Samarin Bana Chapter 6

Samarin Bana Chapter 3

This entry is part 3 of 6 in the series Samarin Bana na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele

03

[11:10PM, 10/11/2016] Rahamat Nalele 👯:

Dake SAILUBAH Tace kanta na mata ciwo sai kawai KHAMIS yasha Sha taletale ya fara saukesu ita da RAMADAN

Sannan yakai XEE ya wucce gida 

Aranar ne aka ‘daura Auran Saudat da mijinta Aminu

Qarfe bakwai RAMADAN yana gaban SAILUBAH yana lallashinta tatashi aje kai Amaryar da ita

Tace dan Allah karabu dani kaina namin ciwo

Yace haba Auntyna bata da qawar da tawucceki pls dan Allah badan niba tashi kije

Sanin halinsa da naci yasata tashi tayi wanka tashirya kicin wasu riga da siket na atamfa sun amsheta matuqa

XEE tayi dariya Tace aigwara da ‘dancin naki yasaki tashi dan abinda kikasoyi Sam bai dace ba

Ta feshe jikinta da turare suka fitoh

Lokacin yayi daidai da xuwan angwaye masu ‘daukar amarya

Nan samari masu ji da kai suka yimusu cah akai wannan Yace sushiga motarshi wannan Yace tashi

Ahaka dai suka shiga motar wani Abbas yajasu Cikin sauri sanda ya fitta daga layin ya fara tafiya ahankali

Ya kalli XEE Yace qawarki tayimin dan Allah kiban ita

Tayi murmushi Tace indai SAILUBAH ce nabaka ita

Nan yacika da murna yace xan iya samun numbarta Tace eh mexai haka

Ahaka yadinga Jan XEE da xance tana biye mishi duk akan SAILUBAH ne

Tana jinsu tayi shuru

In ta ‘kaice muku awannan daran SAILUBAH tayi samari kusan shidda masu aji da nera

Kuma sanda suka Nace suka samu numbarta

Dukda ba magana take musu bah. XEE CE take aran bakinta

Gidan Amaryar Saudat yayi kyau Sosai dan Babban gidane. Saidai tana da abokiyar xama Rabi’a…..

Abin takaici😔

Sunfito xasu koma gida. motar Abbas suka shiga inda yajasu sun hau titi yana jansu ahankali dan bayaso yadena kallan masoyiyar tasa SAILUBAH

Basai XEE tahango saurayinta Surajo da wata mace a motarsa ba. Kasan cewar sun kunna wutar motar yarinyar tana duba wani book dake hannunta

Kallo ‘daya xaka musu Kasan suna cikin nisha’di.

Gaban XEE ya fa’di  hankalinta ya tashi toh dama XEE kishine da ita Sosai akan sahibin nata Surajo

Aiko cikin qara Tace Abbas yabi mata Su

Cikin rashin fahimtarta ko ya bishi

Har suka kai wata unguwa wai ita bacirawa inda sukayi parking a’kofar wani gida

Abbas ma yayi parking kusa dasu

Cikin Xafin nama tayi yunquri fitta daga motar…  SAILUBAH tariqe hannunta Tace karkiyi wani abu pls kibarsu mukuma gida

 cikin xubar da hawaye Tace naga alamar bakisan kishi bah bakisan miye so ba. Tunda baki ta6a tsaida mutum ‘daya ya mantar dake duniyar marasa SOO bah

Wlhi kinji na rantse miki ‘daukewar numfashine kawai xai hanani xuwa ga waccan maci amanar

Nan tafuzge hannunta tafuta daga motar

Tana xuwa ta kwankwasa musu gilashin motar

Budurwar tabu’de tana fa’din kai karima kincika naci toh munsiyo miki ice-cream ‘din

XEE Tace karimar uwarki……..

Aiko da sauri Surajo ya fitoh daga motar cikin tashin hankali danjin XEE Yace meya kawoki nan My XEE

Cikin maseefa Tace sunan nan ya fitta daga bakinka

Munafiki axxalimi makiri dan iska ni xaka yaudara

Kana tare dani. Kuma kowane lokaci fa’damin kake ni ka’daice budurwarka.

Ashe qarya kake.

Ta fashe da kuka tana fa’din na tsaneka

Kasa nabaka yardata gabaki ‘daya….

Yau Aurena da kai saura wata biyu amma kake Neman wata……

Kuttumar uba  Auran ki dashi wata biyu

Budurwar tatambayi XEE da mamaki

XEE tamata mugun kallo Tace bagaki gashi ba Ki tambaya shi man

Cukume wiyan rigarsa budurwar tayi cikin tashin hankali Tace idan kasaba yaudarar mata ni baka isa ka yaudareni ba

Saura sati biyu Aurena dakai ashe kanacan kana neman wata harda kai sadakinta ‘dan rainin hankali ni xaka rainama wayo…..

XEE ta qara tsaida idanta akansa cikin sanyi Tace abinda Tafa’da gaskiya ne

Yayi shuru duk ya burkice

Tayi murmushin takaici Tace kaxo gidanmu ka kar6i sadakin ka na tsaneka…..

Tana fa’din hakan tayi cikin motar Abbas yajasu suka bar gun

Duk lallashin duniyar nan ba wannan SAILUBAH batama XEE akan tayi shuru tayi kuma hakuri ba Amma taqi sauraranta

Haka Abbas ya kaita gidansu Sannan ya juyo da kan motarsa ya dawo da SAILUBAH gida

Akan idan RAMADAN yayi parking 

Yace toh Allah ya tashemu lafiya dan nasan baxa ki tsaya saurara taba awannan lokacin sai munyi waya

SAILUBAH tamai murmushin yaqe Tace toh. Dan ba qaramin ciwo kanta yake mata ba

Tana shiga gidan nasu RAMADAN ya bita har ‘dakinta

Yace shi kuma wannan Waye

Ta kallesa ka’dan Tace ban sani bah

Yanayin da tayi magana dashi shiya tabbatar mishi ciwan kan nata bai saketa bah

Dan haka ya bu’de dirowar da take saka magun gunanta ya ‘dauko mata maganin ciwan kan ya bata da ruwa. Sai taqi kar6a

Sam SAILUBAH batasan magani danjinsu allura

Dake yasan da xaman wannan sai yahau lallashinta akan tasha

Tace nace baxan shabako. ko Ana dolene

cikin fusata Yace Wlhi saikin Sha so kike Ki hanani bacci cikin nutsuwata

Ta kalleshi cikin qarfin hali Tace wai me yasa kagama raina nine RAMADAN

Yace ba rainaki nayiba Auntyna kawai dai Kinsan baxan iya bacci bane kina Cikin ciwan nan dan Allah dan Annabi kisha kitemaken

Sarai tasan inba Sha tayiba baxai barta ba. Kuma da gaske baxai iya yin baccin ba

Dan haka ta kar6a tasha kamar xatayi kuka

Yayi Murmushi dan yasan ba qaramin sa’arta yaciba wajan shan maganin da tayi

Sanda ya barta nakusan minti goma Sannan Yace dan Allah Auntyna Waye Wanda ya saukeki amota

Ta xubamai ido Tace miye damuwarka RAMADAN dan Allah

Baxaka tausayamin cikin wannan halin da nake cikiba saika dameni da surutu

Ya sosa qeya Yace Wlhi nafi kowa damuwa da duk ciwan daxai cafkeki

Amma dan Allah kitemaken kigayamin Waye shi

Tace me sona ne

Yace tab yanxu kina sanshi kuma

Ta kallesa Sosai Tace ai kallo ‘daya na mishi naji ina sansa har cikin xuciyata

RAMADAN ya galla mata wata muguwar harara batare daya San yayiba Yace hmm

Lalle bakiyi sa’ar masoyi ba

Tace meyasa

Yace kallo ‘daya na mishi nasan bai cika sharu’dan da kikeso agun Wanda kikesan aure ba

Tashi tayi daga gadan nata Tace me ka hango  atare dashi wanda bai cika shara’di na ba. Bayan yana da ku’di daga ganin motar daya ke tuqawa. kai ka sani

Yace eh da alama me ku’dinne Amma Wlhi xakisha kunya duk ranar da kika fitoh dashi kika nuna ma jama’a shine mijin da xaki Aure

Ta waro ido. Me kake nufi

Yace yayi muni da yawa ga Wasu haqora da suka mishi cakaro cakaro abakinsa

SAILUBAH tayi shuru tana so ta hango Abbas a idanta Amma takasa dan ita ba kallan tsaf tamasa ba

Kuma dama tacema RAMADAN tana san shine dan ya barta da surutunsa kanta namata ciwo

Ganin da RAMADAN yayi tashiga tunani shiya sashi shafa gefan fuskarta tuni ta farfa’do daga tunanin nata

Yace gaki kyakkyawa abinki Amma xaki Auri me kama da aladu….😆

SAILUBAH ta shagwa6e fuska Tace kai ni har naji na tsane shi

Yayi Murmushi Yace innine ke Wlhi in yaxo gobe baxan futa ba……

Taqara shagwa6a fuska Cikin shagwa6a Tace yanxu kenan idan yaxo gobe karna fitta

Yace in nine ke ba

Tace nifah bana san Auran mummuna

Yace na sani ai. mexai hana kice mishi ammiki Miji

Ta qura mishi ido tana san tunanin wani abu. yayi saurin katse mata tunanin da cewa no fah. ki fita idan yaxo Amma kiqare mishi kallo Wlhi xaki yarda da xancena. Yafa’da yana mai miqewa har yakai ‘kofa. Tace ina fatan dai kaci abinci. Yace banci bah dan abincin biki ne agidan

Tace ai yayi da’di

Yace tuwan 😳

Da suka sama miyar kabewa kai Gaskiya ba xanci ba Wlhi. Dan natsani kabewar nan

SAILUBAH tayi Murmushi dan tuno qiyayyar dake tsakaninsa da tuwo. Sam ya tsani tuwo musamman asaka kabewa amiyar (kunsan kano da kabewa Allah ya basu hikimar sarrafata😆 )

Tace ka tsaya in dafama ko indomie CE

Ya dawo ya kama hannunta Yace baki da lafiya Auntyna ki barshi. xansa momy ta dafamin. Ina san kihuta banasan Ki wahala kinji

Tace toh ‘daukar min alqawarin xakaci

Yayi Murmushi da jefanta da wannan shu’umin kallan nasa

 Tuni gabanta ya fa’di tanemi rikicewa

Ganin haka yasashi shafar gefan fuskarta Yace na’dau miki alqawari xanci.

Shuru tayi harya bu’de ‘kofar xai fitta cikin wata wahalalliyar murya Tace dan Allah kar kaje club yau

Ya san idan ya qara gigin kallanta tabbas xai hanata bacci yau

Dan haka batare da ya juyo ba Yace toh naji

Alkawari

Nayi

Ya fitta daga ‘dakin

SAILUBAH sai taji hankalinta ya kwanta dan tasan tunda Yace baxaije bah toh baxai je ‘dinba

Kwantawa tayi tafa’da tubanin XEE

Allah Sarki yanxu haka tanacan dana kukan nata

Tayi Murmushi wai miyema soyayya ne

Sam SAILUBAH batasan soyayya ba

Dan tana fara soyayyar RAMADAN yake katse mata jin da’dinta

Ita dai abinda yake gabanta shine Auran me ku’di

Ahaka bacci 6arawo yayi awan gaba da ita

RAMADAN ko yana kallan Su FAWAS na shirin xuwa club Yace baxai jeba

Sukace me yasa Yace Auntyna ta hanani xuwa yau

Kai Aunty LUUVAH me yasa tayi haka. Cewar KHAMIS

FAWAS Yace share kawai muma mun fasa xuwa.

RAMADAN yayi dariya Yace nasan xa’ayi haka

KHAMIS yajah tsaki Yace naso hutawa Wlhi

Dole haka sai gun ‘yan matan nasu sukaje kawai 

XEE ko tasa iyayanta tayi agaba tana musu kuka

Da tashin hankali suke tambayart lafiya

Nan tagaya musu Komai taqara da cewa Wlhi BABAH na tsani Surajo. Bana sansa. Kurku ha’da ni Aure dashi dan baxan ta6ayi masa biyayya bah

Kuma ai ana Aure ne dan biyayya Wlhi mamah baba baxan ta6a yimasa biyayya ba nidai bana san shi yanxu

Dake iyayan nan ne masu San ‘ya’ya nan suka hau lallashinta da cewa gobe xasu aika masa da sadakinsa basai ma yaxo bah

Nan hankalin XEE ya kwanta

Takira SAILUBAH take gaya mata yanda tayi da iyayan nata

SAILUBAH Tace Wlhi banso rabuwarku bah dakun sa santa kanku dai da yafi

XEE tajah tsaki Tace Wlhi Sam SAILUBAH bakiyi bah

Da Kinsan xafi da ra’da’din da nakeji araina da baki CE haka ba

Washe gari misalin qarfe biyu ne suke da lectures

Dan haka RAMADAN ya biyoma Auntyn nasa

Ta kallesa da kyau Tace baxan iya xuwa bah

Yace Amma gaki garau mexai hanaki xuwa 

Tace ni nasan abinda nake ji

Yace Auntyna akwai ranar da xaki nemi karatun nan ido rufe Ki rasa shi

Me yasa bakya san karatu ne Auntyna. yana da amfani fa. Wannan CE damarki idan kika bari takubce miki ya wucceki kenan har abada

Duk da in san karatu irin na Aunty XEE tafiki

Amma da antashi magana sai kice wai aibake ka’dai bace kike qin karatun

Ta galla mai harara. Cikin raini tace wai in tambayeka man

RAMADAN ya faketa da ido. Taci gaba da fa’din

Ni da kai waye babba

Yace ke

Tace meyasa kake sani agaba da fa’da sai kace Kaine Babban nice qanwar

Yace Auntyna kin kasa ganewa Sam.

Shi karatu idan yaxo gareka kamashi kake da kyau dan kai kake da cin moriyarsa. Ina guje miki ranar da xakiyi Aure kisami Miji me in barin Matarsa fita karatu. Ya hanaki cigaba alokacin dake kike ganin dacewar hakan

Tace na rigada nagama tsarama kaina rayuwar aurena. Insha Allah xata xomin yanda ya dace

Yace koh

Tace kwarai

Yace amma inaji ajikina baxaki samu yanda kikeso ba

Ta galla mai wata muguwar harara tace insha Allah xan samu fiye da yanda nake so mugu kawai

Kaga kaje kawai karka tsaya cikani da surutu ‘dan rainin hankali kawai. Ta qarashe da nuna 6acin ranta

Yayi Murmushi Yace toh shikenan Allah yabaki lpy Auntyna saina dawo 

Har yakai kofah Tace RAMADAN Yace na’am.

Taqara harararsa Tace kayi kyau Sosai. Tafa’da batare da tasaki fuskarta ba.

Yadawo gareta ya kama hannunta da shafa goshinta. Ba xafi agoshin Yace Allah yabaki lafiya Auntyna kema kinkyau Sosai

Tace kaci abinci ko Ya’daga mata kai alamar eh kana ya mata kiss a hannu ya fitta yana cewa natafi

Tabishi da kallo tana jin da’din qamshinsa.

RAMADAN yana futa bai da’de ba Abbas ya yaxo gidan

Da sauri  SAILUBAH takeyin shiri burinta taje taga munin Abbas ‘din da RAMADAN yace

Aiko bayan sun gaisa  ta qura masa ido……..

Eh Gaskiya ne

shi baqine bai cika kyau ba. Kuma da gaske yana da hakwara Amma basu sashi muni bah. Yanda tadinga tunanin xata gansa abin bai kai haka ba. Dan yana kyansa daidai gwargwado

Amma taji aranta Sam bata sanshi dan maganar  gaskiya RAMADAN yayi nasarai jefa mata qiyayyarsa

Yace ya kikayi shuru haka kina kallona

Tace hmm ina takaicin abinda xan gaya maka ne

Yace duk abinda xai futo daga bakinki baxai ta6a xama takaici agareni bah

Tace ina da mijin Aure na…….

Da sauri ya kalleta cikin wani hali Yace maganar gaskiya kike gayamin dan…….

Ta katse shi da fa’din. Baxan maka qarya ba

Yayi shuru cikin wani yanayi narashin jin da’di

Can Yace toh Allah ya ha’dani dame kamarki ina barin nan

Tace ina maka fatan samun wacce tafini

Yace Nagode

Haka tana kallo ya juya motarsa yabar harabar gidan nasu

Tana shiga ‘dakin Kakah  kiran XEE ya shigo wayarta

Tace ya akayine XEE

Daga can XEE Tace hmm Ki saurari xuwana Tace Allah ya kawoki ta ajiye wayan

Kakah Tace yadai jikin naki Tace da sauqi. Tace Toh Madallah

Dama inasan cin tuwan dawa ne miyar ku6ewa. SAILUBAH tafa’di hakan cikin marairai cewa

Kakah Tace toh ai sai ayishi yau

Kusan qarfe shidda da rabi 6:30pm XEE taxo gidan nasu

Tace qawata ina cikin wani hali

SAILUBAH Tace ai in baki shiga ba a tambayeki dan rabuwarki da Surajo lokaci ‘daya ba abubane wanda xai barki haka cikin Sauqi

Tace Kin san Allah na manta da wani Surajo dan nariga da nacireshi kwata kwata daga raina

Ni damuwata itace KHAMIS

Wayyo Allah na  SAILUBAH yau yarannan ya rikitani

Ya jefamin sanshi araina lokaci ‘daya

ashe dama duk wannan burgenin da Nake cewa yana yimin Ashe na fara sanshi ne dama haka so yake shiga xuciyar mutum farat ‘daya

Wayyo ni XEE yaxanyi dasan Wanda na girma qaramin yaro

Saiga hawaye ya xubo mata

Cikin kuka tacigaba da fa’din watoh nafito daga department ‘dinmu ‘daxo ina tafiya ahankali dan wata gajiyace ta kamani lokaci ‘daya

Ban kalli gabana Sosai ba. basai kawai nayi tuntu6e ba. Nayi taga taga xan fa’di.

Sai gashi ya yanko kwana……

Cikin sauri ya kama hannuna da janyoni  jikinsa.

SAILUBAH Kaina ya sauka a qijinsa

SAILUBAH na shaqi qamshinsa

SAILUBAH saida xuciyata tabuga hankalina ya tashi dan jin wani fitinannan filing daya kusantoni

Sunkwi da kanta XEE tayi

Tayi shuru agun hawaye yana cigaba da xuba mata

Kana ta’dago ta kalli SAILUBAH da tasaki baki ido hanci tana kallanta

Tace wlhi jinayi dama in dauwama a haka a qirjinsa dan jin yanda qamshinsa yake shiga hancina

Daga nan saime….. SAILUBAH Tafa’da cikin buqata hankali tashe

XEE tajah numfashi Tace daga nan sai yayi saurin sakeni cikin ‘dan nuna tsoro Yace am sorry Aunty XEE nayi abinda bai dace bah dan Allah kayi hakuri

Nayi shuru ina kallansa

Ya marairaice tamkar xaiyi kuka kamar yanda RAMADAN yake miki inya miki lefi. yaci gaba da fa’din. Xan shiga damuwa idan bakiyi magana bah

Nace hmm karka damu Bakomai bakayi abinda bai dace ba. Daka barni ai dana sha qasa Qanina

Yace Yauwa dama naxo induba ko kin fitone. Mutafi in saukeki agida sai kuma naga RAMADAN Yace min kina fitowa yanama Cikin motar ma

Nace toh muje

Kinsan Koda muka shiga motar sai Satar kallansa nake. Yayinda shi kuma ya sake sunata hira da RAMADAN

Ahaka suka saukeni suka kaqara gabah

Ayanxu dai haka Wlhi SAILUBAH damuwata ‘daya shine inga KHAMIS ko hankalina xai kwanta

SAILUBAH ta galla mata harara Tace wai ina hankalinki ya tafine.

Ya xaki SO qaramin yaro dan xubar da aji

Yanxu ke kanki bakiji wani iri da kunyar  gayamin da kikayi ba

Kalleki mace har mace Amma kirasa wanda xai burkita miki kwanya sai KHAMIS qaramin yaro

Kina wani maganar ya rungumeki ni runguma nawa RAMADAN yayi min akan hakan

Kin san ta6a hannuna agun RAMADAN  bakomai bane

Ya riga da ya sabarmin da hakan

Idan kuka nake rungumata yake yana lallashi inyi shuru. Haka idan shi yana cikin damuwa kwantar da kansa yake ya shagwa6e tamkar jariri in lallashi

Agabanki yasha yimin kiss a kumatu a hannu Amma ni meyasa banji san shi ba

Eh idan ya ta6ani inajin xirrrr Amma ban ‘dauki hakan a matsayin Komai ba dan dama bansa wani abu araina bah

Kawai kinbi shshashar xuciyarki kinfa’da soyayyar qaramin yaro waima KHAMIS.

Tsaki XEE taja cikin takaicinta Tace hmm to dama ke me xakiji Bayan ba sanin soyayyar ki kayi ba

Sam bakisan miye soyayya bah

Kina maganar na kamu da soyayyar qaramin yaro ai bani na halicci xuciyata bah

Inasan KHAMIS kuma Wlhi in ban Auresa ba baxan ta6a yin Aure ba kinji na rantse

Cikin Baqin ciki hawaye ya xuboma SAILUBAH Tace ai sai kije ki nemama kanki mafuta. Tafa’da da Takaici

XEE takalleta Tace ki fahimce mana. Wlhi SO matsifane so balaqi ne. Shuru SAILUBAH tayi mata

Haka XEE taqarashi kukunta ta hakura tatafi dan SAILUBAH Sosai takasa fahimtarta.

Koda RAMADAN yaxo gun SAILUBAH bai sameta da warwala ba sai yayi tunanin ko dan rikicinsu na ‘daxo ne. Yace waya ta6amin Auntyna. Taqi kulashi

Cikin kalar tausayi Yace Wlhi in bakiyimin magana bah Xanyi kuka

Ta kallesa. Dariya ta kamata. Toh kayi mana.

Yayi Murmushi ai kuma ya wucce tunda kinyi maganar harda dariya pls meyake damunki. Ko wancan mutumin yaxo ne kuma kinji kina sansa haka a munin nasa

Ta 6ata fuska cikin shagwa6a Tace hmm yaxo Amma Nace mishi inada mijin Aurena

Cikin farin ciki Yace Allah Auntyna

Tace Wlhi

Yabata kiss a hannu Yace Yauwa gwara da kikace mai haka

Da xakiban dama da kin samu Wanda ya dace da ra’ayinki.

Tace kamar ya

Yaje feta da kallan nan nasa. Nanko jikinta ya mutu ta rikice mai

Dama haka yakeso danya samu yanda yake so

Hannunsa cikin nata idan shi ma cikin nata Yace so nake duk wani saurayin da kikayi Ki fa’damin dan in tayaki gano Wanda ya dace dake da kuma ra’ayinki

Ya rigada ya gama kashe mata jiki saita ‘daga mai kai kawai alamar toh

Yayi Murmushi da ficcewa daga ‘dakin dan yasan hirar tasu taqare tunda jikinta ya mutu

Shuru SAILUBAH tayi ta bishi da kallo harya fittan

Kana ta kwanta tana tunaninsa

👯👯👯

Sun ha’du Su uku kamar yanda suka saba dan xuwa club. Amma sai FAWAS Yace suje gidansu  Aymana budurwarsa

Nan sukaje

tafitoh cikin nutsuwa. Yarinya ‘danya shakaf.

Join our WhatsApp Group Here

Series Navigation<< Samarin Bana Chapter 2Smarin Bana Chapter 4 >>
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *