Gudun Kaddara Part 1 Book 2

This entry is part 1 of 3 in the series gudun kaddara Book 2

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

BOOK 02 PAGE 01

COEUR BRISE(BROKEN HEART)

https://chat.whatsapp.com/Gbut9ibvwWM8JPk0qoMEiZ

“hasbunallahu wani’imal wakil” ama ta sake furtawa a karo na barkatai cikin adadin da batasan yawansa ba na faduwar da gabanta yakeyi. Tun lokacin da motarta ta saitu saman hanya zuciyarta ta fara wani irin tsinkewa da batasan meye dalili ba. Ta laluba tunaninta kaf bata hangi wani abu daya faru ko zai iya faruwa da ita ba,hakan ya sanya ta alaqanta faduwar gaban da sauyin yanayi ko kuma tabuwar sashe na jiki da yakan iya faruwa haka siddan ba tare da wani dalili ba.

Turaren data gama feshe amarya da shi ta sakarwa gwaggon amaryar da suke kira da inna batula duk da ce matan da takeyi ta riqe,amma yawan hayaniya dake wajen da kuma yadda hankalinta taji sam bai kwanta da zama a wajen ba,taji tanason tayi nesa da hayaniyar ya sanya hanakalinta baikai kan abinda inna batula ke fada ba.

Tana sake nesa da wajen tana dan jin relief cikin ranta. Sai ta taka can nesa kadan da wajen da ake gudanar da kamun amarya,inda wasu fararen kujeru ke ajjiye a wajen zaman jiran wanda keda buqatuwar zama a kansu.

Kujera daya taja ta zauna akai tana zare mayafinta dake saqale a kafadarta guda. Light purple veil ne wanda a iya idanu kadai kana iya qiyasin adadin tsadarsa ba tare da ka kai ga tabawa ba. Hannunta tasa ta shafi dogon farin wuyanta da ta yima ado da wata siririyar sarqar gold me matuqar tsari da daukar idanu,duk kuwa da cewa adadin yawan jelar sumar kanta tadan rufe wani sashe na wayar amma hakan bai hana bayyanuwar kyawunta ba. Iska ta furzar daga bakinta,ta zaro wayarta qirar iPhone 15 tana duba lokaci. Dududu basu haura awa hudu da baro gidan ba,amma kuma batasan meye ne yaketa fusgar hanakalinta zuwa gida ba. Sake duba lokaci tayi,ta shirya daga nan ta wuce gurin dinner din ‘yar qawarta ne,kuma qananun mintuna suka rage lokacin ya cika,amma cikin ruhinta sai taji kaman ba zata iya qarasawa can gurin daya bikin ba.

Dafa qasa bibi tayi tana miqewa bayan ta shafa addu’arta

“Kiramin modu maza,gida nakeson komawa,sultana ita kadai kamar mayya,wancan ja’irin ba ya hanata fitowa saboda kawai neman fitina” bibin ta fadi tana gyara yafen lallausar mayafin doguwar riga cotton dake jikinta

“Yarinyar da har kuka zargawa igiyan aure kuke taraddadin kun baro a gida bibi?” Inna hassu ta fadi tana kama haba hadi da sakin siririyar dariya

“Naga alama ko haihuwa sultana tayi ba zaki daina lelenta ba bibi” jakarta kawai ta miqa hannu ta dauka tana riqeta a farin hannunta da yasha jan lalle sannan ta dubi hassun ta gefe

“Kwadaiji dashi,ni na wuce,idan sun dawo ciki kya gaya musu”

“Muje nayi miki kiran modu din” inna hassu ta fada tana ajjiye sevenniours din hannunta a gefan gado.

Kaman yadda bibi ta buqata din hassu bata gayawa kowa zata tafi din ba,saboda karanta da tayi kaman hankalinta ya karkata ga gida don haka ta qofar baya ta bude mata suka fice. Suna tafe suna dan taba hira jefi jefi.

Danne danne kawai takeyi cikin wayarta ba tare da tasan ainihin me take dubawa ba,tayi nisa a tunani ta jiyo muryar bibi din da hassu. A hankali ta cira kanta tana duban sashen da take jiyosu din,sai ta maida wayarta jaka tana ci gaba da dubansu har zuwa sanda suka iskota

“A’ah,kema kina ta nan?” Bibi ta tambayi ama tana dubanta. Kai ama tadan gyada tana sakin fuskarta

“Na gaji ne haka kawai kaman wadda tayi wani aiki,abokin tafiya gida ma nake nema”

“Shikenan an huta neman modu,ga bibi ita dinma gidan takeso komawa ta baro wai shalelenta ita kadai” harara bibi tadan watsawa hassu

“Kekam idan baki rage magana ba wataran sai an kumbura wadanan lebunan,muje ko hamdiyya,idan sun gama raye rayen kya gaya musu mun wuce mu” bibi ta fadi tana bin bayan ama da tayi gaba tana qoqarin fiddo key din motarta.

Shuru ne ya wanzu cikin motar,daga ita har bibi babu me cewa komai. Haka kawai jikkunansu da bakunansu ke a mace. Duk da akwai surukuta tsakani,kuma duk da dadewar zaman hamdiyya dasu bata cika sakewa qwarai da bibi ba. Har yau tana surukuta da ita,kamar yadda take bata girma yadda ya kamata.

Tamkar masu rakiyar gawa haka sukayi cikin motar. A nutse ama ke tuqi wani abu da batasan meye ba yana mata kai kawo qasan zuciya har zuwa sanda suka isa gidan. Horn biyu batayi na uku ba daya daga cikin security na gidan suka dage mata gate ta cusa hancin motar nata.

Sai data tsaida motar sannan ta zagayo ta budewa bibi. Bibi din tayi bismillah ta sanyo qafafunta a waje sannan ta miqe ta fito,ama ta maida.murfin motar ta kulle tana jin bibi tana cewa

“Yau gidan kamar anyi shara haka,ba kowa?” Itama ama ta kula da hakan

“Wataqil suna ciki suna hutawa” ama ta bata amsa tana riqe mata ‘yar purse dinta. Tunda dai daga ita sai ita din tasan dole ta rakata zuwa ciki.

Bibi na gaba tana biye da ita. Daf da zasu sanya kai zuwa ga sassan bibi din sautin muryar tanja ta mamayi kunnuwansu

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,na shiga uku jama’a kuzo ku ganemin sultana”

“Sultana?” Bibi tabi qarshen muryar tanja da tambaya da sunan sultana din. Yayin da ama taji kamar an finciki wani abu daga cikin tsakiyar zuciyarta haka kawai ba tare da tasan dalili ba.

Kamar wadanda aka kafe a wajen haka sukayi carko carko harsai da tanja ta iskesu hannunta saman ka hawaye na sharafinsa saman fuskarta. Tamkar an tunkudata haka ama taji,ta rabe ta gefan bibi cikin sassarfa ta durfafi tanja. Hannunta ta riqe gam tana cewa

“Ke mene haka tanja?,meye zaki dagawa mutane hankali haka?”

“SULTANA ce,ta mutu wallahi,ama kizo ki gani”

“Waye ya kasheta?!” Bibi da ama suka hada baki gurin fada kowanne sautin muryarsa na nuna zallar tashin hankali

“Maina ne!,Aliyyu ne wallahi,shine naga shigarsa dakin” wani irin mahaukacin bugu dukkaninsu zukatansu sukayi

“Maina?,aliyyu?” Ama ta maimaita a fili,yayin da kunnuwanta suka dode na wasu ‘yan sakanni kafin tabi ta gefan tanja tana wuceta zuwa ciki da wani mugun sassarfa har tana gogar kafadar tanja din ba tare data lura da abinda take aikatawa ba.

Duk a saurin da takeyi qafafunta rawa sukeyi kaman zasu lanqwashe

“Maina ne?,me ya yiwa sultanar?,da gaske kasheta yayi?,kada dai ace baqar muguwar zuciyarsa ce ta kitsa masa haka?,amma aliyyun duk zuciyarsa zai iya iya kisa kuwa anya?” Tambayoyin da suka dinga yi mata gizo kenan kafin ta samu Isa ga dakin. Tambayoyin da suka dinga sanyata taji kamar tayi tsuntsuwa ta isa ga dakin ta tabbatarwa idanunta abinda tanja ke fada din.

A kwance kuma lullube ta sameta saman gadon,tamkar kwatankwacin yadda ake lullube gawa. Tashin hankali me tsanani ya sanya tanja ta kasa wani motsin arziqi bare ta suturtata da riga. Don tunda ta janye bargon sau daya ta fahimci meye ne maina ya aikatawa sultanar.

Da sassarfarta ta qarasa gadon zuciyarta na yankewa tana kuma raya mata da gaske sultana ta rasu. Ta miqa hannu tana janye blanket din,amma kuma cikin wani irin mahaukacin shock ta sakeshi tana kauda kai zuciyarta na bugawa da wani irin yanayi kamar zata tsinke daga qirjinta

“La haula wala quwwata illa billa” ta fada da mugun qarfi bayan lokaci guda kwanyarta ta gama gaya mata meye ne ya fara faruwa da sultana din kafin ta mutun.

“Ya kasheta din ko?,ni dama na sani,jikina dama yanata bani,da biyu kenan ya turani biki yace bazan tafi da ita ba” bibi dake qarasowa cikin dakin ta fada jiki da muryarta dukka suna rawa,tanja dake bayanta tana qoqarin riqeta gudun kada ta fadi.

Hannu takai itama zata yaye bargon,saidai tuni ama tasa hannu ta ruge blanket din da kyau wani abu yana tsaga zuciyarta. Koda mutuwa sultana tayi ba zataso bibi taga abinda idanunta suka gani ba,koda mutuwa sultana tayi ba zataso bankadar asirinta ba,koda mutuwa kuma sultana tayi ba zataso bibi taga abinda xai xamewa zuciya da ruhinta miki ba,miki kuma na har abada

“Ki barni naga fuskarta,ki barni nayi mata kallon qarshe” bibin ta furta da wani irin mugun rauni da ya sanya hawayen idanun ama zubowa

“Bata mutu ba bibi,kada kije fa ki fadi” ama din ta furta da confidence tana riqe hannun bibi din da kyau. Ganin hakan bazaiyi ba sai kawai ama ta miqe daga wajen ta kama hannun bibin tana jayeta daga dakin

“Na miki alqawarin sultana ba zata mutu ba bibi,na daukar miki wannan alqawarin”

“Hamdiyya sultana ce fa?” Bibi ta fada furucin na fita daga qasan zuciyarta

“Na sani bibi”

“To meye Aliyyu yayi mata?,me ya sameta?” Ta jefa tambayar ga ama din,don ta karanci wani abu saman fuskarta. Qasa ama tayi da kanta tana qoqarin hana idanunta fidda hawaye karo na biyu

“Ba lokacin wannan bayanin bane bibi kiyi haquri,sultana nada buqatar ganin likita” ama ta fadi tana zame hannunta daga na bibi bayan ta tabbatar ta nesantata daga dakin,sannan ta juya da hanzari ta koma dakin sultana din.

Da kanta ta daga sultana din bayan ta sanya tanja ta dauko wasu kayan ta sauya mata. Jinin daga gani saman gadon ita kanta ya firgitata ainun.

“Zan fita da sultana ki kulle dakin,kowa ma a gidannan banason ya shigo dakinnan har sai na dawo,koda bibi”

“To” tanja ta fada har yanzu jikinta da zuciyarta suna rawa,saboda gani takeyi tamkar sakacinta ne ya jawo komai, tunda bibi a hannunta tabar amanar sultana.

Har sun shiga mota ita da tanja dake rungume da sultana wadda har zuwa yanzu bata motsa ba bibi ta qaraso. Kallo daya ta yiwa fuskar sultana din ta janye idanunta zuciyarta na sake bugawa tare da yin rawa. Bude daya side din tayi ta shiga

“Muje hamdiyya,bazan iya zama ba” ita kanta ama dukka hannunta rawa sukeyi,wannan ya sanya dole modu driver ya karbi tuqin motar. Sauran ma’aikatan gidan da su sukayi saura na tsaye carko carko cikin alhini ba tare da sanin ainihin abinda ke faruwa cikin gidan ba har motar ta fice

Series NavigationGudun Kaddara Part 2 Book 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *