hankali zufar ta fara ragywa tana bushewa da kanta,sai ya daga kansa yana bude idanunsa a hankali

“Meye hadin sa da nanny fadeela da har zata biyoshi cikin mafarkinsa?,me yasa duk yadda yakai ga kame kansa da idanunsa daga kan kowacce diya mace,amma hakan bai rabashi da tarin mafarkan kasancewa da wata diya mace dako fuskarta bai taba samun nasarar

gani ba? mafarkinsa na yanxun ya kusa yin

dai dai da yarinyar dake yawan zuwa debe

masa kewa,duk da baisan saurin murya ko ta

fuskarta ba,ya tsani wannan mafarkin da ko

yaushe idan ya yishi take sake haukatashi ya

maidashi mabuqacinsa,lalurar da ya dauka

yayi adabo da ita,ya tasa ta gofar da zai yaqi

hakan,yawan nauye nauyen da yake dorawa

kansa da ayyuka babu ji babu gani,ya dauka

sun isa su cire wannan buqatuwar daga

jikinsa. Yasan yayi nasara da idanunsa da

kuma zuciyarsa,ta yadda duk tarin matan dake

kai kawo a gabansa dama bayan idanunsa,bai

taba daga kai ya kalli wata yaji shaawar

kasantuwa da ita ko kuma ta burgeshi

ba.amma ta bayan fage, wata mace guda daya

tal da baisan wace ba na neman matsanta

masa,cikin watannin da duka duka basu gaza

biyar na.

Siririn tsaki yaja shi daya cikin dakin,ya

miqe cikin matuqar mutuwar jiki ya nufi toilet.

Alwala ya daura,ya dawo ya tsaya gaban

wardrobe ya cire qaramin towel ya goge lemar

jikinsa,ya saki towel din ya koma makwancinsa na dazu. Duk da bayason kwanciyar rub da ciki ko kadan,amma yau din ta zame masa dole haka ya kwanta a rub da cikin yana qangame dukka pillows din dake kewaye dashi.

****Tsam fadeela dake sanye da uniform dinsu,cikin tsafta kulawa da kuma tsaarin sãahar ta rige hannun sãahar din tana langabar da kai

“Ni ba itace zata kaini ba Allah kece zaki kaini” ta gadi a mugun shagwabe tana daf da sakin kuka. Waiwayowa hajiya qarama tay,tadan hade fuska

“Me yasa bakiji uktie,ta yaya nanny zata kaiki school,shin tama iya mota da kike zancan ta kaiki makaranta? idan kuma kinaso ki makara ne shikenan” labiba dake tsaye riqe da key din tata motar da zata miga fadeelan makaranta,saboda driver dinta da hajiya garama ta aika ta jefawa fadeelan harara,sannan tace

“Ta ina zata iya mota? bayan ba itace dasu ba a gida?‚an saba hawa motor din kasuwa?” A nutse säahar ta dag kai,kallo daya tayi mata ta bawa banza ajiyarta,don tun zuwan labiba gidan ta gama karantarta,ta kuma yi aji guda ta sanyata a ciki.

“Allah mommy ta iya,Allan kuwa”

“Ke ko ta iya bazan bayar da motata ba,saidai ku ira a wanke wata cikin motocin gidan nan sannan a kaiki” ta fada cikin fushi ta juva da zummar komawa cikin gidan

“Zo nan labiba” hajiya garaman ta kirayeta,ta dawo a fusace ta tsaya tana huci

“Bata key din ta tuqaku,saiku tafi tare ki dinga monitoring dinta kada ayi miki barna” fuska ta hade cikin fada take magana

“Allah kune kuke sangarta yarinyar nan,sai abinda takeso sannan za’a yi mata?”

“Waishin ba daga jikin kakanta da mahaifinta kudin motar suka samu ba?” Haiiya garama ta jefawa labiba tambayar. Sak labiba tayi tana duban tsakiyar idanun hajiyan,itama kafeta tayi da kallo. Sometimes kamar yarinyar tana manta waye ita,har suso wuce gona da iri a wasu lokuttan,shi yasa takanyi hakan,saboda makaho yasan cewa fa ana ganinsa.

Jiki a sanyaye ba tare kuma data sake cewa komai ba ta migawa saahar key din.

Kamar ba zata karba sannan tasa Hanna ta karba,tana ji a ranta wasu lokutan wasu mutanen suna da bugatar a koya musu hankali,a kuma basu darasin rayuwa.

Jikinta ta kalla babu buqatar sai ta koma ta canza kaya,doguwar riga ce da hijab dinta madaidaici duka golden yellow,sai wani adon wani abu me kama da lace da akayi daga qasan hijab da rigar sai slippers dake qafafunta.

Juya muqullin tayi tana duban

motar,qirar motar ba baquwarta bace duk da tana da tsada,ta saki boyayyen murmushi,tana rige da hannun fadeela daketa tsallen murna sukayi gaba,labiba dake cika tana batsewa ta biyo bayansu.

Kafin labiban ta iso tuni ta bude front seat ta sanya fadeela,ta zagaya sashen driver ta bude ta shige,dole da tazo back seat ta bude ta shigan tana qwafar raina mata wayon da sãahar din tayi

“Ko ba komai yau mun samu new driver” ta fadi don ta baiwa sãahar din haushi

Sarai ta jita,amma saitagi nuna hakan,murmushin da ya subuce mata ma kauda kanta tavi gefe don kada ta gani

“Zakiga new driver gain idonki” ta furta gasan zuciyarta.

Hira sukeyi da fadeela irin wadda suka saba,daga yadda suke hiran kadai zai gaya maka zallar shaquwar dake tsakaninsu da kuma gaunar juna,labiba na zaune a baya kamar zata fashe,ita taso samun wannan damar, amma kuma bata sameta ba koda quater dinta,yanzun ga wata banzan nanny daga sama tazo ta mamaye rayuwar yarinyar.

Sai data tabbatar fadeela ta shiga class,ta kuma sanya hannu akan kawota sannan ta fito. Zata tada motar mrs sadeega ta sanvo kan tata,dole ta tsaya suka gaisa “Kina aiki me kyau miss säahar, kowa ya kalli fadeela yasan tana samun canji garara,hatta da performance dinta a class ya qaru,tiny baby ta fara komawa chubby ma sha Allah”

“Alhamdulillah” sãahar ta fada,ita kanta tana jin dadi ko yaushe yadda yarinyar ke wayar gari da goshin lafiyarta da kuxarinta suna garuwa,basu jima ba sukayi sallama,mrs sadeega ta wuce su kuma suka fice.

Ta cikin mirror ta dubi labiba dake zaune a bayan ta toshe kunnuwanta da earpiece tana bin waqoqin turawa tana gyada kai,murmushin mugunta ta saki, saita take motar ta qara mata gudu. Da sauri labiban ta daga kai,ta zare earpiece din daga kunnenta

“Ke meye haka? ki rage gudu da Allah” tana kaiwa nan ta maida earpiece din. Da kadan kadan ta sake garawa motar gudu fiye da dazun,tuni labiba ta cire earpiece din harma da wayar duka ta ajjiye,cikin fada da tashin hankali take magana

“‘Wai bakya gani ne,wanne irin gudu ne

wannan?,kashemu zakiyi ne,dake fa nake

magana!” Kunnen uwar shegu tayi da ita,salma

sake qara gudun da tayi,ta shiga kurdawa

tsakanin motoci tana overtaking,ta tuna

da tsohuwar dabi’arta na mugun gudu a

hanya,don a baya saida yaa Saifullahi yasa aka hanata mota na wasu watanni sannan ta bari.

Tun labiba na hayaniya har ta fuskanci

hayaniyar ba zata kaita ba,ta koma lallashi

da kwantar da murya,amma sãahar kam ko

a jikinta,ta dinga shimfida gudu da ita,sai ga

labiban tana sakin hawaye,kowanne sashe a

jikinta rawa yakeyi,don babu abinda ta tsana a

mota irin gudu.

Daga bakin gate din gidan ta tsaida motarta bude ta fice abinta tare da bar mata

key din a jikin motar,tayi knocking gofar gate

din,daya daga cikin security din ya taso ya duba wacece sannan ya bude mata. Baya yaja cikin rusunawa,saboda sosai Allah ya sanya ma ma’aikatan gidan gaba daya gain wani irin girmanta. Yadda suke mu’alama da masu aikin gidansu haka ta dauki kowa cikin gidan,tana girmamasu qwarai, irin girman da duka cikin gidan ba wanda ke basu irinsa,bugu da qari me hannun kyauta ce ita,a hakanma afifa tace mata saita rage,don kada su lura da ita din wace,su sanya ayar tambaya a kanta.

“Madam ya na ganki a qasa?” Ya fada da ‘yaf gaurayayyiyar hausarsa da bata fita tarr

“Daga waje na sauka”

“Welcome” ya sake fadi yana dage gate din don yasan yana jinkirin budewa labiban yau shine mutum na farko da zata fara saukewa kwandon rashin mutuncinta na safe.

65

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*8

DON MARTABAR MANZAN ALLAH ME

FITARWA KIYI HAKURI KIYI HAKURI.

Hankalinta kwance tama manta da wani abu da ta yiwa labiban,ta gama shirinta tsaf ta canza kava,tana duba saqon afifa a waya da take gaya mata mahmud nason a bashi dama yazo ganinta,sai taji sallamar hajiya qarama cikin matsakaicin parlor din da daga shi sai hallway na dakunansu,don ba kasafai take fita babban falonsu ba indai ba kitchen zata ta shiryama fadeela abinci ba.

A nutse ta daga kai tana amsa

sallamar,kamar kullum hajiya qaraman cikin shigar alfarma dake nuna zallar alfaharinta take,labiba ce da tayi firgai firgai ke take mata baya,ta zamu daya daga cikin kujerun ta zauna idanunta akan sãahar tana karantar yadda yarinyar sam wani abu baya mata kwarjini ko va tsoratata

“Barka da safiya” ta gaidata cikin salon data saba gaisuwa,sai data gyara zamanta sannan tace

“‘Barkanki,ya kwanan uktie?”

“Alhamdulillah ta amsa mata tana qogarin katse kiran dake shigo mata waya.

“Ya akayi kikayi gudun wuce sa’a haka da labiba.har kina shirin hallakata?” A nutse ta sake kallon labiba sannan ta maida kan hajiya garama

“Ni din?”

“Kefa” ta amsa kai tsaye tana kallonta,tare da mamakin yadda take bada amsa lokuta da dama kanta tsaye,kamar ba wadda ke aiki a qarqashinsu ba,ita din kuma sai ta gaza daukan kowanne hukunci koda da zazzafar magana ne,abinda bai taba faruwa ba tsakaninta da duk wani me hidima dake qarqashin ikonta.

Ajiye wayarta sãahar din tayi sannan tace

“To bansan sanda akavi haka ba,don normal driving nayi yadda na saba,saidai ko a idonta ne ya zamana gudun daya wuce qaida,asalima a waie na sauka nabar mata motarta ta qarasa shigowa da ita,kina iya tambayarsu idrith dake bakin gate” yadda tayi maganar a miqe kai tsaye yasa hajiya qarama duban labiba

“Wallahi qarya takeyi,jini na saura kadan ya hau” labiban ta furta kamar zata saki kuka

“Bansan waye me gaskiya a tsakaninku ba,sai kiyi haquri, tunda bakison hudu next time karku sake hada mota” baqinciki kamar zai kashe labiban haka ta juya ta fita, sãahar kuwa ko daga kai ta kalleta bata sake yi ba.

“Ina fatan magungunan nan sun qare kamar yadda na irgasu?” Hajiya garama ta fada bavan ficewar labiba,wayar ta kuma ajiyewa,ta dora idanunta duka cikin na hajiyan. Wani abu me qarfi hajiyan taji tattare dasu,sai ta zame ganinta tana cewa

“Kin zubamin ido baki amsamin tambayata ba”

“Sun qare‚na yau kawai ya rage”

“Kin tabbatar?” Saita jinina kanta kawai ba tare data ce komai ba. Tsam hajiyan ta miqe tana mata wani kallo

“Yayi kyau,cikin satin nan ganwar mahaifin fadeela zata dawo rayuwa damu cikin gidan nan,banason komai ya canza daga cikin sharudan dana gindaya miki,and then….magungunanta duka zasu dawo hannuna,duk lokacin da zata sha ki kaimin ita tasha sannan ta taho,wasu lokutan tafiye tafiye na kasuwanci na suna kamani,idan hakan ta taso zan damqa su a hannunki ta yanayin daya dace” daga haka ta juva tana fita daga falon.

Kasa dauke kallonta sãahar tayi daga kanta,haka kawai a yau din wani qaqqarfan zargi ya taba zuciyarta,sai taji gaba daya zuciyarta tayi mugun matsewa da takurar son jin wanne matsayi hajiya qaraman ke dashi a gurin fadeelan.

Kusan zaman banza tayi a gurin,ta kasa tabuka komai,zuciyarta da kwanyarta nata jujjuya mata al’amura masu dama game da rayuwa,hango kanta ta dinga yi shekarun baya,lokacin da adam ya maidata mahaukaciya tuburan,ya dinga shayar da ita gubar allurai da magungunan da suka kusa sanyata amsa sunan mahaukaciyar me license ma,tsoro ya shigeta bayan wata zuciyar ta ayyana mata.

.. hajiya garama na

daya daga cikin masu wanna hali da dabiar.

Wani gumi ne ya karyo mata,ta yaya zata bari hakan ya faru da zuciya da ruhin da suke da rauni,salihar zuciya da kyakkyawan ruhin da basusan sabo ko cuta ba,sam sam….ba zata taba bada wannan damar ba,zata yi dukkan me yiwuwa ta katange fadeela daga dukkan wata cuta muddin ranta matugar ta samu kuma tabbaci da yaqinin abinda take zato din,sai inda qarfinta ya qare.

Sau uku baaba ramatu na wuceta,tun batayi magana ba harta tambaya

“Antyn fadeela lafiya kike yau kuwa?” Dan garamin murmushi ta saki tana gyara kwanciyarta cikin sofa

“Lafiya lau nake baaba, kasala kawai nakeji”

“Jiki da jini dama,to Allah ya garemu da lafiya”

“Ameen ya hayyu ya gayyumu” ta amsa mata tana maida idanunta ta lumshesu

Dawowar fadeela daga makaranta ne ya tasheta a wajen,yau gaba daya zancanta na dawowar sister nadeeya ne(haka take kiranta kamar yadda taji abby dinta wani lokaci yana kiranta da shi),ta hana sãahar yau sakat,alamu sun nuna akwai qaqqarfar shaquwa a tsakaninsu,bata samu hutu ba sai da suka kammala komai,ta hau google meet ta kira mata abby dinta,ta ja mata qofar dakin ta barta a ciki. Tun wancan ranar bata sake bari nasu take barin parlor din ko gurin,har sai ta

kammala sannan ta biyota tana bata labarin hirar da sukayi da abby dinta.

Tana kitchen tana hada mata abinci ta

shigo da gudu da tab din a hannun ta

“‘aunty,don Allah sister nadeeya zaki kiramin” ta

fada a marairaice,murmushi ta saka ta ajjiye

wuqar hannunta,ta goge ruwan hannun nata

jikin towel,ta koma ta watsapp din da aka

budeshi saboda ita kadai ta kira matan,cikin

sa’ a tana online sai ta miga mata ta koma aikin

nata,ita kuma ta juya da gudu ta fice.

Tun daga kitchen din take jiyo hirarsu da

dariyarsu,allai nadeeyan uwa ce da fadeela keyi da ita sosai. Har ta gama abincin ta

baro zuwaira hirar bata qare ba,sai ta wuce

dakinta ta daura alwalar sallar la’asar. Tana

idarwa fadeelan na shigowa rungume da tab

din,murya qasa qasa tace

“Sister nadeeya tace na kawomiki ku gaisa,nace abby ya hana sai an fara tambayar mutum tukunna,don Allah aunty nanny zaki gaisa da ita?” Murmushi ya subuce mata, fadeelan badai jin magana ba,saita miqa hannu ta kamota jikinta,ta karba tab din ta ajjiye a gabansu,fuskar nadeeya ta fito sosai a screen din.

Murmushi ya wadaci fuskar nadeeya, okaci daya da idanunsu suka gauraya waje daya kowa yaji wani abu game da dan uwansa

“Barkaaa” nadeeva ta fada tana waving hannayenta wa sãahar

“Barka kadai” sãahar ta maida mata itama cikin murmushi

“Yamma ne nan ko? to kin yini lafiya auntynmu?” Murmushi ya sake subucewa

sãahar tare da jin nauyin kiranta anty da nadeeya tayi tunda ko a ido kana ganinta zaka san sun kusa sa’anni da ita idan ma zata girme mata to da kadan ne

“Lafiya alhmdlh sister nadeeya,ya karatu?”

Cikin jin dadin sunan data ambaceta dashi da qaramar dariyar farinciki tace

“Karatu ya qare, in sha Allah nan da kwanaki uku ina tare da ku,nazo naga the world talented nanny dinmu” murmushin sãahar ta sakeyi

“Ma sha Allah,to Allah ya amince sisternmu” matsowa fadeela tayi tana sake zayyano mata dame dame zata taho mata da shi. Saahar din zata matsa don ta basu guri nadeeya tace

“Don Allah karki tafi,yanzu kin fini iya ji da rigimammiyar ‘yar nan,ki zauna kya tayani lissafa wadan nan kavan wasan da taketa fadi,ta dauka ni abbynta ce da zan mata tawagar kaya?” Ta fada tana dariya. Murmushi saahar ta saki,sai ta koma ta zauna,wayarta na hannunta ta hau watsapp tana duba kwantan sagonni;,lokaci lokaci takan daga kai ta kallesu cikin ban sha’awa da burgewa idan sukayi wani abun,duk sanda zata daga kan sai sun hada idanu da nadeeya,saidai su sakarwa juna murmushi.

******Washegari aka bude daya dakin da tun zuwan säahar din yana rufe,saboda me dakin wato nadeeya din bata nan. Dukka furniture din din ciki aka fidda,aka shirya sababbi,sannan aka maida mata kayanta ciki aka sake gyara dakin da kyau. Fadeela da suke tare da sãahar din ta kasa sukuni saboda murna,dole karatun ranar da ba’a yi ba kenan,sai ta barta.

*******Karfe hudu da rabi na ranar lahadin motar da take mallakin nadeeya ta shigo da ita katafaren farfajiyar gidan mahaifin nata.

Seatbelt dinta ta cire tana duban ilahirin harabar gidan,ita sam banda Dr jarma din yace lallai ta sauka a nan din,da sai ta gama kwanakinta a gida sannan zata zo gaidasu,sam zama a gidan koda na minti daya ne bai taba mata dadi ko kuma ya burgeta ba,bawai don bata samun kulawa ko wani abu na jin dadin rayuwa ba.

Oofar motar ta bude da kanta ba tare data jira tarin ma’aikatan dake yungurin mata hakan ba,fuskarta a sake,kasancewarta mutum itama me fara’a da haba haba da al’umma cikin kuma kulawa take amsa barka da dawowar da kowa keyi mata,bayan tafiyarta karatun data shekara hudu tana yinsa,wanda a shekara hudun sau biyu kacal tazo gida bisa tsarin yaa toufeeq da yace baison yawo,idan karatun zatayi tayi basai tazo musu gida ba

A haka ta gama gaisawa kaf dasu,sannan ta tuqe ga hajiya mansura dake tsaye tana faman doka mata murmushi

“Lale maraba da dawowar diyata cikin aminci”

ta furta tana yunqurin kamo nadeeya zuwa

jikinta. Kadan tadan zame tana murmushin

itama

“‘Na sameku lafiya?”

“Wannan gaisuwar sai a ciki za’a yita,abbanku

yana toilet yana qarasawa shiryawa,muje cikin

tukunna” waiwayawa tayi tana bawa masu

aikin umarnin shigowa da jakankunanta

“A’ah,ai basai sun shigo dasu ba,zan wuce

gidan yaa toufeeq ne” fuska tadan bata

“Me zakiyi a can nadeeya?‚ga gidanku?”

“Fadeela nacan na jirana,zanfi jin dadin can

din” ta bata amsar tana takawa zuwa cikin

gidan rungume da wata jaka data sako kaya masu muhimmanci a mazaunin tsaraba wa mahaifinta. Baki galala da kallo hajiya mansura ta bita dashi, cikin ranta tana jin wani irin kishi yana kamata,a fakaice kamar anaso ne ayi wining a kanta,bayan tarin nasarorin da akaci a kanta,har yanzu wannan matar…

..wannan

mutum dayar ta gagara cimmata yadda ya kamata,tsakaninsu kar rasan kar ne, amma har yanzu qudurinta bai isa ga inda taso ya qarasa ba,MUTUM DAYA TAK! Ita ta samu dukka wasu damarmaki da taso ace ita ta samesu,duk da tayi musu nisan zangon da suke da imanin kasantuwarta a cikinsu abune mai wahalar yiwuwa,wannan ya rage garfi da kaifin wasu damarmakin nata ainun WACECE?!

AMSARKU TANA GABA_.

Juya cokali kawai takeyi cikin abincin da hajiya mansura ta gabatar mata,tana kuma amsa tambayoyin dr jarma. Gaba daya hankalinta bai waien, Allah Allah kawai takevi a tashi daga zaman cin abincin da akace an shirya da sunanta don tayata murnar dawowa,cikin ranta tana fata da addu’ar kada Allah yasa dr din yace ta zauna tare da su.

Yana tsame hannunsa itama ta tsame nata tana gogewa da tissue,haiiya mansura ta kalli plate din nata

“Ya haka kuma?,banga kinci komai ba”

“alhamdulillah ‚naci abinci a jirgi”

“Abincin jirgi wani abinci ne? ki zauna ki garasa ci, yanzu zan yiwa su taiba magana su sake gyara miki dakinki” tana gama maganar nadeeya na miqewa,ta goya jakarta tana duban dr jarma

“Abba zan wuce gidan yaa toufeeq,fadeela tun ina hanya tasa ake kirana”

“Alright,ki mintsinemin kumatunta ja’ira,tunda tayi sabuwar nanny ta rabu da zuwarmin, kullum kuma nayi kiranta cikin bani labarinta take,ki gaya mata nayi mata garin salary akan abinda ake biyanta,ina mata godiya da kyau da kyau,don da alama tasan aikinta sosai” murmushi nadeeya tayi,tana jin dadin yadda Dr bai hanata tafiya ba,sanann kuma ita kanta tana jin sãahar har ranta,duk da basu dade da sanin juna ba,amma tana jin tamkar ta dade da saninta.

Sai da taga sun dau hanyar barin gidan ta sauke ajiyar zuciya,koda ta yiwa dr alqawarin zasu zo suyi kwanaki da fadeelan,batajin zata iya wuce kwana daya ko biyu.

Guri hajiya mansura ta samu ta zauna bayan fitar nadeeya

“‘Dr inason magana da kai” kansa ya cire daga wayarsa da yake dannawa,daya hannun nasa kuma yana sakace da toothpick

“Nikam nace ba,bai kamata ace kana raye ba amma dukka yaran da Allah ya baka basa rayuwa tare da kai,ka tattarasu ka barsu a wani guri na daban,ni kaina da nake matsayin uwa a waiensu sam babu wata shaquwa a tsakaninmu” a nutse ya ajjiye tsinken sakacen yana dubanta

“Tohhhh…

…yau kuma wajen qarama dinne

ya koma wani guri na daban?,kin manta suna rayuwa ne garqashin gidan da toufeeg ya gina da kansa? nadeeya da ita tafi sabawa,a hannunta ta garasa girmanta, taoufeeq dinma kusan hakane,sannan shi namiji ne wanda banda gaddara da a yanzun yana qarqashin kulawar matarsa ne,so a ciki bansan meye matsalarki ba” ya qarashe maganar yana kafeta da idanu.

Ajiyar zuciya ta sauke,dama tayi zaton hakan daga gurinsa,yadda qarama ta tattare yaran gaba daya ta maidasu qarqashin mulkinta ita kadai yana mugun ci mata tuwo a qwarya,wanann dalilin ya sanya ta tattara labiba ta miga mata ko hakan zai sanya a samu wani sauyi,amma dai jiya i yau babu wani abu da ya canza

“Shikenan” abinda ta fada kenam cikin suyar zuciya ta miqe tana tattare gurin,zuciyarta kamar zata fito ta qirjinta. Binta shi kuma yaci gaba dayi da kallo,yana mamakin yadda har zata iya gaya masa wannan maganar akan qarama,ko ta mance cewa ta silarta ta sanshi?,ta silarta ta zama abinda take a yanzu take kuma amsa sunan da take amsawa na matarsa.

Dukka wannan shi ba damuwarsa bane,abu daya ya sani,duk abinda zai takura yaran ya sakasu cikin qunci zuciyarsa ko qangani bata so,muddin dai wannan abun bai kaucewa hanyar addini da al’ada ba,can qasan rai da zuciyarsa yasha kasa runtsawa cikin dare,he have feeling of guilt akan TOUFEEQ da NADEEYA,saidai har yanzu kwanyarsa ta kasa gaya masa meye ainihin tagamaimen laifin?,idan ya matsa da bincikar kansa kuma sai matsanancin ciwon kai ya saukar masa.

_uhmmmmm hmmmmm_

Turus ta tsaya cikin mamakin ganin cewa ba wani mummunan abu bane ya sameta sanadiyyar ihunta data jiyo tun daga toilet din dakinta. Suna rungume da juna ne ita da nadeeya kamar wadanda suka bace tsahon shekaru sal yau suke ganin junansu.

Nadeeyan ta daga fadeela tayi juyi tayi juyi da ita har babu adadi sai kawai sãahar din ta saki murmushi ta juya ta koma ta garasa abinda takeyi,saboda taga basa ganin kowa sai kansu,masu aikin gidan nata wucewa da kayan nadeeya din zuwa cikin dakinta

“Ya zaki tafi?,ki tsaya mana mu gaisa” muryar

nadeeya ta ratsa kunnensa sãahar dake

yunqurin komawa ciki. Waiwayowa tayi tana

murmushi

“Ai naga baku gama ba” ta fadi tana duban

nadeeva da take sake ganin wasu kamanni

saman fuskarta,tana ji a jikinta kamar ta santa

a wani guri daban kafin wannan lokacin.

Karamar dariya nadeeya ta saki tana

takowa zuwa inda säahar ke tsaye

“Indai nida ukhtie ne wallahi bakiga komai ba”

saita buda hannuwanta tayi hugging säahar

kadan tana murmushi yadda larabawa ke

marabtar ‘yan uwansu

“‘Fatan na sameku lafiya” ta fada tana janye

jikinta,fuskarta cike da fara’a

“Alhamdulillah”

“Tambaya ta farko,don Allah me uktie takeci ta fara kumatu?” Dariyar da sãahar bata shirya ba ta subuce mata,yadda nadeeya tayi tambayar tana riqe habarta da yatsarta,da alama da gaske abun yana bata mamaki,ko ba’a gayawa sãahar ba alamu sun nuna mata nadeeya mutum ce me barkwanci da faran faran da yawan surutu

“Ki nutsu ki huta,zaki ganewa idanunki” baaba ramatu ta bayar da amsar tana dariya

“En lallai to nima ko dole aci dani, bari na garasa” nadeeya ta fada tana daukar garamar suitcase din data rigo suka wuce ciki tare,saahar ta koma kitchen,fadeela tabi bayan nadeeya.

66

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

DON MARTABAR MANZAN ALLAH ME

FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA

KAYANMU

To kusan yinin ranar fadeela na tare da nadeeya,har sai da sãahar tayi mata dan biki

“An samu sister nadeeya an manta da ni ko?”

Dariya tayi,ta taho da gudu ta rungume sãahar din ta baya tana fadin

“A’an Aunty,sorry”.

Duk da säahar din na dan basu guri tana Kame kanta a dakinta,amma duk da haka nadeeyan bata qyaleta ba,komai saita sanyota a ciki,kota biyota dakin ta fiddota,da dare ma sai gata da dalleliyar kaftan abaya ta mata me kyau da sulbi ‘yar saudiyya

“Ga tsarabarki aunty nanny” sosai kyautar ta burgeta,ta kuma yaba tare da yi mata godiya.

Cikin sati guda kacal da dawowar nadeeya sukayi wani irin sabawa da sãahar,sabon da ita kanta sãahar batasan lokacin da ya faru ba,kafin cikar sati biyu sai suka zama tamkar wasu ‘yan uwa. Abubuwa da yawa na kula da fadeela tare suke yinsa,idan tayi wani abun,wani abun nadeeya ce zata karba.

Wani irin qaunar sãahar nadeeya takeji har cikin ranta,bata sani ba,ko don bata taso da

‘yar uwa sa’arta kamar sãahar din bane? to amma kuma akwai LABIBA da HASEENA,SU din kusan zata iva cewa sun dan rayu tare,to saidai ko kadan bataii abinda takeji game da sãahar ba,ko don ita din tana da wasu dabi’u

da kuma halaye tare da wasu qualities da bata

taba ganinsu daga gurin su biyun da suke

kamar sune dolenta ba?.

Zuwan nadeeva sai ya sanya itama ta dan

sake,takan fita zuwa gida tayi wasu awanni ta

dawo,a nan ne afifa ke tsokanarta,wai nadeeya

nason qwace mata faada,tayi maganar tana

dariya. Afifa tasan labarin nadeeya kaf daha

bakin säaharduk da basu taba ganin juna ba.

Murmushi kawai säahar ta saki

“Bestie,da alama har yau bakisan matsayinki a

guri na ba” hararar wasa ta jefa mata

“Na sani mana,tunda gashi har yau kingi

amsar mahmud yadda ya dace” zancan da ya

sanyata miqewa kenan,ta lalubi mayafinta tana

maida rolling din kanta

“An ambato maqiyin naki ko?”

“No,kawai inason na biya a wankemin kaina sannan na wuce gida,yau na yiwa fadeela algawari zan dafa mata burabusko ita da nadeeya….tashi don Allah ki kaini,saiki saukeni a gida” gyara kwanciyarta afifa tay!

“Bazan iya ba,ki dauki motar ki kawai ki dinga amfani da ita”

“Kin manta ni din nanny ce?” Ta fada tana murmushi,don zuwa yanzun ita dadin sunan ma takeji,hakanan rayuwar da takeyi din tana bata wani irin nutsuwa,ta kauce daga idanun maza kwata kwata,gidan ya zame mata kamar wata mafaka

“Kina sauri ne kawai ki gudu kada ku hadu da abba” murmushi tayi tana maida agogon hannunta

“Duka koma meye zakice bazan musa ba,tashi don Allah kafin ya dawo mu hadu” hakanan afifa ta mige,ta dauko abaya ta dora saman kayan jikinta tanata mita,ta dauki key din motar tabi bayan sãahar din.

A kitchen ta tadda maama,tayi mata sallama,sai ta waiwayo tana dubanta

“Zo nan sãahar” ta kirata tana tsame hannunta daga ruwan da take wanke alayyahu,ta yiwa baaba rabi sign saita fita a kitchen din,ta barsu su uku

“Zauna” tace da ita bayan ta jawo kujeru guda biyu dake kitchen din ta zauna a daya.

Cikin mutuwar jiki kamar wadda aka yiwa tayin zama bisa garwashin wuta ta zauna

“Wannan rayuwar ba ita nake da muradin ganin kinayi ba,nafi bugatar ganinki a dakin mijinki kamar kowacce mace,kije ki sauya tunani ki kuma canza shawara” iya abinda tace kenan da ita.

Duk da kalmomin da tayi amfani dasu ba masu yawa bane amma nauyinsu ya cika mizani taf,jiki a salube ta mige ta sake iaddada mata sallamar sannan ta fito.

Tuni har afifa ta tayar da motar ta kuma barta a kunne saita shige seat din gaba ta maida murfin ta rufe,afifan tadan juya kadan ta kalleta,saita dauke kai ba tare da tace mata komai ba ta motsa motar zuwa gaba,ta saki hon kadan,baaba habu ya taso ya bude musu yana musu fatan sauka lafiya.

Suna gogarin fita a layin motar Dr mamman girema na shigowa,ya kuma gansu,don haka yasa driver dinsa yin slow da motar har suka hade a tsakiya,ya sauke Glass din motar yana duban afifa da idanunsa dake saye da gilashin garawa ido qarfin gani

“Sannu da dawowa abba”

“Yauwa sannu,ku dawo ciki,inason ganinku” hantar cikin sãahar ce ta kada,don bata manta da awa gudan da suka share dashi a waya ba wancan satin,yau din sai da tayi kamar ba zatazo gida ba,so amma zuciyartat a damu dason ganin maamanta,wannan dalilin ya sanyata fitowa.

A gofar gate afifa ta faka motarta kalli sãahar da gaba daya takejin wani rugugin tashin hankali yana sauko mata

“‘Muie ko?”

“‘Na shiga uku afifa,wallahi zancan mahmud ne” wani duba afifan tayi mata

“‘To ai yayi kyau” da kallo tabi afifan,ganin yadda tayi hankalinta kwance bata ma wan damu ba,ga furta sunan Allah da qarfi tana runtse idonta da sauraron bugun da zuciyarta takeyi,ta bude murfin motar tabi bayan afifan.

Tuni har ya isa falonsa yana cire hularsa ya ajiye yana zare agogon hannunsa. Kamar kaiin da aka watsawa ruwa suka samu guri qasan carfet suka zauna,yanayin fuskarsa shine ya fadar musu da gaba tun baikai ga cewa komai ba,a yadda yake da sauqin kai da kuma haba haba da iyalansa,dole yanayinsa a yau ya sanyasu a fargaba.

Sosai ya zauna saman sofa yana maida bayansa ya jinginar da kujera yana dubansu daya bayan daya

“Aishatu” yayi kiran afifa da ainihin sunanta,kai tadan daga kadan sannan ta amsa

“Na’am abba”

“Me kike jira har yanzu baki gabatar min da mijin aure ba?” Shuru ta danyi tana dawurwura,saita rasa me zatace da abban. A halin yanzu tana da samari da a qalla sun kusa mutum hudu,kuma dukkansu da aure suke sonta,saidai babu wanda ta maida hankalinta a kansa

“Na sani nasan komai,saboda haka kije na baki wata uku ki karancesu ki fitar da wanda kikeso a cikinsu”

“‘ In sha Allah abba” dauke dubansa yayi ya mayar kan sãahar,a jikinta taji irin duban da yayi mata,wasu daga cikin maganganunsa kuma suka dawo mata

“Na miki alfarma na kuma daga miki qafa saboda banason na matsanta miki,na kashe miki gishirwar yin aikin duk da sam aikin bai dave dake ba,amma na barki kinje kinvi saboda babu haramci sai tarin lada a cikinsa..

… okaci yayi da zaki tsaya ki fuskanci

wanda yake sonki da gaskiya.

“Ummee,a ina maganarmu ta kwana? ya muke ciki?” Yayi mata tambayar da a waienta tamkar gatse ce.

“Abba‚bamu gama fahimtar juna ba” gafarsa daya ya dora kan daya

“Ta yaya zaki fahimci juna bayan akwai nisan tazara a tsakaninku?,to ni na gama nawa,na gama fuskantarsa,hatta bincike nayi a kansa,babu wata matsala tattare da shi,abinda kawai ya rage shine ke ki fuskanceshi,don haka daga yau yana da lasisin zuwa gurinki zance a duk lokacin da ya buqaci baka,sannan damar fuskantarsa da kike da ita wata daya ne kacal,daga lokacin duk abinda naga ya dace zan iya yankewa” sanda ya sauka a zancan yayi daidai da jin tsargawar gumi me dumi daga kowanne sashe na jikinta,sai take jinta kamar ba’a zaune take dai dai ba,batu fa abba yakeyi na aure a karo na biyu cikin rayuwarta,bayan ko shekara hudu cikakku batayi ba daga fita daga siradin data afka ba,tayi zaton saita debe shekara koma ma babu wanda yayi mata sha awar yin aure bare akai ga batun yi mata tayinsa

“Ku tashi kuje,Allah yayi muku albarka,banason kuma kowacce takai magariba a waje ba tare data nufi inda ta dosa ba”

“To abba” afifa ta samu damar fadi,yayin da sãahar keta qoqarin ganin ta mige ta fita a falon ba tare da an samu matsala ta fadi qasa

ba.

“Kaini nasarawa kawai,na fasa wankin kan” abinda sãahar ta fadi kenan tana kwantar da kanta jikin kujerar tana jin toro da fargabar hukuncin da abban zai iya yankewa a wata gudan daya deba mata

“Aure fa kenan,aure da mahmud,ta karba sadakinsa.ta amsa sunan matarsa,har ta hada shimfida dash.

“A’uzu bi kalimatillahit tammati min sharri ma khalag” taji bakinta yana furtawa bayan runtse idanunta da tayi. Kadan afifa ta waiwayo ya dubeta,sai ta mayar kan titi,a irin wannan yanayin ba kasafai ta fiya son yiwa sãahar din magana ba,don haka batace komai ba har sai da suka iso katafaren gate din gidan,tana shirin fita afifa tace da ita “Take care of yourself…. kada kie ki zurafafa tunani,kinsan dai kina da ciwon kai” kai kawai ta gyadawa afifan,ba tare dat waiwayo ba ta wuce kai tsaye zuwa qaramar qofar dake manne da gate din daha gefe ta fara knocking da wani irin sanyi da mutuwar jiki kamar wadda aka yiwa mugun duka.

Allah ya taimaketa sanda ta shigo gidan nadeeva tana tare da fadeela,ta jiyo kakacinsu a dakin nadeeyan,kamar ma game suke bugawa ita da ita,sai ta sulale ta wuce dakinta ba tare data bari sun ankara da dawowarta ba,don a yanzun kadaici kawai take bugata,batason hayaniya ko doguwar hira.

Kwance kawai tayi tana saqa da warwara,ba tabbatuwar aure a kanta ba,’ah….ambatar kalmar kadai tana sanyata fargaba da razani,wai ta yaya zata iya hada muhalli da wani d’a namiji kuma wai a kirata matarsa? iya wannan tunanin kadai juya mata kwanya yakeyi tare da gara sanyata a wata dimuwa da kuma damuwa.

Gab da magariba ta shiga wanka,ta fito ta shirya cikin wata lallausar riga me hade da wandonta,ta sanya hijab tayi sallar magariba,taci gaba da zama saman abun sallar,tana jin motsi da gilmawar nadeeya da fadeela,wani lokaci harda baaba ramatu.

Tasan ba lallai su san ta dawo ba,saboda duk wani qwan lantarki me haske ta kasheshi,sai dim light kawai.

Har nadeeya ta gota dakin ¡ilkinta ya bata kamar akwai mutum,saboda kana iya jin gamshin turaren sãahar me sanyi da baya buya yana ratsa qofar zuwa hallway din.

Komawa tayi da baya ta murda qofar,sai ta bude,ta sanya kai cikin mamaki bakinta dauke da sallama,sãahar dake shirin tayar da sallar isha’i ta dakata tana amsawa

“Antvn fadee,har yaushe kika dawo haka?,muna can muna jajenki,i called you several times amma ban sameki ba? mutuniyar tana can tana dakon dawowarkita kasa zaune ta kasa tsaye tun dazun‚bakinta da labari” dan lumshe ido tayi cikin murmushi

“Nafi awa da dawowa,na shigo ne banjin dadi shi yasa na kebe”

“Ya salam! me ya sameki?” Nadeeya tayi maganar sautin muryarta na nuna tsantsar kulawa damuwa da qauna

“It’s not something serious,i felt relieved”

“Really?” Kai ta gyada tana murmushi,saboda ta hangi wani irin damuwa da kulawa da ita shigen na afifa

“Bazan gayawa faadee dinki ba,if not ta zama itace patient din,please zakiyi joining dinmu muyi dinner?” Kai tadan yada gefe

“Banajin yunwa,amma zanyi qoqari ko ban fito dinner ba,zamu hadu kafin animan”

“Is okay,Allah yasa kaffara ne’ta fadi cikin mutuwar jiki ta juya ta fice tana jawa sãahar qofar. Ajiyar Zuciya ta sauke me qarfi,tana mamakin yadda suka damu da ita da al’amuranta a lokaci guda haka.

Sai wajen Tara na dare,dai dai lokacin kwanciya baccin fadeela sannan ta shirya ta fita don tayi mata shirin bacci,aikin kulawar ya rage mata sosai tunda ko yaushe nadeeya na kula mata da ita koda bata a kusa. Qaramin hijab ta zura ta fito a dakin.

Kasancewar qofar dakin bata kammala rufewa ba tun bata gama shiga ba ta fahimci video call sukeyi,duka ita da fadeelan na samon gado sunyi rub da ciki,sun sanya system din nadeeya din a gaba suna faman surutu.

*HUGUMA*

*_TABARMAR KASHI_*

67

“‘yauwa maji….gata nan” nadeeya ta fada

tana murmushi idanunta akan fuskar sãahar.

Tsarguwa kawai tayi,tasan hirarta akeyi

kenan batasan itakam wanne irin gauna

nadeeya da fadeela ke mata ba da basa gajiya

da ambatonta ba a duk wurin da suka zauna

ba

“Marhaban da ita‚ta qaraso mu gaisa” wata

nutsatsiyar murya dake dauke da accent na

arabic ya fidda amon maganar.

Bata da wani zabi,tunda taji abinda ta

fada,uwa uba sunan maji ba bago bane a kunnuwanta,suna ne da a galla tana jinsa daga bakin nadeeya da fadeela yafi sau uku a rana.

A nutse ta taka zuwa gefan gadon,nadeeya ta zauna sosai tana juyar mata da fuskar system

din zuwa tata fuskar

“Ma sha Allah, intee jameela” murmushi sãahar ta danyi,tana dan sadda da kanta daga kallon tata kyakkyawar fuskar,fuskar da shekaru suka fara bayyana samanta,amma kuma bisa dukkan alamu kyakkyawar kulawa da ingatacciyar rayuwar da take ciki bai bar tsufa ya bayyana ba. Wani irin kyau me daukan hankali wanda dukka kamanninta sune tsaf bisa fuskar nadeeya a yanzu

“Ki dayra,wesh wella famille?” Ta tambayeta da tantagaryar labarancin larabawan Algeria

“Maii namu larabcin fa ba irin naku bane”

nadeeya tayi magana da shagwabar da sãahar

bata taba gani tayi ba

“Ya salam, ina mantawa ne,kina lafiya? ya kuma iyalinki?” Murmushi ta sake

“Alhamdulillah, da fatan kina lafiya”

“Alhamdulillah, Allah yayi albarka,naji dadin ganinki,na san sunanki da kyau,amma bansan fuskarki ba” maii ta fadi mayalwacin murmushin dake dauke da nutsuwarta ta halitta na fita a fuskarta. Har qasan zuciyarta tana jin dadin yadda idanunta ke iya hango sauyi daga jikartata,fadeela rayuwarta ce,tana mata wani irin so da zata iya cewa soyayyar da takewa toufeeq da nadeeya ce tayi tsuntsuwa ta koma kanta,fadeela ita daya ce makamin data tabbatar a yanzun dukkan maqiyinta dake Nigeria zai iya amfani dashi ya cutatar da ita,cutarwar kuma ta risketa kai tsaye har gasarta Algeria. Cikin dabara ta sulale ta wuce wardrobe din fadeela tana fidda mata kayan bacci,saidai hakan bai hanata jin wasu hirarrakin nasu sama sama,duk da bata dora hankalinta a kai ba.

Tana fita daga closet din taji an daneta an riqeta qam qam,kafin tace komai muryar fadeela ta ratsata

“Albishir dinki aunty nanny” dariya taso kubce mata,saboda yadda tayi hausar ma kanaji kasan ba iya karin maganar tayi ba,saita zura hannu ta kamota ta dawo da ita gabanta

“Wannan hausa taki….to ba laifi goro”

“Ni bana cin goro,amma dai..

.. ki tayani

murna,am very happy today,

next week abby zai dawo” sai ta qyalgyale da dariya tana nuna zallar murnarta. Da kyau sãahar ta kama hannuwan fadeela cikin nata tana tayata murmushin,duk da hakanan taji zuciyarta ta harba ba tare da wani dalili ba

“Am so happy nima fadee,congratulations” rungume sãahar din tayi,itama sai ta buda hannayenta ta sanyata sosai a jikinta tana tayata murnar.

*******Cikin kwanakin gaba daya shire shiryen dawowarsa akeyi cikin gidan,nadeeya gaba daya ta kasa zama,ita da fadeelan batasan waye yafi wani murna da zumudi ba,itadai ‘yar kallo ce,amma kusan kullum sai an fita shopping na dawowar abbyn fadeela.

Tun tana janye jiki har nadeeya ta sakata tsundum a harkar,tunda ta fahimci sãahar din ta iya mota ta hanata sukuni,duk inda zasu saita marairaice mata akan tayi drive nasu

Zuwa gurin,hakanan ba yadda ta iya take karba su tafi.

Sai a sannan ra fahimci siyayyar da suke fita sukeyi,a nata gurin tsabar son yawo ne irin na nadeeya,qananun kayayyakin amfani dake sashensa ake canzawa,abinda taji hajiya qarama na cewa nadeeyan tayi magana da company suzo su sauya masa komai kamar yadda aka saba,amma son yawo dai yasa tace da kanta zata siyo komai. Duk da ko sau daya bata taba takawa sassan sa ba,amma bataga wani abu daya baci ko ya lalace da za’a sauyashi ba. Kamar nadeeya tasan me take tunani, ranar suna tafe cikin ShopRite tana zaban wasu turarukan daki na ruwa masi shegen tsada,ta dan ja tsaki kadan ta waiwayo tana duban sãahar dake amsa wayar afifa

“Aunty N,don Allah tayani zaben turarukan nan mana,yaa toufeeq akwai shi da taste a zabi inason kome na siyo ya zama unique” zare wayar taki daga kunnenta tana duban nadeeya,duk lokacin data ambaci sunan

TOUFEEQ sai taji gabanta ya fadi,ranta kuma ya baci

“Basu isa bane haka sis nadeeya?” Ido tadan fidda

“Da saura,indai yaa ya dawo daga tafiya muddin ya wuce one month yakai two to sai an canza masa irin wadan nan kayayvakin” batace komai ba sukayi sallama da afifa,ta tako gurin zuciyarta na tuna mata maganganun da sukayi da afifa yanzu akan mahmud. Ta fuskanci ta garfi da yaji mahmud din yakeson kafa kanshi a gidansu tare da maida kansa dan gida,to amma zata gani indai ana siyan so a dole.

Sosai ta nutsu ta zaba wasu kalolin, wadanda ita kanta nadeeya sai data yaba

“Wow,gaskiya u are the best selector” murmushi ya qwacewa saahar din,saita koma gefe tana jiran su kammala.

Tana ganin yadda suka koma zaben kayan da zasu saka ranar da abby din zai dawo, nadeeyan tayi tayi tazo ta zaba itama,saita girgiza musu kai alamun a’ah,fadeela ta marairaice kamar zata saki kuka,ta rige hannunta kam

“‘Please anty N”ta fada itama kamar yadda taji nadeeya ta koma ce mata

“Okay,kije ki zabarmin fadee na,koma meye i will accept it” da haka ta samu ta barta,bayan sun kammala kuwa sai gasu da leda wai duka kayanta ne na tarar abby

“Wai wai,sis nadee, thank you, amma kayan is too much gaskiya” murmushi ta sake

“‘Wallahi Allah ko?” Ta fada tana duban sãahar

“Ina jinki ne kamar wadda muka fito ciki daya da ita,banajin banbanci tsakaninki da yaa toufeeq “

ambatar sunan ya sake sanyata lumshe idanu sannan kuma ta budesu, Allah ya sani bata qaunar jin sunan sam,saidai don babu yadda zatayi,shi daya ne tal ambaton sunansa yake sanyata jin faduwar gaba.

A falonsu na biyu ta barsu baaba ramatu tana tayasu duba siyayyar ta shige dakinta ta watsa ruwa,sannan ta wuce kitchen don ta samar musu da abinda zasuci,saboda fafur sukaqi girkin zuwaira,sal ya zamana ita ke musu girki su hudun,nadeeya fadeela ita sai baaba ramatu. Ta sauya musu abinci sosai,daga girke girken fararen fara zuwa abinciccikan hausawa da abincin yaran maamanta wato buzaye,sai na yaren abbanta wato shuwa,duk da har yanzun bata tantance yarensu ba su din, amma kana kallonsu kasan babu ta inda suka hada Jini da HAUSA banda yaren dake bakinsu,a ido kuma sai ka rantse zo na kasheka da hausan basu sani ba. Ita dinma mutane da yawa kallon da suke mata kenan.

Tun a ranar suka gama tsara bin guard airport su taho da abbyn fadeelan, harda sunanta suka jefa a ciki, murmushi tayi can qasan zuciyarta tace “Saboda gayyar sodi” amma a zahiri batace dasu dai komai ba,ita haka kawai take jin dama me gidan da suketa zumudin dawowar tasa zaiyi zamansa a can,cikin gidan yaci gaba da kasancewa iya yasu yasu mata.

********Ana gobe zai dawo nadeeya ta hanata sakat,duk da yana da cook dinsa permanent da yake masa girke girke tare da tanadar dukkan abinda yakeso,qwararren cook daya qware waien sarrafa nau’ikan abinci,cook din da ake biya da kudade masu nauyi,samfurin albashin wani ma’aikacin na wata guda……amma duk da haka nadeeya sai data shirya nata dafe dafen

“Yaa moha ya jima baici abinci na ba,zan bashi mamaki wannan karon,zaiji canjin taste” yadda nadeeya keta sanyata a abubuwa tana zugewa yasa a wannan gabar don kada taji babu dadi ta karba ragamar yin fried rice.

Saidai kuma a daddafe ta gama hada kayan bugata ta ajiye,saboda wani ciwon kai da ya saukar mata lokaci guda,sauqin abun taji suna maganar evening flight ne,sai tasa a ranta zuwa goben xata warware in sha Allah. Ba wanda ta gayawa a cikinsu don kada su sanya damuwarsu a kanta,ta kawowa walwala da farincikin da suke ciki naqasu,sai ta wuce daki kawai ta kwanta abinta.

Washegari ta kammala komai akan lokaci,duk da har lokacin tana dannewa ne kawai amma bata dawo dai dai ba,tana gamawa ko wanka bata iyayi ba ta koma gado ta nade tana sauke numfashin,sauqin abu daya tana fashin sallah,a haka bacci yayi nasarar daukarta.

Da zumudinta fadeela data gama shirinta tsaf ta shigo dakin,tana tsammanin ganin sãahar ta shirya,sai ta sameta akwance tana bacci, zuciyarta a karye fuska a jagale ta koma falon

“Ta gama shiryawa?” Nadeeya ta tambayi fadeelan tana qoqarin cire wayarta daga chargy

“Sister nadeeya,bacci ma fa anty N din takeyi”

“Bana tunanin lafiya qalau take gaskiya, kamar na fahimci bata da lafiya” baaba ramatu ta fada fuskarta na nuna alhini. Take damuwa ta bayyana saman fuskarsu gaba daya

“Rabu da ita fadeela muje,may be ma jiyan bata samu isashen bacci ba.na fuskanci kamar tana da zurfin ciki”

“Alamu sun nuna kam” baaba ramatu ta maidawa nadeeya amsa sai suka fice baaba ramatun na rakasu da addu’a. Har sai da suka garasa ficewa ta dauke idanunta tana girgiza kai sai wasu qwalla masu dumi suka biyo kuncinta,ta saka gefan yalwataccen mayafin jikinta ta goge sannan taci gaba da abinda takeyi cikin falon.

*******Cikin tarin nutsuwa kamewa da kuma kwarjinin nan nashi yake saukowa daga cikin jirgin tare da jerin matafiya da suke jerin first class.

Ba abinda zaka fara hangowa sai

kyakkyawar farar fatarsa din nan me surkin ja ja,wadda bata cika wani fari me yawa sosai ba saboda surkin jaa din da take dashi.

Sanye yake da button up shirt me dogon hannu cream color dake da maballai gun metal color hakanan slim fit trouser din jikinsa me sulbi ya kasance kalar button din rigar tasa,wasu lafiyayyun loafers ne a gafarsa kalar trouser din jikinsa,nannunsa daure da tsadajjen agogon rolex daya fito sosai sakamakon tattare dogon hannun rigar tasa da yayi kadan ya rage yakai gwiwar hannunsa.

Kwantacciyar sumarsa da tasha gyara take a kwance luf cikin wani tsari da gyara me daukan hankali sai glowing takeyi,hakanan eye glasses din da yayi amfani dashi ya sake fidda kyawawan qwayoyin idanunsa dake da wani yawa.

Ko sau daya bata daga qafa ba wajen sauke tata gafara a duk inda ya ajjiye tasa ba,tana yi tana shagar qamshin lallausan turarensa daya zama abu na farko da ya fara jan hankalinta game dashi,duk bayan wucewar kowacce daqiqa sai taji kamar zuciyarta zata narka a kansa, tsahon awannin da suka dauka kadai a jirgin a tare tana jin kamar zata zauce a kansa,duk da cewa ko kalmar ZO bata hadasu ba,hasalima bata zaton ya ganta. Tana yawan ganinsa a shafukan MEENAL YA’AQOUB

AJI,amma batasan cewa hotuna rage masa kyau da kwarjini sukeyi ba sai yanzu data ganshi physically

“Hi mr man” ta fadi tana dan qara sauri don ta cimmasa,ganin baiko san tana biye dashi ba. Wani faduwa gabanta yayi lokacin da ya waiwayo ya zube mata idanun nan nasa dake da wani irin kwariini da maganadisu “How can I help you?” Kalmar sai tayi mata nauyi,taji kuma ta muzanta,abinda yasa tadan diririce kadan kenan,tayi gyaran murya sanda yake juyawa zaici gaba da tafiya ganin bata da abin cewa

“Mmmm….. ammm,kamar nasan fuskar nan taka,idan ba damuwa….may i get your phone number?” Wani irin haushi da takaici ne ya kamashi,ya tsaya cak har ta cimmasa,ya waiwayo yana dubanta

“What amount do you need?” Hannayenta ta harde a girjinta,tana dan ware idanunta kadan akan fuskar sa,cikin zuciyarta tana jin wannan din dama ce me kyau a gareta,don haka ta saki murmushi kadan

“Five hundred thousand to one million” waiwayawa yayi yana duban jibril,hannunsa daya a aljihun trouser dinsa

“A bata” va dawo da dubansa gareta

“Wannan va zama shine lokaci na farko kuma na garshe da zaki yarda magana ta sake hadamu” daqa haka ta kewayeta yayi gaba cikin qasaitaccen takun nan nasa,ransa yana sake baci,zuciyarsa na motsuwa,yana in tsanar mata da halinsu gaba daya,ya gama yarda kudi yana gaba da komai a wajensu!,kuma tabbas zasu iya aikata komai akan kudi. Yaja tsaki har baisan adadi ba,zuciyarsa na sake quntata a duk inda ya gifta ya tsinci idanuwansu suna binsa da kallo duk da bawai kallon nasu yakeyi ba,amma yana ji a jikinsa, kyakkyawar fuskar yarinyar na dawo masa

“Ya tsani mace me kyau,hadari ce,ya yadda da wannan” ya sake jaddada maganar can qasan zuciyarsa.

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

68

Tun daga nesa da ya hangi angel dinsa bacin ran ya fara narkewa,saidai wannan miskilar fuskar tasa na nan a hade,murmushi bai kubce mata ba sai da yayi hugging fadeelan,wani sanyi da nutsuwar ruhi na saukar masa,hancinsa ya zuqi daddadan turaren sãahar da take amfani dashi,qamshin ya cika masa zuciyarsa da kwanyarsa gaba daya. Zamewa tayi sannan ta duga har qasa tana gaidashi tare da yi masa maraba da zuwa,sosai murmushi ya wadaci fuskarsa,yasa hannu ya kamota yana amsawa da lallausar muryarsa dake nuna zallar gaunar diyar tasa “Waye ya koya miki angel?” Murmushi ta saki

“Anty N”

“she taught her a lot” nadeeya dake tsaye tana dubansu ta qara masa haske ita kanta tana jin alfahari da sãahar din.

Miqewa yayi tsaye yana kallon nadeeyan,fuskarsa a dan hade,saita langabe kai tana dubansa,abinda yasa ya zare hannunsa daga aljihun wandonsa ya miqa mata,dariya ta kubce mata itama ta bashi sukayi musabaha, she’s very proud with him,ta yarda yayanta miskili ne na qarshe,yana da wuyar sha’ani wasu lokutan,musamman idan kayi masa bahaguwar fahimta,amma kuma mutum ne me tsananin kula da damuwa da duk wanda yake alhakin hakan yana rataye a kansa,a yanzun tasan fushi yakeson ya gara nuna mata,amma ta karya lagonsa. Haka suka jera su uku,sun sanyashi a tsakiya,yana riqe da hannun kowa a cikinsu sun baibayeshi da surutu. Duk da rashin son magana da hayaniya irin nashi amma yana qoqarin bawa kowa hankalinsa,har suka isa inda motocinsa suke jiransa,daga daga cikinsu BMW sabuwar qirar shekarar Jason ya bude musu suka shiga ya maida murfin ya rufe.

Har yanxu hannunsa na cikin na fadeela yana mamakin yadda tayi kumari,ta ciko sosai ta murie, ta gara haske gashinta ya qara kyau da tsaho,komai nata ya canza sosai

“Abby baka tambayi anty N ba….bata jin dadi,tana bacci ma muka fito, sister nadeeya tace a ayaleta wai” saita karyar da kanta gefe bayan ta gama bashi labarin. Kanta da tun jiya sãahar ta gyareshi tsaf ya shafa

“That’s right ‚ku barta ta huta,she will be okay in sha Allah” sai ta magaleshi da kyau tana murmushin jin dadi.

“ya kamata ayi doubling salary dinta ko?” Yayi

maganar yana duban fuskokinsu. Murmushi

nadeeya tayi tana gyada kai

“Yaa salary din da har yau ba’a taba karbarsa

ba?”

“Like how?, Ya mata kadan ne?” Kai nadeeya ta

girgiza

“Bana tunanin haka,tunda mommy qarama ma

kafin tayi tafiya last week naji tana tambayarta

tana bugatar qari ne da taqi karbar salary

dinta? amsar dai kawai No ce,tace bata bugata

ne a yanzun,tafi sha’awar kula da fadeela

kyauta,wannan ya qaramin qaunarta da ganin

girmanta sosai yaaya” ta qarashe maganar

tana kallon fuskarsa. Shuru yayi yana juya

maganar nadeeya a ransa,zuciyarsa sai yaji

sam bata aminta da tsarin ba

“She must collet her salary,coz banga muhallin kulawa da ita a kyauta ba,we can afford all her needs da abinda muka mallaka,basai anyi mana aiki kyauta ba” dan murmushi kadan nadeeya tayi,ta karanci har yanzu akwai wannan zafin cikin ransa bai gushe ba

“Kyautatawa ce fa yaya” waiwayo yayi ya kalleta,kamar zaice wani abu sai kuma ya fasa ya maida hankalinsa ga hanya,cikin ransa da zuciyarsa ya soke tsammani ko ganin kyautatawa daga dukkan wata macace muddin ba wadan nan jinin nasa ba.

Kamar ko wanne lokaci idan ya dawo tafiya irin haka,yakan dauki wasu mintuna a farfajiyar gidan,saboda dukka ma’aikatan gidan masu masa barka da dawowa,ya bincika wasu abubuwan ya tabbatar komai haqqinsa ne ya sansu sannan ya wuce ciki nadeeya jibril da fadeela na biye dashi. Jibril ya ajjiye duk wani abu daya danganceshi ya sallami jibril din don shima yaje gida ya huta,su elyas zasu kasance dashi nadeeva ma sai ta wuce sashensu don ta kammala masa komai don yace abinci zai fara ci,yau kam tace nasu zaici,tacewa jacon yau duk abincin daya shiryawa ogan nasa saidai yayi haquri,yana dariya kasancewarsa me saugin kai, kuma yasan barkwancin nadeeya yace babu komai

“Amma madam,ya za’a yi da abincin?”

“Kaie dashi kuci kai dasu Jason kafin su wuce” cikin farinciki ya dinga juye musu abincin yana fita dasu,duk da cewa dukkan wani dake aiki a qarqashin gidan yafi qarfin ci sha da kuma suttura masu kyau,toufeeq yana daga parlor dinsa yana jinsu,baice komai ba,amma kuma zaiga wacce rigima ce ta sanya nadeeva bayar da kyautar abincinsa bayan yunwar da yakeji,kuma tasan baya son missing abincin

Jacob din,ya yarda dashi da girkinsa,expert ne sosai ta wannan fannin,shi yasa salary dinsa yake na daban. Sai daya sallami fadeela da wasu daga cikin tsarabarta dole saboda yadda ta matsa masa ta bashi guri ya samu ya shige bedroom dinsa din ya watsa ruwa kafin ya zauna cin abincin.

Kowa taqi kulawa a gidan da tarin kayan wasanta da bata gajiya da tara shirginsu,ta wuce kai tsaye dakin säahar.

A nutse ta maida murfin gofar ta rufe,ta qarasa gefan gadon ta ajiye kayan tana kiran sunanta,ganin bata motsa ba sai ta haye saman gadon tana janye duvet din data qudundune a ciki

“Anty N,abby is back,kinga abinda ya siyamin,yace sai ya huta zai daukomin sauran” wata miqa tayi tana jin dukka jikinta yana mata ciwo,dole ta yaye bargon ta miqe ta zauna tana karbar kayan wasan.

Kusan dukka basuyi mata ba,saboda yanayin lafiyar fadeela da take kiyayewa,ta zabe wadanda basuyi ba a ciki tace mata

“Wannan ki ragesu ki ajjiyesu ba yanzu zakiyi amfani dasu ba,saikin qara samun lafiya da kyau soon in sha Allah” kayan tabi da kallo,da alama tanason kayan,to amma tana bin maganar sãahar qwarai,duk yadda tace mata tayi abu ko ta bari tofa zata bi ne. Dole ta miqe suka wuce dakin fadeelan,ta tayata jera na jerawa,sannan ta dawo dakinta ta sauya pad dinta,ta daura alwala yadda zataji dadin jikinta ta fito parlor dinsu.

Da baaba ramatu da nadeeya duka suna kitchen suna kacaniyar hada komai yadda zai dace da tsarinsa,a can ta taddasu

“Yauwa anty N,yanzu nake shirin shiga naga ilkin naki”

“Karki damu,alhmdlh,naji sauqi” ta fada tana karbar shirya abincin,nadeeya ta koma baya tana kallonta,har ta kammala shirya komai tsaf,cikin burgewa nadeeyan ta kasa shuru

“Wow.ma sha Allah,anty N,anya ba catering kikayi ba?” Murmushi ya qwace saman fuskarta data dan canza kadan saboda baccin

da tayi

“Aikin maama na ne da anty farheen”

“Nice name” nadeeya ta sake fada tana

murmushi, zuciyarta kuma na mata kokwanto

akan sãahar. Kota wanne bangare a waye take

matuqa,kuma ta iya komai fiye da yadda ita

din zatayi,ta zarta a abubuwa da yawa,bataga

wata alama ta bugatar yin aikin nanny ba sam tattare da ita, komai nata na nuna wayewarta

da zurfin iliminta,to amma she’s very kind,suna

in dadin zama da ita dukkansu,sai sukejin

kamar wani gibi ne dake cikin rayuwarsu aka

cike musu shi da ita,she’s nice person,batason

tayi mata wata tambaya da zata bata mata

rai,ko tayi silar da zata tafi ta barsu.

Ba yadda nadeeya bata juya ba akan

tazo suje su gaisa da abby din koda ba zata

zauna cikinsu suci abinci ba ta girgiza kai

“Saurin me kikeyi sister nadeeya? munafa gida daya,kuma yau yau ya dawo shima,yana bugatar ya samu isashen lokaci daku,zamu gaisa ne” da haka ta doje tayi zamanta kitchen tare da baaba ramatu dake shirye shiryen yi musu tuwo yau,hakan ya yiwa sãahar dadi,don ita kanta tayi missing dinsa kwana biyu

“Yadda kike maqalewa wannan bagin abun,ban zaci kina iya cin tuwo ba ai” baaba ramatu ta tsokaneta sanda take kunna gas tana dora ruwan tuwon a tukunya. Janye coffee din tayi daga bakinta tana murmushi

“Inaci sosai baaba,tuwo abincine me sirri al a cikinsa”

“Tabbas,amma mutan gidan nan basu sani ba,zuwanki yasa fadeela ta fara ci,amma ada idan nayi saidai naci abina ni kadai,ya kamata ki rage shan wannan bagin abun ko zakiyi kumari” murmushi ta sakeyi

“Na iya kalolin tea baaba,amma nafi jin dadin wannan din,kamar wata jarrabawa” baki ta tabe tana murmushi

“Jarrabawar ne ma,dake da baban fadeela bansan wanda yafi wani ba” a wannan gabar batace komai ba,sai taci gaba da sipping coffee din har ta kammala ta kamawa baaba ramatu wani aikin,daga bisani da zuwaira ta shigo saita sakar musu,ta dauki wayarta

kuma.

Karo na uku nadeeya ta iso masa da coffee din cikin wasu qawatattun kofuna da butarsu a tsakiya masu ruwan gold,bakinta dauke da addu’ar Allah yasa wannan ya zama na garshe.

Sai daya balla mata harara sannan ya sauki qaramin cup din butar yakai bakinsa,kurba yayi ya hadiye,sannan ya dago dubansa yana kallonta bayan ya dora cup din saman tray din

“the taste is still not good,lemme ask you” ya fada yana ritsata da idanunsa da gwara yasa bulala ya zaneta akan irin wannan kallon nasa

“Don kinje karatu sai kika daina girki gaki yar gata?,wanne mutum zaki jewa a haka kuma kice sunanki mace?” Owalla ce ta cika mata ido,shifa yaa toufeeq damuwarta dashi kenan,akan tsafta da girki yanzun nan za’a ji kanku dashi,sannan baima tsaya yaga abinda ta dafa masa ba iarabar shan coffe dinsa ya motsa masa yace shi zai fara sha,ita sam ba ruwanta da wani coffee,bai dameta ba,shi yasa ma bata damu da iya hadashi yadda ya kamata ba

“Am sorry yaa,nifa coffee kasan am not a big fan of it” sake wurga mata harara yayi

“C’mon,come and serve me” yayi furucin yana duban siriryar wayarsa da yakeson maido network din gasar nan.

Sai data gama serving nasa din sannan ta mige da sauri,

“Ina zuwa yaaya” yasan bita da kallo,baice komai ba yaci gaba da danna wayar tasa yana jiran Jacob yazo ya hada masa coffe din har ta

fice.

Da kadan kadan qamshin shinkafar yake shigar masa hanciwani irin aroma da yasan bana Nigeria bane,tun baiyi niyyar kallon abincin ba har ya maida dubansa kai kallon farko girkin yaja hankalinsa,sai ya maida dubansa ga wayar yadan qara hanzarin don ya kammala abinda yakeyi din ya taba abincin yaji ko ya dace da taste dinsa.

Da sallama cikin hanzari ta isa kitchen

din

“Madam coffee, zan samu coffee?” Ta tambaya sãahar dake goga kubewa a grinder

“Yau kuma sister, lafiya?”

“Me zanyi da wannan bagin abun naku” ta fadi tana dariya cikin salon tsokana

“Yaa moha ne zai sha”

“Eheenn,kinji ko?,yanzu na gama zancan,itama yanzu ta gama sha,Allah dai ya taqaita muku” cewar baaba ramatu,nadeeya ta tayata da

“Ameen dai baaba” murmushi kawai tayi ba tare da tace musu komai ba,ta matsa gaban mini coffee maker din ta juye masa sauran ta hada a wani madaidaicin vacuum tumbler me rige zafi ta miga mata

“Yauwa,thank you anty N,nasan zaiyi dadi duk da bansan dadinsa ba,amma qamshin was so perfect” ciki jin dadi ta juya ta fice.

Yana gama aikin da zaiyi din Jacob na isowa da coffee din,ya rusuna cikin girmamawa ya ajjiye masa

“Thank you” yace da Jacob,wanda sosai yakejin nauyinsa idan ya gode masa bayan ya masa hidima,shi a ganinsa shi ya cancanci yayita gode masa har qarshen rayuwarsa,sai

Jacob din ya juya yana barin wajen bayan ya gyarawa fadeela kujerarta wadda ta bada hankalinta dari bisa dari akan game din da takeyi a sabuwar game din daya hado mata a kayanta

“Ajjiye kici abinci angel” ya fadi yana qoqarin bude coffee din

“Da anty N yanzu nakeci abby,kuma ma na goshi,ta bani abinci sosai kafin mu tafi airport” idonsa ya lumshe yana qara jin dadin yadda alamu ke nuna irin tsantsar kulawar da take samu.

Ya sake yunqurawa zai bude nadeeya ta iso,kai tsaye ta dora tumbler din saman table din tana murmushi

“Here’s your coffe yaaya” duban kyakkyawan tumbler din yayi sannan ya maida kallonsa ga fuskarta

“Daga ina?”

“Kasha kaji yaya,i assure zakaji dadinsa sosai”

“Thanks ajjiye a nan” sai ya maida hankali yana bude wanda Jacob ya kawo masa,ganin hakan ya sanya cikin sauri ta bude masa natan,wanda ta rigashi budewar,take tururinsa da qamshinsa suka cika wajen,qamshin da yaja hankalinsa,ya kuma binne na Jacob har baka iya jin scent din nasan.

Tura masa gabansa tayi tana marairaicewa,hakanan yasa hannu ya dauka, yakai bakinsa yayi sipping. Sam baisan yana lumshe idanu ba,baisan ma sosai yake sha ba har sai daya daga tumbler din yaji ba komai,sai yaji yayi saurin qarewa,nadeeya na gefe cikin jin dadin yadda ya shanye din tas ba tare da yayi qorafi ba,sai kawai ta tura masa plate din abincin,wannan karon baiyi musu ba ya dauki spoon din ya fara ci.

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

69

Tunda ya fara ci din baice komai

ba,cikinsa kawai yake kaiwa,wani dadi da

gardin abincin yana ratsa kunnensa da

kyau,zai iya cewa ya manta rabon da ya

dorawa harshensa abinci me dandano irin

wannan,cike da qamshin ganyayyaki da spices

masu gara lafiya da qamsasa abinci.

“it’s delicious ko abby?” Fadeela dake leqen

idonsa ta fada,kai ya gyada kawai

“Anty N ce ta dafa fa,ta iya abinci sosai”

dakatawa yayi da cin abincin,ya maida

dubansa ga nadeeya

“how a nanny turn to a cook?” Cikin gogarin daidata kanta ta masa gamsashen bayani ganin yadda ya hade rai nadeeya tace

“Tafi kowa iya girki a gidan nan,ka tambaya fadeela,coffe din nan ma ita ta hadashi” ransa yadan baci kadan,saboda ba’a kowanne hannu yakeson yaci abinci ba

“Amma…..you know my rules?”

“Am sorry yaaya,ta fimu tsafta da komai da kimai Allah i swear” shuru ya danyi,sai ya ture abincin ya balle gorar ruwa ya zuba a cup ya fara sha.

Ranar har dare suna tare har sai da sãahar ta kira nadeeya a waya fadeela tazo tayi mata shirin bacci

“Kizo ku gaisa saiki dauketa please anty N”

“Sorry nadeeya,ina uzurine ta nan haka,ki daure ki kawomin ita”

“Okay” ta amsa mata tana kashe wayar.

Basu jima ba suka snigo fadeela rungume dia ledojin tarin tarkacenta na cive ciye da wasa,daya hannun nata wata ledar ce, wadda ta tuburewa abby din nata sai daya bawa anty N din tata kyautar doguwar riga,sai wani designer din turare wanda zahirin gaskiya nashine na qashin kansa da yake amfani dashi wasu lokutan ya siyosu don ya ajjiye fadeela ta sanya rigima,to be honest baison sharing personal abubuwansa da mutane,amma fadeela ta daukarma anty N dinta.

Sai data gama shiryata tsaf ta gudu gurin abby din nata tace yau a can zata kwana,ta dawo ta gama shirin nata baccin sannan ta zazzage ledar. Komai na ciki ya dauki hankalinta sosai da sosai,daga turaren har doguwar rigar, kana kallonsu kasan na musamman ne,tayi murmushi tana sake in gaunar fadeelan da yadda itama take sonta,ta yiwa kayan guri ta kwanta.

********Kamar kowacce safiya bayan alfir ya gama ketowa,yayi dukka azkar dinsa da addu’o’in sa,gym yake shiga wanda a nan hantsi yake riskarsa.

Guri ne dake cike da dukka qarafuna da nau’in kayayyakin motsa jiki,wajen yana da girma sosai, kuma an masa tsari me kyau,kamar ba cikin gida aka yishi ba,kai kace daya daga cikin ire iren guraren motsa jiki na alfarma da aka gina ne domin neman kudi.

Farare qal din sport wear ne a jlkinsa na kamfanin LULULEMON ATHLETICA,da suka fidda qirar jikinsa qwarai,shafaffen cikinsa dake da wani irin tattarar muscles,singalilin qafafunsa dake dauke da gargasa,a tsaye suke kyam suma da alama naman gurin ya saba da zallar gudu da motsa jiki,dantsensa da hannun rigar ya kamashi tsam shima,ya hada zufa sosai amma hakan bai sanya ya rage gudun treadmill machine din ba.

Sai daya gama iya lokutan daya saba yi din sannan ya tsaida treadmill din, vana furzar da iska daga bakinsa yana dan fidda numfashi me kauri ya sauko,ya dauki water bottle dinsa ya bude ya kafa kai yana shan ruwa. Sai daya kusan shanyeshi ya ajiye bottle din,ya zari qaramin towel din dake ajjiye musamman a guri daban yana goge zufar. Ba abinda bakinsa da zuciyarsa ke marari irin dandanon coffee din jiya,duk yadda yaso ya kauda kai yanzun haqurinsa ya tuqe,a yadda ya gama motsa jikin nan shi kadai jikinsa yake bugata,sai ya tsugunna ya sassauta daurin takalmin qafarsa,ya ajjiye towel din ya fita daga gym room din.

Yana tafe a veranda din da zata kaishi sassansa ma’aikatan da suke da aikin safe suna kawo gaisuwar su,da hannu yafi amsa musu sannan ya wuce cikin tsayayyen takunsa dake nuna zallar lafiya da mazantaka.

A falo ya zare takalmansa,ya zura wasu dake ajjiye a gurin ya qarasa shiga cikin falon,hancinsa na jiye masa qamshin girkin Jacob,mudassir da ya kammala gyaran sashen yana feshe ko ina da wani freshener na musamman dake kashe qwayoyin cuta,kafin ya kunna kowacce humidifier dake aiki a lungu da saqo na sassan,ya rusuna yana gaidashi. Dan dakatawa kadan yayi da tafiyar yana amsa gaisuwar tasa,tare da qoqarin karantarsa

“Ya akayi?” Ya jefa masa tambayar,kansa a qasa yana shafa kan nasa

“Sir, matata ce ke labor tun jiya,amma bata haihu ba,so na barosu ne a asibitin inason tafiya da wuri”

agogo ya kalla sannan ya maida dubansa kansa

“Me yasa kazo aiki?,me yasa baka nema excuse ka tsaya ka kula da amanar da aka baka ba?” Ya fada cikin kaurara murya da alamun fada

“Banason ne..”

“Bakason me?,c’mon,saboda baa jikinka abun yake ba?, maza ka yiwa elyas magana,idan kuma saiiad ya shigo kace nace ya maka sallamar da zata isheka” godiya sosai ya zube yana masa,bai tsaya saurarensa ba ya wuce.

Har yayi gaba ya dakata yace

“idan ta wuce awa daya ka canza mata wani asibitin”

“Yes sir,in sha Allah” daga haka ya wuce hanyar da zata sadashi da hallway. Duk da yanayin da rayuwarsa ta tsinci kanta a ciki amma Allah ya zuba masa masifar tausayin mace me ciki,koda kuwa cikin qarami ne,saboda har yanzu idanuwansa suna iya tuna masa wahalar da maji tayi,tun daga farkon cikin nadeeya har zuwa qarshensa,har yau bai manta ba.

Wannan tunanin ya darsa masa ganin dacewar kiran majin ya gaya mata ya dawo,da wannan qudurin ya shiga dakinsa,saidai kafin yakai ga alkatawa sal ya manta menene ma yace zaiyi din,yakai gauro yakai mari amma ya kasa tunawa,sai kawai ya zare kayan jikinsa ya fada wanka.

Da sallama a bakin nadeeyan ta tura gofar dakin fadeela ta shiga,murmushi ya wadaci fuskarta tana kallonsu

“To bama dole kiyi kumatu ba? don Allah ki gani,da safen nan an tasheki ke daya kina cin kayan dadi ke kadai abinki” dariya kawai suka saka mata

“‘Ke da baki tashi da wuri waye zai rage miki?”

Saahar ta fada tana goge hannun fadeela da tissue. Hamma nadeeya tayi

“Yanzunma wallahi yaa moha ne ya tasheni don Allah coffe zaki taimaka ki bani na kai masa da sauri,kada yace ya fasa sha nayi jinkiri ” kai sãahar ta daga tadan kalli nadeeya tana mamaki a ranta,don anyi jinkiri kawai sai mutum yace ya fasa shan abu?

“Indai sauri kikeyi to yanxun kam sai milk tea wanda na dafawa faddee,babu coffee”

RA

“Ya salam….a zubamin nayi shahada,idan kuma nasha maruka to kin jawomin tare zamuyi jinya” ta fada tana zare ido.

Miqewa sãahar tayi cikin fuskar mamaki

“Maruka kuma? haba dai”

“Allah ba komai bane wajen yaa moha,yaushe ya daina ne? tafiyata karatu fa” maganar sai tadan daure mata kai,to amma batason tsawaitawa tunda ba huruminta bane,don haka fadeelan na biye da ita tana bata labarin tsaurin yaa moha din har suka isa kitchen, itadai tana saurarenta harta gama zuba milk tea din a wani siririn qawataccen silver flask, qamshin flavour din da yakeyi da su cardamom gaba daya ya cika kitchen din

“Yawuna ya tsinke Allah,wannan wanne irin tea ne? don Allah anty N ki ragemin” dariya nadeeyan ta bata,yadda tayi maganar da gaske cikin marairaicewa

“Ya rage miki,bana zaton zai iya shanyewa” dukka ta zaro fararen idanunta waje

“Wa? niii?yaa moha din zance ya ragemin abu?,idan kin ganni a lahira kaini akai” da mamaki ta juyo tana dubanta

“Wanne irin mutum ne shikam haka?”

Abinda takeson cewa kenan,amma saita maida maganarta ta hadiye. Idan ta saba yin hakan da nata yayyun,nan din ai ba gidansu bane,kowa da irin tsarinsa da nasa ra’ayin,so ba huruminta bane.

Yana amsa waya ya fito daga dakinsa,yayi fes cikin wasu fararen kayan still, da alama zabinsa kenan farin abu ko kuma abu me haske,musamman idan ka duba vanavin furniture din dake qawataccen falonsa. Da ido ya tsire tea din har ya kammala wayar,ya kashe ta ya ajjiye wayar a gefe yana hada hannayensa guri daya,kafin ya maida dubansa ga nadeeya

“Me ya hau kanki ne?,wannan yanzu coffee ne?ko dama inashan tea da madara?” Tasan dama tsaf hakan zai iya faruwa,don haka ta sake maida fuskarta kalar tausayi

“Ba wancan yaaya…amma please kasha wannan,idan baiyi ba Allah na rantse, kayimin hukunci”

“Ya isa,Gate out” ya fada calmly,da sassarfa ta juya ta fice tana dafe qirjinta saboda arzigin data auna yau bata shiga ukunsa ba.

Kaman bazai sha ba kamar dai jiya,sai qamshin ya buwayi hancinsa,a daqile ya dauki cup din idanunsa akan TV ya kurba. Kasa wassafa komai yayi a ransa, saboda qamshi da gardin madarar daya kai masa ko ina,karon farko bayan shekaru masu dama ya samu tea din da yafi masa coffe dadi.

_tom,nikam nace tun yanzu MR JARMA?,WAI YA HADUWAR ZATA KAYA NE? KOWA NA YABON DAN UWANSA BA TARE DA YASAN WAYE SHI BA.MUJE ZUWA_

*DON ALFARMAR ANNABI MUHAMMADU

ME FITARWA KIYI HAKURI KIBAR MANA

KAYANMU*

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI *

Page 70

. Baisan ya akayi ba,shidai ya tsinci hannunsa riqe da empty cup,ya maida a hankali ya ajjiye yana tunanin rabonsa da shan madara a tea,sai gashi yanzu ya shanye ta tsaf,har yana jin buqatar qarin wani tea din,to amma bayason ya aika din,zaidai binciki yadda ake sarrafashi.

*********A tsaye suke suna fuskantar juna,duk da cewa ita din bashi take kalla ba hakanan akwai ‘yar tazara a tsakaninsu. Irin kallon da yake mata kadai zai gaya maka zallar yadda zuciyarsa ta narke da soyayyarta

“Zan tafi.don Allah ina roon kici gaba da bani dama”

“Allah ya kiyaye ka gaida gida” ta fada tana

Juyawa,zuciyarta a quntace saboda abubuwa biyu,na farko tasa yasa an tilastata ta bashi damar zuwa zance gidan mutane,taso ta furje amma Dr girema ya kirata da kansa,yayi masa irin fadan da bai taba mata irinsa ba,sannan kuma ya tabbatar mata wa’adin sati biyu kacal ke gareta,ruwanta ta bashi dama ta bude masa zuciyarta ta fadada tunaninta su fahimci juna,ruwanta ne kuma taqi. Maganganun dr sun daga mata hankali sosai,don bai taba mata magana da salon fada da bacin rai irin haka ba.

•Ci gaba da kallonta mahmud yayi har zuwa sanda ta bacewa ganinsa,ya sauke hannunsa yana furzar da iska daga bakinsa,sannan ya juya yana nufar inda gurd dinsa da ya masa rakiya yake. Hakan yayi dai dai da shigowarsa ta qaramar qofar gidan,yana sanye da wani lallausan yadi da aka yiwa dinkin african kaftan na maza,fuskarsa ta cika da wani irin kwarjini,elyas da jibril na biye dashi.

Dawowarsu kenan daga masallacin layinsu wansa aka gudanar sa taro da akanv duk sanda aka samu dama,kusan duk wan ke muqami ko babba a unguwar yana halartar taron. Lokaci guda idanunsu suka sarge ana juna,murmushi mahmud ya saki cikin hanzar ya maida akalarsa zuwa gabansa

“Sir” ya furta yana saluting nashi cikin murmushi,fuskar toufeeg ta motsa kadan alamun murmushin shina yayi, ya migawa mahmud din hannu

“Barka da yamma sir”

“Barka,kana lafiya?”

“Lafiya alhamdulillah,kwana da yawa sir,tun a

Singapore,ban zaci zamu sake haduwa nan kusa ba”

“Gashi Allah ya nufi hakan” ya fadi yana maida hannunsa ga aljihunsa fuskarsa a dan sake ba kamar yadda take ba

“‘Gaskiya ne,ina fatan zamu sake haduwa anan kurkusa”

“In sha Allah” ya fada yana gyada kanshi

“Nazo ne wajen qanwata da kuka riqemin a gidanku”

“A nan din?” Ya fadi cikin mamaki

“Yes sir” ya fada yana waiwaya hadi da

duban inda sãahar ta tsaya a dazun. A ran

toufeeq din ya danji mamaki,me kuma zaya

kawo qanwar mahmud gana gidan?,ko cikin

qawayen nadeeya ne?,shine tunanin da yafi

kwanta masa

“She’s my soulmate,inata qoqarin ganin mun

dai daita ne,she’s my wife to be in sha Allah”

sake daurewa kansa yayi,har ya kalla ainihin

sashen cikin gidan ba tare da ya shirya ba,sai

ya gyada kai yana sake bashi hannu

“Allah ya taimaka” ya fadi ya zame hannunsa

bayan sunyi musabaha yayi ciki.

Dab da zai shiga sashensa nadeeya ta

fito tana laluben sãahar sabida shurun da taji

tun bayan fitarta,tayi masa sannu da zuwa

ya amsa yana tambayar fadeela,sai tace

masa tayi bacci yanzun nan bayan ta gana

jiran dawowarsa,yana wucewa ciki yana gaya mata ta kawo masa cottee nan da kamar awa daya, murmushi ta saki gain yadda ta zama addicted da coffee din nanny,shi da baya cin komai a hannun kowa. Har ya zarta ya dawo da baya yana tambayarta waye yayi bago a gidan?

“Nanny N ce,ko ba mahmud ba?” Kai ya jinjina,sai kuma yayi gaba ba tare da ya sake cewa komai ba,amma can qasan ransa cike yake da mamaki,mahmud ke son nanny din gidansa?,abun sai yaji baiyi making sense ba,so amma shi din ba mai damuwa da shiga rayuwar wasu bane,don haka tun bai isa sashensa ba ya tattara lamarin ya watsar.

Sai daya gama komai ya sauya kayan jikinsa zuwa wata shirt,v neck ne daya fidda sirrin ginannen girjinsa me yawan gargasa,sai dogon wandon joggers pants,qafarsa saye da socks da baya rabo da ita yawancin lokuta.

Farfajiya ce ta musamman da akayi mata gofa daga cikin falonsa, wanda aka qawatata da wasu irin sofas masu retractable canopy a samansu,wanda zasu baka daman zama comfortable kamar kana kan gado,samansu ya zauna yayi relaxing sosai sannan ya kunna system dinsa bayan ya duba lokaci ya tabbatar lokacin da suka sanva don yin meeting dinsu through video call da directors na companies dinsa dake gasashe daban daban lokacin ya cika,ya bude system din ya saita komai sannan yayi group call in general.

Ba jimawa kusan kowa ya daga din,mutanene da sukasan muhimmancin lokaci da kuma na aikinsu,don haka komai suna yinsa ne akan lokacin da aka tsara zaa yi din. Cikin salo da qwarewa da sanin makamar aiki suke tattaunawa,da zallar qwarewa a harshensa na furta kalmomin yaren turanci,a haka suka cinye awa guda cif,wanda basu qara ba kuma basu rage ba aka tsaida taron,suka sanya wani lokacin da zasu sake haduwa su tattauna.

Sake zama yayi saman sosai saman sofa din,yana gyara rumfar dake saman sofa din. A yanzun yana jin aminci da nutsuwa sosai akan kasuwancinsa,dukka directors dinsa amintattu ne,ya tabbatar koda babu shi zasu iya gudanar da kamfanin fiye ma da yadda zaiyi.

Wayarsa ya ciro ya lalubi number nadeeya,bugu daya ta daga

“Yaa gani nan,kana ta baya ne?”

“Yeah be hurry”

“Okay tom” ta amsa masa,tana maida dubanta kan säahar dake hada coffe din zata dora masa

“Don Allah yafi na ko yaushe,zan tambayi wani abune, inaso a bani da wuri,kinsan yaa moha shi da girki two and one ne” murmushi tayi tana girgiza kai,tuni ta fahimci hakan al,yanason laflyayyen abincihakanan baya shiri da yunwa.

Tun kafin ya kashe kiran da ya yiwa nadeeyan yaga kira nata shigowa wayar tasa baisan number din ba bashi da niyyar picking,saidai yana gogarin katse kiran nadeeva din kiran ya shigo ya daga lokaci guda ba tare da ya shirya ba,dai dai lokacin kuma true caller dinsa ya nuna masa sunan me kiran AMEESHA!.

lya sunan kawai ya haifar da wani irin bala’i cikin zuciyarsa,lokacin da sautin muryarta kuma ya baqunci kunnensa sai ya ja fikinsa ya sauko daga saman sofa din yayi tsaye,kowacce jijiya ta jikinsa tana miqewa

“Ina fatan kana lafiya,babu wata doguwar gaisuwa,don na tabbatar ba amsamin zakayi ba…..inason naga ‘yata,inason a bani lokaci nazo na dauketa tayimin hutu,tunda nasan zuwa sati me zuwa zasu fara exam,upper kuma sun gama..

“‘Stop!” Ya tsaidata a tsawace, yanajin wani abu na masa tururi tun daga zuciyarsa zuwa saman fuskarsa

“Lokaci na farko kuma na qarshe da zanyi warning dinki,ki cire a ranki cewa kin taba haihuwa da toufeeq jarma,ki cire a ranki cewa kina da ‘ya a duniya tare dani,wannan shine gargadina gareki” yayi maganar yana nuna gabansa cikin wani irin fushi da deepness a cikin muryarsa

“Ta yaya? ka taba ganin an raba uwa da

‘yarta?,laifin dana aikata tsakanina da ubangiji na ne,so bai shafi alaqata da dangantakata da

‘yata ba,inata kawaici,inata dannewa,ina tsoro da fargabar kiranka,for what! fadeela yata ce, kuma har abada ba’a taba canzawa tuwo suna”

“Idan kin isa ki kusanceta da taqi daya tak!,kiga yadda sunanki zai sauya” ya fada cikin tsawa da matsanancin fada

“Bazan kusanceta a zahiri ba,amma zan kusanceta ta hanyar da duniya zata sake shaidawa diyata ce halak malak’

“Go ahead. karki fasa,zan nuna miki other side dina da baki taba gani ba,stupid idiot” ya fadi yana wurgar da wayaryasa hannunsa ya shafi sumar kansa da qarfi hadi da yarfar da hannunsa.

“Ka dinga yawan ambaton Allah duk sanda zuciyarka ta zafafa” daya daga cikin maganganun maji suka fado masa a ransa,sai ya koma da baya da baya ya zauna gefan sofa din,qafafunsa a qasa,ya lumshe idanunsa yana kiran

“Hasbunallahu wani’imal wakil,wala’udwana illa alazzalimin,ya hayyu ya qayyumu birahmatika astagis, aslih li sha’any kullah,fala takilni ila nafsy darfata ainin” a hankali sai numfashinsa dava fara canzawa sakamakon tuna wace ameesha da tabon da ta barwa rayuwarsa ya fara daidaita.

Duban sãahar data shirya tea din nadeeya tayi

“Don Allah anty N,taimakeni,magana mukeyi me muhimmanci da maji banason ta katse,ki migawa yaa moha din,yana ta baya idan kuma ta falonsa zaki shiga ki tambaya guards zasu saita miki” duban nadeeyan tayi,sai taji ta kasa musanta mata. Ba sau daya ba ba sau biyu ba,a kwanaki goman da yayi da dawowa tana nemanta alfarma taje su gaisa,har ta gaji ta daina,batason taji wani abu a ranta kota dauka wani abune na daban,don haka ta gyada kanta tana gyara yafen dan mayafin pakistani dress din dake kanta,wanda ya lullube asirin sumarta me tsaho cika santsi da kuma laushi,ta juya a hankali tana fita a kitchen din

“Maji tace tanaso yau ku gaisa, wana biyu bataga fuskar diyarta ba,kamar ma tace akwai maganar da zakuyi,zan rige wayar harki dawo”

“Alright” ta fada tana murmushi,haka nan itama Allah ya sanya mata gaunar matar kamar yadda take gaunarta,tana burgeta,tana da wata irin kamala da dattako sosal.

Haka nan takejin gafafunta babu nauyi sanda ta nufi gofar bayan da zata sadata da farfajiyar da yake din, taci gaba da takawa a nutsen,sassanyar iskar dake gurin tana kada turaren iikinta zuwa kowanne sashe na wajen.

Kafin ta garaso ta hangi mutum zaune saman bagar sofa din da aka yiwa farar shimfida,saidai bata iya ganinsa fuskarsa saboda yayi qasa da kansa. Tana sake kusanto gurin tana kasa sarrafa idanunta daga dauke dubanta daqa kansa,cikin jikinta takejin kamar tana dosar wani mutum ne data taba saninsa ko ganinsa,a haka har ya rage saura taqi kadan ta cimmasa,ta bude bakinta da taji ya soma rawa da nufin yin sallama,dai dai lokacin da ya daga fararen manyan idanunsa da suka rune zuwa kalar jaaa.

*HUGUMA*

* TABARMAR KASHI_*

Page 71

Guri guda idanunsu suka hade,wani abu me matugar garfi ya fusgeta,ya kuma ratsata tun daga tsakiyar kanta har zuwa tafin qafafunta,a hankali tray din dake hannunta ya sulale yayi d’ai d’ai a gasa,bata bawa kanta wani option ba da ya wuce juyawa cikin hanzari da sassarfa tana barin gurin.

Ko motsawa baiyi ba daga inda yake zaunen,tamkar an dasa shi a wajen ya bita da kallo harta qule ta bacewa ganinsa. Kaf tunaninsa ya katse ya kuma tsinke,babu abinda ke kai kawo a fuska da kuma zuciyarsa sai fuskarta,his ex president……me takeyi a gidan? wayo ya kawota cikin gidan?. A hankali ya sauke dubansa kan farantin da yayi d’ai d’ai a gurin,komai ya kama gabansa,tunanin da ya darsu a ransa ya sanyashi zaro wayarsa ya sake kiran number nadeeya,bugu daya ta dauka

“Waye kika aiko ya kawomin coffee?”

“Am sorry yaaya,muna magana ne da maii nannyn fadeela ne”

“Nanny?” Ya tambayeta da wani irin murya

“Eh yaa,am sorry ya mohai didn’t intend to offend you” bai tsaya ce mata komai ba ya kashe wayar kawai

“What if itama ta shigo rayuwar su ne ta cutar masa da fadeela?” Shine kawai abinda ya samu zuciyarsa na jaddada masa,dukkan alamu sun nuna she’s not in need bare yace hakan va sanyata aikatau,bata fito daga gidan da suke da qaramin qarfi ba bare yace a buqace take,ko kuma ta cancanci tayi aiki a wani guri, qaramin aiki ma irin wannan, she’s well educated,tana da qualifications din da zata iya samun aiki ako ina Nigeria da waienta,amma sai ta zauna yin aikin nanny?no…ko daya zuciyarsa bata kwanta masa da hakan ba,kai tsaye ya tashi a wajen,ya bulla ta falonsa ya shiga ya dauki wayarsa ya fara neman layin mommy qarama.

Da gyar ta isa dakinta saboda wani irin bugawa da zuciyarta keyi,kamar zata balle qirjinta ta fito ko kuma ta amayota ta baki.

Gefan gado ta samu ta zauna tana maida numfashi,idanunta dukka a rufe,tana ganin shacin inuwarsa ta cikin duhun rufaffun idanunta

“Yaa moha,shine toufeeq? daddyn fadeela? ‚yayan nadeeya?” Ta yiwa kanta da kanta tambayar,wanda motsin fadeela da sunan kiranta da takeyi tun kafin ta shigo dakin ya sanyata bude idanuwan nata,sai ta mige da hanzari ta fada toilet ta maida gofar ta rufe.

Tsaye tayi a jikin gofar tana jin sautin siriryar muryar yarinyar tana kiranta,sai zuciyarta ta gaza jurewa da shurun da tayi mata

“Anty N idan kin fito maji na jiranki” saita sake mata gyaran muryar alamar ta amsa

‘i love you anty” ta fada tana dariya ta fice.

Hawaye masu zafi ne taji sun taru mata a ido,yarinyar ta saba gaya mata wanann kalmar duk sanda ta danyi wasu awanni bata ganta ba,a yanzun data gaya matan sai takeiin kamar furucin da zai shiga tsakaninta da ita kenan na qarshe ita fadeelan ……koda wasa batajin zata iya lamuntar zama gida daya da MT jarma,mutumin da ya wulaqantata,ya tozartata,yaci mutuncinta,mutumin da baisan darajar dan adam ba,sai taji tana jajantawa fadeela,yarinyar batayi sa’ar uba ba sam,ta fito daga tsatson da bai dace da halayyar yarinyar ba.

Wani kuzari ne yazo mata da ya sanyata bude gofar dakin ta fito,ta nufi qofar dakin ta murza mata key sannan ta dawo da sauri ta jawo luggage dinta ta fara zuba kayanta a ciki.

Cikin mintuna galilan ta gama hada dukka kayanta waje guda,dama ba wasu kaya masu yawa take bari cikin gidan ba,tunda kowanne sati tana zuwa gida ta maida wasu ta dauko wasu,ta zari Vail dinta dake saman couch ta nannade kanta zuwa wuyanta,ta jawo luggage din ta bude qofar dakin fa fito.

Tana sako gofarta a hallway din suka bangaji juna ita da nadeeya wadda ga biyota da iPad din ta bata maji din kamar yadda maji ta bugata. Da sauri nadeeya taja baya tana kallonta mamaki kadan na nunawa saman fuskarta

“Ina zuwa haka da akwati da yammar nan?”

Sosai tayi gogarin dadaita muryarta

“Gida zan koma nadeeya” razani ne ya nuna

sosai a fuskarta,sai lokacin ta samu damar

qarewa birkitaccen yanayin sãahar din kallo

“‘Gida kamar vaaya anty N,me ya faru?”

Hannun nadeeya ta laluba ta sanya mata key din dakin a hannunta

“Kuyi haquri,bazan iya ci gaba da zama tare daku ba”

“Me kike cewa säahar? don Allah me

mukayi miki? …baaba ramatu!” Nadeeya ta

gwalawa baaba kira a rude ganin sãahar ta

ja luggage dinta tana barin hallway din zuwa

falonsu,wanda daga shi sai babban falonsu sai

fita daga sashen gaba daya.

Kiran baaba ramatu din da tayi yaja

hankalin fadeela ta fito daga dakin nadeeya

din

“Baaba,wai anty nanny ce kawai ta hada

kayanta wai gida zata koma”

“Subhanallahi,me ya faru?,me akayi mata?”

“Wallahi ban sani ba baaba” nadeeya ta bata

amsa ita da fadeelan suna rige rigen cimmata.

A falon garshe suka tareta har baaba

ramatun

“Haba Khadija,me ya faru haka rana tsaka zaki

ce gida zaki koma”

“‘Ba komai baaba,na ajiye aikin ne” teddy din hannunta fadeela ta yar,ta kama hannun sãahar ta rige tsam

“Don Allah anty karki taft,idan kuma zaki tafin bari na dauko kayana mu tafi tare” zuciyarta ta sosu da yadda taga yarinyar ta rude lokaci daya,sai ta tsugunna a gabanta tana riqe da hannayenta

“Tafiya ta zama dole faddee na,kiyi haquri kinji,babu komai, sister nadeeya tana tare da ke,zata kula da ke,hakama baaba ramatu” saita zame hannun zata miqe,amma fadeelan taqi sakinta,ta fara hawaye tana cewa

“Allah ni bazan zauna bake zanbi”

“Am sorry my faddee” ta fada tana shafa sumarta da ta gama gyara mata ita dazu da azahar,tayi mata ado da wasu pink din ribbons.

Zame hannunta tayi ta soma nufar waje,tana qwararawa kanta gwiwa daga raunin da zuciyarta ke shirin yi,batason ta karaya har taji ba zata iya tafiya ta barsu ba,tanason ta tsira da mutuncinta,wanda ta tabbatar idan tana gidan a qarqashinsa babu inda mutuncinta zaije,tunda har ya nemi take mata kima da martabar ta a muhallin da ba nashi ba….yaya kenan zai faru a yanzun da zata zamanto qarqashin ci da sha da inuwar gidansa?.

Iska me zafi ya furzar daga bakinsa sanda ya gama jin komai daga bakin hajiya garama,zuciyarsa bata nutsu ba,yafi gasgata akwai manufa cikin shigowarta rayuwarsu,don haka zuciyarsa tafi aminta da sallamarta daga gidan,koda ko wanne irin kulawa take bawa fadeelan.

A hankali kunnuwansa suka fara jiyo masa sautin kukan fadeelan,ya mige a nutse yana riqe da wayarsa a aljihunsa,ya kuma tunkari barandarsa ta inda yake iya ganin komai dake faruwa a farfajiyar gidan.

Itace a gaba janye da luggage dinta,fadeela na biye da ita,nadeeya da baaba ramatu kuma suna biye da su cikin hanzari da alama suna nufin dakatar da ita ne,sauran maaikatan gidan kuma sunyi carko carko cikin damuwa,kowa ya kasa aikata komai,saboda basusan maqasudin abinda ke faruwa ba.

Ransa ya sosu da ganin yadda fadeelan ke binta gudu gudu sauri sauri,amma ko sau daya bata tsaya ba bare ta waiwayo ta dubi kukan da takeyi ba

“Fadeela!” Ya kirata a tsawace,abinda bai taba yi ba tsahon rayuwarsu shi da ita.

Dukkansu suka tsaya cak,har saahar din da kiran nasa yayi wata irin tsawa a tsakiyar kanta,ta kuma runtse ido tana fatan Allah ya sanya ba dukan fadeelan zaiyi ba.

A zafafe yake takowa har ya iso gurin

“Tashi ki wuce ciki!” Ya fadi da muguwar tsawar da ta sanya nadeeya ja baya da sauri ta koma bayan baaba ramatu ta boye,saboda a yau din gaba daya a birkice take ganin yaa moha din.

“Abby tafiya zatayi ta barmu,me mukayi mata,don Allah ka bata haquri”

“Ba abinda kukayi mata,ko bata tafi ba daman zan sallameta,saboda bata dace ta rayu daku ba” maganganun nasa sai suka zame mata tamkar zubar dafi tsakiyar naman zuciyarta,tana da muradin ko sau daya ta waiwaya ta sake kallon fadeelan dake kuka iya qarfinta saboda ita kadai,amma kalmarsa ta sanya ta lanqwasa zuciyarta taci gaba da takawa ba tare data waiwayo ba. Tsawar data sake ji ya yiwa fadeela karo na biyu ya sanya qwallar dake magale a idanunta qarasa gangarowa,zuciyarta na kwarara da wata matsananciyar tsanarsa,sai ta qara sauri tana ficewa a gidan,lokacin da ya sanya hannu daya ya dauketa cak ya nufi cikin gidan,ta qwalla garar kiran sunanta full, abinda bata taba yi ba

“Anty saahaaarrrr” kamar zata shide,sai ya dageta ya rungumeta tsam a jikinsa zuciyarsa na wani irin bugawa a mugun jargiy,yana jin kamar ana yankar naman zuciyarsa.

Duk yadda taso riqe qwallarta cikin mota amma abun ya faskara,sai tasa tafukan hannayenta kawai ta lullube fuskarta tana sauke hawaye masu dumi qwarai,ba abinda ke dawo mata cikin kwanyarta sai sautin kukan fadeela da yadda ta qwalla kiran sunanta har zuwa sanda sautin ya dusashe daga kunnuwanta. Sanda suka isa qofar gidansu ta cire kudin ta miqawa me napep,yana fadin

“Hajiya ga canjinki fa” ko waiwayowa bata iyayi ba ta daga masa hannu,ya fuskanci me take nufi sai hau zabga godiya yaja macnine dinsa yayi gaba

Baaba habu ne ya karba mata kayan,yadda yake mata sannu da zuwa yaji batace komai ba sai ilkinsa ya bashi akwai matsala,don haka bai sake cewa komai ba ya migawa jamilu luggage din yace ya garasa mata ciki da ita.

Can gasan magoshinta tayi sallama,falon nasu ba kowa kaman yaushe,yana nan a tsaftace da qamshinsa,da kuma ac dake bada iska me sanyin dadi,sai gamshin sanwar dare dake sirarowa kai tsaye daga kitchen dinsu.

Baaba rabi ce ta fito daga kitchen din sai taci burki tana cewa

“Ah ah,maraba da farar diya,kece yanzun nan akan hanya?” Kai ta gyada muryarta can qasa

“‘Nice baaba rabi,barkanmu da yamma”

“Yauwa barka kadai” daga haka tayi hanyar bedroom dinta tana tambayar maama

“Basu jima da fita ba ita da afifa”

“To yayi” abinda ta fadi kenan ta wuce shige dakin nata.

Saman gadonta ta zube kamar wata kayan wanki tana qoqarin samarwa kanta saugin abinda takeji a zuciyarta,tayi lamo idanunta a rufe tana jin yadda zuciyarta ke gonewa. Inda ace ta san wannan gidan nasa ne,inda tasan ace wannan ahalin nasa ne inda ace tasan wannan diyar tasa ce…..to babu shakka,duk yadda zuciyarta zata kai ga tausayinta ba zata taba rabarsu ba.

Duk iya yadda yake tunanin zai iya lallashinta ko kuma ya bata baki amma abun ya faskara,har ya gaji da lallashin,ya koma bakin window din dakinsa yayi tsaye yana duban farfajiyar gidan, zuciyarsa na masa mugun zafi. Me yasa suna zamansu lafiya suna lallaba rayuwarsu zata shigo ta hargitsasu?,bayajin fadeela ta taba kuka irin wannan,koda kuwa ranar data rabu da mahaifiyar da tayi silar kawota duniya ne. Wai me yasa ne su mata basu da tausayi?,basu da imani?,a duk sanda zuciyoyinsu masu cike da ra’ayoyin qeta da son kai ta mosa musu,tabbas sai sun shiga rayuwar dukkan wanda suka hara sun aiwatar da koma meye sukayi niyya. Bayajin zai saurari kuka ko rigingimun fadeela,zata gaji ta haqura ta bari, dole ta koyi rayuwa babu mutanen da zasu zame mata baraza ko matsala,kamar yadda suka tashi shi da NADEEYA,suka rayu kuma a hakan,babu kuma wani abu da ya canza kalar qaddararsu,gasunan cikin qoshin lafiya da wadatar Allah.

Series Navigation<< Tabarmar Kashi Chapter 5
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *