kwankwason jimina book 2

Kwankwason Jimina Part 2

This entry is part 4 of 3 in the series kwankwason jimina book 2

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

BOOK TWO

paid page :002

__

“Layla Auwal Hamidniyya… Nawraah Junaid hamidniyya?”

Suka jiyo wata siririyar muryar a bayan su tana kiran sunayen su. Da sauri suka juya.

Wata matashiyar budurwa ce haka ba zata dara shekarun su ba. Sanye cikin riga da skirt ta nannade jikinta da wadataccen mayafin . Fuskar ta dauke da gilashin na karas agajin gani…

“Ga mu” Layla ta amsa ta .

Nawraah ta ja ta tsaya itama suna jiran cewa ta bakin ta.

Yarinyar ta daga hannu tayi nuni da wani ofishi a bayan su tace,

“Ana kiran ku a dean’s office.”

“Toh Allah yasa kalau” Layla ta fada tana sauke zuciya.

Nawraah ta juya tana duban yarinyar data shige su tayi tafiyar ta.

Ofishin suka nufa suka shiga ciki

Hadadden office ne mai matukar kyau da ya sha kaya masu matukar tsada da kyau.

Bakunan su dauke da sallama suka shiga. Na’urar sanyaya waje ta doka musu sanyi mai matukar dadi da ratsa jiki.

Zaune take akan kujerar dean. Kai ka dauka itace dean din.sanye cikin doguwar riga baka ta abaya design din Dubai ta nade kanta da mayafin abayar. Yayinda gaban ta dan zame shi ana hango gashin ta,

Nawraah ta sake jin matar ta sake futa a ranta. Musanman da tayi wannan shigar tamkar ba matar aure ba. Sam ba sanin darajar igiyar aure a rayuwar masu kudi?

“Kece Layla ko. ? Ke Kuma Nawraah?” Ta tambaye su tana mai nuni da nawraah a matsayin itace layla . Ta Kuma nuna Layla ta ta nuna ta itace Nawraah?

Nawraah tayi murmushi tana sake jinginar da kanta ajikin bango tace,

“Mune. Itace Layla ni Kuma Nawraah”

“Ahh Mashaa Allah Ashe ban manta ba.. da farko dai yadda kuke kallon nan nawa magana ta gaskia ba nice dean ba. Amman zan iya cewa mukamina a jami’ar nan ma yafi ta dean. Kun gane?”

“Eh” suka hada baki wajen amsa ta.

Dr bintu ta mike tsaye daga zaunen da take tana duban su tace,

“Maraba da shigowar ku jami’ar Al-Haramein dake nan babban birnin Naduka… Muna farin ciki da kasancewar ku atare da mu. Don kaunace tasa muka baku gurbin karatu anan din daga yau yazuwa ranar daza ku kammala karatun ku idan Allah ya amince”

“Aamin”suka amsa ta

Landline wata waya dake kusa da ita ta janyo tasaka wasu numbers ta kara a kunnenta ba jimawa ta katse kiran bayan tace da na wayar,

“Zo yanzun nan Ina office”

Gyara zamanta tayi tana duba agogon wutsiyar hannunta sai ga shigar wani yaro nan ya dan saka kayan sa masu kyauu .yanada Kuma da kyawun sa tubarkallah

“Ma! Ga ni”

“Sannu da kokari”

Matashin ya sosa keyar sa, Yana duban su ta gefen idanu.

“Bakomai Ma..”

“Yauwa kasan meya sana kira ka?”

“Aa”

“Well just the usual ne dai … volunteer work ne kawai.. zakai da wannan students din”

“okay ko’ina da koina za’a nuna musu?”

“Inda ya dace ..wajajen zaka kai su “

Har ya Kai bakin kofa sai ya juya wajen su Nawraah,

“Kune ko?”

Nawraah da Layla suka dubi Dr bintu dake gyara zaman mayafin ta. Murmushi tayi tace musu,

“Zai nuna muku bangare bangare na cikin jami’ar ne.”

“Okay mungode. “

“Ina sauran mazan?’ dr bintu ta tambaye su ganin bata ga su Ashfeef ba”

“Zasu zo suma anjima kila”

“Toh Allah ya amince amin”

Fita sukayi… Saurayin na gaba suna biye da shi abaya. Yanata kalle kallen lungu da sako kamar matsoraci ganin ba kowa awajen ya juya ya ce da su,

“Sunana Imraan….

NA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

Series Navigation<< Kwankwason Jimina Part 1Kwankwason Jimina part 3 book 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *