kwankwason jimina book 2

Kwankwason Jimina Part 1

This entry is part 3 of 3 in the series kwankwason jimina book 2

KWANKWASON JIMINA!!
(MAI WUYAR SHAFAWA)
🦩🦯🦾

✍️: MX

ZAFAFA BIYAR 2024

BOOK TWO

paid page :001

_

__

welcome to Al-Haramein university Naduka shine kalmomin da wani babban majigi kusurwa kusurwa yake rubutawa yana kuma haska kowanne sashe na cikin makarantar.

Daga can gefen inda suke gangarawa suna tafiya…. Wani babban majigi ne na daban dake rubuce da manyan bakin faculty of social sciences … Daga can gaban sa Kuma wani tankamemen waje ne a killace an rubuta da,

DEPARTMENT OF CRIMINOLOGY/SOCIOLOGY

Abunda ke rubuce kenan da manyan baki masu sheki da nuna haske, a jikin wani katafaren signboard na karfe mai tsada. Wanda shi kansa signboard din kasan yaci kudi …

    Wani hadadden gini ne tamkar irin gidajen nan na Cappadocia dake Istanbul . Tsaf zaka dauka hotel ne ma saboda tsananin yadda yake da kyawu. Can suka nufa inda sunan course din da zasu karanta yake.

Ga manyan motoci nan a faffake an faka su a harabar adana motocin bangaren. Tundaga kan furofesoshi kowanne da sunan sa a wajen da motar da zasu faka. Daga rank din furososhi zuwa daktoci da manyan students na postgraduate students zuwa undergraduates students…

Sai da suka tsaya suka bawa idanunsa abincinnsa. Dakyar Nawraah ganin lamarin ba na karewa bane yasa ta janye hannun layla suka shiga cikin department din.

Mai karatu idan nace zan zayyano muku adadin kayyakin kudi masu tarin yawa da aka kashe wajen zuba ado a department dinna Kai dama makarantar bakk daya sai ace sharri ne.

Amman duk inda makaranta ta manyan kasashen duniya da suka hada kai suka tunbatsa da kudi wannan makaranta ta kai, Kai harta zarce sauran wasu makarantun.

Sauran daliban dake ciki suka tsaya suna duban su Nawraah cike da kyama. Kayan su ba designers ba sannan kallo daya zakai musu ka tabbatar yayan malam ne mai dattin hula na soro.. (talakawa)

Dube duben supervisor office suka shiga yi sun rasa . Layla ta ceda Nawraah,

“Mu tambayi wadannan daliban mana su nuna mana ko?”

“Laylus da dai mun kyalle su kawai dubu yadda suke kallon mu tamkar sunga Kashi. Haba mana”

“To ai dole suyi tunda ba taba ganin mu sukayi ba. Uwa uba ba Wanda zai Rena mu. Kinsan dai wannan kayan na jikin mu mun kashe wajen dubu uku uku na kowa “

Nawraah tayi murmushi kawai. Suna rike da hannun juna suka nufi wajen wasu yammata su hudu. Yan gayu ne na bugawa a jarida . Kowacce sanye cikin tsadaddun kayan sawa. Dauke da manyan wayoyyin zamani a hannun su.

“Assalamu alaikum” suka hada baki wajen musu sallama

Yammatan suka tsaya suna binsu da wani irin kallo na renin hankali. Guda daya ce ta amsa musu sallamar itama ba wai fuska a sake ba

“Tambaya muke” Cewar Layla.

Daya daga cikin yammatan ta daga Kai tana duban tundaga tafukan kafafun su ya zuwa fuskar su tace,

“Ba ku akayi wa warning bane wai?”

“Warning Kuma?” Layla ta tambaye ta tana duban Nawraah..

“Eh . Yan talla ne mana. Na gane fuskokin ku ai. Ke kaman awara kike sayarwa, ke Kuma bandashe. ” Ta fada tana Mai nuni da kowaccen su

Layla ta bude baki zatayi magana. Nawraah ta riko hannunta da sauri ta kakaro murmushi tace.

“Mu ma dalibai ne kamar kowa.. kaman yadda kowannen ku yake cikin jami’ar. Sai dai Alhamdu Lil Laahi. Mu yan tallafi(scholarship) ne ba iyaye ne suka biya mana kamar ku ba…”

Tana karasa fada ta ja Layla suka bar wajen.

“Ki kyale ni naje naci haka kaza ta uban su”

“Calm down Laylus. Maganar ta wuce. Bamuda wani option dai illa mu basu hakuri Koda wani abun zaj taso na daban su iyayen su sunada shi suna cikin halin samu. Mu kuma namu iyayen na cikin halin rashi. Allah yasa mu dace,

“Aamin Nawraah. Shikenan tunda kin gama magana . Amma gaskia ba zanyi tolerating ba gaskia. “

“Inshaa Allah. They won’t be next time “

“Tohm Allah ya amince din. “

Suna tafe suna karanta dukkanin abunda aka saka a bakin ofishin malamam. Da haka har suka karasa kan sunan ….

“Layla Auwal… Da Kuma Nawraah Junaid…

INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?

KU MARMATSO KUSA…🔊

ZAFAFA BIYAR 2024

ZAFAFA BIYAR!!!
ZAFAFA BIYAR!!
ZAFAFA BIYAR!!

1

AMEENATUH🧕💖: MAMUH GEE

2

TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣:BILYN ABDULL

3

GUDUN KADDARA🏃🐾:SAFIYYAH HUGUMA

4

KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯:NANA HAFSATU (MX)

karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

Series NavigationKwankwason Jimina Part 2 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *