Gudun Kaddara Part 2 Book 2

This entry is part 2 of 3 in the series gudun kaddara Book 2

GUDUN ƘADDARA

H U G U M A

BOOK 02 PAGE 02

Wani irin zuciyar ama keyi cikin qirjinta

“Maina?,maina?,me yakai maina aikata irin wannan mummunar ta’asar duk da cewa sultana halalinsa ce?” Tambayar data dinga yawo kenan a qirjinta tana sanyawa zuciyarta wani irin zafi. Zallar rashin imani da tausayi kawai ta hango tattare da maina din wannan karon,abinda bata taba gani ba tattare dashi,yana da zafin zuciya,yana da tsananin fushi,amma sam bashi ta gefen bushewar da rashin tausayi,hasalima cikin halittarsa tausayi yake,yana kuma daya daga cikin abinda yasa tayi bore a shekarun baya tayi GUDUN K’ADDARA,amma kuma sai gashi yanzun alamu na gwada mata dukka wani dagewa da taqarqarewarta wajen gujewa qaddarar kamar ma biye take da nata sawayen qafa da qafa.

Sam bibi ta rasa ma wanne irin tunani zatayi,gaba daya kwanyarta ta toshe,da waye zata tarbi wannan babban tashin hankalin?,waye zaya tayata dauka?,waye zai iya?,kawai sai ta fidda waya tayi kiran aba ta gaya masa kai tsaye asibitin da zai sameta ba tare data qara komai akai ba.

Rufe ido ama tayi tana jin bugun zuciyarta har bibi ta gama waya da aba,ta sani dole zaya sani,kuma a yau din itama bata goyon bayan aliyyu,hakanan ba zata iya tare masa komai ba daga zazzafan hukuncin duk da zaya fuskata daga familyn MAYAK’I.

Wayarta ta fidda har yanzu jikinta yana rawa,ta lalubi number wayar Dr chafa’atou. Amintacciyar likitarta qwaya daya tal cikin asibitin da ya kasance wajen karakainar familyn MAYAK’I,duk da a yawancin lokuta home service ne ake musu,sai idan ta baci irin haka

“Ki shirya keda wasu likitocin gamu tafe da mata lafiya,amma don Allah J’ai besoin d’intimité(ina buqatar sirri)”

“Ne vous inquiétez pas(kada ki damu),zaki samu sirri har fiye da yadda kikeso in sha Allah” Dr chafa’atou ta amsa mata cikin bata tabbacin da yayi gaining mata wani dan qaramin qwarin gwiwa.

Suna isa aka fidda gado,bisa rakiyar dr chafa’atou da kanta suka dauki sultana zuwa ciki. Bibi da ama din duka suka taka zuwa cikin suma tanja dake share qwalla tana biye dasu. Daga ama har bibi ba wanda ya samu qwallar ta fita daga idanunsa bare ya samu sassaucin radadi da tashin hankalin da yake ciki,hakanan duka su biyun duka gagara zama zaman tsararrun kujerun dake lubby din wanda aka tanada musamman saboda zaman jiran tsammani irin haka.

Kimanin mintuna ashirin suna a haka kafin ama taja wani zuzzurfan numfashi

“Indai baki zama jaruma ba hamdiyya sai yaushe?,ke zaki bawa kowa qwarin gwiwa kuma ke zaki zama jagorar kowanne tashin hankali da zai ruftowa a halinki” wani sashe na zuciyarta ya gaya mata cikin qarfafa gwiwa,maganar data taso tun daga can wani saqo na zuciyarta,ya kuma bata qarfin gwiwar dosar bibi.

Hannuwan bibi dukka biyun ta kama tana karantar tsananin tashin hankalin dake kwance saman fuskarta. Ko kadan bataga laifi ga hakan ba,don kuwa koda itace fiye da haka ma zai iya fuskantarta. Duk da cewa a yanzun tana kyautata zaton tana jin fiye da abinda bibi keji cikin qirjinta. Ko ba komai duk tsiya sultana tatace,ga kuma wanda kuma yayi barnar ya kasance wani sashe me girma na jiki da zuciyarta

“Kiyi haquri bibi ki zauna,tsaiwar tayi yawa haka” ama ta furta cikin laushi. Tsakiyar idanun ama bibi ta kalla,kaman zatayi magana sai ta fasa,tabi ama din har zuwa sanda ta zaunar da ita,sannan ta koma bakin qofar dakin da suka shiga da sultana tamkar me jiran qofa. Dakin dai ta zubawa dukka idanunta,duk wucewar daqiqa daya sai bugun zuciyarta ya qaru,tayi imanin inda ace ayau tana dan qaramin hawan jini babu abinda zai hanashi hauhawa,wataqila yakai jallin da zaya sanyata zubewa. Ko a yanzun ita daya tasan me takeji,musamman da take duba agogon hannunta take ganin yadda daqiqoqi ke shudewa ba wani motsi daga cikin dakin.

Su biyu ne cikin dakin suke checking na sultana,amma daga ita har Dr nadra ba wadda yanayin da suka riski sultana be ratsasu ba.

“Wanne mahaukacinne yayi mata irin wannan mummunar fyaden?” Dr nadra ta fadi tana zare glasses din idanunta bayan sun tabbatar da cewa dole sultana na buqatar stitches ta ciki da waje,stitches din me me yawan da ko haihuwa tayi iyaka kenan

“Ban sani ba Dr……amma kuma….J’ai entendu des nouvelles(naji wasu labarai)kwanaki kaman sun mata auren gida da cousin din mamanta fa…..Je pense(ina tsammanin)daren farkonsu ne yaje mata da gagggawa irin ta matasan yanzu,kinsan kusan dukkaninsu a kame suke”

“Wanne irin daren farko ne haka DR…..baki lura da ciwon dake gefen idanunta fa?,ina tsoron da wuya idan bai taba lafiyar idanunta ba….. kalli fuskarta fa da kyau Dr” hannu dr chafa’atou ta miqa tana juya kyakkyawar fuskar sultana data sauya saboda kumburi da kuma jazur din da tayi

“peut être(maybe)ko tayi masa taurin kai ne…” Ta fadi a mugun sanyaye,saboda ita kanta yadda idon dake bangaren hannun hagunta yadda ya daga din sosai ya sanya mata shakka da kokwanto.

Basu buqaci kowa ba cikin qananun ma’aikata,dr chafa’atou da dr nadra su suka gyara jikinta tsaf bayan sun tabbatar da dawowar numfashinta dake fita a hankali a hankali kamar ana sammata shi,sai da suka tabbatar da daidaituwarsa sannan suka fara mata aikin dinkin,wanda sai da suka fara dinne suka sake fahimtar adadin yawan barnar da maina yayi mata.

“Sai idan ta farka sai ayi checking idanunta dinna,sabida kumburin da kwanciyar da fatan wurin tayi yayi yawa” Dr chafa’atou ta qarashe bayaninta idanunta saman fuskar aba oncle bashar oncle umar da oncle issoufou,bibi ama da aunty ta’ibah matar oncle umar data biyo bayansu daga baya.

Iska me zafi aba ya furzar daga bakinsa. Komai yana jinsa ne tamkar almara cikin kunnuwansa,maina?, aliyyun shi ya aikata wannan ta’addancin akan marainiyar Allah?,koda akace an aura masa ita ai ba lasisin ci mata zarafi irin haka aka bashi ba.

“Ba za’a shiga dakinta ba, za’a barta taci gaba da baccinta har sai ta huta sosai ta tashi da kanta,kuma koda ta tashi din bata buqatar hayaniya,saboda abinda ya faru da ita din zai zaman kaman dai dai yake da RÃPÉ ne a wajenta”. Dukka idanunta ama ta sanya ta kalli dr chafa’atou kafin tayi qasa da kanta. Kalma mafi girma da muni da tunda take bata taba ganin kalmar da aliyyu ya tsana a duniya irinta ba,tayi fama dashi kan ya shiga harkar kasuwancinta,tafiye tafiyenta da dukkan wani sabgogi da suka shafeta,amma game da harkar qungiyarta ta yaqi da fyadewa qananun yara da mata…. Ko sau daya batayi wahalar gayyatarshi ba,shi da kansa ya shiga saboda mummunar tsana da gabar dake tsakaninsa da abun,sai gashi yau kalmar na shirin lanqwashewa cikin jikinshi.

Akwai kyakkyawar kula cikin asibitin da koda babu me jinyarka za’a kula da kai. Hakan ya sanya sukayi zaune kawai cikin farfajiyar da zata sadaka da dakin. Wani irin zama maras dadi da bakuna duka gaza furta abinda ke cikin zukata,sai saukar ajiyar zuciya lokaci lokaci daga zukatan al’ummar wajen. A yanzun basu da wani sauran zanceme amfani da suke ganin zasu tattaunashi,farfadowar sultana da dawowarta cikin hayyacinta shine abu guda daya filo mafi muhimmanci da kowa ke sanya idanu da ran ganinsa.

Har zuwa lokacin da lokaci ya cika na zaman ganin maras lafiya ya cika sultana bata motsa ba,wani irin baccin takeyi wanda ko juyawa batayi,abinda ya sake tasar hankalin bibi kenan,har ta fara fidda qwallar da a baya batayi ba

“Hamidou…..idan har yarinyar nan ta rasu gwara su gayamin kawai,ni din musulma ce,zan kuma iya daukar qaddarar rashinta,kamar yadda na dauki qaddarar rashin mahaifinta da ma mahaifiyarta gaba daya” kamar ana tsira mashi a qirjinta haka ama keji,duk sanda ta tuna cewa aliyyu shine sila na faruwar komai…..shine musabbabi na wanzuwar ahalin cikin wannan mummunar halin sai taji wani irin nauyi ya sake saukar mata,sai taji tamkar ta nutse a wajen. Kuka daga idanun mutum me shekaru ba abune da kowacce zuciya zata iya dauka ba,bibi bata danya dangana ba sanda suka buqaci tafiyarsu gida da alqawarin bata kulawa har sai da aka dangana da ita dakin sultana,ta kuma gani da idanunta yadda qirjinta ke dagawa da komawa tabbacin akwai numfashi a gangar jikinta

“Bazan barta ta kwana ita daya ba”

“Zan zauna da ita bibi,zan koma gida na shirya na dawo” ama ta fada tana jin cewa duk duniya itace ahaqqu da daukar wannan nauyin.

Bibi bata musanta ba,saboda ita din shaida ne na yadda hamdiyyan ke iya hidima ga kowanne yaro na gidan tamkar daga cikinta ya fito,sai ta juya tana fita a dakin, zuciyarta da bakinta fal da addu’ar samun sassauci wa sultana.

Daga ita sai tanja cikin mota,saboda aba ya dauke tsohuwarsa a tasa motar. Barinsu tayi,saboda ta tabbatar a barnar da yaronta ya tafka dole suna buqatar kebewa da tattauna abubuwa masu yawan da ta tabbatar ba lallai taso jin wasu abubuwa ba. Ta musu uzuri,kuma dukka wanda zai zargi aliyyu ko yaga laifinsa tana tunanin itace mutum na farko game da hakan.

Tun saman hanya ta gaza jure isarta gida ta taras dashi,zuwa lokacin ta tabbatar koda bai dawo gida ba to yana a kusa da gida din. Tasan cewa zaiyi wuya ya dawo a lokacin da ya saba saboda ya sani shi din me laifi ne,don haka ta soma lalubar number dinsa ta wayarta.

Tun bugun farko éteindre(a kashe take)haka computer ta gaya mata,amma tayi burus kaman bata fahimci yaren da computer din ke magana dashi ba ta shiga maimaita kiran nasa babu ji babu gani,saidai kuma amsa daya ce dai ake bata,dole ta maida wayar gefanta ta aje tana jan doguwar qwafa hadi da ajiyar zuciya. Wato yasan ta’adin da yayi shi ya sanyashi kashe dukka wayoyinsa?,batajin wannan lokaci zata daga masa qafa ko qanqani,kafin aba ya hukuntashi itace mutum ta farko da zata fara masa nata hukuncin.

Batasan inda bibi da aba suka tsaya ba amma dai ta rigasu isa gida,maimakon ta zarce sassanta sai kawai ta wuce sashen bibi din tana karbar key din dakin sultana data damqa ajiyarsa a hannun tanja.

A nutse ta bude dakin cikin sanyin jiki,ta sanya hannu ta kunna makunnin fitilar dakin. Tarwai haske ya gauraye dakin,yamutsatsen gadon da ta tabbatar akai sultana tasha dukkanw ata azaba daga hannun maina ya bayyana cikin idanunta. Takawa tayi a nutse din tana nufar gadon,har tsakiyar ranta tana jin abinda maina din ya yiwa sultana. Koba komai ita din diya macace,kuma tasan irin zafi da radadin da kowacce mace ke fuskanta a duk lokacin da zata rasa wannan abun me muhimmanci cikin rayuwarta koda kuwa an karbeshi ne cikin lallashi riritawa da kuma soyayya,ballantana uwa uba kuma karba ta fun qarfi,karba ta qarfa qarfa da nuna izza isa da iko.

Hannu ta sanya ta tattare dukkan abinda ke saman gadon,kama daga zanin gadon da ya gama baci da jini zuwa pillow din da tuni ya zame daga cikin gidansa, blanket dinta da shima jini ya taba,sai kayan sawarta da suka gama zama tsumma.

Sanda take rungume da zannuwan gadon zuwa toilet din sai taji zuciyarta tayi nauyi,data waresu cikin toilet din ta fara wankesu kuwa dukka qwalla da zafin da zuciyarta keyi wanda taketa riqewa sai ya gaza riquwa. Wata siriryar qwalla tabi ta gefan idanunta tana bin jinin da kallo,tausayin sultana ya tsargama zuciyarta irin wanda bata taba ji ba. Wannan zallar rashin imani aliyyu ya gwada mata,wanne laifi tayi masa da zafi haka daya zabi yiwa rayuwarta wannan ta’addancin?,ba zata qyale maina ba koda kowa kuwa zaice a daga masa qafa. Zaiyi wuya a yawan jinin data gani jikin zanin gadon yarinyar bata buqaci qarin jini ba. Cikin raurawar zuciya ta dinga wanke zanin gadon zuwa blanket din,abinda tsahon rayuwarta bata taba yi ba da hannuwanta.

Cikin mintuna arba’in ta kammala wankesu tas duk kuwa da nauyinsu,ta koma ta kintsa dakin shima tamkar ba hamdiyya abdu me kano ba. Tana kammalawa bibi na turo qofar dakin,sai ta saki siriryar boyayyar ajiyar zuciya da bibin bata isketa tana tsaka da wanke kayan da haidar din yayi aika aikarsa akai ba.

Series Navigation<< Gudun Kaddara Part 1 Book 2Gudun Kaddara Part 3 Book 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *